Ya fashe da kukan bakinciki da tausayin Zarah yana cikin rudani da tashin hankali,kuskure daya yayi na kusantarta amma har ciki ya shiga?yanzu yaya zayayi da wane ido zai kalli Zarah? wane hali WALEED zai shiga ?Sam baya ta kanshi domin yana ganinshi a matsayin Wanda yayi babban kuskure ,,
Kuka yake sosai kanshi kasa ya dafe jijiyoyin kansa dake barazanar katsewa da hannu biyu,gabadaya kanshi ya kulle baisan me zai faru ba bayan bullowar cikin,,
Idanun Muneera dake zubda hawaye na kyam a kanshi zuciyarta na harbawa tana jin takaicinsa akan abinda ya aikata ko kadan batai wannan tunanin ba na Zarah na iya daukar ciki kuma bata taba tunanin zasu banzatar da ita ba bayan ta tafi idan da cikin ya zube fa?idan da wani abu ya sameta fa?
Cikin kunar zuciya muryarta na sarkewa tace"Dole kai kuka KHALEED saboda kafara ganin sakamakon abinda ka aikata, na tafi na bar muku Zarah amma ace bawanda ya kula da ita bawanda ya ko damu da duba halin da take ciki ?kwana guda zungur batare da abinci ba"
KHALEED ya rage volume din kukanshi hawaye masu zafi suna zubo masa domin yana son Zarah ya damu da ita fiye da tunani, saide bazai iya kusantarta ba hakan zai fama mishi ciwon sonta kuma bazaiso WALEED ya fahimci tana ranshi ba.
Muneera na sheshsheka tace"Bansan wadanne irin zuciyoyi gareku ba idan har WALEED bai dubota ba kai bazaka dubota ba?Zarah ce fa matarka ,diyarka ,kanwarka amma baka damu da sanin halin da take ciki ba don kawai tunaninka ya nuna maka WALEED na sonta "
Numfashinta na daukewa ta cigaba da cewa "Kan ka kawai kasani bakasan damuwar marainiya kuma mai sonka ba ,da WALEED ne nasan bazaka iya kwanciya batare da sanin halin da yake ciki ba"
KHALEED ya fara wani kukan kanshi kamar zai fashe saboda azabar ciwon da yake cikin kuka da raunin murya yace"Kiyi hakuri Mama dan Allah ki gafartamin"
Muneera na jin bakinciki da kakkausar murya tace"Zarah zaka roka saboda itace kaiwa laifi da ya kusa sanadiyyar rayuwarta da dan cikin ta ,kuma inaso kasani da zaran Zarah ta samu sauki zaka medata dakinta saboda da kai ya kamata tayi rayuwa saboda kai take so kuma take matsayin matarka dake dauke da danka ko yar ka a cikinta "
Ya matse lips zuciyar shi na radadi ya fara girgiza kai bazai iya cigaba da rayuwar aure da wacce yasan dan'uwanshi na so ba.
Muneera tace "Nade fadamaka agabanka WALEED yace baya sonta don haka baya sonta bawanda zai masa dole"
KHALEED ya dago jajayen idanunshi dake jike da hawaye yana kallonta, time da WALEED ya karyata shi yasan cewa itama ta fahimci karya yake amma yanzu jin cikin harta sauya ,ko kadan bazai iyaba, bazai iya kara zama da Zarah a matsayin mata ba saboda itace zabin WALEED dinsa.
Dakyar ya bude baki yace"Mama...WALEED bazai..."
Ranta bace Tace"kadena kiramin WALEED anan Zarah zaka kira itace kamayar abin tausayi da kake kokarin rusawa rayuwa"
Tsananin zafin da zuciyarsa keyi bai iya cewa komi ba sai hawayen da yake cigaba da yi yasan bazata fahimci yadda yakeji ba yana son Zarah sosai yana son cikin jikinta amma wajibi ne ya hakura da ita, da adane yaji Zarah nada ciki zaifi kowa murna amma yanzu baya farinciki dashi ko kadan saima wani nauyi da kunya da suka dabaibaiye shi. Bayason ta zauna da cikinshi na tsawon lokaci harta haihu sannan dan'uwanshi ya aure ta, bayason hakan ta faru yaso nan da dan lokaci tagama idda WALEED ya aure ta amma yanzu bai ki cikin ya fita ba saboda WALEED ya samu damar aurenta cikin kankanin lokaci batare da sauyawar wani abu daga jikinta ba batare da ta haifi zabaya ba batare da burin danuwanshi ya dade bai cika ba,
Suna cikin haka likita ya shigo ya isa gaban gadon da take har ruwan dake shiga sun kusa karewa ya kara gudunsu suka karasa shigewa ya sauya wata ledar ya kalli KHALEED yace "Ya kamata akawo abinci me gina jiki da madara da fruit da ruwa kafin ta farka don zata iya farkawa kowane lokaci da zaran ta farka a tabbatar ta samu abinda ta ci ko ta sha"
KHALEED yayi wa maganar tunkan yayi yunkurin tashi Muneera ta tashi ta fita sosai taji haushin abinda suka aikata na barin Zarah da yunwa dole ta nuna masu bacin ranta,
Tana fita doctorn ya fita KHALEED yabi kofar da kallo zuciyar shi na zafi yasan dole Muneera tai fushi dashi shima kanshi haushin kansa yakeji.
A hankali ya juyo da fuskarshi kan Zarah idanunta lumshe tana meda numfashi a sannu, yanajin sonta da tausayinta lokaci daya hannunsa na rawa ya kama nata,sabbin hawaye suka gangaro masa a hankali yace "I'm very sorry Baby I'm really sorry" ya karasa da yiwa hannun nata kiss.
Ya zame hannunsa yanajin dama bata shigo rayuwarsu ba da duk hakan bai faru ba zai auri mata daban danshi ma ya auri tashi masoyiyar but zuwanta duk sun fada kogin sonta ,ko da yaushe yana fifita farincikin danshi akan nasa, ko da cikinshi jikinta bazai maidata ba don yana da yakinin WALEED bazai wulakantata ba zai so dan cikinta zai kula dashi kamar nashi yaran,
Ya sunkuyar da kansa kasa tuno babban kalubale da aikin dake gabansa WALEED yana fadin baya sonta itama tana nuna batason shi kuma Muneera ta umarceshi ya medata dakinta.
Muneera nashiga gida kai tsaye ta nufi kitchen kafin ta shige ciki kunnuwanta suka fara juyo mata sautin kukan WALEED taja ta tsaya tana kallon wurin, tana yamutsa fuska ta nufi dakin tana mamakin kukan me yake ,
Tana zuwa bakin kofar dakin taja ta tsaya tana juyo sheshshekar shi tana jin haushinsa a hankali ta tura kofar ta shiga ,da budewarta WALEED yayi tsitt ya fara goge fuskarshi da bedsheet yana sunne kai kasa,
Ta tsaya ta kare masa kallo kamar yanaso ya nuna ba kuka yake ba sai tayi kamar bata fahimci komi ba a hankali tace "Kamar sautin kuka na keji?"
Ya dan kalleta itama idanun jawur dagani tasha nata ya girgiza kai yafara dan tari sannan yace"Ciwona ne ya dan tashi tundazu naketa tari"
Ta kalleshi sosai sarai tasan matsalarshi a hankali tace "To kasha magani Allah ya sawwake" tana gama fada ta juya ta fita ta rufe mai kofar ,
WALEED ya kwanta hawaye na sake bin fuskar shi zuciyarshi na radadi yana ganin duk daddynshi ne yasa star dinshi cikin wannan mawuyacin halin, ya matukar tsorata da yadda ya fito da ita lifeless, yana fa sonta sosai amma ya zabi bar masa ita domin ya samu farinciki meyasa zai ki kulawa da ita?
Muneera kuwa fasa shiga kitchen tayi tana jin haushi da takaicin WALEED wai Zarah yakeso kuma har yanzu yana sonta, ta matse face,koma de yane dole ya hakura da ita saboda Zarah na dauke da ciki da tayi tunanin zaiyiwu ya aureta amma yanzu bame yiwuwa bane dole ta koma gidanta.
Dakinta ta shiga ta dauki wasu kaya da jikkarta ta fita ta shiga mota driver yaja suka fara tsayawa suka siyi abinci da su fruits sannan suka nufi asibitin,
KHALEED na zaune ya zubawa Zarah ido yana jin matsanancin tausayinta da kunyar farkawarta don bai kyauta mata ba .Muneera ta shigo dakin ta matsa ta ajiye kayan hannunta ta kalli ledojin ruwan taga har ankara saka daya ta zauna kan seat tana kallon Zarar,
KHALEED nata kallon fuskarta da take daure yana jin ciwon bata mata rai da yake ko da yaushe don yasan zata kara fushi dashi sosai bayan sallamarsu,
Dakin shiru na wani lokaci duk idanunsu na kan Zarah ta fara dawowa hayyacinta a hankali ta fara kokarin bude idanunta ta samu ta bude su ta rufe ta sake budewa tana ganin biji_biji ta dora su akan KHALEED ,duk time da ta ganshi tana jin farinciki amma yau din tana ganinshi gabanta ya fadi a hankali ta meda kallonta gun Muneera batai tunanin ganinta ba don batasan yaushe ta dawo ba Muneera ta matso ta rike hannunta tace"Sannu Zarah Allah zai baki lfy"
Hawaye suka cika idon Zarah tai saurin meda idonta ta rufe tana kukan zuci zuciyarta na ciwo tana jin kamar tai ta kururuwa ko zata samu saukin ciwon da take ji,
Duk yadda taso ta rike kukan ta kasa tafara rera kuka meban tausayi da karya zuciya,
Hawayen tausayin marainiyar suka zubowa Muneera ta kalli KHALEED tana hawayen tana nuna mai kaga abinda ka haifar ko.
KHALEED ya cije lips ya tashi ya fita a dakin zuciyarshi na zogi ya shiga mota ya kife kanshi da sitiyari yana kuka meyasa kowa ke ganin laifinsa? kuma ba laifinsa bane laifin zuciyarshi ne da bazata iya ganin WALEED nason abu bata mallaka mishi shi ba indai yana da hali,
Zarah nata kuka Muneera na hawaye tace "Kidena kuka diyata dan Allah kiyi hakuri"
Zarah ta dan tsagaita kukanta zuciyarta na radadi amma ta kasa denawa gabadaya, seda ta kwanta asibity sannan zataga KHALEED taso ace ya nuna kulawarsa akanta ko da yane,
Likitane ya shigo ya samu duk suna kuka ya tsaya yana kallon Muneera ranshi ya baci kamar ba dazun ya gama masu bayanin matsalar Zarah ba,
a hankali yace"Hajiya nayi maku bayanin matsalar yarinyar nan bai kamata ana kara daga mata hankali ba zai iya sa cikin jikinta ya zube ko kuwa ku rasa ta yafi ku rika kwantar mata da hankali kuna bata kulawa ta musamman"
Muneera jinjina kai kawai tayi, ya kara duba ruwan ya fita,
Zarah kuwa natsuwa tayi kamar taji yace ciki?wannan na nufin tana da cikin daddy jikinta,wani irin farinciki ya lullubeta tare da bakinciki lokaci daya tuno daddy ya saketa yanaso ya sadaukar da ita ga wanda bataso ta matse lips ta bude ido tana kallon cikinta hannunta daya da drip daya rike hannun Muneera tana jin son shafar cikin,fushi da daddyn shi bazai hana taji kaunarsa ba,
Muneera data fahimci hakan ta zare hannunta daga nata ta fara kokarin hada mata malt milk tasha ,
Zarah ta meda hannunta akan cikin ta lumshe ido tana jin dadi tana dauke da cikin Daddy masoyinta muradin zuciyarta ko da basu tare zata rika jinshi da kallonshi tana matukar farinciki da shi,
Muneera ta hada mata ta dawo ta zauna a hankali ta fara kokarin tada ta,ta dan tada ta ta dauki cup ta dora mata a baki,
Zarah ta bude idonta ta kalleta ta bude baki ta fara kwankwadar madarar sai da ta shanye sannan ta dauke bakinta tana meda numfashi ,
Muneera ta dauko ayaba ta dan kanga mata a baki ta juyar da kai don batajin cin komi wannan ma tasha don cikinta dabata so tai loosing ,
Muneera ta medata ta kwantar da ita tana binta da kallon tausayi,
KHALEED yasha kuka har seda aka kira ishai sannan ya fita yayi sallah ya nufo dakin zuciyarshi na harbawa, jikinshi sanyaye ya tura ya shiga dakin ba kowa ga ledojin ruwan duk ba ko daya da alamu duk sun kare ya samu seat ya zauna kanshi kasa ya fara tunaninta, yana hakan yaji karar bude kofar toilet baiyi yunkurin dagowa ba saima kara kurawa kasan tiles ido da yayi ,
Muneera na rike da Zarah tayo mata wanka suna ganinshi duk fuskokinsu suka sauya ,suka karaso Muneera ta zira mata Riga ta gyara mata kwanciya ta rufa mata bedsheet ta zauna ta kalli KHALEED da alamu duk hankalinshi baya kansu,
A hankali tace "Lafiya?"
Ya dan dago ya kalleta ya kalli gadon bakinshi na rawa yace "Ya jikinta?"
Muneera tai masa wani kallo na tuhumar dama ya damu daita ne tace"Gatanan da sauki"
Ya sunkuyar da kansa ganin kallon da take jifarshi dashi dama beso tasan yana cikin asibityn sai da aka kwashi minutes sannan cikin sanyin murya yace "Zarah ya jiki?"
Zarah da idanunta ke lumshe tai kamar me bacci duk da taji shi zuciyarta na bugawa shikenan sunan baby ya kaura daga bakinsa sai taji batason sunan nata,
Dukkansu sun san idanta biyu ranshi ya soyu jin ta mishi shiru itako Muneera bata damuba don ya cancanci haka,
Muryarshi sanyaye yace"Sai da safe "ya tashi ya fita Zarah taji kamar ta rikoshi ya kwana anan bakowane ya kamata yayi jinyarta ba saishi amma yana gudunta,
Yana fita ya shiga mota ya nufi gida duk illahirin jikinshi na zafi har cikin zuciyarsa yana isa ya fada toilet ya shiga shower ruwa nata bugunsa yanata nishi, da tafiya dakyar ya fito daure da tawul ya haye bed ya kwanta ya rufe da duvet ya rumtse ido gam zuciyarsa na kuna yayiwa Zarah magana tai masa shiru wata kila tana mai kallon azzalumi me son kanshi, a hankali jikinshi yakara yin ringis ya bude rufar ya fito ya sha magani da milk ya koma ya kwanta yana cikin ciwo kanshi zuciyarshi jikinshi gabadaya.
WALEED kwance yayi har sai su Muneera sun dawo ganin har 10:pm ya sa ya kasa hakura ya watsa ruwa ya saka kaya ya dauki key din motarshi ya fita yana fita ya nufi gidansu HAMEED ko zai fadamishi ya rage jin zafin heart, ya sameshi kwance rungume da pillow yana waya da rabin ransa yana ganinshi ya tashi zaune yana kallonshi,
WALEED na tsaye yace" Ya yau najika shiru"
HAMEED na binshi da kallo yace"Eh ban fita ba"
WALEED ya yamutsa fuska ya rasa ta inda zai fara fadamai yace"OK sai da safe "ya juya
HAMEED yace" I hope all is well?"
WALEED ya girgizakai yace "Zarah na asibity"
Da tashin hankali HAMEED yace"Meya sameta?"
WALEED na jin ciwo yace "baya wuce yunwa da damuwa daddy yaki kula daita "
Ran HAMEED bace yace "kai bazaka kula daita ba?wai mike damunka ne?"
WALEED ya kalleshi ranshi na baci yace"Good night"ya juya ya fita,
HAMEED ya wafci rigarshi ya zira ya fita dasauri ya sameshi cikin mota ya bude ya shige ,
WALEED ya tada motar yana tunanin halin da zai sameta ciki,
HAMEED na kallon titi yaja tsoki yanajin takaicin WALEED da yana kuka da ciwon bazai iya rayuwa babu ita ba yanzu kuma yanata wani shan kamshi.
Suna isa asibitin suka nufi dakin WALEED ya bude dakin idanunsa suka sauka akan Zarah gabanshi ya wani irin faduwa sakamakon ido hudu da sukayi ya dauke idanunshi suka karasa ciki,
HAMEED yace"Mama yame jiki?"
Muneera ta kalleshi tace"dasauki HAMEED "
Idanunshi kan Zarah yace"Zarah ya jiki?"
Ta bude idanunta dake lumshe ta kalleshi ta meda ta rufe batare da tace komi ba,
WALEED tunda ya shigo idanunshi na kan drugs dinta don yasan ko miye problem dinta idanunshi suka tsaya akan wani magani dake cikin jerin drugs dinta tunda ya ganshi ya rasa duk natsuwarsa jikinshi ya fara dan rawa zuciyarshi na zafi yace"Mama yame jiki?
Ta kalleshi fuskarta bawalwala tace"dasauki"
Baiyi wata magana ba ya juya tare da fadin" seda safe"ya fita da sauri
Muneera da HAMEED suka bishi da ido ganin yadda yake sauri yana fita ya fara hawaye ya shiga mota ya kwantar da kai jikin seat zuciyarshi na tsananin zafi.
Jikin HAMEED sanyaye yace "mama sai da safe Allah yabata lpy" ya juya ya fita,
Yana zuwa ya bude motar ya shiga ya samu WALEED nata kuka hawaye na zarya kan face dinshi,
Ya yamutsa fuska yace"WALEED bansan kuma meye matsalar ka ba Zarah de kasamu nan da 3 months zata zama taka...may be ma wani abu bai ko shiga tsakaninta da daddy ba kaga nan da kwanaki zata iya zama mallakinka"
WALEED ya kalleshi yana jin ciwo yace"Zarah batawa bace ta daddy ce shi kadai,tana dauke da cikin daddy"
HAMEED ya fiddo idanu gabanshi na faduwa bakinshi na rawa yace"Ya akai kasani ?kana da tabbaci?"
WALEED yace "Yanzunne na sani na tabbatar da naga drugs dinta " yana rikice ya riko hannun HAMEED yana hawaye yace"Shikenan na rasa Zarah bazan taba mallakarta ba inasonta sosai"
HAMEED ya cije lips yana cikin tashin hankali ,cikin sanyin murya yace"Na sani aminina kuma na tabbatar rasata zai saka wani hali shiyasa nake ta kokarin nusar da kai kadena cewa baka sonta tunda yabar maka ita ashema hakan bazaiyu ba "
Ya dafa shi yace"Kayi hakuri kayi kokarin mantawa daita kamar yadda kake yi "
WALEED na hawaye yayi shiru yana hango yadda zai cigaba da rayuwa batare da ita ba ,
Sun dade cikin motar suna ta tunani WALEED yaja ta ya kai HAMEED gida ya wuce gida yayi kwance kan kujera yana tunani duk ciwon da yayi ada da bai sameta ba ya dawo ,
Zarah bataji komi ba dan bai mata ya jiki ba Muneera kuwa abun ya bata mata rai sosai tana mamakin su,
KHALEED ya kwana cikin tsananin ciwo a hakan ya tashi da safe a daddafe ya hada masu breakfast da kanshi don yasan Zarar zataso yayi wanka ya nufi asibitin,
Kamar jiya kwance ya samu Zarah yau ya samu likita na mata allura ta cannula dake jikinta ya zubawa fuskarta ido tana ta matse lips alamun tana jin zafi ,
Tausayinta ya kamashi yasan duk shine silar wannan yanajin kamar ya hana alluran, likitan na gama yi mata ya fita,
Sannan ya samu ajiye kayan hannunshi muryarshi sanyaye yace "Mama ina kwana ya jikinta?"
Batako kalleshi ba tace"tana samun sauki"
Ya kalleta yace "Zan tafi office idan akwai abinda ake bukata"
Tace"Allah yabada saa"a takaice,
Zarah idanunta lumshe zuciyarta nata harbawa tana jin kamar ta rungumeshi ta mishi kisses tana matukar kewarshi, yanajin tsoron ya mata ya jiki tasake masa banza ya kara shiga wani halin duk da yana son jin muryarta ya hakura ya juya ya fita,
Muneera ta hada breakfast tazo ta tadata tana mata kallon tausayi tace"Kici ko kadan ne Zarah "
Zarah ta zubawa abincin ido dajin kamshin tasan shi ya dafa tana tuno time da suke cikin soyewa da daddynta idanunta cike da hawaye ta bude baki ta rika amsa ,
KHALEED ya isa office yana aiki yana tsayawa yana hutawa yasan bai lafiya sosai da zaije asibity yasan dole suyi admitting dinshi amma bazaije ba don baisan family dinshi sukara shiga damuwa ,
Bayan WALEED yayi sallar asubane ya samu bacci karfe 11 ya farka da matsananciyar faduwar gaba baisan cewar da KHALEED yayi yabar masa Zarah ba ya rage masa wani ciwo sai yanzu da ciwon nasa ya dawo fill ,
Yaje yayi wanka ya fito ya saka black jeans da white riga ya shiga mota ya nufi asibitin yana shiga Zarah ta juyar da fuskarta gefe, yawa Muneera yame jiki ya tambayeta ko akwai abinda suke bukata tace aa ya fita ya koma gida yana jin haushin juya masa bayan da tayi yanajin tana sane tayi hakan ,
Muneera ce tai ta jinyarta cikinsu bawanda ya taba kokarin tsayawa wurin fiye da 2hr dukkansu basa lpy ba kamar KHALEED da wani lokaci har juwa ke dibarshi saboda tsananin ciwo,
Zarah na samun sauki sosai saboda kulawar da Muneera ke da ita tana kuma kwantar mata da hankali,
****
Bayan wata daya,
Da dare habu da Ladingo suna zaune habu na jin radio yace"Ai Ladingo jibi nakeson tafiya birni na dubo Zarah "
Ladingo na kallonshi tace"Da kayi hakuri a kara ko wata biyune sai kaje ka dubota yanzu duka yaushe da Hjyar tazo kuma su ganka ,kasan wani lokaci kana fin 3months baka leka su ba ,kayi hakuri a kara wata biyu nan gaba sai kaje ka dubota"
Habu yace"Amma yanzu ai ya kamata nasan halin da take ciki saboda abinda ya faru daita "
Ladingo tace"Hakane kasa a ranka lafiyarta lau kuma karka manta maganar daka fadawa hjya da zata tafi "a rike amana" yanzu zasu yiwa zuwanka fassara kuma baza suji dadi ba kayi hakuri ka bari ai watanni sannan kaje nasan bazasu yi wani tunani ba "ta lumfasa tace" Amma fa shawarace idan kana ganin batai ba sai ka tafi amma ya kamata murika tuna alherin baya"
Ya juya kai yace"bazaki gane ba Ladingo Hankalina ba kwance ba amma zan kara jinkirtawan har zuwa wani lokacin"
Bayan 2weeks time din cikin Zarah na 2months da kwanaki aka sallamesu ba laifi jikinta yayi kyau saide laulayi irin na masu ciki da kewar mijinta data damu zuciyarta,
Muneera ta kira driver ya dawo dasu gida sannan ta fara hada masu abincin rana,
Zarah na kwance kan bed taji bazata iya barin Muneera ita kadai a kitchen ba, ta taso ta shiga kitchen ta sameta ,Muneera ta kalleta tana murmushi tace"Zarah daga dawowa asibity sai shigowa kitchen? "
Zarah tai murmushi tace"Mama ki bari na tayaki ko kadanne"
Muneera ta girgizakai tace"A,a ki bari ki kara warwarewa inkin koma gidanki kin cigaba da aikin"
Ta kalleta jin ta ambaci gidanta dama hakan zaiyiwu? Wani sanyi ya mamaye ruhinta ta kasa cewa komi ta fita ta kwanta falo tana kallo tana tunanin KHALEED dinta tana hango zasu koma rayuwarsu medadi da kaunar juna.
Da rana KHALEED ya siye abinci yaje kai musu ya samu an sallamesu ya nufo gidan don kawo masu abincin ,
Yana shigowa ya samu zarah kwance Muneera kuma na ajiye abinci tsakiyar carpet dan a nan zasuci.
Muneera ta dago tana kallonshi duk ya gama karewa yayi kasusuwa,
A hankali yace "Naje na samu an sallameku"
Fuskarta bawalwala tace"eh an sallame mu sai na kira driver muka dawo"
Yace"Toh" ya ajiye musu take away ya juya zai koma,
Muneera na jin haushinsa shi ko tausayin kansa baya ji tace"dawo ka zauna"
Ya juyo ya kalleta ya dawo ya zauna kasa ta kwalawa WALEED kira ya fito a daki shima duk ya kare sai tsawo daya kara ranta badadi tace"Ku zauna muci abinci"
WALEED ya dan kalli KHALEED ya dauke idonshi ya zauna kusa dashi suka zuba suka fara tsakura,
Muneera ta zuba a plate suka faraci da Zarah ,zarar nata kallon KHALEED tanajin tausayin yadda yakoma,
Suna cikin cin abinci Muneera ta kalli KHALEED tana jin tausayin shi ta kirashi"KHALEED "
Sai da gabanshi yayi mummunan faduwa yana tsoron me zata fada ya kalleta ya sunkuyar da kai yace"Naam"
Tace"gobe zaka dauki Zarah ku koma gida tunda ta samu sauki"
Zuciyoyin KHALEED da WALEED sukai mummunan bugawa lokaci daya,
Zarah kuwa taji dadi a ranta zata koma gidanta su raini cikinsu atare.
Muneera ta cigaba da cewa" kasan abinda ya dace da kai, kaffara zakai Azumi 60 ko ciyar da miskinai 60 cewar da kai ka haramtawa kanka ita "
Kan KHALEED ya dauki wani irin matsanancin ciwo yanajin kamar ya ciresa yayar ga zuciyar sa da yake jin kamar zata buga ya kasa magana har tsawon minti biyu ya tattaro kalaman bakinsa yace"Mama kiyi hakuri da abinda nariga na aikata amma bazan iya meda Zarah ba saki ukku nai mata"
Ran Muneera ya baci a fadace tace"waini KHALEED anfada maka ana saki ukku lokaci dayane?to saki daya ne ko da dubu kai mata"
Ya sunkuyar da kai zuciyarshi na tsananin zafi hawaye suka ziraro masa bakinshi na rawa yace" idan da matsayin dayane yanzu na kara mata biyu"
Zuciyar Zarah tai mummunan dokawa tana radadi ta rufe fuskarta da hannu ta fasa kuka tana jin tsanar KHALEED a zuciyarta ,yaune aka sallameta daga asibity yau ne yakara mata saki biyu lokaci daya hakan ya tabbatar mata babu digon sonta a zuciyarshi baya kuma tausayinta ko kadan,
WALEED kuwa wani irin hali ya shiga yanajin ciwo da tausayin kansu gabadaya kukan zarar na taba masa heart,
Ran Muneera yakai kololuwa wurin tashi har batasan time data rike baki ba saboda maganarsa ta matukar tsorata ta ,jikinta yayi lakwas ,
Zuciyarta na ciwo tace"KHALEED ka nunamin ban isa da kaiba ka nunamin yanzu kayi girman da abinda kaso shi zakayi ina baka umarni kana bijirewa ?nace kame data saika kara sakinta shikenan kai kasani"hawaye cike da idonta suka zubo akan kumatunta,
KHALEED na hawaye yanajin kamar jijiyoyin brain dinshi zasu tsinke yace"Mama ba haka bane ki fahimceni dan Allah, WALEED na son Zarah bazan iya cigaba da zama da ita ba"
Idanun WALEED jawur yace "Bana sonta daddy ba itace wacce nakeso ba kayi kuskuren fahinta ta"
Muneera na hawaye ta tashi tabar wurin ta shige toilet tai tsaye tana kuka gabanta na faduwa KHALEED ya kona mata zuciya sosai kanta ya kulle batasan ya rayuwar family dinta zai kasance nan gaba ba,
Zarah na kuka shabe_ shabe ta kalli KHALEED zuciyarta na radadi ta tashi ta shige daki tai kwance tana kuka me ban tausayi tana ganin KHALEED ya zalunceta zalunci mafi girma,
Tun dazu KHALEED ya zubawa WALEED jajayen idanunshi dake zubar da hawaye ranshi na suya a fadace yace"Kai ka haukace ? Baka da hankali da zaka rika fadin baka sonta a gabanta?WALEED ni zaka rika karyatawa a gabana? a gabana aka haifeka nine nan nai maka huduba na rada maka Suna na kuma raineka nasan komi naka komiye shi amma kake karyata ni,to bari kaji ko kana sonta ko baka sonta wlh saika aureta kuma da ita kadai zakai rayuwa stupid"
Kan WALEED kasa tamkar daddynshi na mishi fada fuskarshi kumbure yana hawaye shima yanajin ciwon fadin da yake baya sonta ya tashi ya nufi dakinshi zuciyar shi na zafi,
KHALEED yayi zaune awurin yanajin gidan da duniyar na juyawa yana jiyo kukan Zarah daga daki zuciyar shi na kara radadi, idanunshi na rufewa da budewa ya tashi ya shiga dakin ya sameta kwance kan bed jikinshi na rawa yaje ya zauna bakin bed din da take kai a hankali ya kirata"Zarah... kiyi hakuri... nasan ban miki adalci ba.. naso kaina da yawa.. amma kimin uzuri soyayyar da WALEED yake miki tafi tawa yafini sonki ya fini bukatarki kuma zai fini kula dake"
Zarah na kuka ta dago fuska tana jefa mai kallon tsana tace"Nasani Daddy kuma na fahimta, na fahimci cewa baka sona baka son duk wani abu daya danganceni bayan da ka gama shayar dani gubar soyayyar ka me mugun kisa"
KHALEED yayi shiru yana kallonta yanajin kalamanta kamar tana soka mai kibiya,
Tana matsanancin kuka tace"ka cuceni Daddy ka yaudareni ka hargitsamin rayuwa"
Zuciyar KHALEED na tsananin zafi idanunshi jawur kamar zai kuka yace "Zarah!!!! ki saurareni"
Idonta rufe Tace"Ni kawai ka kyaleni ka fita ka bani wuri ba na son ganinka na tsaneka wlh"
Tari ya sarke KHALEED ya fara tari zuciyarshi na matsanancin zafi da radadi hawaye na bin idanunshi kanshi na juyawa,
Ya tashi tsaye ya fara tafiya a sannu yanajin kamar zai kife yana isa bakin kofa yayi taga_taga kanshi ya bugu da kofa ya janye jiki ya bude kofar ya fita,
Zarah na jin bugewarshi da kofar ta dago kai da sauri ganin ya fita yasa ta tashi tana kuka ta fita falon harya fita ta bude taga ta tsaya tana kallon yadda yake tafiya kamar zai fadi ta na hawaye,
KHALEED ya rasa meke masa dadi cikin duniyar yanajin kamar mutuwa zaiyi don ciwon ya wuce misali, ya nufi motar gidan driver ya taso dasauri ya bude mai ya fada ciki ya jingina da kujera yana numfashi dakyar yacewa driver"kaini gida"
Driver yaja motar zuwa gidan nashi yana driving yana kallon KHALEED dake cikin matsanancin hali,
Zarah na ganin yadda ya koma wani irin tsoro da tashin hankali ya ziyarceta ta dawo kan kujera ta zauna tana rarraba idanu tana hawaye ta fara tunanin me ta fada mai ne?a hankali maganganunta suka fara dawo mata ta fiddo idanu tai saurin tashi ta sake leka windown tana kuka zuciyarta na kuna daddy ne fa meyasa zata fadamai irin wannan kalaman bata lura da halin da yake ciki? bata tunanin wani abu ya sameshi Idan wani abu ya sameshi fa? Ta dawo ta zauna kan seat tana hawaye tana jin haushin kanta fatan ta kar wani abu ya samu daddynta bazata juri ganinshi cikin wani hali ba,
KHALEED na cikin mota yana ta nishi zuciyarshi na ciwo Zarah na ganin baya sonta ya yaudareta yana tuno kalamanta "ka cuceni ka yaudareni ka hargitsamin rayuwa.....ni kawai ka kyaleni ka fita ka bani wuri bana son ganinka na tsaneka"
Ya fara tari tuno kalmar na tsaneka yanajin kamar ranshi zai fita,
Driver na kallonshi yace"yallabai ko mu juya asibity ?"
KHALEED ya girgizakai ya samu dakyar yace "A,a"
Driver yayi shiru don ba yadda zaiyi amma yasan yana bukatar temako har suka isa bakin gate ,
KHALEED ya bude motar ya kai 2minutes yana kokarin sauka sannan ya samu ya fito ya bude gate ya shiga ciki yana tafiya dakyar yana ganin jiri idanunshi na rawa yana isa bakin kofar shiga cikin gidan ya fara kokarin budewa yanata jawo numfashin shi dake niyyar daukewa a hankali ya nemi numfashin ya rasa idanunshi suka rufe jikinshi ya saki ya zube a wurin ,
Muneera na toilet tana jin yadda Zarah ke fada mishi maganganu ta karashe dirshewa zaune a cikin toilet din tana hawaye masu zafin gaske abinda take gudu kenan tasan nan gaba kadan zata nemi barin gidan da kanta saboda son kan diyanta,
Zarah na zaune tana ta hawaye taji karar bude gate tai saurin tashi ta leka taga driver ne da saurinta ta nufi ciki ta dauko gyale ta fito da dan gudunta wurin motar driver na kokarin rufewa bakinta na rawa tace"Dan Allah ka kaini gidan daddy "
Ya kalli idanunta da suke zubda hawaye ya daga kai ta bude motar ta shige yaja zuwa gidan tana ta zubda hawaye tana cije lips da jin zafin maganganun tana regretting fadamasa su bai cancanci ko makamantansu ba shine ya ceto rayuwarta ya kula daita shine Wanda take amsa sunanshi Zarah KHALEED,
Suna isa da hanzari ta bude motar ta nufi ciki tana hawaye gwara taje ta bashi hakuri ta rarrashe shi, tana shiga zuciyarta tai mummunan faduwa hangoshi yashe bakin kofa ta kwartsa kara ta nufeshi da gudu tana kuka tana zuwa ta zube gabanshi tana kidime kamar mahaukaciya ta rarumoshi jikinta tana kuka tana nishi take bubbuga fuskarshi tana cewa"Daddy... Daddy... ka tashi dan Allah wallahi ina sonka...ba haka bane" shiru baya ko da numfashi,
Ta rungumeshi tana kuka me ban tausayi can zuwa da saurinta ta lalubi aljihun shi ta fiddo wayarshi ta bude dasauri hannunta na rawa ta latso number Muneera tai ta ring baa dauka ba ta cigaba da kira tana kuka da nishi, Muneera nata jin ringing wayarta ta tashi tai alwala domin ta kaiwa Allah kukanta ta fito ta dauki wayar wani kiran ya kara shigowa ganin KHALEED yasa ranta baci kamar karta dauka ta daure ta dauka jikinta sanyaye ta kara kunne,
Zarah na matsanancin kuka tace"Mama !!!...Mama nashiga ukku nakashe daddy..daddy ya mutu"
Zuciyar Muneera tai mugun karyewa jikinta ya dauki rawa ta fara memeta"Innalillahi wainna ilaihi rajiun....innalillahi wainna ilaihi rajiun...." Hawaye na wanke mata fuska tana tuno mutuwar mijinta yanzu kuma dan data fiso ta dauke, jikinta kamar ba nata ba ta jawo hijab ta saka tana takawa dakyar ta nufi dakin WALEED,
Ta bude kofar ta shiga ta jingina da bangon dakin tana hawaye WALEED na zaune yana hawaye ya dago fuska yana kallonta ,
Cikin raunanniyar murya tace"WALEED ka tashi Allah yayiwa Daddyn ka rasuwa."
WALEED yaji saukar maganar a kunnensa tamkar dukan guduma idanunshi suka lumshe yayi baya zai leme kan bed ,
Muneera ta razana tsoro ya mamayeta wani irin karfi yazo mata tai kanshi da gudu tai saurin rikoshi kafin ya kai kwance tana firgice cikin tashin hankali ta rika bugun fuskarshi da karfi tana kiran sunanshi "WALEED WALEED WALEED !!!"
A hankali ya bude idonshi zuciyarshi na mugun bugu tana ganin ya farfado ta fara sauke numfashi tana wasu hawayen tsoro ,
WALEED na dawowa hayyacinsa ya yunkura ya tashi dasauri ya zari key ya fita dakin da gudunshi bai yadda daddynsa ya rasu ba bazai taba yadda ba daddy bazai mutu yabarshi ba, tana biye dashi suka shiga mota ya jata da gudun tsiya zuwa gidan yana driving yana kuka yana tuno soyayya da gata daya samu a wurin daddynsa,
Suna isa bai ko kashe motar ba ya bude ya banka cikin gidan aguje yana shiga ya hangi Zarah durkushe tana rungume da KHALEED tana ta kuka ,Zuciyarsa ta kara tsananta ciwo idanunsa na zubda hawaye yafara tuno mummunan mafarkinsa acikin shi ba abinda bai faru ba daddynshi yaso Zarah itama ta soshi sunyi aure har da samun karuwa ga rasuwar daddynsa Wadda bata da bambanci da kisan da yayi masa saboda shine silar komi.
Jikinshi na rawa ya karasa dasauri ya amshe shi ya rungumeshi jikinshi yana kuka yana kallon fuskarshi yana fadin "Daddy..don Allah karka mutu ka tashi..!!!!"ya karasa da dora kanshi a kirjinshi yana matsanancin kuka me taba zuciya,
Muneera ta shigo gidan haryanzu jikinta na rawa tai tsaye idanunta na zubda hawaye tana kallon KHALEED dake sheme a jikin WALEED zuciyarta na zafi bata so yayi irin wannan mutuwar ba ta bakinciki da bacin rai tana cikin fushi dashi.
*SHIGAR SAURI*
Painful love story
Romance special
Writing by
*MAMAN MAMY (SHALELE)*
*Wattpad@mumies122*
*Dedicated to my close friend ikra Rukayyat*
*Devoted to identical twins hassan & Husain 80k*
*Small gift to my real fans*
*PROFICIENT WRITERS ASSOCIATION*
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/
TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09
Page > 67&68
*Ina kuke Mata ?? Maman mujaheed me kayan gyara ta kawo sabbin kayan sace zuciyar oga, cikin sauki tauraruwarki zata haska, tana turawa ko ina ga me bukata seya tuntubi wannan number👉🏼 0806 672 6866*
Suna ta kuka Muneera na kallon su tana matukar tausaya masu ta tuno time da daddyn su ya rasu KHALEED yayi kuka amma a karshe ya hakura shine yayi komai har aka kai shi kabarinsa.
Ta share hawaye ta nufesu tana takawa dakyar tana jin kamar zata fadi,har ta iso ta tsaya ta kara kallon kyakkyawar fuskar danta Wanda tafi so fiye da komi sabbin hawaye suka kara zubo mata, dakyar ta bude baki tace"WALEED kuyi hakuri hakanan,Ka kamashi mu tafi dashi ayi mishi sutura"
Zarah ta zaro ido ta kara fasa kara ta rike kafafun shi gam tana matsanancin kuka,
WALEED ya dago a zabure idanunshi na zubda hawaye yana kallon Muneera.
Muneera ta sake cewa" kuyi hakuri"cikin raunanniyar murya.
Jikin WALEED ya dauki matsananciyar rawa cikin firgici yace"Mama bai mutu ba" ya sake kallon fuskar KHALEED ya dago yace "Bai mutu ba Mama"
Hawaye suka gangarowa Muneera tace "WALEED KHALEED ya mutu kayi hakuri"
WALEED ya fara girgizakai yana rikice ya juya ya kalli Zarah dake ta kuka yace"My Star bai mutu ba... Daddy bazai barni ba"
Muneera ta kureshi da kallo kamar ya zare ,
Ya tashi dasauri jikinshi na rawa ya sabeshi ya fita da dan gudunshi ,Muneera tabi bayanshi da kallo tana gudun ya fadi.Ta juyo ga Zarah data kife kai kasa tana cigaba da kuka ta dagota jikinta ta riketa gam suka nufi kofa.
WALEED bai saurare su ba don gabadaya bai cikin hankalinsa ya tada mota yayi gaba bayan yasa KHALEED ciki ya dauki hanyar asibity bai yadda ya mutu ba kuma bazai taba yadda ba .
Muneera tabi motar da kallo cikin karfin hali ta tsaida napep suka shiga suka bi bayanshi ganin ba gida ya nufa ba,
Suna ta binshi ya tsaya bakin wata asibity ya fito ya daukeshi ya shiga ciki dashi da gudu,
Muneera ta sauka akan adaidaitan tana kallon asibityn idonta cike da hawaye ta kama Zarah dake ta kuka suka nufi ciki batare da ta kara bibiyar me adedetan ba,me napep nata kallonsu yadda suke cikin tashin hankali yasa ya tada mashin yayi tafiyarsa.
Su Muneera na shiga asibityn ta zaunar da Zarah kan bench dake zagaye da duk asibitin ta zauna gefenta don tasan WALEED bazai jima ciki ba zai fito saboda KHALEED ya riga ya mutu.
Suna zaune tana ta tunanin baya kyautatawar KHALEED gareta da yadda yayi rayuwa, zuciyar Zarah na cikin ciwo mutuwar KHALEED daban take jinta da tasu baffa domin bazaa hada ba.
Sun dade awurin fiye da hour WALEED ya fito daga cikin asibitin jikinshi sanyaye yana duba gefensa ya hangesu zaune duk sun shiga tunani kan Zarah a kafadar Muneera,
Ya karasa ya zauna gefenta ya dora nashi a dayar kafadan yana zubar da hawaye.
Muneera na cikin tunani ta jishi a jikinta ta kalleshi a hankali tace "Mu tafi gida WALEED hakuri za kuyi"
WALEED ya lumshe idonsa ya bude zuciyar sa na zafi cikin dasashshiyar murya yace"Mama daddy bai lpy"
Gaban Muneera ya doka tace "Bai rasu ba ?"
Ya girgizakai muryarsa kamar zai kuka yace"Amma kila mutuwa zaiyi"ya karasa da gumtse kukan shi.
Muneera da Zarah sukai wuff suka tashi tsaye gaban zarar nata up and down, Muneera tace"Muje na ganshi"
Ya tashi suka bi bayanshi suna cike da dokin ganinshi,har bakin wani daki sannan yaja ya tsaya bayan yabawa kofar dakin baya yana tsorace da yadda KHALEED yake,su Muneera suka kutsa ciki suka samu KHALEED kwance da drip ga oxygen jikinsa yana jawo numfashi dakyar numfashin na sarkewa kamar me cutar Corona.
Muneera ta juyar da kanta don bazata iya cigaba da kallonsa haka ba ,jikin Zarah na rawa ta karasa bakin gadon tana kallonshi tana kuka ta kamo hannunshi ta rike tana cewa"Daddy karka tafi kabarni dan Allah,, ina sonka sosai"KHALEED na cigaba da neman numfashi baisan a ina yake ba ,tana kuka ta sulale kasa ta cigaba da rerawa gwanin tausayi.
WALEED na waje ya jiyo kukanta ya shigo dakin yana ganinta hawaye suka kara zubomai ya isa gunta ya kamota jikinshi zuciyar shi na zafi ya kama hannun muneera yaja su waje ya zaunar da su akan bench ya zauna gefe ya rufe fuskarsa da hannu biyu yana hawaye ji yake dama zai iya daya medo ciwon jikinsa kalaman likita daya tuno yasa shi cire hannu a fuskarsa cikin tashin hankali "Jininsa ya hau sosai that cause him heart failure zai iya rasuwa kowane lokaci"
WALEED yayi saurin tashi tsaye zuciyarsa na bugawa ya fita daga asibityn a guje yana driving yana hawaye ,harya isa gidansu HAMEED saide bayanan ya koma mota ya dauki wata hanya don yasan bazai wuce can ba ,
Yana zuwa majalissar yaja ya tsaya ya kife kansa jikin sitiyari batare da ya fito ba, HAMEED na cikin friends ya dago ido yana kallon motar hankalin shi kacokam ya koma kanta yayi tsimul ya tashi yaje ya bude motar ya shiga,
Zuciyarsa ce ta karye lokacin da yaji ajiyar zuciyar WALEED,
Cikin sanyin murya yace"WALEED minene?"
WALEED yayi shiru yana cigaba da hawaye.
HAMEED yasan tatsuniyar gizo bata wuce koki yace "Na gaji WALEED damuwarka tasa ko abinci bana iyaci sosai kullum kuka kamar wata mace ko gajiya ba kayi?"
Fuskarshi daure yace"Na gama hada kayana tafiya zanyi wani wuri can in komai ya dedeta zan dawo"
WALEED ya dago idanunsa dake jawur ya kalleshi da mamaki ,sai de suna hada ido yaga idanun HAMEED din jawur cike da tausayi da damuwa,ya matse lips tare da meda numfashi bai damu da maganarsa ba don yasan yanajin kowane ciwon da yake ciki,
A hankali yace"Daddy baya lafiya ko numfashi baya samu seda temakon oxygen ,HAMEED tsoro ya kamani bana son Daddy ya barni"
HAMEED ya dafe goshi yanajin haushin kansa idanunshi suka ciko da hawaye cikin sanyin murya yace"Kayi hakuri zai samu lpy idan Allah yaso"
WALEED ya lumshe ido ya jinjina kai ya sake yin ajiyar zuciya yace"Inason in fitar dashi waje saboda a kula dashi sosai amma bansan ta ina zan fara ba"
HAMEED na jin tausayinshi yace"Wane asibity yake?"
WALEED yace"Royal hosp"
HAMEED ya matse lips yace"Kana da kudi ne hannunka?"
WALEED yayi shiru sannan yace"Bazasu wuce 2Millions ba...amma zan siyar da motata na kuma san bazaa rasa wurin Mama ba"
HAMEED ya kalli motar yayi nazari sannan yace"Royal hospital na da kwararrun likitoci sosai tana daya daga cikin asibitocin da ake ji dasu a birnin nan ,sannan tana da tsada sosai ,WALEED idan kace zaka fiddashi waje zaa kashi kudi sosai"
WALEED nata ajiyar zuciya yace"I don't care komai ya kare nide in samu daddy "
HAMEED ya gyada masa kai yace"daddy yafi komi amma kayi hakuri muga kwana biyu ,sannan 2 million baza tayi komiba a asibitin nan ma, akwai 5million's wurina zan turo maka ita kar kaiwa Mama maganar kudi yanzu domin nasan tana cikin tashin hankali"
WALEED yace"Nagode sosai"
HAMEED yace "Ka kwantar da hankalinka Daddy zai samu lpy muje naga jikinshi"
WALEED ya tsaya yana kallonshi idanun HAMEED jawur, tamkar dan'uwansa yake jinsa shiyasa bai boye masa komi ya tada motar suka nufi asibity.
Suna zuwa suka wuce Muneera dake zaune a bakin kofar suka shiga ciki,acan suka samu Zarah tayi kneel down a jikin gadon da KHALEED ke a kai tana ta kallon yadda yake numfashi ko kyaftawa batayi tsoronta daya numfashin ya dauke kafin budewar idonta.
HAMEED da yaga halin da yake ciki hankalinshi ya kara tashi ya kama Zarah tana ta kuka tana mikawa KHALEED hannu harya fiddata sannan ya kalli WALEED yace "Ka kula dasu plss zanje na dawo"
Ya juya ya fita daga asibitin hawaye na fitowa daga idonsa, mashin ya tara ya hau ya kaisa gida ya shiga dakinsa ya jawo wata paper ya tsaya yana kallonta papern gidanshi ce bayan da ya dawo daga India daddynshi ya bashi ita they're preparing to get him married amma yanzu dole ya siyar da gidan don daddy ya samu lpya saboda KHALEED ba daddyn WALEED kadaine ba har dashi don ya temaka masa ta fanoni da dama, ya daga kanshi sama yana tuno how friendly he's,hawaye suka zubo masa ya soka papern aljihu ya fita dasauri ya shiga cikin gidansu ya fadawa mom dinsa Daddyn WALEED bai lpy sannan ya sake fitowa ya tada mota ya nufi majalissa don neman me siya.
Yana zuwa ya fara fada masu kudi yake so very urgent yanason siyar da gidanshi wani ya masa rakiya wurin wani alhaji suka tafi yaga gidan ,gidane me kyau angama komai har faint kudinsa zasu kai 10million's ganin suna bukatar kudinne yace ya siya 7M ,
Abokinsa ya kallesa zai Magana HAMEED yace ya kawo don bai da time.
Sai da ya amshi kudin ya turawa WALEED sannan yayi salloli ya nufi asibityn zuciyarsa na zafi,
A can ya samu dad da mom dinsa a bakin dakin zaune don doctors sun hanasu shiga yaje wurin WALEED ya zauna ,su mom dinsa suka karawa Muneera yame jiki suka ajiye abinci da fruit suka tafi.
Ba jimawa sai ga maman farouk tana ganin Muneera ta fara hawaye tai zukunne gabanta tana sharewa ta dago tace"Daga gidan nake driver ke fadamin KHALEED ba lpya nayi tunanin wannan asibitin ce kusa da gidansa na taho, kiyi hakuri zai tashi da yardar Allah "
Muneera ta goge hawayen da suka ziraro ta daga kai, Maman farouk ta koma ta zauna tana nan har kusan 10pm sannan ta tafi.
Bayan tafiyarta wata doctor tazo ta kara duba KHALEED jikin na nan dai bawani cigaba ta fito fuskarta jawur ta wuce,
HAMEED nata tunani ya meda kallo gun Zarah tana zaune har ta gaji da kukan sai hawaye da suka ki barin idonta ,she's pregnant kuma yasan bataci komi ba hakan kan iya haifar da wani abu, ya dafa kafadar WALEED dake cikin dogon tunanin taya zai cigaba da rayuwa ba daddy? Ya zai iya kula dasu Muneera? Ya juyo ya kalleshi,
HAMEED ya mishi nuni dasu da Idanunshi can ciki yace "Is better su ci abinci"
WALEED ya matse lips ya tashi ya isa gun abincin dake wurin ya bude ya fiddo ya hada plate biyu, baiwa HAMEED magana ba yazo ya dauki plate guda ya nufi Muneera ya zauna gab ita cikin sanyin murya yace"Mama ki dan ci wani abu"
Muneera ta girgizakai tace"Ka meda abincin nan HAMEED na koshi"
HAMEED yayi shiru bazai iya gane adadin ciwon da take ji ba as a mother nashi kawai ya sani a hankali ya sake cewa "Mama ki ci abinci Daddy na iya warkewa ke kuma ki kwanta nasan bazaki so hakan ba"
Muneera ta dan kalleshi sai taji nauyin kin karba ta mika hannu da niyyar amsar plate din memakon ya bata sai dauko spoon yayi ya kai bakinta,
Hakan ya tuno mata KHALEED yadda yake bata abinci da kwantar mata da hankali, hawaye cike da idonta tana kallon fuskarshi ta bude baki ya fara bata .
Shi kuwa WALEED ya dauki abincin ya tashi tsaye ya juya ya kalli Zarah idanunta a lumshe ya karasa wurinta ya zauna gefenta ya kira sunanta "Zarah ki danci wani abu"
Ta bude idanunta dake jawur ta kalleshi wani bakin ciki ya taso mata daddy bai lpy amma har maganar abinci yake mata ko da yake ai shine silar komi ba don shi ba da ba abinda zai samu daddy ,ta meda idanu ta lumshe batare da tace komi ba,
WALEED ya sake cewa"Zarah Plsss ko kadan"
Ta sake bude ido ta kalleshi tana tuna dazun har wata my star ya kirata dashi tana jin ciwo a zuciyarta tace"Bana...jin..yunwa"a rarrabe saboda kukan da tasha.
Yace "Na sani plss eat for our baby"
Taji maganar wani iri ashe fa tana da ciki saide cema cikin our da yayi yasa zuciyarta tuna wani abu hawaye suka zubo mata ta amshi plate din ta debo abincin ta kai baki ta fara taunawa tuno sakin da KHALEED ya mata a yau ya sata kwarewa ta fara tari Muneera da HAMEED suka yo kanta WALEED na firgice yayi saurin kawo lemu ya bude ya kafa mata, tana dan sha taji zuciyarta ta kara tsananta zafi dandanan jikinta ya dauki rawa ,
WALEED ya zaro ido tare da kallon lemun hannunshi tuno ulcer ya sashi mikewa tsaye da sauri .
Muneera ta rikice ta rike ta tana kallon yadda jikin ke girgiza,
HAMEED kam yana tsaye yana kallonsu baiga dalilin da zaisa WALEED bata lemu ba bayan yasan bazai rasa gas ba gashi da sanyi, bai gama tunani ba yaga WALEED ya sungumeta ya nufi office din doctor yayi sauri yabi bayanshi ,
Muneera ta bisu da kallo zuciyarta na tsinkewa, suna zuwa likita ya fara dubata yana fada meyasa aka bata lemu madara ya dace da ita. Ya rubuta wasu magunguna HAMEED yaje ya siyo da kudin aljihunsa ya dawo WALEED ya bata madara da drugs din nan take jikin ya rage rawa idanunta kulle tana ta meda numfashi ,
Doctor ya rubuta musu wata paper yace su kaiwa nurse waje,WALEED na amsar papern yaga admitt baice komi ba ya mikawa HAMEED ya sake daukarta suka fita daga dakin, ganin da HAMEED yayi baibi ta kan nurse ba ya nufi wurin Muneera da ita ya sashi cewa"Baka ganin tana bukatar Hutu?"
Zuciyar WALEED na bugawa da sauri hankalinsa na kan KHALEED yace"She will be OK "
Zarah na jinsu tana jin haushinsa har suka isa ya ajiyeta ,Muneera ta riketa tana dubata da mata sannu ,
Washegari
Anan HAMEED ya kwana sai da safe ya tafi kawo musu breakfast har lokacin KHALEED bai farfado ba, iyakar tashin hankali sun shigeshi ko likitocin sai kai kawo suke ganin har yau bai dawo hankalinsa ba,badai kamar wata baturiya da tafi kowa shiga da fice wurinsa.
Habu bai kwana da shirin tafiya birni ganin Zarah ba ya tashi harya fita da niyyar fita gona ya dawo Ladingo na tsakar gida yace"Yanzu zan tafi birni"
Gabanta ya fadi tace"Lahiya?"
Yace"Lahiya lau"
Tace"Kadai kasa hakuri da ka kara masu lokaci"
Yace"Umm tafiya zanyi"ya shige daki ya dauko wasu kudade ya fito yace"Sai na dawo"
Tace"Adawo lahiya agaidasu"tana girgizakai
Karfe 6 ya shigo gidan nan driver ke fada masa suna asibity hankalinshi ya tashi yace ya kaishi asibityn.
Yana shiga wurinsu Muneera ta sunkuyar da fuska wasu hawayen na taruwa idanunta,ya kalleta ya tsayar da kallon shi kan Zarah da ta koma kamar 1 ,ya meda kallonshi ga WALEED yaga yadda ya k'are, zuciyarshi ta karye ya isa gaban Muneera ya zukunna gabanta yace"Hajiya ya mai jiki?"
Muneera tace"Dasauki"muryarta dishe,
Yace"Allah ya bashi lahiya ya tashi kafadunshi"
Tace"Ameen"
Yayiwa WALEED yame jiki ya juya yana kallon Zarah.
Tana cikin duniyar tunani batasan ma yazo ba sai da ya isa gabanta yace"Zarah kuyi hakuri kinji" sannan ta kalleshi sabbin hawaye suka fara zubo mata ya jinjina kai yana matse lips da kyafta idanunshi dake niyyar kawo ruwa ya leka a window yana kallon KHALEED nata fama da numfashi ya girgiza kai yana fatan samun saukinsa.
Bayan ishai duk suna cikin dakin hankalinsu a matukar tashe ,wasu na zaune wasu tsaye sunata kallonshi dakin tsit kamar ba mutane, KHALEED ya fara juya kai abubuwa da suka faru last na dawo masa zuciyarsa na zafi,
Suko ganin yana juya kai yasa su farinciki Zarah tai saurin matsawa gab dashi tana sabbin hawaye,
WALEED yayi saurin fita kiran doctor,
KHALEED ya bude idonsa amma baya ganin komai sai duhu yana son magana ya ji ya kasa dakyar ya dago hannunsa ya zame oxygen dake a hancinsa yana jawo numfashi ya bude bakinsa yace"Za..rah"sunan ya fito dakyar,
Zarah na gefe wani sonshi da tausayinshi ya kara mamayeta,
Ya kara cewa"Zarah"da murya irin ta masu ciwo.
tana hawaye tace"Gani nan Daddy"
Su WALEED suka shigo da Doctor ganin yanason mgna yasa doctor din tsayawa don taji maganar idan zata fito dede saboda faduwar da yayi.
Yana juya kai ba tare da yasan me yake ba yace"Ki yafemun...ina..son...ki"ta jinjina kai tare da rufe bakinta dan kar kukan da take ya kufce.
WALEED na jin abinda yake cewa ya fara hawaye zuciyar shi na zafi ,
Su Muneera sukace "Sannu KHALEED"doctorn tai masa kuri tana cigaba da kallonsa batare da tayi komi ba.
KHALEED yana numfashi yace "Ma..ma" sai kuma ya sauya da kiran "WALEED.. I'm sorry..bansani ba..banason ta haihu... bana son ta haifi zabaya... banason wani abu ya sauya daga jiki....."Muneera tai saurin zuwa ta meda oxygen din jikinshi tana fadin " Innalillahi wainna ilaihi rajiun"tana kuka.
Zarah ta kifa kanta jikin gadon tana kuka duk tsananin ciwon duk da baya hayyacinshi da sunanta ya farko da kuma Kalmar so bayan ta fadamai bata sonshi ta tsaneshi fadin bayason ta haihu bai mata ciwo ba don tasan yadda yake fada kafin aurensu kuma tasan abinda yake kokarin aikatawa kafin ya kwanta ciwon.
HAMEED da WALEED hawaye suketa yi ba kamar WALEED da zuciyarshi ke barazanar fitowa jin kalaman sa bayan duk sadaukarwar da ya masa da jajircewarsa har hakuri yake basa.
Kawu habu kam na tsaye idanun nan cike da hawaye ya kasa gane komi,
Doctorn da kanta ta matsa kusa dashi ta fara hada wasu allurai na rage ciwo tai masa ta juyo jikinta a mace tace"u should go out plss"
Duk suka fita Zarah ta yunkura ta tashi zata fita doctorn ta kalleta tace"Ki zauna ki kula dashi"ta fita bayan ta kara kallon KHALEED din.
Zuciyar WALEED ta kasa dena ciwo ya tashi ya fita can bayan asibitin yayi tsaye yana raira kuka ,
HAMEED ya biyoshi ya sameshi bai hanashi ba yayi tsaye yana kallon shi sai da ya bari yasha kuka yana ganin zai rage masa ciwo sannan ya kama hannunshi yace"Ya isa, ka dawo hayyacinka kar ya farfado ya nemeka"
Suna tafiya ya bashi hankici ya goge fuskar suka koma su ka zauna.
Can cikin dare ya sake cire oxygen yana ru..wa,Zarah ta fita ta fada musu WALEED yaje ya fadawa doctorn tazo ta dubashi tace a bashi milk instead of ruwan idan zai iya sha ,
HAMEED yaje ya siyo ya kawo WALEED ya dan bashi yadan surba ya bari,ya meda shi ya kwantar dashi ta mayar masa da iskan ta masa a
allura bacci ya daukeshi.
*SHIGAR SAURI*
Painful love story
Romance special
Writing by
*MAMAN MAMY (SHALELE)*
*Wattpad@mumies122*
*Dedicated to my close friend ikra Rukayyat*
*Devoted to identical twins hassan & Husain 80k*
*Small gift to my real fans*
*PROFICIENT WRITERS ASSOCIATION*
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/
TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09
Page > 69&70
*Ina kuke amare da suke niyyar shigewa daga ciki?Maman mujaheed ta dauko kayan gyara na musamman domin ku suna da kyau sosai cikin sauki tana turawa koina ga me bukata seya tuntubi numbern ta👉🏼 0806 672 6866*
Har wanshekare yana bacci babban Dr yazo ya dubasa da safe ya mishi wasu alluran ya tafi ,da rana ya sake dawowa ya samu still yana bacci Muneera na gefe ya tambayeta ya tashi ne? Tace a,a yayi tsaye yana kallonshi sannan ya duba drugs and injec dinsa ya yamutsa fuska ya ciro waya yayi kira minti biyu ta shigo da sauri kafin tai mgna yace"Dr fati wace irin allura ki kai masa last? "
Ta kalli KHALEED ta meda kallo gun Dr tace"DT na masa last"
Ya kurawa KHALEED ido tace"Akwai matsala ne?"
Yace"no in dai hakane baccin sa yayi yawa "
Ta sauke ajiyar zuciya da hankalinta har ya tashi tace"yana da bukatar shine "
Dr ya kara matsawa gun KHALEED din yana kara duba jikinnasa duk bai gamsu ba ya fara tapping fuskarsa yana kiran sunansa "KHALEED..KHALEED"
KHALEED kam bai ko motsa ba wani nauyayyen bacci ne ya daukesa saboda ya dade bai samu baccin ba,
Doctor ya sauke numfashi ya dago ya nufi kofa suka jera suna tafiya yace"let's give him sometimes bp din nashi ya fara sauka ana samun cigaba "
Tai murmushi suna kai wani office ta shiga Dr salis na zaune tana shiga ya saki murmushi me sanyi yace"jiya da yau gabadaya kina nan bazaki koma gida ki huta ba?"
Ta meda masa murmushi taje ta zauna kan kujera tace"Tafiya zanyi ai"
Yace "To ko na kaiki?"
Tace"A,a zan tafi da mota ta"ta tashi tsaye ya bita da kallo yace"Saina shigo"
Tana murmushi tabar office din nasa ta koma nata office ta dauki jikarta ta nufi gida.
Da marece da likitan ya kara zuwa duba KHALEED still bai tashi ba ya daura masa drip Su Muneera duk hankalinsu ya kara tashi sunata addua,
KHALEED bai farka ba sai washe gari da safe ya fara bude idanunsa a sannu har suka bude ya kalli dakin sannan ya kalli gefensa inda Muneera da Zarah suke duk da yana cikin ciwo bai hanasa murmushi ba can ciki ya furta"Mama"
Ta saki murmushin tausayi tana jindadin farkowarsa,
Ya kalli Zarah zuciyarshi ta dan harba ya kakaro murmushi yace "Zarah"
Hawaye suka zubomata ta kara matsawa kusa dashi tana gogewa,ya juyar da kanshi kallon WALEED yasa shi yin murmushi me fadi yace "WALEED" tare da mika masa hannu,
WALEED na karamin murmushi yaje yasa nashi tare da zaunawa gefensa,
Ya kalli HAMEED ya masa murmushi HAMEED ya mayar masa,ya cigaba da kallon mutanen dake dakin harda su farouk da habu da wani friend dinshi awurin aiki.
Ya meda idanunshi ya rufe wani baccin ya kara daukeshi.
Wanshekare Habu yace zai koma gida don yaga jikin da dan sauki Muneera tai ta godiya yana kallon Zarah dake kanjame suka fita WALEED ya kaishi mota ya nufi kauyen su.
Yana shiga Ladingo na zaune ta rafka tagumi ta fashe da kuka ,kwana daya zaiyi amma har yayi ukku gobennan take niyyar binsa don bazata iya cigaba da zama cikin tunani ba cikin zuciyarta har ji take yama mutu.
Ya zauna tare da sakin numfashi ya rike sandarshi gam yace"lahiya kike kuka?"
Ladingo ta watsa mai harara tace"kwana ukku baka nan kana tambayar lahiya?"
Ya langabe kai yace"Kiyi hakuri inacan Alhaji ba lpy yana kwance mina_mina, ai Ladingo banyi tunanin alhaji zai tashi ba yadda na sameshi"
Tuni ta manta tana kuka hankalinta tashe tace"Ya jikin nashi?da sauki ko?"
Ya matse baki yace"Imm da sauki sosai tunda haryana gane su waye wurinsa"
Ladingo ta girgizakai ta kara gyara taguminta tace"Allah ya bashi lahiya ni kaina da baka dawo ba da saide abi bayanka dani"
Yayi murmushi yace"Ladingo sai hakuri ki doramin ruwan zafi ki kawomin fura yunwa nakeji "ya Mike zai shige daki,
Tace" ai dole duk ka fad'a"ta nufi murhu.
Suna cigaba da jinyarsa Dr fati tafi kowa kula dashi su kansu sunfi son kiranta idan wani abu ya taso Mama take kiran Muneera har sun dan saba,HAMEED na asibitin kullum har tambayar WALEED yake akwai kudi don idan sun kare ya karasa basa 2M da suka rage masa,WALEED sai de ya kallesa yayi shiru yana mamakinsa bai taba tunanin HAMEED zai damu har haka ba yanata hidima kamar dai daddynsa ne kwance.
Jinya yake don haka bamai masa wata maganar da zata tuno masa wani abu ko bata ransa tunda ya farfado ya fara neman mafita domin haryanzu akwai aiki agabansa yana kwance yake saka da warwarar neman hanyar bullewa.
****
Bayan wata biyu
Ya samu lpya saide karasa warwarewa da dare aka sallamesu suka koma gida dukkansu suna cikin farinciki da samun saukinsa suka baje falo suna fira ,
HAMEED ya tashi zai tafi,
Muneera tace"Allah ya hutar da gajiya HAMEED angode"
Yayi murmushi ya juyo ya kalleta yace"Seda safe"
WALEED na biye dashi har bakin motarsa HAMEED ya juyo WALEED ya mika masa hannu sukai musabaha bai saki hannunsa ba yace"Na rasa me zan fada amma ka sani bazan manta wannan ba har'abada"
HAMEED yayi murmushi ya jinjina kai,
WALEED ya saki hannun nasa sannan yace"Ina sonka sosai..."
Bai karasa ba HAMEED yayi dariya yace "A,ah ka bari husna ta fadi wannan dan Allah"suka sake dariya tare, suna dariya HAMEED ya bude mota ya shige sai da y tada sannan ya daga mai hannu yayi gaba.
WALEED na tsaye har yabar gidan ya sauke ajiyar zuciya yana jinshi wasai Daddy ya samu sauki ya koma ciki,
Bai jima da komawa ba Zarah ta tashi ta shige daki ta kwanta saboda bacci da yawa a idonta ,Muneera na hamma saboda bacci tace"WALEED ka kamashi ku shiga ku kwanta"
Ta kalli KHALEED tace "Sai da safe"
KHALEED ya mata dan murmushi ya meda kallonshi gun WALEED da ya taso zai rikesa a hankali yace "Zan iya" ya tashi a hankali ya nufi dakin da kanshi yana zuwa ya haye gado ya kwanta,WALEED ya shigo dakin jikinsa sanyaye yaje ya kwanta gabansa,
Idanun KHALEED bude yake kallon kan WALEED yana tuno Kalmar baya sonta ,ya rumtse ido bai iya jin zai hakurin safiya kafin suyi maganar gwara yasan abinda ke ranshi,
Idanun WALEED kulle yana adduar bacci yaji KHALEED na cewa"WALEED ka amince ?"
WALEED ya dakata ya juyo yana kallonsa yace"Daddy?"
KHALEED na kallon kwayar idanunsa yace"Zaka aure tan?"
WALEED ya matse lips sakamakon gabansa daya fadi Zarah ce fa Matar daddy da ke dauke da cikinsa ,Zuciyarshi ta tuna mai da kuma masoyiyarka tauraruwar ka,ya rumtse ido yana jin ciwo wani irin nauyi ya mamaye shi,
KHALEED nata kallonsa ganin bazai magana ba ya lumshe ido ya bude cikin sanyin murya yace"Idan baka aureta ba wani zai aure ta"
WALEED ya bude ido yana sabon tunani yana jin nauyi amma hakan zaisa daddy farinciki bugu da kari zai raini ababen son daddy zai basu kulawa sosai,
A hankali yace "Kome kakeso Daddy kamin magana koma miye"
KHALEED ya saki murmushi yanajin karin sauki yace "Allah ya maka albarka nagode sosai"
WALEED ya kalleshi a cikin su wa ya kamata yayi godiya? shine ya dace ya gode masa amma memakon haka shine ke gode masa,bai kara cewa komi ba ya juya ya kulle ido yana hango fuskar Zarah da kila ta zama tasa nan gaba,
KHALEED ma rumtse ido yayi yana dan nazari har bacci ya daukesa.
Basu tashi da wuri ba saboda sundade basu samu natsuwar yin bacci haka ba har karfe tara,
Muneera ta tashi ta dan gyara gidan sannan ta shiga kitchen tai musu indomie tana ajiyewa kan dining ta juya da niyyar zuwa kiransu sai ga KHALEED ya fito yana sanye da armless riga fuskarshi da faraa yace"Mama sannun ku fatan kin tashi lpy?"
Tana murmushi tace"Eh ya karfin jikin?"
Yace"Alhamdulillah "
Ta ja masa kujera ya zauna tace"Bari na taso WALEED ita Zarah barinta zan ta kara hutawa"tana rufe baki WALEED yace"Mama good morning"
Ta juya garesa tana dan murmushi tace "Lpy lau ya gajiya?"
Ya ja kujera ya zauna ya bude warmer yaga indomie ya dago yace"Mama patient ma ita zaici?"
Ta kalli KHALEED tace"Indomie na dafa ko akwai abinda kakeso?"
KHALEED ya harari WALEED sannan ya girgiza kai,
WALEED yayi murmushi ya zuba masu ta zauna duk suka sa spoon suka fara ci.
Suna cikin ci Zarah ta bude kofa ta fito WALEED da KHALEED na saitin ta dukkansu suka kalli gun kasa_kasa batare da an fahimci sun kalli wurin ba,tana sanye da riga da sket atamfa cikinta ya dan fito ,
WALEED ya meda idonsa kan plate dinsa ya cigaba da cin abincinsa,
KHALEED ya cigaba da kallonta a asibity kullum da hijab jikinta baisan cikin ya fito ba yana mamaki ya dauke idonsa.
Zarah ta zauna kan seat duk bata kula sun ma kalleta ba Muneera tace "Zarah har kin tashi ?"
Ta daga kai ta gaidata tare da WALEED sannan ta kalli KHALEED tana jin sonshi tace "daddy ya jiki?"
Yace"Dasauki"a takaice batare da ya kalleta ba,
Ta zuba indomin ta fara danci a bakinta babu dadi hakanan ta cigaba da cin a sannu.
suna gab gamawa muryar KHALEED sanyaye yace"WALEED idan ka gama ka kai Zarah antenatal "
Duk suka ji maganar wani iri WALEED ya daure yace "Toh"
Muneera shiru tayi tana ganin kokarin KHALEED da kulawarsa da tuno last zamansu kafin ya fadi ta lumshe ido ta bude ba yadda ta iya tunda ya riga ya tsinka duk igiyoyin auren.
Zarah kam gabanta ne ya rika faduwa tana ganin hadata da WALEED din kamar wani abu ne daban duk da tasan KHALEED din bai lpya ta zubawa plate din gabanta idanu da suka cika da hawaye zuciyarta na zafi kafin yan seconds hawayen suka rika diga cikin abincin dake gabanta,ta tashi ta shige daki ta wuce toilet tana kuka a hankali don kar suji ,tana hakuri tana dauriya amma dolene tai kuka wani abu da bata taba gani ko jin ya faru ba shine yake shirin faruwa da ita.
Ta dade da tashi bawanda yayi ko da motsi kowane idonshi kasa,Muneera ta katse shirun da mikewa ta dauko maganin KHALEED ta dawo ta fara ballar masa tsoronta daya su koma asibity ko kuwa ayi me kankat saboda kafin Likita ya sallamesu ya gargadesu da bata masa rai da barinsa cikin damuwa,
Tana gama ballar masa ta mika mai ya amsa ya fara hadiya daya bayan daya ,yana shanyewa tace"Ka koma daki ka kwanta ka kara samun Hutu"
Baice komi ba ya tashi ya nufi dakin ya kwanta yana hana ranshi baci zuciyarshi na fadamai WALEED zai kula da ita.
Muneera ta nufi daki aka bar WALEED zaune shi kadai akan dining yana tunani Zarah bata sonshi ya gama fahimtar hakan.
Akan gado ta samu zarar idanun jawur taiwa cikin kuri tana kallonshi Muneera ta zauna ta dafa cinyarta,
Zarah ta kasa dagowa su hada ido sai ma kara sunkuyar dashi tayi,
Cikin rarrashi Muneera tace "Zarah bai kyauta miki ba shima ya san haka, amma ina rokon ki dan Allah karki rainasa ta hanyar yin watsi da maganarsa ,kiyi masa biyayya ki basa girmansa"
Zarah bata ji dadin Maganar ba yaya zaai ma soyayyarsa ta barta harta bijire masa? tana jin bai kyauta mata ba amma ba zata ki maganarsa ba saboda tana sonshi,
Kasa cewa komi tayi ta daga kanta wasu hawayen na kara cika mata ido ,
Muneera tai murmushi tace "Allah ya miki albarka ki tashi kisa hijab ku tafi jinya tasa namanta da awon"
Ta tashi ta dauki hijab ta fita falon WALEED na ganinta da hijab ya taso Muneera ta biyo bayanta tace masa"Idan kun dawo ka biya ka dauko masu kayansu su dukan"
Ya kalleta yace"To mama sai mun dawo "ya juya ya fita ta bi bayanshi jikinta sanyaye har bakin mota ya bude mata ta shiga ya shiga ya rufe ya dauki hanyar asibitin.
Tunda suka shiga motar bawanda ya kalli wani ,motar shiru har suka isa ya fita yana niyyar zagayowa ya bude mata ta bude ta fito yana ganin haka yayi gaba tabi bayanshi jiki a mace,
Ya siya kati suka shiga ganin likita a tare ,Ta rubuta masu test har dana fitsari duk suka yo suka dawo da result ta duba ta dago tana tambayar " Matarka ce?"ganinsu yara kuma tsaran juna.
Maganar tasa zuciyarshi zafi ya girgizakai yace"she's my sis"
Tace"OK ki tashi ki hau gadon can "
Zarah ta tashi ta hau gadon likitan ta tashi taja masu labulen daya rufe gadon ta fara dubata,
WALEED yaji kamar ya tashi ya fita amma ya zauna yana jiran fitowar su.
Mintuna 15 suka dauka sannan suka fito Bayan ta zauna tayi rubuce_rubuce ta dago tana kallonshi ta cikin glass tace"Cikinta lafiya lau sai de jininta baya normal state a kula da ita sosai ga wasu drugs zaku dawo nan da 2weeks"ta mika masa papern ,ya amsa ya rike ya dan kalli Zarah,
Likitar ta kalleta tace"Ki kwantar da hankalinki ki rika cin abinci kinji"
Zarah ta lumshe ido
ta bude ta tashi tai gaba,WALEED yayiwa doctor sallama ya koma mota suka dauki hanyar gida ,suna isa ta bude tai shigewarta ciki,
Ya kashe motar ya dauki ledar drugs dinta ya shiga, a falo ya samu Muneera zarar na gefe Muneerar na fadin sunyi saurin dawowa ,ya ajiye kayan gefensu ya sake fita ya nufi gidan KHALEED ,
Tunda yayi parking yake tuno ranar da suka zo wurin hankali tashe ,yana kallon gate din ya kashe motar ya fita ya bude gidan ya shiga yana tafiya a hankali yana kallon inda ya samu KHALEED kwance tuno halin da ya sameshin yasa idanunshi cika da hawaye ko yaushe yana tuhumar kanshi domin shine sila ya dauke ido ya bude gidan ya shiga,
Watanni babu su cikin gidan amma haryanzu gidan na kamshinsu yanata kallon falon ya wuce bedroom,
Idanunsa suka sauka akan bed din nan da ganinshi ya sashi suma bed daya samu masoyiyarsa kwance akai bayan daddynsa ya gama kasancewa da ita a matsayin mata,zuciyarsa ta harba ya kawar da kai tare da rumtse ido yana hango yadda ya sameta jikinta nata rawa,
Da sauri ya nufi wardrobe dinsu ya jawo katon trolley guda biyu ya fara cusa kayayyakinsu daya bayan daya ya kwasa da yawa ya rufe yaja akwatinan waje tare da rufe gidan.
12:45 ya koma gidan ya ajiye kayan Zarah a falo ya shiga dana KHALEED ciki,KHALEED ya kalleshi ya kalli kayan yayi shiru,
WALEED yace"Daddy ya jikin? Mama tace a dauko su"
Ya matse lips tare da daga kai yana jinshi takure ,WALEED ya sake fita ya nufi gidan su HAMEED ya sameshi har lokacin yana bacci yayi tsaye kansa sannan yayi murmushi ya fara magana "Ka tashi lokacin sallah yayi"
HAMEED ya bude ido ya kalleshi yayi hamma ya tashi zaune yace"Ya daddy da jiki?"
WALEED yayi murmushi yace"Da sauki sosai"
HAMEED ya mike yace"Nasha bacci jikina kamar an jibgeni, Bari nayo wanka mu fita masallacin"ya tashi ya shiga toilet,
Yana fitowa ya zira kaya ya fara shafawa fuskarsa lotion suka ji daddynshi na kwala mishi matsanancin kira yana doso dakin,HAMEED ya tsaya da shafa man zuciyarsa na harbawa har daddyn ya shigo, cikin fada yace"HAMEED har kayi girman da zaka siyar da gidanka batare da sanina ba?"
Gaban HAMEED ya kara dumm ya sunkuyar da kai,daddyn na masifa yace"Da kai nake magana"
HAMEED ya kalli WALEED da ya sunkuyar da kai a hankali yace"Ka jirani waje"
WALEED ya tashi jikinsa sanyaye ya fita yana fita HAMEED yace"Kayi hakuri daddy"
Daddyn yace"Yimun shiru ka fadamin me kayi da kudade masu yawa haka?"
Murya sanyaye HAMEED yace"Daddyn WALEED ne baya lpy WALEED bai da kudi shine na siyar da gidan na basa kudin sauran suna wurina"
WALEED na bakin kofa yanajin maganar HAMEED idanunshi sukai Ja wannan abota ce ko yan'uwantaka?gidanshi ya siyar saboda lafiyar daddynsa bayan ya hanasa siyar da motarsa ,ya fara tafiya zai bar kofar idanunshi cike da hawaye yana tunani ashe son da HAMEED ke masa harya kai haka?dame zai saka masa ne ? don ya masa komi tunda har daddynsa ya warke ,
Daddyn HAMEED yayi shiru jin dalilin HAMEED ,
HAMEED ya dago kai yace"Dan Allah daddy Kayi hakuri"
Daddyn ya sauko da murya yace"Amma meyasa baka tambayeni ba? "Ya numfasa yace "shikenan da muna maganar next week a tura neman aurenka yanzu ba maganar sai time da Allah yayi"
HAMEED ya jinjina kai yana matse lips zai hakura har lokacin,daddy bai kara cewa komi ba ya juya ya fita daga dakin,HAMEED ya tashi ya karasa shafa man yana dedeta kanshi ya fita ya samu WALEED tsaye bakin motarshi yayi murmushi yace "Sorry muje in mungama sallah mu wuce gida na gaido daddy har na cika cikina da abincin Mama"
WALEED ya kallesa ya kakaro murmushi ya bude mota ya shiga ya tada,HAMEED ya shiga yanata jawo labarai bayan sunyi sallah masallaci suka wuce gidan ,
Suna zaune Muneera ta gama ta fara kaiwa Zarah nata a daki don tunda ta shigo dakin tana kwance ko hijab ta kasa cirewa ,ta jera masu dining suka zauna Su hudu suna ci HAMEED nata yaba girkin .
Da dare Zarah ta taya Muneera dinner tana ta fama da hijab,ana gamawa ta shige ciki Muneera ta kara kai mata nata ciki don tausayinta ta keji sosai,
KHALEED yasa spoon yana dan cin abincin zuciyarsa na kan Zarar ta ci ko bata ci ba ?meyasa bata fito ba ? Bai shirya magana ba sai tsintar kanshi yayi da cewa"Mama Zarah ta ci abinci?"
Har a zuciyar WALEED yaji badadi wani irin abu ya taso masa baya banbantashi da kishi ya hadiye ya cigaba da cin abincinsa.
Muneera ta kalli KHALEED tace"Can take son ci naga anan bata wata sakewa ta ci"
Bakin KHALEED ya mutu jin sakewa, shi so yake su koma kamar da matsayinsa na uba ita diya ,yana kula da ita tana son shi da girmamashi,
Suna kara ci WALEED ya mike yana balle botira alamun zai shiga wanka yayi gaba,Muneera na fargaba ta kalli KHALEED tace"Ka dai cireta a ranka din ko?"
Bai bata amsa ba sai murmushi me sauti yayi sannan yace"Tunda na fahimci WALEED na sonta nayi haka Mama ,yanzu ina mata kallon kanwatane kawai"
Muneera ta dan murmusa tai shiru tana tuno sabbatunsa lokacin da yake akan gadon asibity,
KHALEED yayi shiru yana magana a heart bai kallonta fa bai kuma yi komi ba iyaka de yana kula da lafiyartane amma har....Sai kuma yayi shiru sannan yace shiyasa nake son tsarina ya tafi cikin lokaci.
Muneera na shiga ciki ta samu Zarah tace"Zarah ki dena takure kanki ki saki jiki cikin yan'uwanki dan Allah "
Zarah ta daga kai don bata fatan ranar da zata bijirewa maganar Muneera ,daganan ta fara fitowa suna zama dining bayannan har suna kallo a falo daya,WALEED da KHALEED cikinsu bame mata dogon kallo itama ta kasa yiwa daya daga cikinsu haka ,ko cikin jikinta ma duk ta dora idanunta a kanshi the next thing da zata tuna shine KHALEED soyayyar bata goguwa,
Suka cigaba da rayuwa hakanan sosai suke bata kulawa komai WALEED ya samo zai kawo ya ajiye don ita da cikinta fruits dinnan dai har gajiya suke su rube saboda wasu na tarda wasu,Muneera kuwa wani lokaci abincin sai Wanda Zarah ta zaba ,KHALEED kam hakan na masa dadi sosai .
office din su KHALEED tunda ya dawo suka fara kawo masa aiki gida yanayi da yaga ya samu sauki yasa ran komawarsa sati me zuwa.
****
Bayan two weeks
Ranar KHALEED bayanan WALEED kuwa yana dawo da ita daga awo ya fice,daga ita sai Muneera saiga su Ladingo sun shigo tare da kawu habu,Wani farinciki ya mamaye Zarah ta fara murmushi domin ta gaji tana son ta samu relief,
Zuciyoyin su Ladingo sukai rauni ganin ciki a jikin Zarah basu sani ba ba kuma suyi tsammani ba sukai sukuku amma sunji dadi sosai da samun KHALEED ya samu lafiya ,
Suna nan har dare WALEED ya dawo suka gaisa yawuce ciki,KHALEED na shigowa yayi ido hudu da Ladingo ya sunkuyar da kai yanajin kunya ya gaisheta ta amsa tana ta masa sannu sannan ya fita ya samu kawu Habu suka gaisa sannan ya koma ciki yanajin nauyin ganinsu.
Ba kowa dakin sai su, Ladingo na sallar shafa'i da wutiri Zarah ta zo ta zauna gefenta tana jiran ta sallame ,Ladingo na sallamewa ta juyo tana kallonta ta rame cikinta ya turo amma a haka yafi lokacin da suna jinyar KHALEED asibity, tana dan motsa baki saboda lazimi da takeyi ta dan tsaya tace"Ya ya Zarah?"Ta karasa da kallon kwayar idanunta
Zarah ta danyi shiru idanunta cike da hawaye tace "Dan Allah inna ku tafi dani"
Ladingo ta bita da ido tana kara kallonta ada ta rasa wa zata tausayawa Zarah? WALEED?ko KHALEED? don duk ta karancesu kuma ta fahimci halin da suke ciki,amma yanzu haka har tafi tausayawa KHALEED saboda bai lpy he's (albino)duk da haka ya sadaukar da soyayyarsa Wanda sanadin hakan ya kusa tafiya barzahu.
*SHIGAR SAURI*
Painful love story
Romance special
Writing by
*MAMAN MAMY (SHALELE)*
*Wattpad@mumies122*
*Dedicated to my close friend ikra Rukayyat*
*Devoted to identical twins hassan & Husain 80k*
*Small gift to my real fans*
*PROFICIENT WRITERS ASSOCIATION*
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/
TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09
Page > 71&72
Fuskar Ladingo hade da muryar rashin jindadi tace"Zarah so kike ki gujesu a lokacin da suke cikin bukatar ki?"ta numfasa tace"Zarah sune mutanen nan da suka ceto rayuwarki suka temaka miki,ke kuma saiki gujesu a lokacin da suke cike da bukatarki?wane hali kike tunanin zasu shiga bayan kinsan duk suna kaunar ki"
Cikin rauni tace"Zarah ki zama me tausayi dan Allah, kuma idan kin bimu Kina tunanin zakiyi rayuwar data fi wacce kikeyi anan dadi?ko kina tunanin samun masoyan da suka fi su?"
Zarah tayi tunanin rarrashi da tausayawa a wurin Ladingo amma sai taji akasin haka jin tana jefo mata tambayoyi,wasu hawaye masu zafi suka zubo mata tana jin tausayin kanta bakinta na rawa tace"Inason na samu natsuwa inna...."ta karashe da kuka,
Idanun Ladingo sunyi ja tana tausaya mata amma soyayyar da suke nuna mata ta wuce a ji tausayinta a hankali tace"Ki samu natsuwa Zarah, ki natsu acikin yan'uwan ki suna son ki sosai, ki rungumi kaddarar rayuwarki ,ke baki jin kunya ne ? domin dagani har Habu bamai iya tunkarar Hjy ko Alhaji da maganar nan"
Zarah ta sharbe hawaye da majina tana tausayin kanta,
Muryar Ladingo can kasa tace" ki tausaya masu Zarah dan Allah ki kwantar da hankalinki ku cigaba da rayuwar ku"
Zarah ta daga kai tare da cewa"Tom"cikin kuka,
Ladingo ta jawo kanta ta rungume ta lumshe ido tana meda numfashi nan ne gatanta nanne aka fi sonta da bata kulawa kuma nan zata fi natsuwa akan can da surutun zai koma na dawowarta da juna biyu,ita kanta Zarar ba ta tunanin zatai hakurin rashin su don tana son su sosai.
Jin motsi yasa ta saki Zarah ita kuma tai saurin tashi ta nufi toilet,Muneera ta shigo dakin ta wuce kan bed ta dau pillow ta sake fita .
Duk da Muneera bata dakin basu kara maganar ba har washe gari suka hadu kitchen su ukku sukai girki suka hadu a dining har da habu anan su kaita gaishe_gaishe sannan suka cigaba da ciye_ciye KHALEED ya riga tashi domin a takure yake ya tafi aiki ,bayan su Ladingo sun gama su kai shirin tafiya,su Zarah sukayo masu rakiya har bakin motar WALEED Ladingo nata kallon Zarah da tausayi ,Habu kuwa ko kallonta bayason yi sabida kar zuciyarsa ta raya masa wani abu.
Suna masu waving suka bar gidan Muneera ta jawo Zarah jikinta suka nufi ciki ,
***
Yau kusan wata biyu bata sashi a ido ba, tayi tunanin tayi rashin barcin ta gaji, yanzu ba zata iya wani hakuri ba, ko ba komi idan ya ganta zai ganeta kuma zai kula ta ko na minti biyu ne,
Cikin shirinta take tana sanye da doguwar rigar atamfa da rigar likitoci akai idan ta fito aiki bata sake bibiyar fuskarta amma sai tsintar kanta tayi da duba madubi duk da bata shafa komi ba sai da ta tsaya tana tuhumar kanta akan duba madubin na miye? ta kasa bawa kanta amsar ta sauke ajiyar zuciya ta zare rigar saman ta gyara white gyalenta akai jikinta sanyaye ta dauki keys dinta ta shiga mota ta nufi skye bank.
Da isarta ta samu wuri tayi parking ta kashe motar sannan ta fito tai mata key waigawar da zatayi taga idanun mutanen dake kan layi duk a kanta, ba yaune take garin ba a cikin year ta fahimci ita din abun kallo ce bata damu ba don harta saba indai ba ta asibity tana shan kallo a asibityn ma don ba kowa ke zuwa ba wasu kuma zasuyi mata kallon Baturiya.
Ta shiga ciki tana tafiya a natse tayi zaton data shigo zata ganshi ashe ba haka ba sai tayi wurin bude account akan zata bude ,da layi ba laifi ta koma gefe ta tsaya a karshe de tasan kafin azo kanta zata ganshi indai yana ciki.
Tana tsaye tana tunaninshi, kyawunshi saukin kai da kuma abinda taji daya tsaya mata a zuciya kullum ta tuno tanason warwarar zancen , minti goma kacal da tsayuwarta taji kamshin turarensa ashe dai ita me saa ce tai saurin daga kai tana kallon yadda yake saukowa daga bene da sauri,
Ta kara gyara tsayuwa don ya kula da ita sosai, yana saukowa haskenta yasa shi kara kallonta sosai domin bayan likitar daya gani a asibity bai taba ganin irin halittar ba a cikin garin,yana dubawa sai yaga ashe Dr dince da kanta ya fasa zuwa inda ya nufa yayi wurinta, bai manta yadda tai ta kai kawo wurinsa ba, bayan haka yana jin tausayinta da duk me irin lalurarsa,yana nufota ta fara dan murmushi harya karaso yana dan murmushi yace"Dr ya aiki?"
Tace"Lpy lau ya karfin jiki?"
Yayi murmushi yace"Alhamdulillah ,,Lpy ko?"
Tana murmushi tace"Na zo buda account ne"
Ya waiga ya kalli layin Yace"Ayya ga layi kin tarar zaki jima sosai yau mutane sun cika ko zaki dawo gobe? Ko kawai kibarmin details dinki saina bude zuwa gobe sai na kawo miki asibity"
Ranta wasai zata kara samun damar ganinshi tace"To ba matsala nagode sosai zanje mota na dawo "
Cikin muryarshi me sanyi yace"Muje"suka nufi kofa tare ,suna zuwa bakin motar ta bude ta fara duba takaddun, ai dole ta bude account gashi har zai zo asibity dan ita kadai ,mutane dake bin layi nata kallonsu ganin halittar iri daya kyawawa kuma (Albino's)
Yana tsaye ta gama hadawa ta miko mishi tare da kudade tana zaune cikin motar tace"Nagode sosai"
Ya kalli nata idanun da suke kamar dark blue ba irin nashi ba yace"Babu komai"ya juya ya koma ciki,
Ta rufe murfin motar tana murmushin jindadi ta tada motar aranta tana ayyana yadda zata ki zuwa aiki gobe daganan zai kai mata sakonta har gida.
Ta na komawa asibity bata dade da zama ba Dr salis ya shigo ranshi bace fuskarnan hade da kakkausar murya yace"Ina kkje?"
Tana masa kallon bangane ba tace"Ina fa? Tun dazu ina asibityn nan"
A fadace yace"Rufewa mutane baki ,Ina kkje?"
Ta kawar da kai tana yamutsa fuska saboda matsa mata da yake sosai data dan fita ko bai ganta ba zai shiga tashin hankali,
Ranshi bace yace"Ohk.. ohk zan kira musty"ya juya zai fita
Fuskarta daure Murya can ciki tace"Ai ban lpya ne"ta karasa da dafe kanta.
Ya juyo yana mata wani kallo yace"Mike damunki?"
A hankali tace "Kaina"
Jikinshi yayi sanyi ya dawo yace"Kin sha magani?"
Ta daga masa kai tana lumshe ido kamar gaske,
Yace "OK tashi na kaiki gida"
Ta tashi ta dauki jikkarta tai gaba yabi bayanta yanajin tausayinta,suna zuwa bakin mota ya bude mata ta shiga ya shiga ya tada suka fita daga asibitin,
Yar tafiya kadan yayi ya shiga wata quarters yayi parking bakin wani karamin gida ta bude ta fito tana yaushi shima ya bude ya fito,
A hankali tace "Nagode"
Yanajin tausayinta yace "Sannu ki ajiye wayarki a kusa sannan idan kinji ciwo sosai ki kirani"
Ta daga mai kai tace"Kar ka fadawa yaya"
Ya daga mata kai,ta juya ta shige gidan tana tafiya a hankali, tana shiga ta baje akan kujera tana meda numfashi ta bude jaka ta fiddo waya tai unlock dinta tana kallon screen din da murmushi dama ace ya kira yanzu taji dadi sosai da zai samu no din wayarta ,a hankali ta lumshe ido tana tuno jinyarshi tana kara tausaya mai, tunda ta ga halin da yake ciki ta tausaya mai ranar da yake sabbatu ranar ta sawa family din alamar tambaya ,hakanan take jinsu kamar yan'uwa kila ko dan taganshi zabaya irin ta
Shi ko Dr Salis ya nufi asibity zuciyarsa cike da tunani ,da yanzu Dr fati ta dade da zama tashi da yanzu sun zama maaurata amma momynsa ta hana ita bata yadda danta ya auri zabaya ba yana lafiyayye,
Wacece Dr fati?waye Dr Salis?
Dr fati diyar abokin daddyn Dr Salis ce ,Mamarta da babanta ba albino bane sunata haihuwa a haihuwarsu ta shidda kwatsam suka haifeta albino sun ji daban amma hakan bai hanasu farinciki da samunta ba suna renonta tana samun soyayyar yan'uwanta dangi har da makota babu wata kyama, shekaru hudu mamarsu ta haifi autan ta shima zabaya suka zama su biyu ne albino a gidansu kuma sune iyaye da yan'uwa suka fi ji dasu akan sauran saboda suna da bukatar hakan, tana girma aka sata school bayan shekaru ta gama degree dinta ,daddynta na neman mata aiki sai daddyn Salis ya samar mata a cikin birni , ya kuma nemi ta zauna a cikin gidansa ,tunda ta zo garin ta ga sabuwar rayuwa da sabon sauyi ko ina tayi kallo har mutanen gidan su Dr din, a hankali kuma suka saba da ganinta ,kullum tare da Dr Salis suke fita aiki saboda asibityn da suke aiki daya cikin kankanin lokaci suka fara soyayya Dr yaje ya fadawa daddynsa yayi murna ta waya yake bawa abokinsa labari shima yaji dadi,mahaifiyar Dr Salis kuwa tunda taji ta nuna rashin amincewarta, kowa ya gama sanin suna soyayya sai da akazo maganar aure momynshi ta kara daga hankali akan bata yadda ba, ta dungi musgunawa Dr fati a karshe de da bakinta ta koreta daga gidan lokacin daddyn shi bayanan, yana dawowa yace saita dawo ko ya saketa Dr Salis da yayyansa su kaita bawa daddyn hakuri duk da sun san bata kyauta ba amma basa so hakan ya zama silar rabuwar auren iyayen su.
Daddy da Dr suka Samar mata gida a quarters suka cigaba da kula da ita,dukkansu tunani suke wataran Mommyn Dr zata sauko zasuyi aure amma har yau taki aminta saboda bata so jikokinta su kasance albino's ko kuwa Dr fati ta gurbata masu zuria, ya zama bayan jikoki har jikokin jikoki aita haifuwar albinos,
Dr fati ta shiga damuwa bata taba tunanin tana da lalura ba sai da ta zo garin sai da Mommyn Dr ta k'i ta karara.Tayi kuka ita kadai, ta ji dama zata koma dai_dai da kowa amma ba yadda ta iya haka Allah yake son ganinta.
Daga soyayya suka koma kamar yan'uwa sai a dade bai iya ce mata I love u ba duk da yana sonta din sosai,A hankali soyayyarshi ta bace a zuciyarta batare da ta sani ba sai gashi ta hadu da KHALEED Wanda ita bata kaiga gane ta fada son shi ba,
*Cigaba*
Ranar bata kayyade kira nawa Dr Salis ya mata ba kafin marece saboda yaji jikinta bai manta ba kullum idan su kai waya da yayanta saiya sake bashi amanarta akan ya kula masa da yar kanwarsa,
Shi ko KHALEED a ranar yayi kokari ya buda mata account dinta tausayi take bashi kasancewarta albino yasha fama yasha tsangwama ta dangi da jamaa bazai taba manta wannan ba duk jindadinsa a duniya.
Yana tashi office ya nufo gida akan hanya yaga me masara yayi parking motarsa yaje ya siya ya cigaba da tafiya baiyi nisa ba yaga me awara ya tuno last time Zarah ta ci sosai ya sake fita ya siya sannan ya nufi gidan .
Bayan yayi parking ya dauko jakarsa da ledojin ya shiga ciki Zarah na zaune kasa ta mike kafafu cikinta ya kara girma don yanzu watanshi shidda ne da kwanaki ,Muneera na kusa da ita hankalinsu duk akan film din waaris da ake haskawa a dadin kowa startime,
Ya dan kalli Zarar tana nan sillenta sai dan fadi da cikin yasa ta yayi sallama,"Assalamu alaikum"
Zarah naji tayi saurin gyara zamanta tare da gyara kafadun rigarta duk da lafiyarsu lau,Muneera ta amsa mai sallamar tana mai sannu da zuwa ,ya karaso ya zauna yana amsawa sannan ya mika mata ledar hannunshi,
Muneera ta bude tayi murmushi sannan ta mikawa Zarah tace"Ga tsarabarki"
Zarah ta amsa ta dan kalli wurinshi batare da ta kalli kwayar idonshi ba tace"Nagode Daddy "
KHALEED yayi dan murmushi da iyakarsa baki ya dan cije lips ya kagara ya ganta ta fara sakewa kamar baya amma yasan hakan bazai faru ba har sai ta haihu har sai ya bar gidan saboda yasan shine damuwarta ,a ganinsa da ya tafi WALEED zaiyi duk kokarinsa wurin cusa mata soyayyar shi.
Ya tashi zai shige ciki WALEED da HAMEED sukai sallama suna dariya,
Muneera ta amsa tana kallonsu tace"Aifa bakwa gajiya kullum zaku shigo da wani salon kuke shigowa"
HAMEED ya gaidata sannan ya meda kallonshi gun KHALEED ya gaidashi,KHALEED na amsawa yace "Mama duk rashin aikinyi ne ya jawo haka kuzo ga aiki na samar maku"
Duk sukai dariya suna ganin abun wasa sai gani sukayi ya zuge jikkarsa ya fiddo wasu takaddu ya mikawa HAMEED daya ya mikawa WALEED ,
HAMEED ya fara zaro ido ya mike tsaye yana cikin tsananin farinciki,WALEED ma na gama karantawa ya mike yana cikin jindadi marar misaltuwa,
HAMEED yaje ya zukunna gaban Muneera yace"Mama duba kiga daddy yasamar mana aiki yanzu mun zama Doctors a imperial Mama ki mana godiya"
Muneera wani irin sanyi ke ratsa zuciyarta tana mai kallon KHALEED tana jin kamar ta meda shi ciki ya kara zama cikinta na tsawon lokaci sannan ta kara haifoshi saboda soyayyarshi a hankali tace "KHALEED kullum ina alfahari da kai kamin komai a rayuwa nagode...Allah ya kara maka lafiya ya kara maka arziki ya baka mace ta gari"
Tunda ta fara magana KHALEED ya sunkuyar da kai idanunshi sunyi ja zuciyarsa na kuna inama bai taba saba mata ba?Yana kula yadda take shiga damuwa lokaci zuwa lokaci kuma yasan bakomai ne ke sata haka ba sai tunanin yadda zasuyi rayuwa nan gaba da Zarah, amma duk da haka tana alfahari dashi.
WALEED na cikin farinciki yana kuma cikin tausayin KHALEED jin da yayi Muneera na masa adduar samun mace ta gari bayan ya samu amma yabar masa duk da baida masaniya ko zai kara samu,
Ya tafi ya rungume shi yana hawaye yake cewa"Daddy....Daddy.... Daddy..."ya rasa me zai fada masa kowace kalma yafi karfinta ya kuma fita daraja,abinda dai ya sani kawai shine yana sonsa,a hankali yace "Daddy I love you"
KHALEED ya rungumeshi yana meda guntayen hawayen dake cikin idonsa yana jin farinciki haka yake so ko da wane lokaci family dinsa su zama cikin farinciki ko da kuwa shi baya ciki.
Zarah na zaune ita dai bata cikin farinciki nata farincikin KHALEED ne kuma ta rasa shi, acikin zuciyarta tace ya damu da kowa bandani,hawaye suka cika mata ido sanin da ta fara kuka zata wargaza masu jindadi yasa ta jawo ledarta ta bude awaran ta rika debowa tana gutsira tana kyafta idanu,
Bayan mintuna KHALEED yayi breaking hug din yace"Bari na shiga ciki na watsa ruwa"ya tashi ya nufi dakinsu yana shiga ya ajiye jikka ya sauke ajiyar zuciya ,abu biyu ya rage masa yanzu yasan zasu temaka sosai saboda itama Zarah jininsa ce.
HAMEED da WALEED suka game su nata murna HAMEED ya kalli WALEED yace"Gida zan gudu na gwadowa daddy"
WALEED yace "Sai goben yana kara kallon takkadar hannunsa"
HAMEED ya juya zai fita ya juyo yace"Zo ka kwashe kankanar ka "
WALEED ya dago ya kallesa ya ajiye papern ya bishi wajen,
Muneera bata kara bi ta kallon waaris ba ta shiga tunanin rayuwar danta ko a ina ya samo duk wannan halayyar ? wasu lokuta tana tuno maganar Kaka da take cewa zaiyi jin kai.ta tabbatar harsashen yana zama gaskiya.
Zarah ma bata kara kallon TV din ba haryanzu tana sonshi tana son ta sake jin muryarshi medadi da sanyi tana fadamata "I love u baby"ta kasa manta kowane moments nasu Wanda shi tuni yayi fatali da irin tunanin,
KHALEED wanka yayi ya fito sukaci abinci tare da WALEED saboda sun makara su Muneera har sunyi dinner dinsu bayan sun gama suka danyi kallo suka koma daki suka kwanta,
Tunanin Dr fati ya fadowa KHALEED ya kamata ya kirata gobe tunda safe ya kai mata sakonta ya duba agogo karfe 11:15 ganin its late yasa bai kira ba.
HAMEED na komawa gida ya shiga ya samu su daddynsa da papern sukai murna sosai daddyn ya kalleshi yace" Yanzu nima na samu kira ka samu aiki a royal hospital"
HAMEED ya gumtse fuska dariyarsa ta bace,
Daddyn yayi murmushi yace "Kai da twin bro dinka amma"
HAMEED ya saki fuska yayi dan murmushi yace "Amma daddy nafison Imperial din "
Daddyn ya daga kai yace"Ba matsala"
HAMEED ya tashi ya fita dakinsa yana murmushi yana tunani da zaran ya samu aiki nan gaba zai aure husnar sa yayi missing mace wani lokaci yanajin inama ya bude ido ya ganshi da ita.
Dr fati ta kwana dokin gari ya waye taga KHALEED shi ko Dr Salis kwana yayi tunanin rashin lpyarta,
Tunda safe KHALEED ya kira Dr fati tana ganin kiran no wani dadi ya mamayeta duk da batasan no dinshi ba,ta dauka tana dan murmushi tace"Ina kwana?"
Cikin sanyin murya yace"Kintashi lpy?"
Tace"Lpy lau "
KHALEED yace"Tun jiya aka buda miki naso na kira amma its late ,yanzu in zan fita aiki zanzo asibity na kawo miki"
Dr fati ta danyi murmushi tace"yau banje asibity ba ban lpy ina gida ka sameni a quarters dake bayan asibity gida na ukku"
KHALEED yace "OK saina zo" ya kashe kiran,
WALEED daya fito wanka yana saurarenshi ya dauke ido ya cigaba da shiryawa hakanan yaji yanason sanin ina KHALEED zaije wacece suke waya da ita?domin yanason ya fara sabuwar rayuwa.
Bayan sun gama shiryawa sukai breakfast suka fita tare da nufin KHALEED zai tafi bank shiko WALEED asibity, WALEED ya dauke hanya sannan ya bula yana bin bayan KHALEED ,
KHALEED na isa gidan ya samu Dr fati tsaye da Dr Salis yana mata ya jiki,kallonsu kawai KHALEED yake tayi a cikin mota yana mamakin yadda Dr ke son albino baya gudunta.
Shi ko Dr motar yabi da kallo har KHALEED din ya fito daga ciki ya karaso wurinsu ya bawa Dr Salis hannu suka gaisa,
Suna gaisawa Dr Salis ya nufi motarshi ya kama hanyar asibity yana hango wani abu akan zuwan KHALEED din,a zuciyar shi yanajin indai zaiyi adalci ba laifi bane.
Anan ya wuce WALEED yanata kallonsu sam baiji dadi ba ya so KHALEED ya samu wata kyakkyawa kamar zarah ko wacce ta fita ba kamar Dr fati ba,Dr fati kyakkyawa ce tana da hanci da baki madedeci girarta baka kwance tsawonta kamar na KHALEED din tana da dan jiki kuma babbace kallo daya ya mata ya gane tayi 27 ko 30 ,a hankali ya tada motarshi yabar quarters din,
Su kuwa Dr Salis na wucewa KHALEED yace"Ya jiki?"
Tai dan murmushi tace "Alhamdulillah "
Ya mika mata papern ta amsa ta duba ta dago tace "Nagode kwarai"
Yayi murmushi ya shiga mota ya tafi,ta koma gida tana farinciki burinta ya cika ta samu no dinshi ya kuma san address dinta tai shiru tana tunanin miye amfanin duk hakan? Zuciyarta ta bata amsa da So ,
Ta danyi jimm itace zata fada mishi kalmarso kenan? Itace zata nemeshi? Tasan bai wani damu da ita ba itace dai zuciyarta ta kawo mata sabon Lamari.
WALEED ya tafi da tunani zuciyarsa na fada mishi idan suka dedeta zai kasance yana tare da me kula da lpyarshi amma baiso ta kasance albino ba.
Da dare KHALEED ya dawo hakanan tunanin Dr fati ya dawo masa shi dai yana tausaya mata gata mace,ya shiga ciki ya kira ta,
Tana kwance tana bacci don dole gobe ta fita aiki ta kwana sai taji ring ta dauka ganinshi yasa ta tashi zaune tana murmushi ta dauka ta kara a kunne,
KHALEED yayi sallama yace"ya jiki inafatan da sauki"
Tai murmushi me sauti tace"Naji sauki gobe ma zan fita aiki"
Sai taji ya sauke ajiyar zuciya yace"Sannu sai da safe"
Tana cikin wani yanayi tace"Nagode"ta kashe ta koma ta kwanta tana murmushi ,
Shi kuwa yana gama wayar yaga WALEED tsaye bakin kofa bai ko damu ba ya ajiye wayar ya nufi toilet wanka,
Haka suka cigaba da gaisawa ta kira ya kira har suka saba, ranar asabar saita gayyaceshi akan ya kawo mata ziyara,
Ya shirya cikin kananun kaya kamar yadda ya saba sun masa kyau sosai duk da yake dama shi din me kyau ne karfe 4:30 ya nufi gidan nata,
Sai da akayi laasar sannan ta fara shiri cikin doki take makeup ji takeyi kamar bata taba farinciki ba irin yau ,da tambayar ya kawo mata ziyara ya amince,ta gama kwalliya fuskarnan tasha makeup ta bude wardrobe ta tsaya zaben kayan da zata saka ta jawo wata doguwar rigar atamfa green ta kanga ta mata kyau amma sai taji batayi ba ta janyo wata doguwar rigar ta material lace fari da kwaliiyar purple taji itama batayi ba ,tai tsoki ta daga kayan sama ta janyo wani material lace pink color tana kangawa ta saki murmushi ta fara sakawa tana shirya firar da zasuyi a ranta.
Yana isowa bakin gidan yayi parking ya kure dan karamin gidan da kallo da akwai tarin tambayoyi kanshi ina family dinta? Meyasa take zama ita kadai?.
Zuciyarshi ta bashi zaka ji idan ka so,Ya lumshe ido ya bude ya dauki wayarshi yayi dialing no dinta da yayi saving da doctor,
Tana cikin dora dankwali ta ji ring din wayar dake kusa akan mirror tai sauri ta dauka ta kara a kunne,
Yayi dan murmushi yace"Ina waje"
Dadi ya kara mamayeta tace"ina fitowa yanzu"ta meda kallo a mirror ta daura dankwalin ta baya ta dan dagashi sama har gashinta ya dan fito, ta dora dark pink gyale a kafada ta dauki turare body roll ta kara murzawa, ta ajiye ta dan kalli kanta na seconds ta juya ta dauki milk purse tasa wayarta ta saka flat shoes suma milk ta nufi kofar da sauri tana cike da dokin ganinshi.
Yana cigaba da kallon kofar gidan ta bude ta fito tana tafiya a natse kanta kasa, ya tsaya yana binta da kallo yadda yaga tasha kwalliya, tayi wani bauu a ido yadda duk Wanda ya hango zaiso kara dubawa ,
Kafin ta karaso ya bude ya fito ya tsaya tana karasowa kamshinta medadi ya buge nashi kamshin ,ta dan kalleshi tai murmushi tace"I'm sorry na barka kana jira"
Yayi dan murmushi ya girgizakai yace"Don't mind"
Su kai shiru su duka,
Tai murmushi tace"Mu shiga daga ciki kasha ruwa"
Ya kalleta ya karayin murmushinsa me kyau yace"kamar Zaifi mu fita waje"
Ta daga kai tana jindadin hakan a ranta ,
Ya zagaya ya bude mata mota ta shiga ya dawo ya shiga ya tada motar su ka dau hanyar wani bright garden ,akan hanya suna shiru music din this is life na playing very low ,idanunta na gaban motar thinking of what to say while shi hankalin ya rabu biyu yanason sanin wacece ita.
A hankali yace "so u reside here alone?"
Tana dan murmushi tace"Yes"
Ya danyi jimm sannan yace"What about ur family? "
Ta sake yin murmushi tace"I have my family ,Mommy Daddy ya musty and...."tai murmushi me sauti ta sunkuyar da kai ta dago a hankali tace"I've happy family"
Yayi dan murmushi jin maganarta yaji dadi sosai jin hakan amma yana son kara sanin abubuwa game da ita zaifi samun natsuwa,
Da muryarshi me dadi yace"Aiki kawai kike anan?"
Tace"Ihm an samar mun aiki anan"
Ya kalleta yace "Wane gari?"
Tace "Tunga state"
Lokacin sun iso baice wani abu ba sukai parking ta bude ta fita ya kashe motar suka jera suka nufi cikin kayataccen wurin ya siye drinks suka je kan wani table suka zauna aka kawo masu drinks, ya dauka ya zuba mata a cup ya zuba,su ka dauka a tare su ka sha,wurin tsitt iska nata kadawa ko ina ya kalleta yace"Garin ku akwai nisa kuwa"
Ta jinjina kai ta ajiye cup dake hannunta,
Yayi shiru bai fahimci tana cikin wata matsala ba ko da yake bazai sani ba a yanzu,
Muryarta ta katse shi tace"Kai fa?"
Ya kalleta yayi murmushi yace "I love my family Mom WALEED And Zarah"ya karasa da lumshe idonsa.
Tai murmushi tace" She's ur wife ko?"
Ya kalleta ya sake lumshe ido ya bude da murmushi bakinsa yace"No she's my sister "
Tai karamin murmushi amma a fahimtar ta kamar bond din yawuce nan yadda ya farko yana cewa he love her dasauran kalaman da yadda Zarar ta shiga damuwa sosai,
Bayan ya fada mata haka sai yaji yanason fada mata gaskiyar he never tell any one before,
Zuciyarta na cike da wasi_wasi tana so ta ji yana da aure ko ya taba ?ta bude baki zatai masa tambayar kafin ta furta yace"she was my wife before,amma I divorce her for my brother "
Ta kura masa ido jin wani abu da batai tsammani ba ,
Idanunshi su kai ja Sai da ya hadiye miyau me zafi yanajin ciwo a heart dinshi Yace"yana sonta dole na rabu da ita even though she's pregnant "
Dr fati tana ta kallonshi jin amsar tambayoyinta yasa hawaye suka cika idonta a hankali suka ziraro daga ido daya tasa yatsanta ta daukesu tana tausaya mishi,
Yayi dan murmushi ganin tana goge hawaye yace"Babu komai it's normal"
Ta kure shi da ido tana kallon shi ya dauki lemu yasha ya danji relief sannan yace"Banajin boye miki komi u r like friend "
Ta cigaba da kallon shi jin kallon Kawa kawai yake mata a zuciyarsa.
Yana kallon wani wuri yace"If I had known daban aureta ba"ya karasa da kallonta ganin ta shiga damuwa sosai yasa shi murmushin daya bayyana fararen hakoransa ya sauya zancen da cewa "Bani labari ,u r engaged da Dr ko?"
Ta jinjina kai tana matse lips a hankali tace "That was before" tuno abubuwan daya faru yasa ta fara hawaye,
Ya meda hankalinsa kanta zuciyarshi na zafi dama ta dade tana fadamai tana da damuwa amma bai ga alamun hakan ba.
Muryarta na shaking tace"We r in love amma Mamansa bata sona"
Ta dago hannunta tana kallo ta jujjuyashi tace"Just because I'm Albino batason ta samu zuria...Albino"ta karasa da rufe bakinta da hannun tana boye kuka zuciyarta na tsananin zafi.
Idanun KHALEED da suka koma ja na kanta, yana mata kallon tausayi zuciyar shi kamar zata fito labarinta ya taba mishi zuciya miye laifin Albinos? Allah ne ya haliccesu haka badon sun zaba ba,don me zaa rika kyamarsu da nuna masu kamar su ba mutane bane,
Ya kawar da kanshi gefe farko baisa zai kara aure ba saboda ya rasa wacce yake so da tsoron kar ya haifi albino irin shi amma yanzu son auren ya shige shi ba da kowa ba sai da ita duk da kwakwalwarsa ta gama lissafin *Albino + Albino =Albino's* he really don't care .
*SHIGAR SAURI*
Painful love story
Romance special
Writing by
*MAMAN MAMY (SHALELE)*
*Wattpad@mumies122*
*Dedicated to my close friend ikra Rukayyat*
*Devoted to identical twins hassan & Husain 80k*
*Small gift to my real fans*
*PROFICIENT WRITERS ASSOCIATION*
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/
TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09
Page >73&74
Ya juyo da fuskarsa yana yi mata wani kalar kallo dabai taba yi mata irinshi ba, lokaci daya soyayyar ta shige shi sakamakon tausayi, ya fara kare mata kallo sai yaga ta kara masa kyau fiye da yadda yake ganinta duk da sai a yanzu ya kula da gashinta da yadan fito wanda kalarshi ta kasance fari amma hakan bai sashi sauyawa ba,
Ya hadiye komi a hankali yace"Sorry ,idan bata son hada zuria dake just because u r albino tana iya haifuwar su batare da hakan ya faru ba"
Ta tsayar da hawayenta tana kallonshi,batasan ana fuskantar duk Wadannan ba sai a garin nan, muryarta na sarkewa tace"Haka kayi rayuwa anan?"
Da idanu ya nuna mata "Eh"ya kara da cewa" amma bandade ba mahaifina ya kaini karatu waje "
Ta matse lips dinta ita din iyayenta basu da wannan halin ,da anan take sai dai tayi hakuri,
Ganin ta shiga dogon tunani yasa shi cewa"Kar ki damu komi lokaci ne"
Ta daga masa kai ta dauki lemu tana kurba don taji sauki,
Su ka dan kara fira sannan suka shiga super market dake cikin wurin yayi mata shopping suka fito suka nufi gida,a bakin kofar gidan yayi parking ya fito harya zagayo ya bude mata tana zaune tana tunani ,ya kalleta na seconds sannan ya kirata "Doctor"
Ta dago kai a hankali idanunsu blue and green suka hadu ta dauke nata ta fito a motar tana gyara gyalenta a kafada,
Tana tsaye ya bude boot ya dauko kayanta ya mika mata ta amsa tace"Nagode"
Yayi murmushi yace "Sai yaushe kuma?"
Wani dadi ya lullubeta ta mayar masa da murmushi tace"Ko yaushe u r welcome"
Ya jinjina kai yace"Bye miss u"
Ta kalleshi tana murmushi ta wuce ciki miss u din da yace ta sata jindadi sosai,
KHALEED ya koma mota ya dauki hanyar gida yana tunanin ta, idan har yace zai aureta sai ya sauya tsari domin ranar Monday din nan yake tsammanin kiran lecturer dinsu da yayi masa alkawarin duk in yaso dawowa London ya nemesa, bayan ya saki Zarah ya neme san kiransa kawai yake jira ya bar kasar gabadaya.Amma yanzu dole ya kara watanni saboda yanason ya dauketa su tafi tare bayason ta kara fuskantar wani bakinciki bayan Wanda ta shiga ya tabbatar in suna tare bazata fuskanci hakan ba,
A masallaci ya tsaya yayi salloli bayan ishai ya shiga gida Muneera na ganinshi sukuku taji gabanta ya fadi Tana kallon shi tace"Lafiya lau kake KHALEED?"
Ya daga mata kai ya danyi murmushi yace "Ciwon kai ya dan taso mun amma yanzu zanje in kwanta"
Tana tausaya masa don baa kwanaki sai yayi tace"Sannu Allah ya sawwaka"
Yace"ameen"yana kallon falon yana neman Zarah da ido ganin batanan yasa shi wucewa dakinsa ya shiga wanka.
Bayan ya fito suka hadu falo Muneera tayi tuwo miyar Kuka suna ci yana tunani ,dukkansu sun lura da yanayinshi sai suka tsinci kansu cikin damuwarsa,
Ya danci ya tashi ya koma ciki ya shiga toilet yayo brush ya fito ya kwanta yana nazari da Sannu zuciyarsa ta bijiro mai da idan bata Sonka fa? idan haryanzu Dr salis dinta takeso fa?
Yayi saurin jawo wayarshi ya kirata baida isashshen time ya kamata ya gama komi cikin lokaci kafin ya kure masa,kiran na shiga ya ji b'i_b'i alamun she's busy,
Ya kurawa kusurwar dakin ido yana tunanin tana waya da Dr ne suna soyayya,wani kishi ya taso masa ya meda wayar ya ajiye ,Zuciyarsa ta kasa hakura ya kara dauka ya kirata,
Tana kwance ta dauka tai shiru,
Cikin sanyin murya yace"Ba kiyi barci ba?"
Tace"Uhmm! Ina kwance"
Yayi shiru ,tace"Ya gajiya?"
Yayi murmushi yace "Babu, gobe da safe ma inaso in kawo miki ziyara"
Ta tashi zaune tana murna, har yana jin motsinta tace"am..am sai kazo u r always welcome"
Yayi murmushi yace "at 8 insha Allah"
Tace"Nagode"
Jikinsa sanyaye ya kashe wayar yana kallon screen dinta,
Da safe lahadi ya tashi jikinsa a sanyaye sukayi breakfast kowa na masa ya jiki, ya koma daki ya fara shiryawa domin zuwa wurinta,
WALEED ya shigo ya zauna gefen bed yanata kallonsa a mirror, KHALEED ya hangesa ya juyo yace" WALEED ya dai?"
WALEED yayi shiru idanunsa kasa ya bude baki a hankali yace "Daddy ba ku dace da ita ba"
KHALEED ya zuba mai ido sai yayi murmushi mai ciwo yace"Saboda tana albino ko?"
WALEED ya dago ya kallesa ya meda kansa kasa yace"A,a "cikin zuciyarsa yana fadin Zarah ta fita komi.
KHALEED yace "To meyasa?"
WALEED yayi shiru, KHALEED ya matse lips ya juya ya cigaba da shiryawarsa ,WALEED ya kasa kara cewa komi ya tashi zai fita,
KHALEED yace"Nima irinta ce WALEED ko kamanta?"
WALEED bai juyo ba ya fita zuciyarsa na zafi yana inama ya daina sonta ya samu wata dai kamar Zarah,
KHALEED na gama kimtsawa ya fito yanata kamshi ya wuce su Muneera da Zarah ya fita ,Zarah na zaune cikinta yayo sama ta bishi da karamin kallo tana ji a jikinta wani abu na shirin faruwa,
Yana cikin mota yake hada kalmomin da zai tunkareta harya isa ya Ciro waya ya kirata ,bata kashe wayar ba ta fito ba kwalliya bakomai tayi wani b'attt ,ya fito a motar yana kara kallonta ,
Tana dan murmushi tace "Barka da safiya"
Yayi murmushi yace "Na sameki lpy?"
Ta daga kai tana kallon yadda yayi kyau cikin kananun kayan jikinsa,
Cikin sanyin muryarsa yace Ban gaji da ganinki ba shiyasa nai sammako"
Tai murmushi tace "Nagode"
Suka yi shiru sannan yace"Yau baki gayyaceni ciki ba"
Tai yar dariya tace"U r welcome "ta nufi gidan tana gaba yana baya,
Ya shiga ciki yana kallon wurin da ganinsa tsohon gini ne amma yasha gyara sosai, bata zauna ba ta kawo masa dan toast bread da coffee ta ajiye gabansa ta koma kujerar dake facing dinsa ta zauna tana kallonsa ,
Ya kalli plate din yayi murmushi ya riga ya kimtsa kafin ya fito hakanan ya dauki coffee din ya dan surba ,ya ajiye cup din yace" Gidanki na da kyau sosai "
Tai murmushi kawai ta yi shiru tanason ta ji meya kawosa tadesan ba Kalmar so bace,
Bayan minutes fuskarsa na kallonta ta tsinci muryarshi da cewa "Doctor misali idan nace inasonki zaki amince ?"
Ta kalleshi tai dariya ta dauke fuska tana ganin wasansa ne yake tai shiru,
A hankali ya memeta "Inason na aure ki idan kin amince"
Ta zuba mai ido tana kallon yanayin yadda yake maganar idanunshi na yi mata wani kalar kallo,
Ganin batace komi ba ya sashi cewa"Idan kina tare dani bazaki fuskanci kyama da gori ba doctor, nasan komi, za muyi rayuwar farinciki tare "
Hawaye su ka fara zubo mata na farinciki tana sonshi tun yana asibity ta ji ta damu dashi da danginsa ,ta ji matukar dadi da ya furta mata Kalmar so ashe dama yana sonta? ta fara tuno daga haduwarsu zuwa yanzu yadda yake nuna mata kulawa da yadda jiya tausayinta ya bayyana karara a fuskarsa , dama hausawa na cewa idan da So da tausayi....
Ganin hawayenta yasa zuciyarsa yin sanyi ya sauke numfashi ya lumshe ido yadan natsu ya bude ya fara rarrashinta "I'm sorry Nasan baki sona kina da zabi amma ina son ki dan bani dama zan koya miki sona a hankali"
Ita da ke kuka sai dariya ta subuce mata ya tsaya yana kallon fuskarta ganin dagaske dariyar ce yasa shi murmusawa yana kara kallon yadda dariyar ke kara mata kyau,
Tana dariyar me mixed da hawaye tace"Ashe dama kana sona? Nayi zaton ni kadai nake dakon soyayyarka ,tunda naganka a asibity na ji na damu da kai shine dalilin da yasa bansamu sukunin zama ba har saida ku ka bar asibitin ,bayan nan kuma na kasa hakurin rashinka, na tuno wani yazo dubaka yake fadawa Dr kai manager dinsu ne shiyasa naje na bude account don kawai na samu damar rinka ganinka"
Tana murmushi tace " ashe dama kana sona?"ta jefa mai tambayar.
Ya lumshe ido zuciyarsa na kara tausayinta tashi zuciyar Zarah kadai ta So sai yanzu da ta fara kamuwa da nata ,
Ya bude idanunsa yana kallon idanunta yace "Inason ki doctor"
Ta sunkuyar da kanta kaunarshi na kara shigarta ,
Yayi murmushi me sanyi yace"Zuciyata ta dade da kamuwa, to yaushe zamuyi aure ? Inason ki gabatar dani awurin su Dad...nan da months zan koma London ina fatan ba matsala? "
Ta dago ido ta kalleshi cikin dan jin kunya tace "Ka samu Dr salis ka fadamai komi"
Ya jinjina kai yace "Ki bani no dinsa"
Ta fara karanto masa bako kuskure hakan ma ya taba ranshi yayi saving ya dago ya kalleta tai saurin dukar da fuska kasa,ya mike tsaye yace"Sai munyi waya"
Ta tashi tana fadin"Sai ka dawo da anjima dai"ta karasa da kallonshi
Ya sakar mata murmushi ya juya ya fita a gidan ,Dr fati ta ruga bedroom ta fada kan bed tana mulmula dadin da takeji yawuce misali ,
KHALEED na isa gida ya samu Muneera har kitchen Zarah na gefe tana dan kama mata aiki, ya kalleta tana ta zukewa ta koma very silent duk idan ya kalleta bai jin dadi, ya meda kallonsa ga Muneera yace"Mama inason magana ne"
Muneera tace "inajinka"tana cigaba da aikinta
Ya kalli zarar da hankalinta na kan zobo da take hadawa ,yace"Mama akwai wacce muka daidaita da ita"
Kirjin Zarah ya doka hawaye suka cika mata idanu ta dage kokarin medasu.
Muneera ta tsaya da komi tana kallonshi da dan murmushi ai itama batason zaman shi hakanan abun ya dameta ,tace"Nayi farinciki yaushe zaka kawomin ita?"
Yana murmushi yace "Sai kome ya dedeta yanzu inason ki samu su kawu agama magana"
Ta dan rage faraa tace"Wacece ?"
Ya dan sosa gefen fuskarsa yace"Doctor fati"
Zarah ta dan dago ido ta kalleshi tana cikin bakinciki shikenan ya manta da babinta har wata zata maye gurbinta ,
Muneera tai murmushi tace "Allah sarki ai tana da kirki tayi hidima da kai sosai Allah yasa alheri kaje ka samu kawun kuyi mgna "
Yace"tom "ya juya ya fita,
Muneera ta cigaba da aikinta batare da ta kula da halin da Zarah ke ciki ba,
KHALEED ya koma daki ya kira Dr salis yanaso su hadu yace ya samesa gidansu ya masa kwatance har gidan batare da bata lokaci ba KHALEED yaje ya samesa su ka gaisa Dr salis nata kallonsa tunda ya kirasa zuciyarsa ta kara bashi hakuri akan bazai samu Fati ba,
KHALEED na kallonshi yace"Dr ta bani labarin soyayyarku its painful and I'm sorry inaso ka shigemin gaba inason na aure ta"
Dr salis yayi murmushi me ciwo yace "Hakane kaddararmu ,naji dadin hakan kuma ina maku fatan alheri"
Fuskar KHALEED sake yace"thanks"
Dr salis yace"Zanyiwa Daddy maganar kome kenan zakaji daga gareni"
KHALEED ya masa godiya ya masa sallama ya juya ya tafi yana cikin dan farinciki ,
Zarah ta kasa cin abincin kirki saboda yadda zuciyarta ke tsananin zafi da ciwo basu fahimci komi ba WALEED ya fita ya siyo fura Muneera ta dama mata itama din bata sha sosai ba ta barta, da dare KHALEED ya shirya ya tafi gidan kawunsu suka gaisa dashi yace"Yaya iyali kuna lpy ko?"
KHALEED yace "Lpy lau ,dama inason na kara aure har mun daidaita shine nazo na sanar maka"
Kawun yace"Masha Allah aure sunna ce me karfi bawani abu idan lokaci yayi sai ka sanar dani abinda ake ciki"
KHALEED yace"Nagode sosai"
Kawun nasa yace"Ina ita waccan fatan tana lpy?"
Yayi shiru yasan bai san abinda ya faru ba a hankali yace "tana nan gida wurin Mama"
Kawun yace"Hakan Nada kyau Allah ya raba lpy"a tunaninsa tayi tsufa ,
KHALEED ya masa bankwana ya tafi ,Akan hanya Dr fati ta kirashi ya dauka ya kara a kunne yana cikin tunanin time da mutane zasu san me ke faruwa cikin gidan nasu yasan zasu sha zagi da gori sosai ,
A hankali tace "Zaka zo yanzu na hada dinner da kai"
Ya danyi murmushi yace "Ko banzo gun dinner ba dole nazo fira don already ma ina hanya"
Tai yar dariya tace"Inajiran ka"
Ya kashe wayar da dan murmushi fuskarshi ya cigaba da driving har bakin gidan yayi parking ya isa kofar ya fara knocking ,ta bude kofar tana ta kamshi da zuba masa murmushi ya shiga ciki ga warmers nan a jere suna jiransa, bayan ya zauna,tana farinciki tace"My Special girki nayi inason ka saki jiki ka ci da yawa"
Ya kalleta yana murmushin jindadin sunansa My yace"Ni I'm full"
Ta dan harareshi tace"Ka ma fara bari na zuba maka ko kadan kaci plss"
Yana murmusawa yace"Kiyi zamanki ni ba bako bane agunki ,kin saba gani ana bani inaci ai"
Tai murmushi tuno zamansa Hosp ,ya meda kallonsa a kulolin ya bude yaga tuwon semo a cikin fararen ledoji ya dago ya kalleta da murmushi ya bude dayar yaga bura busko dayar kuma miyar ganye ,ya sauka kasa ya zauna ya dauki tuwo daya ya fara warwarewa yana magana "My tun banci ba abincin nan special ne awurina kuma nasan dole yayi dadi tunda My tayi shi domin ni kadai"
Tai murmushi tace "Thanksu My"
Ya zuba miyar dake ta kamshi yasa cokali ya gutsiro yasa baki, abincin very tasty amma sai yaji bazai hadashi dana Zarah ba ,
Ya danci sannan yace"Na samu Dr munyi magana dashi yace zai nemeni"ya kara da cewa"ba ruwansa baida matsala"
Dr fati ta jinjina kai ,suka cigaba da firarsu ta masoya.
Su Muneera sun hallara dining suna jiran KHALEED saboda yau ba aiki amma bai dawo ba zuciyar Zarah na kara tsananta zafi,Muneera tace kowa ya ci abincinsa ,Zarah ta danci cin nata ya zama dole saboda Muneera ta samu ta shige ciki ta kwanta akan gado tana kukan zuci da yafi na fili ciwo,
Tana wucewa WALEED yace"Yanzu nan mama kin yadda ya aureta?"
Muneera ta harareshi tace"Banason haka ita Ba mutum bace?idan KHALEED akaiwa haka zaka ji dadi?ko da yake time da akai masa baka da wayo "
maganar Muneera tasa WALEED yin shiru ya tashi yabar wurin ranshi badadi,
Muneera ta shiga daki taga Zarah kamar tayi bacci ta rufo mata dakin ta dawo ta zauna,
KHALEED sun sha fira kamar wadanda sukayi shekara sannan tayo masa rakiya itace ta bude masa motar ya shiga ta rufe tana murmushi da daga masa hannu harya tafi,
Cikin farinciki ya shigo gidan Muneera na kallo ya zauna yana ce mata sannu,
Ta amsa tana kallon yadda ya saki jiki sosai ta ji dadin hakan sosai, nan ya bata labarin yadda su kai da kawu tayi jimm tasan akwai matsala idan auren WALEED ya taso , bata nuna masa hakan ba suka gama hira yawuce ciki,
Cikin dare Zarah da duk abinnan idonta biyu ta tashi zaune ta kalli Muneera dake bacci ta shiga toilet tayi fitsari ta dawo ta zauna bakin bed tana cigaba da kukan zuci yadda kasan zaai mata kishiya haka takeji ta rasa mafita haka tayi kwanan zaune kafafunta kuwa sukai sutum_sutum fuskarta ma ta kumbura sosai,
A haka su kai sallar asuba Muneera bata lura ba Sai da tazo gaidata Muneera ta kalli fuskarta taga tashin hankali ta kalleta har kasa taga kafafunta sunyi suntum,
Ta yunkura ta tashi tsaye hankalinta tashe ta rikota tana kallonta tace"Zarah lpy kike?"
Zarah ta daga kai tana boye damuwarta,
Muneera ta girgizakai tace "A,a baki lpy kwanta ki mike kafa "ta fita ta nufi dakin su WALEED tai ta knocking basu bude ba ta tura ta shiga taga basu dawo daga sallar asuba bane ta fito dasauri zata koma wurin Zarah suka shigo a tare kowane da jallabiya jikinsa, suna ganinta duk gabansu ya fadi don bata cika fitowa ba a irin wannan lokacin ,ta tare su tana magana da sauri da dan tashin hankali" WALEED muje ka duba Zarah bata lpy"ta nufi dakin dasauri
Jin da su kayi ta ambaci Zarah ba lpy suka kara shiga tashin hankali su kai cikin dakin da sauri har bakin gadon da take kai suka tsaya suna kallonta a tsorace ,WALEED ya bi kafafun da fuskar da kallo ya matse lips dinsa zuciyarsa na tsananin zafi,
Muneera na gefenta hankalinta duk a tashe ganin WALEED din yayi tsaye kawai tace " WALEED ko dai asibity zamu tafi?"
WALEED ya girgizakai jikinsa yayi mugun sanyi yace"Bari naje na sayo wata allura a bata breakfast kafin na dawo "
Ya juya ya nufi kofa KHALEED da hankalinsa ya kai kololuwa wurin tashi yabi bayanshi a falo ya taraddashi yace"WALEED mike damunta ne?"
WALEED ya juyo ya kalleshi fuskarsa a takure cikin damuwa yace"A zaune ta kwana jiya batai bacci ba "
Zuciyar KHALEED ta fara wani irin ciwo bai cewa WALEED komi ba ya juya ya koma dakin wani irin gumi na tsatstsafo masa yana matukar tsorace ,jiya ne yayi maganar aure shine batai bacci ba,yayi tunanin zuciyarta ta hakura da abubuwan da suka faru ashe har yau bata dena masa wani kallo ba bata dena yin wasu tunani akansa ba,
Muneera tana kitchen tana hada abinda zata ci,ya Zauna bakin bed din da Zarah ke kai yana kallonta idanunta kulle ko motsi batayi dagani tana cikin wani hali,
Yana cigaba da zufa a hankali yace "Zarah mike damunki?"
Tai shiru tana jin kuka tambaya yake mike damunta bayan yasan shine damuwarta ,
Ya kasa dauke ido akanta yanajin tausayinta da tashin tabon sonta, cikin sanyin murya yace"Zarah kiyi hakuri dan Allah "
Yanzu dinma batace komi ba sai matse lips da tayi zuciyarta na rawa,
WALEED ya fita siyen maganin yana tafiya yana tunani zuciyarsa na matsanancin ciwo tana tuno baya tana dama KHALEED bai yanke hukuncin bar masa ita ba, gashi duk da tasan bazaya aureta ba amma ta kasa cireshi a ranta,Shi kanshi bai iya mata dogon kallo sai yaji kamar yana aikata laifi.
Muneera na kitchen tana hada mata tea da Fried egg tana tunani tun jiyan da taga sanyin jikinta yayi yawa ta fahimci tana kishin auren amma batai tunanin zata iya kin barci ba duk a tunaninta lokacin data dubota bacci take,kanta ne ya rika wani irin sarawa tana hango yadda family din zai kasance nan gaba ,zuciyarta na bata WALEED bazaiji dadin rayuwar aure ba saboda Zarah bata sonshi sannan iyalen KHALEED dana WALEED baza suyi zumunci ba saboda bazaa samu jituwa a tsakani ba.
Tana cikin tunanin ta hada ta koma dakin KHALEED na tsaye ya harde hannayensa yana ta kallon gadon, ta dan kalleshi sai zufa yake hadawa ta matse lips tana ganin laifinshi duk da ya yi hakuri bai saketa ba da watan watarana WALEED zai manta da ita zai samu tashi amma ya ki to gashinan idan shi ya hakura ya cireta a ransa ita ta kasa haka.
Ta Zauna tana bata abincin zarar na ci batare data kalli kowa ba wani irin kuka na cinta amma baiyiwuwa yanzu a tunaninta basu gane komi ba,
Kafin WALEED ya dawo wani irin zazzabi ya sauko masa dakyar ya dawo ya shigo jikinsa mace ya hada alluran ya mata ,yana mata bacci ya dauketa,
Muneera na ganin daga allura sai bacci yasa ta juyo ta kallesu daya bayan daya zuciyarta na ciwo sannan ta tashi ta fita a dakin kanta na kara tsananta ciwo, me zatace musu ?ai sun fahimci komi.
WALEED nata kallonta ya dan kalli KHALEED yaga yadda zufa ke tsatstsafowa tana gangarowa saman kanshi zuwa fuska ,
Ya so yayi mishi bayani akan zata warware idan tayi baccin bp da kumburin zai dan sauka amma ya kasa saboda daya bude baki zai iya kuka, ya juya ya fita ya shiga dakinsu ya haye gado ya lullube ya rumtse idanunsa zuciyarsa na masa matsanancin ciwo.
KHALEED ya kasa barin wurinta yanata hada gumi shima baiso hakan ta faru ba tun months na baya ya kamata yabar garin amma rashin lpy ta shigo ciki ,sai yanzu da yake niyyar tafiya kuma Dr fati ta shigo rayuwarshi kuma yasan dama Muneera dakyar zata amince ya tafi hakanan batare da aure ba,
Ya kai awa awurin sannan ya fito a falo ya samu Muneera kwance ta zubawa wuri daya ido tana kallo.
Zuciyarsa ta kara ciwo bai nufeta ba yasan tana tunanin laifin daya mata ne, ya nufi daki acan ya samu WALEED ma kwance hakan ya kara masa rauni da ciwo yanajin jiri ya hau gadon ya kwanta gefe yaja bedsheet shima ya rufe jikinsa ya kulle ido.
Kowanensu na cikin ciwo amma bawanda ya fada ko yasha magani ,wayoyinsu su kaita kuka amma ba wanda ya iya dauka ,
Muneera bataga fitowarsu ba kuma bazata iya wani motsi ba yadda kasan an zare mata duk lakkar jikinta haka jikin ya koma ga matsanancin ciwon kai da bugun zuciya tana kwance wuri daya.
HAMEED da yaga har 11 WALEED bai fito aiki ba kuma ya kira ya kira shiru ya fito a asibitin ya nufo gidan jikinshi na bashi ba lpy ba.
Yazo yayi ta knocking shiru ya bude ya shiga kai tsaye a falo ya samu Muneera halin da ya ganta cikine ya sashi saurin isa wurinta a rikice yana kiran sunanta "Mama Mama" amma shiru babu amsa ya kwalawa WALEED kira ya tashi da sauri ya shiga dakinsa cak ya tsaya kallonsu duk suna kwance ko yadda ya tura kofar ya isa ya tada su amma suna kwance hankalinshi ya matukar tashi ya karasa ya yaye bedsheet din fuskar KHALEED ta bayyana idanunsa rufe baya motsi,
Zuciyar HAMEED ta karye ya fara zubar da hawaye ya janye na WALEED shima idanun nasa a kulle baya motsi ya fasa kuka jijiyoyin kansa duk sunyo waje ya....
*SHIGAR SAURI*
Painful love story
Romance special
0 comments:
Post a Comment