Yana fita ta mike da kyar ta shiga toilet ,Sae da tayi wanka sannan ta tsaya tana wanke kayanta da su ka baci ,Muryarshi taji yana fadin "Twee……"
Tabe baki tayi tana fadin "Sabon salo ……"
Jin karar ruwa ya sashi shiga binta toilet din ,Waro ido yayi tare da karbar kayan da ke hannunta yana fadin "Twee meye kike haka……?
Kallonshi tayi tana fadin "Me ka gani……"
Kamo hannunta yayi yana fadin "Kar ki sake kin ji ko I'ld do anything for you……Bara na kawo maki wasu ruwan kiyi alwala kin ji ko ……"
Gyada kai tayi a sanyaye tana kallonshi har ya fita sannan ya dawo dauke da ruwan ,shi da kanshi ya dinga zuba mata tana alwalan har ta gama ya kamata suka fito ,sannan ya shinfida mata abun sallah ……Har ta kabbara sallah sannan ya koma toilet din ya wanke kayan Tare da wanke toilet din sannan ya fito ……
Lokacin ta gama Sallan ta daga hannu tana addu'a ,Gefenta ya zauna tare da daga hannun shima har ta shafa sannan ya shafa yana fadin "Ameen……"Tare da janyo ledar daya shigo da ita ya fara budewa ……
Duk abunda ta fada shi ya sawo mata sae chocolate da ya hado dashi
Pistachio ya bude tare da debo kadan a hannu yana fadin "Oya open,your mouth……"
Bata fuska tayi tana fadin "Zan ci da kaina……"
"Ban yarda ba bude na baki da kaina……"
"Maleek ……"ta fada hankali
"Na'am Twee……"ya kwaikwayi muryarta
Hararanshi tayi sannan tace "Stop calling me wani Twee baka san sunana ba……"
Kashe mata ido yayi yana fadin "Na fi kowa sanin sunanki Twee amma baran iya fadi ba……"
"Me yasa? ta fada tare da waro ido
"Baran iya kiran matata kamar ina kiran wata cousin dina ba……"
"To ni bana so……ka kirani Safeena ……"
Bae ce mata komae sae wani sanyayyan kallo da ya bita dashi tare da kara mika mata pistachio din a bakinta ,wannan karon bude baki tayi a hankali tare da runtse ido ……
Sae da ya gama bata ta koshi sannan tace bacci zatayi ,daukarta yayi ya daurata saman gado sannan ya dawo ya tattara gurin ya komo ya zauna bisa stool din dake gefen gadon tare da langwabe kai
"Twee ina zan kwanta……"
Shiru ta masa har sae da ya kara maimatawa sannan tace "Ga kujera a can mana ……"
Marairaicewa yayi yana fadin "Wallahi Twee fadowa zanyi ……"
A Zahiri ta yarda da fadowar zaiyi don itama,idan bacci ya dauketa saman kujeran dakinta sae dae ta farka ta ganta kasa ……
"Ka dauki blanket ka shifida a kasan carpet to……" ta fada ba tare da ta kalleshi ba
Kara marairaicewa yayi yana fadin "Twee Allahu ,So kike mura ya kamani ko ,don ba JB bane ko ……"
Kallonshi tayi tana turo baki sannan ta matsa can karshen gadon ta kwanta tare da juya baya ……tsadaddan murmushi yayi sannan ya canza kaya ya dawo ya kwanta bayanta ……
"Maleek duk can filin ba isheka ba sae ka dawo kusa dani ……"ta fada tare da mikewa tana fadin "Ba matsala bara na koma kasan ni……"
Saurin rike bargon yayi yana fadin "Allah ya baki hakurI Twee dan Allah karki koma kasan wallahi zan matsa sosae kin ji ko ……"
Da sauri ya matsa can karshen gadon ya kwanta sannnan itama ta kwanta ……
《》《》《》《》
,Cikin kwantar da Murya hajiyarsu ke fadin "Boka mun nemi zoben mun rasa bayan an ajeshi da asuba ……"
"Wannan sakacinku ne Shafa……"ya fada cikin budaddiyar muryarshi
Aunty zuby tace "Ba yarda za'ai a taimaka mana boka…Daga baya sae mu nemi zoben ,don wallahi Diyata na can banda kuka babu abunda take tun jiya da ta samu labarin sun bar kasar………"
"Za'a taimaka maku idan kun kawo zoben ……ku tashi ku tafi "ya fada cikin daga,murya
"A taimaka boka……"
Kallon da ya jefa masu ne yasa hajiya mikewa tare da jan hannun Aunty Zubyn zasu fita ,har sun kai kofa yace "Ku dawo……"
Cikin kyarma suka dawo suka tsugunna , Aunty Zubyn ya kurawa ido yace "Za'a taimaka bayan kin biya man tawa bukatar……"
Hajiya ta kalla ,tayi saurin daga mata kai alamun ta yarda kawae ……Sannan ta kalleshi tace "Na yarda ……" ta karashe maganar kamar zatayi kuka ,da ta tuna warin da ta shaka farkon da ya fara saduwa da ita ……Wanda daga lokacinne bata kuma yarda tazo gurin ba sae yau da fadilan ta takura mata da kuka ……
Dariya yayi da karfi yana fadin "Jeki waje ki jirata Hajiya……"
Mikewa tayi ta fita babu alamun damuwa a fuskarta ……Kusan minti goma da fitowar tata ta fara jiyo ihun Aunty Zubyn ……Mota ta koma ta zauna tare da lumshe ido har Aunty zubyn ta dawo da idanuwanta jawur ……
"Allah ya isa ……"ta fada lokacin da take kokarin shiga motar
Dariya hajiyar tayi sannan Aunty zubyn ta tada mota suka bar gurin ……
Suna shiga harabar Gidansu suka ga wata yar tsamurmurar budurwa ta fito daga part din Uncle Abba……Tabe baki Aunty Zubyn tayi tana fadin "Ina Amfanin fiddawa saurayi part a harabar gida ……"
Kallonta hajiyar tayi sannan tace "Ke ma kya fada in dae Abbah ne ,ya dinga kwaso mata kala kala kenan har garin Allah ya waye,wallahi na fara gajiya kada yaje ya dauko mana wata cuta ……"
Kwala mashi kira Aunty Zuby tayi ganin ya biyo budurwar yana bata wani abu da alama kudine ……Sae da ya sallameta sannan ya matso yana fadin "Aunty zuby daga ina haka keda hajiyarmu……"
Hararanshi tayi tana fadin "Ina ka samo waccen shegiyar kuma……"
Dariya yayi yana fadin "Oh Aunty zuby wallahi ba shegiya bace, Baby ce ……Ziyara ta kawo man yanzunnan ……"
Hararanshi ta kuma yi tana fadin "Ka dae kiyayi kanka wallahi ,idan ba haka ba kana zaune cuta zata kasheka ……"
Dariya yayi yana fadin "Haba Aunty zuby cuta bata kasheki sae ni ……"
Banza ta masa suka shige ciki suka barshi
《》《》《》《》
Tafiya yake amma sam hankalinshi ba a gurin kidan dake tashi cikin motar yake ba ……
Solution yake nema ta yarda zai rama rashin kirkin da Maleek ya mashi jiya ……Decision kawae ya yanke bara ya cika mashi kudin shi ba zai mashi wayau ne yace yana jiran wasu kudi ne ,Sai bayan ya saketa shi kuma ya aura sannan ya fada mashi gaskia rungumar da yayi mata ce ta sauran kudinshi ……sannan ko gidan da yake niyar bashi ,takardun fake zai bashi yarda bara su mashi amfani ba ……Wani murmushi ya saki tare da dukan sitiyarin ya ci gaba da bin wakar ……
Wasu tsadaddun yan mata suka tsayar dashi ,tun kafin ya tsaya ya kare masu kallo ,dukansu ba na yarwa ……
Parking yayi tare da rage glass yana fadin "Yane ……"
*FEEDOHM💞*
[7:35PM, 11/8/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
© *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM💞_*
*Devoted to Ummi A'isha👌🏻*
*Bestowed to Aunty Sis💕*
4⃣0⃣
Wata daga cikinsu tace "Can Fadama zamu ko zaka taimaka ka saukemu……?
"Ku shigo ba matsala……" ya fada yana spreading arms dinshi ……tunda suka shiga motar ba wanda ya sake magana har yayi parking sannan suka bude zasu fita ……
Wacce ta fara magana ya kalla yana fadin "Excuse……"Dawowa tayi ta zauna tare da dagawa sauran hannu alamun tana zuwa
Cikin sigar yaudara yace "Har zaki tafi baki fada man sunanki ba baby……"
"Raliyah……"ta fada dauke da murmushi
Duk da gabanshi ya fadi na jin sunan hakan bai hanashi sakin murmushi ba tare da fadin "Wow nice name ……Bani digit dinki mana……" Karanto mashi tayi yayi saving da Baby R sannan yace "Me zakuyi anan ?
Yar dariya ta saki sannan tace "Munzo mu huta ,ko zakayi joining ne ……"
"Wow baby dama kinsan am incomplete wallahi ,Muje kawae ……"ya fada cike da zakuwa……
Bude motar sukayi suka fito tare sannan ta matsa kusa da yan matan ta masu magana ……yanajin suka dauki dariya a tare sannan ta dawo gurinshi ……Receiption suka shiga suka karbi keys guda biyu sannan suka fito ……
Room daya yan matan ne ,Sae gudan room din shida Raliyah……
Shafin badala suka bude shi da ita ,kusan Awa Uku suna abu guda sae da hankalinshi ya dawo jikinshi sannan ya duba ya ga bata kusa dashi ……"Baby ……"ya dan kira sunanta ,amma shiru
Lekawa toilet yayi yaga wayam babu ita sannan inda ta aje kayanta nan ba babu komae ,bai damu ba dan ya saba da harkar yan mata ……ya tabe baki tare da watso ruwa sannan ya dawo ya dauki kayanshi ya mayar ya leka dakin da yan matan suka sauka ko can ta tafi ……
A kulle ya iske dakin shima ,Fitowa yayi waje amma ko alamunsu babu ……Mamaki kwance a fuskarshi don tun da yake harkar da yan mata bai taba samun wacce ta tafi ba tare da ta karbi kudi ba ……"Ke kika sani nonsense ……dama kin tsaya ko kudi kin karba da kin huce takaici ,don ba kara ganina zakiyi ba nonsense ……" ya fada tare da fiddo phone dinshi yayi deleting numbertah ……
《》《》《》《》
"Me ke faruwa Twee ko sun fada maki wani abune da kika shiga ……" Ya karashe maganar tare da rungumota jikinshi
Lumshe ido tayi tana fadin "Sunyi duk wani test amma basu gano komae ba Abdul Maleek sae dae sun bani wani magani sunce nayi amfani dashi zuwa one week a gani …… "ta karashe maganar idonta cike da hawaye ……
"To Sorry karki yi kuka kin ji ko ……"
Gyada kai tayi a hankali tare da kara kwantar da kanta jikinshi "Daki zamu koma ko mu fita ki ga garin……"
Girgiza kai tayi alamun aa sannan ta duka tana fadin "Ka yarda ID card ……"
Kafin ta kai ga dauka har ya dauke ya mayar aljihu yana murmushin yake ……
Ta dade tana kallonshi sannan tace "Bakka da gaskia ne?
Waro ido yayi yana fadin "Me nayi Twee?
"Babu……" ta fada a takaice
Hannunta ya kama suka koma cikin dakinsu ,sannan ya hada mata ruwan wanka tayi ,ya wanke kayan da ta fitar sannan ya dawo ya zauna yana yarfe hannu tare da fadin "Twee ko sannu ko ……"
Cikin wasa ta harareshi tare da fadin "Sannunka na account dinka……"
"Haka kika fada Twee……?
Gyada kai tayi tana tsuke baki
"Zakiyi man bayani Twee……"
"Kai ma din zakayi bayani ne……" Ta fada dauke da murmushi
Tallabe kai yayi yana fadin " What is the screat of your beauty and glamour Twee……"
Banza ta mashi ta janyo wayarta tana kokarin kunnawa ……ganin taki kamawa ya sa ta kalleshi a shagwabe tana fadin "Help me wit your Phone Abdul Maleek ……"
Damka mata wayar yayi a hannunta sannan ya mike ya kunna Tv ya dawo ……
Abba ta kira suka gaisa sossae yana tambayarta ina Abdul Maleeku ……
Sae da ta kalleshi sannan ta kawar da kai tana fadin "Baya nan Abba……"
"Idan ya dawo ki ce ina gaidashi kin ji Safeena ,sannan dan Allah ki natsu yanzu ke ke kasanshi ba shine kasanki ba ,ki tausasa halshenki kin ji ko ……"Gyada kai tayi a hankali tana kallonshi kasa kasa ……
"Zaki gama wayan Twee sae kin fada man dalilinki na man karya……" ya fada yana watsa mata kallo ……
Sae da ta gama wayar sannan ta kira Maryam ,itama sun dade suna fira cikin jin dadi ,Cikin Wasa maryam ta dinga zaro mata magana mai cike da hikima tare da kwatanta mata meye asalin so sannan meye shaawa ……
Sae da sukayi kusan One houe suna waya sannan ta juya zata mika mashi wayar ……
Murmushi tayi ganin bacci ya daukeshi ,sannan ta matsa da kyar ta cire mashi takalminshi tare da safar dake kafarshi ta mayar da kafafuwan saman kujera……
Ta dade tana kallonshi tare da yaba kyawun halinshi ,Ko kadan baya kyamarta shine ke wanke duk kayan da ta bata harta pant shike wankewa duk da tsotsar da ke makalewa jiki amma bai taba cewa a yarda ba ko da ita tace ,Sannan baya jin komae ya kwanta kusa da ita tare da rungumeta har safe haka zai tashi jikinshi kaca kaca kamar shi ke jinin ……
Lumshe ido tayi tare da bashi wani matsayi na musamman a ranta ……Sannan a yarda ta fahimta JB ya rainawa hankali ba sakinta zaiyi ba……
*Lemme See su waye a team dina*
*TEAM JB……ni dae💞💞*
Drop your comment amma yan ™JB kadae 08066598868 ……kar naga ™ ABDULMALEEK Don kun man yawa 😡😡
*FEEDOHM💞*
[9:08AM, 11/10/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
© *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM💞_*
*Devoted to Ummi A'isha👌🏻*
*Bestowed to Aunty Sis💕*
4⃣1⃣
*Gaisuwarku ta dabance Sisters👄 Sawwama,Pherty,Faxy fashion,Maman khadija,Hafsat mai shariff,Billy galadanci,Safiya huguma,Hajjace,Khaleesat haydar,Asmy b,Maryam kaumi ,Muneera,Sanah Matazu,Mrs splendid,,Parrot,Meela Adeel,Jiddah Aliyu……🌹*
Hannunta dake saman kafarshi taji ya kamo tare da bude ido a hankali yace "Why're staring me……"
"Me zan Kallah a nan ……"ta fada tana kawar da kai
Janyota yayi da karfi jikin tare da kwanto da kanta saman kujeran yana fadin "Zo na gwada maki abunda kike kallo ……"
Turo baki tayi tare da mikewa tana hararanshi……Lokaci guda ta dafe kai tare da sakin gigitacciyar kara sannan ta fado jikinshi ……
A rude ya mike zaune ya rike dukkan kafadunta "Menene Safeena ,Fada man,kinji meke faruwa ,Bude idonki ki ganni kin ji ko……" ya fada a gigice ……
Ganin ta cigaba da yin karan ne ya sashi rungumeta sossae tare da tofa mata addu'a ……Jiyayi dukkan jikinta ya saki tana fitar da lumfashi da karfi……
Duk ya gigice yana kiran sunanta "Safeena……
Rungumeta yayi sossae yana tofa mata addu'a har sae da Lumfashinta ya koma dae dae ……
A sanyaye ya dago fuskarta "Menene Safeena……are you Ok?ya fada tare da kura mata ido
Still Razanannar kara ta saki sannan ta hankadashi gefe guda da dukka karfinta tare da mikewa daga jikinshi ……Kujeran da suke zaune tayi baya ta fadi dashi baya……
Kafin ya yunkura ta fice daga dakin da gudun tsiya ……Shima binta yayi har sae da ta kusa fita harabar Hotel din sannan ya samu ya riketa da kyar ……
Duka take kai mashi ta ko ina amma bai saketa ba……Mutanen dake gurin babu wanda yayi niyar taimakonshi don kowa harkar gabanshi yake ……
Dakyar ya samu ya sabata a kafada ya komar da ita dakin tare da saka keys sannan ya direta ……Birgima ta fara a kasa tana wani irin kuka mai cin rai ……
Dafe kanshi yayi ya koma ya jingina da bango idanuwanshi jawur ,shi kanshi da zai samu yayi kukan da yafi samun sauki ……Tunaninshi ya tsaya cak lokacin da wani bakin hayaki ke fita daga jikinta ……
Kara ya saki yana fito da idanu waje ,Tundaga inda yake tsaye ya kai guiwarshi kasa har zuwa kusa da ita tare da tallabota jikinshi yana girgizata
"Nothing will happen to you Safeena ……"ya fada tare da sakin kuka ……Addu'a ya fara tofa mata duk wacce ta fito bakinshi ……Kamar wuta haka jikinta yake saboda masifar zafin da ya dauka amma hakan bai sakashi sassauta rikon da ya mata ba ……
Ganin hayakin bai daina fita ba ya sashi rarrafawa yana rungume da ita ya fito da zam zam din da Malam ya bashi yana shafa mata a dukka jikinta ……
Kusan Minti biyar sannan hayakin ya daina fita daga jikinta sae wani uban duhu da fuskarta tayi kamar an shafa mata charcoal…… ,Lumshe ido yayi hawayen dake makale suka gangaro saman goshinta ……Ta dan jan lumfashi da karfi ……
"Safeena……"
A hankali ta fara bude idonta da suka kada sukayi jawur har ta sauke saman fuskarshi ……
Hannunshi ya daura yana zagaye fuskar tata da tayi duhu ,a hankali ya furta "Are you Ok ……"can kasan makoshi……
Girgiza mashi kai tayi a hankali tana nuna shi da hannu tare da kwace jikinta ta koma ta makure jikin bango……A Sanyaye ya bita har jikin bango ,Matsawa ta fara yi tare da sakin kuka tana girgiza mashi kai da hannu ……
"Kiyi Magana mana Safeena……"ya fada kamar zaiyi kuka ,
Kasa magana tayi sae dae kukan da ta sake da karfi tana girgiza kai ,
"Nine ba kya so nazo gunki Safeena? Ya fada don ya fahimci kar ya matso take nufi
Da sauri ta gyada mashi kai tana kuka ……Lumshe ido yayi yana fadin "To yi hakuri ki bude baki ki man magana, sae na tafi kinji ko……"
Juyawa tayi ta hade kanta da bango tana kuka ,Asanyaye ya matsa tare da dafa bayanta yana kiran sunanta ……
Juyowa tayi ta fara dukanshi da karfi tana turashi ……A sanyaye ya mike ya fara tafiya da baya har ya kai bakin kofa ,sannan ya bude ya fita tare da rufe kofar a hankali ya jingina da ita ……
,Kanshi yayi bala'in daurewa ,Tambayoyine ke zagaye a kwalwarshi wanda ya rasa wacce zai amsa a ciki ,fito da wayarshi yayi ya fada dialing number granny ,Da sauri ya datse kiran yana girgiza kai "No ……"
Ganin tsayuwar bara ta mashi ba ya sashi zaunawa bakin kofar har tsawon awa daya ,sannan ya mike kamar an tsikareshi ya fita harabar hotel din yayo alwala ya dawo ,Sae da ya kunna karatun kur'ani sannan ya bude kofar dakin ya shiga kamar barawo ……
Karkashin gado ya hangota kwance da alama bacci takeyi ,Tausayinta sossae ya darsu a zuciyarshi ya karasa gurin tare da tsugunnawa ya janyota a hankali ,Har ya fito da ita bata farka ba ,Daukarta yayi ya kwantar da ita saman gado ,sannan ya zauna yana kallon fuskarta da tayi kamar an shafa mata charcoal ……
Cikin jikkarsu ya dauko cotton da zam zam yazo yana goge mata fuskar a hankali ,Cikin sa'a duka bakin ya fita ta koma fresh da ita ,Addu'a sosae ya tofa mata sannan ya mike ya rufe dakin ya dawo ya kwanta gefenta ,har lokacin kira'ar sheikh sudais ke fita daga wayarshi ……
Rungumeta yayi sosae sannan ya kashe light ya rufesu da bargo……
《》《》《》《》《》
Uncle Abbah ya shigo falon rike da bakar leda ,Ganin Abban Safeena zaune ya sashi komawa baya ya boye ledar a aljihu sannan ya shigo da sallama ……
"Alhaji barka da wuni……" Ya fada harda dukawa
Cikin Fara'a ya amsa "Barka kadae Abbah ya gurin su hajiyar ……"
"Suna lafiya lau Alhaji sun ma ce a gaidaka……"
Mikewa yayi yana fadin "Madallah " sannan ya bar falon ……Mintina kadan Aunty Fatee ta fito tana hararanshi "Kai shine tun dazu hajiya tace ta aikoka amma dan iskanci sae yanzu kaga damar zuwa……"
"Ance maku ni banda aikin yi ne……Malama dallah ki karba sannan ki kirata ta maki bayani ……"ya fada yana mazurai
Fizge ledar tayi ta juya tana surutai ……
"Ke nufinki bara ki bani kudin petrol ba ……"
Karamin tsoki ta sake ta wuce ta barsa a gurin ,Shima kwafa yayi ya fita yana fadin "Zamu hade ne wallahi ai kar ta san kar ce……"
Sae da ta rufe dakin sannan ta bude ledar ta zazzageta saman gadonta ……Kullin maganine guda biyu a cikin daure cikin takardar nama ……
Tabe baki tayi sannan ta dauko wayarta dake jone a jikin socket ta kira Hajiyar ……
"Ya kawo hajiya……"ta fada jin hajiya ta dauka
"Yayi kyau ,kina ina yanzu ……"hajiyar ta fada
"Ina dakina mana ……"
"Yauwa magani na karbo maki don na gaji da zaman banza Fatee ,ina amfanin zaman da kike babu da babu jika a gidan ……"
Yatsina fuska tayi tana fadin "Kema kya fada……"
"Yanzu ga magani nan kulli biyu ki zuba mashi dukansu a abinci ,Ki tabbatar yaci yau dinnan ……"
"To na meye hajiya……"ta fada a hankali
"Gidanshi na gaskia zai koma……"ta fada kai tsaye
A razane tace "Mutuwa hajiya?
"Kanin ubankine da bazai mutu ba ……" ta bata amsa kai tsaye
,A sanyaye tace "amma hajiya ko ya mutu fa hakkin takaba kawae nake dashi, meye amfanin hakan ?ba kara na zauna ba ko sato mana na dinga yi ……"
"Rufe man baki sakarai ,ai da yake yarda kike banza haka kowa yake ,to bara kinji kina saka mashi yaci ya shure ko motsi bara ya kara ba sannan zaki tattara komae Uncle Abbah yazo ya karba kafin mutane su taro ……"
"Safeena fa Hajiya……"
"Ta mutu……" ta fada a takaice
Yar dariya Aunty Fatee ta saki tana fadin "Yanzu naji batu Hajiyarmu ……"Sannan ta yanke wayar ta shiga wanka ,Mintina kadan ta fito tare da tsantsara kwalliyarta sannan ta dauki ledar ta shiga kitchen da ita ……
Da sallama ta shiga dakinshi yana zaune da computer gabanshi ta duka tana fadin "Abban Safeena baka gajiya da aiki……"
Dan murmushi yayi yana kallonta sannan yace "Ke kuma bakya gajiya da yawo ko……?
Share maganar tayi tana fadin "ka sauko kaci abinci gaskia ……"
"Kin hado man da ruwan zafi ko ……?ya fada yana karewa abincin kallo
"Kaga na manta wallahi ,Amma bara ns zuba maka abincin sannan na tafi na daura ruwan zafin ……"
Da murmushi yace "Thank you ……"
Zuba mashi abincin tayi tana fadin "Ka sauko kaci kafin na dawo dan Allah ,wallahi bana son kana zama da yunwa……"
Rufe computer yayi ya sauko yana fadin " Na sauko hajiyata ……"Sae da taga ya dauko spoon ya saka a cikin abincin sannan ta fita tana waigenshi da murmushi kwance a fuskarta……
*FEEDOHM💞*
[2:17PM, 11/10/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
© *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM💞_*
*Devoted to Ummi A'isha👌🏻*
*Bestowed to Aunty Sis💕*
4⃣2⃣
Aje Spoon din yayi ya mike a sanyaye ya rufo dakin ,sannan ya dawo ya dauke duk wani takardunshi masu mahimmanci da kudinshi dake aje ya kai toilet ya rufo da keys ,sannan ya wurga keys din bayan mirrow ……
Abincin ya debi rabi ya zuba a leda sannan ya bude glass din window ya jefa bayan gida ,Wayarshi ya fito yana dialing number Safeena amma a rufe ,ta Abdul maleek ya gwada har tayi ringing ta katse bai dauka ba……Rufe wayar yayi ya sakata a pocket na wandonshi sannan ya dube dakin ya dawo gaban abinci ya kwanta kamar matacce ……
Turo kofa tayi harda yar wakarta ,ganinshi a kwance ya saka ta tako har gabanshi tana wank girgiza tare da tabe baki "Bikin sallah ……"ta fada tana hambare hannunshi dake cikin abincin
Drawer ta bude ta fito da tilin takardu tana fadin "Idan sunje can sun fitar ……"yana ji ta kira Uncle Abbah tace zata bar takardun a falo idan yazo ya dauka ……
Sannan ta fita da gudu tana ihu kamar mahaukaciya ……Hawayen da yake dannewane suka gangaro mashi na tausayin kanshi da diyarshi ……Hannun riga ya saka ya goge jin tana taho da masu gadin gidan tana fada masu Alhaji ya rasu……
Kukane kwance a fuskarta kai da gani zakayi tunanin hakan ne a ranta ……"Shikenan Alhajina ,Asirina ya tonu na shiga uku ni,Fateema ……"Abunda take fada kenan tana kallon masu aikin dake tsaye cirko cirko ……
A hankali ya fara motsa hannunshi ta yarda zasu gani sossae ,Bala sabon driver tun bayan tafiyar Abdul maleek ne ya zabura yana fadin "Yana motsi wallahi ……"
"Ku kamashi akaishi asibiti dan Allah ……"cewar mai gadi tare da nufoshi ya dagashi ,
Aunty Fatee kam tsaye tayi ta kasa motsi yayin da kukan da take shima ya tsaya cak ,Har sae da su Bala suka fita dashi sannan ta dawo hayyacinta tabi bayansu ……
Da yake balan shi ke driving cikin mintina biyar suka kaishi FMC……
Yarda suka shiga asibitin a rude suna ihu yasa akayi saurim shiga dashi emergency……
《》《》《》《》《》
A wahale ta fara bude idanunta da har lokacin suke jawur ……Daga kai tayi tana kallon Abdul Maleek da idanuwanshi ke lumshe sae dae ba bacci yake ba sae dae karatun Alkur'ani da yake bi a hankali ……
"Abdul Maleek……"ta fada kasan makoshi
Da sauri ya bude idon yana fadin "Twee are you ok……"
A hankali ta gyada kai tare da fadin "Ruwa……" kallon bakinta da ya bushe yayi sannan ya zura hannu cikin dan karamin fridge din dake gefen gadon ya dauko mata bottle din faro ……Yana budewa ta karbi da sauri tare da kallon sama tana shan ruwan ……
Sae da ta kusa shanyewa sannan ta saki hannunta kasan gadon tare da sakin sauran ruwan tana fadin "Abdul Maleek……"
Kallonta yake cikin tausayawa sannan yace "Na'am Twee ya akai ……?
"Headache……"ta fada tana runtse idanu
Gefen kanta ya kama yana fadin "To yi hakuri Sannu kinji ko ……"
Kuka ta saki a hankali tana fadin "Dukan man shi ake Abdul Maleek da karfi ,kace su daina ……"
Rike kan yayi yana tofa mata addu'a har sae da ta fara lumshe ido sannan ya saki yana fadin "Sorry Twee ……"
Tabe baki take tana juyar da kan tare da kiran sunanshi bayan duk wani fitar numfashinta ……Bai gaza ba gurin amsa kiranta ,har sae da ta bari don kanta sannan ta koma baccinta ……Kara gyara mata kwanciyar yayi saman kirjinshi yana bin karatun kur'anin cikin natsuwa ……
Tunda asuba ya mike ya cire da kayanshi da suka baci yayi wanka sannan yayi sallah ,Yana addu'a ta fara motsi da kai a hankali tana kiran sunanshi ……"Abdul maleek……"
Da sauri ya matsa tare da rike mata hannu yana kallon fuskarta da bakinta da ya bushe yayi fari fat ……A hankali yace "Twee menene?ina ke maki ciwo……"
Lumshe ido take tana budewa a hankali tare da kiran sunanshi,Kusan minti biyar sannan ta budesu tar saman fuskarshi tana kallonshi ……"Inna lillahi wa inna ilaihirraju'una……" ya maimata mata a hankali
Ganin ta amsa ya sashi talloba ya zaunar da ita jikinshi "Kiyi wanka kiyi sallah ko Twee……"ya fada a hankali
Noke kafada tayi tana fadin "Abbana Abdul maleek……"
"Na kira maki shi……"ya fada cikin sigar lallashi
Juyar da kai tayi tana kallon bango ba tare da tace komae ba……Wayarshi ya janyo ya kashe karatun kur'anin sannan ya fara kiran Abban amma wayarshi a kashe ……
Kamo Hannunta yayi yace "Twee kinga asuba ce Abba bai bude wayarshi ba ,kiyi hakuri kiyi sallah zuwa safe sai na kira maki shi kin ji ko……"
Kallonshi tayi na yan mintina sannan ta sauke kafufuwanta daga gadon tana kokarin mikewa ……kamar an jehota ta dawo tare da sakin kuka tana fadin "Kafana Abdul Maleek ……"
Saurin duba kafar yayi amma bai ga komae ba ,ya dago yana kallon yarda ta dage tana kuka bil hakki da gaskia ,Dan murmushi ya sake sannan ya cire jallabiyar da yayi da sallah da ita ya aje tare da daukarta ya kaita toilet din ya aje ……
,,Kamar wasa yaga kafafunta na rawa bayan ya ajeta zai juya ,Saurin tallabota yayi jikinshi yana binta da kallon mamaki "Twee me ke faruwa ne……"
Dukar da kai tayi tana share hawayen da suka cika mata ido tare da fadin "Sorry for disrupting……"
Saurin kamo hannunta yayi yana kallon cikin idonta "Look Twee karki kuma fadin haka kinji , ko kin manta har kudi aka bani don inyi jinyarki ……?
Saurin kallonshi tayi ,ya gyada mata kai yana fadin "Yeah 10m ya bani ,ni kuma zan mayar masa da 20m ya barni na kare rayuwata ina jinyarki ……"
Bata san lokacin da murmushi ya subuce mata ba ,jan hancinta yayi yana fadin "Me kike so yanzu ……?
Shiru ta masa tana rufe ido
"Baki iya wankan ne Twee……"ya fada a hankali
"Zan iya ……"ta fada da sauri
"Nima bance zan maki ba ai Twee don ban shirya hakan da JB ba……"ya karashe maganar kamar an mashi dole ,Sae yanzu ma yake kara jin takaicin JB da yake neman,ya miyar dashi kamar wani wawa ,wae ya mashi jinya sannan ya sakar mashi ita ……
"Ka bude man zip din sae ka fita ,Zan san yarda zanyi ……"ta fada a hankali
Lakuce mata hanci yayi sannan ya saka hannu ya juyo da ita jikinshi ya zuge mata zip din ,yana kallon fuskarta ……
Dan murmushi yayi tare da shafar digon bakin dake tsakiyar bayanta sannan ya fita daga toilet din ……
Da kyar ta samu tayi wankan tana kuka ,Sae da ta daura towel ta sa Pad sannan ta kwala mashi kira cikin muryar kuka don yanzu ba laifi jinin ya rage zuba sosae ,kawae idan ta kwanta baccine take bata jikinta ……
"Kuka kikayi ko Twee……"ya fada yana kallon kwayar idonta
Shiru ta masa tana turo baki ,Bisa Abun sallah ya ajeta ya dauko mata jallabiyar da ya cire ya saka mata tare da hijab sannan tayi sallan daga zaune don kafafunta basa tsayuwa sosae……
《》《》《》《》
"Wae kawae sae naga 'ta kwaso na maguzawa ta tankara' _Aunty Sanah matazu ta hanani zagi_ yana motsa hannu ……"cewar Aunty Fatee dake tsaye phydiartric tana waya da Hajiya……
"Sae akae ya kuma ……"hajiyar ta fada cikin,zakuwa
A sanyaye tace "Sae na kaishi asibiti……"
"Anyi Asararki Fateema wallahi,Na Zubaida dan a gida na haifeki da sai ince musayarki aka man asibiti,Banda kila doluwa bara ki ida karashi ba a dakin……"
"Hajiya sae da ba na tattaro masu aiki sannan ya fara motsa hannun ,taya zan karasa shi gaban mutane ……"
"Ke ai ya karasaki dan ubanki ……" ta fada tare da kashe wayar tana sababi ita kadae
Fadila dake zaune ta kalleta tana fadin "Shi Abdul Maleek din bara ya dawo ba tunda boka yace jiya zata rasu……"
A Fusace tace "Sae ki kirashi kiji dan ubanki ,kina ganin wannan banzar uwar taki tana neman ja man asara kina kira man wani Abdul maleek can ……"
Tabe baki Fadilan tayi tare da fadin "Ko tashi asarar yake gani ……" hadi da mikewa tabar mata falon
Abban kam Yana kwance sanye da Oxygen likitan ya shigo zaya debi jininshi ,wanda kusan sau uku kenan ana shigowa ana dibar saliva dinshi tare da jini ……
Bude ido yayi tare da rike hannun Likitan yana mashi alama ya cire Oxygen din ,Da mamaki likitan ya shire yana kallonshi ,Mutumin da aka kawo ake kiran ya mutu amma ya bude idonshi tar yana kallonshi……
A sanyaye Abban yace "Ka fita ka fada masu na rasu……"
"A kan me ……? ya tambaya a razane
"Haka suke so Doctor……Dan Allah ka fada masu zakaga farinciki kwance a fuskar wadda ta kawoni ……"
"Me yasa Kake so ace ka rasu Alhaji "
"Karka damu ……"Ya fada a sanyaye
"To idan suka bukaci gawarka fa ……"ya jeho mashi tambaya
"Sae ku basu wadda a ka nemi mai ita aka rasa……"ya fada kai tsaye
Yar dariya likitan yayi yace "Alhaji basu sanka bane da zamu basu gawar wani ,sannan ba abu bane mai yiyuwa ……"
Shima dariyar yayi mai cin rai sannan yace "Akan abun duniya suke neman halakani ,abunda ni na tare da gumina ba wani ya bani ba ,matar da ta kawoni ni da kaina naji tana waya da mahaifiyarta akan zasu zuba man magani a abinci na mutu ,shine banci abincin ba sae nayi pretending kamar naci ,sae da ta tara mutane sannan na fara motsi har aka kawoni nan ,Akwae aibu don nace ka fa masu na rasu……" ya karashe maganar murya na rawa
Cikin tausayawa yace "I'll prepare anything Alhaji ,Zan basu gawar da aka riga aka nade da likafani ta yarda rufewa kadae zasuyi ……sannan wannan criminal act ne dole a shigar dasu court ……"
"Na riga na shigar da kara likita ……"
"Good Alhaji ,amma yaushe har kayi reporting ko ka saka wani ya maka hope ka bayar da evidence naka……"
Yar dariyar yake ya saki yace "Court dina bata bukatar wani Evidence ,gaban Alkalin akayi komae ,kawae mu jira lokaci ,lokacin da zasu karbi hukuncinsu ……"
Girgiza kai likitan yayi cike da tausayi ,sannan ya fita ya sanar da su Aunty Fatee cewa wanda suka kawo ya rasu ,Sannan zasu shirya gawar zasu basu zuwa anjima kadan ……
Kafin lokaci kadan Asibiti ta cike da mutane ,masu kuka nayi masu dariya nayi , Ciki har da mutanen JB da family na maryam ,Granny kadae ce bata sani ba ……
Idan akace Maryam ba diyarshi bace babu wanda zai yarda a gurin yarda take kuka na fitar hankali ,Mum dinta ce ta fizge wayarta ganin tana neman kiran Safeena gurin tare da fadin "Maryam ba kya son Safeena ne ……"
Cikin kuka tace "Ina Sonta Mummy Abbanta ne fa ya rasu ,shine bara a barni na fada mata ba ……"
"Idan har kika fada mata a haka Maryam ba kya sonta ,sannan bara ta taba mancewa da Kece kika fada mata rasuwar Abbanta ba……"
"To Mummy bani na fadawa Abdul Maleek ko addu'a su mashi dan Allah ……"
A sanyaye ta mika mata wayar ,ringing daya ya dauka yana fadin "Munyi fushi tunda sae yau kika kiramu ……"
"Abba Abdul Maleek ……"ta fada cikin kuka
A rude yace "Me ya sameshi Maryam ……"
Kai tsaye tace "Ya rasu……"
A Razane ya kalli Safeena dake zaune tsakiyar gado tana game ,Suna hada ido yayi saurin barin dakin ya fita waje tare da yanke wayar ……
"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un " ya dinga maimatawa har ya dawo da natsuwarshi Kamar yaro ya tsugunna bakin kofar dakin yana kuka ……Sae da yayi mai isarshi sannan ya goge fuskarshi ya koma dakin ……
Turo baki tayi tana fadin "Da waye kake waya……?
Murmushin Yake yayi yace "Da sweetheart dita……"
Tabe baki tayi ba tare da tace komae ba ,A Hankali ya matso ya zauna saman gadon tare da janyota jikinshi "Sorry……" ya furta da zance biyu ……
"Twee Gobe mu koma gida ko……" ya fada a hankali
Murmushi tayi tace "Kaima din ka gaji ko ……"
Juyo da ita yayi yana fadin "Kalleni Safeena ……Karki kuma fadin kalmar na gaji a bakinki kin ji ko……"
Gyada kai tayi a hankali tana kallon fuskarshi ……
Wayarta tayi kara ganin sunan JB ya Sashi saurin kai hannu ya dauka ……ba tace mashi komae ba sae binshi tayi da kallo ……
*FEEDOHM💞*
[4:05PM, 11/11/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
© *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM💞_*
*Devoted to Ummi A'isha👌🏻*
*Bestowed to Aunty Sis💕*
4⃣3⃣
Wayarta tayi kara ganin sunan JB ya Sashi saurin kai hannu ya dauka ……ba tace mashi komae ba sae binshi tayi da kallo tana murmushi ……
Kamar jira yake a dauka ya ce "Baby Sorry ……Abba ya riga mu gidan gaskia ki dawo gida gobe……"
"To ……" Abdul maleek din ya fada a takaice tare da datse wayar ,yana girgiza kai ……lallae jahilci mugun ciwone da tare suke a haka zai fada mata rasuwar mahaifinta kamar yana fada mata rasuwar mai shagon unguwarsu ……lallae JB Dom ne ya fada a hankali
"Me ya fada ……"ta katse mashi tunani
"Cewa yayi na dawo mashi da matarshi "ya fada yana murmushin yake
"Sae kace mashi me……?ta fada a hankali
"To nace masa Twee……"Ya karashe maganar yana yake
Itama murmushin tayi a hankali ba tare da tace komae ba ……
《》《》《》《》
Cikin mintina kadan aka hada masu gawar da zaa basu suka tafi ,likitan ya koma yana fadawa Abban cewa akwae wata yarinya dake kuka kamar ranta zai fita a waje ……
Yana fadin haka Abban ya gane Maryam ce ,Ce ma likitan yayi ya kira mashi ita a sirrance
Family din maryam likitan ya tsaida har sae sa su Aunty Fatee suka tafi sannan ya shiga da Maryam din office dinshi inda Abban ke aje ……
Dafe kirji tayi tare da waro ido tana fadin "Abba ko fatalwarshi ……"
"Abban dai Maryama ……" ya fada dauke da murmushi tare da mika mata hannu ,Likitan ta kalla taga ita yake kallo dauke da murmushi sannan ta tabbatar da Abban ne zaune ……
Da gudu ta matsa kusa dashi tare da tsugunnawa gabanshi ,cikin kuka take fadin "Abba suka ce ka rasu wae ……"
"Ban rasu ba Maryam kinji ,amma a gurinki ……"ya fada cikin sigar lallashi
"Abba Aunty fatee ma ta dauka ka rasu sae kuka take ,bara na kirata na fada mata ta daina kuka……"
"Kul Maryam a gurinki kadae nake a raye kinji ko ……Karki fadawa kowa ban rasu ba ……"
"To me yasa Abba"
"So suke na rasu Maryam ,shi yasa na basu guri su ci abunda ke cikin duniyar ……"
Kamar yarda ya dauki Safeena haka ya dauketa bai boye mata komae ba Kuka ta dinga yi tana "Allah ya isa Aunty Fatee,Me Abba da Besty suka maki ……"
Rasuwar ta tara mutane yarda baa tunani ,wasu na bakinciki wasu na farinciki ……
Abba kam daga asibitin tasha ya nufa ya shiga motar kaduna……
《》《》《》《》 《》
Takardun da Uncle Abba ya kai hajiya ta zubesu saman gado tana dubawa……
"Zuby duba man wadannan takardun na uban meye wannan yarinyar ta dauko……"ta fada lokacin da ta daga wata takarda dake kumshe da kudin da companyn ya bayar bashi ……
"Wannan ai takardar bashi ce da Alhajin ya bayar……"cewar Aunty Zuby tana hararan takardun……
"Tab ……zo ki gani Hajiyarmu babu ta gida a nan don duk irinsu nake gani ……"
Watse takardun sukayi kasa ,amma babu takardar ko da fili a ciki ,daga ta kudin da ya bayar bashi sae ta kudin da aka biyashi ,Ciki har dae da takardun safeena na primary school……
《》《》《》《》《》
Cikin bacci yaji ana kissing lips dinshi na kasa,kai hannu yayi ya buge bakinshi tare da gyara kwanciya……ji yayi an dallah mashi mari da karfin tsiya ,ya mike a zabure yana waigege rike da kumci ……
"Uban waye ya mareni……"ya fada cikin jarumta amma zuciyarshi harbawa take da karfi ,Jin anyi shiru ya sashi mikewa yana waigege ya fita daga dakin ……
A falo ya iske mum dinshi tana kallo ,ganin yana waigege ya sata kallonshi da sauri tana fadin "Lafiyarka Son…… "
Kai tsaye yace "Ina fa lafiya wani shege ya mareni ina bacci……"
Yar dariya tayi tana fadin "Mari kuma JB? to gaskia babu wanda ya shiga dakinka yanzu ……ko dae mafarki kayi……"
Tsaki yaja yana fadin "Da Allah ni mum bansan jikina bane?to ba wani mafarki ……mari na akayi kuma wallahi sae na mari kowa na gidan nan yau……"
"Allah ya baka hakuri……"ta fada kamar tana tsoronshi
Mikewa yayi ya tattaro duka yan aikin gida daga tsofaffi har yara ya dawo falo……
Babu laifin zaune babu na tsaye ya bisu da maruka bibiyu ,bai dagawa kowa kafa ba……
Sannan suka mike suka tafi cike da takaicinshi ,dama kuma idan da sabo sun saba da halinshi……
《》《》《》《》
"Da gaske gobe zamu tafi gida……"ta fada a hankali tana kallon gefenshi
"Eh Twee kiyi hakuri kinji ko ……"ya fada tare da kwantota a jikinshi……
A hankali tace "To me yasa AbdulMaleek……"
"Kirana akayi baffa baya lafiya……Ko bakya son komawa mu zauna anan Twee?……" ya fada cikin sigar lallashi……
Girgiza kai tayi a hankali ba tare da tace komae ba ,Wayarshi ta hau ringing ya sa hannu ya dauko ganin sunan Abba a jiki ya sa ya mike a hankali tare da zareta jikinshi ya sauka saman gadon ……
Binshi tayi da kallo a sanyaye idanunta suka ciko da kwallah ,Ta saba gabanta yake waya amma daga jiya zuwa yau ya canza gaba daya sae ya fita yake daukar wayar ……Hawaye suka ciko mata a ido ta saka bayan hannu ta share ,wani gefen na zuciyarta ke fada mata ko dae shima ya gaji ne ……Sunan Allah ta furta a hankali kamar yarda taji yanayi tare da kifa kanta a filo ta saki kuka mara sauti ……
Yana Dauka yaji muryar Abba ,a kidime yake tambayarshi shi dinne koko wani ne……
"Nine Abdul maleeku……"Abban ya fada cikin sanyin murya
"Abba kuma maryam ……"
Datse mashi maganar yayi yana fadin "Tace maka na rasu ko Abdul maleeku……?
Gyada mashi kai yake kamar yana kallonshi ……
Shi kanshi Abban yasan mamaki ne ya hada Abdul maleek din magana ……
A hankali ya warware mashi komae,tare da fadin "Ina Maharaja hotel yanzu haka a kaduna……"
Sun dade suna magana sannan Abban ya kashe wayar ……
Cikin Farinciki ya koma dakin ,Shi kanshi ya godewa Allah da bai fada mata ba ,to da yanzu sae yace mata me kuma ?ya tabbata ko gabas da kudu zata hadu barata yarda ba ……
Cikin shauki ya kira sunanta"Safeenah……"
Banza ta mashi tana kukanta kasa kasa……
Shima bai tsammaci zata amsa mashi ba ,ya matsa jikin socket ya saka charge sannan ya shige toilet yayo wanka…… ya fito yana yar waka a hankali……
Tsaki ta saki da karfi tare da kara sautin kukan nata ……Ido ya waro cike da mamakinta ya matsa yana fadin "Twee kukan me kike ……"
Dago fuskarta yayi ya tsaya yana kallonta ……ganin bilhakki da gaskia kukan take kuma da alama ba yanzu ta fara ba ……don daga yanayin idonta zaka gane ta dade tana yinshi ……
"Ya salam Tweena me aka maki……Sorry ki bar kukan ki fada man me ke faruwa?ko na maki laifine……?ya karashe maganar cikin sigar lallashi……
Rungumeta yayi sosae yana lallashinta…… amma taki danka mashi ,lokaci guda duk ya rude idanuwanshi sukayi jawur "Twee bakya lafiya ne "
Banza ta mashi ta cigaba da kukanta ahankali……
"Look dan Allah ki man magana kinji Safeena……Me ke faruwa?wani guri ke maki ciwone Twee……?
Ganin yana niyyar yi mata kuka ya sakata bude baki a hankali tace "Ka gaji Abdul Maleek……"
*FEEDOHM💞*
[2:20PM, 11/12/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
© *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM💞_*
*Devoted to Ummi A'isha👌🏻*
*Bestowed to Aunty Sis💕*
4⃣4⃣
Ganin yana niyar yi mata kuka ya sata bude baki a hankali tace "Ka gaji Abdul Maleek……"
A rude yace "Dame na gaji Twee?
Da hannu ta nuna mashi kanta tana kallon kasa……
Kafadarta ya riko da sauri yana kallonta sannan yace a sanyaye "Ni na fada maki na gaji Twee……?har ga Allah baya son wannan kalmar ta gajiya tana fitowa da ga bakinta
"Look Safeena ……Wallahi Billahillazi kinji na rantse maki da Allah ban taba gajiya da ke ba……"ya fada a hankali
A hankali tace "Ka gaji mana……"
Rumtse idonshi yayi da sauri sannan ya bude yana fadin "Kalleni Safeena…… har rantse maki fa nayi ……"
Shiru ta masa tana kallon kasa ……dago Fuskarta yayi ya hade da tashi yana kallon cikin idonta ……a hankali yace "Kin yarda ban gaji ba Twee……?
Girgiza kai tayi alamun aa ……A sanyaye ya saketa tare da mikewa yana kallonta ……
Kayanshi ya fiddo ya saka ba tare da yace mata komae ba ya dauki wayarshi ya bar dakin……
Jikinta yayi bala'in sanyi ta bi bayanshi da kallo……
Bayan mintina kadan ya dawo rike da leda a hannunshi ,ajewa yayi ya dauko plate sannan ya dawo ya juye kebabs din ciki ya mika mata ba tare da yace komae ba ……
Kin karba tayi ta mayar da kanta kasa ……ko baa fada mata ba ta san fushi yake da ita tunda bai taba mata haka ba ……
Gabanta ya aje mata plate din ya juya da niyar tafiya yaji ta riko hannunshi tare da sakin kuka a hankali tana fadin
"Sorry………"
A sanyaye ya dawo ya zauna tare da rike kafadunta yana kallon fuskarta ,hannu ya saka ya share mata hawayen sannan yace "Ya isa hakanan kinji ko ,Wallahi bana kaunar wannan kalmar na fitowa daga bakinki ,Dan Allah ki daina Safeena……"
Gyada kai tayi tare da kwantar da kanta jikinshi tayi lamo ……
"Tashi ki ci abinci kinji ko……"ya fada tare da dago kanta
Wayarshi ta fara ringing ya mike yana fadin "Bari na dawo kinji Twee……"
Hannunshi ta rike gam tayi rau rau da ido
"Dawa kake waya tun dazu kake fita ……?ta fada har da dan guntun hawaye
Haka kawae ya samu kanshi da farincikin tambayar da ta mashi ……Shirun da yayi yana kallonta ya sata sakin hannun nashi tare da komawa ta kwanta ……
"Abba ne Twee……" ya fada tare da dagota
Ba ta kalleshi ba tace "Shine kuma sae ka fita……"
"Bude idonki ki kalleni Safeena ,dama shi yasa kike kuka dazu ……?ya fada yana aika mata da sanyayyan kallo……
Bude idon tayi tana kallonshi da fararen idanuwanta wanda ko da tayi kuka mintina kadan zasu juye su koma fararensu ……
Tun daga farkon wayarshi da Maryam har zuwa Wayar da sukayi da Abban ya fada mata cikin natsuwa da sigar lallashi ……
Abunda yake gudu shi ya faru don kuka ta sake mashi bata yarda ba Abbanta na raye ……Ita bata yarda ba……
"Baki yarda dani bane Safeena?ya fada kamar zaiyi kuka
Fuskarshi ta rike da hannayenta tana girgiza mashi kai "Abbana Abdul maleek……"ta ke fadi kamar numfashinta zai bar jikinta
"Wallahi Allah yana raye Safeena ……bai ci abinci da ta bashi ba……"
"Ni dae ban yarda ba ka kaini gurin Abbana shi kadae nake dashi Abdul maleek dan Allah……"
Wayarshi ya dauko ya kira Abban akayi rashi saa,wayar tashi a katse ……Abincin ma kin ci tayi ,Dole ya tafi ya nema masu private jet da zai maidasu gida da safe ……
Ko da ya dawo kukan take kamar ranta zai fita ,Kasan carpet ya zauna tare da kura mata ido ,kamar wasa yaji hawaye na bin kumatunshi……
……A hankali ta sauko daga saman gadon tare da dawowa kusa dashi ta rungumeshi sosae tana fadin "Ina Son Abbana Abdul maleek Shi kadae nake dashi sae granny ……Mamina ta rasu sannan Hassanata ma ta rasu ta barni…… dan Allah ka kira manshi Abdul maleek……"
Rungumeta yayi sosae yana kara trying number Abban ,ji da yayi ta shiga ya sashi dagota tare da kanga mata wayar a kunne ……
Sun kusa awa biyu suna magana Da Abban,banda lallashinta babu abunda yake ……Dakyar ta yarda ta aje wayar sannan ta kalli Abdul maleek din tace "Anya Abbana ne Abdul maleek ……?
Kuka ko dariya ya rasa abunda ya dace yayi ,Ita da ta gama waya Da Shi amma take tambaya ko shine da gaske ……Harara ya sakar mata yace "Bansani ba……"
Hawaye ya gani sun taru a idonta ,yayi saurin rungomota yana fadin "Allah ya baki hakuri Twee ,wallahi shine ko anayin muryar mutun sak ne……?
Girgiza kai tayi a hankali ……
Duk da hakan bai sa hankalinta ya kwanta ba ta mike ta fara hada masu kaya ……
"sluggish girl……da cewa nayi Twee tashi kije can ki dawo…… kuka zaki man kice kafarki zai kare……"ya fada yana kashe mata ido
Littafin dake hannunta ta wurgo mashi cike da kunya tana fadin "Ai kaine ke cewa bana iyawa ko nace na warke……"ta karashe maganar tana turo baki
"Ba wani nan ……Ke dae kawae slothful lady ce……"ya fada yana kwaikwayon muryarta
Hararanshi tayi cikin salo da jan hankali sannan ta dan cije lips dinta na kasa ta cigaba da abunda take……
《》《》《》
"Wallahi zuciyata ke masifar tashi kwana biyun nan……"cewar hajiya tana yatsina fuska
"Kisha magani mana Hajiyarmu……"Cewar Aunty zuby tana kokarin daukar gyalenta da ke saman gadon hajiyar ……sannan tta kara da fadin "Bara mu je mu dawo don na lura fadila bara ta barni na zauna lafiya ba indae ba ganin yaron nan ya dawo tayi ba……"
Bata fuska tayi tana toshe hanci sannan tace "A dawo lafiya……"
【】
"Boka ka tabbata ta rasu ,kuma yaronnan har yanzu bai dawo ba……"Aunty zuby ta fada dake durkushe gaban boka……
Dariya yayi yana fadin "Ta dade da mutuwa ……don aljanun da muka tura mata ba kanana bane suna tafiya ne da wuta ,duk wanda suka raba sae sun konashi …… Maganar dawowarshi kuma Yarinyar ta shigo mu dubata yau dinnan zai dawo in dae bukatarmu ta biya ……" ya karashe maganar yana kallom kirjin Fadila
Su duka biyun suka mike daga tsugunnin da suke suna kallonshi cike da tsaro ……Aunty zuby kam bata tunanin zata yarda boka ya sadu da diyarta ,haka ita fadilar ke ji bara ta yarda wannan kazamin ya rike ko da hannunta……
"Ki jiramu daga waje……"Cewar bokan yana nuna Aunty Zuby
Kallon uku saura kwata fadila ta mashi cike da jarumta tace "Idan ta jiramu kayi uwar me dani……"
Kafin ta rufe baki Aunty Zuby ta amshe "Fice mu tafi fadila wallahi baran taba yarda wannan mummunar halittar ya kusanceki ba,Har yanzu ina sonki ban shirya kwasar takaici ba ……"
Dariya ya saki da karfi yace "Ita Uwar taki da ta yarda na kusanceki bata kaunarki ne ……"
Fadila ta bashi amsa cike da tsiwa "Uban me ya shafeka da uwarta ,wannan ita taji zata yarda amma ni tawa uwar bara ta yarda ba ……Dama sae da na fadawa hajiya wannan tsinannen bokan babu abunda zai iya amma ta nace tace ya iya aiki ……Mummy dallah mu tafi tun kafin na kifar da shegun tukwananshi……"
Tunda Boka yayi maganar jikin Aunty Zuby yayi sanyi har sae da fadilan ta jata zasu fita sannan ta dawo hankalinta ……
Duka dakin ya dauki ihu kamar zaya tsage cikin wata irin murya bokan yace "Jeki yarinya ku tafi ke da uwar taki muga me zaki amfana mata……JELILI ka sakar mata mafi munin cuta har tsawon rayuwarta ……"
A fusace Aunty Zuby ta juyo tana fadin "Ta Allah ba taka ba tsinanne……"
"Kin san da Allah kika zo nan ……"ya fada cikin karaji……
Dan karamin tulun dake gefen hannun Fadila ,ta juya tare da takeshi da takalminta tana fadin "Na fi karfin ka tsinanne ……"
Fashewar tulun yayi dae dae da karar da bokan ya saki tare da yanke jiki ya fadi kasa ……Wani jinine ya fara fitowa daga jikin tulun yana nufar gurin da bokan yake kwance ……
Sannu sannu har ya fara mamaye dakin ……Da sauri Aunty Zuby ta fizgi fadila suka bar dakin suka fada mota ……
A motar maganar bokan ke ta yawo a kanta ,Kenan hajiya ba santa take ba tunda har ta bari boka ya kusanceta ……
Wawan birki Aunty Zubyn ta taka ganin guguwa tayo kan motarsu ……Addu'a ta fara nema amma duka sun bace mata tunda dama ba iyawa tayi ba ……da kyar ta kakaro "INNA NAKAFU MIN RABBANA YAU MAN ABU SANKAM DARIRI……"
Cikin dakewa Fadilan tace "Mum karki jira ki tada motar mu tafi kawae aikin wannan shegen bokan ne……" Bata rufe baki ba taji kamar ruwa na fita daga karkashinta da sauri sauri……
A Rude ta saka hannu ta laluba pant dinta lokaci guda tana kallon Mum din a kidime "Muje mum karkk tsaya ……"ta fada cikin tsawa ……
Kunna motar tayi zata bi ta cikin guguwar ta wuce ,Kamar an fizge motar daga hannunta haka taji sannan tayi ta juyi dasu cikin daji ……
Cikin kidima Fadila ke fadin "Mum kiyi Addu'a mana sannan ki rike motar kin tsaya kina kwalalo ido ……"
"ALLAHUMMA INNI A'UZUBIKA MINAL KUBSI WAL KABA'ISI……"Abunda ta fada kenan tare da balle marfin motar zata fita……
*FEEDOHM💞*
[12:40AM, 11/13/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
© *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM💞_*
*Devoted to Ummi A'isha👌🏻*
*Bestowed to Aunty Sis💕*
4⃣5⃣
ALLAHUMMA INNI A'UZUBIKA MINAL KUBSI WAL KABA'ISI……"Abunda ta fada kenan tare da balle marfin motar zata fita
Bala'in da suke ciki bai hana fadilan cewa "Amma mumy kinji kunya duk da bana zuwa islamiyya amma Umman Safeena ta taba fada man addu'ar shiga toilet ce wannan……"
Kafin ta rufe baki Aunty Zubyn ta bude motar ta fita ……Har lokacin motar bata daina juyi ba don haka ta bi ta kafar Aunty zubyn ta cigaba da juyi a sama……Kusan minti Talatin fadila na ciki tana ihu Aunty Zuby kuma kafarta tayi daga daga ……
Motar ta tsaya cak don kanta ……sannan fadilan ta samu ta fito tana tangyadi tare da kwarara amai ……
Bata lura da Kafar Aunty Zubyn ba ta zauna tare da dafa kafar tana rike da ciki ……
Ihu Aunty Zubyn ta saki tare da janye kafar da sauri……
Kallon kafar tayi tana fadin "Mumy ai ke kika ja kanki da kin tsaya da kafarki bata ji ciwo haka ba……Amma shine kika fito ki ka baroni wato duk abunda zai faru dani ya faru ko?Allah ya kara ai……"ta fada har lokacin tana amai
Juyar da kai Aunty Zubyn tayi tana hawaye ba tare da tace komae ba ……
Dakyar Fadila ta mike ta je bakin titi ta samo wani mai mota aka dawo aka saka Aunty Zubyn sannan suka tafi gida ……
Tsaki mai motar yayi lokacin da fadila ta fita yana fadin "Haba hajiya kin san kina da matsala kuma sae ki zauna man gaban mota ……"
Kallon gurin tayi sannan ta kalli bayan rigarta tare da sakin tsaki " Sae ka aje motar kaga idan ba'a wanke maka ba banza jarababbe sae kace ba cikin jini uwarshi ta haifeshi ba……"
Cike da mamaki yace "Daga taimako ……?
Bata jira shi ba tayi cikin gida ta bar Aunty Zuby da mai motar ya fiddo ya juya ya tafi yana yaba rashin kunya na fadilan……
Asibiti aka kaita Cewa akai kafar barata ta gyaru ba sae dae a yanketa gaba daya ……A sanyaye hajiyar tace a yanke ……
《》《》《》《》
A kaduna suka sauka ……
Sannan suka kira Number Abban ya fada masu room number da yake ……
Safeena na ganinshi ta kwace hannunta daga na Abdul maleek ta nufeshi da gudu ta rungume tana kuka ……
Shima kanshi Abban kuka yake kamar karamin yaro ……
Abdul maleek dinne yayi jarumtar lallashinsu har sukayi shiru ……sannan Abban yace su tafi Katsina su sauka gidanshi ……
Ya fada mata inda ya jefa keys din da inda takardun suke yace ta dauke…… shima yana nan zuwa nan da dan lokaci kadan ……
Mota daya suka dauka daga ita sae shi a baya ……
Hancinta yaja da karfi ganin tunda suka baro gurin Abban bata mashi magana ba ……
Yar kara ta saki cike da shagwaba sannan ta kwantar da kanta a kafadarshi tana hararanshi kasa kasa ……
"Twee nayi laifine ……?
Banza ta mashi ta lumshe ido kamar tana bacci ……Hannu ya saka ya shafi gefen wuyanta a hankali tare da mintsinawa ……
"Biyu kenan ……"ta fada bayan ta saki yar kara
"Ke ce Twee kinki kulani ……"ya fada tare da kwantar da kanshi saman kanta
"Shine sae ka mintsine ni ……"ta fada a hankali
"To yi hakuri……"
Shiru ta masa ganin driver ya maido hankalinshi kansu……
【】
Kamar yarda Abban ya fada gidanshi suka sauka harda Abdul maleek ……da yake darene babu koma kofar gidan yana rike da hannunta har tsakiyar falon ……
Hannunta ya saki ganin Aunty fatee tana saukowa daga saman benen tana waya ……,Kallonshi Safeena tayi tare da matsawa sosae jikinshi ……
Aunty Fateen bata lura dasu ba har sae da ta sauko falon sannan ta lura da safeenar…… tayi saurin datse wayar tana kallon Safeenar cike da tsoro ……
"Ke Safeena ke ce ……"ta fada arude tare da nunata da hannu ……
Kwantar da kai tayi tana jefa mata kallo sannan tace "Na canza maki ne……"
Kuka Aunty Fatee ta saki tana fadin "Baki canza ba Safeena ……"
Tabe baki tayi tana kallon Abdul maleek ……
Kusa da Ita Aunty Fatee ta matso cikin kuka tana fadin "Safeena Asirin mu ya tonu Allah ya dauke mana Alhaji Safeena kaiconmu Diyata……"
"Kaiconki dai Aunty Fatee ……Ubanki ya rasu ……to meye a ciki idan Abbana ya rasu?Allah ya ji kanshi ……"ta fada tare da jan hannun Abdul maleek suka shiga dakin Abba dake bude ……
"Shiga ki gani wallahi da gaske nake Safeena ya rasu ……"Cewar Aunty fatee tana jan majina ……
Rufe kofar sukayi ……Wani bakin ciki ya tare mata makoshi ganin an watsa komae na dakin da alama takardun ake nema ……
Girgiza kai tayi a hankali hawaye suka biyo mata a kumata
"Shiiii ……"ya fada tare da daura hannunshi saman lips dinta
Hadiye kukan tayi ta koma ta zauna tana kallon Abdul maleek dake kokarin janyo Mirrow ……
Aunty Fatee kam suna shiga dakinta tashiga ta kira Hajiyarsu amma har ta kare ringing bata dauka ba ……JB ta kira cikin saa yana kusa da wayar ya dauka
"Safeena ta dawo kuma ta warke Jabir ……"Abunda ta fada kenan ta datse wayar sannan ta fito waje ……
Fitowa sukayi dauke da jikka A hannun Abdul maleek ……da sauri Aunty Fatee ta tare tana fadin "Ina Zaki da ita Safeena meye kika kwaso ……?
"Kudinsa ne da takardunsa ……"ta fada kai tsaye
Cikin rudu tace "taya zaki kwashe kudin bayan bake kadae ke da gadonsa ba……"ita kanta Aunty fatee ji tayi kamar an fizgo maganar daga bakinta ……
"BARRISTER ABDULMALEEK AHMED……Lauyan Alhaji ina da hurumin da zan kwashe duk wasu kaddarorinshi tare da sa hannun kuto har zuwa lokacin da zaa raba maku gadon……" Abdul maleek ya fada tare da fito ID card dinshi dake dauke da kyakykyawan hotonshi cikin rigar lauyoyi……
Amsar ID card din tayi ta buda ,bata yi mamaki ba tunda dama tasan Barrister ne tun da dadewa ……mika mashi tayi ta juya a sukwane ta koma daki ……
Kallon Safeena yayi da ta bude ido da baki tana kallonshi ……kunnenta ya kamo ya rada mata "Duk burga ce Baby ……"
Dariya tayi don ta yarda burgarce sae dae ID card din da ya nuna fa?
Dakinta ta shiga ta dauko makullin motarta don tun lokacin da maigadi ya batashi tare da takardar da yace Abdulmaleek ya bashi bata kuma bi ta kanshi ba……
Mika mashi keys din tayi suka bar falon ……
A Mota ta kalleshi a hankali tace "Ina ……"
Katse ta yayi yana fadin '"Ina na samo ID card ko……?
A hankali ta gyada mashi kai tana kallonshi ……
"Copy ne jiya da muka sauka nasa aka man printing tare da lamination ……"Sannan ya kalleta yana fadin "Muje gidanmu mu kwana ko?
Dan murmushi tayi tana gyada kai ……
Bayan yayi Parking kofar gidansu ya juyo da murmushi a fuskarshi yace "Kinga gidanmu Madam ……zaki iya kwana kuwa?
Hararanshi tayi tare da bude marfin motar ta fita ……bin bayanta yayi har ta shiga zauren ya riko hannunta yana fadin "Sae ki baroni Twee……"
Banza ta mashi tana kokarin zame hannunta daga cikin nashi ……a kunnenta ya matsa yace "Sorry……"
Fuska a daure tace "Ka gyara maganar da kayi sannan ……" ……
Lumshe ido yayi sannan yace " Safeenata zata kwana gidan Baffana ……"ya fada cikin wata irin murya ……
Kallon juna sukayi tare da murmushi lokaci guda wanda su kadae suka san fassararshi……
Inna sahu ta karbeta hannu bibiyu ……sae da suka zauna sannan yace bara yaje ya dawo ,Jikkar gaba daya ya aje bayan dakin Baffa cikin kejin kaji sannan ya daura buhunnan taki a sama tare da tsummuna……
Ya Tabbata tuwon dawa inna sahu tayi ……Fita yayi ya sawo mata Chips da Tabouleh gefe guda ……
Sannan ya dawo ya iske har Inna sahu ta kawo mata tuwon da miyar kuka tsanwa shar da ita bata fara ci ba ……Suna fira da Nana da tunda ta dawo ta gane Safeenar ta makale mata ……
Gabanta ya aje sannan ya zauna yana kallon yarda ta sha kunu tare da janyo langar tuwon ta fara ci ……Bai ga fuskar cewa taci abunda ya sawo mata ba Har taci tuwon ta koshi ba tare da ta kalleshi……
【】
JB yana kwance da sabuwar yarinyarshi Aunty fatee ta kirashi ……
Mikewa yayi zumbur yana kokarin mayar da rigarshi ……Yarinyar da ta riga tayi nisa a bukace take dashi tayi saurin riko hannunshi……
"Baby ina zaka please……?ta fada idonta a lumshe
"Sorry baby…… Feenata ce ta dawo yau zanje na ganta ……"ya fada yana kokarin daukar wayarshi
"Karka man haka Jabir wallahi a bukace nake kaima ka sani ……"ta fada idonta cike da kwallah ……
Hannunshi ya fizge yana hararanta "Meye nawa a ciki ……"
"Da kasan zaka man haka da baka tado man da feelings ba ,dan Allah ka taimaka man karka barni haka JB……"ta fada hawaye cike da idonta
Kallon uku saura kwata ya mata tare da fiddo kudi cikin wallet dinshi ya aje mata "Duk yarda zakiyi kiyi ki samu natsuwa ……dama na fada maki inada wadda nake so kuma ta dawo …I wishes you all the best baby………"
Girgiza kai tayi a hankali tana kallonshi har ya bar dakin sannan ta mike tsaye saman gadon tana girgiza ……Maciji ta koma bakikkirin tare da silalewa ta window ta fita ……
*FEEDOHM💞*
[4:52AM, 11/13/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
© *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM💞_*
*Devoted to Ummi A'isha👌🏻*
*Bestowed to Aunty Sis💕*
*SISTER SAWWAMA HERE'S YOUR CHPPY DEAR ENJOY❣*
4⃣6⃣
Gurin Aunty Fatee ya wuce a tunaninshi Safeena tana gidan ,Ko gaisawa basuyi ba ya tambayeta "Ina Feena din ……?
Tabe baki tayi tana fadin "Sun fita amma na tabbata gidan hajiyarsu ta tafi ……"
Mikewa yayi yana fadin "Bara naje can na samesu ……" bata ce mashi komae ta sae binshi da kallo da tayi ……
A gidan Granny ma wayam ya iske don cewa tayi bata san ma sun zo ba ……
Wayar Safeenar ya kira amma a kulle……
Ta Abdul maleek din ma a kulle ,karamin tsoki ya ja sannan,ya mike ya fita ba tare da bankwana ba ……
Da kallon Mamaki granny ta bishi a ranta take fadin ……Meye ruwanshi da dawowarsu zai rude haka ……
A Bakin motarshi yaga budurwar da ya baro ……tsaye tana jiranshi a fusace ya karasa yana fadin "Uban me kika biyoni na maki anan……?
Shiru ta masa tana kallonshi ……
"Nonsense ……"ya fada tare da bude motar zai shiga ……
Rike hannunshi tayi tana fadin "Kaine mutumin da ka fara kusantata Jabir …kuma dole ka aureni…"
Dariya ya sake yana fadin "Amma baby baki da hankali taya zan iya auren macem da na kusanta a titi?
"Amma kasan kaine mutumin da ka kauda man budurci ko……?
"Wannan ba abunda ya shafeni bane Baby na maki dole ne……ko ba ke kika kawo kanki ba……"bai jirata ba ya shige mota ya barta ……
《》《》《》《》
Sae da yayi wanka ya shirya cikin riga da wando sannan ya shigo gidan ……duk tunaninshi bata tashi ba yanzu amma yana kutsa kai ya ganta tana wanke wanke Nana na mata dauraya
Bata fuska yayi sosae sannan ya karasa gurin yana hararan Nana ……babu shiri ta mike ta bar gurin ……
Kafarshi kawae ta kalla ta cigaba da abunda take ……Ganin tsakar gidan ba kowa ya sa ya Dagota karfi yana hararanta ……
Turo baki tayi tana hararanshi kasa kasa tace "Meye haka ……?
"Ki wuce ki koma daki ……"ya fada babu alamun wasa a fuskarshi
Kallonshi tayi sannan ta dauke kai tare da komawa ta cigaba da wanke wankenta ……
Daki ya shiga ya dauko mata hijab dinta tare da jikkar kayansu sannan ya fito yana fadin "Inna mun tafi zan maidata gida ……"
Inna Sahu ta fito tana fadin "Da safe haka Abdul maleek ka tsaya a kawo mata koko mana wallahi tun dazu na aika a sawo mata basu dawo ba……"
"Hajiyarta ta kirani yanzu idan munje can tayi kalacin ……"ya fada tare da daura mata hijab din saman kafadarta yayi gaba ……
A sanyaye ta bi bayanshi ,inna sahu ta biyota tana mata addu'ar a sauka lafiya ……
Bayan motar ta bude ta shiga tana turo baki ……Bai ce mata komae ba ya tada motar……Har sae da yayi parking Layout gaban wani katon gida ……Sannan ya juyo yana kallonta na yan mintina "Twee Fito muje ……"
Ba ta dago kai ba haka bata tanka ba ……Bude motar yayi ya fito ya dawo bayan ya zauna tare da kamo hannunta ……
"Twee Dan nace ki bar wanke wanken shine kike fushi ……"ya fada a hankali
Banza ta mashi tana kallon kasa……
"Kin taba yin wanke wanke a rayuwarki safeena ……?
Kallonshi tayi a hankali sannan tace "Idan ban taba yi ba sae aka ce maka ban iya ba kuma……?
"Allah ya baki hakuri ……mu shiga ciki, Tunda Asuba JB ke kirana ……Na fada mashi yazo nan ya iskeni ……"
Kallonshi tayi tare da fadin " Gidan waye nan ?
"Gidan da JB ya bani ne Safeena ……"ya fada yana kallonta
"Kenan zaka sakeni……? ta karashe maganar kasan makoshi
Kallonta yayi na yan mintina sannan ya bude motar tare da jan hannunta suka fita ……Kamar yarinya take binshi tare da kallonshi har suka shiga wani katon falo sannan ya zaunar da ita yana lumshe ido ……
Kujeran kusa da ita ya zauna ……Ya fito d a Envelop guda biyu daga cikin aljihunshi ya aje saman hannun kujeran tare da mayar da kanshi ya kwantar ……
A Sanyaye take binshi da kallo tare da karewa ilahirin falon kallo……Sam hankalinta baya ga tsaruwar falon yana ga Envelop din da Abdulmaleek ya aje ……
Wayarshi tayi kara ya dauka tare da fadin "Kashigo……"a takaice ……Sannan ya juya ya kalleta tare da mikewa ya koma saman hannun kujeran da take ……
"Ko kina sona Safeena……? ya fada kamar yana mata rada ……
Duk da faduwar da gabanta yayi hakan bai hanata sake mashi harara ba tana fadin "Bana sonka ,idan ka tashi kaman saki dari …Hakan ba zai sa na koma hannun JB ba"
Yar dariya yayi tare sa kissing goshinta don ya gano tsatsar kaunarshi a idonta "Sha kuruminki Twee uku kadae zan maki ,amma ki daure ki koma gurin JB kinga kudin da ya bani fa suna da yawa sannan ga katon gida……Dan Allah madam bai burgeki ba…… sae dae ban sani ba ko bakin ciki kike man ……"
Karamin tsaki ta saki tare da mikewa tsaye tana fadin "Idan na san wannan abun zakayi da ban biyoka ba ……bani takardar na tafi……"ta fada tana mika mashi hannu
Dariya yayi yana fadin "Twee ki bari ya zo man na damka mashi amanarshi a hannu mana……"
Bata saurareshi ba ta nufi kofar fita…… bin bayanta yayi yana dariya da envelop din yana fadin "Allah ya baki hakuri Twee ga takardar taki……"
A fusace ta fizge envelop din tayi gaba tana kokarin danne kukan dake niyar subuce mata ……
Aharabar Gidan sukayi karo da JB ……kamar sakarai ya saki baki yana kallonta tayi wani fresh da ita "Beaut……"ya fada yana shafar sumarshi……
Ganinn hawaye a idonta ya sashi fadin "Meye na kuka Fennat?Ke da ya kamata kiyi farinciki *ZAN RAYU DAKE* yanzu baby……"
Kallon da ta watsa mashi ya makale sauran maganar……sae da ta fito titi sannan ta samu abun hawa ……
Gidansu Maryam ta nufa kai tsaye……
【】
"Good Job……"JB ya fada tare da mika mashi hannu……
Murmushi yayi mai sauti sannan yace "Ka ganta ne ……"
"Yeah na ganta da takardarta a hannunta yanzu da zan shigo ……Naji dadi sossae Abdul maleek kayi man abunda banyi tunani ba …… "
"Eyeh ……Karka damu " ya fada tare da daukar wayarshi yana latsawa
"Ina Copy na takardar da ka bata?
Envelop din dake aje ya mika mashi hankalinshi naga wayarshi ……
Karba yayi ya aje sannan yace "Sae dae kayi hakuri Abdul maleek wallahi kudin da nace zan baka basu samu ba……dama companyn mu na sayar to har yanzu ba'a bamu kudin ba sae zuwa karshen month dinnan zan turo maka ……"
Yar dariya ya saki yana fadin "Karka damu"
Dariyar mugunta yayi sannan ya bude envelop din ya fito da takarda guda biyu ta sama an yi rubutu dan gutun :【NI ABDULMALEEK AHMED BAWA BAN TABA TUNANIN ZAN IYA SAKIN MATATA SAFEENA BA ……INA MATUKAR KAUNARTA TA YARDA BAZAN IYA RAYUWA BABU ITA BA ……MALAN JABIR GA CHEQUE DIN NAIRA MILLION 20 NAN NA LINKA MAKA KUDINKA…… KA BARMAN SAFEENA MU KARE RAYUWA DA ITA……】
Wata wawar shakara ya wa Abdul maleek din yana fadin "Wallahi baka isa! sae ka sake man Matata ……"
Tunkude JB din yayi yana fadin "A tunaninka kowa wawane kamar ka Jabir?Tun ina shekara biyu nake zuwa islamiyya kuma har yanzu ban daina zuwa neman ilmin ba ……Malan jabir ko da na auri Safeena banyi niyar sakar maka ita ba saboda ina mata son da kai baka mata…… kasan meye AUREN KISHIN WUTA?na tabbata amsar bata wuce aa ……to Abdul maleeku yasan me ake nufi AUREN KISHIN WUTA sannan yasan meye makomarsa ……Kana fadin *ZAN RAYU DAKE* amma ka kasa jinyarta na dan lokaci ……a hankan zaka rayu da ita Jabir?Sannan saboda batan basira ka rasa wanda zaka ce ya auri Safeena sae Ni Abdulmaleek ?har ma na maka jinyarta ta warke sannan na sakar maka ita kamar wani sakarai?………Kasan tsawon shekaru nawa na dauka ina lallashin soyayyarta Jabir?Sannan na sameta cikin sauki na saketa kamar wani mahaukaci sabon kamu?zauna kayi tunani da kyau JB……"
Kara shakareshi yayi yana nushinshi da karfi……
"Wallahi sae dae mu duka mu rasata……" abunda yake fada kenan ……
Tun Abdul maleek yana kokarin kauce dukan da JB ke mashi har ya fara ramawa ganin abun ba mai karewa bane ……
Dambe sukayi sossae kamar bara su rayu ba ……sae da suka daku dan kansu sannan suka rabu kowane ido kamar garwashi……
JB ya nunashi a harzuke yana fadin "Wallahi sae ka sake……"
"Wallahi baran saketa ba……"
*FEEDOHM💞*
[5:35PM, 11/13/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
© *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM💞_*
*Devoted to Ummi A'isha👌🏻*
*Bestowed to Aunty Sis💕*
4⃣7⃣
"Mu zuba mu gani ……Waye ubanka a garinnan?me kake takama dashi……?cewar JB din
"Ba wanda nake takama dashi sae kaina ……Uba kuma bandashi ,kai kuma da kake takama da ubanka ,zamu gani idan ya isa ya sani sakin Safeenah……"
"Safeena tawa ce ,idan ba haka ba kowae zai rasa……"
"Kaine ka rasata JB……"
A fusace JB ya bar Gidan yana fadin "Kowa zaya rasa wallahi babu wanda ZAI RAYU DAKE SAFEENAH……"
Banza yayi dashi ya zube saman rug yana mayar da numfashi ,tun tasowarshi bai taba dambe irin haka ba ……Dan karamin tsaki yaja sannan ya mike ya shiga dakin dake kallon falon ……
Toilet din ta bude ya sakarwa kanshi ruwan zafi na tsawon awa saya sannan ya fito ……Allah ya taimakeshi ya aje kaya a gidan ya dauka ya saka sannan ya shigowa da Safeena motarta ya fita da tashi ……
Gidansu ya koma ya dauko jikkar da ya aje bayan dakin Baffa sannan,ya kaita bank ya aje ya wuce office dinsu ……
《》《》《》《》
Fadila ta kalli Aunty Fatee tana fadin "ni fa Aunty fati ba lokacin period dina bane amma sae bleeding nake ……"
Kallonta tayi tace " Ko dae kin manta lissafine……"
Tabe baki tayi tana ware kafada sannan ta kalli hajiya dake zaune gaban,gadon Aunty Zuby tace "Hajiya har kin karbo test din……?
Girgiza kai tayi tana fadin "Sunce idan idan,sun fito da result din sister baraka zata kawo mana ……"
Da sauri Aunty Fatee tace " Wae hajiyarmu tun yaushe baki jin dadin ni ban sani ba……"
Hararanta tayi tace "Dama yaushe zaki sani tunda rabon da na ganki tun bayan rasuwar mijinki kina can kin saki baki ,takardun ma kinki ki nema……"
Ta bude baki zatayi magana Sister baraka ta shigo rike da result din ……Aunty fatee ta karba tana dubawa ……lokaci guda ta saki kara tana fadin "CIKI HAJIYA……"Uban kuka ta saki tana cigaba da fadin
HIV/AID :Positive
HEPATATIS:Positive
Shikenan mun shiga uku Hajiya mun lalace ……
Yanke jiki hajiyar tayi ta fadi a sume ……
A Yashe aka dauketa aka bata gado ……
Kusan awa daya ta farka sae dae barin jikinta baya amfani ,a rude Aunty Fatee ta je ta fadawa Nurse din suka shigo tare ……
Duk Wani test da zasu mata su kayi suka tabbatar da paralysis ya kama hajiyar ……
Ko da ta farka da "Na shiga uku ni Shafa ……Ina na samu Ciki" ta bude ido
"Gurin Boka" Aunty zuby da ta farka lokacin ta fada tana kuka ……
Aunty Fatee ta saki kuka tana fadin "Muke da shiga uku Hajiyar ace uwarmu da cikin shege……"
Fadila kam mikewa tayi ta shiga toilet tare da cire dankwalinta ta linka ta sa sannan ta yarda pad din ganin pad din bata mata wani amfani sannan ta fito ta zuba masu ido suna koke kokensu……
【】
Safeena kam tana isa gidansu maryam ta iske Mum dinsu a falo……
Da sauri ta tare ta rungumeta tana mata ya hanya cike da tausayi
Kuka ya kwace mata ,Mum din ta fara lallashinta tare da bata baki ,don duk a tunaninta Rasuwar Abban nata takewa kuka……
Kwala maryam kira tayi ta fito ……ai kuwa makalkale Safeenar tayi kamar zata kadata ……sannan ta jata dakinta ta rufe kofa tana fadin "Besty karya suke maki Abba na raye na wallahi ……"ta fada lokacin da ta zaunar da Safeenar saman gado
Cikin kuka tace "Na sani besty……"
Idon maryam din ya ciko da kwallah ganin Safeenar na kuka tace "Baki warke ba besty?
*"Na warke"ta fada cikin kuka
"Besty so kike nima nayi kukan ,Dan Allah kiyi shiru kin ji menene to?
"Abdul maleek ne besty……"
Da sauri maryam din tace "Wani abu ya sameshi ……"
Takardar ta mika mata tare da komawa baya ta kwanta ……
Sae da ta gama karantawa sannan ta kalleta tana fadin "Ashe baki da wayau besty……"
Da sauri ta mike tana kallon maryam din ……
Daure Fuska maryam ta kuma yi tana fadin "Yeah ban taba sanin baki da hankali ba sae yau Safeena ,da mutuncin Abbanki kike neman ki zubar mashi dashi a idon Abdulmaleek……meye ribarki idan kinyi auren kisan wuta kin koma hannun jabir?Abun kunya ma Safeena har da yardarki ……ya kike tunanin idan Abbanki yaji kinyi aurene idan kika warke ki koma gidan jabir saboda shi,bara ya iya jinyarki ba sae Abdul maleek ko besty ?drivernki dake karkashin Mahaifinki ……to bara kiji wallahi Abdul maleek babban barister ne hakanan ya cigaba da kaiki makaranta ……kuma wallahi Safeena indae har Abdul maleek ya sakeki ki manta da ni maryam a rayuwarki……"
Kuka take tana fadin "Wallahi maryam bance ya sakeni ba shi ya bani takardar yanzu ,kuma wallahi banyi niyar na rabu dashi ba haka banyi niyar na aureshi bayan na warke na ya sakeni ba ,Shin banda wayau ne besty koko ban san banbancin SO da SHA'AWA ba Besty ……Abdul maleek ke Sona kuma ina ina sonshi ……jabir kuma sha'awata yake ni kuma sha'awarshi ki fahimceni mana ……"
Duk yarda maryam din takai ga daurewa amma ta kasa ,rungume Safeenar tayi tare da sakin kukan itama ,don ko kadan bata son abunda zai shafi kawartata ……duk wani farinciki na Safeena tana fata su rabashi biyu ……haka duk wani bakin ciki,nata tana fatan a rabashi uku ita ta dauki biyu ……
Sae da suka ci kukansu sannan Maryam din ta koma tana lallashi Safeena "Dan Allah kiyi shiru wallahi wasa nake baran iya rabuwa da ke ba kinji ……"
Shirun tayi tare da kallon maryam din tana fadin "Na sani besty kawae ina kukan,na batawa kawar da tayi Shekara biyar tana raba duk wani,bakincikina ta dauka ,sannan kawar da ta man abunda babu wani mahalunkin da ya kwatanta man shi a rayuwa……Dan Allah ki yafe "
Dariya maryam din tayi sannan ta janyo takardar tana karantawa da karfi 【Safeena ko da yarda na aureki banyi niyar na sakeki ba bayan kin warke ,Wallahi na aurekine don na RAYU DAKE Har abada ……Dan Allah Madam ki karbeni a matsayin miji ko da baki son haka wallahi nafi dacewa dake a rayu nafi Jabir Kaunarki nesa ba kusa ……ki yarda dani Safeena ina maki wani irin So mai wuyar fassara na maki alkawarin bara ki taba kuka dani ba……Tun lokacin da na fara ganinki a bikin beeba na fara sonki dabi'unki da komae naki abun burgewa ne gareni safeena……nayi farinciki sosaae da mahaifinki ya daukeni a matsayin driverki sannan nayi bakinciki lokacin da naji zakiyi aure ……Dan Allah KI YARDA DANI Ina matukar kaunar ki Safeena…… ……by 8:00pm zan zo na daukeki mu dawo gida kinji ko ……Much love 】
Fizge takardar tayi ta fara yagawa tana fadin "Wallahi sae na rama……"
Dariya maryam din tayi sannan ta mike da debo mata abinci ta kawo mata ……
《》《》《》《》《》
Sae da harka tayi nisa sannan Uncle Abbah ya fara kokarin wando ……
Wata uwar zabura yarinyar tayi tare da mikewa tsaye tana kallon PPart dinshi "Kutmar can a hakan da kake kokarin shigata……"
*FEEDOHM💞*
[4:53AM, 11/14/2017] Feedohm💞: 💧💧 *ZAN RAYU DAKE🌹*
🌹🌹🌹
🌹🌹
🌹
© *_Haske Writer's Association_*
( _Home of expert & perfect writers_ )
*_NA_*
*_FEEDOHM💞_*
*Devoted to Ummi A'isha👌🏻*
*Bestowed to Aunty Sis💕*
4⃣8⃣
Wata uwar zabura yarinyar tayi tare da mikewa tsaye tana kallon PPart dinshi "Kutmar can a hakan da kake kokarin shigata……"
Janyota yayi jikinshi yana fadin "Haba Baby kamar wata yarinya da Allah ki tsaya mana wallahi yau set na gold zan baki……"
"Uwar Gold zaka bani Abbah ……ka mayar dani yar iska da wannan kazantar zan tsaya ka shigeni lallae baka da hankali……"
PPart din ya kallah tare da mikewa zumbur yana kallon gurin ……wasu kurajene suka feso jawur dasu ga gurin ya tsatstsage yana fitar da jini kadan kadan ……Kallon gurin yake a tsorace ,duk da ya san akwae kuraje amma basu kai girman haka ba ……wani farin abu yaga yana kokarin fitowa ……
Su duka suka kurawa gurin ido ……Lokaci guda suka mike tsaye ganin karamar tsotsa fara daga tsakiyar gurin ta fito tana yawo saman kuraje ……
Gyalenta ta dauka ta fice da gudu tana fadin "Allah ya isa shege ……"
Shikam maida wandonshi yayi ya nufi asibiti inda su hajiya ke kwance ……Ya fada masu a rude……
Cikin maganar da bata fita Hajiya tace "Hate ka kaishi a dubashi ……"Aunty Fatee ta mike Ta bi bayanshi ……yayin da Aunty Zuby ta bisu da harara ……fadila kuma kwashewa tayi da dariya……
Sample na gabanshi suka dauka tare sa dinbar jininshi ……da result ya fito HIV/AID kadae ne positive ……sannan nurse din tace basu gano,wata cuta ba game da gaban nashi illa iyaka suna tunanin yawan bin matane yasa gaban nashi yayi haka ……magunguna suka rubuta masu……
《》《》《》《》
Da kyar maryam ta samu Safeena ta yarda suka je gidan granny wajen hudu na marece ……
Fira suka sha sossae da ita…… Anan ne ma maryam ke fada mata abunda su Aunty Fatee sukawa Abban Safeena ……
Hajiyar batayi wani mamaki ba don tasan zasuyi abunda yafi haka……
【】
JB kam tunda ya koma gida ya kasa zaune bare tsaye ,yawo kawae yake tsakanin falo da dakinshi ,ko da mum ta mashi magana ……tsawar da ya sake mata dole ta koma daki kamar wata diyarshi ……
Kiran wayar Safeena yayi amma har ta katse bata dauka ba ,wani abu ya tokare mashi lumfashi ,ya koma ya zube saman gado tare da dafe kanshi ……
Uban duka aka sake mashi a bayanshi da karfi ,gantsarewa yayi sannan ya mike yana kalle kalle ……Zuciyarshi ta buga da karfi ganin labulen window na dagewa wani iska na fita daga dakin ……
Cike da bacin rai ya yaye bargon dake shimfide saman gadonshi yabi iskar da duka yana fadin "Ni zaa wa iskanci ……to wallahi nima ba karamin dan iska bane ,duk shegen da ya kara dukana ya raina uwarshi……"
Bai rufe baki ba aka daukeshi da mari ……kamar sabon kamu ya kaiwa iska duka cike da rashin tsoro "Na lura wani salom iskanci zaa kawo man na dukana ,to wallahi bana tsoron ko wane dan Iskan aljani……"
Kofar toilet dinshi ta bude da karfi ,ya bi da gudu ya kamota ya rufe yana fadin "Baza'a barta bude ta ba yan iska a rufe nayi raayin ganinta ……"
Kamar mahauci ya dinga surutu shi kadae cike da jarumta ……Sae da komae ya tsaya sannan ya mike ya fita daga dakin ……Har aka gama magrin bai bar surutu ba……
Tunaninshi daya inda zai samu safeena suyi magana yanzu ……"Dutsin safe……" ya fada da karfi tare da daukar mota ya fita ……
Tun kafin ya shiga gidan yake kwala mata kira kamar zaya tashi sama ……Suna zaune da granny ya fado falon yana haki ……
Cikin hargowa yake fadin "Amma Safeena Abdul maleek ya cika babban shege mara alkawari……"
Kallonshi sukayi su duka ba tare da wani ya amsa mashi ba ……
"Kin tsaya kina kallona ki fito muje ki karbo takardarki ……"
"A gurin wa?Granny ta fada har lokacin tana kallonshi ……
Fizgo Safeenar yayi da karfi ya mikar da ita ya hadeta da jikinshi ……lafiyayyen mari ta sakar mashi tare da fincike jikinta daga rikon da ya mata ……
Cikin mamaki ya ke kallonta dafe da gurin da ta mara "Abunda kika aitaka yanzu ya nuna man kina bayan Abdulmaleek Safeena……?ya fada cikin konar rai
"Akwae jahilar macen da zata kwarewa mijinta baya dama ……? ta fada tare da tsareshi da ido
Dauketa yayi da mari yana fadin "Ni zaki ciwa amana?wallahi baki isa ba…… ke tawa ce kuma dole ki dawo hannuna ……"
Bai rufe baki ba Maryam ta daukeshi da mari tana fadin "Akwae Ubanda ya haifawa Abba ita a family dinku……?
Ya daga hannu da niyar ya rama yaji an rike hannun "Karka kuskura ka taba ta wallahi domin shine kuskure mafi muni da zakayi a rayuwarka ……"cewar Abdul maleek da ya shigo yanzu
Kamar wani mahaukaci ya shakereshi
"Abdul maleek karka tabashi ……"granny ta fada tare zuwa kusa dasu ta nuna jabir "Jabir fita ka bar man gida dan girman Allah……"
"Wannan ne gida?ya fada yana watsa mata kallo
"Ko ma menene nace ka fita Jabir ……"
"Zan fita amma wallahi Sae dai mu duka mu rasata indae har na bar Safeena kowa ma ya barta ……"
"Naji ikon Allah jabir kasan kana sonta me yasa ka saketa?Tunda baa maka dole ba ka saketa cewa akayi ta dawo gida a sama mata magani ta koma ,kai kuma kace mamarka tace ka saketa ,to me kake so a maka yanzu jabir.……?
Banza ya mata
Kamar guguwa ya bar gidan Zama Abdul maleek yayi suka gaisa da granny ……Safeena da maryam suka shige daki abunsu ……
Nan yake fada mata da yayi niyar shigar da Aunty fatee kara sae dae rashin shedu ya hanashi saboda Abban bai riga ya ci abincin ba bare a ce an kaishi asibiti an tabbatar da poison suka saka a ciki……
Sae da ya fadawa granny gaskiyar bai boye mata komae ba hatta aikin da yake sannan ya kara da fadin zai tafi da Safeena yanzu ……
Cewa tayi,"Ba komae Abdul maleeku fatan mu Allah ya sanya alkhairi cikin zaman ku ……"
Sannan ta mike ta samu Safeena da Maryam zaune ,Sossae ta ma Safeenar fada sannan tace ta tashi ta bi mijinta su tafi ……
Turo baki tayi tana fadin "Wallahi granny baran bi sa ba ……"
Juyar da kai granny tayi tana fadin "Tunda kika taso nake lallashinki Safeena amma wannan karan kaniyarki zanci wallahi ……"
Maryam ta amshe "Wannan karan bana bayanki besty ,ki tashi kawae ku tafi ……"
Ganin da gaske suke ya sata daukar hijab dinta tana turo baki ta fita ,maryam ta bita har bakin mota tana mata magana amma sam bata kulata ba .……
Bayan motar ta bude ta shiga ,bai ce mata komae ba yama maryam bankwana suka tafi ……
*FEEDOHM💞*
0 comments:
Post a Comment