Bayanta little ta biyo tana mata surutu,ita kuma tak'i bite mata,ganin tak'i kulata,ta nufi ikram,dan tasan mutuniyar ba kulata za tayiba, yanzun y'an mulkin nata sun motsa.......
Daga ita sai lkram suke firansu.......
Gajiya tayi da zaman wajen ta mik'e cike da kasala duk da ba bacci take jiba,ta gwammace ta bar gurin,gaba d'aya jikinta kamar bata da cikakkiyar lafiya,ko magana ba tayi musu ba,ta mik'e ta bar gurin.......
Kallonta kad'ai suka yi,little ta kalli ikram,itama kallonta tayi tana d'aga mata gira,alamun meke damunta............
Kafad'a ta d'aga alaman itama mata saniba.......
Ci gaba sukayi da firansu,ita kuma ta k'arasa bedroom en su,jikinta duk ya mata nauyi,akan bed ta zube ta rasa meke mata dad'i........
Ajikinta take ji tayi missing wani abu,amma ta rasa mene wannan abun da ya kasance mai muhimmanci haka da har take jin duk wani joint na jikinta na mata ciwo.......
Kamar za tayi kuka, saboda tunanin abun da ta rasa fahimtar ko mene ne......
Tana wannan tunanin bacci yayi gaba da ita,ko dinner batayiba,ko da mamy ta aiko ikram ta kirata,cikin bacci tace ta k'oshi,baya sake sanin inda kanta yake ba sai da asubah,shima tashinta akayi,cikin kasala kamar lokacin da zata kwanta,ta mik'e, tana idar da sallan ta koma saman bed........
Ko da suka tashi shirin skul,komai tana yine kamar Mara laka,haka suka yiwa mamy sallama,malam shehu ya d'ebesu sai skul.......
*★★★CHINA.....★★★*
Tun bayan shigansa libry en,ya nemi guri ya zauna,karatu yake sonyi amma ya kasa,duk wani hope nasa a ranar ya rasa shi,haka yake ta bud'e shafukan d'aya bayan d'aya, amma ya kasa komai.......
Hak'ura yayi ya rufe,tafiba yake yana tunanin ya rasa abunda zaiyi tuna,gaba d'aya jikinta babu dad'i.........
Kamar Mara lafiya haka ya k'arasa yinin ranar,ganin haka yasa ya dan ganta hakan da gajiyan da ya d'ebo......
Wanka kad'ai yayi,shirin bacci yayi yabi lafiyar gado.........
Haka rayuwa taci gaba da tafiya,lokaci na ci gaba da gudu,ta ko wane b'angaren ana samun ci gaba.......
*★★★NIGERIA.....★★★*
Cikin shekaru biyu 2 da suka rage ada,yanzun gashi har lokacin ya sake zuwa,inda yanazun yammatan mamy an dad'a zama big girls,tuni sun dad'a wayewa kasancewar mu'amala da many an yara,suma sun san abunda duniyar ke ciki......
Shirye² dawowan Boss ake sosai,had'e da bud'e masa hospital da daddy ya kammala Gina masa,an kammala komai sai jiran dawowansa,da kowa ke buri........
Tafe suke a k'afa kasancewar tasowansu daga islamiyyan (USMAN BIN AFFAN) dake tsallaken k'ofar gadon k'aya.........
Sai fira suke,kasancewar yau malam shehu baya nan shi yasa suka dawo k'afan.........
Suna daf da isa gida,hankalinsu gaba d'aya tana kan firan da suke......
Horn ake ta bayansu kamar kunnensu zai stage saboda k'ara.....
Afusace little ta juya da niyyan tsiwa ga mai horn en...........
Wani sabon (RR) black colour, ya faka gefensu,had'e da sauke glass,sallama ya musu............
Little rik'e da side en west nata, tana kad'a k'afa,ta amsa tana jiran taji me zai ce.......
"Idan babu damuwa hajiya ina son magana da ke", abunda ya fito daga bakinsa kenan.......
Jikinta yayi sanyi ganin irin kallon da yake mata,take ta kasa cewa komai,duk tsiwan da ta tunkaro shi da ita take ya koma ganin mugun kwarjini da ya mata........
Kai ta sauke k'asa,tana fad'in "kayi hak'uri bazamu samu damar tsayawa nanba,sai anjima"........
Tana gama fad'in hakan ta ja hannun jiddah suka k'arasa k'afafunsu sauri........
Ci gaba tayi da binsu har sai da yaga inda suka shiga,kafin yayi murmushi.......
Reverse yayi ya bar line en,da matsanancin gudu........
Suna shiga parlor suka tarar da mamy tana waya,zama sukayi har ta ida wayan........
Cike da farin ciki,ta kallesu tana fad'in "idan Allah ya kaimu nan da 1week yayanku zai dawo".........
Fitowan ikram kenan daga d'aki,ta tsinci maganar,tsalle tayi had'e da fasa k'ara,wanda yana hankalinsu........
Kallonta kad'ai sukayi kowa cike da fargaba,da gudu ta k'araso gurin ta fad'a kan cinyan mamy,tana ci gaba da ihun........
Sai lokacin suka fuskanci dalilin yin k'aran nata,tsaki jiddah tayi tana fad'an "amma dai wannan yarinya koi sha³,kin sa duk na tsorata wllh,tana hararanta,ta mik'e ta bar gurin........
Tun kafin ta k'arasa d'aki ta fara cire hijab en jikinta.........
Alwala kad'ai tayi ta sake kayan jikinta,after isha lokacin za suyi dinner daddy ya dawo,nan mamy ke sanar masa dawowan jabeer, sosai yayi farin ciki tare da fatan alkhairi.......
Har ya juya zai koma sama ya dawo yana fad'an "amma!! Mamyn yara an jima ki tunamin akwai shawaran da nake so muyi,bana son na manta,so ki tunamin zuwa anjiman".........
Amsawa tayi tana murmushi, shi kuma ya bar gurin,tashi itama tayi ta nufi kitchen, abincinsa ta had'a kan tray,ta nufi d'akin daddyn........
Zama tayi ta had'a masa abincin,tana niyyan tashi ya dakatar da ita,yana fad'in ki jira na kammala mayi maganar yanzun,tun kafin na manta"......
Murmushi tayi ta koma ta zauna,bar ya kammala tana zaune........
Gyaran murya yayi kafin ya fara da cewa "dalilin da yasa nace akwai shawaran da zamuyi da ke ba kan komai bane sai kan yara........
Yabawa da halayyar yaran nan da muka d'auki d'awainiyarsu tun kafin wannan lokacin,da yadda suka girma a hannunmu,duk wani gata da ya kamata muyi musu munyi,sai dai ina ganin wannan gatan shi ne mafi girma" d'an daka tawa yayi kafin yaci gaba da magana...........
"Ba komai ne wannan gatan ba da ya wuce had'a jabeer aure da jiddah,yin hakan ina ganin shi ne babban gatan da zamuyi musu,haka ina tunanin shi ne kad'ai zai iya rik'e amanarta,amatsayinta na marainiya".........
Murmushi mamy tayi da jin shawaran da yafi komai faranta mata rai,ta jima da wannan burin a rayuwarta sai dai ta barwa zuciyar ta,kuma ta duk'ufa da addu'ah kan Allah ya tabbatar da alkhairinsa akan al'amarin idan har da alkhairi aciki.......
Nan ta fayyace masa abunda ta jima da shi a zuciyarta,murmushi kad'ai yayi tare da addu'ah ta fatan Allah ya had'a kansu,...........
Wai Dama daddy itace shawaran???? Da ka ya amsa mata yana murmushi.....
"To amma daddy bakayi observing wani abu tsakaninsu yaran nan,kafin tafiyan jabeer?" Mamy ta fad'a..........
"Wani abu kika ga ya faru?", daddyn ya tambaya yana kuma neman K'arin bayani.......
Murmushi tayi kafin ta tuna masa ranar da jabeer d'in zai koma,da shigan jiddah gida tana kuka,har zuwa cewa da jabeer en yayi akan yayi mantuwa.........
Sannan ta d'ora da cewa "a ganina hakan ya nuna suna son junansu amma basa so ne a gane".........
Sosai maganar yayiwa daddy dad'i da ya kasance hasashensa yayi dai²........
*(UHMMM!! nikam cewa nayi a jira aji ta bakinsu kafin yanke hukunci...)*
Kan little firan ya koma,inda daddy yake cewa a tambayeta aji ko da wani wanda yake sonta,dan yafi son aurar dasu lokaci gida,ba lallai sai sun kammala karatuba..........
Ranar yau kam ta kasance mafi fad'in ranaku a wajen wannan family na ALHAJI MUHAMMAD BARODO.....
Da wannan farin cikin gidan ya kasance,duk da cewa su yaran gidan babu wanda yasan da maganar, an barta ne zuwa lokacin da likita bokan turai zai dawo.........
*★★★ONE WEEK LATER.....★★★*
*THURSDAY MORNING...*
Wayewar garin na alhamis yazo cike da nasarori masu train yawa,inda jabeer yake jinsa kamar wanda aka d'aukewa wani nauyi,bayan shafe shekaru 6 a kasar ta china..........
Wanda kuma ajiya hukumar makarantar ta yaye d'aliban tare da lambobin yabo da girmamawa da ya samu,daga makarantar............
Farin ciki yake ciki Mara misaltuwa a wayewar Safiyan,kasancewar rana ta k'arshe a gurinsa a *"FENCING CAMPUS"*.........
Da wannan ya tattara duk wani abu mallakinsa yayi sallama da sauran jama'an da suka saba bayan dawowan sa,ya nufi airport...........
*SAFE TRIP YAH BOSS.......* ๐ซ๐ซ๐ซ
*★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★ ★*
Shiri ake sosai na tarbansa,tun wayewar garin babu wanda ya zauna,sine d'ora wancan,sauke wannan.....
Har fiye da shud'ewar wasu awanni......
Dai² lokacin da agogon Nigeria ya nuna k'arfe 2:30pm suka kammala duk wani shirin tarbansa,sai shirin tafiya taronsa da suke............
Wanka sukayi,ko wacce ta zauna Rana baje hajar basirarta wajen k'awata fuskanta da had'd'd'en make-up.........
Sai da suka shade 1 hour kafin cikin gudu² aka fara tseren saka kaya,Don baifi mintuna ya rage jirginsu ya zauna ba.......
Ga mamy sai kuransu take akan su sakko,amma sun mak'ale a sama (kamar wasu tsuntsaye...)........
*~Keep Following Fan's... ~* ๐๐๐
*_SMASHER ๐ค๐ป๐_*
[21:08, 12/13/2017] Sister Hawwa: ๐ ๐ *RAYUWAR WANI......*
_{ฦกลษ'ส lฤฑสษ...}_
๐ ๐
๐น
*สษฌฦกrแง ฤ
ลษ แฟณwrฤฑษฌษฌษล...*
*แชแง.*
_HAWWA M.U {SMฮSHฮฃR}._
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*INA GODIYA DA ADDU'O'INKU MASOYANAH ALLAH YA BAR ZUMUNCI....* ๐๐ป๐๐ป๐๐ป
*_KUMIN UZURI FAN'S NA KOMA SKUL YANZUN BA KOWANE TIME ZAKUNA GANIN POSTING ENABA,COZ WANNAN SHINE LAST SEMESTER NA.......IDAN NA SAMU TIME SOSAI ZAKUNA JINA KAMAR KO WANE LOKACI........LOVE U OLL...._* ๐๐๐
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)........*
*℘ฤ
ษ ษ 37↔38*
Da k'yar mamy ta samu suna sakko,shima sai da ta shiga d'akin ta korosu,gown ne ajikinsu black colour,colour en touches en ne ya bambanta,nan jiddah anyi da red,yayinda na little ya zama pink,veil kowacce ta ja,kalar touch en jikin gown nata,rolling sukayi,kafin suka janyo wani uban hill shoe........
Da k'yar suke tafiya akan sa,bama kamar little tana tafiya kamar zata fad'o, a haka suka saukko k'asa........
Mamy na zaune suka sakko bata kallesuba har suka k'araso,kallonsu tayi ta d'auke kai........
Kallon juna sukayi, kafin suyi murmushi tare da d'aga kai.........
"Mamy mun tafi",suka fad'a......
"Karku tafi ku dawo ku zauna",ta basu answer......
Eyyahh mana mamy kiyi hak'uri yanzun fa can zamu tafi.......
Bata kulasuba har lokacin, da gudu² suka nufi hanyan fita,ikram na bayansu......
Sunzo daf da zasu fita,garin sauri k'afar little ta zame gaba d'aya ta tafi sai junta tayi a k'asa zaman yan bori.......
"Autchhh!!" Ta fad'a tana runtse ido...
Dariya gaba d'aya parlor suka saka mata,har mamy da komai ya faru akan idonta.......
Ganin babu mai mata sannu yasa ta fara kuka,still dariyan sukaci gaba dayi,da k'yar ta mik'e tana bin wall en parlor tayi waje bata kula suba......
Da gudu suka biyo bayanta lokacin har ta kusa da motor en da zasu fita da shi........
Mamy na daga Parlor take fad'in "Allah ya dawomin daku lafiya,ku kula da hanya,banda driving en rashin hankali", amsawa sukayi suna daga wajen.......
Key ne a hannunta tana tafiya,da gudu jiddah ta fizgesa tana fad'in "tabbb wallahi bamu shiryawa driving enki ba yau,barema da kike jin haushin munyi miki dariya".......
Kai ta jijjiga tana fad'in "wallahi Allah ya ceceku yau da sai kun gwammace baku bari nayi driving ba"........
Babu wanda ya kula ta,haka suka shige,ikram na back seat........
Belt tasa kafin tayi warming motor, da hanzari suka bar harabar gidan sai airport........
Tun tasowansu daga k'asar ta China,basu suka sauka a Nigeria ba sai misalin 5:15pm a agogon 9ja.......
Dai² lokacin da suke sakkowa daga cikin flight en su lkram suka k'araso gurin..........
Daga baya suka hangoshi yana sakkowa sanye da black suit, ya dad'a haske da fresh,ga wani class da ya dad'o,steps yake tsallakowa a hankali cikin takun k'asaita,kamar ba Shiba........
Little ce ta fara hangoshi,baki ta sake tana kallonsa tun daga nesa,jiddah ta tab'a tana mata nuni da hannu.......
Abunda take mata nuni da tabi da kallo.......
Hangoshi tayi yana takowa yana kallon side ensa,ko zai ga wanda yazo d'aukansa.......
Badan little na gurinba babu lallai ace zata ganesa,da gudu lkram take k'ok'arin wucewa.......
Jiddah ce tayi k'arfin halin kamo hannunta,tana jijjiga mata kai,alamun A'a.......
Kai ta sunkuyar tunawa da tayi shi en ba muharrraminsu bane........
Suna tsaye har ya zo zai giftasu,little ce tayi maganar da cewa "welcome back yah Bos..........
Da sauri ta rufe bakinta,ganin zata fad'i abunda bata shiryaba........
Kallonta yayi had'e da wani mugun harara da ya Watson mata.......
Ba tare da ya kulataba yayi gaba,da sauri suka bi bayansa,har bakin motar da baiyi tunanin shi ne wanda suka zo da shiba.........
Har ya gota motan,lkram ta masa maganar,dawowa yayi da baya,yana fad'in "ina driven?"..........
Ganin jiddah na k'ok'arin shiga driver seat ya bud'e ido sosai,tare da komawa baya kad'an,yana fad'in "are u d driver?".....
Kai ta sunkuyar k'asa,kafin taci gaba da cewa "OK we can go ai,tunda mun shirya mutuwa", yana gama fad'in hakan ya nufi front seat, nan ya zauna ita kuma little ta koma gefen ikram da ta shige back seat............
Ita kam da k'yar ta ja k'afafunta ta bud'e front seat en ta zauna,addu'ah ne kad'ai a bakinta tun da ta zauna har sai da suka shigo haraban gidan sannan ta samu nutsuwa........
Banda godiya ga Allah babu abunda take,da haka tayi following nasu back,har sun kusa da shiga parlor........
Shigowansu parlor da sallama yasa mamy dake zaune mik'ewa tana murmushi na jin dad'i da Allah ya dawo mata da tilon d'anta namiji gida lafiya..........
Zama suka yi,bayan sun gaisa da mamy ta masa murnan kammala karatunsa............
Sai murmushi yake,har zuwa lokacin da mamy tace ya je yayi wanka ya huta, kafin suyi dinner,na murnan zuwansa........
Mik'ewa yayi ya nufi d'akin sa da aka gyarashi fiye da lokaci tafiyarsa,sosai d'akin yayi matuk'ar burgeshi, an canja komai na d'akin, sai k'amshin da ke tashi aciki na freshener.......
Sanyin da d'akin ya d'auka da k'amshin data shak'a ya haddasa masa kasala.....
Da k'yar ya samu yayi wanka,yana fitowa,ya zaune k'alk'ale jikinsa.........
Cikin k'ananan kaya ya shirya,red polo da black jeans,ya sakko dining ya nufa nan ya tarar da mammy,little, ikram zaune parlor,suna firan irin sauyawar da tayi bayan komawarsa...........
Wanda a shekaru biyu baya da yazo bai yi wannan canjinba........
Murmushi kwance kan fuskansa,ya k'araso ya nemi guri ya zauna,nan akaci gaba da firan da shi.......
Shigowan daddy ya katse musu firan da sukeyi,cikin farin ciki ya sake su,guri ya samu ya zauna,suna ta masa barka da dawowa,amsawa yayi kafin ya kalli jabeer da ke ta faman smile yana fad'in "likita bokan turai"............
Dariya suka saka gaba d'aya parlor........
Anata fira,sai da aka tashi yin dinner, lokacin ne daddy yake tambayanta jiddah......
Kallon kallo aka shiga yi,kafin suka ce masa tana sama.........
A tsakiyan parlor aka dire kayan abinci ranan dan yafi musu balance........
Kiranta daddy yasa ayi,little ta tafi cikin sassarfa harta tura d'akin tana kiranta,jin shiru yasa ta tura k'ofan toilet..........
Ga mamaki ta k'ofan a bud'e yake,dube² ta fara amma bata gantaba.....
Har ta juya zata koma ta jiyo nishinta a space en dake jikin gadonsu.......
Tunanin ta me take a gurin,ci gaba tayi da kiranta,jin bata answer ba,ta nufi gurin da sauri.,..........
Kwance ta sameta ta kifa akan cikin ta,sai juyi take,tana nishi sama²,cikin azaba da rashin sanin halin da take ciki........
K'ara little ta sake,wanda ya janyo hankukansu daddy,da gudu suna rige² suka k'araso d'akin.........
Ganin halin da take ciki yasa cikin rud'ewa jabeer ya d'auki ta,a kan bed ya shimfid'eta........
Lokacin yayi dai² da idanunta da suka fara lumshewa a hankali,har suka gama kullewa,jikinta ya saki,take ta dena motsi.........
K'ara lkram da little suka saki,a tare suka nufi inda take........๐ญ๐ญ๐ญ๐ญ๐ญ๐ญ
*~Keep Following Fan's.... ~* ๐๐๐
*_REAL SMASHER ๐ค๐ป๐_*
[21:36, 12/14/2017] Sister Hawwa: ๐ ๐ *RAYUWAR WANI......*
_{ฦกลษ'ส lฤฑสษ...}_
๐ ๐
๐น
*สษฌฦกrแง ฤ
ลษ แฟณwrฤฑษฌษฌษล...*
*แชแง.*
_HAWWA M.U {SMฮSHฮฃR}._
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*HUH!!! ๐คฆ๐ป♀ FAN'S KUNA BANI DARIYA,ESPECIALLY U GUYSSSSS DA KUKE MAGANAN KAR ACE JIDDAH TA MUTU,IRIN CHAT ENKU AKAN HAKAN YA SANI NISHA'DI SOSAI.......ALLAH YA BARMINKU HAR A AL'JANNAH....#SO MUCH LUV FAN'S.......* ๐๐๐
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
*_INA KIKE Y'AR UWATA KUMA ABAR K'AUNA,★★★QUEEN ACID ๐น★★★ ARADU WANNAN PAGE WA KE KAD'AI NA BADA KYAUTARSA....INA JIN DAD'IN ADDU'ARKI GARENI,INA GODIYA SOSAI ALLAH YA BAR K'AUNA...._* ❤
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)........*
*℘ฤ
ษ ษ 39↔40*
Gaba d'aya sun k'ank'ameta, sai jijjigata suke, ganin sunk'i barinta,yasa abun ya bawa jabeer da ke tsaye yana son duba abunda ya faru da ita,yi musu tsawan da babu shirin suka saketa,kowacce ta koma gefe suna hawaye............
Tsawon wani lokaci tak'i farkawa,duk temakon da ya bata na gaggawa.......
Hannunsa yasa cikin gashin kansa ya bajesa,had'e da furzar da iska mai dumi,idanunsa har sun soma canja colour zuwa red..........
Rashin isassun kayan aikima baiyiba,k'asa har k'asa amma idan mutum baida lafiya sai dai wani ma ya mutu,saboda rashin kayan............
Wani uban tsaki ya saki,yana d'auke zufan da ya tarun masa a forehead ensa.........
Daddy ya kalla cikin takaici yana fad'in "dad sai dai mu wuce hospital"............
Bai k'arasa ta ja ajiyan zuciya........
Cikin sauri suka kalleta,suna rige² wajen zuwa kusa da ita,sun manta da warning na yah Boss.........
Juyawa yayi shima yana kallonta,ganin tana juyi kan gadon yasa,bai jira ya sake cewa komaiba........
Nufanta yayi,ba tare da ya bi ta kan su lkramba ya sureta,sai waje...........
Abaya su lkram suka biyoshi,yana sta a motar ya fisgi motar ko su ikram en dake bayansa basu samu daman shigaba,ya mata key..........
Da matsanancin gudu ya isa wani private hospital dake nan cikin sharad'a.......
D'aukanta yayi ya nufi ciki da ita,ganin haka nurses en suka nufo shi da niyyan ansanta.............
Bai basuba haka suma basu bashi hanya ya wuce ba
............
K'aran da tayi had'e da damk'an cikin ta,ya dad'a birkitashi,cikin wani irin voice yayi masu tsawan da yasa suka bashi hanya,gaba kad'ai yayi suka biyo shi abaya............
Magana Duke amma hankalinsa baya Kansu,kan dole suka hak'ura suka zuba ido........
Room en da yake daf da shi ya shige tare da kwantar da ita,nan ya shiga dubata............
Cikin k'ank'anin lokaci ya gane inda matsalan ta ya nufa..........
Allurai ya mata had'e da sa mata drip,take baccin wahala yayi gaba da ita.........
Sai lokacin ya samu hankalinsa ya kwanta..........
Zama yayi a gefenta,tana bacci kallonta yayi tun daga up-down,sai lokacin ya kula da kayan dake sanye jikinta..........
Wani haushi yaji lokaci guda..........
"Ta yaya har ya fito da ita a haka"
Ya tambaya kansa,ganin babu answer ya kau da tunanin...............
Kanta babu ko tight,haushin kansa yaji ganin duk yabi ya damu da abunda ya shafeta,da yanda ya gama rawan jiki a gidaba.............
Yayi tsaki yafi a k'irga tuna hakan.........
Kiran phone ensa daddy ya shiga yi,ganin ya barsu cikin gidan,kafin su fito har ya tafi.......
Sai su lkram dake kuka suna k'ok'arin komawa da baya.........
Ci gaba tayi da Kiran phone en,amma har sama da 20 miss call's ba a d'auka ba.........
Hak'ura yayi da kiran,parlor suka koma,dai² lokacin da yake k'ok'arin sake Koran nasa,kusa da su sukaji ring en phone en...........
Sai lokacin suka tuna abunda ya faru da yanayin yanda abun ya zo musu.........
Hak'uri sukayi,sun zuba ido zuwa lokacin da zasu dawo..........
Motsinta ya tabbatar masa da ta farka, juyawa yayi ya kalleta.........
Kafin cikin yanayin jimami ya ce "ya jikin naki,hope babu wata damuwa?".........
Kai ta d'aga masa,alaman babu komai.......
Danshin da taji k'ark'ashita ya tabbatar mata tayi mugun staining, cikin firgita ta kalli kanta,gaba d'aya ta gama bata gurin da take kwance...........
Sheshek'an kukanta ya jawo hakalinsa kanta cikin hanzari ya kalleta da alamun neman K'arin bayani akan kukan da take............
Idonsa ne yakai kanta,sai a time en ya tuna dalilin ciwon nata..........
Dafe kansa yayi,yana tunanin abun yi,can ya samo mafita........
Wata nurse yama maganar,cikin wad'anda yama tsawa d'azun,bayani ya mata akan yana so ta taimakata.......
Babu musu ta shiga room en,ficewa yayi ya nufi gida,sai yanzunma ya tuna da yanda al'amarin ya faru.........
A parlor ya tarar da su sunyi jigum²,suna jiran jin wane hali take ciki yanzun.......
Shigowansa yasa hankulansu dawowa kansa,nan aka shiga rige² wajen tambayansa ya jikin nata,amsawa yayi,kafin ya bata little umarnin ta kawo masa kayanta yana jiranta.........
Amsawa tayi tare da mik'ewa cikin sassarfa ta had'a mishi kayan........
An sa yayi ya juya zai bar parlor, "dan Allah yah na biyoka?" Little ta fad'a tana rangad'ar da kai,wani mugun kallo da ya wullo mata yasa ta sauke kai k'asa.........
Ta san dama abunda zai biyo baya kenan,ficewa yayi ba tare da ya ce uffanba........
Cikin mituna da basu wuce 30 ba ya dawo da kayan,da zata sa.......
Lokacin har ta gyara jikinta,sai dai kukan da take still...........
Tun da ya shigo yake jiyo sheshshek'ar kukantan,daga cikin toilet en.........
Mamaki yake na tarar da hakan........
Kayan ya ajiye kan bed,waje ya nuna fita,da nurse en suka dawo,ya tsaya bakin room en..........
Sai da ta gama shiryawa tukun ta fito,kan bed en ta koma ta sake kwanciya,still sai sheshshek'an kuka take..........
Shigowansa ya sake tarar da ita tana yanda ya barta,kallonta kawai yayi,ya d'auke kai.........
Ganin ta k'i shiru,face enta har ya fara tasawa,yasa ya bud'e baki da k'yar yana fad'in "kinma mutane shiru ko kuwa sai na zo nan?"........
Babu shiru ta had'iye kukan..........
Gaba yayi yana ci gaba da fad'in "idan kin gama kukan ki sameni waje"........
Cikin sauri ta mik'e dan dama zaman ya isheta ga dare da ya soma nisa,da sauri² ta biyo bayansa duk da ba wai tana jin dad'in jikintan bane.........
Tsayawan da tayi yasa ita kuma tayi gaba,ci gaba tayi da tafiya a hankali sai waige² take ga gurin babu mutane sosai,tsorone ya shafeta da yasa jikinta ya fara rawa kamar mai jin sanyi,take hawayen da ta nema ta rasa suka sake ballewa kamar an bud'e tap............
Kasancewar gurin babu yalwar haske sosai,ga dogayen bishiyu,banda kukan k'wari babu abunda kake ji..........
Tana tsaka da tafiya ta bugi wani Dutse da yasa ta tafiya da baya......
Idonta a rufe tana jiran ta k'arasa kaiwa k'asa..........
Ga mamaki ta,ji tayi an tarota,ajiyan zuciya ta sauke,amma da sauri tayi k'ok'arin fisge jikinta,tunawa da tayi da inda take.........
Rik'eta yayi sosai,ganin yanda take a tsorace,yana fad'in "ina zaki kuma?"......
Jin muryansa ya sa ta fuskantan shi ne,amma har lokacin jikinta rawa yake........
K'ok'arin mik'ar da ita yake,sai dad'a cukuikuyeshi take duk ta mak'aleshi.......
Hak'ura yayi da ita a jikinsa ya fara tafiya........
One step forward yayi k'afan nasa ya zame,da baya ya tafi,duk k'ok'arin sa na ganin bai kai k'asa ba hakan ya gagara......
Kwanciya yayi a k'asa da ita ajikisa,dai² lokacin da ya kai k'asa lips ensu ya..........................
*~Keep Following Fan's...~* ๐๐๐
*_REAL SMASHER ๐ค๐ป๐_*
[21:47, 12/15/2017] Sister Hawwa: ๐ ๐ *RAYUWAR WANI......*
_{ฦกลษ'ส lฤฑสษ...}_
๐ ๐
๐น
*สษฌฦกrแง ฤ
ลษ แฟณwrฤฑษฌษฌษล...*
*แชแง.*
_HAWWA M.U {SMฮSHฮฃR}._
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*_KUMIN UZURI FAN'S KAN,RASHIN JINA DA WURI DA BAKWAYI YANZUN,ABUBUWANE SUNMIN YAWA YANZUN DA K'YAR NAKE SAMUN TIME EN DA NAKE TYPING.....ALWAYS U ARE WITHIN MY K'ALBEEYYY LOVE U OLL...._* ❤
*_WELCOME BACK SURUKI,ALLAH YA BADA SA'AN EXAM YA FITO DA SAKAMAKO MAI KYAU......@HASSAN ATK TANKO...._* ๐๐ป๐๐ป๐๐ป
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)........*
*℘ฤ
ษ ษ 41↔42*
Dai² lokacin lips ensu yayi clashing,wasu stars ne suka gilma a idanunsu,had'e da wani irin electric shock da ya ratsa jikinsu......
Tsorone ya dad'a kamata,k'ank'ameshi ta dad'ayi fiye da rik'on da ta masa na farko,ci gaba yayi da k'ok'arin mik'ewa,ita Kuma tak'i tashi daga jikinsa,ganin haka kan dole ya mike da ita ajikinsa,ko daya mik'e hak'ura yayi ya d'auketa ya ci gaba da tafiya tana jikinsa har bakin motar ya isa da ita a hannunsa.......
Kwanciya tayi akan wide chest ensa,hannayenta zagaye a wuyansa duk ta nad'esa kamar wata (micijiya),jikinta a sake saboda kasalan da take ji wanda bata tab'a tsintar kanta a cikin irinsa ba sai yau,dama tafiyan da k'yar take yinta,saboda k'afanta duk ya rik'e da k'yar ta iya fitowa daga room en,yanzun kuma ta samu anyi lifting enta,banda smiling ba abunda take........
Front seat ya ajiyeta kafin ya juya zai shiga mazaunin driver, kallonsa take tana murmushi har ya zauna,warming car en yayi,kafin ya juya a hankali ya kalleta,ganin idanunta a rufe yayi tunanin ko bacci take ji,da sauri ya bar harabar hospital en ya nufi gida da ita.........
Motan yayi shiru,tamkar kuramene aciki,haka har suka isa gida......
Tana jin lokacin da yayi horn har zuwa gyara parking da yayi a parking lot,ya jima tsaye yana kallonta.......
Tunaninsa inda zai fara tashinta yake,ya kai kusan five minutes ya kasa tab'uka komai,ganin yana b'atawa kansa lokaci yasa ya fito daga motor en,zagayawa yayi ya bud'e, still ya sake yi a wajen,zuwa can yayi k'arfin hali ya d'agota tare da mannata ajikinsa,ajiyan zuciya sukayi lokaci gida,da k'afa ya tura k'ofan ya nufi cikin gida da ita........
Sai da yaje daf da parlor sannan ya tsaya yana waigen bayansa,tunaninsa ta yayama zai shiga da ita a haka? Rashin mafita yasa shi sauke ajiyan zuciya,yasan dai dolensa ya shiga gidan......
Hak'uri yayi ya nufi cikin parlor da sallama,yana addu'ar Allah yasa babu kowa a parlor.......
'Dago kansa yayi jin maganar mamy dake zaune,shi kenan ya fad'a a zuciyarsa.......
lkram da little kam har sunyi bacci a parlor kan jiran ganin dawowarsu,da abun ya k'ine suka kashingid'a bacci kuma yayi gaba da su nan,duk k'ok'arin da mamy tayi kan su tafi d'aki suka nace kan jiran ganin dawowansu.........
Amsa masa tayi tana mik'ewa tsaye,ganinsa d'auke da jiddah a hannun,tunaninsa wani abun ya faru kuma,hankalinta a tashe ganin yanda jikinsa yayi sanyi yasa ta tsorata,matsowa tayi tana fad'in "son me ya sameta??......
Ganin yanda hankalinta ya fara tashi yasa yayi murmushin k'arfin hali,da k'yar ya d'aga k'afansa ya nufi inda take yana fad'in
"huh!! Mamy she's feeling fine fah"...
Yana squeeze da face nasa........
Murmushi tayi jin amsan daya bata...
Amma still tana neman K'arin bayani, fuskantan hakan yasa ya kalleta tare da fad'in "bacci tayi mamy kafin mu zo gida"......
Eyyahh!! Kaita d'aki toh.....
Staircase ya nufa da ita a hannunsa,a hankali take sauke numfashi,hakan ya tabbatar masa da bacci take.....
Akan bed ensu ya shimfid'eta, veil en kantane ya zame gashin kanta dake tsefe ya baje kan pillow, wani ya kwanta kan face enta.....
Har ya juya zai fita ya dawo dai² saitin kanta ya d'an rage tsayinsa,gashin ya janye mata gefe,kafin ya juya ya bar d'akin.......
A k'ofan room en nasu sukayi clashing da mamy tana k'ok'arin shiga d'akin, murmushi tayi had'e da cewa
"Sannu son,ko abincin baka ciba,muje ciki kaci",hannunta d'auke da tray....
Juyawa yayi tana bayansa,a bakin bed en ya zauna,mamy ta ajiye masa tana fad'in
"Son ka tsaya min da daughter zanje na dawo yanzun"...
Tana gama fad'a tayi hanyan fita a d'akin....
Abincin ya fara ci,bai wani ci sosaiba ya ture komai had'eda jingina bayansa jikin d'ayan side na bed en,a kan fuskanta idonsa ya sauka,kallonta yake da yanda take baccin peacefully,hot cute lips nata idonsa ya sauka a kai,bai tab'a kallonta kamar na yauba,sai yanzun ne ya gano ainihin kyaun da Allah yayi mata.....
Tasbihi yake a zuciyarsa, yana ci gaba da kallon cute face nata,bai san lokacin da wani smile yayi escaping masa ba.......
Wani feelings ne ya shiga masa yawo a jiki,take jikinsa ya gama mutuwa........
Dai² lokacin mamy ta shigo,tana fad'in
"Son maza je ka huta,sai da safe"....
Murmushi yayi ya fito daga room en, yana mata sallama........
Tun shigansa room en kwanciya yayi,idonsa a rufe yana tuna moment ensu......
Murmushi ne keta escaping daga lips ensa,haka ranan ya kwanta cike da farin ciki.......
*★★★IN THE MORNING...........★★★*
Dai² lokacin da za suyi break, kowa cike da murnan ganin jiddah na sakkowa daga stairs suke kallonta, suna mata tsiyan gawa tak'i rami....
Murmushi kad'ai tayi ta nemi guri ta zauna,daddy ne ya fito nan suka shiga gaisheshi......
Amsawa yayi cike da kulawa yake tambayanta jikinta,amsawa tayi kanta a k'asa......
After sun gama break,suna zaune parlor daddy yayi gyaran murya tare da kallonta jabeer yana fad'in
"Yallab'ai baka mana bayanin ciwon dake damuntaba har take suma,gashi yau kuma mun ganta garau,wane siddabarun kayi mata?".....
Ya tambaya lokacin da gaba d'aya parlor akasa dariya........
Jin maganan da aka d'auko yasa jiddah ta zame jikinta ta nufi sama,mamy ce tace "ina zaki daughter?? Marairaicewa tayi ta nuna sama tana fad'in, " yanzun zan dawo mamy......
Kai ta d'ago mata,barin gurin tayi kamar wacce k'wai ya fashewa aciki......
Daddy ne ya juya ya kalli jabeer karo na biyu had'e da mai²ta tambayan da ya masa tun farko.....
Da k'yar ya iya masu daddy bayanin menstrual cramp ne,k'arin bayani yayi musu da irin matsalolin da zata iya fuskanta nan gaba,
Da hanyoyin da za a magance matsalan......
Sai bayan da ya gama tukun,daddy ya kalleshi yana murmushi, kafin ya kira sunansa,d'agowa yayi jin irin yanayin da daddy ya kirashi da shi ya tabbatar masa da maganar da zaiyi masa tana da muhimmanci......
Nutsuwa yayi yana jiran jin me dad en zai fad'a haka......
Akwai muhimmin al'amarin da ya faru kafin dawowarka,tunda abun yazo da haka bana buk'atar b'ata lokaci,dakatawa yayi kad'an....
Little ya kallah yana fad'in
"Maza kiramin y'ar uwarki"....
Amsawa tayi tana mik'ewa,tare suka dawo da jiddan, kowacce ta nemi guri ta zauna......
Ci gaba daddy yayi da fad'in
"Mun Riga mun yake hukunci ba tare da tambayar ra'ayinkuba,sai dan mun san hukuncinmu karb'ab'b'ene a gurin ku a ko wane irin lokaci".....
Jikinsu duk ya gama yin sanyi da maganar da yakeyi......
"Ba kan komai nake magana ba sai kanku",ya nuna jiddan da jabeer,gabanta ne ya fad'i jin maganar,kafin tayi wani yunk'urin tunani taji yana fad'in..
"Mun yake hukuncin had'aku aure,badan komai sai dan dacewar hakan da muka gani,da kuma sakamakon abundnt muka fuskanta kuma akan ku kuna son juna.....
Jin maganar sukayi kaman wani thunderstorm da sauri suka kalli juna cikin tashin hankali..............
*~Fad'owar alk'alamina yasa ni dakatawa.....~* ๐ณ๐ณ๐ณ
*~Keep Following Fan's...~* ๐๐๐
*_REAL SMASHER ๐ค๐ป๐_*
[21:50, 12/16/2017] Sister Hawwa: ๐ ๐ *RAYUWAR WANI......*
_{ฦกลษ'ส lฤฑสษ...}_
๐ ๐
๐น
*สษฌฦกrแง ฤ
ลษ แฟณwrฤฑษฌษฌษล...*
*แชแง.*
_HAWWA M.U {SMฮSHฮฃR}._
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)........*
*℘ฤ
ษ ษ 43↔44*
Tun da daddy ya fara maganar, basu sake fuskantan me yake cewa ba har ya gama....
Sun dai tsinci kalamansa na k'arshe da yake cewa "Allah yayi muku albarka,nasan dama bazaku bamu kunyaba".....
Kan little ya juya yana fad'in "kar kiyi tunanin babu ke cikin wannan maganar,idan da wanda kike so ki sanar da shi mahaifanki na son ganinsa,nafi son na aurar da ku lokaci guda,Allah yayi muku albarka, zaku iya tafiya",
Nan ya sallame su...
Da k'yar jabeer ya bar gurin,kasancewar shi ya fara tashi a gurin,d'akinsa ya nufa,yana shiga ya kwanta kan sofa,idanunsa a kulle,tunani yake sonyi kan maganar daddy,shi toma ta yaya za ace suna son juna,ya tab'a nuna wani abune da yake bayyana yana son nata ko kuwa?
Gaba d'aya ya kasa tuna komai,sai dai yasan shi ba wai yana k'inta bane,Kuma babu abun k'i a tare da ita......
Haka ya yini cikin tunane² wanda daga k'arshe dai mafita d'aya ce,gare shi itace amincewa da auren....
Ga jiddah kam tun da suka koma d'aki suka zauna kowa da tunanin da yake akan maganar....
Little duk ta dameta da maganar da daddy yace har ita,shiru tayi mata can da ta isheta ta watsa mata harara cikin fad'a² tace,
"To wai me kike so nace ne,in ce miki karki yi abunda daddy yace ko kuwa yine baki da niyya,kinbi kin dameni tun safe sai maimaita magana d'aya kike,ki k'yaleni nima dan Allah nayi tunani akan nawa prob en please".....
Tana gama fad'a ta hau kan bed ta kwanta had'e da rufe ido.....
Matsowa little tayi kusa da ita,cikin sanyin murya take fad'in
"Kiyi hak'uri y'ar uwata banyi haka dan na b'ata miki raiba,tun tasowarmu muka kasance tare,bama k'aunar abunda zai shiga tsakaninmu,me yasa yanzun bazaki fuskantar dani hanyan da zanbi na samo mafita ba? Me yasa kike k'ok'arin yin fushi dani".........
Kuka ne yaci k'arfin ta kan dole tayi shiru badan ta soba.....
Jin she²k'an kukanta yasa Jidda saurin mik'e wa ta rungumeta....
Bata yi magana ba sai patting bayanta da take,cikin yanayin damuwa ta fara magana....
"Hak'uri za muyi yanzun duka mu nemi abunyi,amma ina zuwa ta fad'a lokacin da ta saketa"...
Fita tayi,bata jima ba ta dawo da phone en mamy a hannunta tana fad'an "bari na kira sis hubbey duk yadda za ayi muna buk'atar had'uwa da ita,if possible Muje gidansu a yau".....
Wayanta ta kira tana picking,
Ta fara tambayanta,
"Ello sisi are u at home?"
"Yeahhh!!" Ta bata answer
Ok ki jira zuwanmu anjima.....
Tana gama fad'a tayi hanging kiran...
"Oyaaa tashi mu shirya,yanzun bamu da lokacin b'atawa"...
Tana gama fad'a tayi toilet, har ta fito little tana zaune ta buga tagumi kamar wanda aka ma mutuwa..
Tun da ta fito take mata magana,ganin tak'i kulata,ta matso kusa da ita,yanayin da ta ganta ya tabbatar mata da ta dad'e da yin zurfi cikin tunani...
Tab'ata tayi,nan ta d'an firgita kafin ta kalleta da murmushin da bai kai zuciya ba....
Ki ta shi muyi sauri kar mamy ta hanamu fita kinsan idan yamma yayi sosai bamu da halin fita koh,Kuma yanzun ba skul bare mu had'u a can tomorrow.....
Cikin sanyi jiki ta mik'e, kallonta kawai jiddah tayi,kafin ta jijjiga kai,ta juya ko kwalliya bata da lokacin yinsa,cikin sauri ta d'auki dogon gown ta saka,Rolling tayi da veil had'e da janyo flat shoe tasa,zama tayi bakin bed tana jiran fitowan little....
Sai da ta sake mata magana sannan ta samu ta fito,da taimakonta ta samu ta shirya,cikin rashin kuzari suka fice...
Babu kowa parlor, d'akin mamy suka nufa nanma bata nan,a kitchen suka tarar da ita,fad'a mata sukayi,da farko hanawa tayi,ganin yanda suna dage suna begging nata kafin ta amince...
Cikin sauri suka bar gidan,sai red blocks.....
Gidan babu kowa sai ita d'aya, a parlor suka zauna,nan suka zayyane mata komai......
Dariya tasa ta mik'e tsaye tana juyi cikin parlor had'e da tafa hannunta,tana fad'in "ni banga abun damuwa a cikin wannan maganar ba gaba d'aya, men's laifin yah boss kin san da cewa shi ne irin guy en da y'an mata ke yayi,kina yin saken da ya kufce miki sai dai ace miki sorry,amma a nawa shawaran kiyi addu'ah da kuma biyayya,karshe zaki tsinci *RIBAR BIYAYYA* (sweerei sawwamas book)....
Kallonta suka tsaya yi,kafin cikin jin haushin dariyan da ta sake sawa little ta mik'e,hannun jiddah ta kama suka nufi hanyan fita daga gidan....
Da gudu ta biyo bayansu tana kiransu,k'in kulata sukayi,suka ci gaba da tafiya.....
Saurin shan gabansu tayi tana basu hak'uri, da k'yar ta samu suka dawo...
Dariyan ta had'iy,zama suka yi suna fuskantar juna,kafin cikin nutsuwa ta fara basu shawaran da take ganin shi ne yafi.......
Sosai zuciyansu ya samu nutsuwa da maganarta,har kowacce ta saki jiki suna ta dariya,bayan sun gama firansu suka mik'e tare da yi mata sallama suka nufi hanyan komawa gida.....
Kasancewar yau basu taho da motar ba,yasa suka fito,a k'afa suke tafiya suna firansu cikin nishad'i kamar basu suka fito da damuwa ba daga gida.....
Sun fito suna ta tafiya suna dariya,kasancewar an tuna rayuwarsa secondary school da irin tsiyan da suka yi lokacin,mutum suka gani tsaye a gabansu ya nad'e hannu yana faman smirking......
Kallonta kawai sukayi suka d'auke kai,tafiya suka ci gaba da yi,jiddah ce ta tab'a little cikin fad'a tace
"Sisto kamar naso na tab'a ganin wannan face en some where else"....
"Uhmmmm!! Maybe",
Abunda ya fito daga bakin little kenan,dai² suna k'arasowa bakin titin....
Tsayawa sukayi suna tsai da tricycle..
Sun jima suna tsayarwa amma duk wanda ya taho wani a cike wani Kuma yace ba can zaijeba.....
Gajiya sukayi da tsayawan,duk face ensu ya nuna hakan...
"Ai ga irinta nan,ni ban san me ya kaiku fitowa without car ba,yanzun kawai mu koma idan mukayi sallah zuwa time en mama sun dawo,kunga sai driver ya kaiku"...
Ta fad'a confidently.....
Wani mungun birki yaja a gabansu wanda yasa suka yi saurin d'agowa,suna bin motar da kallo....
Fitowa yayi yana takowa a hankali har ya zagayo gabansu...
Sallama yayi musu,jiddah da hubbey suka amsa,amma little d'auke kai tayi,gaisawa sukayi,duk maganar da suke tana jinsu amma sai ta dad'a matsawa gefe....
Kallonta yayi,kafin ya juya gurinsu hubbey da suka sakar masa fuska,inda zasu ya tambaya yana sake kallonta side en da little take...
Da k'yar ya samu suka fad'a masa,sai da suka sha artabu kafin ta amince ta ta ko wajen Motan,ko da little taga jiddah na k'ok'arin shiga back seat,da sauri ta fizgo hannunta,tayi sauri ta shige,had'e da rufewa....
Da ka hubbey ta mata nuni kan tayi hak'uri ta zauna front seat en, shiga tayi suka yi sallama......
A bakin get ya tsaya dai² lokacin da jiddah ke masa godiya ta bud'e motar zata fita...
Tsayar da ita yayi yana mata maganar little,ita kam ta tsufa da shigewa ciki,dan tun tsayawarsu a gurin ta fice....
Babu komai in sha Allah zan mata maganan idan na shiga yanzun, zuwa nan da one week,duk yadda mukayi sai kaji....
Har ta juya da niyyan fita karo na biyu,ya sake tsayar da ita yana fad'in
"Ammm!! Amma da kin bani ko da phone en kine,idan na dawo sai nayi calling naki ba,duk da zan hak'ura ne dan ba yadda zanyi ne,amma one week yayi min nisa......
Da murmushi ta juyo,kayi hak'uri,mukam ba a bamu daman amfani da phone ba a gida,idan ka zo kayima gateman maganar zai sanar mana....
Godiya yayi mata,sukayi sallama ta fito daga Motan tana murmushi tana waving masa...
Fitowan jabeer daga gidan zai tafi masjeed,lokacin yana sauri har an tada sallah.....
Dai² lokacin idonsa ya sauka kan Jidda dake d'aga ma guy en hannu,dukkansu da murmushi a fuskansu....
Tsayawa yayi yana kallonta da mugun mamaki a fuskansa,tsayawa yayi ya kasa tafiya,har Motan ya bar line en...
Juyawan da tayi da niyyan shiga gida,idonta ya sauka akansa,yanayin yanda ta Ganshi yayi matuk'ar bata tsoro..
Cikin tsoro take takowa a hankali har tazo daf da shi.............
*~Keep Following Fan's...~* ๐๐๐
*_REAL SMASHER ๐ค๐ป๐_*
[20:25, 12/17/2017] Sister Hawwa: ๐ ๐ *RAYUWAR WANI......*
_{ฦกลษ'ส lฤฑสษ...}_
๐ ๐
๐น
*สษฌฦกrแง ฤ
ลษ แฟณwrฤฑษฌษฌษล...*
*แชแง.*
_HAWWA M.U {SMฮSHฮฃR}._
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
_Ina matuk'ar godiya da sadaukar min page da kikayi,y'ar uwa kuma masoyiya,Allah ya k'ara miki baseera hazak'a,hikima,tabbas kin isa a kiraki da sunan Masoyiya,ina godiya da k'aunarki gareni *QUEEN HAUWA HAUSY ๐ธ๐ป* Writer of *KURMIN DAJI...*_
_SAK'ONKU A KULLUM YANA ISOWA GARENI MASOYANA,KUMA MASOYA RUBUTUNA,A KODA YAUSHE INA ALFAHARI DAKU A DUK INDA KUKE,SOYAYYA TARE DA K'AUNARKU ACIKIN JININ JIKINA TAKE GUDANA......I SO MUCH LOVE'S U...._❤
_THE WHOLE PAGE IS FOR U GUYSSSSS..... *RAYUWAR WANI FAN'S*......_
๐น๐น
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)........*
*℘ฤ
ษ ษ 45↔46*
Ta gefensa ta ke k'ok'arin rab'awa za ta wuce,dai² ta zo kusa da shi tana niyyan giftawa...
Fizgota yayi ta fad'o jikinsa,cikin kaushin murya yake magana,
"Daga gidan wace uwar kike yanzun,waye wanda na ganku tare,mene alak'arki da shi???"
Gaba d'aya yanayin sa ya birkice,ya koma mata abun tsoro,idanunsa sun koma jaa saboda bacin rai, gaba d'aya ya gama firgitata......
Kukane ya kwace mata dai² lokacin da ta kasa magana....
Dafe kansa yayi saboda kukan da take,sakinta yayi ya shiga jan hannunta,cikin gidan suka nufa, ta parlor suka ratsa suka wuce,har sai da ya danganata da bedroom ensa,nan ya saketa,juyawa yayi ba tare da yayi magana ba,ya ja k'ofan ya rufe,ya sake juyawa ya fice daga gidan.....
Lokacin da ya fito mamy na zaune kan idonta komai ya faru,tana masa magana,kasancewar baya cikin hayyacinsa yasa ko jinta ma baiba,ya shige,kafin ya sake fitowa ya sake fita ta gabanta.....
Binsa tayi da ido bata ce komaiba,sai yanzun taga yanayin da yake ciki,har ya fice bata sake masa magana ba...
Koda ya je masjeed en tuni an Idar da sallah,guri ya nema cike da jin haushin rasa jam'i yayi sallan...
After ya idar yaci gaba da zama yana addu'ah cikin masallaci,har akayi ishaa,sannan ya kamo hanyan dawowa gidan...
Tunda ya rufeta cikin d'akin, ta tsaida kukan,kanta da ke sunkuye ta d'aga tana k'arewa d'akin kallo,sai yanzun ta fahimci inda ya kaita...
'D'akin a tsaftace,sai k'amshin da ke tashi,ko wata macen albarka gurin tsafta....
Katse tunanin tayi ta nufi toilet ensa alwala tayi ta fito har ta idar da sallah bata ji shigowarsa ba,tana zaune har aka idar da isha,ta shi tayi tayi sallah....
Ci gaba tayi da zaman jiran gawon shanu....
Fitowansa daga masallaci ya nufo gida,ya rasa me ke masa dad'i a yau,banda siraran tsaki babu abunda yake....
Har ya k'araso gida...
A parlor ya yada zango,gaba d'aya yama manta da ya ajiyeta a d'akin sa....
Mamy da fitowanta kenan,ta idar da sallah,ta tarar da shi zaune,yayi powering TV, amma hankalinsa gaba d'aya baya kan abunda yake kallo....
Kusa da shi ta zauna,kansa ta shafa,cikin yanayin damuwa ya kalli side en da take,kamar wani k'aramin yaro ya Shiga juya kai,kafin ya fara magana,
"Mamy me yasa zata tsaya da wani a gabana,
Why! Why!! Why!!!....
Cikin tsawa² yake maganar wanda har little dake sama sai da tayi saurin fitowa daga d'aki....
"Kuma bayan tsayawa da shi da tayi har da exchanging smile nd after oll,she wave at him.....
Why she do oll dis a lot of thing to him??"
Why!!?
Ya sake tambaya lokacin da ya had'a kansa da kujeran..
Idanunsa sun gama rinewa da b'acin rai,kamar yanzun abun ya faru.....
Mamy kam kasa cewa komai tayi sai kallonsa da take,ta tabbatar He's in deepest jealousy nd he already losses his temper...
Addu'ah ne fall bakinta,tana rok'on Allah ya yaye masa, wannan za a sha fama irin wannan matsanancin kishi haka,wacce zai aura za ta sha fama...
Mik'ewa tayi ta nufi fridge, ruwa mai sanyi ta dauko had'e da glass cup..
In da yake ta dawo ta zauna,dan ta san duk wannan abun da yake kishi ne yake damunsa.....
Ruwan ta mik'a masa ya karb'a ya sha,sake kwantar da kansa yayi idonsa a rufe.....
Sai ajiyan zuciya ya saki,ya jima a haka,kamar mai bacci...
Sai da mamy ta tabbatar da ya samu nutsuwa,sannan ta fara magana tana shafa kansa....
Cikin sanyi murya ta fara magana,Haba son sai kace ba kaiba,ina ka kai iliminka,tunaninka da wayewarka???
A duk lokacin da kake cikin fushi,abu na farko da ya kamaceka shine yaiwata fad'in *"hasbunallahu wani'imal wakil....Allahumma inniy a'uzu bika minal hammi wal-huzn,wal-ajazi,wal-kasal,wal-bukhli,wal-jubn,wa-a'uzu bika min galabatid-daini wa k'ahari-rihal....(au)wa dal'iddaini wa galabatir-rijal...*,me yasa ka kasa dai² ta nutsuwarka,ka kuma kasa had'iye fushinka???
Ya kamata kafin ka yanke ko wane irin hukunci,kaji dalilin mutum na aikata hakan....
Yanzun ina ka kai jiddan,tun d'azun da ka shigo nayi magana baka amsaniba....
Sai yanzun ya samu zuciyarsa ta fara sauk'i daga mugun rad'ad'in da take masa,sakamakon mai²ta addu'o'in da mamy ta tunasar da shi....
Tunawa yayi ya fa kai ta bedroom en sane,tun d'azun....
Kallon mamy yayi,ya kuma juya ya kalli hanyan stairs, mik'ewa yayi ya bi hanyan room en nasa...
Dai² bakin door en ya tsaya ya zaro key ensa,bud'ewa yayi ya Shiga....
Zaune ya ganta ta buga tagumi da hannu biyu,fuskanta duk ta tasa,saboda kukan da tayi...
Daf da ita ya tsuguna,hannunsa ya d'ora kan laps enta...
Firgita tayi,tayi saurin d'agowa ta kalleshi,mugun tsoronsa take yi yanzun,a tsorace ta fara ja baya daga kan gadon,tana neman hanyan guduwa,kamota yayi sosai ya rik'e ta,irin rik'on da ba zata iya kwacewaba....
Kuka tasa, gaba d'aya ya dad'a firgitata.....
Zama yayi akan bed en had'e da rungumeta tsam a jikinsa,yana hura mata iska a kunnen,yana patting bayanta,har ya samu ta tsaida kukan sai ajiyan zuciya da take saki da k'arfi,saboda jimawa da tayi tana kuka...
Sai da ya tabbatar da tayi shiru,sannan ya saketa,hannunsa ya sa ya goge mata hawayen da ke kan fuskan nata....
Mamakinsa take,gani take kamar ba yah jabeer da ta saniba,gaba d'aya ya rikitata,ko iya yau aka barta da al'amuransa sun sata a shock....
Sauka yayi daga kan gadon,Sai da yaje bakin k'ofar d'akin,ya juya kad'an ki sakko mamy na son magana,daga haka ya juya ya fita.....
Sai da ta d'an jima kad'an kafin ta samu damar sakkowa ta fito a hankali,cikin sanyin jiki take tafiya kamar kazar da k'wai ya fashewa a cikin.....
A parlor ta tarar da mamy gefe kuma yah JB ne,guri mamy ta nuna mata....
Kusa da k'afanta ta zauna a k'asa,kanta ta d'ora akan k'afafunta,tana wasa da yatsun hannunta....
Nasiha mai ratsa jiki mamy tayi musu,kafin ta juya kan jiddah tana fad'in...
"Daughter ina son ki fadamin waye wanda ya kawo ku d'azun, me yasa baku fita da mota ba?....
Kukan dake k'ok'arin sake dawo mata,ta fara kokawar mayarwa...
Sai da ta sha fama kafin tayi nasarar dai²ta kanta...
Cikin sanyinta ta fad'awa mamy,bayanin duk abunda ya faru,tun daga ganinsu har zuwa kawo su da yayi gidan da kuma ganin da yah Boss yayi musu....
Tana gama fad'a kukan ya sake k'wace mata,sai sheshshek'an kukanta dake tashi a gun.....
"Ya isa daughter, nasan dama bai tsaya yayi bincikeba ya yanke hukunci, ina fatan kuma ba dukanki yayiba,dan yanzun zan sab'ar masa"....
Ta fad'a like seriously...
Sai lokacin ta d'ago ta kalleshi lokacin da yake murmushi wanda ya bawa kyawawan hakoransa da wushirya ta ratsasu damar bayyana,baya ga beautiful point nasa daya lotsa.....
Wani kyau ya mata,ga girma da yake k'ara yi mata a kowane lokaci....
"A'a mamy,babu abunda yayi min,a ganinama koda dukana yayi mamy ya cancanci yayi hakan,a matsayinsa na yaya gare mu,hak'k'i ne akan sa ya bamu duk wata kariya,daga abunda yake ganin zai cutar damu,ko zai zame mana matsala"....
Maganar da ta fito daga bakinta kenan,wanda tayi matuk'ar bashi mamaki,sai yanzun yaji duk wata kunya ta rufe shi,akan abunda ya aikata mata..........
๐ ๐ *~#Teem J²~...* ๐ ๐
๐ ๐
๐น
*~Keep Following Fan's...~* ๐๐๐
*_REAL SMASHER ๐ค๐ป๐_*
[21:23, 12/19/2017] Sister Hawwa: ๐ ๐ *RAYUWAR WANI......*
_{ฦกลษ'ส lฤฑสษ...}_
๐ ๐
๐น
*สษฌฦกrแง ฤ
ลษ แฟณwrฤฑษฌษฌษล...*
*แชแง.*
_HAWWA M.U {SMฮSHฮฃR}._
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
_SORRY FAN'S DA RASHIN JINA DA BAKUYIBA JIYA,CHAT ENA YA BANI MATSALA JIYA,KUMA WAYAN SAI A SLOW.......REALLY LOVE U GUYSSSSS....๐๐๐_
*#ANA MUGUN TARE* ๐ค๐ป๐ค๐ป๐ค๐ป
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)........*
*℘ฤ
ษ ษ 47↔48*
Nadama game da dana Sani fal zuciyarsa....
Godiya yayi ga Allah da yasa baya cikin jerin mutanen da anayi musu laifi sai duka.....
Nasiha mamy ta sake musu,kafin tace
"Ku tashi na sallameku"...
Shi ya fara mik'ewa ya nufi hanyan stairs...
Kallon side en da take yayi,yana murmushi har ya kai bakin staircase ya fara haurawa...
Tashi tayi da nufin zuwa d'aki don a lokacin jinta take gaba d'aya a takure...
Toilet ta nufa da niyyan tafiya ta watsa ruwa ajikinta....
Tuna yanda suka k'arke da yah Boss d'azun har wani sweat ne ya dinga d'iga a jikinta,saboda tsoron yanayin da ta gansa ya bata,duk da ba zafi garin.....
Shigowan daddy gida ya tarar da mamy zaune,draman su jabeer duk ya dameta....
Ko shigowansa bata saniba,sai da yazo kusa da ita....
Tab'ata da yayi ta dawo daga duniyar da ta lula.....
Ajiyan zuciya da tayi,yasa ya zauna kusa da ita,kafin ya fara tambayanta,
"Meke damunta da take irin tunanin haka?"
Labarin abunda ya faru yau kuma yanzun ba da jimawa ba,ta bashi,dariya yayi irin tasu ta manya,yana jinjina al'amarin....
"To ai kinga yanzun sun dad'a tabbatar mana da soyayyar da ke tsakaninsu....
Fatan dai Allah ya tabbatar da alkhairi aciki"....
Furucin daddy kenan da ya kama hanyan room en sa.....
Hiran suka d'ora akan yanda al'amura suje faruwa da wad'anda zasu faru nan gaba......
Tana k'arasa shiga d'akin little tayi tsalle ta diro gabanta,tana tambayanta me ya faru a parlor???
Hararanta tayi tana fad'in "me yasa bakije kin jiba da kanki".....
Tana gama fad'a ta fad'a toilet, bayan ta gama shiryawa,nighty enta ta zura ta haye bed,had'e da fara karanto addu'o'in kwanciya bacci......
Da mamaki little ta kalleta,ganin bazata iya shiruba yasa ta ce
"Me kenan kike shirinyi,kwanciya tun yanzun ko dinner fa bakiyiba".....
Ina ruwanki da cikina,ko naci ko kar naci wannan ni ya shafa,kin jefani a wak'i'a kin gudu kin barni,Allah yaso ni da na sha bugu yau hannun yah Boss....
Dariya ta fara har da rik'e ciki,saboda mugunta,tana fad'in ai kece ba abunda zai miki,d'agowa tayi tana kallonta a k'ule ta fara magana
"Wallahi ko ki denamin dariya ko idan na tashi ramawa sai kinyi kuka"....
'Dif little tayi harda rufe bakintan,tasan kad'an da aikinta......
"Amma sis ba yah Boss zaki fad'awa ba ko?"
Ta tambaya.....
Ohoo! koma wa zan fad'awa ruwana ne ai.....
Juyawa tayi ta sake kwanciya,little dake tsaye ta juya ta fice daga bedroom en....
A parlor ta tarar da su gaba d'aga,yau basa jin cin abinci a dining,sun baje nan,warmers en a Jere a nan cikin parlor....
Yah Boss da yayi tunanin jiddah ce ta sakko,ya juya da sauri,yana ganin little ya juya had'e da sakin karamin tsaki.....
Koda mamy ta ganta ita d'aya,tambayanta tayi ina jiddan,karyan ciwon kai tayi,tasan ko kiranta akaje yi ba fitowan za tayiba.......
Ga yah Boss kam Ya'u ji yake kamar yana had'iyan magani,dan rashin ganinta a gurin dinner,duk da yasan haka kawai tak'i fitowa,babu wani ciwon kai,har aka gama bai ci wani abincin kirkiba,ya mik'e yabar parlor.....
Ko da ya haura stairs d'akinsu little ya nufa,k'ofan ya tura tare da sallama....
Yanda little ta barta haka take,jin muryansa yasa ta saurin jan duvet ta rufe jikinta har kanta bata bariba,ta k'udunduna gaba d'aya,k'irjinta banda dukan 100² babu abunda yake......
A bakin bed en ya zauna tare da mata magana,amma ko Motsi tak'i yi,bare yasa ran zata tashi.....
Nasan ba bacci kikeba,kina jin duk abunda nake fad'a,ko ki ta shi ko kuma yanzun d'agaki da kaina......
Babu shiri ta mik'e zaune,tare da dad'a k'ank'ame blanket en.....
Murmushi yayi mai sauti,kanta a k'asa tak'i yadda su had'a ido.....
Tambayan dalilin rashin zuwanta dinner yayi,amma ta kasa magana,duk sonsa da tayi magana k'i tayi haka ya tashi ya fita bayan ya mata sallama.....
Ranan itama little bata jira yin firaba ta haura sama.....
Tana zuwa taga yah Boss ya fito daga room en sai wani mugun smile yake.....
Kallonsa ta dinga yi kamar wanda ya zame mata sabuwar halitta....
Yana d'agowa yaga irin kallon da take masa,harara ya watsa mata,yayi gaba abunsa......
Kanta a k'asa har ta shige d'akin, lkram sarkin bacci har tayi sana'ar tata.....
A gurguje itama ta kammala shirinta na kwanciya, ta haye kan bed en.....
Sai a lokacin jiddah dake karanta *RICH DAD POOR DAD* mugun yawansa yasa ta kasa gamawa har yanzun,ta rufe,tare da juyawa tace a kwai magana ba bacci za kiyiba....
Mik'ewa little tayi daga kwanciyan da tayi tana sauraronta.......
Kan guy en d'azun ta fara magana,da yadda sukayi duk tayi mata bayani...
Ke ni rabu dani da wannan maganar karki sa kaina yayi ciwo....
Sakin baki jiddah tayi tana kallonta,bata sake ce mata komaiba,ta juya ta kwanta.......
A zuciyanta take sak'a maganar da ta mata yanzun,da kuma irin wad'anda sukeyi,yanda little ke zak'ewa akan tana son aure amma yanzun ji abunda ta fad'a,kamar ta bugeta haka take ji.....
Amma a ranta ta k'udure abunda za tayi,za tayi maganin little.......
Bata sake d'aga maganar ba tun daga lokacin,ta rabu da ita,sai dai k'udurin maganinta,duk lokacin da ta sake mata magana akan tana son aure......
Da safe ko da suka tashi,a kitchen jiddah ta tarar da mamy tana aikin break,kama aikin tayi itama,sunata fita kasancewarsu mamy ta mayar abokan firanta,nan jiddah take bata labarin abunda ya faru jiya da yanda suka yi da little ta dad'a maimaita mata......
Dariya tayi bata ce komaiba har suka kammala had'a break en.....
Lokacin da suka gama break kafin daddy ya fita,mamy ta tarar da shi,nan ta sanar masa abunda jiddah ta fad'a mata.....
Shima dai dariya yayi,zama ya sake yi,zama itama mamy tayi.....
Kafin ya fara magana.....
"Duk abunda ake ciki a yanzun,idan shi yaron ya dawo,jabeer ya same shi suyi magana duk yanda sukayi zanji idan gaske yake,to bama son b'ata lokaci akan al'amarin"......
Amsawa mamy tayi kafin ta rakashi har k'ofar parlor,sannan ta dawo ciki.......
Tana shirin shiga d'aki,ta tarar da jabeer yana sakkowa shima,tsayar da shi tayi,har sai da suka gama maganar da zasuyi akan sak'on da daddy ya bayar....
Amsawa yayi,yayi mata sallama nan ya bi bayan daddy zuwa office......
*★★★ONE WEEK LATER...★★★*
Kamar yadda sukayi alk'awari,ranar ta kasance ta alhamis,da yamma suna zaune parlor, gateman ya shigo cikin hanzari,nan ya fad'a sak'on da aka turoshi.....
Mamy ce tayi magana tare da bashi umarnin a bud'e parlorn bak'i.....
Har jiddah ta sakko zata tafi,little na mak'ale a d'akin tana kallonta,ba tare da tayi yunk'urin bintaba,tana shirin fita daga parlor jabeer dake k'ok'arin shigowa ya tsaya cak, ganin irin kwalliyan da tayi.....
Tunanin da yake yi bai bashi damar tsayar da itaba,har takai bakin parlor bak'i.....
Ta d'aga k'afanta kenan za ta shiga ya tsaida ita,lokacin da ya dawo daga duniyar tunanin.......
Tsayar da ita yayi,haka ta tsaya,tayi still a gurin,har ya k'araso,baiyi magana ba,ya wuce gaba har cikin parlor.....
Baiyi tunanin da mutum a ciki ba sai da ya shiga......
Kishi ne ya motsa,ganin mutum zaune,nan zuciyarsa ta fara tafasa,me wannan abun ya zo zaima princess ensa,ba dai sonta yake ba, idanunsa har sun fara canja colour, haka ya daure ya k'araso tare da mik'a masa hannu suka gaisa,kafin tambayansa ya biyo baya,duk cikin dauriya yake aikata komai......
Tana tsaye a gurin ganin shigansa yasa ta juya ta koma cikin gida....
Ko da mamy ta tambayeta fad'a mata tayi jabeer na tare da shi......
Bayani guy en ya masa,tun daga had'uwansu da dalilin zuwansa yayima jabeer...
Sai lokacin hankalinsa ya kwanta,har ya saki jiki suka sha fira....
Kamar wasu friend haka sukayi ta fira rana,sun jima tare har ya tashi tafiya....
Sai da ya rakasa har bakin motansa,nan yake cewa
"Eyyahh!! Friend gashi mun had'u ba tare da sanin juna ba,
Ni sunana jabeer".....
Yah Boss ya fad'a yana kallon guy en da murmushi a face nasa......
"Umar farouk shi ne sunana ni kuma", guy en ya fad'a.....
Ohhh!! Nice to meet u....
Yah Boss ya fad'a......
Nan sukayi sallama da juna,har sai da ya fita tukun,jabeer ya juya ya nufi cikin gidan.......
0 comments:
Post a Comment