A zahiranci ba PP zata sawo ba haka kawae tayi ta yawo cikin gari ba tare da sanin inda zata ba bakin round din dandagoro taga Maleek yayi parking ya tsaya kusa da mai recharge card ...I tama parking din tayi bayanshi ta fito ta jingina tare da harde hannu tana kallonshi ...Sam bai san da zuwanta ba sae da ya juyo da niyyar tafiya sannan ya ganta da sauri ya matso kusa da ita tare da sake mata lallausan murmushi "Maimakon ki kirana ni daukoki sae ki fito madam bayan kinsan aikina kenan " ...ya karashe maganar cikin salon soyayyar da bata boyiwa ...
Itama murmushi ta sake tare da mika hannu "bani keys din "
Da mamaki ya mika mata duk da bai san abunda zatayi dashi ba ...karba tayi tare da balla mashi harara ta juya tana fadin "iskancin da ya kawoka nan ya maidaka bisa okada idan kuma baka da ko sisi ka dabi sayyada akoma gida ......"
Sajenshi ya shafa tare da sake lallausan murmushi ya rakata da ido ...yana ganin ta koma a motar da tazo da ita ta bar wannan din a rufe ...sam bata bashi haushi ba din duk abunda zatayi barata taba kona mashi rai ba sae ma kara burgeshi da take .........
Sai kusan 11 ta koma makarantar tun kafin ta shiga hall din ta jiyo muryar Uncle Abba yana fadin "fibroids are most common growth in a woman reproductive system many woman with fibroids have no symptom at ...............
To me ya hadashi da fibroids ta fada a ranta tare da kutsa kai cikin hall din ...shigarta ya datse mashi sauran maganarshi wani ja irin murmushi tare da daka mata tsawa
"ke ............
"Sir Safeena khaleed dae...... " itama ta fada a tsawance
"get out idiot ,ni zaki fadawa sunanki safeena ……�
"Mendotic idiots dae sir ...ni dae kai ,kai a tunani lecture din na zo na yi mtsee kai kasan safeena ta wuce nan ,Maryam karbi keys dinki nan gaba menstrual ko menopausal zai maku ........." ka karshe maganar tare da wurga mata keys din
A harzuke yace "dan ubanki safeena ni kike fadawa haka ……�
Yar dariya ta sake "ashe ma kasan sunana ,good kar ka kuma zagar man uba ,ka duba da kyau a lecture hall muke ,baa falon dad ba da aka saba zuwa maula ,nan baka da hurumin zagina kai ko a,gidan ma ka zageni nima har gida zanje na samu tsohuwa mai dattin kallabi ........."
kafin yayi yunkurin bata amsa,ta bace kamar walkiya a fusace ya dauki tools dinshi ya bar wurin ko office,bai shiga ba ya wuce gidansu .........
銆娿€娿€娿€娿€嬨€嬨€嬨€�
Tana kwance landline din dakin tayi kara ta tabbata babu mai kiranta sae Abbanta,cikin sauri ta dauka tana share hawayen dake neman zubo mata a ido "Abbah ......"ta fada a hankali kamar me shirin kuka
"Safeena ki sameni garden yanzu kinji ko "
"to "ta fada tare da saukowa daga saman gadon takalmin ta zura sannan ta ja bakin gyalenta ta fita......gefe ta iskeshi ya shingida yana karanta dailytrust ,gefenshi ta zauna tare da lankwashe kafafuwa tana kallonshi ,aje newspaper yayi ya sake mata murmushi kamar ko yaushe
"Safeena me ke faruwa � ...ya fada wit serious tlk
"Abbah a ina �
"Safeena bakya jin maganata ko me yasa bakya da kyakykyawar alaka da dangin maminki safeena ,ko kadan bakya darajasu me yasa ko don kina ganin mamin taki bata rayane �
Idonta ya ciko da kwallah tayi saurin damke hannun abbanta tare da kallonshi "Abbah me nayi dan ALLAH ..."ta fada da shagwababbiyar muryarta
kallonta yayi na seconds sannan yace "me ya hadaki da Uncle dinki �
"Sorry Abbah... " ta fada a hankali tare da goge hawayen da suka zubo mata
"To meye na kuka kuma yarinyar Abbanta ……"ya fada cikin sigar lallashi ,har ga Allah idan akwae abunda ya tsana bai euce kukan diyarshi ba duk duniya babu abunda yafi kauna sama da yarinyarshi
"Sorry Abbah zagan,man abbana yayi ni kuma baran iya jurewa ba ka yafe man kaji ........."
FEEDOHM 馃挒
[11:03PM, 10/21/2017] Feedohm馃挒: 馃挧馃挧 *ZAN RAYU DAKE馃尮*
馃尮馃尮馃尮
馃尮馃尮
馃尮
漏 *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM馃挒_*
*Devoted to Ummi A'isha馃憣馃徎*
1鈨�2鈨�
"Baki man komae ba Safeena amma ki kyautata alakarki da dangin maminki ji ko ,bara na kira Abdul maleek ya zo na aikeki abukur gidan inna kinji ko idan,kinje ki kwana acan bana son damuwa ......"
"to ……"ta fada a hankali tare da gyara zama
Wayarshi ya fito ya kira Maleek din da kanshi sannan ya mata fada sabida ya san halinta sarae idan taje Abukur dole sae sun kwabsa da inna suke rabuwa ……kafin Maleek din ya iso yace taje ta shirya
Ko minti talatin bai dauka ba ya iso da ganinshi kasan ya wahala bai fito daga motar ba kamar yarda ya saba sae ma kifa kanshi da yayi a sitiyari ……�
Zagayawa tayi ta side dinshi tana kallon yanayinshi haka kawae taji ya bata tausayi first time a zamansu ……"Maleek baka lafiya ne?ta fada a hankali tare da leka kanta ta glass din motar
Duk da yana jinta amma sae yayi shiru yana sauraren ko zata sake magana a yanayin da tayi……kamar ta sani bata kuma cewa komae ba sae bude kofar da tayi tare da knocking din sitiyarin �
Kalar tausayi ya sake komawa ya dago yana langwabe kai kamar yaro karami……dariya ta sake da ta kara kashe mashi jiki ya bude baki yana kallonta
"Madam" ya fada cike da shauki duk zaman da suke bata taba mashi dariya irin haka ba
Dage gira tayi tana fadin "Yes common bani guri nayi driving din don baran yarda ka jani da irin wannan yanayin ba ,koma wancan side din ka zauna……�"ta nuna mashi gurin mai zaman banza
Kallonta kawae yake cike da mamakinta sannan ya tsallaka ya zauna ……bata kuma cewa komae ba har suka fita daga garin ganin ba kara kulashi zatayi ba ya sashi lumshe ido tare da langwabe kai yana tari
Saurin kalloshi tayi tana fadin "Abdul Maleek baka lafiyane �
Kamar yaro ya daga mata,kai tare da kokarin saka idanuwanshi cikin nata ,bata bari suka hada idon ba tayi saurin janye nata tana fadin "Sorry……�"
銆娿€娿€娿€娿€嬨€嬨€嬨€�
Karfe hudu na marece Aunty faty ta shirya ta tafi gidansu dake layout a can ta tarad da aunty zuby yayarta da suke uwa daya suna falo suna fira da hajiyarsu mafi yawan firan ta safeena ce da Abbanta,wanda dama firar kenan idan sun hadu , kusa da zubyn ta zauna tare da jefar da jikkarta tana dafe kai
"Wadannan mutanen su suke su saman ciwon kai wallahi , hajiya gaskia na gaji da wannan zaman ki san abinyi ……�" cewar Aunty faty
Harara hajiyar ta sake mata tare da fadin "meye kuma ?
"Meye ma bai faru ba hajiya , safeena fa aure zatayi da dan former minister abunda kuma bara ya yiyu ba……�
Aunty zuby ta katseta "ke tsaya dallah wane former minister,please ki bar wannan batsar taya diyar AISHA zata auri wani dan mininster baya ga namu yayan nan zaune gida?
Tabe baki Aunty fatyn tayi tace "ke ma kya gani dae……hajiya kice wani abu mana ga fadila nan ta girmewa safeena bare ma fauzy da rabi kuma su duka babu wanda yayi aure sae safeena?haba hajiya kar dae ace da gaske mutane suke munyi gadon bakin jinin gurinki ?
Cikin fusata hajiyar tace "ke dallah rufe man baki ,gidan uwar wa kuka yo gadon bakin jinin?sae ku bari kuga idan tayi auren ya'yanku basuyi ba sannan kuzo ku man tsegumi ……�
Kallon juna sukayi tare da kashewa suka dau ihu "Hajiyarmu……�"
Aunty zuby ta bude jikkarta tana fadin "kinga yar uwa ga wani sabon hadi daga sabon shehi kya gwada sakawa ogan a kasan pillow kafin hajiya ta warware komae ……�"
Bata bar gidan ba sae wajen isha'i ta koma , sam bama tasan safeenar bata nan ba tun da dama ba nemanta take ba sae da ta hadawa Abban safeena komae na bukata sannan tayi wanka ko sallah bata tsaya tayi ba ta shiga part dinshi tare da garin maganin da zuby tabata da zasu rabu ……cikin saa yana toilet yana wanka ta daga pillownshi ta bar bada kadan sannan ta mike ta bar dakin ta koma nata
Jin wayarshi na ringing ya sashi fitowa daga toilet din ba tare da yayi alwala ba , bakin gadon ya zauna yana duba wayar ganin safeena ce ya sashi kiranta tare da shigidawa saman gadon yana sauraren yarda ta dage tana zuba shagwaba wae bara ta kwana gidan Inna ba saboda ta mata wulakanci ita gida zata dawo ……�
Dariya sossae yake cike da so yana fadin "Haba SaFeenata ke da kakar taki , kinga dare yayi kiyi hakuri gobe da kaina zanzo na dauko ki kinji ko ……�"
Cikin shagwaba tace "Abba cewa fa tayi baran kwantar mata a wannan tsohon gadon nata ba ……�"
Yar dariya ya sake a hankali ……dif wayar ta dauke girgiza kai yayi ganin chajin shi ya dauke shi bai ma san baya da chaji ba sae yanzu "Safeena �
FEEDOHM馃挒
[11:03PM, 10/21/2017] Feedohm馃挒: [3:47AM, 10/18/2017] Feedohm馃挒: 馃挧馃挧 *ZAN RAYU DAKE馃尮*
馃尮馃尮馃尮
馃尮馃尮
馃尮
漏 *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM馃挒_*
*Devoted to Ummi A'isha馃憣馃徎*
_Assalamu Alaikum dan Allah masu bibiyar littafin *BAKONMU HASKENMU* su gafarceni na daina posting dinshi for some reasons Amma insha Allahu nan gaba zai fito amma bata social media ba sannan kuma bata siffar novel ba ,ko ma tayayane insha Allahu zaku ganshi kuma nasan sae yafi maku dadi fiye da ta novel...._
1鈨�3鈨�
Ita kam safeena tana jin wayar ta yanke ta fara bubbuga kafafuwa kasa tare da turo baki , muryar inna ta jiyo ta shigo dakin tana fadin "Ayi dae mu gani dan uban mutun dama na fada har gida mara kunya zai iskeni anan nima zanci kaniyar mutun"
Dan turo baki tayi tana hararanta ta kasan ido tare da barin dakin gaba daya
Dariya inna ta sake sannan ta shinfida abun sallah tana fadin "Naga yarda mara kunya zai shigon daki ya kwana tunda nima bada kudin uban mutun na cika na sayi gidan ba"
Daga waje Safeena ta bata amsa "ai da yake aikin gwamnati kike ko business da zaki iya sayan wannan gidan "
Kamar jira inna take tayi wuf ta fito tana fadin "to mara kunya fada man ubanki ne ya saya man da zaki fadan magana ……� "
Ganin idan ta biyewa inna rigimar ba karewa zatayi ba tunda dama tana da cikinta ya sakata langwabe kai tana lumshe idanuwa tace "Haba kakus ni fa ba haka nake nufi ba , kece tunda nazo kinki ki saurareni sae tsiya kike , ni kuma Allah ma ya sani ko lafiya banda ita hakanan nazo gaidake saboda kwana biyu ban ganki ba , amma idan zuwan nawane bakya so to kiyi hakuri gobe da safe sae in tafi ……"
Dayake Inna irin mutanan nanne masu masifar son jikokinsu ya saka jikinta yayi sanyi don ta yarda da cewa safeena batta lafiyar , kusa da ita ta matsa tana fadin "Kece Safeena sam baki da mutunci muddin idan mutun ya iskeki gidanku sae ki rufe ido kiyita rashin kunya bayan a zahiri ba haka kike ba ,amma komae ya wuce kinji ko zo mu shiga ki fadan meke samunki sae a aika a siyo maki magani,sannu kinji ko ,haba shi yasa naga duk idanuwanki sun canza Allah sarki……" ta karashe maganar tare da jan hannunta suka koma dakin
Sabon tara Inna ta sake mata tana lallabata kamar wani kwae ,a bisa kafarta ma tayi bacci
銆娿€娿€娿€娿€娿€嬨€嬨€嬨€嬨€�
Tunda safe mahaifan JB suka samu Abba a gida , da yake yasan da zuwansu sossae yasa Aunty fatee ta shirya masu duk wani abun bukata ,sunyi farin ciki sossae da karramawar da aka masu ,nan take suka bayar da kudin neman aurensu naira dubu dari biyar ,Yayan Abba ne ya yanka masu sadaki naira dubu dari biyar , nan take suka fito suka bayar sannan aka saka masu ranar aure nan da wata biyar ……�
Iya rudewa Aunty faty ta rude lokacin da Abba ke fada mata yarda sukayi da mutanen , kasa boye bakincikinta tayi tace"Million daya fa kace Alhaji ,kuma shine zaku bayar da ita kamar kun sayar……�"
Dan murmushi yayi yace "Million daya shine kamar na siyar da diyata fati ?
"Kwarae kam Alhaji , kaga dae diyar nan amanace kar mu bayar da ita ga mutanen da basu son darajar kowa ba ,don wallahi duk yawancin musu mugun kudinnan basu san darajar kowa ba"
"Atunanina fati mutumin nan bai fini komae ba don haka bana tunanin zai wulakanta man diya tunda ya san itama ba daga gidan tsiya ta fito ba ……�"
Shiru ta masa tana karkada kai a hankali……mintina kadan ta dauka sannan ta mike ta koma dakinta ,wayarta ta fito ta kira hajiyarsu ta fada mata komae Hajiyar ce mata tayi ta jira zata nemeta ……�
銆娿€娿€娿€娿€娿€嬨€嬨€嬨€嬨€�
A Sanyaye ta kira sunanshi ganin zaya tashi motar "Maleek"
Zalla soyayya ya juyo yana kallonta ba tare da ya amsa mata ba , so take ta tambayeshi amma sam ta kasa , ta rasa wanda zata fadawa damuwarta cikin yan kwanakin nan , sam Abba yaki saurarenta kullun ta tunkareshi sae dae yace ta jira shi yana aiki idan ya gama zai kirata haka zatayi ta zama amma sam bara ya nemeta ba ……idonta ya ciko da kwalla ba tare da ta sani ba……
Lumshe ido yayi lokacin da kwallar ke fitowa daga kwayar idonta wani irin sonta ke fizgarshi duk da ya san cewa ta kusa mashi nisa ……�
Cikin sanyin murya yace "Madam dan Allah ki koma cikin motar muyi magana ,ba dan na isa ba ……�"
juyawa tayi da sauri ganin kukan na niyar subuce mata ga mutanen dake kai da komowa a harabar makarantar bayan motar ta fada tare da kife kanta a cinya tana kuka bata san lokacin da take surututai ba tare da kiran sunan Abbanta"Abbana me na maka dan Allah?me ya saka zaka juyan baya bayan kasan kai kadai ka rageman Allah ka jibanci lamurrana ni marainiyace kafi kowa sanin halin da nake ciki ……�"
*FEEDOHM馃挒*
[11:03PM, 10/21/2017] Feedohm馃挒: 馃挧馃挧 *ZAN RAYU DAKE馃尮*
馃尮馃尮馃尮
馃尮馃尮
馃尮
漏 *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM馃挒_*
*Devoted to Ummi A'isha馃憣馃徎*
1�4�
Cikin sanyin jiki shima ya shiga motar , kifa kanshi yayi a sitiyarin yana kallon yarda ta matse kanta da cinyoyinta ,wani irin sonta ke fizgarshi a sanyaye yace "Madam dan girman Allah ki bar kukan ki fada man me ke faruwa�"
Girgiza kai take a hankali ta kasa magana ,ina ma zata iya da ta fadawa maleek cewa Abbanta ne ke neman juya mata baya ,amma sam barata iya jin zata yarda da wani mutun ba a rayuwarta har ta iya fada mashi matsalarta �
"Please Madam dan Allah kiyu shiru wallahi bana jurar kukan mace bare ma naki madam ko bakya lafiyane�
Tambayar duniyar nan ya mata taki kulashi sae ma wani sabon kuka da take ……hankali ya tashi motar ya fita daga makarantar direct dutsin safe ya nufa da ita ,bakin gidan Granny yayi parking a iya zaman da yayi da ita yasan nan kawae take zuwa ta samu farinciki ……�
Cikin sanyin jiki ya fito ya bude mata motar sae a lokacin ta dago da kanta ta ga inda suke da sauri ta fito ta shige gidan ba tare da tace dashi komae ba bayanta ya bi da kallo tare da lumshe ido
Tana shiga gidan ta durkushe a tsakiyar falon tana kuka , Granny dake zaune bisa doguwar kujera ta mike tare da karasowa gurinta ……�
"Menene kuma Hussaina ,fada man me ke faruwa �"
Cikin kuka tace "kaka shin Abbana bai san shi kadae gareni ba � ko ya manta cewa mamina batta raye ?aka me yasa yake neman juya man baya �"
"Me ya maki Hussaina�"
"Granny Abbana ya daina sona�"ta fada tana shashshekar kuka
"Karyane Hussaina ko ma mene Allah ya fisu , kin fi kowa sanin kece rayuwar Abbanki me ya saka zaki damu ,bana son wannan kukan kinji ko ,tare da Abdul maleek kika zo �"
Daga mata kai tayi a hankali tana sharan kwallah
"Jeki kira manshi "
Ahankali ta mike ta fita ganin ba motar ya sakata dawowa ta fadawa kakan ya tafi ……
銆娿€娿€娿€娿€娿€嬨€嬨€嬨€嬨€�
Alhaji khaleed kam tun da ya zauna office ya,kasa tabuka komai ……cikin kwana kinnan ya rasa meke damunshi sam baya kaunar Safeena ta rabeshi amma idan bata kusa dashi sae yaji ita kadae yake bukatar gani ……har ga Allah ya san duk duniyar nan babu abunda yake kauna sama da diyarshi amma ya rasa meke damuwa ……
Wasu yan siraran hawaye ke bin kumatunshi yayin da zuciyarshi ke bugawa da karfi,tsoro da fargabar rasa diyarshi yake ,yana sane da yanayin da take shiga yan kwanakinnan……cikin sauri ya janyo wayarshi tare da kiran Abdul maleek don ya tabbata ko wane yanayi take Abdul maleek zai fi kowa sani
Ringing daya a na biyu ya dauka tare da barin office dinsu ya fita harabar court din , kamar yana ganinshi ya russuna yana gaidashi
Cikin rawar murya yace "Maleek ina safeena tana lafiya dae ko?"
Karo na farko daya farawa uban gidanshi karya yace"Alhaji tana lafiya lau yanzu na kaita makaranta na dawo "
"Bata cikin damuwa ka tabbata Abdul maleek ……?
"Alhaji tana cikin kawayenta ma suna karatu kuma banga alamun damuwa a tattare da ita ba ,Alhaji lafiya ?
"Ba komae Abdul maleek dama kawae ina so naji yarda take ne ,Abdul Maleek ba kai safeena unguwa kadae na saka ba harda amanarta na baka don Allah ka kular man da safeena ……�"
《》�《》
Aunty faty kam daga gidan hajiyarsu gidan Aunty zuby ta nufa ,a falo ta iske ta zaune ita da mijinta ,janta tayi daki sannan ta fito da wasu magunguna ta mika mata a hannu �
"Kina jina ko ki tabbatar kin saka mashi a ruwan wankanshi na safe sannan ki zuba mashi a abincin da zai fara ci a safiyar gobe……shi da wannan shegiyar diyar sae daga hannu ……�"
Dariya ta sake tana fadin "Sae Aunty to ina na safeenar kin san dae sauran wata biyu bikinta ,kuma ni wallahi bana son wannan shegen auren don bara ta yiyu diyar Aisha tayi aure ba ta bar yayanmu zaune ……�"
"Ke kau me kika ci na baka na zubana mashi maganar yace sae ana saura sati bikin zaa sakar mata jini kinga kau dole ango ya kora masu yar su a matsayin bazawara ba budurwa ba ……idan akace a hana auren tana budurwa to kinga zata iya samun wanda ya fi wancan tunda dan ubansu kamar a jininsu yake ……�"
*FEEDOHM馃挒*
[5:06PM, 10/20/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
© *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM💞_*
*Devoted to Ummi A'isha👌🏻*
1⃣5⃣
"Amma Aunty zuby kina tunanin JB din zai rabu da ita ……yana fa sonta kada ya nema mata magani yaki sakinta ……"ta fada a sanyaye
Harara ta sake mata"Baki yarda da abunda na fada maki ba kenan ……shi banzane da zai zauna da mace tana bleeding ,kiyi amfani da kai mana ,tunda uwarta ta yi ta barmu itama babu abunda zata iya , ke dae kawae ki zuba man ido ……"
Mikewa Aunry fatin tayi ta sabi jikkarta tana fadin "Bara na wuce aunty zuby komae kenan na kiraki ,yauwa hajiya tace ki aika Fadila ta karbo maki sakonki ……"
Kusan tare motarta data Safeena ta shiga harabar gidan Abdulmaleek dinne ya fara parking sannan Aunty fatin tayi a tare suka fito da safeenar ,da Sauri aunty fati din ta matso tana fadin "Feena ina kika tsaya tun dazu nake kiran wayarki naji ko kin dawo gida ……"
Harara ta sake mata kasa kasa tace "ki godewa Allah da baki sameni ba, don da kin samu da baki samu damar fita ba……"
Kwantar da murya tayi tana fadin "haba feena me yasa kike man haka yanzu neman naki ma a waya laifine ……"
"kya ji dashi Aunty fatee ,Maleek gobe da safe kaje dutsin safe granny na nemanka ……"ta karashe maganar tare da yin gaba abunta
Aunty Fatee ta juyo tana kallon Maleek daya zuba masu ido yana kallon duk abunda suka ,lallae sae yau ya tabbatar da safeena bawae shi kadae bane batta so aa duk wanda ke rabe da ita ne takewa haka ,amma tana da kyakykyawar dangantaka da mutanen da bata da wata alaka dasu ……
"Abdul maleek kaga safeena ko, yanzu dan Allah abunda take man ya dace ……?
Dan girgiza kai yayi a hankali yana kallonta ,cigaba tayi da fadin "Wallahi Maleek sam safeena bata da halin kirki ,yarinyar muguwace bata da tausayi ,kai kanka jiba yarda duk ka lalace ai lokacin da kazo ba haka kake ba ,ni……"
Katseta yayi ta hanyar cewa "hajiya sae Allah ya kaimu ……"bai jira abunda zata fada ba ya bar gurin , ko motar bai tsaya dauka ba ……
Daga nan gidan granny ya nufa da yake sun riga sun saba shiga kawae yayi ya isketa a falo tana gyangyadi ……
"Yar tsohuwa kuma bacci ake yi " ya fada cike da xolaya
"Abdul maleeku ne ,yaushe ka shigo ……"
"Yanzu wallahi madam tace kina nemana ……"
"Eh aikenka nake son nayi a daura gobe idan Allah ya kaimu ……"
"Allah ya kaimu goben ……"so yake ya mata zancen safeena amma yana kunya daurewa yayi ya dukar da kai yana fadin "Hajiya ni ko dan Allah ko kin san meke damun Madam ne naga tana cikin damuwa……"
A jiyar zuciya ta sake sannan tace "Abdulmaleeku laifina ne ki bibiyar jikata ……"
"Ya laifinki kuma hajiya ……?
"Karka damu kaji ko ,na yarda da kai sissae Abdul maleeku idan Allah ya kaimu gobe zan fada maka wacece safeena ,tana rayuwane kewaye da makiyanta ……"
Wata yar takarda ta fito dauke da address da number waya a kasan number an rubuta Malam ibrahim daurama ta mika mashi tana fadin "Ga address da number wayar mutumin da zaka nema , zaka karbo man sakone daga gareshi idan kaje ka kira numberta zamuyi magana dashi ……"
Karba yayi ya mike yana mata bankwana
Ko da yaje gidan bai iske nana a tsakar gida ba ,da yake yanzu tana samun saukin Inna tunda yana kawo kudi da kayan abinci ……Dakin inna ya leka ya gaida ita lokacin har nanar tayi bacci ……kudin cefanen gobe ya bata sannan ya tafi inda yake kwana don so yace tunda safe ya wuce aiken granny ……
《《《《《》》》》》
Baisha wahala gurin gane malamin ba ,da yake sanannene ,bayan sun gaisa ya masa bayanin daga inda yake cikin faraa ya amsheshi sannan ya saka aka kawo mashi fura mai sanyi …… ,shi ganshi ya gamsu da malamin domin yana cike da kamala da natsuwa sannan a falon da aka saukeshi babu komae face litattafan addini da,kamshin miskin dake tashi ……Ga tsantsae kama da yake da granny kamar an tsaga kara ,ko baa fada mashi ba ya san cewa dan uwanta ne,……
Waya ya fito ya kira granny suka gaisa cike da barkwanci yana tambayarta ya safeena,……
Baiji me take cewa ba sae dae yaji yace "In Allah ya yarda babu abunda zai cutar da safeena don Allah ba Azzalumin bawansa bane ,wancan ma da sukayi Allah ya ara masu rana ne kafin ya karbi abunsa ……"
Sun dan,jima suna maganganunsu kafin ya kashe wayar yana kallon fuskar Abdul Maleek din yace "Kanaji muna ta surutu ko ……"
"aa bakomae wallahi "ya fada fuskarshi dauke da murmushi ……
Dan murmushi malamin yayi sannan ya mike ya shiga wani daki ya,fito rike da wani dan karamin littafi na larabci sae wata karamar kwalba kamar almiski ya mika mashi yace ya kai mata ……
*FEEDOHM💞*
[9:37PM, 10/20/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
© *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM💞_*
*Devoted to Ummi A'isha👌🏻*
*_YA ILAHI 🤦🏻♀ jama'a ku duba da kyau ba novel bane kawae happy birthday nawa billy ladan amma ba wae yana nufin zan cigaba da typing dinshi ba ……wasu ma wae na badu complete document aa ba document ba decomo😂😂_*
1⃣6⃣
Wajen Karfe 11 ya dawo katsina sae da yaje office yayi signing sannan ya wuce gidansu safeena don yana bukatar kara ganinta kafin ya wuce gidan granny ……
Garden ya hangota zaune ita da wani mutumi duk da sun juya baya hakan bai hanashi gane JB bane ……wani abu ya tokare mashi kirji bai karasa ba ya juya da sauri zai fita karo yayi da mutun ya dago yana fadin
"Sorry……"
"Sorry ……"itama ta fada cikin saurin maganarta tare da dukawa ta dauko mashi,key dinshi da ya fadi ……
"Very Sorry ban lura da kai bane kaji ……" ta fada tana kallon fuskarshi
Gaba yayi abunshi yana kallon kasa ba tare da ya amsa ba ……ita kam binshi tayi da kallo har ya bar harabar gidan sannan ta sake ajiyar zuciya, ta shige gidan da sauri tana kwala kira
"Aunty Fatee……!
Aunty fateen ta fito daga part din Abbah tana fadin "wannan kira haka fadila kamar mai shirin cika gidan ……"
"Aunty nayi gamo wallahi duk na rude ……"
"To Allah ya kyauta ,tukun ma me ya rudaki haka ……"
"Wani gentle na gani ya fita daga gidan nan Wayeshi Aunty ……"
"Mtsww ke mahaukaciya ce wallahi shine zaki shigo kina kwala man kira haka , to ba wanda ya fita anan sae dae idan da aljan kikayi gamon……"
Itama karamin tsakin taja sannan ta zube saman kujera tana kallon labulen dake yayewa a hankali ……ganin safeena ce ya sakata sake jan wani karamin tsakin tana daukar remote……
Kujeran dake facing din fadilan ta zauna ba tare da ta kulata ba ,gyarawa tayi ta kwanta sossae tana danna wayarta ……
"Ke bakya iyawa mutane magana dan ubanki ……"fadilan ta fada tana kallonta,
"Mtsww ni wallahi na rasa me ke damun hajiyarku ,tana ganin mutane na hauka bara ta iya kaisu asibiti ba ,salon su fara dukan mutane kuma a rasa yarda zaayi dasu ……" ta fada hankalinta na ga wayarta
Aharzuke fadilan tace "ke da ubanwa kike ……"
Kallonta tayi na yan mintina sannan ta mike ta bar gurin ……
《《《《》》》》
Abdul maleek kam jiki a sanyaye ya karasa gidan granny sakonta ya bata sannan ya zauna ……ba tare da bata lokaci ba ta fara bashi labarin ……
*_TUSHIYAR LABARIN……_*
Abdul maleeku kamar yarda ka sani sunana Hajiya rabi mijina kuma Alhaji shehu tun lokacin da bai da komae na aureshi har Allah ya bude mashi kasuwa arzikinshi ya fara bunkasa ……ina da kawata aminiya hajiya shafa'u mahaifiyar su Fatee auntynsu safeena kenan ……shafa'u aminiyatace sossae duk wani sirri nawa dana mijina ta sanshi babban kuskuren dayi kenan na sanin sirrin mijina da tayi ,a
lokacin bata da gurin zuwa sae gidana ,na mayar da ita kamar yar'uwata na saki jiki da ita yarda baka tunani ……mijina ya san amintar dake tsakaninmu da ita don Haka shima ya sake da lamarinta
Kwatsam sae naji mijina na neman auren shafa'u harga Allah ban kawo komae ba a raina don nayi imani matar wani bata auren mijin wata ……bayan lokaci amarya ta tare gidan mijinta na kuma rungumeta kamar da ,amma sae dae ita sam bata daukeni a bakin komae ba face kishiyarta makiyarta ……tana zuwa da shekara daya ta dire yarinyarta mai suna zubaida haihuwar yarinyar tazo da salo iri iri don har ta kai bana daukar diyar sae ace tsinkulinta nake ……
Kasan kowa da irin kaddarar da Allah ya daura mashi to ni kaddarata ta rashin haihuwace don sae da nayi shekara 18 da aure sannan na samu haihuwa na samu AISHA,a lokacin Shafa'u tana da yara uku ZUBAIDA ,SARATU,HINDE ,bayan na haifi AISHA ne ta haifi FATEE DASALMANU Wanda ka fi sani da UNCLE ABBA
Akokarin maigidanmu na ya hada kanmu guri guda amma sam abun ya gagara kamar yana gini ne ana rushewa
AISHA ta tashi cikin tsana da tsangwamar yan uwanta ko kadan basa kaunarta dalilinsu kuwa shine ta fisu kyau sannan ko wa yazo gidan baya da magana sae tatata tana da saurin shiga rai farat daya ……
A irin wannan halinne har ta girma cikinsu sannan abun Allah duk ta rigasu samun mijin aure ……wannan auren ba karamin tada hankalinsu yayi ba don na tabbata lokacin ne hajiya shafa'u ta fara neman bokaye ……
Amma da yake Allah ya kadarta sae tayi auren to babu makawa akayi shi bayan bikinne da watanni kadan Allah yayiwa mijin namu rasuwa ……a tunanina lokacin kishin zai ragu tunda wanda akeyi domin shi ya rigaya ya tafi amma ashe abun ba haka yake ba lokacin mane duk wani kishi,nawa ya koma gun diyata saboda tana auren masu kudi ……
Bayan lokaci kadan zubaida itama ta samu miji bata cika shekara daya ba ta haihu ……sae sabon tsegumi ya tashi cewa Aisha bata haihuwa ,sam daga ni har ita ba wanda ya damu domin haihuwa ta Allah ce haka dangin mijinta basu nuna komae ba dangane da rashi haihuwarta ……
Sae da zubaida ta haifi Fadila ,maryam da jamila sannan ALLAH ya bawa AIshata ita ya'yanta yan biyu duka mata……
*FEEDOHM💞*
[1:29AM, 10/21/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
© *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM💞_*
*Devoted to Ummi A'isha👌🏻*
1⃣7⃣
Lokacin da AISHA ta haifi su safeena sae zancen ya banbanta hajiya shafa'u ta rude akan itama kyawawan jikoki take so kamar nawa ……sae ta fara tunanin idan diyarta ta auri Abbansu safeena to tabbas itama zata haifi kyawawa , ta manta da mai kyau da mai muni duk na Allah ne ……
Alokacin fatee kadae ta rage mata tayi aure sae ta fara bin bokaye a kan lallae Aisha ta mutu fatee ta aureshi ……
Ina Zaune gidana Aisha ta sameni tana kuka tace ita kam ta gaji da wannan rayuwa kusan watanta 5 tana bleeding abun ba tsayawa ,sunje asibiti ance ba maganin asibiti ya makamata su nema ba ……
Ni da kaina naje daura na fadawa dan uwana malan ibrahim shi yace man asirine a ka mata amma insha Allah zaa magance haka ……
Lokacin dana fada mata cewa tayi "Haba Ummi taya zaa ce asiri ya kamani bayan kullun cikin tsarkake addinina nake ga Allah fa nake neman kariya gaskia ba asiri bane kawae ana so a hadani da yan uwana ……"
Nace "a Kul Aisha ,don kina tsarkake addininki sae kuma akace Allah bara ya jarabeki ba ?shin lokacin da akama mqnzonmu asiri shi rashin tsarkake addinin ne ya saka ya kamashi ? Aisha ki natsu ko da a masallaci kike kwana Allah zaya iya jarabki ta ko wace hanya ,ki dauka wannan itace kalar jarabawar da Allah ya daura maki ……"
Haka ta tafi tana kuka ,bayan kwana 10 da naji shiru sae na tashi naje har gidan na sameta ……tun daga bakin falon naji muryarta cikin kuka tana fadin "Ka sawake man dan girman Allah ALHAJI wallahi baran iya wannan rayuwar kaskancin ba ,baran juri ina matarka ba amma kullun cikin wulakanci su kansu yayan da ka haifa baka kulasu ……"
Cikin hargowa yake fadin "Har sae kin bari na sawake maki Aisha ,hanya a bude take kina iya tafiya abunki ……taya zan zauna da mata kamar ina zaune da wani namiji sam wallahi baran jura ba ……ya'ya kuma da kike magana ko yanzu kika tsallakesu na tabbata wadda zata zo zata kula dasu ……"
Kasa karasawa gidan nayi na juya jiki a sabule ko gida ban iya komawa ba tasha naje na hau motar daura na iske malan Ibrahim cikin kuka na fada mashi abunda ke faruwa
Blackseed ya bani mai da garinshi tare da garin magarya yace na bata ta dinga wanka dasu tana sha man blackseed din sannan ya hada man da pure almiski tare da olive yace duk ta dinga amfani dasu ……sannan ya dauko husnul muslim ya hada man yace ta rike azkar……
Haka na dawo da wannan hadin na wuce gida kafin zuwa safe na kai mata ……sae dae daga bakin kofar na jiyo kukan su safeena hakan ya tabbatar man da cewa aikin gama ya gama ……
Ganin tana kuka ga yara duka biyu a hannunta ya sakani karban yaran ba tare da na tambayeta baa sin zuwantan ba ……
Kusan watanta biyu Alhaji khaleed bai leko mu ba ,cin yayanshi da matarshi duka yana hannuna ……da na gaji na taka har gidanshi na iskeshi a can na iske Aunty fatee zaune a falo suna fira hankali kwance
Lokacin ne na kara tabbatar da abunda malan ibrahim ya fada man ,ina tabbatar maka ban baro gidan ba sae da takardar sakim Aisha a hannuna ……
Haka muka cigaba da rayuwa yau da dadi gobe babu ,magunguna kuwa kullun cikin hado mana malan ibrahim yake amma sam abun kamar kara cigaba yake
Cikin yan kwanakinne muka samu labarim cewa Abban safeena zai auri fatee ……duk a tunanina zan ga damuwa a fuskar Aisha amma sam abun bai dameta ba sae dae fatan alkhairi da ta masu ……
Har akayi bikin Alhaji khaleed da Fatee bai nemi yaranshi ba sannan ni kuma ban nemeshi ba akan maganar yaran ……
Bayan Auren da shekara daya ne Allah ya ma Aisha rasuwa ba tare da wani ciwo ba kawae mun wayi garine ta rasu ,daga hajiya shafa'u har iyalenta babu wanda yazo man gaisuwa har yau ……shi kanshi Alhaji Khaleed din bai zo ba sae da aka shekara biyu lokacin su safeena sunyi wayau sossae ……
Da kuka yazo ,yana tabbatar man cewa wallahi bai san meke faruwa ba ,Allah ya kyauta na bishi da ita don har ga Allah duk da ba cikin hankalinshi yayi komae ba amma tabonshi na raina ……
Yana zaune Safeena da nafeesa suka shigo rike da hannun juna ……da yake ba saninshi sukayi ba ko kallon inda yake babu wanda yayi a cikinsu ……
Cike da kunyarsu ya mika hannu zai dauki Nafeesar da yake tafi Safeenar hakuri ……yarinyar ta washe baki zata je amma safeenar ta kabe hannun tana hararanshi tare da janye hannun nafeesar suka koma gurina ……
Hakan ba karamin dadi yayi man ba tunda ban hanasu zuwa gurin babansu ba amma gashi safeenar ta hana yayartata ……
"Safeena ku zo kunji ko 'dan Allah ku matso naji dumin ku ya'yana ……"ya fada tare da kara mika hannu
Cikin maganar da bata cika mata baki ba tace "bala a zo in ba ,Nafeesa um um kalki je ,idan kika je balan yan'maki siwi ina ba ……"
Dukar da kai yayi yana hawaye ,sossae naji tausayinshi ya kamani na kalli safeena don ina da tabbacin tunda tace kar nafeesar taje bara taje ba nace "Husaina Abbanki fane ,kuje kunji ko ……"
"Balan je ba ……wallahi balan je ba " ta fada tana jiniyar kuka
*FEEDOHM💞*
[6:52PM, 10/21/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
© *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM💞_*
*Devoted to Ummi A'isha👌🏻*
1⃣8⃣
Cikin sanyin jiki ya kalleni sannan ya sadda kanshi a kasa ,tausayinshi ya kara kamani na janyo hannun safeena ina fadin "Zaki sha siwi husaina ……"
"Ni nafeesa zamu sha a tare kaka ……"
"Yauwa to indae zaki sha kije gurin wannan sae ya sayo maki kinji ko ……"
Kallon nafeesar tayi sannan ta kalli Abban nata dake duke kamar me neman gafara ,Janyo hannun nafeesar tayi ta matsa gurinshi tana kallonshi ……
Da sauri ya rungumesu yana fitar da numfashi a hankali ……mintina kadan tayi sannan ta fara kokarin kwacewa daga jikinshi tana dukanshi a baya tare da fadin "Sakeni ka bani siwi in ……kaka yaki bani siwi ina nafeesa sakeshi kema ……"
Tun daga lokacin kusan kullun sae yaxo gidan Fatee kam har lokacin sun kulle mashi baki baya iya tabuka komae a kanta da su kaga ya fara ja da baya da lamurransu sae suka zuga fateen ta koma kissa da kisisina tare da kokarin dole sae ya maido su safeenar gidanshi domin zata fi kula dasu ……
Alokacin da yazo man da zancen zai karbi yayanshi ban musa mashi ba domin na tabbata safeena ba kanwar lasa bace duk da tana karama sannan duk wanda aka bawa rikon safeena to tabbas indae zai cuceta sae shima ya koka ……matsalata daya kawae nafeesa domin Allah ya zuba mata ruwan hakuri sak mahaifiyarta ce ,don tasha safeenar ta janyo fada a kama nafeesar a daka kuma bara ta taba cewa ba ita bace tayi lafin ……sannan nayi imani cewa yanzu yana kaunar yaranshi fiye da zato ……
Da dubara aka dauke yaran daga hannuna aka mayar da rikonsu ga Fatee……
Wata ba hagguwar rayuwa suka soma a wajen fatee ,idan Alhaji na gida zata tarairayesu amma idan baya nan cuta kala kala zata masu ,a lokacin basu wuce shekara biyar biyar ba amma aikin gida babu wanda nafeesar bata iya ba ……Safeena tana samun sauki sossae domin duk abunda zaa mata zata nemi hanyar fanshewa ……
Ranar juma'a naje gidan dubasu kamar yarda na saba duk sati ……
Tun daga harabar gidan naji fatin na bala'in wae ta aje gwangwanin madara amma Safeena ta zubar dashi ……
Ihun dana jiyo ne ya sani hanzarin karasa ciki Nafeesa na gani tana duka da handbell kamar tana dukan wani kato , cikin sauri na karbeta ina fadin "Subhanallah ya haka fateema me ke faruwa ne ……?
A harzuke tace "dan uwar yarinyar nan na aje madara duka yau na fasata amma ta zubar man da ita duka ……"
"Fateema ai hakuri ake da yara kinji ko ……ina safeenar take ……" na tambaya ina karewa falon kallo ko zan ganta
Daga saman benen naji ana fadin"kaka ganinan sarkan ne yaki wucewa ……yauwa ya wuce bara na fito……"
Ta fito da gudunta tana harara kasa kasa ko baa fada ba nasan da Auntyn tata take ……kallon nafeesar tayi da har yanzu tana hannuna tace "kiyi shiru Allah ya saka maki tunda Allah ya sani bake kika zubar ba ……"
A sanyaye nafeesae tace "Ni na zubar mana ……"
"Dalla can ni fa ce na zubar ba na sani ba shine ta kamaki tadaka ai na rama maki don na kwashe sarkokinta duka na zubar a masae ……"
Hannu ta daura saman kai tana sallallami kafin ta nufi sama da gudu ta duba inda take aje gold dinta babu komae ……
Ina jiyo ihunta na tabbatar da abunda safeenar ta fada gaskiayane ……ko kadan banji haushinta ba kafin fateen ta fito naja jikokina muka bar gidan ……
Sun kusan wata gurina da kyar na yarda na bashi su
Ko Wata daya baa kulla ba akace man wae nafeesa ta fado daga saman bene kanta ya fashe an kaita asibiti ……
*FEEDOHM💞*
[7:46PM, 10/21/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
© *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM💞_*
*Devoted to Ummi A'isha👌🏻*
1⃣9⃣
A kidime na iskesu FMC a harabar asibitin na iske Alhajin ya fito a rude ,tun daga lokacin jikina yayi sanyi ,na tareshi ina tambayarshi lafiya
"Nafeesa ta tafi Umma ……"abunda yake fada kenan
Jiki a mace na karasa dakin da suke a can na iske Safeenar kwance saman jikin yar uwar tata tana kuka ,Su fatee suna tsaye cirko cirko kai da gani jikinsu yayi sanyi
Saitin kunnenta ta matsa cikin kuka take fadin "Idan baki tashi ba nafeesa baran,baki sweet dina ba ……kinganta nan a bayana na boye ,ki tashi kinji ……"
Tana jin tafiyata ta dago a tsiwace tana fadin "Karku zo nan ,kada wanda ya matso kusa damu ……"
"Safeena ……kalleni nice fa " na fada a sanyaye
Da sauri ta juyo ta rungumeni tana kuka ……"Kaka nafeesata kalli jini a kanta ……wae Abbana yace bara ta tashi ba ,ai dae zata tashi ko kaka?wasa nake mata zan bata sweet din kaka so nake kawae ta tashi ,tsaya ki gani ……"
Komawa tayi kusa da ita tare da rike mata hannu tana fadi "Kinga sweet din tashi na baki to ,bude bakinki na saka maki akwae dadi ……"
Sossae na rungumeta ina sauke ajiyar zuciya tausayinta ke ratsa dukkan jikina Atare a ka haifesu rabuwarsu dole tayi mata kunci "Kaka kuma ba ita bace ta batawa Aunty fati gaban mirrow ba ni ce kaka, amma ta kamata ta jehota daga bene……"
Maganar ta dakeni sossae nayi saurin dagota daga jikina ina kallonta cike da shakkun abunda ta fada
Cikin kyarma nace "me kika ce Safeena ……"
"Kaka ba ita bace tawa Aunty fatee laifi ba nice nayi kawae don taga shaidar da tayi mani don ta dinga ganeni a jikin Nafeesa shine tace nice ta kamata ta jeho daga saman bene ……"
"Wace irin shaida Safeena ……" na fada a rude
Hannun rigarta ta dage ,wani tambarin dutsin guga ya fito sossae a hannun "Kin ganshi kaka tun lokacin da ta man shi ina kuka sae Nafeesar itama ta dauka tayi wa kanta don taji zafin da naji ita ……"
Daukarta nayi na fita daga asibitin da sauri ba tare da na furta kalma ko daya ba ……
Daddare Abbanta yazo daukarta sam kin bashi ita nayi sannan ban fada mashi abunda ke faruwa ba na barshi akan daga saman benen ta fadk ……
Tun daga lokacin rikon safeena ya dawo hannuna Abbanta kuwa kullun yana gidana tare da diyarshi sannan banyi kasa a guiwa ba gurin bata magunguna da addu'o'in kariya daga sammu haka bata da ruwan wanka da ya wuce ruwan ganyen magarya ……
Tun tana kankanuwa ake binta da mugunta amma Allah na kareta asiri kuwa ita da kanta idan tana wasa zata kawo man layu tace tsinta tayi tana rami ……sae idan mun kwancesu sae kaga sunan Safeena da rubutun ajami ……
Haka muka cigaba da rayuwa har sae da takai shekara 18 lokacin ne na tabbata babu wani mahalukin daya isa ya cutar da ita indae ta fannin zama ne sae dae ko ta asiri domin babu wanda ya wuce shi ,Sannan ne ta koma gidan ubanta ……
_*CIGABAN LABARIN……*_
Tunda ta fara bashi labarin kanshi na kasa sae da yaji ta tsaya sannan ya dago a hankali yana kallonta ……
"Kaka kina sane da Aunty fatee ta kashe mata yar uwa kuma kika barta ……"
Yar dariya tayi tace "to ya zan mata Abdul Maleeku ?zan kasheta ne nima ……"
"A'a kaka amma ai akwae hukuma ……"
"Kwarae kam akwae hukuma ,shi yasa muka barta da babbar hukuma wacce bata da kudi ko nasaba da zata iya sayen alkalinta ……"
Lumshe ido yayi tare da mikewa "Kaka zan tafi nagode sossae ……"
"Allah ya kiyaye yau de baran ce ka tsaya kaci abinci ba bare ka cinye man dan wanda na rage na dare ……" ta fada cike da zolaya
Dan juyo yayi yana dariya "abun har da gori ……"
"Eh mana ,kaje kayi aure ka tsaya kullun kana gaban yar kanwarka kana soke kai kana kiran Madem……" ta karashe maganar tana kwaikwayon yarda yakewa Safeena idan sunzo gida
Fita yayi falon yana dariya ,har ya bar unguwar bai bar dariyar Kaka ba ……Sossae tsohuwar take burgeshi duk da jikarta yake wa aiki amma hakan bai hanata fada mashi magana ba ……
*FEEDOHM💞*
[6:57PM, 10/22/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
© *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM💞_*
*Devoted to Ummi A'isha👌🏻*
2⃣0⃣
Gyaran murya yayi bayan ya kammala lecture din sannan ya daga kai yana kallon gefen da yan matan ke zaune "Safeena khaleed ……"
"Yes Sir……"ta fada a hankali tare da kallon matashin lecturer dake tsaye gaban bar din
"Meet me in my office now……"ya fada tare da tattara DDs dinshi
Gabanta ne yayi bala'in faduwa ta bishi da kallo har ya fita daga chamber din "Akan me zan sameshi a office Maryam ……"ta fada tana kallonta
"Nima abunda nake tambaya kenan Feena ,ko kuna da wani issue ne dashi ……"
Tabe baki tayi tana parking takardunta da ta zubar a saman kujeran "No……Beside ma ban taba magana dashi ba ……"
"Ki je kiji abunda zai ce maki but you shld take care……"ta karashe maganar tana kallon fuskarta
"What ever ma i should deal wit it ……ki jirani yanzu zan dawo"
"Imagine har kin san ma yanzu zaki dawo……pee!!
Bata kuma cewa komae ba ta dauki phone dinta ta fita ……area da office din nashi yake sam babu hayaniya a hankali ta tura kofar office ta shiga dauke da sallama ……yana shingide saman kujera ido a lumshe kamar mai bacci ……
Bude idon yayi kanta tare da sake mata murmushi ……itama murmushin ta mayar mashi tana kallonshi
"Have a sit Feenat ……"ya fada yana nuna mata kujeran dake facing tashi
Sossae ta zauna tare da tallabe kumatunta tana kallonshi ,gaba daya natsuwarta ta maida kanshi ……
"You're Suprise na kiraki ko ……"
Gyada mashi kai tayi ba tare da tace uffan ba
"Ki bar mamaki kinji baby ,as classic as you bai kamata kiyi mamaki ba dan handsome kamana ya nemeki you deserve it ……nasan kullun kina kallon mirrow kuma kinyi nayzing kyawun dake gareki ……"
Yar dariya ta sake tana maimaita handsome a ranta ……ta tabbata ko drivernta Maleek ya fishi nesa ba kusa ba ……
Ganin tana dariya ya sakashi dawowa bisa desk din dake tsakaninsu ya zauna "Feenat baby ……kinsan rayuwar duniya taimakeni na taimake ka ne ko ……"
Yar dariyar ta sakeyi tana kallonshi,bata so ta katse mashi hanzari ta fi son ta kaishi har inda take bukata ……
"Feena duk wasu da kike ganin sun fuce da first class da taimakon mu ne ……kema abu mai saukine ki fita fresh indae zaki hau hanya ,ki bani in baki baby ba rowa ,ni nan da kike gani idan na tsayawa yarinya ko VC bai isa ya ta ka ta ba ……"
"Kaman gwari gwari Sir yarda zan fahimta……"
Yar dariya ya sake yace "kamar wata bakauya ,to ina nufin ki taimakeni na taimakeki kema ,……"
"Wane irin taimako Sir , kudi kake bukata ko me ……amma a nawa tunanin ni bana bukatar taimakonka"
"Oh Feenat kamar ba wayayya ba ……ok i means mu dinga making love ……karki damu babu wanda zai sani ……"
"Good anzo gurin ,ban taba tunanin kai wawa bane sae yau karka manta Safeenat Khaleed ce a gabanka yanzu ……idan ka saba lalata yaran mutane to ni nafi karfin jakkancinka ……"
Yar siririyar dariya ya sake yana fadin "Yarinya kina wasa da result dinki ……"
"Ko kuma kana wasa da aikinka ba……"ta fada tare da fito wayarta ta kunna
Tun daga farkon shigowarta har maganar da sukayi yanzu tayi recording ……
Mikewa tsaye tayi tana fadin "Ni ba irin jahilan matan da zan shigo office din mazinaci irinka ba kai tsaye ba tare da na shirya ba ……"
A firgice ya mike yana nunota "Ke ni zaki wulakanta wallahi baki isa ba ……"
"If you step one hnd I'll chop your leg's ……A Tunaninka zaka karbe wayar ne daga hannuna ……so look here ……"ta fada tare da kanga mashi wayar a fuskarshi ……
Recording din da tayine yaga anyi forwarded to GRANNY,MALEEK &Maryam……
"Nasha fada maka ni ba jahilan yarinyar da zan shigo office din mutumin irinka,bace ba tare da na shirya ba ……"
Tuni zufa ta fara wanke mashi jikin tsabar tsoro da nadama suka mamaye fuskarshi cikin rudu yace "Ki rufa man asiri dan Girman ALLAH Safeena ki goge wallahi ba yin kaina bane Uncle dinki ya sani dan Allah kiyi hakuri wallahi da kyar na samu aikinnan idan kika nuna wannan abun wallahi licenses na aikina za'ayi cancel dan girman Allah ki yi hakuri……"
"I Know Uncle Abba ko ……kayi sharing tears dinka dashi……" ficewa tayi ta barshi a tsaye rike da kai
Tana isa ta karbi phone din maryam ta goge recording din Allah ya sota maryam din bata duba text din daya shigo ba ……Har ga Allah batayi niyyar yad'a shi ba ta tura masu recording din don ta kwaci kanta don ta tabbata idan ba haka tayi,ba yana iya karbe wayar da karfin tsiya sannan ya mata abunda yaga dama……
Wayar Abdulmaleek ta kira taji ta a kashe ,sossae taji dadi don dama taga txt din baiyi delivering ba ……bari tayi kawae idan sun hadu ta karbi wayar ta goge tunda ta lura ba cika hawa whatsApp din yayi ba ……Granny kadae ce bata shakkar taganshi saboda ta tabbata barata taba fadawa wani ba ,ita kanta tasha fadawa safeenar cewa karta yarda ta tonawa dan adam asiri komae girman laifin da ya mata ……
*FEEDOHM💞*
[8:10PM, 10/22/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
© *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM💞_*
*Devoted to Ummi A'isha👌🏻*
2⃣1⃣
Maryam ta kalla da tunda ta dawo take kallonta ,janyo hannunta maryam din tayi tana kara karantar yanayin fuskarta ……cikin sanyin murya tace "Feena me ne ?are you ok……?
Dan murmushin dole ta sake ta gyada mata kai tana kokarin mikewa tsaye
"Safeena are you sure……kina lafiya "ta sake fada domin har lokacin hankalinta bai kwanta ba da aminiyar tata
"Assured Maryam me kika gani ne ……"
"Nothing amma ya kukayi dashi ……"ta fada tana kallon gefensu
"Oh ni Safeena meye na damuwa ?kinga maryam karki damu dama cewa yayi wae Uncle Abba ya nemi phone dina bai samu ba shine ya kirashi yace ya fada man wae Hajiyarsu Aunty fatee batta lafiya ……"
"Kin tabbata Feena?kuma shine sae ya kiraki office dinshi ,kinga ni wallahi sam hankalina bai kwanta ba tunda kika tafi wallahi saura kadan na bi ki sae gashi kin dawo……"
"Common ni tashi ki ajeni gidansu hajiyar ma na gaidota, Number Maleek bata shiga……,meye na tashin hankali kamar naje war na horrows ……"ta karashe maganar tana hararanta
Kofar gidansu Hajiyar Aunty fatin ta ajeta ,ita kanta maryam din taso ta shiga ta gaidata amma sam safeena taki barinta
Daga bakin gate sukayi sallama sannan maryam din taja motarta ta tafi ta barta ……
Wani dadi taji da ta jiyo muryar Uncle Abba a falo suna magana da hajiya ,saboda sallamar ta zame mata dole ya saka tayi masu ……
Hajiyar ce ta amsa tana kokarin boye kiyayyar dake idonta "A'a Amaryace a gidan yau …Yau ina na kalla nayi sallah?rabon da kizo nan gidan ai har na mata………"
"Amaryan Jabir Bala …ko sama da kasa kika hada kika kallah meye nawa ciki ,Allah ma yasa da alwala kikayi sallar………"ta fada tana kallon Uncle Abba
Dariya hajiyar ta sake don bata san magana ta yaba mata ba "Kaniyarki Safeena ina kika taba jin anyi sallah ba alwala……"
Tabe baki tayi tana kallon Uncle Abba da har lokacin bai tanka ba
"Abba ……" Ta kira sunan ba tare da ta sakaya ba
"Yeah Abba ko ba sunanka bane ,na lura kiran uncle din da nake maka kamar ina cutar kaina ne, shi yasa na kira sunan da uwarka ta saka maka ……"
Tafa hannu hajiyar ta fara tana sallallami "Safeena kanki daya kuwa? Kawun naki kike fadawa haka ,kanin uwarki fane……"
"Sorry hajiya nima da haka na dauka amma yanzu na banbance meye yan'uba ……kai na dawo kanka "ta fada tana nuno Uncle Abban da mamaki ya hanashi cewa komae
"Last warning karka kuma sa wani kare ya nemi yaga man mutunci ,Idan kuma ka kara nima zan yaga rigar tsohuwa……"
"La hauwala Safeena ni ……" hajiya ta fada tana nuna kanta
Harara ta sake mata "yana da wata tsohuwa ne bayanke ……?
Uncle Abba ya taso yana fadin " Ke baki da kunya ,Barni da ita inci uwarta hajiya ,dan uwarki har gida zaki shigo kiyiwa Hajiya rashin da'a ……"
Hajiyar ta tareshi tana fadin "Barta Abba kira man iyayen nata yanzu ……"ta karashe maganar tare da share hawayen munafunci……
Juyawa tayi ta bar masu gidan ,ko ba'a fada mata ba tasan Meeting za'ayi kanta kuma ta shirya tazo sannan duk wani dan iska da yayi niyar takata a gurin zata wankeshi yarda ya dace ……
《《《《《》》》》》
Abdulmaleek kam aikine ya cakude mashi yau, ga Zaria yana son yaje amma bai samu lokaci ba sae dae ya turawa CC dinshi script din ta email dinshi saukinshi ma sun daga mashi duk wani abinda za'ayi a makarantar sae dae a turo mashi ta email sae dae duk wata yakan shiga makarantar sau daya ……
Case din da yayi na yau ya bala'in rudashi na wata yar budurwace da bata wuce shekara 18 ba ,ta tari mota a bakin dandagoro bata je tasha ba, zata je garin Charanchi cikin rashin saa duka passingern motar mazane sae ita kadae mace ……sae dae suka fita gari sannan suka sauka hanya suka yanka daji suka mata fyade ,su hudu ne mazan amma babu wanda bai yi amfani da yarinyar nan ba
( _yan uwa mu guji tsayar da mota ko'ina muna shiga kara duk jiran da zakayi a tasha ka jira domin kariyar lafiyar mu……wallahi hakan na faruwa sau tari ……_)
Sai da yayi sallar la'asar sannan ya bude wayarshi Number Safeena ya fara nema lokacin tana kwance a daki ita kadae tana kuka ,bata da wani wanda zatayi fira dashi taji dadi a yanzu ……
Tana jin wayar na ringing ta kyaleta har sae da ta katse dan kanta ……Muryar Abbanta ta jiyo a falo yana kiran Aunty fatee ……da saurinta ta leko tana kallonshi ,a hankali ya daga ido ya kalli kofar dakinta baiyi tunanin tana bakin kofa ba ,suna hada ido ya mika mata hannu ……
*FEEDOHM💞*
[2:47PM, 10/24/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
© *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM💞_*
*Devoted to Ummi A'isha👌🏻*
2⃣2⃣
Cikin sanyin jiki take kallonshi da idanunta da suka kawo ruwa,ta kasa gasgata cewa Abbanta ne yau ke mika mata hannu tazo gareshi ……Rabon da ta ganshi kusan wata biyu kenan ……
"Common Safeena……" ya fada tare da ware duka hannuwanshi
Da gudu ta taho tare da fadawa jikinshi ya maida hannayen duka ya rufe ……shi kanshi ya san yayi missing diyarshi ba kadan ba
Aunty fatee da ta fito jin yana kiranta tayi mutuwar tsaye tana kallon ikon Allah ,Ayarda Aunty zuby tace mata shi da Safeena sae daga hannu amma tun baa je ko'ina ba gashi yau rike da ita a kirjinshi ……
A haka ya shiga dakinshi da ita yana bubbuga bayanta a hankali ,bakin gadon ya zaunar da ita sannan shima ya zauna
"Sorry Safeena ……"ya fada yana goge mata fuskarta
"Insha Allahu baran sake nesa dake ba kinji diyata ,wallahi ina sonki ni kaina ban san meke damuna ba kinji ko ,kiyi tayi wa Abbanki addu'a Safeena ……"
Kasa magana tayi saboda tsabar farinciki sun dade suna fira Ko Aunty fati bai nema ba haka itama bata shigo ba ……
《《《《《》》》》》
Abdul Maleek ganin bata dauki wayar ba ya sashi bude whatsapp dinshi , Text din da ta turo mashine ya fara budewa da mamaki ganin tunda take dashi basu taba magana ta chat ba ganin audio ne ya sashi ko mawa cikin motar sannan ya kunna yana ji ……
"Me ake wa Safeenatah……" ya fada tare da yarda wayar da karfi
"Inna lillahi wa inna ilaihir raju'un … …" ya ke fada ganin hankalinshi na neman barin jikinshi
" _Uncle dinki ya sani……_ " abunda yake maimatawa kenan a ranshi ……
"To wane Uncle din ?…kar dae ace ya taba madam ?waye shi ?… Madam kadae zata iya fada man "……da sauri ya fada neman numberta
Ya kira yafi sau 10 bata dauka ba ,motar ya tada ya juyo ya nufo gidansu
Har falon ya shiga amma bai tarad da kowa ba sake tryinh number tayi lokacin ta shigo dakin yin sallar isha'i taga kiran ……
Cikin farin ciki har da juyinta tace "Abdul maleek yauwa ina nemanka ……"
"Madam ina cikin falonku……"
"Good bara na zo yanzu ,am kazo da wyar da kake chat da ita ……"
"Yauwa……" bata fi minti biyar ba ta fito kanta ko dan kwali babu ,yanayin da ya ganta ne ya sashi jin dan sanyi sanyi kura mata ido yayi har ta karaso ta zauna kujeran dake kusa da tashi ……
"Ka bude whatsapp dinka……"ta fada tana kokarin kunna tv
Karantar yanayinta yayi na yan sec sannan yace "A'a Madam amma bara na bude yanzu……"
Cikin sauri tace "aa karka bude bani na tura wani abu tukun ……"
Juyar da kai yayi sau biyu idan ya fahimceta bata so yaga abunda ta turo ……"to me yasa bayan ita ta turo ,ko bata san ta turo mashi bane ……"
Katse mashi tunani tayi ta hanyar mika mashi hannu tace "Bani phone din na tura Maleek……"
Ya fahimci gogewa zatayi kuma idan ta goge baya da evidence akan abunda yake tunanin zaiyi akan wannan lecturer ……
Murmushi ya sake mata tare da kokarin lalibo wayarshi yana fadin "Bara na fidda maki pin din madam……"
Juyawa tayi tana fadin "Quick……"
Da sauri yayi copying din audion a private Files dinshi sannan ya maida text din unread ya mika mata ……
Mintina kadan ta goge abunda take so ,zata mika mashi wayar taga wata number kamar a dp dinta picture din Fadilar Aunty Zuby ce,fasa bashi tayi sae da ta bude picture din ta tabbatar da Fadilan ce sannan ta bude text din da aka turo ……ba komae bane sae pictures din love da tayi mashi sending wasu ma duk basu bude ba ……
Gabanta taji ya fadi sossae ta kalleshi da sauri wanda dama ita yake kallo ……a sanyaye ta mika mashi wayarshi tare da mikewa tsaye
"Madam kin tura ko ……"ya fada don ganin yanayinta ya canza
*FEEDOHM💞*
[8:27PM, 10/24/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
© *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM💞_*
*Devoted to Ummi A'isha👌🏻*
_*Aunty Sis* Here is your page All negative material circulating in you body stream be evacuate ,Rebuke every refuge of sickness, May llah destroy the grip and operation of sickness upon your life and our lovely sultee,Any evil power moving through your body loose your hold , May the Merciful be with you through out your life I HEART YOU❤❤❤_
2⃣3⃣
A sanyaye ta gyada mashi kai tana murmushin yake ……wayar da ta miko mashi ya bi da kallo don ganin mai ya canzata lokaci guda ……
"Baran je school ba gobe ……" yaji tana fada lokacin da take kokarin barin falon
Kafin ya bata amsa ta wuceshi ta shige daki ……missed call din JB ta gani tana kokarin kiranshi ya kira
"Wife ina kika shiga haka……?ya fada lokacin da ta daga wayar
"Ina magana da Abdul maleek ne ban san ka kira ba ……"
"Baby meye haka ,wa ya kawoshi gurin matana da daddare haka……? ya fada cikin daga murya
"Ni ce na kirashi wat ur business dere……?itama ta fada cikin daga murya
Sauko da murya yayi kasa kasa yana fadin "calm down baby meye na bata rai kuma to naji i made a mistake na kishin yarinyar da 3 weeks ta zama matana ,shikenan ko ……"
Dan murmushi ta sake a hankali ,sannan ta sake jiki suna dan fira sossae ……
《《《《《》》》》》
Hajiya kam duka yaranta ta tara ranar ta da fada masu abunda safeenar ta mata har gidan har kari ……
Uwar ashar Aunty zuby ta sake tana fadin" Wuyan yarinyar nan ya isa yanka hajiyarmu har gida ta shigo ta zageki kika ki bari Abba ya karya man shegiya ku barni da ita wallahi har gidan uban nata zan tarad da ita sae naci uwarta tunda bata da kunya……"
Hajiya tace " Waya fada maku nima kyaleta nayi ? yanzu haka akwae layar dana karbo gurin boka nan da sati biyu zaa yi amfani da ita ya rage sauran sati daya bikinta kenan zaa zauna meeting anan gidan ,ni da kaina zan kira uban nata nace ya turo man ita ,a kujeran da zata zauna anan zaa aje layar na tabbata bara ta tashi daga gurin ba sae da yankewar jinin da zai zame mata babbar cuta ,dan na yau ba irin na jiya bane wallahi har tsutsa sae ya sakar wa shegiya ……"
Aunty Fatee tace "Kai dan Allah hajiya sake fada ko naji dadi ,Yauwa nikam Fadila ta fada maku Tana son driver Safeenar……"
Hajiya tace "ke rabu da shashashar wofi ,ina ita ina driver ,banda tana ma banzs ta rasa wanda zata so sae drivern safeena salon sake zubar mana da mutunci ……"
Kallon kofa Aunty Fatee tayi sannan ta kalli hajiyar tana fadin "Wa yace maku driver ne kadae ?to wallahi Abbas yaron da nake aike ya fada man cewa lawyer ne babba hakanan yake mata basaja yana nuna shi talaka ne ……"
A rude Aunty zuby tace "Da gaske Fatee ……?
"Wallahi kuwa bara ma na kara tabbatar maku ……" nan take ta sake kiran Abbas din a wayar kuma ya sake maimaita mata cewa kusan kullun sae yaga Abdulmaleek din cikin high court sanye da kayan lawyoyi har ma yace idan ya kara ganinshi zai dauko masu photonshi ya kawo masu ……
Yar dariya hajiyar ta sake tana fadin "kaga shegen yaro da arzikinshi yana boyewa a,a Su fadila an samu miji ga kudi gashi kyakykyawa ko ba komae muna mun samu masu kyau a cikin jininmu ……"ta karashe maganar tana buda。
Aunty Fatee tace "ba nan gizo ke sakar ba Maleek din fa kamar Safeenar yake so……"
Harara hajiyar ta sake mata "Daena wannan zancen banzar……Su kadai Allah ke so da zasu dinga samun komae a rayuwarsu……"
《《《《《》》》》》
"Abdul maleek zo nan " ta fada tana ya fitoshi da hannu
Ba musu ya matso yana kallon fuskarta " Waya baka Apple wrist din hannunka ……"
Dariya ta subuce mashi yana kallonta kasa kasa sam ya manta bai canza kaya ba da zai taho hannunshi ya murza a hankali still fuskarshi dauke da murmushi ,shi kam mamakinta yake kamar wani barawo "Maleek bana son wannan halin da ka fara dauka jibi shaddar dake jikinta ……ina kake samun kudi cikin kwanakinnan ?ka tsaya matsayinka Maleek karka ce zakayi abunda ya fi karfinka ……"
"Karfin hali ……wae sata a lahira "ya fada a ranshi
Dagowa yayi tare da kafeta da ido yana kara jujjuya maganganunta a ranshi ,cikin sanyin murya yace "Madam oga ne ya bani 100k wannan month din……"
"Sae ka rasa abunda zaka saya Maleek sae wannan ?shin babu wanda zaka taimaka mawa a rayuwarka ……Maleek kasan marayu nawane abinci ya gagaresu a yau kadan amma Maleek ka cire 40K sa sayi wrist…kayi tunani Maleek kafin ka aikata abu ……"
Maganganunta sun ratsashi sossae yafi karfin minti Goma yana kalllonta yayin da ta dukar da kai tana danna wayarta ,Sae da ta dago sannan ta lura da yarda yake ……mikewa tayi tsam ta bar gurin ta koma can nesa dashi ta zauna ……
*FEEDOHM💞*
[4:45AM, 10/26/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
© *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM💞_*
*Devoted to Ummi A'isha👌🏻*
2⃣4⃣
Ranar monday Tunda safe Abdulmaleek ya fara ciku cikun yarda zaa soke lincense na aikin wannan lecturer din da Uncle Abba ,gurin CC aka fara turashi ,baisha wahala ba tunda yana da evidence a hannunshi ,nan take ya nuna masu ,sannan yaje court dinsu aka saka mashi hannu sannan ya sake dawowa office din CC din ,within 6 hours akayi cancelling lincense dinsu ma aiki suka koma dasu da wanda yayi secondary school bassu da maraba ……
Duk abunda yake sam safeena bata sani ba bare Abbanta da ko maganar bata fada mashi ba ……
Tana kwance gida maryam ta kirata lokacin ma suna waya da JB tayi holding taJB din ta dauki ta maryam din "Hello besty……
Cikin farinciki maryam din tace "am very happy besty anyi cancelling lincense na Bashir Mahmoud kuma ana rumour cewa a kan kiran da ya maki ne jiya besty……"
Uban tsalle tayi ta diro daga saman bed din ba tare da ta sani ba tace "How comes besty wallahi karya ne ba akan case dina bane sae dae wani abu daban gaskia……"
"Na rantse maki da Allah feena kan kiran da ya maki ne ,ke bama shi kadae ba harda Uncle Abbanki wallahi ni kaina am wonder tunda kince man nothing happen ……"
"Excuse kina ina yanzu?Let talk serious please……"
"Wallahi besty ki……"
Katse tayi tana fadin "Nay answer me……"
"Ina school Feena……"
Cikin sauri ta dauki hijab ta saka ta dauki wayarta Napep ta tsaida ta hau ba tare da ta kira Maleek ba ,inda suke zama ta iske maryam din ba tare da ta bari ko,zama tayi ba ta kama kafadar maryam din tana fadin"That are so fortifd against your story besty ……How comes please let once again assl my ears besty ……"
"Kai besty sit down awhile mana wallahi ni kaina i might not believe without the srnsible and true avouch of mine own eyes ……"
Ahankali ta zauna tana dafe kai ,"Sam ban san yarda hakan ta faru ba besty wallahi ba da sanina akayi cancelling lincense dinsu ba ……To waye yayi haka besty wallahi na rude who did this ……"
Cikin Sanyin jiki tace "Amma Feena baki tunanin Abba ne ?beside ma did he do anything bad to you besty……?
"No ba Abbana bane wallahi,……"
"To wa kika san ya san ya kiraki think……"
"Only you ,Granny and Maleek nawa forwading yarda mukayi ,kuma ke kanki maryam baki san na turo maki ba sae da na dawo na karbi phone dinki nayi deleting text din ,true talk besty Lecturer din ya nemeni da iskanci amma Nayi excping Maryam……"
"To bakya tunanin Maleek ne ……"
Harara ta sake mata tace "Driverna fa ina ya san hanyar da zaiyi cancelling lincense din wani ,beside ma bai san na tura mashi ba ……"
Suna tsaye a gurin Bashir din yazo a rude kamar ya fasa ihu yana tambayarta me yasa ta mashi haka ,rokonta ya fara tayi hakuri ,yayi bala'in bata tausayi cikin sanyin murya tace "Wallahi Sir banda masaniya akan wannan abun ,babu yarda zaayi na saka ayi maka haka kai dan,adam ne ban san iya mutanen dake rayuwa a karkashinka ba yi maka haka na nufin durkushe duk wanda ke rayuwa a kasanka ……" hakuri ta cigaba da bashi kamar zatayi masa kuka ……
Tana barin gurin ta tafi gidan granny ta fada mata duk abunda ke faruwa ,Ita kanta mamaki abun yake bata ce ma Feenar tayi ta kira mata Maleek yanzu ……
Mintina kadan ya isketa a gidan ,da fara'arshi ya gaida granny yana satar kallon Feenar dake aikin danna wayarta kamar bata san da zuwanshi ba ……
Dagowa tayi ta sake mashi harara ganin yana satar kallonta "Kabar kallona da dullos eyes dinka Maleek……"
Murmushi yayi mai fitar da sauti yana kallon granny da ta tallabe kunci tana kallonta "Idan bakyaso a kalleki ki shiga cikk mana ……"granny tace
Dan turo baki tayi ta jan kallabinta tana fadin "Wallahi granny har da ke kesawa Maleek dinnan yana kara raina ni ……"ta karashe maganar tare da shigewa dakin
《《《》》》
Sauran sati daya bikin Safeena hajiyar su Aunty fatee ta kira Abban Safeena tace lallae ya turota meeting gobe da safe ……Ce mata yayi Allah ya kaimu goben insha Allah zata zo ……
Safeenar ya sama dakinta ita da su maryam lokacin suka dawo daga rabon IV ya fada mata cewa gobe taje gidan hajiya zaayi meeting sannan baya son yaji wani abu ya biyo baya ,sossae ya mata kashedi sannin halinta ya tabbata idan taje komae na iya faruwa ……
Fuska ta bata tana fadin "Abba to wa zai kaini ……"
"Ki kira Abdul Maleek mana ……"
Rau tayi da ido kamar zata fasa kuka tace "Abba two days numbershi batta shiga …Abba ka kirashi ko baya lafiya ne please kaji ………"
"to meye na bata fuska kuma ……ance maki baya lafiya ?zan kiranshi zuwa gobe ……" ya fada yana kallonta
*FEEDOHM💞*
[4:30PM, 10/27/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
*_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM💞_*
*Devoted to Ummi A'isha👌🏻*
2⃣5⃣
A hankali ta lumshe ido tana goge kananan kwallar da suka zubo mata ……photonshi ke yawo a brain dinta sam batayi tunanin zatayi kewarshi haka ba ……�
Wayarta ta dauka ta kurawa ido kamar tana karantar wani abu sannan ta saka hannu a hankali tana danna number shi ,batayi zaton ta riketa a kai ba in ba yanzu ba ……har ta gama ringing bai dauka ba ,wani dan karamin tsoki ta sake tare da saka bayan hannunta tana share kwallah da suka zubo mata …… Wahale tajuyo tana kallon maryam dake rike da wayarta tana latsawa ,zatayi magana kiranshi ya shigo mata……�
Sanyayyar Ajiyar zuciya ta sake tana kokarin maida murmushin dake niyar kwace mata ,kamar mai tsoron wani abu ta kanga wayar a kunnenta ……�
Hadaddiyar muryarshi taji cikin sanyi yana mata sallama ……�
Rufe ido tayi sannan ta amsa sallamar tana fadin "Abdul Maleek……�"
Rufe ido yayi da sauri sannan ya bude ba tare da ya amsa ba, kusan minti biyar sannan yace " i'm sick at heart madam……�"yayi maganar kasan makoshi
"Wat's wrong Maleek have you had quite Tis ……�"ta fada a hankali
"Bana da maganinshi Madam just pray for me ……�"
Yar kwallan dake idonta ya gangaro "Maleek kaje asibiti a duba ka man please babu ciwon da baya da magani bare na zuciya ……�"
"Not so madam ,i'm too much in the sun ……"Ya fada a hankaki yana dafe da goshinshi ……�
"Please Ab……�"
katse ta yayi "Nay Madam Nagode da kulawa ina maki fatan alkhairi a rayuwar aurenki ……"katse wayar yayi tare da dafe kanshi da ya dake bala'in juya mashi kamar an tsikareshi ya fara hada kayanshi cikin wata karamar jikkar sannan ya fito ya shiga mota ,gidansu Safeena yaje ya shigar da motar sannan ya dauki jikkarshi a hannu tare da mikawa maigadin keys din motar yace ya bawa Madam da safe da wani karamin kit ……�
Tasha ya nufa direct motar zaria ya nema duk da lokacin dare ne hakan bai hanashi samun motar ba ……�
Safeena naji ya datse wayar ta sake kuka a hankali tare da fadawa cinyar maryam din ,dan bubbuga bayanta maryam din take tare da fadin "Sorry……" jin ta fara shirune ya saka maryam din cewa "You love him Feenat ……�"
Cikin tsawa tace "No I don't love him……he's just my driver nd he's such a kind and humble to me i really missed him……�"
Dan girgiza kai maryam din tayi a hankali don sam bata yarda cewa feena din ba din ba son Maleek din take ba……�
《《《》》》�
Kamar yarda Abba ya fada mata tunda safe ta shirya cikin riga da zani na atamparta ko kwalliya batayi ba don daga meeting din gidansu maryam zata wuce a can zaayi komai zuwa dare a daukesu akaisu tourist lounge inda zaayi friend's day ……�
Tana shiga harabar gidan sae da gabanta ya fada a hankali taja kafarta ta karasa falon da ake meeting din ,kowa ya hallara ita kadae ce babu gefen iyaye daban haka gefensu na jikoki daban ,su fadila ta kallah ko wace tasha kunu kamar basu taba dariya ba ……tabe baki tayi tana Spreading arms dinta sannan ta matsa ta zauna a kujeran da babu kowa a sama ……�
Tabe baki ta kuma yi jin uncle Abbah ya bude taro da addu'a tana fadin "Sabon salo ……�"
Kamar jira Aunty zuby take ta wani nunota da hannu tana fadin "ki shiga hankalinki Fenna meye sabon salo a ciki � addu'arce baki saba ji ba a bakinshi koko me ciki……�"
Cikin dakewa ta watsa mata harara tare da fadin "Ko addu'ar nace ban saba ji ba a bakinshi laifine ……"
"Watch ur word's wallahi dama meeting dinnan don ke akayishi sakaran banza mara kunya ……�" cewar Aunty Bilky dake harde kusa da hajiya
Tabe baki ta kuma yi tare da sakin dan tsoki tunowa da kashedin da Abbanta ya mata jiya daddare ……�
Aunty Zuby tace "Zaki iya fada mana dalilinki na zuwa har cikin gida kiyiwa hajiya rashi kunya Safeena ……�"
Ido ta fito waje tana fadin "Me tace na mata ……�"
"Kin Fi kowa sanin zagin da kika mata mara kunyar banza……�"cewar Uncle Abbah
" Baran ce ban zageta ba tunda ta riga ta fada sae dae nan gaba idan Abbah ya kuma shiga harkana to har gidan zan kuma zuwa na zageta har da wanda tace na mata yanzu zan hada mata ……�" ta fada ba tare da wani shakku ba a fuskarta
Cikin sanyin muryar munafukai Aunty fatee tace "Amma Safeena kin kyauta sabida Allah komai Abbah ya maki ai kawunki ne tsakaninku bai kamata ki huce kan Hajiyarmu ba ,ko ba komae ai kakarki ce kema……�"
Dariyar shakiyyanci ta saki tana kallonsu daya bayan daya ba tare da tace komae ba ji tayi Uncle Abbah na fadin "Kuma dan Uwar yarinyar nan ……�"
"Dallah dakata malan karka kuma zagar man uwa wallahi duk abinda zaku fada zan jure amma banda zagin uwata ……�"ta katse mashi magana tana nunashi da hannu
Aunty Zuby ta taso tana fadin "An zageta din dan Ubanki wato ke Safeena baraki taba girmama mu ba a matsayin yan uwan uwarki ba ko ……�"
"Me kuka taba mata Aunty Zuby ……" ta fada tare da kafesu da ido daya bayan daya
Hajiya kam ko kala bata ce tun da suke maganganunsu sae yanzu da ta dago da niyar magana Aunty bilki ta tsayar da ita da hannu tana fadin "Barmu da ita hajiya Zaki biyamu ne abunda muka maki ke da uwar taki ……"
A Harzuke tace "Yeah uwar me kuka mamana a rayuwar banda cuta da zalunci shi kuke so na ramata? no wannan na barku da Allah amma ni wanda kuka man zan iya biyanku na tabbata ku duka baku wuce ku ce kun sayi rigar 1500 ba kun bani well ga kudinku "ta bude jikka ta ciro rapper ta 500 ta zube saman hannun kujeran da take zaune sannan ta cigaba da fadin
"ke kuma Aunty fatee bai wuce kice kin man wahala ba wanda nasan karya kike da wayauna na dawo gurinki ,zan iya rantsewa sau daya kika taba man wanka kika wanke man kashi sannan kika goya yar uwata……idan kina bukata ki dauko zani kizo na rama maki goyonki sannan kiyi kashi kiga idan ban wanke maki ba ……�"
Bata Saurari kowa ba ta mike zata fita ,jin lema a zaninta ya sata kallon kujeran da ta zauna da sauri ,gabanta ya fadi ganin gurin yayi staining da yawa a tunaninta two week's kenan da gama period dinta ……�
Dakewa tayi tare da sake masu harara tayi hanyar fita ,ji tayi su duka sun dauki shewa tare da tabawa ……�
Tajuyo a fusace tana fadin "Cikin ku babu dan iskan da baya menstruation so i don't care idan nayi staining a gabanku……then kadan dan iskan da ya kara kirana da sunan diyarshi da na fita daga wannan gidan yau……"
Tana jinsu suka sake kwashewa da dariya Fadila na fadin "Dama uban wa zai kiraki da diyarshi a haka ……"
Bata kulasu ba ta fice daga gidan makwabtan gidan ta shiga da yake suna gaisawa da budurwar gidan ……Pad ta bata tare da sabon pant ta yi wanka ta canza ,kafin ma ta fito wankan har ta sa washing machine ta wanke mata zanin sannan ta sakashi a dryer ya bushe ta bata ta maida ……�
*FEEDOHM💞*
[8:33AM, 10/28/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
© *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM💞_*
*Devoted to Ummi A'isha👌🏻*
*Bestowed to Aunty Sis💕*
_Assalamu Alaikum Dan girman Allah kar warda ta sake bina pc tace na bata book daga farko ,wallahi na gaji sam baran iya ba binku ina baku ba ,shi kanshi copying 20 tis ba abu bane mai sauki ,sannan tun daga farko na fara posting dinshi ban tsallake ko da one page ba a duk groups din da nake sae kuma nayi nisa a dinga saka man wani sabon aiki to gaskia baran iya ba…… idan kina so sae anyi nisa sannan ki fara bin book to kamata yayi kiyi starred dinshi ……kar ki man magana naki tura maki kiga kamar wulakancine baran iya bane gaskia 🤒🤒_
2⃣6⃣
Party sossae akayi na kece raini amma sam hankalin amaryar baya jikinta wajen 10pm aka gama partyn ……Safeena kin shiga tayi motar JB din duk nacin shi sae dae ya hakura Maryam ta tafi da ita ……
"Feena wae lafiya kike ?ki zauna sossae man……" Maryam fada tana kallonta
Girgiza kai tayi a hankali tana matse idonta ba tare da tace komae ba ……
Kamo hannunta Maryam din tayi tare da damkewa cikin nata "Feenat me ne……?
"Am totally comfortless Maryam ……"Ta fada tana kallon window
"Fada man mene Feenat ……" Ta sausauta murya tare da kamo hannunta
"Ki kaini gidan granny please ina son magana da ita yanzu ……"ta karashe maganar tare da mikewa daga kujeran motar da sauri har tana bigewa ……
Shiru maryam tayi ganin idonta ya kawo ruwa kadan ya rage ta sakar mata kuka………dafe gefen cikinta da ke murda mata da karfi tayi ta kwantar da kanta saman cinyoyinta……
Kofar gidan granny din tayi parking ta fito tare da zagayowa ta bude gefen da Feena din take tana kallon yarda take ta uwar zufa duk da sanyin motar ……
Dafa bayanta tayi tare da dukar da kanta tana fadin "Sorry besty mun iso ……"
A wahale ta dago sannan ta mayar da kanta ta kife a saman cinyarta tana cije upper lip dinta da karfi , tafi kusan minti biyar sannan ta sauko da fararen kafafuwanta da ke sanye da hills red kasa ……a dafe ta fito daga motar tana dafa Maryam ,sae da ta gama saukowa gaba daya sannan ta juya tana kallon inda ta zauna lokaci guda ta kalli Maryam tana share hawaye da bayan hannunta na dama……
Dan murmushi maryam ta sake tana girgiza mata kai a hankali "I'll clean……" ta fada tare da kama hannunta ta rufe marfin motar suka shiga gidan Granny din ……
Maryam nayin Sallama granny ta amsa tana fadin "A'a kaga yan albarka Haba shi yasa tun dazu nake jin kamshin amare Allah yasa kayan partyn nima aka kawo man ……"
Karasa sukayi falon maryam na fadin "Wani kayan party zaa kawo maki granny? to ki ci su da wanne hakora ……"
Yar dariya granny ta yi tare da rufe fridge din ta juyo tana kallonsu ,lokaci guda ta zubawa Feena ido tana fadin "Lafiya kike rike ciki Safeena ……"
Bisa doguwar kujera maryam ta daurata ,tayi saurin zamewa tana kallon ta tare da sake kuka ……
Idanuwan Maryam itama suka kawo kwallah tana fadin "kar ki kwanta a kasa Feena ……"
"Maryam so kike na bata mata kujeru?ki barni a nan tun dazu nake saki aiki Maryam……"ta karashe maganar cikin kuka
"Nace maki baran gyara bane Feena?ko nace maki na gaji ne? karki kwanta a tiles akwae sanyi besty……"ta fada murya na rawa
Granny ta matso tana fadin "Me ke faruwane Maryam?bata lafiya ne?husaina menene……?
Wani kuka ta sake mai ban tausayi maryam ta zame jikinta tare da rungumeta tana fadin " granny period take kuma cikinta na mata ciwo sossae shine tun dazu take kuka……please ki mata magana ta bar kukan……"
Dan Karamin tsaki grannyn ta sake tana fadin "Ban san shashancin banza ,ta ci gaba da kukan mana dan kaniyarta ……dallah ku tashi ku bani guri ……kai wallahi ku zo ku fice man daga gida ma tun kafin na sab'a maku……" ta karashe maganar tana nuna masu kofa
"Granny cikinta ke ciwo fa sossae ……"cewar maryam
"Wallahi zan ci mutuncinku baki daya…… ciwon cikin ne bak'on abu gurinku ko ko me a ciki?Don iskanci sae ku sani gaba da kuka akan Abunda ya zama dole kuyi kuma ku ke yi duk month……Maryam ki jata ku barman falo ko naci mutuncinku ja'irai kawae ……"
Kuka Safeena ta sake tana fadin "Granny ba normal jini bane da na saba yi ……"
A dan fusace ta jiyo tana watsa masu harara "Die normal ne dan gidanku?wallahi maryam zanci mutuncinki ke da kika kawo man ita ……"
Mikewa Maryam tayi tare da kama hannun Feena tana fadin "Besty sorry kin ji ko…… tashi muje daki na hada maki ruwan wanka ki canza kaya wadannan sunyi staining da yawa ……" Mikewa tayi a hankali tana cije lips dinta na kasa tare da dafa Maryam ……a Tare suka kalli inda ta zauna su duka ukkun sam ba kalan jini bane gurin yayi powly black kamar charcoal ……
"Safeena ,Maryam me ye haka ku ka kwaso man a falo ……?cewar granny tana bin gurin da kallon mamaki
Cikin rawar murya maryam tace "granny tun dazu menstruation din Safeena ya koma haka ,granny ban taba ganin haka ba a rayuwana…… please dama yana komawa black?
Shiru tayi kamar tana tuna wani abu ,lokaci guda ta nufi Safeena tare da sa hannu ta juyota tana kallonta "Safeena da karfi da zafi kike jin menstrual din yana fita ko? ta tambaya duk ta rude
Gyada kai tayi a hankali tana kallonta ba tare da ta amsa ba ……Rufe ido granny tayi gam tana nuna masu su shiga daki kawae ,haka maryam ta riketa har bakin gado ta zaunar da ita har lokacin idonta na rufe ta dafe gefen cikinta "Sorry Feenat you'll be ok kinji ko besty……"abinda ta fada kenan sannan ta shiga toilet ta hada mata ruwan zafi sannan ta dawo ta kamata ta shiga da ita ……Dan bakin gadon da ta zauna ma har yayi stain,yaye bedsheet din tayi tare da lekawa falo zata tambayi granny din ko tana da katuwar leda ta shimfidawa Safeenar sannan sae ta saka mata bedsheet gudun kar matress din tayi staining ,hango Granny tayi inda suka barta tsaye kamar an dasa ta ……Jikinta ya kara yim sanyi ta matsa a hankali tana fadin "Granny ko kina da babbar leda irin ta cikin buhun sugar haka ……?
Juyowa tayi ta kalli Maryam din tare da girgiza mata kai tana fadin "Maryam tun yaushe Safeena ta fara wannan abun?
"Granny bayan ta dawo daga gidansu Aunty Fatee meeting tace man ta fara ,kuma ta fada man duka two weeks kenan da ta gama normal period dinta ……shin dama ana irin haka granny she's too unwellfull am scared na rasata ,wallahi tun dazu take kuka ko zamu kaita asibiti ne?tunda da motan mu ka zo ……"
Wayar Safeena ce ta fara ringing Maryam ta dauko ganin My Future husby ya sata gane JB ne ta daga cikin sanyin murya tare da sallama
"Maryam ina Feenat din ……?ya fada jin ba muryar ta bace
"She's too unwell JB ta samu bacci ne ……"
"Me ke samunta Maryam?kuna ina yanzu ?i wanna see her please……"ya fada a rude
Kallon granny tayi sannan tace "don't mind ta samu sauki har ma tayi bacci zuwa da safe kunyi magana ……"
"Please kuna ina?
"Dutsin safe gidan granny JB please ba sae kazo ba tayi bacci wallahi ……"
Ba dan yaso ba ya hakura yace da safe zaizo ya ganta sannan ta aje wayar ta shiga kitchen ta hado mata coffee ta dawo ta wuce granny har lokacin tana tsaye ……Da kyar ta samu tasha coffee din sannan ta gyara mata inda zata kwanta ,sae da ta tabbatar ta kwanta sannan ta dawo falo gurin granny ta zauna tare da fito da wayarta ta kira Mamanta ta fada mata tana gidan grannyn besty acan zasu kwana
《》《》《》《》
A Hankali yake juyi ci kadae bisa madaidaicin gadonshi zufa ko ta ina ke yanko mashi mummunan mafarki yake akan wata kyakykyawar yarinyar dake ta gudu cikin daji tana kuka ,bayanta wasu irin mugayen halittu ke binta a guje ,dae dae wani katon rami kafarta ta daki wani dutsi ta fadi kasa ,gangarawa ta farayi zata fada cikin katon ramin yayi saurin damko hannunta ya rufeta da kirjinshi ……mugayen halittun dake binta suka zo suka wuce ba tare da sun lura da su ba ……yana ganin sun wuce ya dago fuskarta tare da yaye gashin da ya lullubeta mata fuska yana kallonta ……
A firgice ya farka yana kiran "Nana ……" tare da karewa duka dakin kallo ganin rana ta fara shigowa ta windown dakin ya sashi mikewa da sauri tare da leka window, calender dake manne jikin bango ya kalla tare da dafe kanshi ya juya baya "I failed……"hawaye suka gangaro mashi a hankali saman chicks dinshi
0 comments:
Post a Comment