Meelat ta zagaya inda kujerar shi ta fad'i ta d'aga ta gyara mishi, sannan ta kalle shi tace " kwantar da hankalin ka, zauna muyi magana. "
Ba musu Ado ya laluba mazaunin shi, ya koma ya zauna, Meelat tace " Ado bazan b'oye maka ba, ada a tsari na babu mutum irin ka, kuma babu nak'asasshe a ciki, balle kuma makaho wanda mata suka fi gudun aura, zabin mijina shine had'ad'd'en saurayi, kyakkyawa, me ilimi, kuma d'an wani fitacce wanda duniya ta san shi, kuma, wanda zai rik'a sani nishad'i a koda yaushe, kuma wanda yake matuk'ar k'aunata da tausayi na, amma yanzu had'uwata da kai ya sauya mun rayuwata gaba d'aya. "
Meelat ta numfasa, sannan ta ci gaba da cewa " a yanzu nafi k'aunar zama da mutum irin ka akan na zab'i zama da wanda yake da dukkan abubuwan da ni nake muradin ya had'a, a yanzu muradai na na baya dukkanin su sun rushe, dalili na anan shine, farko yanda naga ana gudun auren nak'asassu irin ku yasa ni kuma naji ina sha'awar auren irin ku, ban sani ba ko ta dalilin haka Allah ya ji k'ai na ya sani cikin Aljannar sa, dalili na biyu kuma tausayin ka ya sa na fara jin k'aunarka cikin raina, sannan Allah ya wadata ka da ilimi, wanda ko shi kad'ai zai sa nayi alfaharin zama da kai, kana da kyawawan d'abi'un da kowa ya zauna sai ya amfana da tarayya da mutum irinka, sannan kana da kyau, ina mai tabbatar maka da cewa koda baka amince ba to tabbas insha Allah Nak'asasshe shine mijina. "
Ado ya yi shiru, tare da kyakkyawan nazari akan maganganun Meelat, jin shirun ya yi yawa ne yasa meelat ta kalle shi tace " kayi shiru," Ado yace " Hajiya na rasa abun cewa ne, gaskiya kin zo da babbar magana me cike da k'alubale a ciki, idan kin kalle ni fa ni makaho ne, sannan talaka, idan na amince da auren ki ina zan ajiye ki, da wane kud'i zan kula da ke, ni ba ido ba balle in fita in nemo, hajiya me zaki ci da mutum iri na, d'an k'auye, wanda ko boko bai tab'a yi ba."
Meelat tayi murmushi, sannan tace " na tabbatar fa tuni kana sona, kana tsoron bayyana mun ne saboda ganin yanda Allah ya halicce ka, da kuma ganin matsayin da nake ciki na arziki, to ka sani bana k'aunar wannan matsayin muddin akwai masu rayuwa a doron duniya kwatan kwacin irin wadda na riske ka a ciki, iyaye na kuma a hankali zan shawo kan su su amince, babbar damuwata shine ka amince. "
Ado ya yi shiru, yana mamakin wannan baiwar Allahn, Meelat tace " Ado ya kuma kayi shiru," Ado yace hajiya tunani nake yanda za'ai hakan ta yiwu, kamar ni ace na auri mace irin ki."
Meelat ta had'e rai, tare da fad'in " dan ka rasa idanu ba yana nufin ka rasa komai bane, dan kana talaka ba yana nufin baza ka iya yin rayuwa kamar kowa bane, dan kana Nak'asasshe ba yana nufin kai ba mutum bane kamar kowa, Ado kar ka b'ata mun rai, a yanzu kai ba talaka bane tunda Allah ya baka wadatar ilimi da wadatar zuciya, baka san me irin halinka Allah yafi basu ikon cin ribar rayuwa ba, sannan daga nan idan mun gama magana zamu wuce gidan da ni na siya da kud'i na, kuma a yanxu na mallaka maka shi halak malak, motar da aka d'auko ka aciki, d'aya daga cikin motoci na ne, na baka ita halak malak, Drivern da ya d'auko ka ba nawa bane, naka ne, kuma bana buk'atar godiya a gareka, nayi domin Allah ne, idan kuma har kana so ka bani tukuici ne to sai kace ka amince zaka aure ni, hakan ne kad'ai a yanzu zanji ya faranta raina, Amma ban tilasta maka dole ba. "
Ado ya share hawayen shi, sannan yace " hajiyata bani da bakin da zan gode miki, se dai in cigaba da yi miki addu'a Allah ya d'aga darajarki, kuma na amince da k'udurin ki, kema kika amince kika zab'i zama da mutum iri na, taya ni zan k'i amince wa zama dake hajiyata, lallai na yarda so halitta ne, kuma babu ruwan shi da kyan fuska, ko wani abu, ban tab'a ganinki ba amma na kamu da k'aunarki sanadin muryarki har kasa bacci nake yi, Allah ya tabbatar da alkhairin sa, idan kin koma gida kiyi istihara domin neman zab'in Allah, nima zan je inyi. "
Su Rukeey ne suke ta faman neman ta, suna cikin neman nata ne suka hango ta can nesa ita da wani, tunkaro wajen suka yi, suna isowa suka ga ashe Ado makaho ne, Real khady tace " Meelat wai ke menene nufin ki na kula wannan Nak'asasshen, Ruqeey tace " dalilin baya wuce na taga ta zubar mana da mutunci, wannan talakan kike kulawa. "
Daga Ado har Meelat sun ji ciwon maganganun da su Real Khady suka yi, Meelat ta kalle su tace " Nak'asasshe shine wanda na zab'a a matsayin miji a gareni, ban fad'a muku ba duk saurayin da kuka ga na bawa lokaci na har yaga murmushi na to tabbas shine zab'i na? to ku sani, talakan shi na zab'a, kuma muddin bakwa so muyi fad'a da ku to ku daina Aiban ta mijin da zan aura."
Rukeey da Real khady suka saki baki da hanci tare da zaro ido suna mamakin jin furucin Meelat, Real khady tace " Ai kuwa tun wuri ki canza shawara wallahi, kafin na fad'a wa Dad, Rukeey tace " Meelat akan wannan abun ta nuna shi da yatsa, kike fad'a mana magana? "
Real khady tace " barta zo muje, ta ja hannun Rukeey suka bar wajen. "
Sam Meelat bata ji dad'in yanda suka yi da k'awayen ta ba, sannan bata ji dad'in abin da suka yi wa Ado ba, kallon shi ta yi, tare da bashi hak'uri, Ado yace " bakomai karki damu, nasan hakan zata faru, shiyasa ma na shirya wa faruwar hakan da yin hakuri da juriya, dan haka kar ki damu. "
Meelat tayi murmushi, sannan tace " tashi muje mu d'auki Inna muje kuga gidan, in da hali ma a yau nake so ku tare tunda komai an zuba a ciki, Ado ya yi murmushi yace " to muje, " suka tashi, suka shiga mota sai gida wajen Inna.
……………………
B'angaren Nass kuwa, tunda ya fita daga d'akin Dad d'in shi, sai ya nufi d'akin shi ya kulle kan shi, kayan d'akin ya shiga wurgi dasu duk ya ji wa kan shi ciwo, hango giya ya yi a gefen gadon shi, yaje ya d'auka, tare da b'alle murfin kwalbar, ya kai baki zai sha sai maganganun Meelat suka fad'o mishi, lokacin da take cewa " _kaga wannan makahon ya fi ka hankali da tunani_ " abin da keta dawo mishi kenan, wurgi ya yi da kwalbar giyar ta fad'i k'asa ta tarwatse, be tab'a son mace kamar yanda yake son meelat ba, duk da yasan kyanta da sha'awar su suka rinjeye shi zuwa gare ta har ya ji yana son auren ta, shi da ya maida mata kamar rigar sakawa, be tab'a yin nadamar rayuwar da yasa kanshi a ciki ba sai yau, fad'a wa kan gado ya yi, yana jan wahalallen numfashi mai cike da b'acin rai, daga haka bacci ya yi awon gaba da shi.
Meelat da Ado ne gaban Inna suna kora mata bayani, banda kukan dad'i babu abinda take yi, sai da tayi mai isarta sannan tayi shiru, Inna ta kalle su tace " Allah ya saka miki da Alkhairi 'yar nan, kamar yanda kika taimake mu kema Allah ya cigaba da tallafa wa rayuwarki, wallahi kamar kin sani Ado yana fita babu dad'e wa sai ga mai gidan yazo karb'ar kud'in haya. "
Meelat tayi murmushi, sannan tace " bakomai inna, ku tashi muje kar lokaci ya tafi, tashi sukai dukkan su, Inna ta fara d'ibar kaya Meelat ta kalle ta, tace " Inna ki bar komai anan, ko ku bawa Almajirai, duk abinda kuke buk'ata akwai acikin gidan, Inna tace to 'yar nan, Almajiran Malam aka kira sukai ta kwasar abin da suke buk'ata, harda kayan abincin da Meelat ta kawo, sai farin ciki suke, ko ba komai suma sun shaida karamci irin na wannan baiwar Allahn, bayan sun gama kwasa suka fito dukkan su suka ja gidan, suka shiga mota sai sharad'a, suna zuwa k'ofar wani tafkeken gida, dan gaskiya ba laifi yana da girma sosai, suka firfito suka shiga cikin gidan, hmmm wayyo Ashe had'uwar tana ciki, plat ne gangariya an zuba manya manyan set d'in kujeru masu Adon ja da bak'i da ratsin ash kalo, sai tafkeken tv na bango, ga d'akunan bacci har uku, kuma kowanne da band'aki a ciki, sannan acikin kowane d'akin baccin akwai wata k'ofa da zata sadaka da wani had'ad'd'en lambu, wato wurin shak'atawa, me cike da fulawoyi masu d'an karen k'amshi, sai kuma ta kai su had'ad'en kicin yasha kaya, sun dad'e a kicin Meelat na nunawa Inna yanda zatai amfani da abubuwa kafin ta kawo musu 'yar aiki, bayan ta gama nuna wa Inna ko ina, sai suka dawo falo, ta kunna musu tv, sannan suka zauna, godiya suka k'ara yi mata, tare da shi mata Albarka, sannan tayi musu sallama ta shiga mota sai gida.
Tana zuwa gida ta tarar da Dadyn ta da Mumy a tsaye, kuma kamar ransu a b'ace yake, k'arasowa inda suke tayi, sannan ta kalle su tace " Dady, Mumy, meke faruwa na ganku kamar kuna cikin damuwa? "
Dady ya kalle ta a fusace yace " daga ina kike? "
Gaban Meelat ne ya fad'i, tunani take kar dai ace su Real khady sun zo sun fad'a wa su Dady ne.
Muje zuwa
urs BKšš
[1/7, 10:44 AM] Bk: šššššššššš
NAK'ASASSHE MA MUTUM NE
šššššššššš
Writen by BILKISU Z. YA'U (š
±K)
_(Yar gatan exclusive)_
♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
_(Home of peace, honour and super writer's)_
SADAUKARWA GA: MEELAT A.H.K
This page is Dedicated to:
MASOYAN BK
_Lallai baka tab'a gane masoyan gaske sai abu ya same ka, masoyana ku kwantar da hankalin ku, ciwo ke shiga farad daya amma sauk'i sai a hankali, Addu'arku tana tasiri a kaina, 'yan'uwa Abokan aiki yan exclusive, ina godiya matuk'a, da sauran grps grps daban daban da wad'an da suka kirani, da wad'an da suka yi min txt, da wad'anda suka yi min Addu'a ta nan cikin whatsapp a groups da private nagode sosai, Allah ya saka muku da mafificin Alkhairin sa, Allah ya barmu tare, wallahi naji dad'i sosai, godiya mara iyaka_šš»šš»šš»
RUKEEY CE (HABIBTY)
_Oh ya Allah! ta ina ma ni zan fara, habibty kina matuk'ar k'aunata, kuma nima hakan take, kina shiga damuwa sosai muddin kika ga BK ta shiga wani hali, kina fin BK farin ciki a lokacin da kika ganta cikin farin ciki, shiyasa kika samu gagarumin matsayi me matuk'ar girma a cikin zuciyar BK, tabbas babu abin da yake dasa farin ciki a zuciyar bawa sama da ya gane hak'ik'anin masoyansa, wallahi ina Alfahari da samun masoyiya kamarki, Allah ya k'ara mana k'aunar juna, ya bar mu tare_
Page 50 to 55
Meelat ta kama kame kame irin na marasa gaskiya, daka mata tsawa Dadynta ya yi, abinda bata tab'a fuskanta daga gare shi ba, nan da nan ta zabura jikin ta na rawa, tana so tayi mishi bayani amma tana tsoron abinda zai biyo baya.
Dady ya sake kallon ta yace " wato ki rasa wanda zaki zab'o ki kawo mana a matsayin wanda zaki aura sai nak'asasshe, nak'asasshen ma Makaho, " Meelat ce ta bud'e baki zata yi magana, Dadyn ta ya d'aga hannu ya wanka mata mari, tare da nuna ta da yatsa yace " daga yau bazaki k'ara fita ko ina ba muddin ba wajen aiki zaki je ba, shi ma sai da security. "
Meelat da ke dafe da kunci ta kalli mahaifinta, tana mamakin yau shine da marin ta duk akan tace Nak'asasshe shine zab'in ta, kuka ne ya kub'ce mata, ta ruga ta haye sama da gudu sai d'akin ta, tana shiga ta fad'a kan gado ta fashe da kuka me tsuma zuciya, _nima komawa gefe nayi ina taya ta koka wa_
Sai da muka sha kukan mu muka k'oshi sannan muka yi shiru, tashi Meelat ta yi saboda kiran sallar magrib da taji ana yi, ta shiga bayi, ta yi Alwala ta yi sallar magriba, bayan ta idar ta d'auko Qur'ani ta bud'e, ta fara karantawa, k'ira'ar Ado take so tayi, amma ta kasa, tana nan tana ta rero karatu har aka kira sallar isha'i, ta dasa aya ta tashi ta yi sallar isha, bayan ta idar ta sake mik'e wa tayi nafila, sannan daga k'arshe tayi shafa'i da wutri, bayan ta idar ta duk'ufa rok'on Allah mafita akan lamuran ta, tana addu'a tana kuka gwanin ban tausayi, tana gama addu'ar ne 'yar aikin ta, ta shigo da sallamar ta, meelat ta amsa, abinci ta kawo mata, ta jera mata a kan dining d'in d'akin ta, bayan ta gama jera wa ta fita, tana fita Meelat ta tashi taje kan dining d'in ta d'an tsakuri abincin kad'an sannan ta tashi ta canja kaya tasa na bacci ta haye kan gado, ta dad'e tana tunane tunane kafin bacci ya sure ta.
Yau wajen sati d'aya kenan amma Ado be sake saka Meelat a idon shi ba, Abun yabi duk ya dame shi, gashi be san gidan su ba, balle yasa a kai shi, Yau ma kamar kullum yana zaune A falo ya zuba uban tagumi yana sana'ar tashi wato tunanin Meelat, Inna ce ta fito daga kicin rik'e da abincin Ado a hannun ta, su inna an fara murjewa kamar ba ita ba, lallai talauci shine babban ciwo, Allah ka azurta mu da dukiya ta halak, Inna tazo ta ajiye abincin a gaban shi tare da fad'in " Ado ga abincin ka nan, tun d'azu nake ta tambayar ka a zubo kana ce min ba yanxu ba, gashi nan ka ci kar ya huce."
Ado yace " Inna bazan iya cin komai ba muddin ban san a wane hali wannan baiwar Allahn take ciki ba, " nan Ado ya kwashe duk yanda suka yi da Meelat a Shoprite ya fad'a wa Inna, ya k'arasa maganar shi da fad'in " kuma nima Inna ina sonta."
Inna ta d'auki salati tare da sallalami, tace " Yanzu Ado banda wauta irin taka ina kai ina wannan yarinyar, ko so kake sai kasa iyayen ta sun tozarta mu? "
Ado yace " Allah ba zai basu damar cutar da mu ba koda da mugayen furuci ne, tunda ya ga zuciyar mu muma bamu da niyyar cutar kowa, hasalima ta kanmu muke yi, kuma ni ban tab'a sawa a raina zanyi soyayya da ita ba har in aure ta, hasalima ita ta fara yi min maganar. "
Inna tace " to Allah ya tabbatar da alkhairi in matar ka ce, amma ka bi komai a sannu kaji dai na fad'a maka," Ado yace " insha Allah " nan dai suka ci gaba da tattauna wa game da rashin zuwan ta.
B'angaren Meelat kuwa, duk ta bi ta rame saboda tunani da damuwa, bata cin abinci sosai kamar da, gashi tana matuk'ar so taga Ado amma ba hali, saboda Dady ya sa mata matakan tsaro.
Yau ta kama asabar ba aiki, fitowa ta yi daga d'aki da niyyar ta rok'i Dady ya barta taje gidan su Rukeey da Real khady, turus tayi, sakamakon ganin su zaune a falo Dady na ta basu labaran ban dariya suna ta darawa, kallon ta suka yi dukkan su, Meelat ta k'araso falon ta samu waje ta zauna tare da kallon su d'aya bayan d'aya tace " Dady nah, Mumy nah, da Aminai na naji dad'in ganin ku duka a dai dai wannan lokacin, sannan ta k'ara kallon Dadyn ta tace Dady dan Allah ina son yin muhimmiyar magana daku duka. "
Dady ya kalle ta, duk tabi ta lalace ta rame, sai yaji sam be ji dad'in yanda ya ganta ba, Dady ya kalli Meelat yace " muna jinki "
Meelat ta goge hawayen ta, sannan ta kalli Dady tace " Dady bawai dan baka isa ka hanani bane in hanu, A'ah ni mai yi maka biyayya ce akan komai har abada, sedai dan girman Allah ka fad'a mun dalilin da yasa baka son in auri Nak'asasshe? "
Dady ya kalle ta yace " dalilin ai a bayyane yake, kuma kema gashi nan kin fad'a Nak'asasshe, yaje ya auri 'yar uwarsa nak'asasshiya mana, ni bani da wani dalili, na dai fi son naga kin auri lafiyayyen miji ne kamar kowa. "
Meelat ta sake kallon dukkanin mutanen d'akin tace " shin acikin ku akwai wanda zai iya kawo mun Aya ko hadisi da ya yi hani a kan Auran nak'asasshe? " dukkan su suka yi shiru, Meelat tayi murmushi sannan tace " amsar itace babu aya ko hadisi da ya yi hani ga auren su, "
Meelat ta sake kallon Dadyn ta tace " Dady ni 'yarka ce, k'addara ni Meelat nak'asasshiya ce, idan kaga mutane suna gudun aure na ya zaka ji?, ko an samu me aure na se dai ya aure ni saboda dukiyar da muke tare da ita, ba wai dan Allah ba, wadda tana k'arewa guduwa zai yi ya tafi ya barni. "
Meelat ta cigaba da cewa " Dady Nak'asassu Abun tausayi ne, saboda gudun su da Ake yi, tsakanin mu da su se dai mu mik'a musu kud'i su amsa mu wuce, dai dai da rana d'aya babu me zaunawa dasu a cikin mu domin ya fuskanci matsalar su, kowace mace tana Aure ne saboda ibada ne, kuma bautar Allah ce, idan haka ne meyasa baza mu bari Allah ya yi mana zab'i ba, muna zuwa muna auren wad'anda sam basu san darajar aure ba, da sun auri mace sai su sakota,
Dady, Mumy, Aminai na, kuka sani ko ta sanadin auren wannan bawan Allahn yasa in samu sakamako mai kyau wajen Allah idan na mutu? idan surutun mutane kuke gudu to d'an adam a rayuwa ba'a iya mai, ko menene kayi sai an samu masu yabonka da masu zagin ka, amma in muka tsarkake zuciya sai Allah ya taimake mu,
Dady in dan saboda dalilin ni 'yar masu kud'i ce, zanje ince zan auri talaka to nasan dukkan ku kun sani, Allah ne me azurta bawansa a duk lokacin da yaso, kuma yana iya karb'e wannan dukiyar aduk lokacin da yaso, ku sani yaku iyaye na babu wani mai kud'i wanda yake da tabbacin d'orewar kud'in sa har mutuwa, kuma babu wani talaka da yake da tabbacin d'orewar talaucin sa har mutuwa, sanin wannan sai ubangijin da ya jarabci bayinsa da kasancewar su a haka. "
Meelat ta numfasa, sannan ta cigaba da cewa " bayin Allahn nan suma ba su suka halicci kansu ba, halittar su aka yi, da ace kowa yana da ikon zab'ar yanayin halittarsa to da ina mai tabbatar muku da babu wani nak'asasshe da za'a samu a duniya, to halitta ta Allah ce, shi yaso ya gansu a haka, kuma ba dan baya k'aunar su ba. "
ya ku iyaye na, ni Meelat 'yarku, har yanzu fa a raye nake ban mutu ba, shin bakwa tunanin nima Allah zai iya jarabtana da nak'asar nima.
Dady wallahi Nak'asasshe ma mutum ne, sun ma fi wasu lafiyayyun mutanen a wajen Allah, saboda da su da lafiyayyun mutanen babu wanda yafi wani a gun Allah sai wanda yafi jin tsoron sa, yawancin nak'asassun nan suna da ilimi, da d'abi'u da halaye na k'warai daga mazan su har matan su, Ado yana d'aya daga ciki, Ido ne kawai Allah be bashi ba, Amma Allah ya hore mai k'wak'walwa ya karanci Qur'ani kuma yasan litattafai da dama na addini, daga k'arshe ya ku iyayena dan girman Allah idan maganganu na sun b'ata maku rai kuyi hak'uri ku yafe mun, kuma zan ci gaba da bin umurnin ku har k'arshen rayuwata, kuma a shirye nake da auren duk mijin da kuka zab'ar min a matsayin mijin aure na. "
_Abu ne me kyau tunatar da iyaye, amma ta hanyar da ya dace, sai ka dai-dai ci lokacin da suke cikin farin ciki, tare da yi musu magana cike da lafazi tattausa, ba'a d'aga murya sama yayin da ake yiwa iyaye magana, Allah yasa mu dace."_
Meelat tana gama magana d'akin ya yi tsit kamar ba kowa, sun dad'e a haka sannan ta kalli Dadyn ta sai kawai taga yana hawaye, hankalin Meelat ya tashi, da sauri taje kusa dashi ta durk'usa ta rik'o hannun shi itama tana kuka tace " Dady dan girman Allah kayi hak'uri, ka daina kuka kar kasa Allah yai fushi dani, ka yafemun ban fad'i haka dan in b'ata ranka ba, ka yafe min, ta kifa kanta a kan jikin shi ta saki kuka me tsuma zuciyar me saurare.
_topha me yasa dady kuka? anya zai amince da Auren Ado da Meelat kuwa? Ina Nass ne wai, shin ya hak'ura ko yana nan akan bakan shi?_
Muje zuwa
urs š
±Kšš
[1/7, 10:44 AM] Bk: šššššššššš
NAK'ASASSHE MA MUTUM NE
šššššššššš
Writen by BILKISU Z. YA'U (š
±K)
_(Yar gatan exclusive)_
♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
_(Home of peace, honour and super writer's)_
SADAUKARWA GA: MEELAT A.H.K
This page is Dedicated to:
~FAIZA UMM AMRA
_faiza umm amra kin sambad'o min Addu'ar da dole ne na gode miki, wallahi naji dad'i 'yar'uwa, Allah ya saka miki da mafificin Alkhairin sa. Wannan shafin naki ne kiyi yanda kike so dashi yasin_
Page 55 to 60
Dady ya share hawayen sa, sannan ya d'ago kan Meelat da ta d'ora a jikinsa take ta faman kuka, girgiza mata kai ya yi alamar tayi shiru, sannan ya share mata hawayen ta.
Dady ya kalle ta fuskar shi d'auke da murmushi yace " Baby ke kad'ai Allah ya bamu a duniya, kuma ina matuk'ar godiya da baiwar 'ya d'aya tilo me cikakken hankali, ilimi, da tunani, ina Alfahari da kasancewar ki 'ya agareni, tabbas kin tunatar dani, kin wa'azantar dani, Allah ya shi miki Albarka, yasa sauran 'ya'ya su yi koyi da hali irin naki, idan kun had'u da sirikin nawa kice mishi inason ganin shi gobe, da misalin k'arfe hud'u da rabi. "
Share hawayen ta tayi cike da farin ciki, tana mai duk'ar da kai wai ita kunya, Aminanta ne suka k'araso kusa da ita, suka had'a baki wajen fad'in " Dan Allah kiyi hak'uri abin da muka yi miki bisa rashin fahimta, Rukeey ta k'ara da cewa tabbas kin fimu tarin hujjoji, kuma kin k'ara tunatar damu muhimmancin d'an adam kuma wulak'anta d'an adam sam bashi da amfani, saboda duk d'aya muke, kuma insha Allah zamu bawa Ado hak'urin abin da muka yi mishi a shoprite gobe idan yazo nan gidan. "
Dady ya kalle su yace " wato sirikin nawa kuka yiwa rashin mutunci ko, to ku zo nan ku karb'i hukunci, ya hau laluben abun bugu kamar dagaske bugun nasu zaiyi, su kuma Real khady da Rukeey suka danna a guje suna dariya sai cikin d'akin Meelat, Mumy ta da Meelat suna ta musu dariya, Dady ya kalli Meelat yace " Matar Makaho ko da akwai wata maganar ne, game da sirikin nawa? " tashi Meelat tayi cike da kunyar iyayen nata, ta haye sama itama.
Washe gari, ta kama ranar lahadi, wajen k'arfe sha d'aya na safe Meelat ita da k'awayen ta sun gama shiryawa, dan sunce tabbas k'afar su k'afarta sai sunje d'auko ango tare, bakin Meelat tamkar gonar auduga saboda yau zata ga masoyin ta.
Bayan sun gama shiryawa suka fito, suka wuce har d'akin Mumy, suka yi mata sallama, sannan suka fito suka shiga Mota sai sabon gidan su Ado wanda Meelat ta basu kyautar shi.
Suna isowa k'ofar gidan suka yi fakin, sannan suka fito daga cikin motar, sautin karatu suka ji yana fito wa daga cikin gidan, Meelat ta kalli Aminanta cike da farin ciki, fuskarta d'auke da murmushi, tace " kunji ko, kunji shi can yana karatun Qur'ani ko, ai ni kam nayi dace. "
Su dai su Real khady basu ce komai ba, sai murmushi da suke wanda yake bayyanar da gamsuwar su akan abin da Meelat d'in tace.
Shiga cikin gidan suka yi d'auke da sallama a bakin su, Inna ce ta amsa sallamar tasu, tana fad'in " oyoyo 'yar inna, lale marhabin, sannunku da zuwa, ku shigo mana. "
Bayan sun shiga sun samu waje sun zazzauna, sai aka shiga gaishe gaishe, bayan an gama gaisawa Inna ta kalli Meelat tace " 'yar inna kwana biyu shiru muna ta zullumin ko lafiya, gashi bamu san gidan ku ba, shi kuwa Ado duk yabi ya rame, bashi da wata magana sai taki, idan zan bashi abinci yaci to tabbas maganar ki nake yi mishi."
Wata irin k'aunar Ado Meelat taji ta daki zuciyarta, tare da jin matsanancin tausayin shi.
Real khady ta kalli Inna tace " Inna wata 'yar matsala ce na sab'anin fahimta da aka samu, amma yanzu komai yayi dai-dai, Mahaifin Meelat ya amince da Ado a matsayin sirikin shi, kuma yace ma yana son ganin shi anjima da k'arfe hud'u da rabi. "
Inna ta washe baki tare da fad'in " to Alhamdulillah, Allah ya tabbatar da Alkhairi, yasa ayi damu. "
Ado ne ya fito daga d'akin da ya zama makwancin shi, yana fad'in Inna ke da su waye ne kuke ta hira haka? "
Yana lalube yana shirin zama dai dai inda Meelat ke zaune, Inna tayi sauri tace " kai da mutum anan wajen," sai ya doshi d'ayar kujerar, inna tace " wannan ma da mutum Akai, ya doshi wata Inna tazo da sauri ta rik'e shi, tana fad'in sai kewaye kake faman yi, su dai su Meelat sai dariya suke yanda suka ga yana ta kewayen d'akin, " Ado yace " Inna bak'in namu har nawa ne? " zaunar dashi tayi a kan two siter, sannan tace " Meelat ce da K'awayen ta, suka zo. "
Zabura ya yi yace " da gaske, ina take, Hajiyata, dama kina nan? "
Ita dai Meelat bata ce komai ba banda murmushi kawai da take ta yi, inna ta kalli su Rukeey tace " kuzo muje ku tayani aiki," suka mik'e dukkansu har da Meelat, Inna ta kalli meelat tace " A'a banda ke zauna," ciki suka shiga, d'akin baccin Inna, tace su zauna, ta kawo musu lemuka kala kala, Rukeey ta kalle ta tace " inna aikin fa? " Inna tace " ba wani aiki, kawai wayau nai muku ku basu waje su gana. " nan suka zauna suka yi ta hira da inna tana ta saka su dariya.
Meelat ta d'ago da kanta ta kalli Ado idon ta ne ya ciko da k'walla saboda ganin irin ramar da ya yi, duk ta sanadin tunanin ta, ji tayi yace " Hajiyata " da wata irin sassanyar murya, kallon shi tayi tace " Na'am, ya kake, ya kuma k'arfin jiki? "
Ado yace " Alhamdulillah, ya kwana biyu, Allah yasa dai ba wani abu akayi miki ba a gida, game da maganar mu? "
Meelat tace " ba abin da aka yi min, hasali ma albishir nazo yi maka akan amincewar Dady na, game da maganar auren mu, kuma yace " kaje yana son ganin ka k'arfe hud'u da rabi, zamu jira har lokacin ya yi, sai mu tafi gaba d'aya. "
Ado ya sakko daga kan kujera cike da tsananin farin ciki, ya laluba ya tabbatar da gabas, sannan ya kai goshin sa k'asa, sai da ya jima yana jero godiya ga magaliccin sa sannan ya d'ago da kan shi.
Nan fa suka duk'ufa hira fafa, su kuma mutanen Inna suna can tana ta basu labari, bayan Inna ta gama abinci ta zuba wa kowa nashi, aka kai wa su Meelat nasu, bayan sun gama cin abinci suka yi Alwala, suka yi sallar azahar, shi kuma ado ya tafi masallacin da ke kusa dasu.
Bayan sun idar aka ci gaba da hira, k'arfe hud'u dai dai Meelat ta kalli Ado tace " ya kamata ka tashi ka shirya muje, " Ado yace " eh to mu yi sallar la'asar mana, tunda naji anfara kira."
Bayan sun yi sallar la'asar ne, ado ya dawo daga masallaci, Meelat ta jawo ledar dake kusa da ita, ta mik'a wa Ado, tace " wad'annan kayan zaka sa, ba dan na raina naka ba, dan Allah,"
Ado ya yi murmushi, sannan yace " kisa a ranki a duniyar nan kaf babu wani abu da zaki buk'ata daga gareni in kasa yi miki shi, " ya karb'i kayan, tare da yi mata godiya.
Cikin d'aki ya shiga domin yasa kayan, su Real khady ne suka fito daga d'akin Inna, suna fad'in " iyayen soyayya sai ku tashi muje koh. "
Ado ne ya fito daga cikin d'aki, ba Meelat kad'ai ba hatta su Rukeey sakin baki suka yi suna kallon shi, yayi kyau sosai, kayan sun karb'i jikin shi, tamkar ba d'an talaka ba, sutura kenan mutuncin d'an adam.
Tashi suka yi gaba d'ayan su, suka yi wa Inna sallama suka shiga mota, suka d'auki hanyar gidan su Meelat.
Bayan sun iso gidan su Real khady suka shiga cikin gida domin tabbatar wa da Dady isowar Angon Meelat, basu dad'e da shiga ba suka fito, suka ce ya shiga, gaba d'ayan su suka shiga cikin falon, ya samu waje daga gefen kujera ya zauna, ba yanda Meelat bata yi dashi ya zauna kan kujera ba amma yak'i, suna nan zaune tare dashi Dady ya fito daga cikin d'akin shi, hakan yasa su Meelat suka mik'e gaba d'ayan su suka basu waje, Momy ce ita ma ta fito daga cikin d'aki da lullub'in ta, ta zauna, Ado ya rissina, tare da gaishe su, dukkan su suka amsa, Dady ya kalli Ado yace " Malam Adam kai mazaunin wace unguwa ce, wanene mahaifin ka? "
Ado yace " Iyaye na sun rasu, sakamakon hatsarin mota, " nan dai Ado yayi wa Dady bayanin asalin shi.
k'warai sun yaba da hankalin Ado, Dady yace " na yaba da hankali, had'e da natsuwar ka, saboda haka nan da sati me zuwa ka turo Magabatan ka, " Ado yace " Dady kamar yanda na fad'a maka iyaye na sun rasu, se dai Akwai Malamin mahaifi na, tamkar uba yake a gareni, idan an amince zan sanar dashi, sai ya wakilce ni."
Dady yace " ba damuwa ko shi d'in ma ya wadatar. "
Ado yace " Nagode Alhaji, Allah saka da alkhairi, suka yi sallama da Dady har da Mumy ma, sannan suka tashi suka shiga daga ciki, Mumy ce ta kira Meelat a waya ta sanar da ita bak'on ta na jiran ta.
Su Meelat ne suka sauko k'asa, inda Ado yake zaune, sun d'an tab'a hira sannan Ado yace zai koma, Meelat ta bashi sabuwar waya dal acikin kwali, TECNO W5, tace " gata nan nayi maka cajin ta, duk sanda cajin ya k'are ka bawa Inna ta caja maka, zan rik'a kira akai akai, Ado yai mata godiya sosai, sannan suka yi sallama tasa aka kai shi gida
Kafin satin da Dady ya d'ibar wa Ado ya zagayo, ya tashi yai tattaki yaje har Kauyen su meelat yai bincike ya tabbatar dagaske 'yan can ne, Dady yaje har unguwar da iyayen Ado suka fara zama, daga k'arshe yaje unguwar da suka tashi daga cikin ta, duk kyakkyawan shaida Ado ya samu a gun jama'a, sannan yaje wajen 'yan'uwan sa mabarata, suma kyakkyawan shaida ya samu a wajen su, dama abin da Dady yake so ya tabbatar kenan.
kafin sati ya zagayo, Meelat ta turo wa Ado da drivern shi, yaje ya sami Malamin shi yai mishi bayani, malam yayi matuk'ar farin ciki, kuma yayi mishi kyakkyawan Addu'a, da fatan Alkhairi.
Yau ne ranar da Dady ya d'ibar wa Ado kan ya turo da magabatan shi, Dady da kanshi ya tura mota aka d'auko Malam, suka tattauna, An tsaida rana nan da wata biyu kan sadaki dubu goma, nan take malam ya ciro sadakin ya bayar, kuma Dady yace bayan sadaki basa buk'atar komai, hatta gidan da zasu zauna shi zai basu, nan fa malam yai ta zuba godiya, daga k'arshe suka yi sallama, aka maida shi gida.
Gari ya d'auka, ko ina ka duba labarin auren Ado da meelat kawai ake yi, ko ina ka duba cikin Tv, redio, jarida duk sanarwar sa ranar auren ne kawai.
B'angaren Nass kuwa, tsaye yake a d'akin shi, sakamakon ganin hoton Meelat da Ado ana sanarwar sa ranar auren su, gumi ne yaji yana zubo mishi, shaid'an ne yake ta sak'a mishi, yaje kawai ya d'auke ta ya b'oye ta, har sai an aura mishi ita.
muje zuwa
0 comments:
Post a Comment