Ido ta sake bud'ewa tana son gasgata zatonta da abunda idanunta suka gani...
Anya kuwa ta ga dai²?....
Kai wannan ba gaskiya bane,ido ta shiga murzawa,amma me zata gani tana bud'ewa ta sake yin arba da k'afar JIDDAH nad'e a cikin bandage.....
*INNALILLAHI WA-INNA ILAIHI RAJI'UN!!!*
A bunda ta shiga maimaitawa kenan,har zuwa lokacin da ta ji zuciyanta ta fara sauk'i.....
Har su DADDY suka fito tana rik'e da k'ofan motor en,ta kasa cikawa bare su samu su fito da JIDDAN zuwa cikin gidan.....
Ta jero mata sannu yafi a k'irga,amma duk da haka bata matsa daga gurin ba....
DADDY ne yayi k'arfin halin yjn magana
''Hajia da kin matsa ai ya shiga da ita cikin gida ko,sai ki ci gaba da kallonta''.....
Da k'yar aka samu MAMMY ta matsa YAH BOSS ya fito da ita daga cikin motor en ya nufi cikin gida,su kuma suna binsu a baya....
Bama kamar MAMMY da tafi saurin binsu duk inda YAH BOSS ya d'auke k'afarsa nan take mai da nata....
A parlor ya direta akan rug en gurin,pillow MAMMY ta kawo aka jingina mata a bayanta.....
Sai lokacin MAMMY ta shiga sake jero mata sannu,fuskanta duk tausayi ya cika ta....
DADDY kam da YAH BOSS y'an kallo suka koma,yanda MAMMY ta shiga ji da JIDDAH tamkar kwai....
**********
Ko da LITTLE ta shigo gida lokacin bayan sunyi sallama da FAROUK akan zai dawo zuwa dare don yayima DADDY barka da zuwa....
Ta shigo da murnanta ta haura sama,rashin ganin SISIN nata shi yasata jin babu dad'i,ta tabbata sun tafi....
Haka tayi wanka,ta kwanta kan bed take bacci yayi gaba da ita....
Har suka dawo daga hospital tana sama bata san wainar da ake toyawa ba....
Gajiya da kwanciyan tayi,tunawa da batayi sallan Asar ta juya tana duba wall clock ensu....
Da sauri ta mik'e ta nufi toilet....
Sai da tayi wanka tukun ta d'auro alwala,bata tsaya shafa ba ta zura dogon riga,ta kabbara sallah....
Yunwa ne taji yana neman lahanta mata kayan ciki ba shiri ta ajiye hijab en tayo waje....
Har ta gama sakkowa idanunta basu kai kan mutanen da ke parlor en ba........
Burinta kawai ta samu abunda zata sawa cikinta.....
**********
''Wai ni kam garin yaya wannan abun ya faru ne?''
Tayi tambayan tana kallonsu DADDY....
YAH BOSS ya nuna mata da hannu.
Saboda haka ta mai da hankalinta kansa..
Bai san da shi take magana ba sai da ta furta
''Da kaifa nake JABEER''....
'Dagowa yayi yana kallonta kafin cikin sanyin jiki ya furta
''TSAUTSAYI ne MAMMY kuma Allah ya K'ADDARA faruwan haka''...
Hannu ta d'aga masa tana fad'in ''nasan da haka,cewa nayi garin yaya hakan ya faru?''...
''MAMMY nimafa bansan ya akayi hakan ta faruba coz na rigata yin gaba''......
Ko kafin ya k'arasa MAMMY ta katseshi da fad'in
''Zancen banza kenan,kai kana babba amma kai ne a gaba''....
Nan ta shiga fad'a ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba,tamkar zata ari baki haka tayi ta masa fad'a.....
Kansa yana k'asa ko tari baiyiba sai da ya tabbatar ta gama,sannan ya shiga bata hak'uri.....
Banza tayi da shi,bata tankasa ba....
Duk abunda suke DADDY na zaune ko 'A' bai furta ba har tayi ta gama,murmushi kad'ai yayi....
**********
Maganar MAMMY kad'ai ta tsinkayo acikin kanta wanda ya sata juyawa ta kalli gurin.....
DADDY ta hango zaune yana murmushi,da gudu ta nufi gurin sai da ta je daf da gurinsa ta ankara da YAH BOSS tsaiwa tayi chak tana washe baki...
Cikin sanyi ta k'arasa tana fad'in ''barka da dawowa DADDY''....
'Dagowa sukayi gaba d'aya suna kallonta...
'Daya bayan d'aya ta shiga kallonsu,kamar yanda suma sume kallonta....
Kan k'afar JIDDAH dake mik'e ta sha rawani da bandage idonta ya sauka....
Zare ido tayi,cikin kid'imewa ta nufeta....
Ko kafin ta k'arasa hawaye har ya soma ambaliya a face enta....
IKHRAM da ta shigo da sallamarta,duk jinta take a gajiye....
Kan sofa ta samu ta cilla skul bag enta,tana zare socks en k'afanta....
Sheshshek'an kukan LILLTE ya ratsa kunnenta...
Kallon gurin tayi nan idonta sukayi arba da abunda ba tayi tsammaniba...
Mik'ew tayi ta nufesu babu tambaya itama ta bi bayan LITTLE.....
Kuka suke kamar sune suka ji ciwon ba ita ba.....
Ita kam ta zuba musu ido tana kallon ikon Allah,ta kasa ce musu komai,sai da sukayi mai isar su,dan kansu sukayi shiru.....
DADDY ne ya kalleta bayan sun gama shan kukan nasu da fad'in ''y'ar gidan MAMMY bakya gane kowa ne?''...
Suprisingly ta kalli inda tajiyo maganar...
DADDYN dai ta gani yana mata murmushi....
Ihu ta fasa,tana tafe hannu take fad'in
''Allah DADDY ban san ka dawoba,an dawo lapia?''...
''Lapia k'alau,ya makarata?''....
''Babu dad'i'' ta fad'a tana b'ata rai....
Dariya yayi,ba tare da ya sake magana ba...
Haka suka ci gaba da zama jugum,motsi kad'an JIDDAH za tayi suna faman jera mata sannu.....
MAMMY ce ta tashi da taimakon LITTLE da IKHRAM suka shirya dinner...
Su JIDDAH ana zaune,sai dai tayi ta binsu da kallo...
Koda lokacin sallan maghreb yayi,a inda take zaune MAMMY ta taimaka mata tayi alwala,tana daga zaune tayi sallanta....
Ranan kam a nan cikin parlor sukayi dinner,after sun kammala aka dasa fira,har zuwa time en bacci...
Koda DADDY yace ma YAH BOSS ya kai JIDDAH d'aki ba a son ran MAMMY hakan ke faruwa ba,kawai dai tayi shiru ne....
Haka ya d'auketa zuwa bed room en su,after ya kwantar da ita,ficewa kad'ai yayi ba tare da yayi magana ba....
Da ido JIDDAH ta rakashi har ya k'arasa ficewa daga d'akin....
Murmushi tayi gano irin yanda yake had'e rai idan an sashi d'aukanta....
Kanta ta d'ora kan pillow ta lumshe idanunta,tana shak'an perfumes ensa da sukayi saura a jikinta,kamar wacce aka shafawa...
************
Ganin kowa ya watse parlorn hakan ya sa MAMMY tabi bayan mijinta....
Abun duniya duk ya isheta,akan mene za ana sa JABEER yana d'aukan JIDDAH,ai yin hakan sab'awa addini ne,ta yaya baligi kamarsa zai kinkineta,ita da ba muharramarsa ba,duk da larura ne yasa,ita kam bazata zuba ido tana kallon haka yana faruwa ba....
Sai da ta bari sun gama shirin kwanciya,sannan ta shiga yiwa DADDY k'orafin abun,sannan ta fad'a masa dalilinta na ganin rashin dacewar hakan....
Murmushi yayi,bai tanka
ta ba,sai da ta gama sannan ya fara magana...
''Duk abunda kika fad'a haka ne,na san ba dai² bane,buh idan kika duba,cikinku akwai wanda zai iya d'agata bare ya canza mata gurin zama?''....
Kai ta kad'a masa,alaman
A'a....
''To kinga kuwa sai kinyi hak'uri,dan a yanzun shi kad'ai zai iya d'awainiyar d'agata daga nan zuwa can,amma kiyi hak'uri komai lokaci ne,bana son ki dinga kawo wasu tunanin na daban a ranki''....
Murmushi kad'ai tayi,tana neman gurin kwanciya.....
''Haba my LADY bacci tun yanzun,ni ko tarbar kirki ban samu ba,ana jinyar y'a,tun d'azun kamar nayi laifi...
Ai yau tun da na dawo sai an lallab'ani nima zanyi bacci,kuma kowama zaiyi''....
Ita kam kalamansa kunya ma suka sa taji,ba shiri ta rufe idonta tana juya baya.....
************
Har ta fara bacci ring en wayanta ya farkar da ita..
Bata tsaya son sai ta gane mai kiran ba ta d'auka...
Cikin murya da ke nuni da mutum ya fara bacci,tayi sallama...
Amsa mata yayi,cikin sanyin murya yake fad'in
_''Am so sorry,MY QUEEN na katse miki bacci''..._
Bata ce komaiba,tayi shiru tana sauraresa...
_''Ya k'arfin jikin naki?''...._
Babu shiri ta nemi baccin dake idonta ta rasa,tana ma kanta question
''A ina yasan bata da lapia?''....
_''Kinsan ikon Allah ba ta yadda baya kasancewa,a jinin jikina nasan kina cikin prob''_
Maganarsa ta daki kunnenta...
Dafe kai tayi kenan a fili tayi maganar tata ko me?...
_YEAH_ ya bata amsa...
Wayan ta katse,babu shiri ta kasheta gaba d'aya,chest enta na bugawa into paster...
Ita kam wannan ko dai ALJANI ne bata sani ba,komai nata ya sani,hatta maganar da za tayi a zuciyanta yana jinta...
Nan ta shiga tunanin mafita ita d'aya.......
*_~#TEAM J2~_*
*_REAL SMASHER._* 🤞🏻😘
[7:03PM, 3/28/2018] rєαl ѕmαѕhєr 💃🏻: 💠💠 *RAYUWAR WANI......*
_{ơŋɛ'ʂ Ɩlıʄɛ...}_
💠💠
🌹
*Viawattpad@realsmasher01.*
*©® 2018.*
*28/mąrcɧ,2018.*
*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ...*
*ცყ.*
_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~_________________________~*
*ADDU'A YAYIN CIRE TUFAFI.*
_BISMILLAH!!_
*ADDU'A IDAN ZA A FARA ALWALA.*
_BISMILLAH!!!_
*_~#HISNUL-MUSLIM.~_*
*~_________________________~*
_Sisinah ina miki fatan alkhairi arayuwa,ubangiji ya tashi kafad'unki,ina missing enki sosai na rashin kasancewa tare da ke.._
_Wish u quick and speed recovery *MY HUBBEEY* ,I so much heart u dear.._ 💔💔💔
*~_________________________~*
_*MY MEINERH (LITTLE)* kina nan acikin birnin zuciyata,soyayyarki ta dabance,ban had'aki da kowa,sha sha'aninki wannan page en gaba d'ayansa na kine,ke d'aya..._ 👌🏻
_I so much miss u dear,feeling lyk crying till tomorrow...._ 😭😭😭
*Heart u nd miss u cweety 💔*
*~_________________________~*
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)........*
*℘ąɠɛ 67↔68*
Tunanin mafita ta shiga,tana kwance ta ja jiki ta jingina bisa pillow....
To waima wane irin mataki ya kamata ta d'auka?
Tayima kanta tambayan...
Zuciyanta ne ya kasu biyu ko wanne da irin tunanin da yake kawo mata...
'Daya na fad'a mata ta sashi a blacklist...
Kai ta kad'a yayin da zuciyanta ke fad'in
_''noooo dont even try''....._
''To wai ya zanyi ne kam'' ta sake tambayan kanta...
'Dayan zuciyan ne yace
_Kibi a sannu har ki gane wanda ke bibiyanki.._
Finger enta tasa a baki tana ciza,tana ci gaba da tunani,da haka har bacci ya d'auketa garin tunani...
Ko da Asubah ma MAMMY tazo har d'aki tasata tayi alwala ta gyarata yanda zata fuskanci alk'ibla,haka tayi sallanta har ta idar...
Azkar tayi na safiya da maraice,tana zaune har gari ya gama wayewa sosai rana ta hudoo...
Sallah tayi raka'a biyu ta ci gaba da addu'o'inta zuwa rana ta gama game garin baki d'aya....
_(YIN SALLAH RAKA'A BIYU BAYAN RANA TA HUDO, MUTUM YA IDAR DA SALLAR ASUBAH,YA ZAUNA YANA AMBATON UBANGIJI A INDA YAYI SALLAH,BAYAN RANA TA HUDO YA TASHI YA SALLACI SALLAH RAKA'A BIYU,ANNABI (S.A.W) YACE:''KAMAR MUTUM YAYI AIKIN HAJJI DA UMRAH NE TARE DA SHI...)_
_Allahya bamu ikon aikatawa...._
Kamar ko wane lokaci yauma haka YAH BOSS ya d'aukota daga d'aki zuwa parlor...
Sai b'ata rai yake shi a dole bai so hakan ba...
Cikin zuciyansa ko fal farin ciki haka yake ji,ga wani tausayinta dake ratsashi...
Amma uban girman kai da miskilancin nan nasa ya hana masa ya nuna..
A nasa ganin yin hakan zai sa ta raina sa...
Sai da ya direta sannan ya koma yayi shirin ficewa daga gidan....
Haka LITTLE ta kammala shirinta itama ta sakko kusa da sisin nata ta samu guri ta zauna,suka hau jinyan su biyu...
IKHRAM da ta fito daga d'akin MAMMY Kusa da su ta zo ta zauna tana gaida su...
Suka ci gaba da fira,don d'ebe mata kewa....
*IN D EVENING...*
Sallam HUBBEEY ce ta katse musu firan da suke...
Da murnansu suke welcoming nata...
Sai da suka gama tsokanar juna kafin ta mik'e zuwa inda MAMMY take ta gaidata....
Firan suka ci gaba da yi,nan ta kalli JIDDAH da salon tsokana take fad'in
_''Allah sarki matar babban yaya an zama gurguwa''...._
Dariya suka fashe mata da shi,nan ta murgud'a musu baki tare da fad'in
_''Eh naji babu komai,ai dai bazai daina sona ba ko me zai sameni''....._
Dariya suka sake sawa...
''Waye ya fad'a miki bazai daina sonki ba?''...
''Lallaima yarinya kin yaudari kanki,idan bai daina sonki ba to kuwa zai miki amarya''....
Suka ci gaba da tsokanarta....
Banza tayi da su bata sake kula suba...
Su kuma kamar wad'anda ta sa suci gaba....
Sai sunyi shiru sai su ci gaba....
''Allah sarki gurguwar amarya shi kenan haka zaki dinga fama da cangala k'afa...
Haka za a bamu rabin sadaki''.....
Ko K'arasawa basuyiba tasa kuka nan su kuma suka samu abunyi dariya suka sata gaba suna yi.....
YAH BOSS da ya shigo yanzun ya tarar da su suna ta faman dariya,ita kuma hakimar sai kuka take......
Sallama yayi ciki²,ya shiga takowa cikin takunsa na k'asaita....
Babu wanda ya ga shigowarsa cikinsu...
Juyowa LITTLE tayi tana tsaka da dariya ta hango shi yana takowa inda suke....
Bakinta ta rik'e tana dungurin HUBBEEY da IKHRAM da suke ta faman dariya....
Shiru kowacce tayi tana rik'e baki.....
Kallon su yayi d'aya bayan d'aya,rashin gaskiyan da ya gani a kan fuskokinsu ne yasa shi cilla musu harara ya juya yana haura stairs en d'aya da d'aya....
***********
*MONDAY EVENING..*
Da yammacin ranar Litinin,da yawa daga cikin course mate en su suka zo duba JIDDAH...
Haka aka dinga zuwa dubata daga k'awayensu,k'awayen MAMMY da ma abokan DADDY na kasuwanci...
Haka JIDDAH ta ci gaba da jinyan jikinta har zuwa tsawon sati uku...
*************
Sosai jikinta yayi kyau,zuwa wannan lokacin JIDDAH ta saba da ganin sak'onnin mutumin da bata san ko wayewa ba a fuska,sai dai sunansa da tayi saving MUHAMMAD...
Tana farin ciki haka zata d'auka kiransa,su jima suna shan fira..
Ko ina suna tare da juna akan waya...
Shak'uwa mai k'arfi ta shiga tsakaninsu....
Har ta kai idan basu kasance tare da junaba na yini d'aya ko wannensu zai kasance cikin ALHINI....
'Ban garen LITTLE da FAROUK ma ba a barsu a baya ba,dan kuwa soyayya suke nunama juna mai cike da tsafta ga girmama juna....
Ko da wasa babu wanda yayi tunanin cewa JIDDAH tana soyayya da 'BOYAYYEN MASOYIN nata.....
Wannan kenan....
***************
Tsawon wannan lokaci an samu chanje² ta fuskoki da dama....
Kamar ko wane lokaci yauma zaune DADDY yake akan cuition yana duba DAILY NEWS PAPER....
Da farin medicated glass sanye a idanunsa....
MAMMY tayi sallama hannunta d'auke da tray,samansa lemone na sob'o cikin babban jug na glass....
Da fara'arta ta k'araso ta nemi guri kusa da shi ta zauna,tana fad'in
''Barka da hutawa''.....
'Dagowa yayi yana ninke newspaper en..
Saman table en dake gabansa ya d'ora yana fad'in ''kamar kuwa kinsan ke nake ta zuba ido naga ta inda zaki fito''....
Murmushi tayi dake nuna tsantsar farin ciki
''To ai gani yanzun,Allah yasa dai lapia''..
Tayi maganar tana saurarensa taji abunda zai fad'a....
Sai da yayi murmushi irin nasu na manya,kafin ya fara magana...
''Eh to shawara ce dai nake so muyi kan maganar yaran nan,mu ga abunda ya kama ta ayi,idan yaso,sai mu tsaida matsaya guda d'aya''...
Ajiyan zuciya tayi,tana mai dad'a nutsuwa kan abunda yake son su tattauna...
''Gaskiya dai Alhaji na dad'e da wannan tunanin,kawai dai nayi shirune naji me zaka ce akai''....
Ta fad'a cikin sigar tabbatar da abunda ta fad'a...
''To dakikayi shiru ina amfaninsa?
Kinsan da cewa lokaci ba jira yake ba,yanzun da banyi maganar ba haka zaki zuba ido kenan?''...
Shiru tayi babu amsa
Shi kuma yaci gaba, ''dalilin da yasa nayi wannan maganar kuwa shi ne
Yanzun tun da Allah yasa AMINATU ta samu wanda yake sonta da gaskiya,me zai hana ba zamu d'auko wannan tsohuwar maganar ta had'a JABEER da JIDDAH aure,lokaci yayi da ya kamata ace muma mun sauke nauyin da Allah ya d'ora mana..
Baya ga haka,su y'ay'an zamani ne,ba kamar muba,kana iya b'ata lokaci kana bawa d'anka tarbiyyah da zarar ya fita waje ya had'u da sha³n abokai ko k'awaye sai su canja masa tunani..
Shi yasa naga dacewar tak'aita lokacin nan da zuwa watanni biyu masu zuwa''....
Ko kuwa me kike ganin ya dace ayi...
Fuskanta cike da farin cikin maganar tasa,ta amsa masa da
''Duk hukuncin da ka yanke ai an riga an gama kuma,mu namu aikatawa,abun da zance dai ba zai wuce Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa ba''...
Ta fad'a tana murmusawa...
To shi kenan Allah ya nuna mana lokacin muna masu rai da lapia....
''Yanzu abunda yayi saura magana da yaran ki ji ra'ayinsu,kafin nan ni kuma zanyi magana da yaron da yake zuwa wajen AMINA...
Zan kuma tuntub'i JABEER kan maganar auren nasu''.....
DADDYN ya fad'a...
''To shi kenan in sha Allah zan musu maganar,Allah yasa muji alkhairi....
*#AMEEEEN....*
*_~#TEAM J²~_*
*_REAL SMASHER._*🤞🏻😘
💠💠 *RAYUWAR WANI......*
_{ơŋɛ'ʂ Ɩlıʄɛ...}_
💠💠
🌹
*Viawattpad@realsmasher01.*
*©® 2018.*
*31/mąrcɧ,2018.*
*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ...*
*ცყ.*
_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~_________________________~*
*ADDU'AR SHIGA BAN'DAKI.*
_BISMILLAHI!!! ALLAHUMMA INNIY A'UZHUBIKA MINAL-KHUBSI WAL-KABA'ISI.._
*ADDU'AR FITOWA DAGA BAN'DAKI.*
_GHUFRANAKA...._
*_~#HISNUL-MUSLIM.~_*
*~_________________________~*
_Masoya *Y'AR GARUWA* ina mai baku hak'uri sakamakon bazan samu damar posting ba yau,coz bana cikin yanayin da zan iya dogon typing yau.._
*_#Luv u oll..._* ❤
*~_________________________~*
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)........*
*℘ąɠɛ 69↔70*
Tsaf suka kammala shirinsu na tapiya skul,dan kuwa zuwa wannan lokacin sosai ta samu sauk'i,MAMMY suka ma sallama suka wuce,inda LITTLE ke driven...
JIDDAH na gefenta gurin mai zaman banza,tana d'an duba lecture note nata,coz tsawon 2 weeks kenan bata lek'a skul enba,tana jinya....
Sai dai yanzun kam Alhmdllh jikin yayi kyau sosai,saboda tana da jiki mai kyau....
Tafe suke,in da ba komai ke tashi cikin motanba sai wak'an P.SQUARE nd DAVE SCOTT mai taken ''BRING IT ON''....
Kowa da tunanin da yake har suka shiga cikin skul en...
Parking tayi suka fito,cikin salonsu mai burgewa suka fara ratsa hanyan har suka kai lecture venue en nasu....
Tun daga shigarsu sai zuwa ake ana duba JIDDAH ga wad'anda basu samu damar zuwa gidaba....
Ranan haka suka wuni cikin skul sai after 4:00pm sannan suka samu daman samun sarari....
A gajiye suka koma gida,bama kamar JIDDAH da ta kwana biyu bata lek'a skul enba....
Zuwansu gida basu tsaya k'asaba suka haura sama,sai bayan maghreb suka sauko shima,firane ya zaunar dash,sai jiran dinner da suke...
Sai kuma MAMMY da ta sanar da su tana son ganinsu...
Kowa jiki a salub'e haka suka tarar da ita a parlor tana zaune daga ita sai IKHRAM da tayi pillow da cinyanta...
Neman gurin zama sukayi kowa da abunda yake sak'awa a ransa...
Bata ce musu komaiba,har zuwa shud'ewar wasu mintuna....
Su kuma kowa yana sauraren jin ta inda zata fara magana...
Shigowan YAH BOSS,hannunsa sak'ale da lab coat ensa yana tafe cikin k'asaita...
Ya k'araso cikin parlor,MAMMY ya gaisar kafin ya mik'e yana shirin haurawa sama..
Dakatar da shi MAMMY tayi ta hanyar fad'in
''Idan ka gama abunda kake ina son ganinka''...
Dawowa yayi yana zama,fuskansa na nuna alamar damuwa coz baisan me zata fad'a ba,shi kuma gashi baya cikin type en da idan kace zaka fad'a masa magana ka jaa lokaci...
Bai cika son zama cikin damuwa ba shi yasa,ek'ok'arin guje mata...
''Kaje ka huta tukun,ai ba inda zaka yanzun da dare kam ko?''....
Kai ya kad'a mata,yana fad'in
''No MAMMY gara dai kiyi maganan,idan na haura yanzun babu tabbas na dawo nan maybe sai da safe,coz akwai aikin da zan k'arisa''....
Kai ta kad'a alaman ta gamsu da maganarsa,kafin ta fara magana....
"Dalilin da yasa nace ina son magana da ku,sa'one da DADDYNKU ya wakiltani na sanar daku dukanku..
Ku ba yara bane da za ana fama da ku,kun riga kun mallaki hankulanku....
''Kai kaine babba cikinku,saboda haka kai zaka nunawa k'annenka hanyar da za subi wajen yi mana biyayya,idan bakayi hakanba to suma suna iya yin fatali da hakan..
Babban abunda yasa na kasance tare da ku a yanzun,baya wuce taso wani tsohon magana da na tabbata acikinku babu wanda ya manta da ita,sai dai ina son tunatar daku..
Kun riga kunsan maganar da DADDYNKU ya yanke kan maganar aurenku,ya bar maganar ne saboda son had'aku da yake duka ya aurar lokaci guda,sai dai ya bar maganar zuwa lokacin da AMINATU zata samu tsayayye,kuma wanda babu k'arya a lamarinsa''....
'Dan dakatawa tayi,tana kallon yanda kawunansu ke a k'asa,kamar basuba,kafin taci gaba....
''To Alhamdulillah Allah ya kawo lokacin,wanda a yanzun haka nake farin cikin sanar daku DADDYNKU ya tsaida lokaci nan da watanni biyu masu zuwa''..
Ta fad'a fuskarta tana mai bayyana farin cikin da take ciki....
''Kai JABEER kai ne babba kariga kasan da wannan maganar,kuma da amincewarku akai hakan tun tuni,shin ka tuna wannan maganar?''...
'Dagowa yayi ya kalleta,yana fad'in
''Eh MAMMY''...
''To Masha Allah,tunda baka manata ba,kuma ina fatan baku mantaba ko?''..
Amsawa sukayi suma,nan dai MAMMY ta d'anyi musu nasiha,kafin ta sallamesu,ta nufi d'akinta...
Da k'yar suka bar parlor jikin kowa yayi sanyi saboda nasihan nata ya shigesu,sai kace mai bada WASIYYA haka ta musu,shi yasa jikinsu duk ya mutu....
Haka suka nufi d'aki kowa shiru babu maganar kirki....
Har suka kwanta babu wata fira,kowa da tunanin dake ransa....
B'angaren LITTLE kam murna take kan CIKAR BURINTA,wato FAROUK sai dai nasihan MAMMY ya hana mata murnan nata ya bayyana...
Ga JIDDAH itama ta rasa fahimtar al'amarin zuciyanta,coz ta kasa tantance wanda tafi so tsakanin
MUHAMMAD da kuma YAH BOSS en nasu...
Tunaninta ya tsaya cak,burinta ta bambancewa zuciyarta matsayin kowanne,amma abun ya gagara...
Har yanzun a position d'aya take jinsu...
''Shin ina mafita?''
Tayiwa kanta wannan tambayar yafi a k'irga,amma ta kasa...
Kuka tasa k'asa²,wanda yasa LITTLE mik'ewa zaune tana tab'ata...
''SISINAH whats going wrong?''....
Rashin amsa yasa ta fara lallashinta,amma kamar dad'a zugata tayi,sai da tayi mai isarta sannan tayi shiru...
''Kin san dai sis bana son ganinki cikin irin wannan halin,ko mene ne yake damunki bazanso ki kasance cikin damuwa ke d'ayaba,amma tunda baki so na sani,zan tayaki da addu'an neman sauk'i,kiyi hak'uri ki daina kukan nan please kada kanki yazo yana miki ciwo''.....
''NOOO!Sisinah ba wai banson ki sani bane,ni kaina nasan yaudaran kaina nake,amma bari kiji YAYA ABUN YAKE''....
Nan ta kwashe labarin abunda yake faruwa kaf ta sanar da ita....
Dogon ajiyan zuciya tayi,kafin ta dafa ta,tana fad'in
''NOOOO!sisi bakiyi ba dai² ba,sai dai kin kusa yin ba dai² ba,amma anawa shawaran,yanzun abu d'aya ya dace kiyi...
Duk da kasancewar YAH JB matsayin d'an uwa gareni,bazan so idan har bakya sonsa kiyi shiruba,coz ke zaki cutu....
Mafita d'aya ne,shi ne kiyi musu jarabawa tunda kin kasa bambance wanda zuciyanki ke so,me zai hana ki cema da MUHAMMAD en kina buk'atar ganinsa,tunda baki tab'a yin hakanba
Ina tabbatar miki da cewa idan yak'i amsa tayinki to ki tabbatar ba soyayyarki a tare da shi,maybe kuma yana da wata manufa akankine''....
Kinga daga nan saikima kanki da kuma iyayenmu adalci.....
Sai yanzun taji zuciyanta yayi mata fayau babu damuwa kamar d'azun...
Tunani ne ya sake bijiro mata,itakam ta yaya zata iya bijirewa umarnin wad'anda suka rufa musu asiri,gaskiya dai itakam ba zata iya aikata hakan gare suba,ko dama ace babu soyayyan YAH BOSS en a ranta,gara ta sadaukar da farin cikinta wajen faranta musu suma...
Wannan shawar da zuciyanta ta bata,shi ta yanke zatayi amfani da shi,da niyyar neman MUHAMMAD en ko dan ta fad'a masa gaskiya kan lamarinta,sai dai tsoro daya baibaye mata zuciya,ko zata iya?''......
Sosai taji dad'in shawaran zuciyan nata,in da tayi fatali da shawaran sisin nata,da murnanta ta janyo phone enta tana bud'e hospot nata....
Kamar wanda ake jira,sak'onsa ya fad'o cikin phone en nata....
Kamar yadda sukayi da LITTLE haka cikin dabara ta sanar da shi maganar son ganinsa da take....
Dariya ya mata,kafin ya bata amsa da
_''Kimin alk'awari koda kin ganni bazaki gujeniba,bayan kin san ko ni en waye..._
_''Ni kuma nayi miki alk'awarin bayyana miki kaina,soon''_
Sai da ta tabbatar masa da hakan,kafin suka tsunduma tafkin soyayya....
Haka suka b'ata lokaci mai tsayi suna musayar kalamai masu sawa zuciya nutsuwa,kafin sukayi sallama da junansu,suna jin kamar su kasance a haka kada su rabu....
Da k'yar suka rabu yana mai mata albishir na zuwansa nan da k'arshen satin,sukayi sallama,zuciyoyinsu fal farin ciki......
*#Kuyi hak'uri da wannan fan's coz banjin dad'i 2dayz,luv u oll...* ❤💋
*_~#TEAM J²~_*
*_REAL SMASHER._*🤞🏻😘
💠💠 *RAYUWAR WANI......*
_{ơŋɛ'ʂ Ɩlıʄɛ...}_
💠💠
🌹
*Viawattpad@realsmasher01.*
*©® 2018.*
*12/ąpril,2018.*
*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ...*
*ცყ.*
_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._
*~__________________________~*
*ADDU'AH IDAN ZA A FARA ALWALA*
_BISMILLAH!!!_
*ADDU'AH IDAN AN GAMA ALWALA*
_ASH-HADU AN-LAA ILAH ILLAH,WAHDAHU LAA SHARIKALAHU,WA-ASHHADU ANNA MUHAMMADIN ABDUHU WARASULUH..._
_ALLAHUMMA JA'ALNIY MINAT-TAWWABIYNA,WAJA'ALNIY MINAL MUTA'DAHHIRIYNA..._
_SUBHANAKALLAHUMMA WABI HAMDIKA ASHHADU ANLAA ILAHA ILLA ANTA ASTAGHFIRUKA WA-ATUBU ILAIK..._
*_~#HISNUL-MUSLIM.~_*
*~_________________________~*
_Y'an uwa muna godiya bisa addu'o'in da kuke mana,na rashin lafiyan sisinah,cikin ikon Allah ta samu sauk'i,masu kira,text da masu zuwa gida duk muna mik'a godiyarmu gareku,Allah ya bar zumunci.._
*_#REALLY HEART U..._* 💔💔💔
*~_________________________~*
🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂
*HAPPY!*
*HAPPY!!*
*BIRTHDAY!!!*
*TO U DOUGHTER.*
🍻🍻🍻🍻🍻🍻🍻🍻🍻🍻🍻🍻🍻
_May God shower his choicest blessings on you. wishing you happiness, good health and a great year ahead._
🍫🍫🍫🍫🍫🍫🍫🍫🍫🍫🍫
K A S
H B
A U A'
D B
I A A
J K
A A D
T R
🌹 *_(KHAIRAT)._* 🌹
🍭🍭🍭🍭🍭🍭
_Appy bufday dougheeey,wish u many more years ahead,happy fruitful years..._
🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂
*~__________________________~*
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)........*
*℘ąɠɛ 71↔72*
Washe gari haka ta tashi fal da murna,sai dai gefe d'aya kuma fargaba ne a cikin ranta,na yanda zata fuskanci abunda ke shirin faruwa...
Haka ta labartawa LITTLE yanda sukayi da MUHAMMAD en Nata.....
Itama ta taya ta murna sosai,ganin yanda sisin nata ke tsaka da murna,duk da ta b'oye mata damuwar da take ciki...
Duk wani k'ok'ari JIDDAH yinsa take na ganin ba a gane tana cikin damuwa ba...
A maganar da sukayi da LITTLE akan MUHAMMAD en ta b'oye mata da yawa,kan yanda ta tsara zata tafi da al'amarin...
Fatanta baya wuce tayi komai cikin ruwan sanyi kuma ba tare da an rafkota ba...
Kullum haka take juyayin lamarin da yanda komai zai kasance,tun ranar da ya sanar mata zaizo..
Dan kam zuwa wannan lokacin al'amuran har tsoro suka fara bata,bare kuma yau en da ta san komai zai faru,duk k'ok'arinta kada tayi abunda za tayi DA NA SANI...
Sai dai duk da haka ta dagewa zuciyarta kan practising da kuma hanyan da zata bi tayi solving Case en,idan ta ga yana k'ok'arin rikice mata.....
Haka duk tsayin kwanakin da ya d'iba mata wanda ita JIDDAH ta gansu ne kamar wad'anda ake jaa da K'UGIYA....
Yau en ta kama ranar SATURDAY gaba d'aya suna gida...
Maimakon su kasance a parlor kamar yadda suka saba,saima dad'a k'ulewa da sukayi a d'aki su biyun sun bar MAMMY da AUTARTA IKHRAM a parlor tun breakfast,suka tsere,basu ko k'ara waiwayon parlon ba....
Kowa da abunda yake,sai fira da suke jefi²,kowa da waya a hannunta,tana nata hark'allar...
Game enta take bugawa na ''CANDY CRUSH'' cikin kwanciyar hankali...
K'aran text message ya dameta..
Banza dashi tayi kamar bata jiba,zuwa can kuma kamar wacce aka tsikara tayi MINIMIZE na game en ta tafi dubawa...
Aranta dai mita take coz cikin kwanakin COMPANY sun takurata da turo sak'o...
Shi yasama yanzun sai da tayi tsaki kafin ta tafi dubawa tana mita...
Sunan da taga yayi appear ne yasa ta jin wani matsanancin fad'uwar gaba da bataji irinsaba,wanda sai da ya haddasa mata rintse idanunta....
Sai da ta d'auki tsawon lokaci kafin ta iya k'arfin halin bud'ewa,ta soma bin alphabet en da k'yar...
Kamar mai shirin koyon had'a bak'ak'e haka ta fara binsu d'aya bayan d'aya,yahun bakinta har d'aukewa yake,saboda tsabar tsoro.....
(ko meye dalilin ohooo)...
Da k'yar ta iya karantawa,cikin hargitsewar da bata tab'a tsammanin zata sameta ba,ba shiri ta hantsilo k'asa,lokacin da tayi arba da abunda ya fad'a,idanunta sun gama bayyana a fili tamkar zasu fad'o...
LITTLE dake kusa da ita tayi saurin kallonta tana fad'in
''Sisi lapia kuwa kike?ko dai da matsalane?''...
Haka ta jero mata tambayoyin da bata samu amsar suba sai nuni da tayi mata da phone en dake yashe akan bed....
Hannu ta mik'a ta d'auko ta fara dubawa...
_Assalamu alaikum warahmatullah..._
_Gimbiyata fatan kina cikin k'oshin lafiya,idan babu wata matsala ina mai alfaharin sanar da ke k'arasowata nan da zuwa 4 Hours...._
_BISSALAM..._
Dogon ajiyan zuciya LITTLE tayi
''Haba cweety yanzun wannan en har abunda zai tayar miki da hankali ne,bayan ranace da zata kasance miki d'aya daga cikin ranakun farin cikinmu,dan Allah ki bar damuwa akan wannan abun,bana son wani abu ya sameki,pleasee kinji durling sis''..
Ta marairaice mata kamar zatayi kuka,hakan datayi shi ya sa JIDDAH sakin jikinta,amma da ka kalleta zaka gano irin rud'in d take ciki....
'Daga kai tayi ta kalli wall clock en dake d'akin taga d'aya saura kwata,wata sanssanyar ajiyar zuciya tayi,ta mik'e ta shige toilet....
Alwala tayi ta dawo ta shimfid'a pray mat..
Sai da tayi nafila tukun ta mik'a kukanta ga sarkin da babu tamkarsa,kan ya kawo mata agaji bisa wannan lamari da tayiwa karan tsaye ba tare da sanin kowaba sai LITTLE....
Ta jima tana addu'ah kafin ta idar,ta ci gaba da lazimi tana k'ara neman sauk'i cikin al'amuran....
Yinin ranar tayi shi ne ba cikin nutsuwarta ba,dan ko magana bata cika yi ba gudun kar a harbo jirginta.....
*3:55pm.*
Ya k'araso cikin gidan,horn yayi baba ya bud'e masa get en,a parlon bak'i ya yada zango,tun kafin ya k'arasa ciki ya fara kiran line nata...
Zaune take ta gama shiryawa,sai dai gaba d'aya zuwa wannan lokacin tayi losing hope,tana zaune kan stool kiransa ya shigo..
Sai da ta tattara nutsuwarta kafin ta iya d'auka,bakinta na furta kalmomin sallama...
Yayinda chest enta banda dukan Tara² babu abunda yake,jin voice ensa ya k'ara rud'ata...
Cikin wani irin yanayi ya furta
_''Ranki shi dad'e idan har anmin izini,ina son sanar dake k'arasowana...''_
Yana d'an murmushi....
Da k'yar ta had'a kalmomin
_''U r highly wlcm''..._
Ajiye wayan sukayi,ta tsaya dube²,amma ta rasa ma me take nema,k'afanta ta d'aga da tayi mata wani mugun nauyi ta nufi closet ensu,wani rantsatstsen lace ta d'auka botter milk had'e da red colour na vail,fation jewelry's ta d'auka wanda suma duka red ne...
Abundai ba a magana bare da ya samu farar fata sai ya hau sosai,yayi mata matuk'ar kyau...
Kamar kazan da k'wai ya fashewa a ciki haka ta jaa jiki ta zura plat shoe enta red colour tayi hanyan fita....
Da ido LITTLE dake waya ta rakata,kafin ta iya cewa
''Cweety ba ko sallama zaki tafi,tunda sahibi yazo,ni tsoro nakema kada ya k'wacemin fada dan naga take²nsa'',nan ta sa dariya...
Ita dai bata kulata ba tayi saurin ficewa daga d'akin har ta kusa riskar stair case rana jin dariyan LITTLE....
Lokacin da tazo wucewa ta parlor babu kowa shi yasa har ta fice ba ta had'u da kowaba...
Tun da ta doshi hanyan parlorn ta ji wani matsanancin fad'uwar gaba wanda ya ninka nada da take ji,dakewa take son yi amma hakan ya gagara...
Sai da tayi yak'i da zuciyanta kafin ta iya samun k'arfin gwuiwar dosar k'ofan da zai sada ta da cikin parlon..
Baya ga addu'ah da take ta faman jaa,duk wanda yazo mata shi take karantawa...
Idonta ta runtse had'e da sanya k'afanta na dama a cikin parlon tana karanta sallama....
Yana tsaye ya juyama k'ofan baya,wannan dalilin shi zai hana kayi saurin gane wanda ke tsaye...
Bayansa ta kallah tana mai k'arasowa cijin parlon,har lokacin idanunta na kansa....
Zama tayi tana sak'a abubuwa da yawa a ranta,yayinda tunaninra ya gaza fassaruwa ga tarin tsoro da ya dad'a shigarta,kanta a k'asa tana wasa da yatsun hannunta,idanunta kuwa tamkar zasu fidda ruwa haka take jinta...
Bai juyoba,kamar yadda yak'i yin magana har lokacin tun bayan sallaman da ya amsa mata...
Sai da taga abun ba na k'are bane ta d'ago cikin murya mai cike da son yin kuka ta furta
''Bismillah ga gurin zama...''
Murmushi yayi mai cike da k'warin gwuiwa,a hankali kuma ya shiga juyowa....
Ganin fuskarsa shi ya haddasa mata k'idasa rud'ewa,cikin abunda baifi k'iftawar idoba ta mik'e tsaye tana nuna shi da yatsa,cikin inda² take fad'in
''Ka....ka........kaine?''......
*#Nima dai nan na shiga d'agowa dan ganin wanda JIDDAH ta gani....*
_FAN'S KUMIN AFUWA NA JINA SHIRU 2 DAYZ,BUH AN 'DAN SAMI PROB NE,DA YASA KO ONLINE BANYI TSAYIN WA'DANNAN KWANAKI..._
_INA NAN TARE DAKU HAR KULLUM..._
*_~#TEAM J²~_*
*_REAL SMASHER._*🤞🏻😘
[3:55PM, 4/14/2018] rєαl ѕmαѕhєr 💃🏻: 💠💠 *RAYUWAR WANI......*
_{ơŋɛ'ʂ Ɩlıʄɛ...}_
💠💠
🌹
*Viawattpad@realsmasher01.*
*©® 2018.*
*14/ąpril,2018.*
*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ...*
*ცყ.*
_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._
*~__________________________~*
*ADDU'AH YAYIN FITA DAGA GIDA.*
_BISMILLAHI TAWAKKALTU ALALLAH WALA-HAULA WALA-QUWWATA ILLAHBILLAH._
_ALLAHUMMA INNIY A'UZHUBIKA AN-ADILLAH,AU'UDALLAH,AU'AZILLAH,AU'UZALLAH,AU'AZLIMA,AU'UZLIMA,AU'AJHALA,AU'YUJHALA ALAYYA.._
*ADDU'AH YAYIN SHIGA GIDA.*
_BISMILLAHI WALAJNA,WA-BISMILLAHI KHARAJNA, WA-ALALLAHI RABBANA TAWAKKALNA._
*_~#HISNUL-MUSLIM~_*
*~__________________________~*
🎂🎂🎂 *HAPPY!*🎂🎂🎂 *HAPPY!!* 🎂🎂🎂 *BIRTHDAY TO YOU!!!* 🎂🎂🎂🎂
*Count your nights by stars, not shadows. Count your days by smiles, not tears. On your birthday, count your age by friends, not years...*
🍻🍻🍻🍻🍻🍻🍻
_Once again happy bufday to u_ *SAWWAMA & MARYAM IPTEEN.*
_wish u many years ahead,happy fruitful years..._
🎂🎂🎂🎂🎂🎁🎁🎁🎁🎁🎁🎁
*~_________________________~*
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)........*
*℘ąɠɛ 73↔74*
Wani kallo take masa mai cike da tsantsar mamaki,hannunta a sama har zuwa lokacin ta kasa sauke shi k'asa....
Wani killer smile yake jifanta da shi,hannunsa zube cikin pocket ensa...
Kad'a kansa yayi yana fad'in
''Yeahhh!is me''
Lokacin da ya k'araso inda take tsaye,jikinta banda rawa babu abunda yake...
Bayaga tsantsar tsoron dake tare da ita,ganin yana daf da k'arasa cike gap dake tsakaninsu yasa ta juya cikin sauri zata bar gurin....
Hannu yasa ya fizgota,a jikinsa tayi masauki,wanda hakan ba k'aramin jefasu yayi cikin wani irin yanayi da basu tab'a kasancewa ba....
Kukan da take k'ok'arin b'oyewa tun d'azun shi ne ya fito fili...
Warm hug en da ya dad'a bata shi ya tsaida ita...
Tuni ta nemi kukan ta rasa,a haka suka ci gaba da tsaiwa har na wani lokaci...
''YAH ka cikani zan zauna ne''
Bai cikata ba har ta gama fad'an abunda zata fad'a ko ''A'' bai ceba,saima tafiya da ya soma tana jikinsa...
Kan sofa ya musu masauki,ita kuma sai mutsu² take na son k'wacewa dan har lokacin tana cikin shock....
''Please YAH kada wani ya ganmu''
Murmushi yayi da ya k'ara masa kyau,ya lakace mata hanci..
''Ke kuma ga d'an karen tsoro koh''
Kai ta kad'a masa..
''Idan wani ya gani sai me? k'arshe dai maganar ta je kunnensu DADDY koh?
to nima haka nake so,ko zasu taimaka gobema su ce a d'aura aure''
Ya k'arasa teasingly...
K'afanta ta shiga bugawa a k'asa,ta cuno d'an bakinta gaba...
Hakan da tayi ba k'aramin dariya ya bashi ba,cikin magana k'asa² yake fad'in
''Ko dan gaba ki guji cunomin wannan bakin dan zanyi maganinki ne''
''Me za kayi?''
''Nima ban sani ba,sai dai ko da kin sake bani da damar hukuntaki yanzun,amma.......sooner''
Ya k'arasa yana murmushin mugunta....
Hak'oranta ta washe,tana fad'in
''Hakanma yayi dai²..''
''Me kike nufi?'' ya tambaya
_''DUBAWA ZA KAYI''_
Maganan yayi escaping,dafe bakinta tayi tana kad'a kai...
Ido ya bud'e yana kallonta,hannu ya shiga tafawa,cikin salon tsokana
''OK bari to na duba''
Ya shiga k'ok'arin d'agota yana dariya...
''Wayyoo! YAH dan Allah kayi hak'uri baran k'ara ba''....
Ganin suna kokawa da shi,yana niyyan cire vail en dake kanta,yasa ta kwace jikinta daga nasa da gudunta ta bar kusa da shi,tana haki...
Dariya sosai ya shiga yi,wanda tunda suke tare gida d'aya bata tab'a ganinsa cikin irin wannan yayinba,abun har mamaki yake bata wai dama haka YAH BOSS en yake,amma su kullum yana wani had'e masu fuska...
Dalilin da yasa suka sa mishi YAH BOSS kenan...
Tayi nisa cikin tunaninta,har bata san lokacin da ya tashiba...
Hannunsa da ya d'ora kan cinyanta,shi ya farkar da ita daga mafarkin da take...
''Tunanin me kike haka?''
''Babu komai''...
Ba don ya yarda ba,ya k'yaleta,sai don bai son takurata....
Hannunsa ya kalla,nan yaga yanda lokaci yayi matuk'ar gudu..
''Kinga kinsa lokaci ya k'ure mana,bamu yi abunda ya kawomuba''...
''Nifa ba ruwana''...
Kafin ta k'arasa ya shiga fad'in
''To laifin waye?
Ba ke kika mak'aleminba''...
Kamar za tayi kuka haka take kallonsa...
Murgud'a bakinta tayi,tana hararansa...
Huh!''lallai yarinya kin samu sake,ni kikema haka?
Lip ensa na k'asa ya d'an cije,Buh ba komai zanyi maganinki''...
Ko kafin ya sake yin magana,kiran sallah ya katsesa...
Shiru sukayi na wani lokaci,suna maimaita kiran sallan da sukaji...
''Muje lokacin sallah yayi,mayi maganar letter,yanzun tunda kin ganni hankalinki ya kwanta,ki daina mafarkina''...
Ya fad'a yana winking eye en sa
d'aya...
Kukan shagwab'a tasa,shi kuma ya shiga dariya,cikin sauri ta fice daga parlorn tayi cikin gida...
Bin bayanta yayi,yana murmushi...
Tana shiga parlor bata tsaya ba tayi hanyan stairs,dai² lokacin ya k'araso cikin parlon...
Sautin dariyansa da ta jiyo a bayanta,yasa ta juyo tana cuno baki
''Allah bashi kaci sai na rama''...
''Mene naji ana za a rama?''
Maganan MAMMY ta katse su...
Juyowa sukayi duka suna kallon inda maganar ta fito...
Tana zaune kan sofa tana murmushin jin dad'in ganinsu a haka...
Dawowa JIDDAH tayi,ko kafin tace wani abu,YAH BOSS ya bawa MAMMY amsa
''Kawai fa MAMMY rigimarta ce ta motsa''
''A'a fa kaga ban son haka,da gani laifin kane,tunda kace babu komai''...
Kansa ya shiga shafawa,yana murmushi...
''Dama na sani ai,kai kam ka zama BABBAN KWABO''...
Aifa dajin haka me JIDDAH za tayi inba dariyaba...
''MAMMY kinganta ko,kice ta denamin dariya''
Uwa zaiyi kuka yake kallonta,ganin har hawaye take saboda dariya...
Hakan da yayi yasa MAMMY dariya
''Maza kuzo kuga YAYANKU yana shagwab'a''
Tayi maganar dai² lokacin da IKHRAM da LITTLE suka k'araso cikin parlorn...
Ita kam LITTLE kallonsa kad'ai tayi tana tab'e baki..
IKHRAM kuwa kusa da shi taje ta zauna,tana b'ata rai,ita a dole tana tayashi....
Katse firan sukayi suka nufi yin Sallah,bayan nan suka d'ora a inda suka tsaya...
*9:20pm*
Kowa ya k'ule a d'aki,text ne suka shiga tururuwar shigowa cikin phone en dake ajiye gefen pillow...
Dai² ta idar da sallah ta mik'e,wanka tayi,ta gama shirinta cikin nighteey enta...
Wayanta ta janyo ta shiga chat enta,cikin farin ciki da annashuwa da bata tab'a tsintar kanta a cikiba haka take chat a wannan dare...
Tarin tambayoyi da suke cikin kanta sun mata yawa,wanda take son yinsu,amma ta kasa,haka ta barma kanta abun a ranta zuwa lokacin da zata ji daga bakinsa....
LITTLE ce ta fito daga toilet,sai da ta bari ta kammala shirinta na kwanciya,sannan ta kalli JIDDAH dake ta faman murmusawa...
Har ta kwanta ta juyo tana kallonta
''Wai kam CWEETY bafa kicemin komaiba akan bak'on naki''..
A d'an kaikaice JIDDAH ta kalleta tana dariyan da ita kad'ai tasan ma'anarsa...
Uhmmm! ''kin san kuwa wani abu?''
Shiru bata ce mata komaiba,hakan da tayi yasa JIDDAN sake kallonta...
''YAH BOSS ne bak'on ba wani daban ba''....
Ai kafin ta k'arasa sai ganin LITTLE tayi a tsaye a kan bed en ta dafe chest enta da hannu,tana dad'a zare idonta...
Dariya sosai JIDDAH take ganin yanda LITTLE en ta firgice lokaci d'aya...
''Uhmmm! dama kin zauna dan wallahi baki ga komaiba,da kece ni kuma kiyi yaya lokacin da kika gansa a tsaye in front of u?''...
Kamar wata marainiya haka ta zauna jagwaff a kan bed en tana tallafe kumatunta duka ta side biyu...
Ta kasa magana,ita kuma JIDDAN tana niyyan yin magana kiransa ya katseta,screen en ta nunawa LITTLE dake binta da kallo..........
*_~TEAM J²~_*
*_REAL SMASHER._* 🤞🏻😘
[4:00PM, 4/16/2018] rєαl ѕmαѕhєr 💃🏻: 💠💠 *RAYUWAR WANI......*
_{ơŋɛ'ʂ Ɩlıʄɛ...}_
💠💠
🌹
*Viawattpad@realsmasher01.*
*©® 2018.*
*16/ąpril,2018.*
*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ...*
*ცყ.*
_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._
*~__________________________~*
*ADDU'AR TAFIYA MASALLACI.*
_ALLAHUMMAJ'AL FIY K'ALBIY NURAN,WAFIY LISANIY NURAN,WAFIY SAM'IY NURAN,WAFIY BASARIY NURAN,WAMIN FAUQIY NURAN,WAMIN TAHTIY NURAN,WA-ANYAMINIY NURAN,WA-ANSHIMALIY NURAN,WAMIN AMAMIY NURAN,WAMIN KHALFIY NURAN,WAJA'AL FIY NAFSIY NURAN,WA-A'AZIMLIY NURAN,WA-AZZIMLIY NURAN,WAJA'ALLIY NURAN,WAJA'ALNIY NURAN,ALLAHUMMA A'A'DINIY NURAN,WAJA'AL FIY ASABIY NURAN,WAFIY LAHAMIY NURAN,WAFIY DAMIY NURAN,WAFIY SHA'ARIY NURAN,WAFIY BASHARIY NURAN,ALLAHUMMAJ'ALLIY NURAN FIY K'ABARIY,WA-NURAN FIY IZAMIY,WAZIDNIY NURAN,WAZIDNIY NURAN,WAZIDNIY NURAN,WAHABLIY NURAN._
*_~#HISNUL-MUSLIM.~_*
*~_________________________~*
_Masoya novel en *Y'AR GARUWA* ina mai baku hak'urin jina da kukayi shiru kwana biyu,in sha Allah zan ci gaba nan da wani d'an lokaci._
*#Really luv u irin wujiga-wujiga ennan...* ❤
*~_________________________~*
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)........*
*℘ąɠɛ 75↔76*
Da sallama ta d'auka kiran,tana murmushi...
Silalewa tayi ta kwanta,idonta a lumshe saboda wani feeling dad'i da take ji,wanda jinta take tamkar bata tab'a kasancewa a cikinsa ba iya rayuwarta...
A zuciyanta kuwa godiya take ga ubangiji da ya k'addara wannnan al'amari,fuskanta d'auke da tsantsan farin ciki....
Duk abunda take akan idon LITTLE,tun da ta tallafe kumatunta,tak'i bari su huta,haka take zaune tana jiran lokacin da zata gama...
Waya suke kamar da,yana dad'a bayyana mata asirin zuciyarsa,ita kam jinta take kamar ba a duniyar take ba...
Wani sanyi na dad'a ratsa mata zuciya,haka suka kwashe tsawon lokaci,suna abu d'aya..
Ba dan sun soba suka hak'ura,coz dare yayi sosai,nan sukama juna sallama,uwa baza su rabuba...
Idanunta ta shiga bud'ewa da take jin sun mata nauyi...
LITTLE dake zaune har lokacin idanunta suka sauka akai,hakan ba k'aramin tsoro ya bata ba...
Mitsikasu ta shiga yi,coz ita tayi tsammaninma tayi bacci tun da taji shiru,batayi tunanin tana zauneba still,coz tun da suka fara wayan idanun suke a rufe...
Ajiyan zuciya tayi lokacin da ta gane SISIN nata ce zaune tana waiting enta kan son jin labarin yanda aka haihu a ragaya.....
''kin san kuwa irin tsoron da kika bani,har ga Allah nayi tunanin kinyi bacci zuwa yanzun''
''Ta ina zanyi bacci banji labarin inda aka kwana ba''
Ta fad'a tana mai dad'a baza kunnuwanta ga JIDDAN...
''Ke wallahi son labarinki ne yake had'ani da ke''
tana mai hararan LITTLE take maganar..
Ita dai bata ce,komai ba sai dai ta zare hannayenta daga tagumin da tayi...
Haka dai JIDDAN ta bata labarin abunda ya faru daga zuwanta zuwa lokacin da taga face nasa...
Dogon ajiyar zuciya LITTLE tayi tana mai dad'a jinjina al'amarin...
''Kinga ikon Allah koh sis,ke da kina tsammanin mutum biyu,sai gashi kin tarar da duka mutum d'aya ne,gaskiya na jinjinawa YAH BOSS a wannan fagen...
Sai dai har yanzun ban daina mamakin yanda akayi ya aikata haka ba,Allah da wani ya fad'amin zaiyi haka bazan yarda ba,amma sanin ikon Allah ya wuce haka dole ne ka amince
Allah ya sa mu dace''...
Gaba d'aya suka amsa da ameen,suna masu kwanciya,kowa da tunanin da ke zuciyansa...
*A WEEK LATER.*
Yau tsawon sati guda kenan da faruwar wannan al'amari,wata shak'uwa da soyayya wacce basu tab'a tsammanin nunawa juna ba ko da a labari,ita suke nunawa junansu..
Sai dai duk da hakan tun daga ranar suke wasan b'uya tsakaninsu..
A b'angaren JIDDAH da ta jiyo alamun zai k'araso guri take yin hanzarin barinsa..
Kasancewar a kwanakin bai cika dawowa gida da wuriba,wani lokacin har sai sun kammala dinner yake dawowa...
Wata ranar ma haka zai dawo ya tarar kowa ya shige d'akinsa..
Da safema ya sake ficewa da wuri,kasancewar yanzun suna yawan samun patients...
Sai dai duk lokacin da ya dawo afrer ya kammala abunda zaiyi suyi waya duk da a gida d'aya suke rayuwa,had'uwa ta musu k'aranci...
Yau ya kama k'arshen sati,gidan kuma tunda suka tashi sallan asuba basu zauna ba suna ta fama da aiki...
Ba su suka gama ba sai around 10:00am shima dan sun kasance su 5 suke aiki,coz MAMMY ba irin matan da suke sangarta yaransu da rashin aiki bane...
JIDDAH suka bari a k'arshen fitowa daga kitchen kowa ya tafi wanka...
Sai da ta kammala gyara kitchen en,sannan ta fito tana sauri zata d'akinsu...
A kan hanya sukayi karo,lokacin yana sakkowa daga stairs,yana d'aura watch a tsintsiyar hannunsa...
Ita kuma tana k'ok'arin hawa,tana tafe tana duba hannunta data buge da k'ofa garin sauri...
Karo sukayi da juna,hakan yasa JIDDAH dake k'asa tayi baya zata fad'i,saurin sa hannu yayi ya tarota..
Idanunta a rufe sabida ta gama tsorata sai ta kai k'asa..
Sosai ya rik'eta uwa wacce za a k'wace masa ita,jikinta sai rawa yake saboda ta gama tsorata...
Kallonta ya shiga yi,duk da babu makeup a face enta tayi matuk'ar yi masa kyau..
Ko kuma dan ya kwana biyu bai ganta ba yasa yake ganin haka...
Jikinta ta shiga k'ok'arin k'wacewa daga garesa,amma ta kasa,saboda irin rik'on da yayi mata...
''Please YAH ka sake ni na wuce''
Kanta a k'asa take maganar
''Idan na k'ifa?''
Shiru tayi babu amsa,shi kuma ya ci gaba da kallonta...
Muryansa k'asa² yake magana
''Laifin me nayi kike b'oyemin kanki?''..
Bakinta ta cuno gaba,kome ta tuna kuma tayi murmushi...
Hakan da tayi yasa shi yin k'wafa had'e da cije lower lip nasa,yana mai gyad'a kansa...
''To ae ba laifina bane''...
''Hakama zaki ce ko?''
Yayi tambayan fuskansa babu alamar wasa...
Ganin bata bashi amsa ba yasake ta,take ta sake tafiya zata fad'i,coz dama a jikinsa take...
Da hannayensa duka biyu ya sake tallafota,sai da ya tabbatar ya tsaida ita sannan ya sake ta,yana shirin sauka,har ya gota inda take...
Ta furta
''Thanks!''...
Kamar bai jitaba ya ci gaba da tafiya...
Jingina tayi jikin bango idanunta a rufe ta lula duniyar tunani..
K'amshin perfumes en sa masu matuk'ar dad'i da kwantarwa da mutum hankali suka cika mata hanci....
Da k'yar ta iya jaan k'afafunta ta bar gurin saboda kasalan da k'amshinsa ya saukar mata...
Haka ta shiga bedroom en,komai yinsa take cikin rashin k'warin jiki...
Ko a toilet da ta shiga kwanciya tayi a cikin kwamin wanka,badan komai ba sai dan dad'in da ruwan yayi mata....
Da k'yar tayi wankan ta fito,shima sai da LITTLE ta dameta da kira sannan ta fito ba don ta gaji da ruwanba...
A yaune ake sa ran zuwan iyayen FAROUK gidan dan neman auren LITTLE,bisa rakiyar shi kansa FAROUK en..
Tunda suka zo,FAROUK da LITTLE suke tare a guarding suna fira..
Har su DADDY suka gama abunda za suyi...
Kiran uncle ensa shi ya katse musu firan da suke..
''To mu zamu wuce,kai kam nasan dai ba yanzuba,ko?''
Ya tambaya yana murmushi..
Kame² FAROUK en ya shiga yi kamar mara gaskiya..
Dariya kawai UNCLE en nasa yayi,yana fad'in
''Ka same mu a gida''...
''To UNCLE''....
Haka suka ci gaba da firansu cikin nishad'i,da nunawa juna kulawa ta musamman...
Kwance take kan bed en abun duniya duk ya dameta,ta san ko ba a fad'a mata ba,tabbas YAH BOSS fushi yayi da ita..
Damuwa duk tayi mata tawa,ta kasa tunanin mafita...
Mik'ewa tayi ta nufi hanyan fita saga d'akin,a parlor tayi masauki..
Haka wunin ranar ta yishi sukuku,magana ma bata samun damar yinta sosai..
Koda MAMMY ta ga yanayinta da ta tambayeta,cewa tayi bata jin dad'i ne...
Sannu ta mata,ta kuma shaida nata ta nemi magani ta sha....
Ko da darema da za ayi Dinner bata wani ci abinci sosaiba,haka har aka gama fira kamar yadda aka saba,kowa ya fashe,sai ita da LITTLE...
Gajiya LITTLE en tayi ta bar gurin,amma itan still tana zaune,tun da YAH BOSS ya fita ko flash be had'a su ba a wunin ranar,ta san kam ba k'aramin fushi yayi da ita...
Tana wannan tunanin bacci ya d'auketa a parlon...
*********
Shigowansa kenan gidan a gajiye saboda tun bayan da suka sallami bak'in DADDY ya fita d'aurin aure daga can kuma suka wuce Dinner party,sai yanzun ya samu kansa...
Har yayi parking ya shigo cikin gidan,shiru babu motsin kowa..
Har ya wuce zai haura stairs en ya juyo ya nufi dinning,sai bayan da ya zauna kamar an ce ya d'aga kansa ya ganta kwance tana bacci...
Mik'ewa yayi ya nufi inda take,har ya zo kusa da ita yana tunanin abunda yasa take bacci ita d'aya a parlor...
Wani murmushi yayi tunowa da yanda sukayi da safe kafin ya fita...
''Allah sarki beautyna,na walar dake yau,ba komai yasa nayi miki haka ba,sai saurin da nake ban son makara''...
Yana binta da kallo yake maganar yanda babu mai ji sai wanda yake closer to him...
Kneeling yayi a gabanta,ya shiga shafa face enta...
Cikin baccinta taji ana tab'a mata fuska,cikin mayen bacci ta shiga bud'e idanunta,ganinsa a durk'ushe a gabanta yasa taji mamaki,tayi saurin mik'ewa ta zauna....
''YAH kayi hak'uri please,nasan kana fushi da ni ne''
Tana maganar kamar za tayi kuka..
Shiiiii!ya fad'a yana girgiza mata kai..
Shiru tayi tana binsa da kallo
''Ba kiyimin laifi ba''
''To amma me yasa ka manta da ni?''
Uwa wacce za tayi kuka take maganar idanunta na son zubar da hawaye...
Kusa da ita ya zauna yana mai had'a jikinsa da nata..
''Don't cry baby,
Bakiyi laifi ba,hasalima ni namiki laifin,tun da na fita ban kirakiba,
Buh!it will never been happen,ok?''...
Kai ta kad'a masa tana dad'a kwanciya a jikinsa,banda ajiyan xuciya babu abunda take...
''OK! maza tashi muje na baki abinci,nasan da wuya idan kinci''
Ya fad'a yana k'ok'arin sa hannunsa akan plat tommy enta...
Dad'a k'ank'amesa tayi ta hana shi aiwatar da abunda yake son yi...
Murmushi yayi ya mik'ar da ita tsaye,hannunta ya jaa sukayi dinning,da kansa ya bata abincin,a cewarsa ae shi ne da alhakin kula da ita tunda shi ya jaa hakan ya faru......
Sun jima a gurin kafin suka mik'e da nufin barin gurin..
Har sunje bakin stairs ya koma,wutan ya kashe..
Duhun da ya gauraye wajen yasa ta k'ank'ame rillern stairs en...
A cikin duhun ya taho har dai² inda ya barta...
Jinsa kusa da ita tayi masa wani mugun rik'o wanda shi da kansa sai da hakan ya bashi tsoro...
Light en Phone nasa yayi powering yana haskata duk tabi ta k'ank'amesa...
Murmushi kad'ai yayi ya d'auketa,yana tsallake steps en..
Room ensa da taga yana nufa shi yasata zaro ido waje...
''YAH me zanyi kuma a d'akinka?''
Wani killer smile yayi,cikin rad'a ya furta
''Yau ai tare zamu kwana,dama ai ni kija jira''
Ba shiri ta dire daga jikinsa,da gudu ta bar gurin ta shige d'akinsu...
Shi kuwa nan ta barshi yana kwasar dariya...........
*_~#TEAM J²~_*
*_REAL SMASHER._*🤞🏻😘
[6:26PM, 4/17/2018] rєαl ѕmαѕhєr 💃🏻: 💠💠 *RAYUWAR WANI......*
_{ơŋɛ'ʂ Ɩlıʄɛ...}_
💠💠
🌹
*Viawattpad@realsmasher01.*
*©® 2018.*
*17/ąpril,2018.*
*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ...*
*ცყ.*
_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._
*~__________________________~*
*ADDU'AR SHIGA MASALLACI.*
_A'UZHUBILLAHIL AZIYM,WABI-WAJHIHIL KHARIM,WASUL'DANIHIL-K'ADIYM,MINASH-SHAI'DANIR RAJIYM,BISMILLAHI WASSALATU WASSALAMU ALAA RASULILLAH ALLAHUMMAFTALIY ABWABA RAHMATIK..._
*_~#HISNUL-MUSLIM.~_*
*~_________________________~*
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)........*
*℘ąɠɛ 77↔78*
Da k'yar ya tsaida dariyan da yake ya shige bedroom en...
A jikin k'ofan ta jingina bayanta tana tuna yanda sukayi da YAH BOSS yanzun,sai yanzun abun ya soma bata dariya..
Tana ta faman zuba smiling ta nufi closet ensu..
Nighteey enta ta d'auka ta nufi toilet..
Tun kafin ta kammala abunda take ta soma jiyo kiran da ake mata a waya..
Cikin sauri tayi ta fito,ko kafin ta k'araso har ya katse..
Tsaki tayi ta d'auka phone en coz ta san mai kiran..
Tun kafin tayi wani yunk'uri, wani kiran ya sake shigowa..
'Dauka tayi tana murmushi,tun kafin ta kai ga yin magana,maganarsa ta dakatar da ita..
''Ina kika shiga ne,ina kiranki?''...
''Ina shirin kwanciyane''...
''Ok bari na k'yaleki tunda dama nina tasheki''
Ya fad'a yana jiran jin me zata ce..
''Uhmmm!''
Kad'ai ta iya fad'a tana bin lafiyar gadon...
Hira suke cikin nunawa juna kulawa ta musamman,suna cikin hiran ne daf da zasuyi sallama yace mata
''Wai d'azu me yasa kika gudu?''
Shiru tayi tana murmushi..
''Matsoraciya kawai,ni na zata jaruma zan aura,ta dinga bani jaruman y'ay'a,sai gashi na b'ige da auren matsoraciya''....
Dariya sosai tasa masa kafin ta bashi amsa da
''Tsoro ae halak ne''...
''Heyy!madam inji wa yace haka?bani aya ko hadith da yace haka''...
_''INNAL KHAUFI HALALUN''_
Ai tana fad'an haka suka sa dariya gaba d'ayansu,JIDDAH ko har da hawaye tsabar mugunta,kuma ta fuske kamar ba ita ta fad'a ba....
''Wannan dai larabcin kine''
''Ai dai nayi k'ok'ari duk da haka''....
Cike da tsokanar juna sukayi sallama...
_#Sabahul khair j².._
*********
MAMMYN yara zauna muyi magana,DADDY ya fad'a yana kallon MAMMY da ta shigo d'akin....
Jin hakan yasa ta nemi guri ta zauna a kusa da shi..
Ina so muyi shawara kafin wayewar gari game da yanda auren yaran nan zai kasance...
Kwashe yanda sukayi da iyayen FAROUK yayi ya sanar da ita,sannan ya d'ora da fad'in
"Yanzun haka mun yanke ranar auren nanda wata d'aya,saboda haka sai a fara shirye²,dan na san ku mata a kwai ku da son bidi'a,duk wani abun buk'ata sai a sanar da ni"....
Ya fad'a yana dariya....
Addu'ah tayi na fatan alkhairi,daga haka suka ci gaba da firansu,cikin nishad'i...
Ganin haka yasa nayo waje....
*********
Kwanaki sun dad'a jaa,tun daga ranar da DADDY yama MAMMY maganar auren batayi sakaciba,dan kuwa cikin satin ta nemi mai gyaran jiki ta gaske..
Duk da suna zuna zuwa skul hakan bai hana kyan da sukayi ya bayyanaba..
Kullum sai an musu gyaran babu fashi....
Hidimar biki ya tashi ganga² kowane gefe babu zama...
DADDY da kansa ya tambayi kowa abunda yake so,haka suka zayyana masa babu b'ata lokaci...
Da kansa ya bada oder akan komai da ake buk'ata,dan cewa yayi bai yarda MAMMY ta kwashesu du bar k'asar ba..
Saboda idan ta tafi dawa zasu zauna,lokacin da ya mata maganar dariya lamarin yabata...
Tasan gaskiya ya fad'a,shi yasama bata wani damu ba da ya shaida mata ya riga ya bada order komai...
Godiya had'e da addu'ah su ta masa,na samun bud'i...
*********
Ranar ta yau ta kasance Jumu'ah tun bayan da aka sakko a masallaci ya dawo gida...
Wanka yayi ya gama shirinsa cikin k'ananan kaya,black nd red colour...
Sosai kayan suka amsheshi,banda k'amshi babu abunda yake zabgawa...
Dai² saitin bedroom ensu suka had'u da shi yana shirin sauka k'asa...
Kallon juna sukayi,sukayi exchanging smile..
Har ya wuce ta,ta ce
''YAH anguwa za kane?''
Wani killer smile ya saki kafin ya juyo...
''Yeah!zance zani,kin san ku biyu za a kawomin,da wani abu ne?''
Wani takaici ne ya k'ulleta,a fusace ta juya ta shige d'akin ba tare da tace komaiba..
K'ofan ta buga da k'arfi,wanda shi da kansa sai da yaji bugun...
Kan bed ta kwanta a kan cikinta,kamar za tayi kuka,duk kuma sai taji haushin kanta kan tambayar da tayi masa...
K'aran shigowan text ya sata d'agowa tabi wayan da harara,kamar bazata duba ba,zuwa can kuma ta jaa wani tsaki,ta bud'e...
_Ki sameni a guarding ina jiranki,amma kar a tahomin ana kumbura fuska..._
Abunda ya rubuta kenan....
Wani sanyin dad'i ne ya ziyarceta,har bata san lokacin da tayi tsalleba...
Cikin sauri ta shirya ta had'e cikin fitted gown na wani robber yard bak'i,jan vail tayi rolling da shi,face ennan ta sha make up...
Cikin takunta mai burgewa ta fito ta nufi guarding en...
Tun daga tahowarta yake binta da kallo,a zuciyarsa kuwa fad'i yake
''Wato munyi anko kenan''...
Da sallama ta k'araso...
Maimakon ta zauna kan seats en dake gurin sai tayi zamanta kan grasses en tana wasa da su....
Sai da ya jima yana kallonta ba tare da yace komaiba,zuwa can kuma ya sauka k'asa kusa da ita....
Phone ensa ya fiddo daga pocket,ya shiga d'aukanta a photo...
Duk abunda yake bata saniba,shi kuma sai murmushi yake...
''D'an d'ago kiga wani abu''
Kanta ta d'aga tana kallonsa,hasken flash en da ta gani shi yasa ta gane me yake nufi...
Murmushi ta sakeyi ta sunkuya....
Cikin salon tsokana ya kalleta yana fad'in
''HAYATEEY!''
Tun daga cikin brain enta har cikin fingers enta sai da kowane gab'a ya amsa....
Ido ta lumshe saboda dad'in sunan da taji ya ambata...
''Tashi ki rakani zancen,dama ke nake jira''
Ko second ba a k'ara ba ta ware idanunta a kansa tana masa wani birkitaccen kallo''
Shi kuma fuskansa babu wasa yaci gaba da magana
''Oyaaa!tashi mana karki b'atamin lokaci''
Ya mik'e yana gyara tsaiwansa...
Kallonsa taci gaba dayi,shi kuma ya had'e fuska kamar gaske....
Hawayen da suka fara sauka kan fuskanta,su suka sashi saurin rage tsawonsa yana fad'in
''Ya salaam!!!''
Rarrashinta yake amma kamar wacce ya dad'a zugawa,sai da tayi mai isarta sannan tayi shiru...
Shi kuwa gogan banda aikin goge mata hawayen ba abunda yake....
''Mene abun tada hankali anan HAYATEEY?idan kikace bakya sofa an gama magana,bazan k'ara ba ko da kuwa a wasane''...
Aifa jin ya fad'i haka yasa ta kuma b'are baki tana wani sabon kukan....
Kansa ya dafe yana kallonta..
Sai da ya had'ata da Allah sannan tayi shiru...
Kallonta yayi yace
''Mene kuma ya sake faruwa?''
''Ba kaineba wai kace ko da wasa ba zaka sake fad'a ba,kenanma da gaske ne maganar da ka fad'a''....
Ta fad'a tana share k'wallan dake gefen fuskanta...
''OHHH! HAYATEEY da wasa nake ba gaske bane,bakina ne ya fad'i hakan,babu wata y'a mace da take burgeni ko zata burgeni idan ba keba''....
Ya d'an saurara yana kallonta...
Bakinta ta cuno ita nan tana fushi...
Kallonta yayi yana rik'e kunne
''Pardon please HAYATEEY,kar nayi miki kuka''...
''Kayi mana nima ae ka sani nayi''
Tana murgud'a baki
''Ohh!hakama za kiceba?''
Ta kad'a masa kai...
Murmushi yayi ya jingina jikinsa a nata
''Tunda so kike nayi baran yiba''...
Kamar k'aramin yaro haka yayi maganar,yanda yayi shi yasa ta dariya....
Ganin ta ware shima yaji dad'i sosai,nan kuma yaci gaba da janta da wasa da dariya har ya samu ta ware gaba d'aya....
Fira irinta masoyan da suka juk'u da begen juna ita suke,suna exchanging kalamai masu ratsa zuciyan mai sauraro,haka suka kasance tare har na wani tsayin lokaci...
***********
Yau kimanin sati biyu kenan da saka ranan auren...
Wanda hakan ya rage saura sati biyu dai² kenan...
Cike parlorn na MAMMY yake da y'an kawo lefe daga tawagar gidansu FAROUK...
Kaya sunyi sosai ta inda sai d'agawa ake ana sam barka...
Bakajin komai sai maganar mata suna shewa...
MAMMY na zaune gefe ita da MAMMAN HUBBEEY suna firansu...
Haka taro ya watse,inda MAMMY ta cika su da garan kayayyaki,kowa ya tafi yana murna............
*~#Ni da nake gefe kuwa cewa nayi wannan ai bakuga komaiba,ku jira bikin ya k'araso........~*
*_~#TEAM J²~_*
*_REAL SMASHER_*🤞🏻😘
[6:34PM, 4/18/2018] rєαl ѕmαѕhєr 💃🏻: 💠💠 *RAYUWAR WANI......*
_{ơŋɛ'ʂ Ɩlıʄɛ...}_
💠💠
🌹
*Viawattpad@realsmasher01.*
*©® 2018.*
*18/ąpril,2018.*
*ʂɬơrყ ąŋɖ ῳwrıɬɬɛŋ...*
*ცყ.*
_HAWWA M.U {SMΔSHΣR}._
*~__________________________~*
*ADDU'AR SHIGA MASALLACI.*
_A'UZHUBILLAHIL AZIYM,WABI-WAJHIHIL KHARIM,WASUL'DANIHIL-K'ADIYM,MINASH-SHAI'DANIR RAJIYM,BISMILLAHI WASSALATU WASSALAMU ALAA RASULILLAH ALLAHUMMAFTALIY ABWABA RAHMATIK..._
*_~#HISNUL-MUSLIM.~_*
*~_________________________~*
*Dyed in the wool to my beloved Mom H.Maryam H.S (Magarya Family)........*
*℘ąɠɛ 79↔80*
Kwana biyu tsakani kayan JIDDAH suka iso wanda DADDY shi ya d'auki nauyin komai tun daga kan kayan d'aki har zuwa Lefen YAH BOSS...
Dan kuwa cewa yayi tukuicin da zai basu kenan na sashi farin cikin amincewa da hukuncinsa,ba tare da sun yi masa gardama ba...
Akwatinane masu d'an karen kyau,kowanne dank'are da kaya,dan ko rufuwa basayi...
Kowa sai murna yake,yanda DADDY ya narka dukiya akan auren y'an lelen nasa...
Kaya sunyi kyau sai fatan zaman lafiya ga amaren da angwaye,da ma su kansu iyayen amaren da angwayen....
Lokaci na dad'a tafiya bisa shud'ewar sekonni,zuwa mintuna,hakama awanni suke biyo baya,yayinda dare ya shiga za ka tarar har sapiya tayi Daren ya tafi kenan kamar yanda yini ya wuce...
Haka ce ta kasance ga ragowar kwanakin da sukayi saura,zuwa yau ya rage sati 1,acikin satin ne kuma MAMMY ta hana su JIDDAH fita,kullum suna cikin gida,shima babu mai ganinsu sai ita sai kuma mai gyaran jikin su...
Damuwa kam YAH BOSS ya shigeta na rashin ganin HAYATEEYN nasa,sai dai kullum su kasance tare a waya kamar ba gida d'aya suke rayuwaba.....
Tun yanama MAMMY magiya ta bar shi ya ganta har ya zo ya hak'ura....
Fushi ya shiga yi da y'an gidan gaba d'aya,idan ya fita tun safe baya dawowa sai dare,shima sai ya tabbatar kowa yayi bacci,sannan zai shigo gidan...
Kwance take har ta fara bacci k'ishi ya dameta,tun tana daurewa har dai ta ga ba abunda zata takura kanta akai bane...
Tashi tayi ta sauka,cikin kitchen ta shiga ta d'auka goran ruwa da cup,sai bayan ta sha tukun ta fito....
Wutan ta kashe ta juya zata koma,ta hango shi yana rufe k'ofan parlor...
Still tayi a wajen kamar an shukata ta kasa motsi...
Rabonta da shi tsawon kwanaki 10 kenan...
A matuk'ar gajiye yake,hakan yasa baiyi k'asa a guiwaba ya juyo da k'arfinsa...
Karaf idanunsa suka sauka akanta tana tsaye cikin kayan bacci...
Sam JIDDAH ta manta wane irin kaya ne a jikinta,shi yasa har ta ci gaba da tsaiwa...
A hankali ya ci gaba da takowa har zuwa gabanta...
Kamar a mafarki haka suka tsaya kallon juna,tamkar sababbin halitta....
Sihirtaccen K'amshin da jikinta ke fitarwa,da azababben kyaun da tayi shi ya dinga fisgarsa,amma yana daurewa coz yasan shaid'an ke son shiga tsakaninsu...
Kallonta ya tsaya yi yanda tayi kyau cikin shigar baccin,kome ya tuna yayi saurin kawar da kansa yana fad'in
''A'uzhubillahi minash-shaid'anir rajiim''
Hakan da yayi shi ya ankarar da ita,da sauri ta kalli jikinta,idonta ta fiddo waje,kafin wani lokaci ta b'ace a gurin....
'Dagowa yayi da niyyar mata magana sai dai ya nemeta ya rasa...
Dak'yar ya iya barin gurin saboda halin da ya tsinci kansa aciki....
Tunda ta samu ta bar gurin bata k'ara gigin fitowaba tun daga ranan,suka koma wasan b'uya....
***********
Shirye² sun fara nisa komi ake su HUBBEEY ana kan gaba,dan ko *I.V* da yawa cikin course mate ensu ita ta basu a skul,tunda abun ya zama na zamani,wanima a phone za a turo maka kuma kaje...
Shi yasa ma da yawa basu wani damu ba,yayin da kad'an daga cikinsu suke k'orafi,sai dai babu wanda yabiya ta kansu.....
A haka har aka soma shiga cikin satin biki...
************
Tunda kwanakin suka dad'a kusantowa,shirye²n nasu ya dad'a k'arfi,sune gurin saloon ga zaman henna da aka d'auko matar har gida.....
Yau ya kama ALHAMIS kuma tun daga ranar aka tsara za a fara gudanar da events en bikin,in da za a fara da KAMUN AMARE.....
*4:30pm*
Harabar gidan dank'are take da jama'ah wad'anda aka gayyata,dama y'an ganin k'wak'waf...
Dan kuwa akwai y'an gaiyyar sod'i wad'anda babu wanda suka sani,k'aunar zuwa ganin me akeyi ya kawo su...
Sai a round 5:00pm amaren suka fito sanye cikin wani rantsatstsen shadda,sun sha ado...
Gefensu kuma MAMMY ce da MAMMAN HUBBEEY sun kamosu,har mazaunin da aka tanadar musu...
Kowa ya nemi guri ya zauna,masu gulma nayi masu sa albarka nayi...
Can kusa² da amare na hango tawagar masoya RAYUWAR WANI,abun har mamaki ya bani,sun sha ado tun daga matan aure har zuwa kan wad'anda suke hanya,ko wacce ta basar gudun kar a raina su,kun san mutanen ba sauk'i......
Hasken flasher ke tashi ana bada selfie...
Gaba d'aya wunin ranar haka akayi shi babu namiji,har aka k'are taron kamun,kowa kuma yayi nasa guri....
********
A washe gari kuma ranar JUMU'AH za a gudanar da dinner...
Tunda misalin k'arfe 7:00pm motocin suka fara jidar y'an mata zuwa gurin da za ayi dinner...
Wato *JAMEYS PLAZA* daga sama aka rubuta boldly,gurin a matuk'ar tsare yake babu zancen wani ya karewa wani,haka mutane suka zauna kowa a seat ensa...
In da *MR DJ* ya soma sakin sauti,wanda idan ba mutum ya kama kunneka ba ba yadda za ayi kaji me yake cewa....
A can gida kuwa,amaren ne zaune make-up artist's en sun dage sai fente musu fuska suke,kowacce burinta tayi abunda za ace ita tafi y'ar uwarta....
Gefensu HUBBEEY ce cikin kwalliyarta wanda idan ba mutum yayi da gaskeba ba lallai ne ya iya ganeta ba,saboda kyaun da ta k'ara......
Cikin weeding gown blue colour da silver en head nd shoe,,haka ma duk wani abun ado dake jikinsu ya kasance siver, sosai suka fito acikin shigar tasu kamar a sace su a gudu,shigarsu iri d'aya komai da suka saka a ranar...
Haka aka rako su wasu daga ciki suna d'auke da k'asan rigunansu saboda yanda suke jan k'asa,har bakin motor....
Nan ko wacce aka nuna mata inda za ta shiga...
Tsaiwa sukayi suna kallon juna,kafin sukayima juna murmushi had'e da rungume juna,sakin juna suka yi kuma suka juya a tare...
Gaba d'aya wad'anda ke gurin suka sa sowa na abunda suka yi,ba k'aramin burge mutanen sukayi ba....
Har bakin motor en aka kai kowacce,tare da bud'e musu suka shiga....
Tun daga fitowarsu har shigowarta cikin motan akan idonsa komai ya faru,sai dai kasancewar motan mai duhun glasses ba lallaine ka gane da mutum a cikiba...
Ta shigo da sallama a bakinta,kanta a k'asa ta gaida shi...
A ciki ya amsa yana wani d'auke kai...
''Uhmmm!miskilancin ya motsa kenan''
JIDDAH ta fad'a a zuciyarta...
'Dauke kai tayi itama tana kallon gefenta,haka sukama juna shiru kamar basa cikin motar...
'Barinsu LITTLE kuwa firansu suke babu damuwan komai a tare dasu,haka suke tafiya cikin nishad'i....
Motor en na tsaiwa y'an matan suka fito don tarbar amare...
Haka suka jeru amare da angwaye na tsakiya sai wasu abokan FAROUK da kuma abokan aikin JABEER da suke gurin,wanda suma ba a barsu a bayaba gurin rakiyan angwaye....
Har mazauninsu suka rakasu,sannan kowa ya nemi gurin zamansa....
Komai da akeyinsa a wannan ranar anyi shi ne bisa wayewa da kuma tsari,coz mafi yawan kaso na gurin y'an boko ne....
Lokacin ne *MC* yakema amare da angwaye barka da zuwa..
In da aka bud'e taron addu'ah,kafin kuma aka buk'aci tak'aitaccen tarihin amaren daga b'angaren babbar y'ar uwarsu kuma aminiyarsu wato *HABIBA IDREES SA'EED (HUBBEEY)*....
Cikin takun k'asaita tamkar wahainiya haka ta bayyana gaban dubban jama'ar gurin,a tak'aice ta bada tarihinsu da yanda sukayi gwagwarmayarsu taree....
Banda tafi da maganganun mutane bakajin komai,kan yanda ta burge kowa,tana gamawa aka sa mata tafi...
Bayan ta koma ne aka koma kan angwaye,b'angaren FAROUK kam ba shi da matsala,don kuwa yana da abokai sosai...
A bangaren YAH BOSS ne aka so a kuskure,sai dai Allah ya taimaka akwai wani friend ensa da suke aiki yanzun,wanda shi ne ya zame masa kamar amini saboda tasu tazo d'aya....
Haka akaci gaba da gudanar da taron,amare na high table,sai washe baki suke kowa na farin ciki...
Duk da kafin zuwansu ya nuna miskilanci yanzun kam ya sake kamar ba shiba ko dan ganin yanda FAROUK suke ta fira ne yasa shima ya d'an fara sakewa....
Kamar daga sama JIDDAH ta fara jin maranta na harbawa,shiru tayi ta dafe kai,baya ga
''Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un''
Ba abunda bakinta ke furtawa...
LITTLE ta tab'o cikin rad'a take cewa
''Sis ina cikin matsala,gashi ba magani kusa,nasan tawa ta kare yau kam sai abunda hali yayiwu''...
Kamar za tayi kuka take bata labarin...
''Me kike nufi ne?''
''Uhmmm!ke dai bari,i think menses ena ke tafe''
''Dama baki lissafa kwanakin ba ne?''
''Banda abinki muna cikin wannan season en ta ina zan iya tunawa?''
Ta bata amsa uwa za tayi kuka
''Eyyahhh!don't mind dear anything will be fine''
Hannunta akan kafad'anta take mata maganar...
Uwa za tayi kuka haka ta juya,tana kallon taron jama'ar....
Haka take zaune duk jinta take cikin damuwa....
Da kad'an² ciwon ke k'aruwa wanda take dauriya tana dannewa gudun kada a gane halin da take ciki...
Wani mahaukacin murd'a mata da yayi yasa tayi k'asan table en tana damk'e gurin idanunta a rufe gam,d'ayan hannun kuwa yana kan seat en da take ta dunk'ule shi...
Da sauri YAH BOSS ya kalleta ganin abunda takeyi...
A birkice ya shiga tambayanta
''HAYATEEY! are u ok?''
Tambayan da yayi mata shi ya dawo da hankalin LITTLE kansu,k'asa tabi sis en nata tana jijjigata...
Ganin ta kwanta tana juyi a gurin, YAH BOSS a gigice ya kinkimeta ya nufi hanyar fita da ita daga gurin...
Bayansa LITTLE tabi aka bar jama'a da tambayan meke faruwa....
A bakin motar YAH BOSS ya tsaya ya kalli LITTLE dake kuka
''Ki koma ciki kada kuma gurin ya zama babu kowa,shi dawa kika barshi,maza koma muma xamu dawo kinji''...
Badan ta so ba haka ta koma,shi kuma ya kwantar da ita a back seat,shima ya shiga...
A 360 motar tasu ta bar harabar gurin,drivern na tambayansa asibitin da zasu...
''Kaimu wanda yake kusa''
Amsar da ya iya bashi kenan,hankalinsa na kan JIDDAH da gaba d'aya sai dad'a cukuikuyeshi take saboda azabar da take ji...
Zip en rigan ya zuge,ya bud'e rigan sosai,dai² saitin maranta ya sa hannunsa yana mata massaging gurin...
Ciwon taji yana d'an lafawa kad'an...
Kafin su k'arasa hospital en ciwon ya dad'a k'arfi har ya so yafi na farko...
Wani irin juyi tayi a jikinsa,take kuma jikinta ya saki,ta sank'ame,tuni ta daina motsi..........😭😭😭
*_~#TEAM J²~_*
0 comments:
Post a Comment