Meelat ta kalle su tace " ku tashi mu wuce gida kawai wancan dak'ik'in ya b'ata mana lokaci. "
Real khady tace " to su kuma wad'annan ina zaki kai su da naga kin taho da su? "
Meelat tace " ke dai muje, ko menene ma ma yi maganar daga baya."
Tashi suka yi gaba d'ayan su suka nufa motocin suka shisshiga, Ado motar su Meelat suka shiga, da Meelat da Ado da Iro suna baya, ita kuma Real Khady da Rukeey suna gaban motar, Rukeey ce ta ja motar, driver ya shiga ta securitys, suka d'auki hanya.
Nass ne yai tafi da hannun shi, tare da fad'in a motsa Mazaje, nan da nan suma suka shiga nasu motocin suka bi su Meelat a baya.
Suna zuwa dai dai bakin titin da su Ado suke zama suka faka Motocin, Meelat ta kalle su tace " to anzo wajen da zaku sauka, "
Suna kici kicin bud'e k'ofa su fita Meelat tace " ku tsaya a bud'e muku," bud'e musu ta yi, sannan ta ciro dubu goma ta mik'a musu, Iro ya karb'a ya mik'a wa Ado a hannun shi.
Ado ya girgiza kai yace " A'a Hajiya ki bar kud'in ki, ni wannan karramawar taki ma kad'ai ta ishe ni. "
Meelat tace " meyasa ba zaka karb'a ba? "
Ado yace " tun da nake bayan Inna ta da malami na, sai wannan Yaron da yake min jagora babu wani me sha'awar rab'ata sai yan'uwa na nak'asassu, ada nai tunanin ko ni kad'ai ne, sai daga baya na lura duk wani nak'asasshe haka yake fuskanta, tsakanin mu da mutane sai in sun zo bada sadaka su mik'a mana su wuce, ban tab'a tunanin magana zata had'amu dake ba, ni ina zuwa ne kawai domin samar wa zuciyata abin da take so, sai gashi kinzo wajena kuma har kika saurari matsalata, ni wannan kad'ai ma ya ishe ni farin ciki a rayuwa Hajiya, Allah ya saka miki da Alkhairi yasa ki gama da duniya lafiya, " yana maganar yana goge hawayen da ke fitowa daga idanun shi.
Meelat uwar tausayi itama hawayen take yi, ba ita kad'ai ba hatta su Rukeey ya basu tausayi, share hawayen nata ta yi, sannan ta kalle shi tace " Babu kyau mai da hannun kyauta baya, ka karb'a nice na yi niyya.
Babu yanda bata yi da shi ba ya karb'i kud'in nan amma ya k'i karb'a.
Sai da tace ba zata k'ara zuwa Shoprite ba sannan ya karb'a tare da yin godiya, su dai su Real Khady kallon ikon Allah kawai suke yi.
Fitowa suka yi daga cikin Motar, har sun juya zasu k'arasa wajen Musa dake can gefe yana ta faman kallon ikon Allah, Meelat har sun ja sa wa Motar su Key sai Ado ya juyo, Meelat tace wa Rukeey " tsaya karki tafi," Real Khady se surfa mata masifa take, tace " wai ke yau meke damunki ne haka," ita dai Meelat bata kulata ba, fitowa ta yi daga cikin Motar, ta k'arasa inda su Ado suka ja suka tsaya, tace " lafiya me kuma ya tsaida ku? "
Ado yace " dama……, ya kasa fad'in Abin da yake son cewa, Meelat tai murmushi tace " suna na Jameela, ana ce min Meelat," daga haka sai ta juya ta shige cikin motar su, suka ja sai gida.
Nass ma da suke can baya nesa da su suka ja motar su, suka ci gaba da bin su Meelat a baya, duk inda suka bi suna biye da su har suka k'araso katafaren gidan su Meelat, Shi kanshi Nass ya jinjina dukiyar da aka narka aka gina wannan gidan, sai da ya d'an jima a k'ofar gidan, sannan suka juyar da kan motar su, suka nufi gida.
Real Khady da Rukeey ne suka tsare Meelat da tambayoyi a kan sai ta fad'a musu abinda ya faru d'azu da kuma tsakanin ta da wannan makahon, suna cikin Mota ko cikin gidan basu bari sun shiga ba tukun,
Nan Meelat ta kwashe duk abinda ya faru a shoprite ta fad'a musu.
Rukeey tace to shi kuma makahon fa, me kike nufi da baki lokacin ki da kikai haka?"
Real Khady tace " yauwa tambayar mana ita dai, kar taje ta zubar mana da aji haka kawai, kuma wai ma tsaya, ba ce mana kika yi duk wanda muka ga har kin je gare shi, kuma har yaga murmushin ki shine zab'in ki ba, to idan kina wa kowane kare da doki haka taya za'ai mu gane wanne ne daga ciki?"
Meelat ta kalle su tai murmushi, ta lura yau haushin ta suke ji, musamman ma Real Khady, saboda kawai ta saurari bawan Allah kuma ta sa shi a cikin motar su.
Meelat tace " haba guys ku kwantar da hankalin ku, kawai taimako ne, amma Abun mamaki shi kad'ai ne na taki sa'a yana da Abu d'aya daga cikin abubuwan da nake so ace zab'i na ya mallake su, in har na same shi da sauran abubuwan da nake muradi to tabbas shine miji na, ta b'alle murfin Motar ta fice ta shige gida abinta, ta barsu nan zaune turus da mamakin ta."
Meelat tana shiga gida ta tarar da Dadyn ta ya dawo daga malesia, da gudu ta je gare shi, tana fad'in oyoyo Dady nah, ta rungume shi cike da farin ciki mara misaltuwa.
Dady yana dariya yace " to d'aga ni mana ko sai kin k'arasa ni," Meelat ta d'ago ta zauna daga gefen shi, tace Dady yaushe ka dawo? "
Dady yace " kuna fita ba dad'e wa na shigo," Meelat ta kalli Mumy tace " Mumy shine baki kira kin fad'a mun ba koh," tayi rau rau kamar zata yi kuka. "
Mumy tayi dariya, sannan tace "Dadyn naki ne yace kar a sanar dake, har sai kin dawo. "
Meelat ta kalli Dadyn ta, tace " Dady ina tsaraba ta? " Dady yace " zan baki, amma sai kin bani labarin siriki na da kika samo mana.
Meelat ta rufe ido, sannan ta tashi da gudu ta haye sama, su Dady suka bita da kallo suna dariya.
Meelat tana shiga d'akin ta ta tarar da shi a gyare, bayi ta fad'a ta shek'a wanka, ta yi Alwala, sannan ta fito ta tsantsara kwalliya, ta shimfid'a daddumar ta, ta yi sallah, bayan ta idar tayi Addu'a, sannan ta kwanta kan gadon ta, Makahonta ta tuno, sai ta yi murmushi, rufe ido ta yi Amma abin mamaki shi take tunowa lokacin da yake mata magiya karta sa a d'aure su, sannan ta tuna lokacin da yake mata godiya, A zuciyar ta tace " Allah sarki ashe suna jin ciwo a kan ko in kula da ake nuna musu, ashe suna jin dad'i lokacin da mutane suka nuna musu kulawa, ta dad'e tana tuno abin da ya faru tsakanin ta da Ado kafin bacci yai awon gaba da ita.
……………………
B'angaren su Ado kuwa, suna k'araso wa wajen Musa suka yi mishi sallama, Ado ya sami waje ya zauna.
Musa Gurgu ya bi Ado da kallo, yana jinjina karambani da siyar da rai irin nashi, yace " Ado daga ina kuke haka? "
Ado ya bashi labari tun daga Farkon fara zuwan su Shoprite, har zuwa yau da ya gansu tare da Meelat a Mota.
Musa ya numfasa, sannan yace " wallahi Ado ka yi taka tsan-tsan da irin wad'an nan mutanen. "
Ado yace " insha Allah ba abin da zai faru sai alkhairi," ya ciro kud'in da ta bashi ya nuna wa musa, sannan ya cire dubu biyar ya ba musa, musa ya karb'a ya zari dubu uku yace " sun isa, Allah saka mata da alkhairi," sauran dubu biyun Ado ya ba Iro kyauta, shima Iro cike da murna yai mishi godiya, Sannan suka ci gaba da hirar su.
B'angaren Nass kuwa suna shigo wa cikin gida suka faka Mota, da sauri ya shige cikin gida b'angaren Dad d'in shi ya nufa, da sallamar shi ya shiga d'akin, ya taki sa'a kuwa Mum ma tana cikin d'akin, fad'i take yauwa gashi nan ma ya dawo.
Nass ya samu waje ya zauna, sannan ya kwashi gaisuwa, Dad ya kalli Nass yace " Naseer maganar ka muke yi a game da matar Aure, kana da wadda kake so ne ko mu baka zab'in mu? "
Nass yace " yes Dad, akwai yarinyar da na gani nake so, gidan su yana nan a Tudun Nufawa. "
Dad yace " ya sunan ta, kuma waye mahaifin ta? " Nass yace " no Dad ban san sunan ta ba, kuma bansan sunan mahaifinta ba, dan Allah Dad ku je ku nemar min Auren ta. "
Dad yace " ok gobe zamu tafi, ni da Uncle d'inka nemar maka auren ta, " Nass ya washe hak'ora, sannan yace " na gode Dad," ya tashi ya fice daga d'akin cike da farin ciki. "
TOPHAπ³
muje zuwa
urs π
±Kππ
[1/7, 10:43 AM] Bk: ππππππππππ
NAK'ASASSHE MA MUTUM NE
ππππππππππ
Writen by BILKISU Z. YA'U (π
±K)
_(Yar gatan exclusive)_
♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
_(Home of peace, honour and super writer's)_
SADAUKARWA GA: MEELAT A.H.K
Dedicated to
MEELAT A.H.K
_MY BLOOD! meelat, sarauniyar matan duk africa, jarumar jarumai, gwanar gwanaye, fitacciyar dukkanin fitattu, tauraruwar taurari, na fad'a kuma kece zahra, Allah ya k'ara d'aga darajar ki my meelat, So akan ce had'i na rabba, zuciya ke kad'ai ta duba, kin zamo jini na, babu na biyun ki, masoyiyar k'warai kenan, masoyiyar gaske, waye zai tab'a ki a yanzu yasha mamaki, Allah ya raya ki musha biki, ranar wuni zanyi ina kwaso shoki yasin ko da kid'a ko babu kid'a_
Page 35 to 40
Yau ta kama Lahadi, yau ma kamar kullum Meelat ta shirya tsaf domin tafiya Shoprite, hakan ya zame musu tamkar jiki ne ita da Aminan ta du ranakun da basu da aiki sai sun je, tana fitowa suka gaisa da Mumy da Dad d'in ta, sannan tai musu sallama ta fito, turus ta tsaya wurin motoci ganin Aminan ta har sun zo amma basu shiga ba.
K'arasawa ta yi wajen Motar su, tace " wannan wane irin sabon salo ne kuka tsiro da shi? " Real Khady ce ta dalla mata harara ba tare da sunce komai ba, Meelat tai murmushi sannan tace " Allah baku hak'uri, Dady ya dawo sai ku shiga ku gaisa ai, kallon ta suka yi har suna had'a baki wajen cewa " haba, dagaske?" basu jira jin amsar ta ba suka yi cikin gidan da gudun su.
Meelat ce ke ta faman jiran su har yanzu basu fito ba, tsaki ta ja tace " wad'annan zasu b'ata wa mutane lokaci, sai ta bisu cikin gidan, su kuma da biyu suka yi mata haka dan su rama abin da ta yi musu jiya, koda ta shiga tana musu masifa dan me zasu zauna daga gaisawa, banza suka yi da ita, sai da suka gama zuba surutun su duk dan taji haushi, sai wajen sha d'aya sannan suka fito, sun fito da Motocin su kenan su kuma motocin su Gwamna, wato Dad d'in Nass suka kutso cikin gidan, su Meelat suka basu waje, sai da Motocin Gwamna suka gama shigewa sannan suka ja nasu suka tafi.
Suna tafe suna hira sun share Meelat, Meelat tai murmushi a ranta tace ku gama naku zan rama nawa in mun je can.
Gwamna ya samu kyakkywan tarba shi da k'anin shi a wajen Dadyn Meelat, bayan sun gaisa sai Uncle d'in Nass ya yi gyaran murya, yace " abin da ke tafe da mu shine, d'an mu ya ga 'yar wajen ka yana so, shine muka zo nema masa auren ta, idan ba wani tsayayye. "
Dad cike da farin ciki yace " nayi matuk'ar farin ciki da zuwan wannan rana, Amma ai mini hak'uri har in ji ta bakin yarinyar, bata nan ne, yanzu suka fita.
Uncle zai yi magana Gwamna ya yi saurin cewa " ba matsala," ya ciro katin Uncle me had'e da lambar waya a jiki ya mik'a wa Dadyn Meelat, yace " gashi nan duk yanda ake ciki ka sanar mana ta lambar da ke jikin wannan katin. "
Mahaifin Meelat yace " ba matsala insha Allah, nan dai suka yi sallama, ya rako su har inda suka faka Motocin su, suka shiga suka d'auki hanyar komawa gida.
B'angaren su Meelat kuwa, suna isowa wajen zaman su Ado ta fara dubawa, bata ganshi ba, kuma da zasu zo ma bata ganshi a bakin titi ba, dudduba wa tayi ko zata ganshi amma babu shi babu alamar shi, sai taji duk ta damu, dawowa gun su Real Khady ta yi ta zauna, se dai yau duk hirar da suka saba, da kuma wasannin da suke yi babu wanda Meelat ta yi, suma su Rukeey duk sai suka ji ba dad'i, tambayar ta suka shiga yi lafiya tace " musu ba komai," basu wani dad'e a wajen ba suka juyo suka dawo gida.
Tun ranar da su Meelat suka ragewa su Ado hanya bata k'ara ganin Ado ba, ko taje shoprite bata ganin shi, haka ma a bakin titi wajen zaman su, duk tabi ta damu, tayi iya tunanin ta wajen gano dalilin da yasa ta damu dashi haka, tun tana k'aryata zuciyarta a kan bata son shi har tazo ta gasgata, saboda damuwa da tayi sosai a kan lamuran shi, da kuma wani mugun tausayin shi da take ji.
B'angaren Ado kuwa typod ne da zazzab'in maleria ya b'oye shi, gashi lokacin sanyi ne mura ta yi mishi kyakkyawan kamu, da yaji sauk'i kwana biyu sai ciwon ya dawo, d'an kud'in da Meelat ta bashi da su akai ta se mishi magani har suma suka k'are.
Yau kusan sati d'aya kenan Meelat bata k'ara sa Ado Makaho a ido ba, kuma gashi ta kasa mantawa da shi a ranta, yanzu ma kwance take a d'akin ta, idon ta rufe, amma shi kawai take ta gani, zumbur ta mik'e tsaye bayan ta tuno da mafitar inda zata same shi.
Fitowa tayi daga d'akin ta, ta sauko falon k'asa, Mumy ta tarar ita da Dady suna hira, Dady ya kalle ta yace " yauwa 'yar halak dama maganar ki muke yi sai gaki, zauna kiji."
Meelat tace " Dady dan Allah ka yi hak'uri ka bani dama in je gidan su Rukeey in dawo please Dady," ta k'arasa maganar cike da shagwab'a.
Dady yace " to je ki dawo, amma kar ki dad'e," cike da murna tayi godiya sannan ta juya tace wa Mumy " sai na dawo Mumy."
Mumy tace " sai kin dawo ki kula da kanki. "
Tana fita harabar gidan masu tsaron ta suka taso tamkar jira suke, a tare suka faffad'a cikin Motocin su, suka fita daga cikin gidan.
Bakin titi dai dai in da su Ado ke zama suka faka Motocin nasu, se dai yau ma kamar kullum Musa ne kad'ai ba Ado a wajen, fitowa Meelat ta yi daga cikin Motar ta yi tattaki har zuwa inda musa yake zaune, tayi mishi sallama, ya amsa, bayan sun gaisa tace " dan Allah wannan bawan Allahn da ke zama nan kusa da kai fa? "
Musa yace " Ado makaho kike nufi koh? "
Meelat duk da bata san sunan shi ba har yanzu, amma sai tace " eh shine, ina yake? "
Musa yace " Allah sarki, ai Ado yana gida a kwance bashi da lafiya, shi yasa ma kika daina ganin shi a nan. "
Ana fad'in bashi da lafiya Meelat gaban ta yayi wani irin mugun fad'uwa, k'arfin hali tayi tace " dan Allah ko zaka iya kaimu gidan su? "
Musa Gurgu ya yi shiru yana nazari, can sai yace " eh to zan raka ku, amma gaskiya bazan shiga Motarku ba," Meelat tayi murmushi, sannan tace " to muje "
Musa Gurgu yana gaba su meelat na biye dashi, tana kallon yanda yake ta jan jiki, k'walla taji ta tarun mata a ido, a ranta tace Allah sarki, shi kuma a haka yake tashi rayuwar, ko wannan ma kad'ai ka kalla ya ishe ka gode wa Allah, tare da k'ara jin tsoron shi.
K'ofar wani rub'ab'b'en gida ya shiga da su, dan gefen gidan ma da kara aka gewaye shi, Musa ya kalle su yace " nan ne gidan, bari na shiga na sanar da su zuwan ku, be jira amsawar su ba ya fad'a cikin gidan, Inna ya tarar a tsakar gida tana 'yan kaye kaye, ya gaishe ta sannan ya shaida mata sunyi bak'i, Inna a tunanin ta 'yan uwansu ne na k'auye suka ziyarto su, tace wa Musa ya shigo da su.
Musa ya fito, yace musu su shigo, ya juya Meelat ta bishi, ya yi mata jagora har cikin gidan.
Da yake masu tsaronta ta dakatar da su a k'ofar gidan, ita da Musa kad'ai suka shigo ciki, Inna ta yi mata kyakkyawan tarba, ta shimfid'a mata tabarma ta zauna, sannan suka gaisa, bayan sun gaisa ne Inna ta kalle ta tace " se dai baiwar Allah ban shaida ki ba, " Meelat da take gaf da fara kuka tace " Inna sunana Meelat, duk zan wuce nakan tsaya mu gaisa da su Ado, to kwana biyu ne ban ganshi ba, shine da na tambayi wannan ta nuna Musa, yace mini bashi da lafiya, shine nace ya rakoni in duba shi.
Inna tana jin sunan da ta ambata sai ta washe baki, tace " sannu baiwar Allah dama kece Meelat d'in da Ado ke yawan bani labari, naji duk irin kyautar da kike mishi, Allah ya saka miki da Alkhairi, tashi muje in kai ki wajen shi. "
Meelat ta mik'e ta bi Inna har d'akin da Ado yake, kwance suka tarar da shi yana ta bacci, Meelat ta k'ura mishi ido ya rame sosai, fuskar shi ta k'ara kyau, bin d'akin da yake a matsayin makwancin bawa tayi da kallo, sai ta duk'ar da kanta ta fashe da kuka, kuka take sosai kamar ranta zai bar jikin ta, Inna ta taso da sauri tazo inda Meelat take tace " kiyi hak'uri 'yar Inna, ai Ado yaji sauk'i sosai, dan kafin ma ya tashi daga bacci sai da muka sha hira dashi, bari ma in tashe shi ku gaisa."
Meelat ta d'ago kai tare da fad'in A'ah Inna karki tashe shi, zan dawo Anjima ko gobe insha Allah," ta ciro kud'i a jakar ta kimanin dubu Ashirin ta mik'a wa Inna, sannan tace " kuma zan aiko da sak'o Anjima kad'an, Inna tayi ta mata godiya, tare da sa mata Albarka."
Inna tace " amma bazai ji dad'i ba idan na fad'a mishi kinzo ban tashe shi ba, amma tunda kince zaki dawo shikenan, mun gode sosai, Allah ya saka da Alkhairi, Allah ya bar zumunci. "
Meelat ta mik'e ta fito daga d'akin, inna ta yi mata rakiya har k'ofar gida, sannan suka yi sallama, k'arasawa suka yi bakin titi inda suka faka Motocin su, zaro dubu biyar ta yi ta mik'a wa musa, yana ta faman godiya, Drivern ta ta kalla ta mik'a mishi dubu dari biyu tace " ka tafi kasuwa ka had'o kayan Abinci ka kai gidan da muka baro yanzu, in be isa ba ka kira ni a waya ka fad'a min," Driver yace " an gama ranki ya dad'e, ya shiga mota ya juya, su kuma suka shiga motocin suka yi hanyar gida, suna tafe tana share hawayen da ke gangarowa kan fuskarta, A zuciyar ta tace Allah sarki, yanzu dama akwai wad'an da suke irin wannan rayuwar, tausayin su ya mugun kamata, suna tafe tana tunani tare da zubar da hawaye har suka k'araso gida.
Bayan sun faka Motocin ta fito ta shiga falon d'auke da sallama, har yanzu iyayen nata suna zaune a falo suna hirar su, k'arasawa tayi kusa da Dadyn ta ta zauna, sannan tace " sannunku da hutawa," a tare suka had'a baki suma wajen yiwa d'iyar su tilo sannu da zuwa.
Meelat ta kalli mahaifin nata, duk da bata cikin yanayi na jin dad'i, amma sai ta dake saboda bata so iyayenta su gano hankalinsu ya tashi, k'ak'alo fara'ar dole tayi a fuskar ta, tace " Dady na dawo muyi maganar yanzu.
Murmushi Dadyn ta ya yi, sannan yace " Gwamna yazo gidan nan satin da ya wuce, yazo nema wa d'an shi auren ki, " wani irin hantsilowa tayi daga kan kujera tare da zazzaro ido tace " Dady mahaifin Nass kake nufi? "
Dady yace " eh shi, ko bakya son shi ne? "
Meelat tace " Dady wallahi bana k'aunar shi, bashi da hankali, balle tunani, bashi bane zab'ina, Dady ina da wanda nake so,"
Dady yace " to Alhamdulillah, wanene wanda kike so?
TAB'D'IJAM
muje zuwa
urs π
±Kππ
[1/7, 10:43 AM] Bk: ππππππππππ
NAK'ASASSHE MA MUTUM NE
ππππππππππ
Writen by BILKISU Z. YA'U (π
±K)
_(Yar gatan exclusive)_
♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
_(Home of peace, honour and super writer's)_
SADAUKARWA GA: MEELAT A.H.K
Dedicated to MMN LABYB
_Mmn labyb BK ta yaba matuk'a da son da kike wa nak'asasshe ma mutum ne, kuma tana godiya sosai matuk'a gaya da addu'arki gare ta, tana godiya, Allah ya saka da Alkhairi, yabar zumunci Ameen, sannan Meelat da Ado makaho sun ce a gaishe ki, wannan shafin naki ne, kiyi yadda kike so dashi._
Page 40 to 45
Meelat ta kalli mahaifin ta tace " Dady dan Allah ka d'an bani lokaci, zan kawo shi wajen ka.
Dady yace " to na baki nan da sati d'aya," Meelat ta kalle shi tace " haba Dady sati ya yi kad'an, ina laifin wata d'aya, sai kace kun gaji da gani na.
Dady ya yi dariya, sannan yace " Meelat kenan, duk yanda muka kai ga sonki ai zamu fi farin ciki mu ga kina d'akin mijin ki, to an baki wata. "
Meelat tace " to Dady," tashi ta yi ta haye sama, ta kutsa cikin d'akin ta, kwanta wa ta yi saman gado tana k'ara hango hoton gidan da su Ado suke ciki, tunani take dama akwai masu irin wannan rayuwar, zuciyarta ta tausaya musu matuk'a, kuma ta k'uduri aniyar taimaka musu, Driver ne ya k'wank'wasa d'akin ta, ta bashi umurnin shigowa ciki, bayan ya shigo ya duk'a k'asa tare da d'an rissinawa yace " ranki ya dad'e na kai musu, babu abin da ba'a siya ba na kayan abinci, wallahi da nakai tsohuwar nan kuka ta kama yi sosai, tama kasa cewa komai sai…………, Meelat ce ta d'aga mishi hannu, tace " bana son dogon bayani, tashi kaje. "
Bayan ya fita a fili Meelat tace " Allah sarki bayin Allah, sai yanzu na fahimci dalilin had'uwar mu da kai Ado, Allah ya kawo ka cikin rayuwata ne domin in taimake ka," ta share hawayen da ya zubo mata, dak'yar ta samu bacci ya d'auke ta.
Dady ya ciro wannan katin da iyayen Nass suka bashi, ya shigar da lambobin cikin wayar shi, tare da kira, sai da ta kusa katsewa sannan Uncle d'in ya d'aga, bayan sun gaisa Dadyn Meelat ya gabatar da kanshi, sannan ya basu hak'uri, tare da fad'a musu ta riga da ta fitar da zab'in ta, Uncle d'in Nass yace " ba damuwa, Allah ya tabbatar mana da Alkhairi, " Dadyn Meelat yace " ameen " ya k'ara basu hak'uri, sannan suka yi sallama.
Uncle d'in Nass suna gama wayar ya tattara duk abin da yake ya aje, ya fito sai gidan gwamna, bayan sun gaisa da Dad d'in Nass sannan ya fad'a mishi duk yanda suka yi da mahaifin Meelat, Dad d'in Nass yace " shikenan ma, dama nafi son ya auri 'yar aminina, bari yazo sai mu tattauna akan maganar. "
………………………
B'angaren su Ado kuwa tashin shi kenan daga bacci, ya yunk'ura ya tashi ya fito, ya tsaya bakin k'ofar d'akin shi, Inna ce ta hango shi da sauri ta taho wajen shi tana fad'in " d'an Inna ka tashi, zo kaima kaga Alkhairin da wannan baiwar Allahn ta yi mana," ta zo ta ja hannun shi, Ado yace " Inna da wane idon zanga abin da kike son nuna min d'in? " Inna tace " kai dai taho, " sai da tabi kayan nan d'aya bayan d'aya ta d'ora hannun shi a kansu tare da yi mishi bayanin duk abin da ya tab'a.
Ado cike da farin ciki shima yace " Inna wanene yai mana wannan alkhairin? " Inna tace " wa kake tunani banda wannan d'iyar Albarkar meeltat, " cikin sauri yace " Hajiya Meelat kike nufi? " Inna tace " eh ita ce" Ado yace " tazo gidan nan ne? " Inna tace " tazo kana bacci, musa ya kawo su nan gidan, kuma ita tace kar a tashe ka, zata zawo anjima ko gobe. "
Ado yace " Allah sarki Hajiya ta, Allah ya saka mata da Alkhairi," Inna tace " Ameen d'an Inna, bari na juye maka ruwa kaje ka yi wanka" Ado yace " to Inna," bayan ta juye mishi ruwan wanka ta kai mishi bayi, sannan ta kai shi har ban d'akin saboda jikin shi har yanzu babu k'arfi sannan ta fito.
Bayan ya fito A dai dai Ana kiran sallar la'asar, Alwala ya yi, sannan ya shiga cikin d'akin shi, bayan ya laliba kayan da Inna ta aje mishi kan katifar shi ya saka, sannan ya tayar da sallah, yana idarwa kuma ya kama karatun Qur'ani.
Karfe hud'u da kwata Meelat ta tashi daga bacci, da sauri ta diro daga kan gado, taje ta yi Alwala tayi sallah, bayan ta idar sannan ta tashi taje ta yi wanka, bayan ta fito ta tsantsara kwalliya, sannan ta saka doguwar riga yar kanti kalar blue da fari, ga wasu duwatsu a jikin rigar, gaskiya ta yi kyau sosai, ta d'auko mayafin doguwar rigar ta saka, ta d'auko jakar ta da takalmi kalar kayan ta saka, sannan ta fito daga d'akin ta sauko k'asa, babu kowa a falon, d'akin Momy ta wuce, ta tarar ta shiga wanka, zama ta yi a d'akin tana jira ta fito, bata dad'e ba tana jiran ta sai gata ta fito.
Mumy tace " Baby yanzu kuma sai ina? "
Meelat tace " wallahi Mumy wani bawan Allah ne bashi da lafiya zanje gidan su na dubo shi," Mumy tace " to sai kin dawo, ki kula da kanki, kuma kar ki dad'e kiin ga yamma tayi," Meelat tace " to Mumy nagode sai na dawo."
Meelat ta fito ta shiga Motar ta, Drever ya ja suka fita sai hanyar gidab su Ado, suna isowa suka faka motocin su, Meelat ta fito tun daga k'ofar gida take jin k'ira'a me d'an karen dad'i tana tashi, ta shiga cikin gidan tare da yin sallama.
Inna ta Amsa cike da fara'a tace " 'yar albarka kece tafe, bakya gajiya, " Meelat tace " eh Inna nice," bayan sun gaisa Inna tace " muje yana cikin d'aki, " tashi suka yi suka doshi d'akin Ado, har yanzu yana kan buhun shi wanda yake a madadin dadduma yana karatu, zama tayi a can nesa da shi, Inna ta fita ta ci gaba da aikace aikacen ta, meelat kuwa k'ura mishi ido tayi, tare da sauraren daddad'an k'ira'ar shi.
Yana kai k'arshen surar da yake karantawa ya dasa aya, tare da yin Addu'a ya shafa, sannan yace " Hajiya sannu da zuwa," Meelat tayi murmushi, sannan tace " yauwa, ya k'arfin jikin ka? "
Ado yace " Alhamdulillah, na samu sauk'i, Meelat tace " to Allah ya k'ara sauk'i, yasa kaffara ne. "
Ado yace " Inna ta fad'a mun Abun alkhairan da kikai mana, Allah ya saka da Alkhairi, ya biya ki da gidan Aljanna. "
Meelat tace " ba damuwa, yiwa kaine ai, gobe asabar zaka iya zuwa shoprite? "
Ado yace zan iya insha Allah, ai naji sauk'i sosai, Meelat tace to zan turo a d'auke ka goben, sai ka shirya da wuri," Ado yace " insha Allah," sun dad'e suna hira, daga k'arshe Meelat tai musu sallama, ta fito cikin farin ciki ta tafi gida.
B'angaren Nass kuwa, bayan uncle d'in shi yazo ya fad'a wa Dad d'in Nass sak'on Mahaifin Meelat, Uncle d'in yana fita Dad d'in Nass ya ciro waya ya kira shi, yace duk inda yake ya zo gida ya same shi yana son ganin shi, Nass a lokacin yana club suna watayawa da yan mata, babu yanda ya iya, haka ya yakice su ya taho gida domin amsa kiran Dad d'in shi.
Yana k'arasowa ya faka motar shi, tare da b'alle murfin mota ya yi cikin gida da saurin shi, yana shiga direct sashen Dad d'in shi ya wuce, yau ma suna tare da Mum d'in shi d'akin suna hira, k'araso wa ya yi, ya samu waje ya zauna, yace " sannunku Dad gani, Allah yasa dai lafiya? "
Dad ya kalle shi yace " kan maganar yarinyar da ka tura mu gidan su nemar maka auren ta ne, haba Nass yana jin haka ya gyara zama tare da washe hak'ora, yace " sun bani ita ko Dad? " Dad yace " yau mahaifin ta ya kira, kuma ya shaida mana cewa muyi hak'uri yarinya tace ba kai take so ba, tana da wanda take so, saboda haka ni na zab'ar maka yarinyar da zaka Aura, 'yar amini na Alhaji umaru, sai kaje ka ganta ku sasanta. "
Nan da nan annurin fuskar Nass ya d'auke, ya mik'e tsaye, sannan yace " wallahi muddin ban Auri Meelat ba to kuma bana son taku zab'in, ku barni na zab'o da kaina, yana gama fad'in haka yasa kai ya fice daga d'akin. "
Washe gari Ado ne ya shirya kamar yanda suka shirya shi da Meelat, bayan ya gama shiryawa yai wa Inna sallama, ya tafi bakin titi inda ya tarar da Musa Gurgu zaune, Ado ya zauna kusa da shi suka fara hira.
Suna cikin hira ne wata mota fara k'al me shegen kyau, tazo ta faka a gaban su, bayan Drivern ya yi fakin d'in motar ne ya fito ya zo har inda su Ado makaho suke zaune, bayan ya yi musu sallama, suka gaisa, sannan ya dubi Musa yace " Meelat ce ta turo ni in zo in d'auki Ado in kai shi inda take, Ado ya yi murmushi, tare da mik'ewa tsaye, Musa ya kalli Ado Makaho yace " Ado sai ina? " Ado yace " kaga ana jira na, amma in na dawo duk yanda muka yi da ita zan sanar da kai, Musa yace " to sai kun dawo," suka yi sallama Ado da driver suka d'auki hanya sai Shoprite.
Basu dad'e suna tafiya ba suka iso wajen, saboda gudun da Drivern ya yi.
Koda suka iso su meelat basu k'araso ba, bayan Driver ya yi fakin sai ya bud'e K'ofa ya fito, ya zagayo b'arayin da Ado yake zaune ya taimaka mishi suka fito daga motar, wani k'ayataccen waje ya zaunar dashi kan wata had'ad'd'iyar kujera, sannan ya kalle shi yace " ka d'an jira ta ta k'araso, " Ado yace ba matsala
Driver yasa aka kawo wa Ado lemu ya bud'e mishi, sannan ya koma wajen motar shi ya d'ane saman motar yana jiran zuwan Meelat, dan cewa tayi ya kula dashi, kar ya sake ya bar shi shi kad'ai ya jira har tazo.
Bayan Ado ya gama shan lemun da Driver ya mik'a mishi sai ya yi hamdala ga ubangiji, sannan ya fara karatun Qur'ani da k'ira'ar nan tashi me shegen dad'i, yanda kasan yaron sudais.
Yana cikin karatun ne su Meelat da aminanta su Ruqeey suka danno kai da motocin su, suna fitowa ta hau waige waige, se dai bata hango shi ba, sai da suka shigo ciki sosai sannan ta hango shi Can nesa da inda suke, wata kyakkyawar Ajiyar zuciya ta saki farin ciki taji ya lullub'eta sakamakon ganin shi da tayi, suna zama sun fara hira ta tashi tace musu tana zuwa.
Wajen Ado ta nufa kai tsaye, daga inda suke zuwa inda yake akwai tazara a tsakani, ko da ta isa wajen har yanzu karatun yake yi, kujera ta ja ta zauna, sannan ta zuba tagumi da hannu biyu tare da k'ura mishi ido, tana matuk'ar jin dad'in k'ira'ar shi, bata katse shi ba har sai da ya kai aya, tare da jero dogayen Addu'o'i sannan ya shafa, yana shafawa Meelat tace " Amincin Allah su tabbata a gareka. "
Ado yace " Ameen Hajiyata, tare da ke "
Meelat tace " kana burge ni, saboda baka sanya da karatun Qur'ani."
Ado ya yi murmushi, sannan yace " haka ake so bawa ya kasance a koda yaushe ko menene mutum yake yi ya rik'a ambaton mahaliccin sa, walau karatun Qur'ani ko tasbihi, dan bawa bashi da tabbas akan ranar da Allah zai d'auki ran shi, baka san lokacin da Allah zai d'auki ranka ba,, shiyasa a koda yaushe ake so bawa ya rik'a aikata alkhairi, domin samun guzuri mai kyau. "
Meelat tace " Allah mai iko, baka gani amma Allah ya baka baiwar ilimi," Ado yace " tabbas Allah ya halicce ni a makaho bana gani, Amma ina godiya a gare shi har kullum da ya bani baiwa da basira na fahimtar Addini na, Allah kenan, in ya hana ka wani abun to sai ya azurta ka da wani Abun.
Meelat ta numfasa, sannan tace " Har yanzu fa bansan sunan ka ba, " Ado ya yi murmushi sannan yace " sunana Adamu, Amma anfi kirana da Ado Makaho."
K'ura ma Ado ido ta yi, ita dai har ga Allah tsarin rayuwar shi ya yi mata, Meelat tace " ina so ka bani labarin ka, ma'ana tarihin rayuwar ka."
Ado ya bata tarihin rayuwar shi tun daga lokacin da yake k'arami, da lokacin da ya rasa iyayen shi suka je k'auye akai musu kora da hali, har zuwa dalilin fara yin barar shi. "
Ado yana dasa aya yace " to hajiyata kinji tak'aitaccen tarihi na, shesshek'ar kukan ta ya ji, Ado yace "Subhanallah! Hajiya me yasa kike kuka kuma, ko nai miki laifi ne, dan girman Allah Hajiyata ki yi hak'uri ki daina kuka, bana k'aunar in ji damuwa a muryar ki, balle har inji sautin kukan ki, ita dai Meelat kuka take sosai, kuma bata ce komai ba, sai da ta yi mai isar ta sannan tayi shiru.
Ado ya lalubi Aljihun shi ya ciro hankici, ya juyo inda ya ji sautin kukan ta ya mik'o hannu yana lalube, yace " Ungo ki share hawayen ki hajiyata," karb'a Meelat tayi tare da yi mishi godiya, se dai sam hawaye ya kasa tsayawa a kan fuskar ta, ta kalle shi tace " Ado "
Ado yace " na'am hajiyata "
Meelat tace " zaka aure ni? "
Gaban shi ne ya hau luguden fad'uwa, saboda razana da ya yi sai da ya fad'o k'asa daga kan kujerar da yake zaune, amma da sauri ya mik'e tsaye ita ma ta mik'e, da wata irin murya me cike da firgici, tsoro, tashin hankali, Ado yace " iyeeeeeee, niiiiii!!! ? "
Muje zuwa
0 comments:
Post a Comment