BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM...*
_WANNAN LITTAFI K'AGAGGEN LABARINE WANDA NA K'IRK'IRA DA KAENA,BAN RUBUTA SHI DAN YA ZAMA CIN FUSKA GA KOWABA,IDAN KA/KIN GA WANI ABU DA YAYI KAMANCE²NIYA DA RAYUWARKA/KI KUYI HAK'URI BAN RUBUTA SABODA KUBA........._
_HAKA KUMA BAN YARDA AYI MIN GYARAN KODA WASALIBA SAE DA IZININAH,BAN YARDA KUMA AJUYAMIN LABARI TA KOWACE FUSKABA,AEKATA HAKAN SABAWA DOKATACE,WANDA DUK YAGA KUSKURE ACIKI INA BUQATAR YA SANAR DANI,DAN NA SAMU NA GYARA..........._
*MASU TAMBAYANA NOVEL PC DAN ALLAH KUYI HAK'URI KUNA BANI WAHALA DA TURA MUKU,KUYI HAK'URI KU DUBA GROUP'S DA AKE TUROWA,WANI LOKACIN SABODA NAUYI DA TEXTS SUKEYI,SAI NAYI CLEARING CHAT ENA,KUMA INA RASA MUHIMMAN ABUBUWANA,PLEASE........*
_INA MUKU FATAN ALKHAIRI MASOYANA,INA KUMA ALFARI DA KU A DUK INDA KUKE.NA GODE........._
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)........*
*℘ąɠɛ 1↔2*
Yarane su uku ruk'e da hannun juna banda gudu babu abunda sukeyi,duk burinsu bai wuce su isa gida akan lokaciba,biyu mata dayan kuma namiji,k'aramar ciki CE ta bud'e baki tana haki,amma hakan bae hana maganarta fitowaba,cikin yaren da kana ji kasan Mae shi bae gama k'warewaba,take cewa "wae adda jiddah ina zamu da muke gudu,tun da aka tashifa muke gudu,kuma wllh duk na gaji", namijin ne ya karb'a da cewa "ke ikram baki da hankali ne,kin manta inna batada lapia muka barta ita kad'ae", ba tare da wacce aka kira da adda jiddah ta tsayaba tace "kai sadeeq to mene na ce mata bata da hankali??, Kiyi hak'uri addah bazan sakeba......
ci gaba sukayi da tafiya cikin sauri, har suka fito ∂aga surk'uk'in dajin da ya raba hanya Biyu.....
Hango bukkarsu dake gefe na ci da wutane yasa jiddah fasa k'ara Mae ban tsoro, haka ta nufi bukkar da gudu lσkαcιn da ta saki hannun " yan uwan nata....
Duk wannan budurin da ake sai a lokacin hankulan jama'ahhh ya kawo kansu,da gudu jama'aahhh suka nufo bukkar da wuta ta riga ta gama ci sai hayak'i dake tashi a gurin, alamar wani abu ya k'one......
Tun k'aran da tayi bata kuma sanin inda kanta yakeba,gani kawae akayi ta fad'i a k'asa,lokacin hankalin wasu jama'aar dake gurin ya koma kanta, dan ganin ta farfad'o........
Mik'ewa tayi a razane,tana waege²,tuna Inda take da abunda ya faru yasa ta kwasa a guje,ta nufi bukkar da ta riga ta k'one,sai shatin gurin da yake hayak'i........
Tsugunawa tayi a gurin tana kuka mai tsanani da ban tausayi,tana damk'ar k'asar gurin,lokacin ne "yan k'annenta suka nufo Inda take,banda kuka babu abunda suke.......
An rasa Mae rarrashin wani,mutanen da suka zo gurin ne, wani ya daure yana tambayarsu "mai yake faruwa? Sadeeq ne ya d'ago da k'yar yana fadin "innarmu ce bamu ganiba,kuma gashi gidanmu ya k'one", "Ina innar taku ta tafi?" "innalillahi wa-inna ilaihi raji'un", abunda gaba d'ayan mutanen gurin ke
fadi kenan,to ina innar taku ta tafi?? Umma bamu saniba, mun tafi makarantar a rugar malam bello,da muka dawo kuma bamu gantaba, wani dattijone ya matso kusa da su,ya dafa shoulders en sadeeq tare da fadin "yaro ya akayi haka ta faru,waya ya fad'a muku? "mufa a nan muka barta a kwance bata da lafiya,wayyo mu shi kenan innarmu ta mutu ta bamu...........
Ikram jin an ambaci inna ta mutu sae lokacin ta fad'a kan cinyar jiddah tana fad'in "wayyo addanmu shi kenan dagaske inna ta tafi ta barmu??........
Kuka ssae suka ci gaba da yi,baba ard'o sai rarrashinsu yakeyi,yana basu hak'uri............
Kowa sai salati yake a gurin,ikram ta k'ank'ame jiddah sai ihu take,hak'uri kawai mutane suke basu,da haka kowa ya watse ya bar gurin,ba tare da kowa yayi tunanin rabasu a d'an nasa muhallinba.....
Ganin duk mutanen gurin sun watse,an barsu su kad'ai babu wanda yayi tunanin taimakonsu,jiddah ta mik'e ta nufi dai² gurin da take ganin shatin bukkar tasu,tana zubar hawaye,ta sunkuya ta fara d'iban k'asa tana zubawa akan tokar da take gani,ganin tana yi yasa sadeeq da ikram matsowa kusa da ita,sukaci gaba da zubawa tare,har sae da suka rufe gurin tukun,waige² ta fara,can daga nesa ta hango wani k'aton dutse,zuwa tayi tana son d'aukowa,amma ta kasa,hakan ne yasa ta dage,ta fara turoshi,da k'yar take iya mirgino shi,har ta kawo shi daf da gurin,sannan ta tsaya tana maida numfashi,sai haki take,addu'ah suka mata duk da sunayi suna kuka........
gashi basu da wani guri da zasu kwana,jiddah ce ta mik'e,hannunsu ta kama ta fara jansu,Suna tafiya Suna waigen gurin da basuyi tsammanin akwai ranar da zata rabasu da shiba arayuwa...........
*_SMASHER ������_*
���� *RAYUWAR WANI......*
_{ơŋɛ'ʂ lıʄɛ...}_
����
��
*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ...*
*ცყ.*
_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)........*
*℘ąɠɛ 3↔4*
Tafiya suke,da ganinsu Kasan Suna tattare da damuwa,ikram kam har lokacin bata bar kukan da take ba,sai rarrashinta jiddah take amma abun ya gagara,ganin hakane yasa ta kyaleta,dan kanta kuma tayi shiru.......
Dare ya fara shiga lokacin ne suka fito daga cikin jejin da rugar tasu take,dake tsakanin zainabi da riruwai,cikin garin(doguwa L.G.A) dake Kano State, sun shigo suna kalle² domin su samu gurin da zasu kwana,kafin su ci gaba da tafiya,zuwa in da Allah zai nufa su ci gaba da rayuwa.......
Wata y'ar rumfa suka gani,a hanyar kasuwar garin,ciki suka nufa suka zauna,manne da juna,sai kalle² suke,garin yayi shiru,babu abunda ke tashi sai kukan karnuka,ikram na rungume ajikin jiddah,a haka suka kwana a gurin ba tare da fargabar komaiba.......
Sanyin asubah ya farkar da jiddah,a hankali ta Shiga tashinsu,bud'e ido sukayi suna murzawa,ganin ta mik'e suka bi bayanta,gaba sukayi gurin wata rijiya,da k'yar suka samu suka janyo ruwa a ciki,alwala sukayi da gani kasan ba wai dan sun iya bane,kawai dai suna yi ne a matsayinsu na musulmi.......
Cikin rumfar suka koma,a nan suka bubbuga sallar da tafi ace basuyi ba.....
Garin ya d'an fara haske,suna zaune sun rasa abun yi,ga damuwa da suke ciki,ga yunwa,uwa uba kuma babu kud'in siya,sukam da wanne zasuji??.........
Suna nan zaune,ba tare da sun samu mafitaba,gashi basu San Inda suka nufa ba........
Wata Mota suka hango irin akori-kura ennan,ta biyo fasashen titin,kallonta suke har ta gota su,tsayawa motar tayi a d'an gabansu,ganin haka jiddah ta yankewa kanta hukunci,gara subi motar can kawai duk inda zata gara su bita,ko sa samu sauk'in rayuwa a inda zasu..........
Kama hannunsu jiddah tayi suka mik'e,motar suka nufa cikin sand'a,dan kada aji alamunsu,a hankali har suka k'arasa kusa da motar,suna zuwa ta d'aga ikram tasata a ciki,saddeq kam da kansa ya hau,itama ta kama ta shiga,tenpol ne aka rufawa mortar,ciki suka shige,idan ba Sani kayi ba,babu wanda zaice a kwai mutum a ciki,kuma har uku,babu wanda yace ko "uhmm" tunda sukayi shiga har lokacin da motar ta fara tafiya,godiya akwai takewa Allah da ya kawo musu mafita, lokacin da duk a mutane suke k'ok'arin juya musu bata.........
Tasan a yadda mutane suke Nuna musu halin ko in kulada lamarin nan ya faru,babu mai taimakonsu da ko da k'wallin gishiri,dai² lokacin da duk a fi buk'atar taimakon..........
Kayan gona ne a ciki,wasu a buhu,wasu kuma a kwando,ganin kayan yasa yunwar da suke ji ya motsa,take suka hau ci,ba tare da jiran umarnin kowaba.....
Sai da suka koshi tukun,nan kuma suka fara neman ruwan sha,amma babu,kan dole yasa suka hakura......
Motar sai gudu take akan titi,ba tare da samun matsalaba,sai d'an ramuka dake kan titin ya sa su d'an tsagaita da gudu,da sun wuce suci gaba,bacci ne ya d'aukesu,tun bayan da suka ci,suka k'oshi......basu suka farkaba sai da akazo,kwanar dawaki......
Lek'e suke,suka ga har yanzun tafiya suke,d'ata da guavan suka sake ci,sai da suka ji babu yunwan tattare da su kafin suka hakura........
Bayan azhur motarsu ta tsaya a dai² kasuwar y'an lemo dake na'ibawa,cikin karamar hukumar kumbotso..........
Jin an bud'e k'ofar motar da kuma rufewa,yasa jiddah lek'owa,ganin babu kowa a wajen,tayi saurin dirowa daga ciki,ikram tayi saurin kamowa tana k'ok'arin sakkowa,tajiyo alamun tafiyar mutane..........
Sadeeq kam har ya sakko, tana ajiyeta a k'asa masu motar na zuwa gurin, "kai me kuke a nan? Mutumin ya tambaya....
Tsorata sukayi da tambayan,sunyi tsammaninma ya gansu,lokacin da suke sauka daga motar,a firgice suka juya suna kallonsu, "maza ku tafi gida Ku daina tsayawa idan an aikeku kunji ko? Mutumin ya fad'a, da saurin su suka kama hanyan barin gurin.........
Tafiya suke kamar zasu tashi sama dan saurin da suke yi,gani suke kamar za a ganesu k'arshe ma ko ya koma dasu can garin,.......
Kallonsu kawai mutumin ya tsaya,da mamaki a fuskarsa,ganin basuyi magana ba kuma sai sauri suke..........
Har suka b'ace daga gurin,sannan ya dawo da ganinsa kan abunda zaiyi......
Kayan suka fara saukewa daga cikin motar,sai da suka gama saukewa,anan yaga 'barnan da suka masa,amma tunaninsa bai bashi Sune ba,tunda ba daga motar ya gansu suna sakkowaba,a tsaye kawai ya gansu,sbd haka sharewa kawai yayi,ya koma cikin motar,tare da yiwa masu kayan sallama,ya bawa motarsa wuta,ya juya zuwa inda ya fito.............
Tafiya kawai suke ba tare da sun san Inda suka nufaba,haka sukaita bulayi acikin garin na Kano, sunzo wajejan unguwa uku,anan suka samu wani line da yake shiru,shiga line en sukayi,unguwan duk incomplete buildings ne a wajen,hakan ne yasa basu b'ata lokaciba suka nemi guda daya,suka shige,nan ne ya zame musu gurin kwanciya,har na "yan kwanaki..........
*SMASHER ������*
���� *RAYUWAR WANI......*
_{ơŋɛ'ʂ Ɩlıʄɛ...}_
����
��
*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ...*
*ცყ.*
_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)........*
*"YAN UWA RABIN JIKI,INA MATUK'AR JIN DAD'IN ZAMA DAKU,AKODA YAUSHE BANIDA BURIN DA YA WICE RAYUWA TARE DA KU,ALLAH YA BARMIN KU....HUBBEEYY DA MEINERH*
*℘ąɠɛ 5↔6*
Maganar abinci kam ba a maganar inda zasu same shi,sai dai wata rana idan yunwa ta ishesu sadeeq ya fito yana zagawa gida² yana bara,wasu su basu wasu kuma su Kore shi,ga zagi da ake had'a masa da shi,amma a haka yake zuwa kullum babu maganar zuciya...........
Idan yayi yawon barar tasa wata rana ya rasa,haka zai dinga cewa "za akai Sahara",haka zai d'an tattara 'yan kud'ad'en su samu su sai garau² domin to she wata k'ofar.........
Duk ranar da bai samuba haka zasu wuni cikin mawuyacin hali.......
Duk da k'arancin shekaru nasu, hakan bai hanasu fuskanta rayuwaba.........
K'wanaki sunci gaba da wucewa babu wani sauyi aciki sai ma k'arin k'unci da suke dad'a fuskanta.........
Ganin babu chanji yasa dolensu yanke shawarar barin unguwar,kad'ai suje suna zaune a nan yunwa ta hallaka su,ba Sani za a yiba,sai sai idan anji wari a duba...........
A ranar basu bari sun dad'a jan lokaci ba suka kama hanya.........
Tafiya kawai suke ba su san inda suka nufa ba,kayan jikinsu duk yayi bak'i duk daud'a ta ko ina saboda rashin wanka,gaba d'aya jikinsu yayi wani iri,duk kamanninsu ya sauya,da gano ka ga abun a tausaya......
Amma mutane sai dai su kallesu.....
Duk inda suka ratsa mutane zai kallonsa suke,kamar anga sababbin hallita.......
Tafiya suke sai da suka zo dai² gyad'i² sannan suka sake d'auke hanya, Maiduguri road suka bi,suka ci gaba da tafiya........
Tafiya suke babu k'ak'k'autawak'ak'k'autawa,sai da suka sake yada zango a dai² chicken plus sannan suka yada zango........
Waige² suke su samu gurin da zasu samu su huta,kafin su samu abunda zasu sawa cikinsu........
Kowa da abunda ya same shi acikinsu.....
Sun rasa me ya kamata ma su yi yanzun,babban abun tunanin shi ne,ynzn ina suka nufa da zai zame musu gurin kwana.......
Tunda su kam ba kowa garesuba bare su nufi inda yake ko zai tausayawa rayuwarsu.........
Ganin mutane na shiga cikin gurin,kuma idan sun shiga said suga sun fito da Leda,a hannunsu......
Ya sa suka fara murna sun samu inda zasu na cin abinci ynzn,sauran gurin kwanciya kuma,abunda suka mufad'a kenan lokacin da suke k'ok'arin shiga gurin.......
Tura k'ofan gurin suke,amma sun kasa abunka da ba "yan gariba,kuma babu a house,bare su san yanda za ayi..........
Wani mutum da ya zo yana k'ok'arin shiga ne,suka matsa bayan,yana bud'ewa suka bishi a baya,har cikin gurin.....
Guri suka samu suka zauna suma,kamar yadda sukaga ya zauna,suna jiran a mik'o musu nasu kason........
Shiru suka kaga babu wanda ya kula su,hakan yada suketa raba ido kamar shege a rabon gado......
Tahowar wani waiter d'auke da plates da aka sashi order,yana tafiya idanunsa suka zauna akansu,ido ya zare waje yana kallinsu kafin ya dire plates en dake hannunsa,ya nufo inda suke.......
Idonsa taf da bala'in ganinsu ga b'acin rai dan gudun kada saken da sukayi har wad'annan almajiran suka shigo yasa su janyo masa asara........
Tunkarosu yayi yana zazzaga ruwan masifa,"uban me kukeyi anan wajen?, ya tambaya.......
Kallonsa suke kamar ba zasu bashi answer ba,cikin sanyin jiki sadeeq yace "sadakan abinci mukaga anayi shi tasa muka zo amsa muma"..........
"Kan uban can wane d'an iskanne yace muku kyauta Mike rabawa? Saboda gamu iyayen marayu,ko gwamnati ba jurar cigar da su takeba bare mu da muka kashe mak'udan kud'ad'e kuma komai dan riba ake yinsa ba dan fad'uwa ba...........
Ku tashi kuyi waje tun kafin nasa ayi waje daku,nan gurin babu abincin sadaka"........
Ya fad'a yana zare ido.......
Sum² suka mik'e suna kallonkallon jama'ar gurin da zasu san shigowarsuba sai hayaniyar da suka ji,da fad'an da waiter yake musu...........
Ficewa sukayi suna kallon plates en dake kan tables en gurin,sunata had'iyan yawu..........
Wajen gurin suka nemi gefe suka zauna,abun tausayi,tsawon wani lokaci babu wanda ya kula da halin da suke ciki,bare ya tausaya musu da Koda garin kwakine ba sugar bare ruwa........
Ikram har ta fara kuka saboda yunwan ya wuce misali..........
Suna nan zaune suna jiran tsammaniba daga gurin ubangiji........
Wani alhajine da yazo wucewa zai shiga gurin ya gansu zaune sun had'a kai da guiwa,ga ikram dake kuka,su kam jiddah da sadeeq suna zaune ne amma babu mai cewa komai,kana ganinsu zaka karanci damuwa akan fuskokinsu.........
Kallonsu yayi ya girgiza kai,duk sunyi datti gashi da gano kasan yunwa suke ji,wucewa yayi yana kallonsu........
Har ya shiga gurin yana waigensu,wani waiter ya kira ya bashi ordern abunda zaiyi had'a masa........
Tafiya yayi ya had'a masa takeaway, ya dawo ya kawo masa.........
Murmushi yayi kafin yayi masa nuni da yaran dake wajen gurin........
"Ka bawa yarancan dake waje", ya fad'a....
Fita yayi ya nufa gurinsu,ganin ya nufo su yasa suka hau kalle²n ina zashi,ganin su yake nufowa yasa suka hau tsuma..........
Mik'a musu packages en ya shiga yi amma an rasa mai karb'a acikinsu..........
Saima matsawa baya da suke kamar sunga abun cutarwa........
Ci gaba yayi da mik'a musu,amma sai suka ci gaba da matsawa daga gurin........
Abun ya matuk'ar b'ata masa rai,hakan yasa ya bud'e baki da niyyar yin maganar.........
Cikin bala'i ya kallesu yana fad'in " kar ku mai dani wani d'an iska mana ina binku kuna komawa baya,kada Allah yasa ku k'arba wa kukayiwa,dan kun samu ma an taimaka muku,kunyiwa kanku"...........
Yana gama fad'in haka ya juya da niyyar Barin gurin,hannunsa rik'e da ledojin............
*_SMASHER ������_*
���� *RAYUWAR WANI......*
_{ơŋɛ'ʂ lıʄɛ...}_
����
��
*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ...*
*ცყ.*
_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)........*
*℘ąɠɛ 7↔8*
Da gudu sadeeq yabi bayansa yana bashi hak'uri yana fad'in " kayi hakuri malam idan ka tafi da shi bamu da Wanda zai bamu dan Allah ka temaka ka bamu,munji ance saidawa ake shiyasa bamu karb'a ba tunda bamu da kud'in siya,kaga k'anwata har ta fara kuka, dukanmu yunwa Muke ji".........
Ya fad'a yana goge k'wallar da ta sakko masa akan fuskarsa,saboda maganar da mutumin ya fad'a,akan iyayensu da basa ma duniyar..........
Tausayin halin da yaran suke ciki yasa ya mikama sadeeq,bai sake maganaba,ya juya zuciyarsa cike da tausayin yaran ya koma bakin aikinsa.........
Godiya suke masa,shi kam ko takansu bai sake biba haka ya nufi ciki.........
Tunani duk ya addabi zuciyarsa,akan me iyaye zasu dinga sakaci da yaran su? Dubi dai wad'annan yaran,me zaisa idan har iyaye sun damu da "ya "yansu suyi sakacin da zasu fito bara??.............
Da murna kwance a fuskokinsu na samun abincin kyauta,suka farwa abincin da ci,hannu baka hannu k'warya haka lokaci k'ank'ani suka farwa abincin da ci babu ji babu gani...........
Kafin wani lokaci mai tsayi har sun cinye,sai packages en da ke gabansu.........
Bakin wani famfo suka nufa,suka sha ruwa tare da wanke hannayensu,daga nan suka ci gaba da tafiya don gurin basuga alamun zasu zamu gurin kwanciyaba............
Cikin nassarawa G.R.A sukayi kasancewar unguwar ta masu kud'i,rayuwarsu suke wani bata gaban wani..........
Sun jima suna bulayi cikin unguwar kafin suka samu gurin da zasu kwana,karkashin wata bishiyar mango,anan suka yada zango,har dare ya riskesu,suna zaune ba tare da sun samu abunda zasu shimfid'aba..........
Akan k'asar gurin suka kwana,yayinda sauran al'ummah ke cikin gidajensu," ya"ya suke kwance kan abun kwanciya mai kyau,yau ga wasu ko gidan basu da bare abun kwanciya........
Koda gari ya waye,nan fa aka fara artabu tsakaninsu da yunwa,unguwan shuru kamar babu wata halitta mai rai acikinta.......
Neman mafita suka fara,inda suka yanke shawarar neman Koda aikataune.......
Haka jiddah ta fara shiga gidajensu dake unguwar ko Allah zaisa su dace.....
Gidan na farko data shiga,bayan ta Haida mayar gidan take cewa "wiki nake nema,idan akwai wani abu da za ana miki", bud'ar bakin matar sai cewa tayi " na rasa wadda zan d'auka aiki sai ke k'azama dubafa kiga irin gidan da nake ciki,amma na d'auke ki aiki ai memakon ki gyaramin sai dai ki k'aramin daud'a".........
"Ke waye ma zai d'auke ki wani aiki duk wanda kuwa ya d'auka ya had'a kansa da aiki"..........
Yi maza ki ficemin a nan tun kafin nasa a Sakar miki karnuka,Tana yi tana yatsine fuska kamar taga abun k'i............
Haka ta kama ta fice a gidan,duk da k'arancin shekarunta hakan ba zai hanata fuskanta k'alubale ba.........
Haka ta dinga shiga gidajen,duk gidan da ta shiga da kalar wulak'ancin da za a mata,wanima har sai an tunkud'ota waje,amma bata fasa k'arasa shiga gidajen ba...........
Ganin babu nasara a cikin wnn lamarin,ta yanke shawarar subar unguwar kawai shi zaifi musu kwanciyar hankali,tunda duniyar ta zama masu tausayin talaka basu da yawa,mutane sun sama Kansu son duniya............
Haka suka kama hanya sauka fice daga unguwar.......
Basu san ina kuma zasu nufaba,sun fito titi sai waige² suke sun rasa madafa...........
Wani eatery suka hango daga tsallaken titi......
Shawara suka yanke kan kawai fara suna zama acan, idan Allah ya taimaka musu,mutane sun ci sun rage game tausayi idan ya gansu a wannan halin zai tausayi musu............
Gurin suka nufa suka zauna,da yawa mutane idan sun gansu a wnn halin ga wad'anda basu da tausayi talaka har zagi suke sha..........
Ganin abun ba na k'are bane yasa ta dole suka koma tamkar mabarata a gurin,idan mutum ya fito zai tafi sun dinga binsa kenan ya temaka musu da abunda zasu ci abinci yunwa suke ji............
Wasu su tausaya musu,wasu kuma su hantare su akan zuwama da sukayi kusa da su...............
Haka rayuwa taci gaba wullawa da su acikin wannan matsanancin yanayin,ba tare da samun mafita ba........
Lamar kullum yauma zaune suke bakin eatery en,suka kallon shiga da fitar mutane,daga ciki........
Wata had'ad'd'iyar motor ta Parker a gurin,ta kusa 5 minutes a tsaye,amma na cikin ta bai fitoba,haka kuma bai kashe motanba,duk son mutum da ya gane ainihin mamallakin motar hakan bazai yiwuba,kasancewar glasses en masu duhune...........
Zuwa shud'ewar mintuna 7,aka bud'e kofan motan kad'an.........
K'afa d'aya aka sauke waje,hakan ya tabbatar da cewa namiji ne,sanye da cover shoe k'ira mai matukar kyau,da gani kasan naira ta koka akai.........
Sai da ya sake d'iban 3 minutes a haka ba tare da ya fitoba...........
Gajiya yayi da zaman dan kansa ya fito,ya tura kofan motar yayi gaba,tafiya yake cikin isa da tak'ama,kamar wani mace,macenma irin "yan high class sbd yanda yakeyi ko wata macen albarka...........
Tafiya take cikin sauri, hannunta d'auke da robber faro da ta cikota da ruwa,robber ko murfi babu saman robber,haka take rik'e gam da ita,tana saurin ta ruski " yan uwanta data bari zaune kan kwalin indomei da suka tsinto,ya kasance musu abunda suke bacci akai yanzun.........
Tafiya tana kallon robber ganin yanda ruwan yake kad'awa aciki,tana gudun kada ya zubo...........
Wani mugun karo sukayi lokaci guda ta sake robber ruwan nata,gaba d'aya ya zube masa ajiki...........
K'aran saukan mari ne ya sata d'aga kai ta kalli abunda ke gabanta,saurayi ne matashi, fuska cikin matsanancin b'acin rai..........
Hankad'ata baya yayi cikin kaushin murya ya fara mata masifa "ke wace dabbace,mahaukaciya da zakina tafiya ba tare da kina kallon gabankiba"........
Ganin ta kafe shi da ido,tak'i cewa komai ya sake d'aure fuska,nan ya shiga surfa mata ruwan rashin mutunci,ita kam tana tsaye kamar wacce aka dasa,duk da maganganunsa sun tab'a mata zuciya,musammanma da ya kiranta da dabba,mahaukaciya,almajira,ji take uwa ta d'ora hannunta a ka tayi ta kuma,amma babu yandata iya,haka ta juya taci gaba da tafiya ba tare da tace masa ko ci kankaba,sai a lokacin hawaye suka samu damar zuba daga idanunta...........
Kamar mai jiran wani abu haka ya bits da kallo cikin k'unar rai,haka ya tsaya yana k'are mata kallo,cikin abunda baifi motawar second ba take ya juya cikin sauri ya bar gurin zuciyarsa sai tashi take,saboda ganinta da tayi...........
Sai a lokacinma yaji haushin kansa da ya tsaya ya kulata.........
Motar ya koma, ya zauna,jikinsa ya kalla take yaji kyankyamin kansa da kayan dake jikinsa..........
Blue polo dake jikinsa ya kama ya cire daga jikinsa...........
Farin singlet ya bayyana,fisgan motar yayi da k'arficikin bacin rai yake driving en har ya isa cikin unguwan sharad'a NNDC quarters........
A fusace ya fito daga motor en ya nufi cikin gidan..........
*SMASHER ������*
���� *RAYUWAR WANI......*
_{ơŋɛ'ʂ lıʄɛ...}_
����
��
*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ...*
*ცყ.*
_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)........*
*℘ąɠɛ 9↔10*
Ko da ya shiga parlor bai kula kowaba ya haura stairs....
Direct toilet ya nufa,ya sakarwa kansa shower....
Yafi 40 minutes kafin ya fito d'aure da toilel a k'ugunsa.......
Bakin bed en ya zauna,zuciyansa duk babu dad'i,shi kansa k'yank'amin kansa yake ji ynzn,"grain yayama hakan ya faru", ya rasa wanda zai hugging sai wannan k'azamar yarinyar........
Duk haushin kansa yake ji,da bai tafi yana latsa phone ba duk hakan bai tab'a faruwa........
Ya ja tsaki yafi a k'irga,amma duk da haka bai daina jin haushin kansa ba,da kuma ita yarinyar da ko hak'uri bata iya bawa mutaneba ta masa laifi amma ta masa basa hak'uri..........
Wani ruwan ta koma da niyyar d'ebowa kasancewar suna buk'atar ruwan,amma gashi ya b'are,koma shi wnd yayi mata asaran ruwan maimakon ya bata hak'uri saima marinta da yayi........
Dai² gurin ta kai hannu ta shafa,tana furta "Allah ya isana mugu kawai".........
Inda ta bar "yan k'annenta ta nufo,yana tafe tana 'yan wak'ok'inta,har ta k'araso.......
Dubawa tayi taga sai ikram kad'ai kwance kan kwalin da ya zame musu kamar gado........
Tambayarta ta shiga yi,"ina sadeeq?".......
Gashi can adda,juyawa tayi tana son gano inda yake.......
A can tsallaken titi ta hangoshi,tana tafe tana tsalle² kamar yaron biri......
Da gano kasan tsallen murna ne yake yi,hannunsa d'auke da leda, tana tafiya tana d'ago musu ledan,murmushi fall fuskansa..........
Tahowa yayi zai tsallako,lokacin kuma wani black Homer ya dawo kai......
Cikin k'araji jiddah ke fad'in, "a'a, ka koma,kar ka taho,tana yi tana masa nuni da hannu alaman ya da ka ta da tahowan da yake,amma ina..........
Ci gaba yayi da matsowa,zai da yazo tsakiyan titin,dai² lokacin Moran na k'arasowa.......
Sai da yayi dama sannan ya dawo,ya gangara gefen titin.......
Da k'arfi drivern ya taka birki,cikin hanzari ya fito,wani babban mutumne a bayansa yana fad'in *SUBHANALLAH!!*....
Muyi sauri malam Shehu kar ya rasa ransa,ya samu raunuka ssai......
Cikin hanzari ya mik'a hannu yana k'ok'arin d'aukansa amma jiddah ta k'ank'ameshi, banda k'ok'arin karb'ansa babu abunda mutumin yake tak'i sakinsa......
Wani mutum cikin irin masu d'aukan rahotone yake fad'in cikin tsawa da fad'a "ke sallah ki sake shi a kaishi inda za a masa magani,kin kama kin rik'e shi idan an bar miki shi wace uwar zaki masa?"......
Jin ya ambaci mutuwa yasa ta sake shi,dan ita lam har ga Allah tayi tsammanin guduwa zasuyi da shi shi yasa tak'i bari a d'aukeshi tun da farko........
A baya suna bi mutanen har bakin motar.......
A baya ya sasu,bayan ya kwantar da sadeeq da bai san inda kansa yake ba......
A front seat suka zauna shida alhajin,daga nan sai asibitin NASARAWA.......
Direct A & E akayi da shi,sun tsaya sunyi cirko² kamar wasu zakarunda ke fad'a........
Likitoci sun duk'ufa akan yaron dan ganin sunyi nasaran samun rayuwarsa........
Sai da aka d'ibi awanni 3 suna kansa duk dan ganin ya farfad'o........
Amma ina,sunyi k'ok'arin tsaida jinin dake zuba a jikinsa,daga nan kuma suka shiga treating en jikin nasa,in da yaji ciwuka...........
Jiddah kam suna zaune a waje,banda kuma babu abunda suke yi,rungume da juna,tausayin halin da suke ciki ne ya kama alhajin sai hak'uri yake ba su amma sun kasa yin shiru......
Shi kuwa d'an dattijon driver duk hankalinsa ya tashi ganin halinda suka kawo yaron,gano yake kamar bazai rayuba,ya kasa zama banda zarya babu abunda yake a varender........
Duk k'ok'arinsa na ganin ya kwantar da hankalinsa amma ya gagara nutsuwa........
Zuwa wani tsayin lokaci sannan wani doctor ya fito........
Alhajin ne yayi k'arfin halin tunkararsa yana zuwa take cewa "doctor ya jikin yaron? Ya farfad'o?"......
Kai likitan ya girgiza masa kafinbyake cewa,"yanzun dai ba wnnba mun samu jinin ya tsaya sai dai a wnn lokacin muna buk'atar Jini saboda ya rasa Jini ajikinsa,rayuwarsa tana cikin hatsari idan had ba a samu jininba nan da wasu awanni........
Cikin halin ko in kula alhajin yace muje likita a gwada nawa idan zai masa babu Matsala sai a d'iba.......
Tafiya suke har suka k'arasa office en likitan..........
Waya yayi lab,ba a d'auki lokaci mai tsayiba,aka k'wank'wasa door en,umarni ya bada,take aka shigo,bayani ya masa akan abunda yake buk'ata,ya juya suka fito tare........
Lab suka nufa,bayan an gwada jinin,babu wata matsala da yake d'auke da ita.......
Ba a wani b'ata lokaciba aka shiga da jinin d'akin da sadeeq yake,likitan ya jona masa..........
Sakkowa yake daga staircase en fuskar nan kamar an aiko masa da sak'on mutuwa.......
Babbar mace ce zaune tana binsa da kallo tun lokacin da ya fara sakkowa,har ya k'araso cikin parlor ya nemi guri ya zauna kan sofa........
"Wai *JABEER* meke damunkane,ka shigowa mutane gida babu sallama,ina jinku har little tana maka magana amma ko kallon inda take bakayiba,meke damunka??" Ta tambaya.....
'Dagowa yayi yana kallonta kafin yace "babu komai", babu komai kuma ka shigo mana gida a haka? Ko kuwa kana tunanin zan yarda da abunda ka fad'a,kasan nafi kowa Sanin halinka ko??
Wayanta dake kusa da ita yayi k'ara,dubawa tayi cikin hanzari ta d'auka tana fad'in "Alhaji har yanzun munjiku shiru,baku shigo garin bane,tun d'azu kace kuna mariri", sai anan ta dasa aya......
Jin maganar da yake mata yasata rafka salati, "wane asibiti kuke?? To in sha Allah gamunan",ta bashi answer cikin zak'uwa......
Hanging wayan tayi tana fad'in little yi maza ki shirya,ki cewa baba Laure ta shirya abinci a basket zamuje hospital daddynku sun samu accident, a hanya.........
Cikin damuwa little har ta fara hawaye take cewa mammy amma dai basuji ciwo ssaiba.......
"A'a basu bane wani yaro suka buge,basu ji ciwoba,yi Sauri kafin na fito ki fad'a mata", ta fad'a tana bin hanyan stairs cikin sauri........
💠💠 *RAYUWAR WANI......*
_{ơŋɛ'ʂ lıʄɛ...}_
💠💠
🌹
*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ...*
*ცყ.*
_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)........*
*WANNAN PAGE EN NAKUNE*
_AUNTYNAH KHADIJAH (MAMAN K²)_
_ZAITUNA_
_BILKISU Y'AR ABBAH_
_AUNTY HALIMA (HALIMA SAHAD)_
*INA NAN TARE DAKU A KULLUM*
*INA GODIYA DA K'ARFIN GWIWA DA KUKE BANI FANS AKODA YAUSHE INA TARE DA KU,GODIYA GA D'AUKACIN MASOYA NOVEL EN RAYUWAR WANI 😍😍😍...*
*UP!*
*UP!!*
*UP!!!*
_UMMU BASHEER INA TAYAKI MURNAR KAMMALA LITTAFINKI (RAYUWAR NAJWA) ALLAH YASA KI FARA (ZURI'A D'AYA) LAFIYA KI GAMA CIKIN SALAMA KAMAR YADDA KIKA GAMA WNN LAFIYA,ALLAH YASA SAKON DAKE CIKI YA ISA INDA KIKE SO..._
*NAZO GAREKI SAJIDA (MAI Y'AR MAHAUKACIYA)*
_MUNFA GAJI IDAN BAZAKIYI MANA TYPING KULLUMBA ZAN JA ZUGA MU TAFI SRIKE......MUJI EHEMM GOBE_
_MY BESTIE *MUNEERAH* YASEEN HAR KE IDAN BA KULLUM MUKE SON GANIN TYPING ENKI,IDAN BA HAKABA TAMMMMM..._
*℘ąɠɛ 11↔12*
Yana nan zaune a parlor har mamy ta fito,cikin shiri ita da little,hanyar kitchen little ta nufa Don d'auko basket da zasu tafi da shi......
Kallo kad'ai yake binsu da shi sai Saudi suke,amma ko motsawa baiba saima squeezing da yake da face nasa......
Mamy ce sun zo fita ta juya tana kallonsa take fad'in "jabeer ka taso ka kaimu Nassarawa hospital"........
Dad'a yatsina fuska yayi kafin yace " mamy banjin dad'ine yanzun kisa sani driver ya kaisu"......
"Allah ya sawake", ta fad'a tare da juyawa tana kallon little muje,taja hannunta sukayi waje.........
A harabar gidan ta hango sani zaune kusa da habu mai gadi sai fira suke,suna dariya......
Hangosu da tayi yasa ya task da d'an gudunsa yana fad'in "hajiya barka da fitowa", yauwa sani dama asibitin nasarawa zaka kaimu, "to hajiya" ya fad'a lokacin da ya juya ya nufi parking lot.......
Har inda suke ya iso da motar,babu b'ata lokaci suka wuce,sai nassarawa hospital.......
Ba su sha wahalaba suka gano inda suke,kasancewar akwai phone.......
Lokacin da suka k'araso gurin yayi dai² da fitowan doctors en sun gama masa duk wani abu daya kamata ayi masa........
Doctor ne ya matso da Daddy yana fad'in "congratulation sir munyi nasarar ceton patient enku, yanzun haka zamu iya ganinsa sai dai banda hayaniya,duk da dai ynzn yana bacci"......
Hannu ya mik'a masa tare da masu fatan samun sauk'i na patient en masu,yayi gaba.......
Da gudu little ta k'arasa kusa da daddy tayi hugging nasa tana fad'in "daddy we all miss u,how about ur patient????
Kanta ya shafa yana fad'in "alhamdulillah my little".....
"Daddy amma baiji ciwo ssai ba ko?" Ta tambaya fuskanta da damuwa........
Tafiya ya fara yana fad'in "A'a my little sai dai min duba tukun zamu san adadin yadda yake a ynzn"..........
To daddy Allah ya bashi lafiya.......
"Ameen my little", ya fad'a lokacin da yaja hannunta suka nufi k'ofan d'akin.......
Mamy ce ta fara magana "to daddy mu kuma sai ku barmu nan muna jira, ka kama hannun yarka kunyi gaba babu magana??"........
Sai lokacin daddy ya juya yana murmushi yake fad'in "eyyahh mammyn yara amin afuwa kinsan idan ina tare da lovely daughter na bana gane kowa"......
"To ai sai kiyi,ya mai jikin?" Ta tambaya....
Alhamdulillah amma bamu san halin da yake cikiba sai mun duba tukun........
To Allah ya bashi lafiya.......
"Ameen", ya amsa suka d'unguma cikin d'akin.........
Tunda su mamy suka zo basu kula da yaran dake zaune a gurin ba,sai bayan sun shiga d'akin,kamar ance little juya ta gansu........
Tsalle tayi had'e da rafka ihu yana fad'in "wayyooo!! Daddy na babu,kaga bayanka", dad'a k'ank'ameshi take tana ci gaba da juna masa.......
Many ce ta mata tsawa tana fad'in "kanki d'aya kuwa little kike mana ihu haka,sai kace bakiji me doctor ya fad'a ba kafin mu shigo"............
Bayan daddy ta shigo ta b'uya tana lek'osu kamar wacce idan ta fito zasu tafi da ita.........
Mamy ce ta juya tana kallonsa,tsayawa tayi kamar status......
Daddy ne ya juya tunawa da 'yan uwan yaron sun barosu waje,baiyi tunanin sun biyosu a baya ba........
Ganinsu yayi tsaye bakin k'ofan ruk'e Da juna........
Murmushi yayi kafin ya maida kallonsa kan Mamy dake tsaye still ta kasa motsi......
Mamyn yara wad'annan sune y'an uwan yaron......
Murmushi tayi tana fad'in "Eyyahh!! Allah sarki sannu kunji"....
Kalle² suke sun kasa sakin jiki sai bin gefe suke,sai lokacin little ta fito daga bayan Daddy tana dad'a k'are musu kallo.......
Gadon suka nufa kusa da sadeeq da akema k'arin jini, daddy ne ya dakatar dasu ta hanyar fad'in "A'a kasa ku tasheshi kunga ya samu bacci,zai samu sauk'i da izinin Allah.........
*_SMASHER 🤞🏻😘_*
💠💠 *RAYUWAR WANI......*
_{ơŋɛ'ʂ lıʄɛ...}_
💠💠
🌹
*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ...*
*ცყ.*
_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*WANNAN PAGE EN NAKUNE Y'AN TIME WRITERS,KUN ZAMA JININ JIKINA,GASKIYA YAU KUN FARANTAMIN MUSAMMANMA......*
_AYUSHA ILYAS._
_Y'AR GIDAN NA IKKE._
_Y'AR ALJANNAH._
_RUQAYYAH HASSAN UTHMAN._
_JAMILA MUSA. AND_
_MY BESTEI MUNEERAH._
*ALLAH YA BARMINKU,KU JIMA KUYI K'ARKO,YA KAREMINKU SHARRIN MAK'IYA MAHASSADA......ONE LOVE TIME WRITER'S ❤...*
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)........*
*℘ąɠɛ 13↔14*
Mamy kam banda kallonsu babu abunda yakeyi,ganinsu kamar wasu sabbin kamu,a hauka.......
Amma tunanin da ya addabeta shi ne,su kuwa wad'annan yaran ina iyayensu da danginsu da suke rayuwa cikin daud'a,wanda gara wani almajirinma da su......
Duba da yadda kayan jikinsu ya koma,yayi bak'i duk ya ya fara rab'ewa dan kansa.......
Abincin da suka shigo da shi mamy ta janyo basket en,zubawa tayi a plate t mik'a musu,kafin wani lokaci had sun tasheshi a aiki,kallonsu kawai many take cike da tausayin irin rayuwar da suke fuskanta........
Idon little kamar zai fad'o Kansu,ganin sun share abincin basu ko rageba,take fad'in "mamy ki k'ara musu basu k'oshiba", murmushi kad'ai tayi,tana kallon yadda duk ta cukuikuye daddy,ta hanashi sakat........
Har suka tashi tafiya ba ta bar jikin daddy ba,sai dariya mamy take mata,sukayi musu sallama suka wuce gida tare da daddy.........
Lokacin da suka koma,bayan sun gama duk wani abu na al'adarsu.....
Daddy yana kwance lokacin ne mamy ta zauna gefensa,tun da yaga ta zauna ya san akwai maganar da zata fad'a.......
Tashi yayi yana kallonta,kafin yayi murmushi da fad'in "mamyn yara yadai kika zauna shiru?".......
Wallahi daddy akan yaran nan ne gaba d'aya abun tausayi,kamar ba y'ay'an mutumba,kayan jikinsu sun fita hayyacinsu,kuma dad'in abunma da gani yunwa taci jikinsu..........
Dan Allah daddy alfarma nakle nema,nasan bazaka k'iba,ta d'an yi shiru kafin taci gaba da cewa "idan Allah ya kaimu muka gano inda "yan uwan yaran suke,ka temaka musu da gani suna cikin mawuyacin Hali"..........
Murmushi yayi mata tare da cewa "an gama uwar gidana kuma amaryata........
Dariya bara sosai dan duk lokacin da haka ta fara,ko tamasa abunda ransa yayi dad'i haka yamata kirari.........
*Next morning...*
Tun da safe mamy sun gama shirya duk wani abun da za a buk'ata........
D'akin little ta nufa kwance ta sameta tana sana'ar tata,tashinta ta shiga yi,amma da k'yar ta iya tashi,saboda k'aunar bacci........
"Saiki tashi ai ki shirya,idan kuma bazakiba mu baki gida ke kad'ai", mamy ta fad'a lokacin da ta juya zata fita........
Ai da sauri ta diro daga kan bed en,daga ita sai Nicker's da vest,ta nufi banyan toilet en dake cikin room en,tana tafe tana mitsikka ido,da k'afa ta tura k'ofar..........
Ko cikin toilet enma kafin tayi wanka ta fito ta jima saboda baccin ba wai ya isheta bane........
Cikin shirinsu suka fito ko break a tsaitsaye sukayi suka nufi hospital, matar baba mai gadi suka tarar a d'akin tana zaune kan kujera,sai jiddah da ikram dake kwance kan tabarma suna bacci.........
Zuwan su daddy yasa su tashi suna binsu da kallo,babu wanda suka iyawa magana............
Mamy ce tayi murmushi tana kallon ikram dake ta wulla ido tana kallon su d'aya bayan d'aya tana fad'in "y'an mata zo", tashi take k'ok'arin yi jiddah ta mata ta zaunar,ta hanata tashi,kallonta tayi tana kanta a k'asa kan dole ta koma ta zauna,sai dai kallonsu kawai da take........
Mamy ce tayi murmushi tana fad'in "y'ata me yasa zaki hanata zuwa,ki k'yaleta mana,bamu da niyyar cutar da ku.........
Kanta a k'asa bata iya sake kallon kowaba,little dake kusa da daddy ta matso kusa da mamy tana cewa "mamy ki basu abincin ko suna jin yunwane", "u are right my dougher",tare da janyo kayan da suka zo da su.........
Bayan ta gama had'a musu komai,ta kalli iya ladi race "iya zaki iya tafiya gida ki huta zuwa yamma,sai ki dawo",godiya tayi ta musu sallama ta kama hanya ta fice ta nufi gida........
Daddy kam tunda suka shigo ya duba jikin yaron,jikinsa duk yasha plaster, kansa nad'e da bandage, abun tausayi,fita yayi waje ya kira number doctor......
Yana nan zaune har doctor ya k'araso gaisawa sukayi,kafin daddy ya shiga masa complain akan rashin farkawar yaron,tun da suka zo ko Motsi bai yiba........
Tare suka shiga d'akin ya duba shi.....
Bayani yama daddy Cesar babu wata matsala farkawa ne kawai baiyiba,kuma hakan ya samu ne sanadiyyar allurai da aka masa........
Waje suka koma,nan daddy ya ke fad'awa doctor yana son canjawa yaron hospital ne,idan hakan zaiyiwu,shawarwari ya bashi kafin akan ya bari yaron ya farfad'o kafin ayi komai.......
Godiya yayi masa sukayi sallama,ya koma d'akin,shi kuma ya koma bakin aikinsa........
Bayan ya dad'a duba jikin nasa yayi musu sallama sai wuce office, har bakin Kofa mamy ta rakasa suna ta raha, ya tafi,ita kuma ta koma taci gaba da kula da sadeeq........
Suna zaune ta kalli jiddah dake bakin gadon kusa da sadeeq ta k'ura masa ido ko k'iftawa batayi........
Mamy ce ta sake kallon jiddah tana murmushi tace "y'ata ina ne gidanku,aje a fad'a musu kasa hankalin iyayenku ya tashi gashi tun juya ba a san ina kukeba" sai lokacin ta samu tayi shiru tana sauraron amsar da zata bata............
Kuka jiddah tasa, gani take kamar a lokacin inna ta mutu,sai yanzun ta sake jin d'acin mutuwar tata........
Ganin bata da niyyar yin shiru yasa mamy take mamakin wannan lamari me ya sa take kuka daga tambaya.......
Shiru tayi tana kallonta ta kasa cewa komai,can kuma cikin she²kar kuka jiddan tace "mu bayan nan bane".....
Cikin mamaki mamy ta sake kallont tace "ba anan kukeba,ina iyayenku suke?????".......
Cikin kuka jiddah ta bawa mamy labarin abunda suka gani ranar da suka tarar wuta ta k'ona musu gida da innarsu da basu ganiba.........
Jikin mamy yayi sanyi da labarin da taji,little kam fuskanta duk ya b'aci da hawaye,saboda akwaita da saurin kuka.......
Haka suka wuni a hospital en jikinsu duk a mace,duk motsin da zasuyi idon mamy na Kansu,tausayinsu duk ya isheta,gasu k'anana da su,amma haka zasu k'addarar take ba yadda zasuyi dole su karb'eta hannu 2²...........
Ko da daddy ya dawo da gamma da zasu tafi gida,sai da mamy ta same shi da maganar tafiya da su jiddah,kasancewar sa mutum da tasan hak'k'in d'an adam da kuma tausayi,take ya amince da tafiya da su........
Bayan sun gama abunda zasuyi lokacin baba ladi ta dawo,suka mata sallama suka tafi........
A hanya sai kalle² suke har suka shiga unguwar NNDC,katafaren gidan da sukaga motarsu ta tsaya suka saki baki,suna kalli,tun daga gate suke kalle² har suka shiga cikin gidan, da ka ga yanayinsu kaga wad'anda basu saba ganin irin wannan gine² ba,ko alabari basu san da irinsa ba,bare su da suke cikin daji babu yadda za ayi ma kace zasu gani a TV........
A parlor suka yada zango ikram data ta kasa zama,sai tab'a sofas en take tana murmushi........
Mamy ce tace "yawwa little maza kuje d'aki jiddah tayi wanka,sai kuzo muyi dinner"..........
Amsawa tayi tayi gaba jiddahna Binta a baya,har suka shiga d'aki sai da ta nuna mata yadda za tayi,ta had'a mata ruwan wanka,kafin ta fito ta barta.........
Ta jima a cikin toilet tana k'arewa gurin kalli,ita kam ko nan akace ta kwana ai ya isheta bare kuma cikin d'akin.........
Fitowanta ta samu little tana jiranta,cikin sauri suka gama shiryawa,tana k'ok'arin maida kayan da ta cire,little ta nuna mata wani gown data fito mata da shi,da k'yar ta yadda taxa,ita acewarta wannan kayan turawane ba zata iya sawa ba........
Sun sha drama kafin ta amince tasa....
Lokacin da suka fito parlor sun tarar da mamy da ikram tayi fes da ita,mamy ta mata wanka ta gyara ta gwanin sha'awa kamar ba itace take cikin daud'a ba........
*_~Keep following fans~_* 😘😘😘
*_SMASHER 🤞🏻😘_*
[17:59, 12/5/2017] Sister Hawwa: 💠💠 *RAYUWAR WANI......*
_{ơŋɛ'ʂ lıʄɛ...}_
💠💠
🌹
*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ...*
*ცყ.*
_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*GAREKI ISLAH TASI'U WANNAN SHAFIN NAKI NE*
*SHAGALI.........* 💃🏻💃🏻💃🏻
_BARKA DA SAUKA SIS ISLAH,ALLAH YA RAYA BABY CIKIN AMINCI KUMA KAN SUNNAH......UBANGIJI YA BAKI LAFIYA MAI 'DOREWA,FATAN KIN SAUKA LAFIYA,RANAR SUNA ZAMU 'DEBO SHOKI 💃🏻💃🏻💃🏻....._
*LUBABATU NA IKKE...*
_BAN MANTA DAKEBA Y'AR UWA INA MIKI MURNAR AURENKI DA ALLAH YA KAWO LOKACIN,ALLAH YA BAKU ZAMAN LAFIYA YA KUMA KAWO K'AZANTAR 'DAKI 😁....._
*HASSAN ATK TANKO..*
_SURUKII INA MAKA FATAN ALKHAIRI ALLAH YABADA SA'AN EXAM DA ZA KAYI,UBANGIJI YA FITO DA SAKAMAKO MAI KYAU..._
*_~WISH U OLL D BEST SURUKIII...~_* 👏🏻👏🏻👏🏻
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)........*
*℘ąɠɛ 15↔16*
Kallon jiddan mamy tayi sai k'unshe kai takeyi,mamy na kula da ita ganin ta takure kanta guri d'aya yasa mamy tace "jiddah kinyi wankan nan kuwa sosai???"...
Kai kad'ai ta kad'a,many da b'ata yardaba ta matso kusa da ita tana fad'in "muga kanki kin wanke????".....
K'ank'ame veil en da little ta bata tayi da ta cukuikuyeshi akanta.......
Da k'yar mamy ta cire hannunta daga kan ta bud'e......
Kan adank'are yake saboda daud'a rik'e baki tayi tana fad'in "ai ba wanka kikayiba jiddatu,janta tayi sai nok'ewa take,har suka bar parlor d'akinta suka nufa har toilet, sannan tasata ta cire gown en jikinta,kan ta wake mata tun ruwan baya kumpa sai bak'in ruwa dake fita har sai da taga yayi fes kafin ta k'yale kan ta koma sauran jikinta,wanka tayi mata ssai,nan da nan sai gata tayi fes.......
Fatarta da ada tayi duhu ynzn duk ta washe,sai nok'ewa take ita a dole tana jin kunyar Mamy..........
Parlor suka dawo,bayan ta gama shiryawa,ita kanta jin jikinta take wasae iska na shigarta ta ko ina,har wani lumshe ido take saboda k'amshin gel en da mamy ta mata amfani da shi na wankin kai........
Gaba d'aya sun hallara a dining sai mutum d'aya da baya nan,sanin halinsa rashin son yin dinner dole yasa basa bi ta kansa.......
Gurin yayi shiru banda k'aran spoons da plates babu abunda kakeji,ga ikram da jiddah kam ganin sun kasa sarrafa spoons en yasa suka ajiye suka dab'ab'a yatsunsu.........
Har
Suka kammala,nan kuma suka koma parlor aka dasa fira,kasancewar al'adarsuce haka bayan sun ci abinci basa kwanciya sai anyi fira.....
Firan ya kasance tsakanin daddy da little sai mamy dake sa baki jefi²,a haka har lokacin barinsu parlor yayi........
Daddy ne ya fara barin parlor, sannan little taja hannunsu jiddah da tak'i sakin jiki har lokacin, suka nufi d'akinta.........
Ita kuma mamy ta d'auki ikram dake kwance tana bacci ta nufi d'akin da ita,bayan ta kwantar da ita tayi mata addu'ah ta fice daga d'akin.........
Lokacin da jabeer ya shigo ya Tatar parlor babu kowa,bai damu ba ya wuce kitchen Lipton kad'ai yasama cikinsa,ya nufi bedroom ensa,yana watsa ruwa ya nemi guri ya kwanta.........
Jiddah kam an baje akan bed anji laushi,ga d'akin said k'amshin freshener yake,duk sun k'udundune a cikin duvet en,ikram na tsakiyansu da haka har asuba ta riskesu..........
Lokacin da mamy ta samu dady a d'akinsa,ta masa bayanin duk halin da ake ciki game da su ikram,yayi matuk'ar tausaya musu da halin da suke ciki......
Nan yayi alk'awarin kula da su har k'arshen rayuwarsa,ssai mamy tayi murna ta kuma yi masa addu'ah Allah ya bashi ikon kulawa da rayuwarsu gaba d'aya..........
Cike da jin dad'in lamarin sukayi bacci mai cike da annashuwa.........
Tun da safe kafin su jiddah su tashi,mamy ta gama had'a breakfast, komawanta sama yayi dai² da shigowan kira a wayan daddy,ganin baya nan ya sa ta juya tabar d'akin,nata d'akin ta nufa cikin abunda bai wuce 40 minutes ba ta gama shiryawa........
Fitowa tayi ta nufi d'akin little, tashinsu ta shiga yi,little kam ta kasa tashi sai jiddah da yake bata da magagin bacci ta mik'e, maza daughter shiga kiyi wanka,wannan malalaciyar tak'i tashi ma tafi mu barta jiran gida........
Ai wani tsalle tayi ta dire kasa tana fad'in nafa tashi mamy,dariya suka da mata har jiddan da tak'i sakewa,ganin yanda ta b'are baki za tayi musu kuka.......
Ikram mamy ta d'auka tayi d'akinta da ita sai da ta shiryata tukun suka nufo parlor,zaune ta tarar da little da jiddah sun sha ado cikin riga da sket na atamfa,kayan dai² jikin jiddan tunda ita little sun d'an mata yawa kad'an.........
Dining suka nufa,don yin break, har sun zauna mamy ta kalli little tace "je kiyima yayanku magana ya sakko muyi break".......
Lokacin da ta je kiransa yana toilet,bara tsayaba tayi fitowarta,break sukayi har suka gama bai sakkoba,ganin haka suka fice daga gidam basu kira sakkowansaba..........
Tafiya suke a hanya mamy tasa daddy ya tsaya a JIFATU STORE.......
Siyayya tayi musu ssai na kayan sawa,tak'ama da cosmetics kamar zasu bud'e wani k'aramin shopping store sannan suka nufi banyan Muhammad Abdullahi Wase Hospital (Nassarawa Hospital)........
Sakkowan jabeer daga stairs yaji gidam shiru,nan ya tabbatar gidam babu kowa sai shi kad'ai, dining ya zauna bayan ya mammals break ya fice shima daga gidam ya nufi company daddy........
Tun kafin su k'arasa suka had'u da baba sani driver yanata sauri zai fita daga hospital en......
Little ce tace "mamy kinga baba driver can", kasancewar suna gaba daddy kuma suna binsu a baya.....
Magana suka masa,sai a lokacin suka kula da yanayin da yake ciki...........
*~Keep Following Fans...~* 😍😍😍
*_SMASHER 🤞🏻😘_*
[14:42, 12/6/2017] Sister Hawwa: 💠💠 *RAYUWAR WANI......*
_{ơŋɛ'ʂ lıʄɛ...}_
💠💠
🌹
*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ...*
*ცყ.*
_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*WANNAN SHAFIN NAKU NE K'AWAYENA.....*
AMINA SALISU MUSA (MEINERHTER)
AMINA IBRAHIM SALIS
AISHA ABDULLAHI ABUBAKAR
HABIBA IDREES (HUBBEEY)
HABIBA YAHYA HAROUN (HABIBATEEY)
HUSSAINA HUSSAIN TIJJANI
NA'IMA KABEER SHU'AIBU
RABI'ATU ADAM MUHAMMAD
ZUBAIDA ABDULLAHI MUH'D..
*ALLAH YA BARMINKU,MU KASANCE TARE HAR ILLAH MASHA ALLAH,REALLY HEART U GUYSSSSS 😍😍😍...*
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)........*
*℘ąɠɛ 17↔18*
Gaba d'aya hankalinsa a tashe yake,duk ya firgice da ganinsa kasan ba lafiyaba......
Cikin wani irin yanayi mamy take kallonsa kafin tayi magana Daddy ya rigata, "Malam shehu lafiya muka ganka cikin irin wannan yanayin,me yafaru??".......
Fuskansa cikin damuwa yake fad'in "inafa lafiya alhaji,Allah yayiwa yaron nan rasuwa a Daren juya,yanzunma saurin da nake na zuwa gidane na sanar da kai,anyita kiranka a waya amma baka samu damar d'aukan wayanba".........
*Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!!!....*
Abunda suke mai²tawa kenan,gaba d'aya suka d'unguma suka nufi d'akin hankalinsu duk a tashe.......
Matar baba mai gadi suka tarar tayi kalar tausayi,da gani kasan tana cikin damuwa,bayan sun shigo suka gaisa tayi musu gaisuwa.......
Little da su suka fara shigowa basu san me yake faruwaba sai yanzun da sukaji anama daddy gaisuwa,kan gadon suka duba,sadeeq ne kwance an rufe shi da farin yadi,an lulleb'eshi.......
Waje daddy ya fita ya kira doctor, yana zuwa anan yake bama daddy hak'uri da labarin yadda abun ya faru, bayan farkawarsa da dare numfashinsa ya shiga season kafin suyi yunk'urin cetonsa Ransa ya rabu da gangar jikinsa,tafiya sukayi daddy ya biya duk wani bill da akai charging ensu,basu d'auka wani dogon lokaci ba aka basu gawan.......
Kuka jiddah take ta k'ank'ame gawan uwa wadda zata mai da shi jikinta,little ma sai hawaye take,da k'yar aka raba jiddah da gawar aka tura shi suka fice daga hospital en,suka nufi gida Don yi masa sutura.........
Tun kafin su k'arasa gida baba mai gadi har ya sanar a line en nasu,mutane sun taru a line en suna jiran k'arasowansu.......
Basu d'auki dogon lokaci ba suka iso,aka shiga da gawan,bayan an gama shirya shi,addu'ah akayi masa kafin aka d'auki gawan akayi waje da ita,jiddah da ikram sai ihu suke suna fad'in "adawo musu da sadeeq ensu,haka aka fice da gawan sa daga cikin gidan........
Duk kiran da akema jabeer a phone bai san anayi ba,tun kafin su zo da gawan har aka gama shirya ta aka fita da ita daga gidam bai saniba......
Tashi yayi da niyyan fita daga office en daddy kasancewar shi yake zuwa yana taimakawa daddy akan harkokin company, phone ensa ya shiga dubawa amma ya nemeta ya rasa,dubawa yake amma still bai ganshiba sai da ya d'auki tsawon lokaci yana nema,kamar wanda aka tsikara ya fito daga office en,motor en da ya zo da shi ya nufa,yana zuwa ya kiran da ya shigo yana katsewa...........
'D'auka yayi nan ya tarar da ruwan miss call's kiran daddy ne ya sake shigowa,cikin sauri ya d'aga.......
"Jabeer ka taho gida yanzun duk abunda kake", abunda kawai daddy ya fad'a kenan ya katse wayan.......
Cikin damuwa ya ja motar ya nufi gida saboda yasan ba a tab'a masa iron wnn kiranba.......
Tun da ya shigo line en ya ga taron jama'a kuma a k'ofar gidansu,cikin gashin hankali ya nufi gida,kobtsayawa baiyi a wajenba ya nufi cikin gidam da saurinsa........
Parlor ya shiga nan ya tarar da mamy zaune da Matan mak'otansu da suka shigo mata ta'aziyyah,little ya hau nema duk da rashin jituwa da suke lokuta da yawa,coz shi ya tsani rashin kunya.......
Fitowanta daga d'aki yasa shi sauke ajiyan zuciya, saboda duk abunda yake tunani ba shi ne ya faruba.....
Komawa yayi waje gurin daddy suka gaisa da jama'an gurin,sai ta'aziya suke masa........
Gaba d'aya tunaninsa ya kulle,to waye kuma ya mutu,shi dai yaga duk wad'anda suke da alak'a da gidan ya gansu,haka dai taci gaba da amsawa,har bayan sallan Maghreb sannan suka nufi cikin gidan.......
Gidan babu kowa duk masu shigowa kowa ya tafi,sai many da su little kawai da suke zaune parlor sunyi jugum² kowa da tunanin da yake.......
Ta'aziyyah mamy tayiwa daddy, cikin sanyin jiki jabeer ma ya mata,duk da shi akwai tambayoyin da suka addabi zuciyansa......
Gaba d'aya tunda ya shigo hankalinsa bai kai kan su jiddah da suke zaune a parlor ba,sai da mamy tace su tafi su kwanta,cikin sanyin jiki suka mik'e,ta gabansa suka zo wucewa kanta a k'asa kallo d'aya ya mata ya d'auka kai,su kuma wucewa kad'ai suka yi,babu wanda yayi magana........
Ko a d'aki babu wata hira kwanciya kawai sukayi babu wata hira,kowa zuciyansu cike da damuwa,bacci b'arawo yayi gaba da su..........
*Bayan kwanaki 40...*
Zamansu a gidan babu wata takura dai² gwargwado many na kula dasu,duk wani abu da za ayima little shi ake musu.......
Bangaren jabeer ba had'uwa suke da shiba, idan ya fita baya dawowa da wuri,yawancin lokaci sun ci zama d'aki,idan little ta tafi skul,haka zasu k'ule a d'aki mamy tayi fad'an har ta kyalesu,tasan lokaci zai zo da zasu zauna ba tare da damuwan komaiba........
Kamar kullum yauma zaune suke a parlor, bayan sallan Maghreb, sun tusa TV. A gaba suna kallon MBC Bollywood, said dariya suke jabeer ya shigo sallama a ciki² yayi ya bisu da kallo,gaisheshi little tayi ita da ikram zuwa yanzun mamy tayi k'ok'arin koyar dasu gaida duk wanda suka gani,idan ya girmesu..........
Ikram ce ta shiga gaisheshi,tana fad'in "yaya shannu da zuwa", tana washe baki.......
Sosai baby ta burgeshi,gata so cute, murmushinsa mai kyau yayi mata had'e da d'aga mata hannu,kallon jiddah yayi da kanta ke k'asa bata ce komaiba,ko gaisheshi bata da niyyah,ransa ne ya sosu ganin ko kallo bai ishetaba,hanyan stairs yabi ya haura sama,da tunanin inda mamy ta samo fyn baby haka
.......
Lokaci kad'an ya sakko k'asan, sai dariya suke,tun da ya fara sakkowa yake kallon jiddah tunanin inda tasan mai wnn face en yake amma ya kasa,hakan tasa kan dole ya hak'ura......
"Ina mamy?" Ya tambaya yana neman gurin zama, "tana d'akinta" little ta bashi amsa.......
Hanyan d'akin ya nufa,zaune ya same ta akan pray mat,tana lazimi,bayan sun gaisa,suna ta fira da shi yake tambayanta ina ta samu yara????
Kallonsa take cike da tuhuma kafin tabashi amsa da cewa "satosu mukayi", murmushi yayi kafin ya ci gaba da cewa ayi hak'uri mamy mamakin ganinsu nake nasan babu mai shigowa nan da dare,to wad'annan dai ba bak'i bane yau tsawon kwanaki 40 da wani abu suna gidannan sannan ka zomin da wannan maganar.........
Cike da mamakin abunda mamy ta dad'a ya kalleta bakinsa taf da tarin tambayoyi,gane hakan da tayi tasa ta d'aga masa hannu tare da fad'in "kaje ka sami daddynku shi zai iya maka bayani amma no bani da lokaci".............
*~Keep Following Fans~* 😍😍😍
*_SMASHER 🤞🏻😘_*
[19:57, 12/6/2017] Sister Hawwa: 💠💠 *RAYUWAR WANI......*
_{ơŋɛ'ʂ lıʄɛ...}_
💠💠
🌹
*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ...*
*ცყ.*
_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*WANNAN PAGE EN NAKI NE SAFIYA BALA (MOM HANAN) IINA MATUK'AR GODIYA DA SADAUKARWARKI GARENI,INA JI DAKE IRIN SOSAI ENNAN 😍😍...*
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)........*
*℘ąɠɛ 19↔20*
Murmushinsa mai kyau yayi tare da kwanciya saman bed enta, "am sowei mamynah,ban sansu bane,ko nace ban tab'a ganin suna", ya fad'a yana lumshe ido.......
"Taya zaka sansu tunda kun d'aura abota da zaman waje" mamy ta bashi answer.....
Wani murmushin ya sake yi lokacin da ya tashi da ga kwanciyan da yayi....
"Allah ya huci zuciyan mamynmu",ya fad'a yana ficewa daga d'akin......
Parlor ya koma ya nemi guri ya zauna yana danna phone ensa,hankalinsa rabi na kansu duk da hiran a gurin jiddah ba wai tana jin dad'in hakan bane,iya ka amsanta a duk tambayanta da little ta mata,amsanta d'aya ta kad'a mata kai......
Har wajen 9 suna zaune,shikam jabeer tunaninsa d'aya su wad'annan basu da mafad'i ne a gida da zasu kai wannan lokacin a gida mutane......
Ganin sun mik'e ya bisu da kallo a tunaninsa fita zasuyi amma sai yaga sab'anin haka,d'akin little yaga sun nufa,ganin hakan ya sa shi tsayawa da abunda yake,mamakinsa ya k'aru to sukam baza a nemesu a gidaba......
Fitowan mamy daga d'akinta ya shi dawo da hankalinsa kanta,yana son tambayanta amma babu hali,kan dole ya hak'ura ya zubawa sarautar Allah ido.....
Kusa da ikram ta nufa dake bacci kan sofa,kallonsa tayi had'e da fad'in "maza son kaimin daughter d'akinsu little tayi bacci", amsawa yayi da kai,ya mik'e ya nufeta,ganin haka mamy ta juya ta nufi komawa d'aki.........
'Daukanta yayi ya nufi d'akin little, shiganshi yayi dai² da lokaci da jiddah ta d'ago kanta idonta akan face NASA ya sauka, ko daga bacci ta ta shi bazata tab'a manta wannan face enba, ko da zuwa ace ta sha giyan wakene.......
Amma da Saudi ta maida kanta k'asa har ya shigo ya kwantar da ikram,ya juya zai fita,ya sake dawowa,kallonta yake yana son tuna inda yasan mai kama da ita amma ya kasa,dole ya hak'ura ya juya ya fice..........
Kwanciya tayi bayan ta ga fitansa,ko da little ta fito daga wanka,bata kula da wani sauyi da aka samuba,nightee enta tasa ta kwanta tana karanto addu'an kwanciya.......
Ganin tunanin bazai kai mata ba itama ta kwanta,tare da switching light en d'akin........
Da safe kam da wuri ya sakko parlor ya nemi guri ya zauna,ya jima a zaune a gurin amma baiga fitowan kowaba.....
Fitowan ikram tana tsalle kamar wata y'ar barewa,tana ganinsa ta nufi inda yake tana fad'in "yaya shannu,ina kwana", da fara'a ya amsa yana ruk'o hannunta,tare da tambayan "what's ur name?" Kallonsa take tana kallon bakinsa kamar mai son gane me yake nufi....
Amma ta kasa,saima gashinsa take k'ok'arin hargitsawa da ya sha gyara,sai gocewa yake ita kuma tana tsalle tana son kamawa sai dariya take tana dad'a tsalle, ganin ta kasa ya sa ta koma gefe tana kumbura baki ita nan a dole tayi fushi,dariya sosai yake yarinyar ta burgeshi, bai tab'a samun kansa da son yara ba sai a kanta,janyota yayi yana fad'in sorry baby,baki fad'amin sunankiba...........
Da d'oki ta CE "Ni Ikram addanah kuma Jiddah", aransa yake fad'in ba dai wannan yarinyar da ya ganiba jiyan take nufi.......
Tsaki yayi lokacin take ya kautar da tunanin a ransa,fitowan mamy yasa shi murmushin tare da fad'in barka da fitowan mamynmu,nan ya gaisheta,ita kuma ikram tayi tsalle ta nufi gurin mamy ta rik'e hannun mamy suka nufi kitchen........
Fitowan little tana dariya a guje,ta nufi parlor,d'agowa yayi yana kallonta da gudu Jiddah take binta a baya tana fad'in "dan Allah ki bani kallabina kinga banson zama babu d'ankwali,cikin siririyan muryanta take magana, shi kuma gogan yana zaune,yana kallon drama da suke,gashin ta ya sauka har kan chest enta,duk da k'arancin shekaru irin nata, yayi mamakin ganin gashi kamar haka a kan yarinyar kuma 'y'ar Africa,baiyi tunanin samun hakan ba a Africa.........
Da k'yar little ta bata ita kuma ta murgud'a mata baki ta nufi hanyan komawa d'aki,mutum ta gani zaune ya kafeta da ido,da saurin ta d'auke kai tana had'a hanya,da gudu ta k'arasa shigewa d'akin ta turo kofan da k'arfi......
Dariya suka saka mata gaba d'aya banda jabeer da ya tsaya kallon su,mik'ewa yayi ya nufi stairs tare da kiran little, ya juya ya shige........
*~Keep Following Fans...~* 😍😍😍
*_SMASHER 🤞🏻😘_*
[11:00, 12/7/2017] Sister Hawwa: 💠💠 *RAYUWAR WANI......*
_{ơŋɛ'ʂ lıʄɛ...}_
💠💠
🌹
*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ...*
*ცყ.*
_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*AHAYYYEEEE!! FANS KU TAYANI MURNA DA GODIYA ANMIN K'YAUTAR BABY,ALLAH RAYA MANA BABY HANAN,INA GODIYA SISINAH SAFIYA BALA DA K'YAUTAR DA KIKAMIN,ALLAH KARE HANAN DAGA SHARRIN MASU SHARRI...... ❤❤❤*
*Y'AY'ANAH SANYIN IDANIYATA KHADIJAH (KHAIRAT),MARYAM (KHAUSAR) WANNAN SHAFIN NAKU NE,KAUNARKU DA JININ JIKINAH TAKE YAWO,ALLAH YA ALBARKACI RAYUWAR KU............UR'S MOMMAH ALWAYS HEART U BABE'S..... 💔💔💔*
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)........*
*℘ąɠɛ 21↔22*
Guri ya nema ya zauna,in no time little ta shigo da sallama, ya amsa a k'asa d'an nesa da shi ta samu guri ta zauna,tana jiran me zai ce..........
Maganar sa ta katse mata tunanin da take, "ke wad'annan daga ina suke da naga sun kwana a gida nan?? Tambayar data fito daga bakinta kenan???
Kasancewar mamy ta kwab'eta da fad'uwa kowa su waye su yasa tace "nima ban san daga ina sukeba amma sai mamy tace familynta ne,sai sai ka tambayeta".........
Tunanin ya tsaya yi shi zai yasan da yawa daga cikin family na mamy amma bai tab'a ganin ko masu kama da suba, wata zuciyar ta bashi answer da cewa "ka Sani ko daga (RUGA) suke", wannan tunanin shi yafi tasiri a zuciyarsa,take ya kau da wancan,murmushi kad'ai yayi yace "OK u can go", tare da nuna mata hanya.........
Ficewa tayi tana murnan yau babu fad'a tsakaninsu,bare ya doketa,da tsallenta ta isa parlor inda tabar jiddah na jiranta......
Kowa ya hallara a dining inda ikram ta rage ita kusa da jabeer zata zauna, kan dole yasa little komawa kusa da jiddah, a haka sukayi break, amma ga Jiddah kam juya abincin kawai take da k'yar take iya d'aga spoon en tana kaiwa bakinta........
Babu wanda ya kula da ita,sai data mik'e tana shirin barin gurin,mamy tayi mata magana, "ina zaki baki ci abinci ba?",mamy na k'oshi,A'a ki dawo maza plate nake son gani ynzn........
Da k'yar take had'iyan abincin duk tana jinta babu dad'i.........
'Dagowa tayi ta kalli gurin da jabeer ke zaune ga mamaki ta bayama gurin,nan ta zage ta k'arasa cin abincin daman zamansa ne yasa ta kasa sakin jiki,saboda rashin Sabo.........
Haka suka dunga barin gurin d'aya da d'aya.........
Daddy ne yana shirin fita,yake cema mammy "d'azun ina son muyi magana amma na manta,kuma gashi d'anki ya fita"........
Cikin hanzari tace "a'a bai fita ba yana d'aki,bana jin yau zai fita da wuri".........
"Ok,fad'uwa yazo dai² da zama,maganan ne banson ya d'auki dogon lokaci ba a samu matsayaba,kafin na fita zamuyi maganar", ya fad'a yana ci gaba da saka babbar riga,...........
Amsawa tayi tare da taimaka masa ya k'arasa shiryawa,tare suka sakko daga saman,a parlor k'asa suka zauna,daddy ya tura little ta je ta kira yayansu..........
Kafin tayi yunk'urin tafiya har ikram ta rigata da d'an gudunta,mamy ce tace ta dawo,iya kuma ikram ta tura k'ofan ta shiga,a kwance ta Tatar da shi a kan sofa,idonsa rufe,sai da ta je dai² kunnesa tayi masa k'ara aciki,da Sauri ya bud'e eyes ensa yana kallonta yayi murmushi,beautiful point ensa ya lotsa,farare kuma jerarrun teeth ensa suka bayuana,Wanda wushirya ta ratsa ta tsakiyarsu,a nan na hango asalin kyaunsa,yakykyawane ajin farko,duk inda namiji isa yake jabeer yaje harma ya d'ara,farine tar,da yalwatattun idanuwansa,gashin kansa a kwance ya sha gyara,yana da k'irar da DUK wanda ya kalleshi zai ce tabbas akwai k'arfi a tartare da shi,idan ba wanda ya san Shiva,ko yayi magana,za kiyi tsammanin jinsin larabawane,amma ina abun ba haka yake ba,wannan Hausa/Fulani kenan,taro d'an zamani,wanda duk macen da zata d'ora idonta akan sa za tayi sha'awar kasancewar tare da shi..........
Sak'on da aka aikota ta fad'a masa tana dariya,mik'ewa yayi tare da rik'e hannunta suka nufi hanyan fita.......
A parlor suka Tarar dasu,Neman guri sukayi suka zauna........
Daddyne yayi gyaran murya yana fad'in "dalilin kiran da nasa akayi maka,ina so kaje ka duba skul mai kyau, ka yima k'annenka registration nan da sati,duk abunda ake ciki kasanar dani,na baka sati gida,bana son a d'auki dogon lokaci,sannan ka shirya daga nan zuwa k'arshen watannan in Allah ya kaimu za katafi k'aro karatu,sai ka zab'i in da kake ganin ya fi maka".......
Nan daddy ya sallamesu,shi kuma ya kama hanyar da zata sadashi da office........
Parlor ya rage daga jabeer sai su little, kiranta yayi "wato dan uwarki kin dena zuwa skul ko? Kina son daddy yayi ta asara akanki,ke duk term sai kin nemi a canja miki skul,sai kace an fad'a miki a bola yake d'ebo kud'in,saboda tsabar iskanci irin naki, kuma mamy ta samiki ido kin maida mutane yan iska,wllh ki mai da hankalinki jikinki,daga wannan babu chanji idan ba haka ba kuma sai sai kiyita zama a gida babu wata skul da za a sake miki", ya fad'a tare da Dakar mata rankwashi a ka,k'arasa ta sake,tana k'ok'arin tashi ya fisgota ya zaunar tare da zre mata many an idanunsa yana fad'in "kin min shiru ko sai na zaneki", da hanzarinta ta had'iye kukan,tana to she bakinta.........
Mamy ce ta dawo daga rama daddy ta kallesu,yanayin da ta gansu yasan ba k'alau ba,duk sunyi tsuru² kuma ta san ba haka ta fita ta barsuba,shiru tayi ta wuce kitchen,ganin tafiyanta yasa jabeer cewa "kuma kika kuskura kika fad'awa mamy wllh sai na lahira yafiki jin dad'i" tare da hararnta,b'acemin da gani sha³........
Da gudu tabar gabansa,lokacin ya d'ago ya kalli jiddah da kanta ke k'asa yana fad'in "saura ke duk ranan da kika sake ganina baku gaisheniba sai na kusa karya miki k'afar,kina kallona da wad'annan idanunsa naki masu kama da na mujiya..........
Dad'a sunkuyar da kan tayi,hawaye ya fara sakkowa daga idanun nata,ganin bashi da niyyar tashi yasa ta mik'e da nufin barin gurin,a kwance yake idanunsa rufe,sai da tazo dai² kusa da shi taji yace "gidan wace uwar zaki je?" A tsorace ta juya jikinta har rawa yake saboda tsoro,ta kasa bashi answer, "ba dake nakeba?, juyowa tayi tana kallonsa ga mamaki ta idansa still a rufe yake,ai ganin haka bata jira komaiba ta kwasa da gudu tayi d'aki tare da maida k'ofan harda saka key,tana maida numfashi......
Ransa yayi masifar b'aci,wane irin raini yarinyar nan tayi masa da har zai mata magana ta amsa shiru,k'arshema ta gudu,tabbas sai ya gyarawa yaran zama tukun hankali zai shiga jikinsu........
Shigowarta d'aki tana haki yasa little ta d'ago tana kallonta "ke kumafa daga ina?" Ta tambaya....
.
"Ke sai bari nida wannan ennan ne", ta fad'a tana zare ido kamar tana gabansa,dariya little taxa harda buga k'afa tana fad'in "yah jb en ne wannan ennan maza ya jiki ke da shi wllh".......
Tashi tayi ta bud'e k'ofan tana lek'awa........
*~Keef Following Fans..~* 😍😍😍
*_SMASHER 🤞🏻😘_*
[12:14, 12/8/2017] Sister Hawwa: 💠💠 *RAYUWAR WANI......*
_{ơŋɛ'ʂ lıʄɛ...}_
💠💠
🌹
*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ...*
*ცყ.*
_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*WANNAN SHAFIN NAKI NE KE KAD'AI BAN YARDA NA HA'AKI DA KOWABA....*
💞 *QUEEN H∆FSY*💞
*RE∆L SM∆SH£R,PRINCESS ESHAT AYSM & NA IKKE....MUNA NAN KUSA DAKE*
*ALLAH BAR K'AUNA,STARS ENKI SUNA TARE DA KE AKODA YAUSHE....💔*
*KUYI HAK'URI FANS JIYA UZURI YA RIK'ENI SHI YASA BAKUJIBA,AMMA IN SHA ALLAH ZAKUNA JINA AKAI²,A KO DA YAUSHE INA ALFAHARI DAKU.....KUNA RAINA,#IYA WUYA MUNA MUGUN MANNE DA JUNA...❤*
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)........*
*℘ąɠɛ 23↔24*
Mik'ewa yayi ya nufi stairs, ya zo daf da room en little yaji alaman ana bud'e k'ofan, kallonsa ya kai kan k'ofan, lokacin yayi dai² da lokacin da little take lek'e.......
Suna had'a ido tayi maza ta koma,tare da sake rufe k'ofan,a jiki ta jingina,date da k'irjinta,tana zare ido.......
Jiddah data tsorata lokacin da little ke bud'e k'ofan ta kwashe da dariya bar da rik'e ciki,matsowa little tayi tana fad'in maza wllh kici gaba idan kika shiga hannunsu yah JB za ki fad'a ne.......
Kiran da mamy take musu yasa kan dole suka fita daga d'akin,k'asa suka nufa kowacce sai sunkuyar da kai take,Neman guri sukayi suka zauna had lokacin sun kasa had'a ido da shi,duk abunda suke yana kula dasu,d'auke kai yayi kamar baiga abunda suke ba,mamy ta mik'e tana fad'in "zan shiga gidan can an musu haihuwa,yanzun zan dawo", Allah ya kiyaye hanya suka mata,ta kama hannunsu ikram suka fice,gidan ya rage daga jiddah, little sai yah JB,fuska ya had'e uwa bai tab'a dariya ba ya kallesu,jikinta su duk yayi sanyi,ko wacce kanta a k'asa, babu bakin magana.............
Kamar had'in baki suka d'ago jin bai musu maganaba,suna kallonsa,harara ya maka musu,kafin ya fara magana, "urban me kuke kallo munafukan banza", da sauri suka sake sadda Kansu k'asa.......
Little ce tayi k'arfin halin mik'ewa zata bar wajen,wani kallon da ya mako mata yasa ta shiga nutsuwarta batasan lokacin da ta zaunaba,.........
'D'auke kai yayi yace gaba da danna phone ensa,a haka har mamy ta dawo ta samesu parlor shiru kamar gidan makoki...........
Haka sukayi gaba da rayuwa idan yah JB na nan baka tab'a jin kiriniyarsu,amma da zaman ya fita shi kenan kuma sai abunda hali yayi.........
*★★★After Some Days.......★★★*
Rayuwar su suke cike da walwala,zuwa yanzun sun riga da sun zama y'an gida,babu abunda basu saniba,sai sai k'alilan kasancewar akwai saurin fuskanta abubuwa........
Zuwa lokacin daddy ya sashi ya nemo musu lesson teacher da yake zuwa gida yana koya musu,kasancewar basu tab'a zuwa makarantaba,sun d'auki lokaci kafin su samu su iya rubutu,ta b'angaren karatu kuwa,abun sai godiyar Allah, babu laifi idan yayi,sun ganewa,tun idan yanayin basa ganewa,sai idan sun koma little ta taimaka musu,sai gashi yanzun komai yazo da sauk'i,cikin lokacin da suka d'iba a gidan har sun zama y'an gari.......
Ta b'angaren addinima ba a barsu a bayaba,domin kuwa shima malami daddy yasa aka samo,ya fara koya musu huruf da yadda zasu iya had'a bak'ak'e ya basu jimla..............
Abun gwanin sha'awa,mamy kusan za ace tafi kowa murna da kasancewar yaran na d'aya daga cikin type en mutanen nan wato (GIFTED),da ka koya musu zasu gane,abun kam sai godiyar Allah............
JB ne tafe yana danna phone, tun kafin ya k'arasa shigowa,parlorn yayi tsit kamar basu ke hayaniyaba yanzun,kowacce ta kame kamar mutanen arzik'i......
Kallo d'aya ya musu ya d'auke kai,y'ar rige²n gaisheshi suka shiga yi,shi kuma yana wani basarwa,tunda ya dawo babu wacce ta sake yin abunda za a mata magana........
Lokacin da suka had'u a dining ne daddy yake masa tuni da maganar da sukayi kan makarantar su,saboda bata so a d'auki lokaci...........
Ai Daddy an ma samu,kuma an gama komai,dama ranar Monday sukace akaisu interview........
Mamy kam kusan za a iya cewa tafi kowa murna da faruwar haka,sai godiya take k'ama daddy,da haka suka kammala dinner kowa ya watse.......
*★★★Monday Morning...★★★*
Tun da asuba da suka tashi,sallah mamy bata bari sun komaba sai da ta tabbatar sun shirya,gudun makara,kuma yasan idan ta k'yalesu ba saurin shiryawa za suyiba,sai d'oki suke kowacce da abunda take fad'a a haka barin ya gama wayewa,kowa ta fito cikin uniform,a parlor suka fito,suka yi jugum suna jiran gogan nasu.........
7:30am sannan ya sauko yana tace yana maida botir en rigan jikinsa,tun kafin ya k'araso suka fara gaidashi,ikram ce ta tafi da gudu tayi hugging nasa,nan ya sake mata fuska sai surutu take masa shi kuma yana bite mata..........
Ba dan ya soba ya kyalesu sukayi break a tsaitsaye,sai harara yake aika musu,sukam babu wacce ta kula da abunda yake kawunansu a k'asa babu mai k'arfin halin d'agowa ta kalleshi........
Sun a gamawa kowacce ta nufi parlor nan suka d'auki bag ensure,suna ma mamy sallama,sai sun dawo,addu'ah ta musu na fatan alkhairi, kafin suka fice.......
Zaune suka same shi a motar yana kad'a k'afa,kallon juna sukayi ta gefe,kafin suka k'araso gurin.......
"Uban mene kuke jira,kun tsaya b'atamin lokaci,idan baza k'iba ku koma ku zauna kuna wani sunkuyar da kai kamar wasu munafukai", ya fad'a yana maka musu harara...........
Da sauri suka bud'e kowacce kanta a k'asa,fisgan motar yayi,suka d'auki hanya,sunyi shiru babu mai cewa komai,sai ikram dake kusa da shi tana zuba masa surutu,shi kuma yana ta bite mata.........
Su kam sunyi shiru Suna saurarensu,amma babu halin tofawa,da haka suka k'araso, fita yayi ikram ta fita,rik'e da hannunta,suka juya zasu tafi,juyowa yayi yaga basu fitoba,ransa a b'ace ya matso kusa da motar yana fad'in "wace uwar kuma kuke yi aciki,saboda rainin wayo sai kunsa nayi magana kenan,zaku iya fitowa?".......
Sum² suka fito daga ciki,juyawa yayi Suna binsa a bata,har office en PC,bayan sun gaisa,yake masa bayanin sune yaran da zai kawo,nan aka musu interview little kam sun kaita J.S.S 3 dama nan zata tafi kuma kasancewar tana yasan changing skul bai sata ta zama dak'ik'iyaba.........
Ita kuma jiddah sun nuns J.S.S 1 zasu kaita,nan ya nuna musu tafi son a barsu class d'aya,ita kuma ikram aka kaita primary 3......
"Dalilin kaita can shine,karatunta bai kai matakin da zata zauna secondary bagirmanta ne yasa mukayi hakan,amma primary shine level en da tafi da cewa da ita", fad'in PC kenan.......
Shi kuma Yah JB ya dage sai an barsu class d'aya da little, haka PC en ya hak'ura ba don ya soba,ya k'yalesu class d'aya amma da sharad'in nema masu lesson teacher, coz duk k'arshen shekara bayan exams suna, withdrawing d'alibai,wasu repeating, godiya yana PC en,sukayi sallama, sai da yaga wucewarsu class tukun ya juya,ya kama hanyan gida..........
Shigansu class en kallon ya dawo kansu,anga zuk'a² kuma kyawawan y'an mata masu tasowa.......
Kallon juna sukayi suka kalli y'an class en,nan suka zauna kusa da juna ba tare da sun kula kowaba......
Wata yarinya a class en ta kallesu ta watsar ita a dole bata ga abun kallo a tare da suba,su kam ko sanin tanayi basuyiba,suna zaune aka suka zauna har suka tashi daga skul en.........
Fitowa sukayi nan suka fara Neman ikram,can k'ark'ashin lilo suka hangota,tana zaune a k'asa ta baje lunch box enta,bag enta a gefe,kallonta sukayi suka tuntsire da dariya,suna had'a baki gurin fad'in "ikram y'an makaranta", d'agowa tayi ta kallesu tana washe baki,an kiranta da abunda take k'auna.........
Da k'yar suka rabata da gurin suka nufi gate,a nan suka tarar da malam shehu yazo d'aukansu,da murnarsu suka k'arasa dan su kam idan tasu ne kada yah JB ya k'ara kawo su,dan motan koma musu take kamar mak'abarta.......
Sun cika motan da surutu,a raina nace da yah JB ke driving babu mai magan a cikin su,gani za kayi sun koma mutanen arziki........
Haka suka ci gaba da zuwa skul,kullum malam shehu ke kaisu makarantamakaranta,har tsawon kwana uku.......
Babu wata matsala da suke fuskanta,ta b'angaren karatunsu,a ranar ne suna zaune Sai ga wata new student ta shigo class en,Sai da ta tsaya ta k'arewa y'an class en kallo,kowa da abunda yake..........
Wasu matasan y'an mata ta gani su biyu zaune suna fira Sai suke suna dariya........
Kusa da su ta matsa tayi musu sallama,kallonta kawai suka tsaya yi,tayi murmushi tare da fad'in "zan iya zama?".........
Murmushin sums sukayi mata ta zauna,tare da cewa "suna na HABIBA IDRESS zaku iya kirana da (hubbeey),nd u guysss?"...........
Little ce tace "am AMINA MUHAMMAD (little), y'ar uwata kuma HAWWA MUHAMMAD {Jiddah}".........
"Ohhhh! Yeahh nice to meet u guysss, can we be friends??" Ta tambaya......
"No p",little ta bata amsa,ita kam jiddah murmushi kad'ai tayi,suka bata guri ta zauna,haka suka dinga firansu ranar har aka tashi,Sai da suka fito gate sannan sukayi sallama akan Sai gobe, kowacce ta nufi motansu,suna waving wa juna,da exchanging smile..........
Da murna suka k'araso gida,nan suka tarar da mamy zaune,ita d'aya tana watching TV.suna gaida ita ko uniform basu cire ba aka hay bata labarin new friend da suka had'u yau,sun cika parlor da surutu,sunata hayaniya...............
Hangoshi little tayi ya shigo parlor sum² ta mik'e ta wuce ta bar gurin ganin batayi magana ba yasa jiddah mik'ewa ita da ko ganinsa ma batayiba,ta wuce tana shiga d'akin ta tarar da little Sai tuntsira dariya take,still tayi tana kallonta kafin ta ce "lafiyarki k'alau kuwa kike dariya kamar kwancen mahaukata?"..........
Sai da tayi mai isarta tukun ta tsagaita tana fad'in "yah JB Nagano yaseen shi yasa banyi magana ba na baroku", wato mugunta kika so had'awa kenan,Allah yasa ta koma kanji, "ba aminba", little ta fad'a tana murgud'a baki............
*~Keep Following Fans....~* 😍😍😍
*_SMASHER 🤞🏻😘_*
[20:51, 12/8/2017] Sister Hawwa: 💠💠 *RAYUWAR WANI......*
_{ơŋɛ'ʂ lıʄɛ...}_
💠💠
🌹
*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ...*
*ცყ.*
_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*THIS CHAPPY IS UR'S GUYSSSSS,RAYUWAR WANI FAN'S... ALLAH BARMINKU A DUK INDA KUKE....😘😘😘*
💠💠 *RAYUWAR WANI FAN'S CLUB....* 🌹
*_OMG!! YAU KAM KUN SANI NISHA'DI,MATUK'A KUN BANI DARIYA,IRIN IMAGINING HAKA,AMMA DAI KOME NEMA ZAI FARU GABA,KU CI GABA DA BIYONI DAN SAMUN AMSARKU..........#REALLY HEART U GUYSSSSS..😍_*
*HUH!! DUNIYA BUDURWAR WAWA,WAI ME YASA WASU MUTANEN SUKE HAKA NE? ITA DAI RAYUWAR NAN GUDA 'DAYA CE,DAGA NAN SAI CAN,MU GYARA HALINMU KO MASU MU RABAUTA.......ALLAH MANA KYAKYKYAWAN K'ARSHE...👵🏻*
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)........*
*℘ąɠɛ 25↔26*
"Ita dai mugunta ba abun so bane ko mutum ya dena,ko ta koma kansa",jiddah ta fad'a tana hararar little da ta sake tuntsirewa da dariya........
"Allah ya had'oki da yah JB yayimaganinki", jiddah ta fad'a tana shiga toilet lokacin da ta gama cire uniform........
Ko da ta fito daga wanka ko kallon in da little take batayiba,har ta gama shirinta,ganin tana neman guri zata kwanta,yasa jiddan juyawa tana kallonta bakinta bud'e, kafin ta fara magana "haba malama kin san dai lokacin islamiyyah ya kusa kin zo kina neman kwanciya,kima tashi mu wuce"..........
Bazaniba,a fusace jiddah ta juya ta sake kallonta,Ashe yah JB zai ji labarin nan yanzun,ta nufi banya zata fita,Allah bada sa'a dai kin dawo,kamar wacce za ta iya zuwa,ke da ko kallonsa bakya iya yi,shi ne yau har da kai k'ara,Allah taimaka,ta sake fashewa da dariya,tana nunata da hannu........
Haushin dariyan da take mata yasa ta ficewa daga d'akin ta nufi parlor k'asa, mamy ta gani zaune,ta nemi guri ta zauna ba tare da tace komaiba........
Ganin tana kumbura fuska mamy ta kalleta tana fad'in "me ya fara kuma kike fushi?".......
Mamy little ce na ce mata ta shirya mu tafi islamiyyah shi ne wai baza tajeba.......
Jabeer da yake k'ok'arin sakkowa daga stairs ya kalleta jin abundant take fad'a, fuska ya Dada tamkewa tare da cewa "ina little en take?", tambayar tazo mata a bazata dan ba tai tsammaninma yana gidanba,da bazata fad'a ba.........
Tsawan da ya nufa mata yasa ta dawowa daga tunanin da ta tafi.......
"Tana sama", ta bashi answer a tak'aice......
Juyawa yayi ya koma saman,dai² bakin d'akin, nocking ya shiga yi..........
Gama shirin ta kenan cikin uniform ta nufi k'ofan,bud'ewa tayi a tunanintama jiddah ce,amma wa zata gani,jikinta ya hau b'ari ganin irin kallon da yake mata,yasa ta sha jinin jikinta.............
"Me yasa da kikace Bazaniba?".......
Inda² ta fara alaman rashin gaskiya,rank'washinta yayi aka,nan ta dafe gurin,tana bashi hak'uri.........
Wuce ki bani guri kafin nayi k'wallo dake,Allah yasa na sake jin ko a labarin kin ce Bazaniba,ko da zuwa da wasane sha³,sum² ta wuce tabar gurin,abun tausayi haka ta sakko kamar kazar da k'wai ya fashewa a ciki,tafiya suke babu mai cewa kowa komaiba a haka har suka aisa makarantar...........
Har suka tashi daga makarantar bata kula taba,duk yadda taso rarrashinta amma tak'i sakin jiki,k'yaleta tayi itama,ganin ta shiga damuwa yasa little en sakkowa,kafin su koma gida suka shirya,nan jiddah ke bata yadda abun ya faru...........
"Uhmmmm dad'inta d'aya gobe dai zamu rabu da k'aya mu huta", fad'in jiddah kenan........
Jiddah kam bata ji dad'in abunda little taf fad'a ba,ko da idan yana gidan basa wani sakewa,amma hakan bai daceba,k'yaleta itama tayi,duk surutun da take mata babu amsa,ganin haka yasa ta kan dole yin shiru,dan bata san ainihin abunda yasa ta yin shirunba lokaci guda...........
Har suka k'arasa babu wanda ya sake cewa uffan........
*★★Some Days Left...★★★*
Kamar yau aka saka ranar tafiyar yah JB gashi har ta zo,duk murnan da little take da tafiyar,ganin da gaske zai tafi said kuma jikinta yayi sanyi,duk ji take babu dad'i..........
Ko kitchen da suka shiga suna tsaya mamy aiki tunda flight en dare zasu bi,duk jikinsu babu laka,haka har suka gama suka dawo parlor, duk sun gallara a parlor, daddy yayi masa nasiha,kan kiyaye kansa daga yawan mu'amala da turawa,sannan rik'ota da addini,duk da yasan ba mai yin hakan bane,ya masa fatan alkhairi.........
Mamy ya kalla,gane abundant yake nufi,itama tayi masa nasiha mai shiga zuciya...........
Daga nan ya fito,yana kallonsu kamar kar ya barsu haka yake ji.........
Ban da kika babu abunda ikram keyi,iyayen fitsara kuwa har da hawaye,har ya juya zai shiga mota,ya fasa, ya musu alama da su zo........
Da gudu ikram ta isa inda yake ta rik'e shi,tana gunjin kuka..........
Motar ya mata suka k'arasa suka shiga front seat,jiddah da little suka zauna baya,suna d'auke kwallan da ke sakko musu........
Har suka k'arasa airport, babu mai magana,malam shehu na yin parking ya fita,bayansa suka bi suna rab'ewa gefe.......
Kusa dasu ya k'araso fuskansa d'auke da tsadadden murmushinsa nan,d'an fad'a yayi musu,su kuma said mamakin sauyawar halinsa suke a yau,ko dan zai tafi ne yasa ya chanja hali,suke riyawa a ransu,yana gamawa ya juya da niyyar barin gurin,kome ya tuna kuma ya dad'a dawowa,jawosu yayi ya basu hug,kafin ya sake su ya juya da Sauri ganin yadda suka dad's kecewa da kuka...........
*~Keep Following Fans...~* 😍😍😍
*_SMASHER 🤞🏻😘_*
[20:48, 12/9/2017] Sister Hawwa: 💠💠 *RAYUWAR WANI......*
_{ơŋɛ'ʂ lıʄɛ...}_
💠💠
🌹
*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ...*
*ცყ.*
_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*DAN ALLAH FAN'S KUYIMIN UZURI NA RASHIN JINA DA BAKUYIBA,HAKAN YA FARU NE,SAKAMAKON NAYI TYPING TWICE YANA GOGEWA,WALLAHI DUK RAINA BABU DA'DI,SABODA HAUSHI KA'DAN YA RAGE BANYI KUKABA 😩,AMMA KUYI HAK'URI DA WANNAN, #IYA WUYA MUNA MANNE DA JUNA,IRIN K'AK'AM ENNAN.......* 🤝🤝🤝
*WANNAN PAGE BA WA KOWA NA SADAUKAR DA SHIBA SAI GAREKU.....*
*HALIMA SAHAD...*
*TEEMAH CUTE 👌🏻*
*MAMAN BOY 💐*
*GASKIYA INA MATUK'AR GODIYA DA SOYAYYAR DA KUKEMIN,INA ALFAHARI DA KU...* 😘😘😘
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)........*
*℘ąɠɛ 27↔28*
Bai sake koda waiwayowaba har ya shige cikin airport,zuciyarsa duk babu dad'i,rana d'aya ya rabu da kowa nasa, haka ya shige, tun suna ganinsa har ya b'ace musu........
Suna tsaye,sai da suka gaji dan kansu, sannan,suka juya suka shige mota malam shehu yaja suka bar gurin,fuskokinsu duk d'auke da damuwa......
Haka suka koma gida,babu mai cikakkiyar walwala,k'arshe ma sama suka haura suka kyale mamy da y'ar rigimarta,duk sun bata tausayi.........
Tunda aka gama checking kayansu,an kammala duk abunda za ayi musu,kowa na zaune cikin jirgi,har zuwa tashinsu suka yiwa sararin samaniya tsinke,kwantar da kansa yayi jikin kujera,idonsa ya lumshe,yana karanto addu'ar tafiya,har zuwa lokacin da suka dai²ta a sama,tafiya ta mik'a............
Yayi da ya tsinci kansa cikin tunanin da alhinin barin gida.........
*★★★SAFE JOURNEY YAH JB...★★★*✈✈✈
Tun bayan tafiyarsa da kwana biyu,suka koma dai², kowacce ta sake k'afa,har da mik'ewa,k'iriniya ta dad'u babu wanda zai kwab'esu,sun dai san ya tafi amma babu halin hanasu k'iriniya yanzun kam........
Ko makarantar yanzun an sallama musu,duk wani rashin ji sune kan gaba,basa tab'a d'aukan raini,ko cikin cliques ensu da yawa tsoronsu suke........
Duk wanda zai yi maganarsu sai dai yayi a bayan idonsu,idan kuwa suka san kayi,har inda kake za suje,su maka rashin mutunci,idan baka fi k'arfin suba, su maka duka,babu yanda za kayi,shi yasa da an gansu za kaga ana kallonsu,wasu kuma su sunkuyar da kai k'asa,amma babu halin magana........
Ko a cikin seniors basa tab'a d'aga musu k'afa,wannan dalilin yasa PC zab'ansu a matsayin mataimaka daga cikin student leaders.........
Samun matsayin nasu sai ya zama kamar k'ari ne suka samu na ci gaba da duk wata fitina da suke yi.........
Idan kafi k'arfinsu su maka rashin kunya amma baka isa ka tab'a suba,dan zasu had'u ne su k'waci Kansu.........
Lokacin da labarin fitowar sunansu a duty ya riski d'alibai sun tausayawa Kansu matuk'ar,dan sun san no more leg up,ko ya kuke dasu kuwa,sai dai idan an had'u a class a jone.......
Duk ranar dutynsu kuwa jikin d'alibai har rawa yake,kar su makara,su Kansu seniors en sai dai su koma baya,ranar su zasu ja ragamar duty.........
Saukarsu a kasar ta *CHINA* ya ja luggages en sa,sai da ya fito daga airport en,yana zuwa ya samu cab,direct sai *FENGLIN CAMPUS (Medical center of FUDAN UNIVERSITY) XUHUI DISTRICT SHANGHAI..* Tunda ya shigo skul en za a iya cewa ya shigo da k'afar dama duk wani abu da za ayi yana d'aya daga cikin wad'anda suke gaba,baya tab'a sakaci da duk wani abu da ya shafi addininsa,hakama ta b'angaren karatunsa,sosai ya mai da hankali........
Lokaci² sukanyi waya da y'an gida,idan bashida abunyi ko ya tashi daga skul,ba wani tym yake d'aukaba,zai ci gaba da karatu........
Lokacinsa gaba d'aya ya zama na karatu,ko cikin skul da ya gama abunda zaiyi yake ficewa ya nufi hostel,haka rayuwarsa taci gaba da kasancewa tsawon wani lokaci,ba tare da ya yarda wata mu'amala ta had'ashi da chinisawanba,idan sun had'u class za a gaisa,bayan nan kuma babu fuska........
Tun daga lokacin da suka had'u da hubbey basa tab'a rabuwa,ko da a cikin holidays, sun ta zuwa gidajen juna kenan,ya zamana yanzun gidajen biyu duk sun Saba da juna,har aminta mai k'arfin ta k'ullu tsakaninsu...........
*★★★ AFTER 4 YEAR'S...★★★*
Da gudu suka fito daga cikin motar,d'aya na bin d'aya,ta bayan ce take fad'in "dan Allah sisi kiyi hak'uri karki fad'awa mamy......
Ta gabance ta juya ta kalli wacce ke binta abaya tana fad'in "su little an iya ban hak'uri", ta juya tana kyalkyala dariya........
Kema dai sis wallahi kinsan zan sha fad'a ne,kuma kinsan dai idan Boss yaji ba ware ni zaiba,har kema kin Shiga cikin fad'an nasa.......
Mai makon ta tsaya saima juyowa da tayi ta kalleta had'e da yin dariyar mugunta,ta juya ta ci gaba da gudun......
Sai da taje bakin parlor sannan ta tsaya kamar wacce aka danna ma pause.....
Juyowa tayi tana ci gaba da dariya,ganin yadda little ke haki kan gudun da tayi.......
"Amma wallahi kin bani wahala", Cewar little tana rik'e k'afarta,lokacin da ta sha gaban jiddah.....
Yo dole aka miki??? Ban hanya ni na wuce,dad'a tare ta little tayi,tana bata hak'uri.......
Dariyar rainin wayo tayi kafin ta ce "idan kina son nayi shiru ki kawo eating noise sai na rufa miki asiri"........
Ai dama halinki kenan,ki ce akawo cin hanci,bayan kinsan haramne.........
Dariya tayi mai isarta kafin ta had'e fuska tana fad'in "zaki bayar ko kuwa in wuce?", A'a zan bayar ya zanyi?..........
"Da yadda za kiyi,sai ki hana,ni kuma na miki aika²",ta fad'a teethingly...........
Muje dai ai abun naki baya wuce chocolate ko ice cream, idan mun fita anjima ma siya,suka k'arasa..........
As usual mamy na zaune parlor,da sallama suka shigo........
Mamy dake zaune ta kallesu,tana fad'in "da wace gulmar kuka tsaya,a bakin parlor?", da Sauri little ta kallo jiddah dake zaune, ita kam ta kasa zama,saboda rashin gaskiya,tana mata alama da karta fad'a,tana had'e hannayenta alamar rok'o.......
Mik'ewa jiddan tayi ta nufi hanyan stairs tana k'unshe baki,sai da ta tabbatar ta juya baya,sannan ta ce "babu komai mamy", sai lokacin hankalin little ya kwanta,har tana sauke ajiyan zuciya,bayanta itama tabi zuwa d'aki.......
Tana shiga ta rungumeta,tana fad'in " day's my sisi,I love u dear",ta fad'a........
Turata jiddah tayi,ke ni da Allah k'yaleni kin iya dad'in baki,ya maganar alk'awarina?,Haba mana ina sane ai, "A'a kar dai nice kin manta,dan ni ba mantawa zanba", ta fad'a tana d'aura towel ta nufi toilet.........
Da yamma bayan sun gama shiryawa suka sakko k'asan,sun d'auki ado,komai nasu iri d'aya suka saka,sai color da ya bambanta......
Tun kafin su k'arasa sakkowa mamy ke musu kirari,su kuma an fasa musu kai,har tafiya suka chanja,su adole ga manyan mata,haka suka yiwa mamy sallama,suna niyyar fita........
Ikram da ke kwance ta d'ora kanta akan lcinyan mamy ta juya tana kallon mamy tare da cewa "mamy dan Allah nice su tafi da ni", fuskanta kamar za tayi kika.....
Sosai ta k'ara girma,duk ta chanja ta zama wata y'ar budurwa,yanzun tana cikin shekaru 13 yayinda su little ke 17,ana final year a secondary.........
Kiyi hak'uri karki damu kinji baby za muje tare,kinsan ko cewa kikayi zaki ba zasu tab'a bari KI bisuba,ma je daga baya........
"To",kad'ai tace ta maida kanta ta kwantar......
Su kuma suka fice daga parlor,suna mata tsiya........
Ku gaida hajiyan idan kunje,kuma kada kuyi dare,a dawo da wuri........
Amsawa sukayi suka fice,malam shehu ya jasu sai unguwan (RED BLOCKS).......
Tun shigarsu gidan bayan sun gaisa da mama,suka nufi d'akinta,kwance suka tarar da ita tayi d'ai² kan bed,ta sake hanci tana shak'ar iska,duka little ta kai mata a cinya,a firgice ta tashi tana mitsitsika ido........
Wannan ma ai iskanci ne,ya mukayi da ke a skul zaki wani zo ki kwanta bayan kinsan zamu zo,yanzun sai mun tsaya jiranki kin shirya...........
Yaushe muka je har muka tafi gida,kuma mamy ta ce kar muyi darefa......
Sorry sistos yanzun zan gama mu wuce,tayi hanyan toilet.........
*~Keef Following Fans...~* 😍😍😍
*_SMASHER 🤞🏻😘_*
[19:23, 12/10/2017] Sister Hawwa: 💠💠 *RAYUWAR WANI......*
_{ơŋɛ'ʂ lıʄɛ...}_
💠💠
🌹
*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ...*
*ცყ.*
_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
💛💙💜❤🖤💚
*K'AWARTA CE SANADI...*
❤🖤💙💚💜💛
*GAREKI Y'AR UWA ZUWAIRAT (UMMU MARYAM)*
*_INA MIKI FATA DA ADDU'AR KARIYA DAGA UBANGIJI,KI 'DAUKI WANNAN ABUN DA YA FARU A MATSAYIN BA KOMAIBA,ALAMAR NASARA CE SAMUN MAK'IYA,SUYI SU GAMA,BA ZASU SAMU NASARABA DA IZININ MAI DUKA,MUNA FATAN UBANGIJI YA KAREMU DA KARIYARSA,ADUK INDA MUKA TSINCI KAWUNANMU...._*👏🏻👏🏻👏🏻
*STAY BLESSED SISI,MORE GRACE TO UR SHINING ELBOW* 💪🏻
*A KULLUM KUMA A KO INA MUNA TARE,ALLAH KAREMU SHARRIN MAK'IYA MAHASSADA....* ❤❤❤
*KUYIMIN HAK'URI TARE DA UZURI FAN'S, WANNANMA KAWAI NAYI NE,AMMA BANA CIKIN MOOD EN DA ZAN IYA MUKU DOGON TYPING, SHI YASA MA YAU KUKA JINI SHIRU,AMMA KUYI HAK'URI DA WANNAN, INA MATUK'AR K'AUNARKU KAMAR YADDA KUKE K'AUNATA........#HEART U GUYSSSSS....* 💔
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)........*
*℘ąɠɛ 29↔30*
*★★★ CHINA...★★★*
Tun lokacin da ya tafi,ko sau d'aya bai tab'a zuwa,da sunan hutuba har tsawon shekaru 4,duk lokacin da yace zai zo daddy ke hanashi zuwa,har ya kai tsawon wad'annan shekarun.........
Zaune yake,duk kewan familynsa sun isheshi........
Mik'ewa yayi,ya hau had'a kayansa,yana gamawa ya ja luggage ensa,bai zarce ko Ina ba sai airport........
Yana zaune har aka kammala duk wani abu da za ayi,kowa ya shigo,jirgi,daga nan suka d'aga sai gida Nigeria........
*★★★NIGERIA...★★★*
Tunda ta shiga toilet bata d'auki lokaci mai tsayiba ta gama duk wani shirin da za tayi,ficewa suka yi,suka yiwa mama sallama,da cewar sai sun dawo,addu'ah tayi musu,suka fice daga gidan.......
Cikin 212 suka nufa side en Ice,waje suka samu suka zauna,kafin suyi abunda ya kawo su.......
Zaune suke sai firansu suke cikin nishad'i,rayuwarsu babu takura,Suns ta labarin tsiyar da suke a skul,tun daga lokacin da aka basu muk'ami har zuwa yanzun da suke sunema shugabannin d'alibai........
Hubbey ke rik'e da Head student, jiddah assistant, sai little da ke labor, masifa ta dad'u,ynzn kam babu wanda ake shayin a tab'a irinsu kaf skul en,tsiwa kuwa ba a magana,komai girmanka ka tab'asu yanzun za su maka rashin kunya,idan har ka sake ka Shiga 18 ensu.........
Suna ta faman dariya,wani guy ya taho shi bai yarda guy d'an zamani,ya tunkaro table en da suke zaune,maimakon sallama,sai cewa yayi "hey!".........
Wani mugun kallo suka masa,suka ci gaba da abundant suke,maganar duniya sunk'i kulashi,k'arshema guri ya samu ya zauna amma sunk'i bi ta kansa..........
Samarin gurin da abundant ya faru a gabansu me za suyi banda dariya,wasu kam harda ihuuu.........
Haka da ya gaji da zama ya mik'e guiwa a sace,yayin da wasu suka rakashi da dariya...........
Bai sake tsayawa cikin gurin ba ya fice gaba d'aya..........
Su kam sai da suka gama shak'iyancin su sannan suka kama haryar gida,sai firan tsiyar da suka yiwa guy en suke suna dariya............
A airport flight en su na sauka,yana sakkowa tun daga steps en da ya fara sa k'afarsa,ya shak'i iska,ya lumshe eyes ensa,rabonsa da k'asarsa tsawon shekaru 4 kenan,duk wannan tsawon lokacin,yana zaune shi d'aya ba tare da saka kowa nashi a idonsaba,yasan wannan lokacinma da ya fad'awa daddy zai zo hanashi zaiyi,fara ma da yak'i fad'a, sa ganshi kawai,yana son basu surprise yau kam.........
Fitowansa bai zarce ko Ina ba sai gida,banyan ya d'auki shatan tricycle, dai unguwan NNDC quarters...........
Kallon ko ina yake na anguwan nasu,kamar anyi changing, shekaru babu wuya.........
Yana wannan tunanin suka k'araso k'ofan gidan,sallaman mai tricycle en yayi,shi kuma ya ja luggage ensa,sai cikin gidan...........
Da sallama ya shiga gidan,suka gaisa da malam sani, yana masa barka da dawowa,yana k'ok'arin ansa masa luggage en,ya ce ya bar shi,zai k'arasa da kansa,ya masa godiya,ya nufi kofan parlor.........
Babu kowa cikin parlor,yayi sallama,jin ba a amsaba ya shige kai tsaye,sallaman ya sake yi,dai² lokacin da ikram take sakkowa daga staircase.......
K'ara ta fasa,da gudu ta kwasa,sai da tazo gabansa,ta saka tsalle ta d'ane shi......
K'aran da tayi ya janyo hankalin mamy,ya fito hankalinta a tashe,turus ta tsaya ganin abun da batayi zatoba,rik'e da baki,tana kallonsa da mamakin ganin nasa a lokacin da batayi zatoba.....
"Sai ku k'araso ai ku zauna,kun tsaya a nan", ta fad'a da murmushi a fuskarta......
K'arasowa sukayi suka zauna ikram ta mak'ale masa,sai washe baki take,tana ta zubo masa surutu,ko barinsa ya nufa ta gagara...........
A NNDC k'ofan gida suka sauka,ita kuma hubbey malam shehu ya tafi mayar da ita gida........
A dai² k'ofar parlor suka dakata jin maganar namiji a parlor, kuma sun San wannan dai bana daddy bane,to ways? Suka kalli juna,da sauri kuma suka shige parlor da sallama,akan face en sa idanunsu suka sauka,little ce tayi k'ara,ta kwaso a guje ta nufi shi,sai da tazo daf da shi ya dakatar da ita,ta hanyar fad'in "ke bani da hankaline? Ko kuwa bakisan kin girmaba?......
Cak ta tsaya a gabansa,cikin jin haushin kanta da abunda yayi mata,ta juya zata bar gurin.......
Tsawan da ya buga mata,yasa ta juyowa cikin sauri.........
Fuskansa a had'e uwa ba yanzun yake dariyaba........
Take tsoro ya shigeta,jikinta har kyarma yake,kamar ta ganta a lion's cage,zubewa tayi a k'asa,k'afa tank'washe kamar mai Neman gafara......
Ganin abun da ya faru, jiddahdake tsaye ta k'araso gurin,shi kam ko kula da ita baiba,little kad'ai ya iya gani,har ta samu guri ta zauna......
Muryanta ya tsinta a sama cikin melodious voice enta take fad'in "yah sannu da dawowa,an dawo lafiya?".......
Juyowa yayi yana kallonsa inda sound en ya fito,ga mamakinsa,jiddah ya ganin zaune,ga wani uban smile a kan face enta........
Hakan ya tabbatar masa da ita tayi maganar.....
Had'e face ya sake yi,tare da amsawa, "daga gidan wace uwar kike da yamman nan?", ya fad'a.........
Inda² little ta Shiga yi,wata tsawan ya sake buga musu,yana mai²ta musu tambayan.........
Cikin k'arfin hali,jiddah ta bashi answer, amma k'irjinta banda dukan 100² babu abundant yake yi......
Wani kallo ya watsa musu,tare da cewa "Allah ya baku iko,ku ci gaba karki fasa,k'afafuwanku kullum a waje kamar wasu shanshani,idan na k'ara k'afar kwa samu guri ku zauna"...........
Tsaki yayi ya Mik'e ya nufi d'akinsa don ya huta........
Ganin ya bar wajen,yasa little sassauta voice enta yanda ikram zata ji tace "hey! Baby yaushe boss ya dawo?"......
Itama cikin rad'a take fad'in "bai jimaba"........
Kallonsu kad'ai jiddah tayi,ta mik'e ta nufi sama itama,d'aki ta shiga ta kwanta a zaman bed,idonta ta rufe kamar mai tunanin wani abu..........
*~Keep Following Fan's..... ~* 😍😍😍
*_SMASHER 🤞🏻😘_*
[11:00, 12/11/2017] Sister Hawwa: 💠💠 *RAYUWAR WANI......*
_{ơŋɛ'ʂ lıʄɛ...}_
💠💠
🌹
*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ...*
*ცყ.*
_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*INA KUKE ONLINE WRITER'S 🔎, ARADU WANNAN PAGE NA MALLAKA MUSHI KYAUTA,SABODA K'AUNAR DA NAKE MUKU,BAN RAGE KO GUDA DAGA CIKINKUBA,INA ADDU'AH DA FATAN UBANGIJI YA HA'DA KANMU,BAKI 'DAYA......🌏 FATAN ALKHAIRI GAREKU Y'AN UWANAH MARUBUTA....* 📝📚
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)........*
*℘ąɠɛ 31↔32*
Boss kam yana shiga,toilet ya nufa,banyan yayi wanka,ya zura kayan shan iska,ko ta kan abinci baiba,yabi lafiyar gado cike da mafarkai iri² masu dad'i.........
Ganin an barsu su biyun mamy na kitchen,itama little ta bi bayan jiddah da ta tsufa a sama......
Kwance ta tarar da ita, ido rufe kamar mai bacci,magana tayi taji shiru,ganin hakan yasan ba bacci takeba,tab'ata tayi,nanma bata kulataba,sai ido data bud'e tana kallonta,tare da d'aya gira d'aya...........
"Ke yanzu ya zamuyi Boss ya dawo,kinga muna tsaka mai wuya,ga wani uban warning da ya ajiye mana,dole mu shiga hankalinmu,idan ba hakaba,zai mana babu dad'i", little ta fad'a face enta da alamun damuwa............
Banza jiddah tayi mata,sai ma idonta da sake kullewa kamar mai jin bacci.......
"Ke wallahi matsalace da ke,idan wannan banzan miskilancin naki ya motsa,uban kowama yi masa kike", cikin jin haushi little tayi maganar,ganin tak'i kulata yasa ta mik'e ta bar gurin zuciyanta fal haushin iskancin jiddah.......
Kome ta tuna,tana kwancen tayi saurin mik'e wa, har sai da little en ta kalleta,amma ko a jikinta haka ta mik'e ta fice daga d'akin,sauka tayi ta nufi kitchen, mamy ce ita da baba Laure suna aikin had'a dinner,shigowa tayi tana taimakawa har suka kammala...........
Dai² lokacin ana kiran Maghreb Boss ya sakko daga da niyyan tafiya Masjeed,zaune ya samu little a parlor ta kafawa TV.ido tana kallon drama,kallonta kad'ai yayi lokacin da yake k'arasa sakkowa.........
Fitowanta kenan daga kitchen d'auke da Warmer's, ta nufi dining area,ajiyewa ta shiga yi,kamar kullum.........
Kallonsa ya kai kan little,zaune take tana watching drama,a hankali cikin takunsa ya iso gabanta,duk hankalinta na kan abunda take,kunnenta ya kama ya ja.......
"Autch!!! Ta fad'a tana dafe gurin,tana bashi hak'uri,amma yak'i sake mata kunnen,saima murd'ewa da yayi,kamar ya samu kayan wanki............
Mamy da fitowanta daga kitchen zata je yin sallah ta gansu a haka,kai ta jijjiga,tana fad'in "me yene haka kam,kai babu daman ku zauna lafiya,sai kace wasu Tom n Jerry,sake mata kunnen da kake murd'awa,kar ya fice,koma ina masallaci zaka ka tsaya nan sai an idar da sallan", tana had'e face...........
Sakin mata kunnen yayi,had'e da sakar mata wani mugun nock a tsakiyan kai,dafe gurin tayi,ta sake sakin wani k'aran.........
Sunkuyawa yayi yana fad'in "ko ki rufemin bani ko yanzun na karyaki,dan uwarki kina zaune a nan,kin barsu da aiki ga bayinki,dole su gama su baki kici ba?.........
Allah ya bakin sa'a in sake ganin ki a nan kina zaune su suba aiki kiga yanda zanyi dake,Allah saina mugun sab'a miki,ko tunanin sallah bakiyiba bare taimaka musu,kinzo kin hard'e k'afafu,ke ga hakima koh,me yasa y'ar uwarki ita bata zo ta zaunaba,saboda bats son ta hutane ko kuwa? To Allah bakinta sa'a na dawo na tarar dake a nan a zaune,kiga yanda zanyi k'wallo da ke,sha³"...............
Yana gama bambamin fad'an nasa yayi hanyan fita jin an tada sallan,ya k'ara sauri,haushi duk ya ci ka shi,da bai biyewa shashancin wannan yarinyarba da bai makaraba,haka ya k'arasa masjeed en...........
Jiddah dake cikin kitchen ta fito tana dariyar mugunta,harda zama saboda d'aci da taji,tana Allah k'ara wa little, hawayen dake sakkowa daga idonta,suka k'ara k'aimi wajen zubowa,tana fad'in "Allah sai ya sakamin,mutu ba abunda aka masa amma sai bak'in mugunta, daga dawowansa,amma ya dawo kamar wani dodo zaisa ayita shayin masa magana,ta ci gaba da surutanta,tana share face enta..........
Jiddah da ta saki bani tana kallonta,tana ta faman sakin magana,ta ce "maza ki je ya shigo ya ji me kike cewa,wllh kin dai san ba k'yaleki zaiba,zaiyi k'uli² dake ne,garama ki sawa bakinki linzami,yarinya"..........
Ganin tak'i yin shiru sai magana take fad'a duk wanda yazo bakinta, gashi an idar da sallan,juna tak'i yin shiru, yasa jiddan cewa "woooo!! Ga Boss nan shigowa", ai da gudu little ta b'ace daga parlor, d'aki ta shige,nanma bara tsayaba sai a toilet, ta kulle k'ofan.......
Ganin gudun da take yasa jiddah fashewa da dariya,tana fad'in "matsoraciya kawai,duk rashin kunyan da take tak'ama ji yanda ta falle k'afa tana gudu"........
Mik'e wa tayi itama,a toilet en parlor taji alwala yasan kam yanzun little ta kulle k'ofan, babu halin zuwa can,kan dole tayi alwala ta fad'a sallah a nan parlor........
Shigowansa kenan ya ganta tana sallah a parlor, kallonta kad'ai yayi ya nemi guri ya zauna,yana changing channel's.....
Har ta idan,yana zaune yana kallon news da suka watso lokacin,gaisheshi tayi,ya amsa babu yabo babu fallasa,hanyan stairs tabi,sai lokacin ya d'ago yana binta da kallo,yanda take tafiya cikin nutsuwa, har ta bacewa ganinsa,sai lokacin ya dawo da hankalinsa kan abunda yakeyi.........
Mamy ce ta fara fitowa,ita da babynta ikram,a parlor suka tarar da shi,gaida mamy yayi,ikram ta gaida shi,cikin sakin fuska ya amsa..........
Kira mamy ta kwalawa little da jiddah, tare suka fito suna amsawa,little sai bin bayan jiddah take,saboda rashin gaskiya,ko kallonsu baiba,haka har suka gama dinner........
Suna zaune parlor daddy ya shigo,ganin jabeer zaune ya bashi mamaki ssai,amma sai bai nunaba,ya shigo cike da fara'a yana fad'in "mutanen SHANGHAI ne suka ido?",shafa kansa JB yayi ya sauko k'asa yana gaida daddy,cikin sakin fuska sosai ya amsa,yana tambayansa karatun........
Nan Daddy shima ya zauna,ana fira,abinci kuwa a nan ya ci,dan ya k'i yarda a kai masa d'aki, yana ci hana sauraren firan nasu..........
Cikin 2 weeks da yayi a Nigeria sosai yake jin dad'in hakan,shirin komawa yake sosai,little kam banda murna babu abunda take yi,kallonta kawai jiddah take ganin irin murnar da take,shiru kad'ai yayi mata,mata mata magana ba,amma yanda take nunawa kowa zai iya gane hakan akan face enta.........
*★★★NEXT MORNING...★★★*
Ya kama yaune Boss zai koma,da yake weekend ne kowa yana gida,rakoshi sukayi bakin motar,har ya zauna cikin motan,da murmushi akan fuskansa,ya kallesu,zaiyi magana yaga jiddah ta juya da Saudi ta koma cikin gidan.........
Abunda zai iya tunawa,kuma idan har idonsa ba gizo ya masaba,hawaye ya gani akan fuskanta,to mene ne dalilin faruwan hakan,kuma ya ga little sai fara'a take..........
Fitowa yayi da cewa "yayi mantuwa,da sauri yafito ya nufi cikin gidan.......
A bakin stairs ya hangota tsaye ta juya baya,tana hawaye,har yake daf da ita bata saniba,hannunsa ya d'ora kan shoulders enta,ya juyo da ita,cike da tsoro ta bud'e idonta,ganinsa tsaye gabanta,ya matuk'ar bata tsoro,tunanin ta d'aya me ya dawo dashi.........
Tambayan da yake mata cikin rad'a² ya katse mata tunani........
"Me ya saki kika???".....
"Babu komao", ta amsa a tak'aice.....
"K'arya kike,fad'amin gaskiya", ya sake fad'a........
Wani Sabin hawayen ne ya sake sakkowa,gasu tsaye closer da juna......
Ja bata take k'ok'arin yi,ya kalleta, had'e face yayi yana,fad'in "kin tsaya ko sauna mareki", cikin rawar jiki ta tsaya cak, inda take,hannunta yaja sai da suka haura sama,har d'akinsu ya shiga kaita,a tsakiya ya tsaya,still bai saki hannunta ba,ganin har lokacin tana matsar ido,ya janyota jikinsa.........
*~Keep Following Fan's.....~* 😍😍😍
*_SMASHER 🤞🏻😘_*
[22:03, 12/11/2017] Sister Hawwa: 💠💠 *RAYUWAR WANI......*
_{ơŋɛ'ʂ lıʄɛ...}_
💠💠
🌹
*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ...*
*ცყ.*
_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*A KULLUM INA GODIYA GAREKU,Y'AN UWANA DA K'ARFIN GWUIWAN DA KUKE BANI,HAR KULLUM INA TARE DA KU Y'AN UWANAH ABIN ALFAHARINA.....*
*AUNTY KHADIJAH (MAMAN K²).* ❤
*HABIBA IDREES (HUBBEY).* 💃🏻
*AMINA SALIS MUSA (MY LITTLE).* 😍
*INA K'AUNAR CI GABA DA KASANCEWA TARE DA KU,A RAYUWA,HAR KULLUM MASOYINKA SHI KA'AI ZAI KASANCE TARE DA KAI CIKIN WUYA KO DA'DI,ALLAH YA MANA TSAEON RAI MAI AMFANI...#IYA WUYA MUNA MANNE DA JUNA....* 💔❣💔
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)........*
*℘ąɠɛ 33↔34*
Had'e jikinsu yayi guri d'aya,ya dad'a matseta ajikinsa,duk da chest enta da ke dukan 1000² hakan bai hanata tsaida kukan da take ba,lokaci guda hawayen ya tsaya cak.........
Idonta rufe gam,ta rasa wane irin tunani za tayi,kanta na kallon k'asa,lokacin duk wani veins dake jikinta,suka dena aiki.........
Kwantar da kanta yayi a kan k'irjinsa,tana patting bayanta,had'e da hura mata iska cikin kunnenta......
Dad'a lafewa tayi jikinsa,tana sauraren yadda zuciyarsa ke bugawa........
Maganarsa ta katse mata duk wani banzan tunani da zuciyanta ta kasa fuskantar me take son tunawa,handky ya miko mata,banda sanyayyen k'amshi babu abunda yake,a hankali ta shiga goge fuskanta.........
Kamar mai rad'a yake fad'in "mene dalilin da yawa ki kula?"..........
Shiru tayi babu answer, ganin haka,kuma ta dena kukan da takeyi,ya janyeta a jikinsa,zaunar da ita yayi bakin bed en nasu,ya tsaya kallonta,kanta a k'asa,tana wasa da ring enbhannunta............
In minute ya had'e face had'e da cewa "Hey! Ina miki gana kin wani d'aukemin kai,kin bani answer ko saina mareki?".......
Jin abunda yake fad'a, da yanayin yanda yayi maganar ya bata tsoro,cikin inda² ta bud'e baki za tayi magana,ta kasa,saboda sabon kukan da ya taho mata,bakinta ta rufe,ta mik'e da niyyan shigewa toilet..........
Fisgota yayi ta fad'o kan jikinsa,take kukan da take b'oyewa ya bayyana.......
Tsoronsa da ada ya tafi yanzun ya fad'a dawo mata sabo,sak ya koma mata yah JB da ta Sani tun kafin wannan lokacin,jikintane ya soma rawa fiye da da..........
Ganin yanda ya tsorata ta,yasa a hankali ya janyota,sai da tazo daf da shi suna iya jin numfashin juna,kamar mai rad'a yace "mene dalilin kukan??"...........
Haushi ta soma bashi ganin tak'i magana,yasa ya saketa tare da juyawa cikin jin haushin kansa,meya sa zai bite mata,yanzun duk zata rainashi,ya gama zubar da ajinsa........
Tuna hakan da yayi yasa shi sakin tsaki ya fi a k'irga..........
Sauka ya soma daga staircase en,yana tafiya cikin isa,har ya k'araso cikin parlor, zaune ya tarar da su,kallonsa kad'ai daddy yayi baiyi magana ba........
Ita kam mamy bata bar abunba saida tayi magana, "Son me ka koma nema ne da har ka tsaya haka?"......
Rasa amsan bata yayi,sai kansa da ya hau shafawa,zuwa can ya samo abun cewa ta hanyar cewa "ammm!! mamy wani file nake nema,to kuma ma ban ganshiba".......
"Ohhh!! Really", daddy ya fad'a yana murmushi.......
Da sauri ya nufi waje yana fad'in "saduwan alkhairi, na wuce"........
Binsa suka kuma yi har bakin motan,sai da suka ga fitan motar daga gidan tukun suka koma cike da kewansa........
Su little an samu waje,za a sha iska,sai murna take,akan fuskanta zaka iya gane farin cikin da take ciki.........
A d'aki ta tadda jiddah kwance saman bed,idonta rufe kamar mai bacci.......
"Sistor what's wrong?" Ta tambaya tana zama kusa da ita,ta data goshinta......
Jin kan da d'an d'umi tayi tunanin ko headache ke damunta........
Bata kula taba,ita kuma bata fasa magana ba (kunsan little da surutu kamar Parrott)........
Ikram ta shigo,tana fad'in ADDAS daddy na kiranku",tana gama fad'an sak'on tayi waje ko zama ba tayiba........
A parlor suka tarar da su gaba d'aya, ko wacce ta nemi guri ta zauna,kan jiddaha k'asa.........
Daddy yayi gyaran muya kafin ya fara magana........
"Dalilin da yasa nace a kiraku shi ne,tun yanzun ina son jin ra'ayinku ne game da ci gaba da karatu,na san nan da 3-5 months, za ku kammala karatu,yanzun kuma zuwa 2weeks za kuje exam na JAMB, so make sure kun zama ready,bana so ayi wasa,adage ayi karatu,kun fuskanta?"...........
Amsawa sukayi,kowacce sai murna take,dan Dana burinsu kenan,godiya sukayi,mamy ma na taya su,daddy ya sallamesu........
Da murna suka shiga d'akin suka k'ank'ame juna.........
Little ce tayi saurin sakin jiddah tana fad'in "hey!! Madam ina ciwon? Ko har kin warke?......
"Autchhh!!", ta fad'a tare da dafe kai.........
Dariya ssai little take,tana nunata da hannu,gaskiya sis gara miki ma ki bar wannan pretend en,dan ba zai amsuba a gurina,so stop it...........
Isar su filin jirgin na malam Aminu Kano, jikinsa duk babu dad'i kamar wancan lokacin yake jin babu dad'i, garama yanzun akan da shekarun da suka rage masa babu da wani yawa,kamar yau zai dawo cikin family ensa,da wannan ya samu k'warin guiwan,ci gaba da tafiya, har ya gama duk wani abu da zaiyi...........
Zaune yake cikin flight en,ya kwantar da kansa kan seat en da yake,ido ya lumshe yana tuna abunda ya faru kafin fitowansa daga gida........
Murmushi ya sake,lokacin da ya tuna yanda sukayi,take ya nemi duk wani haushin da yake ji ya rasa.........
Da wannan tunanin jirginsu ya Lula cikin gajimare..........
*★★★SAFE FLIGHT YAH BOSS...★★★* ✈✈✈
Ke dillah matsalata dake kenan,in kika fara dariya kamar wacce kanta ya samu kwancewa.......
"Hhhhh!! Lallai kam shi yasa naga duk na shiaga damuwa ba saboda wanda bai damu daniba zai tafiya", ta rad'a tana ya tsina fuskanta......
Ai bazaki gane ba,matsalarki kenan,dan yah boss zai tafi shi ne aka ce miki damuwa nayi?, to ko kad'an ba haka bane,kaina kad'ai kemin ciwo......
"Ohhh!! Sure", little ta fad'a tana d'age kai........
"Kyaji da shi,ni ba matsalata b'ace,sai kiyi ke kad'ai", jiddan ta rad'a tana ficewa daga d'akin.......
"Ko kuma maji da shiba", ta rad'a cikin d'aga murya......
Ita kam bata kulata ba,ta k'arasa sauka.......
*★★★CHINA...★★★*
*SHANGHAI DISTRICT..*
Saukansu a airport, babu jimawa ya isa hostel,cike da kewan gida........
Bayan ya gama gyara kayansa,ya shiga toilet wanka,fitowansa babu jimawa,ya bi lafiyar gado,cike da gajiya bacci yayi gaba da shi,ba shi ya farkaba sai 6:00pm a agogon can......
Wanka ya sake yi,ya shiraya cikin k'ananan kaya,ya fice,wani restaurant ya shiga,dake kusa da su,yayi order abincin da zaici irin namu.......
In a while minutes ya mammal,ya fice direct school libry ya nufa,aka koma bakin fama.............
0 comments:
Post a Comment