*Muna saida kayan mata da na maza suna da kyau sosai kuma cikin sauki muna turawa koina ga me bukata seya tuntubi wannan number👉🏼 0806 672 6866*
*Ina godiya masoya...*
*Pherty abdull... my daughter ina matukar godiya da soyayya Allah yabada saar karatu ya bada me amfani*
Alkali ya gyara gilashi yace" Kotu na bukatar ganin Megari da Habu"
Megari da kawu habu suka tashi suka isa gaban kotu ,
Alkali yacewa me gari "Lokacin da mutanen wannan ruga suka zo maka da labari wane mataki ka dauka ?na neman sanin gaskiya?ko neman yarinyar?"
Megari ya rika raba ido yana zara na mujiya ,
Alkali yace"Kasa cewa danuwanka da yarshi akaiwa haka ya zakaji?"
Megari yayi gum ba amsa,
Alkali yace"Akwai gidajen radio da TV zaku iya kai sanarwa meyasa bakuyi hakan ba? yarinya ta bata amma ana tunanin dawowarta da kanta sabida rashin tsoron Allah? "
Ganin be iya magana ba yasa shi cewa "Zaka iya komawa ka zauna"
Me gari yayi wuff ya juya sum_sum ya zauna,
Alkali ya kalli kawu yace"Kaine kawunta?"
Habu ya jinjina kai ,
Alkali yace"Meyasa baka nemi diyarka ba?"
Kawu Habu yace"Bansan me zanyi akai ba kaina ya kwance jin sherin da aka dorawa dan'uwa na da kisan gillar da akai masa shi da matar shi"
Alkali na kallonshi yayi rubutu yace"Da kaje rugar dauko dabbobi meya faru?"
Habu yace"Sun fadi cewa sun biya wadanda aka kashe nasu dabbobin da nashi a gaban megari, sun kuma ce zasu dauki kudin abincin su, da zuwana shanu hudu na samu kuma nasan dabbobin shehu na da yawa hakanan na daukosu na fito garin nasa su kasuwa na siyar na dawo da kudin gida"
Alkali na jin takaici yace"zaka iya tafiya Malam habu"
Kawu ya koma ya zauna ,
Ran alkali bace yace "Ina mahaifin Murtala me gari ?"
Me gari ya tashi ya karasa gaban kotu yana cikin tsoro kar a damke dashi,
Alkali na masa wani kallo yace"Shekara nawa kayi kana shugabanci a rugar ku?"
Me gari yace"Go..go...goma "dasauri
Alkali yace" Duk shekarun nan haka kake mulkin ? Meyasa baka dauki mataki ba? Bayan kun kashe shi meyasa baka bawa wadanda suka rasa shanunsu hakuri ba tunda kasan shanun shi sun zama na magada"
Tsoro ya kama me gari kar dan shugabancin ma ya rasa yana in_ina yace"Saboda nayi tunanin barawon ne amma duk da haka seda na tura aje rugar su a gano idan yarinyar ta isa don muji ta bakinta da suka samu batanan nafada cewa da ta dawo a sanar zanturo "
Ya kalli Murtala ranshi bace yace "Banyi tunanin Mugun na kusa dani ba ya kulla duk wannan sharrin don lalata rayuwar yarinya Allah wadaran halin ka Murtala" ya karasa yana juya kai kamar zai kuka,
Murtala ya kura masa ido yana jin bakinciki,
Alkali yace ya koma ya zauna ya kalli abokan Murtala yace"Kai ku bamu labarin yadda abun ya faru a daren ranar"
Sun jigatu suka ce"Murtala ne yasa muka kora shanun amma su nasu kadai suka kora shine kadai abinda mu kayi"suna zare kansu,
Murtala na jin ciwo sun tona masa asiri kuma suna so su barshi shi kadai,don da shi kadai ne yasan gaskiyar da sede su kashe shi baxai fadi komi ba,
Ya nuna wani yace"Kai sada kaine ka kashe inna"
Sada ya fiddo ido waje yana juye_juye yace"wallahi tallahi aradun Allah bani bane na buga mata sanda"
Alkali yayi murmushi yayi rubutu jin harya san dame aka kasheta,
Murtala ya kalli dayan yace"Kai ba da kai muka bita ba zamuyi mata fyaden?diyar gidan Surajo ai kaine kafara mata fyade"
Wanda yace ma haka ya rika juya kai yace"Murtala ni?" Ya kalli alkali yace" wallahi bani bane ba ruwana"
Alkali baice komi ba ya dukar da kai ya fara rubutu ,
Shi ko ya nata juya kai yana babu ruwanshi,
Murtala yace "Kai shege yi mana shiru "
Kotu tai tsitt alkali ya gama rubutu ya dago yace"Zan fara jawo hankalin shugabannin kauyuka da su rika sanar da hukuma abinda ke faruwa a yankunan su zata yiwu suna ganin abu a zahiri amma ba gaskiya bane, idan hukuma ta shigo ciki zatai tsatstsauran bincike sannan ta yanke hukunci dede da yadda doka ta tsara ,yin hukunci daka batare da sanar da jamian tsaro ba badede bane kuma ya sabawa dokar kasa, gashi anci zarafin yarinya an kashe mata iyaye an kwashe dukiyarsu still su ake gani mugaye masu laifin,
ina kira ga shuwagabanni da su rika kawo masu laifi wurin ainihin wadanda suka karanci doka da order donsu yi dogon bincike kafin zartar da hukunci"
Ya kara kallon littafi yace"Sakamakon kama Murtala da cin zarafin yaya mata da yi masu fyade da kuma Samar da hanyar kashe iyayen Zarah ,Kotu ta yanke masa hukuncin zaman gidan yari har karshen rayuwarsa da horo me tsanani"
Murtala ya kara tamke fuska sosai yanajin kamar ya shako alkalin ya kashe,
Alkali ya cigaba da cewa"Abokansa da suka temaka masa wurin kisan suma kotu ta yanke masu hukuncin zama gidan yari har karshen rayuwar su amma batare da horo ba"
Yana fadin hukuncin wani sanyi ne ke ziyartar Zarah tana cikin farinciki wadanda suka kashe mata iyaye sun fuskanci hukunci,hakan ce wurin su Muneera WALEED ko gani yake hukuncin da aka yankewa Murtala yayi sauki kyawunshi a harbeshi kawai sannan zaiji dede,
Alkali ya cigaba da cewa "Me gari mahaifin Murtala zai biya kudi kimanin Nera millions 2.5 ga Zarah saboda rarraba da yayi da dukiyarta da kuma bata masu suna da dansu yayi batare da sun aikata laifin komi ba ,wannan shine karshen shariar, kotu bata ba masu laifi damar daukaka kara ba"ya buga guduma da duk saida abokan Murtala suka firgita iyayensu nata hawaye suna kuka aka jasu aka fita dasu zuwa cell,
Me gari zaman dirshan yayi jin million biyu da rabi zaiyo kashinta ga tafiyar danshi gidan kaso yana cikin tashin hankali,
Zarah kuwa wani irin farinciki take ciki kuma tasan duk hakan ya faru ne ta dalilin KHALEED sun tashi suna niyyar fita taje ta rungume KHALEED tana matukar farinciki,
WALEED na gefe yaji kamar an soki zuciyarshi saboda yadda jikinta ya hadu da nashi, yayi saurin kauda kanshi gefe dasauri,
KHALEED ya lumshe ido yanajin farinciki yasa hannu ya riko Zarah jikinshi ta dago fuska tana murna hawaye cike da idonta tace" Nagode daddy Nagode sosai"
KHALEED yayi mata murmushi me kara narke mata zuciya ta kara kallonshi sannan ta nufi Muneera ta rungumeta sosai tana godiya,
Muneera tana rike daita suka nufi mota wannan karen ba HAMEED baizo ba amma ko da suka duba ba WALEED,
KHALEED ya Ciro waya ya kirashi cikin cool voice dinsa yace"Kana ina?"
WALEED da ko fita court din beba ya samu wuri ya zauna yana jinyar zuciyarshi yace"HAMEED ya kirani ina kan hanyar gidansu "
WALEED bai fahimci komi ba yace"OK "ya kashe wayar ya kalli Muneera yace" Mama yana hanyar gidansu HAMEED mu tafi"
Suka shiga mota har da kawu yana gidan gaba yana cikin farinciki shima suka dauki hanyar gida.
WALEED ya duke yana jin kamar yayi kuka wata zuciyarshi ce ke rarrashinshi tana bashi hakuri akan danuwansa ne fa daddy ne...bai gama dawowa dede ba ya tashi ya nufi gidansu HAMEED ,
Su Muneera na isa gida suka zauna falo suna farinciki,
Muneera tana kallon Zarah tace"Ki tashi ki kaiwa baffanki lemu kafin yawuce "
Tana murmushi tace"to"ta tashi ta nufi kitchen ,
Muneera na cikin farinciki ta sauke ajiyar zuciya ta meda hankali ga KHALEED tace"ina alfahari da kai dana inajin dadin yadda kake kula damu da duk yadda kake gudanar da rayuwarka, Allah yayi maka albarka"
KHALEED na murmushi yace "Ameen Mama nima ina alfahari dake"
Zarah na daukar lemu ta tafi dakin da kawu Habu yake ta shiga da sallama yana zaune yayi shiru ya amsa ya gyara zama yana kallonta,
Zarah ta zauna kasa tana murmushi tace"Kawu ga ruwa"
Jikinshi sanyaye yayi murmushi yace"Zarah tafiya zanyi"
Kanta kasa cikin sanyin murya tace"Allah ya kiyaye"
Yace"Ameen "yana kallon yanayinta bata wani damu ba,
A hankali yace" Ki kara natsuwa Zarah ki kula da kanki sosai"
Ta dago ta kalleshi ta jinjina kai tace"Insha Allah kawu"
Yace"Allah ya miki albarka idan na samu lokaci zan rika leko ki"
Cikin sanyin murya tace"Nagode"
Ya duka ya dauki lemu zai zuba a cup yace"Kije ki fadawa hjy zan tafi"
Tace"Tom"ta tashi ta fita,
Ya zuba lemun ya dansha sannan ya tashi ya fito ,yana fitowa su Muneera na fitowa ya nata murmushi da dukar da kai yace"Hjy zan wuce mungode kwarai Allah yabar zumunci ya kara lpy mungode sosai "
Muneera na murmushi tace "Bakomi Allah ya kiyaye a gaida Ladingo"
Kawu habu ya juya zai tafi KHALEED ya kalli Muneera yace "Mama bari na saukeshi saina dawo"
Ta daga kai kurum ya iske kawu Habu ya mishi magana suka shiga mota suka tafi tasha,
Su Muneera na komawa ciki WALEED ya bude gidan ya shigo ya dan kalli Zarah ya nufi bedroom,
Muneera na kallonshi tace "har ka dawo ?"
Ya juyo yace"Eh "
Tana kallon fuskarshi tace "lafiya kake?"
Yayi karamin murmushi yace"Yunwa nakeji"
Muneera tai dariya tace"Anjima kadan daddynka zai shigo da abinci amma ka zauna Zarah ta kawo maka lemu kafin ya dawo"
Jin tace Zarah ne yasa ya kalleta tana ta dan murmushi baice komi ba yaje ya zauna ta tashi ta dauko masa lemun ta tsiyaya masa ta bashi ya hada da hannunta ya danji sanyi a ranshi sannan ya janye cup din yana jin kasala,
Zarah ta koma ta zauna kusa da Muneera suna labarin shariar har KHALEED ya dawo ya siyo masu kaji gashin inji da shawarma da fura me sanyi ,
Muneera ta bude kazar tace kowa ya sauko ,duk suka sauko suka sa hannu suna ci a tare,
Da dare KHALEED da Muneera suna kan dining tunda sukai dinner suke zaune suna labari basu tashi ba ,
Zarah da WALEED kuwa suna karatu a main falo,
KHALEED ya kai duba wurinsu yace"Mama inaga zan samo Wanda zai rika koyawa Zarah karatu inason sakata school JS3 tunda tana meda hankali"
Muneera tace "Hakan yayi kaga nan da shekaru hudu ta gama idan ta samu miji sai ai mata aure in mijin naso tana can seta karo karatun"
KHALEED ya yamutsa fuska yace"Eh shiyasa na keso ta tafi this yr tunda yanzu ta iya wasu abubuwan extra lesson din zai temaka sosai"
Muneera tace"Allah ya temaka ya maganar exam dinsu WALEED? "
Yace"Next month zata fito shima ban kwana yake "
Muneera tai murmushi tace "Allah ya zaba mafi alheri"
Yace"ameen"yana kallon WALEED din,
Bayan kwana biyu KHALEED ya shigo tare da wata Christa da ya samo zata rika koyawa Zarah tayi decent dress cikin atamfa har da mayafi,
Zarah na ganinsu zuciyarta tai mummunan bugawa idanunta suka ciko da hawaye ,tana tunanin wacce yakeso ce zai aura,
Muneera tai mata maraba suka zauna ,
WALEED na kallonta yana ganin daddynsa beyi dace ba a ganinshi tayi masa girma,
KHALEED yace"Mama wannan itace malamar da zata rika koyawa Zarah sunanta Alheri "
Alheri ta sunkuya tace "good evening ma"
Muneera tace "Lpy lau" tana murmushi ta kalleshi tace"tana dai jin hausa ko? Kasan zarar yanzu take koyo"
Yayi murmushi yace "eh tana jin Hausa sosai amma zata rika hadawa da turanci don zarar ta iya"
WALEED yanajin badadi zaa rabasa da kusanci da zararsa yace"Daddy meyasa? Bayan ina koya mata"
KHALEED Yayi murmushi yace "School zan kaita kaga ya kamata a kula da karatun sosai,kai kuma next month exam dinka zata fito tafiya zakai school kaga ya kamata kafara shiri tun yanzu"
Wani dadi ya mamaye WALEED yace"Daddy Aji nawa?"
KHALEED yace "Js3"
WALEED yayi lissafi nan da 4yrs kenan dede da gama school dinsa yana jin matukar dadi a ranshi yayi shiru,
KHALEED ya kalli Zarah yana murmushi yace "Zarah ga aunty dinki sunanta Alheri"
Zarah na murmushi tace "Ina yini?"
Alheri tace "Lafiya lau"tana kallonta
Zarah tai shiru tana nazari tana son school sosai amma yanzu KHALEED tafi so akan komi shine jigon rayuwarta shine mafarkinta kuma farincikinta,
KHALEED ya katse mata tunani yace"Yau zaku fara ki tashi ki dauko kayan karatu kafin ta kawo wadanda suka dace"
Zarah tace "To " ta tashi dasauri ta nufi ciki,
Bayan Sati ,angama shirin tafiyar Zarah school ,
Alheri na koyawa Zarah kuma tana ganewa sosai ranar Monday tunda safe ta shirya cikin uniform sun matukar yi mata kyau KHALEED ma ya gama shirin fita office ya fito ya sameta falo,
Ya kalleta tai mishi mugun kyau yace"Sabuwar daliba yau sai makaranta"
Ta rufe fuska tana murmushi,
Yayi murmushi yace "mu tafi "
Muneera ta fito daga bedroom tazo tasawa Zarah cingum da sweet a jikka tace"sai kun dawo Allah yabada saa nima yanzu zan fita "
Zarah tace "Ameen Mama" suka fita tare ,
Suna cikin mota shiru tanata satar kallonshi cikin suit dinshi sun masa kyau sosai shiko hankalin shi na gun driving sede kamar yana tunani,can zuwa ya kalli Zarah suka hada ido duk suka dauke idanun suna murmushi,
Can KHALEED yace"Kiyi kokari sosai Zarah ki meda hankali "
Ta daga kai tare da cewa"To daddy"
KHALEED ya cije lips dinsa ya cigaba da driving har bakin school ya ajiyeta sannan ya wuce,
Muneera ma tagama shirin tafiya school ta tafi akabar WALEED kadai ya koma baccin safe,
Sai 10:am WALEED ya tashi yayi wanka ya fito cikin shirin shi yana murna ya rufe gidan ya hau mashin ya nufi gidansu HAMEED,
Da yake dakin HAMEED na bakin gate shiga kawai yayi direct yanata bacci ya tafkeshi yace"Kai tashi kaji"
HAMEED ya tashi yana kallonshi yace"wai miye haka? mutum na baccin shi"
WALEED yace "Dallah jira kaji yau Zarah ta fara zuwa school daddy ya sata aji ukku se nan da 3yrs zatai candy dede da graduation dinmu"
HAMEED ya fiddo ido yana murna yace"I'm happy for u mafarkinka zai zama gaskiya"
WALEED ya mishi wani kallo yana murna yace "Insha Allah"
*SHIGAR SAURI*
Painful love story
Romance special
Writing by
*MAMAN MAMY (SHALELE)*
*Wattpad@mumies122*
*Dedicated to my close friend ikra Rukayyat*
*Devoted to identical twins hassan & Husain 80k and Fatima dimple*
*Small gift to my real fans*
*PROFICIENT WRITERS ASSOCIATION*
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/
TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09
Page > 43&44
*Muna saida kayan mata da na maza suna da kyau sosai kuma cikin sauki muna turawa koina ga me bukata seya tuntubi wannan number👉🏼 0806 672 6866*
Ya jawo pillow ya rungume yana cigaba da murmushi ,
HAMEED na kallonshi yace"Allah ya kaimu ranar da zaace WALEED wed Zarah, ranar nasan ba bacci wurin abokina kwana zaai jan casbi"
WALEED ya gumtse face yace "Mi kake nufi?"
HAMEED yana dariya yasa yatsunshi biyu ya matse lips dinsa,
WALEED yayi tsoki yace "Dan iska"
HAMEED ya fashe da dariya yana kyakyatawa ya tsagaita yace"Idan anyi auren ka zuba mata ido kaita kallonta mana"
WALEED yayi murmushi yace "Aka fadamaka kowa irinka ne?"
HAMEED yace"Wallahi yanzu kafini kai naka salon daban ne"
WALEED ya tabe baki yace"Kai me yan mata hudu?"
HAMEED yayi dariya yace"Ai ban zurma da yawa ba"suka cigaba da labari,
Zarah na shiga school ta nata jindadi ganinta cikin yaran masu kudi a cikin uniform aka fara musu register tana jiran taji sunanta taji an kira Zarah KHALEED,
Ta fiddo ido tana waige wata ta daga hannu ta amsa amma shiru dadi ya lullubeta ta daga hannu tana farinciki tace"Present"da karfi,
Yan aji duk suka juya suna kallonta jin yadda ta amsa ,
Tai saurin ajiye hannu zuciyarta na harbawa tana memeta sunan *Zarah KHALEED* sunan yayi mugun dadi,
Ta fara sauke numfashi dadin ya mata yawa cikin zuciyarta fata take ta cigaba da amsa haka har karshen rayuwarta,
Aka shigo masu lesson tana ta tunani can ta tuno begging da KHALEED yayi akan ta meda hankali tai saurin gyara zama tana kallon black board,
Time da 2 tayi KHALEED na cikin aiki tunanin zaran kawai yake yanaso yaje ya daukota,
WALEED na tare da HAMEED ganin biyun tayi yasa shi tafiya daukota,
Har ya kusa kaiwa KHALEED ya kirashi ya dauka yace"Babana"
KHALEED yayi murmushi ya girgizakai yace"Kaje ka dauko Zarah daga school"
WALEED yace"To daddy"batare da yafadamai yana kan hanya ba,
Yana zuwa bakin gate ya sameta tsaye tana ta kalle_kalle ta ina motar KHALEED zata fito sai ganin WALEED tayi ,
Ta dan rage faraa domin ba haka taso ba,
Fuskar WALEED tsuke yace"hau mu tafi "
Ta hau suka dau hanya WALEED na driving yana lumshe ido yana budewa kamar ya bude ya gansu a haka saman mashin suna matsayin maaurata moment din ya mishi yanajin ko bayan aurensu zasu rika dan yawatawa kan mashin bai sani ba har sukaje wurin bump mashin din yayi sama sannan ya dawo Zarah ta fada a bayanshi soft breast dinta suka sauka a bayan shi ,
Hankalinshi yayi wani iron tashi jin wani taushi da dadi dabe tsammani ba ,
Zarah itama tunanin KHALEED dinta kawai take tana tunanin meyasa baizo daukarta ba Sam bataji dadin ganin WALEED ba,
WALEED na cikin duniyar shauki da shaawa ya hango wani bump din gaba yana sane ya bi ta kanshi da gudun ta kara fadowa saman bayan shi ,
Wannan karan saida yasa hannu ya shafi gemun shi tsabar dadin da yaji,
Zarah data tsorata da driving din ta kara matsawa gab dashi a hankali ta kamo gefe _gefen rigarshi ta rike gam,
Yayi wani murmushi me sanyi ya cigaba da driving dinsa shauki na dibarsa,suna zuwa gida ta sauka ta nufi ciki yabi bayanta da kallo yana lasar lips dinsa na kasa yanajin tsananin so da shaawarta,
Tana shiga ta samu Muneera zaune falo taje ta rungumeta tana sauke numfashi,
Muneera ta riketa tace"yar makaranta sannu kun dawo ya school din?"
Zarah tace "Lafiya lau mama makarantar dadi"
Muneera tai murmushi tace"Ki tashi kije kiyi wanka ki sallah muyi lunch "
Tana niyyar tashi WALEED ya shigo ya kalleta fuskarshi bawalwala yace"muga jikkar ki"
Ta kalleshi ta mika mai ta wuce ciki,
Ya zauna ya bude jikkar yana kallon buks din idanunsa suka sauka kan name dake jikin Text buk da aka bata an rubuta Zarah KHALEED,
Wani mugun kishi ya taso masa bakinshi na rawa ya dago ya kalli muneera yace"Mama saboda me daddy zaisa sunanshi memakon sunan mahaifinta?mama hakan fa haramun ne"
Muneera ta kalleshi ta kalli littafin tace"Ina ga ansamu matsala wurin suna ne amma ai hakan ma Lpy lau tunda yanzu shine babanta "
Fuskarshi ya mutse Yace"Mama ni ma banyi using sunan shi ba se ita?"
Muneera tai dariya tace"To saika sauya kaima ka rika using dashi"
Ya bata fuska ganin ta meda abun wasa ya kurawa littafin ido yana jin haushi,
Muneera tace "Ka tashi kaje ka watsa ruwa muci abinci yunwa nakeji ku nake jira"
Ya meda littafin ya saka a jikkar yanajin kamar yasa mata wuta ya ajiyeta ya tashi ya shige ciki,
Muneera ta bishi da kallo tace"Allah ya shiryamin kai WALEED kullum kamar karamin yaro kake"
Zuciyar WALEED na Zafi yayo wanka ya fito ya samesu zaune a dining ya zauna yana kallon seat din KHALEED yace"Ina daddy?"
Muneera na serving dinsu tace"na kirashi aiki ya rike shi sai dare zai dawo "
WALEED ya matse lips ya kagara ya dawo ya mishi mgna a meda sunan mahaifinta ko hankalinsa zai kwanta,
Sunata cin abinci shi ko yana tsakura Muneera ta gama cin nata ta tashi ta shige bedroom,
Zarah ta gama ta tashi ta bita ta dauki buks dinta tana dubawa,
Sai dare KHALEED ya shigo gidan ya shigo dauke da brief case yana matukar gajiye,
Yana shigowa Zarah data kagara ya dawo taji sanyi a ranta ta sauke ajiyar zuciya ta tashi dasauri ta amshi briefcase din hannunsa tace"Sannu da zuwa daddy"
Ya kalleta yana murmushi yace"yar makaranta ya school din?"
Tace"Lpy lau daddy "
Ya meda kallonshi gun Muneera dake masa sannu da zuwa yaje ya zauna yana murmushi yace"Mama nayi kewar ku sosai"
Tai dariya tace"Sannu duk ka gaji"
WALEED yace"sannu da zuwa daddy"
Ya kalleshi yana murmushi yace"naji ance an saki exam din ku"
WALEED na murna ya fiddo ido ya gyara zama yace"dagaske?"domin burinshi yanzu yayi karatun ya mallaki Zarah,
KHALEED yayi murmushi ya girgizakai yace "Ka kagara ne?"
Yace"eh daddy "
KHALEED yace"Very soon ai maybe ma gobe ko jibi"
Ya Mike zai shige ciki WALEED yabi bayanshi dasauri,
Yana shiga ya fara rage kaya ya shigo yana kallonshi yace"Daddy da sunanka kaiwa Zarah registration? "
Ya juyo ya kalleshi yace"Kamarya?"
Yace "daddy Zarah KHALEED na gani a jikin buks dinta"
KHALEED yayi tsoki yace"shirmen director dinne na fadi sunanta amma bai tambayi na babanta ba shaf na mance ...jeka idan na samu lokaci zansa a gyara"
WALEED ya juya ya fita yana jin sauki_sauki ,
Bayan KHALEED ya fito suna cin abinci ya kalli Zarah yace"Zarah KHALEED "
Dadi ya mamayeta tana murmushi tace"present"
Muneera da KHALEED suka fara dariya zarar na taya su ,
Muneera tace"wallahi kuna da abin dariya wai Ya akayi akasa sunanka?"
Yace"Namance ban ba director sunan mahaifinta ba nasan shine yasa mata KHALEED zanyi saurin kiran shi tun kafin ya mata primary certificate da sunan"
Zarah tai saurin cewa"Mama dan Allah abarmin sunan inason in rika amfani dashi "
Duk suka zuba mata ido hada WALEED da yake jin kamar ya rufe mata baki karta karasa,
Zarah ta marairaice kamar zatai kuka tace"dan Allah, banaso a rika kiran sunan baffa ina tuno mutuwarshi da yadda suke kiran shi hankalina yana tashi"
wayar Muneera ta fara ring ta kawadda zancen da cewa "WALEED tashi daukomin wayata"
Ya tashi yana jin kamar yayi burst ya tafi ya kawo wayar ya zauna yana jimami,
Ganin anbar maganar yasa Zarah jindadi ta sauke ajiyar zuciya a boye,
KHALEED ko wani tausayinta ya kara shigarsa tana matukar burgeshi natsuwarta da girmamawarta gareshi, suka gama cin abincin suka tashi suka koma falo suka zauna kallo,
Tunda WALEED ya zauna ya kurawa tv ido zuciyar shi na tafasa ,
Meyasa Zarah zatai using sunan daddynshi? beson ko sunan wani ta raba ,,
Zuciyar shi ta rika bashi hakuri cewa daddyn ka ne fa meze hada shi da ita ?kadena bata tunanin ka da ranka kullum fa suna tare yana ganin kwalliyarta da komi nata dariyarta jindadinta da komi ka kwantar da hankalinka ,ka taba ganin daddynka na soyayya? ba itace gabanshi ba ka natsu kadena damuwa da abinda bazaka taba maganinsa ba saboda bazaka hanata rayuwa tare dashi ba ,kuma da wani can ya kalleta gwara daddy ya kalleta domin bazai taba wani tunani a ranshi ba,
Zuciyarshi ta cigaba da bashi shawara haryayi naam da hakan yadan saki jikinshi,
Kullum haka take KHALEED ke kai Zarah makaranta sunata kara shakuwa domin saukin halinsa yayinda WALEED ke daukota kuma baya ce mata komi har su koma gida ,
Bayan sati exam din su WALEED ta fito ya samu nine credit ,
KHALEED na murna ya dawo gida yana farinciki ya dauko takardar ya kangawa WALEED,
WALEED ya damke ya bude ido da baki yana murna ya rungume shi yace"Thank u daddy I love u so much"
Muneera na murna tace"bani in gani "
Ta amsa ta duba tana murna tace"Alhamdulillah Allah yabada saa Auta"
Ya koma ya rungume ta yana murna sosai,
Zarah ta kalleshi tace"Congratulation yaya"
Ya kalleta yayi dan murmushi yace "tnx"
Suna gama murna WALEED ya nufi gidansu HAMEED da big news shima din ya samu 9 credit sukaita murna tare,
KHALEED ya fara neman musu school a India ya samo masu admission a tare WALEED da HAMEED ,
Iyayen HAMEED sukazo har gida sukai mishi godiya sannan suka fara shirin tafiyar su,
WALEED ya shiga damuwa sosai saboda tafiyarsu baya jure rashin Zarah na kwana gashi zaiyi doguwar tafiya da besan ranar da zai dawo ba ,
Duk yabi ya rame da Muneera da KHALEED suna ganin damuwar rabuwa dasu ce kesa shi rama,
Saura kwana ukku ya tafi yaje wurin HAMEED suka fita kallon ball,
Suna zaune HAMEED na kallon ball yana kallonshi kullum mamaki yake wace irin soyayya WALEED kewa Zarah shi meyasa baya jin hakan ga kowace budurwarsa,
Cikin sanyin murya yace"Gaskiya WALEED ya kamata ka fadawa Zarah dasu daddy cewa kana sonta kafin mu tafi ,saboda kar muje ya zama kai kadai ke dakon soyayyarta tazo ta kara wayewa tace ba kai ma ta ba"
WALEED ya kalleshi jikinshi sanyaye baice komi ba ya cigaba da tunani zuciyarshi na fadamai cewa maganar HAMEED din gaskiya ne,
Bai koma gida ba sai dare ya gama tsara abinda zai fadamata tunda yaje yake so ya kebe da Zarah suyi maganar amma bai samu hakan ba,su kuwa su Muneera busy suke shirye_shiryen tafiyarshi,
Har dare ya kwanta da tunanin maganar da zai fadamatan a zuciya,
Suna kwance ya fara mafarki suna magana da ita ,tana ta kallonshi yace"Zarah akwai maganar da nakeso muyi"
Tana mai kallon up and down A tsiwace tace"banason ji "ta juya zata bar wurin ,
Ya kamota dasauri ,ta juyo tana kallonshi
Cikin daga murya yace" ki tsaya ki saurareni kiji menake fada"a mafarki yake maganar amma tana fitowa fili,
KHALEED da yake jin magana cikin bacci ya tashi zaune yana kallonshi,
WALEED yace "ina sonki wallahi tunda na ganki na kamu da ciwon sonki ki amshi soyayya ta plss"
Zarah tace"Ni??? to Bana sonka ...bana sonka ..ka sakeni"ta kwace hannunta tai gaba,
Ya bita a baya yana fadin"dan Allah ki saurareni wlh idan babuke mutuwa zanyi ki soni ko da kadanne dake kadai zan iya rayuwa"
Ran KHALEED bace fuskar shi jawur yanajin haushin idan babuke bazan iya rayuwar nan ba ya falla mishi bugu,
WALEED yayi saurin tashi zaune idanunshi tarai akan KHALEED ya fiddo ido waje yana kallonshi ganin ranshi a matukar bace,
KHALEED yace"its enough ya isa WALEED ,kullum ina burin gyara maka rayuwa ina kokarin ka zama wani abu kuma don jindadinka amma tunaninka kaf yana kan mace ,to na fasa fidda kai wajen kar kaje ka jawomin matsala ka kwaso cuta kuma bakayi karatun ba ba inda zakaje sai ka cigaba da mafarke_mafarken iskan naka"ya karasa da tsoki yaja pillow yana niyyar barin gadon,
Zuciyar WALEED wani irin zafi take ko kadan bayason bacin ran daddynsa da yake komi don ganin farincikinsa ,kuma shi kanshi yanzu so yake ya tafi karatun daya dawo ya samu aiki ya auri zarar shi,
ya rike hannunshi da sauri KHALEED ya juyo ranshi bace, idanun WALEED cike da hawaye yace "dan Allah kayi hakuri daddy inason tafiya karatun"
A zuciye KHALEED yace"haka zaka tafi kana shashanci?"
WALEED ya girgizakai yana hawaye yace"Wallahi daddy bazanyi komi ba zan kula da kaina sosai"
KHALEED yace"tsoro kake bani WALEED kullum cikin mafarki karka je kafara bin matan banza"
WALEED ya razana jin daddynsa da fadamasa haka hawaye suka kara yawa a fuskarshi yace"Daddy wallahi bazan taba aikata komi ba na maka alkawari zan kula da kaina sosai zan rike mutunci na"
Zuciyar KHALEED tai sanyi ya dafe goshin shi yanajin takaicin maganganun daya fada masa ya koma ya zauna ,
Ya jawo kanshi jikinshi cikin sanyin murya yace "Kayi hakuri banso na fada maka haka ba rainane ya baci"
WALEED ya girgizakai yace "Kayi hakuri daddy ka yadda dani kabarni na tafi"
KHALEED ya cije lips amma zuciyarshi cike take da waswasi yanajin kukanshi har cikin rai yace"Kai shiru zaka tafi amma sai kamin alkawari bazaka kula kowace mace ba karatu kadai zakai"
WALEED na hawaye yace "nayi maka alkawari daddy"
KHALEED ya matse lips yanajin tausayinshi yace"its OK kai shiru kai baccinka"
WALEED yayi shiru ya lumshe idonsa yaso ya fadawa Zarah amma bazaiyiwu ba dole zai bari har se ya dawo sannan ,
A zaune KHALEED yayi bacci wurin rarrashin danuwansa,
Da safe WALEED bai fadawa HAMEED cewa bai fadamata ba ,
Gobe ne tafiyar duk gidan suna sukuku har ta Zarah bata son tafiyar abinci ne gabansu amma bawanda ya iya ci,
Muneera tai karfin hali ta kallesu tace"Duk kun damu kamar gobene fa zai dawo ku kwantar da hankalinku kuci abinci"
Ta matso kusa da WALEED tace"danlele kai a baki zan baka bude ka ci"
Ya bude baki yana amsa kadan_kadan,
Zarah tafara cin nata a hankali,
KHALEED nata kallon abincin tafiyar WALEED yanajin kamar zai rabu da bugun numfasinsa ne Muneera ta kalleshi tace"ka ci abincin ka "
Ya dauki cokali ya fara ci,
Bayan sun gama suka koma falo duk sunyi jugum WALEED na jikinta cikin rarrashi tace"WALEED dan Allah idan kaje kayi abinda ya kai ka ,ka kula da ibada ka kiyaye addininka inaso kayi koyi da da dadyn ka "
Muryarshi sanyaye yace"insha Allah mama"
Zarah na gefe a hankali tace "Za muyi missing dinka yaya"
Ya kalleta ya lumshe ido yanajin natsuwa da sanyi a ranshi ta damu dashi,
Muneera tace"kana jinta ko?"
Ya daga kai yace"nima zanyi missing naku Zarah "
Sukai murmushi tare sai 12 suka kwanta,
KHALEED yayi zaune kan bed ya kasa rumtsawa,
WALEED dake kwance ya juyo ya kalleshi yace"daddy ka kwanta"
KHALEED yace "ya zanyi in rumtsa dan'uwana zai tafi yabarni zan dena jinka kusa dani"
WALEED yayi murmushi yana daga kwance ya rungumeshi yace"Daddy nagode da komai da kayi min a rayuwata u r d best babu kamar ka"
KHALEED ya zagaye shi da hannu yana murmushi yace "ka kula"
WALEED ya jinjina kai,
Tun 3 suka farka a gidan suna shiri saboda 5am jirginsu zai tashi ,
Zuwa 4:30 suka fito daga gidan gabadaya domin rakiyarshi WALEED na zaune gidan gaba yanata kallon Zarah ta mirror "zamuyi missing dinka yaya" na dawo masa yana murmushi,
Har suka isa airport yanata faraa suka samu yan gidansu HAMEED sunyo mishi rakiya su biyun su kai wa juna murmushi ,
Lokacin da zasu shiga jirgi WALEED ya rungume KHALEED da Muneera yana farinciki yanata murmushi yayiwa Zarah bye_bye itama ta daga nata tana masa ya juya ya shiga ,
Bayan jamaa sun gama shiga jirgin ya daga zuwa India.
*SHIGAR SAURI*
Painful love story
Romance special
Writing by
*MAMAN MAMY (SHALELE)*
*Wattpad@mumies122*
*Dedicated to my close friend ikra Rukayyat*
*Devoted to identical twins hassan & Husain 80k*
*Small gift to my real fans*
*PROFICIENT WRITERS ASSOCIATION*
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/
TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09
Page > 45&46
*Muna saida kayan mata da na maza suna da kyau sosai kuma cikin sauki muna turawa koina ga me bukata seya tuntubi wannan number👉🏼 0806 672 6866*
*Congratulation my beautiful sis Aisha alto da gama INDO AISHA ,littafin ya fadakar ya nishadantar kuma an zuba love sosai me kwantawa a zuciya mun matukar jindadinsa kuma muna jinjina miki kan namijin kokarin ki na kirkirar littafin Allah yakara basira da daukaka ,fans🗣 duk Wanda bai karanta Aisha indo ba an barshi a baya, kan nera dari biyu kacal zaku samu completed dinshi*🥰
Bayan jirgin ya daga su KHALEED suka koma gida suna cike da kewar WALEED,
Shima yana cikin jirgi yana cikin kewar ahalinsa musamman Zarah da yake jin kamar ya bude ido ya ganta yana cikin tunani ya bude wayarshi yana kallon hoton ta dake jikin wallpapern wayar shi,
Bayan sun isa ya kira KHALEED yana murmushi yace "Daddy muna school yanzu haka"
KHALEED yace"Sannu dana ya hanya fatan kuna lafiya?"
Yace"ihmm dad"
Yace"Ok anjima zan kira ku gaisa da Mama da Zarah"
Ranshi yayi fari jin zaiji voice dinta yace"OK bye"ya kashe kiran,
Bayan watanni
WALEED sun dade da fara daukar lectures kullum suna tare da HAMEED saboda course dinsu daya,
Acikin course mate dinsu akwai wasu indiyawa guda biyu dukkansu shekarunsu sunfi nasu WALEED don zasu kai 25 amma sunata shigewa su WALEED saboda son su da suke ba da komai ba se holewa don sun San ba aurensu zasuyi ba,
Wacce ke son HAMEED Anjelina tana dan samun fuska domin har gaisawa sunayi da hannu,while Sanjana taki samun fuskar WALEED ko kadan ,
A gida kuwa kusan kullum sai KHALEED ya kira WALEED kuma yana masa nasiha sosai,
WALEED ne zaune shida HAMEED suna duba hand out dinsu su Anjelina suka iso wurin WALEED ya daga ido ya kallesu suna cikin doguwar riga me hannun vest iya gwiwa surar jikinsu ta bayyana gashi sun bazoshi suna ta murmushi ,
Angelina ta mikawa HAMEED hannu tare da cewa "Hi"
HAMEED ya mika mata yace"Hi"
Sanjana tana ta kallon WALEED tana gudun yayi mata wulakanci kamar kullum ta mika masa hannu tace"Hi"
Ya kalli hannun ya dauke idonshi yanajin tashin desire ya tashi yayi gaba,
Ta meda hannunta fuskarta yamutse ranta na zafi,
Anjelina ta dafa kafadarta ta lumshe ido tana bata hakuri,
Ranta bace ta juya ta nufi hostel dinsu tana jin kamar ta share shi saide bata iyawa mugu_mugun son muamala dashi take,
Su kuwa su HAMEED zama sukayi gab da gab jikinsu hade sukayi karatu suka sha fira sannan ya tashi ta mishi rakiya ,
Tana komawa hostel ta samu sanjana kwance ruf da ciki tana tunani,
Ta zauna kusa da ita cikin yarensu na India tace"Sanjana stop Worrying ur self plss ,zaki sameshi kina zaune zai kawo kanshi saurin me kike?"
Sanjana ta kalleta ranta bace tace"I just want to see him very close to me I really want him amma kafin nan inason ya rika sakarmin ko da fuskane"
Angelina tai dariya tace"ki kwantar da hankalinki some love story started with hartred ,kina ganin yadda HAMEED keyi before ya shigo hannu"
Sanjana ta kureta da kallo,
HAMEED na komawa wurin WALEED, WALEED ya kalleshi up and down yace"baka da hankali ko?"
HAMEED da yasan kwanan zancen yace"To miye she's just my friend nothing more"
WALEED na mai wulakantaccen kallo yace"Shifa hada hannun da kuke?ita matarka ce ko kanwarka?"
HAMEED ya zauna kusa dashi yana murmushin ban haushi yace"ko daya I just wanted to feel her soft hand"ya karasa yana mishi wani kallo,
WALEED ya tabe baki yace"Matsalarka ce "
Zarah da KHALEED na cigaba da shakuwa idan dare yayi suna kasancewa tare da KHALEED yana aiki a system dinshi ita kuwa tana assignment ,
Yau an basu assignment har wani dadi take ji duk time da take dashi,yana zaune saman kujera tazo ta gefenshi ta zauna tana murmushi tace " daddy assignment gareni kuma banganeba"
Ya dago ya kalleta da blue and green din idanunshi tanata murmushi,
Yayi karamin murmushi yace"Meyasa bakya kokari Zarah? Duk assignment sai na shiga ciki"
Tace "Daddy inayi bana so ne inyi badaidai ba amma ina kokari nasan anty na fadamaka hakan"
Ya sake murmushi yace" mu gani "
Ta kara matsawa gab dashi ta mika mai littafin ya kalleta ya girgizakai ya bude yana dubawa ya dago ya kalleta yace"kawo biron da wani buk"tai saurin mika mishi ,
ya fara gwada mata tana yi tana kallon bakinshi ,
Muneera ta fito daga bedroom ta samesu haka ta tsaya tana kallon su da shaaawa tana fatan inama KHALEED yana tare da iyalinsa ne haka sede bata tunanin hakan da Zarah,
Tazo ta zauna tana kallo tana kallonsu har ya gama mata ya bata ya dago ya kalli Muneera yayi murmushi ya dora hannu zai kara kunna system dinshi,
Muneera tace"KHALEED yanzu kome ya daidaita WALEED na makaranta Zarah ma natata ya kamata kai aure"
Gaban Zarah ya fadi ta kalleshi tanaso taji me zaice taga fuskarshi ta sauya wani tausayinshi ya mamaye zuciyarta,
A hankali yace"Mama idan lokaci yayi zanyi"
Tace"Sai yaushe lokacin zaiyi KHALEED? "
Ya kalleta yace"Mama wacece zan aura wa zata aureni haka?"
Muneera tai shiru tana kallonshi,
Ya matse lips yace"Mama kamar kina mantawa da wanene ni bame lafiya da zata soni haka"
Muneera tai shiru hankalin ta tashe tana jin tausayinshi tace"Idan ka nema zaka samu KHALEED "
KHALEED ya girgizakai idanunshi sun tara hawaye yace"Mama nine danki fa marar abokai da nayi rayuwa ni kadai, ba wacce zata soni mama plss kidena mun maganar aure yana tunomin abubuwan dana mance"ya tashi ya dauki system dinshi ya tafi part dinshi,
Hawaye ne cike da idon Zarah ta dago ta kalli Muneera da idonta ke jawur tana jin tausayin danta cikin muryar kuka tace"Mama minene matsalar daddy ne ?naji ya fadi baya lafiya"
Jikin Muneera sanyaye tace "Eh bashi lafiya tunda aka haifeshi aka haifeshi da cuta shiyasa kika ganshi haka amma cutar bata hana auren me lafiya"
Hawaye suka zubowa Zarah sai yau ta samu amsar maganarta ashe baya lafiya shiyasa yake fari tasss ,
Tana hawaye ta share hawayen da bayan hannu ta dago tace"Mama dan Allah kudena yi masa maganar aure,idan lokaci yayi zakiga yayi"
Muneera tace "Banason zamanshi haka inason yayi aure ya samu zuria ya kara zama mutum ,Ni zan nemo mishi mata da kaina"
Zuciyar Zarah tai mummunan faduwa kamar ta bude baki tace mama inasonshi takeji zuciyarta nata tunzurata ta fada ta tashi dasauri tana hawaye ta shige daki ta kwanta kan bed tana kuka sanin halin da daddynsu ke ciki,
Shima KHALEED tunda ya shiga ya ajiye system din yayi zaune yana tunani wani abu yakeji a ransa da baya tunanin me yiwuwa ne,shi kawai yanaso yayi rayuwa shi kadai ba tare da aure ba,
Sama_sama yayi bacci wanshekare suka fito cikin shiri suka zauna breakfast duk jikinsu sanyaye suna gamawa suka fita school,
Suna cikin mota yana driving tana gefe tana tunani zuciyarta nasa ta fadamai abinda bazata iya ba,
Yana ta tunani ya kalli sashenta ya ganta takure ta shiga duniyar tunani ya dauke idonshi kanta yana tunanin yadda suke tafiya kullum cikin farinciki,,
A hankali yace "Zarah yau ba magana"
Ta juyo ta kalleshi ta danyi murmushi ya mayar mata yace"Menene ke damunki? "
Ta girgizakai ta juya kai,
Yayi shiru don baisan kome zaice mata ba ya cigaba da driving suna zuwa kofar gate din school yayi parking ta bude ta fita ta leko ta window tace"Allah ya kiyaye daddy"
Ya lumshe idonsa ya jinjina kai ta juya ta shige makaranta,
Ya tsaya yanata kallon bayanta harta shige sannan ya tada mota ya tafi,
Yana zuwa office ya fara aiki yana tuno maganar Muneera daya tuno maganar sai murmushi da kallon da Zarah ke masa su fado masa a rai ,baisan meyasa ba yake yawan tuna murmushinta yau din da take haka baiji dadi ba sosai dalilin haka damuwa ta kara masa yawa ya cigaba da aiki zuciyarshi na ciwo,
Muneera na gida tanata regretting yiwa KHALEED magana ganin duk ya damu amma kuma wata zuciyarta na ganin daidai ne don bai kamata yayi ta zama haka ba ,
Ta tashi ta hada abinci maidadi da juice Wanda yafi so ta ajiye tana jiran dawowarsu,
Karfe biyu da rabi suka shigo gidan dukkansu suna cikin damuwa Muneera na murmushi tace"Sannun ku da dawowa"
Ya kalleta yana dan sakewa yace"Yawwa mama "ya nufi dakinshi,
Yana rage kayanshi ya fito ya zauna kusa daita yana kara sakin jiki yace" Mama yau me kika dafa mana?"
Ta danji dadi a ranta tace" Mutumenka tuwon semo miyar kubewa danya da watermelon juice"
Yayi murmushi yace "Mama kinaji dani duk da kinje school har kikayi"
Tana murmushi tace "Na lura baka ci abinci sosai da safe ba"
Ta kwalawa Zarah kira,
Zarah ta fito da daurin gaba jelar gashinta zube a gefen kafadunta ta tsaya gaban Muneera tace"Mama gani"
KHALEED ya fara kallonta tun daga sama har kasa sannan ya dauke idonshi akanta,
Muneera tace "A,a yana ganki da daurin gaba kinyi sallah ne?"
Ta daga kai tace"Eh wanka zan shiga"
Muneera tace"To kibari mu fara cin abinci tukunna"
Zarah tace"Na koshi "
Muneera ta dan kalleta na second sannan tace"Dazun ma baki tafi dana school ba still yanzu kin koshi ?"
Zarah ta daga kai,
Muneera tace"shikenan "
Har Zarah ta juya taji muryarshi ya kira ta "Zarah"
Ta juyo tana kallonshi ,
Batare da ya kalleta ba yace"Ki dawo muci abinci "ya tashi ya wuce dining,
Ta kalli Muneera da ta mike ta nufi dining tai saurin juyawa ta sanyo hijab sannan ta fito ta zauna,
Muneera tai murmushi ganinta da hijab abubuwa da yawa na zaran na burgeta,
KHALEED ya saki jikinshi yana cin abincin duk da bayajin dadinsa yana cikin damuwa ba don komai ba sai dansu samu suci ,
Ganin ya dagene yasa suka danci sannan ta tashi ta shiga wanka ,
Wanshekare ba islamiyya tana dawowa makaranta saiga kawu Habu da Ladingo sun zo ganinta tana ta murna ta rungume ladingon suka cigaba da murna ,
Sun matukar jindadin ganinta cikin natsuwa da kwanciyar hankali sai wanshekare sannan suka koma,
Bayan wasu month din soyayyar HAMEED da Angelina tayi nisa sosai,
Yau dinnan ta gayyace shi hotel bayan ta gama nuna mai abinda takeso,bai tabayi ba amma kuma yana shaawar hakan saboda yadda suke barin jikinsu a waje dole yayi shaawa bai fadawa WALEED ba ya shirya ya tafi hotel ,
Da zuwanshi kofar dakin yayi tsaye zuciyarshi na up and down yayi ta maza ya bude ya shiga yana rufewa ya juyo ya ganta daga ita sai pant da bra ,kusan sumewa yayi awurin jikinshi ya fara rawa yana jin matsananciyar shaawa da tsoro lokaci daya,
Tana mai sexy kallo da murmushi ta na lasar lips da kashe masa ido ta karaso wurinshi tana cat work tafara shafarshi takai fuskarta dede tashi tana sauke mai numfashi ,
Gab_gab jikin HAMEED ke rawa yayi saurin juyawa da niyyar fita ta kamo hannunshi tana lasar lips tace"Don't leave me plss i love u I want u just only u"
Brain din HAMEED ta kwance gabadaya ya rasa hankalinsa ,ta fara undressing dinsa tana karairaya shi ko yayi kamar gunki tana gamawa ta jashi zuwa kan bed ,
Ya kalli kan bed din yana tuno fadan iyayensa ya rike mutuncinsa jikinsa ba karfi ya fara kokarin janyewa amma ya kasa ta kwantar dashi kan bed ta bishi tana lasar duk jikinshi tana binshi da kisses,
Hankalin HAMEED ya karasa gushewa gabadaya yanajinshi a wata sabuwar duniyar ya balle bra dinta da pant ya cigaba da squeezing dinta yana wasa da boobs dinta yana tsotsa da murzasu yadda yaso yanajin mugun dadi,
A time din shaf ya manta da nasiha bai tuna komi ya fara kokarin kusantarta da temakonta ya gane hanya ya fara sex daita a haukace a matsayin shi na sabon shiga ,
Angelina ta dage ihu tana jin kamar ta hadiyeshi saboda dadi duk tafi jindadinsa kan duk mazan da suke muaamala,
Bayan dogon lokaci da suka dauka suna sex HAMEED ya matukar gajiya yayi kwance yana meda numfashi gabanshi na faduwa bat_batt,
Tana ta meda numfashi kamar wacce tai tsere Tana murmushi tace"How did u feel?"
Ya jujjuya kai yace"Don't know"
Tai dariya ta kara shige masa tace"lets sleep here tonight'"ta fara shafa nipples dinshi,
Yayi saurin tashi zaune ya sauka kasa cikin sauri ya fara meda kayanshi ,
Tace"aa Ina zaka?"
Yana sanya kaya yace"I have to go WALEED zai iya tunanin wani abu"
Tace"and So?"
Ya karasa saka botiran rigarshi yace "Thanks bye" ya fita ya rufo mata kofar,
Tana kallon kofar ta saki killer smile tana kallon gadon ta rungume gadon tana tuno moment din burinta ya gama cika ta sameshi ta bugawa kawarta Sanjana waya,ta dauka tana kwance tace"Meye?"
Tana gyara gashin kanta tace"I have him na sameshi yadda naso"tana dariya tace"HAMEED share his beautiful body with mine..he gave me the best pleasure of lifetime"
Hankalin Sanjana ya tashi tana jin kamar ta jawo WALEED yau tace"did u think zan samu WALEED as well?"
Angelina tace"yes of course "tana murmushi tace" I'm very tired bazan iya dawowa ba sai gobe ki bacci medadi"ta kashe kiran ta fara juyi a gado,
Wayar HAMEED nata ring tana silent ta kai hannu taji ta ta dauko taga ansa best for ever ta dauka ta kara kunne,sai muryar WALEED taji yace"Kana ina ne wai ? dare yayifa"
Tai murmushi me sauti tace"amm sorry ya manta ta anan"tana gama fada ta kashe,
WALEED da tundazu ya kasa bacci saboda rashin HAMEED kusa ya tashi zaune zuciyarshi na dokawa yana jin zargin HAMEED din,
Bayan mintuna kusan ishirin ya shigo yana ganinshi zaune ya dauke fuska ya matsa jikin gadonshi yana cire takalmi,
WALEED yace"HAMEED kasan karfe nawa?"
Ya juyo yana murmushi yace"Ina wurin Angelina munsha karatu sosai"
WALEED yace"kai ko kunya bakaji ka fadamin kanacan ?ni zaka shashantar karatu ? har dasu baro wayarka inata kira sede ita ta dauka"
HAMEED ya tuno da wayar shaf dadi yasa shi ya manta yace "to minene "
Ya fara tube kaya zai shiga wanka WALEED yayi tozali da kisses din Angelina a bayan shi ranshi na suya yace"Yanzun nan HAMEED zina kayi?"
HAMEED yace"wa? Ni? Allah ya tsareni"
A fadace WALEED yace"Me kayo inba ita ba duk jikinka da kisses gashi zaka shiga wanka Kasan zunubin da ka kwasa kuwa?haba HAMEED "
HAMEED yayi tsoki yace "Ni ba abinda nayi"
WALEED na jin haushi yace"shikenan ka cigaba da tarayya da ita idan ka kwashi cuta time din zaka fahimta"
HAMEED yayi dariya yace "tunda kai baka iyawa kabarni naji dadin rayuwata mana kai kuma kaita fama da wet dream kana kiran Zarah...Zarah .....I love u"
WALEED yaja dogon tsoki ya juya mai baya yayi kwanciyarsa,
HAMEED yace"Ni I'm joking mun dan rage zafine kawai amma ba abinda kake tunani bane ya sheikh "yana gama fada ya shige toilet,
WALEED na kwance yake tunanin halin da HAMEED ya fada shi ko yaji shaawar Zarah kadai yake tunawa yaki bari shaawan indiyawan ta danne tata,
Tundaga time din HAMEED da Angelina suka bude shafin holewa duk sanda suka ga dama yayinda wutar shaawar WALEED ke kara ruruwa a zuciyar Sanjana,
Yau KHALEED na dawowa yacewa Muneera" Mama ina shirin kaiwa WALEED ziyara "
Tana murna tace"yaushe ?amma ka kyauta sosai"
Yayi karamin murmushi yace "Mama dole naje naga halin da yake ciki duk da kullum muna waya amma ya kamata naje,nan da 1 wk nakeso inason ne na fara samo gate man da kuma driver da zai rika kai Zarah makaranta "
Muneera tace "Allah de ya muku albarka ,dadewa zakayi hala?"
Yayi murmushi yace "eh inason naga ya rayuwar su a can ke tafiya"
Muneera na jindadi tace"Shiyasa kullum nake karayiwa Allah godiya da ya bani kai KHALEED kana da kokari da hali me kyau"
Yayi murmushi yace "Nagode Mama duk hakan ya faru ne saboda adduoinki da tarbiyyar da kika bani"su kai murmushi gabadaya,
Cikin kwana ukku ya samo musu gateman da driver sannan ya fara shirin tafiyarshi ba tare da sanar da WALEED ba,
Hankalin Zarah ya tashi matuka akan tafiyar don yace baisan ko kwana nawa zaiba bataso yayi mata nisa,
Ranar da zai tafi da dare, tunda safe Zarah take fushi duk ta daure fuska tai shirin makaranta ta fito KHALEED na kallon fuskarta yayi murmushi suka fita yana driving bai ce mata komi ba sai shima ya tsuke fuska ,
Zarah nata duban zai rarrasheta taji shiru ganin sun kusa kaiwa school din idanunta cike da hawaye tace" daddy dan Allah kar ka wuce kwana ukku"ta langwabe kai tace"plsss daddy"
KHALEED ya kalleta yayi karamin murmushi yace"kin gama kumburin?"
Ta girgizakai tace"Aa ni bana fushi da kai"
Yace"Shine kuma ko gaisheni ba ai ba?"
Tai saurin cewa "Ina kwana?"
Yayi murmushi yace "Banaso"
Ta matso shi tace"Dan Allah daddy kaji?"
Yace"Naji"
Ta koma wurin zamanta tana jin sauki,
KHALEED ya kalleta ya dauke kai a hankali yake karantar dabiunta,
Yana ajiyeta ya wuce office da rana driver ne ya daukota ,bai dawo ba sai marece ya zauna sunata dan fira sannan ya fara shiri,
Kusan daya na dare ya gama shiri ya fito Zarah na sanye da kayan bacci ta rabe gefe tana hawaye,
Muneera ma na jin kamar zatai kuka take ta masa adduar isa lafiya,
KHALEED ya kasa hakurin tafiya ya kalli Zarah yace"Zarah sai na dawo ko?"
Ta jinjina kai ta shige daki tana kuka ,
Muneera ta girgizakai tace"Ka tafi kar kuyi late Allah ya kiyaye"
Yace"ameen "ya juya ya fita,
Wurin karfe biyu na dare jirginsu ya daga India .
*SHIGAR SAURI*
Painful love story
Romance special
Writing by
*MAMAN MAMY (SHALELE)*
*Wattpad@mumies122*
*Dedicated to my close friend ikra Rukayyat*
*Devoted to identical twins hassan & Husain 80k*
*Small gift to my real fans*
*PROFICIENT WRITERS ASSOCIATION*
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/
TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09
Page > 47&48
*Muna saida kayan mata da na maza suna da kyau sosai kuma cikin sauki muna turawa koina ga me bukata seya tuntubi wannan number👉🏼 0806 672 6866*
Bayan saukar shi yayi wanka yaci abinci ya dan huta sannan ya shiga hostel din maza yana tambayar WALEED ba wuya ya samu room no din dakinshi saide baya so yasan da zuwanshi ya juya zai fita ya hangi WALEED din zaune a wurin wani garden yana karatu bayanshi kadai ya kalla ya gane shine yana tunanin ina HAMEED din ya shiga ya fito ya hangi HAMEED din shi da Angelina suna fira se dafa shi take tana rungumarshi hankalin KHALEED ya tashi karde irin abinda WALEED dinshi keyi kenan? yana tunani ya koma hotel din dake kusa da school din,
Washe gari suna school ya shiga makarantar yanata yawo ciki har yaje department dinsu WALEED time din sun fito daga lecture HAMEED ya fito shi da anjelina sunata labari suna murmushi ,be tafi ba saida yaga WALEED din yana ta karatu bilhakki ,
Hankalinshi ya dan kwanta duk da dai zuciyarshi na cikin waswasi ya koma hotel,
Rana ta ukku yayi niyyar wanshekare zaije wurinsu da dare yana zaune harabar hotel din HAMEED ya wuce shi baiyi wani tunani ba ya tashi ya bishi ranshi na suya HAMEED na zuwa bakin kofar dakin ya tura ya shiga suka fara lalata shi da Angelina ,
KHALEED yayi tsaye ya kasa tafiya yana ta kallon kofar dakin yana mamakin HAMEED baiyi tunanin hakan ba ko kadan,
Har kusan awa HAMEED bai fito ba wannan yasa ya kara yadda da zuciyarshi ya koma waje ya zauna yana jiran fitowarshi,
Bayan ya jima zaune sai ganinshi yayi ya fito yanata sakin murmushi,
Ranshi a matukar bace yana ganin kankantar HAMEED din yasha gabanshi ,
HAMEED baiyi aune ba sai ganin KHALEED yayi gabanshi zuciyarshi tai wani mugun bugawa dummmm jikinshi ya fara rawa,
Yana zare ido da in ina yace"daddy.... "
KHALEED bai bari ya karasa ba ranshi na zafi ya kifa masa mari ,
HAMEED ya dafe kumci yana hawaye ,
A fadace KHALEED yace"mutumen banza muna can muna tunanin kuna karatu ashe kai kananan ka bude sabon shafin rayuwa ,kalar Wannan tarbiyyar aka baka?don kazo cikin arna sai ka yadda naka addinin da alada ka dauki nasu?"
Hawaye masu zafi na zubowa HAMEED yanajin kamar ya shige kasa don kunya yace"dan Allah daddy kayi hakuri wlh bazan sake ba"
KHALEED ya daka masa tsawa tare da cewa" yimin shiru yanzu nan zan kira daddyn ka duk zasu San me kakeyi anan"
HAMEED ya zukunna yana hawaye yace "Dan Allah daddy kayi hakuri wlh sherin shedanne na maka alkawari na dena bazan sake ba"
KHALEED ya lumshe ido zuciyarshi na zafi ji yake kamar WALEED ne ya samu haka yace"Ka fadamin duk abinda kukeyi kenan har WALEED din? "
Ya girgizakai yace"A,a daddy"
KHALEED yayi shiru yana dedeta kanshi cikin sanyin murya yace"HAMEED a kullum duk inda ka samu kanka ka rika tuna waye kai kuma katuna cewa Allah na ganin ka ,don shine kadai ya kamata ka rika jin tsoro ba mutum ba ,ka bani kunya HAMEED banyi tsammani ba "ya wucewarsa cikin hotel din yabarshi tsugunne,
HAMEED nata hawaye kanshi kasa yana regretting ya tashi ya tafi,
WALEED na kwance yaji shigowar shi baiyi yunkurin bude ido ba don yasan kome zai gani ,
HAMEED din ya karaso bakin gadonshi ya zauna yana hawaye yace" WALEED "
WALEED ya masa banza,
Bai damu da amsawar ba yace"Daddy yazo"
WALEED ya juyo dasauri yace"Wane daddy? Daddy na?"
HAMEED ya ciza lips ya daga kai hawaye suka kara zubomai yace"ya ganni a hotel "
WALEED yayi tsoki yace "Da baka shirya ranar tonon asirinka ba?don kana gani anan abinda kake ba bakin komi yake ba shiyasa bakai tunanin ba ko?"yayi murmushi yace" Yanzu dabara ta rage naka fatana daddy ya fadawa su daddyn ka komai"
HAMEED na cije lips yace "Haka zakace?"
WALEED yace"To me zance ko kuka zan tayaka ?time da kake ihu kana shawagi ai bana kusa"
HAMEED yayi tsoki ya tashi ya koma kan bed dinshi ya kwanta yana cikin tunani ko kadan bacci beyi yunkurin daukarshi ba ,
Da safe KHALEED ya sake shigowa school din da tsarabarsu, WALEED daya kagara ya ganshi ya tarboshi yana cikin farincikin ganin daddynsa,
Suka samu wuri suka zauna WALEED nata murmushi yace"daddy ya su Mama da Zarah? "
Yace"Lafiya lau suke Zarah ta bani sako na baka"
WALEED yace "me?" Yana doki,
KHALEED ya zaro biro ya mika masa yace"Tace ka kara dagewa"
WALEED ya amsa yana dariya yana yaba kyautar,
KHALEED ya tsaya yace"Ina HAMEED? "
WALEED yace"Muna tare bayan ya hangoka ya tashi "
KHALEED ya tabe baki yace"kiramin shi inaso muyi mgna"
WALEED ya tashi ya nata yawo cikin school din dakyar ya gano HAMEED yayi zaune yana cikin tunani ,ya dafa shi yace"Daddy na nemanka"
Kamar bazaije ba yaje bai iya hada ido dashi ba ko yi masa magana ba ya samu wuri ya zauna,
KHALEED yace"Inaso nayi maku nasiha da tsoron Allah ,kuji tsoron Allah duk inda kuka tsinci kanku kar ku bari kyale_kyale ya rudeku ku manta su waye ku ,kullum ku rika tuna abinda Allah ya umarceku da Wanda ya haneku ,ku kula da ibada da dokokinsa se ya so ku ya temake ku akan duk abinda kukasa gaba "
Duk su kai shiru suna saurarenshi,
Ya cigaba da cewa "fatan HAMEED zakai tuban gaskiya ba don ganin ido ba ,ko bayan na tafi karka saki ka sake kwatanta zunubin da kayi ,ka tuna idan har ka cigaba da amsa sunan mazinaci to tabbas mazinaciya zaka aura kuma wataran kana iya ganin danka ko yarka a irin halin nasan bazaka so hakan ba"
HAMEED ya jinjina kai yace"Insha Allah bazan sake ba nagode sosai daddy"
KHALEED yayi murmushi ya jawoshi jikinshi ya shafi sumarshi,
Suka cigaba da labari har suka fita suka zagaya gari tare bayan kwana biyu ya dawo Nigeria,
💞💞💞💞💞💞💞
Bayan wani lokaci su Zarah suka zana JSS ranar da suka gama KHALEED ya bata kyautar system ,
Tana ta murna ta amsa tana godiya tana jin kamar ta rungume shi ko taita tsalle,
Shima din murmushin kawai yakeyi ,
Aunty alheri ta rika koya mata system din da temakonshi har ta iya suka dawo yin karatu a system,
Bayan months da JSS dinta su WALEED suka gama exam ya nata murna zai dawo gida suma suna cike da dokin ganinshi ,
Ranar da zai dawo sukaita kai kawo wurin hada masa abinci bayan sun iso KHALEED ya tafi daukosu ya sauke HAMEED gida sannan suka nufi gida,
KHALEED na ajiye mota WALEED ya fita ya nufi cikin gidan dasauri kusan karo sukayi da Muneera da taji shigowar motar ta taso da hanzari,
Ya makalkaleta suna murna gabadaya,
Zarah ta fito cikin doguwar riga white ta dora black gyale tanata kamshi da murmushi fuskarta tace"Sannu da zuwa yaya"
WALEED ya tsaya kallonta from head to toe tana nan Zarah da yasani sai kara wayewa da tayi da fresh data karayi,Sam bai ji dadin irin wannan welcoming dinba yaso ace tataho da gudu tayi hugging dinshi ,
Yana murmurshi yace"Zarah ya school?"
Tace"Lafiya lau "
Ya sake murmushi ya juya jin shigowar KHALEED sam baison ya fahimci wani abu,
Sunata farinciki ya bude trolley dinshi ya fiddo masu tsaraba ,ya siyowa Muneera sari guda biyu ya siyowa KHALEED agogo me kyau,
Muneera na godiya tace"Ina tsarabar kanwar taka?"
Yayi murmushi yace"Mama banda ita"
Zarah tai murmushi tana ganin yadda yaketa faraa,
Ya fiddo wasu sari din dinkakku dede size dinta har kala hudu daya riga da wando biyu dogayen riguna da mayafai daya da sket ta amsa tanata murmushi ta kalleshi tace"Nagode sosai"
Ya kalleta yana murmushi yasan zatai kyau cikin kayan,
Wan safe weekend ne tunda safe taci ado da sarin me riga da wando harda yafa dan gyalen kamar yadda indiyawa keyi ta fito ba India Sak,
Memakon suce tayi kyau sai dariya sukaita mata WALEED kuwa tunda ya kafa mata ido har baisan daukewa tayi masa kyau fiye da yadda yake tsammani,
Bayan sun gama breakfast HAMEED yazo suka gaisa dasu Muneera sannan suka fita,
Haka suka cigaba da rayuwar har suka koma makaranta bayan tafiyarsu Zarah ta koma SS1,
💞💞💞💞💞💞💞💞
Bayan 3 yrs,
Soyayyar KHALEED ta zamewa Zarah fitar numfashi har tana jin bazata iya rayuwa babu shi ba,shima KHALEED ya fada tarkon sonta batare da ya gane ba ,
WALEED kuwa son Zarah ya zama tamkar bugun zuciyarshi da take bugawa a kowane lokaci ,
Zarah ta kasa yadda zaai ta fadawa KHALEED tana sonshi abun ya matukar mata nauyi tana kuma jin shakkun shi sosai so da dama takan yi yunkurin haka amma ta kasa ,suna gab SSCE wata friend dinta ta bata shawara ta rubuta masa wasika ta ajiye masa a bedroom zai gani,
Ta zauna a class tai nazari sosai inba hakan ba batada wata hanya, ta dauki Biro ta fara rubuta takardan kamar haka *Aminci jindadi da kwanciyar hankali su dawwama ga maabocin murmushi da kyawun zuciya,daddy !! nasan abinda zan fada bai kyautu na fadeshi a gare ka ba amma ba zan'iya cigaba da boye halin da nake ciki ba ,kayi hakuri bansan komiye so ba bansan me ake kira soyayya ba sai da zuciyata takasa sukuni tana tunamun kai dare da rana ,daddy ina sonka irin son da bazai taba gushewa a cikin zuciyata ba kaine farincikina kuma rayuwata fatan zaka duba halin da diyarka take ciki*
Ta gama rubutawa ta tsaya karantawa ta karanta fin so biyar tana jin kunyar wasikar har ta na jin kamar ta yaga ta rubuta mishi *I LOVE U* kawai ta ajiye ,amma kuma kila bazai fahimci sakon ba bazai fahimci halin da take ciki ba shiyasa ta zabi ta barta hakan duk da tana tsorace ,
Ta linke papern ta ajiye tana jiran a tashi ana tashi ta fito sai gashi bakin gate ta bude motar ta shiga yana driving tana ta kallonshi kamar ta fiddo papern ta mika mai ko kuma tafadamai abinda ke cikin zuciyarta tayi dakon so fin shekara ukku ya kamata ya san abinda ke ranta,
Suna isa ta bude mota ta fito ta shiga gidan dasauri tai saa Muneera bata falo bedroom dinshi ta nufa kai tsaye ta bude jikkarta ta dauko papern ta ajiye akan bed ta fita dasauri ta shige nasu bedroom din,
KHALEED ya kashe motar ya kulle ya fito ya nufi ciki yana shiga ya wuce bedroom toilet ya fara shiga sannan ya fito ya fara rage kayan jikinshi idanunshi suka sauka kan papern dake ajiye kan gado ya dan tsaya yana kallonta ya karasa cirewa ya duka ya dauka yanata mamaki ya bude ya fara karantawa,
Tunda ya fara karanta abinda ke ciki zuciyarshi ke zafi yanajin ciwon hakan wadda ke matsayin yarsa ce ke fada masa haka ? ta matukar bashi mamaki ranshi bace ya keta takardar biyu ya karasa yi mata gutsin_gutsin sannan ya sakata a dustbin dake cikin dakin ya fita falon ranshi bace,
Yana fita ya samu Muneera zaune ya saki fuska don bayason ta gane ranshi bace sunata fira can zuwa Zarah ta fito jikinta sanyaye tana sanda, da ka ganta kaga marar gaskiya,
Tana hangoshi taga yadda fuskarshi take bawalwala yasa taji kamar ta juya ta koma haka ta karasa tana kin hada ido dashi ,
Suka koma kan dining KHALEED nata binta da kallon mamaki da bacin rai ,dakyar tayi spooon ukku tace ta koshi ta tashi ta koma daki jikinta na rawa tana tsorace karde su medata kauye ko ya cigaba da doremata fuska haka data shiga ukku don zuciyarta bazata juraba,
KHALEED na gamawa ya koma yayi wanka ya sake fita office yana aiki yana tunanin wasikar wai Zarah ce ta rubuta? Zuciyarshi har karyatawa take,
Don kar su hadu yasa bai dawo da wuri ba har sukayi dinner sannan ya dawo baiko kalli inda take ba yawuce part dinshi,
Hankalin Zarah ya kara tashi tana cikin fargaba ta kwanta dakyar bacci ya dauketa ,
Da gari ya waye suka hadu dashi a dining dukkansu cikin shiri ,
Bakinta na rawa tace"Daddy ina kwana"
Ya kalleta da idanunsa da kyau yanayin ta ma ya isa ka fahimci ita ta rubuta kome yanajin takaici yace"lafiya lau"
Suka gama cin abinci ya tashi ya fita ta dauki jikka tabi bayanshi zuciyarta na bugawa ta bude motar ta shiga ya kunnata yayi gaba,
Ranshi bace yake driving yanajin kamar ya shareta amma ya kasa ya gangara yayi parking cikin Zarah ya wani juya ta kara sunne kai kasa,
Ya juyo da kai yana kallonta da husky voice yace"Zarah!! Da wane suna kike kirana?"
Ta kalleshi muryarta kamar zatai kuka tace"Daddy"
Ya kara fiddo ido yace"ina matsayin ubanki kika rubutamin wasikar soyayya?"
Hawaye suka zubowa Zarah tace "kayi hakuri daddy wallahi ba laifina bane"
Ya daka mata tsawa tare da cewa"Shut up Ni kikeso? Kinfara hauka ne?"
Zarah ta girgizakai tana kuka tace"Kayi hakuri... wlh inasonka"
Abun ya zundumeshi ya rike haba yana kallonta ya rasa me zaiyi yanajin kamar ya kifa mata maruka yace"Get out "
Ta kalleshi ta make kafada tana hawaye, yace "I said get out from my car stupid"
Zarah ta bude motar tana kallonshi tana hawaye zuciyarta na zafi tai gaba tana tafiya tana kuka ,
KHALEED yayi tsoki yana kallon bayanta daukewar idon da zaiyi ya tada motar yaji wani kiiiiiiiiiiiiii an taka burki ya dago dasauri sai ganin Zarah yayi kwance tsakiyar titi,
Zuciyarshi tai wani irin bugawa da yajita har cikin kanshi jikinshi na rawa ya bude motar dasauri ya nufi Zarah dake kwance lifeless yana a matukar tsorace ,
Yana zuwa ya zube gabanta ya jawota jikinshi yana "Innalillahi wainna ilaihi rajiun!!!! Zarah Zarah" Da karfinsa ya rungumeta jikinshi yana kuka,
Mutane sun zagayesu harda Wanda ya kadeta goshinta nata fidda jini ya dauketa da gudu yasata mota ya nufi asibiti daita hankalinshi tashe ,yana driving yana waiwayowa yana kallonta yana hawaye yana cije lips yana zuwa aka amsheta aka shiga ciki daita ,
Yayi tsaye ya rungume hannu yana kallon kasa yana tuno rayuwar da sukayi tun daga farkon zuwanta har zuwa yau yadda take shige mishi yadda take masa murmushi da wasikar data rubuto jiya ya dafe goshin shi yana sabbin hawaye yana a matukar tsorace kar wani abu ya sameta,
Yana kidime ya fiddo waya ya kira Muneera dake hanyar school ta dauka ta kara kunne,
Yana hawaye yace "Mama kizo muna asibiti mota ta kade Zarah"
Hankalin Muneera ya tashi tace"Wane asibity? "
Yace"Imperial"
Ta latse wayar hankalinta tashe ta fadawa driver ya juya zuwa asibitin,
Muneera nata tunani me yakai Zarah kan titi shi da zai kaita bakin gate?
Tana tunani har suka isa dasauri ta sameshi tana tambayarshi"ya akai mota ta kadeta ba kuna tare ba?"
Yayi shiru bai ce komi ba saboda baisan amsar da zai bata ba,
Suna tsaye likitoci suka fito daga dakin a tare suka shiga ciki hankalinsu tashe ,
Suna shiga su kayi tozali da Zarah saman kanta gabadaya an nannadeshi da bandage ga wasu minor injuries a hannuwa da kafarta,
Muneera tai saurin karasawa wurin tana sallallami tana jin tausayinta ,
Shi ko kurawa gadon ido kawai yayi yana kallon ciwukan jikinta yanajin haushin kanshi yadda ya ajiyeta a bakin expressway kuma dole sai ta tsallaka sannan ta isa school dinsu,
Jikinshi sanyaye ya karaso yayi tsaye kanta yana jin kamar ya medo ciwukan jikinshi,
Muneera nata hawaye don sosai Zarah ta shiga ranta tana jinta kamar diyarta ta cikinta ,suna zaune suna jiran farfadowarta har laasar sannan Zarah ta farko cikin fitar hayyaci tana hawaye muryarta kamar ta shekara tana ciwo tafara kiranshi "Daddy.. wlh inasonka... kayi hakuri ba laifina... bane"
Gaban KHALEED yayi mugun faduwa jin maganar agaban Muneera,
Muneera tai saurin sanya hannunta cikin nata tana fadin "Sannu Zarah sannu"
Zarah na cikin ciwo batasan me take ba tace"daddy nakeso Mama wlh nadade inasonshi "
Muneera ta fiddo ido tana kallonta idanunta kulle tana ta fadin shi take so,
Kunya ta kama KHALEED ya juya ya fita daga dakin yaje ya shiga mota yayi zaune tare da kwantar da kanshi jikin sitiyari muryar Zarah na masa yawo a kunne "Daddy wlh inasonka kayi hakuri ba laifina bane".
*SHIGAR SAURI*
Painful love story
Romance special
Writing by
*MAMAN MAMY (SHALELE)*
*Wattpad@mumies122*
*Dedicated to my close friend ikra Rukayyat*
*Devoted to identical twins hassan & Husain 80k Fatima dimple*
*Small gift to my real fans*
*PROFICIENT WRITERS ASSOCIATION*
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/
TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09
Page > 49&50
*Muna saida kayan mata da na maza suna da kyau sosai kuma cikin sauki muna turawa koina ga me bukata seya tuntubi wannan number👉🏼 0806 672 6866*
Zuciyarshi wani irin bugawa take da karfi yaja tsoki yana yamutsa fuska ,Tabbas yana son Zarah yana son farinciki da walwalarta amma ba da aure ba , ya zaai ya aureta yana zabaya marar lpy ita kuwa me lpy kuma me kyau da zata iya auren Wanda ya fishi ai ya kwareta,
Muneera na ciki ta zubawa Zarah ido tana kallonta abun duk ya daure mata kai ,Zarah ta cigaba da fadin tana son daddy idanunta kulle Muneera ta tashi dasauri ta kira nurse suka shigo dakin da sauri,
Nurse din ta fara tapping Zarah tana kiran sunanta"Zarah !! Zarah "
Zarah sai juya kai take tana cikin zafin ciwo,ganin hakan yasa nurse din yi mata alluran bacci ta juya ta fita,
Muneera ta rike gemu tana kallon fuskarta zuciyarta na tunani da dama me yakai Zarah kan titi?abinda take fada ko gaskiya ne?
Ta dauki wayarta ta kira KHALEED yana cikin mota yaga kiranta ya fito ya nufi ciki jikinshi sanyaye ya tura kofar ya shiga bayan ya dan kalli gefen zarar yayi tsaye,
Muneera ta kalleshi sosai tana nazarinshi yayi wani iri dashi tace"Ya akai wai Zarah ta hau titi har mota ta kadeta?"
Ya danyi jimm yana searching me zai fada ya rasa me zaice,
Muneera na masa kallon tuhuma tace"Kanajin abinda take fada bayan ta farko?"
Ya bata fuska yanajin kunya yace"Zafin ciwo ne kawai"
Muneera tace "Zafin ciwon ne yasa ka har ka fita waje?"
Ya daga kai ya kalleta yace"Tausayi kawai take bani"
Muneera tace "To shikenan koma miye zata farko zanji ko minene"
Ya kalli Zarah dake kwance yana jin kamar ya tashe ta ya buga mata warning karta fada mata komi don yanda yaga yanayinta har Muneerar zata iya fada mawa,
A hankali yace"zanje na kawo maku abinci "ya juya ya fita yana tunani barkatai,
Muneera ta maida hankali gun Zarah a kagare take taji miye ke faruwa idan har da gaskene tana matukar farinciki da haka saide bata sani ba ko iyayen ta zasu amince duk da de bata tunanin akwai abinda zasu nema su rasa a gunsu,
KHALEED ya sai masu abinci ya kai masu sannan ya koma gida jikinshi sanyaye yana shiga daki wurin dustbin ya fara isa ya tsaya yana kallon takaddar dayayiwa gutsin_gutsin yanajin son kara karanta ta ,
Ya nata ya mutsa fuska yasha maganin ciwon kai ya shiga wanka ya fito yayi kwance yana kallon sama tunda ya karanta takardar ya kasa natsuwa abinda ke ransa kenan,
Bayan Maghreb Zarah ta farka tana dawowa hayyacinta firarsu da KHALEED ce ta fara fadomata zuciyarta na tsananin ciwo tana tuno yadda yake mata magana a fusace hawaye suka zubo mata ta bude ido tana kallon sama,
Muneera tace" Sannu Zarah Allah yabaki lpy"
Zarah ta juyar da kai ta kalli Muneera kamar yadda tayi zato ba kowa wurin se ita hawaye suka kara zubo mata ta juyar da kai ta fara kuka me sauti,
Muneera ta zauna gefen gadon tana goge mata hawaye cikin rarrashi tace"Sannu Zarah kiyi hakuri "
Zarah na kuka tace"Mama ki bawa daddy hakuri na mishi laifi bazan iya jurar fushin shi ba"
Muneera tace "Laifin me kikayi masa?"
Tana kuka tace"Na fada mai ne ina son shi Mama ki bashi hakuri dan Allah"
Muneera taji dadi a ranta tace "To kiyi shiru zan bashi hakurin yanzu ki daure kici abinci"
Zarah ta girgizakai a hankali tace"Ruwa zansha"
Muneera tace "Ruwa kadai tun safe kike kwance babu komai cikinki"
Zarah tace "Na koshi"
Muneera na jin tausayinta tana tuno time da suka kwanta asibity farkon ganinta ta bata ruwan,
Tana shan ruwan ta kamata tai Sallah a zaune sannan ta kwantar da ita,
Bayan anyi ishai KHALEED ya nufo asibitin da wani abincin da drinks masu sanyi da fruit,
Ya bude dakin ya shiga kamshin turarensa ya game dakin Zarah ta dan bude ido ta kalleshi fuskarshi daure yana sanye da doguwar riga baka da kwalliyar golden jikin wuya da aljihunta ya matukar kyau ta meda idonta ta rufe zuciyarta na bugawa,tana tunanin zai mata magana ko da sannu ce,
Shi ko ajiye kayan yayi ya dan kalleta ya kalli Muneera yace"Yame jiki?"
Tace"Dasauki"
Yace"Allah ya bata lpy"bai kara cewa komi ba ya juya zai fita,
Muneera ma tayi mamakin da bai mata sannu ba ranta a dan bace a ganinta Wanda yace yana sonka abun kulawa ne bare shi da Zarah ta zaba cikin lafiyayyun da yake fada,
A hankali ta kirashi ya waiwayo tace"Ka jirani a waje"ya daga kai ya fita zuciyarshi badadi yana ganin hakan da yake kadai zaisa Zarah ta dena maganar tana sonshi,
Muneera ta tashi ta biyoshi tana samunshi tace"KHALEED banason haka, ina laifin Wanda yace yana sonka? Kanata daure fuska da shan kamshi ko sannu bazaka yi mata ba? "
Cikin ladabi KHALEED yace"Mama dan Allah kubar wannan maganar duka Zarah nawa take ?yaushe tasan so da har zata tunkareni da maganar ,WALEED ne dede ita bani ba"
Muneera na jin haushi tace"Ai tasan da WALEED din ta zabeka kai abun farincikinka ne ka samu mata kamar Zarah me kyau da tarbiyya tunda muke tsawon shekarun nan ka taba gani na mata fada? Saboda ladabinta ,dan Allah kadena daure fuskar nan haka ka saki ranka ku fahinci juna"
KHALEED ya kalli Muneera yana ganin idan yayi hakan baiwa Zarah adalci ba kyanta ta samu lpyayye su haifi yaya masu lpy hankalinta ya kwanta ba shi ba da idan ta aureshi zata iya fuskantar wani kalubalen rayuwar nan gaba,
Maganar bata shigesa ba amma yace"To sai da safe "ya juya ya fita,
Ta bishi da harara ranta na baci don ta fahimci bata shigan ba ta koma ciki,
KHALEED ya koma gida yanata tunani tun abincin da ya danci da safe bai kara cin komai ba saboda rashin kwanciyar hankali hakanan bakomai cikinsa ya kwanta yanata tunanin maganar Muneera zuciyarshi taki aminta,
Wanshekare ma yana shigowa ya ajiye musu abubuwan bukata ya gaida Muneera yayi tafiyarshi wurin aiki,hakan yana konawa Zarah zuciya ganin be damu da lafiyarta ko rashinta ba ta kara shiga damuwa taki cin komai,
Muneera ta hada mata tea da wurin sha biyu ta tadata tace" Zarah ki dan sha saboda maganin da kk sha yayi aiki ba ason shan magani hakanan,
Ba don ta so ba ta kurba sau biyu ta koma ta kwanta idanunta kulle,
Da rana KHALEED ya kara shigowa da abinci kallo daya dinnan ya mata ya ajiye ya juya ya fita Muneera tabi bayanshi da kallo tana jin haushi daga Jiya zuwa yau haryayi rama ta girgizakai tafara kokarin bawa Zarah abinci amma ta ki dakyar ta samu ta dan kurbi fresh milk ,
Bayan kwana biyu da kwantar da ita WALEED ya kira Muneera,
Ta dauka tana faraa suka gaisa har zata kashe yace"Ammm mama Zarah na kusa, kwana biyu bamu gaisa ba"
Muneera tace "Lafiyarta lau yau wata kawarta tazo sun fita gaido kawarsu bata lpy" ta boye masa halin da ake ciki tana gudun ya shiga damuwa,
WALEED yace"To shikenan agaidamin ita in sun dawo "
Tace to sukai bankwana,Zarah na kwance amma ko jinsu batayi saboda zurfin tunani data shiga,
Har bayan kwana bakwai duk ciwon jikinta ya warke amma baa sallamesu ba tayi baki ta rame sosai Muneera na bakin kokarin ta amma zarar bata cin abinci,
Yau tunda safe KHALEED ya shigo asibitin cikin shirin office ya ajiye kayan breakfast dinsu ya gaida Muneera ta amsa muryarta sanyaye don al'amarin Zarah ya fara bata tsoro,
Yace"yame jiki?"
Tace"gatanan "
Jin amsar yasa ya kalli Zarah kanta ba bandage bakin da tayi ta rame shine ya bashi tsoro ,yana ganin zama asibitin ma wahala ne ya fita yaje office din doctor dake dubata,
Bayan sun gaisa yace"Naga ciwon Zarah ya warke sosai ina ganin zamu koma gida a cigaba da kulawa da ita "
Likitan ya girgizakai yace"Tabbas ciwonta ya warke amma still bata lpy tana bukatar kulawar likitoci Bp dinta is high sannan tana da olcer "
Gaban KHALEED ya fadi jin bp yana cikin damuwa yace"likita bayan wannan ba wata matsalar?"
Likitan yace"Eh idan har bp din ya sauka ta kuma rika cin abinci to zamu sallame ku"
Hankalin KHALEED tashe yace"Nagode"ya mika mai hannu sukai musabaha ya tashi ya fita yana cikin rudewa da tsoron wani abu ya samu zararshi don tabbas yasan ya damu da ita tunda ta fadi tana sonshi kullum tunaninshi shine bai lpy dalilin kadai ke hanasa amsar soyayyarta ,
Ya bude kofar dakin dasauri yayi tozali da ita tana kwance yabi jikinta da kallo yana ganin ramar da tayi,
Cikin rudewa ya karasa ciki har bakin gadon baiko tsaya kallon Muneera dake zaune ba,ya fara hada ruwan tea,
Jin kamshin shi da motsinshi yasa Zarah bude ido ta kalleshi taga abinda yake fatanta ace ita zai bawa tana cike da son ya nuna ko da damuwa da ita ne,
Ya gama hada tea ya juyo gareta cikin sanyin murya yace"Zarah tashi "ta kalleshi sukai 4 eyes idanunta cike da hawaye ta yunkura ta tashi zaune ,
Ya zauna gefenta ya bude ledar biredi ya debo yana mata fada"seki zauna yunwa ta kashe ki?aka fadamiki bamuson rayuwar ki?"
Wani dan karen dadi ya mamaye zuciyarta hawayen farinciki suka fara tsere a cheek dinta ta kafe fuskarshi da kallo,
Ya debo bredin ya kai bakinta batare da ya kalli kwayar idanunta ba,
Tana ta kallonshi ta bude bakinta ta diba ya dora mata cup ta dan kurba tafara taunawa a sannu,
Ya dan kalleta ya dauke ido yana jin tausayinta yace"Kidena sa damuwa a ranki Zarah dubi duk yadda kika rame meyasa baki tausayawa kanki ne?"
Muneera tai murmushi tana kallon zallar so da tausayinta a tare dashi ta tashi ta fita,
Shi kuwa gabadaya brain dinshi ta manta daita burinshi kawai Zarah taci abinci ga olcer ga bp akwai gagarumar Matsala,
Yana ta bata tea tana kallonshi tana sha a hankali tace "Daddy ka yafemin bazan sake ba"
Ya dago kai ya kalli kwayar idanunta me cike da rauni da damuwa ,ya yamutsa fuska tare da cewa "Idan kin kwantar da hankalinki kina cin abinci na yafe miki "
Hawaye suka zuraro mata yayi tsaye yana kallon fuskarta, idonta kasa tana in ina tace"Daddy....ina...ina...ina"takasa karasawa ta rufe fuskarta ta saki kuka har numfashin ta na daukewa,
Cikin zallar tausayi ya jawota jikinshi ya rungumeta cikin tsadadden kirjinshi ,
Zarah ta kwantar da kai jikinshi tana cigaba da kuka,
Zuciyarshi na radadi yace"Enough !!!! na sani kina sona and nima ina sonki"
Wata zinariyar kibiya me narke zuciya ta soki heart din Zarah ta sauke wata ajiyar zuciya ta kara shigewa jikinshi tana hawayen farinciki,
KHALEED baisani ba sai tsintar kanshi yayi da yiwa silk hair dinta kiss ya lumshe ido yanajin sonta cikin zuciyarshi bai taba samun kusanci da kowace mace ba fiye daita haka bai shaku da kowace ba fiye daita bayan Muneera bai damu da kowace ba sai ita he's surely in love with her,
A hankali yace "Banason zamanki asibityn nan bana jindadi ki warke hakanan mu koma gida"
Zarah na jin ta warke tace"I love u daddy I really do"hawayen jindadi na zubarmata yadda ya shareta batai tunanin zai furta mata hakan ba ko kusa,
Muneera na waje taji shirun yayi yawa tun takwas har rana ta ganyare gari KHALEED bai fito ba,
Ta tashi daga inda take zaune taje ta tura dakin sai ganin shi tayi rungume da Zarah,
Ta shiga tana dan murmushi tace"wai ka fasa zuwa aiki ne?"
Suka saki juna dasauri ya tashi yana shafar gefe_gefen fuskarshi ya fita ,
Muneera tabi bayanshi da kallo kamar ba shine keta shan kamshi ba ,ta karasa bakin gadon ta zauna tana kallon Zarah data ke sunne kai,
tana murmushi tace "Su Zarah an samu sauki ko?"
Zarah na murmushi ta dage kafada ta rufe fuskarta,
Muneera tai dariya ta girgizakai tana jin sa'ida domin itama ta shiga cikin damuwarsu,
Tunda KHALEED ya fita aiki yake jinshi wasai daya tuno moment din yau se yayi murmushi shi kadai har azahar yana gama sallah ya wuce wani special restaurant yayo masu take away da kayan baking ya nufo asibitin yanajin nauyin muneera don yaji kunya sosai dazun,
Bayan yayi parking ya dauki ledojin ya nufi ciki yana zuwa ya bude dakin tare da yin sallama,
Muneera na zaune kan carpet tana Jan carbi ta dago tana kallonshi ta amsa ,
Ya karasa yana kallon gadon wayam ba Zarah ya ajiye ledojin ya jingina da bango yayi tsaye,
Muneera na binshi da kallo tace"Me kake jira?tunda ka kawo abinda ya kawo ka saika tafi"
Ya kalleta yana dan murmushi yace"ayi hakuri Mama "
Ta watsa mai harara tana dan murmushi ta cigaba da laziminta,
Zarah na wanka toilet ta gama ta bude kofar ta fito daure da karamin tawul tana fitowa idanunta suka hadu da nashi tai maza ta juya ta koma ciki,
Abun nata dariya ya bashi yabi kofar toilet din da kallo,
Muneera tace "Ka tafi tunda kaganta ta samu ta shirya tayi sallah anjima idan kun taso aiki sai ka dawo ka kara ganinta hankalinka ya kara kwanciya"
KHALEED ya kalli Muneera yana yar dariya yace "Mama"
Tai dariya kadan tace"To naga kaima kadan dawo hayyacinka ai gwara ka dawo nafiso ya karasa kwanciya hankalin"
Baice mata komi ba ya nufi kofa yana dariyar maganarta harya shiga mota yana driving yana sakin murmushin maganar Muneera,
Zarah na jin ya fita ta fito ta fara saka kaya don kar kunya ta hanata cin abinci yasa Muneera bata zaulayeta ba sai ga Zarah da zuba abinci tana ci da kanta,
Bai dawo da marecen ba saboda nauyin Muneera sai bayan ishai ya shigo Muneera ta tashi ta fita kamar zataje wani wuri ,
Yanata kallon Zarah dake ta murmushi kanta kasa yace"Baby ya jiki?"
Zarah ta rufe ido da hannu daya tana jin kunya da dadin sunan lokaci daya,
Yace"Ehmm ? Asibitin nan badadi zama cikinta ko?"
Taki basa amsa ta fara wasa da yatsun hannunta,
Yayi murmushi yace "Kinci abinci dazun?"
Ta daga kai ,yace"Yanzu kinsan me na siyo miki? "
Ta girgizakai ,
Ya dauko ledan tsire ya bude gabanta yace"nasan zakici "
Ta kalleshi tana sakin sassanyar murmushi tace "Nagode daddy"
Yayi murmushi jin ta kirashi da daddyn kuma,
Tasa hannu ta dauko tsinke daya ta fara ci tana jin dadin naman sosai ,
Ya fiddo wayarshi yana latsawa yana dan kallonta yadda ta dage cin nama ,
Muneera taji shiru yaki fitowa ta koma dakin ta samu Zarah nata cin namanta,
Ta kalleshi tace"Sai da safe dare nayi inason diyata tayi bacci"
Ya kalleta yana dariya yace"Mama yanzu na shigo fa"
Tace"Eh ka tashi ka bamu wuri"
Yana murmushi yace"Mama dan Allah ayimin hakuri hakanan mun dedeta"
Tai murmushi taje ta zauna tasa hannu tana cin tsiren ta kalleshi tace"kaci abinci ne?"
Ya girgizakai, tace "join us"
Ya kalli Zarah ya saka hannu ya dauko ya fara ci, suna ci suna fira har kusan 10 sannan ya tafi ,
Bayan ya koma gida ya kwanta ba abinda idanunshi ke hangomasa sai Zarah zuciyarshi na jin kaunarta yana ta murmushi bacci me dadi ya daukeshi ,
*************************
Bayan kwana hudu aka sallami Zarah ta warke simul suka koma gida cikin farinciki ,
Zarah wata kunyar Muneera ta rikayi tana ganinta matsayin surika harshi wata sabuwar kunyarshi ta dawo ji,
Bayan kwana biyu da dawowarta kullum da dare Muneera basu wuri take don suji dadin fira tana matukar son abun ya kasance yau ma hakan bayan ta danyi kallo ta shige ciki,
Zarah na zaune kujerar dake nesa dashi ya kalleta yace"Baby dawo nan"ya nuna mata kusa dashi
Ta kalli inda ya nuna mata kusa dashi tana jin kunya ta tashi ta koma kasa ta zauna,
Yayi murmushi yace"Yaushe zaki koma school kusan two weeks bakije ba?"
A hankali tace"Gobe "
Yace"Ok ni bari na tafi na kwanta"ya tashi tsaye,
Ta kalleshi tace"Daddy tun yanzu? "Ya kalleta ta kalli agogo tana duban time,
Yayi murmushi yace"Labarin me zaki bani?"
Tace"Kallo zamuyi"
Yace"kiyi ke kadai sai da safe"
Ta mike itama tace"Tom"
Yayi murmushi yace "kin fasa kallon?"
Ta daga kai yace "OK " ya koma ya zauna yana kallon TV
Itama ta koma ta zauna ya kalleta yana dariya yace"Kinganki ko"
Tana dariya tace"wlh daddy kallon ba dadi idan baka kusa"yayi shiru yana kallon TV yana ganin yarintarta ya kara kallonta sannan ya cigaba da kallo ,
Wansafe ta fito cikin shirin uniform sun mata kyau sosai tana ta sakin murmushi sukayi breakfast suka dauki hanyar school ,
Tana kallon titi ta tuno last daukota da yayi da yadda sukayi dashi ta juyo da kai ta kalleshi,
Yana driving yace"Ya akai baby?"
Tai murmushi tace "kayi kyau"
Yayi murmushi zarar na bashi mamaki wani lokaci yace"Nagode "
Daya ajiyeta sai da ya bata kudi in tana son wani abu sannan ya tafi,
****
Soyayya suke me kayatarwa da shiga zuciya abubuwansu yana burge Muneera ,
Watarana da marece ya dawo aiki Zarar kuma na school ta kirashi yazo ya zauna ,
Muneera tace "KHALEED tunda Zarah ta kusa gama school inaga yafi kyau ayi maganar aurenku da zaran ta gama school din sai a daura"
Ya kalleta yayi shiru dukda yana sonta shide haryau gani yake bata dace dashi ba,
Ta cigaba da cewa"Zanje na samu kawunka suje su tambayo maka aurenta idan har sun amince sai a saka rana "
Zuciyarshi sanyaye yace"To mama Nagode sosai"ya tashi ya wuce ciki,
Bayan kwana biyu taje ta samu kawunsu akan maganar yace zai samu time su tafi,
Bayan sati biyu da maganar suka tafi kauyensu Zarah tare dasu gabadaya bayan an tarbesu sun huta kawunsu KHALEED ya sanarda kawu Habu abinda ke tafe dasu,
Kawu Habu yaji dadi sosai yace"Ai komi na Allah ne idan yaso sai ya halicci mutum baki acikin turawa abubuwa na tafiya ne yanda ya tsara, ba muda matsala da ciwon alhaji domin haka Allah yakeson ganinshi ,Na matukar jindadi da yadda kuka amince Zarah ta zamo surikarku bayan duk temakon da kuka yi mana, na bashi Zarah har'abada fatana Allah yabasu zaman lpy da zuria dayyiba ,wlh alhaji koda cikin yarana ne ya gani yana so zan bashi bare kuma Zarah daya rike ya dauki dawainiyar rayuwarta aimu bamuda abinda zamu biyashi sai de muyi masa addua"
Su kawun KHALEED sunji dadin zancenshi sosai sukace"Mungode Allah yabar zumunci insha Allah zamu dawo don kawo kudin aurenta"
Habu ya girgizakai yace"Ai mu daku duk dayane na bashi Zarah kyauta bama bukatar kome har sadaki ni zan biya mishi ai naji dadi sosai zarah zata cigaba da zama daku har karshen rayuwarta "
Su kawu su kaita godiya kawu habu ko yayita hidima dasu har wanshekare sannan suka taho bayan an tsaida ranar bikin wata ukku bayan candy dinta,
KHALEED, Zarah, Muneera ba zaka gane wanda yafi farinciki ba domin duk suna son abun sosai,
India.......
WALEED karatu suke ba kakkautawa domin final exam na gabato su ya dage sosai domin burinshi yana samun aiki a daura aurenshi da Zarah bai taba kawo zata ce bata sonshi ba kowani zai riga shi ko wani abu can abinda yake ji de Zarah tashi ce mallakinsa ce shi kadai,
A kowace school akwai love birds wadanda suka tsunduma cikin matsananciyar soyayya sune suka fito da wani salo na rubuta sunan masoyiyarka a jiki da tattoo don nuna mata cewa tana zuciyarka har'abada,
HAMEED da yanzu ya natsu bayan ya samu dakyar ya banbare Angelina daga jikinshi yarinyarshi Husna kawai yake tunani,
Ya kalli WALEED dake karatu yace" Gaskiya dole naje a rambadamin sunan husna ,kai ma ya kamata kaje a rubuta maka Zarah inde da gaskene soyayyar"
WALEED ya dago yana murmushi yace"To miye zanje ayi min"
HAMEED ya zaro ido yace"dagaske?"
WALEED yace"kai da karya kake bazakaje a rubuta maka husnar ba?"
HAMEED yace"cab idan kuma ban sameta bafa? sai naita kallon bakinciki?"
WALEED yace "ohh sorry ni zanje domin Zarah tawace ba kokonto"
HAMEED na dariya yace"Allah ya bada saa"
WALEED ya rufe littafi ya jashi yace"muje kagani"
Suka isa wurin me tattoo WALEED na sanye da riga armless ya mika hannunshi ,
Me tattoo ya kalli damtsenshi yace"kyahe her name?"🤣😹
WALEED yace "Star....draw a shining star on "
*SHIGAR SAURI*
Painful love story
Romance special
0 comments:
Post a Comment