Karar shigowar message ya sakashi dube wayar yana budawa new number ce …… _" The more u go away from me,I'll closer forward my self to you.……I May not say any word only my heart will tell you're special Abdul Maleek ……"_
Tabe baki yayi ya mayar da wayar ya aje tare da aje spoon din ya kife kanshi…… hawaye yaji suna neman zubo mashi a fuska "I failed ……I Love you Safeena you're my life i can't asse without you Madam please don't neglect me Safeena Wallahi na fi kowa kaunarki *ZAN RAYU DAKE* Safeenah……" Bayanshi yaji an dafa ya dago da sauri yana share hawayenshi wata yar budurwar yaren igala ya gani ta kura mashi ido ……
Bata fuska yayi tare da sake mata harara yana fadin "What……?
Ganin ba wasa a fuskarshi ya sata juyar da kai sau biyu tana smiling ……"Cutie……"ta fada a hankali ……
Karamin tsaki ya sake ya mike ba tare da ya kara bin ta kanta ba ……ji yayi zaria gaba daya ta isheshi bare ma mafalkin da yayi masifar daga mashi hankali ……
Girgiza kai yayi baya jin zaya iya komawa garin a daurawa Safeena aure yana garin …better ya bari zuwa monday ya koma lokacin ya tabbatar da ya rigaya ya rasa Madam ……Tafiya yake amma sam hankalinshi baa jikinshi yake ba ……mai motar da ke ta mashi horn ya tsaya tare da fitowa yana bala'i ……wanda yake yin bala'in donshi sam bai ma san anayi ba ……
《》《》《》《》
Ranar Saturday da safe granny ta saka aka kira mata Abban Safeena cikin mintina kadan ya iso a falo suka zauna bayan sun gaisa tace "Safeena bata jin dadi ko za'awa iyayen mijin magana a daga bikin zuwa ta samu sauki ……"
A rude yace "Me ke damunta Umma?
Iyakar abunda take iya fada mashi ta mashi bayani ,shi kanshi sae da jikinshi yayi sanyi ya kalleta a sanyaye yace "Umma ina Safeena ……?
"Tana daki tare da Maryam ,na karbo mata wani magani dazu gurin malan habibu nan makwabtanmu kafin mu gama magana naje daura ……"
Numfashi yaja a hankali sannan yace "Idan d'aga bikin ne mafita Umma a kira angon sae a gaya mashi su hakura zuwa lokacin da zata samu sauki ……"
"Gaskia kam dan duk yarda kake tunanin abun ta wuce nan don wallahi yau yadda kasan icce haka take komae Maryam ke mata nan da can ta kasa matsawa saboda azabar ciwon ciki ……garama yanzu naga maryam din ta kamata sun shiga toilet tayo wanka ……"
Maryam ta fito rike da plate zata kai kitchen har kasa ta duka tana fadin "Abba ina kwana ……"
"Lafiya lau Maryama ya jikin Safeena?
Rau rau tayi da ido tana fadin "Ba sauki Wallahi Abba……"
Mikewa yayi jikinshi na rawa ya shiga dakin ,akwance ya isketa tana kallon sama ,juyowa tayi tana kallonshi hawayen dake makale a idonta suka gangaro lokaci guda ta sake murmushi tana fadin "Abba……me yasa?Abbana mutuwa zanyi,wallahi cikina kamar zaya kone Abbah dan Allah ka man addu'a na samu sauki ……"
Da sauri ya matsa tare da riko mata duka hannuwanta yana girgiza mata kai "ki dauki kaddara kinji Safeena ,bara ki mutu ba insha Allahu zaki samu sauki kinji ko ……ba ciwon ciki kawae bane ……"
Kuka ta sake tana fadin "Abba kawae ne?jibi Abbah ……"ta fada tana kokarin mirginawa ta sauka daga shinfidar da Maryam ta mata ……
Dafe kai yayi ganin gurin kamar wacce ta haihu yanzu, sannan yayi powly black sossae "Karki damu kinji ko ……Allah yana ganinki insha Allahu zuwa ranar monday zan nema maki visa a kaiki india indae bai tsaya ba ……"
Gyada kai tayi a hankali tana share hawayen "Abba bana son auren kacewa JB ya hakura Abbana sae na warke ……"
"Daina kuka mana ,ko so kike ki karyawa Abbanki zuciya Safeena?bara na kirashi sae a bashi hakuri ……"ya karashe maganar tare da lalubo wayarshi ya kira JB din yace ya sameshi nan dutsin safe yana son magana dashi yanzu ……
Cikin mintina kadan ya iso ,a harabar gidan yaga maryam a rude yake tambayarta ya jikin Feena……
"Da sauki "ta fada tana rufe window din dakin granny sannan ta mashi jagora zuwa cikin falon granny ……
Cikin Fahimta Abba ya mashi bayanin halin da ake ciki tare da bashi hakuri a dage bikin zuwa ta samu sauki ……
A rude ya fara fadin "A'a Abba dan Allah kar a daga mana biki ,ka taimaka man ka bari a daura auren yau wallahi ,ko ya Feena take zan iya rayuwa da ita na rokeka Abbah dan girman Allah ……"
"Ka kwantar da hankalinka Jabir bawae baran aura maka Safeena bane a'a wallahi kawae ina sone na sama mata magani zuwa wani lokaci sae ayi auren kaga ko a musulunci bai kamata a baka auren yarinya ba tana dauke da lalura ……"
Hawaye ya fara bi mashi fuska yana fadin"Wallahi Abba na yarda zan zauna da ita a haka dan Allah ka barni da ita ……"
Duk yarda Abba yaso ya fahimceshi a fasa auren kin yarda yayi ,Granny tace a barshi kawae a daura auren tunda yace ya yarda "Allah ya alkhairi……" addu'a kam ya shata gurin Abba don ba karamin dadi yaji ba shi kanshi yasan idan aka fasa wannan auren ba karamin bakin ciki zai shiga ba ……ya kuma kara tabbatarwa da JB zai rike mashi Safeena da kyau ……
Dakin da Safeena ke kwance ya shiga ,tana ganinshi ta mike da kyar zaune tana cije lips ……sam bata bakin ciki idan an fasa auren ko kadan saboda ta san babu namijin da zai zauna da ita da wannan kazantar ,daga jiya zuwa yau tayi amfani da pad yafi 50 amma a banza duk inda ta zauna sai gurin yayi staining ……
Rungumeta yayi sossae yana fadin "Feena kina jin Abba na fadin wae a fasa aurenmu?
Da murmushin yake a fuskarta ta janye jikinta tana fadin "To meye JB hakan shine dai dai saboda ina dauke da lalular da babu wani namijin da zai zauna dani ko da minti biyar ne ……"
"Sae ni Safeena wallahi *ZAN RAYU DAKE* A duk halin da kike ……na bawa Abba hakuri ya bar man ke kar a daga bikin kuma ya yarda ……Safeena indae har aka fasa bikinnan son da nake maki karyane wallahi ……ki sa a ranki ni JB *ZAN RAYU DAKE* Ko da lalurar dake jikinki ta linka wannan sau dubu ……Ina sonki Feena soyayya ta gaskia wacce babu algusur a cikinta ki yarda dani……"
Wani kuka ta sake tare da kifa kanta a cinyarshi ……ta rigaya ta yarda cewa Jabir na mata wani irin so wae wuyar fahimta ……
Karfe 12:30pm aka daura auren Safeena Khaleed da Jabir ……daurin auren da ya samu halatta dumbin mutane daga sassa na duniya……
*FEEDOHM💞*
[4:39AM, 10/30/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
© *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM💞_*
*Devoted to Ummi A'isha👌🏻*
*Bestowed to Aunty Sis💕*
2⃣8⃣
_I'll write this in bolc *DUK SHEGEN DA YA KARA KARBAR KUDI AKAN YA TURA LITTAFINA ALLAH YA ISA BAN YAFE MASHI* to you reader duk wacce ta sake bayar da kudi aka tura mata littafina ta karanta Allah ya isa wutar jahannama bal bal🔥🔥 banyi littafina don kudi ba don haka kar wani shege ya kara mayar man da littafi na kudi shegu munafukai suna amfani da basirar wasu suna kasuwanci😡_
"Haba Jabir duka nawa kake da zaka yarda da auren mace da lalura a jikinta……" Mum ta fada a harzuke
Bata fuska yayi sossae yana fadin "Mum nace ki taimaka man ne ……ni ne fa nace na yarda kuma ni zanyi mata komae then meye damuwarku akai ……?
Kwantar da Murya tayi sanin halin dan nata tace " Amma son yarda dad dinka ya man bayani bara ka iya ba……"
"Look mum baki son soyayya bane?ko ba auren so kukayi da dad ba……i can do anything akan Feenatah karku saman ciwon kai please ……"
"Ni dae……"
"Ki saketa idan ke kika aura man ita ……" ya fada tare da mikewa ya shige daki ya barta zaune , binshi tayi tana fadin"yi hakuri son wallahi na yarda kazo ka zauna kaci abinci……"
"Baran ci ba……" ya fada kai tsaye
《》《》《》《》
Su Aunty fatee kam hadadden biki suka shirya na gani da fada duk family da abokan arziki an hadu sae raha ake Inna ce ta kalli Aunty Fatee tane fadin "Fateema ni kam ina diyar taki ? tunda nazo ban ganta ba ……"
Murmushi tayi tana fadin "Safeena amarya…… kinga nima inna tun jiya nake kiran wayarta a kashe amma bara na kira maryam nasan suna tare……"
Cikin jin dadi inna tace "Kira man yar kusuwa kunya ta hanata shigowa ……"
Dariya Aunty fatee tayi tana kiran number maryam ,ringing daya ta dauka tare da sallama ,handsfree ta saka tana fadin "Maryam ina kika kai man diyata duk yau ban ganta ba……"
A Raunane tace "Muna gidan granny aunty fatee ……bata jin dadi Abba bai maki bayani ba……"
Dafe kirji tayi tana fadin "Subhanallah me ya sameta?
Zatayi magana Aunty fatee tace "Ina zuwa maryam ga Abbanta nan naji ya shigo bara naje na sameshi ……" ta katse kiran ta nufi gurin Abban A rude a tare suka shiga part dinshi ko zama baiyi ba tasha gabanshi idonta cike da hawaye tana fadin"Alhaji meke samun diyata? dan Allah ka fada man me ke faruwa da Safeena tun jiya banganta ba yanzu kuma na kira maryam tace bata lafiya……meke faruwane?
Rufe ido yayi yana kallonta duk ta birkice jin cewa Safeena batta lafiya tausayinta ya kamashi sossae a hankali ya zaunar da ita gefen gadonshi sannan ya zauna yana fadin "Ki kwantar da hankalinki Fateema Insha Allahu zata samu sauki ……matsalarku ta mata ce to sae ta zo mata da wani irin yanayi ni kaina hankali ya tashi saboda hakan ma yasa ko asibitin nan bai kaita ba zuwa monday idan abun bai tsaya ba sae na fitar da ita india zata samu kulawa sossae……"
Cikin kuka tace "Meye abun mata alhaji dan Allah ka man bayani sossae ……"
Cikin natsuwa ya mata bayanin jinin dake fita daga Safeena da irin yanayin da yazo mata har sae da ya kai aya sannan ya ja numfashi lokaci guda idanuwanshi suka canza yace "Fateema irin yanayin da Aisha ta shiga shine Safeena ta shiga……"
"Na shiga uku Yanzu abunda ya samu Aisha shi ke shirin samun Safeenata ……Wayyo Allah wannan wace irin rayuwace muke ciki Ya Allah ka tausaya man ka bawa diyata lafiya wallahi itace haskena ……"ta karashe maganar cikin kuka sossae
Ganin ta fishi shiga tashin hankali ya sashi lallashin tashi zuciyar ya fara lallashinta tare da bata hakuri ta dauki kaddara ,da kyar ya samu ta yi shiru sannan ta mike tana fadin "……Ya Allah ka daukewa diyata wannan ciwon ka dawo dashi kaina……"
"Kul Fateema ki daina wannan addu'ar mana kiyi addu'ar Allah ya yaye mata itama ……"
"Ya zanyi Alhaji wallahi da Safeena ta zauna da wannan ciwon kara ni,na zauna dashi ……Dan Allah kama izni naje na gano diyata yanzu wallahi baran iya kara minti goma ba ba tare da na ganta ba ……"
Lumshe ido yayi tare da gyada mata kai a hankali yana sakar mata wani irin kallo ……kalamanta sun tabbatar mashi da Fatee na son Diyarshi har ga Allah wani girma na musamman ya kara mata a zuciyarshi……
Dakinta ta shiga ta iske Aunty Zuby na tattara kayan da yan bikin suka zubar ,Aunty zubyn ta kalleta tana fadin "Ke kuma daga ina idonki yayi ja kamar an maki duka……"
Tabe baki tayi tana fadin" Wannan shegiyar yarinyarce Abbanta yake fada man bata lafiya shine na sake mashi kuka farin ciki dan banyi asarar kudina ba ……shi kuma sae ya shige sossae yana wani jin dadi ina son diyarshi ……"
Dariya ta sake tana fadin "Amma baki da dama wato kukan farin cikin bakiyi asarar kudinki kike ba ko ……?
"To Zuby na bakinciki zanyi ……?
Harara ta sake mata tana fadin "Da banci ubanki ba ……yanzu angon ya sani koko?
Tabe baki tayi tace " Yace man an fada mashi JB dinma ya dage sae an daura auren ya yarda ……kinga bara naje na gano shegiyar don nace mashi yanzu zanje ……"
Dariya ta sake tana fadin "Allah ya kara zafin ciwo……"
Da "Ameen " ta amsa ta fita tana dariyar mugunta
A falo ta iske granny zaune tana shan kunun tsamiya da alama daga makwabta aka kawo mata shi har kasa ta duka ta gaida ita tare da zama kasan carpet tana kallon kasa ……
Wulakantaccen kallo Granny ta watsa mata tana fadin "Su Fateema ne? Hala kunji labarin Safeena batta lafiya? ta fadi maganar da zance biyu
A hankali ta ja majina tana share hawayen da suka zubo mata tace "Eh wallahi Hajiya yanzu ma Abbanta ke fada man shine nazo na ganta ……"
Ita kam kukan ma dariya ya bata ……ta saki dariya irin ta manya tare da rike haba tana fadin"Ikon Allah har da kuka Fateema……"
Salon kukan ta canja tana fadin "Ba dole ba inyi kuka hajiya ……ki duba fa yarinya sae da aurenta yazo ace jini ya balle mata kuma na cuta haba dan Allah ai abun da tausayi ……"
Yar siririyar dariya ta kara saki tana fadin "To fa ……ki shiga suna daga ciki ……"
Mikewa tayi da sauri ta fada dakin tana goge hawaye
*FEEDOHM💞*
[5:39AM, 11/1/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
© *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM💞_*
*Devoted to Ummi A'isha👌🏻*
*Bestowed to Aunty Sis💕*
2⃣9⃣
Safeena na jingine jikin gado maryam na mata fira kadan kadan suna dariya ……Shigowar Aunty Fatee ta batar da duk wani annurin dake fuskar Safeena kallo daya ta mata ta mayar da ldonta ta lumshe tare da zame hannunta daga na maryam
"Subhanallah Safeena garin ya haka ta faru kuma fisabillahi baki kirani kika fada man tsawon kwanakinnan……" cewar Aunty fatee tare da zama gefen gadon
Ko kala bata ce mata ba sae ma kwantar da kanta da tayi jikin gadon tana kokarin janye kafarta dake kusa da Aunty fatee ……
"Safeena ……" ta kara kiranta tare da kai hannu Ta riko hannunta
Da Sauri ta bude idonta tana watsa mata harara" Kar kuskura kiyi wasan ta bani wallahi……"
Kwantar da murya tayi "Safeena meye zafi duba ki fa nazo yi ,wallahi tunda naji bakya lafiya hankalina ya tashi ……"
Rufe ido tayi tana fadin "Aunty Fatee kenan ki bar duk wadannan jokes din ai'nt a kid wallahi ……Irin abunda ya samu mamina shi ya sameni ,Idan har ciwon da Mamina tayi kune sila to nawa waye sila?stop decieving your self please kawae ki tashi ki bar mana gida tun kafin na maki abunda bakiyi tunani ba……"
"Ki saurareni mana……"
"I said get out ko bakya da kaine?ta fada a tsawance, Jiki babu kwari ta tashi,ta fita tana waigenta Maryam dake zaune gefe ta kalli Safeena tana fadin "Amma bakya kyauta……"Shiru ta mata ba tare da tace komae ba
《》《》《》
"Wae Fadila waye kike kira haka tun dazu sae uban tsoki kike mana……"cewar hajiyarsu dake zaune tana yankan kumba
Tabe baki ta kuma yi tare da sake karamin tsaki tana yatsina fuska"Abdul Maleek ne wallahi tun da nake bai taba daga kirana ba sae dae na mashi text shima baya replying……"
"Amma ke sakara ce……Gafara can dallah ni bani numbershi shi din banza ya wahalar man da yar jika……"ta fada tare da mika hannu
"Hajiya me zakiyi da Number?ta fada da alamun mamaki
"Ke dae ki bani mana ,bani nace ba sannan ki kwantar da hankalinki Abdul Maleek kamar kin samu ne shi din banza……"
"ah Hajiya ki daina insulting dinshi mana……" ta fada tana turo baki ……rike baki hajiyar tayi tana mata wani irin kallo ……Spreading arms tayi tana fadin"Yeah ki daina Insulting nashi because I love him……"
"Lallae Fadila ……"cewar hajiyar tare da mikewa ta bar falon ……Fitowa ta kuma yi rataye da gyalenta da gani kasan tsofa yayi gardama gurin "hajiya sae kuma ina?cewar fadila da ta bita da kallon mamaki
Harara ta sakar mata tana fadin "Gurin tsalli zani na kai mashi wannan number tun kafin ki fara duka idan an zageshi ……"
"Ban gane ba Hajiyarmu……"
Gaba tayi tana fadin "idan na dawo kin gane……"
《》《》《》《》
Karfe 10:15 ya iso katsina kasancewar tun da safe ya iso ……Gabanshi ke masifar faduwa banda addu'a babu abunda ke fita daga bakinshi , da kyar yaje gida a bakin zaure ya iske inna sahu tana neman aike saboda duk su nana sun tafi makaranta ……karbar Aiken yayi ya sawo mata sannan ya dawo suka gaisa sama sam yana tambayarta "duk yaran na lafiya……" ta amsa da "Lafiya lau ……" kadan kadan suka taba hira duk hankalinshi baya jikinshi so yake ya kira ko Maryam ce yaji yarda suke amma ya kasa ya dauki wayar da niyyar ya kira ya fi sau biyar amma ya kasa ……
Sassayar ajiyar zuciya ya sake lokacin da yake mikewa ,kawae ya yanke yaje ya gaido Alhaji kila ya samu saukin radadin da zuciyarshi ke mashi ……
A Falo ya sami Aunty fateen zaune tana breakfast har kasa ya duka ya gaidata sannan ya tambayeta ko Alhajin nanan ……
Hankalinta ta maido kanshi sannan tace "Yana wanka Abdul Maleek ka jirashi dama ina son muyi magana da kai……"
Kanshi na kasa yace "Ina saurarenki Aunty Fatee……"
"Yauwa Abdul Maleek dama diyata Fadila ce ta dameni tana sonka kuma kaki kulata ko ta kiraka baka dauka shine nace ta bari na maka magana naji ……"
"Ita tace maki da bakinta tana sona?ya fada tare da dagowa yana kallonta
"Ita da kanta Mana Abdul Maleek ,kuma wallahi diyata ba mummuna bace idan kana so ma bari na kirata yanzu sae tazo ka ganta ,don tace man baka santa ba……"
Murmushi yayi mai fitar da sauti yana fadin "Am sorry to say baran iya soyayya da macen da ta zubar da kunyarta ta ya'ya mata da Allah ya mata tace tana son namiji……"
Shigowar Alhaji ce ta katse maganar ya mike da sauri yana mashi barka da fitowa ,ko zama baiyi ba ya nufi hanyar Fita yana fadin "Yauwa Abdul Maleek zo ka kaini tunda gaka kazo wallahi tun dazu Jabir ke man waya don shaf na manta jirgin marece zasu bi na dauka sae na dare ……"
Bin bayansa yayi yana fadin "to Alhaji……" a zahiri jin sunan jabir da yayi a bakin alhaji ya saka gabanshi yayi mummunar faduwa ……jiki a mace ya fitar da motar suka dau hanyar fita unguwar murya Alhaji yaji yana fadin "Dutsin safe zamuje mu dauko Safeenar Abdul Maleek sae mu samesu bakin round din dandagoro Kano zamuje ……"
Safeena……ya fada a ranshi kasa hakuri yayi ya juya yana kallon Alhajin a raunane yace "Wace Safeenar Alhaji ba tayi aure ba me ya kaita dutsin safe ko acan aka ajeta……"
"Tayi aure mana Abdul Maleeku ,Bata lafiyane shine zamu kaisu kano ita da mijin nata zasu fita india a dubata……"
Lumshe ido yayi hawaye na bin kumatunshi ya rigaya yayi failing ……da yake Alhajin a baya yake sam bai kula da halin da Maleek din yake ba……kofar gidan yayi parking kafin ya zagayo ya budewa Alhajin har ya rigaya ya fito ya shige yana fadin "Shigo Abdul Maleeku……"
Girgiza kai yayi a hankali kamar Alhajin na kallonshi sannan ya kwantar da kanshi jikin gaban motar yana numfashi a hankali……Murya Granny da yaji ta sashi naimo natsuwarshi ya dago da kanshi yana yake……
Maryam da ya hango ya sashi juya masu baya da sauri don ya tabbata tana tare da Safeena Kuma bayajin zai cigaba da rayuwa indae yana kallonta ……
"Dole ka juya man tunda baka da gaskia……"cewar granny dake kokarin shinfida katuwar leda a bayan motar ……
A hankali ya juyo yana yake tare da maida kanshi kasa don har ga Allah baya jin zai iya kallon Safeena a yanzu da ya tabbata ta mashi nisa……"Ba haka bane granny tafiya ta kamani ……"ya fada da murmushin yake a fuskarshi
Zuciyarshi ke neman rusa mashi duk wani plan na kar ya kalleta sam ya kasa jurewa……a hankali ya fara bin kafafuwan mutanen dake tsaye gurin har ya sauke bisa kafar daya tabbata ta Safeena ce ……
Sae da ya lumshe idon sannan ya fara kallonta tun daga kasa har ya kai kan kugunta da razanannan kallo ya karasa kallon fuskarta ……Lumshe idonshi yayi yar kwallar dake makale ta fado maida idonshi yayi ksn kugunta domin ya tabbatar da abunda ya gani ……Tabbas idan idanuwanshi ba gizo suke mashi ba uwar tulluwa ya hango a bayan kugunta sannan ga uban kalar da zanin ya sake daga sama ……
*FEEDOHM💞*
[9:27PM, 11/2/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
© *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM💞_*
*Devoted to Ummi A'isha👌🏻*
*Bestowed to Aunty Sis💕*
3⃣0⃣
A razane ya karasa yana kallonta "Wat happen Madam?ya fada yana kallon fuskarta
Shiru ta masa tare da janye hannunta daga jikin Maryam ta shiga bayan motar……da ita da Abba ne a baya sae maryam da ta zauna gaba ……bakin fita gari suka hadu da family din JB da Suka yo mashi rakiya wanda har mom dinshi ciki ……Bayan sun gama gaisawa maryam ta koma baya JB din ya zauna gaba tare da juyowa yana kallon Safeena ba wata kunya ya kashe mata ido yana fadin "Babynah ya dae?……You'll be ok kinji ko da munje zakiyi enjoying life dinki better than nan garin,I'll be so caring ……"
Lumshe ido tayi tare da kwantar da kanta a kafadar Abba ba tare da tace komae ba ……kallon maryam yayi yace "Sister ya jikin baby?
Ita kam kunya ma ya bata gaban Abban zai dinga kira masu wani baby dan murmushi ta saki tana kallon safeena sannan tace "She's ok……"
"Good " ya fada tare da juya ya fito da wayarshi yana latsawa……Maleek kam da kyar ya iya controlling kanshi babyn da JB ya fada ya hargitsa mashi kwalwarshi ……
Masallacin kankia zuhur ta masu Abba yace su tsaya suyi sallah tukun ……Duk suka fita sae Safeena dake zaune ita kadae ta kwantar da kanta baya ……har Maleek ya gama alwala amma baiga ta fito ba……
Ruwa ya diba a buta ya matsa tare da bude bayan motar "Madam ki fito kiyi sallah……"
Wani irin kallo ta watsa mashi tare da maida idonta ta rufe ……Ajiyar zuciya ya sake a bayyane don ko hararan madam abun so ce sannan yace "Sorry Madam na fahimci matsalarki amma kiyi tunani abunda ke jikinki ba normal Pes bane na ciwone kuma Allah bai yafe sallah baga mai irin wannan ciwon indae ta tabbata a normal pes dinta bane kiyi kokari kiyi sallah tunda tana kanshi ko bakiyi ta yanzu ba sae kin ramata……"
Dan bude ido tayi tana kallonshi idan bata manta ba malamai suna fadin an dauke sallah ne ga macen dake jinin al'ada ba wae jinin cuta ba ……idan har jinin ya zama na cuta to duk lokacin sallah zatayi tsarkine sannan tayi sallarta……
"Thank you……idan mun isa inda zamu zanyi maleek"ta fada a hankali
Murmushi yayi sannan ya mike ya koma yayi sallar lokacin duk sun gama suna addu'a ne sae da ya gama tashi sannan ya dawo suka cigaba da tafiya ……
Kusan karfe 3 Suka isa airport din dan restaurant din dake gefe suka zauna amma banda Safeena dake zaune taki fitowa ……JB ya kirashi "Kai zo nan ……"
Ko nuna yaji alamun kiran baiyi ba har dae Abbah yace "Abdul Maleeku zo mana……"sannan ya matso tare da dukar da kai gaban Abba
"Kazo kaci abinci mana ka ja ka tsaya gefe……"ya fada tare da nuna mashi kujeran dake gefenshi
Dukar da kai yayi yana fadin "No Abba koshi sae dae wanda zaa mikawa madam naga bata fito ba ……"
Kallon motar Abba yayi tare da juyo da kai yana kallon Maleek din sannan yace "Bara ta ci ba Abdul Maleek tunda zamu fito na tambayeta me take so tace man ta koshi……"
"Abba to ko cake na kai mata ……"ya fada a hankali ……Dan murmushi Abba yayi sannan yace "To Abdul Maleeku ka shiga ciki ka dauko mata ka kai mata idan zata ci……"
JB yayi saurin fadin "Abba kyaleshi ba wani cake din da zata ci yanzu……"
"May be taci Jabir kasan tana da kusanci da shi sossae ya fi kowa sanin abunda zake bukata ……Jeka Abdul Maleek ka zabar mata sae ka kai mata kaga idan zata ci kaji ko……"cewar Abba da murmushi shinfide a fuskarshi
Eclair cake ya daukar mata da freshmilk sannan ya nufi motar da addu'ar karta yarfa shi don yafi kowa sanin yarfin madam……
Bude motar yayi ya shiga sossae sannan ya mika mata cake din yana fadin "Madam ga cake……"
Dan Murmushi ta saki sannan ta bude idonta tana kallon cake din ……karba tayi tana fadin "Thanks ……"sannan ta aje bayan motar ta lumshe ido
"Please madam ki ci yanzu dan Allah ……"ya fada kasan makoshi
"Na koshi maleek"ta fada atakaice……
"Dan girman Allah madam ba dan na isa ba……" bai rufe baki ba ta dauko cake din tare da budewa ta kai bakinta tana kallonshi ta kasa kasa ……Tunda ta fara ci ya kafe ta da ido yana jefa mata wani irin sassanyan kallo ……har sae da taci rabi sannan ta dago tana kallonshi ,First time kenan da ta ji kunyarshi a rayuwarta ,saurin maida kanta tayi kasa tare da juyawa ta kalli window ……
A wahale yace "Sorry……
Ba tare da ta juyo ba tace "How did you bear when i insulted you so badly without understanding you?
Da sauri ya bude mata marfin fresh milk din tare da mika mata ……Idanuwanta cike da hawaye ta juyo tana kallonshi,bai dauke nashi idon ba sae ma salon kallon da ya sake mata ……
Muryar JB yaji yana fadin"Kai meye haka why are staring her?common dallah fito malan baka san matar aure bace zata tasa ta gaba da wannan shegen kallo ,Baby what happen?
Saurin juyar da kanta tayi ba tare da ta amsa masu ba tana jin lokacin da Maleek din ya bar motar sae da kamshinshi da ya bar mata rintse ido tayi gam tana fitar da kwallah ……tabbas tana son JB amma ta tabbata tana jin Maleek A ranta to idan hakane tana Kaunar Maleek ne tana son Jabir……
Ganin Maryam da Abba sun taso ya tabbatar mata da tafiya zasuyi……shigowa maryam tayi tare da sake bglass na motar ta mika mata zani ta canza sannan ta kamo hannunta suka fito tare ……Da sauri JB ya karbi hannunta tare da rungumota jikinshi ……
Juyawa tayi tana neman Maleek amma duk arean babu shi sae kamshin turarenshi da ya cika masu gurin ……Hawaye suka taran mata a ido ta daga kai a sanyaye tana kallon JB shima ita din yake kallo ……cikin salo ya kashe mata ido tare da kanne guda daya ……murmushi ta danyi sannan ta juya tana kallon Abba dake gefenta shima ita yake kallo idonshi cike da kwallah Sae maryam dake kallon kasa ko baa fada mata ba tasan kuka take ,idanuwanta suka ciko da kwallah ……"Abba……"ta fada hade da bata baki zatayi kuka
Lumshe ido yayi yana juyar da kai "May God be wit you love……" ya fada a hankali tare da juyawa ya rike hannu Maryam suka tafi
,Wani kuka ta sake tana fadin "Please Abba maryam dan Allah wallahi na fasa zuwa *ZAN RAYU DAKU* Abbana karku barni ……" Ta fada tana kokarin fizgewa daga rikon da JB ya mata……sossae ya kara rungumeta yana shafa kanta har suka shiga waiting room ……
*FEEDOHM💞*
[3:00PM, 11/3/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
© *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM💞_*
*Devoted to Ummi A'isha👌🏻*
*Bestowed to Aunty Sis💕*
3⃣1⃣
*_This page is for you swthrt Aysha hameed🌹 Maryam Auntyn Maleek🌹 Maman hanif🌹 besty firdaws Ahmed🌹 Meenarh parrot🌹 Meela Adeel🌹 Aunty Maijiddah musa🌹Ummi Muhsan 🌹Abdul Maleeku Heart you 💞💞_*
A cikin motar suka iske Maleek zaune ya kifa kai a sitiyari har suka shiga ba wanda yace kala jin sun rufe kofar motar ne ya sashi kunna motar suka tafi ……tafiya suke kamar kurame Abba na kallon window gefenshi Maryam na kallon ta gefenta tana fitar da kuka a hankali ……Maleek kam gabanshi kawae yake kallo ba tare da dauke ido ba ……
《》《》《》《》
Da daddare suka isa hotel din dake kusa da asibitin suka sauka tana rungume jikinshi,har suka shiga dakin sannan ya zaunar da ita gefen gadon ya koma yana kokarin shigo da kayansu ……
Lokacin da ya dawo tana kokarin shiga toilet da sauri ya matsa tare da rungumota jikinshi ganin zata fadin "Baby bara ki jira nazo na kaiki ba……"
Dan murmushi tayi ba tare da tace komae ba ,hancinta ya dan ja yana fadin "Inda kin fadi ba?Karki sake kinji ko zan maki komae kike bukata beside ma me zakiyi toilet din?
A hankali tace "Zanyi wankane nayi sallah……"
Dan waro ido yayi cike da mamaki "Wane irin sallah kuma baby bayan kina Pes……Common muje na taimaka maki kiyi wanka ……"
Shiru ta masa suka shiga toilet din a tare sannan ta kalleshi da raunannun idanuwanta tace "Please ka fita zan iya wankan da kaina……"
Spreading arms yayi sannan ya fita tare da janyo mata kofar ……Mintina kadan ta fito daure da towel sannan ta dauki kayanta da pad ta koma toilet din ta saka ……
"Bara nima nayo wankan ko baby ……"ya fada yana dan rungumota tare da kissing wuyanta ……
Tsigar jikinta ne ta tashi cikin dubara ta janye jikinta tana murmushi ……Shinfida abun sallah tayi shi kuma ya fada toilet din ,Da sauri ya fito yana yatsina fuska "Baby wadancan kayan da kika cire ya za'a maki da su……"
A tunaninta ya san dae wankewa za'ayi sannan yana sane da barata iya wankewa da kanta ba ……Shirun da yaga tayi ne yasa yace "Baby zaa zubar dasu ne ko?
"Zubarwa JB?Ta tambaya tare da kura mashi ido ……
"Yeah baby kinsan dae baran iya wanke wadancan kazantar ba ko?infact ma nayi hating jini ko wane irina kinga kenan sae dae a zubar dasu……"ya karashe maganar tare da fadawa saman gado
Gabanta ne ya fadi ta bishi da kallo sannan tace "Amma kasan baka son jini ka yarda da aurena sannan kuma ka biyoni ai da kayi zamanka nigeria mun taho da Maryam am sure zata man duk abunda nake bukata……"
"No baby jinyarki ai dole sae muharraminki zan maki komae jinin ne kawae baran iya tabawa ba ……please ki dan shiga ki sakasu cikin leda sae na yardo ina son zanyi amfani da toilet din……"
Uwar harara ta sake mashi tare da kabbara sallah abunta ……har ta gama sallolinta yana kwance ya kasa shiga toilet din sae da ta gama addu'a sannan ta dafa bango zata shiga toilet din ……da sauri ya taso yana fadin "Baby nace maki ki bar tafiya ke kadae kada kije ki fadi ……"
Banza tayi masa har ya kaita toilet din ya fito yana rufe hanci ,ko da ta zuba a ledar kin bashi tayi ta kama hanya zata je ta zubar kamar yarda yace ……tana masifar don doguwar riga saboda lokacin da Abbanta yaje US ya sawo mata ita amma tana gani ta jefar da ita a cikin GG din harabar hotel din ……ko da ta dawo yana toilet yana wanka Cikin jikarsu ta bude ta fito da katuwar leda ta shifida saman bed din sannan ta kwanta tare da rufe dukkan jikinta ……ya fito yana goge kanshi da towel ganin ta lullube ya sashi karasa bakin gadon ya zauna yana fadin "Baby ba dae har kin kwanta ba bakici abinci ba……"ya karashe maganar tare da yaye blanket din yana kallon bayanta
Dan karamin tsoki yaja yana fadin "Gaskia wannan abun bai kyauta mana ba baby da yanzu muna can muna enjoying life dinmu wallahi ……ko da yake sati biyu ne zamuyi kuma assure kafin lokacin kin warke kinga daga nan istabul zamu je muyi honeymoon dinmu ko……?
Ba tare da ta juyo ba tace "Waye yace maka sati biyu zan warke ……idan sati biyun yayi ban warke ba fa?
"Daina fadar haka man baby ……yanzu dae tashi kici abinci ……"
Bata kuma cewa komae ba ta gyara kwanciyarta "Au bara ki ci abincin ba baby ……shikenan ai cikinki ne ni dae baran iya kwana da yunwa ba ……"
《》《》《》《》《》
Bayan sun isa garin Abba yace a fara kai Maryam gida sannan suka karasa cikin unguwarsu kusa da wani mai dama fura Abba yace a tsaya yana so Abdul Maleek dinne ya fita ya sawo mashi sannan ya dawo suka karasa shiga gidan ……
Cike suka iske gidan kamar ana wani biki Maleek na rike da ledar Furar suka shiga falon Su Uncle Abbah ne da Fadila anyi rashe rashe kadsn carpet ana cin abinci ……Suna ganin Abban suka mike tare da gaidashi ,daga masu hannu yayi cikin fara'a sannan ya karbi ledar hannu Maleek din yana fadin "Karka tafi Abdul Maleeku yanzu zan fito na baka sako ka kaiwa Hajiyar Safeena"
A falon ya zauna tare da fito wayarshi yana latsawa Number Safeena ya kurawa ido yana yawo da hannunshi saman screen din wayar ……
Fadila ta kalli Uncle Abba tare da kanne mashi ido sannan ta dauki bottle na swan da cup ta rarrafa kusa da Maleek din tana fadin "Ya Maleek ga ruwa ……"
Murmushin yake yayi sannan ya girgiza mata kai yana fadin "Alhamdulillah……"
Dan shagwabe fuska tayi tana fadin "Ruwan ma bara kasha ba?Dan Allah kasha kaji……"
Kallonta yayi na secs ko baa fada mashi ba ya san sarae ita ce Aunty Fatee ke mashi magana sannan itace ke yawan kiranshi da turo mashi message……
"Ka karba mana ……ta sake fada cikin muryar jan hankali "oh na manta ashe ban zuba maka ba sorry……"ta karashe maganar tana kokarin zuba mashi a cup
Samun kanshi yayi da kiran Number Safeena bai damu da iyayin da Fadilan,ke mashi ba ……Cikin saa ringing biyu ta dauka cikin sanyin murya tayi sallama
"Madam……"ya fada tare da lumshe idonshi
Zaune ta mike jin muryan Maleek din sannan ta kalli gefenta inda taji JB ya kwanta amma wayam babu shi tabe baki tayi ganin baya dakin sannan ta maida hankalinta gurin wayar da taji Maleek na fadin "Madam kina jina……?
"Eh ……" ta amsa a takaice
"Ya jikin naki?
"Am okey……"
"Alhamdulillah ……" ya fada tare da yin shiru na yan mintina sannan yaja numfashi tare da fadin "Sleep well madam……ki rike addu'a Nothing will happen to you Madam kinyi duka sallolinki……"
Gyada kai tayi kamar yana kallonta tare da goge yan kwallan da suka zubo mata he's such a caring person ta fada a ranta ,jin ya sake yin shirun ne ya sata komawa ta kwanta wayar na makale a kunnenta
A hankali tace "You done much to me Maleek……" Katse wayar tayi ba tare da ta jira abunda zaice ba ……
Sam ya manta da Akwae mutane a falon sae da ya ga Fadilan ta mike tare da fadawa dakin Aunty Fatee da gudu "Ikon Allah……"ya fada a fili tare da kallon Uncle Abba dake ta faman zuban mashi harara
Yar dariya ya sake mai sauti to meye hadinshi dasu Spreading arms yayi ya mike ganin Abban yana saukowa,Kudi Abban ya mika mashi yana fadin "Hajiyar Safeena zaka kai mawa kace ta fara amfani da wannan gurin maganin kafin na shigo ……"
Hannunsa ya janye daga karbar kudin yana fadin "Zan bata Alhaji akwae kudi hannuna……"
"Ka karba mana ka kai mata ……"Abban yace tare da sake mika mashi
Girgiza kai yayi kanshi na kasa alamun bara ya karba ba "Meye haka Abdul Maleeku gardama zan tsaya da kai?ka karbi kudi ta kaiwa hajiya final……"
"Afuwan Alhaji in dai ni zan karbi kudinka na kai awa Madam dita magani banga amfanina ba a rayuwarka ……dan Allah kayi hakuri na nemawa Madam dita magani da zufar Aljihuna……" ya karashe maganar muryarshi na rawa
Shiru yayi yana kallonshi tabbas Maleek mutunne mai tsananin tausayi da alkhairi shi Kanshi ya yarda da cewa Abdul maleek ya aje diyarshi wani guri na daban a rayuwarshi ……hannunshi ya kama yana gyada mashi kai "Nagode Sossae Abdul Maleeku Allah ya albarkaci rayuwarka……"
*FEEDOHM💞*
[10:24PM, 11/3/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
© *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM💞_*
*Devoted to Ummi A'isha👌🏻*
*Bestowed to Aunty Sis💕*
3⃣2⃣
*_Wannan page din nakine khadija bee bee ta Allah ubangiji ya raya mana ilham da sulteen Aunty Sis💞_*
Shiru yayi yana kallonshi tabbas Maleek mutunne mai tsananin tausayi da alkhairi shi Kanshi ya yarda da cewa Abdul maleek ya aje diyarshi wani guri na daban a rayuwarshi ……hannunshi ya kama yana gyada mashi kai "Nagode Sossae Abdul Maleeku Allah ya albarkaci rayuwarka……"
Fadila kam dan yalolan gyalenta ta dauko dake aje saman gadon Aunty fatee ta fito tana kuka ……Aunty fateen ce ta biyota tana fadin "Ke fadila lafiyanki kuwa me aka maki kike kuka……?
Shiru ta mata ta fita daga gidan ,har ta isa gidansu tana kuka ta fada dakin mamanta ,"Me ke faruwa fadila?Aunty zuby ta fada cikin sauri tare da rungumota jikinta
Cikin kuka tace "Mum wallahi sonta yake……"
,"Wacece ya ke so kuma?waye ma fada man kinji fadila……"ta fada cikin lallashi
"Mum Maleek mana wallahi Safeena yake so kuma na rantse da girman Allah sae dae ya mutu mu duka mu rasa shi……"ta karashe maganar tare da sake kuka da karfi
"To Uban wa yace maki sonta yake?kuma an fada maki ana aure cikin aure ne……Sakara ki kwantar da hankalinki ko jiya Hajiyarmu ta kai numbershi gurin boka kuma ya tabbatar mata da naki ne……"
Share hawayen tayi tana kallon Mum din tata tana so ta gasgata abunda take fada ……Tabbas indae Maleek ya zama nata She's the luckiest person a duniyar nan ……Cikin farinciki ta rungumo Aunty Zuby tare da manna mata dan kiss tana fadin "I Love you Mum……"
Cikin Wasa Aunty zubyn ta harareta tana fadin "Da kinzo zaki daga man hankali akan abunda kinsan dole ki sameshi ……"
"Sorry Mum……" ta fada hadi da turo baki
《》《》《》《》《》
Karar shigowar Message da tajine ya sata bude ido a wahale tare da kallon JB dake kwance bisa doguwar kujera kafafu a hanbare kamar wani sabon arne ……Dan karamin tsoki ta sake tana duba agogon dake makale jikin bangon dakin……
5:15am ta gani wayar dake haske ta saka hannu ta dauka sunan Maleek ke yawo baro baro a jikin message din da aka turo ……Dan guntun message ne ya turo "Madam ki tashi kiyi sallah……"Lumshe ido tayi sannan ta mike da kyar tana kallon inda ta kwanta sam babu sauki, ta fasa a ranta……duk da kwannansu uku ana treating din ta tare magunguna masu dan karan tsada……
Bango ta dafa da kyar tana hararan JB dake ta uban baccinshi sam bai da kula da addininshi wani abu ya tokare mata kirji ,bata samu sauki ba sae da ta dauki robar lemun dake aje gefen gadon ta wurga mashi a fuska ……duk da ta dakeshi sosae amma ko motsi baiyi ba ……tayi tsoki yafi sau 10 sannan ta shige toilet din da kyar tayi wanka tare da tsarki ta fito tayi sallah ,har lokacin baccinshi yake
Kamar ta kyaleshi ta dai daure ta kai hannunta tana dukan pillow da ya daura kanshi a hankali tare da kiran sunanshi"Jabir ka tashi kayi sallah ……"
Hannun da take dukan pillow dashi ya rike gam tare da bude idonshi a hankali "Baby kin cika takura……" ya fada cikin muryar bacci
Tabe baki tayi tana harararshi ta kasan ido sannan tace " Sallan ne takura?
"Baby ai ko karfe 11:59am zan iya sallan asuba tunda baa shiga pm ba ……"ya fada yana kokarin gyara kwanciya
Bata san lokacin da tace "In ji wane jakin malamin?
"Please Ki barni nayi bacci baby promise da na farka zanyi kin ji ko ……"
Banza ta masa ta cigaba da addu'o'in da Maleek ya turo mata ……
《》《》《》《》《》
Duk wani abu da granny zatayi Maleek ne ya fansheta, har ga Allah nema mata maganin musulunci yake iya karfinshi Tun lokacin da granny ta fada mashi cewa ciwon Safeena bana asibiti bane hankalinshi yaki kwanciya…… harta office idan yaje karfe sha biyu yake baroshi ,Duk inda yaji wani babban malami yana gurin……Baya k'ashin kashe ko nawa ake bukata sannan ko Abba bai san me yake ba
Iyakarshi da Abban kullun dare zai kai mashi fura sannan su danyi fira kadan ya tafi…… ko yarda baya yi su gaisa da Aunty fatee saboda wani mugun haushinta da yake ji
Hajiyarsu Aunty Fatee kam ta dage iya karfinta dole Maleek din ya so Fadilanta ko ta halin kaka……
Yau ma tun da safe ta kira Aunty Zuby tace ta turo mata Fadila su tafi gurin bokan tare ……Mintina kadan Fadilan ta zo ,basu bata lokaci ba suka tafi sae da suka fita gari sossae sannan suka yanke daji ……sunyi kusan tafiyar Awa daya sannan suka isa bakin wani burtu dake gefen wata katuwar kuka……
Tun daga waje suke jiyo ihun mace ……hajiyar ta kalli Fadila tana fadin "Ki kiyayi bakinki Fadila idan mun shiga ,ina sane sarae baki da kunya to wallahi wannan mutumin keras yake jira ya wulakanta mutun ……"
Turo baki tayi tana fadin "To ni hajiyarmu ina ruwana dashi ……"
"Na dae gaya maki ki kiyaye sosae……"
Fitowar matar dake ciki ya sasu tsaida maganar da suke ……Sae da suka bar hango matar sannan suka shiga tare da aje takalmansu a bakin burtun ba tare da sallama ba ……Dan tsamurmurin tsohone fuska cike da furfura gashi bakikkirin sae Uban wari yake ……
Yafi minti Talatin yana kallon fadilan sannan ya hade miyau ya juya ga hajiya dake zaune tana kallonshi ……katon bakinshi dake cike da algae ya washe yana fadin " Shegen yaro ya hanaku sakat Shafa'u……"
Gyada kai tayi tana fadin "Kwarae kam boka……"
Wata katuwar tukunya ya fito daga bayanshi ya aje gabanshi yana yan surutai har tsawon minti goma sannan ya dago yana fadin "Shegen yarone mai tsabar riko da addini ba'a zaune yake ba, uwa uba ruwan ganyen magarya shi ya zame ruwan wankanshi ba lalle bane asiri ya kamashi ba ……"
"Haba boka akwae wanda ya gagareka a duniyar nan ……"hajiyar ta fada tare da hade hannunta guri guda
Dariya ya sake yana fadin "Ai Allah baya bamu sa'a akan muminan bayanshi sae dae idan yana cikin kaddararsu shine sae ya ara mana dan lokaci kadan akansu amma shi wannan shegen yaro ko kadan baya sakaci da addininshi ……Hajiya Shafa'u yarinyarki ta fitar man daga burtu……"
A Rude ta kalli Fadilan,saboda sanin halinshi da tayi sam baya da imani ko kadan duka ta kai mata da karfi tana fadin "Boka ka yafe mata ,ke kuma dan ubanki tashi ki koma mota mara kunya……"
Tabe baki tayi ta mike ta bar Burtun, Boka kam tun da ta mike ya raka kugunta da kallo sannan ya juyo yana kallon hajiyar da har yanzu tana rude "Ki shigo daga ciki bukatarki zata biya ……"ya fada yana matse kafafuwa
Babu musu ta mike ta shiga inda ya sa jan labule ya katange ,shima ya bi bayanta ……Sae da ya gama lalata da ita sannan ya dauko wani karamin zobe ya mika mata yana fadin "Komae yayi Shafa'u, ki bawa diyar taki wannan zoben ta aje sae tsakar dare ta tashi ta kalli yamma ta daura zoben saman hannunta na haggu sannan tace Zoben zalleni jeka zuciyar Abdulmaleek ka hana mashi sukuni har sae yazo gareni ……idan har taga zoben ya bace to tabbas zaizo gareta a ranar idan kuma zoben bai bace ba to aikin baiyi ba sae ku sake dawowa a canza wani salon …amma a zahiri akwae yarinyar dake cikin zuciyar tashi wadda kuka kawo kwanaki aka ma wannan aikin…… to ita yake so sossae idan asirin shi bai kamashi ba, to ita zamu sakawa hauka ta shiga duniyar ta yarda bazai iya rayuwa da ita ba…"
*FEEDOHM💞*
[5:10AM, 11/4/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
© *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM💞_*
*Devoted to Ummi A'isha👌🏻*
*Bestowed to Aunty Sis💕*
3⃣3⃣
_I love you din banza ki daina astrayed kanki baby rapidly da na bar novel din kin barni……_🌹
Dan jinjina kai tayi sannan ta karba ta fita a mota ta iske fadilan tana chat abunta sae da ta zauna sannan ta harareta tana fadin "Ba kyajin magana ko ,idan da kin ja mana bala'i fa……?
"Yo hajiya mayan kallo ne ya wani kurawa kirjina ido sae kallo yake sakaran bai ma san duk ciko bane……"ta karashe maganar tana rufe baki
"Mtsew shine sae ki hararashi kuma to wallahi ki kiyayi wancan mutumin ya wuce duk yarda kike tunani……"
Ko da suka koma gida zoben ta bata tace tayi amfani dashi kamar yarda boka ya mata bayani……
《》《》《》《》《》
Dan karamin tsoki ya sake ganin turawan da yan mata yan kasar nigeria dake yawo a harabar hotel din wani uban Feelings ya taso mashi ……Ga mace har mace amma babu amfani "Wallahi na gaji ……"ya fada tare da dunkule hannunshi guri guda
A hankali ya sauka harabar Hotel din gurin wata da ke ta zaune kusa da ruwa da alama yar nigeria ce ……kusa da ita ya zauna tare da mika mata hannu ……
Kallon uku saura kwata ta mashi sannan ta yatsina fuska tana wasa da ruwan dake gabanta ……
Da yake dan duniyane bai bar gurin ba sae da ta saki jiki dashi sossae har tana fada mashi sunanta raliya ita yar kaduna ce karatu ya kawota india ……sossae suka hau fira har ta kaisu da shiga room din da take zaune ……Sae da suka shege ayarsu sannan ya fito ya shiga asibitin gurin Safeena ……
Lokacin ta har fito daga dakin da ake treating dinta tana zaune tana jiranshi ……Da sauri ya karasa kusa da ita tare da rungumota yana fadin "Sorry baby wallahi chocolate naje samo maki kuma babu masu dadi……"
Dan murmushi tayi tare da mikewa tana fadin "Is Okey ……"
Shafu fuskarta yayi yana fadin "Ya jikin naki baby? ya rage sossae……"
Dan girgiza kai tayi a hankali idonta ya ciko da kwallah ta kasa magana ……deep kiss ya mata a lips yana fadin "Sorry karki yi kuka kin ji ko ……Very soon zaki samu sauki……"
Yana rungume da ita har cikin dakinsu sae da tayi wanka sannan ya kawo mata abinci ya aje ya fita yana fadin "Make sure kin ci sossae baby yanzu zan dawo nima ……"
Dan girgiza kai tayi tare da daukar wayarta ta kira granny lokacin suna zaune da Maleek din yana mata bayanin wani magani daya karbo ……Maleek din ta kalla tana fadin "Safeena ce bara na dauka……"dan girgiza kai yayi tare da maida hankalinshi gaba daya ga granny din……
"Menene Safeena daga daukar waya sai kuka koma……"Granny ta fada cikin sanyin jikin
Wani irin kuka mai tsuma zuciya ta sake tana fadin "Granny harda tsutsa yau da naje asibiti……"ta karashe maganar cikin wani irin kuka kamar ranta zai fita
Shiru granny tayi tana maimata addu'a a ranta bata so ta karyawa Safeenar guiwa ita kanta idonta ya ciko da kwallah a hankali ta mikawa Abdul Maleek din wayar don ta tabbata bara ya rasa abunda zai ce mata ba ……ita kam da ta kuskura ta furta kalma daya to ta tabbata da kuka zata fito……
A sanyaye ya karbi wayar tare da kangawa a kunne ……har lokacin kuka take kamar ranta zai fita lokaci guda yaji zuciyarshi na bugawa da karfi da ace zai iya dauke ciwon ya dawo jikinshi babu abunda zai hanashi yin haka ……
"Safeena……" ya kira sunanta karo na farko a rayuwarshi ……Dan sassautawa tayi da kukan jin muryar Abdul Maleek din
"Safeena ko wane bawa da yarda Allah ke tsara mashi rayuwarshi wani ya kanyi rayuwa cikin jin dadi daga farko sae a karshe Allah ya sauya mashi da wahala ,wani kam yana tashi cikin tsanin rayuwa daga karshe Allah ya sauya mashi da farinciki ……Safeena ki dauka wannan itace kaddararki ba kuma dan Allah baya sonki ya daura maki ba sae don ya jaraba imaninki ……"Shiru yayi yana sauraren yarda take fitar da wani irin kuka
"Dan girman Allah ki bar wannan kukan Madam……"ya fada muryarshi na rawa , jin batayi shirun ba ya sashi fadin "Wae meye amfanin jabir da zai barki kina kuka irin haka,Zan zo Madam wallahi baran juri kukanki ba ni zanzo na kula dake ta yarda bara ki samu lokacin da zakiyi kuka ba……"
Cikin kuka tace "No Maleek muma sauran kwana biyu mu dawo ……"daga haka ta yanke wayar
Shigowar JB ce ta sata juyowa a hankali tana kallonshi ……Zaro ido yayi da sauri yana fadin "Meye haka nake gani Baby……?
Inda taga yana kallo nan ta kalla……irin tsutsotsin dake fitowa daga kasanta ne suka gangaro kasan kafafuwanta ……azababben kuka ta sake tare da kifa kanta saman gadon ……
"Kai wallahi baran iya……Tsutsa fa Safeena ke fitowa daga jikinshi ……Kai Bata yiyuwa wallahi Ina Sonki Safeena amma har ga Allah baran iya rayuwa dake ba da wannan abun a jikinki ……zan bayar da ko nawane idan mun koma wani yazo yayi jinyarki amma bani ba……"
Da sauri ta dago tana kallonshi da rinannun idanuwanta ……kafada ya daga yana fadin "Yeah Safeena ina sonki amma baran iya rayuwa dake ba a haka ……ni zan biya kudi wani yazo yayi jinyarki harki warke baby ……Sorry……"
Bata ga laifinshi ba har ga Allah sannan ta san granny kadae ke iya jinyarta a haka ……Wasu hawaye suka zubo mata data tuna cewa yanzu tsofa ya zowa granny ba komae zata iya mata ba a rayuwa ita kanta granny tana bukatar Kulawa a yanzu ……Maryam fa ……Runtse ido tayi gam tana girgiza kai ……
《》《》《》《》
Karfe biyu Hajiya ta tada Fadila tare da bata zoben ……a hannun haggunta ta daura sannan ta kalli yamman tayi kamar yarda boka ya fada amman zoben still na hannunta bai bace ba ……
Kallon hajiyan tayi tace "Hajiyarmu kinga bai bace ba fa……"
"Ki sake gwada wa mana kila ba yi daya yake bace wa ba……"hajiyar ta fada kamar bata so wani yaji abunda take fada
Cikin sanyin jiki ta sake maimaitawa amma still zobe be bace ba ……kusan kwana sukayi suna abu daya amma zobe na nan daram ……kusan asuba fadilan ta kalli hajiya a hasale tana fadin "Wannan munafukin bokan karya yake babu wani abunda zai iya……"
,"Uban wa yace maki bara ya iya komae ba kaji mara kunyar yarinya fada man,uban,wa ya hada auren duka iyayenki idan bashi ba?wallahi ki kiyayi bakinki ……"itama ta fada a hasale don ko kadan bata kaunar ace bokanta bai iya aiki ba……
Tsaki fadilan ta sake sannan ta bar dakin gaba daya ……Falo ta koma ta kwanta cikin mintuna kadan wahallen bacci ya saceta ……ko sallar asuba ba tayi ba har kusan karfe 11 sannan ta mike ta koma dakin hajiyar tayo wanka ta fito tayi breakfast……
《》《》《》《》《》
Tunda JB ya gane raliya bai kara kwana daki daya da Safeena ba ……sannan ko ya shigo dakin ya dinga dode hanci kenan wae wari dakin keyi ……Tun bata jin haushin abun har ta fara ……Saboda dae dae gwargwado tana kokarin gyara jikinta duk da abunda ke fita ……
Sam ita bama taga amfanin shigowar tashi ba tunda ba wani abu yake tsinana mata ba komae ita zata tashi da kyar tayi abunta bata jiranshi……
Tana kwance kalabar da Maryam ta mata kafin so zo ya shigo rike da leda a hannunshi daga bakin dakin ya tsaya yana kallonta "Baby ki shirya gobe zamu wuce……"
*FEEDOHM💞*
[9:05PM, 11/4/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
© *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM💞_*
*Devoted to Ummi A'isha👌🏻*
*Bestowed to Aunty Sis💕*
3⃣4⃣
Dan kallonshi tayi ta cikin mirrow ta watsar sannan ta cigaba da abunda take ba tare da ta amsa ba
"Wae baby sae wani sha man kunu kike ko nayi laifine?ya fada tare da langwabe kai yana kallonta
,Tabe baki tayi tana girgiza kai a hankali sannan ta mike tsam ta koma gefen gado ta zauna tana latsa wayarta……karasa shigowa dakin yayi ya tsugunna gefenta yana bata fuska kamar yaga kashi "Sorry baby wallahi ina sonki matsalar daya ce baran iya zama dake ba a haka ,dan Allah ki gafarceni idan munje gida zan samu wani na biyashi kudi yayi jinyarki har ki warke na tabbata granny barata iya jinyarki ba tunda tsofa yazo haka Abba shima namijine zan samu wanda na aminta dashi sae na maki saki daya na bashi kudi ya aureki yayi jinyarki harki warke sae ya sakeki mu mayar da aurenmu ……"
Binshi tayi da ido lallae JB wawa ne na karshe a tunaninshi wane sakarae zai aureta a haka har ma yayi jinyarta ta warke sannan ya saketa kamar wani wawa……
Hannunta ya kamo duka biyun "Kiyi hakuri baby wallahi ba yarda na iya ne bana kaunar jini bare wanda ke fita da tsutsa,Na yarda zan kashe ko nawane don ayi jiyarki baby ki dawo gareni……"
Har lokacin kallonshi take cike da mamakin maganganunshi a yarda ta fahimta sam JB ba karamin wawa bane a tunaninshi ita zata yarda idan ta warke ta dawo gurinshi ……nadamar aureshi ta,zo mata ……Cikin dakewa ta gyada kai alamun ta yarda da zancenshi "Amma Jabir wa kake tunanin zai aureni a haka?
Yar dariya yayi "Gasunan da yawa baby ,babu abunda kudi bara suyi ba……Ko wannan,driver naki ai na tabbata zai yarda yadda naga ya damu da rashin lafiyarki sannan uwa uba ga kudin da zan bashi ……amma dan Allah karki fadawa Abbanki ni nasan yarda zan ce mashi ……"
"Abdul Maleek kake nufi?……ta tambaya tana gyada kai tare da kura mashi ido
"Eh shi mana ,na tabbata zai iya jinyarki yarda ya kamata na yaba da kulawarshi……beside ma 10m zan bashi yayi jinyarki sannan nan na kara mashi 10m tare da gidana dake GRA ya sakeki bayan kin warke……yayi ko?
Juyar da kai tayi sau biyu bata da tabbacin Abdul Maleek zai yarda ……koda ya yarda ya aureta ta tabbata bara ya saketa ba don ta warke ……Gyada mashi kai tayi alamun ta gamsu
《》 《》《》《》
11:46am Dae dae suka gashi cikin garin katsina gida Abba yace a wuce da ita amma sam tace gidan granny take so , Abban cewa yayi a wuce da ita gidan granny gashinan zai zo a bakin kofar gidan suka iske maryam har ta rigasu zuwa ,da murnata ta bude motar ta kamo Safeena tana tambayarta ya jikin
Tabe baki tayi tana fadin "Ke ba sauki……"
Ahankali ta gyada kai jikinta a sanyaye sannan ta kamata JB na bayansh har cikin gidan ,A falo suka iske granny kwance saman doguwar kujera bata jin dadi tana ganinsu ta mike da fara'a tana taba hannu "Maraba da yan tafiya,ai ban dauka da wuri zaku iso ba……"
Zama tayi kasan carpet tana fadin "Maryam taikaman da ruwa please……" babu musu ta mike da sauri ta bude fridge ta dauko masu bottle biyu tare da cup ta aje daya gaban JB sannan ta dawo ta zauna kusa da Safeena tare da tsiyaya mata ta mika mata tana fadin "Sannu besty……"
Suna gaisawa da granny Abba ya shigo Abdul Maleek ya kawoshi ……Hannu ya mikawa JB din suka gaisa sannan ya juya ya gaida hajiya tare da mata ya jiki Sannan ya juya gurin Safeena "Safeena ya jikin……"
Bata fuska tayi tana fadin "Abba wallahi ba sauki kamar kara man ciwon akayi da naje can……"ta karashe maganar murya na rawa
"To yi hakuri Allah zai baki sauki kin ji ko "ya fada cikin sigar lallashi ,sannan ya juya gurin JB yana fadin "Jabir ya hanya?
"Lafiya lau Abba mun sameku lafiya……"ya fada yana kallon Maleek da ya shigo lokacin Hannu Maleek din ya mika mashi suka gaisa sannan ya matsa gurin granny tare da dukawa yace "Hajiya ya karfin jikin……"
"Baka da kunya Abdul Maleeku jiya ya mukai da kai da safe ……"ta fada tana hararanshi
,Satar kallon Safeena yayi sannan yace "Ayi hakuri tsohuwa……"
"Haba wallahi zaka sameni ne ……"ta fada tana gyada kai ,maryam tayi dariya tana fadin "Haba granny dan kinga mutane zaki dinga daga mashi murya Abdul Maleekun ki fane ……" dariya Abba yayi sannan yace "Ka dauko man wayana ……?gyada kai yayi sannan ya mika mashi tare da zama kasan carpet ya lankwashe kafa ……
Cikin Sanyin murya JB yace "Abba dama akwae maganar da nake so muyi da kai ……"ya karashe maganar yana satar kallon safeena wadda itama shi take kallo tana son taji me zai fada
"A a ba komae Jabir ina jinka……" Maleek ne da Maryam suka mike zasu fita Abba ya dakatar dasu "ku zo nan Abdul Maleek damu da ku duk dayane……" Babu musu suka dawo suka zauna
Cikin ladabi da sanyin jiki yace " Abba dan Allah ka gafarce akan abunda zan fada……" Sosae jikin Abban yayi sanyi yace "Bakomae Jabir ina saurarenka……"
"Abban tun lokacin da Mummyna ta samu labarin Safeena bata lafiya ta kafe dole sae na rabu da ita a cewarta baran iya kula da macen dake dauke da wannan ciwon ba ……Abba yanzu maganar da nake jiya ta kirani tace idan ban saki Safeena ba zata tsineman Albarka ,wallahi na rasa yarda zanyi da rayuwata har ga Allah ina son Safeena amma mummyta ta dage akan sae na rabu da ita ……Babban abunda nake tsoro tsinuwar da tace zata man na tabbata zatayi ……"
Sanyaye Abba yace "Uwa ta wuce yarda kake tunani Jabir tun ,lokacin da ta nuna rashin amincewarta da auren ya kamata kazo ka fada man ,Jabir tsinuwar Uwa ba abun wasa bace ka kiyayeta ,Duk abunda mahaifiyarka bata so ka kiyayeshi domin samun albarkar rayuwa……har ga Allah bazan zargeka ba kayi man halacci sossae na aurenta da kayi ,Ni kaina mahaifin Safeena na yarje maka daka saketa yanzu Idan matarka ce bayan ta warke zan sake baka ita Jabir ,Allah yasa hakan ya zama Alkhairi sannan Allah ya albarka ce ku baki daya……"
A sanyaye ya fito da takarda ya aje gaban Abban sannan ya fita falon da sauri yana dafe kai kamar mai shirin faduwa "Jabir kabi a hankali karka fadi ……"Cewar Abban ganin zai fadi ,sannan ya kalli Abdul Maleek yana fadin "Taimaka Abdul Maleeku ka maidashi gida kada yaje wani abu ya sameshi a hanya ……"Mikewa yayi a sanyaye ya bi bayanshi
Abban ya juyo yana kallon Safeena sam babu damuwa a tare da ita hakan ba karamin dadi ya mashi ba "Safeena kinga yarda Allah ya kadarta maki ko,karki dauki wannan a,bakin komae insha Allahu zaki samu lafiya sannan,ba kasar da zaa maidaki ni da kaina zanyi jinyarki kinji ko ki ci gaba da addu'a ……"
Gyada kai tayi a hankali tana jinjina munafunci irin na JB wae mum dinshi tace zata tsine mashi saboda masifar karya ,Sannan ta kalli Granny da ta rafka uban tagumi duk abun duniya ya dameta……Ji tayi maryam ta kama hannunta tana fadin "Sorry besty……"
*FEEDOHM💞*
[3:44AM, 11/5/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
© *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM💞_*
*Devoted to Ummi A'isha👌🏻*
*Bestowed to Aunty Sis💕*
3⃣5⃣
Abdul Maleek kam a bakin mota ya iske JB jingine kamar yana jiran wani ,Kallo daya ya mashi ya watsar sannan yace "Alhaji yace na maidaka gida……"
"To nagode"ya fada tare da bude frnt sit ya zauna zagayawa Maleek din yayi ya zauna sannan ya kunna motar suka juya ……Sae da suka fita unguwar sannan JB ya kalleshi fuska daure yace "Abdul Maleek ina son ka auri Safeena yanzu……"
Wani wawan burki ya taka su duka sukayi gaba tare da dawowa baya suka daki kujerun da suke zaune ……Wani irin kallo yake watsawa JB din kafin yace "Out of sense……" ya kunna motar ya ci gaba da tafiya
"Seriously Abdul Maleek zan baka 20m da gida ,ka auri Safeeena har ta warke sannan ka sakar man ita na aureta……" wannan karon birkin da ya taka yafi na dazu don har sae da suka sauka saman hanya,Gaba daya ya juyo yana kallon JB din ……
Dafa kafadarshi JB yayi yace "Ka natsu sosae Abdul Maleek na tabbata kudinne suka rudaka haka ,Zan baka fiye da haka in dae kan Safeena ……Abunda nake so ka yarda ka aureta kayi jinyarta yarda ya kamata bayan ta warke sae ka saketa ba tare da ka bari Abbanta ya san ni na saka aurenta ba,Abunda yasa nake son ka aureta Saki uku na mata na tabbata idan dad dina yaji na saketa cewa zaiyi dole na mayar da ita saboda akwae kyakykyawar alaka tsakaninsu da Abbanta ni kuma baran iya zama da ita a haka ba kaga kenan ko yace in maidata auren bara ya yiyu ba ,kai kuma auren kisan wutane zakayi har ta warke saboda idan ta warke nazo nace ka aureta zaa dauki lokaci kafin ta fito kila ma har ka fara jin wani abu game da ita ,dan zaman da zakuyi idan bata lafiya babu abunda zaka ji, aikin kudi kawae zakayi ……"
Girgiza kai yayi tare da jinjina jahilci irin na JB a tunaninshi kudi zasu sayeshi ne wae 20m ko yanzu ya tabbata kudin dake accnt dinshi sun lika abunda yake kokarin bashi ,lallae ya yarda komae ilminka na boko indae babu na addini to da kai da jahili duk daya kuke ……ai ko duniya zata hade baya tunanin zaiyi gangancin sakin Madam ba,bayan ya sameta ……
A jahilce ya kalli JB din yace "taya kake tunanin zata yarda na aureta……"
"Kar ka damu ni zan shirya duk yarda zaayi sae dae ban yarda ka rike ko da hannunta bane da sunan ta birgeka sannan ban yarda tayi kuka ……"
Gyada kai yayi sosae yana kallonshi ……a cikin manyan jahilae ya yankarwa JB katon fili ya ajeshi, ji yayi yana fadin "karanto man account numberka na tura maka 10m yanzu zuwa lokacin da zata warke zan baka sauran ,idan kuma baka da account din gobe zanje na bude maka a bank……"
Murmushi ya saki mai sauti sannan yakaranto mashi accnt number din "Wane bank ne "Jb ya tambaya……"UBA" ya bashi amsa a takaice…… idan yaki karbar kudin zai iya fahimtar wani abu……
Mintuna kadan Alert ya shigo mashi Sae da ya duba sannan ya tashi motar suka karasa gidansu JB din ,a bakin gate yayi parking JB ya fito da card dake dauke da numbershi ya mikawa Maleek din "Ka kirani anjima by 9:30 zanyi saving numberka ……"daga haka ya wuce abunshi
Bayanshi ya bi da kallo tare da tribted dinshi yana fadin "Shugaban wawaye……" A hankali ……
Juya kan motar yayi wani farinciki na ratsa shi wani bangare na zuciyarshi kuwa tsoro yake kar Abban ya ki yarda da wannan zancen bogin ba……
《》《》《》《》
Cup ta mika mashi tana fadin "Alhaji Safeena ta dawo amma bara ta zauna nan gidan ba fisabilillahi, Me yasa baku daukeni a matsayin mahaifiyarta ba……kusan kwana biyu fa kenan duk tunanina zata dawo nan amma shiru……"
"Ba haka bane ba Fateema Safeenarce ta matsa dole sae gidan hajiyarta zata zauna ,kuma naga da nan da can duk daya ne kawae fatanmu Allah ya bata lafiya……"
"Ameen amma ya mijin nata yace ,nayi tunanin ko gidanshi zata zauna ma……"ta fada cike da son sanin halin da ake ciki
Bai kawo komae ba a ranshi ya fada mata yarda sukayi da jabir din ya kara da fadin "Ni kaina nayi mamakin saki ukun dake cikin takardar don duk tunanina bai wuce saki daya ba sae daga baya nayi tunanin kila mahaifiyar tashi tace ya mata haka ……fatana Allah ya sa hakan ya zama alkhairi garemu baki daya……"
Hannu ta daura bisa kai tare da sakin kuka tana fadin "Amma dai wannan dan iskan yarone shikenan don bata lafiya sae ya kama ya mata saki har uku Alhaji ……" Ganin abun nata ya koma hauka ya sashi shareta ……
Wayarshi ta hau ringing ya kalleta "Dan Allah kiyi shiru zan amsa waya " Tare da daukar wayar ya kanga a kunne ……
Daga dayan bangaren JB ke fadin "Abba naje office dinka an fada man kana gida yanzu haka ina bisa hanya zan iya karasowa gidan koko sae kadawo na sameka office din……"
*"Ka karaso mana jabir ……"
"to Abba"
Falo ya sauko ya zauna Aunty Fatee ta biyoshi baya ,Cikin yan mintina Jabir din ya iso har kasa ya gaidashi sannan ya gaida Aunty fatee ya zauna "Ya Abban naka Jabir……"
"Lafiya lau Abba yace ma a gaidaku ……"
"Muna Amsawa ai jiya munyi magana dashi na fada mashi ba laifinka bane jabir……"
Dukar da kai JB din yayi sannan ya saka hannu ya fito da ticket guda biyu tare da mikawa Abban "Abba gashi visa ne na nemawa Safeena zuwa asibitin Madina a dubata to da tare dani na zamu tafi sae Mum dita tace baran je ba ,to Abba kawae sae na maida Sunan Abdul Maleek don na tabbata zai kula da ita sosae ……"
"Wane irin abune Jabir taya zaka daurawa mutun wahala ba tare da saninshi ba ,duk da Abdul Maleeku karkashina yake baran iya take hakkinshi ba sannan Abdul Maleeku ba muharramin Safeena bane da zaiyi jinyarta kaje a soke wannan Visar ba mai yiyuwa bace Jabir……" ya fada cikin daga murya
Kwantar da murya yayi yana fadin "Abba tun ina can na kira Abdul maleek din na fada mashi kuma ya yarda sosae ,bara ma na kira maka shi……"
"Dama ta ya zaiki yarda ,Ban taba sa Abdulmaleek wani abu ba yaki yi man ,wannan karan baran shiga hakkinshi ba ……"
"Wallahi Abba ya yarda ,da sunanka zan saka sae yace na sa nashi zai tafi da ita,……"ya fada cikin kwantar da murya
"Idan ya yarda shi Muharramintane da zasu tafi a tare har yayi jinyarta?
"Abba Safeena bata da aure yanzu , Kana iya ba Maleek din aurenta kafin sun tafi tunda sae sati mai zuwa tafiyar ,Ni kaina na yaba da hankalinshi wallahi babu wanda zai iya kula da Safeena kamar shi ,dole Wanda zai kula da safeena ya zama mai rikon Addini ,hakuri,kyautatawa da juriya Abba ,kuma duka Abdul Maleek yana dasu ,shin Abba kana da wanda zaka tura mai irin wadannan halin yanzu,idan kana dashi lokaci bai kure ba zanje na sake masu wata Visa ,fatana ta samu sauki……"
Aunty Fatee dake zaune ta zaburo tana fadin "Wane irin Safeena ta auri da Abdul maleek kuma?kai jabir wannan ba zancen kamawa bane kamar dae bata da yan uwa sae a dauki aurenta a ba driver ,don yayi jinyarta kawae ,Kaga Alhaji ko Uncle Abbah sae su tafi da ita,ko ni da kaina nayi jinyar ta……"
*FEEDOHM💞*
[5:38AM, 11/5/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
© *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM💞_*
*Devoted to Ummi A'isha👌🏻*
*Bestowed to Aunty Sis💕*
3⃣6⃣
Cikin Sanyin jiki Abban yace " Fateema AbdulMaleeku yana da duk abunda jabir ya fada kuma nima zanso na bashi amanar diyata matsalar kawae shin idan na hadashi aure da Safeena suka tafi ban cuceshi ba?
Karaf tayi tace "Ai ko ka cuceshi Alhaji, ae sae duniya ta zagemu mun dauki diya da cuta mun lakaba mashi don kawae yana karkashin mu……"
Daga mata hannu yayi yana fadin "Fateema dan Allah idan bara kiyi shiru ba ki koma daki tunda babu wanda ya kiraki ……"
Mikewa tayi tana fadin "Wannan ai son kaine ,Kuma wallahi bara ta yiyu ba……"
Binta sukayi da kallo har ta shige daki tana gunguni sannan JB yace "Abba ba cuta, har kudi nace zan bashi yayi jinyarta amma yace bara ya karba ba sannan na fada mashi indae aka sa sunanshi to zai aureta kafin su tafi yace ya yarda ,Wallahi Abba yaron yana kaunarku yarda baku tunani ……"
"Duk da haka jabir sae naji ta bakinshi sannan……ka kira manshi yanzu yazo……"
Ko da Abdulmaleek din yazo Abba ya mashi magana cewa yayi ya amince, dama me neman kuka ne aka jefeshi da tsakuwa , Sai dai baiyi tunanin Abban zai amince da wuri ba haka ……
Farinciki Sosae Abba yake da Maleek din ya amince gidan granny yaje ya fada mata ,itama kasa boye murnarta tayi ta fara guda tare da hamdala tana kwarara mashi addu'a ……Safeena kam tabe baki tayi da Abba ya fada mata don ta riga ta san dawon garin sannan ta dauki alwashin ko ta Warke Abdul maleek din ya saketa bara ta koma hannun JB ba……Maryam ta janyo hannunta tana fadin "Ke bama zakiyi farinciki ba Allah ya baki wanda yafi Jabir din "
Yatsina fuska tayi tace "ke kina farincikine……"
Cikin fara'a ta gyada kai"Sosae besty samun kamar Maleek sae an tona kinga dae drivernki ne amma yana da wadatar zuciya gashi dan gayu ga kyau ga ilimi wallahi ba wanda zai ce baya da kudi ……"
Kallonta tayi tace "Yana burgeki ne besty"
Yar dariya maryam ta sake tace "duk wanda yace Abdulmaleek baya burgeshi yana bakin cikine ……"
Yan mintuna ta dauka tana kallonta sannan tace "Za ki iya aurenshi……"
Harara ta watsa mata tana fadin "Besty akwae shirme wa yace maki zan iya aure maki miji……"
Hannayenta kamo sannan tace "Besty ba shirme bane Indae kina son Maleek na maki alkawarin da mun dawo zaki aureshi……"
Duka maryam din ta kai mata a cinya tana fadin "Sae inyi ya da Ahmad……"
Dariya Safeenar ta sake tana tsuke baki "Oh na dauka an ture gwamnatin Ahmadi……"
Granny ta shigo tana fadin "Mara kunya ana fada maki kina yatsinawa mutane fuska amma kin shigo daki har da kashewa, dama ni nasan a rina ana son dan yaro ana kaiwa kasuwa……"
Harara ta sakar mata tana turo baki tace "Ai duk abunda ba dan Allah akayi shi ba watsewa yake da wuri……"ta karashe maganar tare da murguda baki
"Ke dae kika sani ……"cewar granny sannan tayi gaba tana Fadin "Ke kuma Mayyarta sae ki tashi ki je gida ki gaido mamanki ga Abdul Maleek nan zaizo ya tafi dake ……"
"Kai granny ina ruwanki ……"cewar Safeena
"Kyaleta besty ba komae naji ni mayyarki ce ita kam ko Tayya bata da ita bare mayya ……"
Langwabe kai Safeenar tayi "Nima ai mayyar taki ce besty you done much to me……"
Granny suka jiyo tana fadin "Haba yarinya biye mata, zata tafi ta barki ki zo nan kina man mashau mashau da ido wae ke Safeena bata nan lokacin zanci kaniyarki wallahi ,kuma ki fito ya ajeki gida tunda baku da hankali ku duka……"
Tare suka fito tana rike da hannun Safeenar sannan ta zaunar da ita bisa kujera ,
Abdul Maleek maryam ta kalla dauke da fara'a "Ompo besty……" ta fada cike da zolaya
Dan murmushi yayi yana kallon safeena ta gefen ido ……ta wani hade rai kamar NADIYA DA AHMADI……
"Rabu da su Abdul maleeku za suyi bayani ne gaba kadan ……ka biya gidan Malam ka karbo abunda yace zai baka "Granny ta fada sannan ta mike ta koma daki ,Itama Maryam din fita tayi ta bar falon ,Cikin sanyin jiki ya dawo gabanta tare da zama kasa "Madam kinga ikon Allah ko……"
Yar dariya tayi tana fadin "Ikon naira dae Maleek ……"
Shima murmushin yayi "Kin san komae kenan "
Tabe baki tayi tare da juyar da kai
"Zuwa gobe zaa daura mana aure kin yarda da hakan ……"ya fada yana kallon fuskarta
"Duk cikin aikin kudinne ka tambayi yardata?Bestyna na jiraka a waje da gurinta ka tafi da ka fi burgeni Maleek ,lastly banyi tunanin kudi zasu saye ka ba har ka yarda da irin wannan wahalar ……"
Murmushi yayi mai sauti " In dae kece bana tunanin zanyi wahala Madam, zan iya komae a rayuwata akanki……"
"Gyara kalamunka Maleek cewa zakayi indae akan kudine zaka iya komae a rayuwa……"
Mikewa yayi yana leken fuskarta "A yarda ku ka tsara kenan Safeena ,amma a sannu zaku san waye Maleek da yarda na tsara nawa labarin Madam ,ba irin karen da kuke tunani bane daga ke har Jabir din ……" ya karashe maganar tare da kashe mata ido ……Saurin janye idonta tayi tana kallon kafafuwanshi……
《》《》《》《》
A hasale hajiyarsu tace " Uban meye amfaninki da har zaki bari ya yarda ,sannan dan kina banza sae ana gobe daurin auren zaki zo ki fada man, Yanzu uwarki kike so inyi……"
Shiru tayi tana kallon fadila dake kwance bisa cinyar Aunty zuby tana kuka, Sannan tace "Wallahi hajiyarmu ba yarda banyi ba amma ya amince mashi ……"
Aunty Zuby ta harziko tana fadin " Dallah rufe man baki ,ke ba mace bace dan ubanki ,Wallahi bayan a gida hajiyarmu ta haifeki da sai ince masanya aka mata a asibiti,Ke fadila ta fara fadawa matsalarta amma gabanki aka rushe duk wani plan dinmu ,sannan dan kina wawiya ki kwaso shegiyar kafarki kozai kozai kizo kina fada mana ……"
Kuka ta saki tana fadin "To ni Aunty Zuby ya kuke so nayi maku ……"
"Ubanki muke so ki mana"cewar Hajiya
Cikin gunguni Aunty fatee tace "Sae dae kuyi hakuri tunda lokaci ya kure"
"Sae dae Uban kowa ya rasa wallahi Aunty fatee" Fadila ta fada cikin kuka hade da daga hannunwa sama……
"Dallah rufe man baki dan ubanki ,Ina kika kai zoben da boka ya baki……"cewar hajiya
"Yo ni nasan inda yake" Fadila ta fada
Aunty Zuby ta dago kanta a fusace tana fadin "Tashi ki nemoshi dan bura ubanki yanzu mu koma gurinshi……" Sannan ta mikawa Aunty Fatee hannun "Ke kuma ina kudin da nace ki tahowa da hajiya dasu……"
Jikkarta ta bude tana gungune ta fito da rapper ta dubu ta mika mata ,Fizgewa tayi sannan ta ciri kusan rabi ta mikawa Hajiyar sauran ta bi fadila daki "Kin ganshi koko"
Turo baki Fadila tayi "Yo banganshi ba mummy,ni fa wannan shegen bokan ba abunda ya iya……"
Duka ta kai mata a baki "Dallah rufewa mutane baki sakaran banza uban wa ya hada aurena da ubanki idan bashi ba……"
*FEEDOHM💞*
[5:25AM, 11/7/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
© *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM💞_*
*Devoted to Ummi A'isha👌🏻*
*Bestowed to Aunty Sis💕*
3⃣7⃣
『 *_MEENARH PARROT♣ Wannan page din naki ne kyauta 🌹Don na tabbata ni da ke kadae ne muke_ ™JB💃🏻💃🏻……* 』
Neman duniya sukawa zobe amma sam babu alamunshi a cikin dakin, Hajiya tace su bari zuwa gobe sae a fitar da kayan dakin kila wani guri ya makale ……
『』『』『』『』
Abdul maleek kam ko da ya fadawa Baffanshi abunda ke faruwa fatan alkhairi ya mashi ,Wanda dama ya riga ya sani Baffan nashi baya da matsala ,Nana ma kasa rufe baki tayi don murna har ya fita waje ta bishi da gudu tare da riko mashi hannu ta baya ……"Baddi na zaiyi aure" ta fada tana washe baki
Dan juyowa yayi yana kallonta sannan yace "Ko bakya so ne Nana"
Saurin girgiza kai tayi tana fadin "Ahh baddi ina so mana ,kaga sai in koma gidanka ko?
Murmushi ya mata yana fadin "Jeki ki wa inna aiki kinji ko ……"
《》《》《》《》
*Friday……*
Bayan an gama sallar juma'a a cikin masallacin liman ya daura auren *ABDULMALEEK DA SAFEENA* Duk da ba wani gayya Abba yayi ba amma daurin auren ya tara dumbin jama'a wanda ko bikin farko bai tara su ba ,yawancin mutanen duk abokan arzikin Abdulmaleek din wanda harda Justice Ahmed kabir tare da VC na yar adua ……Jabir ma baa barshi a baya ba don har dad dinshi sae da yazo gurin ……
Yar walima Dad ya hada aka ci aka sha daga abunda ya sawwaka sannan kowa ya watse dob baiyi tunanin daurin auren zai tara mutane haka ba……JB ne yabi bayan Maleek din ganin zai shiga mota ya barshi ,janyo kafadarshi yayi yana fadin "Ba ka ji ana kiranka ba ne"
Lumshe ido yayi yana fadin "Oh JB banji ba wallahi ,ina saurine zan gano jikin madam ne duk yau banje ba……"
Wani tukukun bakin ciki ya tokare mashi wuya ,ya dage kafada yana wulla mashi wani mahaukacin kallo "Ban yarda ka dinga shishshige mata ba Maleek ……"ya fada a hankali
Murmushi yayi mai sauti "Baka san hakkin mace bane akan mijinta?alright bara na fada maka don bana tunanin unguwarku akwae islamiyya ,Madam tana karkashina yanzu dole na kula da ita yarda ya dace ba tare da na gaji ba ……" bai saurare shi ba ya fada mota tare da bata wuta ya barshi tsaye
Kallo ya bishi dashi tare da dunkule hannu yana naushin iska ,Dafa bayanshi da akayi ya sashi juyowa da sauri tare da dukar da kai "Abba ina wuni"
"Lafiya lau jabir ,ga Dad dinka can baya yana nemanka kaje ka sameshi ……" Abban ya fada tare sa shigewa motar dake kusa da JB din suka tafi da wasu mutane ……
Da kyar ya ja kafafuwanshi ya isa gurin Dad din nashi suka koma gida ,A falo ya suka iske Mum dinshi zaune ita kadae ,Dad din shigewa part dinshi yayi ,shi kuma JB din ya zauna falon tare da sake uban tsoki
Da sauri Mum din ta kalleshi tana fadin "Kae da wa Son"
Tsakin ya kara saki tare da fadin "Mum wannan bakauyen ne man "
Tasowa tayi tare da zama hannun kujeran da yake "Me kuma ya maka?
"Mum magana ya fada man ,Don nace kar ya shishige mata ,kuma wallahi sae na dauki mataki bai shani banza ba…… " ya fada cikin daga murya
"To ai Jabir dole sae ka kauda idonka zuwa lokacin da zai sakar maka matarka ,ka daure kaji ko,karka damu da ta warke zai saketa…… "ta karasa maganar cikin sigar lallashi
Yatsina fuska yayi "Mum yunwa na ke ji fa "……Mikewa tayi ta nufi Darea ta dauko mashi trnks na abincinshi sannan ta dawo ta zuba mashi ,Sae da ya fara ci sannan ta nufi gurin dad dinshi……
《》《》《》《》
Da sallama ya shiga falon amma shiru babu motsin kowa a ciki ,yayi minti goma a tsaye amma ba wanda ya amsa sallamar ,Dakin da Safeena ke ciki ya leka tare da sallama, idonta na kan wayarta ta dago a hankali tana mashi kallon kasa kasa ,sannan ta mayar da hankalinta ga abunda take ……
Da murmushi yake fadin "Madam sallamar ma bara ki amsa ba ko?to ai sallama dolene a amsata indae anyita ……"
Harara ta sakar mashi ganin yana kokarin shigowa har da su tura dakin tana fadin "Idan a azuciya na amsa fa?ka bude man daki zafi nake ji maleek ……"
Murmushi ya sakar mata yana kashe mata idanu "Yi hakuri sai na kunna maki fanka madam ……"ya karashe maganar tare da kunna fankar sannan ya karaso bakin gadon ya tsaya saitinta fuskarta yana kallonta
"Wae meye ne kulle Daki kuma ……"ta fada tana bata fuska ba tare da ta dago ba
Hade hannayenshi yayi yana fadin "Allah ya baki hakuri don kada kofar ya dinga kara ne naga ana iska ……"
Banza ta mashi tana latsar wayarta ,Ganin ba kulashi zatayi ba ya saka shi zama gefen gadon tare da zare wayar a hankali "Meye haka Maleek "ta fada cikin daga murya
Yatsanshi ya daura saman lips dinta "Shiii meye na daga murya Safeena ,ko kema baki san matsayin miji a gun matarsa ba ne?ya karashe maganar a hankali tare da langwabe kai gefe guda
Dariya ta subuce mata hadi da watsa mashi harara "Fada man matsayin da kake dashi bayan auren kishin wuta kayi ……"
Tabe baki yayi yana kashe mata ido "ko……"
Gyada kai tayi still tana hararanshi ,Katse maganar yayi ta hanyar tambayarta "kinci Abinci……?
"Shafa kaji ……" ta fada tare da sakin karamin tsoki
"Wow ina zan shafa Madam……" ya fada yana kanne ido
Hararanshi tayi tare da sauko da kafafuwanta kasa ta mike tsaye tana fadin "Idan ka gaji da zaman dakin ka fito ……" bata rufe baki ba ya dagata cak ya nufi hanyar fita da ita yana fadin " Ina zamu koma to madam ……"
Mutso mutso ta fara tana fadin "Ka saukeni Maleek dan Allah ……"Wani wahallen kallo ya watsa mata har sae da ya direta falo sannan ……
A sanyaye ta bishi da kallo ganin farar Shaddar dake jikinshi tayi staining sossae daukotan da yayi ……A hankali ta dukar da kanta kasa tana kallon carpet ,
Ganin yanayinta ya sashi dago habarta yana murmushi "Zan samu clean a ciki madam ……?ya fada saitin fuskarta
A Sanyaye ta gyada mashi kai "Sorry Abdul Maleek ,sae da nace ka saukeni amma kaki ……"ta fada idanunta cike da kwallah
"Kin sani na daukeki ne dole Madam?karki damu kinji ko zan wanke gurin yanzu,Idan naje gida zan canza kayan dama……"ya fada yana sake mata lallausan murmushi ……
Mintina kadan ya fito ya wanke gurin, yana fadin "Ina Maryam da Hajiya ne ?
"Sun fita" ta fada a takaice
"Ok ,ke kin ci abinci ne……?ya fada babu alamun wasa
Dagowa tayi da niyar hararanshi amma ya mata kwarjini tayi saurin mayar da kanta tana girgizawa a hankali
"Ok kina cin Kebabs na dauko maki a mota ko akwae abinci a kitchen na dauko maki ……"
Yatsina fuska tayi tana girgiza kai a hankali
"Wane kike so Safeena "ya fada cikin sigar lallashi ……Saurin kallonshi tayi, Yarda yake magana cikin natsuwa da lallashi kamar ba Maleek ba ,Duk da tasan mai ajine amma yau ya sauya sosaae ……
"Safeena……"
"A kwae a kitchen" ta fada a takaice
Da ya ke ya san kitchen din ya shiga ya zubo mata sakwarane da Miyar egusi da taji danyen kifi sosae a ciki ,Dawowa yayi ya daura mata plate din saman stool din dake gefe sannan ya matsar mata dashi gabanta shi kuma ya zauna a kasan carpet tare da harde kafafuwa yana kallonta……
Ji tayi ta takura ,duk yarda taso ta daure kar tayi mashi magana kasawa tayi "Meye kake kallona haka ……"ta fada lokacin da ta kai lomar sakwaran kusa da bakinta
"Yi hakuri ……"ya fada a sanyaye
bata kuma cewa komae ba har ta gama cin abincin sannan ya dauke komae ya mayar ya dawo
"Na taimaka maki kiyi wanka ……?
Dakyar ta taushi bakinta daga bakar maganar da take niyar kwabo mashi……
"Kinyi shiru madam ……"
"Nagode idan Maryam ta dawo zanyi ……"ta fada fuska a daure
Murmushi yayi mai sauti sannan yace "Ba matsala ,ni zan tafi idan Hajiyar ta dawo kice ina gaidata ……" kafin ta bashi amsa ya bata kiss a gefen kumatunta sannan ya fita da sauri don ya tabbata bara ta iya hakuri ba
Dariya yayi lokacin da yaji tana fadin " Da ka tsaya mana wallahi duk da bana lafiya sae kasha mari ……
*FEEDOHM💞*
[9:01PM, 11/7/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
© *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM💞_*
*Devoted to Ummi A'isha👌🏻*
*Bestowed to Aunty Sis💕*
3⃣8⃣
『 💜💜💜💜💜💜』
*Wannan page din kyautane ga dukka mosayan wannan book din ,nagode da kaunarki gareni*💞
Cikin bacci JB yaji wayarshi na ringing kai hannu yayi ya dauka ba tare da ya bude ido ba
"To karamin dan iska shine tun da ka tafi ka gagara kirana ko ,Ga raliyar banzaye ta gama maka amfani ……"
Waro ido yayi tare da mikewa zaune tsakiyar gadon yana fadin "Wallahi raliya ba haka bane na dawo gida na iske Dad baya lafiya so hankalina ba kwance yake ba……"
Dariya mai sauti ta saki tana fadin "Kar ka gwada man karya JB ……"
Cikin kwantar da murya yace "Ba Karya na maki ba raliya ……" ket yaji ta katse wayar ba tare da ya karasa maganar ba ,Tabe baki yayi yana fadin "Wawuyan yarinya zaki tada mutun yana bacci ……" Sannan ya gyara kwanciyarshi ,cikin mintina kadan bacci yayi gaba dashi ……A cikin baccin ne yayi mafarkin Raliyar ta zo mashi cikin wata irin Mummunar siffa tana fada mashi zatayi tafiyar Shekara dari amma da ta dawo zata nemeshi ……Firgigi ya farka yana lalubar wayarshi tare da sake kiran numberta amma switch off ,Yanayin yarda ya ganta tayi bala'in tsoratashi ,A sanyaye ya mike ya fita daga dakin ya koma dakin Mum dinshi ya kwanta sae dae babu alamun baccin da ke tare dashi……
《》《》《》《》
Ranar da zata su tafi tun da safe Maleek yaje daura gidan Malam ibrahim bayan sun gaisa ne yake fadawa malamin cewa harda tsotsa ke fita yanzu ……
A jiyar zuciya malam ibrahim yayi yana fadin _"SIHIRIL NAZEEF kenan Abdul Maleek Shi kalar Wannan Sihiri yana aikine kawai Ga Mata ……Bokane Zai turo Aljani zuwa ga matar Ya kuma umurceshi da ya rika Fitar mata da jini ta gabanta, Shi kuma Aljanin nan take zai shiga jikinta a cen cikin Jijiyar jininta (veins)."
_Manzon Allah (Saww) yace:……"LALLAI SHAIDAN (ALJANI) YANA GUDANA A JIKIN DAN ADAM AKAMAR YADDA JINI YAKE GUDANA".……Ma'ana: Yana iya shiga duk inda jinni zai shiga, saboda bashi da gangan jiki da zai hana shi yin hakan.
Imamu Bukhari da Muslim suka ruwaito shi (An-Nawaawi, 14/155).……A wani Hadisin Kuma na Imamu Bukhari; Lokacin da Hamma bint Jaash ta tambayi Manzon Allah (saww) game da tsawaitar zubar Jinin (prolonged bleeding) a lokacin haila, Sai Annabi (saww) YaCe, "WANNAN YANA DAGA CIKIN MAKIRCIN SHAIDANUN ALJANNU"……(Imamu At-Tirmidi, da Imamu Bukhari suka Ruwaito Shi).……Imam Ahmad Ya fitar da wani hadisi Cewa, Annabi (saww) YaCe, "FITAR JININ HAILA WANDA YA WUCE QIMA YANA DAGA CIKIN SHAIRIN SHAIDANUN ALJANNU".……(Imam Ahamd da An-Nasa’i suka ruwaito shi).……Duka wayannan hadisan suna nuna mana Cewa duk fitar jinin da ya wuce Qima na haila to akwai sharrin aljannu a ciki
Don haka Zan baka Ruwan Zam-Zam dana karanta ayoyin Rukiya a ciki abawa Safeenar ta rika yin alwala da su tsawon kwana 3……Haka kuma ta rika shan wayannan ruwan sau 3 a rana tsawon kwana 3, In shaa Allahu za'a dace.……Sannan idan ka fita ta nemi *HABBUR RASHAD,FIJIL,KUSTUL HINDI ,HABBATUS SAUDA ,GARIN FUREN ALBABUNAJ* Sai a debi cokali uku na kowane a hada da zuma ta dinga sha kullun ……_
"To ina zan samesu malam……?ya tambaya cikin kwantar da kai
"Da kaje islamic chemist Abdul Maleeku zaka samesu duka insha Allahu ……"
Godiya yayi sannan ya mike suka fita tare har gurin motar Malamin ya rakashi tare da mashi fatan Alkhairi sannan ya dawo ……
Sae da ya biya gidansu yawa Baffa bankwana sannan ya biya islamic chemist ya hado duk abunda Malam ya fada mashi sannan ya dawo gidan Granny din, a can ya iske Abba Suna magana da ita ……
Bai samu ya mata bayanin ba ……ya tsaya suna magana da maryam tana zolayanshi wae tunda aka ta bashi bestynta bai kuma zuwa ba ……
Dariya yayi yana kallon Safeena yace "Ki tambayi bestyn taki idan banzo ba……"
Juyawa tayi tana kallonta "Wae besty yazo?
Harara ta sake mata tana fadin "Ban sani ba……"
"Allah ya baki hakuri besty yau fa zaki tafi ki barni amma shine kike man haka ……"ta fada cikin sanyin murya
Dan kallonta tayi taga ta mata kallar tausayi tace "Yazo fa besty mantawa nayi ban fada maki ba sorry……"
Shima hararan Safeena yayi "Madam bara ki man magana ba ko? ,ko sae munje can ne ……"ya fada cikin zolaya
Banza ta mashi tana fadin "Besty dan Allah ki saka man wancen littafin a jikkana dashi zan tafi ……"
Abba yace su fito a tafi ,kuka sosae suke ita da Maryam da Abban yace bara a tafi da maryam din ba ta rakata ……Dakyar aka fidda safeenar daga jikin maryam din sannan suka tafi daga Su sae Abban ……ko A Airport din ma Ko bankwana Abba baiyi da safeenar ba ya juya ya tafi……
Rungumeta Maleek yayi a jikinshi yana lallashinta……Daga bayansu suka ji Muryar JB na fadin " Wane irin iskancine haka Abdul Maleek……"
Su duka suka juya cike da mamakinshi ashe har nan ya ya biyosu ,Dan waro ido Maleek din yayi yana fadin "Me ke faruwa Jabir ……?
Cikin daga murya yace " Baka san abunda ke faruwa ba kenan ,to saketa karamin mara kunya……"
Dafe kai yayi yana leken fuskarta "Oh Sorry madam ,Sorry Jabir ,na manta cewa kayi na kula da ita sossae ,na fahimci laifina bai kamata na barta tana tafiya ba ……" yana rufe baki ya dagata ya daura saman kafadarshi ya nufi Wroom da ita ……
"To the hell of you thug fox……"JB ya fada cikin daga murya yana nunashi
Duk da yaji zafin zagin amma bai juyo ba sae da ya ajeta sannan ya zauna gefenta tare da dafe kanshi da duka hannayenshi ……
Hakanan ta ji bata ji dadi ba ,Ahankali ta dafa bayanshi tare da fadin "Sorry……"
Kallonta yayi yana murmushi sannan ya zagaya da hannunshi saman kafadarta tare da daura kanshi bisa dayar kafadar ya lumshe ido ……
Suna a haka har a ka kirasu suka mike yana rungume da ita har suka shiga……
A cikin jirgin ma duk wani motsinta a idonshi takeyi har bacci ya dauketa ta kwanto saman kafadarshi ……
*MILLENIUM AL AQEEQ MEDINA HOTEL*
Anan suka sauka anan gab da fara sallar Magrib ,room 12 floor 2 ……
Zaunar da ita saman kujera yayi sannan ya duka yana cire mata takalman kafarta ……Sannan ya dago yana sakar mata wani irin sassanyan kallo , Dole yasa ta saki murmushi tare da kawar da kanta gefe ……
Peck ya mata a goshi "Zanje sallah ,I'ld be back soon……"
Murmushi kawae tayi ba tare da tace komae ba ,shi kanshi bai damu ba ,godiya ma yake da murmushin da ya samu ,Har ya kai bakin kofa ya juyo yana fadin "Tsara ban me kike so ……"
"Addu'a"ta fada a takaice
"Wannan dole ce ,banda ita ……abinda zaki ci……"ya fada yana kokarin gyara ID card dinshi dake kokarin tona mashi asiri
Dan Waro ido tayi "A mosque din"
Gyada kai yayi yana fadin "Yeah ke dae fada"
"Nothing……" ta fada tana tabe baki
"Sae kin fada " ya karashe maganar tare da dawowa kusa da ita "Fadaman please……"
"Bana bukata fa……" ta fada tana bata fuska
"Dan Allah ……"
Banza ta masa tare da jinginar da kai gefe guda "Tunda bakyaso lemme kiss your lips sae na tafi ……" harara ta sake mashi ,ganin ya zauna saman cinyarta tare da dago kanta ya sata fadin " Pistachio……"da sauri tana runtse ido
"And ……? ya fada yana kashe mata ido
"Ice cream ……"
"Sae me……"
"Shikenan ……" ta fada tana murmushi
"Good……"
0 comments:
Post a Comment