*_MAZA_*
{ALLURAR GUBA}💉
_NA_
*_ASMEENAT ZEEYAN_*
*_Kyawawan yabo da godiya sun tabbata ga Allah (SW)! Tsira da amunci suk'ara dad'uwa ga fiyayyen hallita Annabi Muhammad (S.A.W)..._*
_da wannan zanyi amfani da damata na taya y'aruwata murnar kammala littafinmu KWARATA! Wanda narasa me zance da jameela Musa, (meelat) gurin fad'a mata nagode da wannan sadaukarwa da tamun..fatana ga Mrs mabuwayin sarki yabiya mata kowace irrin buk'ata da take nema Aduniya Dan Albarkacin Adadin haruffan dake cikin k'urani, ya Allah kasanyawa su ja'afar Albarka cikin rayuwarsu" kajikan magabata ka kareta daga kowace irrin masifa ta duniya" ya Allah badannin ba se Dan kana Arrahamani Rahim Ameen_
1-2
_BISMILLAHIR RAHAMANI RAHIM_
Abdullahi Fodio Road A birnin Sokoto, Unguwar tayi shiru sakamakon yau ne hutun k'arshen mako yake k'arewa, Duk da cewa unguwar ba maiyawan shiru bace, sabida zirga²r ababen hawa dake yawo a cikinta, but ba mutanen unguwar bane domin gidajen su zubin wad'anda suka martaba Biro ne (y'an Boko) wani madaidacin gida ne Wanda bashida wani bala'in girma" Amma kana dubansa kasan naira tayi b'arin hawaye A wurin Gina shi..." haka zaka tabbatarwa kanka Babu Abunda ake nema na duniya arasa a cikinsa" Gidan yayi shiru bakajin komai se k'arar Nishi k'asa², Irrin na rashin lafiya me kaifin zafi" da d'arsawa zuciya mutuwa ce mafi A'ala gareni" sabida duniyar ta d'auke bawani sauran dad'i se balao'a daban²....." daga cikin d'aki kuwa blanket kad'ai zakaga yana motsi ka tabbatar nanne nishin ke tasowa" yarinya na kwance daga gefe y'ar kimanin kwanaki sittin A Duniya" bacci take cikin aminci da kwanciyar hankali" tsayin sao'i tasoma shura k'afafuwanta da hannayenta tana wani wak'e alamar ta tashi baccin, Kamar mintuna talatin ta hau kuka kada'an² daga bisani Kuma taburkice tana fallah kuka me gigitar da hankalin duk matar da Tasan zafin haihuwa" A gigice wata matashiya ta nufo d'akin wadda Bata gaza shekaru hamsin da Aihuw., cak! tajah ta tsaya..."tare da furta subuhanallah me yake faruwa!? Jin Babu amsa tafara d'aga k'afafuwanta zuwa gurin matar da ke kwance ta yaye blanket" cikin sark'ewar murya tace Innalillahi wa Inna ilaihim rajiun! Asma'u me yasameki...!? Bata iya amsawa ba se ciza leb'e da takeyi Nononta na hagu yacika fammm yayi jajir Yana walk'iyar Azaba" jummmm matar ta zauna ta rungumota, jikinta ya d'auke dawani irri masifaffen zafi" tarasa ma me zatayi..!? se kallon nonon take da yad'auki jah Wanda Babu ko shakka wannan shi yasakarwa Asma'u zazzab'i, tana wannan tunanin Asma'u takatseta da cewa dakyal Inna lami sake ni kid'auki Deena" sakinta tayi jiki sab'ule ta tallafo Deena" ta had'a da jikinta" tana jijjigawa bayan kukan yad'an tsagaita" tace Asma'u ko naje nakira maki Dr. Jameela ne..!? Wata guntuwar k'wallah ta matse kafun tace ko tazo banida kud'in Bata, Kuma kinsan sha'anin lafiya Dole seda kud'i.."shiru Inna lami tayi kafun tace Duk da haka ai inda Kara bazatayi maganar kud'in ba, duba da irrin k'awancenku! Itama Shiru tayi na second biyar tace to shikenan je Innah.." fita tayi tare da goya Deena A bayanta" Asma'u Kuma tacigaba da amsar zogin da Allah ya aiko mata daga Daren jiya zuwa safiyar yau" Inna lami tafe take tana tunanin zuci Wai matar dake cikin wannan Daula tace batada kud'i..!? Ai ko mahaukaci yasan fad'a take" wata zuciyar tace karkiyi mamaki irre-irrensu masu Auren goggun maza da naira tayiwa zaman Dirsha basa Ajiye kud'i suna figa suke bawa masu maganin mata" b'aren zuciyar yace uhumm malamai dai Gudun Kar Amasu kishiya..." A fili ta furta hakane, da irre-irren wad'annan tunani har ta isa gidan Dr. jameela! macce Mai kirki da kawaici da nuna halin dattako. Wanda Abun yasamo Asali ne Daga Iyayenta da suka Ginata da tarbiya irrin ta Addinin musulunci" Sallama tayi A tsakiyar gidan, yaron dake wasa da kekensa ya'amsa da Wa alaikis sallam Ina kwana...!? Tace lafiya k'alau Ja'afar! Ina mamanku!? yace tana toilet" tace to tare da zaunawa saman wani d'an tudu da zai sadaka da d'akin jameelar" zamanta ke da wuya ta futo murmushi d'auke "A" farar fuskarta kana cike da girmamawa tace Inna lami kika zauna anan baki shiga ciki ba!? Itama murmushi tayi tace Babu komai" ai dama Asma'u ce Babu lafiya tace Dan Allah kizo..cikin nuna rashin jindad'i tace wayyo Allah! innalillahi Asmee na ba lafiya!? Gani nan zuwa shiyasa jiya banganta online ba" wlh da ita na kwana Araina kimata ya jiki gani nan zuwa" zataji in Sha'allahu Inna lami tafad'a tare da ficewa" Jameela tsaye tayi tarasa me kemata dad'i, itadai har ga Allah Rayuwar Asmee tausayi take Bata! Macce har macce ga diri ga wayewa, Amma tarasa gatan miji" shi ba talaka ba bare "A" Aje A babin k'addara, dan layinsu Asmee in mijinta be zamo sahun farko a masu kud'i ba" to tabbas sedai na biyu..ba jahili bane bare A kirashi da nakasashen namiji...Yana da ilmi na Addini da na Boko duba da Aikinsa babban lauyan govnatin jaha ne.... Shin ko dai Asmee nada matsala ne ta hanyar gyara shimfid'ar mijinta...!? Shin kodai Ba Auren soyayya tayi da Abban Deena ba!? Yaya za'ayi na tambayi Asmee domin intaimaketa!? Anya banyiwa rayuwarta shishigi ba...!? Haka dai zuciyar Jameela ke jera tambayoyi har saida Ja'afar yace Mamana jikinki zai bushe fa" firgigit tadawo tare da Ajiye gwaron numfashi tayi cikin d'aki A gaban dressing mirror tayiwa kanta mazauni, tashafa mai" tare da murza powder da tozali Ah idonta" tasaka A tamfarta ruwan toka me duhuwa tasanya hijab kalar Madara tare da d'aukar key d'in motarta ta fice gida...tafe take zuciyarta nata sak'e²n Yadda Rayuwar mata ke tafiya A gidajen Aure kowa tashi ta isheshi an rasa ganowa Mazan ne ko mata!? Haka har takai k'ofar gidan Asmee, tayi parking A waje sannan ta shiga gidan..."kanta tsaye tayi d'akin Asmee" kwance ta sameta Kamar ranta zaifita..ta rintse Idonta domin Duk da zamanta ma'aikaciyar jinya taji wani irri yadda Kai tsaye Nono yayi fammmm, jajir Kamar A tab'a yafashe Abunka da jar fata" cikin murya me rauni tace Asmee! Bud'e wutsiyar Idonta tayi alamar ta ganta Amma Bata iya amsawa ba...Jameelar ce tasake cewa me yasa bakije hospital ba.!? Inna Abban Deena!!? Wani zafi Asmee ta k'araji yayi kane² A ziyarceta lokacin da sautin Abban Deena yayi mata bazata A kunne domin itakam Bata Mason taji ana Kiran Abban Deena kusa da itah..." Duk da hausawa sunce ko hannunka yarub'e ba kacirewa ka yada" Jameela jin shirun yayi yawa ne taciro magani tabata ta Sha duk da cewa Bata mata bayani ba ta fahimci meyasa Nonon ke ciwooo kasancewar Nono yayi nauyi yaringa ciwooo yasama zazzab'i harda tashin zuciya Yana samo Asali ne idan k'ofar Madara ta toshe" ko Kuma garin bada maman ansamu shigar wata k'wayar cuta se ta haddasar da irrin wannan ciwooon" bayan mintuna biyar da Shan maganin bacci yad'auketa Jameela tayi murmushi da zummar inta taso hospital zata dawo tabama Asmee shawara akan yadda zata kula da lafiyar nonuwanta..."haka kuwa akayi tana dawowa nan tafara koda ta iso har Asmee ta tashi zaune tad'an ci Abunci Amma tafad'a tana rungume da Deena..."Murmushin k'arfin hali tayi dai² lokacin da Dr. Jameela ke sallama tare da fad'ar maman Ja'afar..." Na'am Asmee na" ya jikin naki..!!!? Tace gaskiya Alhmdullah na jidad'in maganin sosai tunda gani zaune akan d'uwawuna... murmushi tayi me sauti tace Ai Asmee na, laifin kine inkina ciwoooo ba kya zuwa hospital Kuma ba kya cikin Gidadawan matan da za'awayar ma Kai akan sha'anin kiwon lafiya...yak'e tayi meciwoooo akan mak'oshi tace hakane zan rik'a zuwa se tayi shiru.....kallo Jameela tak'are mata ta Aje gwaron numfashi tare da dafa kafad'arta sannan tace Dan Allah kikula kirik'a zuwa hospital ni se inga kina sakaci da lafiyar ki...." K'wallar da Asmee ke rirritawa Kar taxubo sub'ucewa tayi Amma batayi magana ba domin hartakoma ga Allah Bata manta kalaman kakarta hajiya Nana....Wanda A daren da zata rasu ta gaya mata cewa Asmee duk rintsi karki fad'awa wani sirrin zaman Aurenki domin na rantse da Rabbul izzah Babu wata macce da za tace tana gudanar da Rayuwar Aure d'ari bisa d'ari" in tagaya maki 100% tana hutawa gidan miji kid'auka labari ne tabaki na k'arya" Kuma kitunda da kalmar nan da keyawo tsakanin kunnuwan ma'aurata wato hak'uri, kiyi kokarin magance damuwarki da kanki..." Haka maganganun hajiya Nana ke dawo mata tamkar yanzu take wahayinsu gareta Jameela itakam se shafar Asmee take tana fad'in kiyi hak'uri..Dan Allah kidaina kuka wlh bansan ranki zaib'aci ba" da banyi maganar ba......" Asmee Bata San lokacin da bakinta yabud'e mata sirrin zuciba cikin kururuwa take fad'ar wlhil Azim bake kikasani kuka ba Ina son zuwa Amma inada matsala Wanda shekaru bakwai Ina Shirin maidata tarihi tak'i maisuwa Kamar yadda nake gani zan iya... yanzu kaf dubaru na sunk'are na mik'a wuya na yadda Ina cikin rud'anin rayuwa" Wanda yau takai takawo ji nake Kamar nafara yawon Karuwanci sabida mijina yazame mun *ALLURAR GUBA*......
*Muje dai muji me yayi zafi har zuciya ke rayawa Asmee taje tayi karuwanci! Anya Maza nazame ma mata ALLURAR GUBA gaskiya da sake!* Nikam ban amunce ba Akafta....
*Wasu zasuyi mamakiyous da nace se February se gashi nasaki A Watan d'aya wannan yasamo Asali ne sabida Ramadan dake dosowa*
#Comments🔥
#share🔥
[1/30, 10:58] Asmeenat: *_BRILLIANT WRITER'S ASSO...._🖊*
_{pens of freedom, home of exceptional and magnificent writer's}_
*_MAZA_*
{ALLURAR GUBA}💉
*_NA_*
*_ASMEENAT@ZEEYAN_*
3-4
Ji nake Kamar nafara yawon karuwanci sabida mijjna yazame mun *ALLURAR GUBA*..da zafin nama jameela ta d'ora tafin hannunta A bakin Asmee, kana nata bakin na furta innalillahi waInna ilaihim rajiun" haba ke kuwa karkisake irrin wannan magana Dan girman Allah" Ina ganinki cikakkiyar me ilmi!? lokaci d'aya kinaso kibadani tahanyar Furuci irrin na jahilan matan da Basu da wayewar Addinin musulunci!? haba Asmee karki sake Babu kyau kinji...." Cikin muryar kuka k'asa² tace Inshallah nadaina Abun ne yamun yawa narasa tudun dafawa...Rayuwa tazame mun kullum gwara jiya da yau, kullum baya nakeci A gidan mijina...Wanda A baya Ina samun Yana biya mun buk'atata A shimfid'a duk dacewa be sangartani da bada kud'i ba" Amma yanzu baya biya mun" shiru tayi tajah majina tacigaba da cewa wlh Abban Deena nason neman turani na Aikata mafi girman sab'o ga ubangijina yasaba mun da muguwar Jaraba tun bana iya d'auka har takai Ina d'auka yanzu ya k'aurace mun kwata² nayi magiya da rok'o har nagaji... Shiru jameela tayi kafun tace Asmee kodai kina da matsala gurin kwanciya ne...!? D'an tsagaita kukanta tayi tare da kallon jameela Ido cikin Ido" tace ba fallasa kaina nake ba Amma saduwa da Namiji Babu wacce ban iya ba..." Gaba da gaba" goho, hawan Doki, zama da sauransu" gefen ni'ima Kuma Alhmdullah nikaina nasan inada" domin sosai nake tu'ammali da wake da Albasa, Naman kaji da k'wai, da kayan fruits Dama can Abunda ke tauye ni'imar macce rashin ingattaccen Abunci nataka gagarumar Rawa" se Shan kayan mata barkatai da Matan wannan zamanin keyi garin kasamo Damshi seka k'afe to suma se Wanda nayadda dasu nake sha... inkikayi nazari banida matsalar wannan" Doguwar A jiyar zuciya jameela ta sauke kana tace Asmee kina ganin laifin ba naki bane Duba da baya Yanar biya maki buk'atar ki....!? Ba nawa bane domin tunda nasamu cikin faruq na haihu Abban Deena yasoma nuna mun hallayarsa ta Malam bahaushe...Wanda dukansu sunfi bawa dokiyoyinsu da kadarorinsu muhimmanci akan matansu na Sunnah" nayi yunk'urin kaiwa kakata damuwata Amma nuni take mun da Kacokan Rayuwar Aure hak'uri ce, har Allah ya amshi ranta" ko bukatata da Abban Deena kebiya Wlhil Azim yadda jaki ke zuwarma jaka haka yake zuwan mi" Babu d'an Aike Kamar Yadda Annabi Muhammad SAW...yabar labari cewa maza ku aikawa matanku d'an Aike lokacin da kuka had'a shimfid'a.." sanin kanki ne wannan hadisi beyi tasari ga Mazan wannan zamani ba" yafi tasiri ga turawa Domin su basa fad'awa matansu Kamar dabbobi suna aika sak'onsu kafun suje cikin Duniyar macce! Shiru Jameela tayi tanajin Asmee nazubo zance Wanda Babu k'arya hakane kaso tamanin cikin Mazan hausawa se suna da buk'ata kiji ance bud'e min inci..." Ko Kuma ke gyara! Inkuma kinsoma bacci haka zakiji mutum yadda kikasan bunsuru Abundai Babu tsari..." Wanda Arnan da ma basa Afkwa matansu ta wannan siga" Tsayin lokaci sannan Jameela tace Duk zancen ki hakane Asmee Amma zokiji A kunne ta rad'a mata wata wani sirri...lumshe Ido tayi kafun tace aini bana magana dashi tun kwana Arba'in da sukawuce...." Salati Jameela ta d'auka tace garin Yaya Asmee!? Aishi Namiji macce Bata gaba dashi domin itace me cutuwar bashi ba" shi dankin hanashi saduwa ba Abunda yamashi zafi, mata gasunan sun k'askanta kansu da k'imar da Allah yayimasu" Mazan Kuma Allah ya shirya baka shedun su se dai Anje lahira suyi bayani akan Alk'awullah da suka d'auka kafun shaidun Aure...! But duk da haka nafiso kisauke makaman yak'inki kibashi hak'uri nasan zuciyarki zata bijere ta kafe akan kece da gaskiya..." To shaid'an ne yazo maki kijah A'uziya duk lokacin da kikaji haka kuma kitabbatar kinyi Abun da nace na tabbatar Abban Deena bazai tsallakewa tarkon mu ba" murmushi kawai Asmee tayi domin itace Tasan inda dakinta ke yoyo Amma zata gwada shawarar Dr. Jameela Intaji sauk'in nonota da haka dai suka tattauna Rayuwar Auren hausawa Wanda ko wace macce nada tambon d'a NAMIJI sedai godiyar Allah....daga bisani Jameela ta tafi tare da Alk'awarin zata Aiko Abdulrrrahaman yakawo mata madarar Rak'umi, Asmee godiya tayi sosai da karamcin Jameela A gareta" sannan tadawo ta zauna ta tsunduma cikin Duniyar tunanin yadda Rayuwa me juyi ta kowace siga me tafiya" gefen Jameela ta isa gidanta da wani bak'on yanayi Tasan zuciya mugun namace" karta tura Asmee tafara Bad'ala da Aurenta domin tasan ya jarababbiyar macce keji lokacin da ta rasa dare tana wannan tunani baban Ja'afar yashigo Amma ko inda take be kallah ba bare yagane tana cikin damuwa...bayansa tabi da kallo tana jajinta mijin bahaushiya tunda haka suke Duk halayyarsu d'aya...Babu gwani wurin tabbatar da jindad'in Iyalinsa sedai ace wani yafi wani, Dan nata yafi na Asmee" yajima ciki sannan yafito Yana twari Alamar Tasan yananan but ta basar! seda yagaji Dan kanshi yace Wai me akayi ne...!? D'agowa tayi ta zuba masa Idonta kafun tace saukar yaushe...!? Bansani ba y'ar raini inbi gabanki kice saukar yaushe yafad'a da sigar wasa" tasowa tayi daga kwancen da take akan kujera tad'an fad'a jikinsa tace Banga shigowar ka ba baban Ja'afar naje wata Duniya ne! Gemunta ya tallafo yace wace Duniya ce da har zanshigo baki sani ba!? Murmushi tayi me sauti tare da cewa mushiga ciki...bayan sun shiga ya zauna ta d'ora kanta A cinyoyinsa ta kwantar da murya tace baban Ja'afar Halayyar mazan hausawa na mugun tab'a mun zuciya" su Sam basa kula da damuwar Iyalansu, suna son kansu da yawa hakan yajawo mata sun koma mazinata sabida Illar da mazajen su na Aure ke masu..." Shiru yad'anyi kafun yace menayi Kuma!? danshi A zaton shi Bulala maman Ja'afar kemasa Dan yakwana Biyu beyi harka da ita ba..." Tace bakayi komai ba ta labarta Masa halin da K'awarta keciki sosai ya jajinta Al'amarin a zuciyarshi Dan fa dagaskene maza sune ummul Aba isin shigar mata gurin bokaye...sune silar shigarsu shaye², sune silar shigarsu zinace² domin da Mazan sungyara zamantakewar Aure to fa hakkun wad'annan masifun zasu koma tarihi A cikin Al'umnah" A fili Kuma yace kitayata Addu'a Allah ya daidaita tsakaninsu..." Tace zandage mijina.."haka dai suke ta zantawa akan sha'anin......" bayan kwana biyu...misalin 11 na dare Asmee tafito wanka d'aure da towel iya cinya Tasha wasu ruwan mata" da Jameela ta aikomata tun kafun ta shanye labari ya canza A k'asanta...wata muguwar kasala ta sauko mata Wanda takeji yau ko faruq zata iya kusanta in Abban Deena be Bata had'in Kai ba....." Haka ta nufi d'akinshi A jigace koda taje Yana kan gado Yana chatting Babu wani shiri ta zare towel da kanta Idonta sunyi wani mugun kad'uwa irrin na Supper IGO....ad'an hargitse yace ke meye haka...!?
[1/30, 11:01] Asmeenat: *_BRILLIANT WRITER'S ASSO...._🖊*
_{pens of freedom, home of exceptional and magnificent writer's}_
*_MAZA_*
{ALLURAR GUBA}💉
_*NA*_
*_ASMESNAT@ZEEYAN_*
https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
_InnalilIahi wainna ilaihim rajiun" kullu nafsin zai'katul maut, Ina k'ara tayamu ta'aziya d'aya daga Member tamu dake Asmeenat zeeyan fans da tarasu Daren jiya gurin haihuwa Allah ya gafarta Mata dan Alfarmar Annabi Muhammad Allah sarki haulatu sedai suna_
5-6
A d'an hargitse yace ke meye haka...!? Kafun tabashi amsa seda ta rungumeshi jikinta k'am tahad'a wasu yawu kut" murya na Rawa sosai Tace Dan Allah kataimakeni Abban Deena, Ina neman Alfarmarka kayimun Rai ka Agajeni tan Kai nan da zance se tasa kuka...." k'asanta yakalla da tabud'e tana nuna Masa da yatsanta"... ya yatsina fuska Kamar Wanda yaga Kashi, sannan yatureta da cewa kici kayanki Ni Ak'oshe nake" wani mugun bak'inciki taji ya tokare mata wuya Amma ta kwantar da murya Dan ita kad'ai Tasan yatakeji, A kasalance Tace Abban Deena meyasa kake mun haka!? Narok'eka kadubi halin da nake ciki... Tsaki yajah sosai yahankad'eta yabar d'akin Yana magana ciki²... Rub da ciki tafad'i tana wani kuka me sauti ga wata irrn sha'awa na fisgarta batasan lokacin da ta nutsa yatsanta A farjinta ba...ta dad'e tana wasa Da Al'aurarta tana Nishi sama² sannnan tasamu nutsuwa koda tamik'e sperm Duk ya lalace komai" tsoro da tashin hankali sukayi Mata dirar mikiya" takifa kanta A guiwowinta domin Tasan hukunci da Aka tanadarwa masu Istimna'i..yinsa sab'o ne dake jawo Uk'uba da Azaba ranar Alk'iyama...tadad'e tana wanza kuka me cike Da Nadama kafun ta tashi tayi wanka tayi Alwala, bayan tafito tasanya kaya ta tada sallah tana kuka tana Istiggifari akan sab'on da ta aikata" Abban Deena Kuma nacan kwancinsa zuciyarsa nagaya Masa yabari tagane kuskurenta tunda ita da kanta taraba Shimfid'a..." Haka dai har gari yawaye" yafita Abunsa bebi kanta ba! Yabarta Daren jiya namata yawo A zuciya" tana wannan tunanin Kiran Jameela yashigo tad'auka.."but me makon tayi magana se tasa kuka tana fad'ar Nagaji nagaji nagaji" cikin murya me sanyi Jameela tace ganinan zuwa gidanki Asmee kijirani ta katse line" shape² tashirya ko karyawa batayi ba tadai had'awa su Abdul-rahaman Abunda zasuci tayo gidan Asmee" da faruq tafara Karo Wanda yau bema samu Arzikin wanka ba Kuma ga dukkan Alamu be karya ba, tayi ciki zaune tasameta Idanuwanta har sunyi jah sun kumbura" tana ganin Jameela tasake gocewa da hawaye....ta dad'e tanayi Babu me cewa komai daga bisani sannan Jameela tace shikenan ya Isa haka Asmee kinjj" tana shafa gadon bayanta" A hankali tasoma sauke A jiyar zuciya daga bisani ta labartawa Jameela yadda Al'amari yakasance A Daren jiya...."sosai ta tsorata Dan Tasan tsimin da tabawa K'awarta na Isassun matane" Kuma in har Namiji yayi tarayya da macce lokacin da tsimin ke aiki dole yasauke girman Kai Dan bak'aramin dad'i zaiji ba" tadad'e tana jajinta Abban Deena kafun tace Asmee Wai ko Auren soyayya kikayi da mijinki nafara Shakku gaskiya....!? Zaune ta tashi tace uhmmmm Jameela kiji tsoron Auren da aka Gina da tarihin soyayya, naji anacewa ba kasafai yake dad'i ba..ban tabbatar ba seda yafaru akaina....." zanbaki tarihin soyayyata da Abban Deena dakuma yadda lokaci guda komai ya sauya a tak'aice...wata safiyar Assabar da sanyin la'asar A birnin Amurica daga school d'ina nakawo ziyara A wata katafariyar makaranta Wanda A cikinta Akwai wani sashe da Ake koyarda Al'adun Arewa da harshen hausa" hakan yasa kowace Assabar nake zuwa wannan makaranta Domin sabunta yarena.. zaune nake Ina kallon yadda Turawa ke k'ok'arin koyon harshen hausa...na tsunduma sosai ganin Ina kwana batasamu gindin zama A halsunan wasu ba.." kamshin tulalen danaji yasani d'agowa da sauri...kafun fuskata ta shanye mamaki naji yace I hak'uri na katse maki tunani sister" kawar da kaina nayi gefe kafun nace ba komai Amma Ad'an musayar Ido da mukayi nagane yaro ne matashi me kyau da k'uruciya...Ina tunanin yanayinsa yace ko zan iyazama!? Nace bisimillah a tak'aice domin Ni banfiye son maganaba" b'ata mun Rai take, idan dai bani nayi niya ba.....mund'au lokaci A zaune Babu mecewa uffan se shine yace na takura ki ko...!? Se danayi mintuna biyu A yatsine nace ah'ah" tab'e bakinsa yayi danshi A zatonsa banjiba kafun yayi magana nace se Anjima sabida Ni A tsarin Rayuwata banaso wani yashigo sabgata.."Tafe nake Jikina nabani tabbas Ana kallona da kyar nasamu nabar makarantar nakoma tamu" Kai tsaye d'akinmu nashige Ina maida haki" bayan nahuta na d'auko wayata nashiga media...Kamar mintuna talatin Sega Joy tana cewa Asmee kinada bak'o A waje! Banbi kantaba nacigaba da sabgata...! Asmee matawalle" da ke kwance gefe Kuma Tasan naji Joy Sarai halayyata ce nuna halin ko inkula tace kice gatanan zuwa" wuffffff nayi dacewa sorry Joy waye!? Tare sukace Au dama kinji shine kikayi shiru to wlh senace ga kinan zuwa" guntun tsaki najah.....bayan joy tafita Asmee matawalle tace gaskiya Asmee Koguna" wannan ba hali me kyau bane shiyasa kowa se maganar ki yake, Dan kinga kina da kyau shine kike yarfa kowa..." Kallonta kawai nayi na cigaba da sha'anina...A waje Kuma y'an Mata se k'ok'arin b'ata Ni ake ga Wanda yazo nemana" Wanda har Ake gayamasa wani tuggu da Aka had'amun Sunday perty da akeyi Duk sati da daddare, Kuma Ina zuwa, domin maganar gaskiya Ina son Rawa kuma na iya me d'aukar hankalin macce bare Namiji... in har nashiga fili Babu maitake mun" sedai sowa! Haka dai yaji zantukan Kuma hankalinsa yayi matuk'ar tashi yaso yaganni yafad'a mun Amma Besamu damar hakan ba..."hakan dai yayi k'ok'arin ganawa da Pita Wanda inkacire Asmee matawalle pita kadai ne A bokina Kuma yasamu labarin anba pita zunxurutun kud'i yabani kwaya hankalina yagushe duk Wanda nake yarfawa suyimini fyad'e Shima Wanda yazo guna an tallata Masa ne sabida shima anso yamaida yawunsa akaina....in yaso nacigaba da wulakanta mutane......sedai nida Asmee matawalle Duk Abunda Ake bamuda labari, Kuma mafiyawan makaranta har anmatsu safiya ta waye Akawo k'arshen Asmee ko guna haka dai lokaci yaciga ba da tafiya..misalin k'arfe Shidda Wanda yazo nemana jiya yadawo yau" Asmee matawalle taso nafita Amma nace ba'asamu daga haka natsuke bakina se itace tagaji da magiya ta k'yaleni kana Bata fita ba domin itama tanada zafi gurin nuna halin ko inkula Amma nawa yaci u'war nata... Wanda Yazoo nemana ya harzuk'a Ainun haka yasashi bada kud'inshi domin tabbatar da anyi Lafiyayyen party A k'asana..... Misalin k'arfe 9:00 dai² kid'a yasoma tashi Kamar makaranta zata tsage Dumm, dum dum kakeji lokacin Kuma nida matawalle munshirya Kuma bak'aramin kyau mukayi ba" tulalen mu kala d'ayane kullum kwanan Duniya...shiyasa inmuka ratsa Guri ake tabbatar da mun wuce..yau ma haka tafaru tafe muke cikin tsari da natsuwa Wanda kana hango mu zaka tabbatar wad'ancan yara nacikin ganiyar taka Leda A school.......haka har muka Isa Hall d'in....Kamar yadda aka Saba in munshigo yauma hakane....kowa k'ok'arin turo Kai yake...hardai muka samu gurin zama bayan mun zauna shagali yaci gaba da tafiya Kamar Yadda aka Saba...Wata wak'a aka dannah me sauti, sanyi dakuma Sanya mutum cikin halin nishad'i...haka nafita nafara Rawa A hankali mutane suka soma jah baya se dai wasu tsiraru...bayan nayi Rawa nagaji anyi min lik'i sosai Wanda tunda nake ba'atamun irrinshi ba se yau...nafito na zauna...kafun shiga ta biyu...pita ne yazo bayana d'auke da wani lemu da ruwa yace A² d'agowa mukayi tare nida Asmee matawalle.....
#Comments
#Share 🔥
[1/30, 11:01] Asmeenat: *_BRILLIANT WRITER'S ASSO...._🖊*
_{pens of freedom, home of exceptional and magnificent writer's}_
*_MAZA_*
{ALLURAR GUBA}💉
_*NA*_
*_ASMESNAT@ZEEYAN_*
https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
*_SHAFIN NAKINE_*
_Rabi'atu Aminu mamman Dee_
7-8
A² d'agowa mukayi nida Asmee matawalle tare da musayar murmushi" yajah kujera ya zauna tare da d'an jigina bayansa yaturo k'afafunsu gaba.." kafun yace cikin harshen turanci kunfayi kyau manyan yara" matawalle tace kajika kaima kayi kyau tana k'ok'arin bud'a lemon da ya Ajiye..Ni tafara zubama, kana ta tsaya nata.." shikuma tadubi shi tace oya zuba da kanka..." Baki yatab'a yace eh lallai, kinzuba ma Koguna kinzubawa kanki!? ni kice Oya..." So na kuguna zan d'auka..kafun yakai hannu na d'auke nace cikin sigar Wasa se ka girma za'azuba ma...mukasa dariya dukanmu tare da Kai cups Abakunan mu...tundaga wannan lokacin hankalinmu yajuye, biyu² muke ganin mutane domin k'wayar da Doki Rabi ake bashi mu d'aya aka bamu...aka tada kid'a hankalin mutane yakoma can pita yajahmu nida Asmee yakaiwa masu neman Rabamu da Budurcinmu" lokacin da naji hannun wani A nonuwana bana iya dakatar Dashi" haka bana gane ko wanene" Ina Kuma Jin sautin kukan matawalle tana k'yaleni" ah ah" ku k'yaleni banaso Ah ah...Amma haka suke tabi kanta wannan yatashi wannan yazira Koda suka juyo kaina antsere dani..." Aka nemeni Aka rasa" misalin k'arfe hud'u na Assuba na farfad'o A furgice namik'e Ina tambayar me yakawo Ni nan....!??Wanda muka had'u dashi makaranta ne nagani...cakkk komai yatsaya mun Ina matawalle!? shine zuciyata ta Daka mun tsawa akai..." Muryata na b'ari sosai nace bansani ba" kusa Dani yazo yatsaya Idonsa sunkad'a sunyi Jajir Amma beyi magana ba..ganin hakan yasa nodoshi k'ofar fita yarik'o hannuna da cewa Dakata" tsayawa nayi cakkk nakasa ko tako d'aya" muryarsa narawa yasoma cewa Asmee jiya pita yabaki lemo me had'i kinsha keda k'awarki Asmee matawalle" juyowa nayi D'akin na lilo dani" kalamar hajiyata tadawo mun da cewa mutum ba Abun yadda bane, shiyasa ko yamutu se and'aureshi...cike da rikicewa nace Ina take...!? K'wallah yamatse tare da cewa sun keta Mata haddi....maganar tamkar saukar mashi haka ta soki k'ahon zuciyata" cikin wata murya nace sunketa Mata haddi..!? Yace hakane Asmee adaren jiya na nemeki narasa Dan nagaya maki haka dai ya labarta mun komi" jiri naji yad'ibeni Warwas nafad'i k'asa bashiri" yacigaba da magana Amma Sam kunnuwana basa fahimta...! Ganin bana hayyacina yajani muka futooo...Koda muka kawo hostel dandazon y'an makaranta sunkewaye Asmee wadda Ake tunanin ma batada Rai" tunda Na iso mutane suka soma bani hanya" k'asan tafin k'afar Asmee nafara tozali dashi jini yabiyo har yabushe duk anfarfasa Mata fuska" ancire wasu sassa masu muhimmaci A jikinta...Amma tana numfashi hannu tamik'o mun na kwanta Ajikinta dakyal tace Koguna kinga yadda k'addara ta tazo ko..!? Sun rabani da mutuncina Wanda tunda naxo Duniya iyayena ke k'ok'arin killacewa...Asmee ki....Bata fad'a mun mezanyi ba ranta yabar gangar jikinta" cikin kururuwa nake girgizata Ina fad'ar Asmee...hum Asmee hum Asmee" Amma Ina tariga tatafi nikuma daga wannan lokacin bansake sanin Ina nake ba" se bayan kwana biyu nabud'e Ido saman gadon hospital, mutunen da yataimakini na zaune wasu zafafan hawaye suka goce mun! Innalillahim rajiuy tabijjro mun A zuciya nafara tuna waye Asmee agareni! Meyasa ma narasata A wannan karon!? Meyasa pita yaci Amanarmu!? Mutumin da ko A class wurin zaman mu d'aya" Abunci tare muke ci...!? Da k'arfin gaske nace me muka maka pita...!? Nasake somewa Tsayin A wanni nadawo...Tamkar nima namutu haka nakeji...nayi kuka Babu dare Babu Rana haka banason kowa kusa Dani..Rayuwata tazama ramen k'unci komai bak'ik'irin nake ganinsa" Intak'aice Miki meelat hukumar makaranta Bata d'au mataki ba, tasalima cewa akayi Asmee Tasha k'wayar Datafi k'wak'walwarta har tayi sanadiyar takashe kanta da kanta" wannan dalilin yasa nabaro k'asar Amurica nadawo gida Nigeria...domin bazan iya rayuwa Ina kallon su pita da makarantar ba" A lokacin da nadawo kuma se naji cewa Inama nice akaketawa haddi namutu ba Asmee ba! Domin kakata kad'ai natarar Allah yayiwa baffana da Ammeena Rasuwa a wani Ibtila'i da yafaru A burnin saudiya..ank'i A fad'amun ne sabida burin mahaifina nason inzama wani Abu cikin Al'umnah...tana kawowa nan Kuma se tad'anyi shiru tajah majina sosai tace bana iyafad'a maki yadda narayu wannan wunin ban iya misiltawa ba...Wanda har yau bansake neman Koda hoton iyayena ba" domin bana buk'atar hakan" sedai nakan tuna wasiyar baffana ta k'arshe da yayimun A Amurica lokacin da yazo yaga yadda Matan Nigeria sukazama y'an mad'igo, shaye², zinace² sosai yatsoratar Dani Wanda hakan yasa nak'ara zafafa kaina" bana shiri da kowa domin duk wad'anda keson namasu magana lesbianisms girls" Mazan Kuma y'anshaye² ne ko Asmee tanashan shisha lokacin da muka had'u Amma batayi nisaba nice nayi jahadin cetota nakuma rabata da kowa cikin tausayin Allah takimtsu..tundaga wannan Rana Allah yakawo mun Ibtila'in Qunci...komai nawa ya sauya nafara gudanar da sabuwar Rayuwa Wanda kullum kwanan Duniya kakata keyimin nasiha da nuna mun manyan k'addarori har wata Shidda A wata safiyar talata Ina zaune Ina karatun Alk'urani kakata tazooo tazauna inakai Aya..nace lafiya kaka...!? Tace k'alau Dama Wata makaranta naji Ana tallah a gidan Redio shine nace ko zakiyi Applying..!? Shirun da taji nayi yasa ta d'ago Kai, hawaye taga nabin fuskata" harjikinta ke Rawa gurin fad'ar takwara lafiya..!? na had'a hannayena biyu Kamar me rok'on gafara nace Kaka Dan Allah karkisake yimun zancen makaranta Kamar yadda nake fad'a maki kullum nayafe karatu to wlh na yafe har Abadan Duniya..." Shiru Kaka tayi tace shikenan takwara Allah yasa shine Alkhairi ban Amsa ba domin ni atawa hauka k'addarorin da suka sameni se naajesu silar makaranta..haka dai lokaci yacigaba da tafiya nafara sakewa Dan har Islamiya nakanje nad'antaya kaka wasu Ayyuka...da yamma lik'is Ina kwance akan sallaya Sega nasi Almajirin kakata, yace Aunty Asmee kina da bak'o A waje...harara nagalla masa cikin hayagaga nace sau nawa zangayama in akace kakirani tun waje kace bana nan...!? murya sanyaye yace Ihakuri Aunty Asmee tare da ficewarsa" bayan yafita Kaka tazo dafff Dani ta tausasa murya tace haba takwarata meyasa kike hakane..!? Shifa d'an Adam Allah da kanshi yake cewa walaqada karamna bany Adam.." to ke meyasa kike wulak'anta shi!?" jiki sanyaye nace ni kaka ba wulak'anta su nakeyi ba hallayar mutanen zamani nake tsoro yanxu sunk'ware gurin iya yaudara Duk Wanda ka yadda dashi se yaci amanarka shiyasa nidai nafuson Rayuwata nikad'ai" murmushi tayi irrin nasu na manya tace Ai baduka aka taru aka zama d'aya ba.." Kuma ita macce lokaci gareta Aure shine cikar ni'imarta manzan Allah Yace miskinun³ (matsiyaciya ce³) matar da Bata da Aure komai kyanta haka komai yawan Dukiyarta" Asmee Dan Allah cikin masu nemanki kifitar da miji tunda Allah be k'addari iyayenki sugani ba ko zangani..." Kuma kinga Duk inda budurwa ke Kai kinkai....sosai jikina yayi sanyi cikin manemana wa nake so!? Tunda zahirin gaskiya fad'ar so kawai nakeji Amma bantantance meye shi ba...!? A fili kuma nace Kaka ketayani da Addu'a Allah yayimin zab'i mafi Alkhairi tace Inshallah muka cigaba da fira...washe gari da safe Kaka tayi bak'uwa bayan nagaisheta nafita islamiya...se suke magana tace wa Kaka ita Dai Asma'u miji shiru har yanzu ko!? Tace eh ah'ah Dan gaskiya tana samu Bata tsaidawane" A d'an razane tace ke me kikayi to!? Tace me ko nayi tunda Aure lokaci ne! Tace hakane Amma yau tawuce nan...Dan wannan cewa da take bataso Aljanune ke damunta" Afirgice Kaka tace Aljanu!? tace fad'i kanki tsaye Amma fa Akwai mafita" tace inajinki!? Meye mafitar Dan kinga banma kawo komai Araina ba kawai nad'auka Lokacine" tace ah ah shawara d'aya kikaita gurin Malam Isah nagangare malamin Allah ne nagoro kad'ai zakibashi kiga Ijaba ta sauka" murmushi tayi tace wlh ngd Sam bankawo ba gobe da safe da yadda Allah zankaita suka cigaba da firararsu" lokaci yad'anjah Koda nadawo har hajiya ta tafiyarta A gajiye nazauna dacewa Akwai kunu Kaka!? Baki tatab'a tace waike bakya majin kunya u'warmata dake Asameki kinashan kunu...!? Baki na turo dacewa nidai Kaka banason u'war matr nan Dan Allah" tace to kifitar da miji nadaina" cak nad'an tsaya da cewa waike Kaka yaushe zakigane shifa Aure Lokacine dashi Duk ranar da wa'adin zamana yak'are se zamana yazama tarihi...banji me zatace ba nayi Gaba...bayan magrib take ce mun gobe zamuje gurin Malam Isah" nace waye shi Kuma Kaka...!? Ta labarta mun wai Aljanu ne kecewa nace bana Aure Ina walak'anta mutane... murmushi nayi azuciyata nace bayan Allah su shikenan komai yafaru da d'an Adam se ace sune tofa suma suna da hakki..tunda imani yayi k'aranci kowa yamanta k'addara....A fili kuma nace shikenan Allah yakaimu Kaka tace Amin muka d'auki wata firar Daban bamuyi zurfi ba se gayaro Wai ana Kiran Asmee...!? D'aga Kai nayi dacewa je kace waye!? Kakatace kace gatanan zuwa" narai² nayi da Ido bakina na furta haba Kaka inme satar mutanene fa!? Tace yasaceki haka kike kina korar *MAZA* se zagina Ake a gari na'aje baligar macce! Bak'aramin b'aci Raina yayi ba...Amma nabasar dafita Koda nafita wazan gani....!? Dawood.......
[1/30, 11:01] Asmeenat: *_BRILLIANT WRITER'S ASSO...._🖊*
_{pens of freedom, home of exceptional and magnificent writer's}_
*_MAZA_*
{ALLURAR GUBA}💉
_*NA*_
*_ASMESNAT@ZEEYAN_*
https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
*_SHAFIN NAKINE_*
_Rabi'atu Aminu mamman Dee_
9-10
Dawood...murtsuka idanuwana nayi Dan tabbatar da shine ko bashi bane..."!? Kafun na wartsake cikin murya mesanyi yace Allah sarki Asmee kinyi mamakin ganina ko...!? Ban iya bashi amsa ba har yak'aro tako biyu daga inda yake tsaye yayi murmushi tare da fad'ar zuciya natare da Abunda take farauta Asmee, karkiyi wani mamaki tunda kika baro Amurica nake bibiyeda tarihinki har nagano cewa ke y'ar sokoto ce" Amma kafun musoma magana Inaso kibani dama mushiga cikin wuri me sirri, kasancewar tsayuwar saurayi da budurwa inda mutane ke shawagi tsohon yayi ne" ko kuma Gidadawan matasa.." b'oyayyar Ajiyar zuciya na sauke da cewa hakane Ina zuwa..ciki nashiga nagayawa Kaka mutumin da yataimake Ni Ah Amurica ne yaxo... murmushin ta tafad'ad'a da cewa kice yashigo" fitowa nayi Yana jingine da mota na matsa daf dashi nace Salam, A hankali yajuyo dacewa wslm gimbiyar Mata cikin wata siga yayi maganar tare da zuba min manyan idanuwansa Wanda hakan yasa nayi k'asa da Fuskata da sauri bakina nafurta bisimillah...nayi Gaba yabiyo bayana" muna shiga D'akin Kaka yazube k'asa Yana kwasar gaisuwa cike da tarbiya.." daga nan suka d'an tattab'a fira akan Abunda yafaru da Asmee matawalle, har yake cewa Kaka Ai zamani yacanza indai kikaga *MAZA* na good times da macce to jiki tasakar masu Amma daga zaran takama kanta tashiga layin masu girman kai, Kuma kullum kukanta suke nema" Kaka tace hakane Wlh mu A zamanin mu macce mekamun Kai itace *MAZA* ke rububin samu..y'ar dariya yayi dacewa ai Kaka ko yanzu hakane Duk namijin da yayi bariki ya lalata Mata da yawa inzaiyi Aure se yaduba me mutunci, Sam basa Auren budaren nasu sabida kartasan karce Kuma ko anyi sa'a sun Aure su kwana biyu se kiji sun koma zawarawa" Kai Kaka tad'aga dacewa Wlh kafini gaskiya ai Matanne da basa Gane *MAZA GUBA NE* shiyasa suke biye su" dariya yayi sosai yace Kai Kaka kinban Dariya *MAZAN NE GUBA*!? tace Eh Mana baka Auren yarinya meyasa zaka koyamata sonka!?" nutsuwa yayi yace gaskiya Babu dalili Amma ai Kaka lokaci yayi da yakamata Mata sugane *SAMARIN SHAHO* sabida duk saurayin dake da niayar yaudarar yarinya zakiga Yana Mata wayayyun kalamai Yana d'aukarta da mota yau ba'anan gurin hutawa gobe ba'acan to Wanda yacanye soyayyarshi gida me yake marmari dake bare har Ya Aureki!? K'wafa Kaka tayi dacewa gaskiyarka fa Matanma sunfi laifi..haka dai Dawood yasaki jiki suna fira da Kaka Kamar dama sunsaba had'uwa" seda dai sukayi fira tace dashi Bari nabaku guri yace Dama kinyi zaman ki Kaka, ta'aziya ce nazoyi mata na K'awarta Asmee" tace Allah sarki Aiko ka kyauta dan da tadawo munsha fama yanzune ma tafara zama mutum..jinjina Kai yayi dacewa ai nasan za'arina bak'aramar shak'uwa sukayi da matawalle ba" Kaka tace hakane Kuma ta tarar Allah ya Amshe Iyayenta" arazane yace Na'am tace wlh Dawood nanfa Kaka talabarta Masa komai Amma kafun takai k'arshe yayi kuka tamkar macce Kuma zahiri yatausaya min daga k'arshe yarok'i Allah yakai haske kabarin baffana da Ameena dakuma k'awata Asme" duk da kuka da nakeyi natuna baya naji dad'in Addu"oinsa ga mahaifana da k'awata...bayan wani lokaci yatafiyarsa da zummar zaidawo, Dare yacigaba da tafiyarmun cike da tunani domin Duk Wanda beyi rashin u'wa da ubaba Yana cikin ganiyar kuruciyaba to wlh ba'ayimasa mutuwa ba" Kuma besan zafinta ba domin koyaji bazai fahimta ba" haka dai bacci yasureni ina tausayin kaina sabida maraici dayayimun kutse cikin Rayuwata...bayan gari yawaye na idar da sallah nafito Kaka nazaune bisa kujera y'ar tsuggune" nagaidata ta amsa da cewa ke nakejira maganar tafiyar mu" tab'e baki nayi Amma takawar dakai gefe, dole naje nazura hijabina har k'asa muka fita...tafe muke cikin shiru kowa da tunanin zuciyarsa har muka bayyana wurin Malam Isah, Ad'an musayar Ido da mukayi nagane bak'i ne dogo mecikar zati da kwarjini, sajensa dukk yacika fuska k'ura'anai nakewaye kusa dashi, Kuna yanada tarin Almajirai manya da k'anana...masu d'aukar fatawa sosai ake bashi girma A yadda nafahimta da Kaka suka Fara gaisawa sannan Ni" yace meyake tafe damu...!? Kaka ta labarta Masa Babu bincike komai yace bak'in Aljani ne ke son Aurenta...wlh Jameela ba Kaka ba nikaina seda naji wani dum kafun nalasa baki Ina had'a yawu.." Kaka kuma cikin wani yanayi tace to Malam Dan Allah ko akwai taimako da zaamana A koreshi!? Yace Eh Amma da kanta zata rik'a zuwa" da sauri nad'aga kai muka had'a Ido Amma dole najah Au'ziya A zuciyata sabida yadda yad'aga mun gira Yana lashe lab'b'a...Amma Kaka batagani ba se cewa datayi inshallah gobe zanturota, malam yace Allah ka yadda Kuma zanyi iya k'ok'arina Allah shike biyan buk'ata tace hakane tayi godiya sosai muka fito....Araina Kamar nafad'awa Kaka Abunda Malam yamun wata zuciyar Kuma tace ki bar zancen kila ma kece kikaga haka..zahiri nace uhmmm mukaci gaba da tafiya" har mukaje gidan banada wani sukuni se sak'e² nakeyi A zuciyata...washe gari tunsafe Kaka tace natashi naje Babu yadda na iya dole nashirya naje gidan Malam Isah Koda nashiga Yana zaune yayi zama irin na malaman Allah Yana ganina yace sisssssss Asma'u y'an Mata kinzo! na d'ago da cewa Eh ma...ban isafad'ar Abunda zance ba namik'e tsaye jikina na wani bala'in rawa sabida duk yajaye babar rigarsa yayi wani zama da yabbayana penis da y'ay'an marainansa se wani lilo take kamar maciji...cikin tsoro nasoma yin waje da gudu Amma Malam yamik'e da cewa kuriketa Aljanu ne... aikuwa Almajiran Malam suka rik'eni sosai nake kuwa Ina fad'ar wlh Basu bane kusake Ni k'arya yake.....tasssss naji wani Lafiyayyen Mari Afuskata ana cewa ku suwaye da har kuke k'ok'arin k'aryata Malam...!?Axabar Marin yasani d'aukewa inaji Malam nacewa kushiga da ita ciki ganina zuwa zasuyi bayani haka kuwa akayi ana shiga Dani Malam yarufe d'akin...zirrrr yakoma na rintse Idona tare da saka hannayena biyu abakina nabashi baya nahad'e jikina da Bangon d'akin........
0 comments:
Post a Comment