Ire-iren sambatun da take ta yi kenan a daidai lokacin da kwayar ta fara sakinta tana buge-buge da hannayenta. Can kuma sai ta sake 6ingirewa da bacci da taimakon kwayoyin da basu sake ta ba.
Hajiya Khalthum da Honourable Sumaila suna tsaye k'ik'am kamar gumaka, da na kalli fuskokinsu kuwa gaba daya hawaye ne ke rige-rigen sauka a kumatunsu.
Honourable da yafi kowa shan alwashi akan nutsuwa da kamewa da irin tarbiyar da Fatiman take dashi kuwa yafi Hajiya Khalthum shiga cikin matsanancin tashin hankali.
Kuka yake yi riris, da kunnensa yaji Fatima wacce ta kasance babba a cikin 'yayansa bayan rasuwar Ado tana fadin *duk iskancinta a shaye-shaye ta tsaya.*
Wannan itace kalma mafi muni da bakanta zuciya da ya sake ji a shekarunnan tun bayan rasuwar Ado.
Bayan wasu satittika da rasuwar Ado ya zauna yayi wa kansa karatun ta nutsu tare da tallafin nasihohi da nunar dashi kuskurensa da Hajiya Khalthum take yi ya gane lallai fa gatanta yaro ba hanya ce ta 6ullewar kyakkyawar tarbiya ba.
Duk yadda ka kai da son yara dole ka ringa tsawatar dasu akan kuskuren da suka aikata.
Tabbas yasan da saka hannunsa dumu-dumu gurin lalacewar tarbiyar Ado, shiyasa yasa alwashin in Allah ya yarda baza'a sake kwatanta haka a kan Fatima ba, abinda bai sani ba ashe ta baya ta rago yayi.
"Alhaji..."
Hajiya Khalthum ta kira sunansa cikin kuka.
Bata jira ya amsa ba ta ci gaba da cewa
"Lallai Fiyayyen halitta yayi Gaskiya.. abinda ka aikata a baya tabbas shi zaka kwashe a gaba, idan mai kyau ka kwashe da kyau idan mare kyau ne is kwashe mare kyau.
Kuma duk randa kayi zina da yar wani to komai daren dadewa kaima sai anyi da taka 'Yar, idan ba'ayi da ita ba to tabbas sai sakaiya ta fadawa jikokinka.
Alhaji tun kafin muyi aure na dad'e da sanin kana da karancin kamun kai, kuma na samu labarin kad'an daga cikin 'yanmatan da ka lalatawa rayuwa..
Idan baka manta ba har nima ka ta6a neman yin lalata dani, amma da nai nayi maka kaca-kaca sai kace wai daman gwada ni kayi ka 6uge da bani hakuri...
Ko ka manta??"
Ta zazzare idanu tana kallonshi cikin fitar haiyaci, sunkwi yayi da kanshi kasa alamun rashin gaskiya a fili.
"To d'anka Ado irin wadannan munanan halayen naka ya kwaso, daman ai kyawun d'a ya gaji Ubansa ko? shi kam har ma aka had'a masa da alakoron shaye-shaye da bushe-bushe.
Sannan da taimakon mugun gatan da kake gwada masa da kuma 6oye laifinsa da kake yi yasa ya ci gaba da cin karensa ba babbaka, ta hanyar biyan bukatarshi da duk yarinyar da ransa ya kwadaita masa.
Baka ta6a nusar dashi ko yi masa fad'a akan irin wannan halayen nasa ba har Allah yasa ya had'u da yarinyar mai tsada da ya biya fansar fyaden da yayi mata da rayuwarsa.
Alhaji kana tunanin duk da hakan zaku ci bulus ne kai da d'anka? Ina...! Ai dole sai kunyi biyan bashin abinda kuka dad'e kuna aikatawa.
Wai Alhaji kana tunanin bansan kana sana'ar miyagun kwayoyi a 6oye bane? Na dad'e da sani kawai nisan da kayi da baka jin kira da kuma irin k'ok'arin da kake yi na 6oye min yasa na zuba maka ido inga iya gudun ruwanka.
Abinda baka sani ba shine talala Ubangiji yayi maka kafin ya maka mummunar kamu a lokacin da ko kayi nadama bazata amfane ka ba.
Ga irinta nan dai!!! Kaje kana ta k'ok'arin lalata kwakwalen yaran wasu da miyagun kwayoyi ashe kwakwalwar taka 'Yar ta dad'e da lalacewa...
Mummunar abinda kuke aikatawa ga yaran wasu yau gashi an yi wa 'yarka, kaga sai kaji yadda iyayen yaran da aka lalata suke ji a ransu.
Amma barin maka tunatarwa ta karshe!"
Ta tattaka ta matsa kusa dashi fuskarta jage-jage da hawaye da majina.
"Alhaji idan har kana da rabon tsira kuma kana da tunani wannan ne lokacin da ya kamata ka tuba, kayi karatun ta nutsu a rayuwarka.
Ka tsarkake kanka da zuciyarka a farko sai Allah ya dube ka da idanun rahamarsa ya gyara maka rayuwarka sannan ya shirya maka zuri'arka ya tsare su da dukkan sharri.
Na barka lafiya👏🏻👏🏻"
Da sassarfa ta nufi ban daki tana toshe bakinta da hijabinta lokacin da taji wani kakkarfar kuka yana neman ku6uce mata.
Shiru yayi yana tunanin maganganunta a zuciyarsa, jikinsa yayi sanyi sosai, kamar zaiyi nadama sai shaidan ya sake halarto mishi da abinda ya samu Fatima da kuma kaskantaccen mutumin da yayi mata fyade.
"Nura fa? Kaskantaccen yaron da ya tausayawa yana gararanba a gari ya dauko shi yasa aka yi mishi kwakkwaran training dan ya ringa gadin 'yarsa.
Shine zaiyi mishi wannan cin amanar? Lallai dole ya biya akan abinda ya aikata mishi"
Wayarshi ya dauko da nufin kiran Kwamishinan 'yan sanda na nan kanon sai yaci karo da wani sako da ya shigo mishi a dazu lokacin da Hajiya take ta mishi wannan baya nan.
Bude sakon ya fara yi dan ganin abinda ya kunsa, bayan yaga sunan mai aiko da sakon da manyan baki rubuce a saman sakon.
" *USHER*
*Honourable barka da sassafe, nine dai naka Usher abokin harkallarka.*
*Na samu nasarar tserewa a hannun 'yan sanda bayan sun samu nasarar kama ni, amma da yake ina da labarin yanda 'yan sandan jihohi suke nemana shiyasa na yanke shawarar barin kasar nan, dan haka ina so is turo wasu 'yan kudade da basu da yawa, ko miliyan talatin haka sun isa inyi maneji, idan komai ya lafa zan dawo mu cigaba da harka, a hankali sai mu warware"*
Daga karshen wasikar adireshin wani gida ya tura masa ba wannan gidan da yake sauka idan yaje Kaduna ba, sannan yace lallai ya tura akai masa kudaden cash ne kar ya tura masa ta banki, dan bazai iya zuwa banki cire kudi ba saboda nemansa da ake kan yi.
"Kan uba!!!"
Ya lailayo mummunar ashar ya maka kamar Usher ne a gabansa.
Tunawa da inda yake yasa ya fice daga d'akin cikin sauri yana daddana wayarsa, amma a maimakon kiran Kwamishina lambar Killer ya lalubo ya danna masa kira.
"Duk inda kake ka karaso cikin asibiti yanzu-yanzu, na samu labarin inda Usher yake"
Abinda ya fada masa kenan ya katse wayar, hannayensa ya goya a baya ya ci gaba da safa da marwa a kofar dakin, fuskarsa cushe da damuwa, kallo d'aya za'ai masa ayi tsammanin matarsa ya kawo haihuwa saboda tsananin tashin hankali da damuwar da yake baiyane a fuskarsa.
*****
A karo na uku kiran ya sake shiga cikin wayarta, tsai yayi da ransa yana kallon suna da lambar mai kiran.
"Sweet Barrister"
Ya karanta sunan mai kiran a fili yana k'ok'arin boye rashin dadin da yake hi yana taso wa daga can k'asan zuciyarsa.
Kallonshi tayi kawai ta sake maida hankali ga tukin motar da take yi.
"Ki amsa kiran masoyinki mana ko zai barmu da wannan nacin kiran da yake yi"
Ya fada fuskarsa na kallon titi ta bangaren da yake zaune.
Babu musu kuwa ta dauki wayar ta danna a hands-free ta dora a cinyarta tayi sallama da siririyar murya.
Amsawa yayi daga can bangaren da murmushi a fuskarsa kamar yana kallonta.
"Sweetheart ina biye dake a baya fa"
Abinda yace mata kenan bayan ya amsa sallamarta.
Matukar mamaki ne ya kamata, dan haka ta kalli madubin kofar ta dan tabbatar da gaskiyar maganarta.
Kwarai kuwa motarsa ce biye da tata motar, murmushi tayi kawai, wani abu da ta tuna kuma yasa hankalinta ya tashi.
"Na ganka, ina ka nufa ne haka?"
"Duk inda kika nufa nima nan nayi, jani ki kaini duk inda kike so Sweetheart❤"
Haushi ne ya kamata, 'Wawa ko kalaman soyayyar ma bai iya ba'
Ta fada a zuciyarta tayi tsaki kasa kasa.
K'ok'arin danne fushinta tayi ta fara magana da sigar rarrashi.
"Nagode Sweety, amma kayi hakuri, ina tare da brother na ne, anjima kazo gida mu hadu..."
"Kwanaki uku kenan ina zirga-zirga a gidan bana samun kowa, akwai muhimmiyar maganar da nake so muyi da ke ne.
Dan haka ko ki tsaya mu samu gurin tattaunawa ko kuma in biki duk inda zaki je"
Tsaki taja mai karfi da har ya ji daga can bangaren sa, tasa hannu ta katse wayar tana budewa motar wuta da nufin ta guje masa.
Zuwa wannan lokacin Kamal ya cika dam, kiris yake jira ya fashe, sai huci yake shi kadai kamar kububuwa.
Kallonshi tayi shiru kamar bazata tanka ba, sai kuma shirun nashi ya dame ta.
"Ya Kamal?"
Ta kira sunanshi a marairaice.
Juyo da fuska yayi ya kalleta kawai bai tanka ba.
"Kayi shiru, kace wani abu mana pls...?"
"Waye wannan?"
Ya tambaye ta har lokacin bai saki fuskarsa ba.
"Wai wanda muka yi waya? So na yake. Sunanshi Barrister Abdul"
"Ok"
Amsar da ya bata kenan ya juyar da kansa gefe daya. Jin cewa wani yana sonta ma Karin kunar zuciya ne a gare shi.
[23/04 5:16 PM] fareedah: *BARA A KUFAI!!!*
*36)*
Yanda yai saurin shiga gabanta da motarsa yasa dole ta rage gudun da take yi, gangarawa gefen titi tayi ta faka motar, Shima ya faka tasa motar a gaban tata ya kashe ya fito waje ya nufo gurinsu.
Da kamar bazata fita ba wani tunani da ya darsu a zuciyarta yasa tayi saurin fita daga motar ta nufe shi fuskarta babu walwala.
Shi kuwa tun daga nesa yake jifanta da tattausan murmushi.
"Barrister wai miye matsalarka dani? Ina cikin muhimmin uzuri ne na fada maka zan neme ka..."
"Waye wancan a motarki ki?"
Ya tambaye ta yana nuna Kamal din da makullin motarsa.
"Miye damuwarka dashi? Pls Barr ka kyale ni. Ina da wani muhimmin uzuri a gaba na.
Duk sanda na samu nutsuwa zan neme ka"
Tana gama fadin haka ta juya zuwa cikin motarta ranta a 6ace, sauri-sauri take yi tabar gurin tun kafin Barr ya fahimci waye Kamal, ta riga tasan halinta kamar yunwar cikinta, mutum ne mai matukar kwakkwafin bin doka da oda.
Zagaye shi tayi da motarta ta wuce ta barshi tsaye a gurin yana kallon cikin motar, abinda bata sani ba tuni ya fahimci waye a cikin motar, dan haka yake ta bin motar da kallon mamaki.
******
"Oh sheet, ya akai haka ta faru Khadeeja?"
Ya tambaye ta ranshi a 6ace.
Tun farko ya gargadeta akan yawan fita da Kamal din amma taki ji, kanta a kasa, sai matsa yatsun hannunta take yi, ta kasa furta komai.
"Yanzu dole labarin kama Usher ya 6ullah a daren nan, dan haka ki shirya, wannan zazzafan labari ne da ya kamata gidan jaridarku ya fara fitarwa.
Ina fatan kin fahimce ni?"
Raurau tayi da idanunta kamar zata dora hannu a kai ta saka kuka.
"Eh! Na fahimta"
Ta amsa a sanyaye kamar wacce aka zarewa lakar jiki.
Bai bata lokaci ba ya fice daga falon cikin sauri, cikin gida ya nufa dan shiryawa.
"Na fahimceka Daddy, daman bazai yiwu a cigaba da 6oye Kamal anan ba, fito da batun sake kama shi shine abinda ya kamata.
Amma pls Daddy ka tsaurara kwakkwaran mataki a gurin da za'a aje shi, kasan wadanda yake yiwa aiki zasuyi duk mai yiwa dan kar ya tona musu asiri.
Kuyi gaggawar tura case dinshi kotu saboda ayi gaggawar yin shari'ar shi.
Aysha ce take fadin haka ga Abdul muryarta a tausashe, bayan ya gama yi mata bayanin hukuncin da ya yanke na sake kama shi.
*****
A hankali yake jiyo shesshekar kuka ta, da farko yayi tsammanin kunnenshi ne yake mishi gizo, amma jin kukan yana sake k'aruwa ya tabbatar ba gizo bane.
Kallonta yayi shima jikinsa a sanyaye, dukda Abdul ya tabbatar masa ko an kamashi baza'a ringa wahalar dashi ba haka kawai jikinsa yayi sanyi, ga kuma kukanta da yake kara damalmala mishi lissafi.
A hankali us yunkura ya tashi tsaye ya koma kujerar kusa da inda take zaune.
"Khadeejah...."
Ya kira ta a sanyaye, bai jira ta amsa shi ba ya ci gaba da magana, kallo daya za'ai mishi a gane zallar gaskiyar maganar daga zuciyarsa take fitowa.
"Ina sonki Khadeejah !!!"
Da sauri ta hadiye kukan da take yi kanta a kasa ta ci gaba da sauraran maganganun masu kama da saukar daddad'an ruwan sanyi a zuciyarta.
"Wallahi ina sonki Khadeejah, tun washe garin ranar da na dawo cikin haiyacina kika fara burgeni, ina jin wani daddad'ar yanayi yana sauka a jikina aduk lokacin da nake tare da ke Khadeejah.
Da farko nayi tsammanin burgeni kawai kike yi saboda kece kika fara bani taimakon gaggawa a cikin mummunar halin da nake ciki.
Ina sonki! Saboda kina da halin kirki Khadeeja.
Ina sonki!! Saboda kina da halin tausayi Khadeejah.
Idan nace zan tsaya zaiyano kyawawan halayenki zamu dade a nan Khadeejah, a dan zaman da nayi dake na fahimci da yawa daga cikin halaiyarki Khadeejah, amma abinda nake so ki fahimta shine,
Ina sonki!!! Saboda kina da duk wasu halayen kirki da ake bukata a gurin matar aure Khadeejah.
Amma ina jin tausayin kaina da irin wannan matsanancin soyayyar da nake miki, saboda nasan kinfi karfina... ke ba ajina bane... nasan nayi karambani... nayi karambanin fara son wacce take da matsayin uwargijiya a gare ni... amma Allah ya sani INA SONKI!!!"
A daidai wannan lokacin Abdul ya shiga cikin falon da sallama, yana sanye cikin kananun kaya, fuskarshi babu alamun wasa ko kadan.
"Kamal muje ko?"
Ya fad'a yana kallonshi ido cikin ido.
"Kamal ka zama namiji mana?"
Ya fada yana dafa kafadarsa bayan ya lura da idanun Kamal ciccike da hawaye.
Khadeejah kuwa ta zama kamar mutum mutumi Tsabar amsa kuwwar da maganganunsa suke yi a zuciyarta, kanta ya kulle tsaf! Ta rasa irin amsar da ya kamata ta bashi, gashi kuma Abdul ya katse musu wannan kyakkyawar yanayin da suke ciki.
Suna daf da ficewa daga falon Mummy da Amatullahi suka dawo daga unguwar da suka je.
Sallama suka yi ma Kamal duk zuciyoyinsu babu dadi, bayan Abdul ya gama kora musu bayanin irin hukuncin da ya yanke a gurguje.
Amatullahi har ta fara hawaye saboda sabon da ya shiga tsakanin su da Kamal.
Da gudu Khadeejah ta shige cikin dakinta zuciyarta cunkushe da damuwa, kan gadonta ta zube hankalinta a tashe, kuka mai karfi ta fashe dashi kamar wata mahaukaciya.
*****
Yana tsaye a kanta hannunsa rike da zabgegiyar bukata, jikinsa sai tsuma yake yi kamar ya rufe ta da mugun dukan da zai kusa ajalinta yake ji.
"Fatima ina tambayarki a karo na karshe ki fad'a min waye ya koya miki shaye-shaye?"
"Daddy ni fa ba kowa... haka kawai na koya..."
Bulalar ya daga ya zabga mata a bayanta, da sauri ta gantsare bayanta ta zabga uban ihu kamar yana yankata.
Ya daga zai kara zuba mata da sauri ta rike bulalar,
"Daddy ni dai Gaskiya ka daina duka na..."
Ta fad'a ranta a 6ace, fuskarta a daure.
Galala ya bita da kallo yana mamaki, can kuma sai tsananin tsoro ya kamashi, dan haka ya sakar mata bulalar jikinshi a sanyaye.
"Fatima ni kike cema in daina dukan ki?"
"Eh! Duk abinda nayi ma ai laifinka ne Daddy... Tun randa na fara ganinka da Usher naji ya kwanta min a rai, kuma kaima kaga alamun yana sona tunda har yayi maka magana...
Tunda kace bazaka aura minshi ba wallahi shaye-shaye yanzu na fara a gidannan... Idan kuma kana so in daina to ka nemo shi ka aura min shi... haka kawai...? na riga na fada maka ina son shi, duk tattali da tanadin kaina wa shi nake wa, amma saboda mugun abu kace baza ka aura minshi ba... ga wannan mummunar kaddara da ya afka min.. ni gaskiya Daddy ka barni inji da abinda yake damuna..."
Tana gama fadin haka tai hurgi da bulalar can gefe ta wuce dakinta tana tangadi.
Da kallo ya bita kamar wanda aka zarewa laka.
"Baby Booo kaga labarin da nake gani a labaran duniya yanzu kuwa?"
Ta tambaye shi tana yauki da karairaya bayan ta fito daga dakinta.
Gurinshi ta nufo kai tsaye, fuskewa tayi kamar bata lura da halin da yake ciki ba, hannunshi taja ta kaishi kan kujera ta zaunar dashi, gefenshi ta zauna jikinsu yana gugar juna, da remote din t.v tayi amfani gurin kunnawa.
"Hallau dai jajirtattun jami'an tsaron jihar kaduna sun sake kamo babban dan ta'addan nan Usher a karo na biyu, karkashin jagoranci mataimakin kwamishinan 'yan sandan jihar kaduna...."
[23/04 5:16 PM] fareedah: *BARA A KUFAI!!*
*Shekaran jiya nayi kuskuren lamba, 35 ya kamata in sa, ga 36 nan*
Sake gyara zamanta tayi, fuskarta baiyane da matsanancin farin-cikin da ya gaza 6oyuwa.
Tun daga lokacin da ta fara jiyo kamshin ta rasa Usher tasa a ranta gara a fasa kowa ya rasa tsakaninta da Fatima, ganin ta kai wancan gulmar da yayi sanadin da aka kwace wayar Fatima amma dukda haka bata hakura da Usher ba ya kara kona mata rai, tunda Usher ya guje ta ko zancensa bata so taji ana yi a gidan.
"Ka gani dai Baby Booo, wannan dan iskan yaron da Fatima take ta hauka a kanshi ashe tantirin d'an ta'adda ne, shiyasa kayi min dai-dai da ka raba ta dashi, dan Allah kayi iya yinka gurin tsare tarbiyar babbar 'yark..."
Wani kakkarfar Mari da ya sauke mata a kumatu yasa ta dauke wuta na wucin gadi saboda tsabar zafi da radadin da take ji, tsawon mintuna babu abinda take gani sai wasu taurari masu tsananin haske suna gilmawa ta tsakanin idanunta.
Kafin ta dawo haiyacinta ya sake kafta mata wani Marin mai tsananin zafi a kuncinta na hagu, kunnenta ne ya dod'e babu abin da take ji sai dummm....
Bulalar da Fatima ta yar ya dauko ya fara zabga mata iya karfinsa yana bugun yana sambatu, baya ko duba inda yake duka a jikinta.
Ko da ta farfad'o daga shanye azabar marin ruwan bulala take ji ta ko ina yana sauka a jikinta, a gigice ta kwallah wani mahaukacin ihu ta fara neman hanyar tsira da rayuwarta.
"Dan ubanki ni sa'anki ne? Kinsan me yake tsakanina da Usher ne da zaki zo kina min zancen banza?..."
Ihu da hayaniyar da Hajiya Khalthum take jiyowa daga can bangaren ta kamar ba muryar Fatima ba yasa ta nufo falon da sauri.
Tasha alwashin ko kashe Fatima zaiyi da duka bazata ta6a tanka mishi ba, ta barshi yayi abinda yake so tunda shi mutum ne mai tsananin taurin kai, baya jin nasiha, kuma baya jin shawara.
"Alhaji kayi hauka ne?"
Ta fada cikin fushi ranta a 6ace lokacin da ta rike bulalar.
Fincike bulalar tayi a hannunsa ta nufi Haleema wacce bata a cikin haiyacinta, sai numfashi sama-sama take yi na wahala, baki da hanci a fashe, ga gefen kumatunta inda ya zabga mata bulala ya fashe saboda jikinta mayukan bilicin sun riga sun huda fatar ya zama mare kwari, kusan ko ina a jikinta ya fashe da sashin bulala.
Ganin irin mugun yanayin da take ciki yasa da sauri ta nufi dakin Fatima, tana kwance a kan gado tayi d'ai-d'ai ga kwalaben kayan maye nan a gabanta, da alamun su ta gama kwankwada sannan barcin yayi a won gaba da ita.
"Wallahi Alhaji kai azzalumin mutum ne, ka ci gaba da abinda kake yi ina tabbatar maka Allah bazai barka ba.
In banda zalunci da rashin adalci ya za'ayi mai laifi daban wacce zaka huce haushinka a kanta daban?
Ka ci gaba da abinda kake yi, lokacin ka ne, amma karka manta Allah da ya halicce mu yana ji kuma yana gani"
Bam taja mishi kofar da karfi ta koma can falon ta tarairayo Haleema fuskarta na baiyana tsananin tausayinta suka nufi harabar gidan, da kanta taja motar suka nufi asibiti bayan ta kwantar da Haleema a kujerun baya na motar.
*******
Yana daure a cikin tsakiyar rana jikin wani kututturen itace, ya rame yayi baki kirin, ya kara ficewa daga haiyacinsa.
Ya dad'e da fidda rai da sake sabuwar rayuwa a cikin duniya, a cikin kwanaki biyun nan Guru babu abinda yake yawan yi sai istigfari, tasbihi, hallaka, da rokon Allah ya yafe mishi kura-kuranshi ya sake bashi wata dama ko da kadan ne.
Dukda yasan mutuwa dole ce ga ko wane mai rai baya fatar yayi mutuwa irin ta kaskanci a hannun wadannan mushirikan mutanen.
Ya daga idanunshi da kyar ya sake kallon yanda suke rawa a gaban gunkin cikin tsiraici mazansu da matansu, yo cikin tsiraici mana, tunda babu abinda suka d'an kare al'aurarsu dashi sai wasu ganyayyaki.
Tsawon lokaci suna rawa da kid'e kid'e had'e da kora barasa mai tsananin wari, ko tsananin ranar da aka kwallawa basa ji, har zuwa lokacin da ya kamata ace sun shayar da Gunki Jujuba jini kamar yanda suka saba ga al'adar bautarsu.
Kwanceshi suka yi aka janyo shi kiiii a wulakance kamar wani kaskantaccen daban, gurfanar dashi sukai a gaban gunkin gwiwoyinshi a kasa, wasu karfafan mutane guda biyu ne suka bank'are shi kamar za'a yanka rago, wani kuma yazo da shar6e6iyar wuka gayawa jini na wuce da k'ok'on da zai tara jinin a hannunsa.
Runtse idanunsa yayi wasu siraran hawaye suka gangaro daga gefe da gefen idanunsa, kalmar Shahada ya fara yi a fili cikin kankanuwar murya yanda ba lallai ne suji me yake cewa ba.
Har an d'ora wuka a makogwaronsa gunkin yayi wani haniniya mai karfi kamar doki, lokaci kankani filin gurin bautar ya gauraye da wani bak'in k'ura ga iska mai k'arfi yana kad'awa.
Manyan malaman addinin ne suka matsa gaba da sauri aka janye Guru sukai waje dashi, wannan babban alama ce da take nuna gunkin baya bukatar jinin wanda suke niyyar yanka mishi.
"Ka mik'e hanyar nan kai ta gudu, kar ka kuskura kayi waige duk abinda zaka ji yana biye da kai, idan ka waiga tabbas zaka rasa rayuwarka.
Dodo Jujuba baya bukatar jinin ka a yau, lallai kana cikin mutane masu sa'a. Shekaru hamsin kenan muna mishi yanka duk wata amma sau hudu kawai irin wannan ya ta6a faruwa"
Daya daga cikin malaman bautar ne yake mishi wannan bayanin lokacin da suke kwance mugun daurin da akai mishi hannu da kafa.
Dukda rashin karfin jikin da yake fama dashi haka ya zube a kasa yana godiya ga Allah, wani dan tunani da yayi yasa ya yanki hanyar da suka nuna mishi da gudu, ba tare da tunanin ko hanyar zata 6ulle dashi babbar titi ko bazata bulle da shi ba, shi dai kawai babban burinshi ya samu tsira daga hannun mushirikan mutanen nan.
Guru Allah ya tsare.
*****
"Zan sake tambayarka a karo na karshe, ka fada min su waye kake yiwa aiki?"
Bai jira cewarshi ba ya sake danna madannin mai kama da gurin kunna glob, nan take injin ya fara wujijjiga Kamal dama da hagu sama da kasa yana ta rawar dari kamar an tsoma shi a ruwan kankara.
Tun da Commissioner ya tambayeshi a karon farko ya fada mishi sunayen Honourable Sumaila Sanatan Kano ta tsakiya, da Alhaji Tanko daya daga cikin 'yan majalisar jihar kano, da Honourable Ghali Na'Allah dan takarar Gwamnan jihar kaduna a jam'iyyar adawa a matsayin wadanda yake yiwa aiki yake ta gana mishi azaba da injin mai wujijjiga kwakwalwa da jikin masu laifi.
Tun Kamal yana iya amsa tambayoyin da yake masa har ya kasa amsawa, lokaci kadan ya fice daga haiyacinsa, tsananin wujijjiga jin kanshi yake da wani mugun nauyi kamar an dora masa.
"Zaka fada min gaskiya ko bazaka fada min ba??"
Ya sake tambayarsa cikin tsawa yana kashe injin azabar yana sake kunnawa.
"Bari mana Yallabai, kana so ka kashe shi ne?"
Abdul ya fada ranshi a bace lokacin da ya sauke hannu ya kashe injin gaba daya.
Gurin Kamal ya nufa ya tarairayoshi jikinsa yana kallon halin da yake ciki hankalin sa a tashe, tunda Commissioner yaje ganin Kamal din yayi mishi umarnin ya basu guri akwai tambayoyin da zai ma Usher, haka nan ba dan ranshi yana so ba ya fice daga gurin, jin shirun yayi yawa yasa Abdul ya koma ciki dukda ba'a bashi umarni ba dan ganin wane hali ake ciki?
Shine ya tadda Kamal yana neman halaka saboda azaba.
"Miye kake yi haka Abdul? Waye ya baka izinin shigowa ina gudanar da aiki na?"
Wani mugun kallo ya watsa mishi idanunshi jajur, jijiyoyin kanshi sun tashi rudu-rudu saboda tsabar 6acin rai.
"Sir! Haka muka yi da kai?"
Ya tambaye shi fuskarshi a daure.
"Ni kake yiwa magana haka Abdul?"
Ya tambaye shi da mamaki a fuskarsa yana nuna kanshi da yatsa manuniya.
Jingina Kamal yayi a hankali jikin kujerar da yake zaune, da takunsa na cikakken namiji mai ji da jarumta yake takawa a hankali har ya isa gaban Kwamishinan, fuskarsa na baiyana zallar bacin ran da zuciyarsa take ciki.
"Tun farko na fada maka, na samu nasarar kama Usher ne saboda ya amince lallai zai fada mana zallar gaskiyar wadanda yake yiwa aiki.
Tunda ya fad'a maka me kake so ya sake cewa? karya kake so yayi maka?"
Kallon shi yayi wani kallo mai kama da na zargin ko Kwamishinan ya fara kar6ar cin hanci ne.
"Kafin ya amince in kama shi saida na daukar mishi alkawarin baza mu gana mishi azabar da zai fidda shi a haiyacinsa ba..
Yallabai ina rokon ka dan Allah ka bari mu fuskukanci matsalar nan a nutse👏🏻 mu aikinmu kamo masu aikata laifi ne kawai ba wai mu yanke musu hukunci ba.
Dan haka ka bari mu tura shi kotu ta tantance gaskiya ko karyar shi ta yanke mishi hukunci.
Dan Allah👏🏻👏🏻"
Yana gama wannan maganar ya nunawa Kwamishina hanyar fita daga cikin cell din hannunsa daya yana sanye cikin aljihun wandon sa.
Fuskarshi kawai ya kallah yaga yayi mishi wani mugun kwarjini, dan haka sukwi-sukwi ya fice daga gurin ranshi a 6ace.
Dan sam ba haka yaso ba.
Ringing din wayarsa da yake jiyo wa daga cikin aljihun wandonsa yasa ya rage saurin da yake yi Ya zaro wayar daga aljihun sa.
"Wallahi duk yadda muke tsammanin al'amarin ya wuce nan, ka jira ni zuwa yamma, duk shawarar da na yanke zan kira ka"
Yana gama fadin haka ya katse wayar, da sassarfa ya fice daga station din ba tare da ya kalli kananun ma'aikata da suke ta k'amewa suna sara mishi ba.
Yana shiga motar direba yaja suka bar gurin, da kallo yabi bayan motar har suka 6acewa ganinsa, sai tashin kurar motar kawai yake gani.
Wata lamba ya lalubo a cikin wayarsa ya danna kira ya kara wayar a kunnensa, a zuciyarsa sai tunanin irin maganganun da yaji Commissioner yana yi a waya yake yi, ko ina maganganun suka dosa?
"Hello Yusuf! Ka saurare ni da kyau, na canza shawara.
Yaran nan da kuka kama kar ka kawo su nan, kuma bana so kowa yasan da maganar kama su banda ku hudunnan, ku wuce dasu wannan 6oyayyen gidan na unguwar rimi, zan shigo gobe da rana in gansu"
Saurarawa yayi aka amsa mishi daga can bangaren sannan ya katse wayar, cikin cell din ya koma gurin Kamal, wanda har lokacin bai gama dawowa cikin haiyacinsa ba, dan ya wujijjiga ba kadan ba.
Tun daga bakin kofar ofishin kananun ma'aikata suke mika mata gaisuwa cike da girmamawa, sun santa farin sani.
Amaryar Oga ce wacce ta kasance mafi soyuwa a gurinsa, tana sanye da babban hijabi har kusan kafarsa, ta boye kwayar idanunta cikin farin gilashi mai ban sha'awa, biye a bayanta Khadeejah ce hannayenta rike da kwandunan abinci guda biyu.
Da murmushi a fuskarta take amsa musu gaisuwa har ta dangana da Ofis dinshi, fuskarta dauke da tattausan murmushi tayi sallama kafin ta shiga.
Hankalinsa gaba d'aya ya tattara akan laptop din da yake gabansa yana bincike akan D.P.O da Chairman yayi amfani dashi a wancan lokacin da suke son kashe Kamal.
Kasancewar rayuwa tana iya sauyawa ako wane lokaci, da kuma tsawon lokacin da aka dauka daga wancan lokacin zuwa yanzu, da kuma taraiyarsa da 'yan siyasa yana biya musu bukatunsu wannan d'an sandan ba kowa bane a yanzu face Commissioner Musa Musa na jihar kano.
Shiru yayi yana tunani, domin Musa Musa babban abokin Commissioner Sunusi Isa ne, dukda baida tabbacin ko har yanzu Musa Musa yana tare da Honourable Sumaila yasan dole duk yadda za'ayi zasu nemi hanyar fitar da Usher daga cikin cell ba tare da anje kotu ba, ko kuma su sa a kashe shi a cikin cell din dan kar aje kotu ya tona musu asiri.
Musanman a yanzu da za6e yake daf, duk wani abu da zai zama cikas a siyasarsu baza su so shi ba.
Sake zurfafa yayi cikin tunanin wayar da yaji Commissioner yana amsawa d'azu.
A daidai wannan lokacin ne yaji tattausan muryarta tana sallama, d'ago kai yayi ya kalli kofar sukai tozali da juna, da murmushi yake jifanta har ya karasa bakin kofar ya tallabota a kafadarshi suka shiga ciki, akan kujerar zamanshi ya zaunar da ita yana matsa mata yatsun hannunta.
"Ya Abdul ina yini?"
Yaji muryar Khadeeja tana gaishe shi, sai a lokacin ya lura tare take da Aysha.
A mutunce ya amsa mata hankalinshi yana kan matarshi.
Kwandon abincin hannunta ta ajiye guda daya akan teburin gurin, ta kasa cewa komai, sai Aysha ce tace
"Daddy Khadeejah fa ta kawo wa Kamal abinci ne, ko zata iya ganinsa?"
"Eh mana, ina zuwa Baby"
Ficewa yayi Khadeeja ta bi bayanshi da sauri.
"Kiyi k'ok'arin saka shi yaci abinci, dazu ina waje Commissioner ya dan wahalar dashi, amma yanzu da sauki sosai, jirani a nan ina zuwa"
Ciki ya shiga ya tallabo Kamal ya fito mata dashi waje, wani dan karamin Ofis ya shigar dasu sannan ya koma gurin matarsa.
Ganin yanda yake ya wahalce yasa ta she kwandan da sauri ta isa gurinshi tana k'ok'arin tare shi, gani take kamar jiri ke dibar shi.
Da sauri ya dafe wani karamin tebur da yake kusa dashi, ya zauna dakyar akan kujera yana kallon yanda ta rame cikin kwana daya kawai da aka kama shi.
Hawaye har sun fara zuba a idanunta dan tsananin tausayinshi, ga wata zazzafar soyayyarshi da take ji yana ninkuwa a cikin ko wane dakika na rayuwarta.
Hannu yasa ya ya fito ta alamar tazo gare shi, yana ta kokarin dora murmushi ko da na yake ne a fuskarsa.
Yaji dadin ganin ta ba kadan ba, soyayyarta da yake ta kokarin dannewa a ransa sai tasowa take yi tana neman fasa kirjinshi.
Hannunsa duk biyu ta kama da nata hannun tana kuka sosai, ji take kamar ta janyo shi cikin jikinta saboda tsabar so da tausayinshi da take ji.
"I... I love... u... Ya Kamal"
Ta fada muryarta na rawa saboda kukan da take yi.
Lumshe idanunsa yayi yana jin wani sanyin dad'i yana kwaranya a lungu da sako na jikinsa, nan take yaji wani matsanancin kwarin gwiwar da bai ta6a ji ba a jikinsa, yana jin zai iya fuskantar komai da kowa ya rungumi duk irin hukuncin da za'a yanke mishi matukar Khadeejah na gefenshi a matsayin masoyiyarsa.
Yalwataccen murmushi ne yake baiyane a fuskarsa, janyota yayi sosai kusa dashi numfashinsu na bugun juna, dama... dama... dama ace Khadeeja a matsayin matarsa take a daidai wannan lokacin? Tabbas da babu abinda zai hana shi sa harshe ya lashe hawayen fuskarta tsaf, a yanxu da babu damar hakan sai hannunsa yasa yana share mata hawayen, had'e da furta mata tausasa kuma zak'ak'an kalamai masu sanyaya zuciyar masoyiya, yana fada mata irin yadda soyayyarta yayi mishi mugun kamu, da kuma irin tarairayar da zaiyi mata idan Allah ya nufa sukai aure.
Lokaci daya ta daina kuka sai murmushi take yi tana sunne kanta cikin hijabi alamun jin kunya, dakyar ta iya janyo kwandan abincin ta zuba mishi, yana ci a hankali tana zuba mishi shagwa6ar ya cinye gaba daya, tana fada mishi ita da kanta ta girka mishi.
"Ashe dai 'yan matan ta damu dani sosai har haka?"
Ya tambaye ta yana kashe mata idanu😉.
Fari tayi da idanunta sannan ta tura baki
"Allah kuwa Ya Kamal jiya banyi barci ba..😩😢 kuka nai tayi ina tunanin wane hali kake ciki? Sai kuma daga baya na tashi nayi sallah na roki Allah ya dora mu akan azzalumai"
"Ameen Durling girl😘😘"
Da sauri ta kalleshi tana zare ido, babu wanda ya fado mata a rai sai Usher, sai kuma tayi murmushi ta saukar da kanta kasa.
[24/04 7:34 PM] fareedah: *BARA A KUFAI!!*
*37)*
"Ya akayi 'yan matana?"
Ya tambaye ta da murmushi a fuskarsa.
"Ba komai fa samari... kawai yanda ka kira ni da sunan sai ka tuna min da Sweetheart Usher, mutum mai saukin kai da ban dariya, ga burgewa da iya kalaman sace zuciyar 'yan mata"
Murmushi ya sake yi kad'an, sai kuma ya daure fuska
"Ashe daman ba ni kike so ba?"
"Laaaa... Kaine mana. Ai duk wadannan halayen nashi da na lissafo kai kana ninkinsu dari bisa dari"
Sai kuma ta kwa6e fuska cike da shagwa6a tace
"Kuma ma bayan a jikin wannan Kamal din ne aka cire wancan Kamal din? Banbancinku kadan ne masoyi😘"
Sai kuma ta rufe fuskarta cikin kunya.
"Sai da kika gama cemin I love u wujiga-wujiga shine zaki wani ji kunya? Bude idanunki kawai ki ci gaba da jik'ani da zak'ak'an kalaman soyayyarki mai dad'i..."
Dariya sukai gaba daya, fuskokinsu na baiyana tsananin kaunar da suke wa juna.
Fiye da minti ashirin da biyar tana tare dashi tana debe mishi kewa, saida Aysha ta leko tana tsokanarta da tsuntsayen soyayya sannan ta mishi sallama suka wuce gida.
*****
*"Boyayyen sirrin Honourable Sumaila Sanatan jihar kano ta tsakiya ya baiyana..."*
Abinda idanu da bakinsa sukai arba dashi kenan a farkon sad'arar farko na bangon Jaridar.
A tsorace us sake daga jaridar ya tabbatar dai abinda aka rubuta kenan ba gizo idanunshi suke mishi ba.
Cikin sauri har yana tuntu6e ya koma gurin mai gadi da ya bashi sakon jaridar a nad'e wai inji wani mutumi.
"Malam Iliya wai kace waye ya baka wannan sakon ka bani?"
Ya sake tambaya bakinsa har yana tuntu6en harshe.
Kallonshi yayi yana mamakin me kuma ya tsorata shi lokaci guda haka? Dukda dai har su ma'aikatan gidan sun fahimci kwana biyun nan iyalan gidan musamman mai gidan basa cikin nutsuwa, dan wani lokacin ko wucewa Honourable zaiyi zuwa masallacin kofar gidansa yana jinshi yana sambatu...
"Yalla6ai wani bawan Allah mai shigen Ustazu ne ya bani d'azunnan wai idan ka fito in baka, bayan ya tambaye ni kana gari ni kuma na tabbatar masa kana nan"
Rasa abinda zai sake cewa yayi, dan haka ya juya cikin gidan buguzum-buguzum da babbar riga yana sake karanta jaridar.
*"Manyan mutane uku a kasar nan, wadanda suke rike da manyan muk'amai, wadanda sukai fice gurin aikata aiyukan alkhairi a idanun jama'a 6oyayyun sirrikansu sun baiyana.*
*Ashe su din kura ce da kallabin fatar akuya....*
*Ku ci gaba da bin jaridar mu sannu a hankali zamu ci gaba da tona musu asiri d'aya bayan d'aya*"
Sai aka saka hotunansu su ukun suna dariya, wani hoton kuma an nuno shi ne tsaye jikin wani ginin masallaci da ake yi ya bada tallafi, fuskarsa dauke da murmushi.
A kasan hoton aka rubutu
*"Musa a fili... fir'auna a zuciya... ku tambayeshi ko ya tuna da labarin Kamaluddeen wanda suka ta6a samun sa6ani dashi a lokacin da yake a matsayin Chairman? Haske yana daf da baiyana...*
Iya inda labarin ya tsaya kenan, dukda sanyin A.c da ya wadaci lungu da sako na tafkeken falon sai tsiyayar zufa yake yi, wani zafi yake ji ako ina na jikinsa kamar mai saukar zazza6i, lokaci kad'an ko ina na jikinsa sai kad'awa yake yi.
Kanshi ya kulle gam, ya rasa wane irin tunani ya kamata yayi, Kamaluddeen?
Tofin miyau ya fara a gefen dama da hagunsa yana addu'ar mugun ji da mugun gani Allah ya kare😹
Karar wayarshi da yaji ya rarumo ta a tsorace ya kara a kunnensa ba tare da ya duba mai kiran nashi ba.
"Hello ranka ya dade barka da yamma, sunana Lubna.
Ina kiranka ne daga nan gidan Jaridar Haske maganin dubu.
Mun samu wata zazzafar masaniya ne akan 6oyayyun Sirrikanku kai da manyan abokan ka, to ance mu tambayeka waye Kamaluddeen? Shine na kira mu tambayi Karin bayani kafin mu fitar da labarin, kasan idan labarin ya fita a dunkule zaifi daukar hankalin mutane.
Me zaka ce akan haka ranka ya dad'e?"
"Wwwwwannan labarin kazafi ne, kuma ba aikin kowa bane face na 'yan adawa..."
Kit ya katse wayar yana numfarfashi kamar wanda yayi tseren gudun kilomita dari.
Wani kiran ne ya sake shigowa a dayan wayar tasa ya kai hannu ya dauka a tsorace
"Ranka ya dade daga gidan Jaridar Gaskiya...."
Kit ya yanke wayar, cikin mintuna biyu wayoyinsa duka ukun suka dauki ruri kuma duk da bakin lambobi ake kiransa, kin dauka yayi saboda tsananin firgita da tashin hankali da yake ciki.
Daga karshe ma sai ya kashe wayoyin gaba daya.
Kayan cikinsa ne suka takura suka dunkule waje guda, ji yake kamar zaiyi kashi a gurin, a galabaice ya mike dan zuwa bayi.
Takun tsinin takalminta da yake ji tun daga nesa tana nufo cikin falon yasa ya dakata dafe da matarsa da hannu biyu yana jiran karasowarta.
"Haleema har sun dawo ne?"
Ya tambayi kansa a fili, dan yasan duk gidan ita kadaice 'Yar gayu ta bugawa a jarida.
Fatima kullum cikin hijabi take kuma kwalliyarta saffa-saffa ne, ita kuwa Hajiya Khalthum sam duniyar ma bata a gabanta.
Baki da hanci bude yake bin Fatima da kallo tun daga sama har kasa, atamfar Holland ta saka, amma an ciwa atamfar mutunci ta hanyar yin dinkin riga da sket, rigar ta matse ta gam musamman daga wurin kirjinta, kusan rabin nonuwanta a waje suke.
Shima sket din ya kamata tsam ta gurin uwawun, sai daga kasa aka bada fadi sosai saboda a samu a wala gurin tafiya.
Sa6anin hijabin da ta saba sakawa yau gyale ta rataya a wuyanta irinna gogaggun 'yan mata, fuskarta sai sheki take yi tamkar Zahra a cikin taurari, kwalliyar yayi mata kyau sosai da yake daman ita din mai kyau ce.
Daurin ture kaga tsiya ta k'wama a kanta, ta kawo cingam ta jefa a bakinta tana taunawa a yangace, kamar anyi mata dole.
"Daddy barka... makullin mota zaka bani zamu fita da su Adam zuwa asibiti gurin Mummy"
"Amma Fatima da wannan shigar...."
"Dan Allah karka ce komai Daddy, miye amfanin fuska biyun da nake maka tunda babban mummunar halin da nake 6oyewa ya baiyana a gare ku?
Shifa imani da kake gani a nan yake"
Ta nuna saitin zuciyarta da murmushi a fuskarta.
"So ka kwantar da hankalinka, duk wani hijabi ba shi bane.
Kuma bayan shaye-shaye da d'an shakatawa da nake yi babu wani mummunar aiki da nake yi kuma, su ma daga ranar da ka aura min Usher zan daina gaba daya"
Tana gama maganar ta dauki daya daga cikin makullan motocin da ta gansu akan wani dan karamin tebur, juyawa tayi ta nufi hanyar fita tana karkada uwawu.
"Daddy wannan makullin wace motar ce?"
Ta tambaye shi a daidai lokacin da take daf da ficewa daga falon.
Suman tsaye kawai yayi kamar wani mutum-mutumi, tsoro ne ya kara kama shi, a cikin satinnan gaba daya munanan al'mura ne suke ta kawo mishi hari daya bayan daya.
Allah yasa dai ba mummunar lokacin sa bane ya fara kamar yadda mai gobe zatai kyau ya ta6a sanar dashi, kirjinsa ne ya buga daram lokacin da ya tuna sharadin da mai gobe zatai kyau ya bashi akan saduwa da mahaukaciyar nan.
Kar ya kuskura ya tsarkake ko kwana daya a cikin kwanaki sittin bai sadu da ita ba, gashi yau kwananshi biyar baya tare da ita.
Ko a wane hali ma take ciki a can gidan sa na Abuja?
*****
Bindigar ya bude ya nuna mishi mazaunin harsasan, duk harsashi shida suna ciki.
Rufewa yayi yana mishi wani murmushi da ya rasa gane ko murmushin menene.
"Ka gani ko? Na nuna maka ne dan ka tabbatar bindigar ba ta wasan yara bace, a duk lokacin da na harba kunamar bindigar few zata shiga kunnenka na dama ta fita ta kunnen hagu.
Dan haka ina baka shawarar karka kuskura kazo min da wasa.
Ina fatan ka fahimta?"
A hankali kuma a wahalce ya daga kansa alamar eh ya gane.
Wayarsa ya dauko ya kunna, lambar honourable Sumaila ya lalubo wacce akai saving da Excellency ya danna wa kira.
Ringing din farko a na biyu ya dauka, da sauri Yusuf yaja kunamar bindigar ya saita kan Killer da ita, sannan ya kara mishi wayar a kunnenshi.
"Hhello... Excellency.."
Ya fada a tsorace bakinsa na rawa, danne bakinsa daya daga cikin yaran Yusuf yayi da karfi suka dauke wayar daga kunnensa.
Shi kuma ta can bangaren sa da yake yana cikin damuwa bai fahimci a yanayin da killer yai mishi magana ba.
"Killer... wai kai wane irin wawan dabba ne? Tsawon kwanaki biyu kenan ina kiran wayarka a rufe, tunda na tura ka kashe Usher da ka tarar an kama shi me ya kamata kayi?
Ba sai ka nemeni ko a waya kayi min bayani ba? Amma da yake kai dakiki ne saika barni ina ta fargabar a wane hali kake ciki?
To ka tabbatar ka shigo kano gobe da sassafe dan an samu matsala..."
Kit Yusuf ya katse wayar bayan ya gama nad'ar duk maganganun Honourable Sumaila.
Harara ya gallawa Killer sannan yaja dogon tsaki,
"Yanzu kai a jikin wannan mutumin da bai dauke ka da daraja ko kadan bane har kaga Ubangida?
Da mutuncinka da kiruciyarka ka tsaya zaka karar da rayuwarka a wulakance, tunda kaga haka shine mafi alkhairi a gare ka saika bada himma"
Ga mamakinsa ko da ya kalli Killer hawaye ne wasu ke korar wasu a idanunsa.
"Ai bakai kuka ba tukunna, kila sai ka ganka a gaban igiyar rataya za'a rataye ka a matsayin hukuncin d kotu ta yanke maka sannan zaka yi nadama, wanda a lokacin baida amfani"
Tun lokacin da sakon Usher ya riski Honourable wanda Abdul yayi amfani da wata bakuwar lamba ya tura mishi a matsayin Usher ne ya turo su killer ya basu adireshin yace suje kaduna su tabbatar sun kashe Usher.
Ya kuma gargadesu akan lallai kar su kuskura su dawo mishi da zancen banza, ko kuma suce an samu akasi Usher ya gudu.
Abinda basu Sani ba talala Abdul ya shirya musu, suna zuwa gidan basu da masaniya zagaye yake da yan sanda, 'yan sandan kuma amintattun yaran Abdul ne.
Cikin lokaci kadan aka kame su gaba daya, da yake su biyar ne dukda Killer.
A Boyayyen guri aka boye su ko Commissioner baisan da labarin kama su ba, aiki Abdul yake cikin kwarewa yana burin samun kwararan hujjoji a hannu kafin ya gurfanar da wadannan azzaluman a kotu.
Kuyi manage da wannan, ina ta ci gaba da typing😹😹😹😹
[26/04 9:06 PM] fareedah: Murmushi sukai zukatansu cike da farin ciki lokacin da Abdul ya gama zaiyyanewa Aysha kad'an daga cikin irin ci gaban da yake samu a bincikensa.
Khadeeja ce ta dawo kusa da Ayshan ta tsaya ta sake mika mishi gaisuwa dukda sun gaisa da farko.
"Ya Abdul barka da dare, nima mun gudanar da komai kamar yadda ka tsara mana, saida na tabbatar sakon ya iske shi sannan na kira shi a wayar kamar dai yadda ka tsara.
Ya rude fa ba kadan ba, in Allah ya yarda komai zai zo mana da sauki fiye da yadda muke tsammani"
"MashaAllah, haka muke fata"
Aysha ce ta 6ata fuska tana sake gyara zamanta a gaban a gaban laptop din, da yake video call suke yi.
"Sweetheart wai kana nufin yau ma bara ka dawo gida ba?😩😩 ni dai Allah na gaji da rashin ganinka😩😩 su Abee duk sun dame ni da tambayar yaushe zaka dawo?
Pls dukda yau ba girkina bane ni dai ka dawo, ina son jin dumin jikinka a gidannan😩😩"
Saida yayi murmushi jin abinda tace, cikin rarrashi yace
"Baby rigima ko? Kiyi hakuri gobe zan shigo da wuri"
Kukan shagwa6a ta saka mishi wacce babu ko digon hawaye a cikinta, Khadeeja kam da taji maganar ya fita daga sahunta ya koma sahun masoyan ma'aurata sum-sum ta fice daga dakin ta nufi bangaren su.
"Daddy yau kwana biyu kenan fa... kana cikin garinnan bawai baka nan ba ace mun raba gurin kwana... ni dai ka dawo... ni dai ka dawo...😩😩😩"
Dafe kai yayi yana murmushi, sassauta murya yayi ya fara rarrashinta da tausasan kalamai
"Ko kina so in dawo gida wasu azzalumai su kashe Kamal?"
Shiru tayi kamar tana tunani, a sanyaye saita girgiza kai alamar a'a.
"Yauwa Baby na, to kad'an ake jira in kauce a samu damar kashe Kamal ko kuma a sake shi ya gudu.
Shiyasa duk kwana biyun nan ina nan ina gadinsa nak'i matsawa ko ina, zuwa litinin zan tura case dinshi kotu.
Kinga a wannan lokacin zaki fara naki aikin a matsayin ki ta lauyarsa, ko kin fasa?"
Ya k'ark'are maganar da tsokanarta.
"Ah haha de, ya za'ayi in fasa? Ina nan akan baka na"
Ta amsa da dukkan kwarin gwiwarta.
"Yauwa baby, shiyasa tun kafin zuwa kotun nake kara tattara miki hujjojin da zasu taimaka miki gurin wanke shi a kotu"
"Yauwa Sweetheart, shiyasa kullum nake kara sonka. Amma Daddy kana ganin zan iya?"
"Why not? Ni nasan zaki iya sosai ma kuwa Baby, karki sakawa ranki karaya kinji koh? Ina nan a gefenki a matsayin miji, abokin shawara, kuma mai kara miki kwarin gwiwa da baki tallafi a kan aikinki.
Case din Kamal babban case ne kuma in Allah ya yarda nasara a tsaginmu take, cikin lokaci kankani sunan Barr Aysha Azzahra'u zai tumbatsa a ciki da wajen 9ja"
Dariya ta kyalkyale dashi ranta fes, zuciyarta cike da nishadi da jin dadin maganganunsa.
"Ina sonka mijina... Allah ya barmu tare"
"Ameen ya Allah.
Ina Small Ard'o? Kwana biyu nayi kewarshi sosai fa"
Rigarta ta yaye sosai cikinta ya baiyana, yayi girma sosai, saboda kyan fatarta cikin yayi shar gwanin ban sha'awa.
"Hey... Ardo ya kake? Daddy yayi kewarka sosai fa, ina fatan kaima kayi kewa ta?"
Motsi dan cikin yayi daga dama zuwa hagu kamar yaji me babanshi yace mishi, murmushi tayi kawai.
"Ka ga wannan babban alama ce da yake nuna Shima yana kewarka"
Hirarsu suka ci gaba da yi kowa yana baiyanawa dan'uwansa yanda yayi kewarsa, tsawon lokaci sannan sukai sallama.
A daidai lokacin Yasmin tayi sallama ta murda hannun kofar falon ta shiga, fuskarta dauke da murmushi.
Neman sasanci take yi da Ayshan sosai tsakanin jiya da yau, tunda wannan sa6anin ya faru ta dauke mata fuska, kamar dai ita ta kar zomon.
Aysha ta janye jikinta daga gare ta gaba daya kuma ta janye yaran ta.
Ba gaba take yi da ita ba, domin idan suka hadu a falo suna gaisuwa, amma yadda suke zama da suyi ta hira da wasa da dariya Ayshan duk ta daina.
Harsun koma sun dinke da wanda aka samu 6arakar dashi amma ita an barta a tashan wala.
"Aysha magana nazo muyi"
Yasmin ta fada bayan ta nemi guri ta zauna akan kujera.
"Ok ina jinki"
Ta fada hankalinta yana kan laptop din gabanta tana danne-danne.
"Aysha dukda bansan laifin da nayi miki ba pls ina mai baki hakuri, kin janye su Ummita daga gare ni kema kin dinke min.
Bana jin dadin irin wannan abin da yake faruwa Wallahi, kar mu bari shaidan ya shiga tsakanin mu ta hanyar rusa kyakkyawar alakar da take tsakanin mu mai kama da ta ya da kanwa, ba irin na kishiyoyi ba.
Me yake faruwa ne..?"
"Look Yasmin, pls karki nemi ki sake 6ata min rai.
Ko da kike gani na kamar ina da kananun shekaru na wuce kizo min da salon rainin hankali ban ranfo ki ba.
A tunani na kin dauke ni kamar yadda na dauke ki da kima ashe Sam ba haka bane, kinsan wani abu da na fahimta a zaman kishiya da kishiya? Duk yadda mijinsu zaiso ya wulakanta daya daga cikinsu yana samun nasara ne idan d'ayan ta bashi had'in kai gurin cusgunawa dayan.
Dan Allah wata rana idan kuna hira ki tambayi Abdul ina barinshi ya kawo min korafinki a gabana? Wallahi ko da wasa ban ta6a bashi fuskar da zai zo yai min korafinki ba balle har ya fadi munanan kalamai a kanki.
A ganina wannan matsalarku ce can tsakaninku, wai amma har kece zaki zauna Abdul yana maganganun banza a kaina baki taka mishi burki ba.
Ture batun wannan ma, kece da kanki kika turo min su Abee wai suzo guri na in basu abinci, shiyasa naga gara in kama yara na kawai in kina ganin wani alfarma ne kike min na kulawa da su.
Abinda kuma ya sake kona min rai game da ke shine yanda kuka kulle kofarki da safe yara sukaita bugawa dan su gaishe ki da babansu kika ki budewa, kika kwashe wayoyin mijinki kika kulle dan kar in kira shi.
Shiyasa naga gara in kama kaina da yarana tsakanina dake, miji kuwa namu ne gaba daya kowa kissarta ta kwace ta a gurinshi"
Sani matsanancin kunya ne ya kamata, ta sani dukda Abdul yafi son Aysha a kanta ko da wasa Ayshan bata ta6a bashi kofar da zai wulakanta ta ba.
Wasu abubuwan ma ko Ayshan bata so idan Yasmin ta nuna tana so haka take biye mata su tilasta Abdul yayi musu.
"Kiyi hakuri Aysha, na kar6i laifina.
Dan Allah komai ya wuce a tsakanin mu, in Allah ya yarda hakan bazai sake faruwa ba"
"Shikenan! Ya wuce. Kema kiyi hakuri"
Lokaci kankani suka fahimci junansu, aka yafi juna.
Nan da nan suka sake dinkewa, sai gasu suna hira harda dariya.
Ko da su Abee suka dawo kwashe su Yasmin tayi zuwa bangaren ta, tayi musu wanka ta basu abinci.
******
Sannu Sannu yake dogarawa da 'yan sandunanshi guda biyu yana bin gefen titi har ya isa cikin layin.
Yana sanye ne da farar jallabiya kar, ta sauka mishi har kusa da gwiwarshi, kafar wandonshi daya da aka nannad'e har sama shi ya tona asirin guntun kafa d'aya ta rage masa a cikin biyu.
Duk inda zai wuce idan yaga taron mutane biyu ko uku ko daya baya gajiya gurin yi musu sallama irinta addinin musulunci.
Wasu su amsa mishi wasu kuwa su kalleshi su watsar, dukda ya shiryu dai-dai gwargwado har yanzu basu daina mishi kallon wannan tantirin dan shaye-shayen ba.
*(Rashin adalcin wasu daga cikin mutanenmu kenan, maimakon a lokacin da muka ga wani mai aikata sa6o yana k'ok'arin shiryuwa mu tallafe shi da kyawawan dabi'u mu bashi namu gudummuwar a'a, a maimakon hakan ma sai mu ringa nuna mishi kyama da tsoron mu'amala dashi a fili.)*
*Allah yasa mu gyara)*
Shi kam Kabiru ko a jikinsa bai damu da yanda suke amsa shi ba har ya isa kofar gidan su Figo.
"Assalamu alaikum ya 'yan uwa"
Kalmar da ya fara fada kenan da ya karasa kusa dasu, har wani kalkale murya yake irin ta larabawa.
Daga Khalid har Faruk murmushi suke yi, fuskokinsu na baiyana tsananin farin cikin ganinsa.
"Kabiru yaushe aka sallamo ka? Dazu muke maganar ya kamata mu sake leka wa gurinka.
Ya jikin naka?"
Faruk ke fadin haka bayan ya ajiye littafin al-akhdari wanda kaninsa ke karanta masa.
Mikewa yayi ya tarbo Kabirun har yayi mazauni a gefen tabarmar da suke zaune.
"Jiki Alhamdulillahi Figo, na samu sauki sosai Wallahi, jiya da safe aka sallamo mu.
Nagode da dawainiyar da kukayi ta yi dani, Allah ya bar Zumunci Figo"
Daure fuska yayi yana harararsa
"Figo kuma?"
"Au! Yi hakuri aboki Faruk"
Dariya sukai gaba dayansu, hira suka dan ta6a akan irin kallon da mutane suke musu.
"Wallahi ni Kabeeru ko a jikina ban damu ba, a kullum Khalid yana kara min kwarin gwiwa kan cewa kar in damu da me mutane zasu ce a kaina, in ci gaba da tsarkake zuciya ta kawai, komai in zanyi inyi domin Allah.
Shiyasa ka ganni nan idan ba masallaci ba to ina gida, sai kuma idan an samu faskare inje inyi a biya ni.
Yanzu rayuwata sakayau nake ji na, idan Khalid ya tafi makaranta ina gida har ya dawo"
"MashaAllah, haka ake so. Nima a kullum Inna tana kara kwantar min da hankali da yimin nasiha ne, Allah ya kara shiryar damu akan hanya madaidaiciya"
"Ameen ya Allah"
Suka amsa gaba daya.
Al-akhdari Khalid ya ci gaba da karanta musu suna sauraransa cike da nutsuwa da maida hankali.
*****
Abun duniya fa ya taru yayiwa Alhaji Tijjani daurin demon minti, abinda yake gani yafi shan ruwa sauki sai gashi yana neman ya gagara shi.
Duk yadda yake tsammanin al'amarin yana neman ya tsallake tunanin shi.
Yau kwanaki biyar kenan a cikin kwana bakwai da Tsumburbura ta bashi na cewar lallai ya tabbatar ya kashe iyalanshi.
Sai gashi ko k'udan da yake rayuwa a inda Dr. Abida da yaran ta suke ya kasa kashe wa.
Abin kamar wani aikin asiri, ko d yake ya tabbatar suma su Abidan ba haka suke zaune ba, domin duk wasu zafafan tsafe-tsafe da duk aljanun da suke mishi aiki ya tura sun kasa kashe su.
Ko samun damar kusantarsu ma basa yi, yana cikin mugun tashin hankali ba dan kadan ba.
Ana cikin haka ne kuma bagatatan ya tsinci labarin kama Kamal a cikin wata jarida da aka aika mishi da ita har gida ta hannun P.A.
Ya juya P.A danbu da taliya kan cewa wa ya kawo jaridar ya tabbatar masa da cewa amintaccen direban Alhaji Musa ne, babban amininsa.
Ya tambaye shi yace Shi bai aika masa da wata jarida ba.
Lokacin da ya bude shafin farko yayi arba da fuskar Kamal wacce ta dauku sosai a hoton a matsayin dilan miyagun kwayoyi zawo ne kawai bai sake a zaune ba saboda tsananin tashin hankalin da ya shiga.
Fuskar Kamal dinsa marigayi yake gani sosai a cikin fuskar wannan Kamal din.
"To ko dai shine bai mutu ba?"
Ya tambayi kansa da kansa. Da sauri ya kore wannan tunanin bayan ya tuna irin yadda ya yayyanke wasu sassa na jikin Kamal din, bazai yiwu ace yana raye har yanzu ba.
Wayar shi ya janyo ya dannawa Gwamnan jihar kaduna kira da yake mutuminsa ne, dukda suna yawan samun sa6ani a wasu lokutan musanman gurin taronsu na gwamnoni.
"Your Excellency barka da.."
Aka fada daga can bangaren cikin raha bayan an dauki wayar da sallama.
"Ranka ya dade dan Allah wata alfarma nake nema idan zaiyi wu"
Alhaji Tijjani ya fada yana Sosa keya bayan musayar gaisuwar da ya gudana a tsakaninsu.
"Ina jinka Excellency Allah yasa alfarmar bata sha karfin mu ba"
"Wallahi yaro na ne 'yan sandan jiharka suka kama a matsayin mai safarar miyagun kwayoyin nan..."
"Yaronka dai? Kenan kana nufin kai yake yiwa aikin?"
Ya tambaye shi da mamaki a fuska da muryarsa.
"No.. a'a ba haka nake nufi ba fa.
Yaro na ne na ciki na wanda marigayiyar matata ta Haifa min shekarun baya da suka shade.
Na dade da sanin ya rasu, domin ni na binne shi da hannuna, amma a kwanakin baya kawai saina samu labarin yana raye da shi da kanwar matata da sauran yara na anan kaduna.
Ina ta shirye-shiryen yanda zan shigo kaduna dan in gana dasu ne sai kuma labarin kama shi ya riskeni, shiyasa na kira ka dan in roki alfarmar a sakar min shi dan Allah.
Indai yaro na ne dukda tsawon shekarun da muka dauka bana tare ina da tabbacin bazai yiwu ya kasance mai aikata wadannan miyagun laifukan ba.
Dan Allah ko damar sakinshi bazai yiwu ba a bani damar ganawa dashi shi da iyalan nawa, na tabbatar akwai inda aka samu matsala a binciken 'yan sanda"
Shiru yayi yana sauraransa, kuma yana karantar duk maganganunsa, da kuma inda suka dosa.
"Wai Excellency kana nufin kace min tsawon shekaru masu yawa iyalinka suna raye amma kai baka sani ba?"
"Eh kwarai kuwa, haka nake nufi Ranka ya dade.
Dan Allah kayi min alfarma a saki Kamal na dan lokaci dan in damu damar ganawa dasu gaba dayansu.
Bana so in hadu dasu alhalin Kamal baya tare dasu, bayan mun gana dasu ma ana iya sake kama Kamaluddeen din, sai in dauki kwararren lauyan da zai tsaya mishi a kotu har a wanke shi bayan gama shari'ar"
Ya sake fada muryarsa na baiyana tsananin damuwa da tashin hankali, sai jero magana yake reeee kamar an kunna radio, zuciyarsa cike da fatan Gwamnan ya amince da rokon da yake mishi.
"Amma fa Excellency ina ga ka sa6a lamba ne akan maganar nan, domin shi wanda na samu labarin an kama sunanshi Usher ne ba Kamal ba kamar yadda kake fad'a..."
"Ai wannan Usher dai shine Kamal din da nake nufi Ranka ya dade"
"Ok.... na gane... amma kasan irin wannan case din shigan mutum cikinsa akwai hadari ba kadan ba, babu abinda mutane zasuyi tunani sai akwai saka hannuna a cikin safarar miyagun kwayoyin da yake yi.
Amma tunda kaine bazan gagara yi maka alfarmar da ka nema ba, amma tsawon wane lokaci ne kake gani ya ishe ka ku gama ganawar?"
"Ko awoyi arba'in da takwas ma sun isa Ranka ya dade"
Ya fada fuskarsa na baiyana zallar farinciki, a zuciyarsa har ya fara tunanin irin wulakantaccen kisan da zai musu, kuma zaiyi da takatsantsan ne yanda baza a ta6a zarginshi ba, saidai ma Gwamnan ya Kwan ciki, in yaso ya fadi a za6e mai zuwa Honourable Ghali ya samu nasara, dan a 6oye suna gaisawa.
"Ok shikenan, ka kira waya na zuwa gobe, duk yadda are ciki zan neme ka"
Da haka suka yi sallama yana ta zabga godiya kamar anyi mishi albishir da aljannah.
Komai na mai ilmi ya babanta da na jahili, haka zalika aiki da hankali yafi aiki da agogo, kuma idan Allah ya duba kyakkyawar zuciyarka game da mutane sai ya saukaka maka al'amura, duk wasu masu nufinka da mummunar sharri sannu-sannu mugun nufinsu zai ringa juyawa kansu.
A maimakon Gwamnan Dr. Ali Abbas na jihar kaduna yayi aiki da maganganun Alhaji Tijjani sai ya kira Commissioner a daren, ya umarceshi lallai ya turo mishi lambar wayar mataimakinsa Abdul'ahad.
"Your Excellency lafiya kuwa?"
Commissioner ya tambayeshi da mamaki.
"Lafiya kalau, akwai tambayar da zanyi masa ne"
Daga haka bai kara ce mishi komai ba ya katse wayar.
Cikin minti kasa da biyu ya tura masa lambar wayar Abdul din, yana ji kamar ya zama kuda ya makale dan yaji ko wane magana ne Gwamnan bazaiyi dashi ba sai Abdul'ahad?
A lokacin karfe goma sha biyu na dare ne, yana tsaka da shan Coffee a Ofis dinsa suna tattaunawa da Yusuf akan yadda Killer yayi laushi sosai, kuma ya amince zai tona asirin Honourable Sumaila a kotu kiran ya shiga cikin wayarsa. Yayi farin ciki sosai, dan wannan babban ci gaba ne a gare su amincewar Killer zai tona asiri.
Da sauri ya dauki wayar dan yana da lambar dukda ba wai suna wata mu'amala bane a tsakaninsu, duk wani umarni ta hannun Commissioner yake shigowa shi kuma ya sanar mishi, a takaice dai Commissioner ne mai alaka ta kai tsaye da Gwamnan ba shi ba.
"Ranka ya dade da kanka? Ai da aikawa kayi sai inzo in same ka"
Ya fada cike da ladabi kamar yana kallonsa.
"Karka damu Abdul'ahad. Ina so zamuyi magana ce ta fahimta kuma ta gaskiya da gaskiya tsakanina da kai.
Dan haka batun matsayin ni Gwamna ne ka ajiye shi gefe guda, idan zai yiwu ka dauke ni a matsayin yayanka ko abokinka, kai ko kaninka is dauke ni bazan damu ba, babban abinda nake bukata ka fada min zallar gaskiyar zancen da zan tambaye ka.
Kana ji na?"
Gabanshi ne ya dan fadi yana tunanin ko wane magana ne Gwamnan zai mishi?
"Eh ina jinka Excellency"
Ya amsa a d'arare.
"Ko da wata doguwar magana bata ta6a hada ni da kai ba Abdul nasan baza ka rasa jin labarin wasu daga cikin halayena ba na k'ok'arin kwatanta gaskiya da bin gaskiya akan ko ma waye"
Cikin nutsuwa ya warware ma Abdul duk yadda sukayi da Alhaji Tijjani da irin alfarmar da ya nema a gurinshi.
Sannan ya bukaci Abdul ya fada mishi da gaske suna da kwakwararan hujjoji akan Usher ko kuwa kawai hasashen laifukansa suke yi?
Da dukkanin zuciyarsa yake jin ya amince da Gwamnan dari bisa dari, domin gwargwado an sanshi da kwatanta gaskiya da bin ta dukda d'an adam tara yake bai cika goma ba.
Cikin nutsuwa ya gama warwarewa gwamnan shin wai ma waye Usher kuma waye Kamal? Su waye yake yiwa aiki? Waye Alhaji Tijjani?
Girgiza kai kawai yake yi yana jin labari mai tarwatsa kwanyar karamin yaro, Alhaji Tijjani fa? Sanata Sumaila? Alhaji Tanko? Da Honourable Ghali? Jiga-Jigan mutanen da ba Ida jihohin da suke ba hatta makwaftan jihohinsu zasu iya shaidarsu akan cewa su mutanen kirki ne.
Wannan labarin ya girgiza shi ba kadan ba, tun sha biyu da 'yan mintuna da suka fara waya basu daina ba sai karfe biyu na dare.
Gwamnan ya bashi shawarwari masu yawan gaske, kuma yayi mishi maganganu kwarara wadanda suka kara karfafa mishi gwiwa dari bisa dari.
Kuma ya fada mishi duk taimakon da yake bukata kar yaji shayin tuntu6arshi yana daga gefe zai ringa kai mishi agajin gaggawa.
A wannan daren Abdul baiyi barci ba saida ya tattara kundin case din Kamal ya tura wa babban kotun jihar kaduna.
Washe gari babban labari mai jijjiga zuciyar azzalumai da aka tashi dashi shine shigar da case din Usher kotu.
[26/04 9:11 PM] fareedah: *BARA A KUFAI!!*
*38)*
Murmushi sukai zukatansu cike da farin ciki lokacin da Abdul ya gama zaiyyanewa Aysha kad'an daga cikin irin ci gaban da yake samu a bincikensa.

[29/04 8:50 PM] fareedah: *BARA A KUFAI!!*
*39)*
Hankalinshi a tashe ya cire farar babbar rigar shaddar da yake jikinsa, bai damu da dattin da yake dankare a tsakar dakin ba yayi hurgi da babbar rigar gefe daya.
Dukda a kasa yake zaune saida ya sake gwaggwafa gwiyawunsa a kasa kamar mai rokon gafara, ya hada hannuwansa duk biyu alamun kaskantar da kai
"Mai Gobe zatai kyau dan girman Allah ka taimakeni kamar yadda Allah ya taimake ka. Wallahi ina cikin mugun tashin hankali idan aka shigar da yaron nan kotu, dan nasan mutuwa ce kawai zata hana shi ya fadi sunana a matsayin ubangidansa.
Idan kuwa har ya fadi sunana kashi na ya bushe a kasar nan, ko nawa kake so zan biya ka.
Dan Allah ka tura aljanu su hallaka yaron nan, ko kuma kayi mishi asirin rufa baki yanda uhmm bazai iya furtawa a kotunnan ba...
Duk yadda nake tunanin al'amarinnan ya wuce nan, a cikin kwanakinnan babu abinda nake cin karo dasu sai alamun k'arshe na..."
"Tabbas hakane...! bazan 6oye maka ba karshen ka yana daf da zuwa... babu abinda nake gani a cikin al'amarinka sai duhu dund'im"
Mai Gobe zatai kyau ya fada yana ta zana kasa yana sharewa babu alamun wasa ko kadan a fuskarsa.
Hannu biyu ya dora a kai kamar zai rusa ihu, hankalin sa yayi mugun tashi ba kadan ba.
Kallonshi yayi sai yaji ya bashi tausayi, d'an tunani yayi yaga idan ya kyale shi ma gurin wani malamin zaije yaci kudinsa a banza, shi ya riga da ya sani idan Sumaila zai zaga gurin malaman duniya saidai suci kudinsa a banza amma babu abinda zasu iya mishi.
Duhun da yake gani ba komai yake nufi a aikinsa ba face lokacin girbar miyagun aiyukan da yake yi ne yayi.
Dan haka gara shi yaci kudin tunda sun dade a tare.
"Yauwa! Ga wata mafita guda daya. Amma tana da d'an wahala, saidai idan ka bita akwai mafita a ciki"
Godiya ya fara jerowa kamar ma har ya samu biyan bukatar abinda yake nema.
"A cikin matan da kake aure guda biyu, naga akwai daya mai riko da ibada, dayar kuwa 'Yar duniya ce.
To sati biyu kacal zaka jera kana saduwa da uwargidanka ta dubura.
Idan kayi haka ina tabbatar maka bukatarka zata biya"
Ba tare da tunanin me zaije ya dawo a umarnin mai gobe zatai kyau ba ya zube masa mak'udan kudade ya kara gaba, jikinsa har kyarma yake yi ya fice daga dakin, ko sauraran Alhaji Tanko da yazo a bayansa baiyi ba yaja motar a guje yabar gurin.
*****
*"GASKIYA 'DAYA CE. Kaddarar Kamaluddeen (Usher)"*
Sunan da ta sanya wa sabon shafin da ta bude a facebook kenan inda zata ringa tura gaskiyar halin da ake ciki game da shari'ar Kamal.
Sannan ta kara da bayanin cewa
"Ku biyo mu sannu a hankali ta wannan shafin dan saurara da kallon shari'ar Kamaluddeen, wanda a gurinku ba kowa bane face tantirin mai safarar miyagun kwayoyin nan Usher.
*In zaka fad'i fad'i gaskiya komai ta janyo maka ka biya*
Ko me shari'ar zata k'unsa? Shari'a dai mace ce mai ciki da ba'a san me zata haifa ba"
Oganta ta mik'awa wayar ya gani yayi wasu 'yan gyare-gyare sannan ya mika mata wayar, cikin kankanin lokaci ta kirkiri page din.
Sannan tayi sharing ga duk abokanta na Facebook dan suyi liking page din.
"Da kyau Khadeeja! muna matukar alfahari dake a ma'aikatan nan.
K'ok'arin ki da jajurcewarki akan aiki shine abinda yasa kike kara burge mu.
Ki ci gaba da yanda kike yi, idan zaki fad'i fad'i gaskiya komai ta janyo miki kin biya"
Murmushi sukai gaba dayansu, dan wannan kalmar ta zauna a bakin manya da yara da suke aiki a gidan jaridar.
Suna iyakar kokari gurin tsaftacewa da tace labarin su kafin su fitar dashi, shiyasa indai kana son labari na gaskiya nemi jaridar Gaskiya daya ce kasha labari.
Gasu basu da tsoro ko kadan, ko kwanaki can da suka buga labarin wani babban dan siyasa akan yanda yake aikata lud'u da wasu matasa da suke mishi aiki saida gidan Jaridar yayi taga-taga, dan har rufe gidan Jaridar aka yi na wasu satittika bayan an kame manajan tsawon lokaci ba'a san inda aka tafi dashi ba.
Da yake indai mutum zai tsaya akan Gaskiya duk iya tsawon lokaci sai Allah ya bashi mafita, kuma sai Allah ya dora shi akan makiya sai gashi a hankali komai ya wuce kamar ba'a yi ba, an saki manajan bayan ya ci uban wahala.
Duk wannan wahalar baisa ya karaya ba, jinyar kwanaki kadan yayi ya koma bakin aiki suka ci gaba daga inda suka tsaya.
Da sauri ta dauki wayar a lokacin da kiran yake daf da tsinkewa.
"Hajiya Khadeeja kina Ofis ne?"
Ta jiyo muryar Malam Isa makanike yana tambayarta cikin daga murya, ga kuma alamun hayaniya sosai a inda yake.
"Eh ina Ofis. Malam Isa lafiya?"
"Hajiya gani a kusa da ofishin ku, wata mata ce muka kama ta sato jariri, k'ok'arin guduwa take yi shiyasa muka bata jikinta.
Idan da hali kiyi sauri kizo ki dauki rahoto kafin karasowar 'yan sanda..."
Gudu-gudu sauri -sauri ta harhada kayan aikinta ta dauki biyu daga cikin abokan aikinsu suka nufi gurin, bayan ta sake kiran sa ya mata kwatancen inda suke.
Cincirindon mutanen da suke hangowa a gefen titin yasa suka tabbatar da nanne gurin, dakyar aka buda hanyar suka kutsa cikin mutane har kusa da inda matar take.
Tana tsugune a kasa tana share hawaye, fuskarta a kumbure, gefen bakinta da hanci sai jini yake zuba.
Kayan jikinta duk a yayyage, wani sashe na jikinta duk ya baiyana a waje, kunya ne ko tsoro yasa ta saukar da kanta a kasa oho!
Mutanen da suke zagaye da ita kowa da irin tofin ala tsine, da zagin da yake mata.
Wasu daga cikinsu ihu suke suna fadin a kona ta ranta, wasu suna cewa a bari hukuma tayi aikinta.
"Yauwa Hajiya, kinga shegiyar nan, gara da Allah yasa kuka iso akan lokaci"
Isa ne ya fadi haka bayan ya dago kan matan da karfin tsiya ya mikar da ita tsaye.
Nan take suka fara aikinsu suna daukarta hotuna
"Baiwar Allah ya sunanki?"
Duk ta diririce ganin suna ta daukarta da camera wasu kuma suna dauka da wayoyin hannunsu, jikinta da bakinta sai rawa yake yi.
Kamar baza tai magana ba, wani 6arin makauniya da Isa ya kai mata a baki tayi taga-taga zata kifa a kasa ya janyo ta a wulakance ya sake tsayar da ita, dole ta magantu, bakin sai zubda jini yake yi.
"Su... su.. sunana Harira"
"Malama Harira ke 'yar Wace unguwa ce?"
"A kabala... wallahi a kabala nake. Dan Allah kuyi hakuri kuyi min afuwa, Wallahi tsautsayi ne, amma ban ta6a yi ba..."
"Shegiya tsinanniya, da ganin yanda kika kwakwume jaririnnan kina fesa mishi wannan mugun abun ba yau kika saba wannan aikin ba, zaki fad'a musu gaskiya ko sai na 6arar dake?"
Daya daga cikin mutanen da suke tsaye ya fadi haka yana numfashi cike da fusata.
Ma6allin hannun rigarsa taga ya fara k'ok'arin cirewa ta fara magana da sauri
"Kuyi hakuri... wallahi wannan jaririn shine na shida da na ta6a sata..."
Gaba daya gurin suka rude da salati da sallallami suna tafa hannuwa cike da tsoro. Masu raunin zuciya har sun fara hawaye
"Yanzu shi wannan yaron a ina kika sato shi?"
Khadeeja ta tambaye ta jikinta a sanyaye.
"A kawo... au a hayin banki... au na manta a unguwar dosa ne"
Ta fada cikin rud'ani hankalinta duk a tashe.
Haushi da takaicinta ne ya cika mutane da yawa da suke gurin, sun yunkura zasu rufe ta da duka a hakan yayi dai-dai da isowar motar 'yan sanda gurin, hakan shi ya dakatar da mutanen daga niyyar su na dukanta.
Nan da nan 'yan sanda suka tattara ta da hijabinta da jaka da nikaf da aka wancakalar gefe daya sukai gaba da ita, ma'aikacin jarida daya yabi bayansu dan ganin ofishin da za'a kaita.
Jaririn da aka kwace a hannunta kuwa asibiti aka nufa dashi, domin ya galabaita ba kad'an ba saboda abinda take ta fesa mishi.
'Dan sanda daya ne yabi bayan masu kai yaron asibiti, abokin aikin Khadeeja daya ma ya bisu.
Ita kuma ta tsaya tattaunawa da me napep da mal Isa da suka damki matar da yaron a hannunta.
"Tun daga unguwar sarki na dauko ta, sai da muka kara gaba kadan na hadu da wannan bawan Allahn shima na dauke shi.
Amma kafin in dauke shi tun a baya ina lura da yanda yaron yake ta mutsu mutsu saita cusa shi cikin hijabi ta fesa mishi wani abu.
Bayan daukar wannan bawan Allahn shima ashe yana lura da abinda take yi, da yake Allah ya nufa asirinta zai tonu sai yaron yai ta rusa ihu yana zabura kamar wanda yake firgita, tun tana rufe shi da hijabi har ta fito dashi fili tana k'ok'arin fesa mishi abin.
Wannan bawan Allahn ya kalleta yace Hajiya ki bashi nono mana? Budar bakinta sai cewa tayi ba danta bane tana ta fesa mishi abin a ido da hanci yana ci gaba da rusa ihu.
Hakan ne yasa muka dasa mata ayar tambaya na tsaida napep din a gefen titi.
Ganin tana k'ok'arin guduwa yasa muka rike ta muna kururuwar ta sato jariri.
Wannan shine gaskiyar abinda ya faru"
Shima Isa bakanike maimaita mata yayi daga lokacin da ya hau kamar yadda mai napep din ya fada mata.
Godiya tayi musu mai auki sannan ta tattara kayan aikinta ta koma Ofis.
Da daya da daya mutanen gurin suke watsewa har suka tafi gaba daya.
*****
Har kasa suka zube suna gaishe shi zukatansu da fuskokinsu na baiyana tsananin farin ciki da jin dadin ganinsa.
Ziyara ce ta bazata, basu ta6a tsammanin ganinsa a daidai wannan lokacin da al'amura suke kara daukar zafi kamar haka ba, dan kusan kullum sai sunyi waya dashi.
Cikin kankanin lokaci aka dabaibaye gabanshi da kayan sha da na ciye-ciye.
Ruwa kawai ya iya sha saboda gajiyar hanya da suka kwaso.
"Abida.. Wannan ziyarar tawa ta bazata ta dole ce fa, a daidai wannan lokacin ban yi tsammanin zan iya yin tafiya mai nisan haka ba.
Ya gida da iyali? Ina fatan duk na same ku lafiya?"
Ya tambaye ta da muryarsa mai baiyana rauni da girma da ya fara kama shi.
Dan ma shi din dakakke kuma tsayayyen tsoho ne da Allah ya wadace shi da lafiya, yakan dad'e baiyi ciwo ba.
"Lafiya kalau Baba, ya su Inna? Ya bayan rabuwa?"
Ta furta hakan farin cikinta ya gaza 6oyuwa a fuskarta.
Gyara zamanshi yayi ya kalli Abdul da yake zaune can gefe daya.
"Malam Abdul'ahad wannan tafiyar tawa tafiyayya nayo ta domin kai.
Kusan kullum idan muna waya da Abida tana fada min irin jajurcewarka a aiki da kuma gaskiya a gurin aikinka.
Shiyasa na kawo maka wani dan taimako, amma fa idan kana da bukata"
Kallon Dr. Abida yayi ita kuma ta gyada mishi kai alamun ya amshi taimakon.
Kan dattijon yana kasa yana laluben wani kullin leda a cikin jakar fatar da ya karba a hannun jikansa Misbahu.
Wani ruwan magani ya ciro mai kama da ruwan rubutu ya dauko ya mika masa.
"Wannan fuskarka zaka wanke dashi"
"Yanzu?"
Abdul ya tambaya fuskarsa na baiyana mamakin maganarsa.
"Eh yanzu yanzu kuwa"
Ya amsa babu alamun damuwa a fuskarsa.
Khadeeja ce ta shiga kicin da sauri ta dauko masa robar da ake zuba ruwan wanke hannu ta mika wa Aysha, ita kuma ta matsa daf dashi ta kara masa ya wanke fuskar tasa.
Tsawon wasu mintuna idanunsa suna gani dishi-dishi sai daga bisani suka washe gaba daya.
"Da wani canji da kaji a idanunka?"
Tsohon ya tambayeshi.
"Eh da farko dishi-dishi nake gani, amma yanzu normal nake gani"
"Masha Allah! Ga wannan kuma ka shanye yanzunnan bayan kayi bismillah"
Kar6a yayi ya aikata kamar yanda aka umarce shi.
Duk saida ya bisu da kullin ruwan magani yace su shanye bayan sunyi bismillah kamar yadda yaba Abdul, amma su bai basu na wanke fuskar ba.
"Abdul ka karbi lambar waya ta a gurin Abida. Duk abinda baka gane ba ka kira ni"
Yana gama fadin haka ya umarci Misbahu ya tashi su tafi.
"Haba Baba tun yanzu?"
Ta fada fuskarta na baiyana rashin jin dadin tafiyarsa.
Murmushi yayi yana kallonta
"To me zan zauna inyi a gidanku Abida? Akwai wani tsohon amini na a Abakwa tsawon shekaru ashirin kenan bamu hadu ba saidai gaisawa a waya, a gidansa zan kwana gobe in Allah ya kaimu sai in koma gida"
Kayan abincin ta hada mishi gaba daya taba Misbahu ya rike mishi.
"Baba muje in sauke ka a gidan"
Abdul ya fada bayan ya dauki makullin motarsa.
Sunji dadin karamcin Abdul a gare su kwarai, ta gaza 6oyewa saida ta furta.
"Na gode kwarai Abdul.
Baba Allah ya huta Gajiya zan shigo gobe da safe kafin ka wuce in Allah ya yarda"
Har gurin mota suka raka su, suna ta daga mishi hannu har 'yan sandan da suke gadi suka bude get din gidan ya fice da motar.
A hanyarsa ta komawa gida ne yaga wani abin da ya bashi mamaki kuma ya bashi tsoro.
A hanya ya tsaya sayan lemu gurin Alhaji Saleh mai kayan marmari, babban guri ne da yake tashen saida kala-Kalan kayan marmari a cikin garin kaduna.
Duk wani Alhaji mai ji da kansa yana sayaiya a gurinsa.
Wata jibgegiyar mota ya tarar a gurin Alhajin da yake tuka motar yana tsaye yana waya ana zuba masa Apple da kankana a leda.
Sun hada ido da Alhajin ne a daidai lokacin da ya karbi kayan ya juya zai shiga mota.
Nan take Abdul yaga Alhajin sanye da kayan tsafi a tsaye cikin wasu mutane, duk suna sanye da jajayen kaya suna surutai, a hannayensu rike da kwarya mai dauke da wani abu kamar jini.
Hotunan sun bace masa ne a daidai lokacin da yaja motarsa yabar gurin.
Firgigit ya dawo haiyacinsa kamar wanda ya farka daga barci, wai me ma ya gani ne?
Kamar faifan bidiyo haka al'amarin yaita dawo mishi a kai, boyayyiyar fuskar wannan Alhajin wanda mutane basu sani ba ya gani fa?
"Abdul, wannan ruwan da na baka ka wanke fuska ba na komai bane illah na *Buda ido*, idanunka zasu ga laifin da mutum yake aikatawa a 6oye matukar ka hada idanu dashi.
Dan haka ka Kula, kayi aiki da takatsantsan!"
Ya tuno maganganun da Baba tsoho yayi masa a daidai lokacin da zasu rabu bayan ya sauke shi a gidan abokinsa.
0 comments:
Post a Comment