Yanda ta buga mata sammakon zuwa gida da matsanancin tashin hankalin da ya gaza 6oyuwa a fuskarta shine abinda ya bata tsoro.
Da kyar ta iya tsayawa suka gaisa da Yasmin, abokiyar zaman Aysha, kafin taja hannunta suka nufi daki.
"Muhimmiyar magana nake tafe miki da ita kawata, dan Allah ki kulle kofar nan"
Ba musu ta murza key ta kulle kofar ta dawo kusa da ita ta zauna, da yake su Abee a gurin Yasmin suke kwana.
"Kawata kiyi hakuri, dukkan wani tsanani yana tare da sauki.
Pls ki fada min damuwarki inji ko zan iya taimaka miki"
Aysha ta fadi haka cikin rarrashi bayan ta dafa kafadar Khadeeja, wacce take zaune ta kasa magana, lokaci lokaci tana sanya hannu ta dauke hawayen idanunta.
"Dan Allah kawata ki bani hankalinki, ki saurari labarin da zan baki da kunnen basira..."
Nan take ta kwashe duk labarin Kamal ta fada mata, sannan ta nuna mata hotunansa a lokacin da ta tsince shi a cikin daji, bata 6oye mata komai cikin abinda ya faru ba.
Akwai aminci da shakuwa mai karfi tsakaninsu, tare suka yi karatu, dukda ba abu daya suke karanta ba kansu a hade yake.
Ita Aysha ta karanci Law ne, ita kuma Khadeeja ta karanci Mass com.
Lokacin da ta fada mata ita matar aure ce da farko ta zaci wasa take mata, sai daga bisani ta yarda bayan ta gaiyace ta gidanta kuma ta nuna mata kyakkyawan matashin dan Sandan a matsayin mijinta.
"Yanzu kawata wane irin taimako kike so inyi miki?"
Ta tambaye ta zuciyarta cike da tausayin Kamal da tausayin labarin rayuwarsa.
Kuyi hakuri da wannan pls👏🏻 gobe zaku samu mai yawa in Allah ya yarda.
*BARA A KUFAI*
*29)*
"Abban Abee dan Allah ka tsaya ka saurare ni mana..."
Ta fadi hakan tana binshi a baya da sassarfa, bata ko jin nauyin cikinta da ya fara girma.
Wani mugun kallo mai kama da na gargadi da ya juyo ya watsa mata yasa tai sanrarai a tsaye tana kallonshi.
Ganin da tayi yana gaf da ficewa daga d'akin yasa ta sake yunkurawa da sauri tace
"Abban Abee..."
"Ya ishe ki haka Aisha"
Ya kira sunanta gatsau kuma cikin tsawa yana d'aga mata hannu alamar dakatar da ita daga abinda take da niyyar ce mishi.
Tsam tayi da ranta tana kallonshi da tsananin mamaki, a iya tsawon zamanki ta manta yaushe rabon da ya kira sunanta kai tsaye balle kuma yayi mata mugun tsawa irin wannan, ko rantsuwa tayi baza tayi kaffara ba akan bai ta6a mata haka ba, shiyasa yau al'amarin yazo mata da bazata da ban tsoro.
Ko laifi tayi masa cikin hikima da sanyin murya yake nusar da ita kuskurenta, ita kuma sai ta sauke duk wani girman kai ta bashi hakuri, su fahimci juna a take su wuce gurin...
Ganin yanda yake nufo ta da takunsa na dakakken namiji kuma jarumin d'an sanda yasa ta watsar da tunanin da take yi ta tsaya tana jiran karasowarsa.
"In dai akan maganar wannan tantirin d'an ta'addan mai safarar miyagun kwayoyi kike k'ok'arin dakatar da yunkurina na kama shi zanyi mugun 6ata miki rai...
Ki fita daga idanu na Aisha.. ba sai kinyi hakan ne zaki tunatar dani kema tsohuwar 'Yar benelyn bace"
Kirjinta ne ya buga dam! Cikin kankanin lokaci idanunta suka kad'a sukai jajur! Wani mugun fushi da matsiyacin 6acin ran da ya dad'e bai taso mata ba tun tana *Aysha Azzahra'u* ne ya dawo mata sabo dal a zuciyarta.
Lallai sai yau ta yarda da karin maganar nan ta matar bahaushe da take cewa
*Namiji k'udan Zuma ga zak'i ga harbi*
Har ita Abdul zai kalli Tsabar idanunta ya kira ta tsohuwar 'Yar benelyn? To bari ta nuna mishi har yau a d'iyar zahra'u take ba wai an canja ta bane..
Tana daga idanunta da nufin zazzage masa taga wayam! Ashe har ya fice daga d'akin.
6angarensa ta nufa da niyyar ta tadda shi sai taji tashin muryarsa a bangaren Yasmin.
Muryarsa taji cikin fada yana ba Yasmin labarin abinda Aishar tayi mishi
"Wannan ai rashin hankali ne da hauka..."
Jikinta har tsuma yake ta banka kofar ta fada cikin falon ko sallama bata yi ba, Yasmin tana tsugune a kasa tana zare masa takalmin kafarsa, idan ba idanunta ne suke mata gizo ba har murmushi taga Yasmin din tana yi, wato ita ranta fes anyi fada da kishiyarta ita an dawo gurinta ana bata labari...
Da jajayen idanunta take k'are musu kallo duk su biyun, hannuwanta rike da k'ugunta, sai cikinta ya fito cas a cikin rigar da take sanye dashi.
Kallon da take mishi tunani take yi a ranta yaushe har tayi kwantai a zuciyar Abdul da har zai ringa gwada mata kalolin wulakanci irin haka?
"Abduul'ahad"
Ta kira sunan shi a tsaye tana watsa mishi wani wawan kallo da ya rasa ko na miye.
"Babban burinka shine ka farantawa Kwamishina rai ta hanyar sake kama Kamaluddeen ko?
To ina taya ka murna, domin kuwa muradinka yana daf da cika.
Kaje gidan Dr. Abida, Mahaifiyar Khadeeja kawata 'Yar jaridar nan a yau ba sai gobe ba zaka same shi a can!
Idan ka kama shi ka kulle shikenan burinka ya gama cika koh?"
Ta tambaye shi tana wata dariya mai kama da na 6acin rai, ta taka ta sake matsawa daf dashi, ta zube mishi idanunta wadanda bayan ja har kore-kore sukai, taci gaba da cewa
"Amma kuma ka sani, ko kun kama shi baka da ikon yanke mishi hukunci dole saidai ku mika shi kotu.
Idan kuwa hakan ta faru Barrister Aysha Azzahra'u zata bi duk kotun da ka kaishi a matsayinta na lauyan da zatai gwagwarmaya a cikin lauyoyi ta wankeshi.
Tsohuwar 'Yar benelyn zata ceci d'an uwanta d'an benelyn, kaga wannan kyakkyawar alakar tawa da Kamal bai kamata ta tafi a iska ba..."
"Haba mana Aysha dan Allah...."
Wani kallo da ta watsa mata gum tayi da bakinta ta sauke kanta k'asa.
"Karki kuskura ki saka min baki in ba so kike in zage ki ba, da wanda ya aje ki nake yi.."
Tana gama fad'in haka da gudu-gudu ta fice daga falon ta nufi hanyar da zata kai ta 6angaren ta.
Zuciyarta banda tuk'uk'i da k'una babu abinda take yi.
Tana shiga falon ta wasu zafafan hawaye suka zubo mata, da sauri takai hannu ta share tana mamaki, wai yau ita ke kukan bakin ciki akan Abdul'ahad? Lallai wannan rana ya shiga kundin tarihin bak'ak'en ranakun rayuwarta.
Hawayen ne suka ci gaba da zuba tana goge wasu sabbi na sake gangarowa.
Far tayi da idanunta alamun to ita miye ma nata a ciki? Can ta matse musu ita da uban yaran ta, dama dai ba Aisha da Abdul bane, sanda zasu shirya ma bata da labari.
Dan haka ta watsar da damuwar abin a ranta ta fara kokarin kwantar masa da hankali, tunda ranar girkinta ne bazata bari ya tafi akan damuwar fad'an da kishiyarta tayi da mijinta ba.
"Ya Abdul dan Allah..."
Hannu ya d'aga mata kawai alamun ta saurara masa.
Takalman da ta zare a kafarsa ya maida, ya mike ya dauki makullin motarsa da ke ajiye gefenshi ya fice daga d'akin, ummm baice mata ba.
Ranta a 6ace ta bishi da kallo, daman tasan wannan fad'an dole sai ya shafe ta.
Tana wannan tunanin taji ficewar motarsa daga gidan gaba d'aya.
Dogon tsaki taja ta tuge d'aurin d'ankwalin da ta 6ata lokaci tana yi dan ta burgeshi tayi hurgi dashi akan kujera, ta shige cikin d'aki lokacin da idanunta suka fara cika da hawaye.
Bayan sha tale-talen da yai tayi a cikin gari da motarsa ya rasa gurin zuwa a karshe dai Ofis d'insa ya koma ya kulle kansa yana tunani.
Frig ya bud'e ya d'auki gorar ruwa mai sanyi ya kwankwad'e tas sannan yayi hurgi da goran.
Nutsuwa yayi akan kujerar sa yana juyi yake tunanin abinda ya faru dashi da yammacin nan!
Yana daf da tashi a aiki Kwamishina ya aiko kiransa, haka kawai yaji ransa ya 6aci da kiran nan, tsaki yaja, dan yasan tatsuniyar gizo bata wuce ta koki, cikin kwanakinnan ya matsa mishi da zancen sake kamo Usher.
Kamar dai ma a hannunsa ne aka samu nasarar tserar dashi.
Yanda yai hasashen kuwa hakan ce ta tabbata.
"Abdul! Wai me kake ciki ne akan alwashin da kayi na sake kama Usher?
Bincike na ya tabbatar min har yau yana cikin garin kaduna, ya kamata ka sake kamo shi dan sake d'aukaka darajar hukumar mu ta 'yan sanda.
A ina binciken ka ya tsaya ne?"
"Har yanzu ina kan bincika inda ya 6oye ne yalla6ai, zan kamo shi kwanannan in Allah ya yarda"
"Kullum haka kake cewa Abdul, ya kamata dai ka k'ara bada himma.
Zuwa jibi ka tabbatar ka zo min da bayanin duk abinda kake ciki"
"Ok Sir"
Ya amsa da ladabi, sannan ya k'ame ya sara masa.
Da biron hannunsa ya nuna masa kofa, alamun ya fice ya bashi guri.
6acin ran Kwamishina yasa bai tsaya yakai lokacin da ya saba tashi ba ya fice ya nufi gida.
Yana zuwa Aysha bata lura da 6acin ran da yake ciki ba ta tare shi da zancen bai kamata ya kama Usher ba, dan shi ba mai laifi bane, kuma cikakken sunan shi Kamaluddeen.
Daga haka bai barta ta sake mishi wani bayani ba ya sauke duk wani 6acin rai da ya guntso a gurin Kwamishina a kanta.
"Inna lillahi wa Inna ilaihi raji'un"
Ya ambata a fili hankalin sa a tashe,
Lallai ya kara yarda daga lokacin da mutum ya fushi to kamar ya mikawa shaidan linzamin zuciya da harshensa ne.
Sai yanzu da ya fara dawowa cikin nutsuwarsa yake tunanin irin manyan maganganun kuma munana da ya jefi Aisharsa da su, mace mafi soyuwa a cikin birnin zuciyarsa.
"Tsohuwar 'Yar benelyn?"
Wannan kalma tayi munin da ko shi baya son tuna ta.
Kuma wai har shine yaje d'akin Yasmin yana aibata Aisharsa kamar wani bugagge? Da kalmomi marasa kyau irinna rashin hankali da hauka?
"A'uzu billahi minasshaid'anir rajeem"
Sai a yanzu yake neman tsari da shaid'an abinda ya kamata yayi tun da farkon lokacin da ya hau dokin zuciya.
Wani tunani da ya darsu a zuciyarsa yasa ya d'auki makullin motarsa ya fice daga Ofis din da sauri, k'ananun ma'aikata suna k'ame mishi suna mishi a sauka lafiya ko kallonsu baiyi ba, da ya shigo ma hannu kawai ya iya d'aga musu ya shige ciki.
Da yake duk sun San ba halinshi bane wulakanta na kasa dashi sai sukai masa uzuri, suna ta masa addu'ar Allah ya yaye mishi damuwarshi.
Gidan Dr. Abida ya nufa da motarsa kai tsaye, a zuciyarsa yake tunanin wane kakkarfar hujja gare ta da har zata 6oye babban mai laifi kamar Usher?
Wani labari Khadeeja ta ba Aysha da har ta yarda kuma ta gamsu cewar Usher ba mai laifi bane? Har take ikirarin tsaya wa a kotu karo na farko a rayuwarta saboda shi?
Lallai idan basu bashi gamsassun hujjoji akan tuhumar da zaije musu da ita ba to tabbas sai ya tona musu asiri a idon duniya, kuma duk sai ya maka su a kotu an yanke musu hukuncin da yayi daidai da laifin da suka aikata.
*Jaruman littafin A DALILIN 'DA NAMIJI nake fad'a muku🥰🥰😘😘. Mai so ta tuntubeni ta pc dan samun complete labarinsu 1&2&3 akan 300 kacal👌🏻👌🏻 sunyi cakwakiya ba kad'an ba fa, gasu kuma zasu sake taka wata rawar a labarin Kamal😍😍*
*****
Tun daga farko-farkon unguwar idan aka kasa kunne sosai za'a iya jiyo ihu da karajin azabar wanke kafarsa da ake yi.
Makwaftansu sai hmm hmm hmm da zunden shi da mahaifiyarshi suke yi, basu cika tausaya mishi ba balle kuma har su shiga gidan suyi mishi sannu.
Da yawansu cewa suke shi ya jawo wa kanshi? Yanzu ina Honourable d'in da yake ganin ya tsaya mishi har yake kartawa mutane rashin mutunci son ransa?
Duk unguwar baya ganin kowa da gashi, babu wanda yake ganin ya isa dashi, ko mahaifiyarsa bata isa ta tilasta mishi yin abinda baiyi niyya ba.
Yanzu sai ya zage mutum tas, tun daga sama har k'asa, a yanda yake cewa baya jin kunyar uban kowa, duk wanda ya nemi matsa masa saidai uwarsa ta haifi wani.
Shiyasa ko da mummunar kaddarar ta afka masa d'ai-d'ai mak'waftan da suka lek'a gidan da sunan jaje, suma dan zuciyar musulunci ba dan halinsa ba.
Haruna mai maganin karfe gabjejen mutum ne majiyin karfi, shi Inna Tala take d'aukowa duk bayan kwana biyu ya wanke k'afar Kb, wacce babu abinda take yi sai wari, ciwon yana ta sake cin cikin jikinshi ba tare da ta ankara ba.
Duk ranar da Haruna zai wanke ciwon nan ya bad'eta da garin maganin gargajiya to a wannan ranar unguwarnan yini guda kunnensu bazai huta da jin ihu da karajin Kb ba, saboda tsananin azabar da yake sha.
Wurjanjan suke yi daga shi har Kb, in banda mai maganin kakkarfa ne da sam Kabiru bazai ruku mishi ba, amma dukda haka suna ji a jika duk su biyun.
Idan mai maganin ya tafi kuwa yakan dauki fiye da awa guda bai iya cewa komai ba, sai dai maida numfashi da gurmususun wahala.
"Inna..."
Ya kira ta dak'yar yana sauke numfashi d'ai d'ai na wahala.
"Na'am! Sannu Kabiru. In mik'o maka farau-farau d'in ne?"
Ta tambaye shi da kulawa da tausayi a fuskarta.
"Inna dan girman Allah ki taimake ni ba dan halina ba... nasan na dad'e ina sa6a miki, na dad'e ina 6ata miki rai... Sam ba na yin abinda kike so... ba na barin abinda bakya so... Amma dan Allah ki taimaka ko gidannan ne ki sayar ki kaini asibiti... ni kadai nasan irin azabar da nake sha da kafar nan, ji nake wasu abu masu kama da tsutsotsi suna min yam-yam a cikin ciwon... ki taimake ni kar in mutu Inna.. indai Allah ya tayar dani Wallahi bazan sake 6ata miki rai ba...
Zan daina shaye-shaye.. zan daina bin honourable, kuma zan daina jagaliyar siyasa..
Ki taimake ni dan Allah Inna..."
Yana magana yana kuka, k'uda kuwa sai binsa suke yi yam kamar sun sami kwallon mangwaro.
Ita ma Inna kuka take yi, tana ta jujjuya maganganunsa a zuciyarta.
Ina amfanin bad'i babu rai? Kabiru shi kadai ne d'anta da yake raye, a cikin tarihin rayuwarsu kaf gidannan shine kadai babban kadarar da suke da, sai kuma wasu tunkiyoyi nata guda uku a kauye, ko suna raye ko suna mace ma oho, dan saita shekara uku bata leka k'auyen nasu ba.
Tunda duk iyayenta sun rasu, tunkiyoyin ma a hannun kanwar Innarta ta barsu.
Ina amfanin Kabiru ya mutu ya barta da gidannan nan?
Dan haka duhun magriba na fara shiga ta yafa zane a kanta ta nufi gidan Dan asabe dillali da bukatar ta.
Shi kuma da yaga banza ta fad'i raga-raga ya saya gidan, a tayin farko ta sallama mishi babu ko musu, yace taje da anyi sallar asubah zai kawo mata kudin gidan.
Tsabar murna har kasa ta durkusa tana zuba mishi godiya, tana tafe a hanya tana ji a ranta da yaddar Allah matsalolinta sun kusa zuwa karshe.
Washe gari kuwa karfe bakwai na safe ta samo shatar mota suka yiwa asibin sojoji na 44 dirar mikiya, bayan ta dafe kudin gidan a mararta.
Lokacin da likitocin sukai arba da kafar Kabiru kuwa Inna tasha masifa, wani likita mai tsananin zuciya har marinta yayi kamar ba tsohuwa ba, da farko ma cewa sukai baza su kar6e shi ba.
Har kasa ta durk'usa tana ta kuka tana rokonsu, direban motar da ya kai ta shi ya taya ta basu hakuri, ya kara da cewa daga k'auye suke, sakacin mutanen kauye shiyasa suka barshi a gida kafar ta fara ru6ewa.
Direban shi ya tsaya mata ta biya duk abinda aka bukata, cikin kankanin lokaci suka shiga dashi dakin tiyata, bayan sunyi hoto sun gano kafar ta riga ta fara ru6ewa, ga kuma tsatsar wuk'a ya shiga ciki, dad'ewar da suka yi a gida babu kulawar likitoci yasa daji ya fara shiga, magunguna da allurai baza su yiwa kafar ba, babban mafita kawai a yanke kafar.
Dan haka likitoci suka rufu a kansa.
*****
"Yauwa! Kace mene Figo? Ina saurarenku"
Ya fad'a bayan ya ajiye wayar da ya gama amsawa ta tsawon minti goma sha biyar.
Ba tare da kosawa ba Figo da kaninsa suka ci gaba da jiransa har ya gama, ya sake tambayarsa a karo na biyu bayan tun kafin ya fara wayar ya fada masa bukatar da take tafe da su.
Sake gyara zama yayi yace
"Honourable wannan k'anina ne, sunansa Khalid.
Yaro ne mai tsananin kokari a makaranta, duk jarabawarsa na 1 ko 2 yake ci, bai ta6a cin na uku ba.
Aji shidda yake a matakin sakandire, suna gaf da rubuta jarabawar fita.
To naji kana biyawa dalibai kudin jarabawar fita shiyasa na taho dashi kasa sunan shi a list"
Shigowar 'yarsa cikin falon bakin tana yauk'i da kwarkwasa yasa ya maida hankalin sa gaba daya a kanta.
Karamar yarinya ce wacce tun bata tafasa ba take neman k'one wa, domin a kiyasce baza ta wuce shekaru sha bakwai ba.
Ta saka wani kwamemen gilashi wanda ya mamayi kusan rabin fuskarta, ta nad'a siririn gyale a wayarta, sangalin hannunta mak'ale da jaka, ga makullin mota a yatsarta tana karkad'awa.
"Hi Dad"
"Hi Sweetheart, kin shirya kenan?"
Ya tambaye ta bakinsa kamar gonar auduga.
"Eh Daddy"
Ta amsa tana kallonsu Figo a k'yamace.
'Daurin dubu dari ya mika mata
"Ina fatan zasu ishe ki?"
"Ba matsala, zanyi maneji"
Ta jefa kudin a jaka, ta nufi hanyar ficewa daga falon.
"Akan me kake magana ma?"
Ya sake tambayarsa a karo na uku.
Ransa a bace da wannan wulakancin yace
"Ka biyawa kani na kudin jarabawa..."
"I'm sorry to say kun makara Figo"
Ya katse shi fuskarsa babu walwala, bai jira cewarsa ba ya cigaba da cewa
"Yaran da nayi alkawarin biya musu tuni na tura kudaden..."
"Honourable a takaice kana nufin?"
Figo ya tambaya ranshi a 6ace, shi kuwa Khaleed daman kanshi na kasa, murmushi kawai yake amma irinna takaici.
"A takaice kwandala bazan biwa wa kaninka ya zana jarabawa ba"
Hannun Yayansa kawai ya kama suka Mike tsaye, tunda bazai biya ba miye amfanin zamansu?
"Ghali ka tabbatar wannan zuwan tawa gurinka shine na karshe, kuma shine karshen alakar da yake tsakanina da kai.
Wallahi muddin ka sake kira na idan Nazo gidannan ka tabbatar na zo da6a maka wuka ne, gara in kashe ka in rage mugun irin masu lalata tarbiyar MATASA yaran talakawa.
Saidai nima a kashe ni"
Yaja wani wawan tsaki suka fice daga falon, zuciyarsa sai tururi take yi, ya kasa cewa kaninsa komai, dan da kwarin gwiwarsa dari bisa dari ya dauke shi zuwa gurin Honourable din.
*BARA A KUFAI*
*30)*
*Kuyi hakuri pls, jiya banda lafiya ne wallahi*
Lokaci zuwa lokaci yana sa babban yatsarsa ya dauke hawaye daga kwarmin idanunsa.
Sannan ya duk'ar da kai ya ci gaba da rera kira'ar suratul kahfi da muryarsa mai tsananin dad'i da taushi.
Yinin ranar gaba d'aya zuciyarsa a kuntace yake, ya kasa cin komai, banbancinsa da mai azumi kadan ne, ruwan da yake kur6a lokaci bayan lokaci.
Da siririyar sallama a bakinta ta shiga cikin dakin, hannunta na dama dauke da plate, ko da na leka cikin farantin shake yake da indomie yana ta fidda turirin zafi da kamshin dad'i.
A hannunta na hagu kuma kofi ne mai dauke da coffee, shima da zafinsa sosai kasancewar lokacin sanyi sanyi ne.
Sai tashin kamshin kayan su citta yake yi.
A gefensa ta ajiye kayan abincin, ta nemi guri ta zauna tana k'ara gyara zaman mayafin jikinta.
Karatunsa ya ci gaba da yi dan Sam baya son sauraran wata magana daga bakinta, ita kuwa ta sake gyara zaman jiran yakai karshen inda yake son kaiwa ba tare da k'osawa ba, da ta fahimci manufarsa kauda kanta gefe d'aya tayi tana murmushi.
"In kasan wata ai baka san wata ba"
Ta fada a zuciyarta, can kawai saita fara gyangayadi, tana yi kamar zata kwanto a jikinsa tsabar baccin da yake jan ta.
Ganin haka da yayi ai da sauri ya kai aya ya katse karatun, rufe alk'ur'anin yayi ya aje a gefe, ya kalleta na wasu seconds, bubbuga k'asa ya fara yi yana kiran sunanta muryarsa cike da rauni...
"Khadeejah... Khadeeja... Ya kamata ki tafi ciki ki kwanta.."
Firgigit ta farka kamar wacce take barcin gaske, hannunta d'aya tasa tana murza idanunta guda d'aya, ta kwa6a fuska ita irin a dole ya tashe ta daga barci ba da son ranta ba.
"Ya Kamal.."
Ta kira sunan shi a shagwa6e, muryarta can ciki...
"Ka ga fa abinci ne na sake dafa maka da hannuna, tunda Mummy tace min baka ci abinci ba duk yinin yau, shiyasa na shiga kicin na dafa maka indomie mai dadi, matso ka ci"
Kallonta yake yi yanda take fitar da ko wace harafi a muhallinta, murmushin yake yayi.
"Na gode! Amma bana jin yunwa, ki koma dashi kawai..."
Shasshekar kukanta da yake ji yasa ya katse maganar da yake yi, a tsorace ya daga kai ya kalle ta, kanta yana tsakanin cinyoyinta tana kuka...
Sai kuma jikinsa yayi sanyi, yaja flet din zuwa gabansa ya dauki kofin ya rike a hannunsa.
"Yi hakuri dan Allah Iman... kinga ni fa ba nufi na in 6ata miki rai ba.
Is ok! Kinga na dauki abincin zanci"
Ya fada yana k'ok'arin kai lomar indomie bakinsa, da sauri ta kai hannunta ta rike hannun da yake k'ok'arin kaiwa baki, kallonta yayi da mamaki.
Ta saki hannun da sauri bayan ta tuna kuskuren da tayi.
"Ka fara shan Coffee din saboda cikinka ya warware..."
Ta fana tana tura baki, kanta a kasa tana matsa yatsun hannunta.
Da murmushi yake kallonta,
"Yarinya mai nutsuwa"
Ya fada a zuciyarsa, kamar yadda tace Coffee din ya dauka yana kur6a a hankali, sai lumshe ido yake yana jin dadin ruwan zafin, cikin kankanin lokaci ya shanye.
Kallonta yayi lokacin da ya dire kofin a kusa da ita.
"Khadeejah?"
Ya kira sunanta a hankali yana murmushi.
"Na'am Ya Kamal"
Ta amsa a hankali kamar yadda ya kira ta, ta daga kanta da nufin kallonsa, caraf suka hada ido, da sauri ta sauke kanta a kasa tana murmushi.
Haka kawai take wani jin kunyarsa, wani kwarjini da cika ido yake mata,
ta rasa dalilin da yasa haka.
"Na gode kwarai Khadeejah, Allah ya biyaki da dukkanin alkhairinsa"
Ya sake fada muryarshi tana rawa-rawa, kamar zai saka kuka.
Kallonshi tayi da mamaki.
"Godiyar ta mecece Ya Kamal?"
"Godiyar ceto na da kika yi a daji kika kawoni cikin ahalinki, kin cancanci in gode kwarai... saboda ba don ke ba kila da yanzu na dade da ru6ewa, tsuntsaye sun gama caccakar nama na na zama kwarangwal na saje da busassun ganyayyaki.
Kina da zuciya mai kyau Khadeeja, dai-dai ne mutanen da zasu tsinci mutum a cikin mugun hali kamar yadda kika tsinceni su taimaka mai.
Ke kyakkyawa ce Khadeeja, a zuci da fuska da dukkan halayyarki.
Na gode kwarai"
Zuwa wannan lokacin baisan hawaye ne yake zuba a idanunshi ba saida tayi magana tana tura baki.
"Nikam lokacin da na karanta tarihinka naga irin hukuncin da is dauka akan Ado na zaci kai Namijin duniya ne, amma a yanzu kam ina kokwanto? Anya wancan Kamal din jarumi mai dakakken zuciya shine wannan? Ni wannan Kamal din wani ragon maza mai saurin kuka da raunin zuciya nake gani a gaba na, ina wancan Kamal din ya shiga ne🤨?"
Ta karasa fadin haka tana daga mishi girarta daya cikin wani irin salo da ban sha'awa.
Dariya ya kyalkyale da ita, sosai ta bashi dariya da maganganunta, cikin kankanin lokaci ya fara mantawa da damuwarsa, ya saki jiki sosai yana cin abinci tana bashi labarin lokacin da yake cikin loosing memory, ranar da ta 6uya a cikin motarsa ta bishi gidan da yake sauka a nan kaduna, wani gurin yayi murmushi wani gurin yayi dariya.
Lokacin da tace mishi daure ta yayi a jikin kujera ruwan sama yai mata dukan tsiya mamaki yake ta yi, har yana gaddamar shi ba shi ya daure ta ba, dukda ya manta da komai ta ya za'ai ya daure kyakkyawar yarinya kamar ta?
Suna wannan gaddamar Mummy ta shiga cikin dakin da sallama a bakinta, da murmushi take kallonsu, hira suke yi gwanin burgewa, kamar ba su da wata damuwa.
"Baby Iman kuzo ke da Kamal, ga mataimakin Kwamishina ya zo ganinmu"
Dukda sunyi masa bayanin zuwansa tun safe saida yaji gabansa ya fadi, haka nan dai ya fuske ya bi bayan Khadeeja zuwa babban falo dan ganawa da Abdul'ahad.
******
A karo na tara ya sake bankawa karan sigarin wuta ya d'aga zai kai bakinshi, idanunshi jajur.
Da sauri Khalid ya rike hannun da hannun damarsa, sannan ya zare karan sigarin da hannun hagu yayi hurgi da ita a kasa, kafarshi yasa ya mutsuttsuke ta a kasa.
Ranshi a 6ace yake kallon yayan nasa, daure fuska yayi tamau kafin ya fara magana cikin 6acin rai.
"Wai Kai Yaya Faruk me yasa wani lokacin baka zurfafa tunani kafin ka aikata abu ne?
So kake ka kashe kanka saboda Honourable yaki biya min kudin jarabawa?
Ko kuwa zaka kashe kanka saboda kayi alkawarin rabuwa da Honourable Ghali ne...?
Me yasa bazaka yiwa kanka fada ka zama mutumin arziki ko iyayenmu da suka rasu zasu kasance masu alfahari damu bane?"
Kallonshi yake yi galala yana tunani a zuciyarsa, Khalid kaninsa har ya fishi hankali da tunanin abinda ya kamata?
Shikam daman ba komai yasa ya fara jagaliyar siyasa ba sai don ya samu abinda zasu rufawa kansu asiri shi da kaninsa, amma a tsawon lokacin da ya 6ata gurin jagaliyar bai k'aru da komai ba sai gwanancewa a cikin harkar daba da shaye-shaye.
Abubuwa da dama sun faru da ya kamata ace ya hankalta yasan Honourable Ghali ba kaunarsu yake yi ba, zasu yi mishi aiki da karfinsu da jikinsu Amma bai ta6a daukan kudi masu kauri ya basu ba, iya kar sallamar bata wuce 5000 ko 10000, duk yawansu kuwa basa wuce wannan kudin a gurinsa.
Sai kyautar kayan maye da kusan ko wane lokaci cikin yi musu yake, sai kuma kyautar makaman da zasu ringa fita fada su kashe ko a kashe su.
Ko abinda ya faru da Kb ya ishe su babban ishara idan suna da hankali.
Shi kam in Allah ya yarda bazai sake harkar jagaliyar siyasa ba in anyi duniya dan fiyayyen halitta SAW.
"Kayi hakuri Khaleed, na gaza gurin rikon ka da daukar nauyinka kamar yadda mahaifiyarmu ta barmin amana, amma in Allah ya yarda..."
Da sauri Khalid yasa hannu ya rufe bakin Figo, murmushi ne fal a fuskarsa.
"Karka damu Yaya Faruk, ni daman a kullum addu'ata da fata na, muradi na shine ka bar taraiya da Honourable, na dad'e ina nusassheka wannan mutumin Sam baya nufinku da alkhairi.
Idan da gaske ya damu da al'amarinku me yasa bazai kirkiri wani abu dan cigaban rayuwarku ba?
Bai dauke ku da darajar komai ba face na karnukan farautarsa, baya nemanku sai idan bukatarsa ta taso, yaranshi suna can suna karatu a makarantu masu tsada ku kuwa al'amarin karatunku Sam bashi a gabanshi.
Dan Allah kayi k'ok'arin fita daga hanyarsa kamar yanda kayi alkawari, idan kayi hakan ka gama min komai wlh."
Saboda farin ciki rungume kanin nasa yayi yana hawaye, a zuciyarsa yake jin lallai lokaci yayi da ya kamata ya zama sabon mutum mai cike da nagartattun halaye ababen koyi ga al'umma.
Abinda ya fara yi a yinin ranar shine zuwa shagon aski aka aske mishi wata dugujajjajiyar suma da tafi wata tara rabon da taga aski, lallai ya kara yarda a cikin duk wani abu da Allah da Manzon sa SAW suka umarce mu muyi akwai rahama a cikinta, askin da yayi kawai sai yake jin kamar ya sauke wani nauyi ne a kansa, daddad'ar iska ce take hura shi ta ko ina.
Ya shiga kasuwa ya sayo jallabiya kala uku da 'yan ragowar kudaden hannunsa, a yinin ranar gaba daya salloli biyar a cikin jam'i yayi su, ga shi ga al'ummar Annabi, sai yake jin wani sanyi na kwaranya a zuciyarsa.
Allah yasa a d'ore Faruk inkiya Figo😹
*****
Hannayensa duk biyu tallabe suke da kumatunsa yana sauraran wani sabon labari mai cike da tsananin al'ajabi da Dr. Abida take bashi.
"Abdul, ina so ka saurari labarin da zan baka da kunnen basira, a shekaruna da irin tarihin aikina da ka sani kasan nafi karfin inyi maka karya.
Kuma a tsawon shekaru goma da nayi a cikin garin kaduna Wallahi ban ta6a ba wani wannan labarin ba, wani babban sirri ne a cikin rayuwata da ta 'ya'yana.
Kamar yadda ka sani sunana Abida, wannan kuma Amatullahi da ita da wannan"
Ta mika masa hoton marigayi Kamal ya gani.
"Yaran Yayata ce wacce Allah yayi mata rasuwa shekaru goma sha biyu da suka wuce.
Mu haifaffun jihar Bauchi ne, a wani kauye, a Kauyen ma wata ruga ce ta fulani.
Mahaifanmu mu biyu kawai suka haifa, Yayata Harira Mahaifiyar su Amatu sai kuma ni Abida.
Iyayenmu ko a cikin fulani suna da wayewa, Dan kuwa Sun sakamu a makarantar islamiya da boko.
Yayata Harira tana gama Secondry school aka daura mata aure da Tijjani, kad'o ne, amma iyayenmu suka daure zuciyarsu suka aura mata shi dukda sam bai kwanta musu a rai ba.
Iyayen Tijjani masu arziki ne da suke rayuwa a cikin gari, Dan haka Yata Harira tana cikin birni ne da zama ita da Maigidan ta.
Watanni goma cif da auren su ta haifi Kamaluddeen, munyi murna sosai, a wannan lokacin sai mahaifanmu suka watsar da duk wani k'i da suke yiwa Tijjani suka rungume shi a matsayin surukinsu, tunda har ga zuria an fara samu a tsakani.
Watanni uku da haihuwar Kamal aka samu cikin Amatullahi, hankalin Yaya Harira ya tashi sosai, tayi kuka kamar ranta zai fita saboda wannan kazamin gwarnen da tayi.
A lokacin ne kuma mijinta Alhaji Tijjani ya fada harkar siyasa gadan-gadan.
A takaice dai tunda Allah ya nufa Yaya Harira ta haifi Amatullahi al'amarin rayuwarta ya fara canzawa, wani irin rama take yi a kullum kamar wacce ake diba Ana miya da ita.
Bani mantawa wani ziyara da ta kawo mana a lokacin har an saka ranar aure na da Habibu dan gidan kanin baffanmu.
"Abida?"
Ta kira sunana fuskarta na baiyana matsanancin damuwa, a lokacin mun ke6e ne a can bayan gida inda mahaifanmu baza su ji hirar da muke yi ba.
"Na'am Adda"
Na amsa a nutse ina karantar yanayinta.
"Wallahi Abida ina cikin wani hali, kuma ni bansan takaimaimai abinda yake damuna ba.
Tunda na haifi Amatullahi nake fama da wasu mugayen mafarkai masu tsananin ban tsoro.
Nakan ganni a cikin tsakiyar wasu halittu masu tsananin ban tsoro, sai inga wata mummunar tsohuwa tazo tana zuk'ar nono na, kuma abinda yake kara tayar min da hankali shine madadin inga tana zuko farin madarar nono sai inga tana zuk'o jini..."
"Jini kuma Adda Harira?"
Na fadi hakan murya ta na rawa, fuskata na baiyana tsananin tashin hankali.
Da sauri ta rufe min baki alamun inyi shiru kar su Inna suji, tana hawaye ta ci gaba da cewa
"Eh Jini Abida, kuma abinda yake bani tsoro shine na kasa tattauna wannan maganar da kowa, ko Abban yaro (Kamaluddeen. Tana ce mishi yaro ne saboda alkunyar dan fari) ban fad'a masa ba.
A duk lokacin da nayi yunkurin sanar dashi sai inji kamar an kulle min baki, Shima kuma saboda siyasarsu da ta dauki zafi bai ta6a matsa min da tambayar me yake damuna ba.
Na fada miki wannan maganar ba dan komai bane sai dan ki taya ni addu'a, amma dan Allah karki fadawa Inna da Baffa, nasan hankalinsu ba karamin tashi zaiyi ba idan suka ji wannan labarin"
A wannan ziyarar haka tayi shi cikin damuwa, dukda kunya irinta Innarmu ina jin lokacin da yake tuhumarta me yake damunta.
Murmushi kawai tayi ta amsa da cewar Amatullahi ce take damunta da fitinar tsotso.
Tun daga wannan ziyarar da ta kawo mana saida tayi wata goma sha d'aya bata sake ziyartarmu ba, mu kuma kamar wad'anda aka yiwa asiri ko a waya bama nemanta.
Wata rana kwatsam sai ga Alhaji Tijjani da kukanshi wai Allah ya yiwa Adda Harira rasuwa kwanaki uku da suka wuce, da kanin Baffanmu ya nemi bayanin me yasa ba'a sanar dasu tun ranar rasuwar ba sake fashewa da kuka yayi yace ai satinsu uku basu a kasar, sun tafi aikin Hajj a can ne ta rasu.
Sai kuma aka koma murnar ta rasu a kasar fiyayyen halitta SAW da addu'ar Allah ya gafarta mata.
A wannan lokacin ne ya kawo su Kamal suka yi mana sati biyu, dan har aka yi bikina suna gidanmu.
Kwana uku tsakani Alhaji Tijjani ya dawo da zancen wai a bashi aure na dan in rike yaran Adda Harira.
Koda ya samu labarin aure na hankalin sa ba karamin tashi yayi ba, sambatu kawai yake yi kamar ma ya fita a haiyacinsa.
Da yaga sun fara masa kallo mai kama da dora ayar tambaya ya kwashi yaransa yai gaba.
Watanni uku da aure na Allah ya dauki ran Maigidana Yaya Habibu ba tare da yayi jinyar komai ba, mun shiga tashin hankali ba kadan ba, saboda a lokacin ina dauke da karamin cikin Khadeeja.
Da dad'i babu dadi na reni cikinta har na haifeta, ranar da ta cika wata biyu da haihuwa Alh Tijjani ya sake zuwa da zancen neman aure na a karo na biyu.
A wannan lokacin kamar ya rufe mana baki, dan bai bar kauyenmu ba sai da ni a matsayin matarsa, ba tare da wani ja'inja ba aka daura aure na dashi.
A zama na da Alhaji Tijjani naga ga ta da tarairaya ba kadan ba, na hada yarana duk su ukun na rungume ina basu kyakkyawar kulawa.
Shima ko da wasa bai ta6a banbanta Khadeeja da yaransa su Kamal ba.
A gidansa na zana jarabbawar jamb, na samu sakamako mai matukar kyau dan haka ya nema min University mai kyau na fara karatun likita.
A gidansa na samu shaidar zama cikakkiyar likita. Idan na tuna irin wadannan alkhairin na Tijjani a gare ni ina yawaita yi masa addu'a da fatan alkhairi.
Ban fara dawowa daga rakiyarsa ba sai wata rana da na ji shi yana wasu maganganu a waya da suka saka min tsananin tsoronsa a zuciya ta.
"Wai kana nufin d'ana Kamaluddeen? Hahaha to me zai hana Alhaji Musa? Ai tunda na iya sadaukar da uwarsa Harira na hakura to Shima bazan gagara sadaukar da shi ba..."
Ban tsaya jin karshen maganganun ba nayi saurin to she bakina da dankwalin kaina saboda wani kakkarfar kuka da ya taho min, a hankali kuma cikin sand'a na juya zuwa 6angaren mu.
Tun daga wannan lokacin na tsangwami kaina, abinda ban saba ba ada na tsiro dashi wato dagewa da tsananin addu'a.
Rokon Allah nake yi ba dare ba rana akan ya kare ni da yara na daga sharrin Alhaji Tijjani.
Kwana hudu tsakani Allah ya dauki rayuwar Kamal ba tare da yayi jinyar ko ciwon kai ba, dukda nasan idan lokaci yayi da ciwo ko babu ciwo Allah zai dauki ran mutum amma a wannan lokacin na sakawa mutuwarsa ayar tambaya.
Dalili na farko kuwa shine wayar da naji Alhaji yana yi, dalili na biyu kuma shine:
Karfe tara na dare Kamal ya rasu, a wannan daren Limamin unguwarmu yazo sukai mishi wanka, suka hada shi tsap!
Amma saboda dare kaga dole zaiyi kwanan keSo, a wannan daren Alhaji ya dage zai kwana da gawarsa.
Haka kawai naji zuciya ta bata gamsu dashi ba, can cikin dare su Amatu sun gama kuka sunyi barci na tashi sadaf-sadaf naje dakin Kamal din na leka ta window a hankali...
Abinda na gani yayi mugun daga min hankali..."
Fashewa tayi da kuka mai tsananin karfi su Amatullahi suna taya ta.
Dan wannan labarin sabo ne a gare su yau suka fara ji.
Basu ta6a tsammanin miyagun laifukan Alh Tijjani ya kai haka ba.
Tsawon lokaci tana kuka kafin ta ci gaba da cewa.
"Alhaji na gani yana yanke al'aurar Kamal babu tsoro ko kadan a tattare dashi.
Washe gari da asubah ko da naje dakin ya maida gawar ya nad'e tsaf kamar yanda Liman ya barshi.
A daddafe na Bari akai bakwai da rasuwar Kamal, na hada duk wasu muhimman kadarori da na mallaka tare da Alhaji da takardun makaranta na na dauki Ama da Khadeeja kamar zamu unguwa na gudu dasu, ko kusa banyi tunanin zuwa rugarmu ba dan nasan idan zan dafa kur'ani baza su ta6a yarda dani ba.
Saboda dai-dai cikin danginmu wanda Alhaji bai kai makka ba, iyayena kuwa sunje yafi sau biyar.
Shiyasa basu da abin yabo sama da Alhaji Tijjani.
Abinda ban sani ba ashe talala Alhaji Tijjani yai min, duk wani taku nawa yana sane dashi, ashe yasa su Pele su bi bayanmu su kashe mu.
Lokacin da na lura ana binmu tuki nake cikin fita haiyaci ina k'ok'arin tsere musu, tun ina bin cikin gari har na yanki daji da mota ta, basu gaza ba kuwa gurin bin baya na da matsiyacin gudu suna k'ok'arin shan kaina da motarsu.
Wani gida da na hango can nesa dani yasa na kara taka wutar motar zuwa daf da gidan, a saba'in naja hannun yaran muka afka cikin gidan kafin su cim min, dama jaka ta yana makale a kafad'a ta.
A wannan gidan mafaraucin tsoho da yaronsa da matarsa d'aya saida muka shekara d'aya cur.
Ashe gidan yana da kafi irin wanda mutanen da suke yiwa gidaje ko kauyukansu, duk wanda ya nufi gidan in dai da mugun nufi a ransa to katon rafi kawai zai gani.
Su Pele ma abinda suka gani kenan, dan haka suka kona motar da na fita da ita suka je wa Alhaji da labarin sun kona mu kurmus a cikin motar.
Saboda tsoron kar iyayena su tuhumeshi game da mu Ya tura 'yan daba suka cinnawa gaba daya Kauyen wuta.
Daidai mutanen da suka sha da rayuwarsu.
Wannan mafaraucin shine ya taimake ni sosai, kuma yace lallai in taho nan Kaduna, anan ne kawai zan dad'e cikin kwanciyar hankali ba tare da barazanar Alhaji Tijjani ba.
Ya kuma yi min kwakkwaran gargadi kar in kuskura in koma Bauchi anan kusa matukar Alhaji Tijjani yana raye.
To ka ji cikakken tarihin rayuwa ta da ta yara na, a yanzu kuwa Alhaji Tijjani ba kowa bane face Gwamnan jihar Bauchi.
Babban dalilin da yasa muka nemoka shine a yanzu Alhaji Tijjani ya gano inda muke, kuma har ya turo yaronsa Pele da wasu mutane su kashe mu.
Ganin wannan Kamal din da suka yi Sun zaci fatalwar wancan marigayi Kamal dinne yasa suka tsorata suka gudu, amma nasan duk daren dadewa zasu dawo kashe mu.
Shi kuwa wannan Kamal din da kuka sani a matsayin Usher...."
Khadeeja ce ta bashi labarin duk yadda akai ta tsinci Kamal, ta nuna masa hotunan Kamal din a wancan lokacin.
Cikin kankanin lokaci suka wayar mishi da kai akan duk abinda ya shige mishi duhu.
*BARA A KUFAI*
*31)*
Duk da fad'i da girman tsakar gidan sunan ya cika dank'am da mata.
Wasu suna tsaye a gefe zagaye da filin tsakar gidan inda DJ Abdul ke baje kolinsa ta hanyar sakar musu zafafan wakoki su kuma mata suna cashewa da dukkanin karfi da gwanintarsu.
Me jego tana tsakiyar filin rawar tana girgiza kwankwaso kamar zata karye saboda tsabar lankwasa, indai kayi wa Hauwa'u kyakkyawar sani to ka santa da shegen son bidi'a musamman irin ta rawa da karya kugu.
Tsabar son rawa irin nata kina shiga hayin rigasa kika gangara karshen kwanta, da kin tambayi gidan Hauwa'u 'Yar mazari za'a kaiki.
Bafa kudi ta tara ba yasa tayi suna a unguwar, a'a tsabar son rawa irin nata ne.
"Ke ni fa Wallahi idan naji tashin kid'a inda kika san ana kada min gangi a tsakar kaina haka nake ji.
Ai mawak'a sunyi a rayuwa"
Lokuta da dama haka take fada ma kawayenta.
Shiyasa biki ko ba'a gaiyace ta ba indai taji za'a dauko Dj to tabbas ko satar fita ne zata yi taje ta girgiza kwankwaso ta koma gida kafin mijinta ya dawo gidan.
Mijinta Inusa yana matukar bakin ciki da takaicin wannan mummunar dabi'ar tata, yayi nasiha, yayi fada, yayi zagi, wata rana har Hutu ya bata ta tafi gidansu dakyar ya hakura aka dawo da ita amma taki barin rawar nan, sai tayi kamar zata rage sai ta sake komawa ruwa tsundum.
Shekararsu uku da aure bata ta6a samun haihuwa ba sai wannan lokacin, tunda Allah ya sauketa lafiya ta sami d'a namiji babu abinda take lissafi sai ranar suna yazo ta bada dubu goma a dauko mata DJ Abdul.
Kwalayen cingam hudu ta siya ta ba babbar kawarta Hadiza, sannan tace layi-layi gida-gida na karshen kwalta a tabbatar an aika cingam a sanar da cewa
"Hauwa'u 'Yar mazari ta haihu ranar alhamis, DJ Abdul zai baje kolinsa daga karfe biyun rana zuwa karfe goma na dare"
Mijinta Inusa da yayi yunkurin hanata ta hanyar nuna mata mugun 6arin ransa haukace masa tayi, har wasu aljanun karya ta tayar mishi hauka-hauka.
Akan cewa dole ya barsu suyi rawa na kece raini a sunan d'an god'iyarsu.
Matan unguwa kuwa sunyi mata kara kwarai kamar yadda take musu, tun kafin karfe biyu gidan ya cika dank'am da mata babu masaka tsinke.
DJ Abdul kuwa ya kure speakers yana saka musu dad'ad'an wakoki kala-kala, daga Hausa zuwa turanci.
Mai jego tana tsakar fili tana kwaso rawar *Shaku-shaku*, idanunta a rufe, bata ji bata gani shaidan ya rufe mata ido da gangarsa.
Alkawari ta dauka minti d'aya bazatai missing ya wuce ba tare da tana cikin filin rawar nan ba.
A can cikin d'akin mai jegon kuwa wasu mata ne su uku, d'aya tana kwance tana gyangyadi, dayar kuwa lomar abinci take ta kaiwa cikinta, hankalinta yana kan wakokin nan, duk ta kosa ta gama ta fita gurin rawar tayi kallo.
Dayar matar kuwa wacce ta saka tsaleliyar atamfar Holland, ta saka zumbulelen hijabi yadin Kautsar, ya sauka har kasa da gwiwoyinta, wani abun k'arin armashi a shigarta tana sanye da safa a kafafunta, ga kuma nikaf mai kyau ta daura a fuskarta, a hannunta tafkekeyir waya ce take dannawa.
Lokaci bayan lokaci tana daga ido ta kalli jaririn da yake barci akan gadon jarirai hankalin sa kwance, alamun babu abinda yake damunsa.
Wacce take cin abinci tana daf da fita jaririn ya fara tsala ihu kamar an tsunguleshi, bisa dukkan alamu firgita yayi.
"Kai Yaro sai hakuri, uwarka tana can filin rawa tana rak'ashewa, kinga baiwar Allah d'an jijjigashi barin je in kira Hauwa'un"
Ta fad'a bayan ta d'auko jaririn daga cikin gadonsa ta mi'kawa matar nan mai nikafi, ta fice daga d'akin cikin sauri.
Tana kar6arshi ta fara jijjigashi ya'ki yin shiru yin shiru, kamar ma sake tunzurashi take yi, da alamun nono kawai yake bukata.
Ta kalli matar da take barci tace
"Kinga 'kila gajiya da kwanciyar yayi, ga zafi cikin d'akin, mahaifiyarsa kuma bata shigo ba.
Barin goya shi mu leka waje musha iska.."
Kai kawai wacce take barcin ta iya daga mata, dan sosai barcin ya fara cin karfinta.
Farin showel din goyon yaron ta dauka ta goya shi ram a bayanta, tana ci gaba da jijjigashi, a hankali kukansa ke raguwa har yayi shiru gaba daya.
Ta maida hijabinta tsaf ta rufe kamar ba tayi goyo ba, ta fita daga cikin d'akin zuwa tsakar gidan.
Waige-waige ta fara yi ko zata hangi matar da tace mata bari ta kira mai jegon sai ta hangeta can cikin filin rawa tana rawar *A k'ame k'am*, na Ado Isa Gwanja.
Gyada kai tayi da murmushin jin dad'i a fuskarta, da mugun sauri ta bi cikin turmutsutsun mata ta fice daga gidan bayanta goye da jaririn Hauwa'u 'Yar mazari.
Sun rak'ashe, sun cashe, sun gwangwaje, sun jijjiga jiki yanda ya kamata.
Basu ankara da sace jaririn da aka yi ba sai karfe shida na yamma, a lokacin wata babbar Yar Hauwa'u dakyar ta janyota daga cikin filin rawar da cewa tazo tayi wankan yamma kafin a kira sallar magriba.
Har ta tu6e zata shiga bayi saita dawo ta kalli gadon da aka kwantar da jaririn.
"Aunty Hassana ina Mus'ab din in bashi yasha kafin ruwan yasha iska?"
"Mus'ab kuma? Bashi akan gadon ki?"
Waigawa kan gadon sukai basu ga komai ba sai wayam, wacce take barci dazu ma har ta farka ta fita kallon masu rawa.
Kallon-kallo sukai tsakanin ya da kanwar kirjinsu yana wani irin bugawa, da sauri suka fita tsakar gidan Hauwa'u daga ita sai daurin kirji.
Gurin su DJ Abdul Aunty Hassana ta nufa tace su dakata da saka waka ana neman jariri...
Abu fa kamar wasa k'aramar magana tana neman zama babba, an nemi jariri sama ko kasa a cikin cincirindon matan nan an rasa, lokaci daya mai jego Hauwa'u 'Yar mazari ta daga hannu biyu ta dora akai ta yanka wani mahaukacin ihu.
Matan da suka kasance dangin mai jego da dangin miji sai kuka... lokaci daya gidan suna ya koma gidan jimami da koke-koke.
DJ da yaransa tuni sun hada kayansu sun cikawa wandonsu iska.
Mata daya-bayan daya aka fara sa6ewa, ganin za'a watse gaba daya Aunty Hassana ta kulle gidan ta kira kaninta a waya tace yaje ya dauko 'yan sanda an sace jaririn Hauwa.
Kafin kace kwabo gida 'yan sanda sun iso, an tattara mata gaba daya ana bincike, idan ya gagara sai a kwashesu zuwa police station.
Ganin har an kusa gama binciken mata ba jinjiri ba alamarsa yasa mai jego ta sake yanka ihu mai tsananin karfi ta zube a kasa aljannun gaske sun zo, babu abinda take yi sai gurnani da buge-buge suna ihun a fito musu da d'an god'iyarsu.
A daidai wannan lokacin Inusa da wasu daga cikin abokansa biyu suka iso afujajan, labarin abinda ya faru har ya ishe su shiyasa suka taho dan tabbatar da gaskiyar labarin.
Yadda suka tarar da gidan a tsaitsaye ga 'yan sanda yasa Inusa ya zube kasa da6as yayi zaman 'yan bori, hannunsa biyu tallabe da kansa da yake jin kamar zai tsage, dakyar yayi karfin halin sallamar 'yan Sandan nan.
Matan da suka rage ma yace duk su 6ace mai da gani, ai a guje suka ringa ficewa suna godiya ga Allah da addu'ar Allah ya baiyana jariri.
Gida ya rage daga angon karni sai mai jego da 'yan uwansu na jiki-jiki.
Har wannan lokacin Hauwa tana kwance a kasa tana kuka mai kama da na gyare.
"Ku shigar da ita cikin daki akwai hayakin da zan yi mata ta dawo cikin haiyacinta"
Ya fada a hankali yana kallon Aunty Hassana.
Suna shigar da ita yace su fita ya maida kofar dakin ya rufe ya saka sakata.
Belt din wandunanshi guda uku ya hada guri daya ya fara laftarta kamar ya samu jaka, tun aljanu suna shanye dukan da nuna alamun ko a jikinsu har suka gudu Mai jego ta dawo daidai ta fara rusa ihu tana neman matsera.
"Wayyoh... Dan girman Allah Inusa kayi hakuri... Wayyo baya na... Inusa zaka kashe ni... Wayyo jama'a ku taimake ni zai kashe ni..."
Duk yanda 'yan uwan suke dukan kofar da bashi hakuri bai sauraresu ba saida yayi mata jina-jina ya farfasa mata jiki.
Takarda da biro ya dauko jikinsa na rawa ya rubuta mata saki uku ya jefa mata, ya bude kofar ya fice daga gidan gaba daya yana hawaye.
*****
Shiru yayi tsawon lokaci yana mamaki da al'ajabin wannan cukurkud'ad'd'an labari mai kama da almara.
Ba wai bai yarda da labarin bane a'a, tsoron Allah ne ya sake kama shi.
Wannan wane irin zamani ne muke ciki da akan neman mulki na duniya wanda ba matabbata ba mutum zai sadaukar da matarshi da d'anshi na cikinshi?
Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un. Wannan masifa da me tayi kama?
K'ok'arin katse tunanin shi yayi ganin agogon falon ya buga karfe goma na dare.
"Amma Dr. Kinsan sake kwananku a gidannan babban hadari ne ko?"
"Eh na sani Abdul, daman ba anan zamu kwana ba, zamu tafi hotel..."
"No ki bar batun Hotel dinnan.
Khadeeja ku hado kayan da zaku bukata mu tafi gidana ku kwana a can zuwa gobe muga yadda za'ayi"
Ya fada yana kallon Khadeeja wacce da sauri suka nufi ciki ita da Amatu fuskarsu na baiyana farinciki.
Ita kam Khadeeja tafi kowa jin dad'in hakan, ko ba komai dai gidan babbar aminiyarta zata koma.
"Anya ayi haka kuwa? Kar mu takurawa iyalanka, da is bari mun tafi hotel din"
Dr. Abida ta fadi haka tana jinjina kwana gidan Abdul'ahad a zuciyarta.
Murmushi yayi yana kallon Kamal da tun shigowarsa baice komai ba, tun dazu da yake kallonsa babu abinda yake karantowa a fuskarsa sai tsananin damuwa.
"Babu wani takura Dr. Ina so ki fahimci wani abu guda, yanzu duk inda tashin hankali yakai Alh Tijjani yana cikinshi, kuma nasan zaiyi duk mai yiwuwa dan ganin bayanku gaba daya.
Dan haka guri mai tsananin tsaro kuke bukata inda yaranshi bazasu iya kai muku hari ba.
Da yaddar Allah karshensu ne yazo gaba dayansu"
"Allah yasa haka"
"Ameen ya Allah"
"Malam Kamaluddeen. Ba magana? Kasan fa nemanka nake yi ido rufe in mik'awa hukuma..."
Ya fadi haka bayan ya tamke fuskarsa babu alamun wasa ko kadan, kallon shi yake yi yana karantar yanayin da yake ciki.
Kamal kuwa tsabar tsoro har ya fara zubda hawaye, yana goge wasu sabbi suna sake gangarowa kamar wani mace, dama yasan dole a karshe sai ya fada hannun 'yan sanda tunda a idanun duniya shi babban d'an ta'Adda ne.
Muryarsa cike da rauni ya fara magana yana shasshekar kuka
"Yalla6ai... kamar yadda Khadeejah ta fada maka Wallahi na aikata komai ne ba a cikin haiyacina ba.
Ni Wallahi a rayuwata ma ban ta6a fadawa hannun 'yan sanda ba sai sau daya da Chairman Sumaila yayi min sharri suka kulle ni har na kwanaki uku.
Amma ni mutumin kirki ne wanda ba ruwanshi da shiga sabgogin mutane, dan Allah kuyi min sassauci"
Murmushi Abdul yake yi yana kallon yanda yake ta zubo bayani a rud'e, kafad'unshi ya kama ya mikar dashi tsaye a daidai lokacin da su Khadeeja suka fito janye da madaidaitan jakunkuna.
"Kai baka bukatar komai ne Kamal? Gidannan zaku bari na wasu kwanaki"
Abdul ya fada masa haka muryarsa a tausashe.
Jiki a sanyaye yabi hanyar zuwa dakin da ya tsinci kanshi a ciki tun bayan farfad'owarshi.
Ajiye jakar hannunta tayi da sauri tabi bayanshi, yana daf da shiga dakin ta kira sunan shi a tausashe
"Ya Kamalll..."
Juyowa yayi yana kallonta, ita kuwa ta haskeshi da tattausan murmushi, dukda baijin dad'in zuciyarsa sam haka ya daure ya mayar mata da martanin murmushinta.
Jiranta yayi ta karaso suka shiga cikin dakin gaba d'aya.
Tsuru yayi a tsakiyar dakin yana tunanin wai shi me ma ya kamata ya dauka?
"Baby Iman me da me ya kamata in dauka ne?"
Ya tambaye ta a marairaice.
Shiru tayi tana kallon dakin hannayenta biyu rike da kugunta tana tunani.
"Eh toh... ina ga mu dauki gado da katifa da filo saboda gudun kwanciyar kasa🤨🤪😉"
Dariya ya kwashe da ita yana kallon yanda ta fuske tayi maganar, itama dariyar tayi sannan ta nufi ma'ajiyar kayan shi ta nufa ta janyo wata karamar jaka tana zuba duk abinda tasan zai iya bukata a cikin kwanaki uku.
*****
"Aikinki yayi kyau Barira.."
Ya fadi hakan yana dariya bayan ya kar6i jaririn da yake goye a bayanta.
Yana ta barci da taimakon wani abu mai kama da turare da take ta fesa mishi, tunda ta samu nasarar daukarshi da ficewa daga unguwarsu bata samu wata matsala da shi ba.
Da ya fara kuka sai ta kwance shi ta bashi ruwa sannan ta fesa mishi abin ta sake maida shi bayanta.
Fuskewa take a cikin keke napep kamar yaron ta na cikinta har ta isa gida.
Saboda irin harkokin ta dama dan karamin gida ta kama haya ita kadai tana gudanar da harkokinta ba tare da sa idon mutane ba.
Bata nufi gurin Honourable Ghali ba sai karfe tara na dare kamar yanda suka saba ita dashi idan irin wannan aikin ya taso.
Ke6a66iyar gidan gonarsa ta tarar dashi yana hutawa.
"Amma Ranka ya dad'e wannan karon ya kamata ka k'ara yawan sallamar da kake min, nasha wahala sosai kafin in samu nasarar aikin nan"
Ta fada da murmushi a fuskarta, tana sake gyara zaman nikaf din da yake daure a fuskarta.
"Karki damu Barira, za'a kara miki sallama. Bari a dauko miki dari biyu da hamsin madadin dari biyu da aka saba biyanki"
"Ka taimaka ka cike dari ukun dai Ranka ya dad'e"
Dariya yayi ya dauko mata dubu dari ukun kamar yadda ta nema ya damka mata.
Ya amshi jariri ita kuma ta karbi kudi suka rabu zuciyar kowannensu cike da farin ciki.
*****
Karfe biyu na dare ne a daidai lokacin agogon lungu da sako na duk fadin 9ja.
"Tijjahneeehh.."
Dodanniya Tsumburbura ta kira sunan shi da mugun karfi kuma a tsawace, da wani mummunar murya mare dad'in sauraro.
Kiran sunan shi ta ci gaba da yi har sau biyar cikin tsawa dakin yana amsawa kamar ta kafa lasifika a bakinta.
Sauran mutanen da suke cikin d'akin sanye da jajayen dogayen riguna sun d'aura bak'ak'en k'yalle a kawunansu sauke fuskokinsu k'asa sukai kirjinsu na bugun tara-tara.
Daga yanda Tsumburbura take kwala kiran sunan Tijjani shi yake baiyana musu tsananin 6acin ran da take ciki.
Alhaji Tijjani yana gwafe a gabanta yayi sujuda da gwiwoyinsa duk biyu
*(Subhanallahi)*
"Al'amarin rayuwarka yana daf da sauyawa matukar ka bari iyalanka suka kara sati guda a raye Tijjahnee...
Zaka wulakanta... zaka tozarta a idanun duniya....
Zakai mutuwa mafi muni Tijjahnee....
Tafih... tafi... yau tsumburbura batai murna da ganinka ba Tijjahnee....
K'ok'on kawunan iyalanka su nake so insha jini dasu Tijjahnee....
Tafi ka aikata abinda muka umarce ka tun kafin mu juyo da bak'ar rayuwa ta fuskance ka Tijjahnee.... tafih... tafih..."
Sai kuma ta fara wasu sambatu wanda ko kad'an ba'a fahimtar me take cewa.
Minti biyu tsakani ta fashe da kuka da wata murya mare dad'i, can kuma saita fashe da wani mahaukacin dariya kamar an kunna ru6a66iyar radio.
Daga bisani kuma d'if, muryar ta dauke gaba d'aya.
6acewar da tayi shi ya tabbatar musu da yau 6acin ran Tijjani ya shafi kowa, matsalarshi kad'ai ta saurara.
Dan haka daya bayan daya suka ringa 6acewa daga dakin taron suna baiyana a cikin dakunan barcinsu.
Alhaji Tijjani kam tsananin 6acin rai da tashin hankali ya kasa d'agowa daga sujadar da yayi, saida amininsa Alhaji Musa ya d'aga shi sukai wani d'an girgiza take suka baiyana a cikin dakin barcin Alhaji Tijjani.
"Tijjani yanzu me kake ganin za'ayi? Kaji dai umarnin tsumburbura kar iyalinka su kara sati d'aya a raye...."
Hannu ya daga masa alamun ya saurara.
"A yanzu kaina a kulle yake Musa, zuwa gobe kazo muyi maganar"
Gyada kai yayi alamun ya fahimta, daga nan wata girgizar ya sake yi tsulum ya baiyana a d'akin barcin sa, matarsa ya kalla da take barci daidai akan gadon barcinsa kamar matacciya.
Da sauri ya shiga band'aki ya sauya kayan jikinsa ya kwanta a gefenta.
*****
Karfe uku da rabi na dare ya fita da motarsa hannunsa dauke da kwarya wanda ya kusa cika da jinin jaririn da aka sato mishi.
Tsakiyar hanya ya tsaida motar ya tu6e kayanshi gaba daya ya aje a cikin motar, ya fita yayi wanka a tsakiyar titi da jinin jaririn, idanunshi a rufe suke yana zagaye gurin yana zuba jinin a jikinsa har ya k'are...
*BARA A KUFAI*
Duk yadda yaso had'uwa da ita a daren kafin yayi barci hakan yaci tura.
Ta kulle kofarta gam da makulli kuma tabar key din a jikin kofar yanda bazai iya budewa da keyn hannunsa ba.
Kuma ta kwashe yaran ta daga dakin Yasmin ta kaisu dakinta, daga take-takenta ya gane daru ne fal a cikinta.
Daman yasan dole za'ayi hakan, ya lafiyar giwa balle kuma tayi hauka?
Dole ya tafi dakin Yasmin ya kwanta zuciyarsa cunkushe da damuwa, gaba daya yinin ranar yayi ta ne a jagule.
Washe gari da sassafe tun kafin ya fito ta shirya yaran ta tsaf cikin uniform din makarantarsu.
Ita ma Yasmin a ranar 'yan tsiyar suna kusa, dan haka ba tare da sanin Abdul ba ta sake garkame kofar da key bayan sallar asubah.
Ko da yaran suka kwankwasa kofar dan su gaida Daddy da Mummy kamar yadda suke kiran Yasmin, Aysha kuma Ummee.
Ganin ba'a bude ba yasa tace su zo su wuce driver yana jiransu karsu makara, zuciyoyinsu ba dadi saboda rashin ganin Daddy suka tafi makaranta.
Saboda rashin samun barcin dare da wuri ga tunane-tunane yasa bai farka ba sai bayan karfe tara, da sauri ya mike yana sake kallon agogon dakin.
Sallamar Yasmin yasa ya maida hankalinshi kanta yana harararta.
"Me yasa baki tashe ni ba kina ganin lokaci ya tafi, kuma kinsan nazo da baki gidan nan?"
Saida tai fari da idanunta ta fara magana da murmushi a fuskarta.
"In dai bakinka ne baka da matsala, na kai musu duk abinda nasan zasu bukata.
Kaima tun 8 na hada maka ruwan wanka, ganin ka gaji jiya baka kwanta da wuri ba shiyasa ban tashe ka ba"
Bai sake tankawa ba us shige ban dakinta, gudu-gudu yayi wanka ya shirya ya nufi dakin Aysha.
A bude yaga kofar amma bata ciki, wani takarda ya gani nannad'e a gefen kujera ya dauka ya warware kirjinsa na bugun uku uku, Allah yasa dai ba tafiyarta tayi ba.
" *Assalam alaikum, barka da asubah. Na kira wayarka a rufe, kuma na kwankwasa kofar dakin matarka baku bude min ba. Na tafi asibiti..*
Dafe goshinshi yayi zuciyarsa cike da takaici, yaushe wayoyinsa duk biyu suka mutu bai sani ba? Lallai ya gama kai Aysha bango.
Dakin ya koma ya kunna wayoyin, ganin da yayi duk biyun akwai caji kusan a cike yasa ya tabbatar aikin Yasmin ne.
"Me yasa kika kashe min waya?"
Yayi mata tambayar cikin tsawa bayan ya tsareta da idanunshi fuskarshi a tamke.
"Ka... ka.. kayi hakuri... naga ka gaji ne shiyasa..."
"Kuma shine zaki maida kofa ki datse bayan sallar asubah dan kar su Abee su shigo?"
Shiru tayi kanta a kasa, alamun rashin Gaskiya ya baiyana a fuskarta kuru-kuru.
"Kin kyauta"
Ya sake fada yana girgiza kai sannan yayi kwafa, makullin motarsa da wayoyinsa ya kwasa ya fice ba tare da ya kalli abincin karin da ta shirya mishi ba.
*****
Suna zaune akan kujera mazaunin mutum uku ita da Kamal, da alamun wani abu take nuna masa a wayarta dan ya matsa sosai yana kallon wayar tata, da mamaki a fuskarsa.
A hannunsa guda daya littafinnan ne da ya rubuta cikakken tarihinsa da tarihin abinda ya faru dashi, a dayan hannun kuma karamar wayarsa ce wacce take cikin jakar tun wancan lokacin, kokarin kumnata yake ta yi amma taki kawowa.
"Wannan wayar taka fa baza ta kawo ba indai baka jona a caji ba, ko ka jona kila ne ma ta dauka, waya fin shekaru biyar a kashe ba'a amfani da ita.
Ai tashinta sai tsananin sa'a"
Amatu ta fad'a tana sa6e da Khalifa a kafadunta, da alamun wanka tayi mishi dan yana ta kamshi.
Khadeeja ta mikawa shi Kamal yayi saurin kar6ar sa yana mishi wasa.
"Khadeeja ina Mummyn taku?"
Abdul ya fada bayan sun amsa sallamarsa.
"Ina kwana.... Sun wuce asibiti ita da Aysha tun 8"
Ta amsa bayan ta gaishe shi.
Kamal ma gaishe shi yayi a ladabce amma saiya mika mishi hannu sukai musabaha.
Ya amsa gaisuwar Amatu yana tsokanarta ya kwanan bakunta?
"Kamal ka zama cikin shiri, idan na dawo zamu yi magana"
Ya fadi haka a daidai lokacin da yake daf da ficewa daga falon.
Da yake gidansa wadataccen gida ne mai dauke da flat hud'u, matansa suna cikin biyu shi kuma yana cikin daya, dayan flat din an zuba mishi komai da ake bukata suna sauke bak'i a ciki.
A nan ya sauke su Dr. Abida.
Dakuna uku ne da falo da kicin, a cikin ko wane daki akwai bayi shiyasa basu takura ba.
Mummy ta dauki daya, Ama da Khadeeja daya, Kamal yai masauki a dayan dakin da yake daf da kofar falon.
Sun kwana cikin walwala Sam basu takura ba.
A karo na uku ta sake gwada jinin nata, yana nan dai kamar gwajin farko, jininta ya dan hau, kuma hakan ba abu ne da ake so ba duba da yanda cikinta ya shiga wata na bakwai.
"Aysha menene matsalar? Nayi mamaki da naga jininki ya hau, ko a cikin 'yan biyu jininki baiyi haka ba, akwai damuwa ne?"
Murmushi kawai tayi ta sake sadda kanta kasa, saida likitar ta matsa mata da tambaya sannan tace kanta ke ciwo, kuma jiya bata samu barci sosai ba.
"Shikenan, Barin kira Abdul in fada masa..."
"A'a Mummy Dan Allah karki fada masa..."
Ta fada fuskarta a shagwa6e kamar zatai kuka, a daidai lokacin us bude kofar Ofis din ya shiga da sallama a bakinsa.
"Dr. Dan Allah fada min, akwai matsala ne?"
Ya tambaye ta hankalinsa a tashe.
"Eh! Jininta ya hau, kuma hakan babban hatsari ne ga ita da abinda yake cikinta.
Tace min dai jiya tayi fama da ciwon kai, kuma bata samu barci sosai ba.
Idan zaku tafi zan bata wasu magunguna tasha saita kwanta tayi barci isasshe, zuwa dare zan sake gwada jinin nata"
Ta umarci Ayshan ta kwanta a wani madaidaicin gado dan tayi mata awo.
Komai lafiya Lau, dan har scanning tayi mata, ta rubuta magungunan taba Abdul yaje ya kar6a a gurin kar6ar magani.
Yana rike da hannunta suka fita daga Ofis din.
"Baby dan jira ni a nan in kar6o maganin"
Bata tanka ba sai kawai ta nemi kujera ta zauna a reception din, yana shigewa ciki ta tashi tai tafiyarta zuwa gida, daman da motarta taje asibitin.
Ko kafin ya isa gida har tayi wanka, tana sanye da doguwar riga mai kama da shimi ta shan iska, ya sauka mata har gwiwa, tana zaune da kofin tea a hannunta tana kur6a, ga kuma hisnul Muslim a dayan hannun tana dubawa.
Sanin girma da darajar da yake tattare da amsa sallama yasa ta amsa shi, ko kallonshi batai ba ta ci gaba da abinda take yi.
"Baby shine kika taho ki barni da fargabar inda kika shiga.."
Ya fadi haka yana k'ok'arin zama a gefenta.
Shiru tayi mishi kamar ba da ita yake magana ba.
"Matata bani hankalinki muyi magana pls"
"Ni kam banda lokaci"
Ta amsa kai tsaye tana k'ok'arin mikewa da kofin a hannunta.
Riko hannun yayi ya sake zaunar da ita a inda ta tashi.
"Aysha kiyi hakuri... bansan me ya shiga kaina ba a jiyannan har na farfad'a miki..."
"Abdul dan girman Allah ka kyaleni👏🏻👏🏻 Wallahi ko kadan bana so inji muryarka a kusa dani👏🏻 idan kuma zaka sake tunatar dani ni tsohuwar 'yar ta'adda ce bismillah"
Cikin fushi tayi maganar daga karshe kuma muryarta ya fara rawa alamun zata iya yin kuka ako wane lokaci.
Dan haka ta runtse idanunta tana k'ok'arin tausar zuciyarta, ko kadan baya so hawayen su zubo a gaban shi.
Shiru yayi yana sake jin babu dad'i a ransa, wai shine Aysha bata son jin muryarsa a kusa da ita? kamar bazai tanka ba sai kuma yace
"Ni dai ina sake baki hakuri dan Allah, Wallahi banyi niyyar in fada miki wata magana makamanciyar wannan ba, lokacin da kika tare ni da wannan maganar ina cikin mugun 6acin ran da na kwaso a Ofis ne, sai kuma shaidan yayi amfani da fushin da nake ciki ya sarrafa linzamin zuciyata"
Hannuwanta duk biyu tasa ta toshe kunnuwanta dasu, alamun da gaske bata son sauraren shi, kawai saida ya gama da ita ne zaizo yana wani bata hakuri?
A sanyaye ya aje mata ledar maganin a cinyoyinta ya kama hanyar ficewa daga d'akin.
Harara ta raka shi dashi, sannan ta daga murya yanda tasan zai jiyota tace
"Idan kaga dama kaje ka ba matar so labarin ni tsohuwar 'Yar ta'adda ce, mata tamin maganar banza taga yanda zan zubar mata da hakoran gama Wallahi... Ko giwa ta fad'i tafi karfin kiyashi su ja ta..."
Yanda taga ya dawo d'akin da mugun fusata a fuskarsa yasa tai shiru ta runtse idanunta gam, ta gama tsammanin marinta zaiyi tunda ta gama hakikancewa zuciyarta ya daina kaunarta.
Sa6anin abinda tayi tunani cak ya dauke ta ita da cikin nata kamar wata baby ya nufi cikin dakin da ita.
Ciccilla kafafunta ta fara yi tana masifar ya sauke ta, bai dire ta ba saida ya kaita tsakiyar kan gadon.
6alle ma6allin rigarsa ya fara yi yana kusantarta, lura da abinda yake shirin yi yasa ta fashe da kuka mai karfi tana yunkurin sauka daga kan gadon.
Janyota jikinsa yayi yai musu masauki akan gadon, har lokacin kuka take yi dan haka ya hade bakinsa guri daya yana mata wani zazzafar kiss, tun tana mutsu-mutsu da k'ok'arin kwace bakinta har tayi lakwas a kirjinsa, daman ya riga yasan lagonta.
Saida ta natsu sai hawaye take fitarwa kawai, bata San me yasa ba maganar yaki 6acewa daga kwakwalwarta.
A hankali yake shafa bayanta alamun rarrashi yana fada mata kalaman kwantar da hankali da bata hakuri cikin tausasan lafuzza akan laifin da yayi mata.
Tsawon lokaci suna a haka, tun tana hawaye har tayi shiru, daga baya ma wani daddad'an barci ne ya fara kwasarta a jikinsa.
Tun tana k'ok'arin hanashi daukarta har barcin yaci nasarar saceta gaba daya, bai daga ta ba saida ya tabbatar barcinta yayi nisa sannan ya gyara mata kwanciyarta ya daidaita sanyin A.c ya fice daga dakin.
Bai bi takan Yasmin ba dan sosai yaji haushin abinda tayi mishi da safe, dan haka ya koma bangaren su Kamal dan suyi magana kamar yanda yace.
******
"Nura wai ina Moses ya shiga ne? Kwana biyu Sam bana samunshi a waya, kayayyakin gurina duk sun kare.
Ko akwai wani abu a gurinka ne?"
Ta tambayeshi lokacin da ya mike titi sosai da motar, dan zuwa kaita makaranta.
Murmushi yayi ya cije gefen bakinsa ya saci kallonta ta madubi, tunda su ka fito daga gidan ya lura kamar ranta a 6ace yake, shiyasa ya rasa hanyar da zai mata tayin guzurin da ya taho dashi musanman domin ta.
Hannunsa ya laluba a aljihun wandonsa ya dauko kwalbar ya mika mata.
"Kinsan ba'a rasa nono a ruga... Moses tafiya yayi dan ni ma na kwana biyu rabona dashi, kiyi maneji da wannan zuwa anjima saiki bada kudi a kar6o miki wani"
Da murmushinta tayi masa godiya tana rike da kwalbar a hannunta, da ajiyewa zatai a cikin Jakarta sai ta fito daga lecture tasha a hostel dakin kawayenta, sai kuma ta tuna ko taje makaranta yanzu sai nan da awa biyu take da lectures.
Gidan ne kawai yayi mata zafi shiyasa ta gillawa mahaifiyarta karyar tana da darasi da safe ta shirya ta fice.
Dukda an dawo mata da wayarta kwanaki uku da suka wuce Sam bata cikin walwala, still dai ko ta kira wayar Usher lambarsa bata shiga, daman tana gwada kiransa a lokuta mabanbanta da lambobin kawayenta.
Kwanaki can da tsumin soyayyarsa ta taso mata wayar mahaifiyarta ta dauka ta kira shi amma taji a kashe.
Mummy kuma tana matukar saka mata ido a gidan shiyasa bata samun damar kur6ewa a dakinta kamar yadda ta saba a da, dole sai ta shiga makaranta tayi abinda take so a dakin kawayenta.
Bude kwalbar tayi ta fara kur6a Sannu Sannu tana danne danne a wayarta, kafin ta ankara ta shanye gaba daya.
Duk abinda take yi Nura yana kallonta ta madubi yana dariya a fili, yasan ta riga ta zama nama.
"Da...da... dariyar me kake...yi?"
Ta tambaye shi dakyar tana ta zabga hamma akai akai, ko kafin ya amsa mata ta 6ingire akan kujerar bayan motar tana barci.
Daga nan kai tsaye dakin abokansa Lado ya wuce da ita, zuciyarsa cike da farin ciki sai wake-wake yake yi.
"Shege Nura baka da kyau👍🏻👍🏻👍🏻"
Ya fadi hakan yana masa jinjina da babbar yatsarsa lokacin da ya ganshi ya shiga dakin sa6e da Fatima a kafadarsa kamar matacciya.
Akan yagulalliyar katifar da ta gama sud'ewa ya kwantar da ita.
Suka kwashe da dariya gaba dayansu, sannan suka tafa hannu zuciyarsu fal farin ciki.
"An fada maka ni na wasa ne? Inji gwari ya bada magani anci an mutu"
Yayi Karin maganar yana kara jinjinawa kansa.
Nan da nan ya fara k'ok'arin zame wandonsa, daman abinda yasa yai mata hade-Haden magungunan da suka fi karfin hankalinta kenan.
Tun a wancan lokacin da tayi mishi alkawarin kanta saida ya gama saka rai ashe yaudararsa tayi, shiyasa ya daina kar6ar komai na hannunta, kuma yasha alwashin duk daren dadewa saiya d'and'ana ta.
Tsawon lokaci yana abu d'aya kamar ya samu matarsa ta sunnah, yasha tsananin mamaki da yaji tabbas shine na farko da ya fara keta alfarmarta.
Hakan yasa jikinsa yayi dan sanyi, Amma da yake shaidan yana kansa yana kad'a masa ganga bai fasa aiwatar da mugun kudurinsa ba.
Da yake ba'a cikin haiyacinta take ba shiyasa bata bashi wata matsala ba.
Tsawon awa hudu suna bidirinsu a kanta shi da Lado, har a lokacin bata dawo haiyacinta dan kayan da ya hada tasha ba karamin karfi suke dashi ba, idan mai karamin kwakwalwa ne ma sai ya kwana biyu bai dawo haiyacinsa ba.
A haka ya dauke ta a motarta har zuwa cikin layinsu ya aje motar nesa da gidan su.
Kallo daya za'ayi mata a gane abinda akai mata kuma a fahimci ba'a haiyacinta take ba.
******
"Lokaci yayi da ya kamata a tona asirin su Sanata Sumaila a idanun duniya.
Sannan lokaci yayi da ya kamata Dan majalisa Tanko ya girbi lagwadar irin 6arnar da ya dade yana shukawa a doron kasa.
Shi kuwa Dan takarar Gwamnan jihar kaduna Honourable Ghali da alkhairinsa suka baiyana kuru-kuru a idanun jama'a har suka lullu6e munanan sharrinsa lokacin bankad'osu yayi.
Abinda ya bani mamaki kuma ya daure min kai Dr. Duk su ukun sanannu ne gurin jan gaba gaba a aiyukan alkhairi. Ashe shudayen macizai ne a cikin shud'in ciyawa.
Da yaddar Allah lokaci yayi da zasu girbi abinda suka dade suna aikatawa.
Dr. Da wannan Kamal din zamuyi amfani gurin tona asirin mijinki in Allah ya yarda.
Kamal zaka iya tuna gidan da Kake sauka da kayan maye idan kazo nan kaduna?"
Girgiza kai yayi alamun bazai iya tunawa ba
"Yallabai ni fa Wallahi ko su mutanen da kake maganar sunyi amfani dani gurin lalata matasanmu Wallahi na manta dasu, inda Allah ya takaita mana wahalar kafin in dawo haiyacina na sanar dasu Mummy wadanda nake yiwa aikin.
In banda haka kuwa duk wannan rayuwar da kuke fadin nayi gani nake tamkar almara, ko kuma mafarki ne nayi a cikin barci da ina farkawa na manta da shi"
"Zan iya gane gidan Ya Abdul"
Da sauri suka kalleta da mamaki a fuskokinsu, Mummy kam har saida ta tambaye ta.
"Ta ya akai kika Sani Khadeeja?"
"Mummy akwai ranar da zamu wuce na ganshi ya shiga cikin gidan da motarsa, a lokacin da yake muna tare da abokan aikina shiyasa ban tsaya ba"
Ta kirkiri wannan karyar ta fada ma su Mummy, tasan muddin ta fada musu gaskiyar abinda ya faru zata sha fada da Mummy, in ma taci sa'a bata mammareta ba.
Kamal kuwa murmushi yayi kasa-kasa yana satar kallonta, tunda ta fada mishi gaskiyar abinda ya faru kwanakin baya.
Haka kawai yarinyar take mugun burge shi.🥰🥰
"Ok komai zai zo mana da sauki tunda kin san gidan.
Yanzu Kamal wani bukata ke gare ka wanda kake so mu cika maka a cikin kwanakin nan? Domin dole mu baiyanaka a duniya a matsayin dan ta'adda Usher da muka sake komawa a karo na biyu"
Shiru yayi idanun sa suna ciccikowa da hawaye
"Idan so samu ne in ziyarci dangina da 'yan uwa na ba a matsayin kamamme ba.."
"Angama! Ka shirya gobe da yamma zamu shiga kano dan ka gana da 'yan'uwanka"
Ranta yayi mugun 6aci da yadda take ta kiranshi a waya bai d'auka ba, ta sake kallon Fatima da take kwance a sank'ame kamar gawa.
Wasu zafafan hawaye ne suka sake zubo mata da ta tuno bayanin da likita yayi mata d'azu.
"Hajiya kiyi hakuri, mun bata duk taimakon da ya kamata, amma sai hakuri..
Domin an riga anyi mata fyade.."
Da sauri ta kauda kanta wasu sabbin hawayen suna sake gangarowa daga idanunta, tun lokacin da mai gadi ya sanar dasu a rikice ga Fatima kwance cikin mota taji hankalinta ya dugunzuma, a kallon farko da tayi mata tai hasashen abinda ya faru, wasu marasa imanin sun riga sun keta alfarmar 'Yarta.
Amma a yanzu da ta sake jin tabbacin zancen a bakin likita sai taji hankalinta har yafi dazu dugunzuma.
"Miyagun kwayoyi suka shayar da ita kafin faruwar komai shiyasa har yanzu bata dawo haiyacinta ba. Amma in Allah ya yarda zata dawo hankalinta nan ba da jimawa ba"
Bayanin da likita yayi mata kenan da tausasan lafuzza sannan ya sallameta daga Ofis din, ko da ta nemi ganin Fatima yace ba matsala, zata iya shiga ta kanta, amma kar tayi hayaniya sosai.
Tun shiganta cikin dakin taga halinda take ciki ta dauki tsawon lokaci tana kuka, daga bisani ta lalubo lambar Honourable ta danna mishi kira,
ta kira wajen sau biyar bai dauka ba, a yanzu ta sake danna kiran lambarsa a karo na shida..
"Wai dan Allah Hajiya wannan wani irin masifaffen naci ne? Tun da kika kira daya biyu ban dauka ba ba saiki hakura ba..."
"Dakata Alhaji!"
Ta katse shi cikin tsawa da muryarta mai rawa, har lokacin hawaye bai daina zuba a idanunta ba.
"Ba masifaffen naci ne yasa nake ta kiranka ba, na kira ka dan in sanar da kai iftila'in da ya afka maka.. Amma nasan ba lallai ne ka damu ba tunda abu ne da na dade da fada maka ko bai faru a yanzu ba zai faru a gaba cikin zuriarka...
Allah ya sani ban kasance mazinaciya ba Alhaji... Amma jarabtar da Allah yayi min na auren miji irinka shiyasa zuri'ata suke ta girbe abinda ka shuka da hannunka..."
Daga can bangaren kirjinsa ne ya buga dam, da hanzari ya sauka daga kan baiwar Allah mahaukaciya da take a d'aure jikin gado muryarsa na rawa yake tambayarta.
"Hhhajiya mai kike k'ok'arin fada min?"
"Fatima da ka dauki kulawar duniya ka dora a kanta har is zuba mata masu gadi saboda sharrin samarin zamani to a yau wasu sun Sami nasarar yi mata fyade..."
"FYADE HAJIYA??"
Ya tambaye ta da karfi kamar mahaukaci sabon kamu.
"Kwarai kuwa fyade Alhaji!! Dan a yanzu haka ma muna asibiti bata a cikin haiyacinta saboda kayan mayen da tasha...
In takaice maka zance har wankin ciki likitoci sukai mata, saboda tsoron kar ta dauki ciki...."
Wani mugun ihu da ya kwarma mata a wayar da sauri ta sauke wayar a kunnenta ta kashe gaba daya, hawaye ta ci gaba da yi a hankali tana jin tsanar mijinta yana cika zuciyarta.
Daga can bangaren sa kuwa kuka ya fashe dashi ya zube jagab a gefen gadon.
Ita kuwa baiwar Allah mahaukaciya sai ta fashe da dariya kamar tasan me aka fada mishi a wayar, dariya ta ci gaba da 6a66akawa wanda ke kara tabbatar da kwakwalwarta da motsi.
Kallonta kawai yayi shiru sai kuma ya fara maida kayan jikinsa da yayi watsi dasu a tsakar dakin yana shasshekar kuka.
Yana kuka tana kyalkyala dariya a haka ya fice daga dakin yana kwala kiran sunan drebansa, tashin hankalin da yake ciki yasa ya manta karfe takwas na dare har ta gota a lokacin, a haka suka kama hanyar kano shi da direba da rakiyar Killer.
******
"Kamaluddeen!!!??? Yanzu Kaine haka Kamal? Ina ka shiga duk tsawon lokacin nan baka dawo gare mu ba Kamal?"
Kanin mahaifiyarsa Kawu Mustafa ne yake fadin haka cikin kuka da tashin hankali.
Kusan duk wasu manya daga cikin danginsu da makwafta sun had'u a cikin gidan saboda labarin dawowarsa da ya karade unguwar cikin kankanin lokaci.
Da sunzo kuma sai suyi turus saboda a murya ce kawai yake a wancan Kamal din da suka sani, a siffar jiki kuwa gaba d'aya ya canza.
Shiyasa saida kyar suka gamsu eh tabbas fa shine Kamal din da suka rasa tsawon lokaci bayan tambayoyi da sukai masa akan rayuwarsa ta baya, gani suke kamar wani ne yazo zai yaudare su da cewar shine Kamaluddeen.
Saida suka ga duk wanda ya shigo zai daga kai ya kira cikakken sunanshi, sannan ya gaishe shi a ladabce yasa suka kara yarda tabbas shine.
Duk sun damu ya basu tarihin inda ya shiga a tsawon shekarun nan bai waiwayo danginsa ba.
"Mu kam dai tuni mun dad'e da fitar da ran zaka dawo gare mu, abinda yasa bamu yarda ka rasu ba kamar yanda 'yan unguwa suke cewa Malam Mamuda yayi istikhara ya tabbatar mana kana raye, kuma duk lokacin da muka sake tambayarsa amsa daya yake bamu ita ce kana raye, lokacin dawowarka gida ne baiyi ba."
Wan mahaifinsa ne yake masa wannan bayanin muryarsa a sanyaye, dukda girmansa da shekarunsa sai share hawaye yake yi.
Tun bayan 6atan Kamal din yake tuhumar kansa da sakaci da Zumunci, ya wulakanta iyalan kaninshi mai kaunarshi, wanda yana da tabbacin idan shine ya mutu duk tsananin talauci mahaifin Kamal bazai bar iyalinsa su tagayyara haka ba.
Shiyasa duk tsawon lokacin nan bai ta6a gajiya gurin rokon Allah ya dawo da Kamal gida lafiya ba, ko zai samu ya gyara kuskurenshi kar ya mutu Allah ya tuhumeshi akan sakaci da Zumunci.
"Rashin karfi da takaicin da muke fama dashi yasa tunda muka hada 'yan kudi muka bada cigiyarka a gidan radio na wata daya bamu sake bada cigiyar ba, kuma duk sanda muka kira wayarka Sam baya shiga.
Tabbacin da Malam Mamuda ya bamu na cewar kana raye yasa muka kulle gidanku ba tare da mun ta6a komai a ciki ba.
Saidai lokaci bayan lokaci mu zagayo a duba lafiyar gidan"
Kawu Mustafa ne ya fadi hakan Shima yana goge kwallah.
A hankali kuma cikin nutsuwa Kamal ya gyara zamansa akan babban tabarmar da aka shinfida musu shi da Dr. Da Abdul da Khadeejah da ta nace ita saita bisu, da Mummy tace baza'a je da ita ba ta shige ciki tana kuka, dakyar Kamal ya rarrashi Mummy ta bari aka taho da ita.
Bai 6oye musu komai ba daga tarihin rayuwar da ya gudanar bayan rabuwarsa da gida, kafin yakai karshe manya da yaransu kuka suke kashir6in, Chairman yasha tsinuwa kwando kwando, da fatan saukar iftila'i a cikin rayuwarsa kala-kala.
Daga bisani kuma suka karke da addu'ar fatan alkhairi ga Mummy da yaran ta, da kuma Abdul da yayi alkawarin zai tsaya wa Kamal din dan wanke munanan laifukansa a idanun duniya.
"Wai ni kam yanzu ina Chairman yake ne? Yaci takarar dan majalisar da yake nema kuwa?"
Kamal ya tambaya bayan sun natsa da koke-koken da suke yi.
"Ai Chairman Sumaila likkafa ta ci gaba, yanzu fa shi yana Abuja, ya zama Sanata, tun kafin hawan Gwamna Kabiru da yake mutuminsa ne kuma mutane suna sonshi saboda k'ok'arin ayyukan alkhairin da yake yi a fili, Gwamnan ya bashi shawarar madadin dan majalisar jiha ya nemi Sanata, kuma cikin ikon Allah ya bashi nasara.
Amma da yaddar Allah sai ya gamu da masifa da bala'i akan abinda ya aikata maka.
"Sanata Sumaila kace?"
Abdul ya tambaya da sauri.
"Eh kwarai kuwa yaro, sunanshi kenan Sumaila.
Ka san shi ne?"
Bai amsa ba sai wayarsa ya dauko yayi searching Senator Sumaila Dankasa, cikin kankanin lokaci tarihin shi ya baiyana, da kuma hotunansa daga kasa.
Zooming din hoto daya yayi ya mikawa Kawu Mustafa yace
"Shine wannan?"
"Kwarai kuwa shine bakin azzalumin, wanda tarin alkhairansa suka boye munanan aiyukan da yake yi a 6oye"
Da matukar mamaki a fuska da muryarsa ya kar6i wayar ya sake mikawa Kamal
"Wannan shine Chairman din da yaronsa yayi wa kanwarka fyade?"
Gyada kai kawai ya iya yi alamun eh shine, dan ganin hotonsa ya sake tada mishi k'ullatan da ya yiwa Chairman din.
"Abdul lafiya kuwa?"
Mummy ta tambaye shi dan ganin lokaci daya ya shiga wani yanayi mai kama da na rud'ani.
"Iko sai Allah! Dr. Wannan Chairman din fa ba kowa bane face wanda Usher ya zama mishi dilar miyagun kwayoyi.
A takaice Chairman shine Honourable Sumaila.
Lallai Kamal fansarka guda biyu ne akan wannan bawan Allah"
Jikin Kamal har wani tsuma yake yi da yaji bayanin Abdul, ina ma Allah zai hada shi da Honourable a daidai wannan lokacin? Wato dai Chairman yayi nasara a kansa kenan? Tunda har ya samu damar maida shi babban dan ta'adda a idanun duniya.
Lallai yayi nasara a kansa a karo na biyu, Amma in Allah ya yarda lokacin da zai karya alkadarinsa gaba daya yayi.
*BARA A KUFAI!!*
*33)*
*Wannan na jiya ne, komai dare na yau yana tafe in Allah ya yarda. Kuyi min afuwa pls👏🏻*
Irin maganganun da yake ta jiyowa yana tashi sama-sama daga d'akin da yake jikin inda yake daure yasa hankalin sa yayi mugun dugunzuma.
Sake kasa kunne yayi sosai dan ya fahimci akan shine tabbas suke maganar?
"Tsawon 1 month muna ciyar dashi mu bashi magani ba dan komai bane sai don wannan lokacin da muke jira.
Dan haka banga amfanin a yanzu kuma muce a sake barinshi ba, amfanin me yake mana da har zamu sake barinshi?
Yaji saukin da idan muka sadaukar dashi ga *Jujuba* bazaice mun bashi mare lafiya ba, dan haka wannan maganar a barta kawai.
Jibi zamu yanka shi mu ba *Jujuba* jininshi yasha..."
Hawaye ne suka gangaro daga idanunshi, hannu da kafafunshi ya kallah yaga mugun daurin da sukai masa ba mai kwancewa cikin sauki bane.
A daidai lokacin da yake wannan tunane-tunanen d'aya daga cikin mutanen da suke maganar ya leko ya kalleshi sama da k'asa, tsawon mintuna sannan ya koma cikin dakin.
"Shikenan! Shi din zamu sadaukar, naga tabbas ya kara jin sauki sosai.
*Jujuba* zaiyi farin ciki da shan jinin kamarsa, Amma kafin ranar mu ci gaba da ciyar dashi kyakkyawan abinci dan ya sake koshi sosai"
Da wannan maganar suka samu matsayar sadaukar da jinin Guru ga Gunkin da suke bautawa mai suna *Jujuba*
Tun daga wancan lokacin da suka samu hatsari da motar da suka dauko Usher shi bai fada ko ina ba sai kofar gidan *Gale*, Gale mutum ne mai saukin mu'amala da mutane, kuma yana rayuwarsa ne tsakanin musulmai kuma hausawa, halin kirkinsa yasa mutane suke kaunarsa.
Dukda banbancin addinin da yake a tsakaninsu, da yawan mutane sun dauka Gale mabiyin addinin kirista ne, saboda duk ranar lahadi yake daukar wanka ya tafi gurin bautarsu.
Amma kuma a zahirin Gaskiya ba haka bane, Gale mabiyin addinin Gunki *Jujuba* ne, wanda suke daukarshi da matukar girma da daraja kamar shi ya halicce su.
Duk karshen wata suke shayar dashi jinin mutum guda, idan basu samu wanda tsautsayi ya afka kanshi da zasu sadaukar ba haka nan a cikinsu suke duba tsoho tukuf su sadaukar dashi ga Gunki *Jujuba*
Dan sunyi imani muddin basu sadaukar mishi da jini ba to Shima zai daina biya musu bukatunsu, dukda daman ba bukatun yake iya biya musu ba, yana fakewa ne da lokacin da Allah ya saukar da ni'imarsa gare su sai yace Shi ya biya musu.
Wani shaidanin aljani ne ya shiga jikin Gunkin yana kara dulmiyar dasu a halakkiyar hanyar bauta masa.
Shiyasa ko da Gale ya tsinci Guru baiyi kasa a gwiwa ba gurin kaishi can cikin jeji inda mafiyawan mutanensu suke, suka ci gaba da jinyarsa da bashi abinci har ya kawo yanzu da suke shirin yanka shi a gaban Gunki yasha jikinsa.
Da karfi ya jijjiga d'aurin da suka yi masa ko zai samu wata 'Yar dama da zai iya kwancewa sai yaji kamar ma ya sake tamke kanshi ne, mugun dauri sukai masa mai kama da na huhun goro.
"Ashe haka mutane suke ji a ransu da jikinsu idan aka sa lokacin kashe su?"
Wasu hawaye ne suka sake gangaro masa, jikinsa kuwa ko ina kyarma yake yi.
Wai yanzu shine aka saka ranar kashe shi? Babu abinda yake tunawa a ransa sai irin yadda suke kashe mutanen da sukayi kidnapping dinsu ba tare da no digon tausayi ba idan aka ki biyan kudin fansar su.
Wani dattijo da suka ta6a kamawa suka kashe ne ya fado masa a rai, ire iren mutanen da suka kashe suna da yawa amma kashe wannan dattijon ya tsaya mishi a rai.
"Baba iyalinka sunki biyan miliyan biyun da zasu kar6eka a hannunmu, dan haka idan basu kawo kudin zuwa karfe goma na safiyar gobe ba zamu kashe ka!!"
Baya manta yanda kafin mintuna goma da suka fada masa Wannan maganar ya jika wandonshi da zawo mai tsananin wari, zuwa wayewar gari kuwa yayi biji-biji ya fita haiyacinsa, kamar wanda ya shekara guda a kwance yana jinya.
A galabaicen yake rokon dan Allah karsu kashe shi, iyalinshi ba masu karfi bane amma haka suka dauke kansa da bindiga...
Matsanancin da na- sani ne ya lullu6eshi, nan take ya fara istigfari da neman gafarar Ubangiji akan irin munanan aiyukan da ya dad'e yana aikatawa a rayuwarsa, dukda wani sashe na zuciyarsa yana tantamar anya kuwa Allah zai kar6i tubansa?
"Da zaka shiryu shiriya da tsarkakkiyar zuciya, kasa a ranka in Allah ya yarda bazaka sake komawa kan mummunar aikin da kake aikatawa na sa6o ba tabbas Allah zai kar6i tubanka, domin shi ya kasance mai gafara ne kuma mai jin k'ai ga bayinsa..."
Nan take ya tuno wani 6angare daga cikin nasihar da mahaifiyarsa take yawan yi masa kafin barinsa gaban iyayen sa.
******
Cike da nutsuwa a muryarta ta gama warwarewa dattijon da take daukarshi kamar mahaifinta duk labarin abinda yake faruwa.
Dukda a waya take mishi bayanin kallo daya za'ayi mata a gane tsananin ladabin da take mishi, domin kuwa tana zaune ne a kasa kuma kanta a kasa kamar tana zaune a gaban idanunsa.
Daga can bangaren sa shima cikin nutsuwa yake saurarenta har saida ya fahimci ta kai karshen bayanin da take mishi.
"Abida kina ji na?"
Ya tambaye ta daga 6angarensa.
"Eh ina jinka Baba"
Ta amsa tana sake gyara rikon wayar hannunta.
"Ina so ki kwantar da hankalinki, ki sa a ranki Alhaji Tijjani bawan Allah ne kamar kowa, bai isa yayi muku abinda Allah bai kaddara zai faru a kanku ba.
Kin gane?"
"Eh na gane Baba"
Ta amsa tana gyada kai alamar ta gamsu.
"Amma dukda haka bai kamata muyi sakaci wajen addu'a da k'ara mika al'amuranmu ga Allah ba, domin Alhaji Tijjani yana daga cikin hatsabiban bayin da ko kad'an babu Allah balle wani abu tausayi a cikin rayuwarsu.
Tsafin Alhaji Tijjani ya sanar dashi da ke da yaranki babban barazana ne a cikin mulkinsa da rayuwarsa, dan haka zaiyi duk yadda zaiyi wajen ganin ya kawar da rayuwarku daga doron k'asa, dan haka ku dage da nafilfili, kuyi salatin Annabi SAW, kuyi istigfari da tasbihi, ku roki Allah ya kare ku daga sharrin masu sharri"
"To Baba, in Allah ya yarda zamu dage da addu'a"
"Masha Allah! Allah ya tsare mu daga dukkan sharri"
"Ameen ya Allah"
"Nima in Allah ya yarda zansa Inusa ya kawo ni gurinki a nan kadunan, akwai abinda zan ba shi wannan dan sandan da kika ce yayi alkawarin zai taimaka muku"
"To Baba, na gode. Allah ya kara girma"
Da haka sukai sallama dashi tana jin wani kwarin gwiwa a zuciyarta.
*****
Gudu yake iya karfinsa yana ratsa dogayen bishiyoyin da suka yiwa dajin kawanya, sai numfarfashi yake yi kamar mai cutar athma.
Abinda yake kara saka shi takawa da gudun shine ko ya yad'an waiga bayanshi sai yaga Doguwar halittar sanye da fararen kaya mai kama da likkafani tana biye dashi ta kusa cimma shi, a hannun halittar shar6e6iyar wuk'a ce gayawa jini na wuce tsirararta.
Yana cikin gudu ya cimma wata wawakeken rami a gabansa, ko da ya leka cikin ramin da nufin fad'awa ciki dan gujewa halittar sai yaga ashe wuta ce gagga-gagga take ci tana hankoro a cikin ramin, da sauri yaja da baya sai yayi karo da wannan halittar tana tsaye daf dashi tana jujjuya wukar hannunta.
Ya juya a guje da nufin ya afka cikin ramin wutar yaji an daga sama cak an bank'are cikinshi an mik'awa halittar da take biye dashi,
hankalinshi a matukar tashe ya daga fuskarsa dan ganin wane makiyin nashi ne ya hanashi afkawa cikin ramin wutar nan sai yayi karo da fuskar tsohuwar matarshi Harira, tana sanye da fararen kaya irinna wancan halittar, fuskarta a daure tamau idanunta sunyi jajur kamar garwashi wuta.
Halittar da take biye dashi tun farko ta duk'o da kanta suka hada ido sai yaga ba kowa bane sai dansa Kamal marigayi.
"Wayyo... wayyo... wayyo... Dan Allah karku kashe ni..."
Maganarshi ta katse a dai-dai lokacin da Kamal ya daga shar6e6iyar wukar hannunsa Barira ta bank'are cikinsa Kamal ya caka mishi wukar....
"Wayyyyooooo..."
Ihun da ya farka dashi kenan daga mugun barcin da ya kwashe shi a kan gadonsa har yayi mummunar mafarkin halakarsa a hannun matarsa da d'ansa da ya dad'e da hallaka su da hannunsa.
Shiru yayi yana sake maimaita mafarkin a zuciyarsa kamar a wannan lokacin abin yake faruwa, lokaci na farko a rayuwarsa da yaji wani masifaffen tsoro ya rufe shi.
Danshi-danshin da yaji a wandonsa yasa ya kai hannu ya shafo takashinsa😳😳😹😹 ido ya zaro cike da tsoro dan ganin d'anyen zawo mai cike da warin tsiya ne yayi saboda tsananin firgitar da yayi a mafarkin.
Ai da saurin gaske ya fada band'aki jikinsa babu inda baya kyarma.
Bai wani dad'e da shiga ba ya fito bayan ya canza kayan jikinsa gaba d'aya.
Tunani yake akan irin mummunan matakin da ya kamata ya d'auka akan Abida da iyalanta.
Babban barazana ne a gare shi a daidai wannan lokacin da za6e yake matsowa kusa ace an samu wani tabo ko kad'an ne a kanshi, sosai yake da burin maimaita wasu shekaru hudun akan kujerarsa na gwamna, shiyasa bazai ta6a yarda yaba 'yan adawa kofar da zasu abin yarfe a gare shi ba.
Wani kasko mai kama da na k'asa ya d'auko a karkashin gadonsa, tururi mai zafi kaskon yake fitarwa ta samanshi, wani bakin ruwa mai kauri da yake cikin kaskon sai tafasa yake yi shi kad'ai.
Kaskon ya dauka da hannun hagu yayi ya daga shi sama ya shafi gefen jikinsa na hagu yai wani girgiza take ya baiyana a cikin dakin da yake tsafe-tsafensa a cikin gidan.
Nan take ya fara wasu surutan tsafi da sam ba'a fahimtar me yake cewa yana d'ibar ruwan cikin kaskon da yake hannunsa yana watsawa gunkin wata tsafaffiyar tsohuwa da take zaune a tsakiyar d'akin.
Dukda a ido ruwan tafasa yake yi a hannu sam baya jin zafin ko kad'an.
"Bani kudi albarkacin tsumburbura da tasha nonon ki Harira.."
Nan take wannan tsafaffiyar tsohuwar ta fara yi masa aman kudi sabbi kar 'yan naira dubu dubu ta bakinta.
Da na k'ura idanu da kyau sai naga wannan tsohuwar da take aman kudi ba wata bace face Harira Mahaifiyar Kamal da Amatullahi, yar Dr. Abida.
Wacce Alhaji Tijjani ya kaiwa iyayenta labarin rasuwarta ba tare da ya kai musu gawarta ba.
Dif ta dakata da aman kudin da take yi bayan ya ci gaba da surutan tsafi yana zagaye ta, hannunshi yasa ya bugi kanta tsulum sai ga wani aljani ya baiyana a gabansa, dukawa yayi har kasa yayi masa sujada
"Tsumburbura ta baka duniya Alhaji Tijjani... gani a gare ka a matsayin bawan Tsumburbura mai bin umarninka, me kake so a aikata maka yanzu kaga aiki da cikawa...? In dai duniya ce ka samu a hannunka Alhaji Tijjani..."
Aljanin ya fadi haka da muryarsa mare dadin sauraro.
"Kaje Kaduna gidan mataimakin kwamishinan 'yan sanda ka kashe Abida da iyalanta, sannan ka tabbatar ka taho min da k'ok'on kawunansu domin a ciki Tsumburbura take bukatar tasha jini.."
"Angama!!"
6at! Ya 6ace daga gurin bayan ya amsa umarnin da akai mishi.
Ta gabanta ya wuce bayan ya bi ta kan kudin da ta gama amayarwa a kasa.
Idan mutane suna zuwa ATM dan su cire kudi shi Alhaji Tijjani wannan tsafaffiyar matar tasa ita ce ATM dinsa, a duk lokacin da ya bukaci kudi amansu take mishi har sai ya dakatar da ita.
Yana komawa cikin dakin yaji ringin din wayarsa, agogon dakin ya kallah yaga karfe hudu da rabi na asubahi.
*Kamal*
Sunan da ya gani kenan yana yawo akan fuskar wayar dan haka ya dau kiran ya kara wayar a kunne da sauri.
"Ka gama duk tsafe-tsafen da zaka yi ni zan zama ajalinka Daddy"
Abinda aka fara fada masa kenan daga can bangaren bayan ya dauki wayar yayi shiru baiyi magana ba.
"Waye kai?"
Ya tambaya ba tare da ya bari fargaba ko tsoro ya baiyana a muryarsa ba.
Saida yayi dariya daga can bangaren ya amsa da cewa
"Nine Kamal, Kamaluddeen Tijjani, danka na cikinka..."
"Kai Dakata da Allah!"
Ya katse shi da tsawa muryarsa na rawa
"Kamal d'ana ya mutu tun da dad'ewa, kuma ni na kashe shi da hannuna... au! au! ni na rufe shi a k'asa da hannuna... bazai yiwu ace ya rayu tsawon lokacinnan ba tare da sani na ba.. Dan haka ka fada min kai waye?"
Cikin rud'ewa Allah ya matsi bakinsa ya furta cewa shi ya kashe d'ansa Kamal da hannunsa.
Kit aka katse wayar daga can bangaren, da sauri Abdul ya amshi wayar yayi saving din recording din da ya danna daidai lokacin da wayar ta fara ringing, farin ciki ne fal da fuskokinsu, lallai Allah ya kar6i addu'arsu.
Dr. Abida, Kamal, Abdul suna zaune a falon a daidai wannan lokacin bayan sun gama nafilfili suna tsara yanda zasu tunkari Alhaji Tijjani, dan sun san tunkarar babban mutum mai girman matsayi irin nasa da irin wadannan manyan laifukan abu ne mai girgiza kwakwalwa.
Shiyasa dole su samu kwararan hujjoji a hannu kafin tunkarar wad'annan manyan mutanen da laifukan da ake tuhumarsu dashi, idan ba haka ba kuwa sai su kwan ciki, reshe ya juye da mujiya.
Cikin tsofaffin ajiyanta ta bincika ta d'auko layin wayar marigayi Kamal, shine suka yi amfani dashi gurin kiran Alhaji Tijjani.
A daidai wannan lokacin kuma aljanin da aka turo ya hallakasu sai zagaye gidan yake yi ya rasa kafar shiga gidan, duk ta inda yasa kai zai kutsa wani azababben zafi ne yake dawo da shi baya.
Jin da yayi yana neman halaka kanshi yasa ya bar katangar gidan ya koma inda ya fito.
*****
"Baby Iman kin samu wani abu a cikin nan kuwa?"
Ya tambaye ta da taushin murya lokacin da yake k'ok'arin shiga cikin kicin din.
Shikam tun isarsu gidan ya kasa yin wani kata6us gurin binciken da ya kaisu, duk inda Khadeeja tasa kafa anan yake maida tasa.
"A'a ina dai bincikaw..."
Maganarta ta katse a daidai lokacin da wani kyankyaso mai tashi ya taso firr daga cikin wani durowa da ta bud'e.
Da wani mugun sauri ta ja da baya tana zare ido, ganin ya sake tasowa firr kamar zai hau jikinta ta tafi da gudu ta rukunkume Kamal tana kwalla ihun kyankyaso.
Da sauri yayi mata masauki a faffadar kirjinsa yana mata dariya, shikam baiga wani abun tsoro a kyankyaso ba.
Yam- yam take ji ta wuyanta kamar ya shige cikin hijabinta ai da sauri ta zare hijabin tayi hurgi dashi tana sake rungume shi.
"Yah Kamal kyankyaso... Dan Allah ka cire min...😩😩😢😭"
Ta fada cikin kuka, ganin da gaske take kukan yasa ya d'ago ta daga jikinsa yana d'an dudduba ta da idanunsa ko zaiga kyankyason a jikinta.
Sai a lokacin ya lura da yadda rigar atamfar jikinta ya kamata tsam haka ma sket din, hannunta daya ya kama ya juya ta gaba da baya baiga wani kyankyaso a jikinta ba, idanunsa sunki daukewa daga kan kirjinta da sukai tsiri cikin rigarta.
"Baby ni banga wani kyankyaso a jikinki ba.."
Ya fada da sanyin murya yana jin yanayin jikinsa yana canzawa, karo na farko a rayuwarsa da yake jin wani feelings akan wata 'ya mace.
Dukda ya fadi hakan Sam ta kasa nutsuwa, dakyar ta sake shi ta makale a bayanshi ya kashe kyankyason da ya hangeshi can jikin windo.
"Kinga na kashe shi dauki hijabinki kisa"
"A'a ni dai ka kakka6e min.."
Ta fada tana kwa6e fuskarta da guntun hawaye a idanunta.
Saida ya kakka6e hijabin sosai taga babu komai a ciki ya mika mata hijab din ta kar6a, tana rike da shi a hannunta ya sake kar6ar hijabin ya bude fuskar ya nufeta da nufin saka mata.
Kya6e fuska tayi ta kar6i hijabin tasa tana ta tuttura baki.
"Fushin kuma na miye Baby?"
Ya tambaye ta bayan ya nufi hanyar fita daga kicin din, dukda ta saka hijabin yanayin da ya ganta a ciki ya matukar tsaya mishi a zuciya, ashe shiyasa kusan ko wane lokaci idan suna tare da hijabi ko babban gyale a jikinta? Mugun kasalar da ta saukar mishi dole saida ya zube a kujera ya huta tsawon mintuna uku.
Duk da haka tana zaune a dan nesa dashi.
"Ya Kamal ka tashi mu ci gaba da binciken ko zamu samu wani abu kafin zuwan Yaya Abdul"
Ta fada a shagwa6e bayan ta lura sam baida niyyar motsawa daga inda yake zaune.
Bai amsa ba sai yunkurawa yayi ya mike yana kauda fuskarsa daga kallonta, haka kawai yake jinshi a wani mawuyacin yanayi.
Duk tsawon lokacin da suka 6ata dakyar suka samu wata karamar waya a gidan, sai kuma kakka6in kayan shaye-shaye da baza'a rasa ba.
Bayan wadannan basu samu komai ba.
0 comments:
Post a Comment