©️HAFSAT RANO
ALKALAMI TV
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo
WATTPAD: HafsatRano
**********
*MAFARIN KOMAI*.
A guje ta fito daga dakin jikin ta cikin shigar kayan ma'aikatan jinya, da sauri duk suka mik'e ganin ta nufo su
"Ta sauka Dr!" Suka tambaya a rude kuma a tare
"Ina maigidanta?" Ta maida musu ba tare da ta amsa tambayar tasu ba.
Matsowa yayi da sauri yace
"Gani."
"Ok muna so ka saka hannu ne, ba zata iya haihuwa da kanta ba dole sai dai ayi mata aiki."
"Innalillahi, aiki kuma Dr?" Ya tambaya a kideme
"Shine kadai abinda zamuyi mu ceto rayuwarta data abin cikin ta. Kayi hakuri babu lokaci."
"Shikenan, Allah sa ayi a sa'a."
Bin bayan ta yayi, suka je ya saka hannu sannan ya dawo wajen sauran ya tsaya yana kaiwa da komawa.
Bayan shafe tsawon mintuna arba'in da shigar su ta sake fitowa, wannan karon akwai alamun nasara a tattare da ita. Kafin ta k'arasa garesu sukayi saurin isa, fuskar su dauke da alamun tambaya, hannun ta ta mika alamun abata tukwuici kafin tace
"Congratulations Your highness, an yi nasarar ciro muku dan saurayi."
Da sauri ya kalle ta kamar be ji me tace ba, gid'a masa kai tayi alamun gamsarwa, maida kallon sa yayi wajen sauran da duk fuskokin su ke cike da farin ciki yace
"Alhamdulillah ya ALLAH!" Ya furta da karfi
A duniya bashi da wani buri da ya wuce yaga an haifa masa d'a namiji, yau sai gashi Allah ya cika masa burin sa, ba ma shi ba, duk wani makusancin sa yana masa sha'awar haka. Duba da irin tarin dukiyar da Allah ya bashi. Ya hakura ya barwa Allah zabin sa, sai gashi ya bashi a lokacin da beyi zato ko tsammani ba.
A take wajen ya kaure da murna, babu wanda ya tsaya tambayar lafiyar mahaifiyar, tuni kowa ya hau kokarin kiran waya domin sanar da yan'uwa da abokan arziki.
THE ONE AND ONLY HEIR To *MARWAN DIKKO* FAMILY IS BORN.
A daidai lokacin Inno na kwance a gadon asibitin, babu tazara tsakanin dakin da take da babban dakin da aka ajiye Matar Alhaji Marwan, saboda haka tana jiyo hayaniyar mutane me cike da tsantsar farin ciki, kallon jaririyar dake kwance kusa da ita tayi, zuciyar ta tayi rauni, anya? Anya bata zalunci yarinyar ba kuwa? Kallon gefen ta tayi taga jakar da aka hado mata tare da jaririyar, soyayyar ta da kudi abu ne me girma, babu abinda ba zata iya aikatawa akan su ba, sai dai tana tsoron abinda zai je ya dawo gaba, gashi babu ko digon soyayyar yarinyar a zuciyar ta. Abu daya ta sani shine rayuwar jaririnta, rayuwa me inganci da tsananin gata da zai taso da ita. Idan ta tuna wannan sai ta ji ta samu sauki, sai dai fa tana da kudurin komai daren dadewa sai ta karbo shi.
Shigowar su Yalwati da sauran jama'a ne yasa ta ɗan saki ranta, suka shiga daukar jaririyar kowa yana yaba kyawun ta, ita dai Inno jin su kawai take ba tare da ta tanka ba, ganin zasu cigaba da chaja mata kai da hayaniyar su yasa ta rufe idon ta alamun bacci take yi, hakan ya bata damar cigaba da yin tunanin da take akan wannan babban al'amari ne cike da tarin matsaloli a gaba.
Hmm
****
*AMINATU*
Kowacce rayuwa cike take da kalubale, sai dai ni tawa rayuwar da wani salon na sarkakiya tazo min.
Rayuwa ta cike take da abubuwa masu yawa. Duk da haka bazan ce nafi kowa shiga matsin rayuwa ba, sai dai ina da tabbacin ina cikin sahun farko na mutanen da za'a kirasu da wanda rayuwa tayi *Daurin Goro*.
_Eh daurin da nake tunanin babu wani mahalukin da zai iya warwareshi, na riga na sare, na barwa Allah ikon sa, ina kuma kyautata zaton zai kawo min yankewar sa kafin barin numfashi na._ Ajiyar zuciya na sauke ina bitar Rayuwa ta daki-daki kamar a lokacin komai yake faruwa.
Zaune nake a faffad'an tsakar gidan mu wanda ke dauke da dakuna hudu falle falle sai madafi daga gefe, randunan ruwa manya, daga dayan bangaren rijiya ce babba da makewayi a gefenta, gidan gidane babba daya hada da mutane da yawa sai dai kowa yana ɓangaren sa inda babban zauren gidan shi ya haɗa kowa da kowa.
Dakin farko ya kasance dakin Baba, sai dakin Inno daga chan gefe, dakin yara matan gidan ne a kusa dana inno, daga dayan barin dakin Yalwati ne sai dakin samari dake daura da hanyar fita daga shashen namu.
Tsintar shinkafa nakeyi tun kafin rana ta fito gashi har ina neman makara ban samu na gama ba, a gurguje nakeyi saboda lokacin makaranta kar na makara, cikin sa'a na kammala nayi saurin zubawa a ruwan waken dake ta tafasa bayan na tabbatar da dahuwar waken saboda gudun abinda zai je yazo. Gyara wutar nayi ganin ta fara zarewa na karasa gaban rijiya domin yin kwaskwarima. Cikin sauri sauri na zura uniform d'ina wanda duk ya tsofe wani wajen ma ya yage na sake fitowa, lokacin har yaran gidan sun fara fitowa ana layin alwala. Haka dabi'ar gidan mu take, tun tasowa ta kawo yanzu hakan bata chanja zani ba, kafin su gama alwalal sai sunyi fada kashi dari. Murmushi kawai nayi na fada dakin Inno dan gaishe ta, a tsaye na ganta tana kokarin daura dankwali tana ganina ta tsaya.
"Ina kwana Inno.?" Na durkusa har kasa kamar ko yaushe. Bata amsa ba sai kallon kayan jiki na da tayi kadan kafin tace
"Kin gama aikin naki ne da zaki wuce makaranta?"
"Eh." Nace ina kallon ta.
"Kin zuba ko kin gama?"
Iya sani na Karime ke karasa wa idan na zuba, tun da ita ba makarantar take zuwa ba, a darare nace
"Na zuba karasawa kawai zatayi a kwashe Inna."
Dan bata fuska tayi tana yatsine baki kafin tace
"Jeki jira ta karasa yau babu me karasa miki Karime bata jin dadi."
"Toh."
Kawai nace na mike jiki a sanyaye na koma bakin dakin mu na zauna ina kallon yadda rana ta d'aga sosai alamun na makara, ina nan zaune kowa ya fito aka hau hada-hadar shan koko, ban bi ta kai ba ni dai buri na na ganni a makaranta. Sai bayan wajen rabin awa sannan na kammala na sake dauraye kafata na fice daga gidan da sauri kafin Inno ta ankare ta kawo abinda zai hana ni zuwa duk kuwa da na kan yi mamakin dalilin da yasa inno take bari na zuwa makaranta, bayan haka bama kowa ne a yaran gidan ke samun zuwa makarantar ba.
A babban zauren gidan naci karo da Nura, da alama lokacin zaiyi sallah, gaishe shi nayi na wuce ba tare da jiran amsar sa ba.
Tafiya ce mai tsawo kafin ka isa makarantar guda daya jallin jal dake a kauyen, Kamar kullum babu malamin daya shigo har nazo, haka dabi'ar makarantar take, a rana sai ka samu malami daya ne kawai zai shiga duk suna zaune a staff room suna hira, a haka dai muke dan samun abinda muke samu wanda bamu da tabbacin daidai suke koya mana sai dai saboda ba gane wa zamuyi a lokacin ba yasa muke binsu a haka. Musamman ma ni da na taso da son karatu da kuzun zama wani abu a kauyen namu tun bayan ganin da nayi wa jikokin mama Ladi makociyar mu dake zaune a birni, sun kawo mata ziyara, tun daga lokacin na sawa raina zama kamar su, sai dai hakan ba mai yiwuuwa bane duba da irin gidan dana taso.
***
Haka rayuwa ta cigaba da garawa, babu abu daya daya sauya na daga al'adun gidan mu, tun da na taso nasan Inno ita ke ciyar da gidan mu ko nace shashen mu, shiyasa ko babanmu baya mata musu, Yalwati kuwa ta zama kamar ba kishiiyar ta ba, dan bayan na gama girkin shinkafa da waken da karime take fita dashi wajajen sha biyun rana, Yalwati ce zata dora alala, sannan tayi dambu da wake shima a sake fita dashi, duk kuma jarin na Inno ne.
Inno mutum ce wadda tasan darajar nema, bata taba zama haka nan, yau ta buga nan gobe ta buga chan, bayan sana'ar saida abinci har kiwon akuyoyi take yi da kaji, ga sana'ar abin kad'i dangin su kuka da su kubewa, da sauran abubuwa, sai ya zama ma a kaf kauyen namu babu wanda zai kama kafa da ita Indai a samu ne, shiyasa kaf gidan mu suke shakkar ta, babu wanda ya isa ya daga mata yatsa balle Baba da Yalwati da suka zama kamar yaranta, sai abinda tace musu ake aiwatar wa.
*******
Kiran da Karime ke kwala min yasa na ajiye kibiyar hannu na na fito, riko ni tayi da sauri tana haki
"Lafiya dai?" Nace ina kallon yanayin ta
"Ina fa, dalla kowa yana chan kallon bak'in gidan Bature sun zo ke kina nan kina tsifa."
"Dan Allah!" Nace ina fad'ad'a fara'ar fuska ta
"Wallahi ana chan duk ana ta kallon su abin sha'awa, na duba ban ganki ba shine nazo kirankii, kinga motar da suka zo acikin ta, har da wata yarinya kamar girman mu, kinga kayan jikin ta kuwa? Wayyo yan gayu sun ji dadi wallah"
Ta fada tana rik'e haba, da sauri na koma ciki na dauko dankwali na na daura muka fice da gudu, dukkannin mu sirara ne babu kibar arziki, yadda muke gudun kadai zaka tabbatar da yarintar mu, dudu du a lokacin ba bazan bi shekaru goma sha biyu ba, tsiran mu da karime shekara daya ne saboda haka ba zaka gane wani banbanci me yawa a tsakanin mu ba.
Tun kan mu karasa muka ga ana juyowa, hanne ce ta tsaida mu tana dariya
"Ina zaku wai, kallo ya barku ai sun koma gida, sai wani jikon kuma."
Haushi ne ya kamani, duk zuwan da zasuyi ban taba samu na gansu ba har su tafi, a take na kudurce a raina wannan karon babu abin da zai hanani ganin su, ko nima na samu na dorar da labarin su.
Kullum da safe idan na tashi ta kofar gidan nake bi, haka ma idan na dawo, ban taba samun nasarar ganin ko da cikin gidan bane. Gida ne me girman gaske, hade da babban gidan gona da tsayawa fasalta yanayin girman sa ba mai yiwu wa bane. Duk da karancin shekaru a lokacin da kuma yanayi na duhun kai da kauyanci na gane cewa ba karamin masu kudi bane mamallaka wannan wajen, duk a irin wannan lokacin suka zo gaba d'ayan su su jima sosai, idan suka tafi kuma shikenan sai wani lokacin me tsawo.
Gidan Bature kamar yadda mukayi wa gidan da lakabi, sai dai a zahiri ba haka sunan me gidan yake ba, tsari da yanayin gidan da bamu taba ganin kamar sa ba yasa muke kiran gidan da gidan Bature.
***
Tun gabanin magriba garin yake ta hadewa, alamun za'a iya samun ruwa a kowanne lokaci, muna daga kofar dakin mu dasu hanne muna hira da karad'i Inno ta kwala min kira, tashi nayi na karasa wajen ta ina kallon hannun ta
"Yi maza kije shagon Umaru ki siyo min maganin sauro yanayin garin za'a iya ruwa kowanne lokacin."
Karba nayi na juya da niyyar kiran me rakani, dakatar da ni tayi ta hanyar cewa
"Ina kuma zaki koma?"
"Su karime zan kira su rakani Inna."
"Saboda ku tsaya min shiririta a hanya ko? Kin wuce da sauri ko sai na bugo ki?"
Da sauri na juya nayi hanyar waje zuciya ta duk babu dadi, duk yawanmu na rasa dalilin da yasa ni kadai Inno take takurawa.
Sanda na isa shagon ya riga ya rufe, juyawa nayi ina tunanin yadda zanyi, sama na sake kalla naga yadda hadarin ke sake hadewa nayi saurin daga kafata na kara sauri don zuwa shagon dake chan kasa kadan.
Sauri sauri nake nabi ta wani lungu ina kokarin ganin na isa kafin ruwan ya sakko, cikin sa'a na samu shagon yana bude shima yana kokarin rufewa, da sauri na bashi kudin na karbi maganin sauran na juya na kamo hanyar gida a lokacin garin ya kara hadewa.
***
*Gidan Bature*
Dukkanin su suna zaune a babban falon gidan, kallo suke suna hira gwanin sha'awa, sun kusa a ƙalla su goma maza da mata, Ja'afar ne ya kalli Farouk da tun da aka fara hirar yana rike da waya be tanka musu ba, magana suke akan fitar da zasuyi gobe dan zaga gari.
"Ya Farouk." Ya kira sunan shi yana kallon sa
"Uhum?" Ya amsa yana yin kasa da wayar dake hannun sa
"Maganar fita gobe, U haven't said anything bayan kuma kai kadai ne zakayi convincing Dada ta yadda."
Be tanka ba ya sake maida kansa kan wayar kamar ba zai ce komai ba, ganin haka yasa Ja'afar zungurar Amal ya nuna mata bangaren Farouk din, duk ciki tasu tafi zuwa d'aya, babu wani abu da zata nema beyi mata ba sai dai idan bashi dashi din.
Tashi tayi tsam ta isa gefen sa ta zauna ta marairaice murya
"Dan Allah Yah." Hade hannayenta tayi waje d'aya tana sake kallon sa, hararar Ja'afar yayi kafin ya mike yana ware hannayen sa, duk sun maida hankalin su kansa suna jiran su ji me zai ce, takawa yayi a nutse har gaban window dake makale a falon ya zuge curtains din, sama ya kalla yaga yadda garin yayi, murmushi yayi ya tura hannun sa gaba daya waje yana kama sanyayyiyar iska dake kadawa a hankali. Wajen mintinan biyu yayi a haka kafin ya zaro hannayen nasa ya juyo ciki yana kallon su.
"Zan yi magana da Dada, shikenan?"
Ihu suka sa gaba daya cikin murna, yana jin su ya juya da sauri ya fada dakin su, ƙatuwar rigar ruwa ya dauka ya saka hade da takalmin sa na ruwa ya fito ya fice daga gidan gaba daya.
ZAFAFA BIYAR
KAUNAR MU: MAMUH GEE
ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA
GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL
DAURIN GORO:HAFSAT RANO.
IGIYAR ZATO: MISS XOXO
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
DG
Shafi na biyu (2)
******
Lokaci daya iska me karfin gaske ta taso, gaba daya bana ganin gaba na, wani irin tashin hankali ne ya ziyarce ni, na sani sarai idan har na bari ruwan nan ya taba lafiyar jiki na kashi na ya bushe, ganin da gaske bana ko ganin hanya yasa na makale gefen wani shago na kudundune kaina ina jin matukar tsoro. Ina nan makale yayyafi ya fara sauka a hankali, tsoro na ya dadu, zuciya ta tayi rauni sosai, kamar daga sama naji an dafa kafada ta, cikin tashin hankali na dago kaina,ban samu nasarar ganin fuskar kowaye ba, saboda tsananin hasken torch light din da aka sa aka haske ni. Cikin muryar tsoro na furta
"Waye!"
Be amsa ba, ba shi kuma da niyyar amsawar, illa sake dalle ni da yayi, take hasken yayi tasiri rage kaso tamanin cikin dari na gani na, baya da ƙurar da ta riga ta cika min idon nawa, da sauri na mike ina kokarin daidai ta zaman riga ta, na fara alamun barin wajen, hannu naji an saka an riko ni, cikin wata iriyar murya mara fasali ya furta
"Gidan uban wa zaki? Ai wallahi kinyi kadan tsuntsu daga sama gashashshe."
Tsoro ne ya bayyana ƙarara a fuskata jin muryar Garbati, mutumin da ko a mafarki bana fatan hada hanya dashi, waye be san shi ba kaf kauyen nan namu, tantirin dan iska ne, lamba daya, gashi babu wanda ya isa dashi kaf kauyen. Da sauri na ja da baya ina kokarin sake shiga cikin ruwan sosai, damko ni ya sake yi nayi kara da karfi jin zafin rikon da yayi min, ja na ya shiga yi yana kokarin turani cikin shagon da tun zuwa na wajen na lura da yar kofar dake bude, amma banyi tunanin akwai mutum ciki ba, da karfin gaske na hau kokarin kwatar kaina, sai dai ko kusa da hakan ban kai ba , duba da yanayin karfin ba daya ba. Tuni na hau kuka ina magiyar bashi hakuri, tunda ayi ƙarancin shekaru na nasan hakan da yake me yake shirin aikata min. Be saurara ba, ko ma nuna alamun yaji abinda nace, haka ya tura ni ta karfi ya maida kofar ya tura yana sakin wani shu'umin murmushi.
Tuni na watsar da aiken Inno, na shiga ihu da dukkannin murya ta ko Allah zai sa a jiyo ni, dariya ya shiga yi ba kakkautawa.
"Yarinya da kin hakura babu shegen da zaiji ki, uban me ya fito dake a wannan lokacin shegiya."
"Aike na akayi wallahi." Nace ina sharbe hawaye da majina.
"Daidai kenan, idan na ci ubanki zaki gane shayi ruwa ne."
Ya fada yana kokarin matsowa kusa dani.
Sosai na kara karfin murya ta, cikin tsananin tashin hankali, magiya nake masa ina rokon sa, sai dai hakan ba sa ya fasa aiwatar da abinda ya kudurta a ransa. Tun daga nan bansan me ya kuma faruwa ba😭😭
***
***
Tafiya yayi sosai yana mai jin dadin yanayin garin, kafin zuwa lokacin da iskar ta taso, sauri ya kara don ganin ya isa gida, be yi tunanin ruwan zai zo da iska haka ba. Saukar ruwan ne ya rage karfin iskar sosai, hakan ya bashi damar cigaba da tafiyar sa cikin kwanciyar hankalin ruwan na dan taba fuskar sa kad'an-kad'an. Kamar daga sama yaji ihu, ihun ma na mace me karancin shekaru, sai dai karar saukar ruwan yayi tasiri kwarai wajen kasa tantance daga ina ihun yake, hankali ya tashi ya hau neman ta in da muryar ke fitowa, kamar mahaukaci haka ya shiga kai kawo a cikin ruwan, hankalin sa ne ya kai wajen, da wani irin mugun guda ya nufi dan karamin shagon daya gama tabbatarwa daga nan ɗin ne yake jin kukan, beyi wata wata ba yana zuwa ya daki kofar da dukkan karfin sa. Abinda ya gani yayi mugun daga masa hankali, da gudu yayi kansa ya shiga dukan shi, duka me cike da tsantsar bacin rai. Yanayin rashin karfi da a tattare da Garbatin ya hana shi katabus, sai daya yi masa duka sosai sannan ne hankalin sa ya dawo kanta, tana kwance kamar mara rai, abinda ya dade yana jin labarin yana faruwa ga yara masu kananan shekaru ne ya faru da yarinyar nan, yarinyar da dududu ba zata wuce sa'ar Amal ɗin su ba, da sauri yayi kanta ya dago ta, tuni ta sume saboda tsabar firgicin data shiga, wani irin kuka ne ya taso masa, wannan wane irin rashin imani ne?. Da dukkan karfin sa ya daga ta ya sata jikin sa, be bi ta kan Garbati ba da yake kokarin tare shi, har ya kai kofa maganar shi ta dakatar dashi
"Ni kayi wa wannan dukan? Akan wannan yar iskar yarinyar?"
A halin da yake ciki ba zai iya magana ba, saboda haka ya juya da sauri dan ganin ya ceto rayuwar yarinyar. Yana juyo hargowar Garbatin me cike da gargadin abinda zai aikata masa.
Gida ya wuce kai tsaye yana jin kamar zuciyar sa zata bar jikin sa. Har lokacin dukkan su suna falo ya shigo da sauri dauke da ita Baba maigadi na bin bayan sa, a tare duk suka mike suna kallon shi cike da mamaki.
"Yah Farouk..!
Amal ta fada tana zaro
"Bude min daki na."
Da gudu ta yi gaba suka take masa baya, dakin sa ya kaita, ya kwantar da ita saman gadon sa, sai a lokacin ya ga fuskar ta, kallon su yayi duk sunyi cirko cirko kamar sun ga abin tsoro.
"Kira Dada Ja'afar."
"Wacece ita Yah Farouk?" Ya tambaya ba tare da ya motsa ba.
Kallon sa yayi rai a bace daa karfi yace
"Will you go and call her or..."
Da sauri ya juya ya bar dakin, dafe kansa yayi ya sake dagowa yana hararar kowa.
"Duk ku fice min anan, Amal ki tsaya."
Yar rige rigen fita suka hau yi, kowa zuciyar sa cike da tambayar abinda yake faruwa.
Gefen sa amal ta zauna tana kura mata ido
"Yah bata da lafiya?" Ta fada cikin tausaya wa.
Daga mata kai yayi zaiyi magana Dada ta budo kofar cikin tashin hankali.
"Babana,me ya faru?" Ta fada tana shigowa dakin, ganin da tayi mata yasa tayi saurin ƙaraso wa wajen
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, me zan gani haka?"
Hannun sa ya saka cikin na Dadan yana kokarin saita yanayin bugun zuciyar sa.
"Bani ruwa da sauri ke Amina."
Da sauri amal ta tashi ta dauko ruwan, karba ta shafa mata a fuska, sai data yi wajen sau uku sannan ta bude ido tare da sakin wani irin ihu wanda ya karade kusan kowanne lungu da sako na gidan.
Bude ido na nayi wanda yayi min matukar nauyi ina kallon kowa na dakin, a lokaci daya zuciya ta ta shiga tariyo min abinda ya faru, kuka sosai na saka ina jin tsananin zafi kamar an watsa min barkono, riko ni dattijiwar tsohuwar dake kusa dani tayi tana kokarin sani a jikin ta.
"Kwantar da hankalin ki, yi shiru, babu abinda zai faru kinji? Yi shiru karki karawa kanki ciwo."
Abinda kawai naji tana ta maimaitawa kenan yana shiga kunne na cikin wani irin yanayi dana kasa tantancewa.
"Dada asibiti zamu kaita, She's bleeding so Badly."
Muryar sa ta daki kunne na, kallon sa Dada tayi kafin tayi magana cikin harshen turanci.
"Who is she?"
"It's a long story, babu time zan sanar dake komai, for now let's help her please."
Ya karashe a marairaice.
"Owk, Amma Ina son sanin amsar, kasan dai mahaifinku, kasan kuma labari zai kai masa zuwa gobe, i just hope ba kaine ba."
Ta zura masa ido tana son ganin gaskiyar sa. Be yi magana ba, sai ma mikewa da yayi ya fice daga dakin, jim kadan ya dawo yana kallon Amal data makale a gefe tana mun kallon tausayi.
"Zaki rakamu ko?"
Da sauri ta daga kanta.
"Dada ga driver ya dauko motar, muje ko?"
" Shikenan."
A hankali ta daga ni zata mikar dani, wata irin kara na saki me cike da azaba, da sauri ya waiwayo ya fasa kokarin fita daga dakin, da baya da baya ya dawo ya daga ni chak ya fita dani suna take masa baya.
***
Tun Inno na zuba idon dawowa ta har hankalin ta ya fara tashi, ganin tasowar hadarin yasa ta sake shiga tashin hankali sosai, turawa tayi aka kira mata Nura a zaure ya bi bayana, lokacin iskar nan ta taso sosai. Safa da marwa Inno kawai take yi, duk wajen kowa yayi tsit ana jiran dawowar Nura, tsawon mintuna talatin ya dawo hankalin sa a tashe, babu ni babu dalili na, hakan kuma yayi daidai ta tsugewar ruwan, iya kar tashin hankali Inno ta shiga, bata fatan abinda zuciyar ta ke raya mata ya zama ya faru,bata da wata hujjar kare kanta a duk lokacin data shirya karbar muradin zuciyar ta, ko ma ba haka ba, baya cikin yarjejeniyar da sukayi tsakanin su, ko ba komai zata ci darajar nata dan.
Tuni su karime da sauran yaran suka fara kuka, babu me rarrashin wani, ana haka ruwan ya fara tsayawa, gaba daya suka fito dan zuwa nema na, lungu da sako babu alamun za'a same ni, tashin hankalin da ba'a sa maka rana kenan, gida suka dawo kowa yayi jigum jigum ana tunanin ta in da zan ɓullo, duk da zuwa lokacin kowa ya gama saddak'arwa wani mugun abin ya same ni.
Duk suna zaune sunyi cirko cirko, makotan da suka shigo duk sun tafi, yara sunyi bacci sai yan kadan, aka yi sallama a kofar gidan, da sauri su Nura suka fito tare da su Baba.
"Garbati?" Nura ya fada yana kallon su.
"Mune nan." Ilu ya amsa yana jingina a jikin garu
"Lafiya dai ko?" Baba yayi tambayar ganin basu ce komai ba.
Ilu ne ya kalli Garbati kafin ya shiga magana
"Dama akan Aminatu ne."
Da sauri a zabure suka hada baki.
"Kun ganta ne?"
Ilu ne ya dora
"Bamu ganta ba, sai dai mun san inda take, dan munyi iya kar kokarin mu wajen ganin mun taymaka mata, garin haka ne ma Garbati yasha wannan dukan da zaku ga jikin sa haka." Ya fada yana haske Garbatin
"Tana ina?"
"Ina bakin gidan Bature? Daya daga cikin su ne muka kama shi, dan a lokacin da muka je ko numfashin kirki batayi, garin kokarin mu ne ma yasa masu gadin su sukayi wa Garbati mugun dukan nan, sannan ya dauke ta ya tafi da ita."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un."
ZAFAFA BIYAR
KAUNAR MU: MAMUH GEE
ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA
GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL
DAURIN GORO:HAFSAT RANO.
IGIYAR ZATO: MISS XOXO
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan kafin a fara kafta WASAN😁👉🏻📻©Rano
ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
(3)
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Suka hada baki suka fada a tare.
"Yanzu ina ya kaita?" Baba ya tambaya cikin jimami.
"Wallahi muma bamu sani ba, mun dai zo mu sanar ne dan a sani, amma abunda yafi shine mu dunguma muje gidan su, idan yaso sai a sa ya fito da ita. "
"Abinda za'a yi kenan, kai Nura shiga kira min Yahya da Lawan duk mu dunguma, ba dan dare yayi ba ma wajen maigari zamu fara zuwa."
A tare suka fito, Inno na tambayar su yadda ake ciki babu wanda ya tanka mata, suna fita ta sulale kanta na juya mata, tsananin tsoro ya hana ta motsi, idan ta tuna abinda zai faru.
Babu kowa a hanya har suka isa gidan, haske fitilu ne tarwai kamar rana, buga kofar Ilu ya hau yi da dukkan karfin sa Garxali na taya shi, Baba maigadi ya taso a zabure yana tunanin ko sune suka dawo. Yana budewa yayi turus ganin mutanen da be wani waye dasu ba a wannan daren, kallon kallo sukayi wa juna kafin yayi karfin halin tambayar su
"Lafiya dai?"
Lawan da duk yafi zafi cikin su ya bata rai yana leken gidan
"Yarinyar mu da kuka sace muka zo ku fito da ita."
Da sauri Baba maigadi ya kalle su yana tuno abinda ya faru kafin isowar su, kar dai ace? Da sauri ya kauda tunanin yana mai tabbatarwa kansa hakan ba mai yiwu wa bane, yasan waye Farouk, yasan me zai aikata, duk da ance ba'a yabon yaran yanzu, sai dai yana kyautata masa zato ko ba komai yaro ne nutsattse.
"Kayi magana mana, wallahi ko a fito da ita ko mu nuna muku mune muke da garin nan dan uwar mutum."
Garbati ya katse masa tunanin da ya tafi na wucin gadi, kallon su yayi daya bayan daya yana yanke hukuncin abinda ya kamata ya sanar musu.
"Bansan me kuke magana akai ga gaskiya, babu kuma wata yarinya da tazo gidan nan, amma ku bari na shiga ciki na yi magana da masu gidan."
"Karya ne wallahi, karku yarda Malam Ayubah, yaran gidan ne a gaban idon mu ya sungume ta ya tafi da ita, bayan ya gama da ita, Allah ma yasa ba yan yankan kai bane wallahi."
"Subhanallah!"
Sai a sannan Baba yayi magana yana jan murya
"Kayi wa Allah idan diyata na hannun ku ku fito min da ita, hankalin mu gaba daya a tashe yake, dan Allah na roke ka."
"Wallahi Baba bansan komai akan maganar da kuka zo da ita ba, amma me zai hana mu bar maganar zuwa garin Allah ya waye, a lokacin masu gidan ma sun tashi, kunga sai ayi magana sosai."
"Kana nufin mu bar maganar yar mu har sai gobe, bamu san halin da take ciki ba, idan ma cinye ta za'a yi ko kashe ta zuwa goben kaga shikenan ko?saboda ba yarka bace ta bata ba. Toh wallahi ba'a isa ba."
"Ni dai kuyi hakuri dan Allah."
Zasu sake magana Baba ya dakatar dasu
"Mu bar wa goben idan Allah ya kaimu, ita kuma Allah ya bayyana mana ita, ku muje dare na sake yi."
Haushi ne ya taso wa Garbati, ba haka yaso a tashi wasan ba, so yayi su kutsa kai gidan ya samu damar cin uwar yaron nan, kwafa yayi a ransa yana ayyana kalar rashin mutuncin da zai masa idan Allah ya haɗa su. Zai gane ya tana Gaza Boy.
***Karamin asibitin dake garin suka kaita, babu alamun ma ana aiki a asibitin, maigadi ne kawai yayi saura da yar karamar torchlight din sa babu isasshen haske, Farouk kamar zaiyi kuka haka yaji sanda maigadin ke musu bayanin babu kowa a ciki sai majinyata. Juyawa sukayi suka dau hanyar fita daga kauyen baki daya.
A lokacin jiki na ya kara tsami sosai, ko ina ciwo yake min zufa nake kamar wadda ta hadiyi kunama, babu abinda nake sai kuka Amal na tayani, Dada kam duk hankalin ta ya kara tashi, musamman ganin yanayin da na sake shiga daga fitowar mu zuwa yanzu.
Juyowa yayi a hankali yana kallon bayan motar be ce komai ba sai kura musu ido da yayi yana jin kamar ya bude motar ya fita, yasan Amal da raguwar zuciya da saurin kuka, kasancewar ta marainiya wadda bata san mahaifiyar ta ba yasa yake tausaya mata, baya son ko kadan yaji kukan ta, sai dai kukan yarinyar da yake ji yana neman danne kukan Amal din, har ya zama baya jin na Amal din sai nata kawai dake masa yawo a cikin kunnen sa, zuciya da ruhin sa.
Suna zuwa asibitin aka karbe su, suka zauna a reception aka shiga da ita ciki, Farouk kasa zama yayi ya shiga kai kawo a wajen yana ayyana rashin imanin wasu mazan, basu da maraba da dabbobi. Fitowar Dr Iman yasa duk suka mike, kallon su tayi sosai taga babu alamun kauyanci a tattare dasu, dan bata fuska tayi kafin tace
"Kuzo office Ina son magana daku ku biyu." Ta fada tana nuna Farouk da Dada, rufa mata baya sukayi suna shiga ta tura kofar tana jingina a jikin kujerar ta
"Menene alakar ku da patient din nan?"
Kallon Farouk Dada tayi zatayi magana yayi saurin katse ta
"We are Family Dr."
"Good." Tace tana zama
"Kenan my guess was right, kunyi wa yarinya karama at her age aure, sannan saboda rashin imani ka kasa hakuri da kankantar ta, kayi forcing kanka akanta ko?"
"A ah likita..." Dada tayi saurin katse ta, kafin ta k'arasa yayi maza ya sauke kansa kasa a hankali ya furta.
"Haka ne Dr, I'm very sorry, kuskure ne."
Biron hannun ta ta saka a bakinta tana kallon sa, shi a karan kansa ba wani babba bane, bata jin zai dora shekaru 20 idan ya dara to ba zai fi da biyu zuwa da hudu ba, yanayin jikin sa na girma da cika yasa zaka kasa tantance shekarun sa, sai dai duk da hakan ba za'a hada shi da yarinya yar shekara goma da doriya ba. Cire glasses din idon ta tayi ta fara magana a hankali cike da nasiha, dan a yadda tayi niyyar shigar dashi kara duba da yadda ta ga halin da ya saka yarinyar a ciki, sai dai yadda ya amsa laifin sa kai tsaye yasa ya sauko ta shiga nasiha da dukkan kokarin ta.
Hannayen Dada a makale da ita ta zuba su akan Farouk din, mamaki ne karara kwance a fuskar ta, bata gane nufin sa ba, bata gane inda ya dosa ba, tasan shi da tsananin tausayi amma bata taɓa tunanin zai iya aikata daukar laifi a ajiye akansa ba, tuni zuciyarta ta sake tsinkewa, idan har hakan ne kuwa ya tabbata Farouk din ne ya bata musu yarinya, in kuwa hakan ta kasance bata san ya zatayi ba.
Bayan sun fito daga dakin Dr yaki yadda su hada ido sam Dada, yasani sarai tana bukatar gamsasshen bayani, amma baya so ya sanar mata da komai sai ya samu nutsuwar zuciya.
Dakin da aka kwantar da ita suka tura suka shiga, Amal na zaune kan kujera tana bacci, drip ne a daure hannun ta, bacci take sai dai yanayin fitar numfashin ta ya nuna tsantsar wahalar da take ciki, karasa wa yayi gaban gadon yana sake kallon ta.
"Umar!"
Dada ta kira sunan sa, yanayin Muryar ta kadai yasa ya gane abinda zata ce, kasa juyowa yayi har sa data maimaita kiran nasa.
"Na'am Swthrt."
"Ba wasa nake maka ba, kasan kuma ni ɗin ba sa'ar tsohon ka bace balle kace zaka maida ni mara hankali ko wata chan daban, wacece yarinyar nan? Menene alakar ka da ita?"
Juyowa yayi yana fuskantar ta, ganin ta bata rai sosai babu alamun wasa yasa shi takowa har gaban ta. Sai da ya daidaita tsayuwar sa a gaban ta sannan ya fara magana cikin son gamsar da ita.
"Kiyi hakuri idan na bata miki rai, hakan da nayi ba wai nayi ne dan na bata miki ba, wallahil azim bani da wata alaƙa da ita,hasalima bansan wacece ita ba, bansan komai game da ita ba."
"Aina ka samo ta toh idan baka santa ba?"
"A daidai lokacin da Allah ya saukar mana da daya daga cikin ni'imomin sa, a daidai lokacin wani mara imani ya aikata mata wannan aika aikar, babu digon tausayi ko imani a tattare dashi, bansan shi ba, bansan waye ba, ihun ta kadai naji, na taimaka mata."
Kallon sa take har ya kai karshe, ganin bata ce komai ba yasa shi kama hannun ta
"Ki yarda dani, ba zan taba iya aikata wa wata mace makamancin wannan ba."
"Naji! Amma menene dalilin ka na amsa wa likitar nan a matsayin kaine mijin ta? Baka tsoron maganar ta fita, bayan kasan waye mahaifin kuma."
"Hakan shine daidai, karki manta wannan abun babban tabo ne a tattare da duk wata ya mace, da zai iya zama wani babban gibi a rayuwar ta. Banyi hakan da wata manufa ba face don kare mutuncin ta."
Turo kofar akayi, hakan yasa yayi shiru yana duban su, Dr Iman ce sai wata nurse a bayan ta.
Dan dube duben su sukayi suka juya, har ta kai kofa ta juyo.
"Af na manta, akwai alluran da za'a yi mata da safe gobe, , so ka zama around please."
"In Sha Allah."
"Good."
"Kai zaka kwana kenan?" Dada ta fada tana kura masa ido, har zai ce eh sai kuma yayi wani tunanin daban
"A ah, kece zaki taimaka."
"Amal fa? Kalli a yadda tayi bacci."
"Eh zanje na tambaye su idan akwai spare gado sai su bamu mu biya sai ku kwanta akai, dama dare yayi yanzu komawa hanyar nan akwai risk, in yaso ni sai mu kwana a mota."
Dan jim tayi kadan kamar zatayi magana sai kuma ta girgiza kanta kawai ba tare da tace komai ba ta koma gefen gadon ta zauna tana kura mata ido kamar me karanto wani abu a tattare da ita.
***
Da safe na bude ido na ina karewa dakin kallo, daidai lokacin aka turo kofar aka shigo hade da sallama, zuba masa ido nayi ina kallon sa har ya iso gaban gadon, shi din ma kallon nawa yake fuskar sa dauke da murmushi. Juyawa yayi yana kallon Amal dake bacci hankalin ta a kwance, karar ruwan da yaji a toilet yasa ya gane Dada na ciki. Sake matsowa yayi gaban gadon ya furta a hankali
"Ya jikin?"
"Da sauki." Na amsa da sauri ina kallo sa
"Sannu kinji."
"Toh." Nace ina sake bin fuskar sa da kallo kamar me son tuno abu. Murmushi ya sake yi yana kallon drip din dake shiga cikin jikina a hankali, file din dake ajiye saman drawer saka magunguna ya dauka yana dubawa har Dada ta fito.
***Yanayin horn din kadai ya tashi kowa na gidan, a firgice su ja'afar suka fito falo kowa ya tsaya, ba sai an fada musu ba sun san kowa ye, tsoron su daya abinda ya kawo shi a irin wannan lokacin, iya sanin su ma baya kasar baki d'aya. Motoci uku ne suka shigo a jere, kai kawo Baba maigadi ya shiga yi har suka daidai ta a harabar gidan. Cikin shigar sa ta Babban sojin kasa ya fito daga motar fuskar sa dauke da yanayi marar misaltuwa.
"Barka da zuwa." Kawai kake ji kowa na kawo gaisuwa. Jiki a sanyaye su Ja'afar suka dunguma zuwa harabar gidan kowa tsoro fal zuciyar sa.
A daidai lokacin aka fara bugo da mugun karfi kamar za'a balla gate din gidan, hayaniyar mutane ke tashi da alama ba mutane ne kadan ba. Da sauri ya kalli Baba maigadi Yana neman karin bayani.
ZAFAFA BIYAR
KAUNAR MU: MAMUH GEE
ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA
GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL
DAURIN GORO:HAFSAT RANO.
IGIYAR ZATO: MISS XOXO
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_
Mucigaba da shakatawa da wannan kafin a fara kafta WASAN😁👉🏻📻*DG*
©️Rano
ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
ALKALAMI TV
https://youtu.be/LxY42ErBf_8
(4)
*****
Babu wanda yayi kwakwaran motsi a cikin su, kowa da abinda yake ayyanawa a ransa. Jin bugun na sake karfi ne yasa shi juyawa da kansa ba tare da yayi magana ba ya nufi hanyar gate din. Budewa yayi yana kallon mutane dake tsaye, wasu dauke da makami, ganin haka yasa sojojin sa suka yo wajen da sauri. Hannu yasa ya dakatar dasu yana bin mutanen daya bayan daya cikin tsananin tashin hankali, sai dai duk da hakan ba zaka tantance yanayin da yake ciki ba, fuskar sa tana nan kamar ko da yaushe.
"A fito mana da yar mu!" Muryar daya daga ciki ta bakunci jin sa, daya bayan daya ya hau kokarin fassara kalmomin acikin yan sakanni.
Take wajen ya kaure da ihun kalmar da yake da bukatar amsar ta cikin gaggawa. Sake daidaita kansa yayi, ya kuma saka dukkan jikin sa ya fito waje sosai yana sake duban su, mutane ne yawancin matasa sai wasu dattijai guda uku daga gefe, kai tsaye ya nufi wajen su, yana me sake daidai ta kansa. Yana isa ya mika musu hannu daya bayan daya, kwarjinin sa ya cika wajen baki daya. Lawan dake niyyar rashin kirki ya ji ba zai iya ba, girma da cikar haibar sa kadai ta isa ka girmama shi. Balle kuma da shigar sa ta nuna ainihin shi din waye ne. A nutse ya kai duban shi wajen sauran yaran kana ya maida kansa garesu
"Me yake faruwa?"
Ya tambaya yana nuna su Garbati,
"Yar mu wadda take cikin gidan nan muka zo tafiya da ita."
"Yar ku? Kuyi hakuri ban gane kan maganar ba, zuwa na kenan."
"Alhaji jiya daya daga cikin yaran gidan nan ya dauke mana yar mu, bayan mun gaji da neman ta muke samun labari ta wajen daya da ga cikin matasan garin da abin ya faru akan idon sa, toh jiya munzo a daren bamu samu ganin kowa na gidan ba sai Maigadi, shiyasa muka shiryo muka zo yanzu, dan har mun sanar wa maigari ma."
Hannu yasa yana shafa kansa, be tsinci komai a bayanin ba, sai dai ya fuskanci suna zargin batan yar su ne a gidan sa, a gidan nasa ma kuma cikin yaran sa, dan jim yayi kadan yana nazari kafin yace
"Ku bani mintina biyu dan Allah ina zuwa."
Juyawa yayi ya nufi cikin gidan, ya zo shiga Garbati ya daga murya yadda zaiji sosai yace
"Wallahi sai an fito da ita, ga Fyade ga sata, haba ai abin yayi yawa."
Chak ya tsaya da tafiyar da yake, wani irin bugu zuciyar sa tayi, babu abu daya daya ki jinin ji kamar kalmar fyade. Maganganun da suka cigaba ne suka shiga maimaita kansu a cikin kwanyar sa, da sauri ya fada gidan, suna nan tsaye duk a in da ya barsu, daya bayan daya ya shiga binsu da kallo kamar me lissafa su, duk sun tsure iya kar tsurewa sun gama sanin me hakan ke nufi.
"Ina Farouk?"
Shiru babu wanda yayi magana, a fusace ya sake tambaya cikin daga murya sosai. Da sauri har suna hada baki suka ce
"Sun...sun fita da Dada da Amal."
" Ina suka tafi da sassafe haka bayan kuma ku da alama ko dukkanku tashin ku kenan."
"Asibiti suka tafi kai wata yarinyar."
Dafe kansa yayi ganin zancen na fitowa.
"Da yaushe suka tafi?"
"Jiya da daddare."
***
Zama Dada tayi tana jiran Amal ta idar da sallah, Farouk na zaune a kan kujerar dakin yayi nisa a tunani, shi kadai yasan me yake tunawa, alluran da ya kamata ayi mata duk anyi mata. Tana idar wa ta tashi ta je gaban gadon tana kallon ta
"Ya Farouk ta samu sauki ko?" Ta tambaya tana nuna masa ita. Daga mata kai yayi yana murmushi
"Amma mene sunan ta?"
Girgiza mata kai yayi alamar shima be sani ba, murmushi tayi tana sake kallon ta.
"Ina son ta da kawa, me kyau kamar ta cikin cartoon din nan."
"Tashi zakiyi mu tafi ba surutu zaki tsaya yi ba."
Sai kuma ta maida kallon ta wajen Farouk
"Kai ma tashi zakayi muje, idan yaso sai a nemi iyayen ta a sanar musu suzo dan yanzu nasan hankalin su a tashe yake."
"Da wai sai na zauna da ita har suzo ɗin, kinga be kamata a bar ta ita Kadai ba."
"Farouk!" Ta bude idon ta sosai
"Baka da hankali ko? Kasan abinda hakan zai haifar? Lallai kai yaro ne."
"Dadah ki barmu anan nida Ya Farouk dan Allah, kinga idan ta tashi bata ga kowa ba zatayi kuka."
"Toh uwar iya, wallahi tashi zakuyi mu tafi, ba zan iya da matsalar da zata taso ba, na riga nayi magana da wata nurse zasu shigo suna dubata har suzo iyayen nata."
Kamar ya fashe da kuka haka yaji, shi be ga dalilin da zai sa Dada tace sai sun tafi ba, gashi idan ta kafe babu abinda zai sa ta hakura, tashi yayi tsam yana kallon gadon kafin ya juya ya fice da sauri. Kwafa tayi ta ja hannun Amal suka fito, a tsaye ta hango shi tare da Dr Iman suna magana, karasawa tayi wajen
"Dr Barka da safiya."
"Yawwa Mama, ya me jiki?"
"Alhamdulillah, mungode Allah."
"Allah ya kara sauki, zan shiga sai na duba jikin nata."
"Ok Dr, nima zan dan je gida ne na dawo."
"Ok yayi,ka same ni a office idan na gama round zan yi magana da kai, amma yanzu ka koma dakin karta farka taga babu kowa."
Ta fada tana yin gaba,kallon Dada yayi yana marairaice fuska, ganin yadda tayi kicin kicin da fuska.
"Sai ka zauna ai dama abinda kake so kenan, amma wallahi Babana ina ji maka tsoron abinda zai je ya dawo, ba fata nake ma ba, amma baka san halin mutanen mu ba."
"Babu abinda zai faru sai Alkhairi Dada." Ya fada cikin gamsuwa.
"Shikenan, Allah yasa."
"Amin." Yace yana murmushi.
"Zan tsaya wajen ka Yah."
Kama bakin sa yayi da sauri yana kallon Dadan, tsaki tayi ta juya tana mitar sun raina ta.
Ciki suka koma da sauri, har lokacin bata tashi ba tana sauke numfashi a hankali.
****
Zagaye da hannayen sa yake kaiwa da komowa, wani irin tashin hankali me matukar girma yake hasasowa idan har abinda yaji ya zama gaske, ya zaiyi? Da wacce fuskar zai kalli mutanen kauyen. Tabbas idan hakan ta kasan zai dauki mummunan mataki akan Farouk, baya fatan zargin sa ya zama gaskiya dan zai iya yafe shi ba ma a cikin yayansa ba, a cikin dukkan ahalinsa. Duk kuwa da dimbin soyayyar da yake masa duk cikin ya'yansa.
Jin tsayuwar mota yasa ya juyo da sauri yana kallon gate din da tun zuwan sa yake tsaye wajen ya rasa me zaiyi. Idanun sa akan gate din har aka gama budeshi. Ganin motar gidan yasa ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya, duk da baya hango cikin motar amma yasan sune suka dawo, a yau da ace ba tare da mahaifiyar sa suka tafi ba be san abinda zai iya aikata mishi ba, sai dai dole ya saita kansa yaji komai a baƙin ta. Hannun sa ya harde a kirji yana jiran daidaituwar motar da yake ganin kamar da gangan driver yake lankan jin ajiye ta a mazaunin ta.
Dada ce ta fito tana me kallon harabar gidan cikin tarardadin abinda yake faruwa, farko mutanen da ke waje tsaye kamar masu jiran a fito musu da gawa su kaita kushewa, sunyi kungiya kungiya suna tattaunawa, yanzu kuma tsayuwar Janar a harabar gidan ya kara tabbatar mata da abinda take tsoro take gudu ne ya faru. Jiki a sabule irin na wanda yayi fama a filin daga ya isa gareta kafin ta ƙaraso.
"Dadah.!
Ya furta muryar sa a bude sosai me nuna yanayin da yake ciki.
"Muje ciki." Ta fada tana kallon sojojin da sukayi dafifi a wajen suna tsaye cikin jiran cika umarnin uban gidan na su. Be musa ba, sai jan kafar sa da yayi da tayi matukar sanyi yabi bayanta.
Ajiye mayafin ta tayi ta zauna tana daidata nutsuwar ta, dan tabbas ta hango tsananin tashin hankali da firgici a idon yaron nata, kasancewar sa babban soja hakan be sashi zamaar mata tamkar yaron goye a duk sanda yake tare da ita ba. Tabbas haka Farouk yake, a duk yayansa shine ya biyo shi, babu abu daya daya bari nasan tun daga dabi'a da yanayin yadda yake daukar a'alamri, abu daya tasani shine Farouk yana da sanyin zuciya da saurin yarda da komai, banbancin sa da mahaifinsa kenan wanda ya kasance mutum me tsauri sosai da rashin yarda a duk sanda abu ya gifta tsakanin ku, duk yadda kake dashi zai bar ka, barwa ta har abadah kamar yadda suka rabu da mata mafi soyuwa a gareshi bisa babban kuskuren data aikata masa.
Ruwan da aka ajiye a gaban ta ta kalla tana kallon Ja'afar daya kawo ruwan. Dauka tayi ta zuba ta mika masa.
"Sha ruwa Muhammadu, ko zaka ji saukin zuciyar ka."
Karba yayi ba tare da yayi magana ba ya kafa kai ya shanye tas yana ajiye kofin.
"Me yake faruwa?" Ta wurgo masa tambayar tana nakaltar nazarin sa. Sai da ya sauke ajiyar zuciya kafin yayi magana cikin dakiya
"Ni kaina na rasa me yake faruwa, zuwa na kenan, na tarar da wannan tashin hankalin, shin da gaske ne abinda mutanen garin nan ke tuhumar Farouk?."
"Me suke tuhumar shi akai? Maganar yarinya ne ko?"
Ta fada kai tsaye dan tasan kwanan maganar kenan.
"Eh ita Dada, suna zargin Farouk da yi wa yarinyar su fyade sannan kuma ya sace ta, wannan wanne irin tashin hankali ne Dada."
Shiru tayi tana maimaita innalillah wa inna ilaihi raji'un a ranta, abinda take gudar wa Farouk kenan, ya kasa ganewa.
"Dadah dan Allah, ina ya kai yarinyar, kuma shin da gaske abinda suke zargin sa akai ya aikata?"
"Yarinya dai tana asibiti dan yanzu ma daga chan nake, kuma tabbas yazo da yarinya a cikin mayuwacin hali, kuma nayi magana dashi na tambaye shi idan shine ya aikata mata, yayi mun rantsuwar dan musulmi bashi bane."
"Shikenan, Farouk ya gama dani."
"A ah kar kayi saurin yanke hukunci, ka tsaya kaji ta bakin nasa."
"Haba Dadah, yaran yanzu fa sun wuce tunanin mutum, kuma ba'a shaidar su sam, dan wanda kake ganin ba zai aikata abu ba yafi aikatawa."
"Yanzu menene abinyi?"
"Tashi zanyi naje asibitin, gani gashi ga iyayen yarinyar, harda maigari ma."
"Shikenan, amma kabi komai a sannu."
****
Shigar su dakin yayi daidai da sake farkawar ta, a dan tsorace take kallon su, kafin ta maida idon ta da sauri ta kulle su gam. Amal ce tayi saurin karasawa wajen gadon ta rik'e hannun ta, jin an rik'e ta yasa ta bude ido ta sauke su akan ta.
"Ya sunan ki?" Amal ta tambaya dan ta matsu tasan sunan ta.
"AMINATU!"
Da sauri ya juyo, sosai yaji sunan nata har cikin ransa, sauti da amon muryarta ya shiga masa amsa kuwwa, yana jin Amal na fada masa sunan su daya tana murna ya kasa amsa mata, sai ma binsu da ido kawai da yake yi kamar be san me yake faruwa ba.
Hira sosai Amal ta shiga yi mata, kallon ta kawai take yi ba tare da ta gane komai ba, ido kawai tasa mata.
"Zan sha ruwa." Ta furta a hankali, da sauri Amal ta tashi ta dauko mata ruwan, kokarin tashi tayi taji zafi, kuka ta saka yayi saurin tasowa,
"Sannu."
Daga masa kai tayi tana gogen hawayen da bayan idon ta. Ruwan ya bata Amal na tsaye kamar zatayi kuka.
"Gida zan tafi." Tace tana kallon sa.
Zaiyi magana aka turo kofar, wani irin faduwa gaban sa yayi yasa hannu ya rike wajen zuciyar sa da sauri.
"Daddy!"
Amal ta fad'a tayi wajen sa da sauri, rike ta yayi ya matsar da ita gefe bayan ya shafa kanta, Maigari ne ya fara shigowa,sai Baba, Inno na bin bayan sa, sai Lawan Da Yahya. Garbati da Ilu suna take musu baya. Da sauri Inno tayi wajen gadon tana sakin kuka.
Gyaran murya maigari yayi, Inno tayi shiru duk aka nutsu ana kallon sa.
"Garbah!" Ya kira sunan Garbati yana masa alamun ya matso.
"Maimaita abinda kace."
Gyara tsaiwar sa yayi cikin dakiya ya nuna Farouk da hannun sa
"Gashi nan, jiya ana ruwan nan ta gefen daki na naji kamar ana kuka, da har na share sai na kuma jin kukan na tsananta, kamar wasa na dauko toci ta na leko, in haska sai ga tashin hankali, ido na cikin nasa yana aikatawa karamar yarinya, nayi kukan kura na rike shi, muka haure da kokawa, shine fa ya samu yayi min mugun duka, kuma ya dauke ta ya gudu, duk da haka sai dana bisu a baya, naga gidan daya shigar da ita, shine fa nayi gaggawar zuwa sanar da iyayen yarinyar."
Tun da ya fara magana Farouk ke kallon sa, gaba daya jijiyar kansa ta fito, numfashin sa ya shiga fita da sauri da sauri, duk suka zuba masa ido suna kallon sa, Daddy kuwa kasa yayi da kansa yana jin kamar kasa ta zage ya shige, sai dai bashi da ta cewa, duk abinda gaskiya ta bayyana zai goyi bayan ta, ba zai taba goyon bayan zalunci ba ko da daga dan cikin sa ne.
"Kaji abinda ake tuhumar ka dashi, shin kana da abinda zaka kare kanka, duk da dai ga zahirin ganin ku tare da mukayi anan, amma ko zaka fada mana dalilin da ya jawo hakan."
Maigari ya fada yana duban shi, kokarin magana yake ya kasa, motsa bakin sa yake ya kasa, kallon Garbati kawai yake cikin tsananin bacin rai, bai taba tunanin akwai mutane masu aiki irin na dabbobi kamar shi din ba, kallon Amal yayi yaga ta zuba masa ido kamar me son ganin wani abu, ya sake maida kansa wajen Aminatu, itama shi take kallo, tana share kwallar dake zubo mata. Runtse idon sa yayi ya bude ya maida kallon sa wajen Daddy, yanayin daya ga fuskar sa kawai ta gamsar dashi abin da zai je yazo idan har ya kasa fitar da kanshi daga wannan daurin. Kokarin daidai ta kansa yayi ya shiga kokarin magana a nutse duk kuwa da tarin tashin hankalin da yake ciki
"Allah ne..."
"Kai ne kayi mata Fyade ko ba kai bane!" Daddy ya fada cikin k'araji dan ya gaji so yake kawai ya amsa da a ah ko Eh.
"Daddy Wallahi tallahi Allah ne shaida ta..."
"Will you shut your mouth, amsar ka kawai nake so kai ne ka aikata mata Fyade ko kuwa?"
"Fyade!"
Dr Iman da shigowar ta kenan ta karbi kalmar, duk suka juyo suka kalle ta.
"I'm sorry to interrupt, kuna nufin dama yaron nan ba mijin ta bane, fyade yayi mata suka rufa min yace shi mijin ta ne?"
Da sauri Farouk ya kalle ta zuciyar sa na sake tsinkewa.
DAURIN GORO😢😢😥😥😓
ZAFAFA BIYAR
KAUNAR MU: MAMUH GEE
ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA
GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL
DAURIN GORO:HAFSAT RANO.
IGIYAR ZATO: MISS XOXO
LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_*DG* 5
*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo
©*Rano*
(5)
****
Duk suka maida kallon sa gare ta, takowa tayi ciki tana kallon fuskar Farouk din.
"Me kike cewa Dr?" Daddy ya tambaya yana kallon fuskar Farouk din
"Nice likitar data karbi case din yarinyar, a yadda mukayi magana na zata matar sa ce, dan shi dinma ya nuna min hakan, duk da cewa akwai karancin shekarun ta da nashin ma kansa, sai dai ya amsa laifin sa kuma ya bada hakuri, amma kuma naji wata maganar daban duk da ba dani ake ba, amma ina da right na sani saboda matsayi na na likitar ta."
"Babu wata matar shi, makaryaci fyade yayi mata kila ma sai daya sha ya bugu sosai sannan."
Garbati ya fada yana huci. Kasa hakuri Farouk yayi ya kalle shi cikin konar rai
"Sharrin da zakayi min kenan, kasan nasan komai shine kake kokarin jona min laifin da ka aikata?"
"Ni? Ni zaka wa sharri, na ganka ido da ido, shine zaka maida abin kai na, na shiga uku, wallahi Maigari karya yake min so yake ya maida abin kaina."
Sake duban sa Farouk yayi yace
"Kaji tsoron Allah, ka sani akwai mutuwa akwai hisabi, kar kaga idon mutane anan, ka fadi gaskiya ko dan rayuwar yarinya karama."
"Wallahi tallahi sharri yake min, shine ya aikata karya yake min wallahi." Garbati ya fada yana karashe wa da fashewa da kuka kamar gaske.
Dafa kai Daddy yayi ya kalli farouk, ya gaji da wasan yaran nan da suke musu, magana daya yake son ji, idan shi ya aikata ya amsa eh ko a'ah. Rike masa riga yayi cikin bacin rai
"I'm asking u for the last time, Kai ne ko ba kai ne ba?"
Kukan Amal da Aminatu ne ya kara karfi a wajen, juyawa Farouk yayi ya dube su daya bayan daya, sosai kukan nasu yake taba masa rai, kallon Daddy yayi ya shiga girgiza kai.
"Alhaji ina ganin tun da ga yarinyar nan a zaune, duk da karama ce amma ba zata kasa tantance wani abu ba, ina ganin a tambaye ta, idan yaso kowa ne ya aikata mata wannan abin, a cikin su, to fa dole ne a aura masa ita bayan hukuncin da shari'a ta gindaya ga wanda ya aikata irin wannan laifin, dan kaf kauyen nan namu babu wanda zai yarda ya karbi aurenta, musamman yanzu da zance ya zagaya ko ina, ina tsoron sai dai ta karasa rayuwar ta a haka."
Maigari ya katse su, sakin sa Daddy yayi ya hankada shi har sai daya kusa bigewa da karfen gadon, dago idon sa yayi ya sauka cikin nata, wani irin abu yaji ya taba shi, wanda be taba jin irin sa ba, raunin da ya gani a cikin idon ta, yarintar ta da tsantsar tausayin ta suka hadu. Idan har yaji daidai abinda mai gari ya fada, yana nufin aura wa Garbati ita kenan, auren da yake nufin lalacewar rayuwarta har abadah, auren da yake nufin yanker war duk wani jin dadi na rayuwar ta, auren da yake nufin rayuwa da mutum wanda bashi da maraba da dabba, dabbar ma mafi kaskanci acikin dabbobi. Kasa dagowa yayi ya rasa me yake masa dad'i, yana jin sanda Maigari ya kira sunanta, yana jin lokacin da ya tambaye ta, kukan ta ya kara karfi, be san yaushe ba, be san yaya ba, kawai ya samu kansa da amsawa a maimakon ta tun kafin ta samu damar yin magana. Da wani irin karfi Daddy ya riko shi, ya shak'e shi, kakari ya fara kamar wanda yake shirin mutuwa cikin sauri Baba ya shiga tsakani. Yayi kokarin bangare shi daga rikon da yayi masa,
"Alhaji kar kayi mishi illah."
Ya fada cikin tashin hankali ganin yadda idon yaron ya kakkafe
"Barni na kashe shi, ya cancanci haka, ko ma fiye da hakan, barni dan Allah, harbe shi zanyi kowa ya huta." Ya sake riƙe shi sosai, bugu ya fara kai masa ta ko ina, tun Farouk na kokarin kwatar kansa har jikin sa ya saki ya shiga fitar da jini ta ko ina.
Lawan da sauran ne suka shiga tsakani, ganin haka yasa Garbati da Ilu sulale wa su bar dakin suna fita suka ci karo da sojoji, a darare suka gifta su suka bar asibitin da sauri.
Ba karamin duka yayi masa ba, da kyar suka kwace su, duk da haka sai daya hankad'a shi da karfi kansa ya fashe, Amal ce tayi saurin isa wajen sa tana kuka taa dago shi.
Haki kawai Daddy yake, kamar wanda ya shiga filin daga, cikin tsananin bacin rai ya nuna shi da hannu yana kallan su Maigari.
"Maigari, Malam da sauran wanda suke wajen nan, ku zama shaida, ga shi nan, duk hukuncin da kuka yanke akansa bani da ja, kuyi masa duk abinda kuka ga dama babu ruwana, karku duba girma na, arziki na ko khakhi na, kuyi masa hukuncin daya dace daidai dashi."
Ya dora...
"Sai dai ina neman alfarmar kowanne hukunci za'a yanke ya zama cikin kwana biyu, dan zan koma in da na fito."
Juyawa yayi ya nufi kofar fita da sauri yana jin ba'a taba bata mishi rai irin na yau ba. Daya bayan daya suke dinga zamewa suna barin dakin ya rage sai su Inno kawai. Tashi tayi ta dago shi tana kallon fuskar sa
"Baka aikata abinda ake zargin ka dashi ba, amma me yasa ka dauki laifi me girma ka dora akan ka?"
Ta tambaya tana karantar sa.
Mik'ewa yayi yana goge bakin sa yana kallonta
"Bansani ba, bansan dalili ba. Ina ganin hakan da nayi shine kawai mafita."
Juyawa yayi ya bar dakin Yana rangaji, Amal ta bishi da sauri tana kiran sa.
Kuka na fashe dashi, Inno ta harare ni tana zama a gefe na
"Kukan uban me kike?"
"Inno kinga fa kuka yake, duk kuma jini a jikin sa, yana da kirki sosai."
"Toh sai akayi uban me? Ke yanzu karamar ki dake kinsan wani yana kuka, baki ji maganar da mai gari yayi ba, idan na yarda akayi miki aure idan ranar da nake jira tazo nayi yaya kenan?"
"Na'am?" Na tambaya cikin rashin gane abinda take nufi
"Manta kawai, abu daya nake so dake, idan aka tambaye ki kice ba zaki auri kowa ba, babu inda zaki matsa daga nan sai ranar da Allah ya yanke miki wahalar nan."
Gid'a mata kai nayi ina share hawayen dake faman kaikawo a fuskata kamar an kunna fanfo.
Tashi nayi ta taimaka min na wanke fuska ta, ina zama ya shigo fuskar sa anyi dressing ya dire kayan tea ba tare da yayi magana ba ya juya ya sake fita.
***
A hargitse ya shiga gidan, Dada na zaune a falo tana jira shigowar sa, ganin yanayin sa yasa tasan komai ya ɓaci, be zauna ba, ya shiga kwala wa su Ja'afar kira, sai daya tara su duka sannan ya hau fada, sosai yayi musu fada sannan yace duk su shirya kaya zasu bar garin a ranar. Duk suka amsa da toh sannan ya sallame su. Zama yayi cikin kujerar falon yana zare butiran din hannun sa.
"Dadah yaron nan ya amsa laifin sa, dan yau dama ka haife shi ne baka haifi halin sa ba."
"Yanzu menene abin yi? Kana nufin shi baban nawa ya amsa laifin?"
"Ya amsa har ma sun yanke hukuncin bashi auren ta."
Da sauri ta tashi
"Aure kuma? Dududu Baban nawa nawa yake? Karka manta alƙawarin da kayi wa Marigayi."
"Toh ya za'a yi Dadah, tun da yasan ya bata wa yar karamar yarinya rayuwa ai gwara a aura masa ita kawai kowa ya huta, idan yaso sai ya hakura da karatun nasa su zauna anan ɗin tunda irin rayuwar da ya zaba ma kansa kenan."
"Amma ka tabbata shi ya aikata?"
"Nima da ina ta tunanin hakan, amma daga baya daya amince da laifin nasa kinga ai babu maganar tantama, ya aikata din"
"Kai wannan abu beyi dadi ba, amma ita yarinyar fa? Bata fadi kowa ba?"
"Kin ganta dai Dadah, karama ce sosai dan ko Amal ta fita girma da cika ido, ga kuma kauyanci da rashin wayewa, bayan haka ba'a kai ga tambayar yarinyar ba ya amsa laifin sa, kinga ai babu bukatar kuma wani dogon bincike da dai be amsa bane."
"Toh Allah ya sauwake, amma sam banji dadin abin nan ba, amma dai ƙaddara ce dan sam ba haka halin babana yake ba kai ma ka sani, bansan dai me ya faru ba, Allah ya kara kiyaye wa."
"Amin ya ALLAH."
"Bari na shiga ciki, in sha Allah da an gama komai jibi zamu wuce baki daya, su yaran suyi gaba yau, nima ina da ayyukan yi da yawa, dalilin admission din farouk din ne ya shigo dani garin wallahi."
****
Tafiya yake a kasa bayan ya bawa driver umarnin ya maida Amal gida, be san ina yake saka ƙafarsa ba, ya dai san kawai yana tafiya ne akan kasa, sai dai kafatanin tunanin sa ya tafi ne akan abinda ya faru a yan awannin da basu wuce ashirin ba, gaba daya rayuwar sa ta chanja, ya rasa duk wani girma da kima a idon mahaifin sa, haka Allah yake ƙaddara wa bawa ƙaddarar sa, ba tare da ya shirya ma hakan ko yayi tunanin hakan zai taba kasancewa dashi ba.
Tsaiwar babur a gaban sa ce yasa ya dakata yana kallon na kai, Garbati ke da Ilu, cikin kazamar shiga irin ta yan Iskan kauye, sigari Garbati ya busa masa a fuska yana dariya.
"Ango ango."
"Lafiya?"
" Ita ce ta kawo hakan, ka dai ga kadan daga aikin Garbati ko?"
"Bani da lokacin tsayawa magana daku, kamar yadda ban dauke ku a cikin jerin mutane masu hankali ba."
Da haka ya rabe ta gefen su ya wuce, yana jin Garbati na kutuntuma masa ashar, be bi ta kai ba, burin sa kawai ya isa wajen da babu kowa.
Kansa ya haɗa da gwuiwar sa, ba zan iya fadar yanayin da yake ciki ba, zuciyar sa ta yi nauyi, ta cunkushe kamar zata budo kirjin sa ta fito, so yake yayi kuka ko zai samu sauki, sai dai babu ko digon hawaye sai na zuci da ya ka faman yi. Da fari ya so ya tabbatar da gaskiyar sa, ko dan irinsu Garbati masu halin dabbobi, sai dai furucin auren da yaji ne ya rusa komai, ba zai iya barin yarinya karama Kamar Amal ta rayu da Garbati ba, rayuwa irin ta aure me cike da tarin matsaloli, dalilin hakan yasa yayi ma kansa mugun dauri, daurin da yake tunanin har karshen rayuwar sa zai cigaba da bibiyar sa.
Ya jima sosai a wajen, ba zai iya lissafa adadin awowin daya bata ba, ya dai mike ne kawai da niyyar zuwa gidan ko me zai faru ya faru. Sai a lokacin ya lura da irin nisan tafiyar da yayi. Har ya karasa gidan be bar fargabar haduwa da Daddy ba, ya san shi sarai yasan abin da zai iya aikatawa akan shi, abun mafi tsoro a tattare dashi shine bakin sa, baya son wata kalma ta muzantawa ta fito daga bakin sa, ba zai iya daukar hakan ba sam.
Tura gate din yayi yaji shi a bude, a nutse ya tura kansa cikin gidan bakin sa dauke da addua, jami'an tsaron dake zube birjik a gidan ya fara cin karo dasu, duk suka zuba masa ido suna kallon sa, dauke kansa yayi ya haura kofar da zata sadaka da falon gidan. A dan tsorace ya tura kofar yana tarrradin abinda zai tarar, cikin tsawa aka dakatar dashi.
"Tsaya anan!" Da sauri ya tsaya yana maida hannayen sa baya kamar me shirin arcewa.
"John!" Daddy ya bud'e murya ya kwala kira, a guje ya shigo ya tsaya gaban sa.
"Lock him up."
Ya fada yana nuna masa Farouk dake tsaye kamar an dasa shi, yasan dama hakan zata faru.
"Yes sir!" Ya amsa da sauri ya chakumi wuyan Farouk kamar kayan wanki. Tirjiya ya fara yi yana magiya
"Daddy please ka saurare ni, dan Allah Daddy."
Ko gezau beyi ba, sai ma hade rai da ya sake yi yana wa John mugun kallo
"Me kake jira ne?"
Da sauri ya karasa janshi, ya fita dashi.
Tsaki Daddy ya ja ya tashi ya bar falon baki daya.
DAURIN GORO😢😢😥😥😓
ZAFAFA BIYAR
KAUNAR MU: MAMUH GEE
ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA
GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL
DAURIN GORO:HAFSAT RANO.
IGIYAR ZATO: MISS XOXO
LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_*DG*
*ZAFAFA BIYAR NA KUDINE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo
©Rano
(6)
***
Ina kwance ina ta kallon inno tana hada kan abubuwa da suke dakin, Nura ne ya shigo ya karba sannan ya fita dasu, kamani tayi ta lulluba min wani babban Mayafi muka fito, a hankali nake tafiya cikin wani yanayi mara dadi da ba zan iya tantancewa ba, har muka isa gaban motar da ban taba ganin irin ta ba, soja ne ya bude mana gidan baya muka shiga, ya rufe sannan muka dauke hanyar kauyen mu, kasancewar motar rufe take ruf da bakin gilashi hakan ya hana mutanen gari kallon mu, sai dai na lura duk in da muka bi sai an bimu da kallo. A kofar gida ya ajiye mu, Inno ta sake jan mayafin ta kare min fuska ta sosai ta fito dani, mata ne a tsaitsaye kowacce ta fito jin mota, da sauri Inno ta ja hannu na muka shige gida tana hararar su. Muna shiga matan gidan mu suka taso, kowa yana min sannu wadda ta kasance da biyu, daki Inno ta tura ni ta dawo wajen su tana amsa gaisuwar da suke min ta munafurci da gulma. Sun dan jima ina jiyo sautin karadin su, har suka watse, daga nan bacci ya dauke ni, ban sake sanin me yake faruwa ba.
A bangaren gidan Maigari kuwa ya aikata aka kirawo su Baba da Daddy. Inno najin hakan ta rufo ni a daki ta yafa mayafinta ta bisu, Baba be isa ya hanata ba sai dai babu yadda ya iya. Suna zuwa Daddy ma yana zuwa cikin shigar fararen kaya manya, cikin girmamawa suka gaisa gaba daya, Inno na makale a gefe tana jiran taji dalilin kiran.
"Abin da yasa na tara ku anan..."
Maigari ya soma
"Maganar da mukayi akan yaran nan, da kuma alfarmar da shi Alhaji ya nema ta a yi koma a kwana biyu, ina ganin abu daya da zamuyi wa yarmu shine aure, dan babu wani mutum a kaf kauyen nan da zai karbi auren ta, dan hakan ta taɓa faruwa a baya, a karshe saboda yadda yaran gari suka sako ita yarinyar a gaba yasa ta aikata abinda duk beyi mana dadi ba, shiyasa muka yanke hukuncin idan hakan ta sake faruwa, toh duk wanda aka tabbatar da ya aikata hakan xa'a aura masa yarinyar."
"Gaskiya ne." Duk suka amsa cikin gamsuwa.
"Toh yanzu Alhaji idan ka shirya, sai a gabatar da komai a nan."
"A shirye nake ranka ya dade, duk abinda ake bukata sai a sanar dani."
"Gaskiya ina da ja wallahi." Maganar Inno ta katse su,
"Ina dah ja maigari, ya kamata ace a matsayi na na uwar yar nan anyi shawara dani, amma ace kawai a yanke hukuncin yi mata aure babu izini na, yarinyar da dududu nawa take, gaskiya ni ban yarda ba."
Da tsananin mamaki suke kallon ta, babu uwa daya a kauyen nan kaf da irin hakan zata faru har ta tsaya jayayya, kamar bata san kalar wulakancin da yarinyar zata fuskanta ba?
"Menene dalilin ki, na kin abinda muka zo dashi?" Maigari ya wurgo mata tambayar
"Allah ya taimake ka, ni dai kawai bana so ne, ban yarda ayi mata aure yanzu ba, batun maganar mutane kuwa suyi tayi, zan san yadda zan ɓullo musu."
"Kaji abinda maidakin ka tace Malam Ayubah, yar nan dai yarku ce, ku kuka haife ta, duk soyayyar da zamu nuna mata ba kamar wadda kuke yi mata ba, menene ra'ayin ka akai?"
"Ranka ya dade ni dai na amince da maganar auren, ina ganin hakan shine kawai sauki."
Ya fada ba tare da ya kalli bangaren Inno ba, dan yasan idan ya yarda suka hada ido ba zata taba barin sa ya aikata zabin zuciyar sa ba.
"Sauran yan uwan yarinyar, shin kun amince ko kuwa?"
"Mun amince."
"Masha Allah, toh ke sai kiyi hakuri, dama aure a hannun Iyayen maza yake."
"Alhaji Bismillah."
Matsowa Daddy ya sake yi ya zura hannu a aljihun sa ya ciro kudi, alama yayi wa da driver sa ya fito da sauran kayan dake booth ɗin, ganin haka yasa Inno fashewa da kuka ta yi saurin fadawa gidan mai gari. Bisa ga shaidu da wakilan kowanne bangare aka shiga gabatar da daurin auren da ya zamo tsanin farko na duk wata rayuwa da Aminatu zata taka a gaba.
***
Cikin dare ta kasa bacci, babu abinda take sai juyi, bata san yadda zatayi ba, idan har auren nan na nufin katanga da cikar burin ta, zata iya komai akai, duk da babu wanda yasan abinda ya faru sai mutane uku kachal a duniyar nan, amma ba zata bari damar ta ta karshe ta kwace mata ba, wanda auren nan yana nufin rugujewar komai. Har akayi asubah tana bitar abu daya, bata jira gari ya gama haske ba, ta tashi Aminatu ta bata kunu, ta ballo mata magungunan ta ta bata sannan ta dauki yar karamar purse din ta da mayafin ta, ta fice daga gidan. Tafiya me nisan gaske tsakanin kauyen nasu da wanda ke makwabtaka dasu, sanda ta isa gari yayi haske sosai, mutum daya jallin jal data san sirrin ta, sirrin da yake shirin zama tarihi idan har ta aminta da wannan auren, wajen ta tazo, dan samun mafita. Da sallama ta shiga gidan duk matan gidan suka kalle ta cike da mamakin wannan zuwan nata da sassafe haka, gaishe su tayi a tsaitsaye bata damu da irin kallon da suke mata ba ta fada dakin wadda tazo wajen ta.
"Akwai matsala kenan." Ta fada tana kallon ta har ta ƙaraso ciki.
"Ita ce ta taso ni, ina cikin matsala wallahi harira, bansan ya zanyi ba."
"Lallai ai naga alama, me ya faru hala? Ko dai wani abun ya samu yar mutane ne?"
"Kusan haka." Ta cire mayafin ta ta zauna gefen gadon, sannan ta shiga bata labarin komai. Ajiyar zuciya Harira ta sauke bayan ta gama sauraron ta
"Kema dai Inno kinyi sakaci, bayan kinsan dalilinmu da kudurinmu a nan gaba, amma kikayi sakaci da yarinyar mutane har wannan abin ya faru da ita, kina ganin zasu yarda ne su kyale mu duk ranar da gaskiya ya fito? Bayan irin rikon da sukayi wa namu d'an."
"Duk nayi dana sani wallahi, zuciya ce ta d'ebe ni, amma yanzu na gano kuskure na, ki taymaka nidai da shawarar yadda za'a yi da auren nan, idan yaran nan ya dauke ta suka bar kauyen nan kina ganin zai sake dawowa da ita ne?"
"Gaskiya dai, gashi kince an riga an daura auren."
"An daura wallahi."
"Toh mafita daya ce gaskiya idan zaki iya..."
"Zanyi koma menene idan akan d'ana ne."
Murmushi harira tayi ta matso kusa da ita.
***
Kamar kayan wanki haka suka fito dashi, a kwana biyun da yayi duk yai baki ya rame sosai kamar ba shi ba, kauda kai Daddy yayi daga kallon sa, sun riga sun fito a shirye zasu tafi, Dada kawai za'a bari itama dan tace babu inda zata ne, gashi ba zai iya musu da ita ba. Su Ja'afar kuwa tuni suka tsufa a can sai dai Daddy ya ja musu kunne akan maganar, baya son kowa yaji har sai ya dawo da kansa zai sanar musu. Atm card ya ciro ya wurga masa, sai mukullayen gidan.
"Gashi nan, tun da kalar rayuwar daka zaba ma kanka kenan."
Da sauri ya kalli daddyn, sanin hakan me yake nufi ne yasa ya hau rokon sa
"Daddy dan Allah ka tsaya ka saurare ni, wallahi ban aikata abinda ake zargi na dashi ba."
Da wani mugun kallo ya dube shi
"Ni sa'an ka ne Farouk? Ko ka fara shaye-shayen ne dai da gaske?"
"Wallahi ban taba shan komai ba, ka saurare ni kadai nayi maka bayani, wallahi bani da laifin komai."
"You must be a fool, nace baka da hankali sam, idan har kana ganin zan tsaya sauraran ka bayan da kanka ba wani ya matsa bakin ka ba ka amsa laifin ka a gaban kowa, sannan yanzu kazo min da wani banzan zancen ka, toh kayi karya wallahi."
Riko ƙafafuwan sa yayi da sauri yana sake sakin kuka
"Wallahi ban aikata ba, bansan me ya hau kaina ba na amsa, dan Aallah Daddy kar kuyi min haka."
Buge hannun sa yayi ya janye ƙafarsa yana matsawa.
"Idan ka gama haukan naka zamu wuce."
"Daddy ka taimaka min, maganar karatuna fa dan Allah, wallahi ban aikata abinda kake tunani ba, taimakon ta kawai nayi, wanda na dauke ta tamkar Amal."
Tsaki Daddy yaja, ya gaji da jin wannan shirmen nasa, bashi da lokacin da zai kara batawa ya saurare shi, duk wata hujja tasa bata da amfani tun da be kawo ta a lokacin da ya kamata ba, ko a gaban alkali ne to Tabbas ya tabbata mai laifi tun da har yayi saurin amsawa. Duban shi yayi, baya so ya karya masa zuciya, saboda haka ya nuna shi da hannun sa
"Kai yanzu ai na gama da kai, ba zan iya tsayawa sauraren shirmen ka ba. Maganar karatu kuwa in kana so zaka iya neman admission ka soma karatun anan, kar dai ka manta akwai responsibilities na matar ka kanka, so you have to be very careful."
Hannu ya watsa baya ya juya cikin takun kasaita ya fada mota, Amal ce suka fito da Dada tana kuka sosai akan dole ba zata tafi ba, da sauri ya rarrafa gaban Dadan yana sakin kuka me tsuma rai.
"Dada kiyi min rai dan Allah, Daddy ya dau zafi sosai yaki saurarata."
Dago shi tayi ta bude kofar falon ta tura shi ciki ta rufe, motar ta nufa rike da hannun Amal, daddy na ganin haka ya fito.
"Ka barta ta zauna tare dani har zuwa lokacin da za'ayi resuming makarantar su, sai azo a tafi da ita dan Allah."
"Duk yadda kika ce haka za'a yi, mu zamu wuce."
"Allah ya kiyaye hanya, ka kara nazari akan hukuncin da ka yanke wa Babana, duk abinda ka shirya sai ka sanar min a waya."
"Shikenan in Sha Allah."
Matsawa baya sukayi motocin suka fice daya bayan daya, ajiyar zuciya ta sauke ta kama hannun Amal suka juya ciki.
Kaiwa kawai yake da komowa a tsakiyar falon, yana jin an bude yayi wajen ta da sauri ya fada jikinta yana sakin kuka. Bata hana shi ba, tasan zuciyar sa a cunkushe take kukan kadai zai rage masa radadin da yake ji. Ya dau lokaci sosai yana kokawa da zuciyar sa, yana jin kamar ya hadiye ta ya huta da radadi da zafin da take masa, a hankali ta fara sanyi sakamakon addu'ar da yaji Dadan na tofa masa, da sauri shima ya kama yana karanto innalillah wa inna ilaihi raji'un. Sosai hakan yayi masa tasiri kwarai, zamewa yayi ya zauna akan tiles yana sauke kansa kasa.
"Babana..."
"Tashi ka shiga kayi wanka ka gyara jikin ka, dukkan tsanani yana tare da sauki, kuma komai zai warware cikin ruwan sanyi. Ka cigaba da addu'a."
Be musa ba, illa mik'ewa da yayi yana nufar dakin sa cikin tafiyar da tafi kama da wanda ya kwanta jinya me tsawo.
***Ina kwance yau ma kamar ko yaushe tun barowar mu asibiti bana iya aiwatar da komai sai abinda Inno tace, komai yimin ake abinci ma sai ta bani a baki, shigowa tayi tana tura kyauren dakin namu, gefen da muke ajiye kayan mu ni dasu Karime ta nufa, ta jawo ledar kayana ta fito dasu, set uku ne an wanke su sai hijabi daya da mayafi yellow, wata ledar sabuwa da alamun ita ta shigo da ita ta bude ta zuba kayan, takalmi na guda daya samfurin sukwal ta jawo shima ta saka min, sai dan kunne da sarka duk suma na sallah ta ne, ina kallon ta har tapp gama tana jan tsaki.
"Tashi kije ki watsa ruwa maza."
Mik'ewa nayi na amsa da toh na nufi bayin dake tsakar gidan mu, su Hanne na gani da su Karime sun cin kwalliya sun sa sababbin kayan su na sallah, kamar na tsaya yi musu magana sai kuma na fasa na shiga wankan. Mintuna kadan na fito na sake wucesu na shige ciki, da hannu Inno ta nuna min kayan dake ajiye a gefen tabarmar dakin. Dauka nayi na saka na koma na zauna ina tunanin inda zamu ake ta wannan shirin. Fita tayi ta barni a nan, ina ta jiyo hayaniyar yaran gidan sama sama, da gudu naji karime ta shigo gidan tana kiran Inno
"Ga motar chan tazo Inno."
"Naji me bakin aku."
Ta katse ta tana hararar ta, mamaki ne ya kamani, yau Inno ce ke cewa karime me bakin aku, lallai ba karamin bacin rai take ciki ba. Shigowar ta dakin ne yasa nayi saurin kallon ta
"Tashi maza ku kama hanya, saura inji ko in gani, ba dadewa zakiyi ba zaki dawo."
Da sauri nace
"Ina zani Inna?"
"Ban sani ba, tashi nace ki wuce suna jiran ki."
Tashi nayi jiki a sanyaye na fito tsakar gidan, Yalwati da Babar su Hanne na gani a tsaye duk sun sha lullubi, kamoni sukayi muka nufi kofar fita daga gidan. Motar dake ajiye a waje aka bude mana muka shiga, sai a lokacin naga Hanne da Karime a gaba, ajiyar zuciya nayi na ɗan ji sauki tun da bani kadai bace. Ina ji aka tashi motar muka dau hanya. Wannan tafiyar tana daya daga cikin shafukan rayuwa ta da bazan taba mantawa ba.
Rano 😍 ©®HafsatRano
0 comments:
Post a Comment