Malam mudi Asalin su yan cikin k'auyen k'auran wali ne, Almajiranci ya kawo malam mudi cikin garin kano har ya girma, malamin shi ya bashi 'yar shi ya Aura, Malam mudi shi ma yanzu ya zama malamin kan shi, malami ne da ke koyar da Allo a zauren gidan su, suna zaune ne a Na'ibawa, mahaifin malam Mudi ya dad'e da rasuwa sakamakon rashin lafiya da ya dad'e yana fama da shi, hakan yasa malam Mudi ya d'auko mahaifiyar sa wadda suke cewa inna, ya dawo da ita gidan shi, malam mudi yana da mata d'aya mai suna Indo,
Allah ya Albarkace su da d'a d'aya tak namiji, Adam wanda aka sa mishi Ado tun yana yaro, Kuma haka Allah ya halicce shi baya gani sam, se dai Allah ya yi mishi k'wak'walwa da basirar saurin haddace abu a kan shi.
Talakawa ne su fitik, da koyarwar nan kad'ai mahaifin su ya dogara, ita kuma mahaifiyar Ado kusan ita ce ma dai k'arfin gidan tana Aiki a wani gidan masu kud'i, da wannan kud'in ne mahaifin Ado ya kai Ado wajen wani malamin shi, domin ya sami karatu me kyau, haka rayuwa ta ci gaba da kasance masu wata ran Aci, wata ran in ba'a samu ba a hak'ura, da dad'i ba dad'i haka suka ci gaba da rayuwa.
Ado yana da shekara shida A duniya, wata rana maman shi da baban shi suka shirya domin zuwa k'auye gaishe da dangin mahaifin Ado, aka bar Ado da inna a gida, fitar da basu dawo ba kenan sai gawar su aka kawo musu, a hanyar su ta zuwa k'auran wali sukai hatsari, A take a nan suka ce ga garin ku.
Ado da inna sun yi kuka kamar ransu zai fita, daga k'arshe suka d'auki hak'uri, yan'uwan shi na k'aura da kuma dangin matar shi duk sun zo an yi zaman makoki da su.
Bayan kwana Arba'in akai sadaka, tare da yi wa mamatan addu'a sannan kowa ya watse, _hmm rayuwar kenan fa, Allah ka bamu sa'a._
Da yan k'aura zasu tafi suka ce be kamata su bar su inna anan ba, su shirya kawai su koma can da zama, dukkan su basu yi musu ba, saboda gidan kullum gani suke kamar duk inda suka kalla zasu gan su, suka had'o kayan su, suka d'auki hanya sai k'aura.
Se dai bayan wata d'aya da zuwa sai yan uwan mahaifin Ado suka juya musu baya, har da yayan adon wato d'an inna, shi ma ba ruwan shi da su daga shi sai 'ya'yan shi, ga tsangwama, kai a tak'aice dai gani suke kamar su inna sun takura musu, hakan yasa inna kuka sosai, ta k'ara yi wa Mudi Addu'a da sa mishi Albarka, tun da suke bai tab'a nuna gazawar shi kan su ba.
Akwai wata rana da yayan mudi ya shigo ya tarar da matar shi na kuka, daya tambaye ta dalili sai tace " inna ta tsangwame ta ita da 'ya'yan ta."
A lokacin yayan mudi ya yi ta fad'in maganganu wad'an da basu dace ba sam, har yana cewa " gaskiya mutuwar mudi ni ta kwantar, da yana nan har yanzu da baku dawo nan ba, kuma inna yanda ki ke nuna tsana ta tun muna yara haka zaki gwada kan iyalai na."
Inna ce ta kalle shi tana kuka tace " mudi ya fi ka hankali, ya fi ka tunani, kai mudi ya fika biyayya, dole in so d'an da yafi yi min biyayya, mudi be tab'a gazawa da ni ba duk da talaucin da yake da shi har ya bar duniya kullum burin shi ya kyautata min, bai da wani d'an uwan da yake so sama da kai, mudi ya fi ka wadatar zuci, duk da haka ban tab'a nuna banbanci a tsakanin ku ba saboda dukkan ku yaya na ne, ban tab'a yi maka baki ba, yanzu ma bazan yi maka ba, na gode Allah yai maka Albarka, shi kuma mudi Allah ya sa yana kyakkyawan makwanci. "
D'akin da aka sauke ta ta shiga ta d'ebo kayan su ita da Ado ta kamo hannun Ado ta fito, ta kalli yayan mudi tace " nabar ku lafiya," tana gama fad'in haka taja hannun Ado suka fice.
Cikin garin kano suka koma, suka nufi gidan malamin mudi, bayan sun gaggaisa an basu abinci da ruwa sun sha, sai inna ta kalli malam tace " dan Allah malam a samar mana gidan haya me sauk'in kud'i, kuma in sha Allah Ado zai ci gaba da zuwa d'aukan karatu a wajen ka. "
Babu yanda malam be yi ba akan su zauna a gidan shi amma firrr inna tak'i yarda, daga k'arshe dole ya hak'ura, amma yace su zauna nan da kwana biyu ya samar musu.
Haka kuwa akai, bayan kwana biyu malam ya samo musu gidan haya, tsakanin gidan su da na malam d'in ba nisa, sannan suna kusa da bakin titi.
Dama akwai kud'in filin ta na k'auye da ta siyar, su ta d'auko ta biya kud'in hayan, ragowar ta se musu k'ananan katifu biyu, sannan ta siya sauran abubuwan buk'atun yau da kullum, sannan ta d'an k'aro musu suturu na gwanjo masu kyau, sauran canjin ta d'an se musu hatsi.
Haka rayuwa ta ci gaba da kasance musu, yau fari gobe bak'i, duk abnda inna ta wawuro to na Ado ne, tana matuk'ar k'aunar yaron kuma tana tausayawa maraicin shi matuk'a, haka suka kasance har abincin da suka d'an tanada ya k'are, sannan kuma kud'in hannun inna kaf sun k'are, hakan yasa Ado ya fara fita bara bakin titi, tun shima ba a san ran inna ba, dan dai ba yanda zatai ne kawai, tun suna zuwa shi da inna har ya gane hanyar yana zuwa shi kad'ai, amma duk da haka inna bata yarda ya rik'a zuwa shi kad'ai ba, Almajiri ta samo mishi a makarantar malam mai suna iro, koda yaushe bayan an gama karatu sai su wuce bakin titi bara, a can Allah ya had'a shi da musa gurgu, har suka shak'u sosai, shak'uwar da basa b'oye wa juna matsalar su, har Allah ya raya su suka girma suna tare.
Ado dogo ne bak'i, ba laifi kyakkyawan Yaro ne, akwai dogon hanci kamar bafulatani, yana da k'wak'walwa sosai, hakan yasa ya haddace litattafai da dama na addini a kan sa, karatun Qur'ani kuwa idan yana yi kai kasha yaron sudais ne, yana gode wa Allah a yanayin da Allah ya halicci shi, yana da barkwanci sosai kuma hatta maganar sa a natse yake yin ta, yanzu haka yana da shekara talatin cif se dai ya kan yi kuka idan yaga yanda mutane ke gudun su tsakanin su da mutane se dai kawai su zo su basu sadakar kud'i su wuce.
Ado kenan, a yanzu haka kuma zuciyar shi ta afka tunanin sautin muryar baiwar Allahn da take zuwa kusan kullum ta basu kud'i ta wuce har ya kai shi ga kwanta wa.
WANNAN KENAN
WAI WACECE WANNAN DA TAI DACE DA WANNAN SAURAYI D'AN BAIWA HAKA?š¤
_nasan wasu zasu ce BK kinyi hauka ne, makahon zai yi soyayya da lafiyayya me ido, to shin makaho ba mutum bane?š¤š¤š¤, ku dai ku biyo BK kuji yanda zata kaya_
muje zuwa
urs š
±Kšš
[1/7, 10:42 AM] Bk: šššššššššš
NAK'ASASSHE MA MUTUM NE
šššššššššš
Writen by BILKISU Z. YA'U (š
±K)
_(Yar gatan exclusive)_
♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
_(Home of peace, honour and super writer's)_
SADAUKARWA GA: MEELAT A.H.K
This page is dedicated to you
UMMIE XEEY
_Allah ya k'ara miki basira_
page 15 to 20
Alhamdulillah Ado ya samu sauk'in zazzab'in da yake fama da shi har ma ya fara fita, Kamar kullum yau ma Ado makaho da musa gurgu suna zaune a inda suka saba zama, suna cikin hira sai ga motar wannan baiwar Allahn da ke basu sadaka kullum ta danno kai, musa gurgu ya zunguri Ado yace " ga mutuniyar nan ta taho, "
Ado yace " haba da gaske," Musa yace " wallahi ita ce "
k'araso wa Motocin suka yi dai dai inda su Ado suke, ta yi horn, Iro ne ya tashi zai je Ado ya dakatar da shi yace ya bari shi ya je.
Ita dai baiwar Allahn nan tana cikin mota tana ganin ikon Allah, tana jinjina karambani irin na makaho, saboda da d'an tazara a tsakanin ta da su.
Shi kuwa Ado inda kunnen shi ya ji k'arar horn yai ta bi, har ya k'araso dai dai in da motar take, Sallama ya yi mata ta amsa sannan Ado cikin farin ciki ya gaishe ta, mik'a mishi kud'in ta yi tace " gashi " nan fa Ado ya mik'a hannu dai dai saitin in da ya ji muryar ta ya karb'i kud'in, godiya ya yi ta mata, tare da jera mata addu'a kala kala, har ya juya ya tafi bai dena shi mata albarka ba.
Ita kuwa wannan baiwar Allahn bin shi ta yi da ido tana mamakin baiwa ta wannan makahon, kafin daga k'arshe ta ba Driver umurnin ya ja motar, masu tsaron ta suma suka shiga cikin tasu suka kama hanyar gida.
Ado makaho ya koma gun zaman shi ya zauna, cike da farin cikin yau ma ya sake jin muryar ta hankalin shi ya kwanta, murna kamar me.
Ba kowa bace take zuwa tana ba su Ado Makaho kud'i face Meelat, Har ta koma gida tana mamakin baiwa irin ta Ado, Driver na faka mota ta yi cikin gida sai d'akin Mumyn ta.
Tana shiga d'akin ta fad'a kan jikin mumy, tace " mumy na gaji wallahi, yauwa mumy kin san me yau na had'u da makaho d'an baiwa," nan ta kwashe duk abin da ya faru ta fad'a mata.
Mumy ta yi murmushi, sannan ta kalli d'iyar ta ta tace " Ai in dai makaho ne Allah yai musu tarin baiwa mai yawa, gashi dai basa gani amma sai kiga suna da saurin d'auke abu acikin k'wak'walwar su, yanzu dai ba wannan ba tashi kije ki watsa ruwa, kiy sallah sai ki ci Abinci, ki kwanta ki huta babyna."
Murmushi Meelat ta yi, sannan ta tashi ta haye sama, Sallah ta fara yi kar lokacin ta ya wuce, sannan ta yi wanka, ta ci abinci sannan ta kwanta sai bacci.
………………
" Naseer! Naseer!! " mum d'insa ce ke tsaye cikin d'akin sa kusan wajen minti biyar amma be san ta shigo ba, naseer yai firgigit ya dawo cikin hayyacin shi, tare da amsa wa, yace " na'am mum "
Mum tace " me ka ke tunani haka har na shigo baka sani ba, meke damun ka ne kwana biyu? "
Nass yace " Mum wata Beb na gani nake so, se dai da alamu bata sona. "
Mum tace haba nasser dena fad'in haka mana, duk kyawun nan naka, duk kud'in mu da muk'amin mu ace ka nemi auren yarinya ka rasa ina ba zai yiwu ba, yar gidan uban waye? "
Nass yace " mum ita ma 'yar masu kud'i ce, masu tsaronta ma sun fi nawa yawa, ki bari kawai zamu daidaita da kan mu, ba sai kun shigo cikin maganar ba, Amma ki fad'a wa Dad A k'aromn yawan masu tsaro na kar ta raina ni, kuma mum motocin su duk sun fi nawa tsada fa. "
Mum ta yi murmushi tace " to ba damuwa idan ya dawo sai ka fad'a mishi da kan ka, kasan baya son b'acin ranka, duk abin da kake so zai yi maka."
Sun dad'e suna hira, daga k'arshe Mum ta fito, ta bar shi domin ya samu bacci.
WANENE NASEER?
Naseer d'a ne ga Gwamnan garin kano me suna Ahmad Sadiq, yana da mata d'aya mai suna Maryam, suna da d'a guda d'aya tak mai suna Naseer ana ce mishi Nass, iyayen sa suna matuk'ar k'aunar shi, se dai matsala d'aya son da suke mishi ya ja sun sangarta shi, duk abin da yake sam basa kwab'a mishi, ko ya yi laifi aka kawo musu k'ara sam basa d'aukar mataki, sai ma su sa a kulle wasu daga ciki, wasu kuma ai musu korar kare.
Naseer wato Nass matsakai ci ne, fari ne shi, se dai mummuna ne, babu kyau ba kyan hali, Karatun shi duk a k'asar waje ya yi su se dai shashancin shi kawai ya sa a gaba, bin yan mata kamar bunsuru, ga shaye shaye.
Yanzu haka Nass yana da Shekara Talatin da biyar
WANAN KENAN
_Yanzu labarin ya fara_
muje zuwa
urs š
±Kšš
[1/7, 10:42 AM] Bk: šššššššššš
NAK'ASASSHE MA MUTUM NE
šššššššššš
Writen by BILKISU Z. YA'U (š
±K)
_(Yar gatan exclusive)_
♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
_(Home Of Peace, Honour And Super Writer's_
SADAUKARWA GA: MEELAT A.H.K
This page is Dedicated to
AISHAN UMMA
_Aunty nah ta kaina, ina jin dad'in addu'arki gare ni, had'e da shawarwari masu kyau, Allah ya saka miki da mafificin Alkhiarin sa_
_Wanan shafin naki ne_
Page 20 to 25
Kamar kullum yau ma Ado da Abokin sa musa gurgu suna zaune a inda suka saba zama suna hira, duk wanda yazo wucewa yana d'auko abin sadaka yana basu.
Musa Gurgu yace " wato Ado na lura a cikin yan kwanakin nan baka tashi zuwa bara yanzu sai ka ga Wannan Yarinyar tana gab da zuwa. "
Ado ya yi murmushi, sannan yace " Musa ban sanka da sa ido ba, yaushe ka koya? "
Musa Gurgu yace " tun ranar da ka tashi daga Adon musa ka koma Adon Hajiya, " dukkan su suka sa dariya, Musa yace " ni dai bazan fasa gargad'in ka ba akan ka tsaya in da Allah ya aje ka."
Suna cikin hirar ne sai ga Meelat ta shawo kwanar titin da su Ado suke, yau ma kamar kullum ita da masu tsaron lafiyar ta ne gaba da baya, Yau tare take da Aminan ta su Real khady.
Suna tafe suna hira suna k'yalk'alar dariya, har sun d'an gota gun da su Ado suke zaune, juyowar da zata yi sai ta hango su, tai sauri tace wa drivern ta ya tsaya, kuma ya koma baya.
A gefen inda su Ado suke zaune Akwai wani shagon da ake siyar da litattafai kala kala, shagon Real Khady ta hango, har Meelat ta ciro kud'in sadaka zata bawa Driver ya kai musu, sai Real Khady tace su fito su raka ta ta duba littafin da take nema, hakan yasa Meelat ta fasa bada kud'in a kai musu tunda inda shagon yake a gefen su Ado suke zaune.
Fitowa suka yi su uku, suma masu tsaron ta suka b'alle k'ofa zasu fito sai ta d'aga musu hannu Alamun dakatar da su.
Suka k'arasa wajen Shagon, Meelat ta k'araso wajen su Ado tai sallama dukkan su suka amsa, sannan ta mik'a musu kud'in suka yi mata godiya, sai ta wuce ta bi su Rukeey da suka wuce shagon litattafan kai tsaye ba tare da sun jira ta ba.
Ado cikin fushi yace wa Musa " meyasa yau baka sanar da ni zuwan ta ba, dan in mata tarba ta musamman? "
Musa ya k'yalk'yace da dariya tare da nuna shi da d'an yatsa, yace " wallahi mamaki ka ke bani, mu da mutane suke wa kallon k'ask'antattu a cikin su shine kake tunanin 'Yar Manyan Mutane kamar wannan zata so ka hmm."
tsayawa sukai da maganar sakamakon fitowa da su Meelat suka yi zasu wuce, Rukeey tace " ya maganar zuwa SHOPRITE ne za'a je ko an fasa," Real Khady tace " me zai hana zamu je mana Gobe, " Meelat tace " Gobe da Safe k'arfe Goma dai dai."
Duk Maganar da suke a kunnen Ado
Ado ne ya yi ta maimaita sunan wajen da ya ji sun Ambata, yana fad'in " Shoprite Shoprite " yana fad'i yana jijjiga kai
Musa ya kalle shi yace " ban gane ba, me kake nufi da maimaita sunan wajen da suka ambata? "
Ado yai murmushin da ya zama d'abi'ar shi, sannan yace " zan je ne."
Musa ya zaro ido tare da fad'in " Ado, Ado, ina guje maka abin da zai sa a gark'ame ka a gidan yari. "
Ado ya sake yin murmushi yace " kar ka damu, bazan yi abin da zai ja A kama ni ba, balle har a kai ga kulle ni. "
………………
Nass ne zaune a harabar gidan su, wajen shak'atawa, gaban shi kwalbar giya ce amma sam ya kasa sha, saboda tsabar tunanin Meelat, Hannun shi ya dunk'ule tare da daddage wa ya naushi k'afar shi ta dama.
Tunani yake ta yi, yanda za'ai ya k'ara ganin ta a karo na biyu.
Can sai dabara ta fad'o mishi, cikin sauri ya tashi, masu tsaron lafiyar sa ma suka bi shi a baya, mota suka shiga suka yi waje, Motar Nass tana gaba ta masu tsaron lafiyar sa na baya.
Wajen shak'atawa suka nufa, inda ya had'u da su ita da k'awayen ta kwanaki har suka so su yi rigima, babu inda be duba ba amma babu ita ba alamar me kama da ita ma.
Dunk'ule hannun shi na hagu ya yi, ya kai wa na dama naushi, _BK tace ga dukkan Alamu yin hakan d'abi'ar shi ne_
Nass Kallon d'aya daga cikin masu tsaron shi ya yi, yace " Josep zaka iya tuna fuskar yarinyar da muka had'u da ita a dai dai can? " ya nuna mishi wani waje da hannun shi.
Wanda aka kira da Josep yace " yes sir "
Nass yace " da kyau, to ka tafi ka nemo min inda gidan su yake, idan baka samu ba ka nemo min ita yarinyar. "
Josep yace " ok sir, " sannan ya juya da hanzari ya fita, su kuma su Nass suma fitowa suka yi suka shiga Mota suka koma gida.
WASHE GARI
Washe gari Ado ya sa Inna ta kai mishi ruwan wanka, bayan ya fito ya sata ta ciro mishi kayan sallar sa na Bara waccan, ya saka, Inna ta kalle shi tace Ado wannan shirin na yau fa sai ina, sai kace wanda zai tafi tad'i."
Ado yai murmushi, Zai bata amsa kenan sai ga Almajirin Ado me suna iro, wato d'an jagoran shi yai sallama ya shigo, Ado yace " Inna k'arfe nawa ne yanzu? "
Inna tace " k'arfe tara saura kwata. "
Ado yace Alhamdulillah dai dai ma kenan, Inna sai mun dawo Ai mana addu'a, Iro muje kar mu makara, iro ya kama sandar Ado suka fita, Inna ta bisu da Addu'a har suka fito."
Suna fitowa Ado yace wa Iro " Iro ka san Shoprite? "
Iro yace " Eh muna wuce wa ta wurin idan mallam ya aike mu."
Ado yace " Yauwa, to can zamu je, ina fatan kud'in da ya rage dai zai ishe mu zuwa da dawo wa? "
Iro yace " eh zai isa "
Ado yace " yauwa muje bakin titi ka tarar mana me adai-daita, Amma kar ka bi da mu ta wajen zaman mu saboda musa. "
Iro yace " to " suna zuwa bakin titi ya tarar musu Napep suka hau suka tafi.
B'angaren su Meelat kuwa, ta gama shiryawa, tayi kyau sosai kamar sarauniya, tana zaune tana jiran Abokan tafiyar nata.
Muryar su ta ji A k'asa Real Khady na faman k'wala mata kira, da sauri ta fito daga d'akin ta, ta sauko k'asa, suka yi wa Mumy Sallama, yau ma Motar da suka fita da ita daban kuma me shegen tsada, Motar masu tsaron su akwai d'aya a gaban su d'aya a bayan su, suna tafe a jere reras gwanin ban sha'awa.
Josep ya yi yawon har ya gaji, har ya karya kwanar mota zai koma ya sanar da Oga ba labari, kawai sai ga motocin su sun zo sun wuce ta gaban shi, zaro ido ya yi, tare da k'ara duba wa ya tabbatar da ita ce, haba nan da nan yai ribas ya bisu a baya, Wayar shi ya d'auko ya kira Oga, Nass dake zaune a d'akin shi ya k'ura wa wayar shi ido, yana ganin kiran Josep ya shigo da saurin shi ya d'aga yana fad'in " Hello, Josep ya ake ciki, ka ganta? "
Josep yace " yes Oga na gan ta, gasu ma ina bin su a baya. "
Nass yace " da kyau Josep, ka ci gaba da bin su har zuwa inda zasu je, sai ka kira ka sanar da ni."
Josep yace " An gama Oga, " ya katse wayar, tare da ci gaba da tuk'in shi, yana yi cikin iya taku saboda kar masu tsaron ta su gane su yake bi.
_Shin wai ni kam Anya Meelat zata sami zab'in ta kamar yanda take muradi?š¤ waye zab'in na ta cikin su? ko har yanzu bai zo ba? ku biyo ni domin jin yadda zata kasance_
Muje zuwa
Urs š
±Kšš
[1/7, 10:43 AM] Bk: šššššššššš
NAK'ASASSHE MA MUTUM NE
šššššššššš
Writen by BILKISU Z. YA'U (š
±K)
_(Yar gatan exclusive)_
♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
_(Home of peace, honour and super writer's_
SADAUKARWA GA: MEELAT A.H.K
Dedicated to
AISHA A. MUH'D
_Ina Alfahari dake da kuma k'aunar ki gareni, Allah ya saka miki da Alkhairi, yasa ki gama da duniya lafiya, wannan shafin naki ne._
Page 25 to 30
Dai dai bakin Gate d'in Napep ta sauke su Ado, bayan sun biya kud'i suka zauna nan bakin gate d'in suna jira suga zuwan su Meelat.
Ado yace " Iro ka sa ido sosai fa, ai zaka gane wadda ke bamu sadakar kud'i kullum koh? "
Iro yace " Eh zan gane."
Suna nan zaune duk motar da tazo wuce wa idon Iro yana kai
sun kai wajen minti goma sha biyar a wajen suna jiran zuwan su, wasu motoci Iro yaga sun danno kai har guda hud'u, su Meelat kenan, da sauri ya k'araso inda Ado yake yace " ga motaocin su nan. "
Tashi Ado ya yi daga inda yake zaune, Iro ya rik'e sandar shi suka doshi gate zasu shiga, a dai dai An bud'e wa su Meelat gate sun shige da motocin su.
Wani security ne ya hango su yace " kai ina zaku je? "
Ado yace " Yallab'ai ciki zamu shiga. "
Securityn nan yace " to ku biya D'ari biyar kud'in shiga sai ku shige."
Ado yace " Iro yi sauri ka bashi d'ari biyar kar su b'ace mana," Iro ya ciro kud'in ya bada kamar yanda aka umurce shi."
Suka wuce suka shiga ciki, waige waige Iro ya hau yi, hango motar su ya yi, sai kuma ya ga sun fito daga cikin motar, wurin lilo suka nufa.
Iro ya ja Ado har kusa da inda su Meelat suke wasannin su, se dai duk maganar su da dariyar da suke Ado yana ji, dan babu wata tazara a tsakanin shi da su daga inda yake zuwa wajen su, da yake securityn su Meelat tace su bata waje, shi ne suka d'an yi nesa da wurin, Amma idon su na kanta.
Ado farin ciki fal a zuciya, shi dai a rayuwa kawai ya ji muryar ta, sai yaji farin ciki ya lullub'e shi.
………………
Josep ne cikin tashin hankali ya shigo cikin gida, direct d'akin Nass ya nufa, k'wank'wasa wa ya yi, sannan ya bud'e ya shiga a dai dai Nass ya fito daga wanka, cikin farin ciki yana sauri ya shirya ya kira Josep ya kwatanta mishi wajen da suke ya je.
Turus Nass ya yi a tsaye, ganin Josep a gaban shi, Nass yace " Me ya dawo da kai, ina ka baro su? "
Josep yace " sorry Oga, go slow ne yai yawa har yasa suka b'ace mun."
Nass ya d'auke shi da mari tare da kai wa iska naushi, zama ya yi a kan d'aya daga cikin kujerun d'akin shi, kanshi yana k'asa ya nuna hanyar fita daga d'akin yace " fita ka bani waje," Josep ya juya da sauri ya fita daga d'akin kar ya k'ara shan wani marin.
B'angaren su meelat kuwa wasanni sukai ta yi kamar yara, sun hau lilo, sun hau jirgi, kai abubuwan wasanni dai kala kala sai da sukai ta hawa, su kuwa Ado shi da Iro duk inda su meelat suka yi suna biye da su.
Sai da suka gaji lilis sannan suka zauna suka d'an huta, bayan sun huta kuma suka fito suka shiga mota sai gida.
Suma su Ado fitowa suka yi, suka tari Napep sai gida.
Tun daga ranar Ado da Iro suke sintirin zuwa Shoprite, wata ran su je su k'araci zaman su a bakin gate su Meelat basu zo ba, wata ran kuma su taki sa'ar ganin su, musamman ma ranar Asabar da Lahadi ranakun da basa zuwa aiki.
Zuwa yanzu Meelat ta fahimci Ado makaho wajen su yake zuwa se dai ita kad'ai ce ta fahimci haka, amma tayi iya tunanin gano dalilin shi na biyo su nan amma ta kasa ganowa.
shi ma Ado tuni ya gano Ranakun da suke zuwa shoprite, dan gano hakan ne ma yasa ya yi ta sintirin zuwa kullum babu fashi, domin tantance ranakun.
Yau ta kama Asabar, Nass ne ya gama fushin nashi kuma ya kira Josep yace suje ya kai shi dai dai inda yaga su Meelat.
A dai dai suma Meelat sun fito, yau ma kamar kullum da motoci Hud'u suka fito, kuma wasu kalan daban, Meelat da su Rukeey suna tafe suna hira.
Nass kuwa suna isowa dai dai wajen da Josep yaga Meelat sun wuce, suka faka motocin su, Nass ya babbaza su a wajen yace su saka ido sosai a kan duk wata mota da zata wuce.
Motar su Meelat na shawo kwana Nass ya hango ta, cikin sauri ya diro daga saman motar shi, tare da fad'in " mazaje na ganta, ku yi sauri ku motsa, " nan da nan suka faffad'a cikin mota suka bi bayan motar su Meelat.
Suna isowa Shoprite aka bud'e musu gate suka shiga, fakin suka yi, sannan suka doshi inda suka saba zama.
Suna zauna wa Meelat ta juyo da kanta gefen da su Ado suke zama, ilai kuwa suna nan zaune a kusa da inda suke.
Drinks ne kala kala aka kawo gaban su Meelat, suna sha suna hira, kamar daga sama suka ga Nass a gaban su, masu tsaron shi kuma kewaye da su.
Wani irin mugun kallo Meelat ta wurga mishi, Real Khady ce tai magana tace " malam lafiya, gidan ku ba tarbiyya ne zaku tsaya mana a kai?"
Nass ya kalli Real Khady ya yi murmushi, kallon masu tsaron shi ya yi, ya yi musu alamar subar wajen da kanshi, cikin sauri kuwa suka matsa suka bar wajen, sannan ya sake kallon Real Khady ya nuna Meelat yace " kinga wadda nazo gunta nan," sannan ya juyo gun Meelat yace " Beb ina sonki kina wahalar da zuciya ta, mata nawa suke bina suna so, ke kin taki sa'a nace ina sonki kina ja mun aji……. "
Dariyar da Meelat ta kwashe da ita ne ya dakatar da Nass daga ci gaba da maganganun da yake yi.
Duk abin da ke faruwa Ado yana ji
Sai da ta yi dariya mai isar ta, sannan ta kalle shi tace " a hakan mata ke binka baka da tunanin? to bari kaji, kaga wancan Makahon, ta nuna inda Su Ado suke zaune, sannan tace Wallahi ya fika a waje na, ya dad'e yana zuwa wajen nan, amma bai tab'a shiga harkar kowa ba, Sannan na tabbatar akwai dalilin zuwan shi wajen nan saboda ba bara yake ba, zama kawai suke shi da d'an jagoran shi, Amma burin shi ya fahimci yanayin Abin da ya yi sanadin zuwan shi gurin nan kafin ya tunkare shi.
Nass ne ya shek'e da dariya irin tasu ta yan duniya, yana yi yana nuna ta da yatsa, sai da ya yi dariyar sa mai isar sa, sannan ya kalle ta yace " taya za'ai ki rik'a yin magana wadda ta danganci masu ido ki rik'a jingina ta ga makaho?"
Meelat tai murmushi, sannan ta tashi ta tako har inda yake, matsawa ta yi dai dai saitin kunnen shi tai magana a hankali wanda ko su Rukeey da suke kusa basu ji abinda tace ba, tai mishi magana tamkar mai yin rad'a tace " tunda baka yarda ba muje da kai wajen su domin ka tabbatar da magana ta."
Nass ya bita da kallo yana dariya wadda ke bawa Meelat haushi, sannan yace " muje to. "
Tahowa suka yi wajen su Ado, Iro ya kalli Ado yace " nan suka taho fa ita da wannan mutumin, kafin Ado yai magana har sun k'araso, Meelat ce tai musu sallama, Ado ya amsa mata sallamar.
Ado yace " Sannu Hajiya, ina yini? "
Meelat tace " yauwa, ka gane ni? "
Ado yai kyakkyawan murmushin nan nashi dake k'awata kyawun fuskar shi, yace " Ai ko daga bacci na tashi bazan manta da muryarki ba hajiya, Ai dalilin zuwan mu nan ma saboda ke ne."
Meelat waje ta samu gefen inda suke zaune ta zauna, shi kam Nass ya fara hassala.
Meelat tace " waje na kuma, meyasa? "
To kunsan Nak'asassu, musamman makafi, basu iya k'arya, saboda basu saba da ita ba.
Ado ji yake gaban shi na fad'uwa tare da bugawar zuciya da sauri da sauri, sannan yana jin wani farin ciki mara misaltuwa yace " Farko abin da yake kawo ni nan saboda inji muryarki, Sai daga baya nai wani tunani, tun da kke mana Alkhairi bamu tab'a sanin sunan ki ba, hakan yasa na fara sauraron yanayin mu'amalar ki da jama'a, idan na fahimci kina da sauk'in kai in je in tambaye ki, idan kuma naga akasin haka sai in hak'ura in ci gaba da yi miki fatan Alkhairi tare da ci gaba da yi miki Addu'a. "
Meelat tace " Allah sarki, to me yasa ka ke son jin murya ta? "
Ado yace " tun ranar da na fara jin muryar ki naji ina son in rik'a ji kullum, har gizo muryar ke yi min lokuta da dama, Amma dan Allah hajiya kar kisa a D'aure ni, ba raini bane, kawai na fad'a miki gaskiyar abin da kika tambaye ni ne, "
Iro ne ya fashe da kuka, sannan yace " sai da musa yace kar mu zo, kace sai ka zo, gashi ka jawo za'a rufe mu."
Meelat ce tai dariya, sannan ta kalli Iro tace " kwantar da hankalin ka, babu abin da zan muku, juya wa tayi wajen Nass wanda b'acin rai da takaici sun hana shi cewa komai, Meelat tace " yanzu dai ka gasgata zance na koh, ka dai ji da kunnen ka waje na ya zo, amma duk da yana makaho baya gani burin shi ya fahimci hali na kafin ya tunkare ni, kai kuma a ranar da ka fara gani na ka tunkaro ni da maganar so, ba tare da kasan wacece ni, a ina nake, ya halina yake, hakan da ka yi ya tabbatar mun kyan fuskata kad'ai ya rud'aka, ba wani abu ba, to ni har gobe wannan makahon ya fi mun kai, kuma ba kai bane zab'i na ka yi hak'uri ka cire ni daga ranka.
Meelat ta juyo da kallon ta ga su Ado tace " ku tashi mu tafi, " ba musu su Ado suka tashi suka bi bayan Meelat.
Gun su Real Khady su Meelat suka nufa, wad'anda suke a zaune kamar an dasa su, duk wannan wainar da ake toya wa suna zaune basu tashi ba, idon su dai na kai, jira suke ta dawo su sha labari, kuma sai suka ga ta taho da mabarata a cewar su.
Nass na tsaye kamar wanda aka dasa, tsabar b'acin rai yasa ya kasa koda motsawa, zuciyar shi ce ke tafasa yana jijjiga kai, a ran shi yana fad'in wai yau shi ake fifita matsayin nak'asasshe a kan na shi.
_lallai Ado, Nass zai yi layya da naman ka babu ruwan BK da MEELAT._
_Nak'asassu bayin Allah, wato baiwar da Allah yai musu tana da yawa, harda wadda zasu bayyana soyayyar su cikin sauk'i, ba komai bace face GASKIYAR SU, ita ke sa suyi nasara A komai._
muje zuwa
0 comments:
Post a Comment