*Muna saida kayan mata da na maza suna da kyau sosai kuma cikin sauki muna turawa koina ga me bukata seya tuntubi wannan number👉🏼 0806 672 6866*
Me tattoo ya dage ya zana masa dalleliyar tauraruwa a damtse,
HAMEED na gafe yana kallonshi da mamaki baiyi tunanin da gaske yake ba ya tabbatar soyayyar Zarah acikin jinin WALEED take bai tunanin zata fita ko a wane hali,
Ana gamawa WALEED ya kalli hannunshi yana murmushi ya kalli HAMEED yace"Saura kai"
HAMEED yayi dariya yace "Idan an daura zanje a rubuta"
WALEED yayi murmushi ya biya me tattoo suka koma hostel duk time da ya kalli star wani farinciki yake tsintar kanshi ciki wani abunma sai time da Zarah ta zamo jikinsa time din da zata kasance kusa dashi a ko da yaushe,
Ba dadewa su Zarah suka fara zana SSCE two months suka gama ,ranar da su kai final sunsha hotuna da friends, KHALEED yazo daukarta,
Ta nufo motar tana ta murmushi shi kuwa ya kureta da ido yanajin matsananciyar kaunarta ta bude motar ta shiga ta kalleshi tana murmushi,
Yayi kayataccen murmushi yace"Congrat amaryata ina tayaki farinciki kin kammala school"
Tace "Thank u daddy nagode sosai"
Yayi murmushi ya tada motar yana tafiya da ita a slow duk rabin hankalinshi na wurinta yanayinta da tsarin halittarta dole kowane namiji me lpy yayi shaawarta,
Tana ta murmushi ta kalleshi tace"Daddy ina kyautata ?,nayi zaton ina shigowa zaka damka min kyautar tayani murna"
Yana mata wani kallon shaawa yace"Bayan zuciyata dana mallakamiki har wata kyauta kikeso?"
Tai dariya tana jin kunya tace"Daddy yaufa nayi candy kyautar zuciya kuma ainice na fara baka tawa"ta karasa da boye fuskarta,
Yabi ta da kallo yana murmushi ya fiddo wata leda yace "To dama na taho daita ai dole nai miki special kyauta"
Ta juyo tana murmushi ta kalleshi ta amshi bakar ledar ya meda kanshi a titi yana dariya ciki_ciki,
Zarah na murna ta bude ledar taga wata ledar ta dagota sama da sauri abinda ta gani yasa ta sakin ledar a tsorace ta rika bin ledar da kallo an rubuta Lady care a jikin ledar pad din,
KHALEED ya fara dariya yana kallonta,
Bata kalleshi ba ta juyar da kanta tana kallon window ta kara ta kurewa sosai tana jin kunya,
KHALEED na dariya yace "Sorry...I'm teasing u"ta mishi shiru bata kalleshi ba,
yana driving ya jawo ledar da sauran pad din ke ciki da Wanda ta fiddo ya ajiye kasan seat ya cigaba da driving,
Motar tayi shiru gabadaya ya gama bata kunya wani time tana mamakin kalamansa da abubuwan da yake mata,
Ya kalleta yana murmushi A hankali yace" Mama ce tace na siyo miki pad shiyasa na baki tun anan"
Ta kalleshi tana turo baki tai dan murmushi ta sunkuyar da kai,
Suna isa gida zata bude kofa yace"Dauki abunki ki tafi dashi"
Tana jin mugun kunya ta ruga da gudu cikin gida,
Yayi yar dariya ya dauki ledar ya nufi ciki bai sameta falo ba ya zauna ya bawa Muneera ledar,
Tana zaune ta kwala mata kira ta fito tana sunne kai,
Muneera ta mika mata ledar ,zarah tai saurin kyallara ido ta kalleshi dariya ta kama KHALEED ya juyar da kai yana gumtsewa,
Ta amsa tana jin kamar tai kuka ta juya ciki, Muneera ko bata damuba cos da canma tana aikenshi siyowa yanzu ko bata damu da kiran Zarah da tayi ba cos shine mijinta,
Iyakar kunya Zarah taji ta suna gama abincin rana tace yunwa takeji taci nata bayan ya dawo suka zauna dining su kadai,
Ya kalli Muneera yace"Mama ina Zarah bata cin abincin?"
Tana cin abincinta tace"Tace yunwa takeji taci nata tana daki kwance"
Yayi murmushi ya dauki spoon yafara cin abincinsa,
Da dare dole ta zauna cin abinci amma ko sau daya bata yadda sun hada ido ba suka gamaci suka danyi fira Muneera ta koma daki,
Suna zaune su kadai yana murmushi yace"Baby ayiwa daddy hakuri"
Ta dan harareshi tana turo lips ta meda kanta kasa,
Ya tashi ya fita ya dawo dauke da wani kwali ya bude ya fiddo wata hadaddiyar waya me tsada tanata satar kallonshi ya gama hada wayar ya kunna yace"Ga special kyautar daddy "ya mika mata
Tana farinciki jin tata ce ta kalli wayar tai saurin mika hannu ta amsa ta jujjuya tana farinciki ta kalleshi tace" Nagode sosai daddy na shiyasa nake sonka sosai "
Yayi murmushi yace "Ki duba no dina data son da ta Mama kadai ke ciki nayi saving tawa da sweet daddy hakan yayi?"
Tana murmushi ta daga masa kai tace"Thanks u daddy naji dadin wannan kyautar sosai"
Yayi murmushi yace"good night "ya tashi ya shiga daki ,
Tana zaune ta na ta juya wayar tana jinta kamar rai ta shiga message tafara typing message kamar haka...
"Ever since you walked into my life, I have been smiling. There hasn’t been a day when I have gone to sleep with a frown on my face, and it’s all because of you. Daddy !! I am glad that you came into my life Thanks for all the happiness that you gave me... I love u "ta saki murmushi bayan ta tura mai ta shige daki tana murna ta samu Muneera zaune kan bed tana duba littafin adduoi ,ta zauna bakin gadon tana murna tace" Mama daddy ya saimin waya"ta mika mata wayar,
Muneera ta amsa ta kalla tace "Me kyau kuwa daddy ya kyauta"
Zarah ta amshi wayar tana farinciki ta cigaba da latsawa,
KHALEED wanka Yayi ya fito yana annashuwa yayi shirin bacci ya hau bed ya dauki wayarshi sai ga text dinta yayi murmushi ya shiga ya fara karanta text din zuciyarshi na kara narkewa kan sonta ,ya memeta sakon fin sau goma yanata murmushin jindadi ya meda mata reply "The simple three words '''I love you''' will never express how much I love you, My love for u is so deep that I feel I love you more than I love myself"
Time da Zarah taga sakon saida zuciyarta ta dena aiki na seconds saboda tsananin dadi ,
Suka cigaba da ture_turen texts sai da dare ya raba sannan suka kwanta rungume da wayar,
Daganan sabuwar soyayyar handset ta tashi suna cin abinci ma suna ture_ture ,Muneera data lura tayi tunanin ba amfanin zama hakanan tunda ta gama school gwara ayi bikin a huta,
Ran weekend basu da aiki yana zaune gida domin daga aiki sai gida bai zuwa koina ,
Muneera ta shigo ta sameshi tace"Ka shirya kaje wurin kawunka na masa magana zaa rage wata guda na bikinnan dan naga duk kagare kuke"
Ya sunkuyar da kai yana murmushi ,
Tai murmushi tace "Ka shirya kuje ku Sanar da yanuwanta idan sun amince shikenan ,ai kanata shirye_shiryen biki ko?"
Yayi murmushi yace"Dama inaso gobe muje kuga gidan ansa komai amma yanzu sai mun dawo "
Muneera tana murmushi tace"Allah yasa alheri ya baku zaman lpy da zuria dayyiba masu yawa da albarka wadanda zakuyi alfahari dasu kamar yadda nake da kai"
KHALEED kam murmushi kawai yake baice amin ba har ta fita,
Wanshekare su kaje kawu Habu yayi naam da hakan domin ya riga ya mallaka musu ita saboda sun cancanci hakan ,suka dawo suka cigaba da shirye_shirye
Ranar Friday ya daukesu suka tafi gidan tangamemen gida me matukar kyau da tsaruwa Zarah kallon gidan kawai takeyi wai nata ne a ciki zatai rayuwa ta kalleshi suka hada ido suka sakarwa juna murmushi tana matukar jindadi,suka gama zagaye gidan muneera nata Allah yasa alheri suka koma gida,
Aka cigaba da shirin biki Muneera ke gyaran Zarah ciki da waje sunata dokin zuwan ranar,
India....
Su WALEED sun fara exam yana matukar kagare su gama yayi gida ya dau alwashin yana komawa zai sanar da Zarah soyayyar da yake mata zai kuma fadawa KHALEED domin ya cika alkawarin daya daukar masa na bayan yayi karatu zai aura masa muradin zuciyarshi ,
Da dare ne kowane dalibi yana rungume da papers gabanshi yana karatu WALEED na karatun tunanin Zarah ya fadomai ya rasa wace kyauta zai bata ,
Ya rufe papers ya fita waje ya samu HAMEED zaune kwanyarshi tayi zafi yana karatu,
Ya zauna gefenshi yayi minutes zaune sannan yace"HAMEED wace gift ya kamata na bawa Zarah? "
HAMEED ya dago yana kallonshi yace"Allah ya sawwake wai anata exam kai kana ta Zara waketa wani love yanzu"
WALEED yayi tsoki yace"Tunda dama baa karatun se exam tazo ai dole kai yayi zafi da Allah ka fadamin me yakamata in bata kyauta ?"
HAMEED yace"ai itace zata baka kyauta sede idan tsaraba zakai mata"
WALEED ya girgizakai yace"Tayi candy this year sannan wannan kyautar farkoce da zan bata a matsayin masoyinta"
HAMEED yayi nazari yace"zobe ya kamata ka siya mata ka kama hannunta ka sanya mata shi kace mata will u marry me?"
WALEED yayi dariya da tsoki yace "Amma yayi kadan zan hada mata da handset"
HAMEED yace"Eh ai zata temaka"
WALEED yace"To kai me zaka bawa sahibar ka?"
Yace"Zoben alkawari"
Sukai dariya tare HAMEED yace"tafi dan Allah ina da sauran karatu da yawa wlh"
WALEED ya tashi ya koma daki ya cigaba da karatunshi,
Anata shirye_shiryen biki amma KHALEED baiyi lefe ba kaya tsadaddu ya siyo mata na cin biki amma ya cika wardrobe dinta da kananun kaya cos yafi son su shi kanshi bai saka manyan kaya kuma ya lura kananun sunfiwa Zarah dinshi kyau ,gaban mirror dinta ma cike yake da kayan makeup dasauransu,
Saura kwanaki su WALEED su gama exam ya kira muneera yana fada mata ya kusa gama exam,
Tana farinciki tace"Yaushe zaka dawo?"
Yace"cikin next week this week zamu gama exam"
Muneera tai murmushi tace"satin ake bikin daddy idan kazo da wuri zaka samu shagali"
WALEED na farinciki yace"Zan dawo mama naji dadi sosai bari na kira daddyn"ya kashe wayar ya kirashi,
KHALEED ya dauka yace"Doctor ya exam?"
Cikin shagwaba WALEED yace"Daddy shine baka fadamin ba zakai aure?"
KHALEED yayi murmushi yace"I'm very sorry saboda kar na rabama tunani shiyasa"
WALEED yace"daddy dani zaa daura aure insha Allah"
KHALEED yace"Allah ya yadda ka dage kayi karatu dai"
Su kai bankwana dokin zuwa gida ya kara kama WALEED yana jin inama su gama exam yau,
Ranar da suka gama exam su kaita murna da daukar pics na tarihi kowa na cikin dokin tafiya suka fara shirin tafiya gida,
Wanshekare
Da marece HAMEED ya fita da abokinshi WALEED ya gama shiri yana kwance yaji ana knocking ya tashi daga shi sai singlet yaje ya bude yana budewa yayi tozali da Sanjana cikin kananun kaya wandon jikinta iya kugu rigar ta matse ta breast dinta a tsaitsaye,
Hankalinshi tashe yayi saurin dauke ido tare da juyawa ranshi bace yace"Me kikazo yi anan?"
Sanjana na jin kamar tai hauka hawaye cike da idonta ta rungumeshi ta baya tana goga fuskarta da breast dinta a bayanshi tana fadin "I love u WALEED....I need u madly plss ka yarda dani" tana sauke wani irin numfashi tana kara shigewa jikinsa,
Hankalin WALEED ya gama tashi yana jin matsananciyar shaawa yayi ta maza ya hankadeta ta fadi kasa idanunta na fitar da hawaye masu zafi ,
Ya juyo yana kallonta ranshi bace yace"I will never going to love u and don't u ever think that I will share desame bed with u "ya matse lips yace"get out from my room plsss"
Tana hawaye tace"please and please just once "
Ya daka mata tsawa ta tashi ta fita dasauri tana hawaye,
Yayi tsoki ya koma kan bed ya kwanta ruf da ciki mararshi na ciwo shi kanshi yasan yayi namijin kokari rayuwa cikin turawa akwai hatsari sai kayi dagaske ka tsare kanka,
Yana kwance karar wayarshi yasa shi bude ido ya mika hannu ya dauka ya kara kunne,
KHALEED na farincikin dawowar danshi yace"Doctor yaushe zaku taso?"
Muryarshi very cool yace"2"
KHALEED yace"OK sai kun iso can't wait to see u doctor "
WALEED yayi dariya ya kashe wayar ya kara rungume pillows,
Yanajin shi some how Karfe goma jirginsu ya tashi,
Gidan Muneera cike yake da yanuwa da sukazo biki sunata hidima,
Amarya Zarah tasha gyara ta kara kyau sosai jikinta yayi fresh tunda safe KHALEED ya kaita wurin saloon da henna,
Suna isa ta kalleshi tace"Dan Allah daddy da yaya ya dawo Ka dawo Ka daukeni ko baa gama ba"
KHALEED ya lumshe ido yace "To amarya"
Ta turo lips tana dariya ta fita a motar,
KHALEED ya nufi airport yana kagare ya sanya WALEED ido yana cikin airport har jirginsu ya sauka ,WALEED na ganinshi suka rungume juna suna murna ,
KHALEED ya janye jikinshi yana kallon yadda WALEED din ya koma matashi duk da karancin shekarunsa ,
Sunata farinciki suka gaisa da HAMEED suna batun shiga mota akazo daukar HAMEED sukai bankwana ya nufi motar daddynsa,
Suna cikin mota KHALEED na driving WALEED yanata murmushi a kagare yake su isa gida yaga gimbiyar zuciyarshi yana murmushi yace"Daddy Zarah na gida?"
KHALEED yayi dariya yace"A,a na kaita wurin saloon"
WALEED yayi murmushi yana tuno kyakkyawan gashin kanta yasan zatai kyau ,suna dan fira har suka isa ya bude motar ya shiga gida yana murna ,shi kuma KHALEED ya nufi dauko Zarah bayan yayi waya akawo motar daya dade da siyawq WALEED a matsayin gift na gama school kuma dama tun kafin ya tafi ya masa alkawarin hakan,
WALEED nashiga yaga gidan cike da mata ganin haka yasa shi kama kanshi ya shige daki Muneera nata hada masa kayan tarba akafada mata ya iso ta nufi dakinshi dasauri,
Ta shiga tana murna ta sameshi tsaye yana rage kayan jikinshi zai shiga wanka don ya shirya kafin Zarah ta dawo,
tace"WALEED !!! sannu da zuwa dana"
Ya waigo yana murmushi yace "Mama ya kuke ?"
Tace"Lafiya lau ya ka dawo?"
Ya matsa wurinta yana murmushi yace"Na dawo lpy Mama"
Muneera nata kallonshi ya zabge sosai ya kara girma tace"Inacan ina hidima bansan ka shigo ba bari na kawo maka abinci "
Dasauri yace"Mama ba Saturday bane bikin naga jamaa haka?"
Tace"Friday ne shiyasa saura kwana biyu"
WALEED yayi murmushi yace "Mama wai ina daddy zai dauko amarya ne?"
Tai dariya tace"Kauye"
Yace"kauye?"yana mamaki,
Tace"Eh nan cikin gidanku amaryar take "
Fuskarshi ya mutse yace"Bangane ba?"
Tana dariya tace"to Zarah kanwarka itace amaryar"
Wani irin jiri ne ya debeshi lokaci daya yayi saurin rumtse ido ya rike kanshi zuciyarshi na wani irin tukuki kamar zatai burst ,
Muneera tai saurin matsawa gunshi ta rikeshi tace"WALEED lafiya? "
Baiyi kokarin bude ido ba yana dafe da kanshi muryarshi na rawa yace"tun a jirgi kaina ke ciwo "
Muneera tace "sannu kila har da yunwa baka tsaya kaci abincin kirki ba ,ka zauna bari na kawo maka abinci"ta juya ta fita da sauri,
Kafafun WALEED na rawa ya matsa jikin bed ya zauna dabasss yana cikin tashin hankali zuciyarshi na wani irin suya da mugun ciwo idanunshi jawur cike da hawaye bakinshi na rawa yace" Zarah !!... Daddy... meyasa zakumin haka......?"hawaye masu zafi suka fara sulalowa bisa fuskarshi .
*SHIGAR SAURI*
Painful love story
Romance special
Writing by
*MAMAN MAMY (SHALELE)*
*Wattpad@mumies122*
*Dedicated to my close friend ikra Rukayyat*
*Devoted to identical twins hassan & Husain 80k and F dimple*
*Small gift to my real fans*
*PROFICIENT WRITERS ASSOCIATION*
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/
TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09
Page > 53&54
*Muna saida kayan mata da na maza suna da kyau sosai kuma cikin sauki muna turawa koina ga me bukata seya tuntubi wannan number👉🏼 0806 672 6866*
🎈🎈🎈🎂🎂🎂🎂🎂
*HAPPY BIRTHDAY TO ME😁I WISH MY SELF A VERY BEAUTIFUL LIFE &ENDING,TODAY IS MY BIRTHDAY MUNATA KARA TSUFA DA FURFURA😅*
Wani irin juyi duniyar ke masa yana dama mafarkine Zarah da daddynsa???bai taba tunanin hakan ba,
Yana hawaye ya dora hannunsa saitin zuciyarshi yana murzawa yana jin kamar ya fasa ta ya fiddo soyayyar da yakewa Zarah yayar saboda bata amfaneshi da komi ba sai tarin nadama shi din yana son abinda daddynshi keso,
Yana hawaye yake tuno maganganun HAMEED ya dade yana bashi shawarar fada mata amma baiyi ba ,Hawaye suka cigaba da zubar masa yanaji radadi yayi dakon soyayya shekara da shekaru har yanajin bazai iya rayuwa sai da ita ba,
Ya fara tuno kulawa da dawainiya da KHALEED yayi dashi tun haihuwa har zuwa yanzu ko zamanshi turai ya tabbatar da soyayyar daddynsa garesa baya jin zai iya fadin abinda zai hana aurensa da Zarah yasan yana sonta shiyasa zai aureta bazai iya bata farinciki da jindadinshi ba saboda nashi he's his daddy,
Dago idonsa da zaiyi sama idanunsa suka sauka kan pic dinsu daddyn nashi ya dafa kafadar shi ,
Ya kure fuskar da kallo yana tunanin abubuwan alheri da yayi masa da son da yake nuna masa muryarshi na rawa yace"Why daddy...?ina matukar sonta..itace rayuwata meyasa kaimin shigar sauri.....?"
Yana cikin hakan yaji maganar Muneera bakin kofa tana cewa "Eh ku bari ya soyu sosai yayi ja"
Da saurinshi ya fara goge fuskarshi yana dedeta kanshi yayi saurin kwanciya akan bed din ya kulle ido yana hango kyakkyawar zarar shi da yadda suke kasancewa a tare a wata duniya daban me tarin jindadi,
Muneera ta bude kofar ta shigo tana kallonshi ta a jiye tray din hannunta gefen bed tace"sannu WALEED ka tashi kaci abinci kasha paracetamol "
Ya daga mata kai batare da ya bude ido ba ,
Tana jin tausayinshi ta dauko paracetamol ta ajiye gefen bed tace"Ka tashi fa ni mutane na jirana ka tabbatar kasha maganin "
Ya sake daga kai yadda zuciyarshi ke zafi yasan da yayi magana kuka zaiyi,
Ta juya ta fita tasan suna can suna jiranta yanajin rufe kofar ya fara kuka ,kuka me sauti da radadi a zuciya ,yana dafe da zuciyarshi yake fadin "Inasonki.. inasonki Zarah " Lokaci daya yayi tsitt tuno Matar daddy ce ,
Ya dafe kanshi da yayi masa wani irin nauyi saboda abubuwa da suka girmi brain dinshi yanata kuka shi kadai bame jinsa zuciyarshi na cikin azaba,
KHALEED na isa bakin saloon din ya kira Zarah angama mata styling gashi kenan ana henna,
Wata ta kara mata wayar a kunne cikin daddadar muryarta tace"Daddy na"
Yayi murmushi yace Baby..yayan ki yana gida"
Ta fara meda numfashi tana murna ta kalli kunshin ta turo lips tace"Daddy yanzu akemin kunshin bai bushe ba"
Yace"alright zan koma gida idan kingama zan dawo "
Tace"To daddyn mu"
Yayi murmushi cikin zuciyarshi yace "Da sannu zaki sauya shi" ya kara murmushi zuciyarshi na raya mishi wasu abubuwa ya tada mota ya nufi gida,
WALEED nata kuka zuciyarshi na kuna lokaci daya zazzafan zazzabi ya rufeshi jikinshi na rawa ya jawo bedsheet ya rufa yana jin dama hannun agogo ya dawo baya ace bai taba son zarah ba,
KHALEED na isowa ya shigo gidan ya nufi dakin kai tsaye yana bude kofar gabanshi ya yanke ya fadi ganin WALEED cikin bedsheet yana rawar sanyi,
Ya shiga ciki a razane ya hau gadon ya bude WALEED lips dinsa nata shaking cikin tashin hankali yace"innalillahi...... WALEED mike damunka?"
Idanun WALEED lumshe ya budesu ganin fuskar KHALEED hawaye suka ziraro masa yanajin kishi da ciwo lokaci daya ya medasu ya rufe yanajin kamar ana rura masa wuta a dukkan jikinsa,
Idanun KHALEED cike da tausayin WALEED yace"kafadami mana mike damunka?"
Bakin WALEED ya kasa fadin komi sai zuciyarshi da ta fara up and down yana wani irin nishi,
KHALEED ya wani irin razana jikinshi na rawa ya jawo wayarsa ya kira Muneera, saida tai ta ring sannan ta dauka,
Muryarshi na rawa yace"Mama WALEED..."
Gabanta na faduwa tace"Minene ya samu WALEED din? "
Hawayen tausayinsa suka zubomai yace"Mama kizo kigani WALEED bai lpy sosai..yana cikin wani hali"
Muneera ta saki wayar wayar ta sulale kasa hankalinta tashe ta nufi dakin duniya bata son abinda zai taba mata su duka biyun,
Tana shiga zuciyarta ta karye ganin KHALEED rungume da WALEED yanata nishi,
Ta kalli abincin ta ganshi yadda ta barshi ta karasa ciki dasauri idanunta cike da hawaye cikin zallar tashin hankali ta kamo WALEED din tana cewa "KHALEED mu kaishi asibity bai lafiya tun dazu"
Ita da KHALEED suka kamasa suka fito dashi gabadaya hankalinshi bai jikinshi suka sa shi a mota suka nufi asibity dashi ,
Suna zuwa aka amsheshi aka shigar dashi likitoci suka fara dubashi KHALEED ya kasa tsayawa waje yana ciki a gabanshi ake duba WALEED yanata nishi su kai masa allurai harda ta bacci suka sa masa drip ,,amma har lokacin jikinshi zau ,
Likitan ya balle botiran rigarsa ya kalli KHALEED yace"Ka samo ruwa ka rika shafawa a jikinshi da towel"
KHALEED na cikin tausayi yace"Meke damunsa doctor?"
Likitan yace"Ya samu shock ne may be akwai wani abu daya gani ko aka fadamai daya razana shi bp dinshi is high shine ya haddasa masa fever"
KHALEED ya meda kallon shi ga WALEED dake kwance yana bacci yana mamakin minene yaja mishi shock yasan ya kaishi gida to meye ya gani ko yaji da yasa shi wannan halin?
Muneera ta tashi dasauri ganin KHALEED din ya shiga duniyar tunani ta debo ruwa ta dawo ta fara kokarin zare masa riga ,
KHALEED ya kama mata ya cire rigar ya amshi robar ya saka rigar yana matsowa yana shafawa a jikinshi,
Tunanin da yake ne yasa bai ko lura da zanan star dake hannunshi ba Muneera ko ta ganta amma hankalinta baya kai ga hidima ga tashin hankali,
Suna zaune har awa guda Muneera ta kalleshi tace"KHALEED ka zauna dashi zan koma gida idan kuna bukatar wani abu ka kirani zansa a kawo zuwa gobe ko HAMEED ne sai yazo ya cigaba da kula dashi"
KHALEED yanata mata kallon mamaki ranshi badadi yace"Mama me kike cewa ne duk da WALEED bai lafiya bikin zaai?"
Zuciyarta raunane tace"Ya zaai KHALEED? an gama fadawa jamaa har sun fara taruwa sai kuma ace an daga?"
Kamar zai kuka yace"Mama dan Allah a daga auren nan har sai WALEED ya samu lafiya,mama ya zaai biki WALEED na kwance?"
Muneera ta kalli WALEED din ta meda kallo gareshi tace"kar ka damu zai samu lafiya in Allah yaso "
KHALEED yayi shiru zuciyarshi na ciwo ko kadan bayason bikin a wannan halin,
Tace"Na tafi ka kula dashi "ta juya ta fita,
Idannun KHALEED jawur yajawo hannun WALEED ya rike yana cewa" Meke damunka d'ana ? Ka fadamin banason ganinka haka"
Yana cikin haka wayarshi ta fara ring ya kasa dauka duk da yaji ring din kiran Zarah ne tai ta ring harta dauke ta kara kira ana ukkun ya jawota daga aljihu ya dauka ,
Da shagwaba Zarah tace"Daddy tundazu naketa kira kaki dauka na gama tundazu "
Ya yamutsa fuska murya sanyaye yace" OK zan kira driver ya daukoki"
Tace"Driver? Dan Allah daddy kazo"
Ya kalli WALEED yace"Ina asibity"
Gabanta ya mugun faduwa tace"Asibity?"
Yace"Eh WALEED baya lafiya"
Hawaye suka cika mata ido tace"Innalillahi wainna ilaihi rajiun meyasa mesa daddy?"
Yace"Bai lafiya Zarah zan kira drivern"ya kashe wayar yana kara kallon WALEED dake kwance idanunshi suka kai wurin zanan star din hannunshi ya kalleta yana ganin shirmensu ne ya dauke idonsa ,
Yayi dialing no din driver ya fadamai inda zarar take ya kashe,
Tunda ya fadawa Zarah ta shiga damuwa domin tana son WALEED dukda rashin sakin fuskarshi yana kula daita kuma tana son duk abinda KHALEED keso dole ta damu da WALEED domin tasan yafi sonshi fiye da shi kanshi,
Driver na zuwa ya dauketa zuwa gida ta shiga dasauri hankalinta tashe taje wurin Muneera idanunta jawur tace"Mama a wace asibiti aka kai yaya?"
Muneera na sukuku tace"Khairat...."
Ta juya dasauri ta koma wurin mota driver ya dauketa har asibitin ta shiga dakin tana kallon gadon ta karasa tai tsaye baki ta kure WALEED da kallo yana kwance kamar me lafiya amma ga drip na shiga jikinshi ta juya ta kalli KHALEED yayi sukuku hankalinsa na kan gadon tana jin tausayinshi taje ta zauna kasa kusa dashi ta dora kanta akan kafafunshi kamar zatai kuka tace"Sorry daddy zai samu lafiya"
KHALEED ya kalli kanta gashin nan zube har baya yasha gyara ga kunshi tayi matukar kyau daka ganta kaga Amarya ,ya dora hannu kanta yace"Na sani kiyi hakuri karkiyi kuka"
Ta dago tace"Daddy meyasa meshi ?"
Ya matse lips yace"I don't really know but lafiya lau na daukoshi daga airport "
Zarah ta meda kanta ta kwantar jikinshi tace"Zai samu lafiya Daddy "
Yayi shiru yana tunanin maganar doctor ya kagara ya farko yaji me yasa meshi,
Suna zaune sunata kallonshi har azahar su kai sallah anan Muneera ta aiko musu da abinci ko kallonshi ba suyi ba ,
Shi ko HAMEED ya koma gida kowa na farincikin dawowarshi an shiryamai liyafa ya zauna ya cika cikinshi sannan ya kwanta bacci sai kiran laasar ya tashi yayo sallah ya dawo ya shiga wanka don zuwa wurin sahibarshi husna ,bayan ya gama shiri ya dauki gift dinta na zobe yasa aljihu ya fito ya shiga mota ya nufi gidansu WALEED domin ya masa rakiya ,
Karfe 5 da mintoci ya isa ya daga waya ya kirashi taita ring bai dauka ba yayi ta kira ba respond yayi tsoki ya meda wayar aljihu ya rufe motarshi ya nufi gate din ya bude ya shiga kai tsaye,
Cikin harabar gidan yara nata wasa ya kallesu ya nufi bakin kofar main Palo dinsu ya fara knocking ,
Ba jimawa wata bafulata tazo ta bude kallo daya ya mata ya gane daga kauye take yace mata "Mama na nan?"
Tace"Eh shigo"ya shiga ya zauna yana ganin yadda aketa hidima gabanshi ya fadi ganin Fulani birjik yana tunani barkatai Muneera ta shigo falon jikinta sanyaye tana dan murmushi tace"HAMEED ne sannu ku da dawowa"
Yana murmushi yace "yawwa mama ya muka sameku?"
Tace"Lafiya lau"
Yace"inata kiran WALEED shiru bai dauka ba shine nace bari na shigo har mu gaisa"
Tai karamin murmushi tace "Aiko WALEED yana asibity bai lafiya tunda ya dawo ciwon kai da zazzabi baisan inda kanshi yake ba muka kaishi asibity"
Hankalin HAMEED tashe yace"wata asibity Mama? "
Ta fadamai yayi wuff ya mike hankalinshi tashe ko bankwana bai mata ba ya fita da saurinsa ya shiga mota ya nufi asibitin yana tunani wato bikin Zarah ake idan ya fahimta ,zuciyarshi na ciwo yace to dawa? Ya girgizakai yana fitar da iska a ganinshi Zarah bata dace da kowa ba sai amininshi domin shine masoyinta na gaskiya da yayi dakon soyayyarta na tsawon shekaru,
Mintoci kadan ya isa asibitin ya fita ya nufi ciki yana tambaya aka nuna mai dakin ya tura ya shiga da shigarshi abinda ya gani yasa kanshi ya fara ciwo gabanshi ya kara tsananta bugawa Zarah kwance jikin KHALEED ,
Dakyar ya kakaro sallama ya shiga ciki yadan tsaya yana kallon WALEED din yana jin matsanancin tausayinshi ya kalli KHALEED yace"Daddy yame jiki?"domin baida bukatar tambayar meya sameshi,
KHALEED yace"dasauki sosai"
Yace"Allah ya bashi lpy "ya ja kujera ya zauna yana kallon WALEED kanshi ya daure ya rasa taya hakan ya faru gabadaya ya mance da akwai inda yayi shirin zuwa saboda tashin hankali,
Suna zaune har bayan ishai Muneera ta shigo dakin ita da Ladingo da wata mata suna dauke da abinci,
Muneera ta zauna bakin gadon tana kallon fuskar WALEED da tausayi ta kalli KHALEED idanunshi duk sun fada saboda tashin hankali,
Tace" KHALEED ka daure kaci abinci ko kadanne"
Yace"To"
Ta kalli Zarah tace "Ki tashi mu tafi gida ki huta"
Zarah ta girgizakai tace"Anan zan kwana"
Muneera tace "a ina?kinga wurin kwana anan ne?Ki tashi mu tafi"
Zarah ta turo baki kamar zatai kuka ta kalli KHALEED,
Ya daga mata kai yace"Gobe saiki dawo"
Ba musu ta mike tana kallon KHALEED din idanunta cike da hawaye suka juya suka fita,
HAMEED na zaune yana ta kallon ikon Allah yanajin haushi da kishin zarar sai like ma KHALEED take WALEED ya kamata taiwa haka ba KHALEED ba,
Bayan sun fita KHALEED ya kalli HAMEED yace"kaima ka tashi ka tafi dare nayi"
Ya mike tsaye yana kallon WALEED so kawai yake ya farfado suyi magana bayadda zaiyi ya juya ya tafi,
KHALEED ya kara matsawa jikin gadon ya taba kanshi yaji da zafin haryanzu ya taba wuyanshi yaji dasauki,
Yana dauke hannunsa WALEED ya bude idanunsa dake jawur yana kallonshi ,
KHALEED ya rikeshi yana jin tausayinshi yace "sannu son Allah ya baka lpy sannu"
WALEED ya kalli fuskar KHALEED ya juyar da kai gefe hawaye suka gangaro masa,
Muryar KHALEED raunane yace"Meke damunka WALEED? Don Allah ka fadamin abinda ya daga maka hankali har ka shiga wannan halin"
Zuciyarshi kamar zata fito ya daure ya juyo da fuska yana kallonshi yace"Daddy yarinyar da nakeso aka kirani akafadamin an mata aure last week"
Gaban KHALEED ya yanke ya fadi yayi shiru yanajin tausayin shi a hankali yace"Kayi hakuri WALEED ba haka naso ba naso ka mallaki duk abinda kakeso da ace ba a daura mata aure ba yau ina iya nemar maka aurenta,amma an riga an daura kayi hakuri ka manta daita Allah zai baka wacce ta fita"
WALEED ya fashe da kuka hawaye na zuba a idonshi kamar fanfo yace"Na manta da ita daddy dole nai hakan saboda bai kamaceni ba"
KHALEED na jin tausayinshi ya rungume shi yana jin kamar ya tayashi kukan sai da ya fara son Zarah yasan ya so yake akwai radadi sosai rasa masoyi,
Ya nata rarrashin shi sannan ya kamashi yayi sallah ya dan bashi abu me sanyi yasha kadan don KHALEED din yaji dadi yasha drugs ya kwanta ,
Ya rumtse idonshi fuskar Zarah murmushinta da kyawawan moments suna haskawa aciki cikin zuciyarsa ya fara addua "Allah ka mantar dani ita da duk wani abu daya danganceta"
KHALEED na zaune yana gadinshi yana jin ciwon halin da yake ciki,
Dukkansu basuyi barci ba HAMEED ma tunda ya koma komi yakasa sawa bakinsa tunani kawai yake,
Washe gari
Ana sallar asuba HAMEED ya nufo asibitin a kagare yake WALEED ya farfado suyi magana,
Gari ya dan fara haske ya shiga asibitin,
KHALEED na zaune yana fuskantar alkibla yana lazimi ya waigo ya kalleshi yace"HAMEED tun yanzu? "
HAMEED yayi shiru yana kallon WALEED dake kwance kamar yana bacci amma idanshi biyu tunani kawai yake,
Ya meda kallo gun KHALEED yace"Daddy wlh banyi bacci ba nakasa natsuwa"
KHALEED yayi gajeren murmushi yace"Ka karaso ka Zauna ai da sauki sosai "
HAMEED yaje ya zauna yana kallon WALEED din ,
KHALEED ya tashi yace"ka zauna dashi zanje gida na dauko masa kayan sakawa kafin garin ya karasa wayewa"
HAMEED ya gyada kai dasauri dama abinda yakeso kenan,
KHALEED na fita ya matsa ya fara tapping WALEED yana kiran sunanshi,
WALEED ya bude ido ya kalleshi ,
HAMEED yace "Kasan dai yadda kakeson Zarah karka yadda daddy ya kwaceta kafada mishi kana sonta nasan zai bar maka ita"
WALEED yayi murmushi me ciwo hawaye suka taru a idonshi yace"Gobene bikinsu bai kamata nayi hakan ba nasan duk suna son junansu fadin abinda ke zuciyata zai rushe farincikin kowa"
HAMEED yace"kana nufin shiru zakai har ya aureta kana ji kana gani?"
Ya daga kai yace"HAMEED daddy yamin komi shine ya tarbiyyantar da rayuwata har zuwa yau yana komi don farincikina Niko mena taba yi masa a rayuwa?shine kullum ke bakin kokarinsa a kaina amma ban taba sadaukar da komi don shi ba ,na barmishi Zarah kuma ta dace dashi sosai "
HAMEED na jin haushi yace"Kana tunanin zaka iya fiddata a ranka ne? Gashi lokaci daya ka fita hayyacinka saboda rashinta? " ya juyar da kai yace"kar kai ganganci da rayuwarka WALEED"
WALEED yanajin ciwo a heart dinshi yace"zan iya kome soyayyar daddy ba kamar ta ta bace zan iya barwa daddy komai harta zuciyata "
HAMEED yace"to shikenan zanje na fada mishi gaskiya idan baka damu da kanka ba ni na damu da kai"
WALEED ya riko hannunshi yana girgiza kai yace"karkamin haka karka bata farincikin mutane da yawa sabida nawa Zarah tana son daddy sosai ko da daddy ya barmin ita ba zata soni ba kayi shiru dan Allah "
HAMEED ya janye hannunshi yayi tsoki,
murya sanyaye WALEED yace"Nazata ko masoyiyarka ce zaka iya barwa daddy yadda kakeson shi to bare kuma ni danshi"ya karasa cikin kunar zuciya,
Dede lokacin KHALEED ya shigo dakin sukai shiru WALEED ya goge hawayenshi a fakaice ya tashi zaune ,
KHALEED na kallonsu yaji suna magana da zai shigo amma bai fahimci komi ba ya kalli WALEED yace"Shiyasa na dawo nasan yanzu ka farka muje kai wanka"
WALEED yayi karamin murmushi yace"Na warke daddy zan iya "
KHALEED yace"anya?"
Ya daga masa kai ya karasa sauka da kyar ya nufi toilet,
HAMEED na zaune ya rasa yadda zaiyi ,KHALEED yace masa ya hada tea yasha ba don yanaso ba ya hada yasha ya ajiye cup din,
WALEED yayi wanka cikin dauriya amma zuciyarshi nata zafi ya fito yayi sallah KHALEED ya bashi abinci ya fara danci,
Yana cikin bashi Zarah ta shigo WALEED ya kureta da kallo ta nata sheki ta masa mugun kyau ,
Ganin kallon da yake mata yasa HAMEED fadin "Hmm" ciki_ciki,
Ta karaso tana dan murmushi ta zauna kan bed din tace"Yaya ya jikin ?"
Yayi dan murmushi yace"Dasauki"
Tace"Sannu yaya Allah yabaka lpy "
Yace"ameen"
Ta meda kallonta gun KHALEED ta wani turo lips da shagwaba tace"daddy Shine inata cewa ka jira nai wanka mu taho amma ka ki"
KHALEED yayi murmushi yace"To bagashi kinzo ba amma naga ko mai baki shafa ba"
Tai dariya tana mishi kallon love,
WALEED ji yake kamar yabar dakin yadda yakejin kamar ana watsa mai ruwa tafasassu ya daure yana zaune ko kwanciya bai yi ba,
Karfe 9 likita ya shigo dubashi ya aunashi ya kalli KHALEED yace"Ya ci abinci?"
KHALEED yace"eh yaci"
Likitan ya kalli WALEED yace"sannu"ya juya zai fita,
WALEED yace "doctor ka sallameni naji sauki"yanajin idan ya cigaba da kallon irin haka zuciyarshi zata buga
Likitan ya waigo yana murmushi yace "To amma kadan kara warkewa kadan "ya karasa fita,
KHALEED na jindadi yana ganin saukine yace" patient amfara samun sauki'
Sukayi murmushi tare WALEED ya koma ya jingina da pillow yana jin kanshi kamar zai rabe,
Wurin 10 Muneera tazo asibitin WALEED ya daure ya kara yin kwari_kwari,ta gama dubashi ta kama hannun Zarah tace"Mu tafi innarki na nemanki zaku tafi gidan maman farouk"
Zarah ta bata fuska tace"Dan Allah daddy kasa baki wankan lalle zasu min "
KHALEED yayi murmushi ya kalli Muneera yace"Mama duk wannan Jan da tayi dan Allah a temaka"
Muneera ta harareshi ta kalli Zarah tace"Mu tafi anfasa wankan lallen"ta karasa da dariya fuskarta,
Zarah tai dariya ta shige jikin Muneera suka fita,
KHALEED ya bita da kallo shagwabarta na kara sa mishi mugun so da shaawarta,
Ya dauke idonshi ya tashi ya shiga toilet zaiyi wanka,
HAMEED ya kalli WALEED da idanunsa ke rufe hannayenshi a dumtse yanata cijewa,
yace"Tunda haka kace shikenan na tafi"
WALEED ya bude ido cikin karfin hali yayi murmushi yace "sai mun hadu daurin aure"
HAMEED ya kalleshi ya juya ya fita,
A nata shirin daurin aure gobe baki nata zuwa gidan ya cika da mutane maza da mata,
Wanshekare tun asuba KHALEED yabar asibitin ya tafi suna shirye_shirye da abokan aikinsa,
Yabar WALEED tare da HAMEED ,HAMEED nata fadawa WALEED ya fada masa shi kuwa ya kafe ,
Har 12 WALEED ya tashi tsaye ya kalli HAMEED yace"Tashi mu tafi mu shirya "
HAMEED na jin haushinsa yace"Ina zakaje?"
Yace"Daurin auren daddy dole na samu halarta tunda hankalina na jikina"
HAMEED yace"Allah ya kiyaye to"yana ganin wasa yake sai gani yayi ya nufi kofa ya tashi ya bishi dasauri,
Shi ya kaishi har kofar gida yana jinjina dauriyarshi da hakurinsa sannan ya juya ya tafi,
WALEED ya shiga gidan Muneera na ganinshi tace"Patient ya ka baro asibitin?"
WALEED yayi murmushi yace"An sallameni"ya wuce dakinshi,
Muneera taji wata irin natsuwa ta cigaba da hidima hankali kwance,
WALEED na shiga dakinsu ya samu KHALEED ya fiddo kayan daurin aurensa yana zaune ya kurawa pic dinshi da Zarah ido yana matukar farinciki yau zai mallaketa,
Motsin shi yasa KHALEED dagowa yana ganin WALEED ya ajiye wayar yana murmushin jindadi yace"Ya haka?"
WALEED yace"Daddy daurin aure zanje na samu lafiya "
KHALEED ya sake murmushi ya tashi ya bude wardrobe ya fiddo wasu manyan kaya yace"Kaga ko dama nai maka dinkin daurin auren"
WALEED ya amsa zuciyarshi na zafi ya bude kayan farare tass sunsha aiki black ya kalleshi yana murmushi me ciwo yace "Nagode sosai daddy "
KHALEED yace"OK bari naje na shirya mu fita da wuri "ya juya ya shiga toilet,
WALEED ya rike kayan yana musu wani irin kallo ya ajiye su a hankali ya karasa wurin trolley dinshi ya fiddo tsarabar da yawa Zarah ta zobe yana hawaye ya jefashi a dustbin ya fiddo turaren daya siyawa KHALEED ya ajiye,
KHALEED na fitowa wanka ya shiga yayo yana fitowa yaganshi cikin fararen kaya da black hula yayi matukar kyau ya dauki turaren ya feffesa masa yana murmushi yace" Daddy kayi kyau"
KHALEED na kallonshi da murmushi yace "thanks"
WALEED yayi sauri ya shirya suka fita tare,
Zarah na gidan maman farouk ta kara dilketa ta dafa wasu dakwalen kaji masu kara taste sunji kayan hadi ta bata hade da wasu tsumi masu sanya mace leaking,
Zarah na jin son KHALEED tana son farincikinshi ta dage ta shigar dasu duka ,bayannan tai wanka akai mata makeup da ta kara mata kyau ta saka doguwar rigar maroon lace tayi kyau sosai kamar ka sace akai mata wankan turare ,su ka fara selfie da friends,
*Karfe 2:30* tarin jamaar dake masallacin suka sheda auren *KHALEED Ibraheem* da amaryasa *Zarah Shehu*
KHALEED murmushi kawai yake yanajin dadi ko ta ina yasan cewa yayi dace yayi dacen mace mai kyau da komi,
WALEED ko yana jin an daura ya fara ganin bibbiyu zuciyarshi na matsanancin ciwo,
Suna zaune wuri daya da HAMEED ya rike masa hannu yace"HAMEED Mu tafi gida bani lafiya"
HAMEED dake sukuku yasha babbar Riga milk shima ya tashi da sauri hannunsu ya rike hannunsa suka fita ya sashi mota ya dauki hanyar gidansu yana driving yana kallonshi da matsanancin tausayi.
Ayyiriri 😂an daura KHALEED and Zarah kowane hali WALEED zai shiga? Karde HAMEED yaje ya fasa kwan😅runguntsumi kenan🤣
Muje de zuwa
*SHIGAR SAURI*
Painful love story
Romance special
Writing by
*MAMAN MAMY (SHALELE)*
*Wattpad@mumies122*
*Dedicated to my close friend ikra Rukayyat*
*Devoted to identical twins hassan & Husain 80k and u Fatima dimple*
*Small gift to my real fans*
*PROFICIENT WRITERS ASSOCIATION*
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/
TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09
Page > 55&56
*Muna saida kayan mata da na maza suna da kyau sosai kuma cikin sauki muna turawa koina ga me bukata seya tuntubi wannan number👉🏼 0806 672 6866*
*Godiya nake masoyan SHALELE da kukamin wish da adduoi da comments Allah yabar kauna*
Cikin zuciyar WALEED kamar ana zuba masa ruwan zafi saboda yadda take tsananin ciwo idanunshi lumshe hannunsa akan heart dinshi,
HAMEED na driving yace "Sannu WALEED ko asibitin zamu wuce?"
WALEED ya girgiza masa kai yace"Mu tafi gida zan samu sauki"
HAMEED yayi shiru yana kallonshi yasan dama dole yasha wahala kafin ya cire son Zarah a zuciyarshi ,amma yana tausaya masa kafin wannan lokacin zaisha wuya idan ya samu yin hakan kenan,
Suna isa gidan ya bude masa ya rikeshi har dakinshi ya temaka masa ya kwanta a bed ya zauna kusa dashi yace"Sannu"
WALEED ya daga masa kai, ya taba jikinshi yaji zazzabin harya dawo ya tashi ya fita ,asibitin ya koma ya dauko drugs dinshi da wasu kayan ya biya pharmacy ya kara sawo masa wasu da zasu temaka ya dawo ya sameshi yadda ya barshi ,
Yana jin tausayinshi ya tada shi yasha drugs din sannan ya koma ya kwanta hawaye suka gangaro masa ta gefen idanu na tausayin kanshi so yake ya cireta a cikin zuciyarsa amma dukda an daura masu aure baiji wani abu ya rage ba saima karuwa da yakejin sonta na yi,
HAMEED na zaune ya rafka tagumi yanata kallonshi domin yanzu baida temakon da zai masa aikin gama ya riga ya gama,
Bangaren ango KHALEED ko sunsha pics da walima sannan suka bar masallacin yana cikin farinciki,
Zarah ta sauya kaya zuwa lace black da red flowers jiki tayi matukar kyau maman farouk ta dauketa suka koma gida don yau zaa kaita gidanta,
Bayan sun isa ta fito daita tana rufe da white mayafi suka shiga ciki Ladingo ta kaita wurin kawu domin ya mata huduba kafin a kaita gidanta,
Kawu habu na dakin waje shi da wasu tana zukunne gabanshi kanta sunkuye cikin mayafi yana kallonta cikin lallausar murya yace"Zarah yau Allah yakawo mu ranar da zaki tafi gidan mijinki abinda zance da farko shine ki godewa Allah dayasa kika kasance cikin wannan ahalin mutane masu mutunci da tausayi da karrama dan'adam ko da sun fishi, kiyi kokari sosai wurin yiwa mijinki biyayya ki sani ya miki dukkan alheri nan cikin duniya ba abinda zaki iya saka mishi dashi ki dage da bautar ubangiji karki gajiya da hakan domin samun aljanna, muna maku fatan zaman lpy da zuria ta gari"
Zarah na cikin mayafi tana hawaye abubuwan da suka faru baya suna dawowa a zuciyarta tabbas Kawu yayi gaskiya domin batada abinda zata biya KHALEED dashi shine ya ceto rayuwarta ya gyara ma mahaifinta suna kuma ya kwato mata dukiyarta ,
Tana hawaye mazan dake wurin su kaita mata addua Ladingo ta dauketa suka shiga wurin Muneera daita ,suna zuwa ta rungume Muneera tana kuka tana jinta tamkar uwarta data zukunna ta haifeta,
Muneera tai murmushi idanunta na kawo ruwa ta janyeta a jikinta ta dago fuskarta tana share mata hawaye take cewa"Zarah miye na kuka?ba wani wuri zaki tafi ba kina tare damu kiyi hakuri ki dena bata kwalliyarki"
Zarah tai shiru tana ajiyar heart,
Muneera na murmushi tace"Ki kwantar da hankalinki Zarah ina miki albishir da samun gwarzon namiji domin KHALEED jarumi ne me kwazo ta kowane fanni yana kula da duk na kusa dashi nasan zaya kula min dake sosai,kema nasanki da hakuri da biyayya ki cigaba da hakan sannan ki kula da mijinki sosai kisan matsayinshi a yanzu yawuce nada ki bishi sau da kafa ki bashi duk wani hakkinshi ki kula da duk abinda yake so da Wanda bayaso ki kula da walwalarshi da damuwarshi a lokacin daya shiga damuwa kiyi bakin kokarin ki ki kwantar masa da hankali ki zama jajirtacciya wurin karfafa masa gwiwa da bashi gudummuwa ta kowane fanni"
Zarah na sabbin hawaye take jijjiga kai,
Muneera tai murmushi tace"Lastly ki kula da bukatunshi ki zama cikin shiri da dokinsa koda wane lokaci ,gyaran jiki kamshi da kwalliya su kasance koda yaushe tare da ke"
Zarah nata jijjiga kai Muneera tace"Allah ya muku albarka ya baku zaman lpy ya kaimu lokacin da zan Goya jikokina"
Su Ladingo sukai murmushi ,Muneera ta tashi ta basu wuri,
Ladingo ta zauna tana kallonta tace"Fatan bazaki bamu kunya ba Zarah inaso ki dauki duk shawaran da aka baki idan wani abu ya shige miki duhu ki tambayi Mamanki domin ita ba surukarki bace Uwa ce nasan ko yar data haifa iya kulawar da zatai da ita kenan "
Zarah ta kara jinjina kai tana jin son su Muneera da kyakkyawan mijinta ta kowane fanni wato.. KHALEED,
Suka sata tayo wanka ta sauya kaya jikinta brown din atamfa da yellow aciki tai salla aka sake mata make Up,
Wurin karfe biyar motocin kai amarya suka zo aka dauketa zuwa dakinta tana ta kuka,
Fulanin nan na zuwa sukaga tsarin gidan su kaita buga kauyanci itako tana takure kan gado tana jin wani nauyi akanta ,
Ba jimawa da kaita kulolin abinci da drinks da kajivda snacks suka fara isowa sukaci suka koshi sukai hani an😹suka fito tsakar gida suka fara kidan kwarya suna dansewa,
Bayan komi ya lafane KHALEED daketa son kiran WALEED ya kira HAMEED,Ya dauka ya kara a kunne,
KHALEED yace"Ina WALEED kuna tare?"
Yace"Eh muna nan gida inajin anan ma zamu kwana"
KHALEED yace"To bashi wayar nasan tashi na asibiti"
HAMEED yace"Na dauko masa ita amma bacci yake"
KHALEED yace"Bacci yanzu da marece? Kode ciwon ne ya tashi? ganinan zuwa "
Ranshi badadi ya shiga mota ya nufi gidansu HAMEED din,
WALEED dake jin duk abinda suke fada yayi saurin tashi zaune cikin karfin hali ya mike ya fada toilet yayo wanka duk don yaji karfi_karfi ya fito ya meda kayansa ya zauna yanata lumshe ido yana budewa don su rage ja,
Bai dade da fitowa ba KHALEED ya karaso bakin gate din ya kira wayar HAMEED,
HAMEED nata kallonshi WALEED ya mike ya fita yana kakaro murmushi,
KHALEED na hangoshi da murmushi fuskarshi ranshi yayi sanyi ya karaso yana murmushin dole yace"Daddy ango"
KHALEED yayi murmushi yace "Lafiya inata nemanka banganka ba?"
Yace"Wlh daddy bacci ya kwasheni bandade da farkawa ba ma "
KHALEED ya kalli idanunshi da sukayi ja yace"Ka tabbatar lpyarka lau? "
Ya jinjina kai ,
Yace"To shikenan ka koma ka huta idan kaji jikin badadi kayi saurin kirana"
Ya daga kai yace"Thanks u daddy"
KHALEED ya masa murmushi ya koma cikin mota ya tada ya tafi,
WALEED na komawa ya sheme kan bed zuciyarshi na ciwo yana hawaye wani irin kishi ne da tsoro cike da zuciyarshi,
Washe gari,,,
Tunda asuba yan kai amarya suka fara shirin barin garin don yau zasu koma,
Zarah na zaune idanunta duk sun fada tana ta kallonsu,suka gama shiri suna kallonta sukace"Zarah mun tafi aita hakuri da biyayya a zauna lafiya"
Zarah ta rungume Ladingo tana kuka sosai dakyar Ladingo ta samu tai shiru suka tafi,tai zaune falo tana kallon gidan tana hawaye ,
Suna zuwa gidan muneera sukai bankwana KHALEED da kanshi yayita kaisu tasha daga karshe ya basu 50k kudin mota ya koma gida,
Ya shigo ya samu Muneera da wasu dangin kauye ya wuce dakinshi ya shiga wanka ya fito ya meda kananun kayanshi dama yanata jinshi ta kure a manyan ,ya zauna kan bed zai kira wayar Zarah tun jiya rabonshi daita,
Muneera ta turo dakin ta shigo tana murmushi tace "Ango ya gajiya?"
Ya sunkuyar da kanshi yana jin kunya,
Muneera ta zauna gefenshi tace"KHALEED nasan kana son Zarah kuma zakai bakin kokarinka wurin kula daita amma duk da haka ina rokon ka ka kula daita sosai iyayenta sun bamu amana domin suna ganin zamu iya don Allah karka bari ta shiga damuwa ko kunci koda na second's kayi iya kokarinka wurin sata farinciki da bata kulawar data dace"
Jikinshi sanyaye ya daga kai yana jin son Zarah yasan bazai iya barinta cikin damuwa ba ko a wane hali,
Muneera tace "Kuma ka kula da hakkinta ka sauke duk wani hakkinta dake kanka ka tabbatar tana samun natsuwa da kai ka zama tamkar abokinta domin Zarah yarinyace tana bukatar duk Wadannan"
Yanajin kunya da nauyi ya daga kai yace"Insha Allah Mama "
Fuskarta sake tace"A kullum ina kara alfahari da kai kuma bazan dena ba ,Allah yabaku zuria ta gari ina fatan nan da months afara haifamin yara"
Maganar ta girmeshi ya kara dukar da kai yana murmushi,
Tana murmusawa tace"Ka tashi kaje gareta nasan tana can ita kadai maybe ma tana sharar kuka"
Ya mike tsaye yana kagare yabar wurin da sauri yace"Sai da safe"
Tana dariya tace"Tun yanzu?to Allah yakaimu"
Ya fita yana murmushi da jin kunya ya nufi gidanshi wurin sahibarshi matarshi Zarah,
Yana zuwa ya bude gate ya shigar da motarshi ya nufi ciki yana cikin zumudin sanyata idanunshi,
Tana zaune taji karar motar amma batai wani motsi ba harya shigo ya sameta zaune ta na hawaye,
Yayi murmushi ya karasa wurinta ya zauna gaf daita yana mata wani sassanyan kallo me kashe jiki yana kare mata kallo tana sanye da dark purple material lace riga da siket sun mata ciff tai kyau tana ta fidda kamshi medadi sanyaya zuciya,
Baice mata komi ba sai da ya fara daukarta yayi mata mazauni a cinyarsa yana kallon fuskarta yace"Baby why are u crying? "
Ta dan dago ta kalleshi ta kara fasa wani kukan ta shige jikinshi kyawawan breast dinta suka sauka a jikinshi ya lumshe ido ya bude yana jin wani irin feelings,
A hankali ya dauki hannunsa ya dora akan bayanta yana shafawa a sannu cikin cool voice yace"Baby kidena kuka banason ganin hawayenki "
Ta danyi shiru tana ajiyar heart ,ya kwantar da kanshi jikin nata dake jikinshi yace"Me kikewa kuka?"
Muryarta na daukewa tace"Ina missing Mama"
Yayi murmushi ya dagota yace"Duk don Mama kike kukannan?lalle anfi son Mama dani"
Ta turo baki tana kallon hannuwanta,
Yayi murmushi yace "OK Shikenan kidena kuka Mama na kusa dake ko bakije ba ita zata zo tana kewarki"
Ya karasa da dago hannunta yana kallon kunshin daya matukar yin kyau yace"Wow haka kikayi kyau sosai ban kula ba?"
Ta sunkuyar da kanta tana dan murmushi ya janye gyalen dake jikinta gashinta yanata salki da kamshi yace"Masha Allah matata kyakkyawace kai na more"
Tana jin nauyin kalamansa ta meda kanta a kirjinshi ta kwanta tana dan murmushi,
A hankali ya kai bakinsa kai ya manna mata kiss ya cigaba da shafar hannuwanta wani abu na masa yawo koina,
Sun dau mintuna haka sannan a hankali ya jata cikin bedroom suna isa ya kalleta yana kara yaba surarta yace"Baby kije ki alwala"
Bata kalleshi bama ta nufi toilet tana tsorace ,ya fita yayo alwala,
Zarah na shiga ta zukunna tsarki taga alamun jini na tafe ta danyi murmushi tana jindadi a hankali kuma ya gushe tuno Daddy bazaiji dadi ba,jikinta sanyaye tai tsarki ta fito ta zauna bakin gado tana cikin damuwa,
Ya shigo dakin yana kallonta duk ta takure yace "Baby ki tashi muyi sallah"
Kanta kasa Tace"Ai..on ne yazo"
KHALEED na cike da dokin kasancewa daita jin abinda tace yasa jikinshi sanyi ya nufeta ya zauna kusa da ita yana kallonta cikin zolaya yace"Idan kintashi napkin ki bude wardrobe akwai komi aciki"
Ta dan kalleshi ta meda kai kasa tana murmushi jin yace napkin,
Ya tashi ya shinfida carpet yayi sallar walha yanata adduar samun zuria nan kusa badon komi ba sai don farincikin Mamarshi,
Bayan ya gama ya hangeta kwance gefen bed idanunta lumshe ,
Ya tashi ya dauketa ya medata kan gadon ta bude ido tana kallonshi,
Yayi murmushi yace "Kiyi baccinki Ni zan fita anjima zan dawo"
Ta bata fuska kamar zatai kuka tace"Daddy don Allah karka tafi"
Ya koma ya zauna yana kallonta ta meda ido ta lumshe tana son yin bacci,
KHALEED ya rika bin jikinta da kallo yanajin wani abu na tsarga masa a hankali ya kwanta yana karewa fuskarta kallo cute lips dinta na janshi kamar yayi kissing dinsu,
Ya sauke idonshi kan breast dinta marassa girma da suke tsaye ya lumshe ido yanajin desire da son tabasu ya kai hannunsa kai yaji wani soft da dadi dabe taba jiba ya fara shafawa a sannu,
Zarah na jin hannunsa akai ta dan bude idonta kadan tana kallonshi taga wai shine ? ta ganshi idonshi lumshe hannunsa akan breast din ta meda idonta ta kulle tana jin feeling na taso mata ,
A hankali ya fara matsa su yanajin mugun dadi daya zarta tunaninsa ya karasa dora dayan hannunsa kan dayan ya cigaba da matsawa yana kara lumshe ido...
Kuyi hakuri da wanga fita zanyi , tnx
*SHIGAR SAURI*
Painful love story
Romance special
Writing by
*MAMAN MAMY (SHALELE)*
*Wattpad@mumies122*
*Dedicated to my close friend ikra Rukayyat*
*Devoted to identical twins hassan & Husain 80k*
*Small gift to my real fans*
*PROFICIENT WRITERS ASSOCIATION*
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/
TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09
Page > 59&60
*Muna saida kayan mata da na maza suna da kyau sosai kuma cikin sauki muna turawa koina ga me bukata seya tuntubi wannan number👉🏼 0806 672 6866*
Ta gama sallar tai adduoi tana fatan samun zuria ta gari da zaman lpy da mijinta ta tashi ta dan gyara jikinta ta nufi falo,
Tana shiga kamshin jikinta ya gauraye falon ya lumshe ido ya bude yana kallon yadda take tahowa kusa dashi a tsanake,
Ta karaso ta dauki wayarta ta zauna gab dashi tana latsawa ,
Yanata binta da mayen kallo yanajin shaawarta na fizgarshi ya tashi zaune yana bin jikinta da kallo idanunsa sun koma wata kalar daban ya kai bakinsa jikinta yana kara shakar sassanyar kamshinta,
Zarah ta dan kalleshi tai murmushi ya bude idonsa yana kallon lips dinta, da yaso hakurin dare amma sam bazai iya ba yana ganin yana da isashshen lokacin da zaiyi komi har ya samu sallar Maghreb a hankali yace"Baby...!!!!"
Tace"Naam" tana kallon fuskarshi,
A hankali yace "Kinfara sallah?"
Gabanta ya fadi tana jin tsoro ta daga masa kai tare da sunkuyar dashi,
Ya saki murmushi yace"Ya kamata muyi sallah da kowane maaurata sukeyi bayan aurensu"
Tace"To"jikinta sanyaye ta mike tsaye,
Ya tashi ya riketa yana kallon ta yace"Feel free"
Ta kalleshi ya kama hannunta suka shiga ciki yayo alwala ta shiga tayi ya jasu sallah bayan sun gama ya mata addua suka karayin adduoi sosai suka shafa,
Yana shafawa wani sanyi ya ziyarci zuciyarshi ya fara binta da kallon so yana jin kaunarta da son kasancewa daita,
Gabanta nata faduwa tana jin tsoronshi ya tashi tsaye ya nufi bed ya fara cire kayansa ,
Tana zaune kanta kasa batasan me yake ba ta tashi ta yaye gyalen kanta tana daga idanu ta saukesu kan white skin dinshi daga shi sai boxer yana mata wani kallo da ta gama karantar ko na miye,
Gabanta na fat_ fat ta nufi wardrobe da niyyar ajiye gyalenta bai bari ta isa ba ya jawota jikinshi ta kara shan jinin jikinta, a hankali ya fara cire kayan jikinta cikin salo me kashe jiki,
Suna tsaye ya gama zare kayan jikinta ya fara bin jikinta yana shafawa yana sauke numfashi lokaci daya ya dauketa ya dora kan bed ya fara tsotse kowace gaba ta jikinta ba kamar breast dinta da sukafi rikita shi ,
A sannu take sauke numfashi bata enjoying abun sam saboda tsoro da take ciki,
Ya cigaba da romancing dinta yana rikita mata lissafi yana jin mugun dadi cikin kwancewar brain ya hau kanta ya fara neman hanyar shiga bahar maliya,
Zarah ta matse lips dinta da idonta gamm tana jin mugun zafi na ziyartar kwanyarta,
Cikin rikicewa da rashin sanin ainahin hanyar yayita kokarin kutsawa cikinta tanata cijewa lokaci daya ta saki lips dinta sakamakon wata muguwar azabar da taji,
KHALEED ya sauke wani dogon numfashi jin wani dadi dabe taba jiba jinshi duniyar da bai taba ziyarta ba notikan kanshi suka kwance yanajin mugun dadi da shaawa ya cigaba da sex daita yana sauke numfashi da huci,
Hawayene kebin fuskar Zarah tana jin mugun zafin da bata taba jiba HQ dinta kamar babushi jikinta tana matukar jin azaba amma bazata iya ihu ba nishi kawai take hawaye na zubar mata,
Jin ruwa na kara yawa a kogin dadin yasa shi mancewa da kanshi ya manta da kowa ya cigaba da budiri,
Lokaci me tsawo ya dauka akanta yana aiki daya Wanda baisan time da ya dauki har tsawon lokacin ba saboda dadi da giyar so dake dibarsa bayan ya gama samun gamsuwa sosai hankalinshi ya dawo jikinsa ya zare jikinshi ya kwanta gefe yana meda numfashi yana zufa,
Idanunshi a lumshe bayan two minutes ya juya kanshi ya kalli Zarah lokaci daya ya dawo dede ya mike zaune dasauri ya zuba mata ido yana kallonta tana ta kyarma lips dinta na kyarma sosai idanunta lumshe,
Hankalinshi tashe ya jawota jikinshi yana kiran sunanta"Baby...Baby"
Idanunshi suka sauka kan jinin dake kwance a kasanta ,
Idanunshi suka cika da hawaye yana jin tausayinta yace"Baby ki bude idanunki dan Allah bansan wani abu zai sameki ba "
Zarah batasan me yake ba tana jin jikinta, yana rikice yace"Baby dan Allah ki yafemun nayi miki shigar sauri ban tsaya nazartar yadda zanba"ko kadan Zarah batasan yanayi ba,
Idanunshi jawur zuciyarshi na harbawa ya tashi ya saka boxer dinshi ya fita falo yayi dialing no din WALEED,
WALEED na kwance a dakinshi yana cikin tunanin Zarah kiran ya shigo ya dauka ya kara a kunne,
KHALEED yace"WALEED kazo gida yanzu nan "
WALEED yayi saurin mikewa zaune zuciyarshi na zafi baisan abinda zai kaishi gidan ko haduwa daita yace"Daddy bana gida"
KHALEED ya daka masa tsawa yace"Ina fada maka kazo yanzu Zarah bata lafiya"ya kashe kiran
Zuciyar WALEED ta kara tsananta bugawa idanunshi suka cika da hawaye jin zarar shi bata lafiya ko yaso zama zuciyarshi bazata iya hakura batare da sanin halinda take ciki ba ya tashi dasauri ya dauki keys ya nufi gidan da gudu,
KHALEED ya koma wurinta dasauri ya janye zanen gadon ya sauya wani ya ajiye wancan a gefe ya dauko doguwar riga ya sakamata tana saman bed sheme jikinta nata rawa KHALEED ya koma sama ya meda kanta a jikinshi idanunshi cike da hawaye yana jin kamar yayi kuka,tun laasar yana kanta har bayan Maghreb ta wahala,
Cikin yan mintuna WALEED ya iso gidan ya nufo ciki yana rikice zuciyarshi na up and down bai taba tunanin first night dinsu bane yayi zaton an dade da wuce wurin,
Yana shiga falo yaja ya tsaya gidan nata kamshin masoyansa guda biyu dasauri yajawo wayarsa ya kira KHALEED ,
KHALEED ya fito dasauri idanun WALEED rufe zarar kawai yakeson gani yace"Tana ina? "
KHALEED ya nufi ciki yabi bayanshi da sauri,
Yana shiga ya hangeta saman bed jikinta nata rawa zuciyarshi tai mummunan bugawa ganin halin da take ciki kallo daya ya mata ya gane abinda ke damunta a hankali idanunshi suka sauka kan bedsheet da rigar KHALEED dake gefen bed zuciyarshi tai wani irin bugawa a hankali idanunshi suka lumshe ya sulale wurin,
Hankalin KHALEED na kan Zarah yace"Ka bata temakon gaggawa plsss"yaji shiru yana waigowa yaga WALEED sheme kasa,
Ya karasa rikicewa ya karasa wurinshi jikinshi na rawa ya dagoshi ganin ya suma abun ya rikita shi mezesa shi suma tunda abun da ya karanta kenan ?ya tashi da sauri ya dauko ruwa yazo ya fara kwarara masa zuciyarshi na zafi,
WALEED ya farko yana matsanancin tari zuciyarshi kamar zata fito ,KHALEED ya rikeshi ya rasa yadda zaiyi ,
A hankali tarinshi ya rika lafawa yana dan farfadowa ya kalli KHALEED yace"Daddy... zanje na siyo drugs ...da zaa bata"
KHALEED ya kureshi da kallo, bai tsaya ba ya tashi ya fita yana danyin tarin jefi_jefi ya shiga mota ya nufi pharmacy yana tafiya yana share hawaye dake gangaro masa gefen ido harya isa ya siyo ya shiga motar ya nufo gidan cikin karfin hali,
KHALEED na zaune zuciyarshi na tunanin halin da WALEED ya shiga da ganinta shi ya kirashi ne don shine kadai zai iya bari ya duba Zarah amma halin da ya shiga yasa zuciyarshi zargi,
Tunanin hakan baisa ya kara duba Zarah ba har WALEED ya shigo yana sauri ya karasa kan bed din ba tsayawa ya fara hada allurai hawaye nabin bayan idanunshi kadan yana sharewa ya hada alluran ya hau gadon ya mata lokaci daya jikinta yadena rawa sakamakon radadin daya bar jikinta ,
KHALEED na zaune kasa inda WALEED ya fadi yanata kallon WALEED din yana karantarsa ,
Ganin ta dena kyarmar WALEED ya share hawaye da bayan hannunsa ya kalli KHALEED yace"Daddy ga drugs nan kabata tasha "
Yana jin kishin wani ya ganta yace"Ba sai ka kaita asibity ba zata samu sauki"
Yana gama fada ya fita dasauri ,KHALEED nata kallon shi ya juya ya bishi da kallo zuciyarshi na tsananin zafi sakamakon abunda ya fahimta,
WALEED na fita ya shiga mota ya dora kanshi kan sitiyarin yayita kuka, kuka me tsanani Wanda baisan kona miye ba kishi?tausayi ?ko na rashinta?
Zarah data dawo tunaninta jikinta mace ta fara kiran"Daddy...daddy "
KHALEED yaji wani nauyi a zuciyarshi yana jin wani abu idanunshi jawur ya tashi ya zauna gefen bed din yana kallonta da tausayi yanajin sonta da kaunarta ya dora hannu yana shafar gashin kanta,
Ta bude ido ta saukesu akanshi a hankali ta saki murmushi dukda halin da take ciki tanajin dadi yadda KHALEED ya samu gamsuwa daita,
KHALEED bai mayar mata ba saima wani faduwa da zuciyarshi tayi a hankali yace"Sannu Baby"
Ta meda idanunta ta lumshe tana tunanin zai fara karanto mata lafuzzansa masu dadin gaske da kara mata sonshi taji shiru ,
A hankali ta sake bude ido ta kalleshi idanunsa na kanta amma hankalinshi baya kanta batai yunkurin masa magana ba ta sake lumshe idanunta abubuwan da suka shiga tsakaninsu suna dawo mata tana jinjina jarumtarsa,
Ya dau lokaci yana tunani sannan ya kalleta ya tashi ya nufi toilet jikinshi sanyaye ya hada mata ruwan zafi ,
Zuciyarshi na kuna yazo wurinta idanunshi kasa ya tallabota ya fara cire mata rigar ta kalleshi ta meda idonta ta kulle ya gama ya dauketa ya kaita toilet yasata ciki da yake akwai allurai jikinta bataji wani zafi ba ,
Yana zaune kanshi kasa bayason kara kallon naked body dinta bare yaji shaawarta ya mata wanka ya dawo daita kan bed yasa mata kaya ya dauko tea da drugs yabata tasha a hankali yace mata "Sannu" ya rufa mata bedsheet ya dauki Wanda ya baci ya fita ,
Zarah tabi kofar da kallo kamar akwai damuwa tare dashi ganin halin da take ciki yasa tai tunanin shine damuwarshi ranta badadi tana jin sonta warke don su cigaba da farinciki ta lumshe ido bacci ya dauketa,
KHALEED na zuwa wurin washing machine yayi tsaye yana kallon bedsheet din da jini ya bata yanajin bakinciki memakon farincikin da yake ciki kafin zuwan WALEED wani irin tunani zuciyarshi keyi da ya kasa karyata hakan a hankali ya tura bedsheet din ya wanke ya shanya ya koma bedroom din baiko kalli gadon ba ya nufi toilet ya sakarwa kanshi ruwa yana under shower hawaye na bin idanunshi zuciyarshi na suya,
WALEED yasha kuka yana jin kamar ya fiddo zuciyarshi ya yar ya nufi gida ya bude mota ya fito yana tafiya a sannu jikinshi mace yana tunani harya shiga ciki,
Yana shiga ya samu HAMEED da Muneera suna zaune suna fira ,HAMEED na ganinshi ya tashi tsaye hankalinshi a dan tashe,
Muneera ma ta mike dasauri tana kallonshi gabanta na faduwa tace"WALEED daga ina?"
Ya kalleta ya nufi ciki suka bishi dakin tare ,
Yana shiga ya kwanta kan bed ya fashe da kuka yanayi kamar karamin yaro yana rike da heart dinshi,
Muneera ta rikice taje ta rungumoshi jikinta tana kiran "WALEED meke damunka? " idanunta cike da hawaye,
WALEED ya kara manna kanshi da jikinta ya cigaba da kuka me ban tausayi Muneera batasan time data fara kukan ba tana tambayarshi meke damunshi,
Idanun HAMEED jawur ya fiddo syringe da alluran da yazo masa ya hada yaje ya kama hannunshi ya mishi,yana mishi jikinshi ya saki bacci ya daukeshi,
Muneera ta dago da sauri ta kalleshi tace"Miye haka?"
Kamar zai kuka yace"Allurar bacci ce da rage ciwo mama, ki rika wa WALEED addua saboda soyayya yanaso ya kashe kanshi kullum saina masa yake iya bacci "
Muneera tai saurin kallonshi tana innalillahi wainna ilaihi rajiun,
Jikinshi sanyaye yace"Sai da safe "ya nufi waje cikin rauni,
Muneera ta rike gemu tana hawaye tana jin tausayinshi sosai ,
KHALEED na fitowa wanka ya hau carpet yana sallah yana hawaye masu zafi ya gama ya daga hannu yana addua yana kuka bayan ya gama ya tashi yaje gefen bedside ya zauna ya zubawa Zarah idanu yanajin sonta tausayinta da kuma nauyi lokaci daya,
Daren KHALEED HAMEED da Muneera basuyi bacci ba HAMEED na jin zaije ya fadawa KHALEED abinda kenan wata zuciyar na hanashi.
Tun asuba Zarah ta farka tana nishi ta samu dakyar ta tashi zaune KHALEED ya matso kusa da ita yace" Sannu Zarah Allah ya baki lpy"
Tai karamin murmushi ta daga kai ta mika masa hannu ba don yaso ba ya kamata suka shiga toilet ya mata wanka ya nata kauda idanu ya dawo daita yasa mata kaya ta rama sallolin da ake binta shi kuma ya fita masallaci yana yin sallah ya dawo ya dauki key da wayarsa bai shiga wurinta ba ya shiga mota yabar gidan ya nufi gidansu yana driving yana cije lips da takaicin kansa,
Yana zuwa gateman ya bude masa yayi parking ya nufi ciki dakin WALEED ya nufa kai tsaye don dole ya masa interview,yaje bakin dakin ya tura ya shiga Muneera na zaune kan carpet da alamu sallah tai idanunta na kan WALEED dake kwance yana ta bacci ta juyo ta kalleshi,
Ya kalli WALEED din ranshi na baci ya karasa ciki ya zauna yace"Ina kwana?"
Tace"Lafiya lau kasan bai lafiya ne naga kazo tun da safe?"
Ya girgizakai yace"meyasa meshi?"
Ranta badadi tace"WALEED bai lafiya saboda soyayya yanason kashe kanshi jiya HAMEED ke fadamin wai duk abinnan sai ya mishi allurai yake iya bacci"
KHALEED yace"What!!!!!??"ya dafe fuskarshi yana jin kamar ya fashe da kuka zuciyarshi na ciwo,
Muneera ta girgizakai tace"Na rasa wace irin soyayya ce WALEED ya shiga da har yake ciwo saboda ita"
KHALEED na jin tsananin ciwo a heart dinshi ya kalli WALEED din yana tuno star dake hannunshi ya matsa ya bude hannunsa ya ganta baro_baro,
Cikin sanyin jiki ya dauki phone dinshi a wallpaper pic dinsu ne shi daita duk shekarun nan gabanshi na faduwa a hankali ya saka no din Zarah sunanta ya fito da *STAR*
ya cije lips ya ajiye wayar yana kallon WALEED din yanajin haushi da mugun takaicinsa,,
Muneera tace "Ya kamata mu mai dashi asibitin saboda alluran da HAMEED ke masa na iya sashi matsala"
KHALEED ya girgizakai idanunshi cike da hawaye yana tuno time da WALEED kece masa yana son aure time da yake mafarkai time da yake fadamai bazai iya rayuwa babu ita ba da time daya dawo ya fara rashin lafiya har zuwa jiya daya fahimci komi,a hankali yace"Basai an kaishi asibity ba ciwonshi bana asibity bane"yana gama fada ya tashi ya fita zuciyarshi na zafi da tafasa yanajin zazzabi da tsananin ciwon kai,
Muneera ta meda kallonta gun WALEED duka fa he's 20 amma haryasan so?,
KHALEED na fita gidansu HAMEED ya nufa bai kira wayarshi ba ya tura gateman kiranshi yana fitowa yaganshi ya fara kame_kame,
KHALEED ya bude masa ya shiga ya zauna yayi shiru fuskar KHALEED din tabashi tsoro,
Ran KHALEED bace muryarshi dakile yace "Gidansu budurwar WALEED zaka kaini, ina nufin gidan iyayenta"
HAMEED yayi saurin kallonshi gabanshi na faduwa ya rasa karyar da zaiyi KHALEED ya kureshi da ido,
bakinshi na rawa yace"Daddy bansanta...."
KHALEED ya daka masa tsawa "Shut up !!!"zuciyarshi na kuna idanunshi jawur yace"Idan shi ya boyemin kai saika biye mishi?bayan kasan cewa yana sonta tsawon lokaci kuma kasan dalilinta ya shiga halin da yake ciki"
HAMEED ya fara hawaye zuciyarshi na zafi yace"kar kaga laifina Daddy naso fada maka ya hana ya fadamin ka sadaukar da duk rayuwarka akanshi wannan karon ne kadai zai sadaukar maka da wani abu"
KHALEED ya dafe kanshi da yake kara tsananta ciwo yace"WALEED bai kyautamin ba baiyimin adalci ba sam"
Muryar HAMEED raunane yace"Kayi hakuri daddy"
KHALEED na jin kuka yace"zaka iya tafiya"
HAMEED na kallonshi da mugun tausayi ya bude motar ya fita KHALEED ya jata ya nufi gida zuciyarshi na tsananin zafi muryar WALEED na dawo masa time da yake fadin"Wlh Ina tsananin sonta Daddy itace rayuwata...."
Da time da yace masa"Kaje kayi karatunka na maka alkawari da zaran ka dawo zan aura maka zabin zuciyarka"zuciyarshi karye ya gangara bakin titi ya duke yafara kuka ,kuka meban tausayi da kona zuciya ba abinda yake gani da tausayi sai WALEED dinshi donme zaiyi shiru bayan yasan hakan zai cutar dashi?..
Yasha kuka sosai yana dana sanin kasancewa da Zarah a yau domin ba muhallinshi bane bashi ne ya cancanta ya aureta ba ,ya goge fuskarshi da tayi jawur idanunshi ma sun rine ya nufi gida,
Bayan ya isa yayi parking ya kure gidan da kallo yanajin kamar karya shiga jikinshi sanyaye ya nufi ciki ko zama baiyi ba ya nufi kitchen domin ya hada mata breakfast ,
Yana shiga kitchen din zuciyarshi ta tsinke samun Zarah tsaye tana kokarin hada masa breakfast duk da ciwon jikinta yana mata kallon tausayi yanajin sonta ya karasa wurinta yace"Baby me kikeyi haka?"
Ta dan kalleshi tana dan murmushi tace"Naga ka fita kuma kila zaka fita aiki shine nazo hada maka breakfast "
Yana harsaso soyayyar da take masa da wadda WALEED ke mata zuciyarshi na kara zafi yace"Yau bazanje koina ba zan zauna gida in kula da ke sai gobe zan fita"
Ta juyo ta kalleshi ta sunkuyar da kai tace"Nagode Daddy "
Lokaci daya ta dago dasauri tana kallon fuskarshi hankalinta yayi kololuwa wurin tashi tace"Daddy.. na mike damunka ?"ta matsa zata shafo fuskarshi dake jawur,
Ya kakaro murmushi Ya rike hannunta yace" Fever nake kije ki kwanta in gama hada miki breakfast kisha magani ki kara kwantawa ki huta"
Ta girgizakai tace"Daddy naji sauki kaje kasha magani zanyi"
Ya kalleta yace"Banason musu jeki"
Ta kara kallonshi jikinta badadi ta nufi ciki ta fara duba drugs dinta harda PCM da ibuprofen ta dauko su ta bude fridge ta dauko ruwa ta dawo kitchen din yana cigaba da hada mata breakfast tana jin tausayin shi ta karaso tace"Daddy ga magani"
Ya juyo yana mata kallon kauna da tausayi ta ballo drugs din ta bashi ta zuba ruwa a cup ta mika mai yasha ta amshi cup din ta aje tace"Sannu"
Yayi tsaye yana kallonta,
Ta juya ta nufi kofar fita,KHALEED yabi bayanta da kallo yana kallon yadda take tafiya a bude, ya cije lips zuciyarshi na zafi ya juya ya cigaba da abinda yake.
*SHIGAR SAURI*
Painful love story
Romance special
Writing by
*MAMAN MAMY (SHALELE)*
*Wattpad@mumies122*
*Dedicated to my close friend ikra Rukayyat*
*Devoted to identical twins hassan & Husain 80k and Fatima dimple* mantawa nake da rubutaki😜
*Small gift to my real fans*
*PROFICIENT WRITERS ASSOCIATION*
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/
TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09
Page > 61&62
*Muna saida kayan mata da na maza suna da kyau sosai kuma cikin sauki muna turawa koina ga me bukata seya tuntubi wannan number👉🏼 0806 672 6866*
Tana komawa bedroom cikin karfin hali ta gyara bedsheet ta meda pillows mazauninsu ta nufi toilet ta sake wanka ta fito ta saka best da mini sket ta tsaya gaban mirror tana makeup,
KHALEED ya gama hada komi ya dora a dining ya juya ya kalli bedroom din gabanshi ya fadi baya son kallon fuskarta hakan nasa shi shiga wani hali ,
Jikinshi sanyaye ya nufi ciki yana shiga ta juyo tana kallonshi tasha kwalliya tayi matukar kyau,
Kallo daya KHALEED ya mata ya dauke idanunsa zuciyarshi na harbawa jikinshi sanyaye ya nufi toilet ,
Zarah na murmushi ta kirashi"Daddy"
Ya waiwayo da kanshi yana kallonta, ta mike tsaye tana gyara vest din jikinta tana murmushi tace"Nayi kyau?"
Kalmar tai masa nauyi yanajin tausayinta yace"Kinyi kyau sosai "
Ta sunkuyar da kai tana murmushin jindadi ya juya ya shiga toilet,
Tana jin kaunarshi na kara shigarta komi nashi tana sonshi, ta fita falo don ta gyara inda keda bukatar hakan,
Yana Shiga toilet din yayi tsaye yana kallon madubin dake ciki zuciyarshi na wani irin zafi yana tuno marecen jiya yadda ya kasance tare da wacce dan'uwanshi keso ,laifin kanshi yake gani daya kasa hakurin wani lokaci yayi shigar sauri inama hannun agogo zai dawo baya da zuciyarshi ta rage radadin da take na hada jiki da ita ,
A hankali ya fara wanka ya fito yana zuwa bakin bed ya samu ta fiddo masa kayan da zaisa ,zuciyarshi ta karayin rauni yanajin kamar karya saka kayan amma bazai iyaba ,jikinshi sanyaye ya saka kayan ya fito falon ya sameta zaune tana kallo, tana kallon fuskarshi ta sakar masa murmushinta me narka zuciya dakyar ya mayar mata ya nufi dining gudun kar ya shiga falo yazam saiya dauketa,
Yana zama ta taso tazo ta zauna gabdashi tanata kallonshi ,,ya zuba mata abincin ya ajiye gabanta ya fara zuba nashi,
Ta kalli plate din gabanta duk kusan tare suke ci yanzu harta saba da hakan ta dago ta kalleshi harya zuba nasa ya zauna yasa cikali
tace"Daddy batare zamu ci ba?"
Ya kalli fuskarta yanajin tausayinta yace"hakane namanta"
Tai murmushi ta janye plate din gabanta ta saka cokali a nashi ta debo abincin ta nufi bakinshi dashi,
KHALEED ya kasa bude baki saima kallonta da yake ,zuciyarshi na fadamai bai kamata ba,
Jikinta yayi sanyi ta ajiye cokalin tace"Daddy ko zakaje asibity?"
Ya danyi murmushi yace"A,a basai naje ba aikin bani magani"
Fuskarta bawalwala tace"Kada ka damu zan samu sauki"
Ya jinjina kai ya dauki cokali ya fara cin abincin kadan_kadan ,itama ta dauka tana ci, dukansu basu ci na kirki ba suna shan ruwa ya tashi ya shiga bedroom dinta ya dauko drugs dinta ya dawo ya balla ya mika mata ,
Ta kalli drugs din zuciyarta badadi taso ace a baki yabata ta amsa tasha ,
Muryarshi sanyaye yace "Ki koma daki ki kwanta zan danyi aiki a system"
Ta turo lips kamar zatai kuka tace"Na gaji ka daukeni"
Gabanshi ya fadi bayason ta nemi wani abu a wurinshi taki samu saboda yana tsananin sonta tana da wani babban matsayi a zuciyarshi da baya tunanin akwai wacce zata samu hakan sincerely ma itace zuciyarshin
Yayi murmushin dole ya koma ya dauketa in a bridal style har kan bed ya kwantar da ita a hankali yace "Allah yabaki lpy Baby"yana wani tunani
A hankali tace"Nan kusa insha Allah "
Yayi saurin juyawa yana matse lips bayason zuwan ranar don baya jin zai iya zama da Masoyiyar kaninshi danshi,
Ya koma falo ya kwantar da kai jikin kujera yana tunani Zarah na sonshi sosai ko zata iya hakurin rashinsa kamar yadda yakejin zai iya hakura daita?Zuciyarshi ta kawar masa da zancen ta hanyar tuno masa da halin da WALEED ke ciki koma yane ya kamata ya bashi abinda yake so da mafarkin samu tuntuni,
WALEED bai tashi da wuri ba yau sai wurin karfe 10 ya farka da ciwon shi domin alluran sun gama aikinsu,
Yana kwance akan cinyar Muneera Idanunshi suka rika haskomai abunda ya gani jiya ya fara hawaye yana juyi zuciyarshi na zafi,
Muneera ta rikeshi idanunta cike da hawayen tausayinshi tace"WALEED na roke ka dan Allah kayi hakuri kasawa zuciyarka hakurin abinda Allah bai kaddara naka bane ,saboda soyayya kamanta da halin da zamu shiga kana sa rayuwarka cikin hatsari kayi hakuri mana "
WALEED ya kalleta idanunshi jawur yana hawaye yace"Mama kimin addua..kimin addua na dena sonta zuciya ta ciwo Mama "
Muneera ta dora hannunta akan zuciyarshi hawayen dake idanunta suka samu nasarar zubowa saboda tausayi tace"Zaka dena kaide kayi hakuri kadena tunanin ta"
Ya matse lips ya juyar da kai hawaye na zararowa daga idanunshi bazasu taba gane yadda yakeji ba,
Ta goge hawayenta tace"ka daure ka tashi mu tafi asibity"
Idanunshi lumshe yace"Adduarki nake bukata Mama amma ko munje saukin na dan lokacine"
Muneera tace"Innalillahi wainna ilaihi rajiun"tsoro cike da zuciyarta ,,
WALEED ya bude ido yace"Mama sallah zanyi"
Tace"To "ta tashi ta kamashi takaishi toilet ta fito,
Yayi alwala dakyar ya dawo ya zauna yin sallah yayita a zaune yana gamawa ya kwanta wurin,
Muneera taje ta hado mishi tea ta dawo ta fara kokarin tada shi,ya bude ido ya kalli tea din ya girgizakai,
Muryarta raunane tace" Gaskiya WALEED idan bazaka ci abinci ba dole mu tafi asibity don lamarinka tsoro yake bani "
Jin abinda ta fada yasa ya daure yasha tea din da drugs ya koma ya kwanta yana tunanin halin da Zarah ke ciki yanzu ,tunanin na fado masa ya cije lips yanajin kuna a zuciyarshi ,
baisan KHALEED yazo ba saboda yana bacci time din bare yasan ya gano dalilin rashin lafiyarshi kuma firgicewar da yayi jiya dayaga Zarah bata bari ya lura da kallon tuhumar da KHALEED din ke masa ba,
HAMEED da ya kwana tunani ya samu ya tashi ya shirya ya nufo gidan don duba lafiyar abokinshin,
Yana shigowa gidan yaji tsitt ya nufi dakin WALEED ya sameshi kwance ,
Ya zauna kusa dashi WALEED ya bude ido ya kalleshi,
HAMEED na binsa da kallon tausayi yace"ya jikin?"
Ya matse lips dinsa ya sake rumtse ido,
HAMEED yayi shiru so yake ya bashi labari KHALEED ya gano damuwarsa amma yana gudun ciwonshi ya kara tsanani wannan yasa yaja bakinshi yayi shiru,
Muneera ta shigo dakin ta samu HAMEED ya sunkuya ya gaisheta ta amsa tana kallonshi tace"HAMEED ka rika bashi shawara ya rika tunanin halin da zamu shiga kuma akwai mata da yawa duniya idan yanaso saiya samu wadda tafi wancan ma "
Muryarshi sanyaye yace "Mama ina fada mishi amma ya kasa fahimta"
WALEED na hawaye yace "Na fahimta amma na kasa dena sonta ita kadaice a zuciyata kumin addua... na gaji"
HAMEED ya dafashi yanajin tausayinshi yace"Sorryyy"
Muneera kam juyawa tayi ranta na suya saboda mace bai damu da rayuwarshi ba baya tunaninta da daddynshi halin da zasu shiga saboda shi,
KHALEED na kwance jijiyoyin kanshi sunyi rudu_rudu kamar zasu fito sabida tunanin da yake daya fi karfinsu ,Zarah ta farka daga barci ta fito ta wuceshi ta shiga kitchen ,
Yabita da kallo yanajin zafin abinda ya shiga tsakaninsu yayi disvirgin dinta a lokacin yana cikin farinciki amma yanzu kuna zuciyarshi keyi duk in ya tuno hakan,
Yana tuno soyayyar da sukayi daita na kwanakin kamar tayi ta tafiya ya tashi ya bita kitchen din ya jingina da kofa yana kallonta yace"Baby baki tausayin kanki?"
Tana dan murmushi tace"Daddy ai na samu sauki yanzu kaine bakajin dadi dole na kula da kai"
Yayi murmushi me ciwo yace "Lafiya ta lau ni ciwon WALEED ne yafi damuna jiya har suma yayi"
Ta fiddo ido gabanta na faduwa tace"Daddy suma? Innalillahi dan Allah daddy ka kaini in ganoshi ya jikinshi dasauki ko?"
KHALEED yayi murmushi ganin ta damu yace"Dasauki amma baigama warkewa ba domin ciwonshi bana asibity bane"
Ta kalleshi tana mamaki tace"Daddy wane irin ciwo ne yake? "
KHALEED yace "wata kyakkyawace yake tsananin so rashinta ne yasashi duk wannan halin"
Zarah na jin tausayinshi tana tuno yadda tasha dakon son KHALEED da azabar da tasha kafin yace yana sonta tace"Na tausaya mishi ba kowane zai fahimci halin da yake ba sai Wanda ya taba tsintar kanshi ciki..Daddy ina daga cikin wadanda suka dandana zafin so time da kace baka sona naji duniyar tamin zafi a time din har nafi son mutuwa akan rayuwa,dan Allah daddy kayi kokari wurin hada shi da wacce yake so ta amince dashi"
KHALEED ya hadiye miyau me zafin gaske shima hakance yakeji yanzu dukda yana tare da masoyiyarsa amma yafi son mutuwa akan rayuwa,
Dakyar yace"Insha Allah zanyi bakin kokarina koda zan rasa duk farin cikina"
Ta kalleshi tana mamakin statement din karshe ta matse lips ta juya tana gyaran cefane,
Ya shiga ya kama mata suka dafa abincin sukaci tare dukkansu suna tunanin WALEED tana tausayamai saboda halin da yake ciki ta taba tsintar kanta aciki sannan kuma tana sonshi matsayinshi na yayanta kuma jinin mijinta,
Bayan laasar KHALEED yana gama sallah ya shiga mota ya nufi wani super market yana tuno farinciki da dadi da ya shiga daya kusanceta yanajin bai kyauta mata ba idan har bai bata wata kyauta ba ya nufi bangaren jewellery ya tsaya yana duba wacce zatai mata kyau ,
Yana ta dubawa idanunshi suka sauka ga wata sarka mai dauke da kwalliyar W jikinta , hankalinshi ya dauku ga kallon sarkar yana hangota a wuyan Zarah da yadda zatai mata kyau ga sunan WALEED a jiki yayi karamin murmushi yana tuno Star din hannun WALEED ya nufi wurin biya aka fadamai kudinta ya biya ya fito ya nufi gida,
Da shigarshi ya samu Zarah zaune akan seat ta sauya wanka tana cikin riga da sket atamfa tana kallo ,
Jikinshi sanyaye ya nufeta ,tana jin kamshin shi ta yunkura ta tashi tsaye tace"Daddy sannu da zuwa"
Ya zauna yace"Ya jiki?"
Tai dan murmushi ta matse lips tace"Da sauki"
Ranshi badadi ya mika mata ledar hannunshi, ta amsa ta bude ta fiddo akwatin ta dago tana kallonshi tana murna tace"Daddy wannan fa?"
Yayi shiru ya rasa me zai fada a hankali yace"Kyauta ce daga masoyinki"
Ta saki kayataccen murmushi tana kallon sarkar ta kalleshi tace"Nagode sosai daddy da kyautar nan Ina jindadi sosai yadda kake sona "
Ya lumshe ido yayi shiru,
bata damu ba ta bude akwatin ta fiddo sarkar nata walkiya ta daurata a wuyanta ta tsaya tana kallonta tasa hannu tana lalubar W din tana jindadi a hankali tace"Tamin kyau sosai dama K ce a jiki da setafi min kyau fiye da haka"
Ya bude ido ya kalleta yace"Hakan ma tafi miki kyau kun dace..."
Kafin ya rufe baki taje ta rungumeshi gaban KHALEED ya fadi yaji kamar ya zare ta amma bazai iya ba,
Tana rungume dashi tace"I love u so much daddy the whole world is empty without u"ta kai smooth lips dinta ta danyi kissing kumcinshi,
Yanajin nauyin hakan ya janyeta yana murmushin dole yace"I love u tooo "
Zarah ta sake zama kan cinyarshi tana taba sarkar tana jinta kamar zuciyarta,
KHALEED ya kuma janyeta ya ajiyeta gefe ya jawo system dinshi ya bude ya fara aiki yanayi yana dagowa yana kallonta yadda take kallon sarkar tana jindadi,
Cikin zuciyarshi sosai yake tausaya mata yana fatan zata hakura dashi kamar yadda ya hakura daita,
Da dare bai dawo da wuri ba saida yaje gida ya gano WALEED bai nuna masa yasan komi ba ya dawo yana zuwa ya sameta sanye da black and pink rigar bacci bata kai ko gwiwa ba gabanta ragace zalla kana ganin kyawawan breast dinta da haryanzu suke tsaye kyamm ,
Yayi saurin kauda idonshi yanajin bakincikin saka kayan,
Tana tsaye ta kalleshi tace"Sannu da zuwa daddy"
Bai amsa ba idanunshi kasa yace"Baby kidena saka sleeping dress har sai bayan sati daya"
Ta kalleshi tana ganin kamar don karya takura mata ne tana jin tausayinshi cikin sanyin murya tace"Nadena.."ta juya ta nufi bedroom ta bude wardrobe ta fiddo single Zane da yar riga ta saka ta hau gado ta kwanta ta lumshe idonta tana son bacci ya dauketa kafin zuwanshi bazata iya jumirin kallonshi cikin bukatarta ba bata aminceba,
Yana ganin ta shiga yayi zaune yanajin fever da ciwon kai, shima ya fara dandana zafin son don kuwa iyakar kokarinshi ne yake don ceto rayuwar danuwanshi batare da damuwa da tashi ba ya tashi yasha magani ya nufi bedroom din don karta shiga damuwa,
Tana kwance idanunta lumshe amma takasa bacci ba tareda shi ba breast dinta har kaikayi suke ta saba wasan da yake dasu taji shigowarshi tana jiran taji motsinshi ya hau gado sai jitayi ana Jan pillow a hankali,
Ta bude ido ta kalleshi yayi karamin murmushi yace "I'm sorry"
Ta meda mai karamin murmushi ta sake rumtse ido batare da taji haushinsa ba domin tasan tausayinshi kuma tasan yadda yake tafiyar daita da zaran sun kwanta hannunsa yana kasancewa saman jikinta ,
KHALEED ya koma kasan carpet ya kwanta ya runtse ido ya fara tuno dararukan da suka gabata zuciyarshi na zafi akan hakan yakasa runtsawa yanata tunane _tunane yasan ba karamin hali zai shiga ba rashin Zarah amma bai manta time da yakewa WALEED alkawari ba kuma yana ganin yana da ikon bashi abinda yake so..
Muneera nata jinyar WALEED da dare HAMEED ya sake masa alluran bacci yayi bacci,
****
Kusan halin da WALEED ya shiga bakomai bane akan Wanda KHALEED ke ciki ya shiga tsananin damuwa baya barci baya cin abincin kirki kullum tunani yanata ramewa ko office yaje aiki gudane tunanin WALEED da Zarah,
Da yake ba daure mata fuska yake ba zarar bata fahimci komi ba tana kagare ta warke domin su dawo rayuwar soyayyar da suka saba,
Bayan six days
Tana jin ta samu lafiya tafiyarta ta dawo normal tana missing jikinshi sosai ,karfe shidda zai dawo tayo wanka ta tsara kwalliya ta sanya riga da wando ta feffesa turare tana ta murmushi tana jiran shigowarshi,
Ba dadewa taji bude gate da shigo da mota tai saurin fita falo tana sakin murmushi yana shigowa taje zata rungumeshi yayi saurin dakatar da ita yace"plsss"ya wuceta yaje kan seat ya zauna,
Jikinta yayi sanyi ta bishi taje ta zauna gefenshi a hankali tace "Daddy Naji sauki dan Allah kadena guduna a shirye nake da tarbarka domin nayi kewarka sosai"
Hawaye suka fara bin fuskar KHALEED yanajin kamar an danne masa zuciya da abu me nauyi,
A sannu Zarah ta dago ta kalleshi taga yadda hawaye ke zubo masa,hankalinta ya tashi dandanan hawaye suka fara wanke mata fuska tace"Daddy kona maka laifine?"
Bai kalleta ba bare ya bata amsa sai hawaye yake yana cije lips,
Tana cigaba da hawaye tace"Ka yafemin dan Allah idan nayi wani laifi"
KHALEED ya girgizakai yanajin tausayinta da kunar zuciya yace"Bakimin laifin komi ba nine ma nai miki laifi ki yafemin Zarah "
Ta tashi ta koma kan kujerar da yake zaune tasa hannuwa tana goge masa hawaye tana juyakai sannan ta rungumeshi,
Yanajin sonta da kaunarta hadi da tausayamata ya rungumeta yana cigaba da hawaye,
Sun dau lokaci haka sannan ya samu tsaida hawayenshi ta janye jikinta ta goge fuskarta ta tashi ta kawomishi ruwa ya amsa ya dan mata murmushi ta meda mai ta nuna mai yasha ruwan yasha ta amsa tasha ya tashi ya nufi ciki,
Bata bishi ba ta samu wuri ta zauna tai tagumi ta kasa fahimtarshi kwanakin nan ,,
KHALEED na shiga ciki ya bude lokokin madubi ya fito da biro da littafi ya zuba masu ido yana hawaye da bakinciki dakyar ya daukesu yayi rubutu yana gamawa ya duke yana kuka marar sauti zuciyarshi na tafasa yasan bai mata adalci ba bai kyauta ba amma rayuwar kaninshi yake kallo ,,
ya dan jima sannan ya linke papern ya jawo loka ya ajiye ya tashi ya shiga toilet ya shiga shower ruwa na sauka kanshi ya rika sauke ajiyar zuciya,
Yana gama wankan ya fito ya saka jallabiya yazo yawuceta ya nufi masjid duk da akwai sauran time,
Bai dawo ba har ishai yana zuwa shiga gidan ya fara murmushi ya shiga tana zaune da tagumin yaje ya zauna kusa da ita cikin wasa yace"Mrs tagumi"
Taji wani sanyi lokaci daya ta kalleshi ta turo lips tace"Ba kaine ba sai kaita damuwa kana hawaye bakason ko kallona "
Yayi murmushi yace"Tona dena shikenan?"
Ta daga kanta tana murmusawa,
Ya danyi shiru sannan yace"kinason ganin Mama? "
Ta daga kai tana murna tace"Sosai daddy "
Yace"OK ki shirya gobe idan zan fita aiki zan kaiki"
Farinciki ya lullubeta tana jin kamar taje tai hugging dinshi ta daure tayi zaune tana murna tace"Allah ya kaimu"
Yayi murmushi yace "Akwai wani abinda kikeso Kuma?"
Tana mai kallon kauna cikin zuciyarta tace"Kai na keso"a fili ta girgizakai ,
Yace"Dauko mana abinci anan zamuci"
Ta tashi tana jindadin sakin fuskarshi ta kawo abincin suka danci bayan sun gama ta kwantar da kanta akan kafarshi ya kura mata ido yanajin kaunarta kamar yayita kissing dinta ko yayita rafka kuka,
Sun jima sukaje suka kwanta yau ya hau gadon ya kwanta kanshi na kallon sama ,
Ta matsa kusa dashi ta dora mai hannu aciki tana ta kallonshi tana mamakin sauyawarshi har bacci ya dauketa,
Yanata tunani ya meda kallonshi kan beauty face dinta ya janye hannunta ya fita falo ya nata zagaye_zagaye sannan ya zauna kan kujerar dining yana kuka zuciyarshi na tsananin zafi yanajin kamar ya fiddota yayar ranar ma baiyi bacci ba kusan kwana bakwai kenan ba bacci idanunshi,
Washegari ta farka cikin zumudin zuwa gida tun kafin ya dawo masallaci tai sallah ta shiga kitchen egg kadai ta soya ta hada ruwan zafin tea ta ajiye a dining,
Ya shigo yana tafiya a sannu jikinshi ba kwari ko kadan,
Ta kalleshi tana murmushi tace"Daddy ka tashi lpy?"
Yace"Lafiya lau kefa"
Tace"lafiya lau anjiman zamu tafi?"
Ya daga mata kai,
Tana jindadi ta nufi bedroom dasauri,ya zauna ragwaf kan kujera yanajin dama zuciyarshi zata buga ya huta ji yake jikinshi kamar ba nashi ba cikin dauriya ya tashi ya shiga toilet na falo yayi wanka ya shiga ya sameta tana ta shiri cikin walwala,
ya sauya kaya suka fito a tare sukai breakfast ta koma bedroom ta dora mayafi akan material lace din jikinta ta dauki jikka,
Ya shigo yana binta da kallo tai masifar kyau ya dauke idonshi ya bude loka ya dauki takardarshi suka fita daga gidan,
Suna cikin mota yana driving yana matse lips baya lafiya shima yasan hakan amma bata bukatar kwanciya ,
A hankali ya kalleta suka hada ido ta sakarmai murmushi tace "Sati biyu kenan banga mamata ba sai dare zamu dawo gida?"
Ya danyi murmushi zuciyarshi na zafi domin ta tafi kenan zai rabu daita rabuwa ta har abada bazasu taba dawowa a irin wannan matsayin ba hawaye suka cika idonshi ya juyar da kai yana medasu sannan ya cigaba da driving,
Ta lura da hakan ta matse lips ta kasa gano meke damunshi haka saide tausayamishi take abun ya dameta sosai,
Yana ganin sun kusa isa gidan zuciyarshi ta tsananta harbawa yayinda ita kuma take cikin farinciki ,Suna isa megadi ya wangame masu gate ya shiga ciki yayi parking ya kashe motar ya kalleta da jajayen idanunshi da sukai kwanaki haka,
Tai karamin murmushi tace "Bazaka shiga ciki ba?"
Ya dan girgizakai hannunshi na rawa ya zaro takadda daga aljihunshi zuciyarshi na kuna ya mika mata,ta kalli papern ta kalleshi tace"Ta Mama ce?"
Ya daga kai yace"Ku duka har dake"
Tai masa wani kallo tana dan murmushi ta amsheta zata bude ,dasauri yace"Ki bari sai kinshiga ina sauri na makara"
Tana dokin ganin abinda ke ciki ta kalleshi tace"tow daddy dan jira kadan"ta bude papern tafara karantawa,
ya dafe kanshi ya cije lips ya juya kai zuciyarsa na harbawa,
A hankali Zarah ta fahimci abinda takardar ta kunsa ta dago a firgice tana kallonshi hawaye masu zafi suka fara wanke mata fuska,
Zuciyarta na tsananin zafi bakinta na rawa tace"Menene wannan?...daddy ko de bana gani sosai?"
Hawaye suka zubowa KHALEED ya kasa juyowa gareta,
Zarah ta rufe bakinta da hannu ta fashe da kuka tana jin matsanancin tsoro duniya na juya mata tace"Daddy dama baka sona?...idan kuma laifinayi meyasa zaka dau wannan hukuncin?"
Tana sheshheka tace"Wallahi daddy banyi komi ba...."ta kasa karasawa ta bude motar zuciyarta na radadi ta nufi cikin gidan da gudu,
KHALEED ya duke jikin sitiyari yana kuka me taba zuciya kukan so da tarin tausayawa da zafin rabuwa da masoyiya,
Muneera na zaune falo tana bawa WALEED tea a baki Zarah ta fado ciki tana matsanancin kuka taje ta zube gabanta ta dora kanta jikinta tana matsanancin kuka tana juya kai ,
Zuciyar Muneera ta tsinke ta saki cup din hannunta tea din ciki ya zube ta ruko Zarah jikinta a razane take tambayar " Minene Zarah? Me kikewa kuka Zarah? "
WALEED na kallonta yanajin zafin kukan kamar ya rungumeta ya rarrasheta zuciyarshi na tunanin kukan me take haka dagani ba karamin kuna zuciyarta keyi ba,
Zarah ta damkawa Muneera papern dake cumimiye hannunta tana kuka muryarta na daukewa tace"Daddy ya sakeni ...mama saki ukku..nashiga ukkuna"
WALEED ya rumtse idonsa gam sakamakon jin kamar an daba mishi wuka a zuciya ya cije lips dinshi yanajin heart dinshi kamar zata fito ya danneta da hannu,
Muneera tai zumbur ta mike bata gasgata ba saida ta gama karanta takardar me dauke da guntun rubutu me dauke numfashi da tayar da hankali..... "I divorce her thrice"
Ta shiga rudani tana firgice take memeta "innalillahi wainna ilaihi rajiun!!!!"zuciyarta na bugawa,
Tana gama fada taji karar motar KHALEED zai bar gidan tai saurin daukar wayarta ta danna no dinshi,
Wayar KHALEED ta dauki ring yanajin ring din yasan kiran kona miye ya kashe motar yana kuka hannunshi na rawa ya dauka ,
Muryar Muneera raunane tace"Ina zakaje?ka shigo ciki ka sameni"
Ya ajiye wayar ya bude motar yana hawaye ya nufi ciki yana tafiya dakyar kafafunsa sun masa nauyi,
WALEED na jin ciwo ya kwantar da kai jikin kujera yana juya kai yana kuka saboda yadda daddynshi ya wulakanta Zarah saki ukku lokaci daya ashe dama baya sonta? He's regretting barmishi ita don shi bazai taba mata haka ba,
Muneera na tsaye jikinta har rawa yake ya bude kofa ya shigo kanshi kasa ya nufeta,
Tana mai kallon bakinciki da tsananin haushi yana isowa ta daukeshi da gigitaccen Mari,
Zarah tai saurin dafe kuncinta tana jin zafin marin a jikinta,
KHALEED bai ko dafe fuskar ba zafin zuciyarshi ya zarta misali ya sulale kasa ya dafe kanshi yana kuka sosai ,
Ran Muneera bace hawaye suka fara zubo mata bata taba dukanshi ba sai yau bata taba jin haushin shi ba kamar yau ,
Tana hawaye tace"KHALEED ashe baka da hankali bansani ba?kaine ka rubutawa Zarah saki har ukku lokaci daya?ko miye tai maka saika hukuntata idan ka gaza saika kawota wurina amma baka dauki wannan mummunan matakin ba"
KHALEED WALEED Zarah kansu sunkuye sunata kuka ,,
Muneera na hawaye zuciyarta na zafi tace "Ka dauketa ku koma saki ukku lokaci daya guda dayane kuma kasa a ranka kai da Zarah sai mutuwa ce zata rabaku"
KHALEED ya dago fuska yana kuka duk kamaninsa sun sauya kamar bashi ba muryarshi na rawa yace"Saki ukku nai mata Mama..kuma na haramtawa kaina ita har'abada"
Dukkansu hankalinsu ya kara tashi Zarah ta kara volume din kukanta zuciyarta na tsananin ciwo,
Kafafun Muneera suka kasa daukarta ta koma tai zaune kan seat tana kuka da sheshsheka ,
Hankalin KHALEED ya matsanancin tashi mahaifiyarshi daya dade yana sata farinciki yana mata biyayya tana zubar masa da hawaye ya rarrafo ya rungume kafafunta yana cewa"..........
😒
*SHIGAR SAURI*
Painful love story
Romance special
Writing by
*MAMAN MAMY (SHALELE)*
*Wattpad@mumies122*
*Dedicated to my close friend ikra Rukayyat*
*Devoted to identical twins hassan & Husain 80k &dimple*
*Small gift to my real fans*
*PROFICIENT WRITERS ASSOCIATION*
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/
TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09
Page > 63&64
*Muna saida kayan mata da na maza suna da kyau sosai kuma cikin sauki muna turawa koina ga me bukata seya tuntubi wannan number👉🏼 0806 672 6866*
Yana cewa "Dan Allah kidena zubarmin da hawaye Mama kar Allah yayi fushi dani...banyi haka don nasaki kuka ba nayi ne don samun natsuwar mu gabadaya"ya cigaba da matsanancin kuka,
Muneera na zubda hawaye jin kalamanshi yasa ta fara kokarin dakatar da hawayenta domin tasan ta haifi da kullum tana yabonshi tana alfahari dashi yaune daya da yayi abinda bata taba tunanin zai iya aikatawa ba ,
Zuciyarta na matsanancin zafi tasa hannu tana goge idanunta amma hawayen sun ki dena zubowa tana tsananin tausayawa Zarah kasancewarta marainiya,shi maraya duk time da wani abu ya sameshi kewar iyayenshi ne zata fara fado masa yayi tunanin idan suna raye da hakan bazai faru ba ,ba kowane yasan hakan ba amma ita tayi rayuwar maraici tasan yadda akeji dukda ita din tataso cikin gata kuma batasan iyayenta ba bare Zarah data san dadinsu ta kuma rabu dasu cikin tashin hankali.
Muryarta raunane tace" KHALEED meyasa?meyasa zakai haka?"
Ya kwantar da kai jikinta yana hawaye zuciyarshi na zafi yace "Nayi kuskure Mama na kasa fahimtar halin da dan'uwana yake ciki ya dade yana fadamin yana sonta.. aure yake so na nuna mishi bacin raina na hanashi ya hakura ba don yana soba ,ban tsaya tunanin wacece yake so ba sai da naga sonta ya kwantar dashi " zuciyarshi na zafi yanajin bakinciki yace"Sai last week na fahimci Zarah ce masoyiyarsa itace yake yiwa tsananin so da ya kasa hakurin rashinta"
Muneera tai saurin kallon WALEED ,WALEED da kanshi ke duke yayi saurin dagowa a razane jin sirrinshi ya fito fili suka hada ido da Muneera ya fara girgizakai hawaye na kara yawa a fuskarshi zuciyarshi na tsananin zafi yace"Ba haka bane, ba ita bace wallahi bana sonta ban taba......"ya kasa karasawa ya tashi dasauri ya nufi bedroom yana matsanancin kuka me tarin bakinciki meyasa daddy zai masa haka?baya tunanin rayuwarshi ?bazai bari ko sau daya ya sadaukar masa da wani abu ba?taya yake tunanin zai zauna da wacce take son daddynshi ?Matar da suka hada shinfida daya dashi?haba..
Ya haye kan gado yana matsanancin kuka yana ganin laifinshi da ya kasa cireta a ranshi tun ranar daya dawo wani irin haushin kansa yakeji yana ganin duk laifin shine,
Muneera ta shiga tsoro da wani irin rudani kallo daya tai ma WALEED ta fahimci karya yake akan maganar da yake na cewa baya sonta ,hawayenta sukai cak tana tuno dawowarshi da fara rashin lafiyarshi ,,
Zarah tundazu take jefar KHALEED da wani kallo zuciyarta na kuna ashe dama baya sonta tausayinta kawai yake?idan har yana sonta bazai taba sakinta akan wani ba zaiyi kishinta zai boyeta ya killaceta wuri daya amma shine ya saketa saboda wani baya duban halin da zata shiga da tsananin son da take mishi,sai da ya gama morewa daita sannan zai saketa?tana mai wani kallon bakin ciki hawaye masu zafi na zubar mata ta fara tuno ranar daya fara sauyawa da maganar da sukayi a kitchen yake cewa zaiyi bakin kokari wurin bawa WALEED farinciki ko zai rasa nashi, da sarkar da ya bata me dauke da W ,
A hankali ta kai hannunta tana laluba W din cikin bakinciki taja sarkar da karfi har seda taji ciwo sannan sarkar ta katse ta saketa kasa tana jin bakinciki ta tashi da gudu ta shige bedroom tai kwance kan bed tana kukan bakinciki da karya mata zuciya da KHALEED yayi,,
Kan KHALEED jikin Muneera yana cigaba da zubda hawaye ,Muneera na cikin rudu tace"KHALEED da ba kai haka ba yanzu miye amfanin sakinta kanaso duk ku rasata ne kome?"
KHALEED na jin ciwon abinda yayi ya dago yana hawaye yace"Inason WALEED ya aureta ne inason sama mishi farinciki"
Muneera ta kura mishi ido tana ganin kamar baya cikin hankalinshi ,
Ya cigaba da cewa "Yana sonta zai kula da ita zai bata dukkan farinciki"
Muneera ta girgizakai tana hango yadda yake zaro kalaman da yake fada dakyar,
tace"KHALEED ka taba ganin anyi haka?wai KHALEED ko ka manta tsananin son da Zarah ke maka ?kana tunanin zata jure rashinka?taya ma kake tunanin WALEED zai iya aurenta bayan ka taba auren ta ?"
KHALEED ya matse lips yace"Kuskurene nayi na aureta amma bazanyi kuskuren cigaba da zama daita ba har dan'uwana ya rasa ranshi saboda bakincikin rashinta ,Mama idan har Zarah na sona zata so WALEED ,WALEED na tsananin sonta kuma nasan bazai dena ba har'abada ina ganin sonta a kwayar idanunshi kuma bakinshi ma ya kasa karyata zuciyarshi"idanunsa suka hasko masa time da yake wet dreem yana screeming yace"Zasu iya kasancewa tare tunda ba haramun bane aurensu"
Muneera ta dafe kanta na matsanancin ciwo taya hakan zai faru ?su waye zasuje nema ma WALEED aurenta ?yasu kawu habu zasuji ?Suna iya ganin kamar ya wulakanta masu yarinya,ita kanta zaran zata yadda da auren?
Yasa hannu ya debe hawayenshi yace"Inason Zarah amma na hakura na barwa WALEED domin nasan bazatai kuka da rayuwa dashi ba kuma batare data haifi zabaya ba irina"
Muneera ta kalleshi tana jin ciwon maganganun shi tace"Kayi gajeran tunani Allah ne me yadda yaso yanzu da kana tunanin zaku haifi zabayan ne ?nima fa ba zabaya bace KHALEED ,ko da ta auri WALEED zasu iya haifa idan Allah ya tsaro masu hakan ,kai baka tunanin halin da duk zaku shiga?kamanta da WALEED ka dubi kanka yanzu wacece zaka aura idan ba ita ba?"
Kanshi kasa yana sauke numfashi sannu saboda ciwon da yakeji yace"Allah na tare dani, shine masanin komi, zai duba lamarina"
Muneera ta girgizakai tana cikin tashin hankali da ganin halin da family dinta zasu shiga nangaba ta tashi ta wuce bedroom,
KHALEED yabi bayanta da kallo yanajin ciwon yau daya da ta fita zakka a rayuwarshi da ta zubda mai hawaye kuma yayine don idan ya fara shaida mata bazata amince ya saketa ba yana lura da ita yana sane da so da kauna da take mishi ko kusa baza a hada data WALEED ba ,,
A hankali ya dafa kujera ya yunkura zai tashi idanunshi suka sauka akan sarkar da Zarah ta katsa ya koma ya duka ya dauketa ya riketa a hannunshi yana kallo zuciyarshi na zafi meyasa ta katseta ko tana nufin bata son dan'uwanshi ?ya daga kai ya kalli bedroom din yanajin bakinciki da jefar da W din domin WALEED ya rubuta nata sunan a jikinshi Wanda bazai samu damar wankewa ko gogewa ba har'abada,
Yanajin tsananin ciwo ya saka sarkar aljihu ya tashi ya fita yana tafiya dakyar ya shiga mota ya nufi gida don yayi jinyar kanshi,
Muneera na shiga bedroom ta samu Zarah kwance tana ta kuka da hawayen bakinciki tana regretting auren KHALEED tana jin inama tabi Murtala yayi duk abinda yake so iyayenta basu mutu ba tana hannunsu suna rayuwarsu a kauye,
Taje ta hau bed din ta medota jikinta tana hawayen tausayinta ta girgiza mata kai tace"Kiyi hakuri Zarah ki dauki haka a kaddararki"
Zarah ta rungumeta ta sake fasa kuka tana ganin KHALEED bai mata adalci ba ko da aure tsakaninta da WALEED bata sonshi bazata taba sonshi ba kuma bazata iya furta hakan ba,
Muneera ta rungumeta tana hawaye tana tapping dinta tana bata hakuri ,
KHALEED na komawa gida ya samu yayi parking yana tangadi kamar zai fadi ya nufi ciki da shigar shi yaja ya tsaya idanunshi jajawur gidan na juya mishi yana kallon falon yana hango Zarah a zahiri tana masa murmushi ,
Ya kara dala ido yana kallonta ya nemeta ya rasa lokaci daya muryar Zarah ta fara amo a kunnuwansa "I love u daddy.... I really do the whole world is empty with out u"
Ya matse kunnuwansa gam ya durkushe awurin yana matsanancin kuka yana fadin "I love u too ....I love u" ya cigaba da kuka awurin yanajin kamar ana kara bude kirjinsa ana kara zuba masa sonta ,
WALEED na kwance yanata kuka yana tunanin yadda akai KHALEED ya gane, HAMEED ya fado masa a rai ya tashi da sauri ya zari key ya fita ya nufi gidansu zuciyarshi na zafi tana fadamai tabbas HAMEED ya fadawa KHALEED wani abu ,
Yana zuwa gidansu ya nufi dakinshi ya banka kofar dakin da karfi,
HAMEED dake zaune yayi tagumi yanata tunanin halin da family dinnasu ke ciki yayi zumbur ya Mike tsaye yana kallon WALEED,
Idanun WALEED jawur ya nunashi yace"Ni zaka ciwa amana?meyasa zaka wulakanta abotar mu? yanzu kaja daddy ya saki Zarah saki ukku saboda ni baka tunanin halin da zasu shiga kaini kadai kasani, meyasa zakaimin haka? "
HAMEED ya fiddo idanu zuciyar shi na ballawa bai taba jin hakan ta taba faruwa ba bai taba kawo daddyn zai iya haka ba wane irin sone daddy kewa WALEED ? anya ko Muneera ta kaishi son shi? Yana tunanin ya girgizakai yace"Wallahi bani na fadamai ba bansan yadda akai ya gano ba yazo de ya sameni in rakashi gidan budurwarka nace bansaniba daganan ya fara maganganun dana fahimci yasan komi kafin yazo, amma ni babu ruwana aciki duk yadda nakeso in temakeka tunda naga an daura aure na hakura ina ganin aikin gama ya riga ya gama"
A zafafe WALEED yace"Bai gama ba"ya nufi bed ya zauna ya dafe kanshi da hannu biyu yana murzawa sosai yana hawaye yanajin ciwo yace "sai bayan da ta zama cikakkiyar matarshi sannan ya barmin ita,miye amfanin boyon da nake ? sai yanzu lokacin da bai kamata ba sannan zai sadaukarmin da ita ..bazan iya aurenta ba bazan kara kallon inda take ba koda ba aure tsakanin su"
HAMEED ya kalleshi yanajin tausayin su duka biyun yaje ya zauna ya dafa kafadarshi yace"Kayi hakuri kai addua Allah ya sa hakane mafi alheri "
WALEED ya wurgamai wani irin kallo yace" saki ukku ne alherin? Zarah tace ya saka "sai yayi shiru jin bakinshi ya kirata tashi,
Cikin sanyin murya HAMEED yace"Banga laifin daddy ba saboda sonka ne yasa yayi haka kadena ganin laifinshi saboda kai ya katse jindadin rayuwar shi"
WALEED yaja tsoki yana jin kululun bakincikin zarar bata gama warkewa daga duniyar azaba da ya kaita ba ya saketa,
Ya tashi ya fita ya koma mota ya nufi gidan yana huci, da yana jinyar zuciyarshi ne na rashinta amma yanzu bakincikin abinda akai mata ne yake kona zuciyarshi,ya koma gida yayi kwance zuciyarshi na radadi ,,
Muneera ta rarrashi Zarah har tai shiru sukai shiru sunata tunani idanun Zarah lumshe tana tuno time da KHALEED ke sex daita tana jin mugun zafi amma tsananin sonshi bai bari ta iya Ihu ba hakan kuma baisa tadena son kasancewa dashi ba amma shine ya gujeta yabarta time data kara tsunduma cikin soyayyar shi lokacin da take matukar son kasancewa dashi,
Tunanin da sukeyi basu fahimci rana tayi ba saide sukaji kiran sallah Muneera ta tashi tayo alwala ta fuskanci akibla bayan ta gama sallah ta daga hannuwa tana addua tana hawaye tana tausayawa rayuwarta domin sunyi wannan abun amma duk akanta zai kare saboda itace mahaifiyarsu ,
Zarah ma dakyar ta tashi tai sallah ta koma ta kwanta ita kadai tasan tsananin zafin da zuciyarta ke mata ta sani nan gaba kadan zata shiga halin da yafi wannan da take ciki a halin yanzu,
KHALEED ma dakyar ya tashi yayi sallah ya shiga bedroom yasha magani yana hana kanshi kallon gadan amma saida idanunshi suka kalla take ya rika hango Zarah dashi a kwance samanshi yana romancing dinta suna kissing juna,
Ya matse lips dinsa ya rumtse ido yana juya kai kwata_kwata baya ganin dacewar hakan bayason yana tuno abinda ya shiga tsakaninsu saboda nangaba kadan zata zama mallakin kaninshi hakan bai dace ba Sam,
Cikin raunin zuciya ya fita daga bedroom din yaje yayi kwance tsakiyar falo akan carpet saboda samun sauki da kwanciyarshi sai jin kamshinta ya rikayi yana tasowa ya bude ido da hanzari yana tuno ranar da suka kwanta akanshi da hannuwansa da suka rika wasa da breast dinta yana tuno taushi da dadin ,yayi saurin tashi zaune hawaye masu zafi suka zubomai to ina zai tafi ne yaji saukin kewarta?gidansu ya masa nisa don baya son ganin halin da take ciki ko haduwa da ita,anan din kuma duk inda ya duba ita yake gani da sautin muryarta,
Ya cusa kanshi tsakiyar cinya yana nishi sama_sama yana tsananin kewar matarsa amma baya regretting barwa jininshi ita domin yasan Zarah tauraruwace me haske dake haska duk inda ta shiga yasan kaninshi zai kasance cikin farinciki da jindadin rayuwa idan yana tare da ita,
Muneera na zaune akan carpet har laasar tana ta adduoi bayan tayi laasar ta gama addua ta juya kai ta kalli Zarah tana tsananin tausaya mata ta tashi ta shiga kitchen jikinta ba karfi ta samu tai musu indomie da kwai badon ita taci ba sai don diyanta, ta zubo a plate ta shigo ta samu Zarah kwance ta zauna gefenta cikin sanyin murya tace "Zarah ga abinci"
Zarah ta bude idanunta dake jawur ta kalleta ta medasu ta lumshe ta girgizakai don bata jin cin komai,
Muneera tasa hannu ta jawota jikinta kamar wata baby ta hadata da jikinta ta rungume ta dauki fork ta debo indomin ta kai bakinta,
Zarah ta fara gunjin kuka ta bude baki ta amsa tana taunawa tana hawaye,
Muneera na jin kamar tai ta mata kuka ta sani KHALEED bai kyauta mata ba tace"Kiyi hakuri kinji diyata "
Shiru kawai Zarah tayi a hakan tana ganin tana hakuri sosai da ba haka ba da yanzu zuciyarta ta buga masoyinta ne ya saketa saki har ukku time daya ,
Muneera nata rarrashi ta danyi cokali hudu ta kauda fuskarta Muneera ta tashi ta dauko mata paracetamol ta bata don ba shakka tasan dole kanta na ciwo bama shi kadai ba har da zuciya....
Zarah ta koma ta kwanta ta lumshe idanunta tana kewar KHALEED amma tana tsananin fushi dashi don bazata kirashi tsana ba don tasan ko taji haka a zuciyarta to cikin kankanin lokaci soyayyar sa zata dawo fill,
Muneera ta tashi ta nufi bedroom din WALEED yana kwance hannunshi dafe da heart dinshi idanunshi lumshe ,
Tana mai kallon tausayi taje ta zauna gefenshi tace"ka tashi kaci abinci"
Ya bude ido ya kalli plate din ya kalleta ya meda idonshi ya rufe cikin dusashshiyar murya yace"Bazan iyaba"
Muneera na tausayin kanta tace"WALEED idan baka ci abinci ba me zakaci?dan Allah ku rika tausaya min "
Ya matse lips yace"Mama bazan iya ba kiyi hakuri plss "
Ta tashi tsaye da plate din hannunta ta fita zuciyarta na zafi ta nufi hanyar kitchen ta kalli plate din ta kalli wayarta a hankali ta tafi ta dauka ta kira KHALEED,
KHALEED na kwance duniya ta masa zafi ga zafin jiki ga na zuciya ya dauka jikinshi sanyaye,
Muneera tace "Kazo kaci abinci "
Yayi shiru yanajin son mamarsa da jin haushin bata mata rai da yayi yace"Naci abinci tun dazu "
Yana fada ta gane karya yake tasan dukkansu bazasu iya cin komi ba a wannan halin tace"To amma ka kula da kanka"
Zarah ta fadomai a rai kota ci abinci? yanajin kamar ya tambaya ya kasa harta kashe wayar tana kashewa yabi wayar da kallo pic din Zarah dashi ya bayyana tana cikin uniform sunyi selfie su biyu a moto suna cikin farinciki da murmushi a fuskokinsu,
Batare da ya zurfafa kallonta ba ya shiga pic dinshi yayi deleting dinsu duka ya shiga message duk yayi clearing ya meda kanshi kasa yana hawaye zuciyarshi na radadi ya matse lips yace "Plsss forgive me ki yafemin Zarah ki kuma manta dani..."
Muneera ta meda abincin taje a fridge tasha fresh milk me tsananin sanyi ta koma bedroom ta zauna ta kurawa Zarah idanu tana tunanin yadda zata fadawa iyayenta abinda kenan da wane ido zataje masu?
Da dare yayi duk inda KHALEED ya wulga Zarah yake gani cikin kayan bacci tana sakar masa murmushi me sanyi ya koma tamkar wani dan shaye_shaye da abubuwa ke masa gizo ya tashi dakyar ya fita tsakar gidan ya zauna kan wata kujera ya lumshe ido cikin gajiya da galabaita bacci ya kwashe shi,
WALEED bai iyayin bacci ba yanata tunanin wane hali KHALEED ke ciki Zarah kuwa kwance take idanunta lumshe wani irin bacci ke fizgarta sai kuma ta farka a tsorace Muneera na kan carpet tana ibada har gari ya waye,
Tana samu ta bawa Zarah tea ta dansha ta kaiwa WALEED ta dawo falo ta kwanta tana jin zazzabi a jikinta,
Bata dade da kwanciya ba KHALEED da yayi jaruntar fita office don rage kewar Zarah ya kirata ta jawo wayar ta dauka idanunta lumshe,
KHALEED yace"Ina kwana mama?"
Tace"Lafiya lau"
Yace"Ya kuke ya jikin WALEED? "
Muryarta sanyaye tace"Alhamdulillah"
Yayi shiru yanaso ya tambayi zarah ba hali yace"Sai anjima"
Ta kalli wayar wato bazai zoba?ranta na suya ta ajiye ta dukunkune jikinta wuri daya,tana kwance har 12 WALEED da Zarah bawanda ya leko bare su san halin da take ciki ta tashi dakyar ta dauko magani tasha karfe 1 ta shiga kitchen tana hada masu abinci,
*****
Bayan sati
Haka suka cigaba da rayuwa duk sunbi sun rame WALEED yana daki kullum ko fita ya dena saide HAMEED ya lekoshi ya tafi Zarah ko ko wanka batason yi saboda data shiga take fara tunanin KHALEED yadda yake tafiyar daita dakyar Muneera ke sata tayi ba din taso ba,
KHALEED ko ramar tashi ta wuce misali baisan haka zai sha wuya ba kafin ya cireta ba yayi zaton da zaran ya saketa zai manta daita ya hakura Ashe abun ba haka yake ba ,,
Muneera na zaune tagama nazarin zuwa ta sanar da iyayen Zarah don kar suji labari , bata damu ba ko zasu kwaceta daga hannunta don halin da take ciki yana bata tsoro amma bata fatan haka saboda tana jinta kamar diyar cikinta ta saba da ita sosai,
Ta dauki waya ta kira KHALEED,
Ya dauka yayi shiru,
Tace "Gobe zan tafi kauyensu Zarah inaso ka dawo gida kafin na dawo"
Gabanshi ya fadi zama gida gashi ga Zarah ga WALEED ranshi na zafi yace"To zanzo"
Tace"Allah ya bada iko"ta kashe kiran don tasha neman shi yaki zuwa,
KHALEED yayi zaune yana nazari ya azabtu da yawa kewar family dinshi ta dameshi gwara yaje yagansu ya samu peace of mind,
Karfe 8 ya shiga gidan da mota ya nufi ciki zuciyarsa ba bugawa maybe ya fara arba da Zarah ,,yana shiga ya hangi Muneera zaune kan kujera ta buga tagumi kallo daya ya mata ya tsorata da halin da take ciki duk ta rame cikn hanzari ya karasa wurinta ya zukunna yace"Mama baki da lafiya ?"
Ta kalleshi tai murmushi me ciwo tace"Ta yaya zanyi lafiya bayan duk yarana basu lafiya? dubar ka kamar ba KHALEED dina ba ka koma wata halitta daban"
Ya kama hannunta ya rike yana matse lips zuciyarsa na radadi ,
Muneera tace"Ka shiga ka kwanta nide tafiya zanyi dan Allah ku kulamin da Zarah ku duka "
Ya jinjina kai yana jin hawaye cike da idanunshi ,
Ta tashi ta wuce shi ta shiga bedroom ta samu Zarah kwance da kullum jin jikinta take yana sauyawa wani lokaci taji yayi zafi wani lokaci yayi sanyi sosai tana jin wani jiri_jiri da ciwon kai wata ranar taita bacci watarana ya kauracewa idanunta batasan wani ciwo bane ta danganta haka da rashin mijinta da kewarshi,
Muneera ta sameta ta zauna ta rike hannunta tace"Zarah ki daure ki rika cin abinci kina fita waje ,,gobe zanje kauye a can zan kwana wanshekare na dawo"
Zarah ta daga ido muryarta very cool tace"Allah ya kiyaye Mama Allah ya medoki lafiya"Sam bata kawo kauyensu zaa ba,
Muneera tai murmushi ta shafi kanta tace"Bazaki kewata ba?"
Zarah ta dan fadada fuskarta don murmushin baya zuwa ta girgizakai,
Muneera ta rungumeta tana jin kamar su tafi tare amma bazaiyu ba yadda ta ramen dole ko iyayenta basu so su amsheta daga hannunta ,
KHALEED ya dade zaune falo yana fatan fitowar Zarah ya samu ya sanyata a idanunshi yaji sanyi amma shiru zuciyarsa na zafi ya tashi ya nufi ciki,
Ya shiga ya samu WALEED kwance idanunshi bude yaje ya hau bed ya zauna,
WALEED ya kara daure fuska yanajin haushin shi ya juya mai baya ,
KHALEED ya kalli bayanshi yayi murmushi me ciwo yasan dole yaji zafin sakin a matsayinshi na masoyinta wannan ma yakara tabbatar masa da tsananin kaunarta da yake da ya iya fushi dashi,
Ya kwanta ya lumshe ido yana jin saukin damuwarshi ganin halin da WALEED din yake yanzu bai kai nada ba an samu cigaba sosai , a hankali yace "WALEED kana lafiya?"
A dakile WALEED yace "a,a"
KHALEED ya bude ido ya kalli bayanshi yace"Allah ya baka lpy"ya sake rufe idonshi,
Wansafe tunda wuri muneera ta shirya ta samu Zarah ta dansha kunu da tayi ta fita ta shiga bedroom dinsu KHALEED dukkansu basu kallon juna wannan ya kalli gabas wannan ya kalli yamma muryarta sanyaye tace"Zan tafi ga Zarah nan na barmaku amana ku kalamin da ita kafin na dawo idan kuma Allah bai min dawo ba ina maku fatan alheri "
Sukai saurin mikewa suna kallonta hankalinsu tashe tana jin zafin yadda ta samesu ta juya ta fita,
Jikinsu sanyaye suka biyo bayanta ta shiga wurin Zarah ta dauki jikkarta tana dan murmushi tace"Sena dawo ko Zarah ?ki kula da kanki sosai "
Zarah ta sauko da kafafunta tana jin jikinta ta shige jikin Muneera ,suka fita tare suna fita falo ta fara jin kamshin KHALEED ta lumshe ido tana jin dama ta ganshi ta rungume shi ta shaki kamshinshi ko ta samu natsuwa suka fita waje ,
Su KHALEED na bakin motar idanunsa suka sauka akanta zuciyarshi tai wani irin dokawa ya matukar tsorata da ramarta ya kalli WALEED yana ganin laifin sa ne ya kauda kai ya cije lips,
WALEED ma na ganinta ranshi ya baci zuciyarsa na ciwo ya kalli KHALEED yana ganin laifinsa duk shine yasa ta a wannan halin,
Idanunta lumshe har suka kai bakin mota jin kamshin KHALEED ya baje wurin ya sata bude ido ta saukesu akanshi yana budewa Muneera mota da ganinshi ba karamin damuwa yake ciki ba amma meyasa bazai nemeta ba?ta dauke idanunta tana jin haushi a hankali tacewa Muneera "Allah ya kiyaye Mama"
Muneera ta shafi kanta tace"Ameen ki kula"ta saketa ta shiga mota,
Zarah bata jira komi ba ta nufi ciki tun kan hanya ta fara zubda hawaye zuciyarta na ciwo ta shiga bedroom ta zauna tana kuka zuciyarta na radadi yau gata ga daddynta amma bai ko kalleta ba bare ya nuna ya Santa,
Muneera kuwa na shiga driver yaja motar yabar gidan,
WALEED ya juya ciki KHALEED nata kallon motar ya nufi ciki ya shiga dakin ya samu WALEED fuskarshi bawalwala yace"Office zan fita ka kula da Star"
yana gama fada ya juya ya fice,
Zuciyar WALEED ta fadi yana tunanin ina KHALEED yasan duk Wadannan ?ya akai yasan itace star? Ya kalli gefen kafadarshi inda star din take ya yamutse fuska sakamakon zuciyarshi dake zafi,
Zarah nata kuka zazzabi ya sauko mata ta shige cikin bedsheet ta rufe tana cigaba da zubda hawaye,
KHALEED ya koma gida yayi wanka ya shirya ya fita aiki yanata nazarin WALEED miye nufinshi yana nufin ya dena son Zarah ne kome?ya fara aiki yana tunani har azahar ya tuno Zarah yanzu ya kamata taci abinci ya fita ya siyo abincinsu su biyu har da danshi WALEED ya nufi gidan ya shiga ciki yayi tsaye yana kallon dakinta yasan idan ya kirata dole zai kalleta maybe ma har magana ta hadasu Wanda hakan ba karamin damuwa zai shiga ba a hankali ya juya ya nufi kitchen ya ajiye abincin ya juya ya fita yana fatan ta fito ta dauka,,
Zarah kam tana cikin ciwo bata fito ta nemi abinci ba tana tunanin KHALEED na kusa zai shigo ya kula da ita amma shiru ,
WALEED ko wanka yayi ya fita daga gidan gabadaya baiko kalli inda take ba shi a dole sai sun tabbatar cewa baya sonta ,,
Muneera sunsha tafiya tana ta tunanin yadda zata fuskanci iyayen Zarah da wannan abun kunyar har suka isa ta fito ta shiga gidan jikinta sanyaye,
Tana shiga gidan Ladingo na daka ta ajiye tabaryar tana murna tace"Maraba da Hajiya sannunku da zuwa "ta nufi dauko mata tabarma,
Muneera ta fara yar faraa jikinta sanyaye tabi bayanta Ladingo ta kawo tabarma ta shinfida mata ta zauna ta debo ruwa ta kawo mata ta zauna tana murmushi ,
Muneera ta dauki ruwan tasha ta ajiye ,
Cikin doki Ladingo tace" Ya amare? dafatan suna lafiya ? dama bari mu kayi su danyi watanni sai muje dubosu"
Gaban Muneera ya fadi tai shiru ta kasa cewa komi,Ladingo ta nazarci fuskarta tana ganin damuwa akai da tsananin ramar da tayi ta shiga zullumi don dagani ba lafiya ba,
Muneera batace komi ba tana jiran dawowar kawu Habu sai dare sannan ya shigo yana ganinta ya fara murmushi suka gaisa ya shiga ciki,
Bayan yaci abinci suka fito suka zauna wurinta tana cikin zullumi da faduwar gaba,
Kawu Habu yace"Hajiya tunda kikazo bakice komi ba gashi kamar ba lafiya ba wurinku"
Hawaye suka taru a idon Muneera batasan yadda zasu dauki maganar ba bakinta na rawa tace"Da farko ina mai baku hakuri akan abinda zakuji yarane ka haifesu baka haifi halinsu ba bada son raina hakan ya faru da Zarah ba saboda inajinta kamar yar cikina"
Suka kasa kunne suna kallo da saurarenta,
Muneera ta sunkuyar da kai tace"Sati daya kenan da KHALEED ya medo Zarah gida bayan ya mata saki ukku"
Su kawu suka firgita suka fara sallallami suna jin abun kamar ba gaske ba basu taba tsammani ba duk suka sunkuyar da kai sukai shiru,
Hawaye suka zubowa Muneera tana hango tashin hankali da suke ciki tace"Kuyi hakuri nasan bai kyautaba amma shima bai kyautawa kanshi ba domin yanason Zarah ganowar da yayi itace dan'uwanshi keso shiyasa ya saketa, banji dadi ba nayi kokarin ya mayar da ita amma yaki kuyi hakuri dan Allah "
Kawu na cikin mamaki yace"ho umm !!!" ya rasa me zai fada,
Muneera tace"Kuyi hakuri karku amshe Zarah daga garemu duk muna sonta a kusa damu dan Allah "
Ladingo tace"Hajiya daya saketa shin dan'uwanshi na iya auren ta? "
Muneera ta gyada kai tana jin kunya da nauyi,
Ladingo ta dan kalli Habu tace"idan hakane kidena damuwa tunda abinda yayi KHALEED shi yayi WALEED tunda har yana sonta saiya aureta shikenan "
Kawu Habu ya kalleta yace"Amma ni ban taba jin inda akai haka ba"
Ya kalli Muneera yace " Hajiya Naji dadi nagode da yadda kuka temake mu kuka kula da Zarah amma yanzu inaso na dawo da ita gida saboda zamanta anan dinma bai da wata matsala"
Muneera ta kalleshi tasan yana da gaskiya amma kuma rayuwar diyanta takeji tace"Kayi hakuri baa kyauta muku ba amma kada ku amshe Zarah a wurina na rokeku"
Ladingo na jin tausayinta tace"Habu a duba lamarin nan Hajiya na son zama da Zarah idan har saboda ita ka bashi auren Zarah yanzu ma zaka iya ba dayan danta Zarah idan kuma saboda shine to shima abinda yake so kenan dan'uwanshi ya samu lafiya ka duba ka gani ka temaka"
Kan kawu Habu kasa ya nata nazari yanzu in yamedo Zarah nan kauyema taci baya kuma duk wanda zai aureta saboda gadonta zai aureta idan tayi saa ta sami saurayi idan batai ba ta auri me mata ta cigaba da shan wuya da dakau,
Ya dago ya kalli Muneera yace "To yanzu Hajiya kin amincene dayan danki ya aureta?"
Muneera ta daga kai tana fatan yace ya yarda
Yace"Tohhh Zarah de amanace wurina da wurinku dan Allah Hajiya ku rike amana kada azo wani abun ya kara faruwa idan ya faru dole na daukota na kula da ita"
Muneera na hawayen farinciki tace"Nagode nagode sosai insha Allah ba abinda zai faru don zamu kula da ita"
Ya tashi zuciyarsa na zafi ya shige daki sam baiso hakan ba domin bai taba ji anyi haka ba,
Ladingo na zaune tace"Hajiya kiyi hakuri kidena hawaye ai Zarah yarki ce "
Muneera tace"Nagode sosai da temakon ki gareni"
Ladingo tai murmushi,
Zarah na kwance tun kunun safe bakomi cikinta ga masassara ga wani irin ciwo da cikinta keyi tana cikin wahala tai ta hawaye zuciyarta na zafi ganin bawanda ya kula da ita cikin su,
KHALEED ko daya dawo yaga abincin ranshi ya soyu yana tunanin tana fushi dashi kamar yadda WALEED keyi ya ajiye na dare daya siyo ya shige ya kwanta yana tunanin ta,
Kafin gari ya waye Zarah ta galabaita numfashin da takeyi ne kadai banbancinta da matatta kwance kawai take amma ko tashi bata iyayi saboda galabaita idanunta lumshe hawaye na dan bin bayansu time to time,
KHALEED ya tashi fita aiki ya tsaya ya kalli dakin jikinshi sanyaye yanason ganinta ya tafi office,
WALEED na cikin gidan kuma yasan ba kowa amma baije ba don yana mata kallon Matar yayanshi ,
Muneera ta tashi tana ta jin nauyi tasha fura ta kara musu godiya ,suka fito yi mata rakiya har ta Shiga mota kawu Habu yace"mungode sosai Allah yabada ikon rike amana"
Muneera tai murmushi me ciwo don bataji dadin maganar ba Ladingo na daga mata hannu driver yaja motar,
Su Ladingo suka koma sukai jungum suna kewar Zarah da son ganin halin da take ciki,
Muneera ko tagama gane badon Ladingo ba da Zarah tabar hannunsu tana cikin mota hankalinta ya koma gida batasan wane hali zata iske gidan ba tana kagare su isa ,
Suna tafiya motarsu ta samu matsala wanda ya kara musu jinkiri driver ya samu ya gyara suka dauki hanya,
Har Karfe 6pm basu kawo ba ana tashi aiki KHALEED ya nufo gida ya shigewarshi ya zauna yana wani aiki a system dinshi ,
6:30pm su muneera suka iso ta bude motar ta fito ta nufi ciki da sauri zarar kawai takeso ta gani hankalinta ya dan kwanta,
Tana shiga ta bude dakin ta hango Zarah sheme akan bed a razane tace"Innalillahi wainna ilaihi rajiun!!!! "Da karfi ta nufeta da sauri,
Ta haye gadon ta dagota bata ko numfashi ,ta fashe da matsanancin kuka duk jikinta na rawa na ganin halin da take ciki idan har ta mutu ta shiga ukku bazata yafewa kanta ba tana cikin kidima da kuka ta fara kwala masu kira " KHALEED !! KHALEED !! WALEED... Zarah !!!"
A lokaci daya KHALEED da WALEED suka baza da gudu falo suna zuwa kofar dakin duk suka ja suka tsaya suna kallon juna ,
WALEED ya juyar da kai jikin shi na rawa sam bazai iya shiga ba,
KHALEED ya karasa ciki duk jikinshi na rawa ya samu Muneera rungume da Zarah tana kuka,
Hankalinshi tashe ya haye gadon zuciyarshi na matsanancin bugu hannuwanshi na rawa ya amsheta yana dubata ganin bata ko numfashi yasa ya fara zubda hawaye ya dauketa jikinshi ya sauko a gadon ya nufi mota da gudun tsiya,
WALEED na tsaye sede gani yayi KHALEED ya fito da Zarah ya wuce da ita kamar matatta zuciyarshi na zafi ya koma daki yayi zaune ya fara kuka,
Muneera na jin kamar zata zube tabi bayan KHALEED ta shiga ya dauki hanyar asibity da matsiyacin gudu yana gudu yana kuka zuciyarshi na zafi yanaji shima mutuwa zaiyi idan har Zarah ta mutu ,
Muneera na rike da ita tana kuka tana kallon fuskarta tana jin matsanancin tausayinta har suka isa yayi parking ya fito yana cigaba da kuka ya dauketa ya shiga asibitin daita Muneera na biye suna shiga Nurses suka amsheta suka shiga da ita don ceto rayuwarta,
Suna tsaye sunata hawaye har tsawon lokaci sannan doctor ya fito suka kutsa kai ciki don ganin halin da take ciki suka sameta kwance drip na shiga hannunta da gudu ga wasu ledoji bakwai a gefe, Muneera tai zaune ta dafe kai tana kuka KHALEED ya kurawa fuskar Zarah ido yana jin tsananin tausayinta tayi baki ta rame fuskarta ta fada gashinta hargitse kamar ba zararsa ba kyakkyawa suna zaune suna hawayen tausayinta doctor ya turo kofa ya shigo yana kallonsu ,
Ya tsaida kallonshi gun KHALEED yace"Kaine mijinta?"
Bakin KHALEED na rawa yace"a,a.. eh"lokaci daya
Likitan yace"Matar ka tana cikin mawuyacin hali tana dauke da ciwon zuciya, bp dinta ya hau sosai tana da fever da olcer tana kuma dauke da ciki na tsawon sati biyu da kwanaki"
A razane KHALEED da Muneera suka kalli juna zuciyar KHALEED na kuna ya sunkuyar da kai ya dafe zuciyarshi da take tsananin ciwo da mugun bugawa ,
Muneera ta cigaba da kallonshi hawaye na ziraro mata tana cikin tashin hankali,
Likitan yace"Sakamakon barinta da yunwa da akai cikin yaso zubewa ,tana bukatar total care dinku saboda gudun zubewar cikin da kuma rasata gabadaya"yana gama fada ya juya ya fita,
Zuciyar KHALEED na tsananin radadi kalaman doctor na masa yawo akai Zarah na dauke da cikinshi ya fashe da kukan bakinciki da......
Toh fa !!! Zarah is pregnant shin zata haihu? ko cikin zai zube?zai medata ne? Ko zata auri WALEED ?yaya KHALEED zai cigaba da rayuwa?ko mutuwa zaiyi😜,ya rayuwar tasu zata cigaba ???? Akwai cakwakiya sosai... Sai mu hadu bayan sallah😊
Aslm...ina ma fans din shigar sauri fatan alheri sakamakon Ramadan ya kusa kuma littafin da saura shiyasa zan dakata anan sai bayan azumi idan Allah ya kaimu saimu cigaba, ina mana fatan alheri Allah ya kaimu watan ya karbi ibadunmu yasa muna daga cikin yantattun bayi yasa muna daga cikin wadanda zasuga karshen shi,Nagode sosai 😊
Ranar idi zan baku barka da sallah idan mai komi ya kaimu ya kuma bani iko💃🏻
*SHIGAR SAURI*
Painful love story
Romance special
0 comments:
Post a Comment