https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo
(7)
***Tafiya kadan mukayi muka isa gidan, da mamaki nake kallon gidan, gidan da nake da muradin zuwa a koyaushe, murna na hau yi Yalwati tayi saurin hararata, da sauri na nutsu, aka bude mana bayan motar ta gama daidaita a harabar gidan da nake wa kallon aljannar duniya. Tsallen murna su Karime suka hau yi Yalwati ta daka musu tsawa, sum sum sum suka dawo bayan ta suka makale, kofar dake kallon mu wanda ya kawo mu ya nuna mana.
"Bismillah hajiyan na ciki ai."
Sake riƙe ni gam sukayi muka nufi kofar, kafin mu karasa aka budo kofar aka fito, matar nan ce ta asibiti, da fara'a ta tarbemu,tayi mana iso cikin falon, wani irin azababben sanyi me hade da sanyayyen kamshi ya kaiwa kofofin hancin mu ziyara, ina kallon Babar su Hanne na sake bude kofofin hancin ta sosai tana shaƙar iskar da tayi mana maraba, duk muka rabe a kasa nida su Karime, aka shiga gaisawa cikin mutuntawa. Nidai ina ta son kallon ko ina a falon amma babu dama saboda yadda Yalwati ke kara rufa min fuskata, bansan dalilin da yasa take min hakan ba, bayan na ga su Karime da Hanne an bar su suna ta shan kallon su. Ina ta hasashen ina ma nice na more kallon nan. Chan na kurawa katotuwar talabijin din dake girke a bango ido ta cikin mayafin duk da ba wani sosai nake gani ba, wasu mutum biyu babba da yar matashiya suka shigo dauke da manya manyan farantai, ina kallo suka dire gaban mu aka sake gaisawa sannan suka juya suka fice.
"Bismillah ga abinci." Matar ta fada tana nuna wa su Yalwati kwanukan da aka jere a gaban mu, wanda tuni kamshin ya fara sawa na manta yanayin dana baro, ina ji na kamar babu sauran damuwa ko takura a cikin rayuwa ta. Kamar su Yalwati ba zasu ci abincin nan ba, ina ta addu'a har sai dana ji matar ta sake musu magana, sannan suka sauko kowa ta hau diba dan dama nasan kawai kara sukayi wanda ni sam ban san su da ita ba.
"Amal!" Ta bud'e muryar ta tana kwala mata kira, da sauri ta shigo, turus tayi ganin baki taki karasowa
"Ƙaraso mana kika tsaya."
Shigowa tayi tana sake kallon mu.
"Ga kawar ki nan rike ta ku shiga ciki."
Hannu na ta kama, muka bar falon, mayafin na cire muna yin gaba, kallo na tayi tace
"Laaaaa Aminatu."
"Na'am." Nace mata ina murmushi
"Yaushe kika zo?"
"Yanzu muka zo, nan ne gidan ku ashe."
Daga min kai tayi
"Zo muje kiga daki na."
Da sauri na bita, muka shiga dakin nata, dan karamin gado sai single wardrobe da toilet, kan gadon muka fada muka saki dariya a tare.
"Dakin ki mai kyau." Nace ina kallon ko ina, a raina ina raya dama nawa ne.
"Thanks." Ta amsa tana murmushi
"Bari na kawo miki chocolate din da Ya Farouk ya siya min."
Ta fita da sauri, tashi nayi na bude kofar toilet din, tsayawa nayi ina kallon mamaki, bansan ina ne nan ba, na dai ga alamun akwai ruwa a ciki. Rufewa nayi na koma gadon na hau, na mike kafata ina murmushi. A raina na shiga raya dama daki na ne dana more.
Dakin Farouk ta nufa tana kwala masa kira, yana zaune da waya a hannun sa suna magana da Ja'afar ta shiga, kallon ta yayi ya mata alamar tayi masa shiru, tura bakin ta tayi ta nufi in da ta bar kayan chocolate din nata ta dauka, har zata fita sai kuma ta dawo ta tsaya a gaban sa tana dariya
"Kawata Aminatu ce tazo, tana dakina."
A dan rikice ya kalle ta
"Ina zuwa zan kira ka."
"Me kika ce? Su waye suka zo?"
Ya fada yana mik'ewa
"Kawata Aminatu."
Da sauri ya dafa kansa, da gaske kenan anyi aure, wani irin yar yaji tun daga kansa har tafin kafarsa, tunanin kalmar auren kadai na sa shi a wani yanayi. Ashe da gaske Daddy yak masa, kwata-kwata yarinyar nawa take, da har za'a yi mata aure. Gaban mirror ɗin dakin ya isa yana kallon kansa. He's to young for that, idan be manta ba next month zai cika 22years chif.
"Ya Salam." Ya furta yana fadawa gadon
"Me nayi wa rayuwa ta ne? Na daure kaina da kaina, yanzu idan Mummy ta samu labari ya zanyi?"
Da sauri ya tashi, farar singlet ce kawai a jikin sa, sai dogon wando, ciwukan jikin sa na nan musamman na fuskar sa, dakin Amal din ya nufa da dan saurin sa, ya bude kofar da karfi. Suna zaune sun baje a saman gadon suna kwasar chocolate. Tsaye yayi yana kare musu kallo, da sauri yaga ta rufe idon ta ta sauke kafarta kasan gadon, kallon kansa yayi ya sake kallon dakin
"Menene?" Amal ta tambaya tana kallon na.
"Tashi ki rakani wajen su Hanne, kar naje ana jirana zamu tafi."
"Kai dan Allah, ki kwana mana."
Make kafada nayi, takowa ya shiga yi har ya ƙaraso gaban gadon, ya sa hannu ya rike ni, zaro ido nayi ina kallon sa, sai kuma nayi saurin rufe ido na
"Tsoro na kike ji?" Ya fada yana kallon saman fuskata
Da sauri na daga kaina, dariya Amal ta kwashe da ita har da tafa hannu
"Tsoron Ya Farouk kike ji, ai baya suka fa."
Bata fuskar sa naga yayi ya saki hannu na, be ce komai ba ya juya ya bar dakin. Ajiyar zuciya na sauke ina kallon Amal din
"Ni dai muje ki rakani."
Tashi taga nayi yasa ta mike itama ba tare da taso ba muka fito wajen Dada. Babu kowa sai ita kadai, kallon ko ina na hau yi da sauri alamun neman abu.
"Kuzo nan yarana, Aminatu me kike nema naga kina ta kalle kalle.?" Ta fada cikin son ta yi min wayo
"Ina su Hanne?"
Nayi narairai da fuska kamar zanyi kuka.
"Kinga ke anan zaki zauna ke da kawarki, kuyi wasa tare, kuyi komai tare har karatu zan sa ana koya muku, idan kika kwana da yawa sai ki koma gida."
"Har karatu ma zamu dinga yi, kuma ba zanyi girkin shinkafa da wake ba ko??" Na tambaye ta ina kallon ta.
"Girki! A ah banda girki, ai kunyi kankanta sai an kwana biyu, sai share dakin ku kawai da wanke toilet, sai kuma sallah."
Washe baki na nayi, cike da murna na ce
"Ni ba sai an maida ni gidan mu ba ma, ki barni ana kawai."
Dariya suka sa gaba dayan su, nima na bisu mukayi ba tare da na gane dalilin dariyar ba. Abincin dazu aka zuba mana, muka hau ci muna kallo, tuni na manta da komai, muna gamawa Dada ta dauko magani ta bani na sha, sannan tace muje muyi sallah, bazan tuna rabon da Inno ta sakamu sallah ba, babu ruwan ta da munyi ko bamuyi ba, muna idar da sallar muka dora kallon mu, ranar gaba daya ji nayi kamar nafi kowa farin ciki a duniya. Sai gaf da magriba sannan muka koma dakin Amal da a yanzu ake masa lakabi da dakin mu.
****
Gidaje biyu ne manya manyan gaske wanda suka cinye kafatanin layin tun daga gaba har baya, iri daya ne sai dai daya yafi daya girma da komai. Da dukkan alamu mamallaka gidan akwai alaka me karfin gaske a tsakanin su, ko ta yan uwan taka ko ta abota. Gidan farko da yake dauke da tafkeken gate me matukar tsawo da fadi aka yi saurin wangalewa sakamakon karar horn, da sauri mutane biyun dake zaune akan dan bencin zaman maigadin gidan suka tashi suka nufi wajen motar. Babban mutum ne dogon gaske, cikin shigar alfarma ya fito daga ciki, hannun sa dauke da wayar sa yana amsawa, yadda yake magana kadai zaka gane yadda arziki ya samu babban matsuguni a wajen, rike yake da murfin motar har ya gama wayar kafin ya maida duban sa bakin yana murmushi
"Sannun da zuwa Alhaji." Suka ambata a tare cike da girmamawa. Amsawa yayi yana duban chan hanyar gate din.
"Wai tun da mukayi waya kuke zaune kenan, sannun ku da zuwa, Bismillah."
Gaba yayi suka bi bayan sa har kofar da zata sadaka da babban falon gidan, daya daga ciki ne yayi saurin bude masa, godiya yayi sannan ya shiga da sallama, babu kowa a falon nasa, sai sautin suratul bagra dake tashi daga cikin jerin speakers din da suka karawa falon kawa.
"Bismillah, Ina zuwa."
Wuce su yayi ya haura corridor din da zai maidaka part din matar gidan. Yana shiga yaron dake kwance akan sofa yana kallo ya taso da sauri
"Daddy!" Ya rungume shi,
"Kamal, kana nan kana sana'ar taka ta kallo ko, yau babu islamiyya ne."
"Malam ne yace yau ba zai zo ba zai je garin su."
"Ah lallai, yau ranar hutawa ce."
Kallon ko ina yayi kafin ya sake shi yana cewa
"Ina Mamyn taka ne? Naji gidan tsit."
"Tana daki, wai kanta ne yake ciwo na dame ta da surutu shine ta koroni."
"Toh zauna na dubo ta, kai ɗin ne watarana akwai zuba kamar..."
Buga kafa ya fara yi irin ta shawagabbun yara, dariya kawai yayi ya nufi dakin gimbiyar tasa. Tana kwance ta juya bayan ta ya shiga, yadda yaga yanayin kwanciyar ta ta yasa ya gane da gaske kan nata ke ciwo, dan dama gwanar ciwon kance, fasa tada ta yayi ya juya ya koma wajen bakin sa. Sun jima suna tattaunawa kafin su tafi, daga nan ya bada umarnin kar a bar kowa kuma ranar yana so ya huta sosai.
Watsa ruwa ya fara yi, yaci abincin da ke jere a saman dining din part din nasa, sannan ya nufi bangaren Hajiyar sa.
***
Gaba daya ran Inno a jagule yake, ta rasa yadda zata bullo wa al'amarin, gaba daya ji take dama bata amince da bukatar su ba, da tuni zuciyar ta na nutse bata da wani tashin hankali. Babban matsalar ta ma zuwa da tayi wajen Harira da ta tambaye ta labarin yaron ta, yadda ya amsa mata ya nuna cewa bata san komai akan halin da yake ciki ba. Tun bayan abinda ya faru da Aminatu, kullum bata samun isasshen bacci, bare yanzu da ta koma wani gidan sai take ganin kamar babu ita babu cikar burin ta. Duk da sunyi alkawari da Harira akan haka sai dai bata jin zata samu nutsuwa kenan har idan ba dawowa din tayi ba. Ita da zai yiwu ma da sun hakura da komai ta maida ta wajen iyayen ta, hankalin ta ya kara tashi ne saboda samun ainihin labarin waye iyayen ta, kuma dadin dadawa babu hannun mahaifiyarta ko mahaifinta a bin da ya faru, Harira ta rufe ta, ba ta sanar da ita duk wannan ba, yanzu idan suka ki yarda suka hada su dukka suka kulle su fa, bata tunanin duk duniya akwai wanda zai iya fito dasu. Haka zasu kare rayuwar su a ba wan ba kanin. Ita kam abubuwan sun mata yawa.
***
*Sati Daya*
Wasanmu kawai muke nida Amal, bamu da wata damuwa ko kadan, ina matukar jin dadin zaman gidan. Wajen yanayin jikina kuwa sosai magungunan da nake sha suka taimaka min wajen samun lafiya ta. Har na murmure abu na, kaya kuwa na Amal nake sawa kafin nima a karo min nawa kamar yadda Dada tace. Muna zaune a falon Amal na karanta mana wani story book duk da ba gane wa nake ba, idan ta karanta sai ta fassara min da hausa. Sosai hakan ke min dadi. Shigowa yayi fuskar sa babu walwala kamar ko yaushe ya wuce, duk ya rame yayi baki, ina ji dai ranar Dada na masa fadan ya saukaka wa kansa, damuwa babu inda zata kai shi, duk da hakan be chanja ba. Kullum yana aikin waya, a rana sai ya kira Daddy sau nawa ba tare da ya kosa ba duk da hakan baya dagawa, daga karshe ma sai ya sashi a blacklist.
Har ya gifta mu sai kuma ya dawo da baya ya tsaya a gaban mu. Duk muka kalle shi a lokaci guda dan ba kasafai yake shiga harkar mu ba.
"Me kuke yi?"
Ya tambaya yana zaman a hannun kujerar ta gefen da nake. Mika masa littafin Amal tayi tana matsowa
"Story book muke karantawa."
"Kuna son mu fara lesson?"
Da sauri muka amsa, murmushi yayi ya mika mana littafin
"Shikenan anjima zamu fara idan nayi bacci na tashi."
Murna muka hau yi ya wuce ya bar mu yana girgiza kai. Bayan wani lokaci sai gashi ya fito cikin shigar kananan kaya, yanzun ma wayar ce a kunnen sa suna magana da wani, zama yayi yana wayar yana kallon in da muke, har ya gama be dauke idon sa daga kanmu ba, tashi yayi ya wuce dakin Dadah, yau duk wunin ranar a daki tayi saboda ciwon kafarta da ya matsa mata,daga mu sai masu aiki sai yanzu da Ya Farouk ya dawo. Jim kadan sai gashi ya fito dauke da mukullin mota yana jujjuya shi.
"Kuzo muje ku rakani." Yace yana yin hanyar fita, da gudu muka yi daki, muka sako takalmi muka fito, yana tsaye jikin motar suna magana da driver, muna fitowa ya bude mana baya muka shiga shi kuma ya zauna a gefen me zaman banza driver ya data motar muka fita daga gidan. Tunda nazo yau ce rana ta farko dana fita, murna sosai nake ina jin kamar muyi ta dawwama a irin yanayin da muke ciki a yanzu, kadan kadan nake tunawa da yan gidan mu shima ba ko yaushe ba, yawanci nafi tunawa dasu idan Amal tayi bacci ta barni. Bani da sauran matsala komai muke so mukeyi, sai nake jin kamar nafi kowa sa'a a duniya.
Fita daga kauyen namu mukayi baki daya muka shiga cikin gari, a bakin wani babban shago muka tsaya,ya Farouk ne kaɗai ya fita ya bar mu a motar, chan ya dawo da kaya ya zuba a booth sannan muka nufi wani shagon, haka mukayi ta yawo daga nan zuwa nan wani wajen ya shiga damu wani ya bar mu a mota. Bamu muka dawo ba sai yamma likis cike da gajiya dan Amal tun a hanya tayi bacci ta barni.
****Tun daga ranar muka fara karatu da Ya Farouk, kullum da abinda zamuyi, chan baya muke tafiya mu saka babar darduma mu baje sai mun gaji sosai yake kyale mu musamman ma ni, dan mafi ya yawan lokuta ni yake wa karatun dan ita Amal ta wuce wajen.
Muna cikin wannan yanayin Daddy ya turo aka tafi da Amal, ranar nayi kuka sosai nace lallai sai an maida ni gidan mu, da kyar shi da Dada suka shawo kaina na hakura na zauna, amma bani da wani kuzari tun bayan tafiyar ta ta wadda Dada tace min sun koma makaranta ne kuma ba nan kusa bane. Haka dai na hakura na cigaba da daukar karatu da yanzu yafi min komai a rayuwata.
Wata na hudu cif a gidan, sau biyu su Karime suka zo ita da yan gidan mu suka wuni, suka tafi, anan ne suke fada min ai aure akayi min shiyasa nake zaune anan, kuma Inno ce take hanasu zuwa shiyasa. Ban dauki zancen nasu da muhimmanci ba, haka na tattara na cigaba da sabgata saboda ba karamin sabo nayi da Ya Farouk ba, gashi kusan kullum sai ya kira min Amal da daddare munyi waya.
Ranar da bazan taba mantawa da ita ba, nayi bacci na tashi kenan, dakin ya Farouk na nufa da sauri na ina tunanin ko ya zo tashi na ya ga ina bacci ya gudu bayan yayi min alkawarin yau zai kaini gidan mu har na wuni, kwana yace zanyi na fafure nace sai dai yini, yayi ta min dariya yana tsokana ta, ban damu ba,dan zama na anan ɗin yafi min dadi musamman ma saboda karatun da nake yi.
Tura dakin nayi na shiga bayan na kwakwasa ya bani izini, Yana lullube a bargo ya rufa har kansa, kiran sunan sa na fara yi ina k'arasa ciki. Cikin muryar bacci ya amsa min, dariya nayi na haye kan gadon ina jan bargon dan nasan ba bacci yake ba, mafiya yawan lokuta ya saba yi min hakan. Rike bargon yayi yana ja ina ja har na samu na bude masa fuskar sa.
"Laaa bacci karya fa kake ya Farouk." Nace ina dariya, bude idon sa yayi cikin yanayin bacci ya zuba su a kaina
"Bacci nake fahhh..." Ya fada cikin wata irin murya kamar ba tasan ba, jan bargon yayi ya sake rufawa nayi saurin janye wa ina sake yin dariya
"Ni dai ka tashi, ba kaine kace zaka kaini gida yau ba."
"AMINATU pleaseeeeee..., bacci anjima zan kaiki."
'Dage kafada nayi na sake janye bargon ina bubbuga masa damtsen hannun sa. Da wani irin karfi nayi ya riko ni, gaba daya na shige cikin jikin sa, ya jawo bargon ya rufa akanmu. A tsorace nake kallon sa, idon sa a kulle ya sake maidashi ya rufe, zura wa fuskar sa ido nayi kamar wadda ta fara ganin sa, na kasa kwakkwaran motsi, balle na yi yunkurin tashi. Takun tafiya naji yana tunkaro dakin, hade da karar abu kamar ana jan wani abu, janye bargon nayi daga saman fuskar mu na zuba wa kofar shigowa dakin ido tun da dama dana shigo ban rufe ta ba ina sauri. Cikin wata irin shiga ta alfarma, me cike da haiba tayi wa kofar dakin tsinke, tsaye take janye da yar karamar jakar matafiya, sai handbag din ta dake sakale a sangalalin hannun ta. Cikin mintuna da basu gaza biyar ba nayi mata kallon tsaf, yadda naga ta buda idon ta sosai akanmu ya ɗan tsorata ni, cikin tsananin mamaki naji ta kira sunan sa da d'an karfi.
"Son!"
A firgice ya dago idon sa ya sauka a kanta, yayi wani irin tashi da dukkan karfin sa har yana ture ni daga jikin sa, cikin sakin bakin ya furta
"Mom!"
DAURIN GORO😢😢😥😥😓
ZAFAFA BIYAR
KAUNAR MU: MAMUH GEE
ALKAWARIN ALLAH; HUGUMA
GUDU DA WAIWAYE: BILLYN ABDUL
DAURIN GORO:HAFSAT RANO.
IGIYAR ZATO: MISS XOXO
LITTAFI DAYA 200
BIYU 300
UKU 400
HUDU 450
BIYAR 500
*_ZAKU BIYA KUDI TA BANKI TA WANNAN ACCOUNT DIN👇👇_*
2260792279
_MARYAM SANI_
_ZENITHBANK_
saiku tura shaidar biyanku ta maana screenshot ta wannan layin👇👇
*07067124863*
*_GA MASU TURA KATIN MTN SAISU TURA KATINSU ZUWA GA WANNAN NUMBER TAREDA TURA MATA SHAIDA_*👇👇
*09032345899*
_Sayen nagari, maida kuɗi gida masoyan asali😉😻🥰🥰😍😍😘😘👌🏻💃🏻💃🏻_©️®️HafsatRano
*ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo
(8)
***
Kallon mu take babu ko dauke ido cikin wani yanayi, ranta a matukar bace, da sauri ya isa gaban ta yana mika hannu zuwa wajen jakar kayan ta
"Welcome Ma. Ashe kina hanya."
Kallon banza tayi masa, ta wuce shi ta shigo dakin, har in da nake, bina ta cigaba da yi da kallo tana tabe baki kafin tace
"Yanzu akan wannan ka zabi ka katse rayuwar ka, ka hakura da komai ka anan, yaushe ka zama haka Farouk?"
Ta fada tana buɗe idon ta sosai akan sa
"Mummy Please, ki huta sai muyi magana."
"Naki na huta ɗin, kana son ka kashe rayuwar ka abanza kana cemin ma huta, saboda kai kafi kowa tausayi a duniya ko? Abin da kuma nazo na tarar fa, ko shima tausayin ne? Kuna kwance tare amma a waya kana nuna min kai kawai kana son taimaka mata ne."
"Ya Salam... Mummy bafa abinda kike tunani bane."
"Toh mene?" Ya fada a harzuke
Kallo na yayi ganin yadda nake ta binsu da ido kamar na samu tv yace
"Jeki dakin ki Aminatu, anjima sai na kaiki gidan ko?"
Zumburo baki nayi cikin jin haushi na tashi na bar dakin, sakin baki tayi tana dubanshi.
"Farouk!"
"Mummy dan Allah, here me out, idan kika ji komai sai ki yanke min hukuncin da kika ga ya dace dani."
"Farouk wanne abu kuma zanje bayan wanda ka fada min, Ja'afar ya fada min, akwai wani sauran point ne da ban ji ba?"
"Ja'afar...?" Ya ambata cike da mamaki
"Ban isa ya fada min ba ne ko me? Ina chan ni sam hankali na ya kasa kwanciya kai kana nan kana baccin ka da yar yarinya karama, toh wallahi an gama, munafukar kakar taku sai tazo ta warware wannan kullin da tayi, ko da bana gidan naku amma ido na na kan duk wani motsin ku, kuma wannan karon bazan yarda ba wallahi."
Dafe kansa yayi ya juya mata baya da sauri, matsalar mahaifiyar su kenan, ya rasa dalilin da yasa a komai take blaming Dadah, bayan babu wani abu da tayi mata, shi yasa yayi ta iya kokarin sa na ganin ya kwantar mata da hankali amma sai da Ja'afar ya kai mata gulmar, yana jin ta tana sababi kafin ta nemi waje daya ta ajiye kayan ta tana zaman gefen gadon.
Dakin ya bari ya nufi wajen Dadah dan sanar mata kar sai ta fito su hadu, tana zaune akan babbar darduma da alama ta gama sallar walaha kenan, tana dan bitar karatun Alkur'ani, gefen ta ya zauna har ta kai aya ta rufe ta juyo tana murmushi
"Babana an tashi kenan."
"Uhum." Yace yana tankwashe kafarsa
"Dama Mummy ce tazo."
Ya fadi maganar kamar wanda baya so, shiru Dadan tayi cikin nazari, tabbas tasan zuwan nata ba zai zame musu Alkhairi su dukka ba, sai dai abu daya ta take tsoro shine yadda zata dauki maganar Aminatu, tasan ta sarai mace ce wadda take da son kanta, ba lallai ta fuskanci maganar ba, shiyasa take ta kokarin ganin Daddy yasauko ya bar su sun tafi baki daya, idan yaso Farouk sai ya koma makarantar sa ita kuma a sata a ko tasu Amal ce, sai dai hujjar daya bata na cewa wa'adin daya deba wa Farouk din be cika ba yasa ta hakura, sai dai zuwan mahaifiyar shi a yanzu yasa ta ɗan ji tsoron abinda zai je ya dawo. Duk da haka ba zata shiga hurumin da bana ta ba, d'anta ne tafi kowa sanin ciwon sa.
"Ah sannun ta da zuwa, yaushe ta zo?"
"Yanzu." Ya amsa yana kallon yanayin ta
"Madallah, sannun ta da zuwa."
"Uhum." Kawai yace ya tashi
"Dan Allah Dadah... Kinsan halin Mummy, karki bari tayi abinda ba dai-dai ba dan Allah."
Kallon sa tayi ba tare da tace komai ba har ya juya ya bar dakin, tashi tayi ta koma saman gadon ta tana tunanin yadda abubuwan zasu zama.
***
Kwanciya na koma nayi ina jin haushin katse min zuwa gida da matar tayi, ido na a lumshe kamar ina bacci aka turo kofar dakin, da sauri na bude ina kallon kofar, yana tsaye ya rike hannun kofar yana kallon ciki, tashi nayi zaune ina saukowa da kafata kasa
"Ya Farouk wacece datazo?"
"Mamana ce." Ya amsa min yana sakin kofar, ciki ya shigo ya zauna gefen gadon yana matso dani kusa dashi ssosai.
"Kina son ta ko?" Ya tambaye ni yana kallon fuska ta, da sauri na girgiza masa kai alamun a'ah, ware idon sa yayi gaba daya akaina.
"Are you serious! Mamana ce fa."
"Eh ni bana son ta." Na faɗa cike da yarinta
Da sauri ya rufe baki yana harara ta
"Kar na sake ji kin fada, kice kina son ta."
"Ni toh ba masifa take maka ba, ni bana son ta, ni kai kadai nake so sai Amal,sai yan gidan mu."
Murmushi naga yayi, ya rike hannu na cikin nasa ya murza a hankali
"Ni kina so na ko?" Ya tambaye ni
"Eh mana, kana da kirki ai."
"Toh idan kina son na, kiso mummy ma kinji."
A cunkushe na amsa da toh
"That's my girl." Yace yana mik'ewa. A nutse ya juya ya bar dakin ina kallon sa har ya gama ficewa.
***Waya ce a rike a hannun ta sanda ya shiga, yanayin da take magana ya gane akan sa take wayar, kai tsaye wajen kayan sa ya nufa ya tattara abubuwan da zai bukata ya kai chan dakin su Ja'afar ya zuba sannan ya shiga Kitchen yasa masu aikin gidan suka bashi breakfast ya kai mata dan yasan bata karya ba. Ko da ya koma ta gama wayar tana dan dube dube a cikin iPad.
"Mummy gashi nasan baki yi breakfast ba, in Kika gama sai kije ku gaisa da Dadah pls tasan kinzo."
Tabe baki tayi ta ja tray din gaban ta ta bude, juyawa zaiyi ta dakatar dashi
"Ka daina gudu dole muyi magana kaji da abinda nazo, ba zama nazo yi ba ina da abubuwan yi da yawa."
"Watsa ruwa zanyi sai nazo muyi maganar, kiyi hakuri."
"Yayi, ina jiran ka."
"Ok."
Yace ya nufi dakin Aminatu, budewa yayi ya ganta tana kokarin zuge zib ɗin doguwar rigar dake jikin ta, karasawa yayi ya taymaka mata ta cire sannan yace tayi wanka ya kaita, da gudu tayi toilet shi kuma ya nufi dakin su Ja'afar da ya zama nasa a yanzu.
A gurguje ya shirya ya fito dan baya so taje neman sa dakin sa, baya so sam su hadu ita da Mummy su biyu ba tare da shi din a tsakani ba. Aikuwa a hanya sukayi kicibis ta tafi dakin nasa, riko hannun ta suka juya zuwa hanyar fita murnar ta take tsayawa.
Babu driver da alama Dada ta aike shi, sai driver mummy shi kuma baya so ya nuna masa gidan dan be san abinda mummyn zata iya aikatawa ba. Kawai sai ya yanke shawarar su tafi a kafa tun da babu nisa. Fita sukayi a kafa hannun sa sakale cikin nata, tana tayi masa hira duk yawanci akan wayar su da Amal ne, sama sama yake sauren ta, hankalin sa ya tafi akan yadda zai ɓullo wa Mummy. Sun kusa isa gidan suka yi kicibis da Garbati da Ilu, da mamaki suke duban su, sam Garbati be yi tunanin abin a iya nan zai tsaya ba, wani haushi ne ya taso masa, yayi saurin shan gabansu, da sauri ta koma bayan Farouk din tana buya.
"Me hakan?" Farouk ya fada bayan ya haɗa girar sama data kasa.
"Babu komai, kawai dai ajiya ta ta wajen ka nake dubawa, naga alama kuma dai babu wata matsala."
Haushi ne ya kama Farouk, sai dai ba zai biye masa ba, dan yaga alama sam Garbatin baya cikin jerin mutane masu ƙwaƙwalwa, hannun ta ya damke sosai suka raba ta gefen su suka wuce kawai ba tare da yace komai ba. Haushi sosai ya kama Garbati, yaji kamar ya jawo shi ya ta bugun sa ko zai huce, haka yayi ta zage zage Ilu na bashi baki suka wuce in da zasu.
A kofar gida ya tsaya ta shiga ciki ya tabbatar ta shiga sannan ya juya ya bar wajen.
***
A tsaye na tarar da Inno wajen in da take kiwon ta, tana gani na ta saka min ido cike da mamaki, da sauri nayi wajen ta ina murnar ganin ta, murmushi ta k'ak'alo wanda ya zauna iya saman fuskar ta, ta ajiye abinda take
"Ke kuma daga ina?" Ta tambaya tana yin gaba, bin bayan ya nayi lokacin su Karime suka ganni, ihu muka hau yi muka dane juna. Nan da nan aka fara shigowa daga cikin gidan namu zuwa gani na, hakan ya bata ran Inno ta kwala mana kira ni da Karime muka shiga dakin ta, waje ta nuna mana da hannun ta sannan ta fice ta bar mu a dakin bayan ta ja mana kunne akan karmu sake fitowa sai ta kiramu. Hakan da tayi ya rage masu shigowar dan sun sane abinda take nufi, hirar mu muka baje irin ta yarinta nida Karime ina ta bata labarin gidan Bature, murna take tana jin dama ita ce. Chan da azahar Inno ta kira Karime ta kawo mana dambu da wake, rabon dana ci irin abincin gidanmu an jima, ai kowa na saki ciki naci sosai harda k'ari, nasha ruwa nabi lafiyar katifar Inno na baje abina cikin jin dadi.
****
Tun da ya koma gidan yaki yarda sam su hadu da Mummy, rufe kansa yayi a daki ya cigaba da aikin da yake na neman admission din sa tun wajen sati biyu da ya wuce, be samu gama wa shi yasa yau ya dage ya gama. Baya so ya kara bata wani zangon karatun a banza kamar yadda yayi wannan karon, shiyasa ya yanke shawarar chanja akalar karatun nasa zuwa abinda yake da tabbacin zai taimaka masa matuka wajen hukunta mutane irin Garbati.
Knocking din dayaji a kofa yasa gaban sa ya fadi, kin magana yayi aka cigaba da knocking din, ya zata zata hakura ta tafi, ganin da gaske take yasa ya kashe komai ya mayar waje daya, ya nufi kofar cikin tafiya irin ta masu bacci. Budewa yayi tana tsaye ta harde hannun ta. Kallon da tayi masa ne yasa cikin sa murdawa, takardar hannun ta ta ware ta wurga masa.
"Tun da kaki yarda muyi magana, sai ka duba wannan, kuma dole cikin biyu kayi daya, idan kuma ba haka ba, abinda da biyo baya ba zai maka dadi ba, dan na lura sam baka da hankali baka san ciwon kanka ba."
"Mummy..." Juyawa tayi ta bar wajen bata ko sake kallon sa ba. Kasa ya tsugunna ya dau takardar hannun sa na rawa, layi cikin layi ya fara bin rubutun, gaban sa yayi wani mummunan faduwa, a take ya juya da mugun gudu ya nufi dakin da take, yana zuwa tana rufe kofar, bugawa ya hau yi yana kiran sunan ta da sauri
"Mummy dan Allah karki fara, dan Allah Mummy, nasan me nake da hankali na wallahi, zanyi ko menene kika ce amma dan Allah karki min haka."
Babu alamun zata saurare shi, zamewa yayi a wajen ya zauna kansa na juya masa.
Manage 🙏😥©®HafsatRano
*ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo
(9)
***Fitowar ta kenan zata dan taka kafarta ta hange shi a durkushe a kofar dakin sa, da dan saurin ta ta k'arasa
"Babana?"
Dagowa yayi idon sa sun kada sunyi ja ya kalle ta
"Tashi muje daki na."
Ta fada tana mika masa hannu, mik'ewa yayi cikin sanyi jiki yabi bayan ta, Mummy na jinsu ta tabe baki, babu wanda ya isa ya sata ta sauya ra'ayin ta akan abinda ta haifa, ba zata bari tana kallo a lalata masa rayuwa ba dan shi yafi kowa sauƙin kai.
Suna isa dakin ya zame ya zauna kasan carpet din dakin yana jin zuciyar sa na tafasa.
"Menene matsalar?" Ta saka masa ido, tana kallon yadda kirjin sa ke kaiwa da komowa. Shiru yayi ba tare da yayi magana ba ya mika mata takardar Mummy. Murmushi kawai tayi bayan ta gama karantawa ta mika masa, tasan zata aikata fiye da abinda tace ɗin, dan bata shakka ko kokonton hakan, sai dai babu yadda ta iya, musamman da babu wata alaƙa yanzu dake tsakaninsu da ita sai ta ya'ya, amma tana jan girman ta, bata so kuma wani abu ya shiga tsakanin shi da mahaifiyar sa.
"Kayi mata abin da take so kawai Babana, shine zaman lafiyar kowa."
"Dadah....?"
"Shine maslaha, abu ne me sauki, kuma tabbas kayi kokari ma ladan ka yana wajen wanda kayi domin sa."
Matsawa yayi jikin kafarta ya dora kansa a saman, zuciyar sa tayi rauni sosai, ba ya jin zai iya aikata abinda Mummyn tace, ya kuma rasa dalilin sa na son kin amincewa bukatar ta. Shafa kansa ta shiga yi tana ayyana yadda komai yake tafiya.
"Babana..." Ta sake kiran sunan sa
"Kana son Aminatu ko.?" Da sauri ya dago kansa jin tambayar a bazata, abinda yake ta kokawa da zuciyar sa kenan, ya rasa dalilin da yasa yake jin yarinyar har cikin ransa, komai nata yana jin kamar an haɗe shi da rayuwar sa ne, yanzu da Mummy ta kawo zancen rabuwa sai yaji kamar zare wani abu me muhimmanci ne a cikin rayuwar sa. Be san me haka yake nufi ba, sai dai yana daukar ta a matsayin wata babbar ƙaddarar sa.
"Kana son ta ko?" Ta sake maimaitawa
"Nima ban sani ba Dadah, kawai ina jin tausayin ta ne, She's too young for that, sannan na mata plan na good future,."
"Shikenan, Ina da shawara, amma dole sai da taimakon mahaifiyar ta, kaga ni yanzu mahaifin ku ya matsa lallai sai na tafi saboda ciwon kafar nan tawa daya matsa min, da babu irin taimakon da ba zan baka ba, toh mahaifiyar ta ita kadai ce zata taimaka mana, wajen ganin mun samu abinda muke so."
"Ta yaya kenan Dadah?"
"Ka kai ta boarding school, ka damka amanar ta wajen mahaifiyar ta, ka sanar mata da kudurin ka nason ganin ta zama wani abu,nasan babu mahaifiyar da zata ki cigaban yar ta, kai kuma kaga sai ka dawo kayi wa mahaifiyar ka biyayya, kayi karatun ka, ka kara mallakar hankalin kanka, lokacin babu wanda zai fada maka yadda zaka yi da rayuwar ka, a lokacin sai ka dawo, ka cika burin ka."
Da sauri ya tashi ya rungume Dadah,
"Shisa nake sonki Granny, wallahi you are the best."
"Ja'iri." Tace tana kai masa duka
"Allah kuwa, gashi kin kawo solution cikin sauki, idan Daddy yaji labari sai nace masa makaranta na maida ita nima zan koma tawa, kinga ba zai ce komai ba."
Daga masa kai tayi tana murmushi.
Tashi yayi da karfi da kuzarin sa ba kamar dazun da ya shigo ba.
"Bari naje na sanar wa Mummy na amince da komai data ce, sai na fara shiri." Ya fada cike da farin ciki.
Fita yayi da sauri, a kofar dakin sukayi kicibis, basarwa tayi kamar bata gama jin komai ba tayi gaba ya bi bayan ta. Zama tai kawai ya shiga tsara mata zance.
"Mom na amince da bukatar ki, amma dan Allah karki yi mata komai, bata da laifin komai bata san komai ba, idan ma hukuncin ne ni zakiyi wa, amma yanzu zan rabu da ita, zan biki mu tafin idan hakan zai saki farin ciki."
Murmushi ta k'ak'alo wanda ya tsaya a iya saman fuskar ta tace
"Madallah da kai, ka kyautawa kanka, ka kyauta mata, sai ka fara shirin tafiya dan bazan tsaya bata lokaci ba."
"Kiyi gaba dan Allah, zan biyo bayan ki wallahi nayi Alk'awari, ki bari na dan karasa wani abu dana fara, ba zan dau lokaci ba."
Dan jim tayi tana tunanin amince wa, kamar tace a'ah sai kuma tayi wani tunani.
"Shikenan ni zan koma gobe, saura kaki abinda nace, kasan dai sauran ba sai na fada ba."
"In Sha Allah hakan ma ba zata faru ba."
"Jeka toh zan dan kwanta."
Fita yayi ya ja mata dakin, ya wuce dakin Aminatu, budewa yayi ya haye saman gadon nata yana lumshe ido, tunanin yadda komai ya fara ya shiga yi, daga san da ya fita daga gidan zuwa yanzu da yake shirin daukar wani babban tsani a rayuwar su. Yadda komai ya zama kamar a film haka ya dinga bin komai daki-daki. Murmushi yayi ya mirgina gefe yana sake duban komai daya zama mamallakin ta a dakin sai yan abubuwan Amal.
"My Destiny." Ya furta a hankali kamar me rada.
Eh dole ya kira ta da Destiny dan shine kadai sunan da yake ganin ya dace da ita, ƙaddarar sa ce, wadda a yanzu yake jin babu wani abu da zai iya raba shi da wannan ƙaddarar. Haka ya jima a dakin har gabanin magriba kafin ya mike a kasalance ya fada toilet din dake manne a dakin. Alwala yayi ya fito ya tsaya gaban mirror yana kallon fuskar sa.
"A yau shafin rayuwar mu zai fara Aminatu, daga yau ba zan sake barin wani abun ki, ko cutarwa yazo kusa dake ba, nayi alkawarin zame miki babban tsanin cikar farin cikin ki ko da kuwa hakan na nufin... Ko da kuwa hakan yankewar nawa."
A fili yayi maganar, sannan ya juya cike da karshashi ya bar dakin, sallah ya fara gabatarwa kafin ya nemi driver su tafi dauko ta.
***Ina zaune Inno na gefe tana ta aikin lissafin Kudi,yadda ta tsare ni a dakin gaba daya ya sa naji duk na gaji, tun Karime na tayani hira har itama ta gudu ta barni, gashi Inno ta kafa ta tsare ko ina, ina jin su suna wasa a tsakar gida kamar inyi ihu. Sai data gama ta tattare kan kudaden ta bude inda take ajiye wa tayi musu kyakkyawan boyo, har ta rufe sai kuma ta sake budewa da jawo wata jaka, bude cikin ta tayi ya dudduba sannan ta mayar ya rufe, ina kallon ta, ganin zata juyo yasa nayi saurin janye ido na, kallo na kuwa tayi tana juyawar.
"Bacci kike?" Ta tambaya tana matsowa
"Wasa nake son zuwa nayi nida su Karime dan Allah."
"Ba zaki ba." Kawai tace tasa kai ta bar dakin, kuka na saka cike da jin haushi, duk sai naji dama ban zo ba, kallon tagar dakin nayi naga duhu ya fara zuwa alamun dare kenan, Ya Farouk be zo ya tafi dani ba, duk sai naji ina son tafiya. Addu'a na fara yi Allah yasa yazo. Jin shiru shiru yasa na kwanta lamo ina jin haushin kowa, da haka bacci ya fara fisgata. Sama sama naji Inno na taba ni.
"Keeee...ke." Ta bubbuga min jiki na
A gigice na tashi
"Ya Farouk!" Na ambata ina mik'ewa, kallo na tayi kawai cike da mamaki.
"Na'am."
"Tashi maza ku wuce, kin hangame baki kina bacci ko tuwon baki ci ba."
Da sauri na mike, na yayimi mayafi na na fito, a kan tabarmar gidan daidai kofar Baba na hange shi, kallo na yayi nayi saurin jan kafata zan karasa wajen, ji nayi an riko ni, Inno ce ta banka min harara, da sauri nayi kasa da kaina.
"Ku wuce dare nayi." Tayi magana tana kallon bangaren su Baban. Tsam ya mike, yayi sallama da Baban sannan y fita, sai a sannan ta sakar min rankwashi a kai sannan tace su Karime su rakani.
"Uwar rawar kai."
Ta ambata tana jan tsaki. Daki ta fada cike da tunanin abin da zatayi. Ga maganar da yazo da ita wai makaranta zai sata ta kwana, kenan babu ranar da zai sake ta, bayan Harira ta karbi kudin ta tace ko wata biyu auren ba zai ba, sai gashi ana maganar wata biyar, idan tayi sake kuwa sai dai taji ana maganar suna. Dolen ta gobe ta koma taji in da aka kwana, ba zai yiwu ta zuba ido haka nan ba.
***Tun da muka fita bamu wuce gida ba, zakayi kawai muke tayi har bayan sallar isha'i, a mota suka barni suka yi sallah sannan ya je ya siyo mana tsire, sanda suka dawo har na fara bacci, tashi na yayi ya bani naman, ina ci na sake komawa na kwanta. Bansan yaushe muka koma gidan ba, ashe baya so mu hadu da Mummy ne shiyasa yayi ta jan komawar. Ban san me ya faru ba, nidai na farka naganni a dakin Dadah, tashi nayi na koma daki na na sake maida kai na cigaba da bacci na cikin kwanciyar hankali. Wajen bakwai da rabi na sake farkawa, sallah nayi na kwanta akan carpet din na cigaba da bacci. A hankali aka turo kofar, kallon gadon ya fara yi sannan ya hange ni a kasa. Banji takun tafiyar sa ba, kawai sai ji kayi an daga ni sama, dan karamin hijabin danayi sallah ya shiga kokarin cire min, na sake runtse ido na kamar me baccin gaske, ina ji a cire ya ajiye a gefe ya kwantar dani a gadon, ido na ne ya fara rawa alamun baccin karya ne. Murmushi yayi me sauti ya mintsine ni a hannu na
"Wayyo." Na bude ido na ina kokarin yin kuka
"Baccin karya ko?"
"Na gaske ne fa, kaine ka tashe ni."
"Umm amma idon ki yake ta rawa."
Dariya nayi na tura baki gaba, kallo na naga ya tsaya yanayi sosai, babu ko giftawa, hannu nasa naja gashin idon sa cika da tsokana.
"Ouch, kai kika min haka?" Ya tambaya yana taba idon nasa
"Abu zan cire maka fah."
"Karya ne."
"Da gaske." Na saka dariya ina matsawa. Riko ni yayi ya dawo dani kusa dashi.
"Kina son kiyi karatu ko?"
Da sauri na daga masa kai na
"Good... Zan saki a makaranta. Kina so?"
"Ina so wallahi." Na faɗa cike da murna
"Ok Tam, zan saki amma sai kinyi min alƙawarin zaki yi karatu sosai, sosai."
"Zanyi Allah."
"Good."
"Toh yaushe zaka sani, kuma aina makarantar take."
Shafa kansa yayi alamar tunani kafin yace
"Yau zan fara zuwa neman makarantar, in Sha Allah zanyi kokarin ganin an samu, duk da ma anci term daya amma hakan zaki shiga ciki, sai kiyi kokari sosai ki kamo su."
Murna na hau yi sosai kamar zanyi rawa, hannun sa ya rataye a saman kirjin sa yana kallo na, sauka nayi na jawo littafan da muke karatu dasu na fara jera su daya bayan daya. Be yi magana ba, sai murmushi kawai yake. Chan ya mike da sauri yana dafa kai, shaf yaso mantawa da tafiyar Mummy, abinda ma ya tashe shi da wurwuri kenan. Fita yayi yaja min kofar na cigaba da hada littafan cike da farin ciki.
***Har airport ya rakata, ba zatayi tafiyar mota ba wannan karon wai Lagos zata wuce akan wani kasuwancin ta, dole sai dai driver nata yabi bayan ta a mota ya koma gida, sanda suka isa ta kara jaddada masa alkawarin su, amsa mata yayi da toh da haka sukayi sallama. Be koma gidan ba, sai kawai ya bazama neman makarantar da zatayi daidai da Aminatun sa, makaranta yake so me kyau me tsada wadda zata taimaka mata kwarai wajen cikar burin ta, be damu da ko nawa za'a kashe ba, kudin da ya karba wajen Mummy da wanda yake dashi dana Daddy zasu ishe shi komai. Shi dai kawai ya samu ya tabbatar yayi wa dukkan su abinda suke so ba tare da ya fifita daya ba. Sai yamma sannan ya samu ya gama wasu abubuwan, duk da ba dukka ya gama ba amma yaci karfin komai, ya samu makarantar da tayi masa, har ma sun bashi damar ya kawo ta interview. A gajiye ya shiga gida, sallah kawai yayi yaci abinci ya sake shiryawa ya fita, gidan su ya wuce kai tsaye dan yana so su sake magana da mahaifiyar ta, a kafa ya taka a hankali kunnen sa sakale da earpiece suna magana da Ja'afar, har ya kusa karasawa gidan suna magana yana fada mishi yadda komai yake tafiya a gida. Daga nesa kadan yaga ta fito, cikin zulumi, kallo daya zakayi mata kasan ba a nutse take ba, da sauri ya kashe wayar yana kokarin tsaida ta yaga ta kara sauri, har zai juya sai kuma yayi tunanin ko babu lafiya, da sauri yabi bayan ta don tabbatar da babu wata matsala dan yanayin ta kawai ya nuna ba kalou ba. Tafiya take tayi hakan kuma shima be fasa bin nata ba, kamar daga sama ta hango Harira tana nufo ta, ja tayi ta tsaya jikin wata bishiya har ta ƙaraso, ganin haka yasa yayi kokarin juyawa, sai dai kalmar da yaji yasa shi dakatawa yana kokarin ganin yaji komai
"Wai Menene wannan kiran haka, kinga fa shiyasa kawai na yanke shawarar fitowa mu hadu a hanya dan yan gidan ma har sun fara zargin wani abu. " Hariran ta fada tana karasowa.
"Maganar Aminatu ce kin sani ai, fisabilillah bayan kin min alƙawarin ko wata biyu ba za'a yi ba zai sauta ta dawo gida, shiru kake ji gashi ana maganar watanni biyar, kinsan me hakan zai haifar nan gaba."
"Toh nidai bansan ina matsalar take ba, a gabanki na dauki kudin na bawa malam Tsalha da zauren gidan mu, ya tabbatar mana da ba za'a dau lokaci ba, toh ni bansan ina matsalar kuma take ba."
"Ni duk ba wannan ba, yanzu gaba daya bani da kwanciyar hankali wallahi, ni idan zai yiwu kawai ki nemo Hajiyar nan, ayi magana, ta in da ake hawa ta nan ake sauka, na fasa wallahi gwara su karbi yar su."
"Kamar ya? Abinda aka yi yarjejeniya, da zarar yaron nan ya kai matsayin da ake so ya kai din, sai ayi komai cikin sauki, amma yanzu daga farawa kice kin gaji, me ma akayi?"
"Ba zaki gane ba, dalilin baki san yadda yaya suke a zuciyar iyayensu ba, ni kam gaskiya ba zan iya ba, nayi nadamar abinda kika sani na aikata, yanzu zuwa zakiyi ki bani addireshin su, na je na same su a warware komai, na maida musu da yar su, tun kafin ranar da nadama ta ba zatayi min amfani ba."
Wani banzan kallo Harira tayi mata
"Amma dai kamar ba a hayyacin ki kike ba ko? Kar ki manta su waye mutanen da kike cewa zaki je, kina tunanin zasu tsaya sauraren ki? Bayan haka ma wacce hujja kike da ita da zaki nuna musu?"
"Jini ba karya bane Harira, wallahi suna ganin Aminatu ko ba'a fada ba zasu gane tasu ce, bayan haka kinsan dai ina da hoton mijin dana matar da muka dauka a saman file din asibitin su."
Dariya Harira ta saka sosai hadda tafa hannu
"Lallai Innaro, bansan ma kwata kwata tunanin ki baya ja ba sai yau, kinsan kuwa me kike shirin yi? Ina tabbatar miki da kina zuwa zasu kamaki su rufe ki, daga ke har zuri'ar ki kuwa babu wanda zai tsira."
"Ki fuskance ni, akwai matsala ne idan aka cigaba a haka, wadda zamu shiga sai tafi ya yanzu wallahi, idan muka samu yaron nan ya tsinke igiyar auren, sai mu tattara mu mayar musu da yar su, in yaso ita matar data tsara komai sai su kare chan, nidai Buri na d'ana ya dawo, rashin sa ya fara tabani. Nayi nadamar komai wallahi."
"Da kika gama kafa kanki da kudin da kika karba ba, ke fa wallahi san kanki yayi yawa, wato kinci moriyar ganga ko, toh bari kiji in fada miki gaskiyar magana, bansan in da suke ba, bansan aina za'a same su ba, rabona da su tun sanda muka rabu a asibiti, na yagi rabona, bayan wannan bansan komai akan su ba, ke wallahi ko sunan su ban sani ba, na sai tuna sanda Hajiyar take fada mana sunan da take so a sawa jaririyar, Aminatu MD. Daga wannan bansan komai akan su ba."
Wani irin kukan kura Inno tayi ta damki wuyan Harira, tuni kokawa ta rikice tsakanin su. Farouk dake tsaye a gefe yayi mutuwar tsaye tun sanda ya fara jin komai har zuwa sanda abubuwan suka dau zafi. Sosai maganar ta taɓa shi, wani irin mugun tausayin ta ya kara dirar masa fiye da wanda yake ji a baya, an cuci rayuwar ta, an raba ta da gatan ta, sai dai ya kasa gane dalilin daya sa suka aikata hakan, kenan babu sanin mahaifanta, toh wacece wannan data zabi rayuwar yarinyar ta lalace akan wani banzan burin ta mara tushe. Ya kasa gano hakan sai dai ya dau alwashin sai ya tabbatar da duk ya warware wannan daurin, ko da kuwa hakan na nufin....
Jin yadda suke abu kamar yara ne yasa shi magana cikin tsawa dan ba karamin bata masa rai sukayi ba.
"Ku dakata!"
A firgice suka juyo, wani irin bugawa kirjin Inno yayi, ta ɗora hannu a kanta kamar zata fasa ihu
"Yanzu kune kuke kiran kanku matsayin iyaye? Masu tarbiyyar yayan su? Tir daku wallahi."
"Faruku... Tsaya kaji, duk ba abinda kake tunani bane wallahi, yaudara ta akayi..." Katse ta yayi cikin tsananin bacin rai
"Babu sauran girmamawa ko mutuntawa a tsakanin mu. A dah ina miki kallon uwa ne, wadda tasan ciwon kanta dana ya'yan ta, ina ganin girman ki,a matsayin wadda ta kawo Aminatu duniya. Sai dai a yanzu babu ɗaya daga cikin wannan da zai sa na cigaba da ganin girman naki, ki sani a yau ni Farouk, ni zan zame wa Aminatu uwa, uba da dukkan gatan ta, har zuwa lokacin da zan hada ta da iyayen ta, babu kuma daya daga cikin ku da ya isa ya raba auren mu, ƙaddara ce ta haɗa mu, kuma babu wani mutum da ya isa ya raba."
Yana kaiwa nan ya juya a zafafe ya bar wajen, kwala masa kira take cike da tashin hankali, amma babu alamun zai tsaya balle ya saurare ta,kallo Harira tayi cike da tsana tace
"Sai kin yi dana sanin abinda kika aikata min."
Dariya ta saka harda tafa hannu tace
"Ko ke kiyi dana sani ba, uwar yan son zuciya ai nice maganin irin ku."
RanoHafsat Rano
(10)
***
Rai a bace ya shigo gidan, muka bishi da kallo nida Dada, be tanka ba, dan ko sallama a ciki ciki yayi ta yayi saurin wucewa dakin sa, yana zuwa ya maida mukullin kofar ya rufe, shiru mukayi baki daya babu wanda yayi motsi, ni a raina mamakin abinda ya sashi wannan tsananin fushin haka nake, ita kuwa Dadah ina kyautata zaton tasan tabbas koma menene akayi mishi ba karami bane. Har dare be fito ba, naje na buga dakin nasa yafi sau nawa baya budewa, duk na rasa ina zaka saka raina. Komawa nayi na shige cikin kujera nayi lamo na kasa ko cin abinci. Ina kwance na fara kuka kasa kasa, bansan dalilin kukan nawa ba, kila hakan na da na saba da yunwar da ke nukurkusata ne, jin karar bude dakin sa yasa nayi saurin tashi, shi dinne ya fito cikin shigar kananan kaya, fuskar sa tayi fayau kamar wanda yayi ciwo, tashi nayi na zauna sosai ban bar hawayen dake zuba a fuskata ba ya karasa sauka. Da sauri ya ƙaraso gareni ya zauna yana leka fuska ta
"Kuka?" Ya tambaya yana mamaki.
Daga masa kai nayi ina sake matsar kwallar.
"Menene?" Ya furta yana matsar da hannu na daga fuskar tawa, goge min hawayen ya shiga yi yana girgiza min kai.
"Karki kara kuka kinji? Babu abinda zai sake faruwa."
Daga masa kai nayi ba tare da na gane abinda yake nufi ba, matsawa nayi baya kadan na sake kwanciya ina kokarin kama cikina da naji ya murda.
"Kince abibci?"
"Umm umm."
"Ok Ina zuwa."
Ya tashi tsam ya nufi Kitchen din, chan sai gashi da abinci a tray da ruwa, zama yayi a kasa ya tankwashe kafarsa ya nuna min kusa dashi
"Oya..."
Da sauri na sauko dama abinda nake jira kenan, tare muka shiga ci yana bani labarin makarantar da yaje, nan danan na ware na shiga yi masa hira nima, ni na kwashe kayan na mayar na dawo na zauna ina duban wayar sa dake saman kujera..
"Dan kira min Amal dan Allah na bata labari."
Girgiza min kai yayi yana cewa
"Karki fada mata, ki bari kawai sai dai tazo ta ganki da uniform."
"Tohm shikenan." Nace ina murmushi. Mik'ewa yayi ya nufi kofar fita yana cewa
"Kije ki kwanta kinji, gobe da safe zamu fita."
"Toh." Nace ina mik'ewa dá sauri nayi daki.
***Da safe shine ya tashe ni, ya taimaka min na shirya muka fito, dakin Dadah muka wuce yana rike da hannu na, tana ganin mu ta riko ni tana sani a jikin ta, kallon shi naga tanayi cike da tsantsar tausayi. Girgiza kai kawai yayi yace "Zamu wuce Dadah, ayi mana addu'a." Hannu ta ɗora a kaina ta yi min addu'a, sannan ta rike hannun shi shima ta haɗa waje daya da nawa..
"Dan Allah Farouk karka yi wasa da abin da mukayi magana akai jiya, zan iya cewa kwana nayi ban runtsa ba ina tunanin komai."
"In Sha Allah." Ya amsa mata
Sakin hannun tayi tace muje Allah yayi mana albarka. Haka muka fito yana rike da hannun nawa har mota, wannan karon bayan shima ya shiga tare dani maimakon gaba, driver yaja muka dau hanya. Har muka isa makarantar be daina amsa waya ba, bansan da wa suke maganar ba amma tabbas maganar me matukar muhimmanci ce, lokaci zuwa lokaci yakan kalle ni ya sakar min murmushi. Sai daya ga mun doshi cikin makarantar sannan ya ajiye wayar, waje muka samu muka zauna har aka fara zuwa, ina ta kallon komai kamar almara, dandazon daliban dake kaiwa da komowa a cikin makarantar su suka fi jan hankali na, uniform dinsu ma kawai abin kallo ne, cikin tsafta da tsantsar nutsuwa. Sai wajajen goma da rabi sannan wani mutum yayi mana umarni da muka shigo, shiga mukayi muka zauna ya ɗan fita ya barmu. Kallo na ya Farouk yayi yace
"Idan suka tambaye ki sunanki, kice Aminatu Farouk MD kinji?"
Kafin nayi magana mutumin ya sake shigowa, zama yayi ya umarci ya Farouk ya ɗan jira a waje, fita yayi ya rufo mana kofar, kujerar kusa dashi yace na dawo, ya shiga yi min tambayoyi, da yawa ban san amsar ba, musamman bangaren turanci da lissafi, duk da na kan fuskanci wani abun saboda dan zaman da nayi da Ya Farouk da karatun da yake min dukka da turancin yake min su, sai dai ba komai ne nake ganewa ba duba da yanayi da makarantar da nake yi a dah. Tashi yayi ya leka ya sake kirawo shi.
"Mr Farouk, mun mata interview sai dai fa she's left far behind, ya zata iya catching kuwa? I doubt so."
Folding hannun sa yayi yana duban ya Farouk, murmushi yayi ya ce
"Sir munyi duk maganar nan da principal, zamu biya kudin extra lesson da za'a dinga mata har Allah yasa tayi picking, and bani da doubt zata kamosu, tana son karatu sosai so ina da hope akan ta."
"Ok Good, if that's the case, sai muyi komai yanzu, next week Monday ta zama full student, ina ga hakan zaifi."
"Hakan ma yayi, thank you very much."
"It's our pleasure."
Tashi yayi yace ya mu biyo bayan sa, muka bishi wasu offices, duk wasu formalities bamu bar school din ba sai da muka gama su, a ranar aka bani komai har da uniform, murna da farin cikin da nakeyi ba'a magana, haka muka dawo gida ina rungume da komai kamar wani ne zai raba ni dasu.
***
Dukkanin satin a cikin shiri muka karasa shi, sosai akayi min provision na dukkan abinda zan bukata, wannan karon Dada da kanta take tsaye akan komai, da ita aka gama shirya min komai. Sai dai ina lura kamar su ɗin ma hada kayan su suke tayi waje daya,sai dai ban kawo komai ba, na dauka ko wani abun dai zasuyi kawai, ana gobe tafiya makaranta dana matsu ina ji kamar na jawo ranar Dada tasa mai aiki ta rakani gidanmu. Gaba daya Inno tayi laushi kamar ba ita ba, ta rame sosai babu alamun walwala a tattare da ita. Kasa shiru nayi har sai dana tambaye ta ko bata da lafiya ne, ta bini da ido kawai ba tare da tace komai ba. Da muka zo tafiya ta dauko wata leda ta bani wai na makaranta ne, na karba nayi godiya na bawa mai aikin ta rike min, zamu tafi ta sake kirana daki ta hau min nasihar da bazan ce ga musabbinta ba, duk yawanci akan kula da karatu na ne, nidai kawai amsawa nake cike da mamaki, ban taba tunanin Inno zata min kwatankwacin hakan, duk sai naji babu dadi bana so na barta, da muka zo tafiya kuwa har da sharar kwalla ta cike da tausayin Inno da abinda yake damunta da bansan ko menene ba.
Washegari da wurwuri na shirya tsaf cikin uniform d'ina sababbi kal, na zauna zaman jiran Ya Farouk, ina zaune shima ya fito, dan tsayawa yayi da baya yana kunshe dariyar sa, hatta jakar da komai na ajiye a gefe, zaman jiran sa kawai nake, karasawa yayi ya zauna yana dauke kansa. Ban gaishe shi ba, kawai na fara maganar tafiya, kin amsa min yayi ya wuce Kitchen ya hado tea ya fito.
"Jeki nemi abu kici." Yace yana zama cikin kujerun falon, ganin fuskar sa babu wasa yasa na tashi tsam nayi Kitchen din, tea din nima na hado na dauko bread na fito, kamar magani haka nake ci cike da daukin tafiya, yana ta kallo na ta gefen ido har zuwa sanda ya gama ya maida komai Kitchen yazo ya fice, sauri sauri nayi na karasa na sake gyara komai na zauna ina kallon kofa. Chan sai gashi ya dawo dauke da wasu ledoji, a saman kujerar ya watsa su ya wuce dakin Dadah, jim kadan suka fito a tare itama ta shirya alamar tare zamu tafi. Da fara'a ta na gaishe ta, daga nan muka rankaya waje muka shiga mota ina ta murna kamar bakina zai yage. Uffan be ce min ba, yana dai noticing duk motsina. Haka nan yaji ba dadi, ko ba komai akwai matukar shakuwa tsakanin mu, amma hakan shine mafita ga dukan mu. Sanda muka isa makarantar sai naji duk babu dadi, Ina labe a bayan Dadah har aka gama komai, tuni fuska ta ta chanja dana ji an kirawo wata an ce ta tafi dani, da sauri na kankame Dada ina sakin kuka, dariya suka saka baki dayan su, hakan ya kara tunzura ni, hannu na ta kama cikin harshen turanci tace "muje ko?" Kwace hannu na nayi na sake saka kuka ina kallon Ya Farouk, shi dinma ni yake kallo, hannu yasa ya kirawo ni, da sauri na tafi gareshi, maimakon yayi min magana sai yaja hannu na muka fita daga office din, chan baya wajen wasu shuke-shuke ya kaimu, yana zuwa ya cika hannu na yana ja da baya.
"AMINATU..." Ya kira sunana yana saka idon shi a cikin nawa, raw raw na sake yi da idon zan cigaba da kukan, da sauri ya furta
"Ohh Ya Salam! Baki son makarantar ne?" Girgiza masa kai nayi na cigaba da kuka na.
"Toh menene, kin fasa karatun ne?" Nan ma girgiza kai nayi
"Bude baki ki faɗa min kinji." Ya fada yana sake matso wa sosai kusa dani, cikin muryar kuka nace
"Ni ba tafiya zakuyi ku barni anan ba."
Dan murmushi yayi kadan, yasan kwanan zance, lallashi na ya hau yi cikin son gamsar dani muhimmancin hakan, tare da alƙawarin zuwa duba ni kowanne lokaci, da kyar na sa kaina na amince, sai dai ban bar kukan ba, haka ya sani a jikin sa yana shafa bayana a hankali, lamo nayi na kasa kwakkwaran motsi, ina jin shi yana kokarin raba jikina da nashi jin takun tafiya, Dadah ce ta iso wajen tana nazarin mu.
"Babana sallamar ta isa haka nan, karka manta fa muna komawa..." Kallon danayi mata ne yasa ta gimtse maganar tana yin gaba
"Kuyi sauri dai ina mota ni, Aminatu Allah ya bada abinda aka zo nema, banda kawayen banza."
Daga haka ta bar wajen dukkanninmu muka bi bayan ta da kallo babu ko kiftawa, a hankali ya kamo hannu na, ya ciro dan karamin akwati ja me masifar kyau daga aljihun sa, bude ta yayi dan karamin zoben azurfa ya bayyana, ya kama ring finger na ya zura min, yana kallon fuska ta. Babban harafin D cikin wata irin kwalliya shi ya karawa zoben kyau da kawa, kura ma hannun nawa ido nayi cikin tunani me tsawo da bansan me nake son tunawar ba. A hankali cikin wata iriyar magana ya furta...
"Alk'awari kaya ne Aminatu, ki rike Alk'awari, nima zan rike, kiyi karatu, kiyi karatu har sai kin ji kamar kwakwalwar ki xata fashe, a sannan zan tabbatar da buri na ya cika, ina so ki zama cikakkiyar lawyer saboda wani kudiri nawa."
Daga kai kawai nayi ina cigaba da kuka ganin da gasken tafiya zasuyi, gaba yayi kawai nabi bayan shi da sauri, haka muka jera har gaban motar, da wani irin sauri ya fada ba tare da ya sake kallon bangaren da nake ba, ina ji ina gani suka fice daga cikin makarantar.
Jan kafafuwa nayi na wuce ina jin kamar wani babban bangare na rayuwa ta ya bar ni.
****Suna isa gida suka sauke Dadah, kai tsaye gidan su Aminatu ya wuce, Inno na zaune tana kulla kayan miya aka sanar mata da isowar sa, sai da gaban ta ya fadi, amma ta dake tace a shigo dashi dakin ta, shiga yayi ya zauna yana karewa ko ina kallo, a matukar sanyaye ta shigo dakin, bayan tasa Karime ta kawo masa ruwa, zama tayi daga chan gefe tana tunanin ta in da abubuwan zasu fara.
***Rayuwa na shiga yi sosai a makarantar, bani da wani lokacin kaina sai ka karatu, kawata daya ce Asma'u, tare muke karatu muyi komai, bani da wata matsala sai ta rashin Ya Farouk da nake matukar jin sa a jinin jikana. Lokacin visiting nayi sai gashi yazo, shi kadai yazo nayi ta murna, dariya kawai yake ina bashi labarin makaranta da wahalar karatun da nake, tun da ni kullum akwai wani extra lesson da ake min bayan normal lesson da muke yi baki dayan mu, hakan yasa nake shan wahala sosai, wani lokaciin ma sai naji kamar na sare, sai na tuna kalaman sa na ƙarshe, su ne suke sake zaburar dani dan ganin na cika masa burin sa kamar yadda yace.
Lokacin da akayi hutun makaranta, sabuwar principal din da aka sake wadda na lura da zuwan Ya Farouk na karshe sun jima suna magana da bansan ta mecece ba tasa aka kirani, ta tabbatar min da ni bazan je gida ba, anan makaranta zan zauna wajen ta na cigaba da extra lesson d'ina, ranar wuni nayi ina kuka, haka ina ji ina gani kowa ya watse ya bar ni. Rayuwa ta haka ta cigaba da tafiya, ina iya kar kokari na wajen ganin nayi karatu, maganar zuwa gida hutu kuwa na rasa dalilin da yasa bana zuwa ɗin, tun ina damuwa har na hakura bayan munyi wata doguwar waya da Ya Farouk da wayar headmistress din, tun daga nan na watsar da komai na cigaba da karatu na ka- in- da-na- in.
Lokacin da mukaje aji uku ne, akayi hutu sai ga mutanen da ban taba tsammanin ganin su ba, Ya Farouk ne tare da Amal, Dadah sai Inno da Karime, karamin hauka ne kawai banyi ba, amma tabbas zan iya cewa na jima banyi farin ciki irin wannan ranar ba, abu daya na kasa gane kansa, shine yadda Inno tayi laushi sosai, ta zama wata shiru shiru, duk in da nayi tana bina da kallo kawai, wani lokacin ma sai na ga kamar tana sharar kwalla, ban kawo komai ba, na cigaba da nan nan dasu, har suka zo tafiya, sosai naji son bin su, amma kuma nasan hakan ba me yiwu wa bane. Haka suka tattara suka tafi suka barni da tarin kewar su. Tun daga nan karatu na ya kara daukar zafi, babu wanda ya kuma leko ni, sai dai lokaci zuwa lokaci ya Farouk kan kira a wayar principal ta bani, kullum maganar sa daya nayi karatu, haka na cigaba da dagewa sosai. Zuwa lokacin zuciya ta ta gama sanin menene so, menene kauna, abinda nake ji game da Ya Farouk wani yanayi ne da zuciya da ruhi ne kadai zasu iya tabbatar dasu, baki na yayi kadan ya fasalta yanayin da nake ji game dashi din. Har muka shiga Ss2 be sake waiwayo ni ba, kiran da yake min sam ya daina, sai na dauki hakan a matsayin yana son yaga na yi karatu ne, aikuwa na sake jajircewa.
Exams muka fara ta karshen Ss2, wadda zamu shiga ajin karshe, hakan ya sa na kara zama serious, bani da lokacin komai sai na karatu, sosai kuwa nake jin dadin exams din, ranar da mukayi final exams ne na fito ina tafiya a hankali, iska ake kadan kadan, yammaci ne me cike da ni'ima akwai alamun za'a iya ruwa kowanne lokaci, tafiya nake ina tunanin shi, iya sanin da nayi masa nasan shi mutum ne me matukar son yanayi irin na damuna, jin kamar ana min magana ne yasa na dan dakata ina juyowa, wata yarinya ce yar junior session, hannun ta rike da tarin littattafai.
"Kiran ki ake a bayan garden din chan." Tace tana nuna min da bakin ta
"Ni kuma, wake kira na?" Nayi tambayar cike da mamaki
"Kije zaki gani." Ta amsa min tana wucewa abin ta, cike da mamaki na zuba wa hanyar garden din ido, mamakin me kira na nake, har zan wuce hostel sai kuma na fasa na juya zuwa hanyar da zata sadaka da dan karamin garden din makarantar, ina isa na shiga wurga ido na ko zan ga wanda yake kirana, ban ga kowa ba, tsaki naja kadan na juya da nufin barin wajen. Kamshin turaren sa ne ya daki kofofin hanci na, da sauri na juyo, ido na suka sauka akan sa, sanye yake cikin shigar Kufta baka, wadda tasha aiki sosai da bakin zare ɗinkin three quarter , kansa babu hula sai dai yana rike da ita a hannun sa. Cikin wani irin yanayi yake takowa gareni, na kasa ko da kwakwaran motsi balle nayi tunanin abin yi. Ya chanja kwarai, ya zama babban mutum, me cike da kwarjini da tsari, tsananin nutsuwa da tsagwaron hutu sun nuna kansu a tattare dashi, bayan wadannan abubuwan babu abu daya daya chanja a tattare dashi d'in, shine dai Farouk d'ina, wanda nake ganin sa a matsayin rayuwa ta, komai na.
Hannun sa yasa ya murda a saman fuska ta ya bada sauti, da sauri na shiga kokarin boye fuska ta, tsananin kunyar sa ce naji ta rufe ni lokaci daya, wadda ban taba jin hakan ba sai yau din, wanda nake kyautata zaton hakan na da nasaba da yadda zuciya ta ke kara jaddada min matsayin da yake dashi a cikin ta.
"My Destiny..." Ya kirani da sunan da dukkannin bangarorin jiki na sai da suka karbe shi, kasa daga kai nayi balle ya sa ran zan kalle shi, ina jin shi yana sakin dariya kasa kasa, kallon tsaf yake mun tun daga sama har kasa, a yau ya sake tabbatar da cewa Aminatun sa ta kai, ta isa dukkanin yadda yake da muradi.
"Yau ni yar Aminene take jin kunya?" Ya furta yana dariya
Da kyar na harhada kalmomin gaisuwa waje daya na furta
"Ina... Wu..ni?"
"Ah laillai, na yarda yau Aminatu na ta girma, kunya Aminatu? Ya farouk dinki ne fa, this is unbelievable!"
"But I like it." Ya fad'a yana kawo bakin sa daidai kunne na. Da sauri na ja baya, hakan yayi daidai da zamewa ta, cikin zafin nama ya tare ni da dukkan karfin sa, ido na shiga zarewa kamar zan fita da gudu, hannun sa ya saka cikin nawa ya jani zuwa jerin kujerun dake zagaye a harabar wajen, banyi musu ba, na shiga bin sa, ina fatan abinda nake ji a yanzu ya zame min wani tsani da zan sake takawa na rayuwa, sai dai kash!.
RanoONAR TASFAH
11
©️®️HafsatRano
*ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo
***
Hannun sa ya sabule daga jikin nawa ya zauna yana nuna min kusa dashi, a kunya ce na zauna, kafe ni yayi da ido na kasa koda kwakkwaran motsi, duk da hakan be dauke kansa daga kaina ba, yana so lallai sai yaga tasirin da idanun sa suke min, hannu nasa na kamo karshen hijabin nawa na shiga wasa dashi, bin hannun yayi da kallo yayi murmushi.
"AMINATU... Wai Menene hakan ne? Kunya ta kike ji? Akan me?" Duk a lokaci daya yayi min wannan tambayar, ni kaina mamakin kaina nake ji yadda tsananin kunyar sa ta mamaye ni, na kasa kwakkwaran motsi, kwarjinin sa ne duk ya cika wajen, duk yadda naso na sake dashi na kasa, ina jin sa yana magana nayi kus kamar bana wajen, tashi naga yayi, ya zura dukkan hannayen sa cikin aljihun rigar sa, cikin jin haushi yace
"Tun da haka ne, bari na tafi kawai tun da ba'a son gani na."
Da sauri na rike hannun sa,
"Dan Allah karka tafi." Hannun nasa ya kalla sannan ya kalle ni, ya kwashe da dariya, da sauri nayi kokarin zare hannu na amma sai ya rike
"Baki isa ba ai, ana so ana kaiwa kasuwa." Dariya muka sa a tare baki daya, duk kunya ta sake kamani. Komawa mukayi muka zauna muka hau hira, mafi akasarin hirar shine yake min, duk da na dan sake kadan kar yace zai tafi. Acikin hirar ne na daure na tambaye shi karatun sa, wayar sa ya bude ya shiga gallery ya mika min, baki bude nake bin jerin hotunan nasa da suka gama bayyana irin karatun da yayi, no wonder na ganshi ya sake zama babba, ko ina na jikin sa ya murje, irin na ingarman namiji.
"Soja Ya Farouk!" Na faɗa ina kallon sa.
Daga min kai yayi yana dariya
"Burin both Daddy da Mom ne, sannan kuma burin Farouk dinki ne, saboda wani babban dalilin sa."
Jinjina kai nayi ina sake kallon sa.
"Ni da nake tsoron soja kuma..."
"Sai ka mijin ki soja ba, sai ayi yaya? Karki manta fa ance... A wife of a soldier..."
"Can never be a soldier." Nayi sauri amsa masa ina dariya. Dariyar shima ya saka ya kai hannu ya dungure min kai
"Sarkin wayo, toh ba haka karshen yake ba."
Muka kara saka dariya a tare. Hira muka cigaba ba dayi har zuwa sanda aka kira magriba, tashi yayi yana nannade hannun rigar sa.
"Ya za'ayi?" Ya daga min kira sama,
"Uhum." Nace ina tashi nima.
"Kinga ba'a rufe makaranta ba sai gobe, wannan ma dan dai principal din ta hannun damar Mummy ce, kar mu shiga dokar makaranta, zan wuce, amma zan dawo gobe, kinsan da maganar zana waec dinki a Ss2 ko?"
Daga masa kai nayi
"Ok zamu je gida sai kiyi sati daya...
Dagowa nayi da sauri, murmushi yayi min yace
"Daga nan sai a dawo makaranta, kinga ba za'a dade ba zakiyi exams, kina gama wa..."
Be karasa ba, yayi shiru yana sake fad'ad'a fara'ar fuskar sa
"I can't wait ranar nan tazo, duk plans d'ina na ranar ne, Allah dai ya kaimu, zaki yi mamaki sosai."
Bude baki nayi zanyi magana yayi saurin katse ni
"Karma ki tambayi me zai faru ranar, kedai kawai ki shirya mata, it's going to be the biggest day of our lives."
"Shikenan." Nace ina matsawa gaba.
"Ba sallama?" Ya marairaice murya yana bude min hannayenku sa, sarai na gane me yake nufi, dariya nayi, na kara yin gaba, sosa kansa ya shiga yi yana kallo na, sai dana tabbatar nayi nisa daga in da yake sannan na daga mishi hannu ina masa gwalo, da hannu yayi min alamar zai kamani ne.
***
Washegari tun da wuri na tashi, ina nan da d'abi'ata ta dauki idan zanyi abu na tashi da duku-duku na hau shiri, ina ji aka kad'a kararrawar assembly da ake yi a duk ranar da za'a rufe makaranta, a gurguje aka gabatar da komai da ranar da za'a dawo makaranta, kasancewar akwai sauran wajen sati uku kafin a fara Waec yasa aka bawa yan Ss3 hutun sati daya, sai kuma a dawo a fara karatun jarabawar kafin lokacin ta ya zo. Da haka kowa ya hau watse wa cike da farin ciki zuwa gida. Ina tsaye a saman barander classes dinmu na kafa wa gate ido naga shigowar shi, ji nayi kamar zan zame, haka dai na daure na nufi wajen motar, ina zuwa yana fitowa, idanun mu suka sarke waje daya, da sauri na janye nawa na hau gaishe shi, murmushi kawai yayi ya wuce wajen da aka signing, a gaggauce yayi signing din ya taimaka min na dau yan kaya na muka dau hanyar kauyen mu. Sanyin Ac da kamshin turaren da ya bulbula ne suka cika motar, lamo nayi jikin kujera ina jin wani yanayi ne wuyar fassara, magana yake min kasa kasa wanda zaka rantse ba dani ɗin yake ba, idon sa na kan titi sai dai hannun sa daya na rike da nawa yana murzawa a hankali. Har muka isa gida na kasa sakat, shi kuwa babu abinda ya dame shi, sha'anin gaban sa kawai yake cike da tsantsar farin ciki da ya kasa boyuwa a saman fuskar sa.
A kasalance na fito daga motar bayan ya tsaya, gaba nayi kawai dan Allah Allah nake na isa ciki na samu sauƙin abinda nake ji, ina shiga daki yana turo kofar, tsaye yayi kamar yadda ya saba a wanchan lokacin, hannayen sa jingina da makarin kofar, idanun sa na zagaya wa lungu da sak'o na dakin.
"Garin sauri kin manta kayanki Madam."
"Na manta wallahi."
"Dole ki manta ai, kina gudu na, duk kin chanja Aminatu, what's wrong with you?"
Ya fada yana takowa cikin dakin, saurin kasa nayi da kaina ina jin sanda yazo daf dani
"Look at me." Ya furta a chan kasan makoshinsa, a dan darare na dago na kalle shin, sai naga ya cika gaba daya wajen. Tallafo fuska ta yayi ya dago ni
"Kinsan matsayi na wajen ki ko? Kinsan dai ba zan cutar dake ba, then why are you behaving like this? Kamar kin ga bako."
"Ni kawai kunyar ka nake ji Allah."
Na faɗa kai tsaye. Dariya yayi ya saki fuskar tawa ya fada saman gadon dakin, tsaye nayi ina tunanin abin yi, ji nayi ya finciko ni na fado gadon kusa dashi, har saman keyata na buguwa da sangalalin hannun sa, matsowa yayi sosai yana kura min ido
"Shekarar ki 17 if i'm not mistaken, ni kuma i'm 29, nasan abinda ya dace da wanda be dace ba, karki damu, babu wani abu da zan miki da nasan zaiyi hurting dinki, ki daina tsoro na ko kunya ta, ki dauke ni kamar dah, Ya Farouk dinki, ni a waje na,har yanzu yar karamar Aminene nake kallon ki."
Dariya na saka, na kai masa dukan wasa, da sauri ya tare yana hade hannaye na waje daya ya murde su, yar kara nayi kamar zanyi kuka na shiga magiyar yayi hakuri, da kyar na samu ya hakuran, amma sam yaki barin dakin, ni kuma na matsu ya fita dan na samu na watsa ruwa na cire kayan jiki na, kiran wayar da akayi masa ce ta taimake ni, da sauri naga ya daga wayar yana kokarin fita daga dakin baki daya, da haka na samu damar saka key a dakin na aiwatar da abubuwan da nake so.
***Har dare be sake waiwayo ni ba, ina zaune a dakin ban fita falo ba, gidan tsit babu motsin kowa, kaina ke dan saramin saboda yunwar da ta fara addabata, ban dauko komai cikin provision dina ba, gashi naje Kitchen ɗin babu komai balle na samu abinda zan dan taba. Zamewa nayi na kwanta a saman tiles din dakin hannu na rike da wani story book ina karantawa saboda rage kadaita, turo kofar akayi, hannun sa dauke da ledoji manya guda biyu, tashi nayi da sauri na zauna. Ajiye ledojin yayi a gabana ya zauna.
"Ya Farouk yunwa." Nace ina bata fuska.
Tura min ledojin yayi
"Kiyi hakuri abu ne urgent ya fitar dani."
Matsawa nayi na bude na dudduba, kafin na tashi dan zuwa dauko abinda zan juye a ciki.
Bayan mun gama ci na tattare komai na maida na dawo dakin, ban tarar dashi a ciki ba, na shirin bacci na kashe wutar, ina cikin addu'a akayi knocking, tashi nayi na bude, yana tsaye cikin shigar bacci shima, rabawa yayi ta gefe na ya wuce ciki, tsaye nayi a jikin kofar ina kallon sa, har ya haye gadon nawa yana jan dubet zuwa saman kafadarshi.
"Idan kin gama tsaiwar, ki rufe kofar kizo ki kwanta."
Muryar sa ta daki kunne na, jim nayi kamar ba zan motsa ba, sai kuma na shigaa jan kafata da kyar kamar wadda kwai ya fashe wa na isa dayan bangaren, a darare na hau gadon na kwanta gefe daya, ina jin sa ya mirgino zuwa bangaren da nake, ya dora kansa saman pillow na yana saka ni cikin jikin sa. Jiki na ne ya hau rawa kamar mazari, a hankali ya dora bakin sa saman kunne na ya furta
"Let sleep princess, Goodnight."
Manage pls nayi typing ya goge 😥😥😢😓🙏
Comments yana taimakawa sosai wajen motivating writer🙏 Thanks All Jazakumullah bhi khair*ONAR TASFAH*
*OROG NIRUAD*
*RIYAB AFAFAZ*
*EGAP (12)*
***
Kamar tsohuwar munafuka haka nayi ya raba idanu, gaba daya na rasa yadda zanyi, duk na takura,kasa koda kwakkwaran motsi nayi ina jin shi yana karanta mana addu'ar bacci. Bani da kuzarin da zan iya bude baki na, nayi addu'ar nima, haka nayi shiru ina tunanin abinda ke faruwa.
"Princess."
Ya kira ni da sabon sunan da ban san yaushe na same shi ba.
"Uhum ." Nace kamar me ciwon hakori,.
"Please ki saki jikin sa, bacci nake ji nasan kema haka, beside ni mijinki ne, mata da miji basa raba daki sai da kwakkwaran dalili, so kawai ki saki jikin ki dan ba fita zan ba, ina nan anan zan kwana atau."
Ban tanka ba, ina jin sa yana ta kokarin ganin sai na saki jikina, wanda ni kuwa har ga Allah ba iya wa zanyi ba, a yadda nake ji ma yanzun Allah sa nayi runtsawa, yadda yabi ya kanainayeyi, bana jin zai barni na shaki iska me dadi yau kuwa. Har ya gama surutan sa ya fara jan numfashi sannan na sauke ajiyar zuciya, gaba daya bani da sukuni balle nutsuwa da zan iya runtsawa. Sake sake na shiga yi ina tuna wani Novel dana taba karantawa. Da haka bacci barawo yayi awun gaba dani ba tare da na shirya masa ba.
***
Kira wayar sa ce ta farkar dani, baya dakin, na kai duba na wajen wayar, sunan da na gani yana yawo a saman wayar na kura wa ido, har ta gama ta katse wani kiran ya sake shigowa, ita ɗin ce dai, tsam na mike nayi hanyar toilet ba tare da na sake bi takan wayar ba. Tsawon mintuna talatin na dauka a toilet din, gaba daya na hado har da wanka na fito, a gurguje na hau shiryawa ina kallon kofa kar ya shigo, har na gama ɗin kuwa be shigo ba, sai a lokacin na lura ya dau wayar tasa kenan ya shigo ina toilet, ban shafa komai ba sai yar powder da wetlips, na dora hijabi na a saman sabuwar atamfar da na saka ta sau daya a makaranta, blue ce da adon baki anyi mata zanen ganye. Half covered shoe d'ina black na jawo a cikin kayan dana zo dasu na zura na yo waje. Yana zaune a saman kujerar falon, hannun sa rike da mug yana fitar da tururi alamun abu me zafi ne a ciki, shi dinma yayi wanka ya shirya cikin ƙananan kaya black top da wandon su na sojoji, kallo ya hau bina dashi har na karasa ina zama a kasan carpet daidai wajen da kafafun sa suke. Zamowa yayi ya zauna kusa dani kafadarsa na gogar tawa yayi saurin cewa
"Good morning princess."
Murmushi nayi na gaishe shi da ina kwana? Amsawa yayi yana mika min mug din hannun nasa
"Tayani sha wallahi cikana a cunkushe yanke."
Mika hannu nayi zan karba ya girgiza min kai, hanyar bakina yayo dashi a kunya ce na bude ya kafe min cup din, a hankali na shiga kurbar kunun gyadar daya sha madara da sugar, ina sha ina tunanin in da ya samo shi, tas na shanye, ya jawo tissue ya mika min yana tashi
"Anji dadi an shanye min."
Dariya nayi ina karba shi
"Ni kawai dan ka takura ne nasha, amma ba dadi."
"Really!" Yace yana rike kugun sa.
"Umm."
"Ai shikenan, gobe ma rana ce, za'a kawo min ne ba zan baki ba."
"Waya kawo maka?" Nayi saurin tambayar shi dan dama ina son sani. Make kafadar shi yayi ya juya hannun shi
"Ba sai kinji ba."
Murmushi kawai nayi ina ayyana a raina wanda ya kawo mishin, ganin zan bata wa kaina lokaci da tunani yasa na wuce Kitchen ɗin, na wanke mug din na gyara wajen na fito. A tsaye na tarar dashi yana kokarin saka p-cap a kansa
"Muje na ajiye ki a gidan sai yamma na dawo, nima ina da abin yi yau din da yawa."
Da sauri na juya, na dauko yar karamar jakata na saka tarkacen chocolate da sweet na fito, tuni ya shiga mota achan na iske shi muka dau hanya.
Muna fitowa yayi daidai da lokacin da Garbati yazo wucewa a saman machine din sa, gaba daya ya chanja kamar ba shi ba, riga da wandon jikin sa kadai sun isa su fada ma halin da yake ciki, duk yayi baki ya rame bakin sa yayi duhu alamar yasha sigari ya koshi. Kansa yayi da motar, ya ɗan taba shi, take ya fadi a wajen, balle murfin motar yayi idon sa yayi jawur ya fito, Garbati na kokarin mik'ewa cike da masifa ya dira a gaban shi. Kafa yasa ya take machine din, yana kallon fuskar shi.
"Uban waye kai da zaka ture ni, kuma..." Maganar sa ta makale sakamakon wandon daya fara cin karo dashi bayan ya dago. Cikin in da in dah yace
"Me nayi maka?"
Farouk be tanka ba, sai kafa daya sa ya tardes shi, tuni ya baje a wajen bakin sa ya fashe, hannu yasa ya hau zare belt din jikin sa, da sauri na balle murfin motar na fito, na isa wajen, rike shi nake kokarin yi, ya juyo a fusace ya nuna min mota
"Wuce ki koma ciki." Yadda yayi maganar da yanayin fuskar sa, yasa naji yan hanjin cikana sun juya, da gudu na koma na zauna ina rawar jiki. Be wani tsaya bata lokaci ba ya shiga laftawa Garbati belt din nan, ihu yake yana magiya amma sam yaki sauraran sa, Dukan sa yake da dukkan karfin sa, tuni abin ya fara bani tsoro, ganin yadda ya koma kamar ba Ya Farouk ba, ya juye gaba daya ya zama kamar wani horror, kuka na soma a hankali ina daga zaune a motar, sai daya tabbatar yayi masa laga-laga sannan ya ture shi ya nufo motar, da bayan hannu na, na shiga share hawayen fuskar ta. Be ko kalle ni ba, ya tada motar muka dau hanya, ta gefen ido nake satar kallon sa, yadda kirjinshi ke kaiwa da komowa. Sosai nayi mamakin tsananin zuciyar shi. Muna zuwa kofar gida nayi saurin kama kofar motar zan fita, naji ya riko hannu na.
"I'm sorry." Ya furta yana kallon ido na, daga mishi kai nayi ina sake kokarin bude kofar dan har ga Allah na tsorata da yanayin sa. Lock din kofar ya danna, ya matso daf dani, da sauri na kulle ido na zuciya ta na harbawa, tsoro na daya kar nima ya jibgen, a hankali naji saukar light kiss a saman goshi na, sake runtse ido nayi na kankame jikina.
"Ohh shit." Ya daki steering motar,
"Kinga, pls karki ji tsorana, i can never harm you, shi wanchan kuwa zan masa fiye da wannan, wannan somin tabi ne, saboda haka kar na sake jin kinyi kuka idan ina abu makamancin wannan."
"Toh." Nayi saurin cewa.
"Zan tafi." Na nuna masa kofar motar. Dan karamin tsaki yaaja ya bude min da sauri na fita ina yin hanyar zauren gidan. Sai dana shiga sannan yaja motar ya tafi.
Sallama nake tayi a tsakar gidan namu, baki daya komai ya sauya, sosai gidan ya sake tsufa, duk kofofin sun lalace, dakin Inno na kalla naga an dan turo kyauren alamun bata nan, Yalwati ce ta fito daga dakin Baba, da mamaki take kallo na, sai kuma ta fadada fara'ar fuskar ta.
"Wa nake gani kamar Aminene?"
Dariya na saka na karasa ciki.
"Ah laillai, maraba da yan makaranta."
Kasa na tsuguna na gaishe ta, ta amsa sosai, kafin tace
"Shiga wajen Baban naku, Inno dai ta je hayi karbo magani, kinsan duk ba dadi suke ji ba ita da shi."
"Allah ya sauwake." Nace ina tura kofar dakin, yana kwance daga gani yana jin jiki, kallo na yake har na isa gaban sa na zauna.
"Sannu Babah." Na gaishe shi cike da tausaya wa, hannun sa daya naga ya daga min, alamun na matso, matsawa nayi sosai na rike hannun sa ina jera masa sannu. Yalwati ce ta shigo rike da kofin silba cike da ruwan randa.
"Tsautsayi ya gamu dashi ai, faduwa yayi a banɗaki shikenan barin jikin sa daya ya shanye, kin gashi nan baya ko magana."
Kwalla ce ta zubo min cike da tausayin baba, mutum me sauƙin kai da hakuri, bashi da ta cewa kowanne lokaci sai abinda Inno ta gindaya masa, yau shine rayuwa ta juya wa baya haka, da ido yake min alamar nayi shiru, kasa kasa na cigaba da kukan nawa ina masa addu'ar samun sauki. Ban fito daga dakin ba, sai da Inno ta dawo. Tana gaban dakin ta ta baza ledar magungunan gargajiyar data karbo na fito, da ido ta kafe ni cike da mamakin gani na.
"Yaushe kika zo.?" Tun kafin na gaishe ta ta watso min tambayar, murmushi nayi kawai dan hausawa sunce me hali baya fasa halin sa.
"Sannu da zuwa, ina wuni?" Na bagarar da tambayar da tayi min na maye gurbin ta da gaisuwa, amsawa tayi tana cigaba da duba kayan data zo dasu kamar bata damu da zuwan nawa ba. Dakin nata na shiga, duk yayi kacha-kacha, ajiye hijabi na nayi na shiga kokarin ganin na gyara. Ina cikin gyaran ne nazo kan jakar da nake yawan ganin tana ciro ta, ta duba. Hannu nasa da nufin bude jakar ta shigo.
"Kee!" Ta daka min tsawa, da sauri na saki jakar ta sabule daga hannu na
"Me kike yi haka?"
"Um.. um.. dama gani nayi dakin..um yayi datti shine nake sharewa."
Zuwa tayi gabana ta dauke jakar ta bude sip dinta ta saka.
"Yi sauri ki karasa sharar ki fito zaku gaisa da mutane." Daga haka ta fice ta barni, sauri sauri na karasa na fito, na shiga sauran gidajen dake cikin gidan namu. Bayan na dawo ina ta tunanin ina yan matan gidan suke, chan dai na tambayi Inna, sai a sannan nake sanin ashe duk an musu aure. Hanne ta haihu ma Karime kuma ta kusa. Sosai nayi mamaki, naso a ranar na samu me rakani, ana la'asar sai ga kiran Ya Farouk a waje, ban so ba, haka na shiga dakin Baba nayi masa sallama sannan na fadawa Inno yazo zan tafi. Shiru tayi kamar me nazari, sai kuma tace
"Kice masa dan Allah yazo ina son magana dashi."
Da toh na amsa mata na fito nayi wa sauran sallama. Waya yake yanzun ma, ina bude kofar yayi sallama yana dage min kira sama.
"Ina wuni?"
"Lafiya lou, kin gama ai ko?"
"Eh na gama."
"Ok."
Ya hau kokarin data motar,
"Dama inna tace na fada maka tana son magana da kai wai."
Da sauri ya kalle ni
"Kunyi wata magana ne?" Ya tambaye ni
"A ah bamuyi ba." Na amsa. Ajiyar zuciya naji ya sauke kafin yace
"Shikenan zan zo gidan gobe, yanzu ana jirana ne."
Bance komai ba yaja motar muka bar kofar gidan.
***
Tsawon satin haka mukayi shi, babu abu d'aya, daya chanja, kullum zamu kwanta kamar yadda muka fara a ranar farko, tun ina nokewa har na saki jikina ganin babu abinda ya faru, sai dan abinda ba za'a rasa ba.😜 Naje gidan Karime da Hanne, sannan na koma gidan mu sau biyu na sake duba Baba, bansan ko yaje sunyi maganar da Inno ba, ba ta kara dai yimin maganar yazo ɗin ba, sai kawai na share ban tambaya ba.
Daren ranar da zan koma makaranta dukkan mu bamu da walwala sam,sai nace har gwara ma ni ina dan daurewa, amma shi ƙarara ya nuna damuwar sa, hira nake masa da son ganin ya ɗan saki ransa, amma fafur yagi, shinkafa da miya nayi mana a daren ranar, na samu yaci ba laifi dan tun rana be sa komai cikin sa ba. Da wuri yace muje mu kwanta, ranar babu petir a inji be fita ko nan da chan ba. Haka muka yi shirin kwanciya bayan na tabbatar da na gama hada komai nawa a waje daya. Wanka na fara yi saboda yadda garin ya hade rai alamun za'a yi ruwan sama, babu iska ko kadan sai kugin hadarin kawai kake ji. Ina fitowa daga wankan naji garin ya ɗan fara saki, doguwar rigar bacci kawai na zura na haye gado na kwanta, ina kwanciya ya shigo yana haska wa da torchlight ɗin wayar sa, rufe ido na nayi da sauri alamun bacci, wucewa yayi gaban mirror ya shafa roll on dina ya hawo gadon ya jawo ni jikin sa. Muna nan kwance babu wanda yayi wa wani magana, aka soma yayyafi, saki na yayi ya tashi ya bude windows din sosai iska ta shiga zagaye lungu da sako na dakin, yana tsaye ya zura hannayen sa yana kama yayyafin dake sauka kadan kadan. Cikin dan kankanin lokaci dakin yayi sanyi, ruwan da aka farayi da karfi yasa ya sake rurrufe glasses din windon ya saki curtains din. Da sassarfa ya hawo gadon ya kwanta yana ware hannuwansa.
"Alhamdulillah, ni'imar Allah ta sauka." Ya furta yana mirginowa waje na.
Shiru mukayi dukkannin muna sauraron saukar ruwan da karfi a nutse babu hayaniya, irin ruwan da za'a iya kiran shi da peaceful rainfall, babu tsawa babu tsananin iskar nan, hakan ya haifar da wani yanayi a tsakanin mu. Shirun da mukayi kowa da abinda yake ayyanawa, a daidai lokacin Ya Farouk na fama da zuciyar shi akan abinda take kokarin bijiro mishi dashi, duk kuwa da alkawari ne ya dauka wa kansa, amma a yadda yake ji yanzu, tabbas baya jin zai iya cika shi, yadda zuciya da ruhin sa ke azalzalar sa, da ingiza shi zuwa abinda ba haramun bane, sai dai shi din daya haramtawa kansa, bisa wani dalili nasa da yake ganin hakan shine daidai. Sake mirginawa yayi yana kokawa da zuciyar tashi, kaso saba'in cikin dari na tsarin zuciya da ruhin shi sun aminta da abinda yake ji ɗin, yana ganin ba zai iya kuma bata wasu dakiku ba tare da aiwatar da abinda suka riga suka yanke masa ɗin ba.
"Princesssssss?" Ya kira ni yana sake matsowa.
"Kina jina?" Ya sake maimaitawa yana lalubar hannu na. Runtse ido na nayi ina jin yadda numfashin sa ke sauka bisa saman fuskata.
"Uhum." Nace ina kauda fuskata gefe yadda yage faman zagaye hannun sa a saman fuskar tawa.
"Alhamdulillah."
Ya ambata a chan kasan makoshinsa wanda ba karamin me kunne ne zai jiyo shi din ba.
"I can't hold it anymore." Yace yana kokarin chanja karatun dana sani wanda na riga na gama dauka a wajen sa zuwa wani sabon shafi na daban.
Tuni kwakwalwata ta tsaya tsak, ta daina aiki, komai ya shiga chanjawa, a hankali komai yake tafiya har zuwa sanda abubuwan suka sauyawa baki daya. Shafin rayuwa ta na baya ya sake maimaitawa kansa a karo na biyu a siga ta daban.
****Yar karamar ƙwaƙwalwa ta ta gaza aike min da komai zuwa ilahirin sassan jiki na, baki daya bani da kuzarin aiwatar da komai, na gaza tantance abinda nake ji a halin yanzu, karar kafuwar hakora na kawai ke tashi waje daya, tuni zazzafan zazzaɓi me cike da ma'anoni da yawa yayi min rufdugu, ina jin shi yana magana, da dukkan kalmar da zata zo bakin sa, kokari yake yaga ya fahimtar dani komai, bana fahimta, ba kuma zan fahimta ɗin ba. Kalma daya kawai nake iya tantancewa "hakuri" kalmar da yake ta nanatawa kamar a bakin sa aka halicce ta. Da kyar na bude baki nace
"Zan sha ruwa." Da sauri ya tashi ya kawo min, ya taimaka min nasha, sannan ya gyara min kwanciya ta yana kara nanata kalmar hakuri. Bansan sanda bacci ya dauke ni ba, bacci me dauke da ma'anoni da yawa. A yau na sake taka wani mataki na rayuwa, matakin da ba zan iya sanar daku da yanayin da yazo min ba, abu daya na sani, yana cikin manyan matakan rayuwata dana gaza mantawa.
***Komawa ta makaranta ta ruguje, babu wanda ya tuna da hakan tsakaninmu, zuwa da safe naji dama dama, da taimakon sa na samu na sake komawa bacci a karo na biyu, wanda ban samu farkawa ba sai da rana ta daga sosai. Da fuskar sa na fara tozali, yana zaune a gefe na cikin shigar sabuwar shadda fara kal tana sheki , kansa babu hula kamar ko yaushe, yayi kyau ainun, da sauri na maida ido na na kulle.
"Good morning My Dee." Ya ambata yana min peck a saman kuncina, dariya na saka ina rufe fuska ta da tafin hannu na. Tashi yayi ya fita, hakan ya bani damar saurin fadawa toilet, na sake gyara jikina da ruwa me dumi, kayan jikina na mayar na dora hijabi akai na fito, yana zaune gaban sa da babban tray, wuce wa nayi na dau doguwar rigar atamfa me karamin hannu na sake komawa toilet din na saka na dauro dan karamin mayafi a saman kaina na fito. Breakfast din ya tura min gabana yana ciro wasu jerin magunguna daga cikin leda. Sosai naci abincin ya bani maganin nasha na koma saman gado na kwanta. Shi ya tattare kayan ya fita dasu sannan ya sake dawowa dakin.
Kwana biyu muka yi a haka, komai shi yake mana, sosai nake jin kunyar sa, shi kuwa babu ruwan sa, budirin gaban sa kawai yake, a kwana na ukun ne aka matsa masa da kira, dole ya fara shirin tafiya nima na hau nawa shirin dan ma tuni yayi waya da principal dinmu.
A tare muka fito gaba daya, muka dau hanyar makarantar mu, har muka isa hannun sa na cikin nawa, da kyar ya kyale ni na tafi bayan doguwar sallamar da muka tsaya yi.
Sanda na dawo har sun fara wasu subjects din, haka na yi joining aka cigaba dani, kullum dare da tunanin sa nake kwana, dashi nake tashi, duk da hakan ban bari ya shafi karatu na ba, dan ina so yayi alfahari dani. Munyi waya sau biyu a wayar principal, daga ranar ban sake magana dashi ba. Bayan sati biyu muka fara Waec, tuni kaina ya dau zafi na ajiye komai, sai dai kullum da matsanancin ciwon kai nake kwana, nake tashi, a haka nake daurewa nake karatun. Wata guda muka dauka da yan kwanaki muna jarrabawar, a ranar da mukayi ta karshe ne jikina ya kara rikicewa, ban iya fitowa daga examz hall ba, sai da wasu seniors suka taimaka min zuwa clinic din makaranta. Tashin farko ta sani zuwa nayi fitsari na kawo a yar wata container, haka nayi fitsarin na kawo, ta rubuta min wasu magunguna tace su rakani hostel, gobe kafin mu tafi gida sai nazo na karbi result. Haka na koma hostel na kwanta, ban iya aiwatar da komai ba, sosai nake jin jiki, a daddafe nayi bacci har gari ya waye, wata roommate dina ce ta taimaka wajen karasa hade min kayana waje daya.
A nutse nake tafiya har na isa clinic din, Ina zuwa na samu waje na zauna dan bata ƙaraso ba. Can ina zaune tazo, tana gani na ta sakar min fuska
"Shigo ciki ko."
Ciki na shiga ta ban kujera na zauna, envelope ta ciro ta mika min
"Test ɗin da akayi miki baya wani daukar lokaci, ina so dama nayi magana da principal ne shiyasa nace ki dawo yau, toh munyi magana ma kuma dai babu wata matsala tunda dama ashe kina da aure ko?"
Daga mata kai nayi ina juya takardar hannu na.
"Ok Masha Allah, Kinga sai kiyi rainon cikin ki a gida cikin kwanciyar hankali.'
Kaina ne naji yayi wani gingirin, na bita da kallo kamar wadda bata jin Yaren da take min.
"Yes! You are pregnant." Ta fada tana murmushi, wani yar naji tun daga kaina har tsakiyar kafata. Ni kuma? Ciki? Ikon Allah. Tashi nayi na mata godiya na dau magungunan data bani na fito. Sai na rasa ina zanyi, nayi ta zagaye saman barander daga farko zuwa karshen ta, ina kallo ana yayewa daya bayan daya, har ya zama na kowannne dalibi ya tafi, saura ni kadai. Tun ban fara damuwa ba, har abin ya fara damuna, ina tunanin abinda ya tsaida Ya Farouk, bayan yasan yau ne ranar, ranar dani dashi muke jira, ranar da yayi min alkawari da dama akan ta. Waje na samu daf da kayana na zauna ina kallon kofar. A hankali aka zuge gate din, wata bakar mota ta shigo, baka ganin komai na cikin ta saboda glass din ta me duhu ne. Tsayawa naga anyi daf da security man din dake tsaye daura da gate din. A hankali glass din motar ya shiga sauka, hannu ne ya fito, rike da wata farar takarda, hannun na mace ne, dauke da jerin awarwaraye masu matukar kyau da sheki. Takardar da mika wa security man din tare da sanar dashi wani abu. Ina kallo ta maida glass din motar ta rufe, ta juya ta fita daga cikin makarantar da mugun gudu. Ganin security man din ya nufo ni yasa na tashi ina sake riƙe takardar result d'ina, yana zuwa ya mika min takardar cikin harshen turanci yace
"Sakon ki ne inji Farouk."
Karba nayi hannu na na rawa, na bude ido na ya sauka akan abinda ke rubuce baro baro cikin manyan harafi. A take naji kaina na juya min, na fara ganin komai biyu- biyu, dafe kaina nayi da dukkan hannu na na kwalla kara da ta cika makarantar baki daya. Daga nan bansan me kuma ya sake faruwa dani ba.
Rano
ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo
****Daurin Goro*
*13*
© Hafsat Rano
ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo
***
Da kyar na bude idanuna da sukayi min matukar nauyi,na fara bin ko ina da kallo, kwance nake a dakin asibiti, hannu na daure da ruwan drip dake sauka a hankali. Fankar saman dake juyawa kadan kadan na kurawa ido ina son tuno me ya faru dani. Cikin yan dakiku ƙwaƙwalwa ta shiga dawo min da komai, kuka nasa da karfi zuciya ta na matukar suya. Me yasa zai min haka? Me nayi masa? Abinda na shiga tambayar kaina kenan ina kuka sosai. Shigowar principal ne da wata mata yasa na rage kukan da nake, har gaban gadon ta ƙaraso tana min kallo me cike da tausaya wa
"Sannu Amina, kiyi hakuri kinji? Duk tsanani yana tare da sauki."
Ban iya motsawa ba, sai hawayen da suka cigaba da sauka a saman fuskata kamar masu gasar tsere, a yau na sake tabbatarwa da sabon shafin rayuwa ta ne ya sake budewa, shafin da ban shirya masa ba, ban taba tunanin zan riskeni a irin wannan lokacin ba. Juyawa nayi ina runtse ido na ganin duk yadda na juya abinda ke rubuce a takardar nan nake gani,
_"Ni Farouk Kabir Shagari, na saki matata Aminatu, babu sauran wata alaƙa a tsakanin mu, sannana babu wani abu daya shiga tsakani na da ita. Idan ta samu wani mijin, tayi aure."_
Tabbas rubutun sa ne, tun yana koya mana karatu na haddace zubin rubutunsa, kawo yanzu da ya zama duk wasu muhimman takardu na rubutun nasa ne akai. Hannu biyu nasa na rike kaina gam dake barazanar rabewa biyu saboda tsananin ciwo, tun ina yin kuka da hawaye har ya koma sai na zuciya kawai nakeyi. Duk maganganun da principal suke na gaza daukar daya a ciki, ina ji suka juya suka fita. Jim kadan wata nurse ta shigo dauke da ruwan allura, da kallo na bita kawai dan bani da wani karfin hana ta, duk kuwa da tsananin tsoron da nake wa allura yau sai ya zama na nafi tsoron kaina da rayuwar da zanyi akan komai. Ina jin ta tayi min, ban ko motsa ba, cikin kankanin lokaci bacci ya dauke ne da karfin gaske. Wanda nake da tabbacin yana da alaka da allurar da tayi min, dan bana jin akwai wani abu da zai iya sani runtsawa a halin da nake ciki.
Ban farka ba sai da safe, na tashi da tunanin abinda ya faru, kukan na cigaba kamar jiya, dan ina ganin shine kawai zai rage min radadin abinda nake ji. Da taimakon matar jiya na samu nayi sallah, ina sallah ina kuka wiwi, zama tayi a gefe tana jiran na idar, da kyar na samu na kawo sallolin da ake bina,dan tuni jikina ya fara rawa, zuciya ta ta riga tashi, da gudu na fada dan karamin toilet din dake manne a dakin na shiga kwarara amai, babu komai a ciki sai ruwa, a galabaice na gama na fito bayan ta taimakin da ruwa. Kwanciya nayi jikina ya dau rawar sanyi, wani mugun zazzaɓi da ban taba jin irin sa ba ya dirar min a lokaci daya.
***
Tsaye take a gaban desk din ta, wayar tace a hannun ta tana faman juyata,
"Ya zamuyi da yarinyar nan ne? Sam wayar mijin nata bata shiga wallahi, tun jiya nake gwadawa, gashi babu wata hanya da zamu nemi iyayenta."
Tayi maganar tana sake dialing number tasa a karo na ba adadi.
"Akwai tashin hankali, ga saki gata dauke da juna biyu, maza basa kyautawa sam wallahi, wannan wane irin rashin adalci ne."
"Hmm abun dai kam sai dai Allah ya kyauta, ina ganin jira zamuyi kawai ta ɗan ji karfin jikin ta, idan yaso sai a sata a motar makaranta a kaita gida, nasan tabbas zata san gidan iyayenta ai, in ba hakan ba bansan yadda zamuyi ba, kuma kinga ai ba zamu cigaba da rike yarinya a wajen mu ba."
"Gaskiya dai, hakan kawai shine mafita."
Shiru sukayi kowa da tunanin abinda ya ke, takardun biyu principal ta nannade ta hadusu waje daya, ta kwashi abubuwan da zata bukata suka fito.
***
Ƙarar motar data tsaya a kofar gidan yasa yaran lekowa, ganin motar yasa suka hau tsallen murnar ga Aminatu, ga Aminatu, sanin su cewa ita kadai ɗin ake kawowa a mota, dan karamin yaron Yalwati ne yayi jikin motar da sauri, bude motar akayi, duk suka zuba ido suna kallo, a gadarance ta fito, ta tsaya tana karewa gidan kallo, yatsine fuska tayi ta shiga takawa a hankali har cikin gidan. Yalwati na gaban murhu tana gyara wuta, ruwan wankan jego ne akai da za'a yi wa Karime, ta dago da sauri jin takun tafiya haɗe da wani irin kamshin turare daya riga ya game dukkan lungu da sako na gida.
"Maraba." Tace tana goge hancin ta da yayi shabe shabe da majina, kallon tsaf matar tayi mata batare data amsa ba.
"Kece mahaifiyar Aminatu?" Tayi tambayar tana matsowa ciki. Sai a lokacin Inno ta fito, rik'e da kofin kunun kanwar da ta gama matsawa Karimen tasha.
"Lafiya?" Inno tace tana kallon Yalwati da matar.
"Wajen ki tazo wai." Ta amsa tana nufar dakin ta, tabarma ta dauko da sauri ta shimfida a yar inuwar wajen tana nuna mata
"Bismillah ga waje." Kallon banza matar tayi mata sannan ta kalli Inno ta nuna ta da hannu
"Kece mahaifiyar Aminatu kenan?"
"Nice, me ya faru?"
"Dama zuwa nayi na sanar muku, kuje ku dau yarku a makaranta dan yanzu babu wata alaƙa tsakaninta da d'anmu, asirin da akayi masa ya warware sai abi wani sarkin, saki ne ya riga ya sake ta, dawainiyar da yayi da itaa ya isa haka."
Da sauri Inno ta matsa jikin bangon dakin ta, ta kasa cewa komai, kallo kawai ta shiga bin matar dashi har ta zaro takardar dake ninke a yar karamar jakar hannun ta ta yar a tsakar gidan, ta juya cikin takun ta na kasaita bayan ta tofar da yawu ta fice daga gidan.
Da sauri Yalwati ta dauke takardar tayi wajen Inno tana mata magana ganin kamar bata hayyacin ta.
"Lafiya Yaya? Ko jikin ne?" Ta fada cikin kulawa.
Da kyar ta bude baki tace
"Innalillah wa inna ilaihi raji'un.. Na shiga uku na lalace."
Da sauri ta sa hannu ta karbi takardar, sannan ta juya ciki, Karime na zaune tana hawaye, bayan ta gama jin abinda ya samu Aminatu
"Inno..." Tayi maganar tana kallon ta
"Bari naje Karime, idan ruwan yayi Yalwati zata yi miki."
Daga kai kawai tayi, tana share hawayen tausayin yar uwarta. Mayafinta ta dauka, ta dauka yan kudaden ta tayo waje, yara tasa suka kira mata Nura, suka nufi in da zasu samu mota. Har suka isa makarantar bata bar sake-sake ba, wani irin tausayin ta take ji, tabbas tasan ita ce Ummul abaisin halin da Aminatun ke shiga, sai dai tayi nadama, duk da nadamar bata da amfani, amma tabbas tayi dana sanin abinda ta aikata, gashi Baba tun lokacin daya ji komai ya kwanta ciwo, saboda tsabar kaduwar da yayi take barin jikin sa ya shanye, ko a iya haka Allah ya barta ta gane kuskurenta, ballantana tasan akwai wasu sakamakon masu zuwa nan gaba.
***
Ina kwance kamar wadda aka zare wa dukka kashin jikin ta, cikina ke ta ya mutsawa kamar kayan cikin shi zasu fito, a wahalce nake fitar da numfashi ina murkususu. Budo kofar akayi na zuba musu ido, principal ce a gaba sai Inno da Nura, ganin su yasa na saki kukan da nake ta kokarin tsaida shi, da sauri suka ƙaraso wajena Inno tayi kokarin sani jikin ta.
"Sannu kinji." Principal tayi maganar tana ajiye takardun a gefe na. Da sauri na runtse ido na ina jin kamar ta ajiye garwashi tunawa danayi da abinda ke ciki. Ina ji ta hau yi musu bayanin komai,
"Naji dadin zuwan naku, dama muna ta tunanin yadda za'a yi, tun da kunzo sai asa hannu ku tafi da ita, Allah ya kara lafiya."
"An gode Allah ya saka da Alkhairi."
"Amin, dan Allah a kula da ita sosai, akwai karamin ciki a jikin ta, damuwa zata iya haifar mata da matsala, duk tsanani yana tare da sauki, komai zai zamo tarihi in Sha Allah."
Da kallo Inno ta bita, ta kasa magana sai daga kanta kawai da take a hankali, har principal din ta juya ta fita.
"Ni Nura a takardar nan ba yace babu abinda ya shiga tsakanin su bane?" Tayi tambayar tana kallon sa
"Tabbas haka yake a rubuce."
"Allah ya kyauta." Kawai tace tana kokarin tashi
"Ki daina kuka kin daiji me firincifal ɗin tace ko?"
Shiru nayi suka tattare komai da magunguna na Nura yasa hannu muka dau hanya.
***Tun da muka soma tafiyaa na jingina da kujerar motar, na lumshe ido na kamar mai bacci, babu wanda yayi min magana a cikin su har muka isa kauyen namu, sanda muka iso daidai gidan Bature, na bude ido na, jikina ya hau rawa na kura wa babban gate din gidan ina ganin kamar zai bude, gani nake kamar zai fito, kamar zan ganshi tsaye yana daga min hannu, sai dai kash, har muka wuce babu motsin kowa, babu alamun ma akwai mutane a ciki. Muna isa gida Inno ta gyara min hijabi na ta riko ni, ta taimaka min na fito, hannun ta cikin nawa muka shiga gidan, da sauri Yalwati ta taso, tana mana sannu da zuwa. Amsawa Inno tayi ta bude min dakin ta.
"Jeki kwanta." Kawai tace ta rataye mayafin ta saman igiya ta nufi dakin Baba. Ina shiga na tarar da Karime da jaririnta, ta sauri ta taso ta rungume ni,sai a sannan naji wani sabon kuka ya taso min, kukan muka saka baki daya a tare, babu me yunkurin rarrashin wani, sai da mukayi me isarmu, sannan muka samu waje muka zauna, sai a lokacin Inno ta shigo, kallon mu tayi kadan ta wuce wajen daukar abu,har zata fita sai kuma ta tsaya tana duba na
"Taso ki watsa ruwa kafin magriba tayi, ke Karime miki min yaron nan a goya shi magriba ta gabato."
"Toh." Muka amsa a tare, ta karbi jaririn ta fita, cikin rashin kwarin jiki na mike, na rage kayan jiki na, na fito tsakar gidan, ruwa me dumi na tarar a bandakin na watsa na fito. Kayan Karime na saka na sake kwanciya a saman gadon Inno, har aka kira sallah sannan na tashi nayi na sake kwanciya, gaba daya bani da karfin jiki dana ruhi, komai baya min dad'i. A gefe na Karime ta zauna tana jijjigen yaron, kallon ta kawai nake ina hasaso hakan akai na.
"Ya sunan shi?" Na tambaye ta ina mika mata hannu ta bani shi
"Abubakar aka sa masa, amma saddiku za'a dinga ce masa."
Shafa kansa nayi wasu hawaye suka zubo min, nima haka zan haifi abin ciki na, na raine shi ni kadai ba tare da uba ba, bansan wanne irin rayuwa kuma zan sake yi nan gaba ba, hannu na dora a saman shafaffen ciki na bayan na mika mata shi don ta bashi nono. Na shiga tunanin kalar rayuwar da zanyi. Abinci Inno ta kawo mana, na d'an ci kadan dan har lokacin cikina babu dadi, na haye gadon na kwanta ina fatan bacci ya dauke ni
***Cikin dare na kaasa bacci juyi kawai nake, na rasa abinda yake min dadi, har aka kira sallah na mike da kyar na je nayi alwala,. Bayan na idar na zauna saman abin sallar ina fadawa Allah damuwa ta, nasan shine kadai zai kawo min sauki a dukkan al'amari ne. Sai da gari yayi haske sosai sannan na kwanta, bacci ya dauke ni a take. Ina cikin baccin ne naji hayaniya sosai kamar a tsakar gidan mu, da sauri na mike zaune, Karime na gani a zaune gefe na tayi wanka tana cin dumanen tuwo.
"Sannu da tashi, ya karfin jikin?." Tace tana min murmushi
"Da sauki, ya kwanan Saddik?"
"Alhamdulillah."
"Su waye nake jin hayaniya a waje?" Na tambaye ta ina sake kasa kunne na sosai, tabe baki tayi kafin tace
"Dan iskan Garbatin nan ne yazo zai wa mutane hauka, amma Inno tayi maganin su ma ai, bashi da hankali wallahi sam."
Gabana ne ya fadi nayi saurin lek'awa, lokacin suke fita daga gidan, hannu naga Inno tasa ta goge fuskar ta, ganin ta nufo dakin yasa nayi saurin komawa na zauna. Shigowa tayi tana maganganu kasa kasa, chan sai ga Nura yayi sallama a dakin.
"Wai kina kirana ko?" Yace yana zama kasa.
"Waye yayi maganar juna biyun da take dauke dashi? Kasan dai ni dakai kawai muka san maganar."
Zaro ido yayi cikin rashin gaskiya
"Wallahi dazu ne da asubah muke maganar dawowar Aminatun da su Iro(sauran samarin gidan) shine nake basu labarin abinda ma ya faru."
"Toh gashi nan zance ya fita gari, har mutane sun zo neman ba'a si."
Dafe kirjin sa yayi da sauri
"Toh waya fitar da maganar kenan?" Ya tambaya yana zaro ido
"Kaine, da baka fada ba ya za'ayi har a yada, tashi kaje ni kana abu kamar ba namiji ba."
Sum sum ya tashi ya fita, Inno tayi tsaki ita ma ta bar dakin. Kallo na Karime tayi cikin son karin bayani
"Me ya faru Aminatu? Bayan sakin akwai wani abu ne?"
Share hawayen fuska ta nayi na zauna sosai zuciya ta na min daci, a hankali na ce
"Bansan wacce kaddara ce ke tunkaro ni ba Karime, a lokacin da na gama tabbatar wa kaina da tsananin soyayya da nake ma Ya Farouk, a lokacin ya datse igiyar alakar dake tsakani na dashi, ya ruguza dukkan tanadin da mukayi wa juna. Kinsan bayan sakin har cewa yayi babu wani abu daya shiga tsakani na dashi? Bayan a daidai lokacin gwaji ya tabbatar min da ina dauke da ciki har na sati bakwai, Karime ya zanyi da rayuwata da abinda yake ciki na, bayan wanda zai tsaya min ya tabbatar da cewa babu abu tsakanin mu, ina kenan na samo cikin jikina? Wa zai karbe ni dashi?"
Kuka yaci karfin mu dukka, tasowa tayi ta zauna daf dani tana sharen hawayen fuskata
"Kiyi hakuri, tabbas ba'a kyauta miki ba, kuma an zalunce ki, amma bak'ya tunanin akwai sa hannu wani a cikin wannan al'amarin? Kina ganin Farouk zai miki haka kuwa?"
Girgiza kai na nayi cikin kuka nace
"Idan ma sharri akayi masa, yana ina yanzu? Me yasa be zo ya wanke kansa ba? Bayan haka rubutun dake jikin takardar nashi ne, rubutun sa ne Karime, ya kike tunanin bazan yarda ba?"
"Duk da haka, ya kamata ayi bincike sosai."
"Babu wani bincike da za'ayi, aikin gama ya riga ya gama, abu daya na kasa ganewa, laifin me nayi masa da har zai min wannan hukuncin? Menene matsalata?"
Share hawaye nayi na mike ina komawa jikin tagar dakin,
"Amma ba komai, na gode masa sosai da dukkan sadaukarwar sa gareni, hakika ba zan taba mantawa dashi a cikin jerin mutane masu matukar muhimmanci a rayuwata ba, ina jin kamar nunfashi na zai bar gangar jiki na Karime, zuciya ta tana min zafi."
"Kiyi hakuri, karki tsananan ta damuwa ko dan abinda ki cikin ki."
Sosai Karime ta shiga rarrashi na da ban baki, haka dai nake bin ta da ido kamar mutum mutumi, bata hakura ba har sai da saddiku yayi kuka sannan ta kyale ni. Wanka na fara yi na sha kunu wanda shi kadai ne zai iya zama a ciki na a halin yanzu. Wajen azahar sakon kiran maigari ya riske mu. Sai da akayi la'asar sannan Inno tasani a gaba tare da k'anin Baba muka tafi, duk inda muka wuce sai munga ana kallon mu ana magana kasa kasa. Haka muka isa wajen, daga gefe muka zauna muka gaida maigari sannan ya soma magana cikin dattaku."
"Jiya wasu mata sunzo har nan sun same mu, sun gabatar da takardar sakin Aminatu daga wajen mijinta Farouk, bayan nan suka dora da bayanin su kafin sukayi sallama suka tafi. Toh bayan tafiyar su, nasa an karanta min abinda takardar ta kunsa, daga nan na yanke shawarar kiran mahaifin yaron, dan jin abinda yake faruwa, tunda ance ta inda aka hau ta nan ake sauka. Toh bayan kiran shi ne yake nuna min shi sam be san da maganar ba, hasalima shi rabon shi da yaron an kwana biyu, sai dai ya bani hakuri da alƙawarin zai samu lokaci ya shigo. Toh kuma yau sai ga maganar juna biyu ta riskeni, sai na sake komawa baya abinda yake rubuce a takardar nan da suka kawo, in da yaron ya nuna babu wata alaƙa data shiga tsakanin su, shine abin ya daure min kai, na bukaci naji daga gareku, kafin zuwa Mahaifin yaron ko yaron, mu san abinda ake ciki."
Runtse ido na nayi ina karanto duk addu'ar datazo baki na, idan har Farouk be zo ba, be kuma ƙaryata abinda ya rubuta ba, ana nufin za'a sheganta min abinda ke cikina kenan? Wannan wacce irin masifa ce ta kunno min?
"Aminatu..." Maigari ya kira sunana, ban iya amsawa ba sai dagowa da nayi kawai ina goge fuskata.
"Abinda mijinki ya rubuta shin gaskiya ne ko ba gaskiya ba?"
A hankali na bude baki na cikin tsananin kukan da ya soma cin karfi na nace
"Ba... gaskiya bane."
Gid'a kansa yayi cikin gamsuwa yace
"Shikenan, in Sha Allahu komai zai warware kinji, kiyi hakuri."
Da kai na amss kawai, ya karasa bayanin sa sannan ya sallame mu.
***
Ransa a matukar bace yake kutsa kansa falon, tana zaune hannun ta rike da babban tasbah tana ja, tana ganin shi ta fadada fara'a ta
"Soja mazan fama."
Yake yayi kawai ya ƙaraso ya samu waje ya zauna
"Dadah, me yaron nan yake so ya zama?"
Ya ambata yana jan karamin tsaki
"Wanne yaro hala? Ja'afaru ko wa?"
"Farouk!"
"Toh me kuma Babana yayi ehe?"
Cire hular kansa yayi ya ajiye yana goge gumin kansa
"Wallahi wai ya saki yarinyar nan."
Da sauri ta dafe kirjin ta
"Innalillah wa inna ilaihi raji'un! Saki!!! Yaushe?"
Tsakin ya kara ja yana duban kofa
"Dazu maigari ya kirani wallahi, kuma abin takaice wai aikawa yayi da takardar,ba shine da kansa yaje ba, gashi duk numbobin sa na kira a kashe balle nasan ta ina zan fara, ni rabona ma dashi tun zuwan da yayi karshe yace an tura shi wani aiki."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, yau me zanji, wanne irin abu ne wannan? A lafiyar sa kuwa? Kai da sake gaskiya, bana jin Babana zai aikata makamancin wannan."
"Dadah dan yau fa, halin su sai su."
"Duk da haka Kabiru, sam ban yarda Farouk zai aikata ba, aikuwa ba dan dare yayi ba a yau zan bar garin nan, amma tabbas gobe da izinin Allah ina chan, hankali na ba zai kwanta ba sai na ji komai, ka cigaba da kiran wayar tasa ko zaka samu kaima."
"Allah ya kaimu, nima zuwan ya kamani, ina ganin ki fara zuwa sai na biyo ki jibi, dan akwai ayyukan da zan karasa goben, amma idan na koma zan shiga gidan Aboki, zan sanar masa abinda yake faruwa, shine me yabon faruk yanzu sai yasan abinda ya sake aikata bayan na dah, idan yaso sai mu tafi taren musha kunyar a tare, dan bazan iya kallon mutanen nan ba wallahi, da kunya ana ganin mutuncin ka."
"Duk yadda kayi yayi, amma ni kam gobe zan isa da izinin Aallah."
"Allah ya kaimu, sai ku tafi Ja'afar da driver ko?."
"Amin, yayi hakan." Ta amsa har lokacin bata bar mamaki ba, ina alkawarin da yayi mata na cewa duk ranar da Aminatun ta gama karatu zai dawo da ita wajenta, su zauna tare har zuwa lokacin da shima zai nemi transfer ya dawo nan ɗin, me ya faru da babban alkawarin da yayi na taimaka mata wajen hada ta da dangin ta? Kai akwai lauje cikin nad'i, tabbas wannan makirci ne aka shirya, sai dai kai tsaye Mum ce ta fado mata arai, tasan zata iya aikata fiye da hakan ba, amma dai koma menene, zata je taji.
***
Alhamdulillah, nagode kwarai da addu'oin ku 🙏💯 Allah saka da Alkhairi.
0 comments:
Post a Comment