Gurin dinner ya cika makil da dunbin jamaa kae da gani kasan bikine na masu naira .yan mata top class ke juyi tsakiyar gurin ....yayin da hall din ke fitar da wani azababben kamshi ..Daga gefe kuwa wasu yan mata ne su biyu ko wace zaune take hankalinta naga wayarta kirar Iphone6 sam hankalinsu baga cikin hall din yake ba ... ....
Mc ....ya bukaci babbar aminiyar Amarya yar uwa ga amarya ta fito ...
Fitowarta tata ita da Aminiyarta ta saka hall din karadewa da ihu tare da sowa ....
Tana karbar abun maganar gurin yayi tsittt kamar daukewar ruwan sama ...
daga gefe kuwa wasu dandazon samarine ke ihu...banda "Feenah" ...babu abunda suke fada .....
"Sunana Safeenat Khalid Mudassir" .....ta fada kallon kaf mutanen dake cikin hall din ....kafin ta cigaba da fadin ...
"Duk cikin ku nan babu shegen da bai san Engineer Khalid Mudassir ba ...!
Hall dinne ya sake karadewa da ihun mutane ...tayi tsit ..kafin ta daure fuska tace ...
"na dauka bikine na masu naira sai naga abun ya banbanta ga dangin ango ..dan banga alamun akwae arziki a tare da su ba.. kaf dinsu sanye suke da yadin da bai wuce 20 thousand ba ..kuma a haka dan tsabar rainin hankali aka gayyaci Feena? ....
Kanwar ango ta taso a fusace da niyar dauketa da mari don ta gama kuluwa da wulakancin ta .....
Aminiyarta dake kusa da ita tayi saurin rike mata hannu tana hararanta ...
wani Ja'irin murmushi Feena ta sake kafin ta aika mata da wani irin kallon tana fadin ..."Barta Maryam ...ki bar shegiya ubanta ya mutu yana nadamar haihuwarta ....!
Wurgar da ab din tayi sannan tayi gaba abunta ....ishak abokin ango ya tare da murmushi don tunda ta shigo ta tafi da hankalinshi .....
" Excuse me Feenat .!....ya sha gabanta tare da harde hannayensa ...
Wani kallo ta zabga mashi kafin tace ..."what "
" Just Few mints Swky ...ina son contact dinki please"..ya hade hannayenshi guri guda dauke da murmushi ....
itama murmushin ta sake ...tare da zabga mashi mari ...tayi gaba tana fadin ..."take it boy .".
Hall din ya dauki ihu .....har ta fice bai saki inda ta mareshi ba ...!!!
Bayanshi yaji an dafa tare da fadin ...."Weldon ...maganinka kenan .. banga amfanin kula macen da bata san darajar bil'adam ba ...next time idan zaka kula wata ka fara duba dressing dinta before ..."
Bai jira amsar sa ba ya zagayeshi tare da barin hall din...
Amarya kam banda hawaye babu abunda take ....tayi nadamar gayyatar Feenah gurin taronta duk da ita ce babbar aminiyarta amma batayi tunanin zata mata haka ba ...ko ba komae ya kamata ta duba alakar dake tsakaninsu ta yan'uwantaka .......
"Excuse me, ko ma ciki inda na zauna zaka ga hanky ka dauko man trappr dinta a kasa" ..ta fada tare da dalloshi da flash din wayarta ...
Yarda motarta bata amsa mata ba haka bai ko kalli inda take ba ya saka hannu da niyar bude motar ...
Ji yayi ta fizge keys din tare wurgar dashi kasa ...." Har ka isa ina maka magana ka wuceni ...!! Dan gidan uban waye kae ? ..me kake takama dashi ? ...
A fizge ya kalleta ya girgiza kai yana murmushi ...ba tare da yace mata komae ba ya dauki keys din ya shige motar ya barta tsaye rike da mamaki ...
Har ya tada motar yaji tana fadin "Wawan banza bakauye "...
Da sauri ya ja motarshi ya bar gurin gudun matsala ...
A falo ta iske grandmah dinta ta wajen dad ...gaidata tayi fuska Murtuk sannan ta bude fridge ta fito da robar swan ta balle marfin tana sha ....
"Safeena manya..ke dae haka halinki yake " ...kakar ta fads tare kallonta tana girgiza kai ...
Aunty Fati ta fito daga kitchen rike da katon tray a hannunta ta ajiye kusa da kakar tare da tsiyaya mata lemo a cikin cup ta mika mata...
Kakar tace "sannu Fatima Allah ya biyaki kinji ko ..Allah ya jikan Habiba ....!!
"Ameen" ta fada dauke da fara'a sannan ta kalli feena tana fadin ...
"Safeena har an dawo ?
Ba tare da ta kalleta ba tace ..."baki so dawowata ba ko ? ..saboda na tsare maki gidan uba ko ? ..ta dago tare da zuba mata ido tana aika mata da kallon da ke kunshe da tsabar raini ..
Kakar tace ..".kaniyarki Safeena ashe baki da mutunci ...matar ubanki kike fadawa wannan maganar ....?
"Uwata ce ? ....ta fada ta Fada a hasale.....
"Ai kanwar uwarki ce mara mutunci ...matar da tun kina cikin tsumma ta raineki?.ta goyaki ...,ta baki abinci ..ta baki tarbiya ...haba safeena ..!
"Ince abincin ubana ke kawowa ? ko daga gidan kaka ta zo dashi ? ..ina jin tun da ya hada mata garan biki bai kuma aiko mata da ko tiyar shinkafa ba ?
*FEEDOHM馃挒*
[11:03PM, 10/21/2017] Feedohm馃挒: [8/24, 8:27 PM] Feedohm馃挒: 馃挧馃挧 *ZAN RAYU DAKE...馃尮*
馃尮馃尮馃尮馃尮
馃尮馃尮
馃尮
漏 *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM馃挒_*
*this page goings to ...Fa'izahbarwa, Safiyya galadanci , Meela Adeel & It'z Ruky....Allah ya barku da Lanto mai dinki ....馃槀馃槀馃槀馃槀馃槀馃槀馃槀*
2鈨�
Rike baki tayi tana fadin ...Safeena!!!
"Kinga grandy ...idan gulma ta kawoki gaskia ki tafi ...abinci dai na ubanane ...Goyo kuma da kike magana ..ta dauko zani taga idan ban goyata ba ...tarbiyya kuma ai ba da kudinta ta biya man kudin islamiyya ba ...!!ta jefar da robar ruwan tare da shigewa daki abunta ...
"Uwaki nace ...kaji man ja'iran yarinya to dan ubanki ki zo na balle maki zanina ki goyatan mu gani mara kirki !!
Aunty Fati tace..."kiyi hakuri sae dae Allah ya shirya ....!!
Kaka ta amsa da "Ameen Fatima kina kokari ..."
�
Da sauri tayo baya tare da nuna shi da hannu ..."Kaine dan Iskan nan da na aikeka last gurin dinner beebarh kika zuwa ko ?
Da mamaki ya kalleta tare da kauda kai gefe guda yaci gaba da tafiyarshi zai shige cikin falon ...
"Wane dan iska ne ya bar wannan abun ya shigo nan gidan" ....ta fada cikin tsawa tare da nuna Abdulmaleek da hannu ...
Cak ya tsaya tare da juyowa yana kallonta ...kar dae ace wannan yarinyar diyar oga ce ...tab Albasa ba tayi halin ruwa ba .....
Wani yaji yana fada mata ..."wae Alhaji yace a shigo dashi ..".
Cigaba yayi da tafiyarshi ya shige falon da sauri ....itama dawowa tayi cikin sauri ta komo cikin gidan ...tana bala'i ita kadae ...
A babban falo ya iske Alhajin zaune saman kujera ...har kasa ya zube yana gaidashi cikin girmamawa ....
Cikin faraa ya amsa mashi yana fadin ya zauna da kyau ...girgiza kai yayi tare da dukar da kanshi kasa ...
"Abdulmaleek"....Alhajin ya kira sunanshi cikin natsuwa ....
"Naam ."..
"So nake ka baro office ka dawo gidana ...Driver dake kai Safeeena unguwa shine ta kora ..ni kuma bana so na ta dinga fita ita kaidai ...tunda aikin nan da office din duk dayane ...anan ma kafi samun sauki ..tunda akwae boys quarters da zaka zauna wanda zai fi maka sauki ...amma sae kayi hakuri da halinta ..na yaba da hankalinka shi yasa ma na nemoka ...ina fatan ba matsala ....?
: Zufa ta fara keto mashi ta ko'ina ...duk da Ac dake gauraye da. Falon ....a iya saninshi sam yarinyar bata da mutunci duk da sau daya ya taba ganinta ....sannan ko kadan baiyi tunanin itace tayi wannan rashin mutuncin ba .....sannan sam albasa batayi halin ruwa ba saboda mahaifinta mutumin kirki ne ...muryar Alhaji ta katse mashi da tunani da yaji yana fadin ...
"Kayi Shiru Abdulmaleek ko kafi son zama can ne?
Dagowa yayi a wahale yana fadin " Ba matsala Alhaji nagode sosse" ...shi kanshi bai san abunda yake fada ba
Cikin jin dadi yace "Ameen Abdulmaleek Allah ya maka albarka yaji kan mahaifinka ..."
A hankali Alhajin ya juya ga Safeena dake tsaye bakin kofa tare da mika mata hannu ....
Dan takowa tayi har gabanshi ta zauna bisa hannun kujeran da yake zaune ....tana bata fuska
*FEEDOHM馃挒*
[11:03PM, 10/21/2017] Feedohm馃挒: 馃挧馃挧 *ZAN RAYU DAKE...馃尮*
馃尮馃尮馃尮馃尮
馃尮馃尮
馃尮
漏 *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM馃挒_*
*Devoted to Ummi A'isha馃憣馃徎*
3鈨�
Hannunta ya kamo yana karantar yanayin fuskarta sannan yace "Safeena ga sabon driver nan kullun zai dinga kaiki inda kike bukata Bana son matsala wannan karan Safeena"
"Abbah da wannan abun zanyi yawo?...ta fada a dakile
"Kwarae don na gaji da shashancinki Safeena ki kiyaye ni wallahi bara ta yiyu ki dinga wulakanta duk wanda aka kawo aiki karkashinki ba ...AbdulMaleek ba wae yaro kadae na daukeshi ba aa amintaccenane ...!!
Mikewa tayi tana bubbuga kafa tare da turo baki ....
"Mene matsalar Safeena? ...Abbah ya tambaya tare da mika mata hannu ...
"Bana sonshine kawae Abbah last week fa bikin berbah ya raina man hankali ashe ma da motar Abbah na yake tutiya ni dae ......
Katseta yayi yana fadin ..."Wuce Safeenah ..."
Da Sauri ta fara hawan stair tana gunguni ....Bakin part dinta tayi karo da Aunty Fatee wani sakaran kallo ta watsa mata tare da shigewa daki abunta ....
�
Bayan ya bar Gida direct gidansu ya nufa ...Nana kanwarshi ya iske tsakar gida tana wanke wanke ....
"Subhanallah Nana waya baki wannan aikin bayan bakya lafiya? ...ya tambaya a rude tare da matsawa kusa da ita ...
"Ni ce nan dan Ubanka ko zaka dakeni ne mara mutunci " ....Inna Sahu ta fito daga dakinta tana fada ...
"Me ya kawo na duka kuma Inna? Kawae naga bai dace ba tunda bata lafiya a bata aiki irin haka ..Tashi Nana jeki bara na ida kinji ko !!
"Da kyau Uwarta to bana son nakan banza na mata" ....ta fada a harzuke tare da matsowa kusa da Nana...
Nana tace "Bandee ka barsa na ida kaji ....Allah na warke "
A harzuke ya juya zaya fita wayarshi ta dau ringing har ta yanke ba dauka ba ....Sae da ya zauna saman dakalin gidan sannan wayar ta sake kara karo na biyu ....Sunan Oga da ya gani ya sa shi ya dae dae ta natsuwarshi tare da daukar wayar ...
Oga yaji yana fadin "Abdulmaleek kana lafiya kuwa tun dazo Safeena ke kiranka kazo ka kaita saloon baka dauka ba ?
"Wallahi Alhaji ban lura da kiran bane amma gani nan zuwa " ...ya fada tare da mikewa ...
"Ayyah nima abunda na fada mata kenan amma kasan Safeena da rigima " ....Alhajin ya fada a hankali
Dan murmushi yayi yana fadin ..."Afuwan Alhaji gani nan a hanya "
" Ok" ...ya fada tare da yanke wayar ...
Missed call din ya buda a tunaninshi zai ga irin kira uku ko biyu amma sae yaga sau daya ta kirashi shine har ta fadawa Abbanta ...."huh" ...ya fada tare da gyara mirrow din left hand dinshi ....Cikin mintina 10 ya isa gidan ...ga mamakinshi sae ya ganta zaune ita da wani saurayi bisa carpet a harabar gidan don duk tunaninshi zaya iskeshi tana jiranshi amma sai yaga zancenta take hankali kwance .....
Ba wani dalili kawae yaji gabanshi ya fadi ....a sulale ya idasa gurin da suke zaune tare da fadin "Madam gani" a hankali ...
Bata kalleshi ba sae dae saurayin ne ya kalleshi ya dauke kai ....yayi tsawon mintina goma kafin ya sake fadin "Madam Gani fa"
"Uwar me zan maka ....". ...ta fada a fusace
Yaji ciwo amma ya daure tare da dai daita fushinshi yana fadin "Oga yace kina kirana ..Sorry ni sam banga lokacin da kika kira wayata ba "
"Dama taya zaka gani? ..Kwalwa ta tunkushe da tuwan dawa !! ..
Shiru ya mata ba tare da ya kalleta ba ...saurayin nata yace "Feenah please ki sallameshi ya zo ya mana tsaye a kai ya bata mana iskar guri !!
"JB Barsa yayi ta tsayuwa idan ya gaji ya tafi don banga uwar da zai man ba yanzu lokacin da na kirashi ai bai zo ba ...kawae Abbah ya ja man raini !!!
A hankali ya ja kafafuwanshi zaya fita ...sae da ya kai bakin kofa yaji tana fadin " Maleek " ...
Duk da yana cikin bacin rai hakan bai hanashi jin dadin sunan daga bakinta ba ...cak ya tsaya ba tare da ya juyo ba ...
"Ka jira a waje idan na gama zan duba idan da lokaci sae ka kaishi ...."
*_FEEDOHM馃挒_*
[11:03PM, 10/21/2017] Feedohm馃挒: *ZAN RAYU DAKE...馃尮*
馃尮馃尮馃尮馃尮
馃尮馃尮
馃尮
漏 *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM馃挒_*
*Devoted to Ummi A'isha馃憣馃徎*
4鈨�
Abdul Maleek bai bar gurin ba sae da aka kira sallar magrib sannan ya mike yayi alwala tare da sallah a masallacin gidan ...yana fitowa masallaci yaga ta fito raka JB dan kallonshi tayi kafin ta kauda kai tana dagawa JB hannu da wani blwng smile a fuskarta ....Sae da yaja motarshi sannan ta juyo gurin Maleek din ta kafa mashi ido ..
"Zaman me kake mana anan ?
Ba karamin kona mashi rai tambayar tayi ba ya danne tare da fadin "Ke kika ce na jiraki Madam Zan kaiki saloon ko"
"Gidan Uwarka zan tafi da darennan ...kai baka da tunani baka san darajar mace ba ? Common dallah matsa na wuce !! Ta fada kamar idanuwanta zasu fito saboda tsabar harara
Shiru ya mata tare da matsawa ya bata hanya ...sae da ta kusa shiga gidan sannan ta dan daga murya tana fada "Gobe by 7:30 ina jiranka karka bata man lokaci sannan ba kiranka zanyi ba idan kaso ka kai 3pm baka zo ba Bllshit .....!!
Ko saurarenta bai idasa ba ya shige motar ya bar unguwar ....bakin titi yayi parking tare da kwantar da kanshi saman sitiyarin motar zuciyarshi na bugawa da azabar karfi ....kanshi ya dinga bugawa a jikin sitiyarin ko ya samu sauki amma kamar kara watsa mashi gas ake a zuciyar ......
Sae da yaji ana kiran isha'i sannan ya fita daga motar ya gangara masallacin dake kusa yayi sallah ......Gurin mai sayar da abinci ya nufa ya sayi shinkafa da wake da miya take away biyu sannan ya nufi gida ....Garejin da yake aje motar ya kaita sannan ya taka ya shiga shagon da yake kwana ya watsa ruwa tare da sanyo bakar jallabiya ya dauki take away din guda ya nufo gidansu dashi ...
Tsakar gidan yayi duhu Nana kadaece a bakin dan karamin iccen magoron dake a gefe ta kudundune sai rawar sanyi take ....
"Nana " ...ya fada a rude tare da dagota ya hadeta da jikinshi ..."Menene Nana? ..ya akai kika fito ke kadae tsakar gidan duk wannan uban sanyi ? ...ya fada tare da dago fuskarta ...
Kuka ta sake a hankali tare da kwantar da kanta a jikinshi .."Baddee inna tace wae baran kwana ba a dakinta saboda dazu ka mata rashi kunya " ...ta fada cikin kuka
Duk ya rude yana bubbuga bayanta ....Bakinciki biyu suka taran mashi ...."To yi Shiru kinji ko ? Kinci abinci ? ...ya tambaya a hankali
Girgiza kai tayi tare da dago kanta ...
Ba tare da yace mata komae ba ya zaunar da ita bakin dakin Baffa ya bude mata abinci ...da sauri da sauri ta dinga ci kamar wani zai kwace mata sae da ta cinye sannan ya debo mata ruwa a randa ya mika mata .....
"Kin ko shi ko? ...ya fada a hankali ...
Daga kai tayi tana sauke ajiyar zuciya ..
"Baffa ya dawone?
Zata bashi amsa suka ji sallamarshi ....Tare suka amsa mashi sannan nana tayi saurin karbo buhun dake hannunshi ...Fuska sake yace "Nana ba'ayi bacci ba?
"Uhmm " ...kawae tace tare da murmushi ...Maleek ma gaisawa sukayi sannan ya masu sae da safe ya tafi ...Baffa ya bude dakinshi suka shiga tare ...dama ya saba indae yaga Nana tsakar gida to a dakinshi zata kwana ranar saboda bakin Halin Inna Sahu ......
Yar katifarshi ya gyara mata yace ta kwanta sannan ya shinfida buhu yayi sallah tare da kwanciya gurin ko kan ta Inna Sahu baibi ba ...
《《》》
Tunda Safe yayi Wanka ya shirya cikin kananan kaya wando blue sae rigarshi red ...duk da kayan ba masu tsada bane amma sunyi bala'in karbarshi dan turarenshi ya shafa mai saukin kudi tare da kamshi maidadi ..
Karfe 7:00 ya isa gidan lokacin masu aikin gidan kowa ya kama aikin gabanshi. ......
Har harabar gidan ya shiga da mota sannan ya zauna saman fararar kujeru yana jiranta ....
Wajen karfe 8:15am ta fito sanye da kayan sport zata shiga gym dake kusa da garden din gidan ....
Cikin mamaki ya bita da kallo kafin ya mike tsaye ya bi bayanta ....
*FEEDOHM馃挒*
[8/27, 1:25 P
[11:03PM, 10/21/2017] Feedohm馃挒: 馃挧馃挧 *ZAN RAYU DAKE..馃尮*
馃尮馃尮馃尮馃尮
馃尮馃尮
馃尮
漏 *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM馃挒_*
*Devoted to Ummi A'isha馃憣馃徎*
5鈨�
"Madam"...ya kira sunan a hankali ganin zata shige gym ta barshi tsaye ...
Dan juyowa tayi tana kallonshi a murtuke ba tare da tace komae ba ...
"Kince karfe 8:00am nazo ko ? ...ya fada yana kallon fuskarta
"Da yaushe nace kazo ?
"7:30 madam kuma yanzu har pass 8 ....!!
"Sae 12:00pm zanyi lecture din sorry ka jirani " ....bata saurareshi ba ta shige abunta ....
Ji yayi hawaye na neman zubo mashi da yasan haka wannan shegiyar yarinyar tace da bai yarda da aikin ba ....
Babban abunda yafi daga mashi hankali 12:00pm ake tado su nana makaranta ...sam inna sahu bata ba ta kudin mashi sae dae ta bawa yayanta biyu ita kuma indae baije daukarta ba sae dae duk uwar tafiyar dake akwae ta taho kasa ......
A jiyar zuciya ya sake tare da jan kafarshi ya fita ....cikin mota ya koma ya fito da time table dinshi ya duba ...ganin yana da lecture karfe 10 to 12:00pm ya sashi jin dan sanyi sanyi
Yana Shiga yar'adua Unversity ya fara ganin course mate dinshi suna shigowa tsayawa yayi ya ragewa mazan hanya sannan suka shiga faculty of law ....
Lecture ake masu amma sam hankalinshi baa gurin yake ba ganin 11:15 tayi gashi lecturer din baya da niyar fita tunda dama sae 12....Ishak ya kalla yaga shima danna wayarshi yake abunshi .....
Dan taboshi yayi yana magana a hankali .."Zan tafi please idan zaa yi attendance ka man !!
Daga mashi kai yayi ba tare da ya kalleshi ba .....Sulalewa yayi ta kofar baya cikin sauri ya fita ba tare da lecturer din ya ganshi ba .....
Cikin saa kafin 12 din ya isa .....sae da yayi kusan 30mint sannan ta fito sanye da wani farin less mai stone blue sae dan karamin mayafinta blue da karamar jikka a hannunta .....
Duk da bata cika fara'a ba amma hakan ba karamin kyau tayi ba ......
Baya ya bude mata tashiga sannan ya zagaya shima ya shiga ya ja su ....cikin natsuwa yake tukun ta glass din gefenshi yake hango kyakykyawar fuskarta tana latsa waya tare da sakin wani blwng smile dake fito da side dimples dinta ......
Bai lura ba sae dae yaji tana magana cikin fada "back nace maka ...!!
Wani uban burki ya taka tare da yin baya a hankali ....
"Yauwa yayi nan ..." ta fada tare da balle kofar motar ta fita ....
Shima da sauri ya bita ganin abunda zata fitar mawa ....Gabanshi yayi muguwar bugawa ganin Safeena duke gaban Nana tana rike da hannunta tare da sake mata murmushi ....
Duk da ba jin abunda suke fada yake ba amma yana ganin bakin nana na motsawa tare da saka bayan hannunta tana share hawaye
Bai gama mamaki ba sae da yaga Safeena ta daga Nana cak tare da mannata jikinta tana bubbuga bayanta alamun lallashi sannan ta nufo mota da ita ...
Cikin sauri ya koma motar tare da kife kanshi ...wani irin dadi ke ratsashi ta ko'ina ya rasa dalili ....
Har sae da ta zauna sossae ta daura nana saman cinyarta sannan ya tada motar ba tare da ya bari Nana ta ganshi ba ....
Ta madubi yake kallonsu
"Meye sunanki ? ...Safeena ta fada tare da gyarawa nana wuyan hijab dinta daya keshe ....
Cikin Muryar Kuka tace "Nana"
"Shiii ba nace ki daina kuka ba ....yi shiru kinji ..." ...ta fada dauke da fara'a ....
"Oya Nana ba suna bane na gaskia ...meye asalin sunanki !!
"Nana Aisha" ...ta fada hankali
"Yauwa daga yau idan yayanki bai zo daukarki ba karki kuma masa kuka kinji ko , Ni zanzo na daukeki kullun zan biyo tanan kinji ko...dama duk haka suke !!!
Ta fada tare da kauda kanta gefe guda .....da sauri ya kalleta ga mamaki sae gani yayi ta goge idanuwanta da hankyn dake hannunta ....
"Wane Unguwa kuke ?....ta fada a hankali
"Kofar Marusa!! ..Nanar ta fada tare da kallon Safeena ...
"Maleek kofar marusa zamu kai Aisha " ...ta fada har lokacin tana kallon waje ....
Baiyi magana ba sae dae canza akalar motar yayi tare da kura mata ido ta madubi ...
Dae dae primary suka tsaya da yake motar barata shiga ciki ba .....
Su duka biyun suka fita tana rike da hannun Nana ....fitowa yayi ya zuba masu ido tare da harde hannayenshi guri guda...yana sakin murmushi mai fitar da sauti ...
*FEEDOHM馃挒*
[11:03PM, 10/21/2017] Feedohm馃挒: [8/27, 9:25 PM] Yar Lukuta馃挒: 馃挧馃挧 *ZAN RAYU DAKE...馃尮*
馃尮馃尮馃尮
馃尮馃尮
馃尮
*_Haske Writer's Association馃挕_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM馃挒_*
*Devoted to Ummi A'isha馃憣馃徎*
_Gaisuwa mai yawa tare da fatan alkhairi ga duk masoya da ma wadanda basa karantawa ...nagode sossae da kauna ....Ummy Aysha Mrs Maleek ko kuma nace snatcher ....Safeena tace na fada maki idan kin saba snatching din guys to ki daina don Maleek sae Safeena馃槝馃槝馃槝_
6鈨�
Tambayar da ya fara kanshi shin ashe Safeena na da hali mai kyau irin haka ....Baiyi tunanin zaa samu digon tausayi ba haka aranta .....
Hangota da yayi ta fito daga lungun ya sashi kafe ta ido dauke da murmushi a fuskarshi .....tafiya take cikin natsuwa kamar tana jin tausayin taka kasa ....har ta iso kusa dashi bai sani ba .....
Dan karamin tsoki ta ja tare da shigewa motar ba tare da ya sani ba ....ji yayi ta fizgi motar kamar zata bankeshi ........
Kallo ya bita dashi kafin ya tsayar da okada ya bi bayanta baiyi tunanin zata tafi ta barshi ba ....duk da tana ganinshi ta cikin mirrow din motar hakan bai sa ta tsaya ba har sae da takae AlQalam sannan ta shige abunta .....bata gama parking din motar ba ya iso cikin sauri ya sallami mai akodar sannan ya matsa kusa da ita yana fadin ...
"Sorry Madam wallahi ban san kin iso ba !!
Wani kallo ta watsa mashi lokacin da take kokarin rufe motar .....
"Kana aikin me har na wuce ta gabanka? ....ta fada tare da kafeshi da ido ...
""Hankalina baya gurin ne Madam !!..ya fada kamar me rada ....
"Huh ....fada man gaskia ...kana kalleni ko ? ...to fada man ya kaga yanayin tafiyata ...ta burgeka ne ko yaya !!! ....ta karashe maganar tare da wurga mashi keys din ....
Shiru ya mata ba tare da ya kalleta ba ...sae ma lumshe ido da yayi a hankali ...
"Runtun Zunubi ne Maleek...4:00pm zan fito ...." ..ta juya a hankali ta shige hall din .....
Bayanta yabi da kallo tare da jingina da motar a hankali ...lumshe ido yayi jin har lokacin yana jin kamshin turarenta .....
Cikin motar ya koma ya tada tare da barin makarantar ....
�
Aunty bilky ta kalla lokaci guda ta daure fuska tana kurbar lemunta a hankali. ....
Aunty bilky tace "Wae Fatee haka kike zaune da wannan marar kunyar yarinyar tana kallon mutane a dage .....!!
Aunty fatee ta juyar da kai tare da kallom Safeena sannan tace "To ya zanyi Bilkisu sam Alhaji baya ganin laifinta ...kwanaki fa har cewa tayi zata mareni a gabanshi amma ya kasa daukar mataki ",...
Aunty bilki tace "Ke Safeena zo !!
Babu musu ta taso daga kujeran da take ta dawo kasan carpet a gabansu ta zauna tare da harde kafafu tana kallonsu ....
"Ke Safeena ashe baki da mutunci ...dan Ubanki Fateen zaki mara don kina mara kunya ....duka yaushe kika girma ..anan dan ubanki ta gama wahala dake wadda ko uwarki bata maki kalarta ba ...amma!!
Cikin sauri tace "Aunty bilki ki bar saka Ummata a cikin tsiyarku gaskia ...!!
"An sakata din dan Ubanki ..ke kenan babu wanda ya isa dake ..bakyajin maganar kowa sae ta ubanki ...to wallahi mun gama maki komae tunda har muka hada uba da uwarki ..ko kiki ko kiso Mu uwayenki ne shegiya mara mutunci ....!!
Tashi tayi ta shige daki ....drawer ta bude ta fito da turmin zani da rigunan jarirai guda uku da ta saya zata kaiwa Kanwarta ...ta fito dasu falon .....
Bisa kujeran da Aunty bilkin take ta aje sannan ta koma ta zauna tana fadin ...
"Aunty bilki inji da ummana ta haiheni baki wuce ki bata turmin zani da rigar jarirai ba ....??
Daga Aunty bilkin har Aunty fatee bude baki sukayi suna kallonta tare da sauraren abunda zatayi ....
"To ga kayanki nan na biyaki karki kuma zuwa kice zaki man rashin kirki !! ...tana gama fadin haka ta mike tare da barin falon .....
Tana ji Aunty bilkin na zaginta amma ko ta nuna ta san da ita suke batayi ba.....
Gado ta fada tare da sakin kuka a hankali ita kadae ....kamar an tsikareta ta mike tare da daukar Hijab har kasa ta fita da gudu ta wucesu a zaune....har lokacin maganarta suke .....
*_FEEDOHM馃挒_*
[11:03PM, 10/21/2017] Feedohm馃挒: [8/28, 9:16 PM] Yar Lukuta馃挒: 馃挧馃挧 *ZAN RAYI DAKE馃尮*
馃尮馃尮馃尮
馃尮馃尮
馃尮
漏 *_Haske Writer's Association馃挕_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM馃挒_*
*Devoted to Ummi A'isha馃憣馃徎*
*Dear,Sweetheart You're such a lovely,amzing and caring Sister's..we're more than friend's you're sisters frm another mavellous mother ..It's undistpn to have sisters like you ..i gss am the luckiest person in e- world more grease to your hutrs elbow ...UMMIEY XEEY & EXCLUSIVE QUEEN 馃挒馃挒馃挒馃挒馃挒 ..*
7鈨�
Fita tayi daga gidan ko mota bata tsaya dauka ba ta fara tafiya kasa har bakin titi sannan ta tsayar da napep ta shiga ....Dutsin safe low cost ta ce ya kaita ...tafiyar minti 10 ta isa gaban wani ma daidaicin gida ta sauka ta bashi kudinshi sannan ta fada gidan. ....
Wata yar dattijuwa ta iske tana gurza danyar kubewa a jikinta ta fada tare da sakin wahalallen kuka mai fitar da sauti ...
Aje kubewar tayi tana bubbuga bayanta a hankali har tsawon yan mintina kafin ta dago fuskarta tana fadin ...
"Menene matsalar Hussainah ?....
"Ummata kaka ...ina missing nata sossae dan Allah ki barni na kashe Aunty fatee ko zuciyata tayi sanyi kaka ....." ta fada cikin kuka ..
"Kul Husainah kar na kuma jin kin kira kalmar kisa a bakinki ...ke kika halicceta? ..bana so kinji ko ki barsu da Allah da sannu duniya zata basu kashi ....."
Maida kanta tayi jikin kakar tana jujjuya kai a hankali ....
"Tashi kije ki zubo cous cous na nan cikin foodflask ki ci kinji ko !!
"Na koshi " ...ta fada a hankali
"Tashi nace maki ko ...me kika ci ? Kalli cikinki kamar babu yan hanji a ciki !!
Sanin gaskia Kaka ta fada ya sata mikewa a hankali tare da cire hijab dinta ta debo abincin dan kadan ta zauna tana ci ....
Sae kusan Magrib sannan ta fito da wayarta ta kira Maleek ....ringing daya ya dauka ....
Cikin sanyin muryarshi ya mata sallama ....
Bata amsa ba tace "Maleek ka zo dutsin safe ka daukeni yanzu"
A hankali yace "Madam ina asibiti wani friend dina baya lafiya ..."
"Matsalarka ce Maleek ...within 20mints ina jiranka !! ...ta fada tare da yanke wayarta
A hankali ya lumshe idonshi don yanzu sam ba ta bata mashi rai ...sannan ya kalli Fahad dake bawa Ahmed abinci yace
"Fahad idan ya tashi kace masa na tafi dauko madam amma zan dawo insha Allah "
"Ina zaka Maleek ita Madam din barata dubi uzurin da ka fada mata ba ta hawo machine ta koma gida ...!! ...ya karashe maganar tare da jan dan karamin tsoki
Fuska Maleek ya bata tare da fadin "to meye naka a ciki? ..kai tace kazo ka dauketa ?
"Allah ya baka hakuri " ...ya fada tare da aje bowl din hannunshi ...
"Ameen " ..kawae yace ya fice da sauri yana duba watch din hannunshi ....
Ko da ya shiga dutsin safen sae da ya kirata yafi 6times sannan ta dauka tace ya jirata kusa da primary din tana zuwa ......
Fitowa yayi ya zauna saman motar yana jiran ta inda zata bullo .....da yake Hijab ta saka sam bai ganeta ba sae da wata mota ta haskata sannan ya gane ita ce ....
Sumar kanshi ya shafa don ba karamin kyau Hijab din ya mata ba ...sam baiyi tunanin Madam na saka hijab ba ...ganin motar da ta haskata tayo baya ta tsaya dai dai ita ya sashi saukowa daga saman motar ya isa gurin ....
Na cikin motar ne ya fito wani irin kato dashi sae uban ciki bakikkirin sae washe baki yake tare da fadin "Yan mata ina zuwa cikin wannan daren !!
Duk da cikin duhu ne hakan bai hanata zabga mashi harara ba tare da zagayeshi zata wuceshi ....
Mutumin ne yayi saurin kai hannu zai rikota ....Maleek yayi saurin rike hannun yana mashi wani irin mugun kallon..
Bata fuska yayi yana fadin "Bismillah Madam "....
*FEEDOHM馃挒*
[11:03PM, 10/21/2017] Feedohm馃挒: 馃挧馃挧 *ZAN RAYU DAKE馃尮*
馃尮馃尮馃尮
馃尮馃尮
馃尮
漏 *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM馃挒_*
*Devoted to Ummi A'isha馃憣馃徎*
8鈨�
Dan kallonshi tayi tare da hade fuska tace ''meye haka Maleek……�
Bai kalleta ba sae dae wani mugun kallo da ya watsa mata sannan ya juyo yana kallon mutumin da ya fizge hannunshi yana fadin
"How dare are you zaka riken hannu"...
"Please madam lets go" ya fada yana kallon fuskar safeena har lokacin fuskarshi na daure
Dan karamin tsoki taja tare da kallon mutumin na yan mintina lokaci guda ta gama fahimtarshi alhaji SALLAU ne makwabcin su kaka sannan tsohon saurayin aunty fati kafin ta auri Abbanta sannan lokacin da mamanta ke raye tana yawan ganinshi gurinta
Muryar Abdul malek taji cikin tsawa yana fadin"Wallahi ko kabar nan gurin ko na maka rashin kirki babu abunda ya shafeni da ko waye kai "
mutumin ta kalla sanna ta dauke kai tana murumushi tare da fadin "sorry bai san ka bane shi yasa, Abdul Maleek muje "
motar ta fada ba tare da ta jira abunda zasu ce ba
Sai da ya ajeta gida sannan ya tafi
A bakin kofar shiga falo ta jiyo muryar uncle ABBA KANIN aunty fati yana fadin "aunty na samu aiki a school dinsu feenat duk wani,bakin,cikinki zan fanshe maki soon ,kinsan jiya na hadu da abbanta shegen ko sisi bai bani ba ,baya da guri sae na diyarshi "
Yar dariya ta sake tana fadin "kai dama har wani abun kike tunanin samu gurinshi to koni da kake gani,indae ba wannan shegiyar diyar ta saka baki ba bana cin kudinsa yanzu -"
"Barsu zata ci uban tane ko makarantar sae ta gagareta zuwa "
Yaye labulen falon tayi a hankali ta shigo tare da zama bisa doguwar kujeran tana kallonsu � dan kallon aunty fati yayi ya mata alama da ido sanna itama ta kalli,safeena tana fadin "Feena daga ina haka�
BA tare da ta kalleta ba tace "club "
Uncle ABBA yayi saurin fadin "safeena yar gidan dad ni bansan me na maki ba ko magana bakyason yi man, tun da nazo nake nemanki dauko abunci muci atare dama ke nake jira daughter nah "
A banzace ta kalleshi tace "ko ni baran iya cin abinci da kai ba Uncle Abba"
Dan,waro ido yayi yana fadin "kyamata kike daughter ……�
"Bana jin zan iya cin abinci da christian kai kuma bana tunanin kana wankan tsarki ……" ta fada ba tare da ta kalleshi ba
"KE..
"UNCLE tashi ka fita dallah barata yiyu ba har cikin dare ma kuzo ku cika mana falo da warin katti, taya zaku mayar mana da gida kamar wata college ko wane sakarai yazo ya shiga ba tare da ID card ba ,please find your way ……"ta fada tare da mikewa tsaye tana nuna mashi kofa
Aunty fati tace "safeena uncle abba ne fa �
"ko granny ne ina ruwana……"ta fada tare da balla mata harara
Dan kallonshi tayi tana fadin "Abba kayi hakuri Safeena bata bason mutane ka tafi kawae zamuyi,mag ana ta waya ke kuma Allah ya shirya ki"
Dan murmushi takaici ta sake tace "ameen nagode da addu'a AUNTY fati sanna kiyi addu'ar ALLAH ya ganar da barewa uwarta ta fari ko ba komae taji kamshin cutar dake makale da babarta……�
Kallon uncle abban tayi da yayi mutuwar tsaye…… ko kadan baiyi tunanin rashin kunyar Safeena ta kai haka ba ,zaiyi magana aunty fati ta nuna mashi kofa tana girgiza kai
Safeena kam ko da ta shiga daki bakin gado ta zauna tare da rumtse ido sam duniyar gaba daya ta isheta hoton yar uwarta ke yawo cikin KWAKWALWRTA dafe kai tayi lokacin da ta hango aunty fati tana sako hasanar daga saman benen falon babu imani bare tausayi lokaci kadan hawaye suka wanke mata fuska tana buga kanta a hankali jikin gadon
Maleek ko da ya isa gida a bakin kofar dakin baffa ya iske nana lullube da buhu gurinta ya karasa tare da dagata ya zauna sannan ya zaunar da ita saman kafarshi
"Badde yau baka zo ka daukeni ba " ta fada a hankali
"kiyi hakuri nana kinji wallahi aiki ya man yawa yau ,wa ya maidoki ……�
Dan girgiza kai tayi tana washe baki alamun jin dadin tambayarshi sannan tace "baddee sabuwar auntyta ka ganta badde ga kyau ga mutunci cewa fa tayi kullun zata dinga daukoni indae baka zo ba ,baddee ni dae ina sonta wata rana zaka kaini gurinta kaji baddee na "
A hankali ya lumshe ido yana kallon fuskarta duk lokacin da zata mashi masifa sannan yace "anya tana da mutuncin nana ……�
Bata fuska tayi tana fadin "eh man baddee tana da tausayi sannan tace tana sona kaima badde dole ka sota indae ka ganta "
Dan murumshi ya saki a hankali tare da shafa sajenshi idan yace baya son safeena yayi babban sabo duk da ya san ba ajinshi bace amma baya jin zai iya rayu babu ita ,wani irin so yake mata wanda bai san irinshi ba
muryar nana ta katseshi lokacin da take fadin "kai baddee muna sonta ko?kuma gobe ko,kazo daukata baran bika ba "
Zancen ya katse ta hanyar tambayarta ko ta ci abinci ,girgiza kai tayi tana fito da hakoranta biyu na gaba tana lotsa gefen kumatunta ,Murmushi yayi don ya gane salon murmushi Safeena ne ta kwaikwaya ko baa fada mashi ba yau yasan,nana na cikin farinciki
_*FEEDOHM馃挒*_
[11:03PM, 10/21/2017] Feedohm馃挒: 馃挧馃挧 *ZAN RAYU DAKE馃尮*
馃尮馃尮馃尮
馃尮馃尮
馃尮
漏 *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM馃挒_*
*Devoted to Ummi A'isha馃憣馃徎*
9鈨�
Da yake ta bashi timetable dinshi tun karfe bakwae ya iso gidan , inda ya saba jiranta nan ya zauna ,yauma daga gym din ta fito sanye da blue din jeans sae bodysnk fara fuskarta fayau natural beauty da ka ganta kasan bata da matsalar rayuwa a fuska har ta iso kusa dashi bai sani ba ido ta xuba mashi sannan ta saka kafarta ta take mashi yatsun kafarshi tana kallonshi , kafarta ya kalla tare da kallon fuskarta sannan ya kawar da kai
Dan murmushi ta sake mai fitar da sauti sannan ta dan duka tana kallon fuskarshi duk tunaninshi bara ta magana ba sae ji yayi tace "ya dae Maleek me kake kallo haka ……�
kura mata ido yayi ya kasa magana sae murmushin da ya sjbuce mashi "Maleek ka daina kallona da mayun idonka please! ya ciwon kan……�
Lumshe ido yayi sannan yace "Allhmd madam "
"ok muje " ta fada tare da nuna mashi motar tayi gaba ,tsaye yayi yana kallonta ya kasa koda motsi tun daga sama har kasa ya kare mata kallo ,bara ya iya jin zai fita da ita a haka ba......
Saurin shan gabanta yayi ya kwantar da kai yana fadin "Dan girman Allah madam ki canzo tufafi ba dan ni ba ba kuma dan na isa ba wallahi baran iya fita dake a haka ba dan ALLAH madam " ya karashe maganar murya na rawa
Kallonshi tayi na yan lokutta kafin ta juya a hankali ta koma cikin gidan , mintina kadan ta fito sanye da doguwar riga maroon daga samanta ta dan matse sae kasan a bude sae karamar hijab baka , bai san lokacin da murmushi ya subuce mashi ba tare da girgiza kai sannan ya bude mata motar ta shiga ya rufe ,shima ya zagaya ya shiga har ya fita da motar harabar gidan bai kuma magana ba sae dae satar kallonta da yake ta mirrow dake gaban motar
Wayarta tayi ringing ta dauka tare da langwabe kai cikin shagawaba ta fara magana
" baby Allah ban san ka kira ba ,na shiga gym kuma ko da na fito ban duba wayar ba sae da na shigo mota "
Gaba daya ya maida hankalinshi gurin wayar da take ji yayitace "da MALEEK mana "
Shiru tayi na dan wani lokaci kafin tace " na manta na fada maka Abbah yace ka turo iyayenka zasuyi magana fa ……"
Wani wawan birki ya taka wanda har sae da ta buge da kujeran dake kallonta , gaba daya ya juyo yana kallonta a rude
Ta dade kafin ta dago tana watsa mashi harara
"Maleek neke faruwa ……"ta fada tana dafe kirji don har ga Allah ta tsorata
Shiru yayi ya kasa magana sae uwar zufa dake bi mashi fuska maganar tata tayi balain sokar zuciyarshi ............"wae ya turo " abunda kawae yake maimatawa a ranshi kenan
Daure fuska tayi ganin yana neman bata mata lokaci "common dallah meye haka?kaka ganin time na kurewa zaka wani tsaya ka juyo kana kallona � ni dince baka taba gani ba ko mai � dallah mallan juya kayi,abunda ke gabanka bombastic villager……"
Bai juya ba sae dae ya dan seconds sannan,ya juya a hankali ya tada motar suka ci gaba da tafiya amma sam baya cikin natsuwarshi .........
Yana a jeta makarantarsu ya nufa yana shiga aka fada madhi result dinsu ya fito suka tafi suka duba luckily da first class ya fita sae abokinshi ishak ya fita da snd sae Abbas da ya fita da thrd class .........wani dan notice da aka lika gefe dasu ne suka duba sunanshine a ka rubuta in bolc ABDULMALEEK AHMED ana nemanshi senate ............
Senate din suka nufa sae da ms din yayi interview dinshi sannan ya shiga office din VC din
VC din mutumin kirki ya nuna mashi kujera yace ya zauna ,sae da kyar sannan ya zauna cikin dari dari ......
"Meye sunanka�......"ya tambayeshi,cikin harshen hausa
"ABDULMALEEK AHMED sir "......ya fada cikin natsuwa
"Waye mahaifinka wane gari kake Abdul maleek �
"Sir ni dan jahar katsina ne cikin kofar marusa ina zaune da kawunane "
"to ina mahaifinka Abdul maleek……�
*FEEDOHM 馃挒*
[11:03PM, 10/21/2017] Feedohm馃挒: 馃挧馃挧 *ZAN RAYU DAKE馃尮*
馃尮馃尮馃尮
馃尮馃尮
馃尮
漏 *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM馃挒_*
*Devoted to Ummi A'isha馃憣馃徎*
_Duniya baka gane kana cike da mosaya sae baka nan ......ALLHMD dan lokacjn da na dauka bana nan na fahimci abubuwa da yawan gaske banda bakin da zan gode maku sae dae na roki ALLAH da ya saka maku da mafificin ALKHAIRINSA ......aunty SIS wallahi ke ta dabance ta ko'ina mutunci da kimarki su suke kara maki daraja da daukaka ...UMMI A'ISHA banda bakin maki godiya sae dae ALLAH yabaki abunda kike nema duniya da lahira ...HAJJA CE ,PHERTY ,MAMAN HUDA,FAREEDA NABEEL,MAIJIDDA ,...ALLAH YA KAREKU DA DUKKA KARIYARSHI ,馃挒_
馃敓
VC yace "to ina mahaifinka yake"......
"Mahaifina ya rasu ,mahaifiyata kuma tun muna kanana ta rasu ina zaune da baffana tare da karamar kanwata ,sannan nike daukar duk wani,abunda ya danganshi karatuna sir"
VC din ya masa taaziyya tare da fatan rahama ga dukka iyayen nashi ,sannan ya fada mashi cewa result dinshi tunda suka bude makarantar baa taba samun irin nashi ba don haka makaranta ta dauki nauyin karatunshi duk kasar da yake bukatar yayo masters dinshi tare da offer ta aiki a highcourt dake GRA a matsayin barister , sannan makarantar zata nema mashi alfarmar shigaba da karatunshi duk da yana aiki ..."
Nana ta fara fado mashi idan ya tafi wata kasa gurin wa zata ji,dadi � sannan safeena da baya fatan yayi koda one day ba tare da ya ganta ba ya gwammace yayi,ta zama a drivernta ba tare da tasan waye shi,ba...
Cikin sanyin jiki yace ya ya gode amma,shi yafison yayi masters dinshi anan zaria idan,da hali , VC din ya amsa mashi tare da bashi wasu files da zai kai high court din yanzu...
wajen karfe sha biyu da rabi yaje daukota lokacin ta gama cika fam dae dae ita yayi parking sannan ya fito ya tsaya gabanta tare da harde hannaye a kirji cikin natsuwa yace "am sorry madam ...
A tsawance tace " shut up duntolic nonsense , yaushe nace na ka dawo "
Duk da yaji zafin zagin amma sae bai nuna ba illa iyaka dsn murmushin da ya sake iya lebe ...
Dan wrist dinta ta duba tana fadin "1hour kenan ka kara then i shud minus ten k a salary dinka ............
Cikin salon tsokana yace "Madam t10k tayi yawa please ki ragen mana ......"
Harara ta watsa mashi "lets go bullshit ka tsaya kana kallona da mayun idanunka ...wallahi maleek idan kai mayene ka kama mutun bara kai ko ina ba .........
Dariya ya sake a hankali tare da bude mata motar ... komae na safeena burgeshi yake masifarta,salonta,rayuwarta ,da komae nata daban yake a mutane ...
銆娿€嬨€娿€嬨€娿€�
JB kam tunda safeena ta fada mashi sakon Abbanta ya kasa rufe baki company dad dinshi ya nufa , yana zuwa ya iske suna meeting a octgon ... zaya shiga messenger din ya yace Alhaji ya hana a bar kowa a ya shiga har sae sun fito ......
Awulakance ya kalli dattijon yace" don kana dakiki sae kuma yace maka har JB idan yazo ka hanashi shiga ko �
Dukar da kanshi yayi yana fadin "kayi hakuri Alhaji ya ce kada a bar kowa ......
Bai rufe baki ba yaji saukar maruka har biyu "Wawa daga yau idan na sake zuwa gurin mahaifina ka saka jakin bakinka ka man magana villager ............
Meeting room din ya fada ba tare da wani shamaki ba ...dadad din na ganinshi ya mike tare da bada umarnin a katse meeting ...
MG yace "oga meeting dinnan ba is very imprt ka sani ,yana barazana ne ga wannan,company please ka tsaya a ida ......
"JB ya fiye man komae a yanzu ,muje ..." ya fada kai tsaye tare da barin gurin sae da suka je office dinshi sannan suka zauna ya fada mashi komae ......
"wow my son ya kusa zama ango ...mg zan zama grandpa soon am very happy ..."ya fada tare da hugging din JB din
銆娿€娿€娿€娿€嬨€嬨€嬨€�
Auwal abbas ne ya shigo yana fadin wae an canza masu sabon lecturer da zai daukesu anatomy sannan ya aiko by 10 zai shigo idan ya shiga kuma babu wanda zai sake shiga ko fita ...
A hankali ta kalli maryam dake danna wayarta tace " tashi muje zan siyo PP nawa ya kare "
Ido ta waro tana fadin "safeena 9:45 Fa idan ya shigo ya hanamu shiga fa……�
"Ajannah zai raba? ta fada tana bata fuska ...
"a'a amma ...
"look idan bara kije ba ,bani key dinki na tafi,.....
0 comments:
Post a Comment