****
*K*ukan da take ta tsagaita dashi sannan tace umma babu abinda nayi mashi kuma shima baiyi man komai ba, kawai dai ya ɗauko kuɗin nan ya bani ne,
Umma tace to ai so nake inji abinda kikai mashi ne, tunda nidai banga kin fita da wani abun siyarwa ba, raihana tace wallahi umma ki yadda dani babu wani abunda mukai dashi, zulaihat tace man yace yana so na, shine daya kawoni gida ya bani kuma yace zaima canja man waya ,
Ajiyar zuciya umma tayi sannan tace to kidaiyi hankali dan idan anga mace na zawarci kowa kallon sakara marar kamun kai yake mata, kinga dai kin taɓa aure hukuncin zina ga wanda ya taɓa aure kisa ne, idan kuma kikaje kika ɓoye kikayi Allah ubangiji yana kallonki zai linka maki nauhin wahala wanda yafi wannan,
Raihana tace insha Allah umma bama zanyi ba wallahi, umma taci gaba da cewa kuma ga cututtuka sunyi yawa a duniya, kinga idan kikayi sakaci aka cuceki kinfa tashi aiki zaki rasa mai aurenki ne kiyi ta kanki kuma ki nema ma rayuwarkk mafita,
Raihana tace insha Allah, zama umma tayi sannan ta jawo kwallin kuɗin ciki ta fiddo ta fara irgawa, hankalin umma dai ya ƙara tashi ganin kuɗi zunzurutu har dubu ɗari biyar, umma tace raihana kinga yawan kuɗin tunda nake a duniya wallahi ban taɓa ganin ko dubu hamsin ba a hannuna, lallai idan dai da gaske yake kawai kice mashi ya turo,
Raihana tace insha Allah , haka dai umma taci gaba dayi ma raihana nasiha tare da nuna mata illar da zina take haifarwa da kuma masifar da mutum zai fuska idan yana aikata ta, haka dai sukaci gaba da fira jefi jefi , har bacci yayi gaba da raihana, umma taji tana ta magana ita ɗaya babu amsa, tace au ashe kinyi bacci ina ta surutu kamar radio, itama kwanciya tayi, tana tunani iri iri a ranta har baccin itama ya tafi da ita........................,
****
Da safe bayan raihana ta tashi tayi dan abunda zatayi, sannan tace ma umma bari inje gidan gwaggo in kwaso kayana, umma tace mata to, raihana tace umma ko ki bani cikin kuɗin nan inkai ma gwaggo ko 2k ne,?"" umma tace to bari in baki, inda ta ajiye kuɗin taje ta ɗauko, ta bata, raihana ta karɓa sannan ta fita daga gidan,
A gidan gwaggo raihana tayi sallama gwaggo tana shara tace ɗiyar nan ina kika kwana?"" ba tare data amsa sallamar ba, raihana tace ai mun dawo nan unguwar a gidan daka tsalle muka kama haya, gwaggo tace to ai najiki shiru ne, raihana tace kuma banyi dabara ba nace idan kinji shiru na wuce gda, gwaggo tace gaskiya,
Raihana gaishe da gwaggo tayi bayan sun gama gaisawa ne, raihana ta bata kuɗin tace umma tace a baki, gwaggo tace na miye?"" raihana tace wai kawo mata akayi shine tace bara ta kasafeki, gwaggo ta ansa sai godiya take, raihana ta shiga ta tattaro kayanta sannan tayi ma gwaggo sai anjima ta fita daga gidan,
tana fitowa taga badiyya wato uwar ɗakinta da sukai faɗa wanda mijinta yakai raihana asibiti lokacin da tayi rashin lafiya, raihana na ganinta ta cika fuska ta ɗauke kanta, dan ta tsani badiyya tun lokacin da taxo har gidansu tayi mata wulaƙanci,
Dariya badiyya sannan tace daga baya kenan anyi sadaka da karuwa, aikin banza mijina dai yafi ƙarfinki haka za"a balbaɗe ba"a gidan ango ba"agidan amarya, keda mijina kuwa sai gani sai hange,
Tsaki raihana tayi sannan ta juyo tace, aikin banza karw da gudun layya, aike ba namiji kike aure ba, kuma baki cika mace ba da har mijinki zaiga mace yaji yana santa a ranshi, baki iya kula da miji ba shi yasa har yaga wata yaji ta mashi, toni idan baki sani ba ki sani idan kuma kin sani ki ƙara sani, mijinki yaman datti sosai na farko baya wanke baki bare insa ran idan na aureshi zanji daɗi idan ya sumabaceni, baya wanka shi yasa idan ya tun karo mutane suke kauda kansu dan wari yake,
kiji ki tsaftace shi sai kixo kiyi kishinshi, banza wanda baki ajiye komai ba sai shegen kishi da ƙazanta,
badiyya tace Ey naji dai kuma babu ke ba mijina har abadan duniya, raihana tace a banza anma kare wanka, na gaya naki lalurarshi, amma idan ya gyara yazo yabi layin *zawarawa* tana faɗin haka tayi gaba, badiyya ta tsaya a wurin sai zage zage take, raihana dai ba ta sake bin ta kanta ba,
*****
bayan sallahr magrib zulaiha tayo ma raihana waya cewa ga k"b nan zaizo ashe jiya bai karɓi number inta ba, raihana tace E cewa yayi ya raina wayana, dariya zulaiha tayi sannan tace k"b kenan ai shi komai nashi yasha banban, raihana tace shin nidai ina jiran zuwanshi, zulaiha tace to, sallama sukai da juna sannan raihana ta kash wayarta,,,,,
Wayar ta ajiye sannan tace bara taje tayi wanka, umma tace wanka kuma?"" raihana tace E umma baƙo zanyi, umma tace eh lallai a bada himm, dariya raihana tayi sannan ta fita ta zuba ruwa a rober ta ɗauka ta nufi bayi,
bayan ta fito daga wanka sallah isha"i tayi bayan ta gama ta shiga shirin tarar baƙonta,
shiri tayi cikin baƙar rigar da farida ta bata, tayi kyau sosai abinka da farar kala sai raihana ta fito kamar wata balarabiya, ta haɗu iyakar haɗuwa, dan idan raihana ta samu hutu gaskiya zaiyi wuya ka ganta kace tasan wani yare waishi hausa, kana ganin ta labarci zaka fara mata dan tafi kama da larabawa,
ta gama shirinta tsaffa ta koma ta zauna tana jiran zuwan rabin ranta, wato k"b,
wai waye wannan kabir ɗin?"" kabir sangartace ne ya taso ne babu kwaɓa babu kyara a wurin iyayenshi duk abinda yayi mai kyau ne, kuma k"b bayajin magana, yana da "yan canjinshi a hannunshi saboda haka baya san zama da mace sama da ɗaya, dan bature ne sosai, amma kwallon ɗan iska ne, zai iya kashe ma mace kuɗi dan kawai ya biya buƙatarshi ya wuce wurin, dan idan ya saka mace ƙahon zuƙa sai ya zuƙeta sannan zai samu kwanciyar hankali ,
k"b matarshi ɗaya itama bada niyyar aurw yaje ba, iskanci yakai shi iyayenta suka riƙe mashi wuya gam saida ya aureta, hmm k"b ya kware wajen iya yaudara, tantirin ɗan iskane na bugawa a jarida, duk yanda zan faɗa maku halinshi baza ku gane ba amma ku bari muje cikin labarin tarayyar shi da raihana muji,
wai ance raihana taxo, raihana cikin zaƙuwa tace jekace ina zuwa, ta miƙe da sauri jikinta sai karma yake,
umma ta kalleta tayi tsaki sannan tace ki daina wannan rawar kan, ki matse ajinki sosai, kuma ki daina yawan dariya dan dariya ta zubda mutimci idan tayi yawa sosai, kuma tunda ance ana kiranki sai kibi a hankali kuma ki bari yaron ya tafi idan ya daɗe saiko fita, , raihana tace to, umma taci gaba da cewa bari ganin ya ɗauki kuɗi haka da yawa ya baki idan kika saki jiki yana iya tadaki aiki ya barki da raba, raihana ta jinjina kanta alamar gamsuwa, sannan umma tace jeki,
raihana ta fito jiki a saɓule, tayo waje, inda ya ajiyeta a jiya a wurin yake ya haske ƙofar zaurensu da hasken fitalar motarshi yana cikin motar bai fito ba,
Tafiya raihana taci gaba dayi, shi kuma yana cikin mota yana hangenta, hannushi ɗaya ya riƙe sitiyarin mota ɗaya kuma ya riƙe haɓarshi, idanuwanshi ya sake warewa ya ƙura ma raihana ido,
ajiyar zuciya ya sauke sannan yace ikon Allah "yar yarinya ƙarama da ita, amma tana da haluttu masu fizgar hankali, murmushi yayi da gefen bakinshi sannan yace wannan ai shine ɗan ƙaramin gari da arxikin man fetur,
A daidai lokacin da raihana ta iso, sallama tayi mashi shi kuma sauke glass ɗin motar yayi, sannan yace zagayo mana, raihana tace ah ah kadai fito mu koma ƙofar gida, k"b yace ah ah, ai bana iya zama zafi nake ji, ki shigo , raihana tace nidai ah ah, kwaikwayon maganarta yayi cikin sigar yaudara shima yace nidai shigo , yanda yayi abun ya bawa raihana dariya don haka tayi murmushi, yace haba zagayo don Allah in dan ganki ina da meeting ne, lokacin daya kai kallonshi ga agogon hannunshi,
uhum raihana tace sannan ta zagaya ta buɗe gaban mota ta shiga,ta zauna, yace rufo man mota hajiya, raihana tace ai inaga mu barshi haka, girgiza kanshi yayi sannan yayi mata wani malalacin kallon daya sa jikinta mutuwa, murmushi yayi sannan daga inda yake ya duƙo don jawo ƙofar motar ya rufe,
bayan ya rufe ya dawo da kallonshi kan raihana, yace to komu fa?"" raihana tayi shiru, kallonta yayi yana cije leɓonshi na ƙasa, wani irin kallo kallo yake ma raihana wanda yasa duk taji ta takura,
Fuskarshi tana fuskantar gabanshi yace ma raihana kallanni, ba tare daya kalli inda raihana take ba, raihana bata kalleshi ba, yace dake nake magana, juyo wa raihana tayi taga hankalinshi ba kanta yake ba, ta sake ɗauke kanta, yace miyasa baki san kallona ne?"" ban haɗuba??"" ya ƙarasa maganar da muryar dake sa mutum yaji kamar baya da lafiya,
kallonshi raihana tayi ido cikin ido, yace mata jiya ina ta tunaninki kila ma ke kinyi baccinki kinma wani manta dani, raihana tace a,a, nima ina tunaninka sosai, sannan taci gaba da cewa jiya ashe haka ka bani kuɗi masu yawa, miyasa haka?"" murmushi yayi lokacin da yake sassauta ganin idanuwanshi wanda idan nice zan kira kallon da zaki gane kurenki,
k"b yace ai babu komai, raihana tace to ina godiya, yace bama sai kin gode ba, ni bana san kina wani wahalar da kanki wurin kin gode kin gode, haba, raihana tace kaiko ayi ma mutum alkairi bazai gode ba?"" dariya k"b yayi sannan yace gode ma Allah danshi ne ya haɗamu,
raihana tace Alhamdulillahi ala kulli halin ai, yace yawwa, sunyi ɗan fira sannan yace mata zai tafi, raihana tace to, yace muje zan baki saƙo, raihana tace to, fita sukai daga cikin motar su dukansu,
bayan motar suka zagaya ya buɗe but in motar ya fiddo mata wata ƙatuwar jikka, wanda shima kanshi nishi yake ya ajiyeta a ƙasa, sannan ya rufe, zagayawa yayi bayan motar ya buɗe ya ɗauko wata ƙaramar leda ya miƙa mata, yace ga wayarki nan, raihana hannj biyu tasa ta karɓa tare da godiya, kusa da ita ya matsa sosai har tana iya juyo gumin jikinji, jikin raihana ya fara ƙarma, kallonta yayi sannan yace miye?"" tace ba komai gira ɗaya ya ɗaga tare da taɓe baki baki yace uhum, jakar ya nuna mafa yace ga kayan da zakiyi amfani dashi wurin bikin ƙawarki,
ni mutum ne ma"abocin san ado da kwalli idan ina san mace ina so inga tafi kowa, in baki misali?"" raihana ta ɗaga kanta alamar E, yace kinsan fulawa wanda ake ado da ita a gida?"" raihana tace E yace idan ba"a bata ruwa ya takeyi?"" raihana tace bushewa take ta lalace, yace yawwa idan akayi mata ban ruwa ya takeyi?"" raihana tace kyau takeyi kuma ta burge kowa, yace aha, to haka nake so ki zama, duƙowa yayi kusa da ita daidai saitin bakinta ya sumbace ta, { kiss } wanda haka yasa raihana taji ƙafafuwanta basu iya ɗaukarta, shi kuma yaci gaba da cewa zan mayar dake abun ado na dan mke ɗin ta dabance, ya kula da halin da raihana take ciki dariya yayi sannan yace maza jeki gida, shi kuma yayi gaba yaje ya shige motarshi yaja yayi gaba, yabar raihana tsaye a wurin ,
yana shiga mota ya fara dariya yace kam daga sumba yarinya ta ɗauke wutar nepa?"" dariya ya sakeyi sannan yace lallai yarinya kina da aiki baki san k"b ba, dariya ya sakeyi sannan ya daki sitiyarin motarshi yace hmm ba laifinki bane an daɗe ba"a gamu ba, leɓonshi na ƙasa ya cije, sannan ya ƙara volume in waƙar da yake ji yana binta cikin nishaɗi,
ita kuma raihana tana ganin ya tafi yara ta kira suka ɗaukar mata kayan sukayi cikin gda,
umma taga raihana da kaya ɗingim ɗingim tace wannan kuma fa""?"" raihana tace shine ya kawo man wai inyi amfani dasu wurin bikin zulaihat umma tace ikon Allah kawo nan mu gani, jakar suka buɗe suka shiga duba kayan umma tace lallai anan dukiya tayi kuka, raihana ta nuna mata wayar, umma tace wai wai wai, wannan waya raihana da gani ta haɗu, itama kuɗi da yawa aka siya, raihana tace nidai ban sani ba, umma tace to idan dai ya sake dawowa kice mashi ya turo kada yaxo yayi ta maki asara amma dubu gomar da zai baya sadaki kiga ya kasa , bawai rashin su ba, ah ah, zai iya kashe maki miliyan dan ya samu abinda ransa yake so, amma bai iya bada dubj biyar a ɗaura maki aure dashi,
Kinga dai ke zawara ce, duk wanda yaxo wurin ki sau ɗaya so biyu to ki fara mashi maganar aure idan da gaske yake zai turo idan da yaudara yaxo bazaki ƙara ganinshi ba, raihana tace to insha Allah zan mashi magana,
umma tace to dadai yafi, wayar raihana ta fara ruri ta duba dan ganin mai kiranta, baƙuwar number ce, ɗauka tayi sannan ta kara a kunnenta, hello raihana farida ce, raihana tace in sani ƙawata kun dawo kenan?"" farida tace Allah ya yadda, raihana tace yaushe kuka dawo?"" tace jiya, raihana tace masha Allah, Allah yasa ibadar da kukai karɓaɓɓiya tace amin sai mun haɗu bikin farida raihana tace Allah yasa rayuwarmu takai, farida tace amin sannan raihana tayi mata godiyar abunda fa bata, farida tace bata san wannan abun don Allah, haka dai suka ɗanyi fira daga baya sukai ma juna saida safe,
umma tace sun dawo kenan?"" raihana tace Eh umma tace Allah ya cidamu baki ɗayanmu raihana tabi da amin,
sabuwar wayar da k"b ya kawo mata taji ta fara kururuwa, da sauri raihana ta ɗauko ta, dan da chargynta inji shi kuna ya saka mata sabon layi, ɗauka raihana tayi sallama bayan ya amsa, tayi mashi fatan yaje gida lafiya?"" yace lafiya, raihana ta sake mashi godiya yace no wahala, sannan ya sheda mata sai jibi idan Allah ya wurin bikin zulaihat , tace Allah a bamu aro rayuwa, haka dai sukayi ɗan fira daga baya sukai ma juna saida safe ,,,,,,,,
kwanciya tayi dan huta ma ranta, daga kwance suna ɗan fira da umma su duk biyun har bacci ya ɗauke su,
******
*Y*au juma"a, kuma yaune juma"ar da ya kama bikin zulaihat, dan haka raihana tana iya bakin ƙoƙarin wajen ganin ita ta fito dan tana so idan taje a wurin bsta da tsara, shiri take sosai, dan haka nima bari inje in samu chargy dan bama bari a bamu labari ba,
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*Page* 2⃣7⃣
*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*MEELAT MUSA* 🌹
*Wannan page naku ne masoyan wannan labarin a duk inda kuke a faɗin duniya, ina maku fatan alkairi, kuma ina alfahiri daku, fatan alkairi a gareku baki ɗaya, Allah ya ƙara ba kowa zaman lafiya da mijinta, wanda kuma basu da aure Allah ya basu mazaje na gari ubangiji yayi mana zaɓi dan matsayin fiyayen halitta S. A. W, ameen,*
*Asmeenat xeeyan ina maraicinki a kullum kina raina , alkairi ya taddaki har sokotton shehu*
*Hafsat Isa Mamman, godiya mai tarin yawa dan kina nuna mana godiya sosai kuma mun gode, muna maki fatan alkairi tare da duk "yan babban birnin katsina ta dikko ɗakin ƙara, kunya gareku badai tsoro ba,*
***
*S*hiri mai kyau raihana tayi , komai na jikinta da ta saka mai kyau da tsada ne, ta gama shirinta casss, sannan ta fito tayi ma umma sai ta dawo, umma tayi mata fatan alkairi tare da ja mata kunne ta kula da kanta, godiya raihana tayi sannan ta fice daga gidan,
Tana fitowa ta fara ƙusowa cikin unguwa, bakin titi take ƙoƙarin zuwa dan samun abin hawa, tana tafiya hankalinta yana wani tunanin daban, haka tabi ta gefensu ta raɓa, suka fara aikin nasu, zawara uwar san banza, an ɗaurayu pha, kuma wa"aka dafe ne?"" raihana dai batayi masu magana ba taci gaba da tafiyarta, daga can wani ya ɗago murya da ƙarfi yace kinfa yi kyau babu ƙarya, banda kika sa girman kai ai dana zo na kwashe ki, gaba ɗaya wurin suka ɗauki dariya, raihana dai bata juyo ba haka ta wuce tabar sakarkari,
Wani yace kai yarinyar can fa bahba shegiyace, ya fara nuna yanda raihana take tafiya, yace kai amma fa aminu yayi asara wallahi, ai mai kyau haƙuri ake dashi idan kana ganin mai kyau ko ba komai kaji natsuwa, wani yace shegiya kaji turarenta?"" ni wallahi ma zuwa zanyi inba aminu shawara ya dawo layi,
Wani yace yo Allah na tubo idan ta koma gidan Aminu aisai na tsine mata albarka, kai dan bakaji wulaƙanci da yake mata ba, wani yace ai aminu kare ne mara bindi, da Allah ku saurara kuji, shi wulaƙanci babu daɗi gaskiya mu daina janta, amma fa ƙarshen wulaƙanci aminu ya wulaƙanta yarinyar can, wai barba kasan abinda yake cewa?"" gaba ɗayansu suka ce ah ah, yace to ku tsaya kuji abinda uwarsa tace,
Ita maman su aminu ai kunsan aminu yana santa kamar ya mutu ko?"" to uwarshi taje ta tsare aka saketa, ita kuma matar uban tana zuwa tana faɗa masu halin da ita raihanar take ciki, ashe uwar daɗi takeji, ita gwaggo har gaya masu take raihana tana wankau tana surfe kaɗin taliya sai ta yini ta kwana baaci abinci ba, duk abinda raihana tayi sai ita gwaggon taje ta faɗa masu, shine maman aminu tace a barta wai idan ta gurzu da zawarci sai aminu ya mayar da ita, idan ya mayar da ita duk abinda yayi mata wai dole zata haƙura,
Yace aini inasan inje in bata shawara amma yarinyarce bata da fuska kullum fuskarta tana nuni bata wasa da yaro, dariya suka sake sheƙewa, daga nan zancen nasu ya sake salo wasu na cewa raihana irin matan nan ne masu wahalar samu kowa dai yana kiyasta irin ni"imar da Allah yayi mata, labarin nasu nidai yafi ƙarfin ƙwalwata kuxo muje gidan biki,...............
Gidan ya ɗauki harami duk wanda ka gani yana cikin farin ciki kowa yasha gayunshi, a gefe ɗaya kuma zulaihat amarya ce da ƙawayen ta zawarawa da masu aure da wanda Allah bai basu mazan aurw ba, sun haɗu a wurin kowa da abinda yake faɗa, irin dai nasihar nan tasu ta zawarawa ,
Wata ƙawar zulaihat ce tace to nidai abinda nake so na faɗa maki shine, kindai ji rayuwa, kuma yanxun kinsan mahimmacin aure da rashin aure kina nan sai abinda aka dafa aka baki, daki ƙoshi da kada ki ƙoshi suma ƙannenki jira suke a basu, duk abinda kike dashi a gidan aure idan kika dawo zawarci ba bajeshi zakiyi kiyi amfani dashi ba, kaiwa za"ayi a ajiye sai kin tashi wani auren, a gado ɗaya zaku cakuɗa keda ƙannenki, duk abinda zakiyi baki da sirri a gabansu suna kallonki, kuma duk abinda kikai mai kyau ko kishirya haka dake zasuyi koyi, idan suma sunyi aure mijin yayi masu abu kaɗan zasuga gara su taho gida sai suce kema da akayi maki kaza da kaza gida kika dawo, to kinga yanxun sai ki gyara, babu yaji barw kija abinda za"a sake ki, dariya akai baki ɗaya ,
Sannan wata tace kin manta magana ɗaya , baki faɗa ba, a daidai lokacin da raihana tayi sallama, gaba ɗaya suka ɗauki shewa da iskanci,
gangarowa tayi ta iso wurinsu, kowa sai yabawa yake tare da dai irin abun nan namu na mata, zulaihat ce tayi dariya sanan tace kai raihana kinyi kyau , wallahi raihana tace na gode, wata daga gefe tace kai mai kyau da kyau yake inji baƙin jaki daya ga magon doki, gaskiya raihana kin haihu, murmushi tayi batayi magana ba, wata tace miye magon doki?"" wanda tayi maganar tace farin doki ne yasha gayu baƙin jaki yana ganin shi yayi magana kinsan ko a mutane idan kaga wanda yafika idan dai ba hassada kake ba dole ka yaba, zulaiha tace aike bakijin magana, raihana zauna kiji wa"azim *zawarawa*
suka ce muna jinki miye ta manta bata faɗa ba?"" tace to kuna surutu zan faɗa maku?"" raihana tace to kuyi shiru muji don Allah, shiru wurin yayi kamar irin abinda yaran suke cewa mutuwa ta ratsa da ba"ai shiru ba data ɗauka,
Mai maganar kana ganinta kasan batajin magana, kuma itama tasha zawarci ta har ta fefe, idanuwanta sun gama bushewa da rashin kunya,
Zulaihat nidai abinda zance maki shine, kinga nan dai duk ɗaya muke, dan haka munsan sal musan tal, nidai nasan gidan nan zaman haƙuri kikai, kuma haka zaki hau saman katifa kiyi ta juye juye, sanyi dare dana asuba ya hanaki bacci, ama idan kina gidanki mijinki ya rungumeki kiji ɗumin jikinshi kema yaji naki, to abundai duk na temakekeniya ne, idan kuma kinji yunwa abinci biyu zakici gaba ɗaya suka sheƙe da dariya hehehehhhhhh ni dariyarsu ma ta hana inji wane irin abinci zataci so biyu?""
Farida ce tayi sallama ta shigo, raihana da sauri ta miƙe taje tayi mata Oyoyo sannan suka zo suka zauna, farida tace mi ake tattaunawa ne?"" raihana tace nasiha ake ma zulaihat farida tace ke kinyi taki?"" raihana tace aini zawarcin kawai nake amma banyi rayuwar auren ba, farida tace to ku saurara in faɗa maku,
shiru suka sakeyi, farida tace zulaihat nidai zawarci aure nayi, kuma zaman gida ɗan lokaci nayi, amma na gane kurena, kinga na saba kwanciya da mai gida a tare muke kwana ya rungumeni amma ranar dana dawo gida bacci ya gagareni, sannan kuma idan ina kwance na tuno irin abubuwan da suke faru tsakaninmu dan gane da rayuwar aure wani lokaci bana iya bacci saidai in rungumi pillow inyi ta kuka, kuma na gode ma Allah ubangiji ya tsarenk da bana zina, da tuni idan naji buƙatuwa waje zanje a biya mani, don haka zulaihat kiyi haƙuri kiyi zaman ki, kafin ma kiji kina buƙata namiji ya nemeki, ki rufa ma kanki asiri wallahi kiyi zamanki kada ki kuskura baki riƙe mijinki ba,
kije da sabon salo kici kisha tare da mijinki kiyi wanka dashi ki kyautata mashi kiyi mashi biyayya, duk abinda ya kawo ki tattala mashi kayanshi ki kiyaye duk abinda zai ɓata mashi rai duk abinda zaisa shi farin ciki kiyi mashi, ki ɓoye sirrinku ki kuma kiyayi duk ƙawar da zata zo ta baki shawarar banza, kiyi sabta kiyi ado idan mijinki zai fita zulaihat bishi kiyi mashi rakiya tare da addu"oe masu dadi kuma duk abinda ya kawo maki kiyi gadiya kada ki kuskura ki raina ko kiga gajiyawarshi nuna mashi kullum yana ƙoƙari sannan kuma nuna mashi duk duniya ke kinfi ko wace mace sa"ar miji ,
farida ta lunfasa sannan tace ko ya kika ce raihana?"" raihana tace gaskiya wannan batun naki raihana tace nima bari ince wani abu,
Matan bahaushe gaskiya muma muna da tamu matsalar sai mu duba matan yare mu gani?"" sunfimu kula da mazansu , waimu matan malam bahaushe bamu ajiye komai ba sai girman kai da iyayi, ke kinaji da aji kada kiyi ma miji biyayya wai gani kike zibar da girma ne, to gaskiya sai mun aje girman kai idan har muna so mu gyara aljannarmu, zan shi aure ibada ne, kuma duk abinda kikai a gidan aurenki ladace ake rubuta maki, ki kalli mijinki kiyi mashi murmushi idan yaji daɗi lada ne, amma idan kikayi ma wani ƙaton banza zunubi ne,
kiyi gayu kisa turare mijinki ya gani idan yaji natsuwa lada ce, amma idan kince zawarci kiyi wanka kibi titi wani ma kallon banza baki isheshi ba, bare kisa ran samun wata lada, don haka shi gidan aure gaba ɗaya anan kike nema ma kanki wuta kuma anan kike samun aljanna, idan kiyi biyayya a gidan aurenki to lallai zaki sama ma kanki tsira duniya da lahira,
Wata tace to mun gode amma ni ina so inyi wata magana amma nake ganin kamar wuri ya ƙure, amma bari in baku satar ansa mata,
Zulaihat wannan sirrine ni zan faɗa maki amma wasu matan girman kai baya barinsu, zulaihat a gidanki ina so mijinki kafin ya nemeki a kwanciyar aure nuna mashi ke kina buƙarta shi, ki nemi mijinki ba kiyi kwance kullum sai yaxo ya nemeki wannan sirrin idan kika haɗa da tsafta da gyara da kamshi, haƙiƙa ni na gaya maki maza suna san macen da take nemansu dan namiji ji yake shima yakai namiji har kina buƙatar kwanciya dashi, ki riƙe wannan sirrin ki kisa mijinki farin ciki kema sai Allah yasa kiyi farin ciki duniya da lahira {matan aure bance zawarawa ko wanda basu da aure}
To lamarin nasu babba ne, haka dai sukayi ta iskanci da magagganunsu, daga baya akaci aka sha, sannan aka ɗauki amarya zulaihat sai gidan mijinta,
Farida da mijinta ya siyama wata irin ƙatuwar mota, itama ta kwashi masu daga cikin masu kai amarya, ita kuma raihana a motar k"b suka tafi,
ankai amarya a gidan mijinta, sun ƙara mata nasiha, da shawarwari, daga baya kua kowa ya kama gabanshi,
Raihana k"b ya ɗaukota suka nufi gida, a ƙofar gidansu yayi parking, raihana tayi mashi godiya zata fita, ya riƙo hannunta, juyowa tayi ta kalleshi sannan tace lafiya?""" yace ku haka ake biki baku bamu abinci a wurin bikinku, raihana tace ai bansan bakaci ba, yace to bani yana maganar ne cikin sigar iskanci ,raihana tace to bara inje in kawo maka a gida?"" yace ah ah saidai muje mu samu abinci, raihana tace nidai a , a, k"b yace to miye?"" nine fa?" ki yadda dani nine zan aure ki ko kin daina sona ne?"""
raihana tace ina sanka yace to muje, a daidai lokacin daya tada mota, raihana tace dare fa yayi , yanxun 8:45pm kana gani k"b yace haba basar muje kawai hajiya ta, a lokacin daya fara tafiya da mota.....................
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*Page* 2⃣8⃣
*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*MEELAT MUSA* 🌹
*Alhamdulillah*
*****
*S*aida ya fara tafiya da motar sosai sannan yasa hannunshi ya riƙo hannun raihana ya haɗasu yana ɗan murzawa cikin wani irin salo,
Raihana hannunta ta janye wani iron kallo k"b yayi mata sannan yace miye haka?"" nine fa?"" wai miyasa naga kina wani babbasarwa ne?"" raihana tace haba aimu ba yara bane, tunda kana so na ina sanka shi kenan muyi aurenmu mana?""
Hannunshi na dama ya miƙa ya ɗan jawo raihana yace haba hajiyata"" kwantar da hankalinki saurin mi kike?"" so nake mu fahimci juna, raihana tace ai halin mutum baya fahimtuwa dole sai mun zauna tare dakai, idan naje gidanka na fahimceka, k"b yace to naji wannan ba damuwa bane, amma gidan da nake so na sakaki ne bam ƙarasa ginawa ba, raihana tace ai sai ka kama mana haya, idanuwa ya zaro sannan yace da ajina da komai?"" zan auri kyakyawar mace kamarki in sakaki a gidan haya ?"":
Raihana tace ba komai ai yanxun ma a gidan haya muke, k"b yace Allah ya sawaƙe, ai zan siya umma gida, raihana tace da ka siya mata gida kuɗin ai gara kawai kayi hidimar aurenmu, murmushi k"b yayi sannan a ranshi yace lallai yarinyar nan wato wahala zata bani, amma zanyi maganinki,
Parking yayi bai fita daga motar ba, yana yin parking wani ya taso yaxo wurinsu k"b ya faɗa mashi abinda yake so, yaje ya kawo mashi ya bashi kuɗin sannan suka yo gidan su raihana"""",
A ƙofar gidansu bayan ya tsaya ne, yace ma raihana mi kike so ne?"" tace bana san komai?"" yace toni ki tambayeni abinda nake so mana,,,""" raihana tace ai nasan kafi ƙarfin komai murmushi k"b yayi a yace niko duk abinda kike so zan maki, amma nasan ke idan ina san wani abu baza kiyi man ba,
Raihana tace haba miye duniya wanda bazan maka ba, k"b yace komai da komai?"" raihana tace sosai ma, k"b yace to shikenan zanga idan baki da rowa, raihana tace banda ita, amma raihana bata gane ko wace irin rowa k"b yake nufi ba, hhhhh wayyo,
K"b yace to na gode, raihana tace tom, ledar abincin ya ɗauko ya bata yace ga naki nima ga nawa, raihana tace to ngd, matsowa yayi kusa da ita, a daidai kumatunta yayi mata kiss sannan yace saida safe, raihana tace to, sannan ta fita ta shige gida,
K"b yace tou pha ita nan komai sai maganar aure maganar aure, hmmm da kabir kike magana, jan motarshi yayi ya ƙara ma tayarshi iska,.........,,
*****
*B*ayan bikin zulaihat da sati ɗaya, k"b ya sake dawowa gidansu raihana , bayan ta fito suka gaisa tace mashi k"b idan da gaske zaka aureni ka aiko don Allah, k"b yace raihana ina sanki kuma zan aureki amma kiyi haƙuri in gama ginin gidana can gidan yayi maku kaɗan ne,
amma kwantar da hankalinki zanzo neman aurenki kuma in bada sadaki shike nan sai hankalinki ya kwanta ko?"" raihana tace kai ɗayane zaka zo neman aure na?"" yace E idan nazo baga naki dangin ba, sai ayi magana shikenan ko?"" raihana ita dai bata gamsu da maganar nan ba, k"b ya lura da haka don haka yace ma raihana jekice ma umma zan shigo mu gaisa, raihana tace to,
bayan taje ta faɗa ma umma suka shiga tare suka gaisa, sannan yace ma umma zaizo neman auren raihana, umma taji daɗi kuma ta nuna farin cikin ta sosai, dan haka sai yaxo, daya tashi tafiya, haka ya yage bakin aljihu yayi ma umma yayyafin ruwan kuɗi, sannan ya tafi,
raihana ta fita tayi mashi rakiya, tare da godiya, jowata yayi jikinshi ya haɗe bakinshi da nata, har wani lokaci sannan ya saketa, raihana tace wai miyasa kake man haka ne?"" k"b yace saboda nine zan aureki, raihana tace idan kayi haƙuri ai dukana za"a baka ni, yace ai zaƙuwa ce, kinsan ina sanki da yawa raihana, murmushi tayi tama maijin daɗi a ranta ama a zuciyar k"b ƙarya yake baya santa burinshi kawai ya biya buƙatar shi yayi gaba,
Sunyi "yar firarsu daga baya k"b ya tafi, raihana ita gida ta koma, umma tana nuna mata kuɗin kuɗi masu yawa ne ya bata, umma tace to Allah dai ya warwaremana komai, raihana tace amin,
K"b kuma yana tafiya cewa yayi yarinya idan kinsan wata bakisan wata ba, sharrin kabir yawa ne dashi amma tunda kin matsa maganar aure zan turo , kuma zamu bada sadaki , idan anyi man maganar ɗaura aure nasan mafita,......
***
Ita kuma umma da safe haka taje ta faɗa ma gwaggo za"azo neman auren raihana, dan haka a faɗa ma yayunta dan suna da haƙƙi akanta, amma murrr gwaggo ta murje idon ta, tace idan dai sune zasu ɗaura mata aure saidai ta mutu zawara, umma tace duk miye yayi zafi?"" dama dan kada ace ban faɗa ba , na faɗa gwaggo tace ai sai kiji ki sanar da dangin ubanta, umma tace to ngd, sannan ta taso ta taho,
Umma taje ta samu yayun baba da ƙannenshi ta faɗa masu maganar zuwan masu san raihana, sunyi farin ciki sosai kuma sunji daɗi suna addu"ar Allah yasa rayuwa takai,
****
*K*wana huɗu da maganar zai turo kamar yanda ya ɗauki alƙawari haka ya samu dattawan kirki su ukku ya turo ya basu ƙuɗin neman aure da kuma sadaki,
haka sukayo gidan su raihana, anan suka tadda yayun baba da ƙannen shi, saboda dama sune sukace zasu zo nan dan a samu sauƙi,
Sun bada kuɗin neman aure amma sadiki ne sukace bazasu amsa ba, wanda k"b ya turo suka ce ko akwai dalili ne?"" iyayen raihana sukace, ai yanxun idan aka anshi sadakin mutum ganin an karɓa shine zaisa suyi duk abinda suka ga dama, saboda sadaki shine aure , taron ɗaurin aure shedu ne, amma yanxun kune waliyanshi mune waliyan raihana, amma bazamu karɓi sadaki ba, wanda k"b ya turo suka ce shidai ɗan yau baka shedarshi amma zasu shedi ɗansu ba yaron banza bane, abinda yasa suka bada sadaki dan su san kabiru da gaske yake, haka dai sukayi ta magana da kowa wasu hujjojin banza amma daga baya dai iyayen raihana sun karɓi sadakin k"b tare da kuɗin auren da suka kawo,...............
Bayan sun koma sukai k"b bayan duk yanda sukayi godiya yayi sannan ya sallamesu,
raihana yayo ma waya yace amaryata takaina, ina nan zuwa zan ɗaukeki anjima muje kiga in nuna maki wani abu, raihana tace to Allah ya kawo man kai lafiya, yace amin,
umma ce ta shigo ɗaki tace ma raihana ta tashi ta wanke mata wasu kaya gasu can ta fara wanki ta kasa dan masassara masassara take ji, raihana tace to, umma ta kwanta raihana ta fita taci gaba da wankin...............
Bayan ta gama ne, tayi wanka ta shirya, tana jiran zuwa k"b,......€
*Don Allah masoyan littafin , WANDA BAIJI BARI BA kuyi man haƙuri baza ku sake jina ba, saina kammala zawarci, kuyi haƙuri don Allah ana tare*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*Page* 2⃣9⃣
*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*MEELAT MUSA* 🌹
****
*R*aihana zauniyarta tana jiran zuwan k"b , ita kuma umma tana kwance saman "yar yamiɗaɗɗiyar katifarta, ta lulluɓe da wani tsohon zani, magana tayi cikin yanayin wanda bayajin daɗin jikin shi, cikin rawar murya tace raihana, raihana tace umma sannu a daidai lokacin data matsa kusa da ita ta riƙe hannunta tana ƙara cewa sannu cikin yanayi tausawa,
Umma tace yawwa , don Allah kije ki samo man maganin masassara raihana tace umma miyasa bazamuje asibiti ba ne?""" uma tace fara samo man dai, raihana tace to, raihana tashi tayi tsaye ta ɗauki hijabinta sannan ta tafi sayen maganin,
Bayan ta siyo maganin ta dawo ne, zata shiga gida k"b ya iso ƙofar gidansu, yana parking ne, raihana ta matsa kusa da motar yana ganin ta taho ya sauke glass ɗin motarshi a daidai lokacin data isa wurin motar ta dafa ta leƙa,
"yan mata, inji k"b daga ina haka ne?"" raihana tace ɗan aikena akai ina zuwa yanxun zan dawo, yace babu damuwa, raihana ta wuce ta nufi cikin gida,
Shi kuma bayan ya gama parking inne ya fito daga motar bayan ya kulleta ne ya shiga cikin zauren gidansu raihana ya tsaya,
Ita kuma tana shiga a tukunyar ƙasa ta ibi ruwa a kofi ta shiga ɗaki, tana shiga ta matsa kusa da umma ta miƙa ruwa da maganin umma ta tashi ta karɓa tasha, ta gama shane raihana tace to umma k"b yaxo zanje, kai kawai umma ta ɗaga sannan ta koma ta kwanta, raihana kuma tayo waje,
Raihana bata san k"b yana zaure ba, don haka gaba ɗaya ta fito, tana shigowa taji tayi karo da mutum, subahanallah waye?"" inji raihana kasancewar basu da wuta a gidan, adaidai lokacin da take ƙoƙarin haska wayarta, k"b riƙe hannunta yayi sannan ya jawota jikin shi yace mijinki ne, raihana tace har naji tsoro, k"b yace ni kuma har naji daɗi, raihana tace miye kuma abin jin daɗi anan?"" yace matata tana kusa dani, hmmm raihana tace lokacin da take zare jikinta daga nashi,
Kallonta k"b yayi sanann yace waike don Allah miyasa idan zanzo sai ki nemi wata hijabi ki ƙaƙwaba sai kace mata bakyauya wallahi, murmushi raihana tayi sannan tace mu koma dai waje saman dakali mu zauna a daidai lokacin da take wucewa,
Gab zata fita a zauren ne, ya riƙo hannunta sannan yace ni bazan zauna dake ba a waje dan bana so ana wucewa ana kalle manke, raihana tace ai saboda haka ne nake saka hijabi, k"b yace ni gaskiya banasan wannan hijabin da kike sakawa, nifa mijinki ne,?"" ke matana ne, raihana tace ai nasani k"b yace kindai san Allah yana san macen da take kyautata ma mijinta ko?"" raihana tace Eh, yace to nidai gaskiya inasan idan nazo a daina saka wannan hijabin plx,
Raihana tace tom, k"b yace kuma banasan kina man wani zame zame idan na riƙeki to miye a ciki?"" ya ƙarashe maganar yana taɓe baki, raihana tace tom, yaci gaba da cewa Allah ya tsine kuma ya la"anci duk matar da batabin mijinta hada mala"iku, raihana tace na sani, k"b yace to don Allah ki barni ina raɓarki inajin dumin jiki ko zan samu natsuwa, ya ƙarasa maganar cikin yanayin tausayi,
Raihana tace duk naji amma kayi haƙuri duk da nasan ka bayar da sadakinka kayi haƙuri za"a ɗaura mana aure in tare a gidanka kaga sai muci karenmu babu babbaka, k"b yace ai bakisan dalilin da yasa zan ƙara aure ba, raihana tace miye hujjar?""
k"b yace bana samun kulawa, raihana tace to zaka samu insha Allah dan a shirye nake da in kyautata maka 100% k"b yace to Allah yasa raihana tace amin,
haka dai sukaci gaba da firansu amma k"b firarshi tafi karkata wurin maganganun da kwalwar raihana ta kasa ɗauka, daga baya yace mata zai tafi, ta shirya gobe zaizo yakai ta gidan da zai ajiyeta, raihana tace nidai basai naje ba, kai nake so ba gidan ka ko wani abu ba,
k"b yace na sani amma ina so kije ki gani ne kawai, raihana tace tom, koda ya tashi tafiya haka yayi ta nuna baya san rabuwa da ita da maganganu masu jan hankali amma duk a yaudarance yake yi, ita kuma raihana zuciyar ta sai karɓa take, k"b yayi mata saida safe, ya tafi ita kua ta koma gida,
****
*D*a safe bayan raihana ta ɗan gabatar da aikin gida ta ɗan tattaro wasu "yan kayanta zata wanke , tana zaune a wuri da zatayi wanki taji sallama, wani yaro ne tsaye yace ance raihana taxo, raihana tace waye yake kirana?"" yaron yace alhajine, raihana tace waye alhaji ne?"" yace wani ne, tsaki raihana tayi sannan tace jeka ina zuwa, yaron ya fita, tashi raihana tayinta shiga ɗaki ta ɗauki hijabin sannan ta fito dan ansa koran me nemanta,
sannu injin raihana yawwa yace, ina kwana?"" lafiya qalau am nace baki gane ni ba ko?"" raihana tace naso in gane fuskar amma kuma ta shige man, alhaji yace a ina kika santa ne?"" raihana tace a gidan da aka tashemu , yace sosai nine, sake gaisheshi raihana tayi sannan tace Allah dai yasa yanxun ma ba tashinmu zakayi ba?""
dariya yayi irin ta mutanen nan "yan duniya, tsoho ne amma shakiyin tsoho, alhaji yace ai nan ba nawa bane, amma idan kina so zan siya maku shi, dariya raihana tayi sannan tace aimu bama buƙatar gida a haka ma mun gode ma Allah, alhaji yace to dama tun ranar ne nace bara inxo in sheda maki ina sanki,
Idanuwa raihana ta zaro sannan ta sake kallon alhaji a yanda ta ƙiyasta shekarunsa sunkai 75, dariya raihana tayi sannan tace nama ɗauka jikanka kaxo ma neman aurena,
alhaji yace nine na cancanci hakan , ina sanki dan samun irina zaiyi wahala yanxun, raihana tace dole ko yayi wahala saboda duk namiji irinka daya san darajar kanshi ai bazai fara tunkaro ni yace zai aureni ba, alhaji yace kuma shi yasa kuke jibgaro ku rasa masu aurenku, saboda tsabar girman kai,
miye aibu na?"" a lokacin da yake nuna kanshi, yace idan kuɗi kike so ina dasu ina da gidaje duk abinda kike so na more rayuwa zan maki ki kuma haƙƙinki na aure ma duk zanyi to miye a ciki?""
dariya raihana tayi sannan tace to ngd amma kayi haƙuri ni an riga an gama maganar aurena, sai anjima ta shige gida,
alhaji yace ai bakusan arxiki ba tana ganin kamar zan tauye mata haƙƙinta sunfi san yara su auresu ai gashi ann shi yasa kullum ake sako ku kamar tumaki , tsaki yayi sannan yaja saɓa yabar ƙobar gidan,
raihana tana shiga gida hijabinta ta cire ta zauna tace inma banda iskanci wannan tsohon ko uwar mi zai iya yi?"" harda wani haƙƙinki na aure ma duk zan sauke maki, tana kwaikwayon maganar shi, tsaki tayi a daidai lokacin data fara wanki,
Da mare sakaliya ne, raihana tana zaune ita da umma suna fira , farida tayi sallama ta shigo gidan ita da wata ƙawarta wadda ba ƙawar raihana bace, ƙawar ƙwa dai, raihana cikin farin ciki tayi masu sannu da zuwa, suka iso inda suke zaune, bayan sun gaisa da umma farida tayi mata sannu da tsegumin raihana bata faɗa mata umma babu lafiya ba, haƙuri raihana ta bata sannan tace suje ɗaki, tashi sukai suka ɗunguma sukai ɗaki da farida da raihana da ƙawar raihana,
bayan sun zauna ne, suka sake gaisawa, farida tace ke raihana mu mata mun boni, raihana tace miye ya faru kuma?"" farida tace kinga wannan baiwar Allah?"" tace Eh farida tace kawatace, raihana tace ya"akayi kuma bansan ta ba?"" tace yanxun zan baki labari raihana tace ina saurarenki, lokacin da akace za"a bayar da labari idanun wanda suka zo tare da farida ya ciko da hawaye tasa gefen gyalenta ta goge, sannan tace Allah ya tsine ma k"b albarka, raihana ta kalleta tace waye kuma k"b?"" ƙawar farida ta kalli raihana sannan tace k"b shi"umi kenan tantirin kwallon ɗan iskane wanda ya kware wurin iya yaudara da cin amana, idan kika ganshi baya da siffar macuta amma tsumma ne a nannaɗe kinga idan ka warwareshi baka san abinda zaka gani ba?""
k"b ya jefani masifa ya jefani jaza"i shine ya rusa man rayuwata shine mutumin da yayi nasarar rabani da iyayena, ya wargaza man duk wani farin ciki nawa, na tsine mashi kuma tsinuwa ta tabbata kanshi da duk maza masu irin wannan halin,
Raihana da kanta yake a dabaibaye ita a tunaninta kabir ɗan yayar umma ne, tace ai dan iskane nida ya taɓa ɗauke man zani wata rana ina wanka, ƙawar farida ta kalli raihana tace ashe kinsan shi?"" raihana tace ɗan yayan umma nane,.....................
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*Page* 3⃣0⃣
*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*MEELAT MUSA* 🌹
*****
*Ina tare daku kuma ina alfahiri daku masoyana Allah ya barmu tare fatan alkairi a gareku na gode sosai da yanda kuke nuna man kauna, muna tare ina sanku a duk inda kuke saboda kune alfahari na,*
*Hafsat Isa mamman saƙonki ya isa zuwa wurin Asmeenat xeeyan tana gaisheki kuma zata kiraki insha Allah,*
*****
*R*aihana tace gaba da cewa ai idan mahauci ya kashe maka ɗa idan kaga baƙin tsumma guduwa kake, nida babu kunya babu tsoron Allah ya fito yace man yana so yayi fasiƙanci dani!!!""" niko nace kaji masu lima ma zance wuƙa, baza ta tsaya taji inda aka dosa ba, mtswww,
Farida tace ai matarshi tana haƙuri dan ance har gida yake kai mata yana zima dasu, raihana tace ke ai bai taɓa aure ba, farida tace waike wane k"b ɗin kike nufi ne?"" raihana tace haba da Allah ɗan umma sa"a ne fa, a gidan uwarwa yayi aure?"" farida tace ke bashi ba, raihana tace waye wannan k"bn?""
Farida tace wani ɗan iskane mai tafiya da imanin mace a lokaci ɗaya, idan ya kafa maki ƙahon zuƙa sai ya zuƙeki kakaf ya shanye ki ya ɗaurayeki sai yakaiki bola ya zubar, raihana tace kaji ɗan iska, a ina yake?"" farida tace waye ma yasan inda banzan yake?"" raihana tace waike farida ya sunan ƙawar taki ne?"" bata haƙuri sai kuka take don Allah, farida tace sunan ta maryam batta tayi kukan ko ta samu sa"ada dan ko kece abun ya faru dake inajin mutuwa zakiy,
Raihana tace Allah ya rabamu da mummunar ƙaddara, gaba ɗaya suka amsa da amin, raihana tace wai miye ya faru?"" ajiyar zuciya maryam tayi sannan tace ya zama dole a faɗa maki dan kema *zawarace* dole sai munyi ƙarfi da ƙarfi munyi yaƙi da irin wa"anan mazan masu nemar hana zawara zaman lafiya, raihana tace to faɗa inji, maryam tace kamar yanda farida ta faɗa maki suna nan haka sunan yake maryam,
Nayi aure ina zaune da mijina cikin rufin asiri da kwanciyar hankali babu abinda na nema a gidana na rasa, duk abinda ake ci a gidan kowa a gidana anaci ana ci, mijina yana ji dani sosai nima inaji dashi babu abinda na nema na rasa,
Yarana biyu kuma yana nuna man kulawa sosai, kuma yana martaba man "yan uwana na, nima ina martaba nashi, muna cikin wannan zamane Allah ya jarabi mijina da karayar arxiki, muka koma abinda zamuci a gidanma babu shi dani dashi da yara duk muka shiga cikin halin damuwa da takura,
Ganin muna cikin halin wahaltuwa ne na yanke shawarar fara sana"ana haka na fara siyar da abinci ina dafawa ana zuwa gida ana siya, kuma Allah yasa ma neman albarka, fara sana"ana mijina yaji daɗin haka dan yanxun shima ya samu natsuwa da kwanciyar hankali ganin abinci da abunsha baifi ƙarfinmu ba,
Muna cikin haka wata rana wata ƙawata taxo na faɗa mata halin da nake , ta tausaya man sosai sannan nace mata gaskiya na gaji zan kashe aurena ace ina aure amma nice nake cida kaina?"" tace man mufa mata wallahi bamu da adalci wani lokaci dan Allah ya ɗora ma mijina lalura rashi sai ince bazan zauna dashi ba?"" tace man inyi haƙuri tunda ina sana"a ina samun ɗan rufin asiri na, inyi haƙuri wata rana sai labari, haka dai tayi ta man nasiha, tare da nuna man inyi zamana ko a gida nake shima zaman gidan sai nayi haƙuri ita dama rayuwa haka take juyawa take wata rana aji daɗi wata rana kuma aji babu daɗi, to dole duk musulmi sai yaga nau"in jaraba idan dai har ya yadda musulmin ne,
haka dai na yadda na ɗauki shawararta da zata tafi ta ƙara jaddadaman ko a gida ne wata rana zan nemi wani abu in rasa, amma idan nayi haƙuri anan Allah yana gani aure nake kuma bautarshi ce , zai buɗa man ta wata hanyar, nayi mata godiya,
Munyi haƙa da sati ɗaya da ita, wata ƙawata taxo na ƙara faɗa mata kamar yanda na faɗa ma ƙawar farko, sai tace man zauna ki kashe kanki da ƙuriyarki da yarintarki da kanki da komai ki zauna kamar baiwa?"" ai rainin hankaline ma , wallahi maryam na baki shawara ki kashe auren nan yanda kike haɗɗaɗiyar nan sai kin samu wanda yafi shi, amma da shekarun idan kiƙa biye wahala sai ta mayar dake tsohuwa, haka tayi ta bani shawarar banza kuma nahau kanta na zauna, bayan ta tafi mai gida yana dawowa na tada mashi balbalin bala"i ya sakeni,
ajiyar zuciya tayi sannan tace kunsan abinda ƙawar tawa tayi ne?"" gaba ɗaya sukace ah ah maryam tace ni na raina mijina naga gajiyawar shi ashe ita sanshi take, ta kuma je ta aureshi ,,
Raihana ta zaro ido sannan tace subahanallah wannan wace irin ƙawa ce?"" maryam tace mabuƙaciya, tunda da nayi haƙuri da shawarar ƙawata ta farko da abin baikai haka ba, farida tace gaskiya, idan kana tare da mijinka dan ya rasa wani abu ai bai kamata kice zaki fita ba, hmmm inji maryam sannan tace ai ki tsaya kiji ƙarahen zance, raihana tace muna saurarenki,
maryam taci gaba da cewa bayan na dawo gida mamana tace tunda ya sakoni wallahi itama bazata riƙe mashi "ya"yan shi kowa ya riƙe nashi, inaji ina gani ina san yarana aka rabani dasu aka maidai mashi, da yake yar barikice ta tattara yaran nan ta riƙesu tana basu kulawa kamar ina nan,
raihana tace to wai zuwa tayi tace tana sanshi?"" maryam tace ni ina zan sani tunda ba"a gabana akayi ba?""" amma wata ƙawata tace itace ta sameshi tace mashi maryam bata sanka tunda har ta kasa haƙuri dan Allah ya jarabeka da talauci, to ni ina sanka kuma so na tsakani da Allah tunda ai kaga baka da ko sisi, ta dai haɗa da "yar barikinta, tace zata zauna dashi, shi kuma ya aureta,
Bayan aurensu kuma Allah ya koro mashi arziki yanxun baki ga yanda ubangiji ya buɗa mashi ba, dan wallahi wahalar gani ma yake, kinga da nayi haƙuri da ban zauna lafiya ba?""" raihana tace gaskiya ai rashin haƙuri baiyi ba a rayuwa, maryam tace bari kiji zamana a gida,
maryam taci gaba da cewa ina zaune gida ina fuskantar matsalali na rasa inda zan saka raina, idan mamana tana magana nima idan na saka baki ko na bada shawara sai ƙanina yace rufe ma mutane baki shegiya ke wa zaki bawa shawara?"" wanda ma gidanki kin kasa control bare nan gida, tun bana biye mashi har na fara biye mashi, idan yayi abu na rama sai zagi, tun yana zagina abun ya koma hada duka, haka nayi ta fuskantar matsaloli sosai,
muna cikin haka ne, Allah ya haɗanin da tantirin ɗan iskan lamba ɗaya namijin da baya da kunya ko kawaici, gashi Allah yayi masa batsa a rayuwarshi, lokacin daya fara zuwa wurina, rigigi ya tattago maganar aure, ga hidima yana kashe man kuɗi kamar hauka hakan yasa naji daɗi kuma nakd ganin na daice miji,
haka yaci gaba da zugani cikin shauƙin kauna tare da tattalinso tace ɗan iska kuma ya kware wurin iya soyayya, abinda ya fara ceman shine yanxun yaushe zamuyi aurene?"" nace mashi duk lokacin daka shirya danni a shirye nake, yace to abinda nake so dake, kinga gidan da zamu zauna yanxun nake ginawa ban ƙarasa ba, nace mashi ai babu komai a ɗaura mana aure in yaso daga baya zan tare, yace man ai shi bayasan irin wannan sai inga kamar bada gaske yake so na, danshi gaskiya mabuƙacin mace ne sosai danshi a rana gaskiya kafin gari ya waye haƙiƙa yana iya kwanciya da mace so biyar ko fiye da haka,
nace mashi wannan duk ba damuwa bane, dadai irin wannan maganganun ya fara jan ra"ayi na, niko gani nake duk kauna ce, ashe jugunan nan ɗan iskan duk yaudara ce,
muna nan tare dashi duk ya ɗauke man wasu buƙatuna babu abinda na nema na rasa, tarayyata da k"b lokaci guda na canja idan kika ganni zaki ɗauka wata matar minister ce, wannan hidima da yake man yasa na saki jiki dashi, idan yaxo fira muna dan rungume juna, yayi man kiss ɗan taɓa can ɗan shashshafa can, ganin na saki jiki dashi yasa abinda yake man ya ƙara lunkuwa,
wata rana yaxo yace man matarshi tayi mashi wulaƙanci saboda ni, kuma shi bai iya neman mata ba, kuma buƙace yake dan gaskiya idan bai samu an ɗauke mashi zai iya mutuwa , kuma shi babu wanda ya isa ya rabashi dani , yana magana yana kuka, na tausaya mashi sosai nace mashi yanxun miye abunyi?"" yace maryam ki taimaka man kada in faɗa halaka nace to ai nima halakar nake tsoro, hmmm k"b ya ƙwararre ne, dan haka yace man ki rufa man asiri in baki sadakin aurena dake, ki taimaka man don Allah, kinsan da an bayar da sadaki mace ta zama matar mutum don haka gashi, haka ya fito da kuɗi 50k wai sune sadaki ya bani na karɓa, ya ɗaukeni muka tafi,
A hotel ya kama ɗaki kukan ta ya tsanan ta cikin shashshekar kuka tace ya wulaƙantani sosai yayi man abinda tunda nake duniya mijina na sunna bai taɓa man kamar yanda yake faɗi a maganganun shi cewa shi ba raggon namiji bane ba, lallai ranar na yaba aya zaƙinta, haka k"b ya goge ne fess na gurzu lallai na yadda shi namijin ne cikkake,
Raihana tace kema kinyi hauka, ya za"ayi daga ke sai ke namiji ya baki sadaki?"" maryam tace gajiya da zawarci yasa na biye ma zuciya na faɗa halaka, danni banma san matsayina ba,
Taci gaba da cewa haka k"b ya mayar dani gadon kwanciyar wurin samun natsuwarshi , ana cikin haka ne yace man in shirya muje umara, nace mashi gidanmu baza"a bari ba, amma muyi aure kafin lokacin , k"b yace ai har yanxun ba"a ƙarasa guna mana gida ba, in ƙara haƙuri, wani irin ihu maryam tayi wanda har umma saida ta shigo ɗakin da gudu, tace k"b ya cuceni ashe cutar kanjamau ce dashi na bani na lalace ,
Rashin haƙuri yaja man nayi goma babu ɗaya, na rasa mijina, na rasa "ya"yana da nake kauna , na rasa mutumcina, na rasa lafiyata na rasa farin cikina, na rabu da iyayena, kuma bazan samu mai aurena ba har abadan duniya waye zai aureni da cutar h i v, wayyo Allahana ta ɗora hannuwanta a saman kai tana ta shiga ukku ta lalace, ka cuceni k"b Allah ya tona maka asiri,
Umma da shigo ɗaki da gudu tace lafiya?"" waye k"b kuma miye yayi maki?"", raihana da bata gane ko wane kabir ake magana ba, sai mamakin maza take a ranta tace lallai wallahi bata yadda kabir ya yaudareta yayi mata irin cutar da akayi ma maryam ba, niko nace lallai raihana ko wace irin daƙi minalliƙi allaxi ɗiɗif ce? 😂
Nidai har na gane ko waye ake magana amma ita ta kasa fahimta, umma tace farida wai waye ?"" farida tace ai na ganshi da raihana ne, ta ban labarinshi kuma ranar bikin zulaihat shine ya dawo da ita gida, to ina bawa maryam labarin raihana dama, shine ranar nan taxo gida na tace man ina raihana?"" nace mata tana nan ta samu miji zatai aure tace man tayi mata farin ciki,
To ita maryam dama munyi da ita zata kawo man hoton k"b dana faɗa ma mai gidana, yace ta kawo hotonshi a kamo shi dan a hukunta shi, ina ganin hoton ne na gane k"b in raihana ne, salati umma tayi sannan tace innalillahi wa"inna ilahir raji"un, raihana ko zufa kawai take keto mata, lallai k"b ya cika cikakken mayaudari,
maryam ko kuka take sosai farida tace to kinji nace bazanyi ƙasa a guwa ba zanzo in faɗa maki don haka sai ki rufa ma kanki asiri, umma dai har yanxun ta kasa magana, farida dai sai jama raihana kunne ta ƙara sannan tace ma maryam suje, suka tashi suka tafi, saboda tashin hankali raihana ko rakiya batayi ma farida ba,
da daddare da k"b yaxo raihana cewa tayi aje ace bata nan, kuma ta kashe wayarta diff , sai gode ma Allah take kiss ɗin da yayi mata ba"a cikin baki bane da itama tana nan da h i v, O ita 😄,
****
*B*ayan sati ɗaya ne, raihana tasa neman Alhaji ya aiko suyi aure, shiko yace to zaizo amma yanda raihana ta wulaƙanshi shima zai raima, yazo anyi magana kuma an tsaida ranar aure sati mai zuwa za"ayi aurensu,
Tou ku sance tare dani wai shima dan tsoho aji zaija,danma ya samu za"ayi dashi zai raina ma mutane hankali , ya za"a ƙare da k"b?"" wane irin ramuwa ne alhaji zaiyi?"" duk ku biyoni a cikin ci gaban
*ZAWARCI HAƘURI A GIDAN AURE* tare dani jameela musa , nake cewa ku biyo ni danjin yanda zata kaya, shin raihana da alhaji zasuyi aure?"" ko yadai abin yake?"" to duk dai sai munje zamu ji,
ngd💋
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*Page* 3⃣1⃣
*AMEENCI WRITER'S ASSOCITION* 📚✍🏻
*MEELAT MUSA* 🌹
****
*Ummu Farhan ina tayaki murnar fara sabon littafinki mai suna *jameela yanda aka fara Allah yasa a kammala lafiya, ubangiji ya ƙara basira da zaƙin hannu ameen*
****
*M*aganar auren raihana ta karaɗe cikin anguwarsu wasu nayi mata murna sosai dan ta zaunu a gida, masoyanta suna mata fatan alkairi da addu"ar zaman lafiya,
Lokacin da labarin auren raihana yaje kunne k"b ya shiga cikin tashin hankali da takaici wato yarinyar nan shi zata raina ma hankali dan kutumar ubanta a gidan uban uwarta taga ana aure da sadakin wani?""
To ƙarya kike baki biyani duk hidimar da nayi maki ba kin kama kinbi ko ina in ƙanƙame sai kace mai nakuda?"" to zanzo gareki idan kin yadda kin amince dani in barki kiyi aurenki amma idan kika raina man hankali kida aure saidai kiga mata suna gidan aurensu suna jin daɗi su aihu kuma su samu lada, keko saidai ki zama karuwa karuwar k"b, yanda yake maganar ne kamar raihana tana gabanshi,
Tsaki yayi sannan ya zauna saman kujera 1seater ya ɗaura ƙafa ɗaya saman ɗaya, leɓonshi na sama dana ƙasa ya haɗa sannan ya cije su, kanshi ya sosai sannan ya miƙe tsaye da sauri kamar wanda aka yanka da wuƙa, wani irin ihu yayi sannan yace ƙarya kike ƙarya kike "yar gidan talakawa ƙaryarki ɗiyar matsiyaciya, hannunshi ya fara ɗagawa yana nunawa kamar raihana tana gabanshi yana nuna ta yace ,
Zanzo gareki kuma zan faɗa maki buƙata na, idan kin yadda shikenan idan baki amince ba, ko zan rasa rayuwata wallahi aure yafi ƙarfin shegiya banza ƙarya ya ƙarasa maganar da cikin ihu da zafin rai, hawaye suka kwararo daga idon shi, matarshi jin haukan yayi yawa yasa ta rugo da gudu ta shigo ɗakin,
Dan k"b ranshi ya ɓaci sai farfasa kayan ɗakin yake komai na ɗakin yabk ya ɓarar dashi yana ihu kuka yake sosai ƙarya kike , ƙarya kike yana maganar jikinshi yana ƙarma, baki isa ba, tunda nake a rayuwata ban taɓa nema na rasa ba, ban taɓa zubi ba face saina kwashe, don haka sai na kacaccala maki rayuwa sai nayi facafaca dake saina ci ubanki ya ƙarasa maganar cikin ihu,
Matarsa dake gefe tsaye tabishi da kallo wurin ta ya nufa da gudu tana ganin haka ta fice a tsiyace, shima da gudu ya fita, yana cewa da na kamaki yo dasai naci uwarki "yar iska ina cikin masifa kina kallona,
Yana fita wurin motarshi ya nufa, ya ɗauki motarshi yayo gidan su raihana, cikin ƙunar zuciya,
*R*aihana kuma tana zauren gidansu anwani shinfiɗa tabarma ana zance idan da darling Alhaji, firace ake yi cikin shauƙin kauna dan shima ɗan tsohon nan bada ga baya ba, sai wani murmuxa ido yake da bala"i sai ya kashe ma raihana ido, ita ko wani abun idan yayi dariya yake bata ma, shi kuma idan tayi dariya gani yake kamar ta yaba,
firar su suke cikin jin daɗi da kwanciyar hankali, Alhaji yace to raihana nidai gaskiya bana san ayi wani party, dariya raihana tayi sannan tace mai girma Alhaji ai sarki sun wuce nan, yayi dariya Ehen ehen ehenn irin dai dariyar manyan mutane, sannan yace abinda nake so dake ni gaskiya bazan wani je haɗa maki lefe ba, amma ga kuɗi nan nazo maki dashi dubu ɗari biyar zan baki sai kije ki siya duk abinda kike buƙata, maganar kayan ɗaki da komai da komai duk nine zan maki, kuma bazan haɗaki kida ɗaya da tsufin guzumayen nan ba dan hayaniyar yara bata bari mu sheƙe ayarmu ko ya kika ce?"" dariya raihana ta sake kallon alhaji, shima wata irin dariya yayi ta rainin hankali dan shima alhajin bada ga baya ba,
miƙewa tsaye yayi sannan ya gyara babbar rigarshi, ya saka hannunshi ta ciki ya zaro kuɗi kamar yanda ya faɗa haka ya bawa raihana kuɗi sannan yayi mata banƙwana, har zai fita ƙofar zauren su yayi wani muah a tafin hannunshi ya tillo wa raihana, dariya tayi ta shige cikin gida gudu, tana mamakin wannan jarababben tsoho,
Raihana na shiga cikin gida ko hijabinta bata cire ba, wata yarinya ta shigo tace wai ance raihana taxo, raihana tace waye yake kirana?"" yarinyar tace wani mutum ne?"" raihana tace babba ne?"" to ita yarinya a wurinta babba ne don haka ita raihana tunanin ta alhaji tace jeki ce gani nan zuwa, yarinyar ta fita, ita kuma raihana ta ajiye kuɗin sannan tace ma umma tana zuwa, tashi tayi sannan ta fito ƙofar gida,
A jikin motarshi ya jingina ya harɗe hannuwanshi kanshi yana kallon ƙasa, raihana ta fitowa taga k"b gabanta ya faɗi , amma dole tunda ya ganta bata da ƙaryar da zatayi don haka ta haƙura ta matsa inda yake tsaye,
Sallama tayi bai amsa ba, itama matsawa tayi ta jingina da motar kamar yanda yayi itama haka tayi kua daga sallamar bata sake cewa komai ba,
shine ya gaji da tsayuwar sannan ya ɗago kanshi , hannunshi yakai a fuskarshi ya cire glass ɗin idonshi sannan ya saka a cikin aljihun rigarsa na gaba, iska ya cika da bakinshi sannan ya murzar sannan yace,
malama raihana, gaban raihana ne ya bada wani irin dasdasdassss, ɗago kanta tayi ba tare da tayi magana ba, shi kuma yaci gaba da cewa wato a rayuwa ita mace kullum ta raina hankalin mutane, waike nan "yar tatsitsiya dake har kin iya yaudara, raihana tace waye na yaudara?"" kamar jira yake raihana tayi magana yace, wato dan kutumar ubanki ni zaki raina ma hankali?"
yaci gaba da ɗaga murya ma"ana duk wanda basu san abinda suke ba su sani kuma suji, yaci gaba da cewa ƙarya kike dan kutumar ubanki babu macen da ta isa ta latsani saidai in latsa banza in hauta kamar mashin waike ni zaki yaudara to ƙarya kike bake bama uwarki tayi ƙarya,
Raihana ta katse shi ta hanyar cewa duk mi yayi zafi haka?"" yace dan ubanki wuta, raihana tace to sai hauka kake kana man ihu bisa kai ni banma san inda maganar ta nufa ba, k"b yace zan durin uwarki haka nan zanzo inyi ta bauta maki an faɗa maki ni bawan uwarki ne?"" in bada sadaki na, dan kin ɗaukan mahaukaci inji zakiyi aure?"" to wallahi bazan yadda ba,
Raihana tace kai bari ganin ina lallaɓa ka nan da kake gani na, nima kwalluwar "yar tasha ce, idan baka sanniba bara in bada maka, ni nafi ka iskanci kuma nafi ka rashin kunya dan kafff ahalinku babu tantiraya kamar raihana, idan na fara bala"i bana gajiya kuma bana sanyayawa danni idan na fara sai nakai kuma banda alamar zanyi sauƙi, idan maganar arxiki ta kawo kayi ta idan tashin hankali kake so ina da tashar yanxun nan in kunno maka ita,
Wani irin fari yakai ma raihana ya sake kai mata wani, wurin daya mareta ta dafe sannan tace ni ka mara?"" yace an mareki kamar yanda na mareki haka zan keta maki mutunci kicin unguwar nan ina kayana da na baki dan ubanda ya hafe ki?"""" a daidai lokacin daya matsa kusa da ita ya shaki wuyanta, raihana cikin yanayin wahaltuwa tace kayanka?"" anci an cinye ko za"aje a sako ma police headquater wuta bazan bayar ba idan kana da ubanda ya tsaya maka ka kwata,
Wata irin shaka ya sake kai mata ya riƙe wuyan ta gamm, mutane da suke jefi jefi tun basu san abinda ya faru ba, har suka ankara ganin an shaƙe raihana yasa mutane suka fara turawa,
aka fara haba malam sakarta mana kana namiji zaka biye wa mace?"" duk wanda ya taɓa k"b sai yakai wa mutum nushi, ya sake yo kan raihana, yace sai ta biyashi abinda ya bata ko yayi banten baƙin biri da uwarta,
itama kafiyayyar sai cewa take baza ta biya tunda ba roƙarshi tayi ba, k"b ganin raihana itama tantiriyar kanta ce, ya fara saukowa dan raihana ta burkuce kamar mai aljanai bisa kanta ana kare k"b tana cewa sai ta bigeshi, da gudu tayi cikin gida ta ɗauko wani ƙaton faskare tana a matsa a bata wuri yau sai ta raba kanshi da gangar jikinshi,
Gefe ɗaya ya koma yana cewa naga ubanda zai aureki shegiya saidai ki mutu bakiyi aure ba, raihana tace ƙarya kake wallahi Allah yafika shirman kan banza ɗan iska fasiƙi ai ubangiji ma bazai ƙarɓi bakinka ba, tunda bakin kullum cikin batsa da maganganun banza yake, shi kuma hannun kullum yana aikata ɓarna, haka zaka lalace ɗan iska ɗan akuya,
k"b yace zaki ci ubanki sai kin zama abin kyama da kwatanci a duniya, raihana tace insha Allah za"a nunani a kwatantani mata zasu yi alfahiri dani tunda nidai ba tsinanniya ba, kaiko babj namijin da zaiyi irin halinka saidai ya tsine maka da neman tsari da irin halinka,
mota k"b ya shiga yana cewa yaga ubanda zai aureta a faɗin duniyar nan rainaha tace ƙarya kake ai lokacin zaman gida ya ƙare, haka dai ya tafi yana tsitstsine ma raihana yana kukan baƙin cikin abinda ya bata, niko nace ashe kyautar bata je zuci ba 😂
Raihana ta kalli dandazon mutanen dake wurin kowa dai da abinda yake cewa wasu na ganin bata kyauta ba wanda kuma sukasan k"b suna cewa gara data mashi haka, ita dai bata bi takan kowa ba, tayi cikin gidansu , suma mutane da sannu sannu kowa ya kama gabanshi,
Umma da bata san abinda ake ba, dan har raihana taxo ta ɗauki icce bata san inda taje dashi ba, kuma data dawo ma umma tana ɗaki, ta yada iccen a tsakar gida ta shige ɗaki,
***
Amaryar raihana sai shirin hidimar biki take, hankalinta kwance tama manta da batun wani k"bn banza can, don haka ta gayyato farida da zulaihat amma dukansu babu wanda ta bawa labarin yanda sukai sa k"b ba, itama zulaiha bata tambayi dalilin da yasa badashi za"ayi ba,
duk wanda yaji raihana zata auri babban mutum kowa yana cewa ta kashe rayuwarta itako raihana bata bi takan kowa, dan itace ta zauna gida kuma itace tasan abinda taji dan haka duk wanda zai bata shawarar kada ta auri tsoho ta tattara shi a side, abinda taga dama shi takeyi danshi aure babu wani ruwanshi da tsoho ko yaro kaidai ibada zakayi duk wanda Allah ya haɗaka dashi sai kayi ma ubangiji godiya,
K"b yana cikin tashin hankali don ganin yau saura kwana biyu ɗaurin auren raihana kuma ya lashi takobin babu raihana babu ƙara aure har abadan duniya, saidai ta ƙare karuwarshi kuma bazai aureta ba, niko nace Allah yayi mana tsari da irinsu k"b ameen,
*****
*T*ou duk abinda aka saka rana sai yaxo, idan dai da rai da rabo , yau raihana tana cikin farin ckki da jin daɗi, don yaune ya kama ranar aurenta, "yan uwa da abokan arxiki an taru a gidan umma duk wanda ka gani yana cikin farin ciki , kamar yanda suka saba ko ince ma abin ya zamar masu al"ada ƙawayen raihana sun taru suna bada laecture tasu ta zawarawa, nikam wannan karon bazan tsaya ba, wurin taron ɗaurin aure zanje dan inga abinda zai faru,
Hayani tayi yawa a wurin taron ɗaurin auren maroƙa da makaɗa saiyi suke, alhaji ango an shawo babbar riga an kawo hula an kwama a ƙarshen layi, sai yashe baki yake zai samu sardidiya raihana,
Wuri dai ya gama haɗuwa, motoci da babura duk sun kashe bakin titin kasancewar alhaji mai rufin asiri ne, dan haka dai wuri ya haɗu, su iyayen raihana o ince waliyanta, suna sama tabarma zaune shima alhaji nashi waliyan suna zaune a sanan tabarma, wani maroƙi ne ya fara magana a cikin lasifika irin wanda "yan tallar kayan nauhi suke amfani dashi,
a saurara a saurara, ance kowa yayi shiri za"afa , kai jama"a salati goma goma ga manza rahama S. A. W, gabaki ɗaya wurin yayi shiru , kamar mutuwa taxo,
mutanen da suke cikin abun hawa suna jiran hanya an tare masu wurin wucewa duk sun damu, yayin da wasu suke ganin abun rashin kyautawa ne,
Hayani wurin ɗaurin auren ta tashi jin abinda waliyan ango suka cewa yanxun, hankalin waliyan raihana ya tashi, an fasa ɗaura auren alhaji da raihana ashe yarinyar bata da tarbiyyar karuwa ce,
wani ƙanin baban raihana zufa ta keto mashi lokaci guda ya fara kuka harda face majina, abindai babu daɗi ,
wani baban mutum daga gefe zaune haka ya taso ya ƙutso cikin tarom mutane harya iso inda waliyan raihana suke, yana zuwa ya durƙusa gaban shi ya riƙe hannuwan shi yace ina nemar ma ɗana auren "yarku, wani yayan raihana yace kai bakaji ba?"" ance karuwa yace, mutumin ya ɗago kai ya kalleshi yace naji, ita karuwa ba"a auren ta ne?"" yace toshi ɗan naka yace maka yana santa ne?"" alhaji yace duk abinda na bawa ɗana yasan bazan mashi zaɓen banza ba, don haka da farko dai a tsayar da mutane kafin su gama tafiya, haka aka ci gaba da shela tare da faɗin mutane su dawo, haka dai akayi ta dawowa har aka gama taruwa, mutumin ya nemarwa ɗansa auren raihana, aka bashi sanna suka yanka mashi sadaki ya bayar , aka ɗaura auren raihana da angonta, *Faruk Ahmad Hukuma*
abin mamaki duk wanda ke wurin saida hankalinshi ya tashi jin sunan wanda aka ambata, dan fitattacen mutum ne kowa ya sani,
Wani yayan raihana ne yabi mutumin yace bawan Allah ko kaine Ahmad hukuma?""" yace ba nine ba, yace waye?"" yace ɗan uwana ne, yace to faruk ba ɗanka bane kenan?"" yace ba ɗana bane, danshi yanxun haka ma baya nan, yace miyasa ka aurar mashi karuwa?"" yace saboda yafi buƙatar ta a yanxun """ yace miyasa hannu ya ɗaga mashi a daidai lokacin daya isa jikin mota aka buɗe mashi ya shige drivern yaja suka fece daga wurin,
*A* gidan umma kuma har labari yaxo, an fasa ɗaura auren raihana, raihana tasha kuka sosai lallai maganar k"b ta tabbata kenan babu ita babu aure har abada yanxun itace zata zama karuwarshi tunda ga maganar shi ɗaya ta tabbata, haka tayi ta kuka ana bata haƙuri,
hankalin raihana bai kwanta ba sai yanxun da"akazo akace an ɗaura aurenta, umma tace da waye?"" ya za"aɗauki ɗiyarta aje a bawa wani can daban, mutane sukace tayi haƙuri tayi ma raihana fatan alkairi tunda ba"asan dalilin da yasa akayi haka ba, sannan kuma suci gaba da shiri anjima za"azo ɗaukar amarya,,,
Bara muje muyi chargy kafin a tafi kai amarya, wannan wane mijine,?"" saidai mun dawo zamuji,
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*Page* 3⃣2⃣
*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*JAMEELA MUSA*
{ *MEELAT MUSA* }
***
*TSARABAR ZAWARCI*
****
*K*uyi haƙuri "yan uwa kada fa kuga kamar rashin kunya ce, ko ku ɗauki abin da wata mummunar manufa, musulinci ya cire kunya ga abinda ya shafi addini, matuƙar abin da zai ƙaru bayinsa ne ta fuskar addini, domin aure hanyace ta zaman tare tsakanin miji da mata, wanda yadda da juna da amincewa juna da ƙaunar juna ita ke haɗuwa ya kawo dangantakar aure,
Tsantsar soyayya da ƙaunar juna da ganin ƙimar juna da mutuntu juna , idan hakan ta kasance tsakanin namiji da mace, sai iyaye su aminta da cewar lallai "ya"yansu sun haɗa kansu suna kuma son junansu sai su ga ya kamata dasu basu dama su auri junansu,
Daga nan iyaye zasu haɗu suja ragamar shine ake zuwa matakin tara jama"a "yan uwa da abokan arxiki don sheda auren "ya"yansu,
Don kowa da kowa yasan cewa waɗannan masoya zama sukeyi mai muhimmaci irin wanda manzon Allah S. A. W yake wa al"umarsa sha"awa su auri junansu , su raya sunnarsa, su kula da kansu kowa ya kula da haƙƙin ɗan uwansa da ya rataya a kansa,
Kamar kai namiji dole ne ka san cewar zaka iya ɗaukar nauyin matarka na cinta, shanta, suturarta, wurin zamanta dai dai ƙarfinka, kula da lafiyarta , da damuwarta , ka kasance mai sakar mata fuska kuyi wasa da dariya , bawai sakin fuska irin wanda zata rainaka ba, ba kuma sakin fuskar da zata daina ganin girman ka ba, don kowanne irin wasa abu ne mai kyau tsakanin miji da matarsa,
Duk wani mataki da zai jawo ƙarin ƙauna da sha"awa kuyi wasan "yar goye goye , kuyi wasan "yar ɓurum ɓurum, ka rufe mata idonta da ƙyalle , ka rinƙa zungurinta idan ta kawo wawura zata kamaka ka zulle , sai ka wana ta don kada tayi fushi da yawa , taga kana ta zulle mata ta kasa kamaka, sai ka ɗan tsaya ta kama ka, zaka ga tana tsa tsallen murna ta kamaka , zaka ganta cikin nishaɗi tana ta walwala,
kai ma zaka kasance cikin farin ciki nishaɗi , ku yi "yar ƙwallo, duk wani abu dazai sa kuyi cikin nishaɗi, ko walwala kuyi shi,
Ka jawo matarka a jikinka ka nuna mata ƙauna ka saki jiki da ita ka nuna mata tsantsar soyayyarka , ka bata kulawa ta musamman,
Kuyi rayuwa mai kyau da tsabta zaka rayuwarku tana tafiya cikin jin daɗi da ƙaunar juna,
zaka zamo amintacce ba za rinƙa ɓoye maka sirrinta ba, zaka zamo abokin shawararta,
idan ka saba mata da hakan ko wani laifi kayi mata bazata iya faɗa ma kowa ba, zata ɓoye sirrinta har sai ka rarrasheta ta sauko kaji matsalarta ,ki sasanta kanku ba tare da kowa yaji ko ya gane halun da kuke ciki ba,
Idan kuma ke kika ɓata masa yayi fushi dake , kada kiyi ɗagawa domin mijinki ne bashi haƙuri , ki marairace masa da sigar rarrashi da kalamai na ban haƙuri har sai kinga ya sauko ya haƙura sannan ki samu natsuwa,
mijinki ne idan kinyi masa baki faɗi ba, lada zaki samu a wajen Allah don mu "yan gatane munci darajar annabi muhammadu sallallahi alaihi wasallama,
Allah ya bamu addini mai sauƙi bamu zo a lokacin jahiliyya ba, zamanin jahiliyya zamani ne na kafin bayyanar musulci barin wannan zamani kamar shinfiɗa ne ga tarihin musulinci,
*mata don Allah mu kula da wannan a gidan aure*
ki zamo mace mai ladabi
Ki zamo mace mai kara,
Ki zamo mace mai yawan wanka akai akai ki kasance cikin ƙamshi mai daɗi da sanyaya zuciya,
ki zamo kissar taki ta iyayi ce, da gyara da kuƙawa da "yan mijinki da danginsa, da duk wani wanda ya raɓeshi ko yake zaune a ƙarƙashinsa,
ki zamo mace mai iya feleƙe da kwarkwasa da iya karairaya,
ki zamo "yar gayu mai sassanyar magana, mai cike taushi da sanyayyan lafuzza, wato ko yaushe ki zamo mai iya kalma mai daɗi,
ki zamo mace mai iya kwantar da hankalin mijinki duk sanda kika ganshi cikin fushi da damuwa, ki san yadda zaki lallaɓa shi, ki rarrashe shi ya fita daga cikin fushin da yake, kisa shi dariya ya zamo cikin farin ciki da annashuwa,
ki kasance mace mai kissa da sanin sirruka na iya kwamciya ta yadda zaki biyawa mai gida buƙatarsa,
Ya kasamce kinsan hanyoyin da zaki bi don inganta rayuwarku, da farantawa mijinki a wajen kwanciyarku,
Ya zamo kin zama mace da ta san yadda zata yi ta tayar da sha"awar mijinta, ba wai kije ki kwanta masa kamar taliya a cikin ruwa ba, sai yadda ya juya ki , kuskurene hakan,
Ki zamo macen da ta san yadda zata yi wa mijinta yaji daɗi,
ki kasance yadda zaki rinƙa yi masa kiss wato sunba, ki kama leɓensa kina tsotsa daga nan ki tira harshenki cikin bakinsa kina juyawa a hankali yadda zaki sauya masa tunani, ki dulmiyar dashi cikin kogon ƙaunarki,
ki kasance yadda ake hura sanyayyar iska a cikin kunnen miji ta yadda zaki ruɗashi ki tafi da hankalinsa, ya mace a ɗuniyar yake ne?"" to ya riga ya tafi yayi suman daɗi sai kin dawo dashi a hayyacinsa,
idan mai gida yana saduwa dake ki rinƙa ɗanyi sama da duwawanki kina ƙasa dashi kina rungumeshi kina ƙanƙameshi kinayin shashshekar mai kamar kuka ko dariya, kina kai hannunki ƙirjinsa kina shafawa, kina ɗan murza kan mamansa kina shashekar cikin kukan shagwaɓa haƙiƙa hakan shi zai ƙara masa ƙaimi na abinda yake yi zai kasance cikin jin daɗi da annashuwa,
labarinmu, zawarci, *Hakuri ribar aure*
*H*aka dai akaci gaba da hidimar biki cikin kwanciyar hankali, raihana dai gaban ta sai faɗuwa dan rashin sanin waye mijin da aka aura mata,
*D*a marece bayan la"asar haka motoci na alfarma suka fara karakaina a ƙofar gidansu raihana, mutane sukayo can dan duk wurin babu motar yara, duk motar daka gani a wurin idan ka kalleta saika ƙara,
A gefe kuma wata haɗaɗɗiyar mota aka ware dan ɗaukar amarya raihana ga sodoji sun zage ta dan bawa matar oga kariya,
bayan an gama shirin kai amarya raihana sai kuka take kamar zata shiɗe umma sa"a, da sauran dangin umma sai nasiha ake mata, umma ma tayi ma raihana nasiha sosai ta kuma nuna mata darajar aure da girman sa, sannan kuma ta ƙara da cewa ta zamo mai haƙuri da juriya ta riƙe sirrin ta, ta riƙe safta kuma ta zama mai biyayya ga mijinta, kuma tayi biyayya akan duk abinda ya umirceta dashi matsawar bai saɓa addinin musulinci ba,
gwaggo tunda aka fara bikin nan sai yanxun ta leƙo gidan shima ganin kwam ya kawota, dan labari yakai a kunnenta, ta kuwa zo taga ana ta hidima cikin rufin asiri ,
To haka dai kowa ya fito aka fara shiga motoci dan tafiya kai amarya,
Raihana sai kuka take, kamar bazata rabu da umma ba, ita tashin hankalinta bata san waye zata aura ba,waye mijin nata,?"" gaskiya tana cikin damuwa sosai, amma haka dai ta haƙura aka tafi da ita mota, tana ji tana gani aka jata sai gidan angonta faruk wanda bata sanshi ba bata halinsa ba, kuma bata san asalinsa ba, haka motoci suka yi ta tafiya ɗaya bayan ɗaya abun gwanin ban sha"awa, motar amarya raihana kuma tana samun kariya sosai,
Lallai yanxun abunne aka fara mamakiyos dan gidan raihana wani jugunannen gida, haɗaɗɗe tsayawa gaya maku irin tsaruwar shi da haɗuwarshi kauyanci ne,
duk motacin da suka ɗauko amarya dukansu suka shige cikin gidan,
amarya raihana kuwa, wani haɗaɗɗen kafet aka shinfiɗa tun daga bakin inda ta fito mota har zuwa cikin farlon ta, har yanxun raihana kuka take wanda babu wanda yasan dalilinsa,
haka aka kai amarya a ɗakin mijinta aka ajiye ta, kowa sai mamaki yake irin wannan sa"a da Allah ya bawa raihana ,niko nace al"amarin ubangiji ya wuce yanda ake zatonsa,
Farida da zulaihat sai ƙara ma raihana nasiha suke da bata shawarata tayi haƙuri ta zauna lafiya, maryam zawarar k"b itama tayi nasiha sosai tare da fatan zaman lafiya ga raihana,
To da haka dai kowa ya fara watsewa, farida da zulaihat sukayi ma raihana fatan alkairi suma suka tafi gida ya rage daga raihana sai halinta sai kuma masu kadi da suna wurinsu basu san abinda take ciki ba,
bayan kowa ya gama tafiya raihana tana nan zaune, sai kuka take tama kasa cire mayafin bare tasha iska,
tana nan zaune ne taji ana sallama, ita a tunaninta angon ne, dan haka gabanta ya fara faɗuwa ta ware idanuwanta ta cikin hijabinta don ganin ya kalar sa take, ..................
Ina baku haƙuri don Allah gobe idan Allah ya kaimu bazan samu damar yin typing ba, zanyi tafiya ne, don haka ina barar addu"arku, amma insha Allah ranar sunday zakuji ni,
ngd sosai ku kasance tare dani, hakuri dai ribar aure!!!
jameela musa ke maku fatan alkairi,
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*Page* 3⃣3⃣
*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*JAMEELA MUSA*
***
*Fatima Abubakar A First ina tayaki murnar kammala littafinki mai suna , YA ABUN YAKE? Allah ya ƙara basira da zaƙin hannu*
*wannan shafin nakune masoyan labarin zawarci Allah ya barmu tare ubangiji kuma ya ƙara maku lafiyar idanuwa*
*Gargaɗi gareku masu juya man labari gaskiya banajin daɗin abinda kuke man ita rayuwa ba haka take ba, donmi zan tsara labarina in hana kaina zaman lafiya dan in isar da saƙona inda nake so yaxo saboda Allah sai azo ana man duk wanda ya sake juya man labarin zawarci da ko wane irin littafi nawa gaskiya ban yafe ba,*
***
*K*oyan kissoshi gare mu ta wajabta, domin kissa tana daga cikin ingantaccen zaman aure, kuma kissa ita ke sawa mai gida ya ƙara ƙaunarki a zuciyarshi , yaji a duniya babu wacce yake so da ƙauna irinki,
Kissoshi sun kasu kashi daban daban ga misalinsu,
Kissar tafiya,
Kissar magana
Kissar kwalliya
Kissar iya zama da mij
Kissar iya zama da kishiya
Kissar kallo
Kissar tsafta
Kissar tsaftar gida
*Kissar tafiya*:• 'Yar uwa tafiya ma fa iyawace, dole sai kin nutsu wajen yin ta, kada ki rinƙa tafiya bazar bazar kina yi kina tayar da ƙura , kiyi ɗaurin zani leɓatunsa yana jan ƙasa, kiga ƙasan zani yayi baƙaƙirin ko jajir dashi, kayanki ma saurin mutuwa zasuyi dan danan zasu dafe su lalace , hajiyata idan kin tashin ɗaurin zani ki daidaita shi, ki buɗa ƙafafuwanki ki ɗaurashi ya zauna ciff ciff a jikinki yanda bazai harɗeki ba bare ki faɗi, ki rinƙa tafiya sannu sannu kina taku a hankali,
Kina yauƙi , kina yanga kina takun jan hankali, da duk abinda yakeyi sai ya tsaya kallonki, ki rinƙa takon da zai girgiza mamanki, da duwawunki, dole zai raja"a da kallonki, zaki ɗauke hankalinsa, ko wasu matan ya gani a waje bazai iya tsayawa kallonsu ba,
Zaiga ɓata lokaci ne domin duk abinda zai kalla ke kinayin mafiyinsa, tunda dai dole duk tsiyar budurwa zata yafa mayafi ke kuwa a gaban mijinki kike, zaki iya saka ɗamamun kaya da zaki rinƙa juyi a gabansa,
Kina taku kamar hawainiya komai yana rawa yana girgiza ki tafi da zuciyar mai gida a kula uwar gida,
Kissar tafiya kenan,
*Kissar magana*:• to ita kuma sai next page, da haka duka zanyi bayanin su, har ƙarshe, da fatan zaku kasance tare dani *jameela musa*
*ZAWARCI*
*haƙuri ribar aure*
*H*aka tayi ta raba idanuwa dan ganin wanda zai shigo ita dai ta kasa amsa sallamar kuma har yanxun gabanta bai daina faɗuwa ba,
mai sallamar ya gaji da magana ya shiga cikin ɗakin, raihanata dake kallon shi ta cikin mayafinta, sannan tayi magana cikin rawar murya tace ina yini, yace lafiya qalau, yace amarya kixo parlour ina so zanyi magana dake, raihana tace to, shi kuma ya fita,
Raihana ta tashi tabi bayanshi har parlour suna zuwa ya zauna saman kujera 1seater , ita kuma ta zauna a ƙasa, gyaran murya yayi Ehem Ehem, sannan yace Emm raihana, nidai yanxun abinda zance maki shine shawara ɗaya zan baki,
Shawarar kuwa itace, kiyi haƙuri ki zauna lafiya kuma kiyi ma mijinki biyayya, danshi aure ibada ne, kuma ibada mai girma abu kaɗan kika kuskure sai ki faɗa ma wahala,
To kiyi haƙuri akan rashin sanin waye mijinki na tabbata tunda kina da haƙuri zaki iya zama dashi insha Allah ni ina kyautata maki zato,
ni nan nine nayi maki shishshigi a rayuwa ba tare da saninki ko yardarki ba, bayan labari yaxo kamar yanda naji a wurin taron ɗaurin aurenki cewa wanda zai aureki yace ya fasa wai ance ke karuwa ce, wani k"b ya kira ya faɗa mashi,
to ni kuma naje wurin ɗaurin aurenki ne, dan faruk ya taɓa bani labarinki cewa har gidanku ya taɓa zuwa amma akace mashi anyi maki aure, to wannan dalilin ne yasa inajin ance an fasa aurenki banyi ƙasa a guiwa na bada sadakin aurenki,
ni ba babanshi bane, kuma ba kowa nashi bane, kawai dai yaron yana da mutunci da mutum tawa ne, ni maƙocinsa ne, amma ya ɗaukeni kamar uba, dan haka ina baki shawara kiyi haƙuri kiyi zamanki lafiya, amma faruk yana da zuciya dan haka sai kiyi karatunsa dan sanin yanda zaki zauna dashi,
Raihana tace na gode sosai, haka dai ya ɗan ƙara mata nasiha sannan ya tashi ya tafi, itama raihana haka ta tashi ta koma ɗakinta jiki duk babu daɗi,
*WAYE FARUK AHMAD HUKUMA*
Hmmm faruk su biyar a wurin mahaifiyar sa, mata huɗu shi ɗaya namiji, babanshi tun daga mahaifiyar faruk bai sake aure ba, haka suke zamansu cikin mutunci da lumana,
kuma Ahmad hukuma wato mahaifin faruk shahararren ɗan kasuwa ne yana da kuɗi na ban mamaki, kuma ya daɗe da rasuwa, faruk ya ɗauki duk komai na mahaifinsa yana kulawa dashi ma"ana bayan rasuwarsa yaci gaba da irin harkokinsa,
amma ƙannensa suka tada ƙayar baya ya fitar masu da haƙƙinsu haka aka raba gado aka bawa kowa haƙƙinsa kamar yanda addinin musulnci ya tanada,
To faruk tun kafin mahifinsa ya rasu shi dama yake sha"awar akin soja, dan haka mahaifinsa ya tsaya ya dage kai da fata don biyama ɗansa burinsa,
to daya samu aikin soja kuma ya fito babba sosai , bayan mahifinsa ya rasune ya samu wani abokinsa mai gaskiya da amana ya ɗora shi dan ya riƙa kula masa da harkokin, amma shima yana zuwa idan ya samu lokaci, aikin soja ya karɓi faruk sosai yana ta samun ƙarin matsayi sosai,
Faruk ɗan gayune, ma"aboci san kamshi kuma faruk yana da kyau sosai, ganin kyau da Allah yayi mashi kuma ga kuɗi suna gaya mashi ƙarya ga kuma mulki yana ƙara hayaƙa mashi kai yasa faruk ya ɗauki rayuwa wulaƙanci da raina mutane,
ya kasance mabuƙaci ne faruk yana da yawan sha"awa sosai amma baya zina, wannan dalilin ne yasa shi ya ɗauki rayuwar auri saki, daya ga mace yana so zai auro ta, yana gama goge ta zai bata raset,
Lokacin daya ga raihana hankalinsa ya tashi yaji kamar zai haukace, saboda haka yayi alƙawarin saiya auro ta, amma a lokacin da yazo gidansu akace mashi tayi aure , wannan ne yasa yaji baƙin ciki har yaje ya bawa maƙocin sa labari wato wanda ya auro masa raihana,
shi kuma abokin alhaji ne, yaje ɗaurin aurene yaji wannan abu don haka yayi ƙoƙari ya auro masa ita,
kam tsaya muga raihana yanda ta zaunu gida da zawarci zata iya saita faruk kuwa?"" ku byoni muga irin kaifin basira nata,
**
Ci gaban labari,
***
Da safe raihana haka ta tashi tayi sallah , bayan ta gama sallah ne, tabi ɗakin ta da kallo, hawaye ya gangaro daga idonta, tace ikon Allah masu kuɗi sunajin daɗinsu
wannan ƙaton gado duk na mutum ɗaya ne, tace O ko toilet ma ai yafi girman gidansu, gashi an ƙawata shi da kayan "yan gayu, dan sakata wanka ma sai an shiga kwami za"yi, ta sake cewa ikon Allah , ita umma yanxun tana can baiwar Allah niko ina nan cikin daula, haka lamarin Allah yake, haka dai raihana tabk gidan tana zagayawa daidai inda take iya zuwa, ta gaji ta dawo parlou, ta zauna, kallon ƙatuwar tv da take maƙale a jikin bango tayi taga daga bango har bango raihana tace taf muko a gidanmu ko ta girke bamu dashi,
Haka ta miƙe tayo cikin ɗaki ga yunwa tana ji ga bata san kowa ba, kuma bata da number kowa kuma bata san a ina zata samu abinci ba, haka ta haƙura ta dawo ta kwanta,
Bacci raihana take sosai, bata ma san rana tayi haka ba, tana cikin baccinta taji an kai mata wani irin halbi, da sauri raihana ta miƙe dan ganin wane ɗan rashin kunya ne, kafin ta gama miƙewa tsaye taji tana cewa ke ɗiyar matsiyata "yar gidan talakawa har kin samu wuri da zakizo ki sake jiki kina bacci?""
To ai dan uwarki munji labari a gidan naku kamar yanxun idan ba wankau kike ba, to kina can kasuwa wurin siyar da abinci, nan har kinzo kin samu wurin hutu?""
To ki sani yaya faruk yafi ki iskanci kuma ni nasan bazai yadda yazo ya zauna dake ba, sakaran banza ƙazama dake, aimu babu abinda zamuce da wancan baƙin munafikin sai Allah ya isa, dan nayi imani da ɗansa ne na cikinsa bazai yadda yaje ya auro mashi ƙaruwa kamarki ba, to ki saurara da kyau ki jira zuwan yaya idan ya iso gari yau wallahi kashin ki ya bushe,
dan mata ma masu asali da kuɗi yaci uwarsu ya korasu bareke kayan banza, jiki?"" tana nuna raihana da hannu, banza mizai so a jikinki?"" idanuwan ko gashin, kina wani zare ido kamar kinyi karo da kura, duk abinda kike taƙama dashi wallahi yaya faruk ya fiki,
mi kike dashi kyau?"" to yafi ki?" baki da gayu dan bazan ma haɗaki dashi ba, danshi kaff ƙasar nan kafin a samu ɗan gaye irin yayana sai ansha wuya,
Jaka dake, idan zuciya gareki shi idan ya shaƙe sai yaji mutum baya lunfashi yake saki, ƙara kaiwa raihana harbi tayi sannan tace idan yaxo anjimar kinyi mashi bayani danni wata ɗaya na baki a gidan nan,
ɗaya daga cikinsu tace dakata "yar uwa, ƙafarta ta ɗora saman gadon raihana sannan tace kinsan duk abinda zakai da jaki sai yaci ƙara abinda nake dake shine mu anan gidan ba"a wankau sannan kuma ba"a kawo maza dan dake da kwaratan naki duk yaya zaiyi kaca kaca da kanku da bindiga dan shi ana mashi iskanci aikin shi kawai shine sheƙewa, a daidai lokacin da take nuna kan raihana kamar dai an saita ta da bindiga, tace a wannan jakar kwalwar bindiga zata shiga tayi ma ƙoƙon kanki kaca kaca,
hawaye sai zubowa yake daga idon raihana, haka dai suka ƙaraci wulaƙancin su sannan suka jefo mata kuɗi suna cewa maza ɗauki ƙarya nadai san tunda ake a duniya ba"a taɓa ganin irinsu ba, driver zaizo anjima a ɗauke ki a wanko wannan jakin kan, a wanke ƙafafuwanki a yanke maki farci, dandai kin zama matar yaya da nace akaiki ayi maki wanka tsarki, amma ki tabbatar idan kin dawo kiyi wanka mai kyau,
wani ƙaton akwati aka ajiye ma raihana ga kayan da zatayi amfani dashi da turaruka da duk abinda zata buƙata, sannan tace Allah dai yasa kin iya fesa turare?"" dan kinsan shima iya shafawa ne,
haka dai suka ƙarw wulaƙancin su sannan suka tafi, suna fita raihana tayi ajiyar zuciya sannan ta kifa kanta a katifa tayi ta kuka,
Wata zuciyar tace raihana ki tafi, "yan uwanshi sun maki wannan wulaƙanci ina ga shi Ogan yaxo?""
wata zuciyar kuma tace ke banza rufa ma kanki asiri kinji, kin manta baƙar akubar da kika sha a zaman zawarci?"" haba raihana kada ki bani kunya mana kamar ba mace?"" kwantar da hankalinki kiyi amfani da dama ki saki jikinki sai kin mayar da faruk kamar bawanki,
wata zuciyar ta sake cewa na haneki, mutum mai zuciya ai baya zaunuwa, tsaki raihana tayi sannan tayi magana a bayyane tace ƙarya kake, raihana zata ɗora ka saman makarantar da baka taɓa shga irin ta ba,
kuma duk matan daka saka su daban raihana daban kuwa da irin yanda ta iya kula da rayuwar aure, dan raihana taci ɗamara zan zamar maka karuwa kamar yansa akace amma ta cikin gida zaka ga tsantsar rashin kunya wajen kula dakai sannan kuma zanyi haƙuri , har zuwa lokacin da zan anshi matsayi a wurin ka,
wata munafikar dariya tayi sannan ta miƙe taje tayi wanka ta shirya, ta zauna tana jiran zuwan driver,
ta daɗe da gama shiri sannan aka zo aka tafi da ita, mai tuƙa motar sojane, raihana an kashe a gidan baya,
yanda sojan yake bawa raihana girma da biyayya yasa raihana tace a ranta ai raihana taxo bata komawa wallahi,
haka suka tafi har wurin wankin kai idan akace yakai raihana, acan aka wanke mata kai aka wanke mata ƙafarta, aka gyara mata farce, aka funfa raihana ta finfo, har yanxun driver n baifa tafi ba, ana gamwa raihana ta fito, jakar hannunta ya karɓa sannan ya buɗe mata ƙofa ta shige sannan yaja suka fece daga wurin,
raihana tace lallai mai girma da girma yake, murmushi tayi sannan tayi magana a zuciyarta tace ke raihana ajiye girman kai kiyi ma rayuwarki yaƙi, kici arziki har na kusa dake su samu,
Mata mu kula da wani abu ɗaya, wai sai kiga miji da mace a waje kafin ayi aure suna kaunar junansu amma da anyi aure sai wulaƙanci da rashin mutunci a tsakaninsu, kuma wannan ba sakacin kowa bane sakacinmu ne wallahi,
Abinda kike a gidanku idan kinzo gidan aure kin daina, babu tsafta babu gyara komai a barshi tun a zaure wurin zance, kuma kina zuwa kika fara aihu ƙazanta saita ƙaru,
kula da mijinki sai kice wai kunya kike ji, ta kunya ai ta ƙare tunda ya aure ki duk abinda kike ɓiyo kada wani ya gani shi ya gani, yasanki yajiki to miye abun kunya, don Alƙah fa sai mun fitar da girman kai idan har muna san mu zauna lafiya,
Kuma wani sakaci da muke waisai kiga mace bata iya neman mijinta ita a dole mai aji ce sai idan shine ya nemeki, kuma idan ya nemeki sai ki tsaya kina girman kai waike sai kin wana shi, kuma wannan abun da muke wallahi kanmu muke jama raini miji yaji ya tsaneki,
tunda shi sex ba"ayin shi dole sai da amincewar juna, idan anyi ta ƙarfi ko rashin amincewar juna shi baiji daɗi ba, kuma ke bakiji daɗi ba, shi da yayi yana wahalce kema a wahalar kike, bayan mijinki ne, lada zaki samu , idan kin wulaƙanta mijinki mi kikayi, sai kiji mace taje ta haɗu da abokanta tana cewa aini mijina kaza kaza ,idan zai sadu dani saina ja mashi aji sai yayi biyayya kaza kaza, wallahi ba mijinki kikai mawa ba, kanki kikai mawa, kinga ga zunibi a wurin Allah sannan kin rage ma kanki ƙima da marta ba wurin mijinki,
Idan kin hanashi idan wanda Allah bai tsare bane daga nan sai ya fara neman mata idan ke baki so wata tana can tana buƙata sai ya barki da kayanki kin huta, daga nan sai tsya sai kuma ki tashi hankali ki ɗauki makaman yaƙi wai dashi kuma zakiyi adawa, to kina nan kina sakarci wata zata kwace maki a barki da haukan banza, don haka don Allah mu gyara idan muna san ci gabanmu, da kuma samun tsira ranar gobe ƙiyama, Allah yasa mu dace amin,
raihana suna dawowa gida , da sauri ya fito ya zagoyo ya fuɗe mata mota, yana ta bata girma da girmamawa, jakarta ya riƙe mata tana gaba yana bin bayanta har cikin gida, saida ta shiga parlou shima ya shiga ya ajiye mata jakarta a saman kujera sannan ya fita,
Yana fita raihana tace ikon Allah wani aikin sai manya, wani irin juyi tayi sannan ta kalli agogon bangon parloun ta taga 6:02pm, da gudu tayo ɗaki ta shige bayi dan yin wanka, baya ta gama ta fito ta fara shirin ta, kayan da aka nuna mata ta saka sune taci gayu cikinsu, haka ta ɗauri turare ta fara fesa shi wuraren daya dace, dan akwai idan turare yafi buƙatar a shafashi, shima zamu xo wurin,
bayan ta gama shirin ta tsaf ta koma parlou sauran abincin da ta taho dashi daga wurin saloon ta ɗauka taci, bayan ta gama taje ta wanke bakin ta , sannan ta haye gado tayi kwanciyarta,
Bata daɗe da kwanciya ba, bacci yayi gaba da ita, bacci take sosai can cikin bacci taji ƙarar buɗe get ƙarar motocine kawai kake ji suna shigowa, har yanxun basu lunfasa ba, raihana gaban ta yaci gaba da faɗuwa taji kamar fitsari zai zubo mata, wani irin tashin hankali taji lokaci guda kuma zufa ta fara kwararo mata, wata zuciyarta tace haba raihana kada ki bani kunya mana bare har ki sagar ma sauran mata da guiwarsu, sai kace ba mace ba?"" kiyi amfani da irin baiwar da Allah ya baki dan ci gaban rayuwarki,
Tashin hankalin raihana ya ƙaru lokacin dataji ƙarar buɗe ƙofar farlo, wani irin kamshi taji ya fara isowa inda take, jikinta ya fara ƙarma, da sauri ta koma ta kwanta sannan ta lulluɓe kanta cikin bargo,
Kar kuce nayi maku ƙarya nace bazanyi typing ba nayi, na samu dama ne, kuma na dawo lafiya na gode sosai da saƙon fatan alkairin ku yanda yayi ta zuwa man kai tsaye Allah yabarmu tare,
Jameela musa nake cewa ku kasance tare dani,
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*Page* 3⃣4⃣
*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*MEELAT MUSA* 🌹
****
*Masoya littafin YA ABUN YAKE? Ina baku haƙuri ashe bata gama ba, kunji ni da zumuɗi to ina baku haƙuri don Allah bata kammala ba, sai kunyi haƙuri dan naɗan kwana biyu ne pha,*
***
*KISSAR MAGANA*:• "yar uwa ba"a magana da miji cikin tsawa kuma ba"a magana da miji cikin kururuwa da hayani,
Mace bata ɗaga muryarta tafi ta mijinta duk inda mace take da mijinta tana yin ƙasa da harshenta, tana rage zaƙin muryarta tayi sanyi da muryarta ta rinƙa marairaicewa tana maganar cikin kwantar da murya tana lanƙwasa harshenta cikin salon iya kissar magana,
Ta marairaice muryarta tayi ƙasa da ita tayi sanyi kamar mai shirin yin kukua, sai ko rinƙa tausa murya kina yin maganar cikin tattausan lafazi ƙasa ƙasa kamar kina yi masa raɗa,
Maganar da idan kinayi zai tattara hankalinsa ya mayar gareki saboda kin tsumashi da tattausan lafazinki , kin gigitar dashi da daɗaɗɗar muryarki,
Zaki ga idan har kina maganar baya so yaji kin daina, domin yana jin muryar taki tayi masa daɗi sosai,
"yar uwa a kula a yi ƙoƙarin tausasa harshe, ba ki rinƙa ɗaga murya kina hayani ba kamar kina tare da mai gadi ko "yar aiki ba,
Dan kinsan hakan bai dace ba, saboda girma da matsayi da Allah ya bawa miji a kan matarsa,
Don manzan Allah cewa yayi, ```da za a yi wa wani sujjada bayan Allah da mace zata ce zatayi wa mijinta""```
Wuri ɗaya ne akace kada kibi mijinki , idan ya kauce hanya,
Allah yasa mu dace```
*ZAWARCI HAKURI RIBAR AURE*
*****
*T*ana cikin bargo sai mazurai take kamar munafika, shi kuma ya shigo cikin ɗakin baki ɗaya,
Wayarshi ta fara ƙara, bayan ya duba mai ƙiran ne ya ɗauka, hello, yana faɗin haka ya fita daga cikin ɗakin , yana fita tayi ajiyar zuciya, sannan ta goge zufar data ƙwararo mata,
Shi kuma yana fita a parlour ya zauna saman kujera 1seater ya ɗaura ƙafa ɗaya saman ɗaya, bayan ya gama wayarne, ya miƙe ya nufi hanyar ɗakin shi,
Ya daɗe a cikin ɗakin sannan ya fito, ya fita waje, bayan wani lokaci ya dawo dashi da mutumin da yayi jagorancin auren raihana, a parlour suka zauna dukansu, kowa ya kame saman kujera,
Shiru ya ratsa na wani lokaci sannan alhaji wato wanda ya auro ma faruk raihana, yace ina ƙara baka haƙuri a bisa shishshigin da nayi maka, na auro maka yarinya ba tare da izininka ba, dan naji kacr man kaje wurinta,
ni kuma jin ance an fasa aurenta na auro maka ita, amma don Allah kayi haƙuri na roƙeka, ajiyar zuciya faruk yayi sannan ya jingina bayanshi da jikin kujerar ya ɗauki ƙafa ɗaya saman ɗaya ya sake harɗe su,
Robar ruwan dake gefensa ya ɗauko ya zuba a kofi yasha, bayan yasha ne ya ajiye kofin ne, yace Alhaji tunda nake baka taɓa man abinda banji daɗinshi ba, kuma nasan babu abinda nake boye maka,
Amma gaskiya wannan karon an samu matsala, a daidai lokacin da raihana taji wannan maganar da sauri ta sauko daga saman gado dan taji abinda faruk zai faɗa akanta,
Yaci gaba da cewa nidai kasan ban zina kuma bana tare da mazinata, tsakani da Allah nikam bazan iya zama da karuwa ba,!!!!""" gaban raihana ya faɗi "yan cikin ta suka yamutsa, faruk yaci gaba da cewa,
"yan uwana sun kirani sun faɗa man komai , nasan nine nace maka naje wurin ta, haƙiƙa naje kuma ban samu haɗuwa da ita ba, danni a lokacin an gaya man tana da natsuwa da kamun kai, bayan nan ne ta sake hali, to gaskiya nidai kayi haƙuri bazan iya zaman da ita ba, danni ina kyamar mazinaci tun kafin in ganta naji na tsani rayuwarta ban santa,
Alhaji cikin rawar murya yace kayi ma Allab faruk ka rufa man asiri kada ka rabu da yarinyar nan kayi man alƙawari, faruk yace gaskiya bazaka samu wannan ba, Alhaji yace dan girman Allah kada kama haka ka taimakeni dan darajar manzan rahma, S. A. W,
Faruk yace naji amma ka sani wata ɗaya na bata a gidan nan, da tayi su zan korata ta koma daga inda ta fito, Alhaji yace wata ɗaya yayi sauri ka taimakeni don Allah, faruk yace baka san matsalar dana samu da mamana ba kan wancan yarinyar,
alhaji yace kayi haƙuri kabarta ko zuwa 2month ne data cika hakan ni da kaina zanzo in tafi da ita kafin kaxo,
Faruk yace ka yadda?"" yace na yadda, faruk ya sake cewa kayi alƙari?"" alhaji yace nayi alƙawari!!!! Faruk yace babu damuwa, Alhaji yayi godiya sannan ya tashi ya tafi,
Raihana tanaji Alhaji ya fita, da sauri ta ruga ta haye saman gado, tana jinjina wata biyu zatai a gidan nan, hawaye ya zubo mata daga idon ta, ta goge tace lallai haka maza zasu riƙa man wasan kura da rayuwa?""
tace lallai sakayya ce, an aura man aminu bana sanshi , amma shi yana so na, an shi kuma wannan an aura man shi bansan bai san ni ba, shi kuma baya so na, taf ai dama haka rayuwar take,
Bata gama tunanin ba, taji an yaye bargon data lulluɓe dashi, jikinta ne ya mutu ganin wanda ya riƙe bargon a hannunshi, sannan yace ke jaka, sauka wannan gadon a lokacin da yake ɗora ƙafarsa saman gadon kuma ko takalmin ƙafarshi bai cire ba,
Hawan gadon nan sai macen daraja kamilalliya ba irinki ba, dan tsiya da talauci ya ƙare a gidanku gadon ma baza a siya maki ba?"" to saurareni da kyau kiji duk ranar dana sake ganinki saman nan ya ɗan bubbuga ƙafarsa saman gado yace saina lalata maki fata kinji na faɗa maki,
kallon ƙasa da sama raihana tayi mashi sannan tace sannu mai kuɗin sayen gado kaci baya girman ka da ƙimarka kamar yanda na gani a tattare dakai ya wuce ace saboda wannan ƙazamin gadon ka tsaya kana wani tada jijiyoyin wuya ba,
Kuma ni nafi ƙarfin ka kirani talaka , dan duk abinda mai kuɗi yake taƙama dashi Allah yayi man nima, kuɗi kuma da Allah ya baka ai ba yawan ibadarka ko tsare kanka da rashi zina yasa aka baka su ba,
to yau ɗin nan kuma yanxun kasan ni nafi ƙarfin wulaƙanci gadonka banza, sai mi idan ban kwana akan gado ba, a gidanmu ƙasa nake kwanciyata kuma ka ganni ai ban mutu ba, kuma idan na mutu dole a cikin ƙasa za"a rufeni dani talaka dakai mai arxiki kabarinmu baya da banbanci, banbanci ɗaya ne, wanda ya gyara shi zaifi morewa a ciki idan ya shiga, amma dai a duniya ginin iri ɗaya,
wani irin halbi yakai wa raihana wanda harsa da tayi yunkurin amai, yace banza ke harkinsan mai kyau ko mara kyau?""
Raihana tayi magana cikin taurin rai tace ai idan bansan mai kyau ko mara kyau ba, yanxun ya wajabta a gareka tunda ina ƙarkashinka saika ka koyaman idan kuma kaima kan naka kamar nawa dani dakai duk sai mu koma makaranta, wani irin mari yakai mata, tace a cikin sharuɗɗan aure ba duka,
Haushi ya kamashi danshi ba mutum bane mai yawan magana kuma haka baya san magana, kallon raihana yayi sannan yace a gidanku miyasa ba"a saka ki makarantar ba?"" raihana tace dan ansan zan aureka ne, kaga nan da wata biyu na samu ilimi idan nayi gaba naje nayi aurena sai mijin ya sake maida ni makaranta, wani irin ƙululu ya tsayawa faruk a maƙoshi, haushi ya kamashi , har ya juya zai fita ɗakin komi ya tuna?"" ya dawo belt in jikinshi ya cire , raihana da sauri ta miƙe tace lalalalaaaa bari haba yi haƙuri don Allah kada ka dakeni,
jirama zan bar maka gidanka yanxun nan basai wani lokaci ba, Allah ya baka haƙuri don Allah da sauri ta sauka ta fara tattara "yan kayanta,
kallonta faruk yayi sannan yace babu idan zaki je, tunda na riga nayi alƙawari, fita yayi daga ɗakin sannan ya kulle ƙofar ta waje,
yana fita raihana tace kam Allah ya rufa man asiri, daya cicci ubana, kuma insha Allah bazan sake kwanciya a gadonka ba,
Faruk yana fita a farlo zama yayi sannan yace lallai ma yarinyar nan da gaske fa batajin magana wai zataje tayi aurw kam amma duk ranar da ta sake man irin wannan abun wallahi saina zane mata fata, tsaki yayi sannan ya miƙe ya nufi ɗakinshi,
Ita kuwa raihana saidai ta gyara kwanciya tana siffanto kamannin faruk tace kila dan yana da kyau yake wulaƙanci ko miyasa haka Oho, itama dai haka tayi ta juyi har bacci yayi gaba da ita,
***
Da safe faruk ya mance daya kulle raihana ta waje yana tashi wanka yayi ,ya shirya tsaff, sannan ya fita daga gidan,
raihana kuma tana tashi agogo ta duba taga ta makara kuma ko sallah batayi ba, da sauri ta shige toilet tayo alwallah bayan ta gama sallah ne, tana zaune a wurin taji ana taɓa ƙofar ɗakinta,
batayi magana ba, amma tanajin magana ana cewa wallahi momy taƙi ta buɗe , raihana jin an anbaci momy yasa ta miƙe da sauri har tana ganin jiri, tana matsaya ta taɓa ƙofar itama taji rufe gamm,
momy tace ina nan zai dawo ya sameni itama ta fito dan uwata, inji waye ubanta a garin nan?""
hankalin raihana ya tashi saboda bata san matsalar da zata fuskanta ba, raihana tana cikin ɗaki tayi jugum, suma su momy suna farlo sunyi jugum su suna jiran dawowar faruk,
To shidai faruk tunda ya fita harkokin gabanshi yake, ganin baida alamar dawowa yasa momy ta kirashi tace duk abinda yake yanxun nan tana neman shi yace yana zuwa yanxun insha Allah , bayan sun gama wayar ne momy tace wato ita tsinanniya hada wani kulle ɗaki kamar gidan ubanta,
raihana dai tana jin yanda wannan mata take ta ɗaɗɗake mata albarka,
suna nan jugum har faruk yaxo gida, sallama yayi sannan ya shiga cikin farlon, ƙannenshi suna ganin ya shigo bayan sun gaishe shi kuwa ya tashi ya fita, saboda baya da wasa, kuma horonshi ne, idan yana wuri basu zama dan zafi gareshi,
momy tace ina wadda za"a ɗauko ma "yar aikin?"" kai banda kake jakki kidahumi waccan jakar zaka ɗauko ma mai aiki?"" to idan har ina nunfashi babu wanda ya isa ya kawo mai aiki a gidan nan, idan baza tayi da kanta ba ta daina,
faruk yace momy ai dama wai sai kuma yayi shiru, momy tace zance banza, a gidansu wankau takeyi, da surfau ta saba da wahala kamar baiwa, dan haka kaima wankin ka da komai naka itace zata maka, banga dalilin kuma da za"asaka masu gadi tsaronta ba, ai bata kai macen da sodoji zasuyi gadinta ba, dan haka kowa ya kama gabanshi, idan taci uwarta da wahala itama ta gaji ta fece,
je kira man banzar in ganta, dan naji ta rufe ɗaki, raihana tace ikon Allah, zafi biyu kenan ƙannen miji uwar miji da kuma miji, shi kuma sai yanxun ma ya tuna daya rufeta a ɗaki, dan haka ɗakinshi yaje ya ɗauko maƙullin yaje ya buɗe ta, yana buɗe ɗakin ya ganta tsaye a baƙin ƙofa, baiyi mata magana ba, itama batayi mashi ba, ta raɓa shi ta wuce,
Tana zuwa daidai inda momy take zaune saman kujera raihana ita kuma ta zauna a ƙasa, sannan ta gaisheta, momy tabita da kallo , sannan ta kalli faruk daga nan momy bata sake cewa komai ba, shima faruk baiyi magana ba, miƙewa tayi ta fita daga farlon faruk yabi bayan ta, raihana ta taɓe baki tace Allah ya sawaƙe kujerar da momy ta tashi saman ta raihana ta ɗora kanta,
shi kuma a zuciye ya shigo farlon inda raihana take zaune ta ɗora kanta saman kujera yaje yakai mata wani irin halbi , sannan ya shaƙe mata wuya ya riƙe gam har ya miƙar da ita tsaye, sannan yace mi nace maki?"" raihana cikin kuka tace mi kace man ne?"" yace in sake maimata maki ne?"" raihana tace tom,
Nushi da halbi ya shiga kai mata ta ko ina, saida ya tabbatar tayi laushi sannan yace gado kujera bargo komai idan nawa ne, a kiyayi taɓa man ,
A wahalce raihana tace abinci kuma fa?"" faruk yace ki aika gidanku a kawo maki, ba garin kwaki bane da taliyar hausa?""
Raihana taji wani baƙin ciki ya riƙe mata ƙirji, tana so tayi ido huɗu da faruk amma baya yuwuwa, kallon ƙasa tayi sannan tace a ba gidanmu suke da ikon ciyar dani ba, amma idan kaji kai baza ka iya ba, hanya mafi sauƙi ka sauƙe man kowa sai huta,
Faruk yace an gaya maki bazan iya sakinki ba ne?"" raihana tace bance ba, idan har kana iyawa ka sawwaƙe man , tsaki yayi sannan yace idan na tashi aibazanyi shawara dake ba,
raihana tace to magana ɗaya zan gaya maka , ka daina dukana bana so, baiyi mata magana ba, ya juya zai fita, har ya kusa fita daga falon tace don Allah ka kawo man abinda zanci, ko garin kwaki ɗin ne, ina so, yanayin yanda tayi maganar kuma yaga ya wulaƙanta ta, amma abin baiyi mata ciwo ba, wato ko garin zataci, yace naji zan bada a kawo maki, sai kuma mi?"" raihana tace ba komai Allah ubangiji ya tsare Allah yasa ka dawo lafiya, kuma ina addu"a Allah ya kare maka sharri, har yabar farlon tana mashi addu"a,
Shi kuma yana fita, a waje ya samu wata plastic chair ya zauna, addu"ar da raihana tayi mashi yake tunani, tunda yake aure auren shi bai taɓa samun mai mashi haka ba, kuma ya kyautata masu sosai amma ita ya daketa ya mata gori still fatan alkairi take mashi, yace to mata kowa da irin halinshi,
a gidansu yayi waya ƙanwarshi yace ta kawo mashi abinci, da sauri, tace yaya mi kake so yace duk abinda ya samu, tace to,
Bai daɗe dayin wayar ba, sai gashi taxo ta kawo mashi abinci, a inda yake ta ajiye shi kuma ya ɗauka ya shiga ciki ita kuma ta koma gida,
Raihana dake zaune farlo ta rakuɓe a gefe tana zaune ƙasa, tana ganinshi ya buɗe ƙofar ta tashi da sauri taje ta anshi kayan hannunshi tana mashi sannu da zuwa, bai amsa ba, haka ya shigo ciki ya zauna saman kujera a inda ya zauna kusa dashi ta ajiye kayan , sannan ta fara cire mashi takalmin ƙafarshi, da safar,
Kallonta yayi sannan yace miyasa kika cire man?"" murmushi tayi sannan tace kasha iska wai, idan zaka tafi sai in sake sakama , kallonta yayi sannan yace to ga abincin nan, tace tom,
ɗauka tayi bayan ta duba, ita tunda take a duniya bata taɓa ganin wannan abun ba, kuma bata taɓa cin irinshi ba, kallon faruk tayi cikin sanyi murya tace mashi ranka ya daɗe ba"asamu garin ba?"" yace Ey anan ba"a siyarwa sai wannan kici, tace to kaifa?"" yace ns ƙoshi, tace don Allah muci mana, yace ah ah, murmushi tayi sannan tace to yiman lomar manya, sai zan cinye sauran ansar abinci yayi yaci sannan ya bata , tana ansa ta juya mashi baya ta fara cin abincin,
ta ɗauka zaiyi magana taji baice komai ba, ta juyo tace baza kace miyasa na juya ba?"" yayi mata shiru tayi dariya sannan tace banso kaga loma na ne, ko inda take bai kalla ba, yaci gaba da latsa wayarshi,
haka take tayin surutu bai bata ansa, har ta gama cin abincin, sannan ta rufe sauran tace gaskiya na gode Allah ya ƙaro buɗi mai albarka yace amin,
Tashi tayi ta nufi ɗakinta, shi kuma yana nan zaune,
da daddare raihana tayi wanka taci gayunta sosai ta fasa turare duk inda ya dace ƙamshi yakai, sleeping dress inda aka kawo mata cikin kayan da ƙanen faruk suka kawo ta saka, sannan ta ɗauki ƙatuwar hijabi ta saka ta nufi ɗakin faruk,
Sallama tayi ta shiga, shi kuma a daidai lokacin daya fito daga wanka hibajin ta m cire ta linke bayan ta ajiye ta kalli inda faruk yake tace mai gida gani, kallonta yayi ya sake kallonta yace waye yace ina neman ki,?"" tace ba kowa nice naga ya dace inxo faruk yace to ki tafi na sallameki, raihana tace kada kuma sai na tafi kaci yatsa fa, murmushi yayi sannan yace bazanyi ba, raihana tace anya ka ganni da kyau kuwa?"" kallonta yayi sosai sannan yace na gani, tace to Allah ya sani na fita haƙƙinka, banda zunibi, hijabinta ta ɗauka ta saka tace saida safe, yace to, har zata fita, ta juyo da sauri tace kai na manta, bara in tayaka shafa mai faruk da sauri yace a, a don Allah yi haƙuri, matsawa tayi kusa dashi daidai bakinshi tayi mashi muah, 💋 , jinshi yayi ya sandare daga tsaye, ita kuma ta fita daga ɗakin cikin sauri,
tana zuwa ɗakinta ta sauke ajiyar zuciya, tace wai Allah na nayi ƙoƙari fa, goge zufa tayi sannan tace kuma duk zafin ranshi yaga mace yayi shiru, kam lallai dani akai bari muga wanda zai iya rabuwa da wani nan da wata biyu, gado ta haye tayi kwanciyarta bacci mai daɗi ya ɗauketa,
a ɓangaren faruk kuwa , raihana tana fita yabi bayanta da kallo yace lallai shi yasa maza da yawa suke san auren zawara saboda ita ta goge idonta ya buɗe kuma ta mallaki hankalinta, da haka ake samun mata miye zai saka ɓacin rai?"" ajiyar zuciya yayi ya jawo wata jallabiya ya saka dakel ya haye gado, bayan ya kwanta tunanin abinda raihana tayi mashi yake, haka yayi ta juyi har bacci yayi gaba dashi,
****
Da safe raihana wanka tayi ta zuge cikin ƙana nan kaya, sun karɓi jikinta sosai, ta fito farlo dan gyarawa, ganin bata ganshi ba, yasa ta shiga ɗakinshi, yana kwance yana waya, tsayuwa tayi harya gama sannan ta gaishe shi, ya amsa dakel, kusa da gadon ta matsa ta riƙe ƙafafuwanshi tace ka gaji ne?"" gurgiza kanshi yayi alamar ah ah, tace na ɗauka ka gaji yanxun nan dana gasaka da ruwan zafi, kallonta yayi baiyi magana amma har yanxun idonshi kan dukiyar fulaninta yake, ta kula da haka, murmushi tayi sannan ta matsa kusa dashi ta durƙusa tace mi kake kallo?"" shiru yayi ya ɗauke kanshi, inda ya mayar da kan ta koma, tace miyasa zaka haramta ma kanka halal ?"" faruk baiyi magana ba, sai kallonta yake, murmushi tayi ta miƙe, tana juyin rainin hankali, itama tasan dan jan faɗa take abun, tace yanxun dai aiki yayi yawa ni zanyi shara kai kuma tunda saraki ne, sai kayi girkin abinda zamuyi break dashi,
shiru yayi baice komai ba,ganin bazaiyi magana ba, yasa ta fita taje ta fara goge goge, tana gamawa, ta dawo ɗakin, itama saman gadon ta hau , sannan ta ɗora kanta saman ƙirjinshi,
yace waike miye haka don Allah?"" tace nida mijina?"" har kace man miye haka?"" tace to kauna ce, bai sake magana ba, ita kuma bata tashi ba, har bacci ya ɗauketa., kwantar da ita yayi yaje yai wanka, kching ya nufa dan girka masu abinda zasu ci shima yunwar yane ji ,
yana fita raihana tayi dariya, ashe idon ta, biyu, tace waikai mai zafin rai fushi duka harbi da bindiga, sai nayi maganin taurin kai, wani irin tsalle tayi daga kwance sannan kuma yau a ɗakin nan zan kwana in ɗanɗana maka gumin jikina, idan ka tafi wani wuri sai kaji baka iya kwana ko ina sai a bayan raihana, dariya tayi sannan ta tafa hannunta, tace duk macen data bari namiji yake mata wulaƙanci ita taso, nidai zanyi maganin faruk cikin ruwan sayi,...............
Bayan ya gama abinda yake , ya dawo ɗakinshi raihana tanajin motsinshi tayi sauri ta rufe idonta, yana shigowa yace ke tashi an gama,
fara murje ido tayi kamar mai baccin gaske, tace waisu sodoji basu iya tada mata ba idan tana bacci?"" faruk ɗaure fuska yayi sannan yace mi kika gani?""tace to aisu naga ko "yar soyayyar nan basa yi ma matansu, tsaki yayi ya juya fita, dariya tayi sannan itama tabi bayanshi,..................
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
0 comments:
Post a Comment