page 1 to 5
Yau ma kamar kullum Ado makaho yana zaune a gefen titi, inda suka saba zama, shi da wani abokin shi me suna musa gurgu.
Musa gurgu yana ta zuba surutu amma Ado sam be ma san yana yi ba, domin kuwa shi yai zurfi a cikin tunanin da ya jefa kan shi a ciki kwana biyu.
Musa gurgu ne yaji yana ta magana amma Ado bece komai ba, ya kira sunan shi nan ma shiru, sai ya juyo domin yaga yana nan ko ya tashi ya tafi ne, duk da ya san be tab'a yi mai haka ba, yana juyo wa ne yaga yana nan, amma ya yi nisa cikin tunani, sai ya jijjiga shi da k'arfi, yace " Ado wai meke damun ka ne, kwana biyun nan na lura akwai abin da ke damun ka, menene kake b'oye mun ?"
Ado wanda ya dawo daga tunanin da yake ta hanyar girgiza shi da musa ya yi, ya share hawayen da ya gangaro mishi, sannan ya kalli gefen da abokin nashi yake yace " musa ka bari kawai, ina cikin tashin hankali wallahi."
Musa yace " subhanallah! meke faruwa ne wai? "
Ado yace " zuciyata ta haukace Ado, zuciyata ta haukace," sai wasu hawayen suka sake gangarowa kan fuskar shi, ya kalli musa yace " musa wallahi tun ranar da na fara jin sautin muryar yarinyar da ko a mafarki ba za ta tab'a zama mallaki na ba, kunnuwana suke ta amsa kuwwa, muryar ta ta kasa b'ace wa a cikin k'wak'walwa ta, musa kaji dad'in ka, ina ma ni ne kai, ina ma ni ne Allah be hore wa k'afafu ba ya barni da ido na."
Shi ma musa duk da bai gama fahimtar zancen shi ba, nan da nan shi ma zuciyar shi tai rauni, sai hawaye, kallon, Ado ya yi, yace " Ado be kamata ba ace kana fad'in irin wad'anan maganar, kar kai sab'o, Ka gode wa Allah a duk halin da ka tsinci kanka, ko ba kai kake min irin wad'anan nasihan ba, kai fa kana da k'afafun, gani ne baka yi, ni kuwa babu k'afafun, kana da damar zuwa duk inda ka so, ni kuwa babu kafafun da jan jiki nake zuwa nan shi ma da k'yar," Ado yace musa makanta tafi ciwo, ko yaya kake in Allah ya barka da idanun ka kayi babban arzik'i, duk wani abu fa se dai inji sautin sa, ni so nake in gani da ido na ko da sau d'aya ne, amma babu hali, kai kuma kana da idon ganin,"
musa yace " na sani, amma ko a yaya ka ke kar ka yi wa kanka fatan zamowa ni, kar ka sake ka k'ara yin irin wanan maganar ma, kuma kai ta addu'a idan ma kasa son yarinyar a ran ka ne to, Allah ya cire maka sonta a ran ka, dan nasan baya wuce wannan yarinyar da ta ke bamu kyautar kud'i har nai ta kwatanta maka siffar ta, kuma ka san wannan ko a cikin maza masu lafiya ma sai ta zab'a, balle irin mu nak'asassu."
………………
Wata had'ad'd'iyar matashiyar yarinya ce na gani a wani k'erarre kuma katafaren gida, d'akin ta kawai nerar da aka shimfid'a a cikin shi ta ishi wani bawan rayuwar duniya, tashin ta kenan daga bacci, da saurin ta ta diro daga kan gado, toilet ta fad'a da sauri ta shek'a wanka sannan ta fito.
Meelat kenan matashiyar yarinya kyakkyawa me kyan hali, ni dai ina lab'e ina lek'e ta window na saki baki da hanci duk gaba d'aya ina kallon baiwar kyau da Allah ya bawa wannan baiwa tashi, zuciya ta ce take ayyana min anya duk duniya akwai wanda ya ke da kwatan kyawun ta kuwa, kyakkyawa ce lamba d'aya, kuma ajin k'arshe, daga kanta an rufe babin kyawa wa.
Bayan ta gama tsane ruwan jikin ta da had'ad'd'en tawul me shegen taushi, ta shiga shafe jikin ta da mayu ka kala kala masu d'an karen k'amshi da tsada, sannan ta fara k'era wa kanta kwalliya.
Tana cikin kwalliyar ne wayar ta tai k'ara, d'auka ta yi ta d'aga tare da kara wa a kunne.
" Hello Real khady " wayyo Allah, lokacin da muryar ta ta daki kunne na ji nayi sautin ya wuce har k'wak'walwa ta, sai da wayar d'auko muku labarin ta sub'uce daga hannu na.
Wayar ta ta ci gaba da yi cikin natsuwa, da Alamu wadda ta kira da suna real khady fad'a take yi mata, naji meelat tana ta bada hak'uri, tana fad'in yanzu zata shirya.
Tana ajiye wayar ta cikin sauri ta k'arasa kwalliyar ta ta, wasu had'ad'un kaya naga ta ciro riga da siket na atamfa ta saka, d'inkin ya amshi jikin ta, ta tsantsara d'auri, ni dai ina lab'e ina kallo fad'i nake wanan sai kace fannin kwalliya ta karanta.
turaruka wajen kala goma masu shegen tsada naga tana d'auka d'aya bayan d'aya tana fesa wa a jikin ta, ta d'auki glass ta mak'ala a fuska, haba wa ai sai nayi suman tsaye ina kallon kyau da kyau, ita ma kanta sai da ta kalli kanta a madubi, ta k'ara kallo sannan tai murmushin da sai da dimple da wushiryar ta suka bayyana.
fito wa tayi daga d'akin, bodyguads d'in ta ta gani tsaye bakin k'ofa cikin bak'ak'en kaya, jakar hannun ta d'aya daga cikin su ya karb'a sanan suka bi bayan ta suka sauka k'asa.
A falo ta tarar da mumyn ta tana kallo, k'arasa wa ta yi wajen ta, ta fad'a jikin ta sannan tace " mumy barka da huta wa."
Mumy tace " yauwa baby."
Tana jikin mumy sai zuba shagwab'a take.
Wasu yan mata ne guda biyu wad'an da baza su wuce sa'annin meelat ba, sukai sallama suka shigo falon, kujera suka samu suka zazzauna, sannan suka gaishe da mumy.
Meelat tace malamai ai ba, zama zaku yi ba ku tashi mu tafi.
Real khady da d'ayar me suna Ruqeey suka mik'e, dukkan su su ukun sukai wa mumy sallama suka fice.
Garejin gidan suka nufa, bodyguad d'in ta na biye da ita, ga motoci nan reras, amma sun rasa wacce ma zasu hau, k'arshe dai sai ruqeey ce ta zab'ar musu wata zazzafar mota me suna YHUNDAI, wadda ake yayi, kud'in ta zai kai kimanin million goma, driver ya bud'e musu k'ofa suka shiga, bodyguads ma suka shiga tasu, motoci uku suka fita dasu, motar su meelat ce a tsakiya, gaba da bayan su kuma motocin masu tsaron lafiyar meelat ne.
Wani katafaren wajen shak'atawa da wasanni suka nufa, bayan sun gama shak'atawar su sai sukai ta d'aukar hotuna, bayan sun gama d'aukan pictures ne sannan suka zauna a kujeru suna huta wa.
lemu aka cika musu dashi a teburin gaban su, suna sha suna zuba hira.
Suna cikin hirar ne wani had'ad'd'en guy ya nufo inda suke zaune, yana zuwa yace " hy babys," Real khady da ruqeey su biyu suka Amsa banda meelat, kyakkyawan saurayin nan yace " sannun ku yan mata, zan iya zama?"
Real khady da ruqeey ne suka ce mishi bismillah, ya ja kujera d'aya ya zauna, sannan ya sake kallon su yace " Suna na nasir, ana kira na da nass, mahaifina shi ne gwamnan garin nan, kuma na zo wajen k'awar ku ne, ya nuna meelat, ina fatan zan samu karb'uwa a zuciyar ta?"
Meelat ta kalle shi sama da k'asa sannan tace " kayi hak'uri, baka d'aya daga cikin jerin mazan da zan saurara, ma'ana ba irin ka bane zab'i na.
to da yake nass akwai saurin hassala, sai ya mik'e da niyyar zai gaggaya mata magana, bodyguad d'inta suka yo kan shi, shi ma masu tsaron shi suka taso musu.
Meelat ce ta mik'e ranta a b'ace tace " ku tashi mu tafi "
suka tashi suka je inda sukai parking d'in motocin su, suka shishiga suka d'auki hanyar gida.
Nass ya bi su da kallo har motar su ta tashi, sannan ya girgiza kai yace " wallahi ba zan barki ba, sai na yi soyayya da ke," shi ma fita sukai, suka shiga motocin su, suka bar wajen.
A hanya ne Real khady ta kalli meelat tace " wai ke wace irin mace ce, bamu gane nufin ki ba na wulak'an ta duk wanda yace yana k'aunarki, sai an yi magana kice ba shi bane zab'in ki, kin bi duk kin ishe mu, zab'i na, zab'i na? "
Ruqeey tace " kin riga ni a fili na riga ki a zuciya, nima tambayar da nake so in yi mata kenan, me yasa duk samarin da suke zuwa wajen ki, kike korar su, tare da yi musu wulak'anci? "
Meelat ta kalle su tai murmushi, sannan tace " duk bayanin da zan muku akan irin zab'ina, ma'ana irin na mijin da nake so ya zama miji a gare ni to ba za ku gane ba, Amma ku rik'e a ranku, cewa duk na mijin da kuka ga na je gare shi, kuma har ya ga dariya ta to tabbas shi ne zab'in rai na, shi ne kalar mijin da nake so ya zama uban 'ya'ya na "
Rukeey tace " zamu so ganin wannan ranar, da kuma ganin mai sa'ar mallakar ki a rayuwa."
Suna tafe suna hira har suka k'arasa gida
_Wacece meelat? waye Ado? wace yarinya ado yake so? nass yana k'yale ta kuwa, ko kuma dai zai ci gaba da bibiyar rayuwar ta? ku biyo mu a ci gaban shirin domin jin yanda zata kasance_
muje zuwa
Urs š
±Kšš
[1/7, 10:42 AM] Bk: šššššššššš
NAK'ASASSHE MA MUTUM NE
šššššššššš
writen by BILKISU Z. YA'U (š
±K)
_(Yar gatan exclusive)_
♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
_(home of peace, honour and super writer's)_
SADAUKARWA GA: MEELAT A.H.K
DEDICATED TO
EXCLUSIVE WRITER'S
_In na daban, ku ne na daban ku na ware, a tab'a ku an yi kad'an, in anka matsa sai an zare, lafiya ta ku ne, in har babu ku k'warai babu ni, ina sonku over over, Allah ya k'ara mana k'aunar juna, ya k'ara had'e kan mu_š
LIKES AND COMMENTS
#https://www.facebook.cm/Exclusive-writers-fans-E-w-f-192229754142326/
šš»šš»šš»šš»šš»šš»
NAN ZAKU SHIGA DOMIN SAMUN LITATTAFAN MU
page 5 to 10
Ko kafin su k'arasa gida har b'acin ran meelat ya tafi, hirar su kawai suke zuba wa har suka k'araso gida, da gudu bodyguads d'in ta suka fito, suka bud'e musu mota, cike da aji suka fito daga motar ita da Aminan ta, sannan kai tsaye suka shige cikin gidan.
suna shiga falo Real khady ita da Rukey ce suka sami waje suka zazzauna, ita kuma meelat direct d'akin mahaifiyar ta ta nufa, tana zuwa ta tarar da ita tana bacci, bata tashe ta ba sai ta juya ta dawo falon inda ta bar Aminan ta, ko da ta dawo ta iske d'aya daga cikin yan aikin su me suna raliya ta kawo musu Abinci gasu nan kala kala.
Meelat ce ta kalli raliya tace " ki kwashe ki kawo musu d'aki na, ta juyo da kallon ta zuwa ga su Ruqeey tace guys ku tashi mu hau sama," tashi sukai suka haye sama in da d'akin meelat yake, direct dining suka wuce.
Dining d'in dake cikin d'akin meelat yan aikin suka shiga, jajjera musu abincin, sannan kowacce ta zab'i abin da take muradin ci aka zuzzuba musu.
Dukkan su kad'an suka ci, sannan suka tashi daga kan dining d'in, raliya ce ta shigo ta kwakkwashe kayan abincin tai waje da su, sallah sukai sannan suka kwanta sai bacci.
WACECE MEELAT?
JAMEELAT sunan ta, d'iya guda d'aya tak ga wani shahararre kuma hamshak'in me kud'i, kuma fitaccen d'an kasuwa mai suna Alhaji hassan kabir.
Meelat Fara ce, kuma Kyakkyawar yarinya ce tamkar balarabiya, akwai dara daran idanu, ga dogon hanci wanda ko indiyawa Albarka, tana da dimple da wushirya yar baiwa kenan, idan ka ganta tana dariya in kana da raunin zuciya murmushin ta kad'ai ma yana iya sumar da kai, ni kaina da nake d'auko muku labarin na kasa tantance da dariyar ta da d'aurewar ta wanne tafi kyau, sai na gama sakin baki da hanci nai ta kallon ta kafin na daure na ci gaba da d'auko muku labarin, meelat tana da gashi har gadon baya, gaskiya meelat k'arshe ce a fannin kyau, daga kanta an rufe babin kyawawa, tana da farin jini sosai, a kullum sai an biyo ta gida ana sonta, se dai a cewar ta har yanzu bata ga zab'in ta ba.
Alhaji hassan kabir yana da mata d'aya mai suna Hajiya Amina, dukkan su mazauna cikin garin kano ne, A nan Allah ya had'a su har sukai aure, suna da d'iya d'aya tilo wadda suke mutuwar so mai suna jamila wadda suke kira da meelat, kuma suna zaune ne tudun nufawa a cikin garin kano.
Alhaji Hassan kabir hamshak'in mai kud'i ne, ya tara su ne ta hanyar kasuwanci da yake yi kala kala, kama daga kan siyar da motoci, yana da gidajen mai nashi na kanshi, ga tarin gidaje da filaye, ga manya manyan kanti da ya bud'e, ga kamfani kamfani da yake da su masu yawa suma basu da adadi, gaskiya ni kaina ba duka na san iya Abubuwan da ya mallaka nashi ba, amma kuma dukkan su ya same su ne ta hanyar halak, shi kan shi Alhaji hassan kabir bai san iya Adadin Abubuwan da ya mallaka ba nashi na kanshi, balle aje kan maganar tsagwaron kud'in da yake kwance cikin Account d'in shi, kuma mutum ne shi mai kyauta, Abun hannun shi sam bai rufe mishi ido ba.
An sha kawo farmaki domin salwantar da rayuwar Alhaji hassan kabir da ta iyalan shi domin su kwashi dukiyar sa, Allah ne ke tsallakar da su, hakan yasa ya kai report wajen kwamishina na yan sanda aka had'a shi da jajirtattun yan sandan da zasu rik'a tsaron lafiyar su, kowanne daga cikin su mutanen da ke tsaron lafiyarsa kawai sun kai mutum goma banda masu tsaron gida mutum talatin, gidan su meelat katafaren gida ne kuma k'erarre, k'aton gida ne, ko gidan sarakai da yan siyasa albarka ya kai k'arshe wajen had'uwa.
Suna matuk'ar k'aunar 'yar su meelat, shi yasa ma masu tsaron ta suka fi na iyayen ta yawa
Real khady da Ruqeey Aminan meelat ne tun na yarinta har girma, hakan yasa iyayen su suma suka zama aminai ta dalilin su, tare su kai makaranta kama tun daga primary har suka gama, su kai secondry tare, sannan bayan sun gama suka shiga jami'a tare A k'asar waje, kuma duk da iyayen su real khady da ruqeey suna da kud'i amma dadyn meelat ya hana su su kashe ko k'wandalar su kan karatun su, shi yai komai tun farkon karatun nasu har suka kammala.
Gata na duniya kam meelat ta same shi, se dai fatan cika wa da imani, amma duk da daular nan da ta taso a cikin ta be sa tarbiyarta ta lalace ba, tana da natsuwa, hankali, sannan sam bata wasa da ibadar ta, yanzu haka meelat tana da shekara Ashirin cif a duniya, kuma mahaifin ta ya mallaka mata d'aya daga cikin kamfanin shi, wanda yafi kowane kamfani nashi girma, MEELAT kenan yar gatan mumy da dady
WANNAN KENAN
Hud'u saura minti biyar suka tashi daga bacci, meelat ce ta fara tashi sannan ta tashi su ruqeey, Alwala suka fara yi, sukai sallah, sannan suka shek'a wanka, suka sha kwalliyar su, sannan suka fito har da meelat d'in domin ta raka su gida, haka take yi, duk suka zo gidan su sai ta raka su har gida ita da masu tsaron lafiyar ta, wata rana kuma ta sa masu tsaron nata su raka su, sannan su juyo.
……………………
" Ado, Ado wai yau meke damun ka ne ko waje ka k'i lek'owa kana kwance a d'aki, na lura kwana biyun nan akwai abin da ke damun ka, kai da kake da barkwan ci da wasa da dariya, amma kwana biyu ko fito wa daga d'akin ma baka yi, balle in samu yar hirar da aka saba yi min, " kakar ado ce ta shigo cikin d'akin shi take yi mishi wannan tambayar.
Ado yace " ba komai inna kawai dai jikina ne baya min dad'i kwana biyun nan. "
Kakar sa wadda ya kira da suna inna tace " subhanallah! sannu, bari na samo maka magani ka sha," bata jira ta ji amsawar shi ba ta fice daga d'akin.
Bata dad'e da fita ba ta dawo hannun ta rik'e da magani da ruwa a cikin kofi, ta aje gefe guda sannan ta d'aga shi ta bashi, ya sha ta maida shi ta kwantar.
Inna ta kalle shi tace " sannu, Allah ya baka lafiya d'an inna, bari na barka ka samu bacci ka huta."
Ado yace " to inna na gode."
inna fitowa ta yi daga d'akin, tare da gyara mishi labulen d'akin da yasha faci na d'inki har wajen wuri biyar, sannan ta wuce nata d'akin.
WANENE ADO?
muje zuwa dai
urs š
±K
[1/7, 10:42 AM] Bk: šššššššššš
NAK'ASASSHE MA MUTUM NE
šššššššššš
Writen by BILKISU Z. YA'U (š
±K)
_(Yar gatan Exclusive)_
♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
_(Home of peace, honour and super writer's)_
SADAUKARWA GA: MEELAT A.H.K
šTHIS PAGE IS DEDICATED 2 U ACTION BABYš
šššššššššššššššššššš
HAPPY BIRTHDAY ACTION BABY
šššššššššššššššššššš
_Allah ya Albarkaci rayuwarki, Allah ya k'aro shekaru masu Albarka, Allah ya ci gaba da raya ki rayuwar imani, Allah ya sa albarka a cikin rayuwarki wadda ki kai a baya, yasa Albarka a rayuwarki wadda zaki yi a nan gaba, Allah ya baki ikon gama wa da duniya lafiya, Allah ya d'aga darajarki_
_wannan shafin naki ne ke kad'ai_
šššššššššš
0 comments:
Post a Comment