*MEELAT MUSA* 🌹
***
*KISSAR SHAGWAƁA* :• "yar uwa kinsan rayuwa ba ta tafiya daidai yadda kake so, dole saika ƙanƙantar da kanka a wajen wanda kake ƙarƙashinsa, dole ke mace ke aka sani da aji da yauƙi da yanga , don Allah kada ki rinƙa buɗe murya kamar wata gardi idan kina magana da mijinki, kada ki rinƙa sakin baki kina kwakwata dariya,
Dariya da mai gida dariyar aji akeyi mai cike da salo na kiss , duk sadda kike tare da mijinki ki narke masa ki zamar masa "yar beby, duk sanda yake zaune baki da wurin zama sai jikinsa, ki rinƙa masa fira mai ɗan shirme a ciki wadda zata riƙa saka shi dariya,
Kada ki saki ciki a gaban mijinki ki ta faman haƙar abinci yana kallonki , Allah raina miki wayau zaiyi idan kince baza ki iya abu ba, yace duk cin da kike yi?""", Ai kin iya cinye abinci,
Idan miji yana nan kaɗan akecin abinci ana yauƙi da yanga kamar dole kike ci, zakiga gar ririta ki yake yi, idan ya gaji da yangarki ya karɓi cokalin yace shi bara ya baki a baki, ya fuskanci bakya san cin abinci, idan miji yana nan abinci kaɗan zaki zuba a filet, wanda zaki ci, idan kuwa baya nan ki loda abincinki kici ki ƙoshi,
Idan shi zaki bawa abinci ki zubo masa da yawa idan ya fara ci yace miki ya ƙoshi kada ki yadda sa masa rigima kice baki yadda ba idan dai bai cinye ba, yaje wani wuri yaci a can , ke kuma ya barki da wahalar girki yaƙi ci, yita tura masa sai kinga ya cinye,
Saboda abinfi san namiji ya rinƙa ci yana ƙoshi , idan ba haka ba sai ya zama raggon namiji bazai iya biyawa matarsa cikakkayar buƙatar ta ba, kada ki yadda idan mijinki ya shigo daga masallaci sallahn isha"i da daddare yace miki zai kuma fita, sa masa kukan kissa marar hawaye,
Ni bazan yadda ba ka fita ka barni a gidan nan ni kaɗai ba, saidai mu tafi tare idan yace kiyi haƙuri yanxun zanje na dawo sai kice ah ah nidai ban yadda ba, saidai idan zance zakaje, nidai gaskiya banzan yadda ba, sai ka gaya man wurin wacce zakaje, sai kiyi fushi ki juya kiyi cikin ɗaki,
Kina mai kuka amma fa ba kuka mai hawaye ba, zai fasa fitar ya biyoki ɗaki dan ya lallaɓaki ya fice zaman majalissa ko raka wani abokin zance ko kuma shi yaje wurin wata buduwar wai dan ya rag dare, jifa rashin aikinyi, ya bar matarsa ta aure a gida ya tafi neman magana wurin wata budurwa da yasa ba aurenta zaiyi ba,
Idan ya biyoki ɗaki zai baki haƙuri dan ya samu ya fice sai ki miƙe tsaye ki cire hijabin da kika ɗora akan rigar baccin ki ko kuma after dress da kika ɗora kan rigar baccin kice ka nuna man a jikina miye bani dashi?""" mai wata "ya mace tafi da har zaka tafi wurinta,?"" sai ki girza ƙirjinki meye baiji maka ba a halitta daka raina, zaka barni kaje ka ƙarewa wata kallo?"""""
Sai ki saka kuka ki faɗa saman gado haba hajiyata kinsa sheɗaniyar rigar baccinki kin girgiza jikinki yaga komai yana motsi kin faɗa gado yaga komai naki yana rawa kinfa ɗaga masa hankali , babu idan zai fita dole ya nufo inda kike "yar uwa donme bazamu rinƙa jawo hankalin mazajenmu garemu ba?""" zamu bari wasu suna yaudarar mana su a waje ?"" ko zuwan da zaiyi ya ɓata ƙokaci a wurinta suna fira, an ƙwareki bare kuma ya ɗauki wani ya bata kinga ai an rage ki, dan udan yayi niyyar sabowa maki kaza a daren idan yaje ya bawa wata kuɗin ke sai kiga ko ƙifi bazai kawo maki ba,
Kinga sakacinki yaja maki, da rashin kulawa, da girman kai, waike a dole kada miji ya raina ki, wallahi muna sakaci fa ko wani abu ya haɗamu da mazajenmu sai kiga mace wai bata girki bata shara babu wanke wanke, ba wanka ba wanki, sannan kuma bazaki bashi haƙƙinsa ba waike an ɓata maki rai sai ki rama ta haka?"" to wannan bashine gyara ba, wannan ɓatawa kikayi idan miji bamai tsoron Allah bane miye zai hana bazaije neman matan banza ba?"" dama su haka sukeso kinga an barki da hauka, sai ya kawo ido ya zuba maki, kafin ki ankara kuma an tadaki aiki, don Allah mu kula mu gyara saboda samun kwanciyar hankalimu Allah yasa mu dace,............
***
*Zawarci*
*A* ƙofar gida raihana tana fitowa daidai ƙofar gidansu nan tayi tsaye, shi kuma ɗan girman kan yana kallonta baiyi mata magana ba ita kuma bata matsa ba, nan tayi tsaye, tunda yaga bata matso ba kuma bata da niyyar tahowa yasa yayi alƙawari da zuciyarsa ko zasu kwana a haka shi bazai mata magana ba, wannan yana ɗaya daga cikin abinda yasa ya tsani yaje wurin mace, wai idan anzo a wurinsu lokacin suke jin wani rashin mutumci waisu anzo biko, tsaki yayi sannan ya ɗauki ƙafa ɗaya ya ɗora saman ɗaya, wayarsa ya fiddo yaci gaba da latsawa,
Raihana kuma tana ganin haka, wata zuciyar tace mata kam lallai yama raina maki hankali wata tace ba haka ake rayuwa ba, mutumin daya taso daga wani wuri yaxo saboda ke, ya kamata kiyi mashi uziri kiji abinda yaxo dashi sannan kinsan miye mafita,
kallon inda yake zaune saman dakalin ƙofar gidansu , shiko hankalinsa yana kan wayarshi, ganin baida lokacinta yanda ya nuna ma baisan Allah ya ajeta ba, yasa ta sauƙi girman kai ta matsa kusa dashi,
Kugu ta riƙe taɗan jijjiga kamar mai shirin kai masa duka, sannan tace malam ya akayi ne?"" bai ɗago ba kuma baiyi magana ba, ƙara matsawa tayi kusa dashi tace gani........., har yanxun idonshi yana saman wayarshi, baiyi magana ba, raihana tace wallahi idan baza kayi magana ba, zan koma,
murmushi yayi amma bai kalli raihana ba, yace to ai kina iya komawa, sai kixo kaina haka gatsal babu sallama babu gaisuwa kixo ki riƙe kugu kamar zaki zaneni?""" tsaki raihana tayi , kallonta yayi sannan yace ki daina wulaƙanci babu kyau, raihana tace a ina nayi wulaƙancin, murmushi yayi sannan ya ajiye wayarsa a gefe,
hannunta ya jawo ya zaunar da ita kusa dashi, sannan yace barka da yini, yana kallon fuskarta, shiru raihana tayi, Faruk yace miye?"" raihana tayi shiru, sai buɗa hanci take kamar wanda ta kada ƙato,
Faruk yacd ina magana baza kiman magana ba dan nazo gidanku?"" ya faɗi maganar cikin sigar wasa, amma raihana an wani murtuke fuska wai ita anzo biko, murmushi faruk yayi sannan yace muje zanga mom ɗinki, raihana tace ita ba mom ake cewa ba, sunan ta umma, yace to muje in gaishe da umma, raihana tace saboda mi?""" baiyi magana ba, ya miƙe tsaye, ganin yana neman shiga cikin gidansu tace du Allah malam dakata, ina zuwa bara inje in faɗa mata zaka shigo ko?"", dariya yayi har dinfull ɗinsa ya fito, komawa yayi ya zauna,
Ita kuma jiki yana rawa tayi cikin gida, tana shiga ko sallama babu ta faɗa ɗaki, tana ɗa zaro ido, tacd Umma gafa Faruk nan da gaske zai shigo duk kece kikai mana baki , haka zai shigo yaga ɗakin nan umma,?"""
Raihana tace bari inje ince kawai kinyi bacci don Allah, Umma tace haba ba haka za"ayi ba, barshi ya shigo raihana tace haba umma don Allah ji ɗakin nan?""", kalli katifar nan mai kama da tabarma, haba don Allah,
Umma ko a ajiyeshi a zaure ne?"",,,, ko a tsakar gida?"" Umma dai bata sake magana ba, raihana tayi ta magana umma bata bata amsa ba, ganin haka yasa ta tattara katifar da cusa bayan ƙaure ta ɗauke lodin kayansu da aka ɗaɗɗaure kamar ɗakin "yan bodin ta fita dasu takai wani ɗaki, da sauri ta dawo ta sharw ɗakin sannan ta shinfiɗa tabarma, garwashen wuta ta ibo tasa turaren wuta, sannan ta fita............
tana fita umma tace hegiyar mata da zakixo kiyi ta man ƙa"ida, tashi tayi ta fita ɗakin da raihana takai kayan ta samu kaya masu kyau ta saka, amma bata fito daga ɗakin ba, ta zauna,
Raihana kuma a zaure taci karo da faruk, yajowata jikinshi yayi ya rungumeta sosai yana sauke ajiyar zuciya, raihana cikin masifa tace haba don Allah miye haka kasan Allah ya tsine ma masu irin wannan halin babu kyau fa, tana ƙoƙarin kwace jikinta,
Sakinta Faruk yayi sannan yace miye haka?"" miye abun zunubi idan na taɓa ki ne?""" raihana tace du Allah idan kana shigowa ka shigo dare yana yi tayi gaba, saida ta shiga tsakar gida ta juyo dan cewa faruk ya shiga, amma sai taga wayam, gabanta ya faɗi, da sauri ta dawo zaure, baya nan, subahanallah abinda ta faɗa, da gudu ta fito ƙofar gida,
Zaune ta ganshi saman dakali, ajiyar zuciya tayi sannan ta matsa kusa dashi tace miye haka ?"" taɓe baki yayi sannan yaɗan ɗaga girarenshi yace, to ai naji sai faɗa kike kada in shiga gidan naku ki zane ni, hmmm raihana tace sannan tace to muje, kayi haƙuri, yace to miyasa kike cewa nayi xunubi idan na riƙe ki?"",,, raihana tace ai kasan dalili kaima, Faruk yace wane irin dalili ne?"" ki kikasan hakan amma ni bansan komai ba ,
Raihana tace baka sakeni ba?""" idanuwa Faruk ya zaro tare da miƙewa tsaye cikin sauri, yace waye yace na sakeki?""" raihana tace kaine ka rubutu?""" Faruk yace ni?""" yana dafa ƙirjinsa, raihana wallahi ko, sassauta magana faruk yayi sannan yace ina takardar da nayi sakin ne?""" raihana tace tana nan umma ta ɓoyeta, Faruk yace to ni Allah ya sani ban sakeki ba, amma waye ya baki?""" raihana tace nima bansan wanda ya bani ba, amma umma ta ajiye, Faruk ya kalli raihana sannan yace ba kince kada kn sakeki ba?"" raihana tace idan nace ai maganar nawa batayi amfani ba,
Faruk yace waye ya faɗa maki maganar ki bata da amfani a wurina?"" muje gidan, raihana tayi gaba faruk ya bi bayanta , har cikin gida, sallama tayi ta shige ɗaki, bayan ta shiga ta bawa faruk damar shiga, sallama yayi shima ya shiga ɗakin,
Raihana ta nuna masa wurin zama ya zauna, sannan tace bara ta kirawo umma, yace tam, fita tayi shi kuma yabi ɗakin da kallo, yana ɓata fuska kamae yaga kashi, Allah ya sawaƙe, Allah mun gode maka, a daidai lokacin da raihana tayi sallama ta shigo, umma na biye da ita, suka shiga baki ɗaya,
Bayan sun shiga ne, faruk ya cire tabarau ɗin idonsa, ya gaishe da umma cikin girmamawa da ladabi, bayan gaisuwa , raihana ta fita ta kawo ma faruk ruwa, shiru ya biyo na wasu lokutta, sannan faruk ya fara magana, cikin sinnar da kai,
Yace Umma dama naxo ne zan tafi da matata, Umma tace matarka kuma?""" Faruk yace Eh, murmushi umma tayi sannan tace ai ta gama idda, idan akana ra"ayin sake zama da ita, aisai kaje ka sanar da dangin babanta, amma idan ita ta yadda zata sake zama dakai, Faruk yace wata irin idda kuma Umma?""" Umma tace wadda kasan anayi dai kamar yadda addini ya tana da, Faruk yace to waye ya saketa da zatayi idda kuma?"" Umma tace kaine, girgiza kai faruk yayi sannan yace ko ɗaya, ni ban saki *RAIHAN* ba, waye ya baki takardar ne?"""
Umma tace wata mata ce, Faruk yace mu gani?""" Umma tace to ai babu buƙatar gani tunda kasan abinda ka rubuta a ciki, Faruk yace ai da kunga abinda na tubuta da bakice ta gama idda ba Umma, Umma ta kalli raihana sannan tace saki nawa ne yayi maki,?""""
Turo baki raihana tayi sannan tace ai gaya a gabanki ya faɗa maki mana, kai nawa ne ka bayar ma?""" ɗaure fuska faruk yayi sannan yace ban bayar da ko ɗaya ba, ɗauko man takardar nace miki, ya ƙarasa maganar cikin hargowa, tashi raihana tayi a bayan ƙaure inda ta rataye jakarta, ta sauko ta fiddo takardun saki na aminu dana faruk, tazo ta kawo mashi,
ansa yayi sannan ya fara buɗe ta aminu, saki ukku ne ya gani, murmushi yayi ya ajiyeta a gefe, tashi ya buɗe yaga ganda ya bada rubutun haka yake dai, ya miƙama raihana yace ta karanta da ƙarfi kiwa yaji,
Ansa tayi ta karanta, bayan ta gama faruk yace kuma kamar yanda nace idan komai ya daidai zanzo in dawo da ita, don haka yanxun zan tafi da ita, Umma tace a,a ba"a haka, kaga dangin babanta da mutane duk haka na faɗa masu an saki raihana amma ka bari idan Allah ya kaimu gobe zanje in masu bayani, sai kaima kaje , Faruk yace A,a matata ce ni bana buƙatar zuwa wurin kowa tunda nasan banyi saki ba, amma miye ya hana ku duba Umma?"" tace aini kawai raihana tace ka saketa, ni kuma ban iya karatu ba, na duba amma sai kawai na ajiyeta, kuma na tambayeta saki nawa ne tace bata sani ba,
Faruk yace to babu damuwa Allah yasa rayuwarmu takai goben, Umma tace amin, tashi tayi ta fita daga ɗakin, kamar jira yake ta fita, inda raihana take zaune ya miƙe yaje, yana zuwa hannunta ya riƙe itama ya miƙar da ita,
Yace yarinya yau da kin bini munje gida tare, hmmm, raihana tace hmm miye?"" yace ki bari sai Allah ya kaimu goben, raihana tace hmmm , murmushi yayi sannan yace kema kin rama ko?""",
Murmushi tayi, batayi magana ba, agogon hannunsa ya duba yaga 11:02pm yace kinga baɗa inxo in wuce, raihana tace to sai Allah ya kaimu, hannunta yaja suka fita tsakar gida, ƙofar ɗakin da umma take yaje kusa da wurin yayi mata saida safe, amma bai shiga ciki ba muma bai ɗaga labulen ba,
Kuma har yanxun hannunta yana cikin hannunshi, a zaure yace to ta koma, sai Allah ya kaimu, raihana tace tom, saida ya tafi sannan ta kulle gida ta dawo,
lokacin data dawo har umma ta shinfiɗa masu katifarsu, raihana tana dawowa kwanciya tayi, tana kwanciya, umma tace to miyasa kikace man ya sakeki ne?""", Raihana tace Umma mamanshi tace saiya sakeni ne, tsaki Umma tayi sannan tace amma ai da kin duba sai a baka abu bazaka duba kaga miye ba?"", yanxun da baizo ba sai kiyi aure da auren wani akanki?"", ki daina haka na faɗa maki, idan ance an sakeki kawai ki duba ki gani abinda Allah ya rubuta baya gogewa, raihana tace to Allah ya bamu dacewa umma tace Amin,
***
*W*ashe gari wurin 2:58pm, umma tana ta shirin tafiya wurin dangin baban raihana dan faɗa masu komai, taji sallama yayan baban raihana, yana cewa a kawo tabarma suna tare da baƙi, Umma tace to baƙin bama su shigowa bane?""", yace a zaure zamu zauna, umma tace to, ɗaki taje ta ɗauko tabarma ta bashi, yana ansa ya fita da ita,
A zaure bayan baba yaje ya shinfiɗa masu tabarma , aka zazzauna, baba ya kalli Alhaji ya kalli faruk sannan yace to ina saurarenku Alhaji,
wato shi Faruk da safe gidan Alhaji yaje yayi masa bayanin duk yadda sukai da umman su raihana, sannan yace mashi suje wurin dangin baban raihana, saboda abun yaxo haka, to shine lokacin da sukaje suka sameshi da baƙi, su kuma wasu sunje neman auren raihana, saiga su Faruk suma sunxo da nasu zanje don haka aka rantafo akayo gidan su raihana don jin ya abun yake.........,,,
Baba yace to Alhaji kace Faruk bai saki raihana ba, Faruk da yake zaune gefe guda ya duƙar da kansa ƙasa, Alhaji yace lallai bai saketa ba, matsala ce daga gida, kuma haka ya rubuta, baba yace to a kira raihana,
bayan an kira raihana, gaisuwa tayi wa kowa dake wurin , sannan baba yace tsakaninki da Allah saki nawa faruk yayi maki?""" raihana ta ɗago fuskarta ta kalli kowa na cikin zauren sannan ta mayar da dubanta ga baba, tace a takardar daya bani babu saki,
Baba yace miyasa kkace ya sakeki?""",,,,, tace saboda naji mamanshi tace sai ya sakeni, kuma naga yayi rubutu ya bani, dan lokacin da ya rubuta bana cikin yanayin iya magana ne, dana zo gida nace an sakeni, baba yace a lokacin baki duba ba?""" Raihana tayi rantsuwa bata duba ba ,
Alhaji yace taje ta kawo su gani, miƙewa rainaha tayi taje ta kawo, suna dubawa kowa ya gani kuma aka tabbatar da rubutun Faruk ne, dan haka dai akayi dai "yan cecekuce daga baya, Alhaji yace to ayi haƙuri,
Duk abunda ya faru sai ayi haƙuri tare da addu"ar Allah ya kyauta gaba, bayan an gama duka an natsu Faruk yace to zaizo ya ɗauki matarsa anjima, baba yace kayi haƙuri a saka lokaci, Faruk yace shifa lallai yau zai ɗauketa, Alhaji yace kayi haƙuri su saka lokacin?""" Faruk yace tam, baba yace kayi haƙuri, inda raihana take ya kalla sannan yace ke raihana yaushe zaki koma ne?"", jin an kira sunan raihana yasa Faruk ya ɗago kansa da sauri yana kallonta, itama shi take kallo, ƙanƙace idunuwansa yayi sannan ya buɗe su duka, yana jiran yaji abinda zatace,
Raihana tace sai bayan sati biyu, baba yace to Allah yasa rayuwarmu takai, Faruk ɗaure fuska yayi har aka tashi bai sake magana ba, daya tashi tafiya haka yayi wa su baba bulalar kuɗi ya tafi yabarsu da jinya,
bayan su Faruk sun tafine , su baba suka shigo, suka nunawa Umma, Umma tace sun gode wallahi, haka suka ba Umma wani abu daga cikin kuɗin amma furr umma bata karɓa ba, sunyi juyin duniya amma taƙi ta ansa, haka suka haƙura suka tafi,
raihana kuwa waya ta bugawa Farida ta kora mata duk bayani, Farida tace yayi daidai , ya kamata ki kimtsa hajiyata a gyareki ki koma sabuwa, a dilke mana ke, gobe insha Allah zanzo raihana tace Allah ya kaimu lafiya sai kinxo,
Faruk yaji baƙin ciki da raihana bata yadda ta biyoshi ba, duk ki gama zaki zo ki sameni da hukuma kike magana, wato ƙarshn sunan sa, Faruk Ahmad Hukuma, shine yake cewa zata san da hukuma take magana,
****
*D*a hantsi Farida tazo gidansu raihana, bayan sun gaisa da Umma suka shige ɗaki da raihana saidai su ƙulla wancan aka kwance, don haka farida tace mai dilka zatazo yau ta fara mata, kuma ta sallameta , wasu kayan matan da ta siyo mata ta fiddo ta bata, tace aci gaba da gashi hajiyata komin kyau ɗinka sai ka ƙara da wanka,
haka dai taci gaba da bata shawarwari, suna ɗaki har mai gyara jikin taxo ta fara, saida farida taga an fara sannan tayi masu sallama ta tafi gida, ita kuma mai gyaran jiki zata zauna nan taci gaba da aikinta,
Tunda faruk ya tafi har yanxun bai sake dawowa ba, gidansu raihana, yana can shima yana uzirin sa,
***
Kwanci tashi babu wuya a wurin Allah raihana dai ansha gyara an gyaru sosai , kuma yaune ranar da Faruk zaizo ya tafi da ita, dan yace baya buƙatar kowa ya rakata, kuma shine zaizo da kansa ya ɗauki matarsa,
da farida da zulaihat ne kaɗai a gidansu raihana tunda ba wata gayyar arxiki tayi ba, kunsan dai halinmu mu mata, sai ɗora raihana akeyi ana bata shawara mai ɓillewa ba wadda zata halakar da ita ba,
Suna nan har aka kira sallah isha"i saida raihana taci gayunta cikin shiga ta alfarma da burgewa, saida suka tabbatar ta gama ƙimtsuwa sannan sukace ma raihana zasu tafi, farida tace ma zulaihat suje ta ajiyeta a gida, haka suka tattara suka tafi gida ya rage daga umma sai raihan
*F*aruk baizo ba, sai wurin 9:30pm, kamar yanda yayi alƙawari, don haka bayan yayi parking ne, ya samu yaro ya turashi cewa zai shigo tunda baya da number raihana,
ba ɓata lokaci yaron ya dawo yace ance tana zuwa, bayan yaron ya tafi Faruk ya shiga cikin zauren gidan su raihana, bayan ta fito ne, suka gaisa yace suje ciki, juyawa tayi suka shiga tana gama zuiiizuiiii yana bin bayanta,
bayan sun shiga ne, suka gaisa da umma , sun ɗanyi fira sosai, sannan faruk yace ma raihana ta tashi su tafi, yana magana kamar jira take ta fashe da kuka, wiwiii, Umma tace miye haka?"", Faruk dai baiyi magana ba , umma tace bakiji abinda yace ba?""" raihana tace ita bafa yau tace yaxo sai gobe, ko inda take bai kalla ba, umma ma bata sake magana ba, tashi tayi tabar ɗakin,
Tana fita faruk ya miƙe inda raihana take tsaye tana dirdira ƙafafuwanta kamar yarinya ƙarama, duk da ya matsa kusa da ita bai hanata wannan tsallaenba tana kuka, binta yayi da kallo yanda take tsalle tsalle, da idanuwa kawai yake binta da kallo, saida ya gaji da haukan nata sannan yasa hannunshi ya daɗe mata baki,
sannan yace miye?""" tace bazanje ba yau, Faruk yace ƙarya kike sai kinje, cikin shashshekar kuka tace du Allah ka barni sai gobe, yace A, a, zata sake magana ne, yace bana san kina man gaddama, kixo muje, raihana bata sake magana ba,
Faruk ya fito ya tsaya a tsakar gida yana jiran fitowarta, ta daɗe sosai shi kuma yace a ranshi duk ki gama kixo ki sameni, ta daɗe sannan ta fito, kallonta yayi sannan yayi murmushi, yace kije kiyi ma umma saida safe, zaro idanuwa tayi sannan ta riƙe bakinta cikin magana ƙasaƙasa tace rufa man asiri don Allah, hmmm yace sannan yace Umma zamu tafi sai Allah ya kaimu, itama bata fito ba daga ɗaki tace Allah yasa rayuwarmu takai,
Faruk yaja hannun "yar matarsa suka fita daga gidan, suna fita ya buɗe mata mota ta shige ya rufe, sannan ya shina yaxo ya shiga yaja motar suka bar ƙofar gidan,
Tunda suka tafi babu wanda yayi magana saidai shi lokaci lokaci yana kallonta yayi dariya, ita ko ta cusa kanta a hijabi sai kuka take kamar wanda uwarta ta mutu, har suka xo gida raihana bata daina kuka ba , bayan yayi farkin ya zagaya ya buɗe ƙofa ya fito da ita, bayan motar ya buɗe ya tattara wasu takaddu , sannan ya rufe yayi gaba,
Ita kuma tana nan tsaye bata bi bayanshi ba, shi kuma tunaninshi ta taho, don haka yana zuwa ciki a farlo ya ajiye takaddun ya shige ɗakinshi, ya shiga wanka,
ita kuma tana can tsaye sai kuka take tana ƙara riritawa, ta gaji da tsayuwa ta tsugunna a wurin, taci gaba da aikin kuka , faruk baima san tanayi ba, tunda baisan bata taho ba,
Saida ya gama wanka ya shirya ya fito, ɗakinta ya nufa yaga bata nan, ya duba toilet bai ganta ba, da sauri ya fito waje yana dubawa , saida yaxo bakin get ya hango rakuɓe kamar wata munafika, saurin fushi ranshi yaji ya ɓaci da sauri ya isa wurin yana zuwa ya fizgo ta yace wannan wane irin iskanci ne?""", in banda wulaƙanci anan zaki xo ki tsaya kina man wani kukan munafinci sai kin zubar man da mutunci a wurin yarana?""",,,,,
Idan sakarci kukanki banza zakiyi ki bari ki shiga daga ciki, dan kinga ana lallaɓaki zaki raina ma mutane hankali?"""" to ki bari in tafi kada ki sake biyoni ki tsaya anan ɗin kiga abinda zai faru idan na sake dawowa, yana faɗin haka yayi gaba,
muguwa wuya makarantar kare haka tabi bayanshi zunguii zunguiii , shi duk tama bashi haushi don abun fushi Faruk baya rainawa, don haka yana shiga farlo ya ɗauki duk abinda zai buƙata ya shige ɗakinshi, itama tana shiga ɗakinta ta nufa,.....................
yana shiga ɗakinsa tsaki yayi sannan yaci gaba da abunda ya dameshi, ita kuma sai ihu take tana ƙarawa, iskancin ya ishi faruk din haka ya fito ya nufi ɗakinta,
har yanxun raihana tsaye take, tana kuka, faruk yana shigowa ɗakin cikin hayani yace idan baki man shiru ba zan ɗauko bundiga in fasa maki kai na faɗa maki, lokaci guda ta ɗauke numfashinta , kamar ba itace take kuka ba, yace jeki kwanta, simi simi aka wuce aka haye gado, har ta kwanta yace ta tashi ta cire hijabinta, jikinta yana ƙarma ta tashi ta cire , ta koma ta kwanta, sai ajiyar zuciya takeyi, tana kwanciya yace luluɓe, bargo taja ta lullɓe , shi kuma ya kashe fitilar ɗakin yaja mata ƙofar ya tafi ɗakinshi,
Tunda raihana taji batin harbewa bata sake motsin kirki ba, tsaki tayi sannan tace mutum sai masifa sai faɗa sai zuciya, yanayi ya canja amma zafin ran yana nan, haka tayi ta juye juyenta tana tuna Ummarta da "yar yaɗin katifarsu, hawayene suka ci gaba da zubowa daga idon ta da kuka mara sauti, haka tayi ta shashshekar kuka har bacci ya ɗauketa,
Faruk kuma a ɗaki yama kasa yin komai don haka ya tatattara komai ya ajiye shima hayewa yayi gadonshi yayi kwanciyarshi , amma ba bacci yake ba, yayi lamo wanda tafi shiru ciwo ,...............
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*Page* 4⃣1⃣
*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*MEELAT MUSA* 🌹
*Don Allah masoyan littafin WANDA BAIJI BARI BA ina baku haƙuri insha Allah zakuji ni zuwa gobe, kuma in Allah ya yadda da yawa zan maku typing kuyi haƙuri don Allah abubuwa ne sun man yawa, kundai san rayuwar*😉
***,,,,,
*ZAMAN AURE*
*H*aka dai yayi ta juyi amma bacci yaƙi yaxo mashi, tsaki yayi sannan ya sauko daga saman gadon wata zuciyar tace ya tafi wurin raihana wata kuma tace du Allah barta tunda hauka take ji, tsaki yayi a daidai lokacin daya shige toilet, alwalla yayo ya ci gaba da sallah .........,,,,
Ita kuma giwar baccin ta kawai take cikin natsuwa da kwanciyar hankali, hmmm kina bacci amma mijinki yana cikin damuwa, sai mun kula dan fita haƙƙin mazanmu gaskiya,
***
*S*aida ya dawo daga masallaci sannan ya shiga ɗakin raihana, zaune take saman abin sallah ta jingina jikinta da gado kanta kuma saman gado ta ɗorashi, faruk yana shigowa gefen gado ya zauna, saida raihana ta gama addu"a, sannan tace mashi ina kwana?""" bai amsa ba, hannunshi ya miƙa mata alamar gaisuwa, cikin hannunshi ta saka nata, saidai ya haɗe hannun da nashi ya rufe, sannan yace kin tashi lafiya?"""" kai ta ɗaga masa alamar E,
Hannunta ya saki sannan ta tashi daga inda take itama gadon tahau kusa dashi ta zauna, sannan ta ɗora kanta saman kafaɗarshi, tace kayi haƙuri jiya na ɓata maka rai, faruk yace ba komai, kanta ta ɗogo ta kalleshi murmushi yayi mata, itama murmushin tayi,
Zame jikinta tayi daga nashi tahau saman gado sosai sannan ta kwanta, jan bargo tayi da niyyar lulluɓewa Faruk ya riƙeshi taja taja taji baixo ba, juyowa tayi don ganin abinda ya riƙe bargon, faruk taga ya riƙe bargon, buɗe idanuwanta tayi sosai sannan ta mayar dasu a hankali ta lumshe su, yanayin yanda tayi abun yasa faruk yaji kasala ta saukar mashi, ita kuma cikin sheganta tace yadai?"""tana ɗaga girar ta ɗaya, sannan ta tsuke bakinta tare da girgiza kanta kaɗan tayi wasa da idonta,
Cikin wani irin sauti yayi magana, cewa nima bacci zanyi, murmushi raihana tayi sannan tace to saki bargon, saki yayi ta lulluɓe amma bata rufe fuskarta ba, shi take kallo jin bai sake magana ba, yasa tace zoka kwanta, tana nuna kusa da ita da hannun ta, ƙafafuwansa ya ɗago ya haye saman gadon, ya ɗaga bargon zai shiga itama ta riƙe shi gam,
Yace saki in shigo mana, raihana tace gaskiya baka kwanciya kusa dani da wannan kayan ai sai suji man ciwo, dariya Faruk yayi sannan ya kalli kayan jikinshi, yace mi sukayi?""" murmushi raihana tayi sannan tace ba bacci kake ji ba, tana faɗin haka ta lulluɓe duka jikinta hada kanta ta rufe idanuwanta,
ganin ta lulluɓe da gaske yasa faruk ya sake kallon jikinshi , bakinshi ya taɓe a ranshi yace lallai yarinyar nan to mi take nufi da kayan jikina zasuji mata ciwo ne?:""""",,,,, niko nace kaima ko matar ka tazo maka a haka ai kace ta sassauta kayan dan kaji gumin jikinta,
Tashi yayi zai fita daga ɗakin jin alamar yana tafiya yasa raihana buɗe fuskata shi kuma har ya kusa fita daga ɗakin, tace ranka ya daɗe ai sai kace can zamu koma amma ba ka tafi babu bayani bara in taso, tafa gane zuciya yayi amma saita basar dan ta lura abun fushi baya mashi kaɗan, towai namiji da saurin zuciya haka anya yana da daɗin zama?"",,, niko nace sai ki baibaitoshi ki gano bakin zaren sai ku zauna lafiya,
Faruk baiji magana ba, yaci gaba da tafiya, itama da sauri ta tashi ta bishi, lokacin data fita harya shige ɗakinshi ya kulle, raihana tana zuwa ta taɓa ƙofa tajita gam, tace ikon Allah sannu sarkin fushi, kai haka zamuyi ta rayuwar auren dunkum dunkum babu wani wasa babu raha babu magana mai daɗi sai anyi magana sai fushi idan mutum yayi magana kace zaka fasa mashi kai da bindiga kai soja,
tsaki tayi ta wuce saman kujera 3seater ta kwanta, bargon data taho dashi ta lulluɓe tana kwanciya ba daɗewa bacci ya ɗauketa,
Shi kuma yana shiga ɗakinshi saidai yayi tsaki shi duk auren da yake bai taɓa auren mai ƙananan shekaru kamar raihana ba, sai tsatstsauran ra"ayi, lallai tama rainashi, amma bari dan taga yana mata dariya take neman wuce wuri bari taja ma kanta,
Zaman ɗakin ya isheshi tunda ya kasa bacci fitowa yayi daga ɗakinshi da fita zaiyi ganin raihana kwance kuma yasa ya fasa fitar inda take kwance yaje ya yaye bargon da ƙarfi, yace tashi tunda banyi ba kema bazakiyi ba, kallonshi raihana tayi sannan ta mayar da kanta ta kwanta, yace kifa tashi na faɗa maki, raihana tace zero,
Faruk yace zero ɗin mi?""" raihana tace ka faɗi mana, miye ya faɗar dani?""" tace yanxun misali nice mijin kaine matar?"" haka ake tashin miji daga bacci?""",,,,,, faruk yace to nine mijin kene matar haka ake faɗa ma miji magana?""",,,,,, raihana tace bani amsar tambayana, yace bazan bayar ba, ki tashi ki dafa man tea,
Miƙewa raihana tayi sannan tace kai kuma ɗauko bargon to, faruk yace waike wasa nake dake ne?""",,,, juyowa tayi kallonshi tayi sannan tayi murmushi tace nifa komai na saba inayi ana tayani haka nake, don haka ɗauko muje idan ba haka ba, zanga wanda zai share maka ɗaki anjima,
Tsaki yayi sannan ya ajiye bargon saman kujera ya nufi kicin, dariya tayi sannan ta dawo ta ɗauki bargon ta tafi ɗaki, bayan ta ajiye bargon ta shiga toilet brush tayi ta wanke fuskarta, ta fito, shi kuma yana kicin sai ɓata rai yake, tana gamawa itama kicin ɗin ta nufa, bayan taje tayi sallama ta shiga, ko inda take faruk bai kalla ba, sai zuciya yake,
Ganin ya ɓata rai sosai yasa jikin raihana yayi sanyi, ta yanke shawarar kawai ta fita daga kicin ɗin, amma wata zuciyar tace karki fita, yi mashi magana, raihana tace ranka ya daɗe ka zuba citta da kanunfari ne?"",,,, cikin yahaniya yayi mata magana cewa bai sani ba, ganin yanda yayi maganar yasa taja baya da sauri, inda ya fara firan dankali taje ta ɗauki wuƙar taci gaba dayi, tsawa ya daka mata yace ta ajiye ta tashi ta bashi wuri,
kallonshi raihana tayi zatayi magana yace rufe ma mutane baki, kinsan zanyi kalacin saida nayi fushi nakeyi dakaina zaki wani zo kina ma mutane kilbibi, raihana tace kayi haƙuri cikin yahaniya faruk yace naƙi bazanyi haƙurin ba, kuma fita ki bani wuri na faɗa maki,
raihana tace ni ?""",,, faruk yace au dama akwai wata bayan ke?"",,, nace ki fita, fita,,,,, fita tayi tabar kicin ɗin shi kuma yaci gaba da mita, ance maki idan baki man ba, bazanyi dakaina ba?""",,,,, raihana kuma tana fitowa wuri ta samu ta zauna a farlo tana tunanin wannan zuciya ta faruk,,,,,,,,,"""""""
saida ya gama abinda yake ya fito, ɗauko komai yayi da kanshi yaxo ya ajiye, kallon inda raihana take zaune yayi tana ganin haka ita kuma ta wani basar ta ɗauke kanta gefe ɗaya taci gaba da kallon wani wuri daban, idan kinga dama sai kixo muci, raihana tace idan kuma naga haggu fa?"" yace sai ki zauna, tace to haggu na gani kaci dankalinka dama ai bakaso inci ba, shi yasa kake man ihu saman kai,
banza yayi baiyi magana ba, yaci gaba da break ɗinshi duka dankalin daya dafa ya cinye abunshi tasss, kallonshi raihana tayi tare da zaro ido, shima kallonta yayi sannan yace malama lafiya?""",,, raihana tace wato yanxun kowa zai riƙa girki da kanshi a gidan nan ko?""",,,,,, baiyi magana ba, ya tashi ya nufi ɗakinshi, wanka yayi ya fito cikin shirin mai kyau,
Da sauri raihana ta tashi taje ta riƙe jakar loftop ɗinshi ta ansa , ta riƙe, tace ina zakaje?"",,,,, yace zanje wani wuri, marairaicewa raihana tayi kamar zatai kuka tace yanxun haka zaka tafi don Allah banci komai ba a gidan nan?""",,,,,,, faruk yace ba kince kin ƙoshi ba?"" ai da nawa da naki naci idan na dawo anjima zan ƙosar dake, yayi gaba raihana tabi bayanshi da donyi mashi rakiya, haka suka fito har bakin get babu kowa kuma da alama shine zai fita da kanshi, zagayawa raihana tayi ta buɗe mashi motar ya shiga, miƙa mashi jakar tayi ya ansa, shigar da jikinta tayi cikin motar sannan ta haɗa fuskatar da tashi daidai bakinsa itama ta matsa da nata tayi mashi kiss *muah* wani iri faruk yaji a jikinshi yarrrrr sannan ya kalli raihana, murmushi tayi masa sannan ta rito da jikinta daga cikin motar tare da mashi addu"ar dawowa lafiya, harsai daya fita tana ɗaga mashi hannu,
Tana dawowa ta fara gyaran gida, tabi ko ina ta share ta goge fess ta balɓaɗe gidanta da turaren wuta, kicin ta shiga ta ɗora girkin abincin rana, saida ta gama tsaf sannan ta gyara kicin ɗin ta goge ko ina shima turaren wuta ta kunne mashi, sannan ta wuce ɗakinta donyi wanka,
Faruk kuwa tunda ya tafi tuƙi yake amma hankalinsa yana wurin raihana, tunanin lokacin da tayi masa kiss kawai yake saidai yayi murmushi ya shafa wurin, mamakinta yake shidai tunda yake aure bai taɓa katari da mai irin halin rainaha ba, a bayyane yace kina da kula, harya isa inda zaije tunanin abinda raihana tayi masa yake,
lokacin daya je, bayan sun gama abinda suke kowa ya tashi daga shi sai sadiq suka rage, fira suke amma sadiq ya lura lokaci lokaci faruk yana murmushi, sadiq yace mashi lafiya wai?"",,,,,,miƙewa faruk yayi ya tattara abinda zai ɗauka yayi ma sadiq sai anjima, rakiya yayi ma faruk har bakin mota, shi kuma ya shige motarsa ya nufo gida cikin farin ciki,
Raihana anci kyau, an zuge cikin shiga mai ɗaukar hankali tabi jikin nan nata ta balbaɗe da turare sai tashin ƙamshi, tana fitowa abinci taje ta zuba taji tayi bom, sannan ta koma ta wanke bakinta, ta ƙara gyara fuskarta sosai, ta fito farlo, bata daɗe da zama ba, taji dawowar faruk , bata fita ba dan tana tunanin ko bashi ɗaya bane, tana nan zaune harya shigo farlon, yana shigowa da sauri ta tashi a suƙwane taje ta rungumshi, tana mashi sannu da zuwa, riƙe hannunta yayi yana amsa saƙonta cikin kulawa,
Ɗakinshi ya nufa itama binshi tayi , tana cewa ni nayi girki hada kai kuma yayi daɗi, yace to , tace kai kuma sai kayi na dare ai nayi ƙoƙari ko?"",,,,,, faruk yace gaskiya amma sai naci abincin naji, raihana tace yayi daɗi zama tayi saman gado taci gaba da cewa amma baza ka sake fita ba?"",,,, nidai idan baka nan jin nake duk babu daɗi, faruk yace babu inda zanje wanka zanyi inci abinci, , raihana tace to zanjira anan ka gama yace nama ɗauka zaki mn wankan ne?""""
Ido raihana ta zaro tare da daɗe bakinta, kallonta yayi sannan yace to ba ɗaxu kince bazakiyi bacci dani ba wai saina cire kayana ba?""",,, raihana ta rufe idon ta, murmushi yayi sannan ya cire kayanshi ya shiga toilet, yana shiga raihana ta tashi tabar ɗakin tana fita ɗakinta ta nufa tace kaiji shiko kunya ma bayaji inyi mashi wanka, dariya tayi sannan ta ɗauko wayarta farida ta kira,
bayan ta ɗauka raihana ta fara rattafa mata, tana dariya farida tace haba hajiyata kiyi wanka tare da mijinki miye?"" idan kinyi mashi lada zaki samu, annabi yana wanka tare da iyalinsa kuma a cikin bokitin ruwa ɗaya, duk abinda zakiyi ki ƙara shaƙuwa da mijinki yarinya ki daddage kinga zaiso ki sosai kiyi biyayya kuma Allah ya baki lada ya sakaki a aljanna da rahamarsa, raihana tace to gashi nan ya fito zamuyi magana , farida tace to,
Ajiye wayar tayi sannan ta tashi ta nufi farlo, shi kuma yana kwance saman kujera 2seater, wurinshi ta nufa a gefe ta ɗan ɗosana kugunta ta zauna, sannan ta ɗora kanta saman ruwan cikinshi, shi kuma yace baki kawo man abinci ba, yunwa nake ji, raihana tace wayyo na manta, niko har yanxun banci komai ba, faruk yace da gaske?""",,, raihana tace E amma azumi zanyi ma, faruk yace lallai ai sai ki bada himma, bata sake magana ba ta wuce cikin tafiyar jan hankali shi kuma ya bita da kallo har ta fito daga kicin ɗin faruk bai daina kallon hanyar ba,,,,, haka ta fito da abincin ana wani yauƙi tafiyar rainin hankali mai caza kwalwar mai kallo, bayan taxo ta ajiye abincin ne, ta zuba mashi saukowa yayi ƙasa ya zauna, cokali ta ɗauka abincin ta fara iba zata bashi a baki yace nidai bani inci don Allah,
Marairacewa tayi kamar mai shirin yin kuka ta riƙe cokalin sosai tace ita zata bashi gaskiya, kallo ya bita dashi baiyi magana ba, taci gaba da ibar abincin , taɓe baki yayi ita kuma taci gaba da ibar abincin tana bashi badan ranshi yaso ba, haka ya haƙura yaci gaba daci,,,,
saida ya shafe abin tsaff sannan raihana ta zuba wani sannan ta, miƙa mashi tayi yace mi za"ayi dashi?""",,,,,,, tace to bani nima, faruk yace kai ban iyawa gaskiya, raihana tace nima na iya kaima ka iya, yace ke idan kinaci da kanki kici na gaya maki, aje abinci tayi tace tunda baka bani shikenan, yace kin huta to, ajiye abinci tayi ta miƙe ta nufi ɗaki,
Faruk yace raihan zo?"" yi tayi kamar bata ji ba, yace dake nake fa, da gudu ta shige ɗaki, tana zuwa saman gado ta faɗa , faruk abincin ya ɗauka ya bita dashi , yana zuwa saman mirrow ya ajiye sannan yaje saman gadon ya ɗagota kallonta yayi sannan yace miyasa kike kuka?""",,,, raihana tace ba komai kawai bazanci ba,
yace yi haƙuri kici don Allah, tace ai nace bazanci ba, faruk yace kinji kuwa yanda abincin yayi daɗi?""",,,,, ,,,,,, murmushi raihana tayi sannan tace da gaske don Allah?"" yace da gaske nake mana, zo muje farlo abincin yaje ya ɗauka sannan yazo ya kama hannunta suka dawo farlo, zama yayi sannan ya zaunar da ita ya fara bata abincin taci abincin ta dama, dan haka kaɗan taci tace ta ƙoshi,
bayan ta gama ne yace taje ta shirya zasu je anguwa, tace to, ɗakinta ta tafi don shiri, shima nashi ɗakin ya tafi,
Bayan raihana ta gama shirinta tsaff ta fito, ɗakin faruk ta shiga, waya ta tadda yanayi, yana ganinta ya miƙe yana cewa muje, sannan yaci gaba da wayarshi bari zamuyi magana da safe, ya kashe wayar, hannun raihana ya riƙe batayi magana ba, sukaci gaba da tafiya har sukaxo wurin mota,
suna zuwa suka shige faruk yaja suka bar gidan, tafiya sukai mai nisa sosai har suka iso wata unguwa , shiru anguwar take baka ganin kowa kua bakajin motsin komai sai kuka karnuka , a bakin wani gida ya danne horn ɓit ɓiɓit, boɗe get in akayi sannan faruk ya sulala da motar cikin gida,
zaro idanuwa raihana tayi tana bin gidan da kallo haka sukaci gaba da kutsawa get na biyu , shima wani sojane ya buɗe tare da girmamawa wato sarawa, raihana saidai ta kalli faruk ta kalli gidan kana ganin haka kasan alamar tambayane, bata gama tunanin ba, ya sake horn, get na ukku toufa raihana fa gabanta ya fara faɗuwa, tace mashi wai inane nan?""",,, get na huɗu suka shiga raihana kuka ta farayi wayyo Allah don Allah ina zamuje?""",,,,,, ko kallonta baiyi ba suka get na biyar, kai da gaske raihana kuka take , kallon faruk tayi tace mashi don Allah ina ne nan?""",,,,,
Baiyi magana ba, haka faruk yaci gaba da sulalawa har suka iso wani round, an ƙawata wurin da wasu irin filu masu burgewa wani ruwa yakeyin tsalle yana yin sama sai kuma ya kwararo ƙasa, flawers kuwa gasu nan jere abun burgewa da sha"awa, ga wasu irin karnuka masu birgitarwa ga birai daga gefe,
parking yayi sannan yace ma raihana muje, raihana tace waye zai fita kare ya cinyeshi?""" faruk yace dama kare yanacin mutane?""" raihana tace nidai bazan fita ba, yace ashe kuwa yau a mota zaki kwana?""",,,, raihana tace nidai ina nan kaje ka gama abinda kake ka dawo, faruk yace to ai nan gidanmu , raihana tace nidai don Allah banasan haka , yace wallahi mun dawo gida,
Fita muje ki gani bacci nike ji wallahi, kinga gobe idan Allah ya kaimu zanyi tafiya, kuka raihana ta fara kuma ina zakaje ?""",,,,, yace wurin aiki zan koma, muje idan mun shifa ciki sai kiyi ta kukan tunda kuka bai maki wahala fita yayi, sannan ya zagaya ya fito da raihana, tana fita wani soja ya shiga motar yaje yayi parking ɗinta wurin da aka tana da don ajiye motoci,
hannunta ya kama sukaci gaba da tafiya, duk inda suka wuce girmamawa ake, ga oga ga matar oga, ita dai batasan ko inane ba, faruk ya kawota, sai kallon faruk take amma shi baima san tanayi ba,
duk inda aka wuce raihana saita sake waiwayawa tana kallo, haka tayi tayi har suka isa ciki, har yanxun faruk yana riƙe da hannunta, suna shiga saman gado ya zaunar da ita, sannan ya fita, yana fita raihaɓa tabi ɗakin da kallo, salati kawai takeyi tana mamakin mutane ina suke samun kuɗi har suna tsara gidaje haka kamsr basa tafiya lahira, haka tayi ta juye juye tana kalle kalle, idon ta ya sauka kan wasu jikkuna ne ko kuwa akwatina ne?""",,,, gasu nan dai sunfi 30 tana ta kalle kalle, tace lallai, haka tayi ta jiran dawowar faruk har yanxun shiru baizo ba, ta gaji da kauyancinta tayi kwanciyarta,
Shi kuma fitarshi daga wurin raihana mutane ke jiransa tun ɗaxu don hka a cikin gidan wani ƙaton holl inda aka tanada don ganawa da mutane, saboda haka yana can meeting suke, sai 1:30am sannan faruk ya taho a gajiye,
Yana dawowa ya tashi raihana, wai suje suyi wanka, raihana tace ita gaskiya batayin wani wanka yace ƙarya ne sai kinyi kuma tare dani, agogon hannunshi ya kalla sannan yace taso taso, a lokacin daya ke ɗaga ta, raihana kuka ta fara ita kunya takeji, faruk ya zazzagota daga saman gadon da kanshi ya cire mata daga ita sai bra da pant, towel ya ɗauka yaja ta suka shige ,,,
bayan sun gama wankan suka fito, raihana tace wai miyasa zamu zauna anan ne?""" faruk yace saboda nan nake zaune dama tun kafin zuwanki, raihana tace miyasa aka kaini wancan gidan ne?"",,, yace saboda lokacin bansan da aurenki ba, zuwa man yayi kuma ai kinga bana nan, wancan yafi sauƙi nace a ajiyeki acan,
Ita dai batayi magana ba, sai kallonshi take, inda taga akwatinan ya nuna mata da hannunshi yace ga lefenki can, idanuwa raihana ta zaro tare da cewa ina zani da wancan kayan kuma?"",,, yace kiyi taman gayu inajin daɗi, kuka raihana ta farayi, faruk ya jawota jikinshi yace nifa nace maki bana san wannan abun, ni nakine komai nawa naki ne, kedai kawai ki ci gaba da man addu"a kinji?""", raihana tace to , hmmmm ranar dai an gwangwaje sosai, raihana ta kara cin gidansu dan kwata kwata faruk bai sauƙaƙa mata ba,
saida aka fara kiraye kirayen sallahr asuba , sannan faruk ya ƙale raihana, tare suka shiga wanka, suna fitowa faruk ya fara shirin tafiya, saida ya gama shirinsa tsaf sannan ya bawa raihana kuɗin wanda zata riƙe , kuma yace mata akwai masu aiki zasuyi mata komai, raihana tace to, saida ya tashi tafiya, ita dai dukma kunya takeji, da zai tafi raihana ta tashi da niyar rakiya yace no basai kinzo ba, muna da yawa, kwantar da ita yayi saman gado sannan ya lulluɓeta, ya juya ta riƙo hannunshi, juyowa yayi ya kalleta, tace ina maka fatan alkairi Allah ya tsare hanya ubangiji yasa ka dawo lafiya Allah ya tsare ka da sharrin masu sharri, ngd sosai, murmushi faruk yayi sannan ya matsa kusa da ita, saida ya zauna sannan ya sumbaci goshin ta, yace ina sanki, sosai raihan , murmushi tayi batayi magana ba, wayarshi ta fara ringing ɗauka yayi ya miƙe tare da ɗaga mata hannun, yana fita yaja ƙofar ɗakin,
ita kuma raihana kuka tayi tayi tana ƙarawa, Allah ya sani ita dai batasan namiji mai tafiye tafiye, dama faruk ya tafi da ita, haka dai tayi ta kuka, har bacci ya ɗauketa,
Faruk kuwa yana fita, an haɗa motoci dan haka shi kaɗai ake jira, yana fitowa aka buɗe mashi mota ya shiga sai airport, haka ya tafi da maraicin raihan,
****
Watan faruk ɗaya da tafiya amma har yanxun baiyi waya da raihana ba, raihana kuma an wani goge anyi kilinar an wani zama "yan gayu, idan ka ganta baka gajiya da kallonta, ita matsalarta tana so farida taxo amma batama san sunan anguwar ba, kuma ita bata da number faruk haka dai ta haƙura amma tace mata insha Allah idan ya dawo zata xo
Raihana zaune an wani kashe saman kujera , tana ta tunanin duniya iri iri, hafsat ce ta shigo cikin farlon tare da sallma, raihana ta amsa amma bata daga inda take ba, kuma ba baki ta saki tayi dariya ba, tunda ta ansa sallamar ta basae dan tasan ƙarshe wulaanci zata mata,
zama tayi bayan ta zauna tace ma raihana inayini?""",,, raihana tace lafiya qalau, hafsat tace yaya ya aikoni, raihana tace uhum, hafsat tace yace zaiyi magana dake, raihana tace faɗa man number zan kirashi, hafsat ta karanta mata, daga nan bata sake magana ba, hafsat ta gaji da zaman ta, tace ma raihana sai anjima, tace to, daga nan bata sake cewa komai ba, saida hafsat ta tafi sannan ta tashi ta tafi ɗakinta don kiran *Faruku*..................
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*Page* 4⃣2⃣
*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*MEELAT MUSA*
*Gaisuwa ta musamman gareki ya sayyada, mujadda, malama, hafiza, kamila, ustaziyya, hajjajju Rabi Musa Alkairin Allah ya isoki har cikin bargon baccinki*
*Ban manta dake ba Ƙawata Asmeenat Xeeyan Alkairin Allah yakaimu ranar 1/1/2018*
*Wannan feji nakune masoya littafin Zawarci ina tare daku dan kune alfahirina, farin cikinku shine maudu"ina, ina kaunarku sosai*😎
***
*SHAWARA GA MAZA* :• Don Allah don annabi ku riƙa riƙe matanku cikin daraja da mutunci ku tuna fa mata marufar asirinku neeeeee😉 domin duk kyan gida da tsaruwarsa idan akace babu mace a cikin gidan ya zama kangoooo☺ don ko "yan uwanka bazasu riƙa zarya a cikin sa ba, saboda gudun zargi, kada ku wulaƙanta matanku ku rinƙa gani dole tayi maku abu kuna ganinta kamar baiwa,,,,,
To wallahi ba dole bane, saidai kawai tayi don kyautata da kuma neman aljannarta don cewa akayi , idan kun auri mata komai kuyi masu, ku ciyar da ita, ku shayar da ita ku tufatar da ita😌, abinkin da in kunfita kun nemo mune muke girka maku dan tsaron lafiyar🤓 don kuma kuci mai daɗi hankali kwance, kunsan girki iyalikune duk wani koyi munayin koyi da ma"aki S. A. W
To manzan Allah yana zama yayi wasa da dariya da matansa yana tayasu aiki a cikin gidansa ya lallaɓa matansa baya bari suyi fushi baya girman kai, bayacewa shi annabi ne sai komai anyi masa, manzan Allah yana ɗauko kaya daga kasuwa ya kawo har gdansa , manzan Allah yana huɗɗa da talakawa da masu kuɗi da miskinai baya ware wani yace da wannan zaiyi harka, bazaiyi da wancan ba, fiyyen halitta kenan,
Kai kuma ka gama wasa da dariya a waje sai ka dosa gida ka haɗiye rai kamar wani mala"ikan mutuwa,🙄 waikai kada mata suga fuska su rainaka , to raini na nawa kuma?"" ta gama karewa halittarka kallo da daddare., kayi faramfaram kayi wasa da dariya da iyalinka idan kuna cikin nishaɗi da raha kuyi "yar goyo kuyi wasan "yar ɓurum ɓurum ,ka rufe idonka ko ta rufe nata , idan ta kamaka tayi tsalle tana murna ta kamaka,
Kuyi ƙwallon ƙafa, kuyi wasa kuyi rawa tare kuyi "yar tseral, idan ta tafi kicin ka bita tana aiki kana taimaka mata da wasu abubuwan idan yarane daku ka shiga cikin yaranka su sake dakai ka taimaka mata wurin shirin makarantarsu ita tana haɗa break kai kana sa masu uniform, ka taimaka mata wurin basu break ɗin su shaƙu dakai so soka su rinƙajin kaunarka a ransu duk inda suka shiga su rinƙayi maganar Abbansu, duk abinda kayi wa iyalinka ka wadata "ya"yanka da matarka da sutura, kada kai kana fita fess fesss 😇 su suna fita kamar almajirai, wallahi jama"a rainaka zasuyi😔 za,a daina ganin girmanka,
yaro baya mantuwa duk abinda kayi masa yana ƙarami bazai manta ba, duk yanda ka kula dashi da wahalar daka sha akanshi da yadda ka tsaya masa wurin iliminsa yana sane, wata rana sai yayi maka gata, haba bawan Allah ɗanka ne fa, kuma amana Allah ya baka,
Mata don Allah mu kula kada dan an auro mu munxo mun tarar da ɗan da babu uwarsa a gidan mu shiga mu fita mu raba ɗan nan da ubansa, kece kullu masa wannan sharrin kece ƙulla masa wannan makircin, harsai kin rabasa da ubansa, uban ya wulaƙanta masa rayuwa, ƙarshe yaron ya zama ɗan iska, saboda bai samu gatan da zai gyara masa rayuwa ba, kada mu "yan uwa, akwai ranar da zamu mutu , a gama a haɗa ka za,akaika kabari taku ɗaya na ƙafar ɗan adam za,a zana ayi ta haƙawa duk kibarka duk kaurinka a taku ɗayar nan za"a saka ka, bafa za"a ƙara maka ba, a mayar da ƙasa a rufe jama"a su juya su tafi a barka shikenan ,
Suna juyawa sun fara tafiya za,s dawo maka da ranka, """" tashi ka bisu""" ina zaka iya motsi ƙasa ta gama riƙe ka gam?" kaga mala"iku masu firgitarwa wanda girmasu bazai musultu ba,
suyi maka tambayoyi , waye ubangijinka waye annabinka ?"" idan kayi shiri babu amsa su ɗaga guduma su rotsa maka, saboda tsanin duka sai ka nutse a ƙasa har kaje ƙasa ta bakwai ƙasa tace , """fito fito munafikin Allah bazan ɓoye wanda ya saɓi ubangiji ba, """" ta bultsoka kafin ka gama fitowa ƙashinka ya gama gurgujewa , haƙarƙarinka kana dama ya ɓullo na haggu sun karairaye sun gama gutsin gutsin amma a haka za,a sake mayar da halittarka aci gaba da maka tambayoyi,
Allah ka kiyashemu ka nufemu da aikata alkairi Ameeeeeeen,,,,😭🙏🏻
***
*ZAWARCI*
*T*ana shiga ɗaki saman gado ta haye, saida ta kwanta sannan ta fara lalubar number faruk, haka ta shiga ta ƙari ringing bai ɗauka ba, sake kira tayi, shima bai ɗauka ba, saida ta tsinke sannan ya biyo kiran a karo na biyu,,,,,,,
Raihana ta ɗauka da sallama ta fara magana, bayan ya ansa ne, tace Raihana, murmushi yayi sannan yace ai na gane, ya kike?"",,,,, tace lafiya qalau, yace bakiyi maraicin mijinki ba?""",,,,, raihana tace nayi mana, yace gaskiya bakiyi ba, tace miyasa banyi ba?""",,,,, yace da kinyi aida kin kirani mana, tace ai banda number ka, yace ni na damu ke na kiraki inji lafiyarki,
raihana tace lafiya qalau komai , amma inajin babu daɗi saboda baka tare dani, dariya yayi sannan yace nima nayi missing naki sosai, nayi missing ɗin bargonki , kullum sanyi baya barina ina bacci , raihana tace kai nima duk haka nakeji, yace da gaske?"",,,, raihana tace sosai ma, yace to kina so na?"",,,, bata bashi ansa ba taji an banko ƙofa da ƙarfin tsiya,
da sauri ta miƙe gabanta ya fara faɗuwa don ganin wanda ta shigo ɗakin, tabar wayar a saman gado shi kuma sai fama hello yake, lallai wato har kin samu matsayin da Faruk zai ajiyeki a gidan nan ne?""",,,, gaban faruk ya faɗi jin muryar momy, raihana yaji tana cewa Momy sannu da zuwa, momy tace sannu da zuwan uwaki,
Kinxo kin wani bi gado kin lafe kin samu gidan gayu uwarki na gidan haya, hada wani kwanciya saman gado da uwar wa kike wayane?""",,,,, cikin ladabi raihana tace da faruk, momy tace umm lallai, to miyake cewa?""",,,, raihana tace yace ina lafiya?"",,,,, nace lafiya qalau nake, sai yace mi?"",,, raihana tace sai kikax xo ,momy tace to kira man banzan inji,
saboda ke harsai an taso man ɗiya daga gidan aure?"",,, wato ke kina ɗakikin ki kin zauna ki samu lada, ni kuma ɗiyata taxo ta samu zunibi ki shiga aljanna tawa taje gidan wuta, raihana tace momy kiyi haƙuri don Allah,
tsaki tayi sannan tace to bani wayar dan ubanki, ni nama barki ki aihu gidan nan?"",,,,,, bani wayar, da sauri , faruk ya kashe kiran, ita kuma ta ɗauki wayar ta miƙawa momy,
ansa tayi sannan ta duba number faruk ɗin, tace ummm lallai lifepartner ko?"",,,,, to idan na raba ku kuma ya zai koma?"",,,,raihana tayi shiru, momy ta fara zagaya ɗakin tana ɗan ɗage ɗage, wato da nace kada yayi maki lefen nan saidai yayi?""",,,,, kam kenan ba a bakin komai nake ba?"",,,,,, to wuce mu tafi dan ubanki a gidana zaki koma da zama,,,,,,,
kallo raihana tabi ta dashi sannan tace momy yace kada in fita, tsawa ta daka mata sannan tace munje dan uwarki"""",,,,,, raihana ta ɗauki hijabinta tabi bayan momy zugui zugiii, drivern momy yajasu har gidanta.........,,,,,,,,
Ajiyar zuciya faruk yayi sannan yace kai momy ta shiga rayuwar yarinyar nan mi raihana tayi mata ne?"",,,,,, lallai koma miye hafsa ce tayi munafincin amma lallai zatci ubanta wallahi,
suna isa gidan momy, bayan sun fito daga motar wata yayar momy suka gani, tace haba ni na gaji da jiranki har zan tafi nazo bakya nan, momy tace E naje inci uwar yarinyar nan, tace wace yarinya,?"""""""",,,,,,,, juyawa tayi ta nuna mata raihana, tace ina kika sako ta ita kuma?""",,,,,,,
momy tace matar Faruk ce, tunda ya auri tsinanniyar yarinyar nan baida zama lafiya, gaba ɗaya ta burkuta man hakalin ɗa, dan ubanshi har sawa nayi ya saki ɗiyar nan ashe ɗan iskan yaron nan bai saketa ba,
waisai ya rubutu kiyi haƙuri raihana ki zauna a gida idan komai ya daidata zan dawo dake, tana maganar tana taɓe baki ne, yayar tace haka ne?"",,,,,, momy tace E, tace ki rufa ma kanki asiri kada ki kuskura ki shiga rayuwar ma"aurata idan har kikace wannan halin zakiyi haƙiƙa rabo dai aikaki lahira,,,,,,
Cikin bala"i momy tace ai nice rabo kuma saina raba wannan ɗan iskan aure, yarinya tabi man ɗa ta kanannaɗe kamar masifa, duka auren wata biyu da satittika amma har idan baiyi waya da ita ba, zai taso ma ɗiya daga gidan aure takai mata waya, saboda ya raina nasu auren,
da nayi mashi magana nace duk ina masu gadi bazaice sukai wayar ba?"",,,, sai yace wai kada suje su gane mashi mata, sai ita hafsat da mijinta baya kishinta?"",,,,,, to wata biyu kenan, ina ga tayi shekara ko ta aihu?""",,,,,
Yayar momy tace keda ba ruwanki faruk kuma ba ƙalle bane, mata nawa ya aura?"",,,,, ke zaki nuna mashi matar data dace dashi?""",,,,,,,,tunda ya auri wannan ki barshi kiyi mashi uziri, da kanshi zai saketa dan wannan yarinyar ni na bata wata huɗu badai faruku ba?"",,,,,, hmmm dan Allah ki barta, momy tace to wallahi saidai in kaita gidan uwarta can idan ya dawo zai saketa,
Tace kedai barta ta koma gidanta, momy cikin bala"i tace gidanta?"",,,,, harma gidan ya zama nata kenan?"",,,,,,, yayarta tace towai ke wannan masifar duk ta miye?"",,,,,, momy tace koma ta miye wallahi yau gidansu zata kwana, aje can ayi wanka a bayin tsakar gida,
da safe abinda za,aci ma sai yayi wahala, aje kwana biyi baza,asha AC ba, ɗakin uwarki ko fanka babu, bare ledar tsakar ɗaki wallahi bansan ki, bako wani dalili yasa bana kaunarki ba, saboda kawai ina ganin zaki rabani da ɗana, dan na tsani auren zawara, saboda idan ta kama namuji batai mashi sauƙi,
da yana da mata nasan kila yanxun da kinyi waje da ita, wuce mu tafi dan ubanki, yaya momy tana mata magana amma ina, tace wallahi sai raihana ta kwana gidansu, haka ta tasa ƙeyarta suka shiga mota gar ƙofar gidansi takaita, tace a fita yau akwana cikin sauro, haka raihana ta fita jiki a sanyaye, sannan momy ta wurga mata wayarta,
Su momy najan motarsu raihana taga gwaggo tsaye gabanta, wata irin dariya gwaggo tayi tare da tafa hannu, tace an ƙara dawowa?"",,,,,,, ai na gaya maki babu ke babu zaman aure, "ya"ya masu gata ma basu tafi gidan kuɗi ba sai ke?"",,,, ke a suwa?"",,,,,,, dariya ta ƙarayi sosai sannan tace gidan kuɗi sai masu matsayi , ta ɗaga hannunta tayi ma raihana dakkuwa, ta wuce tana dariya,
duƙawa raihana tayi ta ɗauki wayarta ta shige cikin gida, tana shiga wayarta ta fara ringing, Faruk ne, tsaki tayi bata ɗauki wayar ba, wani kiran ya sake shigowa, bata ɗauka ba, Umma dake ɗaki tace waye?""",,,,, raihana kamar jira take ayi magana ta fashe da kuka, umma da sauri ta fito daga ɗaki tana tambayar lafiya?""",,,,,,,,, ashe gwaggo biyowa tayi ta laɓe, raihana tace umma na gaji nidai wannan auren na haƙura dashi kamar kaina farau uwar miji?""",,,,, kullum da abinda zatace nayi mata?"",,,,,,,, uma tace kiyi haƙuri, ɗauki wayarki ana kiranki,
raihana tace bazan ɗauka ba umma faruk ne, umma tace to miye yayi maki?"" wannan laifin ai ba nashi bane, ɗaki kiji abinda zaice, gwaggo dake zaure tayi dariya sannan ta fita tana murna raihana ta gaji da aure, niko nace ai baki tsaya kikaji ƙarshen film ɗin ba,
Ɗaukar wayar raihana tayi, tana ɗauka abinda faruk yace mata don Allah kiyi haƙuri, insha Allah gobe ina nan zuwa, kiyi haƙuri kinji?"",,,,, raihana tace to , yana faɗin haka ya kashe, wayar,
Umma tace miye?"",,,, raihana ta faɗa mata, sannan ta faɗa mata yanda sukayi da faruk, umma tace to kiyi haƙuri ki jira zuwansa, raihana tace to,
Momy tana komawa gida, tun a bakin get take jiyo ihun zainab da gudu ta shiga gidan tana tambayar lafiya?"",,,, amma zainab sai ihu take kamar zata mutu tana sulalacewa tana faɗuwa ƙasa tana kuka mai tada hankali,,,,,,
momy tace dan ubanki lafiya?"",,,,, miye akayi maki ne?"",,,,,,,, zainab tace momy an cucuce an takaita man rayuwa an gama dani Allah ya tsine ma uwar miji marar adalci wanda bata barin surukai lafiya, momy tace waike miye?"",,,, zainaba tashi tayi taje kusa da momy sannan tace momy uwar miji takaini asibiti aka zubar man da ciki, wayyo Allahna kila ma bazan sake samun ciki ba, wayyo Allahana,
momy hankalinta ya tashi a suƙwane da sulale saman kujera tana sake tambayar a bisa wani dalili?"",,,, zainab tace momy cewa tayi na malleke mata ɗa, komai ni kaɗai yake mawa, duk nemansa akaina ya ƙare kuma tace ya sakeni idan bai sakeni ba zata tsine mashi amma yace bazai sakeni ba, ita ta gane ina da ciki shine ta haɗa kai da likita yayi man allura cikin ya ɓare saida akayi man wankin ciki, yiiiiiiiiiiii taci gaba da kuka,
yayar momy dake gefe tace to kinga ishara?""""",,,,,, tun kafin aje ko ina ko?""",,,,,,,, ke kince baki barin raihana ta aihu a gdan faruk toke ɗiyar taki ta samu ciki an zubar dashi, kuma gata tana cewa kila baza ta sake samun wani cikin ba?""""",,,,,,,,,,,,,,,,
Ya kika ji baƙin ciki yau a ranki don Allah?"""""",,,,,,momy tayi shiru, yayarta tace to yanda kikaji yau irinshi ne maman raihana zataji, wallahi ba muyi ma kanmu adalci ke ayi ma ɗiyarki gata, amma ku, kuma ku auro na wasu ku ƙuntata masu wannan rashin adalci ne wallahi,,,,,,,,
kallon zainab tayi sannan tace ya mijin naki yace ne?"",,,,,, cikin kuka zainab tace cewa yayi inyi haƙuri zaizo, yayar momy tace to Allah ya jishemu alkairi, kallon momy tayi da hawaye yake zubo mata daga idon ta, sannan tace kuka ma yanxun kika , kiyi maza ki fara tuba , yau da raihana kika sa aka saki kema taki za"a koro daga gidan aure, kiyi ta kanki ki canja rayuwa tun kafin gaddara tahau maki wadda tafi wannan bala"i,
tana faɗin haka tayi gaba, zainab sai kuka takeyi,,,,,,,,momy ma kuka takeyi,
Umma ce ta tisa raihana a gaba tana tayi mata nasiha tare da nuna mata haƙuri da jarabawa imani ne, komai yayi farko zaiyi ƙarshe kuma duk wanda Allah yaso ɗaga darajarsa to sai anjarabe shi don auna imaninsa tana bata haƙuri ta ƙara da cewa ta saurari zuwan faruk ɗin suji,
ranar dai raihana haka tayi bacci ba cikin daɗin rai ba, tunanin wulaƙancin da momy tayi mata takeyi, saida ta goge hawaye, haka tayi ta juyi har bacci yayi gaba da ita,
***
*F*aruk yana gama sallah asuba, ya fara shirin tahowa, dan gaba ɗaya ji yake kamar ya miƙa hannunshi ya ɗauko raihana, duk ta bashi tausayi dan gorin da momy tayi masu wai basu da muhallin , yace Allah sarki da wata "yar rashin kunyarce ai sai ta zage momy fess dan akwai surukai masu rashin ladabi, amma ita sai bata haƙuri take amma momy ji take kamar ana zugata, hmm insha Allah kun gama haya, aini banma san ba gidanku bane, wayarshi ce ta fara kuka, yakai dubanshi wurin wayar sannan ya ɗauka,
Sallama yayi , tare da cewa momy kun tashi lafiya?""",,,,,,, lafiya qalau ga zainab nan an dawo da ita bata da lafiya tun jiya ,,,,,,, faruk yace miye ya sameta?""",,,,,,, momy ta faɗa mashi duka abinda ya faru,,,,,,,, salati yayi sannan yace to yanxun miye matsalarta?""",,,,,,, momy tace aini kada ma baƙin ciki ya kasheta saboda an zubar mata da ciki,,,,,,,,,,
faruk yace an kaita asibiti ne?""",,,,,,,,, momy tace A, a, faruk yace bari sadiq zaizo yakaita , momy tace to kai sai yaushe zaka dawo ne?"""",,,,,,,, faruk yace cikin satin nan, tace to kashe wayarta tayi, """anan kunga saboda matsatsi da takura irin wanda take mashi dashi da iyalinsa yasa ya ɓoye mata wani abu"""",,,,
bayan ya gama wayar ne, ya kira raihana, ita kuma cikin bacci taji waya tana ta ihu , don haka a gajiya cikin yanayin bacci takai hannunta inda takejin kukan wayar ta lalubo ta ɗauka, a kunnenta ta kara, tare da cewa hello cikin maganar bacci,
shi kuma cikin sigar jan faɗa yace in sani hankalinki kwance kina bacci kinajin daɗin ki ko?"",,,,,,,, uhum tace sannan tace bacci bafa wani daɗine dashi ba, kawai ma dan yana ɓarawo ya saceni , yace to gani nan zan taso yanxun insha Allah, tace to Allah yasa ka iso lafiya ubangiji ya tsare hanya, yace amin, ta kashe wayar,
tana ajiyewa wani kiran ya sake shigowa, sake jawo wayar tayi ta ɗauka tare da karata a kunnenta, tace ranka ya daɗe miye?"",,,, murmushi yayi sannan yace na mance bance maki i love u ba, murmushi raihana tayi sannan tace ngd, ta sake kashe wayar,
murmushi faruk yayi sannan yace anya yarinyar nan tana so na?""",,,,,,, tsaki yayi sannan yace bara in sake kiranta sai tace man tana so na, kirane ya shigo cikin wayarshi don haka yana dubawa ya miƙe tare da ɗaukar wasu takaddu yayi waje,
momy kuwa tana can ta shiga tashin hankali , saboda abun zainab yaci tura kuka take tana ƙarawa saidai ta faɗi dan duk jiya batayi bacci ba, baƙin cikin an zubar mata da cikinta takeyi,,,,,,,, momy tayi rarrashin duniya amma zainab sai wani ɗauke nunfashi takeyi kamar zata bi cikin ta iskoshi,
momy wayar faruk ta kira, number busy ta kira yafi babu adadi amma maganar ɗaya ce, user busy, haka ta haƙura ta zauna tana sauraron ikon mai sama"u,,,,,,,,,
sadiq kuwa sai ƙarfe 10:09am ya iso gidansu faruk , don haka yana zuwa babu ɓata lokaci momy suka kamo zainab akai asibiti da ita, niko nace candai,
Shi kuma faruk sai 9:08pm ya shiga cikin gidanshi tare da motocin da sukayo mashi rakiya, ko parking ɗin kirki ba,a gama ba, ya fice daga motar burinshi kawai yaga raihana,,,,,,,, yana shiga ɗakinta ya nufa, yana ayyanawa wasu abubu a ranshi,
yana shiga yaga gado babu kowa, toilet ya duba bata nan, A,a dubawa yayi ko ina babu raihana, wayarta ya fara kira, bayan ta ɗauka ne, yace kina ta ina ne haka?""",,,, raihana tace to ai ina gida!"""""",,,,,,, wane gida?""",,,,,,, tace ina gidanmu, yace gdanku kuma?""",,,, wannan wace irin magana ce kuma?""",,,,,,, raihana tace ba wata magana bace, kayi haƙuri , ta kashe wayarta, tsaki faruk yayi sannan yace wai yaji tayi?""",,,,,,,,,,, ai sai kije kiyi tayi ba nace kiyi haƙuri ba, haka yayi ta sabbatu kamar raihana tana kallonshi, danshi baisan momy ta korata ba, kawai dai abinda yaji tana mata gorin gida,
tsaki yayi sannan yace lallai inbar abinda nake in taho saboda ke, dan ƙarshen ki wulaƙanta ne, shine zaki tafi gidanku?"",,,,,,, hmm ni ban iya biko ba, nayi na farko tunda nine nayi laifi amma yanxun bansan abinda yasa kika tafi ba, sai ayi maki uziri muga,,,,,,,,,,
Umma tace ma raihana cewa yayi zaizo ne?""",,,,, raihana tace barshi umma wani fushi fushi yakeyi ma, umma tace to ya yace maki?""",,,,,, raihana tace baice komai ba, Umma tace kirashi to kic......,,,,,, bata ƙara maganar ba raihana tace don Allah umma ki barshi, ai cewa yayi zaizo baizo ba, barshi,,,,,, tou pha, abunda dai duk kowa ya kasa ba kowa uziri,,,,,,,,,
tsaki faruk yayi sannan ya sake kiran raihana, bayan ta ɗauka yace waike da kika tafi mi akayi maki ne?""",,,,,,,,,, raihana tace ba komai, yace momy tace wani abu ne?""",,,,, raihana tace tace inxo gda sai ka dawo,,,,,,,,,,, faruk yace dagashi fa?""",,,,,,, tace haka aka tsaya, yace to yayi kyau,,,,,,,,,,,,,,,
Likita ya shedawa momy cewa lallai zaiba ta rage damuwa idan ba haka ba, lallai zata jawa kanta matsala, ya ƙara da cewa tayi haƙuri ubangiji zai bata wani, cikin kuka zainaba tace ciki fa?"""ɗana ?""",,,,, nasha wahalata sai a zubar man da zalinci?""",,,,,,,,,, sai kuka takeyi ganin abun na zainab ya zama hauka yasa likitin fita yabar ɗakin, dan ana kwaɓa kai yana ƙara hawa,,,,,,,,,,,,,,,,
wani tunani faruk yayi don haƙa kiran raihana yayi bayan ta ɗauka yace kiyi haƙuri insha Allah da safe zanzo, raihana tace to Allah ya kaimu, yace amin , sannan ya ajiye waya, shawarar daya yanke itace lallai zai ɗauki raihana kawai yabar garin da ita, har momy ta sauko dan baisan abinda raihana tayiwa momy ba, haka dai ranar ya kwana saidai ya saƙa ya kwance,
***
*Y*ana tashi da asuba, wanka yayi , yana fitowa wanka wayar raihana ya kira cewa tayi sauri duk abinda zatayi yana zuwa gida yanxun nan, yana faɗin haka ya kashe wayarshi, ya wuce masallaci,
Umma kuma tace waye yake kiranki ne?""",,,,,,, raihana tace Faruk ne, Umma tace lafiya?""",,,, raihana tace wai yace in shirya yana zuwa yanxun, umma tace to tashi ki shirya tunda baki san abinda zai kawo shi ba..............................
Copied By
YAYA HAYAT
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
Cool novel, makeup and kitchen2⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen3⃣)
WHATSAPP NO:
+2349030159301
[1/8, 9:44 PM] Jamila Musa Ws: 💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*Page* 4⃣3⃣
*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*MEELAT MUSA* 🌹
***
*MACE TA GARI*:• Abokin zaman ki bazai taɓa yiyuwa ki sameshi 100% ba, don haka zai iya kuskurewa, rayuwar Aure zo mu zauna ce kuma zo mu ɓata saboda haka ba kullum ne za,asha zuma ba, Rayuwar aure tana buqatar haquri juriya da yiwa juna afuwa, Abokin zamanki yana da halaye biyu , mai kyau da marar kyau, idan yayi miki marar kyau ɗin toh ki hararo ɓangaren mai kyau ɗin yin hakan na iya sanyaya miki rai ya kuma rage miki raɗaɗin damuwarki,
Babu yadda xakiyi ki samu abinda kike buri a xaman aurenki 100% domin kuwa a duniya kike rayuwa ba"a Aljanna ba, duk halin rashin jin daɗin rayuwar aure da kikeyi da abokin zamanki akwai wayanda nasu yafi naku muni don haka saiki godewa Allah ki kuma miqa lamuranki gareshi, zaman lafiyar rayuwar aurenki tana buqatar agaji daga wajen Allah saboda haka ki rinqa saka shi a cikin addu"o"inki,
zaman aure yana buqatar sirri saboda haka ki taqaita bayyana matsalolin gidanki ko daga waliyyenki ne, Acikin makusan tanki bazai rasa maqiyan ɓoye ba, da masu maki hassada saboda haka bayyana matsalalin gidankina iya faranta musu sai kiyi hattara da masu baki shawara,
*Nagode sosai saƙon yaxo gareni SAFEENAH IDREES JA"EH { SAFFAH ONEE } nagode sosai da addu"a,*
Masoyana ina tare daku baki ɗayanku duk inda kuke a faɗin duniyar nan saƙon ku yana zuwa gareni ngd sosai da addu"ar ku, masu bina PC idan kunga banyi reply ba kuyi haƙuri don Allah ba ina basarwa daku bane, A, a wallahi abubuwane sunyi yawa ngde sosai da addu"a har kullum ina cewa kune *MAUDU "INA* taku har kullum mai san farin cikinku wato *MEELAT MUSA*
*ZAWARCI*
****
*U*mma tace towai ina zakije ne?"""",,,,,raihana tace Oho Umma nima dai ban sani ba, amma koma dai miye ni bama zan wanije ba,,,,,,,,, umma tace kull kada ki kuskura kiyi haka, mijinki ne idan dai har kina san samun tsira da dacewa da rahamar Allah kiyi biyayyawa mijin matsawar bai saɓi Allah ba,
Raihana tace haba Umma kullum sai ayita koroni kamar wata akuya?"""",,,,,tunda auren bayayi to a haƙura mana,,,,,,,, umma tace kiyi haƙuri don Allah komai yayi tsanani sauƙi bayansa, don haka tashi kibi umarnin mijinki kamar yanda yace, maza kije ki shirya,,,,,,,,,
Miƙewa tayi tare da zuwa ta ɗora ruwan zafi dan tayi wanka, alwallawa tayi ta shiga ɗaki don gabatar da sallah asuba,,,,,,,,,,
Faruk yana dawowa masallaci , ruwan lipton kawai yasha, bayan ya gama ya ɗauki wayarsa ya kira momy don jin yanda mai jiki ta kwana,,,,,,,,, momy tace nidai kawai yarinyar nan a fitar da ita ƙasar waje,,,,,,, faruk yace babu damuwa, ina za"a kaita ne?""",,,,,momy tace *Egypt* faruk yace to haka yayi ?"" Eh tace shi kuma yace to ba damuwa koma miye sadiq yana nan,
Momy tace kai kafi ƙarfin kaxo ne?"",,,,,, yace nima zanzo da zaran na kammala wasu abubuwa, momy tace to ina sauraren ka yace tam sannan ya kashe wayarsa,
Raihana tana gama sallah wanka ta shiga, bayan ta gama wanka ta fito ne, tana cikin shiri ne, taji wayar ta fara kuka, takai hannunta don dubawa, faruk ne, ɗauka tayi tare da sallama yace hajiyata gani a ƙofar gida, raihana tace mai zan shafa ne, yace haba kiyi sauri fito na shafa maki a mota,
raihana tace nidai don Allah A, a yace to gani nan shigowa gidan, raihana da sauri tace A, a nidai A, a don Allah basai kawani zo ba, ina fitowa, Faruk yace sai nazo gani nan shigowa yanxu, ya kashe wayar,
Raihana tace Umma zai shigo, shigowa zaiyi fa, wannan wane irin abune shiga gidan surukai tun safe?"""",,,,,,duk raihana ce take magana, Umma tace to ai shima gdansu ne nan, haba umma sai ya wani shigo kuma?""",,,,,,,,, umma tace Eh, sallamar faruk sukaji, Umma da sauri ta jawo hijabi ta saka, shi kuma yana tsakar gida yana ƙarewa gdan kallo,
Duk ya wani ɓata fuska, sai girgiza kansa yakeyi kana ganin yanda yake abun kasan ƙanƙami yakeji, ga wata kwata da tabi ta ikin gidan ƙarewa gdan kallo yayi sosai yace Alhamdulillah wannan gda kuma har mutum ya biya kuɗi ya zauna a ciki?""""""",,,,,maganar umma yaji tana cewa ka shigo mana,,,,,,,,
Yace tom, wucewa yayi ya shiga ɗakin ko takalmi bai cire ba, ya tsaya a bakin ƙofa ya tsugunna, sannan ya gaishe da Umma, bayan sun gaisa ne ya sake bata haƙuri akan abinda ya faru yace kuma shi bayanan wallahi baimasan komiye ba, amma don Allah ayi haƙuri haka bazai sake faruwa ba,,,,,,,
Umma tace ba komai, miƙewa tayi tace bara aje a kawo maku kuyi kalaci, niko kaji wani ƙarfin hali bata da ko sisi pha, amma don tana so ta nemawa "yar mutumci dole tayi su,,,,,,
umma na fita, raihana ta kallashi sannan tace sannu ɗan gaye, wato baza ka iya cire takalmin ba, saboda kar ƙafar ka tayi datti?""",,,,, kallo faruk ya bita dashi sannan yace miye haka?"",,,,, tace komai ma, amma a ɗakina ai baka shiga da takalmi sai ɗakin mamana?"",,,,,,, tunda shi ba irin naka bane?"",,,,, sai ka gaisheta da takalmi ko?""",,,,, murmushi yayi sannan yace Allah ya baki haƙuri, takalmin ya cire sannan tace zauna, kusa da ita ya matsa ya zauna, amma faruk kana ganin yanayinsa kasan baiji daɗin ajiye jikinshi a wurin ba,
bawai ƙazanta ba ne, A,a yanda komai yabi yayi wani gashi nan dai, shima tsakar ɗakin wata cinyayyar leda ce, rabi da kwata, da wannan ledar ai gara bbu, duk wani iri yakeji,,,,,,, raihana dai ta fahimci haka amma itama basarwa tayi,,,,
Kallonta yayi sannan yace mujje mana, raihana tace bakaji abinda umma tace ba?""",,,,, yace haba muje don Allah wallahi banaso gari ya waye sosai dan momy batasan naxo ba, raihana tace to koma dai miye Umma tace mu jira muyi kalaci,
kallon agogo yayi sannan ya nuna mata, 06:59am tace to miye, kayi haƙuri mana, ajiyar zuciya yayi sannan ya kwantar da jikinshi saman bayanta, tace miye haka sai Umma taxo ta samemu a haka?"",,, kallonta yayi sannan yayi murmushi yace ƙanshinki nake san inji kwana da yawa naga ke bakima yi wani maraicina ba, raihana tace nayi mana, tana magana tana wasa ido, shiko baki ya saki ya bita da kallo, ƙara jawota jikinshi yayi, sosai salon nasu ya canja kundai san ma"aurata, abun kunya ya bani shiya sa nabi umna da sauri dan gani miye zata basu...,
Umma tana fita daga gida, ashe wayar raihana ta ɗauka, wurin wani mai siyar da shayi taje, bayan sun gaisa tace don Allah yakubu ka riƙe wayar nan ka bani shayi, da biredi a toya man wainar kwai, a komai ma dai a bani, yakubu ya anshi wayar ya duba, sannan yace ki riƙe bara a haɗa maki idan kin samu kin kawo,
Godiya umma tayi , ta jira ya haɗa mata duk abinda take so, sannan aka kulle mata a leda tayo gida, tana zuwa, ɗayan ɗakin ta shiga, ta kira raihana, ta fito, wuri ta kawo komai a zuba, sannan tace taje takai mashi,
bayan takai faruk ya ɓata fuska yace shidai ya ƙoshi, taɓe baki yayi sannan yace amma ke kiyi sauri ki gama mu tafi, raihana tace to idan har bazayi kalancin nan a gidan nan ba, kayi tafiyar, murmushi yayi da gefen bakinsa sannan yace to muje, ruwan tea ɗin kawai yasha, ita kuma raihana itama komai ɗan kaɗan taci, tana fita daga ɗakin faruk ya ciro wani coculate ya saka baki, shidai duk wani iri yake ji, kai amma suna da haƙuri, miƙewa tsaye yayi ya saka takalminshi, ya fita tsakar gida,,,,,,,
yana fita ita kuma ta fito daga ɗakin da umma take zaune, tana zuwa kusa dashi yace ki sameni ƙofar gida, tace to, ɗaga muryarshi yayi tare da cewa Umma mun wuce mun gode sosai, umma tace babu damuwa,,,,,,,,,,,,
Yana fita umma ta shigo ɗakin, raihana tace umma zamu tafi, umma tace to Allah ya tsare na gaba, ta miƙawa raihana wayarta, suna ɗan maganane sukaji ana sallama a zaure, raihana ta fito dan ganin ko waye???""",,,,,,,, wani soja ne ta gani a tsaye, yana girmama ta, a matsayinta na matar Oga, ɗan rusunawa yayi sannan yace gashi,,,,, hannu raihana takai ta ansa sannan yace Umma za,a bawa, raihana tace tam,
Cikin gida ta koma, tana shiga ɗaki tace ma umma gashi, buɗewa umma tayi wata "yar ƙaramin jakane, amma kuɗi daffff a ciki, daga umma har raihana idanuwa suka zaro, kafin raihana tayi magana, kira ya shigowa a wayarta, raihana tace shine, umma tace to wannan fa?""",,,,,,
Raihana tace shine yace a baki, nidai na tafi, umma tayi ma raihana fatan alkairi, raihana ta fito,,,,,,tana fitowa ganin motaci masu yawa a ƙofar gidansu yasa taji wani iri, kundai san irin baka saban nan ba??"",,,,,,,to irinshi raihana taji,
Ga kuma wayarta sai kuka takeyi, ɗauka tayi sannan tace ma faruk nidai gaskiya bana iya fitowa ni ɗaya, dariya yayi sosai, sannan yace kauyissss cikin sigar wasa wasa yayi mata maganar dariya tayi sannan tace kauyisss ba amma kuma matar wayisssss, don haka nidai bazan iya zuwa ba wallahi, daga cikin mota yake hangota zauren su, dariya yayi sannan ya ɗaure fuska ya fita,,,,,,,niko nace maza da fuska shanu aka sansu,,,
Yana zuwa inda raihana take baiyi magana ba, hannunta kawai yaja suka fito daga gidan, suna ƙoƙarin shiga motane ta hango gwaggo, kallon faruk tayi wanda shi kuma sai ƙoƙarin ta shiga mota yakeyi, don hankalinsa ba wurinta yake ba, cewa tayi tsaya mu gaisa da mutane, yace tam, ya saki hannunta,
Tace kaima ai dakai za,ayi gaisuwar ne, yace waye zan gaishe?""",,,,,, raihana ta ɗan buɗe idonta, sannan tayi wani ɗan sheganta taka da harshenta, tace kalli can, tana nuna mashi da hannu kallon inda take nuna masa tayi sannan ya maida dubansa wurinta yace waye ita?"",,,, murmushi raihana tayi sanan tace kai tare da buɗe idanuwanta duka matar bbana ce, murmushi faruk yayi sannan yace "yar baƙin ciki dai, ɗaure fuska raihana tayi cikin sigar wasa, a daidai lokacin da take cewa gwaggo ina kwana, kallonta gwaggo tayi sannan ta bushe da dariya,,,, tace,,,,,,,
Mi kikayi wa gwamnati taxo kamaki tun yanxun?""",,,,,, murmushi raihana tyi sanan tace to kindai gani, gadai sirikin naki ku gaisa,,,,,, tace faruk ga ga gwaggo kallonta yayi sannan yace sannu, ina kwana?"",,, kasa ansa gasuwar tayi dan lallai ta gane fuska, cikin girmamawa gwaggo ta gaishe shi, bayan sun gaisa ne, faruk yayi wa gwaggo bulala da ruwan kuɗi,,,, arrrrrrrr gwaggo anga kuɗi aka wani gigice, faruk yaja hannun matarshi aka wani shige mota cikin gdan baya aka wani kashe, suna shiga driver yaje, sauran motocin suka rufa masu baya, tuni suka ɓace dag wurin suka barɓaɗe wuin da ƙura,
Gwaggo sai ƙara kallon motocin take har suka ɓace, sanna ta farfaɗo daga wannan tunanin ta tafi duniyar jinjiyar dukan ruwan kuɗin da faruk yyi mata haka taja jiki a sukwane tayi gda cike da mamakiyossssssssssss,,,,
Umma kuwa kuɗin ta fiddo ta irga ta tusa ta durza ta muza ta jajjagasu har ta gaji da lissafi don haka ta tattara su ta ajiye, dan lussafin yayi mata yawa, kuɗin yakubu kawai ta cire ta fita dan kai mashi haƙƙinsa, bari inbi su raihana, amana takai maki amaryar faruk nace ayyyyyy tafiyyyyyyyyyyyya,,,,,
tafiyar suke sosai sai ɓarin wuta suke bisa titi kana ganinsu kasan gwamnati ce da ƙafafuwanta bisa kwalta take tafiya,,,,,,,,,,,,,
suna isa birnin tarayya, faruk bayan suna ajiye raihana a gida ya wuce office, yana fita raihana bata tsaya wata wata ba, ta haye gado tayi kwanciyarta dan bacci ne a idon ta sosai,,,,,,,,,,,,,,
Faruk kuma a office wani abokin shine yake tayi mashi shegan taka, yace lallai yau tunda raihana taxo har gida sai yaje ya ganota, kallonshi faruk yayi sannan yace wace raihanar zaka gani ne?""",,,,,, yace madam raihana, murmushi faruk yayi ya kalleshi amma baiyi magana ba,,,,,,,
ita kuwa raihana tana tashi bacci wanka tayi amma bata san kayan da zata saka ba, don ita bata taho da kaya ba,,,,,,,, wayarta ta ɗauka ta kira faruk, bayan ya ɗauka suka gaisa tace mashi ya Office?""",,,,,,yace alhamdulillah, tace sannu, yawwa inji faruk, sai ta kasa magana kuma""""",,,,,, sai tace dama nace bara in maka sannu, yace yawwa ngd, yana faɗin haka ya kashe wayar,
Raihana tace tou pha, to yanxun ya zanyi?""",,,,,, niko nace Oho maki,,,,,,, wurin kayanshi ta nufa ta fara bubbuɗewa sai ɗaga wa take ɗaya bayan ɗaya tana zazzagawa, dariya tayi sannan ta ɗaga wata baƙar jallabiya, tace Allah ke zan saka, ɗauka tayi ta zumbula, sannan ta tattara kayan ta gyara su ta mayar,,,,,,,,,,,
tana gama mayarwa tashi tayi ta matsa gaban madubi ta kalli kanta tayi murmushi sannan tace kuma naɗan yi kyau ba laifi, murmushi ta sake yi sannan ta kashe idon ta ɗaya, da harshenta tasa ta laso leɓonta ta ɗan ɗaga girarenta sannan ta sake lumshe ido ɗaya tayi juyi, da gudu kuma tayi parlour kamar wani yana kallonta,
Tana zuwa zama tayi saman kujera 1seater taɗan harɗe tana maganar zuci,,,,,, ,,, zaman ya isheta ta ɗauko wayarta tace umm bara in kira zulaihat yau muyi zuminci, adaidai lokacin data fara kiran wayar,,,,,,,,,,,
saida ta kusa tsinkewa sannan ta ɗauka, cikin isa zulaihat tace hajiyata yadai?""",,,,,,raihana tace ke bansan sakarci kina ta wani mammatse murya ba mai gdan bane,,,,dariya zulaihat tayi sannan tace shegiyar mata ai koce dole ne inɗanja zare, wallahi baki da kirki, raihana tace me nayi kuma?"",,,,,, tace baki zuminci nazo gdan ki kwanaki bakya nan, raihana tace Allah sarki, zulaihat tace kuma bayan wani lokaci na sake dawowa baki nan, raihana tace lallai,,,, zulaihat tace kila zanzo cikin satin nan tunda kin tuno dani,,,,, raihana tace yanxun ma idan kin sake zuwa bana nan, zulaihat tace kinje ina ne?""",,,,, raihana tace saidai mun haɗu,,,,zulaihat tace to Allah ya haɗamu da alkairi, fira suka ɗan taɓa tare da zaulaya dai irin tasu ta ƙawaye aka ɗanyi ma juna shegantaka kundai gane ko hajijoyi?"",,,,,,,
bayan sun gama firan ne, ta kira farida, bata ɗauka ba, tace to ke kuma umma laisal handasetdana kiraki nace munxo lafiya,,,, haka dai taɗan zame saman kujera ta ɗora hannunta saman goshi ta rufe idanuwanta, ko tunanin mi takeyi Oho naga dai hawaye nata zubowa daga idonta,,,,,,,,,
har Faruk ya shigo raihana bataji zuwanshi ba, duk maganar da yayi inawo an tsunduma cikin tunani, zama yayi kusa da ita, yana kallonta ita ko ta dage sai shashsheka takeyi tare da shan majina, irin dai na masu kuka,,,,,,, ɗagota yayi da sauri ta buɗe idonta, tare da goge hawayenta, rumgumeta yayi sannan yace kukan miye?"""""",,,,,
murmushi raihana tayi sannan tace waye yace inayin kuka?"",,,,,nine na gani, inji faruk,,,,,, raihana tace to yaji ne ya zubar man a ido ai,,,, kallonta yayi sannan yace nine ma yajin dariya tayi sannan tace aiko da bazan bari a shanyeka ba, murmushi yayi sannan yace wannan rigar fa?"",,,,,, dariya raihana tayi a daidai lokacin data zame jikinta daga nashi,,, ta fara tafiyar rainin hankali tana cewa to ai ban samu wasu ba, bayanta yabi yana cewa ke zo nan,,,, shiru tayi ta shige ɗaki shima yabi bayanta..................,
****
*T*o zainab mai ciwo dai an samu ɗagawa zuwa egypt don ganin likita,,,, kuma duka momy yaranta ta tattara ta tafi dasu,,,,,,
Faruk yace ma raihana ta shirya suje ganin zainab tace ita dai bazata samu zuwa ba, ya tambayeta dalili amma ta nuna mashi ba komai haka yayi juyin duniya amma tace ita dai yayi haƙuri baza ta samu halin zuwa ba,,,,,,,,,, ya gaji da lallaɓata yace kada Allah yasa kije idan kinje ma bana so ban gode ba kuma bazan gode ba,,,,,, raihana tace to kuma duk miye yayi zafi,,,,, tsaki yayi yabar ɗakin,,,,,,
Bayan ya fita raihana tace ikon Allah, shi bazai gane ba,,,,,, na fito fili in nuna mashi matsalar mamanshi?""",,,,,,yanxun muna zuwa ta ganni sai kuma tace sai faruk ya rabu dani , tsaki tayi sannan ta miƙe ita ta bar ɗakin,,,,,
ɗakinshi ta sameshi yana waya, bayan ya gama tace don Allah kayi haƙuri duka nan banga abin fushi ba, wani irin kallo yayi mata wanda yasa ta fita ɗakin da sauri,,,,,,,,,,,,
Ko da daddare raihana tace mashi ga abinci daka mata tsaywa yayi yace ta fita daga harkarshi, idanuwa raihana ta zaro tare da cewa wannan wane iri wasa ne?""",,,,,,,, waye zai fita harka naka ne?"",,,,,,,,, yace abinci ko?""",,,, tace Eh , kanshi ya girgiza sannan ya ɗaure fuska sosai yace to bazanci ba, sai kuma miye?"",,,,,,, tace sai shi kenan, yace to a samu ayi waje mana, yana nuna mata hanyar waje da hannunshi,, ɗaukar abincin tayi ta wuce simi simi,,,, tana fita yace aikin banza, ke kin iya cewa inyi abu amma ni dan kin raina man hankali baza kiyi abinda nake so ba,,,,
Tashi yayi ya shiga wanka, yana fito yaci uban gayen shi, yayi kyau sosai, tana farlo zaune tun kafin ya fito taji ƙamshin turare, zubawa ƙofar ido tayi tana jiran fitowarshi,,,,,,,,,,,,,,,,,,
sai gashi ko an wani tsuke cikin ƙananan kaya, ko inda take bai kalla ba, murmushi tayi sannan tace ina zaka?"",,,,,,, bai kalleta ba kuma baiyi magana ba, ta sake cewa bakaji ina magana?"",,,, banza yayi mata,,,,, tashi tayi da sauei taje ta kulle ƙofar da makulli, tana ƙoƙarin rugawa yayi mata wata irin munafikar damƙa, yana rikota ya wanka mata wani irin zazzafan mari sannan ya miƙa hannunshi yace bani?"",,,, riƙe ƙugu tayi cikin kuka sannan tace wallahi bazan bayar ba saida ka kashe ni""""",,,,,, ɗaga hannunshi yayi da niyar ƙara kai mata mari da sauri ta duke sannan tayi ɗaki da gudu, a zuciya ya bita da gudu amma kafin ya kawo harta rufe ƙofa,
Dariya tayi adaidai lokacin data haye saman gado, sannan tace waini za,ayi wa zuciya, a fara fitar majalissa, kaje can kayi ta balbaɗa ni, a baka shawarar banza kaina,,,,,
Bazaki kixo ki buɗe ƙofa ba?""",,,,, tace anƙi a buɗe idan kayi fushi kaje kayi bacci, ni kike cewa idan naji haushi?"",,,, tace Eyyyy ka shaƙa ne?"",,,, nace ki fita harkata baza ki fita ba ko?"",,,,,, tace bazan fita ba,,, tsaki yayi sannan ya koma farlo ya zauna,,,, lokaci lokaci saida yayi tsaki , ita kuwa raihana wanka ta shiga, tana fito tayi shiri mai kyau saƙo da loko na jikinta saida ta bishi ta shafeshi da ƙamshi,
Wasu sheɗanun kayan bacci ta ɗauko ta saka wanda dasu da babu ɗaya ne, kallon kanta tayi a madubi ta girgiza kanta sannan tace , bari muji ya za"a ƙare?"",,,,,, ɓoye makullin tayi sannan ta buɗe ƙofar ta fita,,,,tana shiga farlo daga nesa dashi ta tsaya sannan ta riƙe ƙugunta tace gani,,, kace inxo ko?"",,,, to gani na fito bana tsoro,,,,,,,
Da wutsiyar idonshi ya kalleta, murmushi yayi sannan ya kallota dukanshi, yana kallonta tayi murmushi itama wata "yar girgiza ta fara sannna ta juya tana cewa tunda kaji tsoro saida safe,,, ta nufi hanyar ɗaki,,,,,,
Ƙara kallonta yayi sannan yace zo buɗe man ƙofa nace, raihana tace ƙofa ai baka da ƙarfin ansar makulli,,,,,,,idan kuma mutum yana jin shi sojane ya shigo ɗakina, hmm mutum wayyo, ta yarfa yatsanta alamar zaka gane kurenka,,,,,,
faruk yace ke ni kikewa wannan abun?"",,,, raihana tace anyi tunda ɓaɓatun akan kujera ya tsaya,,,, miƙewa yayi yabi bayanta, ita kuma da gudu ta shige ɗaki, tana zuwa ta soke saman gado,,,daga bakin ƙofa ya tsaya yana kallonta, tace mutum sai cika baki, idan ka isa kaxo nan kaga makulin nan,,, ta karkaɗa makullin,, dariya faruk yayi sannan ya shige cikin ɗakin,,,,,wani shu"umin kallo tayi mashi , yace ni bana san wannan abun, raihana tace ni kuma irinshi nake so..................haka kika ce?"",,,,
Zama yayi a gefen gado sannan yace to matso nan mana, kwanciya tayi sannan tace kai kaxo nan mana, murmushi yayi sannan ya hau saman gadon sosai, zata matsa ya riƙe ƙafarta, ya jawota kisa dashi, sannan yace Allah kin ɓata man rai, raihana tace to nace kayi haƙuri kai komai saurin fushi ka daina ni banajin daɗi, yace aikece ɗin , raihana tace nice ɗin miye?"",,,,,,,,, yace to naji na fasa fitar gani a gidan miye zaki bani?"""",,,,,,,,, raihana tace ba abinda zan baka kawai ka zauna ina ganinka inajin daɗi, yace to idan har kina sona ki shirya muyi tafiya tare dake,,,,,,
bana so kina man gaddama kinga idan kika ce man abu ina maki fa, bana san inga kinyi fushi,,,,,raihana tace to yiman gori, tayi maganar ne cikin wasa, dariya yayi sannan ya sake jawota, ya ɗora kansa saman ruwan cikin ta, hmmm babban take wannan karatun yafi ƙarfin rubutu na.....................
[1/8, 9:46 PM] Jamila Musa Ws: 💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
*ZAWARCI*
💦💦💦💦💦
💦💦💦💦
0 comments:
Post a Comment