A nutse ya waigo da fuskarsa yana kallonshi, wani abin da ya kara k'onawa Honourable rai shine ganin fuskar Usher dauke da lallausar murmushi, sai shafa sajen gefen fuskarsa yake yi alamun yana cikin yanayin nishidi.
K'ara tamke fuskarsa yayi tamau alamun ba wasa, kuma duk abinda zai fada daga cikin kololuwar zuciyarsa take.
"Wannan yarinyar da kake gani 'Yata ce! Ina nufin 'Yata wacce aka haifa min ita ta hanyar halak!
Fatima sunan da na rad'a mata.
A bayan ita na dad'e ban kara samun haihuwa ba sai kwanaki can Allah ya sake ba mahaifiyarta ciki ta haifi yara maza guda biyu.
Na rad'a musu suna Adam da Affan..."
Tunda ya fara zancen yake ta kallonsa da matukar mamaki a fuskarsa, ya gaza hakuri dai har saida ya katse shi
"Honourable wannan bayanin duk na menene?"
Wani mugun kallo ya watsa masa na *Karka nemi ka raina min wayau*
"Mun dad'e muna gudanar da hark'alla tare ina ga ya kamata musan tarihin juna.
Dan haka ka ci gaba da saurara ta kawai, wannan tarihin iyalina nake baka"
Ya watsa masa bakar magana mai kama da gatse.
Gyada kai kawai yayi ba dan ya fahimci manufarsa ba, saidan kawai yaji iya gudun ruwansa.
"Ita wannan yarinyar Fatima da kake gani tana karatu ne a Bayero University Kano, yarinya ce mai matukar kokari da maida hankali akan duk abinda nasa ta fuskanta.
Ako wane lokaci tana fifita za6ina akan nata za6in, shiyasa nake matukar kaunarta.
Nutsuwa da kamun kan da take dashi shi yake k'ara sakani jin alfaharin samun 'ya kamarta.
Tabbas ina alfahari da ita a duk cikin yarana.
A kokarina na kare ta daga sharrin mayaudaran samari da miyagun kawaye na nemi zakwakwuran masu gadinta kuma matasa masu jini a jika suna kewaye da ita ako wane lokaci.
Dan in k'ara tabbatar da ita a nutsuwarta yasa na nema mata islamiya mai matukar kyau da tsada tana karatu a ciki.
Ko yanzu da ka ganta daga islamiya take!!
Fatima ita ce babbar 'Yata, sai kannanta maza kanana guda biyu kamar yanda na fada maka, shiyasa nake iya kokarina gurin kiyaye tarbiyarta, kuma ina iya kokarina gurin kareta daga sharrin samarin zamanin nan 'yan karya da yaudara.
Idan lokacin da nake bukatar in aurar da ita yayi zan nemi nutsattsen yaro kuma masanin addini in aura masa ita.
Ina kara jaddada maka wannan maganar ne ba dan komai ba sai dan ka kiyaye!
Zan iya yin komai akan duk wanda ya nemi ya ta6a min mutunci na!!
Iyalina mutunci na ne, duk wanda ya nemi shiga harkarsu ko neman kusanci da mutunci na tabbas zaiga abinda bai ta6a tsammani ba.."
Wata dariya Usher yayi mai kama da na rainin hankali, wannan shine kura da kallabin fatar akuya, mamaki ne fal da zuciyarsa, ya waiwaya ya sake kallon kofar falon da tabi zuwa cikin gidan.
Murmushi yayi sannan ya maida hankalinshi kanshi yace
"Karka damu Honourable.
Hakan da kayi yana da kyau, kasan ance kula da kaya yafi bada cigiya. Na taya ka murnan samun 'ya nutsattsiya.
Amma barin sake tunatar da kai wani abu"
Ya matsa daf dashi yanda har numfashinsu ke bugun juna.
"A shawarce ya kamata ka k'ara tsaurara tsaro a kanta, hakan zai kara taimaka maka matuk'a, saboda....
Ko da yake ba saina bude maka komai a fili ba.
Wannan shawara ce kyauta na baka. Ka dauka in kana so"
Furzar da iska yayi daga bakinshi, ya shafi kwantaccen suman kanshi da yake kwance luf gwanin ban sha'awa. Ya sha gyaran gashi irinna zamani wanda manyan gayu ke yayi, idan ka matsa kusa dashi kamshi kawai yake fitarwa ta ko ina a jikinsa.
"Ni bari inci hanya, sai ka ji ni zuwa gobe da yamma"
Har ya fara takawa zuwa gurin motarsa dawo da baya, ya kalli Honourable da yake tsaye kikam kamar wanda aka zarewa laka.
"Daga nan fa mahad'a zan nufa, nasan duk yara suna can suna jira na.
Shekaran jiya na rarraba kayan nan nasan zuwa yanzu kayan sun isa duk inda ya dace su isa a sassan kasar nan. Zan had'a kud'ad'en gaba daya in tura maka cikin account d'inka"
Ajiyar zuciya mai nauyi ya sauke, kamar mai ciwon baki ya amsa da kyar
"Ok hakan yayi, Allah ya tsare. Sai na ji ka"
Ya amsa fuskarsa babu walwala.
Yana isa gurin motarsa ya shiga ya bata wuta, mai gadi yana bud'e get din gidan ya fice a saba'in.
Honourable yabi bayan motar da kallo zuciyarsa cike da sak'e-sak'e.
Ransa a matukar 6ace yake, ya ma rasa irin tunanin da ya kamata yayi.
Lallai dole ne ma yaci Uban Fatima idan ya shiga ciki, ko wane iskanci ne ma yasa taje gaishe shi bayan ta ganshi da bak'o?
Kai shikam wannan zuwa kano bai yi ta a sa'a ba.
Babban abinda ya kawo shi daga yau daga Abuja wani ganawa ne da zasu yi da mai girma gwamna a daren yau, amma bacin haka yana sati biyu kafin ya shiga kano, kuma bai ta6a ganawa da Usher a gidanshi na kano ba sai dai a Abuja.
Da siririyar sallama a bakinta ta murda hannun kofar falon, bata damu da sai an amsa mata sallamar ba ta kutsa kanta cikin falon tana 'yan wak'e-wak'e.
Haka kawai take jin wani nishadi yana kwaranya a zuciyarta, a dan tunanin da tayi saita danganta hakan da had'uwa da Usher, wanda ya kwanta mata a rai farat daya.
Hijab dinta ta d'age zuwa kafad'arta, sai a lokacin ta lura da tsayuwar matar gidan a jikin d'aya daga cikin windunan falon, ta ba kofar falon baya. hannunta d'aya rike da gefen labulen, da alamun wani abu take kallo a waje, daga ganin yanda hankalinta ya koma ga abinda take kallo ne yasa taji tana sha'awar ganin abin kallon.
Dan haka da sassarfa ta k'arasa gurin windon ta leka dan ganin me ya d'auke mata hankali har ta gagara amsa sallamarta?
Usher ta hango a daidai lokacin da ya nufi gurin motarsa, yana tafe yana bouncing cike da kwalisa. Kyakkyawan matashi mai matukar kwarjini da cikar zati mai d'aukar hankalin duk wata cikakkiyar mace.
A jiyar zuciya mai nauyi suka sauke a lokaci guda, kallon-kallo suka yi a tsakaninsu, fuskokinsu na bayyana tsananin kiyayyar da suke ma junansu.
Harara Fatima ta watsa mata, cike da takaici da bakinciki tace
"Ke dai kam kin shiga uku, Amma wallahi anyi asarar kudin islamiya, mace da auranta bata daina shinshinar mazan waje ba. Wannan masifa da me tayi kama? Ki roki Allah ya shirye ki idan ba haka ba Wallahi wutarki daban ce"
Wani banzan kallo Halima ta watsa mata, sannan taja dogon tsaki kamar bakinta zai fad'o kasa, a zafafe ta fara magana
"Wallahi karki sake kiyi min rashin kunya. Idan wutar taki ce ba saiki saka ni ba?
Kinsan halina tsaf! Zan iya warware duk wani boyayyen mugun halinki a gaban idanun mahaifinki, Idan yaso yayi miki baki kibi 'ya'yan kaji ki d'ai d'ai ce..."
"Hehehe! Wallahi har kin bani wata 'Yar budurwar dariya"
Tayi dariya da shewar rainin hankali.
Ta matsa daf da kunnenta ta rage muryarta k'asa-k'asa yanda ko kusa dasu kike in ba kin kasa kunne sosai ba bara kiji mai take cewa ba.
"Dan Allah ki bada himmar fada masa Aunty Halima, kiyi sauri kar k'uda ya riga dogon bakinki mai shegen gulmar tsiya.
Amma kafin nan ina so ki tuna da naki 6oyayyen sirrin da yake a tafin hannuna..."
Tayi wata dariya mai kama da ta rainin hankali, ta cije gefen bakinta alamun mugunta ta ci gaba da cewa
"Ba gara ma ni ba ko an tsine min zan ci gaba da zama a cikin daular gidan mahaifina ba? Wata kuwa idan aka dankara mata jar Kati saidai ta tattara kayanta ta koma gidan Malam Shehu wanda bai aje ba bai ba wani ajiya ba, a ci gaba da shar6ar arniya mai shocking (miyar kuka)"
Dariya ta kyalkyale dashi bata saurari amsar da zata bata ba ta nufi hanyar da zai sada ta da bangaren da dakinta yake.
"Ke Fatima! keh Fatima..."
Mahaifinta ya shigo cikin falon yana kwala mata kira cikin fushi da hargagi.
[24/03 6:51 PM] Maman Raudah: *BARA A KUFAI!!*
*21)*
Zaro idanu tayi ta dafe kirjinta da hannu bibiyu, da sauri ta waiwayo tana kallonsa, ganin fuskarsa babu annuri da tausayi ko kadan yasa a tsorace ta k'arasa gabansa ta zube a kasa kamar mai rokon gafara, kirjinta sai bugawa yake fafafat! A wannan lokacin da za'a auna jininta tabbas yayi mugun hawa.
A zuciyarta addu'a take ta zabgawa Allah yasa ba maganganun da suka yi da Aunty Haleema yaji ba, da ta gama kad'ewa har ganyenta.
Ta kamo wannan addu'ar ta saki wancan sai kikkifta idanu take yi alamun rashin gaskiya a fili.
Tsawon dakiku sittin yana kallonta da nazartar yanayinta, duk yanda yake tsananin kaunarta sam baya mata da sauk'i idan ta kuskure a gabanshi, zagewa yake yayi mata kaca-kaca kamar baisan daga inda ta fito ba.
Ansha shi ya warke, kuma anyi mishi na daya sam ko da a mugun mafarki baya fatan ai na biyu...
"Ga.. gah... gani Daddy.."
Ta fad'a da rawar murya cike da fargaba idanunta a k'asa tana k'ara mak'ale Jakarta a hammata.
Zazzare mata idanu yayi kamar zaici babu, da zafin rai muryarsa a kausashe yace
"Uban me kika je yi a gurina bayan kin ganni tsaye da bak'o?"
Cikin tsawa yayi mata tambayar kamar zai rufe ta duka.
6oyayyen ajiyar zuciya ta sauke a zuciyarta take hamdala ga Allah da yasa ba abinda take tunani bane, ta sanyaya muryarta kwarai kamar zata fashe da kuka.
"Ba komai wallahi, kayi hakuri, bazan sake ba in Allah ya yarda Daddy"
"Wannan shi ne kashaidi na farko kuma na karshe da zanyi miki akan shiga harkar abokan sana'a ta. Kika san ko da wani irin mutum nake tsaye? In banda iya shege kece har kinsan ki ringa kashewa namiji idanu? To idan aure kike so ki fada min tun wuri in nemo miki mijin da ya dace dake"
Fad'a ya ci gaba da yi ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, akan muddin ta bari ya sake kamata da aikata mishi irin wannan laifin sai yayi mugun sa6a mata.
"Bazai yiwu ina iyakan kokarina akan tarbiyarki da tsare rayuwarki ki janyo min abinda zai zubda mutunci na ba.
Ke daga ma na yanke shawarar ko islamiyar zaki je ban yarda ki ringa tafiya ke kad'ai ba, zan fadawa su Nura su ringa bibiyarki duk inda kika nufa, sai kin dawo gida sannan su tafi harkokinsu.
Samarin nan 'yan k'arya 'yan yaudara bazan ta6a Bari su lalata min ke ba, ina nan ina shiri na musamman a kanki ina gamawa zan nemi nutsattsen yaro in aura masa ke. Idan kuma kin matsu da auren ne tun wuri ki sanar dani"
Idanu da kanta yana k'asa har ya gama surutan da ta dauke su na banza da wofi, maganganu masu kama da busar sarewa a gurinta.
Ko da ta fahimci ya gama kaskantar da kai tayi ta sake bashi hakuri, ta mike ta kakka6e mishi zantukanshi anan inda yayi su ta shige d'akinta.
"Ke kuma tsayuwar me kike yi a jikin window?"
Ya tambayeta yana mata wani kallo mai kama da na zargi.
Luuu... tayi da dara-daran fararen idanunta ta saki labulen windon a hankali ya rufe gaba daya, tattausan murmushi take jifansa dashi tun daga nesa kafin ta fara takowa zuwa gare shi da tafiyarta na cat walk.
Kusan suma yayi a tsaye yana kallonta, tuni ta tafi da kashi saba'in na imaninsa.
Irin wannan tafiyar mai karkad'a duk sassan jiki ana shigar da kafa d'aya ta cikin d'aya yana masifar daukar hankalinshi, yana d'aya daga cikin abinda yaja hankalinsa zuwa gare ta ranar da ya fara ganinta a unguwa uku da suka je yawon kamfen, ga ta da k'irar jiki komai yaji zam-zam a jikinta tubarkallah, gaba da baya ta cika dam! shi yasa ya nace har saida yaga abinda ya ture wa buzu nad'i ta hanyar auren ta.
"Baby Booo gani nayi yamma tayi shiyasa naje gurin dan in saki labulen saboda sauro.
Daddad'ar iskar yammaci mai cike da lafiya da k'ara ni'ima da shauki a jikin d'an Adam da naji yana busowa ta cikin windon yasa na tsaya na shak'i kad'an.
Amma tunda baka so kayi afuwa Baby Booo"
Tana gama fad'in haka da murya mai cike da sanyi da kwarkwasa ta matsa jikinsa sosai cike da shauki tana bank'aro mai kirjinta.
Tasha kwalliya cikin k'ananun kayan da sukai masifar kar6ar jikinta, wata fingilar riga ce wacce da kad'an ta wuce cibiyarta, ta saman wuyan rigar a wawake yake, hakan yasa kusan rabin kirjinta sun burtso ta saman rigar.
Wandon jikinta gajere ne da kad'an ya wuce gwiwarta, ya kama ta tsam-tsam, da yake mai yalwar mazaunai ce sun ciko dam a wandon har ana ganin sashin farin dan pant din da yake jikinta.
Lokacin da Honourable ya isa gidan da yake zuwa ne na bazata tarar da ita yayi sanye da yaloluwar rigar bacci tana kwance akan kujera tayi d'aid'ai tana chatting da samarinta.
Ganinsa yasa tayi saurin danna wayar ta shiga key taje da sassarfa ta mak'ale shi tana fad'a mishi irin yanda tayi kewarshi.
Baiyi minti biyar cikakku da shiga gidan ba Usher ya kira shi kan cewa gashi nan a harabar gidan.
Tana tsaye a jikin window tana lekensa tayi tozali da fuskar Dan kwalisan matashin da ya tafi da imani da nutsuwarta gaba d'aya.
Ko da suka shige cikin falon bakin a gurguje tayi wanka da kwalliya sama-sama ta koma jikin window ta ci gaba da lekensu.
Watsi tayi da tunanin da take tayi ta shafo gefen fuskarsa har zuwa gemunsa tana kara had'e jikinsu guri d'aya.
"Bansan zaka shigo yau ba Baby Booo shiyasa banyi shirin tarbarka na musamman ba. Amma ka fara da wannan"
Had'e bakinsu tayi guri d'aya tana mishi wani wawan sumbata cike da salo da gwanancewa. Lokaci k'alilan ta mantar dashi fad'an da yake yiwa Fatima balle kuma kallon tuhumar da yake mata.
"Wai ni kam Baby Boo wane bako kayi ne da ko Lemu baka ce a kai mishi ba? Ina shirin fa in aiko Fatima ta kawo muku snacks da lemu naga kuma ya tafi"
Ta tambayeshi tana shafa kirjinsa da yake sangam babu ko digon gashi.
"Karki damu, Usher baida damuwa, daman ba dadewa zaiyi ba"
Ya amsa yana lumshe idanu cike da jin dadin abinda take mishi.
Tsabar murnar jin sunansa wanda daman abinda take bukata kenan yasa ta rungume kansa a kirjinta tana kara haukata shi, lokaci daya ya fara gurnani.
Ita daman 'Yar soyayya ce, a kullum kuma a ko wane lokaci cikin shauk'i take. Wannan yana d'aya daga cikin dalilin da yasa yake k'ara sonta.
Ta iya tafiyar dashi kamar matashi d'an shekaru ashirin da bakwai.
Matukar yana kano to tabbas yana ganin gata kuma yana kwankwadar zallar madarar soyayya mai kama da ta indiyawa.
Har wani manta tsufanshi yake yi domin indai yana kano tana had'a mishi kayayyaki da magunguna masu kara kuzari da motsa sha'awa.
A tsarin halittar Haleema Allah ya halicceta ne cikin mutane masu matukar sha'awa, tun tana 'yar karamar yarinya bata da littafan karantawa saina batsa.
Tana karatun tana jin wani shauki da dad'i yana kwaranya a cikin zuciyarta.
Lokacin da ta kai shekaru goma sha biyar kuwa tana karatun tana aiyana yanda idan ta kara girma za'a ringa aikata mata haka a zahiri ne, har wani danshi danshi take ji yana fita a jikinta a wancan lokacin.
Babban abinda ya kara ta6ar6ara rayuwarta shine rashin mahaifiyarta a gurin mahaifinta, sun rabu tun tana yarinya karama sosai.
Fushin irin sakin wulakancin da ya yi mata yasa tayi watsi da rayuwar Haleema kamar ma ta manta da ita a babin rayuwarta.
Mahaifin kuwa babu abinda ya shalleshi da ita, baya saka mata idanu akan tarbiyyarta. Ya kaita gurin mahaifiyarta kuma yak'i.
Ita kuwa matar uban ba sawa ba hanawa, ta zura mata idanu kawai tayi abinda taga shine mata dai-dai a rayuwarta.
Aunty Bola wata bayarabiyar amarya ce da mijinta ya kama haya a gidan da suke haya, Allah ya hada jininta da na Haleema kuwa taita janta a jiki, ita take mata kyautar kwancen kayayyakinta, babban abinda ya kara cutar da Haleema a taraiyarta da Aunty Bola shi ne: Ita bata da wasu fina-Finan da take kallo sai na batsa tana k'ara koyon salo-salo da nau'in soyayya dan ta burge mijinta Kayode, aduk sanda take kallon kuma bata cewa Haleema ta tafi saidai su kalla tare, duk munin guri idan aka nuno tare suke kallo, ga kuma yanayin halittar da take dashi hakan ya k'ara tsumar da ita.
Kusan kullum tana barci ne yatsarta yana cikin gabanta ko kuma taita lilaya kirjinta har sai ta ji dama dama sannan zatai barci.
Kwalliya da gayu take yi sosai domin Bola bata zama da kazami, kuma tana bata kwancen kayayyaki riga da sket da kananun kaya.
Bangis yaron makwafcinsu shi ya fara lalata mata rayuwa bayan ya nuna mata wani blue film a wayarshi, tun tana kallo tana matse-matsen jiki da kafafu har dai ta matsa jikinsa ta lafe, shi kuwa kura ta samu nama ai baiyi sanyi ba gurin biyan bukatarsa.
Tun daga wannan lokacin fa ya bude mata ido da abin duniya ita kuma ta saida mishi da tsakanin cinyoyinta.
Lokaci daya ta zama wata babbar mace mai aji, taci abinda take so a lokacin da take so, tayi yadda taga dama babu mai ce mata 'don me?'
A wasu lokutan ma ita take daukewa Mahaifinta cefanen gida su ragargaji kaji bai ta6a tambayarta menene tushen samun kudad'enta ba, a haka take rayuwarta har Allah ya had'a ta da Honourable Sumaila suka yi aure.
Babban kuskuren da Honourable ya kara tafkawa a gurin rikon aurenta shine yanda yayi sako-sako da rayuwarta da yanayin halittarta, ya dauki Uwargidansa ya maida ta Abuja tana tare da shi.
Ita kuwa Amarya Haleema da 'yarshi Fatima ya barsu a kano, a cewarsa rayuwar yaran Abuja musamman 'yan mata da irin tarbiyyarsu sai wanda Allah ya tsare, shiyasa ya sakar musu duk abinda suke bukata ya barsu a kano.
Ya debi masu gadi ya zubawa Fatima, ita kuma Haleema tsabar kishi da kallon zargi-zargin da yake mata yasa yai kudurin bazai koma da ita Abuja ba, balle har idanunta Sufi haka budewa tafi karfinshi.
Shiyasa dukkansu suke bushasharsu yanda suke so, Haleema ta kakka6o tsohon sim card din ta suka ci gaba da chatting da samarinta, a wasu lokutan ma har gurinsu take zuwa.
Idan zata fita kuwa irin kwalliya da shigan da take yi idan Honourable baya nan zaka rantse ba matar aure bace, shiyasa a kullum bata rasa sabbin samari masu jini a jika.
Ita kuwa Fatima kura ce da kallabin fatar akuya, buga shaye-shaye suke yi da kawayenta a makaranta da gida, ranarda bata da kudi kuwa ta shiga bangaren mahaifiyarta ta dauki wani abun mai daraja ta bada a bata kayan maye, da kadan da kadan har ta zama dilar kayan mayen a gurin kawayensu, duk sati Musa wanda aka fi sani da Moses da ya kawo kaya zai ware mata ya kirata ta karba ta bashi kudadensa.
[27/03 10:51 AM] Maman Raudah: *BARA A KUFAI!!*
*22)*
******
Tsaye k'ik'am tayi mata a ka tana girgiza da karkad'a jiki cike da fitsara da rashin kunya.
Tunda ta dago kai ta kalle ta sau daya tayi iskar kare da ita, kamar bata san da wata halitta a tsaye a kanta ba.
Chat din ta taci gaba da yi hankalinta a kwance, lokaci bayan lokaci tana sakin k'ayataccen murmushi, da yake labarin zuciya fuska ce take fara baiyanawa a kallo daya za'a gane tana cikin matukar farinciki.
"Aunty Haleema magana nake yi"
Fatima ta fadi haka cikin gatsali bayan taga tsayuwar bazai fissheta ba.
Saida ta gama firirita da yatsina kamar bazata amsa ta ba.
"Ina jinki, amma kafin nan ki tashi min a kai"
Harara ta galla mata zuciyarta cike da muguwar tsanarta, wani dan tunani tayi ta matsa gefe kad'an.
"Dan Allah lambar Usher zaki bani?"
Ta fadi haka da d'an sanyin murya tana k'ok'arin danne zuciyarta.
"Usher? Waye haka?"
Shiru tayi bata tanka ta ba, wannan ma ai tambayar rainin wayau ce da rainin hankali.
"Tunda baki da ta cewa pls ki ban guri insha iska"
Ta fada tana hura hanci ranta a bace.
"Bakon Daddy na shekaran jiya, wanda na jiki kina waya dashi dazu a band'aki..."
Wani mugun kallo ta watsa mata mai cike da tuhuma, lallai yarinyar nan ta raina ta, wato ma la6e take mata?
"Tunda har kika iya la6ewa dan kiji da wanda nake waya ai lambar wayar tasa ma kamata yayi ki la6e ki sata, dan haka bazan bada ba.
Idan kuma kina da karfi ki kwata"
Tana gama fadin haka ta dauki wayarta ta haura sama zuwa bangaren Honourable, dukda baya nan yayi sammakon komawa Abuja yau da sassafe.
Shiru tayi tana tunani zuciyarta na k'una, ta rasa hanyar da zata bi ta saci lambar wayar Usher a wayar Auntyn ne shiyasa ta karya kwanjinta ta tambaye ta, dan ko ta samu nasarar daukar wayarta a banza, tunda securityn bude wayar kwayan idanun Haleema ne, saboda tsabar rashin yarda da kai, kuma duk wasu applications masu muhimmanci a gurinta tasa musu passwor ta kulle su, saboda tsabar kula da taka-tsantsan.
Tun kafin ta tambaye ta lambar tayi tunanin bazata bata ba, amma irin maganganun da ta caccaba mata sunfi komai bak'anta mata zuciya.
Wani tunani da ya darsu a zuciyarta yasa ta saki wani kayataccen murmushi, a sukwane ta juya zuwa dakinta ta dauko wani gora da ruwa a ciki kamar zobo, cikin jakarta ta dauko farin gari ta sake gaba daya kullin a cikin goran ta girgiza shi sosai farin ya bace a cikin ruwan maganin.
Saida ta leka falo ta tabbatar babu kowa ta shige kicin da sassarfa, frij ta bude ta dauko wani farin kofi, goran hannunta ta bude ta tsiyaya kadan a ciki ta jujjuya kafin ta maida inda ta dauko kamar bata ta6a ba.
Da saurin gaske ta fice a kicin din zuwa dakinta, dariya ta kyalkyale da ita bayan ta tuno plan dinta.
Nikakken kankana ce wacce aka juye wa gwangwanin madarar ruwa a ciki ta zubawa maganin maye, wannan shine dad'i kan dad'i.
Rub da ciki tayi akan gado tana ta chatting da kawayenta ta what'sapp, tsawon awa biyu tana abu d'aya.
Tana fita falon ta ganta kwance dai-dai akan kujera tana barci, ga wayarta nan a gefe d'aya kusa da kunnenta.
Tsabar murna da farin cikin ganin tana barci yasa ta buga tsalle tana kyalkyala dariya.
"Wa yace dani ba ni ba? Sorry Aunty Haleema kin shiga hannu"
Da saurin gaske ta dauki wayar, ta zauna a gefenta ta sa hannu ta gwale kwayar idanunta guda daya, dayar hannun kuma yana rike da wayar saitin idon, nan take kuwa wayar ta bude.
Tattausan murmushi ta sake ta fara lallatsa wayar tana k'ok'arin shiga contact dan ta nemo lambar Usher.
Ganin contact din da password yasa ta shiga gurin kira, a hankali take bin sunayen tana mamaki a ranta, dukda tasan halinta na bibiyar mazan waje tasha mamakin ganin lambobin maza anyi saving dinsu da sunan kalmomin soyayya.
*Usher Durling*
Hannunta ya tsaya akan sunan, tsaki taja dan haushi, sauri-sauri ta haddace lambar a kanta dan tsabar son da take masa.
Aje wayar tayi kamar yanda ta dauka ta shige dakinta tana danna lambobinshi a wayarta.
*******
Cikin nutsuwa ta sanya hannu ta kwankwasa kofar dakin, a zuciyarta tana kissima irin yanda haduwar tasu ya kamata ya kasance.
Saida ta sake kwankwasawa sannan taji alamun ana k'ok'arin bude kofar.
Kallon-kallo ne ya gudana tsakaninsu na wasu seconds, ya sakar mata tattausan murmushin da ya kusa zauta d'an sauran nutsuwar da ya rage mata.
Fari tayi da kyawawan idanunta tana kallonsa kasa-kasa.
"In shigo?"
Ta tambayeshi da murya sassanya.
Wani murmushin ya sake haske ta dashi ya saki hannun kofar ya juya zuwa cikin dakin, alamun ta shiga kenan, bayansa tabi da kallo tana jin duk wani lungu da sak'o na zuciyarta na sake cika da kaunarshi.
Yana sanye da vest fara kar da dogon wandon jeans, da ta kalli kafadunsa kirar karfi ne a baiyane duk sun cuccure, kirjinsa da ta hango kuwa cike da gargasa bak'i kirin.
Akan doguwar kujeran dakin ya zauna yana kallonta, har wannan lokacin murmushin fuskarsa bai 6ace ba.
Dogon hijabin jikinta ta cire tayi hurgi dashi a tsakar dakin ainahin shigar kananun kayan da tayi ya baiyana, ta tsuke tsam cikin riga da wando masu baiyana surar jiki, gefenshi taje ta zauna har cinyoyinsu na gogar juna.
"Naji dad'in sake haduwa da kai a karo na biyu Sweetheart, hope kaji dad'in gani na?"
Mamaki ne ya sake k'ume shi, ya kasa shiru har saida ya magantu.
"Mahaifinki yana da yarda dari bisa dari a kanki da nutsuwarki kinsan wannan? Amma abinda ya kara bani mamaki shine bayan shaye-shaye ashe ke 'Yar hannu ce"
Ya karasa fadin haka yana janyota jikinsa.
Da mamaki ta dago kanta daga kirjinsa tana kallonsa, sai kuma tayi dariya.
"Taya akai ka gane ina jin dad'in rayuwata da benelyn?"
"Idanu kawai na kallah gane halaiyar mutum cikinsa da wajensa nake yi. Dan haka karki damu, naji dad'in haka"
"Do you love me?"
A bazata tayi mishi tambayar tana kure shi da kallo da dara-daran idanunta.
Dariya kawai yayi, da salon son basar da maganar yace
"Kinsan wani abu? Yanzu fa ba lokacinki bane, lokacin matar babanki ne kinsan haka? Ta dame ni da magiyar insa lokacin had'uwa da ita akwai muhimmiyar maganar da zamuyi, sai kuma kema kika nemi gani na.
And ni kuma wannan lokacin kawai ke gare ni shiyasa na baku lokaci daya, akan duk wacce ta riga zuwa ita ce lucky.
Sai kika riga ta bayan ta riga ki neman alfarmar, ta ya akai haka my dear?"
Tura baki gaba tayi ta sake cusa kanta cikin kirjinsa tana shakar kamshin jikinsa
"Ni ce mai sa'a, kuma ma ni ce nafi dacewa da kai.
Pls sweetheart karka ta6a bata damar ganawa da kai ka ji? Dan Allah kayi min wannan alfarmar"
Murmushi yayi idanunsa suka sauka akan agogo da yake manne a bangon dakin.
"Babe lokacinki ya kare, ya kamata ki tafi"
Da sauri ta kalleshi, tana jin dadin yanda take kwance a kirjinsa zai wani ce lokacinta ya kare? ita kam ba haka ta so ba, ta zaci ko dan sumbata da zafafan runguma da tsotse tsotse zai shiga tsakaninsu sai taga bayan janyota jikinsa da yayi bai ne nemi abinda ya wuce haka ba.
"Ayya mana Sweetheart tun yanzu? Ni wlh ban son mu rabu yanzu"
Yanayin fuskarsa ne ya canza cikin kankanin lokaci, janyeta yayi daga jikinsa ya mike tsaye baice mata komai ba.
Gogaggiyar rigarsa da take ajiye gefen gadon ya dauka ya fara k'ok'arin sakawa, daman haifi minti biyar da yin wanka ba ta shiga dakin.
"Zan tafi idan kin gama zuwa yamma ki kulle dakin ki kai musu makullin"
Yana gama fadin haka ya dauki jakar kayansa da wayoyinsa ya fice a dakin, ko kallonta bai sake yi ba.
Baki da hanci bude ta bishi da kallo tana mamaki, shi kuma wannan wani irin mutum ne? Tayi mishi tallan kanta a kyauta ya fice ba tare da ya taya ba?
Abinda bata sani ba Shi Usher harkokin mata basu dame shi ba, ta nan fannin kuma Allah ya tsare shi, bai ta6a keta mutuncin diya mace ba, ba kuma wai dan yasan zunubin hakan ba kawai shi abin bai dame shi bane.
*
Tana tsaye a jikin windon ta dage labulen kadan tana shakar iskar yammacin mai cike da ni'ina, da yake suna saman farko ne tana kallon duk mutanen da suke zirga-zirga a harabar hotel din.
Mijinta Abdullahi yana zaune a gaban laptop dinsa yana aiki, lokaci zuwa lokaci yana juyawa ya kalle ta yayi murmushi yace
"Idan dai kin gaji ki dawo ciki ki zauna, bana so ki wahala Noory"
Idan ya fadi haka tattausar murmushi take sakar mishi tace
"Angama Noor, kaidai ci gaba da aikinka"
Kamar a mafarki danunta suka sauka akan fuskar wanda ko a cikin magagin barci ta ganshi bazata ta6a manta kamanninshi ba.
Yana tsaye jikin motarsa yana amsa waya, lokaci zuwa lokaci yana daga kansa ya kalli gabas da yamma na cikin hotel din Kaman yana neman wani.
Da mugun sauri ta sake tura kanta ta jikin windon kiris ya rage ta sulmiya kasa mijin ya riko ta da sauri wanda ya isa gurin a daidai lokacin
"Amatullahi kinyi hauka ne? me yake damunki?"
Ya tambaye ta kirjinsa na bugawa cike da tsoro, da ta fad'a da ya gama ganin ta kanshi a rayuwa.
"Yayanmu..! Wallahi Yayanmu ne...!! Ga shi can zai tafi bai ganni ba..!!! Dan Allah ka barni inje gurinsa Noor.."
Ta amsa mishi hankalinta a tashe tana kara cusa kanta ta jikin windon tana lekenshi, ita duk kokarinta ta dira ta nan taje ta dakatar da shi.
Yana rike da hannunta gam ya leka ya hangesa, har a lokacin waya yake yi amma hannunsa daya na rike da kofar mota bangaren mazaunin direba, alamun ako wane lokaci zai shiga yaja motar ya kara gaba.
Hannunta yaja da matsanancin sauri suka fice daga-dakin, gudu gudu, sauri sauri suke taka matakalar da zai saukar dasu zuwa kasa yana gaba tana binshi a baya, tsabar zumudi har hawayen murnar ganinsa ya fara zuba daga idanunta.
Abin takaici da bakin cikin shine ko kafin su sauka kasa, zuwa harabar hotel din bashi ba alamar motarsa, har yaja ya fice daga hotel din.
Turus sukai a tsaye duk su biyun suna waige-waige, da suka tabbatar ya tafi ne sai jikinsu yayi sanyi, daga karshe ma Amatullahi saita fashe da kuka ta fada jikin mijinta Abdullahi.
Rirriketa yayi yana fada mata kalaman kwantar da hankali a kunnenta, ganin hankalin mutane ya fara dawowa kansu yasa yaja ta a kafadarsa suka shige ciki zuwa masaukinsu.
Ta dau tsawon lokaci tana kuka, yana ta rarrashinta cike da kauna da kulawa, ganin hankalin sa ya fi nata tashi yasa ta kwantar da nata hankalin, har ta haske shi da tattausan murmushinta.
Lokaci kadan sai gasu suna kyalkyala dariya gwanin ban sha'awa.
"Hellow Aunty Ama"
Aka amsa wayar daga can bangaren.
"Baby Iman albishirinki?"
Ta fada da murmushi a fuskarta tana sake gyara kwanciyarta akan cinyar mijinta.
"Goro fari, k'atoto"
Ta amsa da murmushi a fuskarta.
"Wallahi yau naga Yayanmu Kamal, a hotel din da muka yi masauki da Noor a kano.."
'Kuuuu Daga can bangaren Khadeeja ta taka burki da matsiyacin karfi, kiris ya rage motar bayanta ya gwabza mata Allah ya tsare, da sauri ta gangara gefen titi tana k'ok'arin parking mai motar bayanta ko ya dunkule hannu ya bude ya watsa mata damuwa, ko kallonshi bata yi ba ta ci gaba da amsa wayar muryarta na rawa
"Aunty Ama da gaske kike yi? Ina yake? bani shi pls inji muryarsa.. Ya kika ganshi?"
Tambayoyi take ta watsa mata a rude ta ma kasa nutsuwa balle ta daidaita kanta taji me take cewa, saida ta kashe ta sake kiranta.
"Iman ina saman bene na ganshi ko kafin in sauka gurinsa ya wuce"
Amatullahi ta amsa jikinta da muryarta a sanyaye.
Shiru tayi daga can bangaren hankalinta a tashe, wasu siraran hawaye ne suka silalo mata. Dakyar tayi karfin halin cewa
"Ba komai, wannan shi ke bamu tabbacin yana raye bai mutu ba, mu ci gaba da addu'a in Allah ya yarda zamu hadu dashi wata rana, akwai lokaci"
Tana gama fadin haka ta katse wayar, kifa kanta tayi a sikiyarin motar tana ta hawaye.
*BARA A KUFAI!!*
*23)*
****
Tunda ya dauki hanyar wuta yake budewa motar yana wuce duk motar da yayi gamo da ita.
Ringing din wayarsa a karo na uku ne yasa ya dan sassauta gudun kad'an.
Ransa ne ya kara baci, me kuma zata ce masa bayan ya riga da ya sallame ta?
"Menene kuma? Na zaci mun gama duk maganganun da zamu yi kafin mu rabu?"
Ya tambaye ta bayan ya daga wayar, muryarsa na baiyana fusatar da yake ciki.
"I'm very sorry Sweetheart, dan girman Allah kayi hakuri da gaddamar da nayi maka"
Ta fad'a daga can bangaren cikin marairaicewa, sai sheshsheka da Jan majina take yi, da alamun kuka take yi.
Tsawon minti biyu yana cika da batsewa, sai jan fasali yake yi kamar bazai amsa ta ba, ita kuma bata daina kukan ba kuma bata katse wayar ba, shi kuma baida niyyar rarrashinta.
"Kace wani abu mana dan Allah.."
Ta fadi haka tana bubbuga kafafu cikin shagwa6a kamar yana kallonta.
"Is ok.. Ya wuce. Amma ki kiyaye sake faruwar hakan ko nan gaba. Yanzu ina hanya ne, zamu yi waya anjima"
"Ina zaka je Sweetheart?"
"Kaduna"
Ya amsa kai tsaye ya katse wayar ba tare da ya jira amsawarta ba.
"Yes"
Ta fadi hakan a fili, fuskarta na baiyana tsananin farin-cikin da zuciyarta take ciki, juyi tayi akan gadon tana kwakwume wayar a kirjinta kamar ta rungume Usher.
Farin ciki take sosai, bata ta6a tsammani taraiyarta dashi zai zo mata da mugun sauki kamar haka ba, sai gashi cikin kankanin lokaci yana neman afkawa kogin so da kaunarta, ita kam daman ta dad'e da nutsewa a cikin kogin sonsa sai nink'aya take yi.
****
"Ya? Daga nan mu wuce dakina ne?"
Ya tambaye ta yana kallonta ta madubin gaban motar.
Tana hakimce akan kujerun bayan motar tana daddana wayarta, jin abinda yace yasa ta dago kai ta kalleshi ta madubin, a lokacin shi kuma ya maida hankalinsa kan tukin da yake yi.
Harara ta galla masa kamar idanunta zasu fad'o, ganin ya dago kai yana kallonta yasa ta wayance ta hanyar sakar mishi tattausan murmushi.
"Haba de Nura, yanzu baka ga yamma tayi ba? Gida ya kamata mu wuce kai tsaye.
Akwai dai sallama na musamman da na tanadar maka, kuma a cikin kayan da na amso ma na ware maka naka na musamman, kasan ina ji da Kai.."
"Ke dallah dakata min!"
Ya fada ransa a bace, ya lura ta ma raina mishi hankali.
"Karki maida ni karamin dan iska mayen kudi mana, ya tuntuni ki kai min alkawari kin gagara cikawa ne? Na fada miki yanzu bana bukatar kudin ki kibani lokaci kawai in huta dake na yini guda.
Tuntuni kike sa min rai amma sai jana a kasa kike yi. Ke kin sani rayuwarnan cud'eni in cud'eki ne, ina miki alfarmomi da dama kina shanawa yadda kike so ba tare da sanin mahaifinki ba shine zaki nemi raina min wayar?"
Kwafa yayi yana cije gefen bakinsa na dama, ya kalleta da jajayen idanunsa ta jikin madubin motar.
"Zan nuna miki ke karamar 'yar tasha ce, na fiki tashanci. A banza ma kike kaima wasu 'yan iska kanki suna abinda suka ga dama sai ni da nake tare da ke ne zaki maida d'an iska.."
"Ayya Nura.. kayi hakuri mana? Ni fa Wallahi ko da kake gani na hakan nasan darajar kaina, ina tsananin tsoron abinda zai ta6a mutunci na, domin nasan hakan babbar illa ne da zaiyi ta bibiyata har jikoki.
Dan haka Gaskiya saidai kayi hakuri in ci gaba da sallamarka da kudi, idan kuma baza ka amsa ba kayi duk yanda zaka yi"
Ta karasa fadin haka tana murguda baki.
Dariya kawai yayi yana ci gaba da kallonta ta madubin
"Ai haka kika ce koh?"
Ya tambaye ta yana girgiza kai dama da hagu kamar kadangare.
"Abinda kunnenka ya ji maka"
Ta amsa babu alaman damuwa ko kadan a tattare da ita.
Haka kawai? Dan yana gadinta yana barinta tayi abinda take so shine zai ringa gindaya mata wasu sharudda kazaminshi dashi.
Duk abinda zaiyi dai bai wuce yace zai had'ata da mahaifinta ba, ko kuma ya daina barinta tana abinda taga dama.
Dan wadannan ko a jikinta, tunda ta samu Usher ya fiye mata komai da kowa, shi kuwa ko ana ha maza ha mata dole sai ta nemi hanyar fita zuwa gurinshi.
Harkokin sana'arta kuwa ta waya kawayenta suke booking idan taje makaranta su kar6a, wadanda ba 'yan makarantansu ba zata ce musu su turo a karba musu a school.
Kayan sana'a kuma duk inda take zata sa Moses ya aiki Gwaska ya kai mata. In yaso saita kara mishi sallama akan kudin kaya.
Dan haka ko da ya kulle alfarmomin da yake mata na samun damar yawo ba abinda zai rage ta dashi.
"Ga shi?"
Ta ciro dubu biyar a jakarta ta mika mishi lokacin da suka kusa isa gida.
Kallon kudin yayi a raine, murmushi yayi yace
"Ai na fada miki bazan sake kar6ar kudin ki ba, ki barsu kawai ki kara jari"
Galala take kallonsa tana mamaki, Nura ne yau ta bashi kudi yaki karba? Ta dage kafada alamun ko a jikinta, ta maida kudadenta cikin jaka.
"Ta fi nono fari"
Yana shiga da motar cikin gidan ta bude kofar ta fice tun bai gama daidaita fakin ba, share shi tayi ko sallama batai mishi ba, tana nufar cikin gidan take tunanin dole zai neme ta, dama dai ba Shi bane mayen kudi, akan dubu daya ko uwarsa kace ya mara tsaf zai tsinketa da mari, da bakinsa ya fada mata haka, ya gwammaci idan ya dafe dubun yaje ya bata hakuri.
Dan haka ta zama kuturwar uwa zama da ita dole, idan bai neme ta dan ta bashi kudin da zai nemi mata ba zai neme ta dan ta bashi kayan shaye-shaye.
Agogon wayarta ta kalla ganin har a wannan lokacin tana kwance tana barci kamar yanda ta barta.
Awa hudu kenan da minti goma sha biyu, dariya ta kwashe dashi tana nuna ta da d'an yatsa.
"Ba saban ba"
Ta fadi haka a fili ta nufi dakinta har lokacin bata daina dariyar ba.
Bata farka ba sai karfe takwas da minti hamsin na dare, mika tayi tana yamutsa fuska, wuyanta da bangaren hannunta sai ciwo suke saboda rashin kwanciyar jin dad'i a kansu.
Kanta da taji yayi mata wani gingirin kamar an dora mata yasa ta tallabeshi da hannu biyu.
Idanunta ne yakai kan wayarta da yake ajiye gefe daya, da mugun kasala ta kai hannu ta dauko dan ganin lokaci, idanunta ta bude gaba daya akan wayar tana mamaki, wani tsoro ne ya kamata lokacin da ta kalli agogon falon taga tabbas fa saitin wayarta ba gocewa yayi ba, karfe tara ne saura minti biyu na dare.
"Wani irin barci nayi haka kamar 'Yar maye?"
Ta tambayi kanta hannu bibiyu akai tana takaicin mugun barcin da tayi.
Motsin fitowa daga kicin yasa ta maida hankalinta gurin dan ganin mai fitowa.
Fatima ce, tana sanye da kayan barci riga da wando, hannunta na hagu rike da kofi ta had'o tea a ciki saboda sanyi-sanyin da ake yi, hannunta na dama kuma wayarta ne tana daddanawa, kan daya daga cikin kujerun falon ta zauna bata ko kalle ta ba, kamar ma bata san da ita a gurin ba.
"Fatima wani irin barci ne kika barni nayi haka mai nauyi akan kujera?"
Ta tambaye ta ranta a bace, gani take ai duk laifinta ne tunda tana gidan amma ta kasa tashinta ta shiga daki.
"Eh to da yake nima barcin nayi, ban wani dad'e da tashi ba..."
"Amma ai dai kin riga ni tashi, ko baki tashe ni Dan komai ba ai kya tashe ni inyi sallah..."
"Yau kuma?"
Ita ma ta katse ta tana kallonta sama da kasa.
"Kin manta rannan da na shiga har daki na tashe ki dan kiyi sallar kika gwasale ni ta hanyar ce min kabarinki daban nawa daban?
Shiyasa nace idan zaki yini ki kwana kina barci akan kujerar nan Wallahi bazan tashe ki ba.
Mutunci daya zan iya miki idan naga dama in shiga bedroom dinki in dauko bargonki in lulluba miki sabo da sanyi"
Tana gama fadin haka ta dauki kofin ta shige dakinta tana murmushi.
Takaici ne cunkushe da zuciyarta ta dauki wayarta ta sake duba lokaci, sai a wannan lokacin ta lura da 10 misscalls din da yake fuskar wayar.
Ganin harda sunan *Alh Tanko Sweety* a cikin wadanda suka kira ta yasa taji wasu zafafan hawaye suna zubo mata.
Wannan mugun barcin da tayi yaja mata manyan asorori da dama, bayan asarar haduwa da gwarzon masoya *Usher durling* harda asarar haduwa da babban dan siyasan nan *Alh Tanko Sweety* wanda yayi mata alkawarin naira miliyan guda matukar tayi mishi yadda yake so.
****
Tana amsa waya a cikin keke napep tana jiran ya bata canjinta ta hangi fitowarsa daga cikin *OSTRICH BAKERY* hannunsa rike da leda mai d'auke da tambarin gurin.
Da yake daga nesa ne gashi kuma dare ne bata ganin fuskarsa sosai, saida ya matso kusa sosai yana k'ok'arin bude motarsa da take kusa da keke napep din.
"Subhanallahi..."
Ta fad'a da sauri muryarta na rawa.
"Malam yi sauri ka bani canji ga Yayana can zan bishi zuwa gida"
Har ya bude motar ya tuna yabar wayarsa a ciki inda ya zauna shan ice cream, dan haka ya nufi ciki da sassarfa ba tare da ya kulle motar ba.
Yana mika mata canji kamar yaki ta fisge ta fita a sukwane, bangaren baya na motar ta bude ta rufe da sauri, ta dunkule guri daya yanda ko ya shiga cikin motar idan bai leka baya sosai ba bazai ganta ba.
Kanshi tsaye yaja motar ya fice daga gurin bayan ya fito daga dauko wayar tasa.
Tun tana hasashen suna cikin tudun wada har ta daina, dan yanda taji ya bude wuta sosai yana gudu, sake gyara kwanciyarta tayi yanda zata ji dadi babu tsoro ko kadan a tare da ita, dan tana da yakinin bazai cutar da ita.
Wakar shaku-shaku ya kunna ya kure speaker sosai yana bin ko wane baiti na wakar cikin kwarewa, a wannan lokacin ne Isa bakanike ya fara kiranta a waya.
Zazzaro ido tayi zuciyarta cike da tsoro, inda Allah ya taimake ta wayar a vibration take, sautin wakar da yake ji yasa baiji kiran wayar ba, da sauri ta katse wayar ta danna a silent.
Sigarin da ya kunna yana zuka da fesar da hayakin hanci da baki shiya fallasa asirin tana cikin motar, ta tsani warin sigari sam, da a sha taba a gabanta gara ayi kashi a gabanta.
Take ta fara tari ba kakkautawa tana rike da kirjinta hannu bibiyu, ganin tana neman kashe kanta yasa ta dago kanta da sauri a lokacin har ta fara hawaye, tarin kuma bai tsaya ba, numfashi take ja sama-sama kamar mai asthma.
Ganinta a cikin motar bai wani tsorata shi sai mamakin da ya bashi, gangarawa gefen titi yayi ya faka motar, a lokacin har ya kusa isa gidan da yake sauka idan ya shiga Kaduna.
Yaga lokacin da ta shiga motar ita ce take tunanin bai ganta ba, duk wani muku muku da taita yi a cikin motar ma yana jinta, yaji kiran da akai mata a waya amma duk ya share yana son yaga iya gudun ruwanta.
Sosai ya fahimci hayakin sagarin ne ke wahalar da ita amma yaki kashewa.
"Me ya kawo ki cikin mota ta ?"
Ya tambaye ta da kakkausar murya bayan ya gama shanye karan sigarin yayi hurgi da dan guntun ta windon motar.
Sam ta kasa magana, sai k'ok'arin daidaita numfashinta take yi, fuskarta kace-kace da hawaye.
Har a wannan lokacin bata yi dana sanin binshi ba.
Ita daman a niyyarta sai taga gidan da yake zaune saita fallasa mishi kanta ta kuma sanar dashi ko ita wacece, idan bai yarda ba ta koma ta dauko Dr. Abida ayi ta ta kare su basu shi.
Ganin da yayi tana kara bata mishi lokaci bata yi magana ba yaja motar zuwa cikin layin, da kanshi ya bude get din ya shigar da motar ciki tunda babu mai gadi.
"Fito"
Ya bata umarni bayan ya bude kofar bangaren da take zaune.
A galabaice ta zuro kafafunta ta fito waje dan tana tsananin bukatar iskar shak'a ba mai tattare da warin sigari ba.
Wani kakkarfar amai ne ya taho mata da saurin gaske ta tsuguna a kasa ta fara kwarara shi, ya kalleta kawai ya wuce ya kulle gidan, tana ta yunkurin ya sake wuce ta zuwa cikin falon gidan ya dauko kujerar dining ya zauna can nesa da ita.
Kallonta yake yi babu alamar ko digon tausayinta a tattare dashi, jira yake ta gama ta fada mishi dalilin da yasa ta shiga cikin motarshi da hankalinta ba tilasta ta yayi ba.
Pure water ya mika mata mai bala'in sanyi wai ta kuskure bakinta dashi, da kyar ta iya kurkurawa sau biyu saboda sanyin ta aje ruwan gefe daya.
"Have a sit"
Ya fada bayan ya dauko mata kujera guda daya irin wanda yake zaune akai.
"Sunana Khadeeja... Kahadeejatul Iman Auwal Sa'eed.
Ma'aikaciyar jarida a kamfanin Jaridar *Gaskiya komai d'acinta*"
Ta fara fad'a mishi da galabaita a tattare da jiki da muryarta har wannan lokacin.
"Waw! That's good my dear. Ashe kin biyo ni dan ki samu damar hira da dilar miyagun kwayoyi Usher ko? Nayi miki murna.."
Zazzaro ido tayi tana kallonsa, sai a wannan lokacin ta fara jin tsoro yana mamayarta, ita me yasa ma ta biyo shi? Rabonsu dashi shekaru hudu kenan ba kwana hudu ba.
A cikin wadannan shekarun tasan zai iya haduwa da koma wasu irin mutane ne su gurbatar da tunanin shi tunda ba'a hayyacinsa yake ba.
"A'a Wallahi ba haka bane.."
Ta fada da sauri muryarta cike da tsoro.
Wata dariya yayi yana kallon yanda take a tsorace
"To Yaya ne?"
Ya tambaye ta bayan ya hade fuska tam yana kara karantar yanayinta.
"Na biyo ka dan in sanar da kai wani sirrin da baka sani ba"
"Ehen ina jinki"
"Ba fa sunanka Usher ba, sunanka Kamaluddeen, kuma kai Yayanmu ne ni da Amatullahi da take aure a Gombe.
Mahaifiyarmu kuma Dr. Abida tana gida"
Ta fada a rude duk ta ma rasa ta yanda zata kamo mishi bayanin har ya fahimceta.
Wadannan idanun nashi sai kara rud'ata suke yi.
Wannan shine babban rainin hankalin da wata 'ya mace ta ta6a yi mishi a iya tsawon rayuwarsa.
Kallonta yake hannuwansa biyu tallabe da gemunsa yana tunanin irin hukuncin da ya kamata yayi mata.
Ita kuwa sai yarfe yatsun hannunta take yi kamar zata saka kuka.
"Nasan zaka ji labarin wani iri, Amma Wallahi da gaske nake yi"
Ta sake fada a marairaice, idanunta har Sun fara tara hawaye.
Cikin falon ya shige ba tare da ya tanka mata ba, shiru tayi tana ta addu'ar Allah ya takaita mata wahala.
Daga kai tayi tana kallon tsakar gidan dan madaidaicin dan tsakar gidan mai kyau, yaji interlock ta ko ina.
Ga haske tar kamar rana, kusan ko wane bango akwai kwan lantarki guda biyu.
Fitowarsa daga cikin falon yasa ta maida hankalinta a kanshi, ganin ya nufo ta hannunsa dauke da igiya yasa ta fara mutsu-mutsu akan kujerar, kamar wacce aka rikewa kafafu kuma ta kasa tashi.
"Dan Allah dan Annabi karka duke ni Yayanmu"
Ta fada da rawar murya, wasu siraran hawaye har sun fara zubowa daga idanunta.
"Ko ina da saurin hannu ai bazan daki mace ba, balle ma wannan kyakkyawar 'yar Jaridar da nake ganin Mari na guda daya zaisa ta iya mutuwa"
Ya fadi haka yana warware igiyar daga nadin da akai mata.
"To me zakai min?"
"Daure ki zanyi, yanda nan gaba ko da wasa bazaki sake marmarin zuwa min da wani salon rainin hankalin ba"
"Ayya.. Ayya... Dan Allah mana Yayanmu..."
"Idan baki min shiru ba zan hada dukda bakinki in d'aure, yanda baza ki iya magana ba balle ki ishe ni da tambayoyi kamar cakwaikwaya"
Cikin minti uku ya daure ta a jikin kujerar, daurin da bazata wahala sosai ba amma kuma bazata iya kwancewa ta gudu ba.
"Dan Allah ka barni in tafi gida, nayi alkawarin bazan sake bibiyarka ba"
Yana daf da shigewa cikin falon ya jiyo ta tana fadin haka, ko waigowa baiyi ba ya maida kofar falon ya rufe 'bam'.
Shiru tayi a tsananin tsorace, ta ma rasa irin tunanin da ya kamata tayi.
Ga shi ta bar wayarta da jakarta a motarsa balle ta kira Mummy ko Amatullahi ta sanar dasu halinda take ciki.
Kukan sauron da take ji a kunnenta yasa take ta juye-juye da kanta, ta tsani kukan sauro da cizonsa, ga kuma sanyi sanyi na iskan hadari da take ji yana kadawa, wani lokacin ma harda rugugin hadari, alamun za'a iya samun ruwa cikin dare ko da asubah.
Tun tana tsammanin zai zo ya kwance ta a cikin kasa da mintina ashirin har ta daina.
Ko motsinsa ma ta daina ji, hawaye na ta zuba a idanunta lokaci zuwa lokaci.
Ita dai tasan babu batun barci a gare ta wannan dare, cizon sauro ma kadai ya isheta azaba.
Karfe goma sha daya da rabi na dare ruwan sama mai masifar karfi ya fara saukowa kamar da bakin kwarya.
Bude baki tayi iya karfinta ta rushe da kuka mai tsananin karfi.
Tunda ya shiga falon ya wuce zuwa dakin barcinsa, wata kwaya ya dauko guda daya ya tattauna ta ya hadiye ya kora da ruwa, nan ya zube akan gado yana barci da taimakon kwayar da ya hadiye ga kuma gajiyar hanyar da ya kwaso.
Bai farka ba sai karfe biyu da minti biyar na dare, a lokacin ma wata masifaffiyar yunwa ce ta tashe shi.
Jin saukar ruwan sama ta windon dakin yasa ta fado mishi a rai.
"Inna lillahi.."
Ya fada a fili ya mike da sauri ya nufi wajen a sukwane, inda Allah ya taimake ta ma har wannan lokacin nepa basu dauke wuta ba.
Amma duk wannan Uban ruwan saman a kanta ya kare.
Da sauri ya fara kwance igiyar da ya daure ta ruwan yana zuba a jikinsu tare
"I'm very sorry Babe"
Kalmar da yake ta maimaitawa kenan ya tarairayo ta gaba daya zuwa jikinsa ya nufi cikin falon da ita.
A bakin kofar falon ya cire hijabin jikinta yayi hurgi dashi dan ya jike jagab yana tsiyayar da ruwa.
Doguwar rigar material din da take jikinta ma a jike take sharkaf, ya manne a jikinta sosai siffofin jikinta duk sun baiyana.
Halin da take ciki na tsananin galabaita da matsanancin jin sanyi yasa bata Kula da hakan ba, hakoranta sai haduwa suke gaf-gaf.
Yana rike da ita har cikin dakin barcinsa.
Ya ma manta ko ita wacece ya juyo da bayanta ya zage zip din rigar jikinta, yana kokarin cire mata rigar tayi saurin make hannunsa tana kuka.
"Ni ka kyaleni... mugu kawai.."
Ta fada cikin kuka.
Sai a lokacin ya ankara da abinda yake k'ok'arin yi, ya saci kallon bayanta da ma6allin bra dinta ya baiyana, a karo na farko a sabuwar rayuwarsa da yaji matsanancin kunya ta kama shi.
Sosa kanshi yayi yana murmushi
"To yi hakuri, tube da kanki barin hada miki ruwan zafi kiyi wanka"
Bai saurari cewarta ba ya shige bayin da yake cikin dakin ya tara mata ruwa mai zafi.
Yana sanar da ita ya hada ruwan ya fice daga dakin zuwa falo.
Saida ta dauki tsawon lokaci tana kuka, ga kanta kamar zai tsage dan ciwo, har wani zazza6i zazza6i take ji, sanin da tayi wankan kawai shi zaisa taji dama-dama yasa ta shiga wankan.
Tana yi tana kuka har ta gama, towel ta gani a rataye cikin bayin ta dauka ta daura.
Kafin ta fito har ya fito mata da kananun kaya a cikin kayansa sabbi ya aje mata a gefen gado, ya dauko mata rigan sanyi duk ya aje sannan ya sake ficewa a dakin da kayanta a hannunsa.
A gurguje tasa kayan da ya aje mata ta kudundune akan gadon ta lullu6a da bargon da aka shinfida a gefen gadon.
Ko da ya shiga ya ganta ta rufa har kanta sake fice wa yayi bai lura da rawar sanyin da take yi ba.
Yana hada tea wani farin ciki da nishadi na kwaranya a zuciyarsa, ya kuma dalilin wannan farin cikin.
Sai 'yan wake-wake yake yi cikin nishadi kamar wani karamin yaro.
Daf da asubah da ya sake lekawa dakin ne ya ganta tana ta juye juye da kara takurewa cikin bargon.
Da ya bud'e ta ya ta6a jikinta zafi zau da sauri ya dauke hannunsa.
"Wayyo... wayyo.. Mummy ki rufe ni sanyi... wayyo kaina..."
Ta fada cikin magagin ciwo tana kara jan bargon dan ta sake lullubewa.
Wani mugun tausayinta ne ya lullubeshi, lokaci na farko a rayuwarsa da yake ji a ransa yasha kwaya a lokacin da bai dace ba.
Tabbas da yana cikin haiyacinsa bazai bari ruwa ya duke ta ba. Kicin ya koma yayi diri-diri ya rasa wane taimako ya kamata ya bata?
Tea ya hada mata mai zafi ya dauki kwayoyin paracetamol guda biyu ya nufi dakin dasu a hannunsa.
Ajiyewa yayi a gefen gadon ya bude ta ya janyota jikinsa gaba daya, ya fara k'ok'arin kafa mata kofin a bakinta.
Kauda kanta tayi dakyar ta bude idanunta da sukai mata nauyi sosai tana kokarin kallonsa, dukda bata da karfi kici-kicin kwace jikinta take yi tana gungunin ita ya daina ta6a ta.
"Ok ga tea da magani kisha sai in kyaleki kiyi barcin ki"
Da zafi-zafin taita kurba har ta kusa shanyewa, ta fincike maganin kamar yaki ta watsa a baki ta shanye da ragowar ruwan tea.
Dangwarar da kofin tayi ta sake rufa har kanta.
Murmushi yayi ya dauki kofin ya fice daga d'akin, a ransa yake jin wani abu
mai kama da tana burgesa yana ta safa da marwa a zuciyarsa.
*BARA A KUFAI!!*
*24)*
Karfe shida na asubah ta farka daga wahalallen barcin da take yi mai cike da wasu irin mafarkai da ta rasa gane kansu.
Amma ta samu sauki sosai Alhamdulillahi.
Yanzu babu zazza6i a jikinta, ciwon kai ma yayi mata sauki sosai sai abinda baza'a rasa ba.
Alwala ta shiga bayinsa tayi, tana tafe tana rirrik'e kugun wandon jikinta, dan yayi mata yawa sosai.
Shi mutum ne mai siffar jaruman maza, ga kuma kiran karfi a tare da shi.
Ita kuwa siririya ce, sai dai tana da cikan kirji da Hips masha Allah.
Saida tayi alwalar ta fito ta tuna babu hijabinta a dakin, bata ma san inda ya hurga mata ba.
Ta nufi kofar dakin zata fita dan ta tambayeshi ina ya ajiye mata ko a jik'en ne ta kakkabe tayi sallar sai taji surutun mutane da hayaniya na tashi a falon.
Kuma da alamun maza ne, dan bata ji muryar mace ko sau daya a cikin surutunsu ba.
Wasu zafafan hawaye ne suka fara zubo mata da taji irin maganganun da suke yi, taga-taga tayi kamar zata fadi saboda har lokacin babu karfi sosai a jikinta da sauri ta rike hannun kofar.
"Ashe da gaske yake mata da yace Shi dilan kayan maye ne? Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un. Wannan wani irin mummunar sana'a ce?"
Tana tsaye a jikin kofar taji yana rarraba ma mutanen da suke zaune a cikin falon kayan mayen, su kuma suna sallamanshi da manyan kudade.
"Oga wannan karon kayan da ka bani basu kai na last time ba fa. Ya kamata ka kara min ko kadan ne"
Taji muryar wani daga cikinsu ya fadi haka.
"Hakuri zaka yi da abinda ya samu Musty. Sabbin customers muka samu a kano, shiyasa ko wane jiha kayan da muke shiga dasu basu kai na ko wane lokaci ba"
Taji muryar Kamal ya amsa da hakan.
"Oga yaushe zaka bar gari?"
Wani ya sake tambayarsa
"Gobe da yamma zan wuce Abuja"
Sauri-sauri ya sallamesu saboda duk rabin hankalinsa yana kanta, bai sani ba ko ta tashi.
Har zai shiga cikin dakin ya dawo falon ya fesa room freshener a lungu da sako na falon, bai manta yanda ta galabaita sosai jiya da yake shan sigari ba, tun kafin abokan sana'arsa su iso gidan yake ta bankawa cikinshi hayaki, suma har sun tayashi busawa.
Wasu 'yan farantai guda biyu cike suke da guntattakin sigari.
Saida ya kakkabe hannunsa ya gyara zaman kwalar rigarsa sannan ya murd'a hannun kofar ya shiga ciki ba tare da yayi sallama ba.
Karo suka gwabza dan tana tsaye a jikin kofar tana kuka, nisan da hankalinta yayi yasa bata ji lokacin da ya murda hannun kofar ba, taga-taga tayi zata fadi yayi saurin tallabo ta.
Da karfi ta make mishi hannun da ya rike kugunta ta galla mishi harara idanunta kamar zasu fado kasa, ga fuskarta kaca-kaca da hawaye.
Yarfe hannunshi yayi kamar yaji zafi yana murmushi, ya kurawa kirjinta ido yanda tudunsu ya taso sosai a rigarsa da yake jikinta.
Ganin abinda yake kallo yasa ta yayimi bargon kan gadon ta rufa a jikinta ta sake fashe mishi da kuka mai masifar karfi.
" *Darling Girl,* kukanki yana saka ni nishad'i.
Pls ki ci gaba da yi"
Ya fadi hakan yana dariya, babu damuwa ko kad'an a tattare dashi.
Dif ta tsaida kukan nata kamar an kashe radio, ta sake gallah mishi wata hararar, gaba-dayanshi ma haushi yake mugun bata.
Kamar ta tashi ta rufe shi da duka haka take ji a zuciyarta.
Wai Kamal dinsu da babu ruwanshi ne ya zama haka? Wannan wane irin muguwar kaddara ce?
"Ya Allah"
Ta fada a fili sannan ta dafe kanta da hannu biyu tana jujjuya idanunta cike da damuwa. Ta ma rasa abinda ya kamata tayi, kanta ya kulle gaba - daya.
"Ina kaya na?"
Ta tambaye shi ciki-ciki, bata ma yi tsammani ya ji abinda tace ba sai taga ya fita daga dakin.
Minti biyu tsakani ya dawo hannunsa dauke da kayanta, a cikin daren zuwa asuba har ya wanke ya baza a fanka sunsha iska ya goge su tsaf.
Tattausan murmushi ta sakar mishi, dama duk tunanin ta idan a jike suke ya zata yi har ta koma gida? Gaskiya taji dadi sosai.
Hannu biyu ta karbi kayan, da murmushi ta kalle shi kasa-kasa
"Na gode Yayanmu"
Sai kuma ta gallah mishi harara da ta tuna ko waye shi a yanzu, ta kara da murguda mishi baki dama da hagu.
Dariya ya kwashe dashi yana nuna ta da yatsarsa manuniya, shi kam ba karamin dariya take saka shi.
Cike da tsiwa ta kalle shi, cikin masifa tace
"Ni ce na zama abar dariya? To na gode, fita ka bani guri zan shirya"
" *Darling girl*"
Ya sake fad'a a daidai lokacin da zai fice daga dakin. Ita kuma ta raka shi da harara.
Kasa da mintuna shidda ta shirya tsaf cikin kayanta ta ninke mishi kayansa ta aje a gefen gadon, ta sake dauro alwala tayi sallah tana ta istigfari saboda kurewar lokaci.
"Zan tafi gida. Na gode da kulawarka a kaina"
Ta fada muryarta a sanyaye tana tsaye a kansa, shi kuma yana zaune a kan kushin yana daddana wayarsa.
Idanunta sai zagaye suke a lungu da sako na falon, tashi-tashin warin sigari take ji.
Idanunta suka sauka akan ash tray din sai kawai ta girgiza kai.
Ya ta iya da abinda ya gagari wuta?
Dago da kansa yayi ya kalleta, hannunsa daya tallabe da kuncinsa, haka kawai sai yaji babu dad'i, wani sashe na zuciyarsa na raya masa kamar kar ta tafi.
"Haba tun yanzu?"
Yayi maganar kamar yana gaban budurwar da yake neman madafar sace zuciyarta.
Ta juya idanunta dan mamakin maganarsa
"Idan na zauna me zan maka?"
"Ko karyawa ai ya kamata kiyi, barin hado miki tea..."
Ya fada yana k'ok'arin mike wa tsaye zuwa kicin.
"Ni kam Alhamdulillah, Ko ruwa na gidan nan bana fatan in sake sha.
Gida kawai nake so in tafi"
"Ok barinyi sallah in sauke ki"
Zazzaro idanu tayi a tsorace tana kallon bayansa da ya nufi cikin daki, karfe takwas da minti ashirin na safe, a matsayin cikakken musulmi ko sallah baiyi ba?
Tafiyar kurame suke yi a cikin motar tunda suka fara tafiya, idanunta a kasa wasa kawai take yi da yatsun hannunta.
"Duk sana'o'in duniya baka samu wanda yayi maka ba sai safarar miyagun kwayoyi?"
Da mamaki ya juya yana kallonta, me ya dame ta da sana'arsa kuma? Rashin sanin amsar da zai bata yasa yayi shiru hankalinsa na kan tukin da yake yi.
"Safarar miyagun kwayoyi bayan haramcin da take dashi a addinance sana'a ce ta marasa mutuncin mutane wadanda shaidan yayi musu fitsari aka ba na irinka ba. Ina hadaka da girman Allah ka daina, Sam wannan sana'ar bata dace da kai ba"
Nanma dai shiru yayi mata kamar baiji me take cewa ba.
"Barni anan in sauka"
Ta fada ranta a bace.
Gangarawa gefen titi yayi yana taka burkin motar har ya tsaida motar gaba daya.
Bude kofar tayi ta fita, ta sake bude kofar bayan ta zura hannu ta dauko jakarta da wayarta ta koma can gefe ta tsaya tana jiran keke napep, ko kallonshi bata sake yi ba.
"Ke 'Yar jarida?"
Ya lek'a kansa ya kira ta sannan ya yafito ta da hannu.
Kamar bazata je ba sai kuma ta d'an matsa kusa da motar bangaren dire ba, fuskarta a daure.
Sosa kanshi yayi yana kallon fuskarsa, dariya ta bashi ganin yanda take wani ciccin magani tana cijewa, basarwa yayi baiyi dariyar ba.
"Karo na farko a rayuwata da naji na tsargu da laifi.
Kuma lokaci na farko kenan a rayuwa ta da nayi hukunci naji ban kyauta ba abinda nayi. Dan Allah kiyi hakuri da abinda nayi miki jiya"
Ya k'arasa maganar muryarsa kasa-kasa.
"Shikenan?"
Ta tambaye shi tana sakama wani mai napep hannu.
Daga mata kai yayi alamar 'eh'
"Ba komai ya wuce. Fatan alkhairi"
Ta daga mishi yatsu biyu ta shige cikin napep din sukai gaba.
Da kallo ya bisu har suka bacewa ganinsa, sannan yaja motarsa ya koma gida.
****
Watanni biyu bayan nan abubuwan da suka ci gaba da faruwa duk ba masu dad'i bane.
Amma ga Fatima 'Yar gidan Honourable Sumaila abubuwa ne masu matukar dad'i da nishadi.
Ta sake tsunduma cikin kogin kaunar Usher tayi dama-dama, dukda dai ba shine yayi mugun damuwa da ita ba ita ce ta damu dashi, shi dai kadaran kadahan, ya kasa wulakantanta ta ko dan saboda darajar mahaifinta.
Aunty Haleema kuwa ya toshe duk wata hanya da zata sa ya kulla alaka da ita, damar da ya bata tun farko ta bari ya kubuce mata.
Idan zata kwana tana kiransa a waya bazai dauka ba, a karshe ma sai ya jefa ta a *black list*.
Ranarda ta kama Fatima tana waya dashi suna musayar kalaman soyayya a tsakaninsu kuwa tayi kuka har taba uku lada, kuma tayi mata kaca-kaca da cewar ta saurari jakar tsabar da zata kulla mata.
" *Baby Booo* nikam akwai wata magana da nake so in fada maka"
Ta fadi haka muryarta a tausashe tana sake rungume shi a kirjinta.
Dago kanshi yayi ya kalleta cikin kulawa
"Ina jinki, Wace magana kenan?"
Yai mata tambayar yana sake tattaro nutsuwarsa zuwa gare ta.
Hawaye ne ya zubo mata shar tasa hannu tana sharewa wasu sabbin hawayen suna sake gangarowa.
Nan take Honourable ya mike zaune akan gadon, hankalin sa a tashe yake rokon dan Allah ta fad'a mishi damuwarta.
Saida ta gama ja mishi rai, tasa yayi mata alkawarin bazaice a bakinta yaji maganar ba sannan ta fara fad'a masa.
"Kayi hakuri *Baby Booo*, kar kayi tunanin nayi sakaci da amanar 'yarka da ka barmin.
Sau uku ina kama Fatima tana waya da wani yaro Ushere yake ko Usher? Na dai manta sunan shi.
Ni abinda yake bani tsoro ma shine kar yaje ya lalata ta, dan irin kalaman da naji tana fada masa ba na mutunci bane.. rannan fa har ji nayi tana ce masa kirjinta..."
Wani wawan mari da ya kaiwa bakinta tsabar tashin hankali da rudani da yake ciki ba shiri ta dafe bakinta tana hawaye
"Ni kuma miye nawa a ciki?"
Ta tambaye shi tana kuka.
Bai saurare ta ba ya kwashi tulun cikin sa daga shi sai gajeren wando ya nufi dakin Fatima a fusace, yana zuwa falo ya nufi gurin kayan kallo ya kwashi wayoyin caji sannan ya fara dukan kofar dakin yana kiran sunanta a haukace.
A tsorace ta boye wayarta da take chatting a kasan gado ta yayimi hijabi ta sanya ta bude kofar da sauri.
Gabanshi ta zube a kasa idanunta a kasa kirjinta na luguden uku-uku.
"Me yake tsakaninki da Usher? Yanzu ya kira ni a waya yana min magana a kanki"
Murmushi tayi, ta sake sauke kanta kasa cike da kunya, ashe tana da matsayi a zuciyar Usher da har zaiyi ma mahaifinta magana a kanta? Shiyasa zato zunubi ko da ya kasance gaskiya ne, a da tayi tsammanin ita kadai take haukar sonshi, ashe shima ya fad'a cikin soyayyarta.
Tattaro duk wani karfin hali da ya rage mata tayi tace
"Daddy... So na yake yi.. kuma nima ina son shi..."
Saukar duka da taji a jikinta babu zato babu tsammani yasa ta gantsare ta kwala ihu, wayar yaci gaba da zabga mata yana maganganu hankalinsa a matukar tashe, tsanar Usher yake ji har zuciyarsa.
"Ni zaki zubarwa da mutunci? Ki rasa wanda zakiyi soyayya dashi sai d'an iska d'an shaye-shaye? Shege wanda ba'asan uwarshi da ubanshi ba? To gara in kashe ki shima inje in kashe shi in yaso nima a kashe ni da dai ki janyo min abin kunya a cikin zuri'a ta"
Saida yayi mata ligi-Iigi da duka ya farfasa mata jiki sannan ya tsallake ya tafi ya barta kwance a gurin, tun tana ihu har ta daina sai gurmususu take yi kamar mai nakuda, ta daku ba kad'an ba.
Duk wannan dukan baisa taji a ranta zata iya ko da tunanin rabuwa da Usher ba, tana sonshi har yanzu. Sai dai ya kashe ta amma Wallahi bazata rabu dashi ba.
Dakyar taja jiki ta koma cikin daki tana hawaye da cije-cijen baki.
"Allah ya isa"
Ta fada a fili ta sake jan jiki zuwa bayi dan ta gasa jikinta.
Washe gari da safe ya kwace wayarta, ya kira su Nura yayi musu kaca-kaca akan sakaci da aikin da ya saka su na tsaronta, ya jaddada musu muddin ya sake kamasu da kuskure makamancin wannan sai yasa an kulle su an yarda makullin.
*****
A daidai wannan lokacin hankalin hukumar 'yan sanda da hadin gwiwar hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi suka fara komawa kan Usher, wasu makwaftan gidan da yake sauka idan yaje kaduna ne suka kai tsegumin shi gurin 'yan sanda da irin 'yan iskan da yake tarawa idan ya sauka a gidan.
Dan haka ya zama babban abin farauta ga 'yan sanda, sun sha kai mishi hari suna kokarin kamashi yana tsallakewa.
Shi kuwa Killer sai hassada ta fara shigarshi, domin yanzu sam Honorable baida lokacin shi, za6e ya wuce, kuma anci nasara, sam baya kaunar yaga Killer ya kusanto shi, duk harkokinshi da Kamal yake yi, dukda dai ya daina sakar mishi fuska kamar da, amma ya kasa tunkararshi da zancen ya fita a harkar 'yarshi, kwarjini Usher yake mishi ba kadan ba.
Kuma a lokacin harkokinsu ya buda sosai, sun kara yawan odan kayan da suke yi da kashi hamsin akan na da.
Manyan kudade suke samu ba kadan ba.
A karshe Honourable ya fatattaki Killer, yace kar ya sake zuwa gurinshi, matukar ba shine ya neme shi ba.
Hankalinshi a tashe ya kira Usher yana mishi korafin abinda Honourable yayi mishi sai bai nuna nuna wani damuwa akan al'amarin ba, yace zai yima mishi magana amma bai sake ji daga gare shi ba.
Wannan shine dalilin da yasa Killer ya koma harkar shaye-shaye sosai fiye da yanda yake yi a da, ya daina neman Usher da Guru kwata kwata, domin a tunaninshi da saninsu komai ya faru, musamman ma Usher.
Shiyasa yasha alwashin idonshi idon Ushe to tabbas sai ya kashe shi.
Kogon dutse ya samu a daji ya maida gurin kwananshi, sai ya kwana biyar a cikinsa bai fito ba, idan yayi mankas da kayan maye yana dad'ewa bai fito ba, saidai ya kira yaran da suke a karkashin shi su Kawo mishi duk abinda yake bukata.
A cikin wannan halin ne Honorable ya nemeshi da cewar yaje ya kashe 'Usher' bayan ya samu labarin nasarar da 'yan sandan jihar kaduna suka samu gurin kama shi.
Yana tsoron azaba tasa Usher ya fadi sunanshi a gurin 'yan sanda, bayan yayi mishi alkawarin zai bashi miliyan goma, sannan kuma zai dora shi a matsayin Usher.
Labarin kama Usher da akayi ya isa kunnen Guru, yana Lagos a lokacin, cikin hanzari ya biyo jirgi ya dira a Kaduna, sannan ya kira yaranshi na Kaduna suka shirya yanda zasu tseratar dashi.
Sun samu nasarar tserewa, amma kuma sai tayar mota tayi musu tsiya, kamar yanda kuka karanta a baya.
*CIGABAN LABARIN*
*BARA A KUFAI!!*
*25)*
Tururuwar motocin 'yan sanda da na 'yan jarida su suka fi yawa a kan titin da abin ya faru.
Tun cikin daren 'yan sanda suke ta safa da marwa a gurin, yanzu kuma da sassafe sun sake ci gaba daga inda suka tsaya a bincikensu.
Daga ko wane bangare sai daukan hotuna suke yi, kama daga kan konanniyar motar, zuwa kan titin da abin ya faru.
Likitoci sun samu nasarar zakulo konanniyar gawar da yake zaune a bangaren direba na motar, ya kone a kusan ko ina na jikinsa, tuni Allah ya d'auki rayuwarsa.
Bayan gawar da motar basu samu komai da zai sake basu hasken inda zasu samu Usher ko gawarsa ba, wannan shi ya tabbatar musu Usher ya tsere, tunda gawa daya ce a cikin konanniyar motar.
Kusan awa biyu 'yan sanda suna abu d'aya, a k'ark'ashin jagorancin mataimakin kwamishinan 'yan sanda Abdul'ahad.
Yana sanye cikin kayan aikinsa na 'yan sanda, wad'anda suka zauna d'af a jikinsa tamkar dan shi aka k'era kayan, ya k'wama wani bak'in gilashi a fuskarsa.
Tun isarsa gurin da sassafe 'yan jarida suke ta binshi ya basu bayani akan abinda ya faru amma sam yak'i basu damar hakan, sai yanzu da ya gama duk binciken da zaiyi ya nemi ganawa dasu.
"Inspector Jocop Markus, abin alfahari ga hukumar mu ta 'yan sanda, saboda gaskiyarsa da jajurcewarsa a gurin aiki, abin baiyi dad'i ba kasancewar ya rasa ransa a gurin fafatawa da tantiran 'yan ta'adda.
A karo na farko da muka samu nasarar kama Usher a hannunmu ya samu nasarar tserewa da taimakon 'yan uwansa tantirai.
Amma da yaddar Allah zamu sake kamo shi, dashi da wadanda suke taimaka masa, da wadanda yake yiwa aiki, da kuma tantiran da suka zo neman Usher dan su kashe shi, duk zamu damka su a hannun kotu ta yanke musu hukuncin da ya dace dasu"
Yana gama fadin haka ya kad'a kai zai shige cikin motarsu wani dan jarida ya jefo mishi zazzafar tambayar da ta saka shi dawowa.
"Yallabai samun nasarar tserewar da Usher yayi sakacin na waye? Na Kwamishina ne ko kuwa na 'yan Sandan da ya zuba suyi gadinsa ne.."
"Sakacin naku ne ku 'yan jarida.
Kasan me yasa na fadi hakan?"
Ya tambaye shi da muryarsa mai cike da kwarjini.
Da sauri Dan Jaridar ya girgiza kai alamar a'a, yana sake gyara rikon camerarsa.
"Babban kuskuren da hukumar 'yan sanda tayi shine da ta kama kasurgumin mai laifi irin wannan ta bari 'yan jarida kuka samu labarin.
Yad'a labarin da kukayi sannan kuka sanar da asibitin da aka kwantar dashi shiyasa abokan harkarsa suka kawo farmaki asibitin bayan sunyiwa Dr. Habeeb barazana da iyalinsa da sukaiwa daurin talala.
Hallau dai yad'a labarin da kukayi shiyasa wad'anda yake wa aiki suka samu labarin kama shi har suka turo a kashe shi dan kada yaji wahala ya tona musu asiri.
Tabbas sunyi kuskure! Domin ni Abdul-ahad nasha alwashin sake kamo Usher nan da kwanaki kadan in Allah ya yarda.
Su kwantar da hankalinsu, ina yi musu kyakkyawar albishir asirin su yana daf da tonuwa a kasar nan"
Yana gama fadin haka ya shige mota direba yaja suka bar gurin, sauran motocinsu suka rufa musu baya.
*****
Sai hada zufa yake yi, daga safiyar da ya samu labarin zuwa yanzu karfe goma ya zaga bayan gida sau takwas.
Ko lokacin da ya samu labarin kama Usher bai shiga cikin tashin hankali kamar yanzu da ya samu labarin tserewar shi ba.
Kai innalillahi... wannan wane irin abu ne? kundin kaddararsa tana ta juyawa a sannu sannu daga mai tsananin kyau da ci gaba zuwa mai tsananin muni da ci baya.
Ya dad'e kwarai rabon da ya shiga tashin hankali makamancin wannan, sai yanzu yake jin wani abu mai kama da danshin dana-sanin taraiyarsa da Usher a zuciyarsa.
Tsinanne Killer duk shi ya jawo kara da kiyashin ya jibga masa, da bai kawo Usher gare shi ba da bai shiga cikin wannan dimuwar ba.
Dan Adam kenan duk ya manta irin lagwadan kudaden da suka samu a dalilin Usher.
Ya zama dole ya ziyarci Malam Gobe zatai kyau, dan gobensa ta dawo da haske da kyalkyalinsa fiye da baya a rayuwarsa.
"Wani irin banzan zance nake gani haka a t.v. Killer? Iskancin me is tsaya yi har Usher ya samu nasarar tserewa daga asibiti.."
"Kayi hakuri.. matsala aka samu Honourable"
Daga can bangaren ya amsa dakyar yana cije baki, dan hannunsa da ya samu nasarar cire harsashin dakyar mugun radadi da zogi yake mishi, dakyar ma ya iya daga wayar cikin karfin hali.
"Matsala? Wace irin matsala?"
"Ko kafin mu isa asibitin an riga an daukeshi, amma nasan ba kowa ne yayi haka ba sai Guru, zan koma kansu daga baya.
Ni yanzu damuwa ta ma harbin da suka min a hannu, kuma an kama wasu daga cikin yaran da naje aikin dasu.
Zan shigo gidanka ka bani na ganin likita sai kuma musan yanda zaka sa a baki a fito da yara na.."
"Amma Kai mahaukaci ne ko Killer? Kana tunanin ni mahaukaci ne kamarka da zan tsoma baki akan a saki yaran da suka je kashe kasurgumin mai laifi irin Usher?
To idan kai kasha kwaya ta fada maka karya ni garau nake, Wallahi muddin ka kuskura kazo gidana sai nasa 'yan sanda Sun kama ka. Ina zaune lafiya bazaka kulla min jakar tsaba ba.
Kai ko a waya karka kuskura ka nemeni matukar ba labarin samun nasarar kashe Usher zaka bani ba."
'Kit ya kashe wayar yana ta zabga masifa kamar zaici babu.
"Wash Allah...."
Ya fadi haka yana dafe cikinsa da hannu biyu dan jin wani mugun murdawa da yai mishi, bakinshi a cakude ya nufi bayi a dudduk'e.
Yana fitowa daga band'aki ya tarar da uwargidansa a hakimce kan daya daga cikin dima-diman kujerun da suka yi wa falon kawanya.
Kamilalliyar mace mai matukar mutunci, wacce a kallo daya za'a hangi nutsuwa da kamalar da yake tattare da ita.
Tana sanye da babban hijabi wanda ya sauka mata har kasa, da casbaha a hannunta tana ja, sai motsa bakinta take yi da alamu istigfari take yi.
Da nutsuwa take kallonshi tun kafin ya karaso kusa da ita, karantar yanayinshi take yi, a labarin zuciyarsa da fuskarsa ta baiyana ta fahimci akwai wani muhimmin abu da yake damunsa.
"Alhaji lafiya kuwa? Me yake damunka haka?"
Ta tambaye shi da nutsuwarta ganin da tayi kamar ma bai lura da ita a cikin falon ba.
"Hajiya..."
Ya fada dakyar sannan ya daddafa ya zauna a kujerar kusa da ita.
"Cikina ya gur6ace Hajiya... na rasa ko me naci ya lalata min cike. Tun safe safa da marwa nake tsakanin falo da bandaki"
"Allah ya sauwake Alhaji, amma ai ba zama ya kamata kayi ba. Ka fito ka karya sai ka kira likita ya duba ka"
"To Hajiya, na gode. Jeki gani nan fitowa"
Ya fada a gundure, so yake ta fita ya samu yai tunanin mafitar da zata fisshesu.
Wayarsa ya janyo ya kira Honourable Tanko daya daga cikin abokan harkallan tasa.
"Tanko wai baka samu labarin abinda yake faruwa bane? Daga kai har Ghali babu wanda ya neme ni dan jin wane hali ake ciki"
Ya fada ransa a bace.
"Kayi hakuri Sumaila, Wallahi nima nan ina wata cakwakiyar ce.
Kasan na shiga takun saka da mai girma gwamna kwanakin baya, to ashe bai hakura ba. Yana kullace dani, jiya na samu labarin yana nema ya kulla min kullalliya a majalisa, shiyasa hankalina in yai dubu ya tashi. Dan bansan me yake shirin kulla min ba.
Dole zan ziyarci Malam ya rufe min bakinsa, dan ban shirya fuskantar matsala a yanzu da nake harin kujerarsa ba"
"Eh to lallai kaima ka shiga matsala, ka shirya yanzu zan fito sai mu hadu mu tafi tare.
Ka kira Malam din ka sanar dashi zuwanmu"
"Sumaila da zafi-zafi akan bugi karfe, ni yanzu ma fa na riga na fito daga gida, ka shirya ganinan tahowa in dauke ka"
Kit ya katse wayar ba tare da ya saurari amsar da zai bashi ba.
*****
Cikin nutsuwa da taka-tsantsan take gudanar da aikinta yanda ya kamata a kanshi, da yake ba wasu ciwuka ne masu yawa a jikinsa ba, kansa ne kawai da alamun buguwa sai kuma dan kukkujewa, tayi mishi duk abinda take ganin ya dace kafin ya farfado, kafarsa da aka harba kuwa daman tuni likitoci sun cire harsashin sunyi dressing gurin, saida ta kwance taga lafiyar gurin ta kara gyarawa ta sake nad'e wa,
Saida ta gama komai ta fara samun nutsuwa a zuciyarta.
Gefen gadon ta zauna tayi tagumi hannu bibiyu tana kallonsa.
Duk abinda ya faru dashi a kwanakin nan ta samu labari ta hanyar jaridu, ga kuma khadeeja da take fada mata duk halin da ake ciki akai-akai.
Ta dade da fidda rai zata sake haduwa da shi a rayuwarta, bata san me yasa ba tun farkon ganin ta da yaron al'amarinshi ya tsaya mata a rai, ta damu dashi ba kadan ba.
Kamar wani dan cikinta haka ta dauke shi, shiyasa bata kyashin yi masa hidima da kwakwalwarta da karfinta da aljihunta.
Allah ne ya kaddara tana da rabon sake taimakawa Kamal din a rayuwarta.
Gidan da su Muver suka jefa Kamal a ciki ba gidan kowa bane saina Mal Ilu mai gadinta.
A wannan daren madakinsa ta kirashi a waya tana kuka ta sanar dashi yaronsu Muktar yana ta suma ga matsanancin zafin zazzabin da yake damunshi.
Shi kuma sai yayi tunanin tunda Dr. Abida mace ce mai matukar tausayi da taimako bari ya sanar da ita halin da yaron yake ciki ko akwai magunguna da zata bashi ya fara ba yaron na taimakon gaggawa kafin da safe a kaishi asibiti.
Ko da taji irin halin da yaron yake ciki motar ta ta dauko tace ya shiga suje gidan nashi taga jikin yaron.
Ko kafin su isa har ya kira mai dakinsa yace ta bude kofar gidan gashi nan zuwa da likita.
*Kunji dalilin da yasa su Muver suka ga kofar gidan a bude*
"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel. Wannan ai Dana ne Kamal wanda ya bata shekarun baya. Malam Ilu ka manta shi ko?"
Ta fada hankalinta a tashe tana sake haske fuskarsa da tocilan hannunta.
Babu abinda ya canja fuskarsa sai haske da alamun hutu da suka baiyana karara a jikinsa.
"Allah mai iko! Kwarai kuwa na tuna lokacin batan nasa Hajiya, ko su waye suka yada shi nan Allahu aa'lam"
Ya fadi hakan yana mamakin girman iko na Ubangiji.
Nan take ya saba shi a kafada yasa shi a kujerun baya na motarta, sannan ya d'auko yaron nashi mara lafiyar ya rungume a kafad'a ya zauna a gaba suka nufi asibitin ta.
Wani tunani da ya ratsa zuciyarta yasa ta sauke Malam Ilu a asibiti ta hada shi da likitan da yake bakin aiki a lokacin, ta bashi umarnin ayi wa yaron duk abinda yake bukata zuwa safe.
Saida ta kwa6i Malam Ilu kan kada ya kuskura ya tattauna maganar tsintar Kamal da tayi a gidanshi da koma waye, sannan ta wuce gidanta da shi, daki na musanman ta ware ta bashi duk taimakon da ya dace shine ta zauna tana tunanin yanda al'amarin ya kasance.
Sallama da shigowar Khadeeja da Amatullahi ne ya sa ta daga kai tana kallon kofar, Khadeeja tana sa6e da d'an jaririn da Amatullahi take goyo mai suna Abdullahi, suna masa inkiya da Khalifa tunda sunan marigayi babansa ne, wanda Allah ya dauki rayuwarsa a sanadin tashin bomb din da akayi a masallacin da yaje sallar juma'a a Gombe, kamar yanda kuka ji a farkon labarin lokacin da Amatullahi ta haihu gurin sabunta katin zabenta.
"Mummy ya jikin nasa?"
Suka hada baki gurin tambayarta duk fuskokinsu da murmushi.
Tun da ta tsinto shi suke cikin walwala da farinciki, kuma sunsha alwashin a wannan karon bara su sake bari ya subuce musu ba.
Musamman saboda irin tuhumar da yake kanshi, da kuma nemanshi da hukuma keyi ruwa a jallo.
Sam basu kyamace shi ba, tunda duk sunsan ba halinsa bane, sana'ar safarar miyagun kwayoyi da yayi wata kaddara ce da Ubangiji yasa dole sai yayi a rayuwarsa, sun daura aniyar maida shi mutumin kwarai kamar yanda yake ada ko da kuwa bai dawo cikin haiyaci da tunaninsa da ya rasa a baya ba. Suna addu'ar Allah ya dafa musu akan kyakkyawan kudurin da suke dashi a kanshi.
****
Wani dogon carbi mai guda dubu ya mika wa Honourable Sumaila ya umarceshi ya za6i daya a ciki.
Zazzaro idanu yayi lokacin da ya kar6a ya ga wanda ya za6a.
"Sumaila ka rufe idanunka, ka tsaida tunani da zuciyarka guri daya ka dauki carbin nan ka sake za6ar guda daya"
Malam Gobe zatai kyau ya bashi umarnin haka fuskarsa turbune da damuwa.
Ko da yayi kamar yanda ya umarceshi sai yaga wancan dai da ya za6a da farko shi ya sake za6a a yanzu.
Girgiza kai yayi alamar akwai gaggarumar matsala, ya umarceshi ya bude idanunsa.
"Sumaila akwai gaggarumar matsala a goben ka, babu haske ko kadan, nan da lokaci kankani zaka fara girbe munanan aiyukan da ka shuka da hannunka"
Mai Gobe zatai kyau ya fada babu alamar wasa ko kadan a tattare da shi.
Tashin hankalin sa ne ya kara ninkuwa fiye da da, ga zafin d'an tsukukin d'akin ga zafin damuwar da yake ciki, haka suka taru suka jika shi sharkaf da gumi.
"Malam a taimaka min, ban dogara da kowa ba sai kai.
*(Wa'iyazubillahi)*
Ka fada min ko menene zanyi dan gobe na ta dawo da haskenta, ka taimaka min Malam"
Ya gurfana a gaban yamusasshen tsohon gwiwa bibiyu yana rokonsa kamar zaiyi masa sujada.
Shiru yayi mishi ya ci gaba da zane a kasa yana share wa, tsawon mintuna biyar kafin ya dago da kanshi shima ya jike sharkaf da gumi.
"Akwai mafita d'aya a gare ka Sumaila, amma fa matukar ka kuskure aka samu matsala saidai kaje gurin wani malamin ba ni ba, kuma ina tabbatar maka idan zaka zaga gurin malaman duniya babu wanda ya isa ya baka mafita bayan wacce na baka, idan ka kuskure ko sau daya to tabbas ka rungume rushewarka a ko wane fanni na ci gaban ka.
Mafitar mai sauki ce, ka samu mace mahaukaciya wacce aka tabbatar ta shekara biyu cur tana hauka, ka maida ta gidanka da zama ka ringa saduwa da ita har tsawon wata biyu.
Kullum kwana ta duniya ka tabbatar ka sadu da ita ko da tana jinin haila ne, kuma karka kuskura ka mata wanka, ka barta da kazantarta ka ringa amfani da ita a haka har tsawon wata biyu.
Wannan maganin kuma"
Ya dauko wani kullin magani dan kadan ya mika mishi.
"Ka ringa shafawa a gaban ka kafin ka sadu da ita.
Idan kayi haka tabbas gobenka zata yi kyau matuka, a bayan kujerar sanata har a kujerar shugabancin kasar nan zaka zauna"
Nan take fuskar Honourable Sumaila ta washe da fara'a, shi Sumaila a kujeran Shugaban kasa? Lallai zai tsula tsiya son ransa, Allah yakai damo ga harawa...🤣🤪
Kyakkyawan sallama yayi ma Malam sannan ya fita waje dan ba Tanko damar shiga ya gana da Malam.
"Ka shiga makabarta da kanka ka samo min harshe da idanun gawar da bata yi sati daya a kasa ba daga yau zuwa jibi, zan hada maka kwallin da zaka sa a idanunka ka fuskanci Gwamna kuyi ido da ido, shi kuma harshen zan hada abinda zaka tauna a daf da lokacin da zaka fara magana da shi.
Idan kayi haka tabbas da kansa zai daga hannunka a matsayin wanda zai gaji kujerarsa"
Malam Gobe zatai kyau ya fada masa haka bayan ya bashi carbi ya za6a kamar yanda yayi ma Honourable Sumaila.
Shima fuskarsa yalwace da fara'a yake ta zabga godiya kamar ya mishi albishir da aljannah, kyakkyawar sallama yayi mishi sannan ya nufi hanyar fita daga cikin tsukukin dakin.
"Ka fad'awa Ghali aikinsa ya fara sanyi, Gobensa tana daf da fara munana, ya nemi jinin jariri sabon haihuwa yayi wanka dashi a tsakiyar hanya cikin tsakiyar dare, kada yayi sallar asubah da isha'i har na kwana uku a rana ta hudu ya tabbatar ya taho guri na kafin ketowar alfijir"
Yana gama fadin haka ya dukar da kanshi a kasa yana wasu sambatu da ba'a gane me yake cewa.
*BARA A KUFAI!!*
*26)*
Tsawon mintuna talatin suna tsaye a harabar gidan suna jiran fitowar Honourable Ghali, dan takaran Gwamnan jihar kaduna a jam'iyyar adawa.
A hannun ko wannensu makami ne rike kaloli daban daban, kama daga kan Barandami, gariyo, adda, wata sharbebiyar wuka gayawa jini na wuce da take rike a hannun Figo babu abinda take yi sai d'aukar ido saboda tsabar washin da ya wuni yana mata jiya.
Kallon wukar a karon farko tsirararta ya isa tsorata mace mai karamin ciki ta samu 6ari.
Duk su goma sha biyun babu wanda hannunshi babu makami mai saurin cutar da rayuwar bil'adama.
Tsawon yinin jiya sun bata shi ne gurin wasa takubbansu saboda yau akwai zazzafar fita da zasu fara da Honourable.
Yau ne zasu fara fita kamfen, kuma zasu fara da guri ne da yake tattare da cincirindon matasa a kaduna.
Hayin rigasa zasu fara zuwa, a fili yake mafiyawa daga cikin mutanen hayin rigasa suna kaunar Gwamnan da yake kan kujerar mulki a wannan lokacin.
Saboda hasashen al'Umma zasu iya kawo mishi tarnaki a cikin rigasar, wata kila ma su raka shi da jifa shiyasa ya umarci su Figo suyi gaggarumin shiri, duk wanda ya nemi kawo wargi ko wani tarnaki a gurin su kaddamar masa a nan take ba tare da wani 6ata lokaci ba.
Fitowar Honourable Ghali daga cikin gidan yayi shigar manyan kaya yasa gaba daya suka kaure da ihun
"Allah ya taya ma.. sai kayi Honourable ko garin kaduna ba kowa.."
Hannu ya daga ya dakatar dasu bayan ya isa gabansu, da muryarsa a nutse ya fara kora musu bayanin duk abinda yake so suyi
"Figo ina so ka raba tawagar nan taka gida uku, kashi biyu zasu bi motoci daban su isa gurin taron su saje a cikin talakawa, kashi daya kuma zasu kasance daga gaba gaba suna lura da duk abinda yake faruwa.
Ina so ku nutsu sosai, kowa ya 6oye makaminsa, karku ta6a nuna tare da mu kuke tafiya, a cikin tawagar dai ku ringa ihu kuna tafi aduk maganar da nayi, ku nuna lallai kuna tare damu a matsayin Gwamnan jihar kaduna na gobe"
Suka sake fashewa da ihu suna masa kirarin sai yayi.
Saida ya jira suka karaci iface-ifacen su sannan ya ci gaba da bayani.
"Matasan hayin rigasa akwai 'yan iska masu shegen zafin kan tsiya, ina so ku sa idanu ku lura da kyau, duk wanda ya nemi kawo wargi ku kaddamar masa.
Bana so ku ragawa kowa, duk tsufan mutum, duk yarintarsa, ba sani ba sabo. Duk wanda yayi mana ko da mummunar kallon da baku yarda dashi ba ku kawar dashi.
Idan kunga abun zai rincabe sosai to kubi rubibi ku 6ace a cikin jama'a. Kar wanda ya kuskura aka kamashi.
Ina fatan kun gane??"
"Mun fahimta Honourable"
Suka amsa a tare suna ci gaba da jinjina makaman hannunsu a sararin samaniya.
"Akwai wasu 'yan daban da aka yo min hayarsu a zaria, alamar da zaku gane mutum tare damu yake zaku gansu sun daura jan kyalle a saman kansu.
So nake kuyi kamar mota uku haka, ta yanda babu wani mai iya kawo mana wargi ko maganar banza"
Dubu goma ya kirga ya basu su dauki shatar mota bus, da cewar idan an dawo zai sallame su.
*****
Tana zaune akan kujerar da yake ajiye a gefen gadon, waya ce a hannunta take daddanawa, lokaci zuwa lokaci kuma tana daga kai ta kalleshi, sai kuma ta saki murmushi ta girgiza kai.
Babu abinda take tunani sai kwanan da tayi a gidanshi da kuma irin dramar da suka yi tsakaninsu.
Dukda dai wasu abubuwan ba masu dadin tunawa bane haka nan take jin al'amarin yana bata dariya da nishadi.
Ko mahaifiyarta ta kasa fada mata gaskiyar abinda ya faru, inda Allah ya taimake ta ranar da abin ya faru Mummy a asibiti ta kwana, tana niyyar dawowa gida da sassafe kamar yanda ta saba sai kuma aka kawo mace mai haihuwa, ko da ta duba level din da take daf take da haihuwa, shiyasa ta tsaya ta karbi haihuwar sannan ta koma gida, a lokacin kuma ita ta koma gida har tayi wanka tayi shirin fita gurin aiki.
Yanzu tsawon wata biyu kenan da faruwar abin.
Daga kai tayi ta sake kallonshi sai taga idanunshi a bude.
Gaba daya idanunshi suna zube a kanta, tana kallonshi ya daga hannunshi dakyar ya mutsutstsuka idanunshi dan tabbatar da ba mafarki yake yi ba.
Ko da ya muttsuka ya bude yaga dai tana nan bata 6ace ba sai ya ci gaba da mamakin ganin ta, yana ci gaba da kure ta da kallo.
"Ko in mare ka ne dan ka tabbatar ba mafarki kake yi ba?"
Ta fada tana juya idanunta sannan ta murguda masa baki dama da hagu.
*"Derling Girl*"
Ya furta a hankali ciki-ciki, da murmushi a fuskarsa, ya dafe kansa da yake mishi masifar ciwo kamar zai tsage.
"Kin isa ma ki Mari yaro na ban rama mishi ba?"
Mummy ta fada da murmushi a fuskarta a daidai lokacin da ta shiga cikin dakin.
Kai tsaye gurinshi ta nufa tana dariyar jin dadin ganin ya farka a daidai lokacin da bata zata ba.
"Ya kake jin jikin naka?"
Ta tambaye shi da kulawa.
Yamutsa fuska yayi kamar zai fasa kuka
"Na dan ji sauki.."
Dariya ya basu har saida Mummy tayi murmushi, ita kuwa Khadeeja dariyar tayi tana kallon yanda yake yamutsa baki.
"Au saukin ma d'a ne? Yanzu me yake maka ciwo?"
"Kaina.. kaina ne yake min ciwo kamar zai tsage"
Ya amsa yana runtse idanu dakyar, da gaske fa kan yake mishi ciwo su Sun dauka wasa yake yi.
"Sorry my boy, daman dole zaka ringa fama da ciwon kan lokaci zuwa lokaci, amma da Sannu zai daina ka ji ko?"
Daga kai yayi alamun ya ji.
Ruwan swan ta tsiyaya a kofi tayi wasu addu'o'i ta tofa a ciki, ta 6allo wasu magunguna ta mika mishi da ruwan
"Ungo, karbi ka shanye maganin da ruwan gaba daya"
Kamar bazai kar6a ba amma dan yana ganin yanda ta gama tofe ruwan da miyan bakinta.
Kallon fuskarta yayi yaga tayi masa mugun kwarjini, Sam bazai iya ce mata bazai karba ba, kawai sai ya mika hannu ya karba, zuciyarsa cike da kyankyani ya shanye maganin da ruwan kamar yanda ta umarceshi.
"Good boy. Ka kwanta ka huta, nan da awa biyu kan zaiyi sauki in Allah ya yarda"
Tasa Khadeeja a gaba tayi suka fice daga dakin dan ya samu hutu.
Runtse idanunsa yayi kamar mai barci yana tunanin wai ta ya ma akayi yazo nan?
Matashiyar 'Yar Jaridar ta tsaya mishi a zuciya tai kane-Kane tun bayan rabuwarsa da ita.
Haka maganganun da tayi mishi akan irin sana'arshi sun tsaya mishi a rai, a cikin kwanakin da suka biyo baya Sam baya jin dadin harkokinsa, kamar wani Mara lafiya haka ya koma, karfin hali kawai yake yi yana yake a cikin abokan harkarsa.
Duk yanda yaso ya sake ganin ta ko da tsiwarta ne tayi masa ya kasa ganin ta, kuma yana tsoron zuwa gurin aikinta kar suyi mishi cunen 'yan sanda.
Kamar wanda aka yi wa wankin kwakwalwa yaji ya kamata ya mika kanshi ga hukuma, gaba daya sana'ar ta ishe shi, gara ya tonawa su Honourable asiri duk a kama su in yaso shi a sallame shi ya ci gaba da rayuwa mai 'yanci da walwala kamar sauran mutane.
Wani layin wayarsa da ba kowa ne ya sanshi da layin ba ya turawa 'yan sanda sakon inda zasu samu Usher dilan miyagun kwayoyi.
Wani tunani da yayi ne yasa ya fara tunanin gara fa ya gudu kafin 'yan sanda su zo kamashi, idan ya bari aka kama shi su waye masu tsaya mishi balle har a daukar masa lauyan da zai jajurce gurin wanke shi a kotu? Kuma ma ai ya kamata yaga 'Yar jaridar nan ya fada mata yaji nasihar ta, saboda ita ma har zai mika kansa ga hukuma... da sauran tunanikan da no kusa baiyi su ba kafin ya sanar da 'yan sanda inda ya kamata su same shi.
Wadannan dalilan da ma wasu suka sa yayi yunkurin guduwa a lokacin kuma 'yan sanda sun riga sun zagaye gidan da yake ciki karkashin jagorancin Kwamishinan 'yan sanda.
A yunkurinsa na guduwa ne suka harbeshi a kafa, sannan suka saka mishi ankwa suka wuce dashi...
Yana wadannan tunane-tunanen har barci ya kwashe shi bai sani ba.
******
Suna tsaye cirko-cirko a tsakar gidan suna jiran fitowar sa, tun misalin karfe takwas da minti ashirin suke tsaye har takwas da minti hamsin tayi.
Tun aikawar farko aka sanar dasu yana cin abinci har yanzu bai sami sararin fitowa ba.
Inna Tala har ta gaji da tsayuwa ta durkusa kasa, lokaci bayan lokaci tana sa hannu ta share kwallar fuskarta.
Gwaggo Amina ita ma tana jingine da bango fuskarta babu walwala, a kallon farko za'a gane tsananin damuwar da take ciki.
Figo ne ya fara fusata dan haka ya karasa cikin gidan da nufin ya sake aikawa a kirashi, tunda ya kira wayarsa fiye da sau goma bai daga ba, a karshe ma ko ya kira bata shiga.
Fitowar Honourable Ghali yasa Figo dakatawa a inda yake, sai kuma ya fara k'ok'arin yalwata fuskarsa da murmushi.
Da hannu ya ya fito sauran abokan tafiyarsa su Tsula, su kuma suka kira Inna Tala da Gwaggo Amina suka karasa gare shi kamar almajirai.
K'ok'arin zube wa kasa su gaishe shi suke yi ya dakatar dasu ta hanyar daga musu hannu, ya kallesu daya bayan daya a wulakance, fuskarsa babu walwala ko kadan ya tsaida idanunsa akan Figo.
"Lafiya tun dazu kuke min aike kamar masu bina bashi? Ko menene ma ai saiku bari sai Allah ya kaimu gobe in neme ku da kaina ba wai ku ringa damuna ba"
Baki bude Figo yake binshi da kallo, k'ok'arin danne 6acin ransa yayi da ya tuna su Inna Tala da suke tsaye a gurin da kuma halin da su KB suke ciki.
"Honourable kayi hakuri, ba ma batun sallamar mu bane.
A gurin kamfen dinnan kusan duk kanmu babu wanda ba'a jiwa ciwo ba, amma muma munyi musu barna fiye da yanda ka umarcemu.
To a cikinmu da Kb da Roja an sassare su sosai, dan Kb ma baisan inda kanshi yake ba har yanzu, dakyar Muver ya samu nasarar fitar dashi daga gurin da tuni sun kashe shi.
A yanzu dai duk su biyun suna gida a cikin mawuyacin hali, babu kudin da za'a kaisu asibiti.
Wancan (Ya nuna Inna Tala) ita ce Mahaifiyar Kb.
Wancan kuma Gwaggwo Amina Mahaifiyar Roja ce.
Sunzo ka taimaka da abinda zasu kaisu asibiti"
Kara had'e girar sama da kasa yayi yai murtuk! Da ya sake kallonsu sai a lokacin ya kula da d'aid'aikun ciwukan da yake jikinsu da taimakon hasken kwayayen lantarkin da suka haske gidan tar kamar rana.
"Amma Figo tun kafin mu fita naja kunnenku akan da kunga gurin na neman ca6ewa ku sa6e.
Dan haka ni yanzu bani da abinda zan iya musu, kunsan babu kudi a kasa, gaba daya kudaden da suke kasa na kamfen ne.
Dan haka Allah ya basu lafiya..."
Kafin ya gama rufe baki Inna Tala ta zube a gabanshi tana kuka tana rokon ya taimake ta kamar yanda Allah ya taimake shi.
"Kabiru shine kadai yaro na da ya rage min a duniya, sauran 'yan uwansa duk Sun rasu tun suna kanana, ka taimakeni kar in rasa shi kamar yanda na rasa sauran 'yan uwansa"
Kuka take bil'Hakki, kamar ma bata san me take cewa ba, babu abinda take tunani sai kafar Kb guda daya da aka sare shi sosai kamar ma ya kusa guntulewa, bata aje ba bata ba wani ajiya ba.
Koko da kosai take yi da safe na sayarwa dan ta rufa musu asiri kar suje maula, idan ya barta dashi a haka ya zata yi?
"Shikenan! Za'asan yadda za'ayi. Ina zuwa"
Ya fada ransa a kuntace sannan ya koma cikin gidan.
Mintuna uku tsakani sai gashi ya fito dansa Yusuf na biye dashi zugwi-zugwi a baya.
Dubu biyar ya kirga ya sake kirgawa dan kar wata dubun ta makale a jikin wata, mikawa Inna Tala yayi hannunta na rawa ta miko hannu zata kar6a.
"Yusufa dauke mu hoto, yanzun nan ka dora a Facebook ka rubuta title dinnan da manyan baki.
*Allah Ya taimaki mai taimako, wasu daga cikin iyayen yaran da hatsarin mota ya rutsa dasu a hanyar dawowa daga gurin sana'arsu kenan Honourable Ghali ya kira su ya basu tallafi. Allah ya baka Gwamnan jihar kaduna mu huta da rayuwar kunci*"
Yana gama fadi yayi Dan murmushi ya gyara zaman hular kansa ya mika mata kudin, ita kuma ta miko hannu zata kar6a aka dauki hoton.
Ita ma Gwaggwo Amina kin bata yayi saida aka dauke su hoton ya sakar mata kudin.
Takaici da bakin cikin duniya ya gama k'ume Figo, bai ta6a jin dana-sanin kasancewa a karkashin Honourable din ba sai yanzu, ransa a bace ya kalleshi yace
"Dubu biyar ne fa ka basu ba dubu dari biyar ba? Wallahi muddin ka dora hotunan nan a Facebook ina tabbatar maka bakin jini da zagi zaka kara ja wa kanka"
Wasu zafafan hawaye ne suka taho masa da sauri yasa hannu ya dauke su, juyawa kawai yayi ya fice daga gidan sauran suka rufa masa baya.
"Amma Dad baka ganin Gaskiya ya fad'a? Ka girmi ajin taimakon dubu biyar har aje ana tallata wa a media.
Takaran gwamna fa kake yi ba takarar kansila ba"
Yusuf ya fadi haka da muryarsa mai kama da ta 'yan daudu.
"Nima nayi tunanin haka Yusufa, goge hotunan kawai karka tura. Balle har 'yan adawa su samu abin yada magana da yarfe a gare mu"
Cikin gidan suka koma gaba daya bayan yaba mai gadi umarnin duk wanda yazo nemanshi kar a bar kowa ya shiga, ace baya nan.
******
Yanda yake ta kallon hotunan kamar wanda ya warke makanta shine abinda yasa dukansu dariya.
Ya dago a hankali yana kallonsu, sauke idanunshi yayi akan Khadeeja.
"Ashe da gaske ne maganar da kika fada min kwanakin baya cewar ni Yayanki ne?"
Saida ta kad'a idanu ta murguda masa baki wanda ya lura hakan ya zama mata dabi'a. Musanman idan zata yi magana dashi ne
"Eh mana, ba na fada maka ka karyata ni ba? Yanzu da kaji daga bakin wacce bazata maka karya ba ai saika yarda, ga kuma kwararan shaidu nan a hannunka"
Ya sake dawo da hotunan cikin wayar daya bayan daya yana ta mamaki a zuciyarsa.
"Ashe yana da iyaye da kannai kamar wadannan yaje yana ta gararanba a tsakanin gurbatattun mutane yana gudanar da gurbatacciyar rayuwa?"
"Wannan kuma mummunar kaddara ce da Allah yasa dole saika rungumeta a rayuwarka Kamaluddeen.
Dan haka yanzu godiya ga Allah ya kamata muyi, da yasa kana da rabon sake shiryuwa tun lokaci bai kure maka ba.
Shi daman babbar illar sa6o ka mutu kana aikatawa baka tuba ba, amma idan kayi tuba na tsakani da Allah kuma lokacin bai kure maka ba tabbas Allah mai kar6ar tuban bayinsa ne ako wane lokaci.
Allah baya hisabi da aikin da mutum ya fara a rayuwarsa, yana hisabi da abinda mutum ya dauwama yana aikatawa har karshen rayuwarsa ne.
Shiyasa ako wane lokaci mu kasance masu yawaita addu'ar Allah ya dauwamar damu akan hanya madaidaiciya da aikata ayyukan alkhairi har zuwa karshen rayuwarmu"
"Ameen ya Allah"
Suka amsa gaba daya harda Kamal.
Mummy ta sake gyara zamanta a kusa dashi, ta ci gaba da magana a tausashe.
"Kamal ina fatan dai a shirye kake ka tuba kabar aikata duk wasu munanan aiyuka da kake aikatawa?"
"In Allah ya yarda Mummy, kuma ni daman tun ma kafin ku same ni nayi niyyar daina mummunar sana'ar da nake yi"
Ya fada kanshi a kasa, da muryarsa sanyi sanyi.
"To masha Allah, naji dadin jin hakan daga bakinka.
Allah ya kara shiryar damu gaba daya"
"Ameen"
"Yayanmu wai dan Allah su waye kake yiwa aikin nan ne? Naji a hirar da akayi da mataimakin Kwamishina yace akwai manyan da kake musu aiki.
Da gaske ne hakan?"
Khadeeja ta tambayeshi da murmushi a fuskarta.
"Kwarai kuwa!"
Ya amsa mata kai tsaye.
"Kina mamaki ne?"
Ta daga kai alamar 'eh'.
"Ai kuwa ki daina mamaki, domin ina tabbatar miki d'aid'ai ne masifun da suka addabemu a kasar nan da ba k'irk'irarsu aka yi ba.
Akwai kuma masifun da hannayenmu da aiyukanmu ne suka janyo mana sai Allah ya jarrabe mu da su.
Kinga a kasar nan nasan mai arzikin da ya Tara matasa da yawa suna mishi garkuwa da mutane, shi yake basu sunan wanda yake so su sato a biya mak'udan kudade ya sallami yaran nasa, kuma da zan fada miki sunan mutumin zaki sha mamaki, domin fitacce ne a gurin taimakawa harkokin addini.
Ko ni kinsan su waye nake yiwa aiki?"
Girgiza kai sukai duk su ukun, jikinsu yayi matukar sanyi.
Lokacin da ya furta sunayen wadanda yake wa aiki kuwa kusan suman zaune suka yi, musanman Khadeeja da take aiki da jarida tasan irin kyawawan labaran da ake bugawa da yad'awa kusan ko wane lokaci akan wadannan miyagun mutane masu fuska biyu, kuma shugabanni a cikin al'umma.
Kiran da ya shigo cikin wayar Dr. Abida shiya katse musu tunanin da suke yi, a sanyaye ta dauki wayar.
"Dr. Pls kiyi sauri kizo, wannan mai haihuwar da aka yi wa tiyata ta fara jijjiga..."
"Subhanallahi.. ba akwai Dr. Muktar a bakin aiki ba?"
"An kira shi a waya mahaifiyarshi ba lafiya..."
"Ok! Ok gani nan zuwa, ku fara bata taimakon da ya dace kafin in karaso"
Gudu-gudu tayi musu sallama ta dauki motarta a dari ta fice daga gidan.
Tana tsakiyar titi traffic light ya tsaida ita, sai duba agogon hannunta take yi kamar ta rufe idanu ta bude ta ganta a asibitin take ji.
A daidai wannan lokacin ne kuma idanunsa suka sauka a kanta, tsawon mintuna yana kallonta dan ya tabbatar ita ce, lokacin da ya tabbatar ita din ce d sauri ya daga wayarsa ya daddanna wasu lambobi.
Ko da aka dauka daga can 6angaren muryarsa sauri sauri yace.
"P. A dan Allah ka fadawa maigida yanzu-yanzun nan! Abida tana raye.."
"Wannan wani irin zancen banza ne? Ta ya ya? Tana ina? A ina take?"
Ya tambaya a rude bakinsa yana ta kyarma saboda tsananin rud'ewa da tashin hankali.
"Tana Kaduna"
*BARA A KUFAI!*
*27)*
A cikin kwanakin da suka biyo baya wata zazzafar shakuwa, kulawa, tausayi, da gwada soyayya irinta jini d'aya ne yake ta gudana a tsakanin Dr. Da yaranta guda uku.
Kamaluddeen, Amatullahi da Khadeeja.
Duk yanda suke tsammanin zasu samu Kamal ya wuce nan.
Mutum ne mai mugun saukin mu'amala da dad'in zama, kuma ko kadan baya jin kunyar ya kwa6o shirme ayi mishi gyara, gyara ko daga gurin Khadeeja ne saurin kar6ar ta yake yi da hannu bibiyu.
Kafarsa kuwa tayi sauki sosai sai dan abinda baza'a rasa ba, har yana dan yawonshi a tsakar gidan, amma yana dingishi kadan-kadan.
Fita ne dai ko kofar gida Mummy ta hana shi, kuma tace duk ranarda ya fita zai gamu da mugun 6arin ranta.
To shima dai da yake fitar bata a kansa ko da wasa bai ta6a gwada leka ko da waje ba.
Sai jikinsa ya kara kyau sosai, alamun hutu suka k'ara zama mishi, yai wani irin kyau luf-luf😉
Dan sai abinda yake so ake dafa mishi, yaci mai kyau yasha mai kyau.
Ko sallah a gida yake yi.
Babban matsalar da suka fara ankarar dashi akai shine yin sallah akan lokacinta.
Wani lokacin har sai Mummy tayi magana zaiyi, amma idan Khadeeja ko Ama ce amsarsa kenan.
"Zanyi anjima"
Ko kuma ya narke fuska yace barci yake ji idan ya tashi zaiyi, da sunce zasu fad'awa Mummy zai tashi da sauri.
Kamar dai yau da yake alwala a tsakar gidan Khadeeja tana tsaye a bakin get tana kallonshi.
Kokarin fita zuwa makwafta take yi, amma ganin yanda yake alwalar yasa ta tsaya tana kallonshi har ya gama, wato dan a bayin cikin dakinsa yake alwalar shiyasa basu ta6a ganin irin kura-kuran da yake tafkawa ba, zuciyarta cike da tausayinsa.
Tana ganin ya mik'e da nufin shiga ciki da sauri ta karasa gurinshi da murmushi a fuskarta.
"Hey 'Yar jarida, baki tafi ba? Ko kina so in raka ki ne?"
Ya fada muryarsa kasa-kasa yana kashe mata ido daya😉.
Kallonshi tayi da mamaki
"Yanzu kai idan nace ka raka ni sai ka biyo ni?"
"Why not? Me a ciki dan Yaya ya raka kanwarsa da yake ji da ita unguwa?"
"Gidan Matan aure ne fa Yayanmu?"
"To nima ai mijin aure ne"
Ya amsa da zallar gaskiyarsa ba tare da kwana-kwana ba.
Dafe kanta tayi da hannun dama zuciyarta cike da takaicin kwa6a irin tasa.
Kusa da ita ya matsa sosai har suna iya jin bugun numfashin juna.
"Ya dai Babe? Na kwafsa koh?"
Ya zazzare ido yana kallonta, sannan ya mika hannu da nufin sauke hannunta da ta dafe kanta.
Lura da abinda yake shirin yi yasa ta kauce da mugun sauri, ta gallah masa harara, ta murguda mishi baki😏.
"Sau nawa na miki kashaidin juya bakin nan?"
Ya tambaye ta yana wani fuskewa a dole shi babba ne.
Dariya ya bata sosai ta dafe bakinta tana dariyar kasa-kasa.
Ko da ta tuna abinda ya kawo ta gare shi sai ta hadiye dariyar, ta matsa kusa dashi kad'an.
"Ya Kamal!"
Ta kira shi da wata tattausar murya da saida tsigar jikinsa ta tashi.
Runtse idanu yayi a hankali yake jin wani abu yana sauka yam-yam a jikinsa.
"Na'am *Darling Girl*"
Ya amsa da kwatankwacin muryar da ta kira shi.
"In baka wani labari?"
Ta tambaye shi tana sake kasa da muryarta.
"Uhmmm"
Ya amsa a sanyaye dan ya fara rasa ta cewa.
"Ka ga fa da nima irin wannan alwalar taka nake yi idan zanyi sallah, amma wata rana da nayi irinta a gaban malaminmu na islamiya saida yayi min magana.
Kasan me yace min?"
Ta tambaye shi bayan ta sake shigar da muryarta can ciki.
"A'a"
Ya amsa da kyar, dan yanda yake ji a jikinsa kamar ya janyota ya rungume ta ko zaiji sauki saukin irin feelings din da take saukar mishi a jikinsa.
Baisan me yasa ba idan yana magana da ita ne kawai yake tsintar kansa a wannan halin, yayi mu'amala da mata da yawa kuma yasha runguma da sumbatarsu bai ta6a jin irin abinda yake ji a kanta ba.
"Ce min yayi fa wai irin wannan alwalar tawa ba daidai bane, kuma wai sai mutum yayi tsarki da alwala masu kyau sannan sallarsa zata kar6u.
Wai idan sallar mutum bata kar6uwa kuma banbancinshi da kafuri kadan ne, har ma fa ya fada min banbancin musulmi da wanda ba musulmi ba sallah ce"
Watsar da duk wani tunani da yake ransa yayi yaci gaba da sauraran bayananta masu cike da nutsuwa da hikima.
"To yanzu ya zan ringa yin alwalar kenan?"
Ya tambaye ta ba tare da girman kai ko jin kunya ba.
Fitar da bata yi ba kenan a wannan lokacin, dan gurin famfon tsakar gidan suka nufa ta nade hannun rigarta ta fara gwada masa yanda ake alwala kamar yanda fiyayyen halitta SAW ya koyar damu.
Sau uku ta maimaita masa ya haddace tsap, yayi kamar yanda tayi babu ko kuskure, har addu'ar da ake yi bayan kammala alwala duk ya haddace.
Tsabar murna yasa ta hada yatsunta tayi masa👌🏻👌🏻👌🏻😍😍 alamun ya burge ta ba kadan ba. Saurin d'auka da haddace abu da kwakwalwarsa take yi yana tsananin bata mamaki. Lallai ya cika dan baiwa.👍🏻👍🏻
Shima sai jin dadi yake yi da yayi abin da ya burgeta, haka kawai yake ta murmushi shi kadai, alamun yana cikin nishadi.
*****
Idanunshi jajur ba kyan gani ko kadan, Tsabar damuwa bakinshi har tururin hayaki yake fitarwa.
Hotunan yake ci gaba da kallo daya-daya yana sake nazartarsu, tabbas sune.
Ina suka shiga duk tsawon lokacin nan suka 6ace a cikin duniyarsa? Shi gaba daya ma ya gama tsammanin sun mutu, kamar yanda yaga konanniyar motar da suke ciki.
Sai girgiza kafa yake yi alamun a cike yake, gaf yake da fashewa.
Ya daga jajayen idanun ya sauke su a kan P.A, ai da sauri ya sunkuyar da kansa kasa kamar tsohon munafuki.
Ya juya da kallonsa ka Pele, Shima sauke kansa yayi jikinsa yana tsuma, yasan fushin mai gida baida kyau ko kad'an, yanzu sai ya huce akan wanda baiji ba bai gani ba.
Kadan ne daga aikinsa yayiwa mutum wata muguwar shakar da zaisa mutum ya fara jiyo kamshin barzahu.
Fitsari ne ya nemi ku6uce masa lokacin da yaga Maigida ya tashi ya nufo su a fusace.
"Ya aka yi har yau suke raye?"
Ya tambayi P.A bayan ya zabga masa wani wawan Marin da saida yaga wucewar wasu taurari masu tsananin haske.
"Waallahi nima bani da labarin suna raye Maigida"
"Kau"
Ya dauke Pele da wani kyakkyawan Mari a karo na biyu.
"Ya aka yi suke raye tsawon wadannan shekarun bani da labari?"
"Kayi hakuri Mai gida..."
Wani wawan mari ya sake dauke shi dashi, dan ya tsani yana tuhumarka da laifi ka bashi hakuri.
Daya daga cikin hotunan ya daga ya nuna saitin fuskar Pele, tana tsakiyarsu Amatullahi da Khadeeja aka dauki hoton, duk dariya suke yi, fuskarsu na baiyana tsananin farin cikin da zuciyarsu take ciki.
"Ina fatan ka samu labarin komai a kansu?"
Ya tambaye shi da murya mai cike da hargagi.
"Eh.. eh... inda suke aiki, gidan da suke zaune, lokacin da suke shiga da fita duk na sani, hatta shagon da suke siyayya duk na bincika"
Ya amsa yana kyarma, sai runtse ido yake yi saboda tsananin zafin marin da ya amsa da hannun Maigidan mai kama da kututturen itace.
"Ka tabbatar ka kawo min kawunansu duk su ukun, ina so kayi musu kisa mafi muni na wulakanci, nasan *Tsumburbura* zata yi murna idan tasha jini a kokon kawunansu.
P.A a tabbatar an bashi isassun kudi da kayan aikin da zasu wadace shi gurin yin aikin"
Yana gama fad'in haka ya watsa mishi hotunan a fuskarsa ya shige ciki, saboda sauri har yana had'awa da gudu-gudu.
****
Tun saukarta a gidan ta fara karantar irin zamantakewarsu ta tabbatar akwai abinda yake tafiya ba daidai ba a tsakaninsu.
Tunda Honourable ya auro Haleema bata ta6a zama na cikakken satibiyu tare da ita ba sai wannan lokacin.
Zamansu babu yabo ba fallasa, kuma babu raini a tsakaninsu, Sam bata bata fuskar da zata raina ta ba.
Taja girmanta kwarai da gaske, ba gaba take yi da ita ba amma idan ba wani kwakkwaran dalili ba bata shiga harkarta.
Shigowar Fatima da siririyar sallama a bakinta yasa ta daga kanta ta bita da kallo, tayi wata firgai-firgai da ita kamar wacce tayi jinyar shekara.
"Fatima zo nan!"
Ta yafi to ta da hannu bayan ta amsa sallamarta, ta nuna mata gefenta alamun ta zauna anan.
"Me yake damunki?"
Ta tambaye ta da tausasshen murya, mai baiyana tsananin tausayi da jink'ai irin wanda yake tsakanin 'ya da uwa.
"Na'am Mummy"
Ta amsa muryarta a cunkushe, fuskarta na kara baiyana tsananin damuwar da take ciki.
"Me yake damunki ne? tsawon kwanakin ukun da nayi a gidannan na fahimci kina cikin matsananciyar damuwa, amma kina kokarin 6oye min.
Wace damuwa ce bazaki iya raba ta da ni mahaifiyarki mu nemo maganinta tare ba? Ko ban kai matsayin da zaki fada min bane?"
Kasa magana tayi, maimakon maganar ma saita fashe da kuka mai tsananin karfi, kifa kanta tayi a cinyarta tana ta kuka.
Bata ce mata komai ba, kyaleta tayi ta zubar da hawayen ko zata samu saukin damuwarta, tsawon lokaci tana kokawa kanta, bayan minti biyar a hankali take rage sautin kukan, tana sauke ajiyar zuciya sauri-sauri, har tayi shiru gaba daya.
"Mummy.. Daddy ya rabani da wanda nake so, sannan ya kwace min waya ta dan kar in neme shi"
Shiru tayi tana tunani, ashe akan so take ta wannan kuncin da damuwar?
"Wanene shi wanda kike so din?"
"Usher... ne..."
Taja sunan da shasshekar murya.
"Usher kuma? Halan shek'ar tsuntsuwa yake da? Idan ban manta *Ush* fassararsa shek'a da larabci"
Dukda damuwar da take ciki saida ta murmusa, sai kuma ta kwa6e fuska.
"Mummy sunan sa kenan fa Usher"
"Auho.. na fahimta! Shi Ushern a ina kika hadu dashi? Kuma me mahaifin naki ya fada miki kafin ya kwace wayarki, dan nasan haka kawai bazai rabaki dashi kuma ya kwace wayarki ba tare da wani kwakkwarar dalili ba"
A gurguje ta bata labarin, amma ta kara gishiri kuma tayi kwaskwarima dan kar Mummy ta goyi bayan Daddyn.
"Ok ina zuwa"
Wayarta ta dauka a gefenta ta duba lokaci, karfe goma saura kwata na dare, tasan dai yanzu baiyi barci ba, a irin wannan lokacin ko suna tare to yana gaban tv ne yana jiran a fara labaran karfe goma.
Dan haka ta danna kiran lambarsa ta kara wayar a kunnenta.
A can bangaren sa kuwa yana tsaye daga shi sai gajeren wando ne, shafa tumbin cikinsa yake yi yana tunanin ta yadda zai afka mata dan ya biya bukatarsa ta yau.
Allah sarki baiwar Allah, tana raku6e tsakanin gado da lokokin gadon tana zazzare idanu, gashin kanta muzu-muzu, babu abinda yake tashi a jikinta sai wari da hamami, kayan jikinta dukun-dukun, amma a hakan Honourable Sumaila yake biyan bukatarsa da ita.
Wani mugun jarabta da Allah yai masa kuwa gamsuwa yake da ita sosai fiye da matan auren shi na sunna.
Murmushi ya saki ya dumfare ta gadan-gadan kamar wani mayunwacin zaki.
Mugun ihu ta kwalla masa lokacin da ya kai hannunsa da niyyar damk'ota, ta suri kujerar zama ayi kwalliya ta daga da nufin maka mishi, da sauri ya goce, ta bishi tana niyyar buga mishi ta ko wane hali, dakyar ya samu nasarar tserewa daga d'akin da gudu.
Yanatsaye a falo yana maida numfashi kiran wayar Hajiya a karo na uku ya shiga cikin wayarsa.
"Hajiya wai ya aka yi ne?"
Ya tambaye ta muryarsa cunkushe, dan kamar bazai dauka ba sai kuma ya dauka.
"Alhaji mun yini lafiya?"
Ta fara da gaishe shi kamar bata fahimci baiyi maraba da kiran wayarta ba.
"Lafiya Lau. Idan ba wani abu zan ajiye waya ina cikin uzuri yanzu"
"Ok.. yaushe zaka shigo ne? Ina ga zaifi mu warware matsalar a nutse fuska da fuska..."
"In shigo? Ai Hajiya ni da shigowa kano sai nan da kwana casa'in.
Dan haka idan ba da wani muhimmin abu ba ku daina damu na dan Allah. Idan kudi kuke bukata zan miki transfer da safe"
Kit ya katse wayar, madadin ya barta a kunne ma dan kar ta sake kira sai ya kashe wayar gaba daya.
Dayar wayar tasa ya dauko ya dannawa Killer kira, wanda a yanzu ya zama dan gaban goshinsa, domin shi ya samo masa mahaukaciya irin wacce Mai Gobe zatai kyau yace ya samo, kuma idan ta nemi yi masa gardama da karfin tsiya Killer yake saita masa ita, daure ta yake gam yaita banka mata kayan maye, sai tayi ligib yake kwance ta Honourable yazo yayi abinda zaiyi da ita.
Abin tausayi idan ta dawo hayyacinta ta ringa kuka kenan tana buge-buge da kayan d'akin. A cikin kwanaki biyar duk ta ji wa kanta ciwo.
Saboda tsoron kar ta gudu idan baya nan daki na musanman ya ware ma killer a cikin dakunan gidan, bayan masu gadi da suke kan aiki ba dare ba rana har su biyu.
A can bangaren Hajiya kuwa rike wayar sansarai tayi tana mamakinsa.
Sai nan da wata uku zai shigo kano? Ah haba dai kila ba'a yake mata.
Amma kuma muryarsa Sam batayi kama da wasa yake mata ba..
"Mummy lafiya kuwa?"
Fatima ta katse mata tunani da wannan tambayar.
"Lafiya kalau Fatima, ki kwantar da hankalinki kinji? Mahaifinki bashi cikin nutsuwarsa a wannan lokacin kinga bai kamata in 6ullo masa da wata maganar daban ba.
Amma in Allah ya yarda gobe zamuyi maganar dashi, nasan kuma zaice a baki wayar ki"
"Mummy to maganar Usher fa? Oh Usher dai Usher dai, ni sunan ne bai min ba, dan kwanakin baya an kama wani mai saida mugayen kwayoyi kuma sunan shi kenan shima.."
"Mummy ba fa nawa Ushern bane, shi nutsattse ne kuma mutumin kirki ne"
"To yayi kyau, Allah ya tabbatar da alkhairi a tsakaninku"
"Ameen Mummy na, shiyasa nake sonki"
Ta fada tana tsallen murna kamar wata karamar yarinya.
Ficewa tayi da murnarta ta bar Hajiya da tunanin a wane hali Alhajinta yake ciki?
******
Zagaye falon suke yi da gudu-gudu, yana gaba yake ta kyalkyala dariya, ita kuma tana binsa a baya tana kukan shagwa6ar da babu ko digon hawaye a cikinsa, hannunta rike da flet din abinci.
Tana cin abinci taje kicin dauko maltina a frig ya cinye sauran abincin da naman ciki gaba daya, ko da tayi magana sai ya fara mata dariya harda gwalo, takaici yasa take binshi dan ta maka mishi flet din ko taji sanyi sanyi.
Da ta fara gajiya da gudun tsayawa tayi a guri d'aya ta fashe da kuka mai tsananin karfi ta durk'usa a kasa ta sa kanta tsakanin cinyoyinta.
Da sauri ya dawo baya yana rarrashinta da kalaman kwantar da hankali, k'ok'arin had'a jikinta da nashi yake yi sai buge mishi hannu take yi idanunta a rufe.
Juyawa yayi kamar ya tafi, yasa gwiwar hannunshi ya naushi bayan kujera yace
"Auch!!!! Wayyo kafa ta..."
A gigice ta Mike tsaye ta nufi gurinsa hankalinta a tashe, yana sane yasa mata kafa tayi taga-taga zata kifa baya ya janyo rigarta ta kifa a jikinsa.
Runtse ido yayi yana jin wani dadi yana sauka a jikinsa ai sai ya sake kankameta kamar zai maida ta jikinsa.
Sai zare ido take cikin rude wa, tunani take da ta fadi baya bata san irin mugun buguwar da zata yi ba, ko da ta ankara a jikinsa take da sauri tasa hannuwanta ta tura shi baya da dukkan karfinta.
Inda Allah ya taimake shi yayi saurin saka hannu ya dafe kujera tabbas da ya fadi kasa.
Zagaye shi tayi da sauri fuskarta a daure ta nufi bangaren dakunansu.
"Ke kuma lafiya kike wani ciccin magani? Ke da waye?"
Ama ta tambaye ta daidai lokacin da take fitowa daga dakin ita kuma tana k'ok'arin shiga dakin, daman wanka taje ta barta a falon tana cin abinci suna hira ita da Kamal.
Ganin bata tanka ta ba yasa ta karasa falon, Kamal ta gani a tsaye fuskarsa jagule da damuwa.
Tana shirin tambayarsa abinda ya faru sai Mummy tayi sallama ta shiga cikin falon.
"Oyoyo Mummyn mu"
Ya fada da dan murmushi a fuskarsa.
"My Boy sau nawa zan tuna maka amsa sallama shine farko Sannu da zuwa ya biyo baya?"
Kwabe fuska yayi kamar karamin yaro
"Afuwa Mummy"
Sai ya amsa sallamar sannan ya sake mata barka da zuwa.
Kafin Amatullahi ta karbi jakar hannunta har ya karba, ya shige mata dashi daki.
A wannan daren Sam hirarsu batayi armashi ba, saboda Iman karad'i ta shige daki tun wuri ta kwanta, bayan ta yiwa Mummy karyar kanta na ciwo.
Shima Kamal cewa yayi ya gaji, barci yake ji, duk ya shiga damuwa saboda fushin da take yi dashi, baisan ya shaku da ita har haka ba sai yau da ta share shi, abinda bai ta6a faruwa tsakaninsu ba tun dawowarsa gidan.
Dan haka ko da ya kwanta ma kasa barci yayi, sai juye-juye yake yana tunaninta.
*****
Karfe biyu da rabi suka yiwa gidan kawanya, basu sha wani wahala ba gurin shiga gidan da tattara iyalan gidan gaba dayansu guri d'aya.
Bayan sun yiwa mai gadi Mal Ilu wani mugun dauri irin na huhun goro.
"Hajiya Abida manyan mata.. ina fatan kin gane ni?"
Ya tambaye ta da jajayen idanunsa yana sosa gashin bakinsa da bakin bindigar hannunsa.
A tsorace ta sake dago kanta tana satar kallonshi, ita kuwa ya za'ayi ta manta wannan fuskar? Pele ne fa, na hannun damar mijinta Alhaji Tijjani a bangaren aikata miyagun laifuka.
Mutumin da yaso ya kashe ta ita da yaran ta bayan da sauran rayuwarsu a gaba.
Ta ma kasa kuka ko kadan, tana ta janyo duk addu'ar da tazo bakinta. Yaranta kuwa sai kuka suke yi hankalinsu a mugun tashe, dan duk sun gane shi.
Wani mugun ciwo da kansa yake yi yasa idanunshi sukai ja, jijiyoyin kansa sun taso rudu-rudu, yanda yake jin kamar zai mutu yasa ya mike yana tangadi ya nufi kofa dan zuwa gurin Mummy ta bashi magani.
Yana bude kofar daya daga cikin abokan tafiyar Pele ya shammace shi ya buga mishi sanda a bayan kanshi, take ya zube kasa a sume.
Pele kuwa jikinsa yana tsuma ya tashi tsaye yana kara kallonshi yana ja da baya a tsorace, daman kuma yana sanye ne da kayan barci farare...
"Wayyo.. fatalwa..."
Abinda ya iya fadi kenan a tsorace ya ci kafar kare, sauran tawagarsa suka rufa masa baya, babu wanda ya sake bi ta kan Mummy da yaranta.
*BARA A KUFAI!!*
*28)*
"Alhamdulillahillathi ahyana ba'ada ma amatana wa ilaihinnushur"
Addu'ar farkawa daga barci suka hi bakinsa yana karantawa a hankali kuma cikin sanyin murya.
Ko kafin su karasa gare shi har ya bude idanunsa yana kallonsu, mik'a yayi kasusuwar hannunsa sai kara suke yi, salati yayi ya gode wa Allah mahaliccin sammai da kassai, ya maida hankalinshi kansu kamar yanda suke kallonsa sun kasa cewa komai, Sun zuba masa idanu kamar wadanda suka warke makanta.
"Sannunku! Sunana Kamaluddeen. Dan Allah ina ne nan? Ni haifaffen garin kano ne a unguwar Fagge, ina hanyar komawa gida wasu 'yan sanda suka tare ni suka jani daji da niyyar su kashe ni, Allah ne yasa ina da rabon sake rayuwa a gaba shiyasa har kuka taimake ni.
Dan Allah ku su waye? Kuma ina ne nan?"
Ya sake tambayarsu bayan ya gama rattabo musu bayani kamar an kunna radio.
Wani murmushi mai kama da na yake Khadeeja tayi, Mummy da Ama dukda tsananin damuwar da take cunkushe a zuciyarsu bai hana fuskar su baiyana farin ciki ba, duk sun fahimci me yake faruwa dashi.
*Kamaluddeen Ya dawo cikin hayyacinsa*
Sanadiyyar dukan da aka yi masa a kansa lokacin da yake fama da matsanancin ciwon kai.
Tun wancan faduwar da yayi akan dutse Dr. Tayi tunanin ko tunaninsa zai dawo, amma cikin iko na Ubangiji sai bai dawo ba.
Yawan complain da yake mata na kanshi na matsanta mishi da ciwo daman alamu ne da suke baiyana ako wane lokaci tunaninsa zai iya dawo wa.
Wannan babban abin farin ciki ne a gare su.
"Nan kana cikin garin kaduna ne, a cikin gida na ni Dr. Abida.
Wad'annan kuma yara na ne, Amatullahi da Khadeeja"
Gyada kai yake yi alamun yana fahimtar duk bayanin da take mishi, ko da ya fahimci ta gama bayanin da take mishi yunkurawa yayi ya mike zaune.
"Na gode kwarai da irin taimakon da kikayi min likita, bani da abinda zan biya ki dashi saidai inyi miki addu'ar Allah ya biya ki da alkhairinsa, Ubangiji ya shirya miki zuri'arki yasa musu albarka"
"Ameen."
Suka amsa gaba daya, fuskarsu na baiyana jin dadin addu'ar sa.
Kallon mamaki suka bishi da shi a lokacin da suka ga ya mike tsaye, wata riga da take ajiye a gefen gadon ya dauka ya saka.
"Kamal? Ina kake k'ok'arin zuwa?"
Mummy ta tambaye shi bayan ta fahimci manufarsa ta tafiya.
Murmushi yayi mata
"Likita ina ga ya kamata in tafi gida, nasan can kano hankalinsu a tashe yake da rashin koma wa ta gida"
"Kamal kasan tsawon lokacin da ka dauka rabonka da gida kuwa?"
Khadeeja ta tambaye shi da mamaki.
Girgiza kai yayi alamun bai sani ba, sai kuma ya fara kallon sassan jikinsa inda su DPO suka jijji masa ciwo, ganin babu ko alamun ciwo yasa ya shafa fuskarsa, sai ya ji ta sulum babu alamun ciwo ko guda d'aya, eh lallai dole ya kasance yayi kwanaki a gurinsu tunda duk ciwukan jikinsa sun warke.
"Shekarunka biyar da wasu kwanaki rabon ka da dangin ka Kamal"
Amatullahi ta katse mishi tunanin shi fuskarta na baiyana zallar tausayinsa.
Bai dawo daga duniyar mamaki da tsoron da ya shiga ba Dr. Abida ta haske mishi fuskarsa da madubin da ta shiga cikin daki ta dauko.
Tsananin tsoro da firgicin da ya shiga saida ya dauke wuta na wucin gadi, wata fuska yake gani a jikin tasa wacce ko kusa ko alama bata yi kama da ainahin tasa fuskar ba.
A tsorace yakai hannu ya shafa fuskar yaji tana nan fa a jikinsa ba fuskar roba bace
"Wan...wwwan...wwannan fuskar...."
"Tawa ce!"
Dr. Abida ta katse masa in inar da ya fara yi yana nuna fuskarsa da yatsarsa manuniya.
Ya bita da kallon mamaki bakinsa na rawa ya rasa ta cewa
"Eh tabbas wannan fuska ta ce a jikin taka.
Ba fuskar kowa bace sai ta d'ana marigayi Kamaluddeen.
A lokacin da Khadeeja ta tsinto ka ta fitarda tsammanin kana da rai...."
Nan take ta bashi labarin duk abinda ya faru dashi tun daga wancan lokacin har zuwa yau dinnan da suke ciki.
"Dan haka batun ma zaka koma kano gurin danginka ka aje shi a gefe daya, a gurin mutanen duniya yanzu Kamaluddeen ba kowa bane face Usher, shi kuma Usher ba kowa bane sai dan ta'adda, dila kuma tantirin mai safarar miyagun kwayoyi, wanda kusan duk jihohin arewacin Nigeria 'yan sanda suke nemansa, a gefe guda kuma wadanda yake yiwa safarar kwayoyin suna nemansa su kashe shi...."
Luuuu.... Ya tafi zai fadi a k'asa saboda tsananin tashin hankalin da yake ciki.
Da saurin gaske Khadeeja da ta lura da halin da yake ciki ta kai hannu da nufin tare shi kar ya fadi kasa sai suka zube akan gado gaba daya, saboda ya fita girma nesa ba kusa ba.
"Wayyo Allah Mummy ciki na.."
Ta fada da kyar, tana numfarfashi saboda ya sakar mata duk nauyinsa.
Sai da suka taru sannan suka murgina shi gefe daya
"Mummy... Ya suma fa"
Amatullahi ta fada hakan hankalinta a tashe tana jijjiga shi.
"Karki damu Ama, samo min ruwa mai dan sanyi a frig, tsananin rudani da tashin hankalin da ya shiga ne yasa jijiyoyin aika sako cikin kwakwalwarsa tsayawa na d'an lokaci.
Zai dawo daidai"
Ruwan sanyin da aka kawo mata take shafa mishi kad'an kad'an a fuska tana tofa mishi addu'o'i.
Cikin kankanin lokaci yaja wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, a hankali ya bude idanunsa ya sauke akan Dr. Sai kuma ya fashe da kuka mai tsananin karfi kamar ba namiji ba.
"Wallahi Allah ni Kamal ba haka halayena suke ba... iyayena sun bani kyakkyawar tarbiya irinta addinin musulunci a iya tsawon rayuwarsu kafin su koma ga Allah... Inna lillahi wa Inna ilaihi raji'un..."
Cikin fita haiyaci yake wadannan surutan hankalin sa a tashe.
Shi Kamal ne da aikata wadannan miyagun laifukan? Ina hankali da tunani da tarbiyyar sa suka shiga?
"Calm down! Calm down Kamal. I'm very sorry. Duk munsan ba halinka bane saboda mun karanta kyakkyawan tarihinka wanda ka rubuta ka aje a cikin jakar kayanka.
Ka dauka wannan kaddara ce da Allah yajarabeka da ita. Sai kayi addu'ar Allah ya baka ikon cinye jarabawa"
Tsawon lokaci suna rarrashinsa, dakyar suka samu yayi shiru dan su nemi hanyar da zata zame musu mafitar da zata wanke duk laifukanshi a idanun duniya.
0 comments:
Post a Comment