"Tunanin dai ko Aminatu, kifa saukaka ma ranki kar ki jawo wani ciwon kuma."
Yake nayi wanda aka ce yafi kuka ciwo na zauna sosai ina kwantar da Saddiku, zaman tayi itama ta hau shiryawa bata sake min magana ba, tashi nayi na fito, nayi fitsari na dan leka dakin Baba, yana kwance idanun sa a bude, na k'arasa na tsuguna gaban sa
"Sannu Baba." Nace ina maida kwallar ido na, bina yake tayi da ido babu halin magana, shiru nayi ina tunanin yadda mutum zaiyi rayuwa a haka, tabbas ba karamin jin jiki yake ba, gashi babu wanda zai taimaka masa da zuwa asibiti, Farouk ne ya fado min, na tuna da yananan yanzu, xan iya neman alfarmar sa ya taimaka masa. Na jima a dakin ina zaune dashi har saida Inno ta kwala min kira, da sauri na tashi na fito, sai nayi turus ganin Dadah na kokarin shiga dakin Inno, gani na yasa ta dakata, ganin haka yasa nayi saurin isa gareta, bansan sanda na fada jikinta ba, na saka kuka sosai. Rike ni tayi muka karasa shiga dakin har lokacin kukan nake, gaishe ta Karime tayi ta tashi ta fita don bamu waje. Tabarma Babba na dauko na shinfida mata, na fita da sauri na debo mata ruwa na ajiye a gaban ta sannan na zauna ina sauke kaina kasa.
"Aminatu, sannu kinji."
Hakan data fada yasa naji zuciya ta ta sake yin rauni, tabbas ni ɗin abar a tausaya min ce,
"Sannu da zuwa Dadah, ina wuni?"
"Lafiya kalou Aminatu, mun same ku lafiya?"
"Alhamdulillah."
Nace ina wasa da hannu na. Inno ce tayi sallama ta shigo Yalwati na bin bayanta, a mutunce suka gaisa kafin su tashi su fita. Muskutawa tayi kadan tana dubana sosai.
"Aminatu me yake faruwa? Me ya hada ki da Babana."
Ta jeho min tambayar ta na riga nasan da ita, kallon ta nayi zan cigaba da kukan da nake ta dakatar dani,
"Kul kina kuka, akan me? Fada min gaskiya me ya faru, kunyi fada ne ko kin masa wani laifin ne?"
"Allah banyi masa komai ba, hasalima rabona dashi tun ranar daya maida ni makaranta, yace sai ranar da muka gama exams zai zo, toh kuma ni tun bayan nan sau biyu mukayi waya, daga nan bamu sake magana ba."
"Zaki iya dauko min takardar da aka kawo miki?"
"Eh."
"Toh bani na gani."
Tashi nayi na bude jakar da nazo da ita na dauko, na fito da takardun guda biyu, kura musu ido nayi a tare, sai kuma na juya na mika mata su dukka ina jin wani iri, karba tayi ta bude ta farko me dauke da sakamakon test result dina, a fuskar ta naga yanayin da take ciki, sosai naga ta sake sakin fuskar fiye da yadda take a baya, ninkewa tayi ta ajiye ta bude dayar, ta jima tana dubawa kamar ne son gano wani abu kafin ta ajiye tana sauke ajiyar zuciya.
"Waye ya kawo miki wannan?" Ta nuna takardar sakin
"Bansan waye ba nima, nasan dai wata mota ce ta shigo makarantar mu, ina kallo ta bawa security man din dake wajen shi kuma ya kawo min, sai dai tabbas mace ce dan naga hannun ta."
"Baki ga fuskar ta ba kenan?"
Girgiza kai na nayi
"Ban gani ba, amma ance tazo gida ma bayan ta je makarantar."
"Nan gidan?" Ta tambaya da sauri.
"Eh ance tazo, kuma maigari ma yace sunje chan wajen sa sun kai masa."
"Good, kira min Maman taku."
Tashi nayi tsam naje na kira Inno, a tare muka shigo na samu gefe na zauna.
"Ko zaki iya gane matar data zo dan Allah?" Tayi maganar tana kallon Inno
"Zan gane ta."
"Yawwa."
Ciro wayar ta tayi ta budo wajen hotuna ta fara nuna wa Inno, duk wadda ta nuna mata sai tace ba ita bace. Ajiye wayar tayi tana murmushi
"Aminatu samu yaro yaje waje ya kira min Ja'afar, suna nan a mota."
Tashi nayi na fito, babu yaro ko daya duk Inno ta kora su waje, hijabin jikin Karime na karba na leka da kaina na kirawo shi. Gabana ne ya fadi da ya fito, sosai yayi min kama da Farouk, sai dai shekaru da Farouk zai fishi da girman jiki.
"Sannu, Dadah ke kiran ka."
"Owk." Yace yana biyo bayana, tsayawa yayi a tsakar gidan na shiga na fada mata gashi, Inno ce ta daga labule tace ya shigo, a gefen tabarmar da Dada ke kai ya zauna yana gaida Inno din, amsawa tayi kafin Dadah tace
"Kana da hoton Abidah a wayar ka ko?"
"Ina dashi."
"Yawwa mu gani."
Budowa yayi ya mika mata, ta kalla ta mika wa inno,
"Wannan fa?"
Girgiza kai Inno tayi tace
"Gaskiya ba ita bace."
"Owk shikenan Ja'afar, zaka iya tafiya."
Tashi yayi ya fita, Dadah ta cigaba da nuna wa Inno dukkan hotunan data ke tunani, amma sam Inno bata ga matar ba, a dole Dadah ta hakura da tunani shin wacece? Ganin ta kasa gane wacece yasa ta yi mana sallama bayan ta sa yara sun shigo da kayan data kawo min ta tafi, da nufin zata dawo gobe idan Allah ya kaimu. Har waje na rakata ina jin kamar na bita, sai dai nasan hakan ba mai yiwu wa bane.
***
Sosai Dadah ta shiga damuwa, babu abinda yafi daga mata hankali sama da abubuwan da takardun nan guda biyu suka kunsa, abubuwa biyu dake da alaƙa da juna da siga daban, idan har ya tabbata Farouk shine yayi sakin ya kenan za'a yi? Bin Ja'afar tayi da ido har ya karasa shigowa cikin falon.
"Wash." Yace yana fadawa saman kujerar.
"Daga ina kake haka kai kuma?"
"Wallahi Dadah zagaye nayi a gonar nan, sai naga girman ta ya karu sosai fiye da dah, ko dan na jima banzo bane ba oho."
"Sai dai hakan, amma ai yadda take haka take, kawai son jikine irin naka."
"Yawwa kai, nace yaushe rabon ka da Babana ne wai?"
"Wai ya Farouk?"
"Bansani ba."
"Sorry, a satin nan ma munyi magana ai."
"Da gaske ko da wasa?"
"Wallahi, kinsan baya kasar sannan inda yake babu wani network me kyau, nima Amal ce ta bani number tasa lokacin da Mummy ta kirani akan bata samun shi a waya, shine na kirashi, wajen kwana huɗu ma ina gwada kiran kafin ta shiga."
"Ina number, maza bani ita."
"Owk bari na dauko wayata a ciki na barta."
Mik'ewa sukayi a tare ya nufi dakin sa, a tsaye Dadah take har ya dauko ya dawo, hannun ta rike da wayar ta. Number ya karanto mata ta saka sannan tayi dialing, bugu daya ta shiga, zama tayi da sauri tana saka ta a handfree, sai dai har ta gama ringing din bai daga ba, cigaba tayi da kira, babu alamun za'a daga ɗin, haka ta hakura ta bari anjima ta sake gwadawa.
"Be d'aga ba."
"Kila baya kusa ne, idan ya gani zai kira nasan."
"Ina ita Abidar take, tana Kaduna ne ko Abuja?"
"Wai Mummy, ina ga tana Lagos, yanzu tafi zama a can ai saboda bussiness ɗin nata yafi a chan haka."
"'Owk yayi, ka gwada kira min shi zuwa anjima idan ya dauka ka haɗa ni dashi."
"Ok Tam, bari na shiga na huta."
Barin falon yayi itama ta wuce dakin ta tana samun magana da Farouk din kafin wayewar gari. Tun tana saka ran zai kira har ta hakura ta kwanta, da safe wajen karfe goma Daddy ya iso, dama shi akwai shi da sammako saboda yanayin abubuwan nasa, zuwa sha-daya suka isa gidan Maigari, ciki maigari ya shiga dasu ya tura kiran su Inno. Lokacin ina zaune muna yar hira da Karime sakon kiran yazo, Hjabi na kawai na dora a saman kayan jiki na muna tafi gabana na ta faduwa. Cikin gidan muka shiga, yanayin takalman da na gani a kofar dakin tasa jikina ya ɗan soma rawa, rike ni Inno tayi muka shiga da sallama, duk suka zubo mana ido, a darare na zauna gefen Inno kaina a kasa na gaishe su, sannan suka gaisa da Kawu kanin Baba da Inno. Kamar wanchan karon yanzu ma maigari ne ya sake sabon jawabi, sannan ya bawa Daddy damar jin ta bakin sa. Wayar Dadah ce ta dau burari alamun kira ya shigo, dan dakatawa Daddy yayi ta ciro wayar, da sauri ta furta
"Alhamdulillah."
Ta daga ta saka ta a handfree
"Assalamu alaikum."
Muryar sa ta daki dodan kunne na, wani irin zabura nayi daga zaune, kowa ya zuba wa wayar ido kamar shi din ne a wajen. Daddy ne ya mika hannu ya karbi wayar
"Kana jina?"
"Daddy barka da warhaka, ina kwana?"
"Lafiya, kana jina, ba wani dogon bayani muke bukata ba, ina fatan kana hayyacin ka dai ko?"
"Eh daddy, a hayyacina nake."
"Good, menene hakikanin gaskiyar takardar sakin daka aiko wa matar ka?"
Shiru yayi, kamar baya kan layin, har sai da Daddy yace
"Kaji abinda nace ko?"
"Naji Daddy."
"Toh ina jinka, me ya faru ka sake ta? Wani laifin tayi maka ne ko menene?"
Kai tsaye yace
"Babu laifin komai, kawai zaman mu ne ya kare."
Da sauri na dago, Ina son sake tabbatar wa kaina wannan ba Farouk d'ina bane.
"Haka kawai kenan ka sake ta ba tare da laifin komai ba ko me?"
"Eh haka nan ne, babu laifin da tayi mun."
Share zufa naga Dadah nayi, Inno kuwa kamar bata wajen, kuma baka isa ka gane yanayin da take ciki ba, ni kuwa sai naji kamar yanzu ne komai yake faruwa, jikina har rawa yake, na kasa yarda da abinda kunnuwa na ke jiye min, ina kallo Dadah ta karbi wayar cikin bacin rai tace
"Babana kaine kuwa? Kasan me kake cewa? Kana nufin duk abinda ke jikin takardar kaine ka rubuta shi? Kuma shine gaskiyar abinda yake faruwa?"
Babu ko digon tsoro balle damuwa a cikin muryar sa, kai tsaye yace
"Ni ne da kaina, kuma duk abinda ke rubuce a ciki shine gaskiyar magana, kuyi hakuri idan na bata muku, Allah ya huci zuciyar kowa."
Kafin ta samu damar sake wata magana kiran ya katse, da sauri tayi kokarin sake kira Daddy ya dakatar da ita.
"Karki kirashi Dadah, barshi kawai, ni ya wulakanta ya nunawa duniya ban isa dashi ba, babu komai amma.."
"Kayi hakuri Alhaji, yaran yanzu ne sai addu'a, idan ka biye tasu sai kayi musu mugun baki."
Mai gari ya katse shi, sannan ya maida kallon sa wajen da muke zaune
"Toh kun ji dai daga bakin yaron, duk da dukkannin mu babu wanda zancen nasa yayi wa dadi, amma dole haka zamu hakura, aure ya riga ya kare, dama shi raine dashi, idan kwanan sa ya kare ko ana so ko ba'a so dole a hakura."
"Amma ba wai na katse ka bane, yarinyar nan fa tana dauke da juna biyu, ya kamata a duba lamarin nan."
Kawu yace yana duban maigari da Daddy,
"Juna biyu !" Suka hada baki a tare cikin tsananin mamaki
"Tabbas tana dauke da juna biyu, ni da kaina naga sakamakon gwajin da akayi mata."
A cewar Dadah tana duban Daddy.
"Amma shine yaron nan zai maida mu yan iska? Lallai ma wallahi, dani yake magana."
Yayi maganar a fusace
"Mubi komai a sannu Alhaji, idan yaso sai a sake tuntubar shi yaron kan maganar cikin."
A cewar maigari.
"Babu bukatar hakan dan yaro ya riga ya nuna baro-baro babu wani abu da ya hada shi da ita, dan haka magana ta kare."
Duk muka juyo da sauri, Mummy ce tana tsaye tayi kyau ainun cikin shigar alfarma, kallon juna sukayi ita da Dadah, kafin cikin bacin rai Daddy yace
"Me kike yi anan Abidah?"
A gadarance tace
"Abinda ya kawo ka, shi ya kawo ni,kasan dai ina da hakki akan Farouk ko? Wanchan lokacin na kyale ka da kayi kokarin bata min rayuwar yaro, akayi masa sharrin da kai kanka kasan ba shine ya aikata ba. Shine yanzu za'a sake ruguza min rayuwar sa bayan Allah ya taimake ni ya gane gaskiya, naji komai a wajen Ja'afar tun ranar da abin ya faru, har zuwa zaman da zakuyi anan ɗin, dalilin zuwa na kenan saboda na karba wa d'ana yanci."
"Danki? Ashe dama kina da d'a?"
"Kafi kowa sani ai, bani da lokacin amsa maka wannan tambayar, maganar d'ana nazo, babu kuma uban da ya isa ya tilasta masa aikata abinda beyi niyya ba."
Kasa magana Daddy yayi saboda tsananin kunyar data rufe shi, kasa yayi da kansa kawai yana jin kamar kasa ta tsage ya shige, jawabi ta shiga korawa maigari, a karshe tace Farouk ba zai karbi cikin jikina ba dan ba nashi bane. Tun da ake maganganun nan jikina yake rawa kamar mazari, tuni zuciya ta ta kekashe, hawayen dake faman kai kawo a saman fuskata ya bushe, cikin dakiya na tashi, na isa tsakiyar wajen, hannu na biyu na hada waje daya cikin wani irin yanayi nace
"Ina rokon duk wanda yake wajen nan, da yayi hakuri, da abinda yake faruwa, ni kaina bansan menene matsalar ba, sannan ina neman wa Ya Farouk afwa wajen ku iyayensa, tabbas bashi da laifi ko daya a cikin duk wani abu da ake tuhumar sa, hasalima shi taimako na yayi. Daga rana irin ta yau na bar maganar nan, zan cigaba da rayuwa ta a matsayin wadda bata taba sanin shi ba, zan manta dashi, zan cigaba da rainon abinda ke cikina, har zuwa ranar da zai zo duniya, ina fatan hakan ya faranta wa kowa."
Ina kaiwa nan na juya da sauri, zuciya ta na tafasa na bar dakin, ina ji suna kwala min kira, ban saurara ba, dan bana jin zan iya sauraron duk wani abu da zasu ce min, maganar da akayi da ya Farouk a waya kadai ta isheni, bana bukatar jin sauran wani bayani, a yau na tabbatar da na rasa shi, rashi na har abadah, zan sake sabuwar rayuwa, duk da bazan ce zan manta dashi a rayuwa ta ba, amma tabbas zan ajiye dukkan shafukan rayuwar mu tare a baya, zan bude sabon shafin rayuwar da bani da masaniyar in da zata kaini.
_"Aminatu ina so kiyi karatu, ina so ki zama abar alfahari sanda zaki sadu da sanyin idaniyar ki."_
Wadannan sune maganganun sa a kullum gareni, wanda bani da masaniyar hakikanin abinda suke nufi, sai dai yau nayi wa kaina alkawarin, zan dauke su a matsayin wani tsani na matakin rayuwar da zan shiga anan gaba.
Hanya kawai nake haɗawa da taimakon Allah na isa gida, da sauri Karime ta tare ni, tana kokarin rikeni na raba ta gefen ta, na shiga daki na hada kaina da guiwa ta cikin rashin sanin makomata. A kaina tazo ta tsaya tana min magiyar na sanar da ita abinda yake faruwa, ban iya ce mata kala ba, har ta gaji ta samu gefe na ta zauna tana rafka tagumi.
A tare suka shigo gidan, kai tsaye dakin Inno suka shigo, Dadah ta ƙaraso gareni tana daga ni.
"Aminatu tashi zakiyi mu tafi, mun gama magana da Maman ki, ba zan iya kyale ki ki raini cikin nan ke kadai ba, maza tashi kinji."
Janye jikina nayi a hankali na matsa gefe ina kallon ta
"Kiyi hakuri Dadah, ba zan biki ba, na gode da hallacin da kuka nuna min, sai dai na yanke shawarar nesantar duk wani abu daya danganci Ya Farouk, ina ganin hakan da zanyi shine kawai mafita a garemu, kiyi hakuri."
"Ya zaki ce haka, kina nufin kin karaya, kin hakura kenan? Ni sam ban yarda da Farouk zai aikata ba, akwai dai matsala, ki bini muje in Sha Allah zamu gani bakin zaren."
"Kiyi hakuri dan Allah, ba zan iya binki ba, hakan na iya haifar da matsala gagaruma a cikin ahlinki, sannan Mummy, ba zata taba karba ta ba, zan yi rayuwa ta, zan zauna anan, tare da yan uwa na dan Allah."
"Aminatu..."
K'asa na tsuguna ina kama kafarta
"Kiyi hakuri Dadah, kiyi hakuri."
Kuka ta saka, ba tare da tayi magana ba ta juya da sauri ta bar dakin.
"Ya Allah!" Na furta da karfi ina zama a kasa, kaina kamar zai rabe biyu saboda tsananin ciwo. Matsowa Inno tayi tana kallo na
"Kin tabbata ba zaki bita ba, zaman nan ba zai miki dadi ba, kinga yanzu da dah ba daya bace."
Girgiza kai na nayi,
"Kiyi hakuri, amma bazan bita ba."
"Shikenan, ki daina kuka kar kanki yayi ciwo, tashi ki kwanta a saman gadon, zanje na yi mata bayani yadda zata gane."
Tashi nayi jikina na rawa na hau gadon na kwanta ina lunshe ido na.
ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo ©️ Hafsat Rano
15
****
Duk hidimar da ake a gidan ban mik'e daga kwanciyar da nayi ba, sake juyawa nayi na maida kaina dayan barin, daga daren jiya zuwa yau na riga na gama yanke wa kaina hukuncin da nake ganin shine zaiyi daidai da rayuwata. Tsawon lokaci na dauka Ina kwancen har lokacin da Inno ta shigo dauke da kwano, a kusa da kafata ta ajiye ta.
"Tashi maza, kici abinci sai kuje chan gidan ki dauko abinda zaki dauka."
"Toh." Nace ina tashi, ajiyar zuciya na sauke na jawo kwanon, fara fita nayi na wanke hannu na da bakina na dawo na zauna na shiga cin abincin a hankali, ina gamawa na chanja kayan jikina, na zura hijabi da takalmi na fito. Dakin Baba na shiga na gaida shi na duba jikin shi sannan muka tafi nida Yalwati. Da yake safiya ce bamu hadu da wasu mutane masu yawa ba muka isa gidan, sojoji ne tsaye a gate din, sai Ja'afar dake magana da daya daga cikin su,yana hango mu ya taho yana fad'ad'a fara'ar fuskar sa.
"Sannun ku da zuwa."
Yace yana tsayawa a gabana, sai dana dan ji wani iri dan sosai suke yanayi da Ya Farouk, dakewa nayi muga gaisa, yanayin yadda yake kallo na yasa na dan ji babu dadi, nayi kasa da kaina har muka shiga gidan ban dago ba. Daddy na zaune suna magana da Dadah muka shigo, da sauri ta mike tana riko ni fuskar ta kamar zatayi ne saboda tsananin farin cikin ganin mu
"Aminatu, kin chanja shawara ko?" .
Yadda tayi maganar cikin farin ciki yasa naji kunya, a hankali na zame jikina na tsuguna a kasa na furta
"Ina kwana Dadah?"
"Lafiya lou Aminatu, nasan dama zaki chanja shawara, Nagode sosai da kika yarda zaki bini." Sai ta maida hankalin ta kan Yalwati cikin fara'a tace
"Sannun ku da zuwa."
"Yawwa ina kwana Hajiya."
"Lafiya lou, ku zauna mana."
Zama tayi a kujerar dake hanya ni kuma na sake gyara zamana a kasan da nake.Sabuwar gaisuwa suka sake sannan suka gaisa da Daddy da ya gama waya. A hankali na dago kaina na cikin girmamawa na gaishe shi, a sake ya amsa yana nazarina. Komawa Dadah tayi ta zauna sannan tace
"Aminatu, zo matso kinji'
Jan jiki nayi na matsa gaban ta, cikin rashin sanin yadda zata dauke abin nace
"Dadah zan dau kayana ne, da abubuwan makaranta."
"Ba zaki bini ba kenan?" Tayi tambayar tana bata rai
Zanyi magana Daddy ya katse ni
"Kiyi hakuri Dadah, tabbas tana da babban uzurin ta na kin amincewa ɗin, Aminatu, kiyi hakuri kinji, kowacce rayuwa cike take da kalubale, idan kayi hakuri sai kaga kaci riba, tabbas nasan ba'a kyauta miki ba, amma bani da yadda zanyi, kiyi hakuri kinji."
Ban iya magana ba sai daga kai kawai da nake kamar kadangaruwa, nasiha ya shiga yi min sosai, sannan ya bani tabbacin duk yadda zaiyi zai nemi Farouk, yaji komai sannan magana ciki sun karba, sun tabbata bazan taba yin wani abu da zai bata sunana ba. Ɗorawa tayi
"Zanyi kokarin ganin na kula da komai naki har zuwa lokacin da zaki sauka lafiya, mun riga munyi maganar jiya. Yanzu ki cire duk wata damuwa a ranki, ki fawwala Allah komai."
"In Sha Allah, Nagode Allah ya kara girma."
Wayar sa ce tayi kara, ya mike ya bar falon, hawaye naji ya zubo min, nayi saurin maida su ina bawa kaina k'warin guiwar bazan yi kuka ba, musanman a gaban Dadah. Bata ce min kala ba, sai kawai ta maida hankalin ta wajen Yalwati tana mata yan tambayoyi. Mik'ewa nayi tsam, suka bini da ido,a hankali na nufin dakin, cikin tarardadin abinda zan tarar ɗin. Turawa nayi, kamshin turaren sa ya daki kofofin hanci na, babu abu daya na dakin daya chanja, yananan tun ranar da muka bar shi, ba tare da sanin cewa na barshi har abadah ba. Kaina ne ya hau juyawa, nayi saurin dafe wa, na shiga har haɗa duk abubuwan dana san nawa ne, cikin dan kankanin lokaci na hada komai waje daya. Kallon wardrobe d'insa nayi, zuciya ta ta kasa hakuri, hannu nasa na bud'e, babban album din sa ya fado, tsugunawa nayi na dauka a hankali na shiga budewa, daya bayan daya nake bin hotunan da kallo, kwalla na taruwa a ido na. Jin takun tafiya yasa nayi saurin tashi, na ciri guda daya na tura cikin jakata na maida sauran tare da rufe wardrobe din. Juyowa nayi da nufin tafiya muka hada ido, tana tsaye ta zuba min ido tana murmushi, murmushi me dauke da ma'anoni da yawa Dauke kaina nayi na tattare kayana zan bar dakin, ta gefen ta nazo wucewa a hankali nace
"Ina kwana?"
Bata amsa ba, dama nasan ba zata amsa din ba, sai dai har lokacin idon ta na kaina, kallon da na rasa na menene, rab'ewa nayi na wuce kawai ba tare da na sake cewa komai ba. Ina zuwa falon na tarar da Dadah, tana zaune tana juya wayar hannun ta, kasa na tsuguna cikin dakiya nace
"Na gama zan tafi Dadah." Girgiza kai naga tayi, ta miko min har karamar jakar hannu. Ajiye kayan hannu na nayi na karba ina kallon ta
"Karbi ki ajiye wajen ki, in Sha Allah zan dinga zuwa ina duba ki lokaci zuwa lokaci, ki kula da kanki kinji? Allah yana tare dake."
"Nagode sosai Dadah, bansan da wanne bakin zan gode miki ba, Ubangiji ya sake miki da mafificin Alkhairi."
Da sauri ta tashi, ta shige dakin ta ba tare da tace komai ba, jiki na a matukar sanyaye na mike, ina karewa ko ina kallo, Yalwati ta tayani daukar kayan, muka fito. Da sauri ya tare mu, ya karbi kayan hannu na har lokacin idanun sa na kaina.
"Daddy yace na mika ku saboda mutane."
Ba musu muka bi bayan sa, ya saka kayan a booth muka tafi. Har kofar gida ya kaimu, sannan ya tayamu sauke kayan yara suka dauka muka shige ciki.
Daki na wuce kai tsaye, na ajiye kayan na jawo jakar Dadah na bude, waya ce yar karama, sai kudi masu yawa, murmushi nayi na ciri wayar na ajiye jakar ina kokarin kunna wayar.
Numbobi biyu na gani akai, daya an saka my number, sai dayar dake rubuce da babban baki, *BABANA* zuba wa number ido nayi ina kallo, babu shakka number Ya Farouk ce, shiru nayi ina tunanin abinda zanyi da ita da Dadah tayi min saving dinta akai, sai dai bani da amsar hakan. Ajiye wa nayi kawai na shiga wata sabgar ina kokarin ganin na manta da damuwa ta.
Kwana uku da tafiyar su Dadah sai ga kiran ta, da murna na daga muka gaisa ta tambayi ni idan akwai matsala, hira muka danyi sannan ta kashe bayan ta kara jaddada min kalmar nan ta hakuri ta na riga na gama haddace ta. Tun daga lokacin muke waya sosai, wani lokacin naga shiru nakan kirata muyi hira sosai. Wata rana muna waya take min maganar Jamb, tabbas nima dama ina son yi ɗin,sai dai idan na duba yanayin da nake ciki sai nace na jira wata shekarar, ko dana fada mata uzuri na bata amince ba, a wannan shekarar take so nayi, babu inda raino ko ciki ke hana karatu. Dole na amince na shiga tunanin yadda komai zai kasance.
***
*Bayan wata biyu*
Ba tare da dogon nazari ba, tabbas yan watannin nan a cikin waha'a nayi su, wahalar rainon karamin ciki zuwa kokarin mantawa da dukkan rayuwa ta ta baya, bani da matsala da Inno, dan babu abun da yake hada ni da ita, iya kar kokari na ina yi ganin na kyautata mata, ita dinma a bangaren ta hakan ne, duk abinda tasan zan nema tana kokarin bani shi. Ranar muna zaune muna hira da Yalwati, wadda yanzu ta zama abokiysr hira ta tun bayan tafiyar Karime, dan Inno ba kasafai take doguwar hira dani ba, kasuwancin ta da ya kusa durk'ushewa ta jajirce ganin ta farfaɗo dashi, dan hakan ya zama ma kowanne lokacin ta me tsada ne a wajen ta.
Nura ne ya shigo, kansa dauke da hular gini, ya zauna daga gefen tabarmar da nake zaune yana jingina da bango cikin matukar gajiya. Cikin tausaya wa nace masa "Sannu." ruwan dake gefe cikin kofi na mika nasa, karba yayi yasha ya ajiye sannan ya ciro takarda daga aljihun sa
"Gashi Aminatu, dukkan bayanin yana ciki tace, ki shirya gobe sai na rakaki ki cike dan tace befi sauran kwana uku a rufe ba, Allah ne ma yasa aka danyi jinkiri wannan karon da sai dai wata shekarar."
Da farin ciki na karba na duba, sannan nace
"Kai amma naji dadi, nagode sosai Yaya Nura, Allah ya kaimu goben ."
"Amin." Yace yana mik'ewa.
"Bari na watsa ruwa a gajiye nake."
"Gaskiya dai, ai da gajiya."
Gyara zama nayi ina juya takardar principal din tamu cike da farin ciki.
Ina shirin kwanciya Inno ta shigo, tsayawa tayi a kaina tace
"Naji kuna waya ina tace miki ki saka?"
Na gane Dadah take nufi, kai tsaye nace mata
"Cewa tayi wai nasa Kano."
Shiru tayi, sai chan kuma tace
"Shikenan Allah taimaka." Daga haka ta fice tana jawo min kofar, ni kuma na gyara na kwanta ina fatan wayewar gari saboda tsananin farin cikin da nake ciki.
Washegari da sassafe na shirya muka dau hanyar zuwa cikin gari dan cike jamb. Bamu sha wuya ba muka gama muka dawo. Ranar jarabawar tazo naje na zana cike da addu'ar samun abinda naje nema. Haka muka dawo gida zaman jiran tsammani. Kwana uku kuwa tsakani sakamakon ya fito, sosai hankali na ya tashi, haka dai na daure nasa aka dubo min. Ban taba zaton zanci haka ba, hamdala nayi ta wa Ubangiji dan nasan ba iyawa ta bace. Dana kira Dadah ma na faɗa mata sai ta hau murna, saura jiran post Utme kuma.
A hankali cika na yana girma, ina kara tunanin yadda zata kasance min idan na haifi abinda yake ciki na, duk da yanzu bana shan wuya sosai sai dan abinda ba'a rasa ba.
Ranar dana gaji da zaman nayi gidan Karime, chan na wuni sai wajen magriba na dawo gida, washegari kuma nayi gidan Hanne. Sosai suke bani sha'awa, yadda suke zaune a dakin su, da dadi babu dadi, suna tare da mazajen su, hakan ba karamin sani tunawa da Ya Farouk yake ba. Haka dai nake bawa kaina k'warin guiwar komai zai wuce.
***
BAYAN WATA SHIDA
Haka rayuwa ta cigaba da garawa cikin hukuncin Ubangiji Ranar wata talata Inno ta fita sayo kaya,tun safe ta fita sai wajen Magriba ta dawo, yanayin ta kawai na kalla na tabbatar babu lafiya, a gefe kawai ta ajiye kayan ta fada banɗaki, ta jima ciki sannan ta fito, dakin ta ta wuce ta kwanta, ina ganin haka na mike na bita dakin, tayi nisa a tunanin ta na shigo, tana gani na ta tashi tana kokarin fita daga dakin,
"Inna bak'ya jin dadi ne?"
"Gajiya ce kawai, sai dan ciwon kai."
"Allah ya sauwake, bari na dauko miki paracetamol kisha."
Nace ina barin dakin, biyo baya na tayi, ni kuma na shiga daki dan dauko mata, a bakin rijiya na ganta tana alwala, tsayawa nayi ta gama sannan na bata maganin, balla tayi tasha ta wuce daki zuwa lokacin an fara kiraye kirayen sallah. Alwalar nima nayi na wuce daki dan yin sallah.
Tsawon sati guda kenan Inno na cikin zulumi, tun ina tambayar ta har na hakura na zura mata ido kawai ina alakanta hakan da yanayin jikin Baban.
Muna zazzaune a tsakar gidan ana yar hira, Baba na daga kofar dakin sa saboda yanayin da ake na zafi akan fito dashi shima yana shan iska. Shigowar bakuwar dauke da sallama ya saka Inno kusan sakin fitilar k'wan dake hannun ta.
"Harira!" Ta furta cikin tsananin mamaki
"Nice nan Innaro, kinga bakuwar daree ko?" Tayi maganar cikin wani irin salo dauke da yar karamar dariya.
"Muje ciki." Inno tace tana saurin fadawa dakin ta, bin bayanta tayi, a hankali naji an turo kofar dakin alamun an rufo ta, mamaki ne ya kamani, na dan muskuta kadan ina tunanin abinda ya kawo matar, a yanayin Inno kawai ya nuna batayi maraba da zuwan nata ba. Tsawon lokaci suka dauka sai tashin magana k'asa k'asa, chan suka fito tare, Inno sanye da hijabi suka fita tare. Har wajen tara shiru bata dawo ba, ina ta sake-saken abinda yake faruwa sai gata ta shigo. Bata yi wa kowa magana ba ta wuce ciki, har zan bi bayan ta sai kuma na fasa ina kunna Radio cikin wayata. Washegari na tashi bani jin dadin jiki na kwata-kwata. Tun bayan dana shiga wata na takwas nake jin wani iri, haka dai na lallaba na d'anyi abinda zanyi, na koma na kwanta. Shigowar Inno dakin yasa na tashi da kyar ina kallon ta, zama tayi a gefen yar katifar tawa, hankalin ta sam baya jikin ta. Kallon idon ta nayi naga yayi ja, sai duk naji babu dadi.
"Dan Allah menene yake faruwa inna? Kullum baki da nutsuwa kamar ma baki daa lafiya ne."
Gyara zaman ta tayi, ta dube ni a nutse tace
"Abubuwa ne da yawa suka tarar min Aminatu, sakamakon abinda na aikata ne yake bibiyata, dan Allah dan Annabi ki yafe min, na zalunce ki ban miki adalci ba, saboda son zuciya irin tawa, ki yafe min dan Allah..."
"Inna? Me Kika yi min haka har zaki bani hakuri, ni wallahi bakiyi min komai ba, iyaye ai basa taba laifi a wajen ƴaƴansu, nice ma zan nemi gafararki, watakila na miki wani laifin ne da yasa ki a halin da kike ciki."
"Kayya, Aminatu. Nidai dan Allah ki yafe min, kuma kiyi min alƙawarin zaki karbi hukuncin dana yanke akanki, shine kadai abinda zan miki na ceceki daga hannun azzalumai."
"Ban gane ba inna."
"Karki damu, yau in Sha Allah zakiji komai, banso sanar miki ba, amma ya zama dole idan ina so na samu sauƙin abinda na aikata."
Daga haka ta tashi ta bar dakin. Kasa binta nayi kawai ina tunanin maganganun ta, ban gane komai ba sai ma toshewa danaji ƙwaƙwalwa ta na neman yi. Mik'ewa nayi da nufin binta naji marata ta rik'e. Komawa nayi na zauna ina yarfe hannu. A hankali naji ta fara saki, na yunkura da kyar na fito, dakin dana gani a rufe yasa na gane ta fita, komawa nayi na haye saman katifa ta na cigaba da juyi ina tunanin maganganun.
La'asar likis ta shigo gidan a matukar gajiye, dakin da nake ta nufo, sallama kawai tayi ta shiga hade min yan abubuwa na waje daya, duk da dama ba wasu kaya bane masu yawa, cikin kankanin lokaci ta gama ta ajiye su a gefe sannan ta fita, cigaba nayi da kwanciyar kawai na zuba wa sarautar Allahu ido, chan ta shigo ta dauki kayan ta sake fita, bansan me hakan ke nufi ba. Da kyar na tashi na gabatar da sallah, idarwa ta kenan ko hijabin ban cire ba Inno ta sake shigowa, hannu na naga ta kama.
"Tashi Aminatu, lokaci na kurewa."
Mik'ewa nayi da d'an karfi na ta shiga jan hannun nawa, hanyar waje naga tayi dani, na cigaba da binta, motar dana gani ce yasa gabana faduwa, bude min tayi Na shiga sannan itama ta shigo, tana rufewa me motar yaja muka bar kofar gidan.
Tafiya mukayi sosai babu wanda yayi magana a cikin su har sai da muka fita daga kauyen namu muka isa babbar tasha, gefe ya samu ya faka ya kashe motar ya fita daga ciki ya bar mu. Yana fita Inno ta juyo tana kallo na
"Inna dan Allah me yake faruwa?"
Kasan kafarta ta zura hannu, sai ga jakar da ta jima tana ajiyar ta, akan cinyata ta ajiye min tana kokarin maida kwallar fuskar ta
"Gashi nan Aminatu, tabbas na zalunce ki, ban kyauta miki ba, na raba ki da dukkan farin cikin ki, ta hanyar rabaki da ainihin iyayenki...."
Ras gabana ya fadi jin abin tace, wani irin juyi naji cikana yayi, nayi saurin dafe wajen ina zaro ido
Bayan hannun ta tasa ta share fuskar ta
"Labari me tsawo Aminatu, sai dai wallahi tallahi yaudara ta sukayi, ba tare da sanin komai ba, na amince musu, nayi dana sani Aminatu, nayi dana sani tun ba yau ba, Allah ne shaida ta. Kiyi hakuri da abinda zan sanar dake, bani na haife ki ba, hasalima bansan iyayenki ba. Rana daya muka haihu da mahaifiyar ki. Sai dai ni haihuwa nayi da kaina ita kuma aiki akayi mata. "
"Watarana naje asibitin ganin likita, a lokacin cikina wata tara har da doriyar yan kwanaki, tare da kawata Harira data rakani, muka hadu da wata Hajiya, kana ganin ta kasan hamshakiyar mata ce, wadda ta jiku da kudi da jin dadi, yadda take ta kallon mu, yasa na dan zargu amma na share. Sanda muka zo tafiya ne ta tsaida mu, ta kira Harira gefe, sun jima suna magana har na gaji na zauna, sannan tazo muka tafi. Kwana biyu tsakani Harira ta bijiro min da maganar data firgita ni, da farko sam ban amince ba, amma yadda ya dinga kwadaita min abubuwan Alkhairin da zamu samu, naji na amince da bukatar su ta indai namiji na haifa zan basu, su kuma su bani tasu indai mace ce. Sai dai na kafa sharadin ba za'a dau lokaci ba zasu dawo min da d'ana, da farko matar bata amince ba, amma da Harira tayi mata bayani sai ta yarda. Bansan me ya faru ba ranar ina kwance sai ga Harira dauke da magani, ta kawo min wai nasha, ban kawo komai ba nasha, kafin wani lokaci na fara nakuda, da kanta ta dauke ni muka nufi asibiti, muna zuwa aka ce haihuwa ce aka shiga dani. Ban dau tsawon lokaci ba na haifo dana namiji, kukan sa kawai nake iya tunawa da yake min amsa kuwwa Harira ta dauke shi ta fita dashi, jim kadan ta dawo dauke da ke, da wannan jakar wadda ke dauke da manyan kudade masu yawa da tsoratarwa, haka ina ji ina gani aka tafi da d'ana, aka bar min ke. Bansani ba ashe Harira yaudara ta tayi, bata san su ba, bata taba ganin su ba sai ranar da muka hadun nan asibiti. Kiyi hakuri tabbas an zalunce ki, duk da bansan alakar ki da matar data tsara wannan abin ba, amma tabbas mahaifiyar ki bata da masaniyar abinda muka aikata."
Saboda tsananin kukan da nake muryata ko fita batayi, bansan a wanne mazauni zan dauki zancen na ajiye shi ba, ji nake kamar zan haukace saboda tsabar firgice, sama sama numfashi na yake fita. Duk addu'ar data zo baki na na shiga karanto wa, ina kokarin ganin na saita kaina
"Kiyi hakuri, tabbas na zalunce ki, ban kyauta miki ba. Bamu da lokaci Aminatu, ga jakar ki nan, da duk kudin dana karba wajen iyayenki, kiyi amfani dasu, domin sanar wa kanki rayuwa me kyau, Harira ta kulla wani babban abu, da bazan iya barin ta aiwatar wa ba, kuma bani da hujjar da zan ƙaryata ta, ko na nuna wa duniya ainihin wacece ita, rayuwar ki na cikin hatsari idan kika zauna anan, zan sauka na koma daga nan, ki kula da kanki, ki kula da kanki. Allah yayi miki albarka."
Kukan ne yaci karfin ta, ta shiga yin shi babu kakkautawa. So nake nayi magana, so nake nace wani abu, amma na kasa, na kasa samun harafi kwaya daya da zai samu zama akan harshe ne har na iya furta shi. Ina jin ta ta bude kofar ta fita, cikin dakiya tace
"Sai watarana Aminatu."
Sai a sannan naji karfi yazo min, na yunkura da sauri na balle murfin motar na fito.
"Inna..." Na kwala kiran da dukkan karfin muryar ta, chak ta tsaya, da tafiyar da take batare da ta juyo ba, k'asa daga kafa ta nayi, hankali naji wani abu kamar ruwa yana bina. Cigaba tayi da tafiyar ta, ina kallo ta bacewa gani na. A wajen na durkushe ina jin numfashi na yana barazanar barin gangar jikina.
Sama sama naji wani mutum yana min magana, ban iya amsawa ba, sai nuna masa motar nake da hannu na. Barin gurin yayi da sauri, chan ya dawo tare da wata mata.
"Taimaka Hajiya mu sata a motar chan bga kamar." Ina ji suka kamani, suka saka ni a motar, daidai lokacin me motar ya dawo.
"Kaine me motar nan?"
"Eh nina, tafiya zakuyi?"
"Eh, amma ga passenger ka nan babu lafiya ai, ka taimaka a mika ta asibiti kusa."
Lekowa yayi cikin motar, ganin yadda nake murkususu yasa shi firgicewa
"Kuyi hakuri gaskiya ba zan iya ba, sai dai idan kunyi niyyar taimaka mata ne toh."
Cikin bacin rai namijin yace
"Ashe baka da tausayi, baka ga halin data ke ciki bane?"
Da sauri ta dakatar dashi
"Anas karka dau zafi, ina ganin haihuwa ce, ya kamata muyi sauri taimaka sai a biya ka malam." Tace tana kokarin shiga motar.
"Muje toh tunda biya zakuyi."
Kwafa Anas yayi a bude motar a fusace ya shiga.
Ignore any error
#Rayuwar Aminatu. 💔💔🙏
Nagode sosai da addu'oin ku gareni, kunsan matsalar ido sai a hankali, yau tun safe nake typing ɗin nan ina yi ina ajiye a hankali saboda idon. Please bear with me Dan Allah 🙏
Rano©Hafsat Rano
(16)
★★★★★
Tsaki kawai yake har suka isa asibitin, zuwa lokacin na bana gane komai, tsananin azabar da nake ji tafi gaban a bayyana ta. Tun kafin motar ta gama tsayawa yayi saurin balle murfin motar ya fito yana kwala kira nurses din, da sauri daya ta ƙaraso wajen motar, suka taimaka aka fito dani, kujerar da ake dora mara lafiya aka saka ni akai, aka nufi labor room dani. Fitowa nurse din tayi ta bashi list ɗin abinda ake bukata, da sauri yaje ya siyo a cikin asibitin ya kawo.
Tsawon lokaci aka dauka ina fama, nasha matukar wuya kafin na haihu, ina haihuwa na suma cikin tsananin wahala. A wannan lokacin suka gyara min jikina ba tare da nasan me ya faru ba.
Sama sama naji suna kiran sunana, a hankali na fara dawowa, ido na ya sauka akan jaririyar dake kwance bisa kirjina, babu ko kaya a jikin ta, kura mata ido nayi, kuka take sosai da dukkan karfin ta.
"Ga tana tabarakallah, lafiyayya kuwa."
Naji nurse din na fad'a wa abokiyar aikin ta. Rasa a wannan matsuguni zan ajiye wannan ranar, ranar da nake gudun zuwan ta, duk kuwa da na hakura na barwa Allah ikon sa, sai gashi tazo min a bai bai, cikin yanayin da ni kaina ba zan iya tantance shi ba, bani da kowa yanzu kenan? Sai wannan jaririyar da bata san komai ba, yanzu ne ma zata fara sanin abinda ke kunshe cikin duniyar nan. Hawayen da bazan iya banbance na farin ciki ne ko na bakin ciki ba suka shiga bin fuskata, ina ji suka cire ta daga jikina, suka shiga gyara ta. Dakin hutu aka maida mu, suka shigo a tare, kallon su nake har suka ƙaraso inda nake, Hajiya ta dauki yarinyar cikin farin ciki, ta shiga jera min sannu.
"Masha Allah, Allah ya raya ta."
"Matso ciki mana ka ga jaririyar." Tace tana kallon sa, yana tsaye jikin kofar yana kallon ciki, a hankali ya tako, ya ƙaraso gaban ta ya leka cikin shawul ɗin da aka rufe ta, murmushi naga yayi, a hankali ya furta
"Tabarakallah Hajiya, kinga baby me kyau kamar a bani."
Dariya ta saka
"Kai fa Anas na manta son yara ne dakai."
"Wallahi Hajiya. Ina son yara."
"Allah ya baka masu albarka."
Da sauri ya amsa
"Amin Hajiya ta."
"Ja'iri." Tace tana dariya. Kallo na tayi
"Baiwar Allah ya kamata ki kira yan uwanki, kinga mu akan hanya muke, idan yaso ko zuwa gobe ne sai mu wuce, nasan ma dai goben zasu sallame ki tun da kalou kike ai."
Ido na ne ya cicciko jin abinda tace, wa zan kira? Bayan bani da kowa a yanzu, wayar ma ko dauko ta banyi ba, ganin yadda duk suka kafa min ido yasa na wayance nace
"Ba anan suke ba, a Kano suke."
"Kano? Toh ai muna yan chan ɗin ne, idan kin yarda damu sai mu tafi tare gobe da safen, idan yaso sai dai su ganki da babyn ki."
"Allah ya kaimu goben." Nace ina kokarin boye damuwa ta. Ido na ne ya sauka akan jakar nan, wani yawu me kauri na hadiye ina tunanin abin yi. Babu inda ta bar ya Farouk, komai nasa ne, hatta yatsun kafarta dana hannun ta nasa ne, hawaye na share a hankali ba tare da na bari sun ganni ba.
Fita Anas yayi ya nufi masallaci, ya bar mu a dakin muka karasa kwana, da safe wajen tara aka sallame mu, mota yaje har tasha ya samo mana, aka zuba kayana muka dauki hanyar Kano a karo na farko a rayuwa ta.
***Isar Inno gida tana kokarin shiga yayi daidai da tsayawar motar, Harira ce ta fito kafin daga bisani matar da suke tare ta fito ita ma. Juyowa tayi tana kallon su, fuskar ta a yanayi me wuyar fassara wa. Karasowa sukayi suka tsaya mata a gaba, Harira tayi dariya sannan tace
"Yau dai ga uwar yarinya nan, sai ki bata ita ta tafi da ita, ki gode wa Allah ma da bata ce zatayi karar ki ba wallahi, dan haka salun alum ba sai kowa yaji ba, shiga ki fito da ita."
Kallon banza tayi masu a tare kafin tace
"Ashe ma ni mahaukaciya ce kamar ke, kina tunanin bayan kinzo kin same ni da maganar banzar ki zan sake amince miki har na sake wani gangancin? Kije duk inda zaki ki tona min asiri, na riga na shirya wannan ranar tun kafin zuwan ta."
"Kina nufin me kenan?"
"Abinda kike tunani."
"Baki yarda da abinda nace ba kenan?"
"Ai yadda dake tun ranar da na gano cuta ta kikayi, a ranar na cire ki daga sahun mutane masu hankali, kuma a ranar na daina yarda da duk wani mutum a doran kasar nan."
"Ina wai yarinyar take?" Matar ta tambayi Harira tana yatsine.
"Kina ji ai ko? Ki shiga ki fito da ita, kinga shiyasa ma muka zo da daddare muyi komai cikin sirri, in Kuma so kike kowa yaji ne toh?"
"Idan kinga dama, ki dauki abin magana ki zagaye duk garin nan ki sanar musu, a nan ne zan gane cewa baki da mutunci."
Daga haka tayi shigewar ta gida, tsaye Harira tayi tana kallon matar, cikin bacin rai ta juya ta nufi mota tana mita
"Kinsan bata min lokaci zakiyi kika kawo ni, bayan kin tabbatar min an gama magana."
"Ja muje kawai aikin banza."
Da sauri Harira tayi wajen motar, kafin ta k'arasa sun ja sun bad'e ta da kura, bin su tayi da gudu tana kwala kiran ta amma basu tsaya ba. Zage zage ta shiga yi cikin bacin rai.
★★★
A gurguje ya hada komai, ya rurrufe ko ina ya fito, baki daya tsawon zaman da yayi a wajen cikin rashin kwanciyar hankali yayi shi, kafatanin tunanin shi na wajen ta, duk da dai yasan ya bar ma mutane biyu amanar komai a hannun su wanda yake tunanin ba zasu taba yi masa ba daidai ba, amma hankalin nasa sam yaki kwanciya, har zuwa yau da suka samu yancin barin wajen, sosai yayi dana sanin shiga aikin soja, aikin da zai raba ka da kowa naka idan ba girma kayi a cikin sa ba, tsawon lokaci ba tare da anji daga gareka ba, babu service balle ka kira wani, idan ma akwai baka da kwanciyar hankalin kiran.
Babbar mota ce sumfurin Hilux suka cika kayan su a ciki, suka dauki hanya. Ife ife ne kawai ke tashi a motar cikin yaren su na sojoji, kowa da abinda ya dame shi wasu ma waka suke bi cikin nishadi da murnar zuwa gida. Kallon su kawai yake ba tare da ya sa musu baki ba, daya gaji da hayaniyar tasu sai ya kwanta kawai ya lumshe idon sa yana jin farin ciki da daukin zuwan nasa gida.
Sanda suka iso Abuja, dare ya soma yi sosai, bashi ya samu isa gida ba sai bayan sha biyu na daren.
Rataye yake da jakar goyo irin babbar nan, sai yar karamar trolly daya riƙe yana jan ta a kasalance, ya ɗan buga gate din, sojan dake tsaye kofar ne ya leko, da sauri ya bude cike da mamaki sa, gaisawa sukayi ya wuce ciki kai tsaye, ganin dare yayi ya sa ya wuce bangaren su, ya tura kofar bakin sa dauke da sallama. Ja'afar na zaune a kan sofa Yana danne dannen waya yaji an turo , dagowa yayi da nufin ganin waye, cikin tsananin tashin hankali wanda yasa saura kadan ya saki wayar hannun sa ya furta
"Ya Farouk!"
Murmushi yayi,
"Kana mamaki ne? Ko ka dauka na mutu ne?"
"Wai yanzu kazo? Yanzu yanzu zuwan kenan?"
"Ga zahiri ka gani, malam karbi kayan ka kaimin daki mana ka tsare ni da tambaya."
"Auw." Yayi saurin karbar kayan yayi hanyar dakin dasu, shi kuma ya fada saman kujerar yana sakin ajiyar zuciya.
"Home sweet home." Ya furzar da iska me dadi kafin ya tashi ya nufi fridge, ruwa ya dauka ya koma ya zauna yasha, sannan ya ɗan mike kafar sa. Jin shiru shiru Ja'afar be fito ba yasa shi kwala masa kira, a zabure ya fito kamar mara gaskiya.
"Kai kuma daga ajiye jaka sai ka zauna, bayan kasan dole zan tambaye ka."
"Bacci ne ya soma dauka ta, afwan, ya hanya ya komai?"
"Normal."
Dan zamowa yayi daga kujerar kadan yana fuskantar shi
"Allah yasa dai abinda na saku kaida Amal kunyi min shi babu shirme ciki, nasan ma dai babu abinda zai sa kuyi min hauka, dan zan iya komai akai wallahi."
"Na'am..?" Ya zaro ido
"Yadda kaji, yanzu dai bari na kwanta, da safe ka shirya da wuri mu wuce, kasan i can't wait any longer."
Tashi yayi wuce daki, a hankali Ja'afar ya zame a wajen yana jin wani mugun tashin hankali. Da sauri ya jawo wayar sa ya hau kiran Amal, har ta katse bata daga ba, haka yayi ta jera mata kiran duk kuwa da yasan ba dole ne ta daga ba, duba da dare yayi.
A falon ya kwana, ba tare da ya runtsa ba, duk kuwa da yasan dole zai dawo dama, amma beyi tunanin dawowar shi a wannan lokacin ba. Lallai akwai matsala babba, matsalar da zata iya haifar da komai.
Manage pls🙏 Yau ruwa yayi mun duka jama'a 😣😣🙄 Saura naji wata tayi min dariya🤫😬 Daurin Goro*
*17*
© Hafsat Rano
ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo
17
★★★★★★
Cikin yanayin da ke bayyana tsantsar farin cikin sa ya tashi, mika yayi hade da salati, kafin ya fada toilet a gaugauce. Be dau lokaci ba ya fito, ya hau shiryawa cikin kaya mafi tsada da kyau, yana yi yana kallon kansa a mirror, murmushi ya saki da ya tuna inda zashi, shigar manyan kaya ce a jikin sa, wadda suka fito da zahirin kyawunsa na bakattsinen asali. Lekowa yayi falon da nufin kira Ja'afar, wayam babu kowa sai kalacin dake zube a saman centre carpet din dake ajiye a tsakiyar falon, tsaki yaja ya fito, ya nufi main part din gidan yana karewa ko ina kallo. Kicibis sukayi da Amal dake shirin fita a yanayi me wahalar fada, da sauri taja baya, cikin yanayin rashin gaskiya tace
"Yahh..."
Murmushi ya sakar mata kafin yace
"Suprice!"
"Saukar yaushe?"
"Jiya kina ta bacci, nasan lokacin kin kai Australia ma dan nasan ki da shegen bacci."
"Waye nake gani kamar Farouk?"
Ta katse su tana fitowa daga kitchen rik'e da babban tea flask me dauke da kunun tsamiya.
"Nine wallahi Mama, ina kwana?"
"Ah laillai maraba da manyan sojoji, sannu da zuwa ya hanyar?"
"Alhamdulillah walalhi ,sai kewar gida, sam aikin nan ba dadi wallahi."
"Toh ya za'a yi, ka gaisa da Daddyn naku dai ko? dan yanzu yake shirin fita."
"Aiko yanzu nake shirin shiga bangaren nasa, bari nayi sauri dan nima Kano zan tafi."
"Za'a je a gano Hajiya kenan, toh karbi flask din nan ka tafi masa dashi, bari na dauko sauran kayan."
"Ko da yake ma..." Ta kalli Amal dake tsaye kamar munafuka tana sauraron su tace
"Daughter zo ki dau sauran kayan ki kai masa na karasa wani aiki anan."
***Tare suka jera yana tambayar ta bayan tafiyar sa, amsawa take har suka karasa part din Daddy, wayar ta dake cigaba da k'ara ta sake katse wa a karo na ba adadi, dariya Farouk yayi
"Sirikin nawa ake wulakantawa ne?"
Sai ta kalle shi da sauri, girgiza kai tayi suka shiga falon a tare, Daddy na zaune ya shirya cikin shigar sa kamar ko yaushe, da tsananin mamaki yake kallon Farouk din har suka ƙaraso ciki, ajiye kayan sukayi akan food mat din da ake jera masa kayan abincin kafin kowannen su ya zame ya zauna, Amal ce ta fara gaishe shi, kana ta mike kamar wadda ake mintsina ta fice da sauri, tana ji Ya Farouk yana bata sakon ta kira masa Ja'afar tayi gaba kawai ba tare da ta amsa ba.
"Barka da Safiya."
Ya furta cike da karsashi ba tare da ya gama karantar yanayin Daddyn ba. Be amsa ba, sai ma wurgo masa da tambaya yayi cikin dakewa yace
"Sai yanzu kake nuna fuskar ka anan ko?"
Kai tsaye yace
"Ayi hakuri Daddy, wallahi tafiya ce ta taso a ranar, na sanar da Ja'afar amma ya fada maka, bayan na kirkira wayar ka ban samu ba, tun da muka shiga jejin nan babu service wallahi, sai jiya da Allah yayi muka fito lafiya."
"Toh... Tafiyar ce ta saka ka yanke d'anyen hukuncin daka yanke kenan? Bayan haka ka nuna min kaine ka haife ni, ka watsa min k'asa a idon duniya ko? Ka kyauta.."
Cikin rashin fahimta yace
"Allah ya baka hakuri Daddy, amma sam ban gane abinda ake magana akai ba, ka gafarce ni dan Allah."
"Rainin wayon naka har ya kai haka? Lallai wuyan ka ya isa yanka."
Kasa yayi da kansa, yana ji Daddyn ya mike, ya shige bedroom d'insa, kasak'e yayi yana tunanin inda maganganun suka saka gaba, sai dai ya kasa gano ko daya. Fitowar Daddyn yasa ya dago, a fuskar sa ya jefa masa takardun guda biyu, kana yace
"Idan kai kana shaye-shaye toh ni garau nake, kuma da hankali na idan kai mahaukaci ne, idan baka gane maganar fatar baki ba, ai zaka gane rubutu ko?"
Da sauri ya dauki takardar ya hau budewa, bakin sa na karanto duk addu'ar da tazo masa, takardar shaidar cikin dake dauke jikin ta ya fara budewa, a take wani matsanancin farin ciki ya lullubeshi, wanda ba zai iya kwatanta shi ba, da k'warin guiwar sa ya bude dayar yana cike da yakinin abinda yace karo dashi a ta farkon na da alaƙa da ta biyu, a wani irin yanayi ya dago hade da mik'ewa tsaye.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Ya furta da karfi yana nuna wa Daddy hannu ba tare da ya iya furta kalma daya ba
"Sannan bayan ka cimin mutunci ta hanyar sakin ta, ka kuma ƙaryata cikin dake jikin ta, shine har kake da gut din takowa inda nake, bansan kuma me kake so ka sanar dani ba."
Da sauri ya dire akan ƙafarsa, yace
"Ban aikata ba, ban aikata daya daga cikin abinda ake tuhuma ta dashi ba a karo na biyu wallahi ban aikata ba, bani da masaniyar komai.."
"Rubutun jiki fa? Ko shima zaka ce min ba naka bane?"
Ya watso masa tambayar yana masa kallon banza, sake kalla yayi da kyau, tabbas rubutun sa ne, me hakan ke nufi? Kira ne ya shigo wayar Daddyn, ya daga yana amsawa kafin yayi hanyar waje kawai ba tare da ya kalli jerin abinci da aka ajiye masa.
Kamar mahaukacin zaki haka ya fito daga shashen, da sassarfa ya isa bangaren su yana kwala wa Ja'afar kira. A zaune ya tarar dashi yana karin kumallo cikin kwanciyar hankali. Watsa masa takardun yayi a hargitse yace
"Kayi min bayanin me ya faru, bayan tafiya ta, ina amanar dana bar maka?"
"Ya Farouk calm down, nayi maka bayani."
"Wanne irin calm down, kasan me kake fada kuwa?" Ya fada a hargitse
"Owk, bayan tafiyar ka, ranar da ka fada min zasu gama exams, muka dau hanya, mun yi nisa sosai har mun wuce Kano ma amma da kadan, motar mu ta samu matsala, abinda yayi delay dinmu kenan gashi yamma tayi and wajen da muke babu abin hawa balle me gyara, da kyar muka sami wani bawan Allah ya juyo damu Kano, muka bar motar a can, washegari Daddy yazo da maganar sakin, bansan me ya faru ba naji dai suna magana da Dadah, the following day muka tafi Shagari tare da Dadah."
Dafe kansa yayi cikin tsananin tashin hankali yace
"Ja'afar, Saki ni? Na sake ta? When, how? Mesa bana tuna komai? Ka yarda zan sake ta kaima kamar Daddy?"
Girgiza masa kai yayi
"Ban yarda ba Ya Farouk, sai dai rubutun da ya zama naka, shi yafi bani mamaki, ya akayi hakan ta faru?"
"Someone is behind this, WallAhi sharri aka kulla min, wani ke son ganin bayana."
"Amma Ya Farouk..."
Ƙarar shigowar messages wayar yasa yayi saurin kallon ta, ta saman notification bar ya ga alamun video aka turo masa ta whatspp, whatspp ɗin ma da ya manta rabon sa dashi, hankalin sa ne ya tafi zuwa son ganin abinda video din ya kunsa, a gaggauce ya danna load, ya zuba wa wayar ido yana jin kamar zuciyar shi zata fashe, cikin kankanin lokaci ya gama loading, videon ya bude. Shine zaune, gaban sa ɗan karamin centre table din dake falon su, rike da papper da biro, rubutun ya kura wa ido, take abinda ke rubuce a takardar hannun sa ya bayyana a faifan video ɗin, shine zaune yana rubuta wa Aminatun sa saki, cikin kwanciyar hankali, jefar da wayar yayi saman kujera yana sakin numfashi da karfi.
"It's a trap Ja'afar, na shiga uku."
Da sauri Ja'afar ya isa wajen wayar ya dauka yana kallo, rubutun tar hade da fuskar Farouk din sanda yake yinshi a cikin falon nan nasu, girgiza kai yayi yana shirin ajiye wayar sakon audio ya shigo, kunna wa yayi muryar Farouk din ta karade ko ina a lokacin da aka kira shi. Sanda yake ƙaryata maganar cikin, zabura yayi ya fisge wayar yana sake saurara, tabbas shine yake magana, amma yaushe hakan ta faru? Ya kasa tuna daya daga cikin ranakun da hakan ta faru. Da sauri ya fada dakin su, ya hau birkice komai na dakin, babu komai sai tarin kayayyakin su da takardun su na makaranta, a hargitse ya sake fitowa, rike da mukullin motar sa dake hannun Ja'afar tun tafiyar sa, da sauri ya tare shi ganin kamar ba a hayyacin sa yake ba
"Barni Ja'afar, Kano zan tafi, daga can na dau Dadah mu tafi wajen ta, ba zan iya zama ba, idan har lissafin cikin jikinta da date ɗin da akayi daidai ne, toh tabbas ta haihu, ko kuma tana kusa da haihuwa, ya kake tunanin zata iya daukar wannan tension din da ciki."
"Let me come with you, ba zaka iya driving ba."
Mika masa car key din yayi ya fada saman kujerar idanun sa sun kada sosai, burin sa daya ya isa gareta, yayi mata bayanin komai. Cikin kankanin lokaci Ja'afar din ya fito bayan ya chanja kaya, suka dauki hanyar Kano.
****
Dadah na zaune hannun ta rike da waya tana sake gwada kiran, karo na biyar kenan tana kira ba'a dagawa, gashi sam hankalin ta yake kwanciyar. kanwarta Fatsim tayi wadda suke kira da Umma Fatsim, tace
"Yaya wai kiran ne har yanzu?"
"Kinga har yanzu ba'a daga ba, gashi sam hankali na yaki kwanciya wallahi, Allah yasa lafiya."
"Toh amin, amma nake ga ai idan ba lafiya ba zasu kiraki su sanar miki, ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai faru sai Alkhairi."
"Allah yasa, anjima sai na k'ara gwadawa."
Hira suka cigaba da yi sama-sama, har zuwa lokacin da aka bude gate din gidan, ta window ta zuge labulen ta leka,
"Ja'afar ne."
Tace tana sakin labulen, da sallama suka shigo, kallo daya zakayi wa Farouk kasan baya hayyacin sa, shine a gaba Ja'afar na take masa baya.
"Babana!"
Da sauri ya karasa gabanta, kamar karamin yaron dake gaban mahaifiyar sa, haka ya dora kansa a saman kafarta yana jujjuya kan kamar wanda ke shirin zaucewa
"Me yake faruwa Ja'afar?"
"Kamar yadda kike tunani ne Dadah."
"Bani nayi ba wallahi Dadah, bani ne ba, sharri aka kulla min, I'm trapped bansan ya zanyi ba."
Dago kanshi tayi
"Mik'e Babana, nasan dama ba zaka taba aikata ba."
"Nasan dama ba zaki yadda ba, ke kadai ce kika yadda dani, amma ni kaina yanzu Dadah ban yarda da kaina ba, na kasa tabbatar wa kaina bani ne na rubuta ba, rubutu na ne, magana tace Dadah, waye zai min wannan? Ko dai ni na aikata ban sani ba? Amma ta yaya? How comes bana iya tuna komai ne?"
"Ba zaka taba aikata abinda zai zama cuta ga Aminatu ba."
Ciro wayar sa yayi, ya mika mata videon yana girgiza kansa
"Nine a videon nan, da hannu na na rubuta sakin Dadah, da hannu na na rubuta, bansan sanda na fara shaye-shaye ba, amma tabbas bana hayyacina sanda na aikata hakan, tabbas yaudara ta akayi, aka sani na rubuta ba tare da na sani ba, sai dai na kasa tuna komai, bana tuna komai Dadah, kaina kamar zai fashe nakeji, zuciya ta namun zafi, idan har akwai mutumin da yake son ganin bayana a duniyar nan, toh tabbas Aminatu tana cikin matsala, zanje na ganta, zan bata hakuri, nasan zata amince dani ko kowa be yarda ba."
"Kaje ka ganta, tana bukatar ka fiye da kowanne lokaci, abinda ke cikin ta na bukatar ka."
Mik'ewa yayi cike da karfin sa, ya juya ya bar falon Ja'afar na take masa baya. Shiru ne ya biyo bayan fitar su, zuciyar Dadah cike da farin cikin dawowar Farouk a lokacin data tabbatar Aminatu na bukatar sa.
★★★★
Tafiya ce mara daɗi musamman gareni, duba da rashin sabo da kuma danyan jegon da nake ciki, kuka yar jaririyar da bansan takamaimai sunan ta ba, ta saka tana wutsul-wutsul da kafarta, dauke kaina nayi daga ɓangaren Hajiyar, ina kallo ta hau jijjigen ta, sai dai bata da alamun yin shiru.
"Aminatu, karbe ta ki sake gwada mata ko Allah zai sa a samu ruwan, kece ma dai kinki cin abinci, dole idan kika je gidan su tilasta miki sa wani abu a cikin ki, ruwan nono sai da abinci zaizo."
Hannu na mika na karbeta, na dora ta saman cinya ta ba tare da sanin takamaimai ta inda zan fara mata.
"Dauke ta ki sata jikin ki mana, shiririta."
Kamar zanyi kuka na daga hijabi na na sata ciki, juyowa yayi bayan muka hada ido dashi, da sauri na janye ido na ina kallon kasan kujerar,
"Hajiya ya za'a yi ne? Itan za'a fara kaiwa ko yaya?"
Gabana ne ya fadi, nayi kasak'e ina jiran amsar ta, waigo ni tayi tace
"Aminatu,wacce unguwar kuke? Kunga an kusa shiga Kanon mu fara rakaki gida sai mu wuce."
Rau-rau nayi da ido na da ya cicciko lokaci daya, na daure na cije nace
"Bansan kowa ba sai mutum daya, hasalima wannan ne karo na na farko dana zo Kanon, sai dai bansan inda zan same ta ba, wayar da xan kira ta na manta ta a gida."
Bude baki sukayi a tare suka ce
"Kina nufin baki san inda zaki ba?"
Daga kai na nayi ina sharar kwalla, ransa naga ya ɓaci, ya kalle me motar
"Idan kaje kwanar dawanau ka sauke mu, sai ta fada maka ita inda zaka kaita, nawa zamu biya gaba daya?"
"Anas..."
"Kiyi hakuri Hajiya, bana so daga taimako mu shiga matsala, kuma kinsan ni a rayuwata na tsani karya, me yasa zata boye mana gaskiyar ta? Sai data ga munzo zata ce bata san inda zata ba?"
"Shikenan."
Tace tana kallo na, kasa na sake yi da kaina ina kuka, zuwa lokacin jaririyar tayi baccin wahala, dan babu nonon sam yaki zuwa.
Sanda muka iso inda yace, inaji motar ta tsaya, ya fita da sauri aka bude masa booth, ya cire kayan su, bude mata kofar bangaren ta yayi yana sake daure fuskar sa tamau.
"Fito Hajiya."
Kallon da tayi masa ya dauke kai kamar be gani ba, ya maida kansa bangaren driver yana tambayar sa lissafin kudin tunda mu kadai ya dauko tun daga chan din.
"Kudin dukka kujerar zaku bayar, ita kuma idan na isa tasha sai ta sauka ta nemi wani abin hawar, iyakata tashar ne kawai."
Lissafa wa yayi ya ciro kudin ya bashi yana yin gaba, a hankali na furta
"Nagode Allah ya saka da Alkhairi."
Sarai yaji, dan har sai da yayi dan alamun kamar zai tsaya, kafin ya kara daga kafar sa Hajiyar na take masa baya. Kuka na saka sosai ina jin bani da sauran gata a duniyar nan. Rayuwata ta kare, ina ji a raina gab nake da mutuwa, sai dai idan na kalli yar karamar halittar dake hannu na, wadda yanzu dukkan rayuwar ta, na rataye a wuya na, sai naji komai ya sake min, zan rayu ko don sabo da ita, na kula da ita.
Ban yi aune ne na ganmu a tashar, sake rungume ta nayi sosai a jikina, motar na tsayawa na balle murfin na fito,ina sake karewa ko ina kallo, a karo na farko na zo Kano, ba tare da sanin inda zan dosa ba. Jakar nan ya fito min da ita, hade da sauran kayana, dauka nayi na matsa daga wajen ina neman inda zan fake don zuwa lokacin har ta kuma tashi tasa kuka, baccin nata baya nisa saboda yunwar dake damun ta. Chan na hango kasan wata bishiya, nayi saurin isa wajen, na rabe ina jijjigata. Nayi nisa a son ganin tayi shiru, kamar daga sama naji muryar sa a kaina
"Kin tabbata ba wani mugun abun kikayi kika gudo ba?"
Dagowa nayi idonmu suka sarke waje guda, da sauri na daga kaina alamun Eh
"Idan kinyi alkawarin sanar dani gaskiya, zan taimaka miki."
"Nayi Alk'awari."
Hannu ya mika ya dauki kayan nawa, na tashi da sauri nabi bayan shi.Daurin Goro*
*18*
©️ Hafsat Rano
ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo
18
***
Adaidaita sahu naga mun dosa, muna zuwa ya mika kayan ciki yace wa Hajiya
"Ku tafi bari na hau wani, zan sameku a gida."
"Shiga." Yace yana nuna min ciki, shiga nayi Hajiya ta miko hannu ta karbi yar jaririyar.
"Kiyi hakuri kinji?" Tace min tana kallo na. Murmushi kawai nayi muka dauki hanya ba tare da sanin takamaimai inda muka dosa ba.
Unguwa ce tsaf tsaf babu cinkoso balle hayaniya, a kofar wani dan madaidacin gida naga mun tsaya, ni na fara sauka sannan ta fito,
"Dauko kayan Aminatu."
Kayan na kwaso ta bude yar karamar kofar jikin gate din muka doshi cikin gidan, da wata dattijuwar mata muka fara haduwa tana zaune gaban fanfo kayan wanke-wanke ne a gabanta tana yi, da murnar ta ta taso ta tare mu,
"Sannu da dawowa Hajiya."
"Yawwa Altine, ana ta aikin ne?"
"Wallahi, jiya mukayi ta zuba ido shiru har dare sannan Ramlah ta hakura ta kwanta."
"Wallahi kam."
"Sannu." Tace tana kallo na, gaishe ta nayi ta amsa sannan muka dunguma zuwa cikin falon, ko ina a share tsaf na samu gefe na rakube ina jin su suna cigaba da hirar tasu inda na fuskanci ita Altinen me aikin Hajiya ce, mika mata kayana tayi tace ta shigar min dasu dakin Ramlah.
"Jeki ki huta Aminatu, nasan kin gaji."
Tashi nayi nabi bayan ta, a gefe ta ajiye kayan, dakin a hargitse duk an barbaza kaya, tattarewa ta hau yi tana mitar halin wadda aka kira da Ramlah ɗin, tana gamawa ta fita, da sauri na haye gadon na kwanta dan ji nake kamar zan fadi, anya ma ina da isheshen jini a jikina ma kuwa? Na tambaya kaina ina karewa ko ina na jikina kallo, na dashe nayi fari tas ga wani matsanancin ciwon kai da jiri da nake ji. Shiru nayi ina ayyana yadda zamu kwashe da Anas, dan da alama mutum ne mai zafi, zan yi kokarin sanar dasu gaskiyar labari na, dan na samu na makale kafin zuwa gaba naga yadda Allah zaiyi dani.
Kukan da naji yana doso dakin yasa na tashi na zauna sosai, Hajiya ce ta shigo rik'e da yarinyar dake faman tsala kuka, zuciyata ce ta tsinke da tsananin tausayin ta, bata da damuwar komai sai ta cikin ta, yunwar dake damun ta itace ta hanata sakat, waya take da alama da Anas ɗin take yi, kafin ta ajiye yana mika min ita.
"Karbe ta ki sake gwada mata, kafin a kawo mata madarar da tausayi sosai wallahi."
"Toh."
Nace na karbeta, fita tayi ta jawo mana kofar, yadda zan fara bata ne ma sam ban iya ba, kici-kici nake tayi na kasa, gashi sai kara karfin kukan nata take, duk na rikice na rude, a haka ta sake shigowa ta tarar dani, hannun ta dauke da bakar leda, da sauri ta ƙaraso tana ajiye kayan kafin ta karɓe ta,
"Baki iya bata ba Aminatu? Na shige su, ai na zata kin iya, shiririta kenan."
Sauke kaina kasa nayi, ta cigaba da jijjiga ta, shigowar Altine da tea flask yasa ta ajiye ta ta shiga hada mata madarar a sabuwar feeding bottle din da aka siyo tare da Madarar, ina zaune ina kallo har ta gama haɗawa sannan ta shiga bata, da sauri da sauri take sha gwanin tausayi, kwalla na share a ido na ta gefe ina godiya da Allah daya kawo min mutanen nan a lokacin da nake tsananin bukatar wani a kusa dani.
Ana gama bata ta koma bacci, kwantar da ita tayi, tana dariyar yadda take fitar da numfashi a hankali.
Kura mata ido nayi bayan fitar su daga dakin, murmushi na saki a hankali na kai hannu na saman kanta ina jin sabuwar soyayyar ta na bin dukkanin jikina.
Ruwan wanka Altine ta haɗa min, ta kawo dakin, ganyen darbejiya naga ana shigowa dashi dakin, kuka yazo min, kukan farin ciki, bansan da wanne bakin zan gode wa wannan matar ba, da kanta ta shigo ta saka ni a gaba tayi min wankan, wankan jegon da iyaye keyi ma kowacce yarsu, a lokacin da nake tunanin na rasa wannan gatan, a lokacin Allah ya aiko min da ita rayuwa ta. Wankan da nayi ba karamin jin dadin jikina nayi ba, ina gama shiryawa aka aikon da abinci lafiyayye irin wanda ya kamata mutumin da yake irin yanayin da nake ciki yaci, sosai naci abincin dan rabona daci tun kafin komai ya sake canja min, dadin dadawar ta tabbatar min da idan ban ci abincin ba, jaririyar tawa ba zata samu ruwan nono ba, hakan ya kara min kaimi wajen ganin naci abincin sosai.
Ina gamawa nabi lafiyar katifar, sam bana son nayi tunanin maganganun Inno, dan ba karamin hargitsa min lissafi suke ba, na kasa gasgata abinda ta sanar min, duk da na riga nasan ba zata taba min karya ba, amma kuma zuciya ta sam ta kasa aminta da maganganun.
Dawowar shi naji yo muryar sa a falon, gabana ne ya fadi da tunanin yadda zamu kwashe dashi, ina nan kwance aka turo kofar, Hajiya ce a gaba sai shi a bayanta, yar karamar kujerar dake dakin yayi wa kansa mazauni, inda Hajiyar ta zauna a gefen gadon tana kallon jaririyar
"Kinga ashe baiwar Allah yunwa ce, gashi yanzu sai baccin ta take."
"Uhum." Nace ina kokarin daidaita zama na saboda yadda naji duk na kasa sakewa.
"Ya jikin?" Ya jeho min tambayar,
"Da sauki."
"Good."
"Kamar yadda kika ganmu, wannan mahaifiya ta ce, sai kanwata Ramlah, sai Altine dake taimakawa Hajiya da yan aike aiken gida, wadda ta zama kamar ma yar uwa ta jini. Babu bukatar dogon bayani mu, mu kadai ta haifa, mahaifin mu ya rasu, sai dangin sa dake Katsina inda muka hadu dake munje wata gaisuwar rashin da akayi, dangin Hajiya duk yan Kano ne, yan karamar hukumar Kibiya, kuma yawancin su suna chan. Ina aiki da federal mortgage bank, in da kanwata take matakin farko a jami'ar northwest."
"Haduwar mu wani iko ne na Ubangiji, duk da haka, ina so ki sanar damu gaskiyar abinda ya dangance ki daya dace muji, ki sani bana bukatar komai sai gaskiya."
Share hawayen dake faman bin fuskata nayi tun lokacin daya fara magana, a nutse na shiga sanar dasu rayuwa ta. Duk da ba komai na sanar musu ba, amma nayi kokarin sanar dasu abinda ya dace su sani kamar yadda ya nema.
Ina kallon yadda yake girgiza kansa, Hajiya kuwa kuka ta saka cike da tausayi na, ina kaiwa karshe ta taso da sauri ta rungume ni.
"Baa kyauta miki ba Aminatu, ba'a kyauta miki ba."
Shine kawai abinda take ta nanatawa, mik'ewa yayi tsam ya iso gaban gadon, idanun sa cikin nawa, yasa hannu ya dauke ta, murmushi yayi min tare da girgiza min kai alamun nayi shiru.
"Wanne suna za'a sa mata?"
Ya fada yana tsura min ido, bance komai ba, na maida kaina kasa ina share hawayen fuskata hade da yiwa Allah godiya, sake maimaita wa yayi a karo na biyu, a hankali na furta
"Duk sunan da ka sa mata yayi."
Murmushi naga ya sake yi, sannan ya kara bakin sa a kunnen ta yayi mata huduba, dagowa yayi yana sauke ta a saman gadon kafin ya kalle Hajiya
"Na sa mata Fatima."
****
Har suka isa kauyen na Shagari babu wata magana data hada su, Allah Allah Farouk yake su isa gidan. Suna isa yayi saurin fitowa ba tare da ya jira Ja'afar ya gama daidaita tsayuwar motar ba, cikin zauren gidan ya shiga yayi sallama da d'an karfi dan babu yaron da zai aika.
Inno na zaune taji sallamar sa, gabanta ne ya fadi ta mike da sauri, idan har ba gizo kunnenta yake mata ba, toh tabbas muryar sa ce, idan kuwa haka ne akwai gagarumar matsala. Sake sallamar yayi hakan ya sa ta kara tabbatar da shi din ne, da sauri ta ciri mayafin ta a saman igiya tayo zauren a rikice.
Zagaye yake a cikin zauren ya kasa tsayawa waje daya, da sauri ya kalli hanyar shiga gidan jin takun tafiya, gaba daya tunanin sa ya tafi akan itace, bayyanar Inno a gaban sa yasa ya dan ji faduwar gaba, yanayin fuskar ta ya nuna akwai matsala, a gajarce ya gaishe ta, ta amsa kai tsaye tana gyara tsaiwar ta.
"Dan Aallah ko zan iya ganinta? Duk da nasan ba lallai ta saurare ni ba, amma ina bukatar ganinta dan Allah."
"Me yasa sai yanzu kake dawowa? Me yasa sai da lokaci ya kure, bayan kayi min alƙawarin zama da ita komai rintse, tabbas dawowar ka a wannan lokaci Farouk bata da amfani."
"Nasan ni mai laifi ne, amma ina da uzuri, ina fatan idan mukayi magana da ita zata fuskance ni."
"Ka makara Farouk, Aminatu ta tafi, bansan inda take ba, bansan ina za'a ganta ba, ya zanyi? Na jira ka, tsawon lokaci baka dawo ba."
A wani irin yanayi ya kalle ta, kansa ya shiga juyawa, wani irin jiri ne ya kwashe shi, yayi taga taga zai fadi, Ja'afar yayi saurin tare shi, da karfin sa ya mike, ya kwace daga rikon da Ja'afar din yayi masa, kallon tsana da kiyayya yake bin ta dashi kafin ya nuna ta da hannu yace
"Me tayi miki da kika watsa rayuwar ta haka? Wanne irin rashin imani ne wannan? Baki san inda take ba, me hakan ke nufi?"
"Bani da zabi ne, zaman ta anan na nufin fadawarta mugun hannu."
"Yanzu kika san a hannun da take? Eh?"
"Ban sani ba."
"Toh wallahi babu wanda zan kyale, bayan sanin alakar dake tsakanin ku, babu abinda zan tsaya jira ko kunya, idan har zaki iya rufe ido, ki koreta a halin da take ciki, wallahi ba zan yi kasa a guiwa ba wajen ganin na bi mata hakkin ta."
"Ka saurare ni, banyi hakan don na cuce ta ba, bani da kowa da zai iya tsayamin, Harira ta wuce inda kake tunani, ya zanyi da raina? Kuskure daya tak, ya zama silar rugujewar dukkan farin ciki na."
Sosai ya koma mata kamar bashi ba, maganganu ya shiga fada mata duk wadda tazo bakin sa, cikin tsananin fushi da bacin rai, da sauri ya juya ya fita, ya fada mota ya bar wajen ba tare da yabi takan Ja'afar da ya biyo shi yana kwala masa kira ba, zauren ya dawo ya tsaya kawai yana tunanin inda Farouk din zashi,
"Dama nasan za'a yi haka, amma ya zanyi da rayuwa ta?"
"Yaushe ta tafi?" Ja'afar ya tambaye ta
"Shekaran jiya."
Girgiza kai kawai yayi, yace Allah ya kyauta.
A kafa ya shiga takawa, ya nufin gidan Bature, a hanya yaci karo da motar yan sanda, sai Farouk dake gaban su, da sauri yasa hannu ya tsaida shi, tsayawa yayi ya bude masa motar ya shiga suka cigaba da tafiya
"Ya Farouk, kana ganin hakan shine daidai? Karka manta wacece a wajen ta fa."
"Na fika sani, ai na fada mata, idan wani abu ya sameta, wallahi bazan kyale ba, wanchan karon taci darajar Aminatun bata sani ba, ba kuma naso na data mata hankali, amma yanzu sai inda karfi na ya tsaya."
Duk da ja'afar be gane inda maganganun suka dosa ba, amma sai yayi shiru ba tare da ya sake cewa komai ba, suna isa gidan yan sandan suka fito, babu wani bata lokaci suka shiga suka fito da Inno, cikin kankanin lokaci kofar gidan ya dinke da mutane, yan kallo, Garbati na zaune a majalisar su labarin ya isar musu, da sauri sauri suka ƙaraso wajen, gaban sa ne ya fadi ganin Farouk ne, boya ya hau kokarin yi a bayan mutane be san tun zuwan sa wajen ya ganshi ba, yana kokarin guduwa yaji an chapke shi, turje turje ya fara yi, yana ihu ganin haka yasa kowa ya hau darewa, suka ingiza keyar shi suka sashi a bayan mota, Inno kasa dagowa tayi saboda tsananin kunya, kuka take har Karime ta ƙaraso wajen dauke da goyon Saddiku tana kuka, ganin Farouk yasa tayi wajen sa da sauri tana rokon sa, hakuri kawai ya bata ya basu umarnin su wuce zuwa kauyen da Harira take. Motar ya fada suka bi bayan su yana jin yau yayi abu na farko daya kamata ace yayi shi tun tsawon shekarun da suka wuce.
Hajiya Inno za'a yi kwanan cell😂😂
#Manage 🚴🚴🚴🚴🚴🤫🤲Hansatu R
19
ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
07067124863
*Ko kuma*
09032345899
*ku ziyarci tasharmu ta youtube don ganin shirye shiryenmu da sauraron litattafanmu tsofaffi da sababbi,karku manta ku dannan SUBSCRIBE kuyi LIKE sannan kuyi SHARING*🙏🏽
https://youtu.be/Zyl7_eSgXuo
★★★★
"Sunana Anas?" Hajiya ta tambaya cikin farin ciki, daga mata kai yayi
"Sunan ki nasa mata Hajiya, ina fatan tayi gadon kyawun halin kirki da nagartarki."
"Wai kin amince Aminatu?" Hajiyan ta juyo tana kallo na, da sauri na daga kaina sama, cikin wani yanayi na furta
"Bani da ja akai, kin chanchanci fiye da haka."
"Allah yayi muku albarka." Tace cikin farin ciki mara misaltuwa.
Gefe ya koma rike da Fatima, ya zauna yana jujjuyata a hannun sa, daidai lokacin ta bude idon ta, hade da sakin kuka, da sauri ya mike
"Iman ta tashi, kinga bakinta Hajiya?"
Yace yana mika mata ita, dariya suka saka baki daya kafin ta miko min ita tana faɗin, maza karbe ki sake gwada mata mu gani." Da sauri na sauke kaina kasa saboda kunyar data kamani, juyawa yayi da sauri ya bar dakin, sai a sannan Hajiya ya ankara, dariya kawai tayi ta cigaba da gwada min yadda zanyi, cikin sa'a kuwa aka samu sai dai babu yawa ga wani irin zafi, yarfe hannu na nake kawai ina cije baki Hajiya namun dariya.
Bayan ta koma bacci na kwantar da ita ina kwanciya a gefen ta, bacci ne ya dauke ni ba tare da na shirya ba.
Na jima sosai ina baccin har sai da mai dakin ta dawo, motsin tane ya data ni, muna hada ido ta sakar min murmushi, murmushi nayi mata kamin na mike ina gyara zama na.
"Sannu da tashi."
"Yawwa." Nace ina yar hamma,
Altine ce ta shigo dauke da Kaskon wuta, ta ajiye ta koma ta kawo kayan wanka, komai sabo hatta bawon wankan da dangin su sabulu, daukar ta tayi, tayi mata wanka hade da gashin cibiya, kafin ta gama dakin ya dau dumi, turaren wuta Ramlah tasa mana ta zauna tana cin abinci tana yi min hira.
★★★
Harira na zaune rike da d'an karamin mudubi tana duba fuskarta, shirya take tsaf daga gani fita zatayi, ajiye komai tayi a gefe ta yafa sabon mayafin ta, tana yan wak'e wakenta cikin farin ciki ta fito, turus tayi ganin yan sanda a tsakiyar gidan nasu, kowa ganin abinda ya kawo su, bata kawo komai akanta ba tayi wajen su, cikin son nuna ita din wayayyace tace
"Lafiya dai?"
Maganar da tayi yasa Farouk juyowa, da sauri yace
"Arrest her."
Babu wani bata lokaci suka damke ta, tana ihu tana komai suka tusa ta cikin bayan motar, sai a sannan ta lura da Inno kanta a sunkuye ta rufe fuskar ta da mayafin kanta. Wani irin amsawa kirjin Harira yayi, cikin tsananin tashin hankali tace
"Innaro?"
"Ko ba ita bace?" Ta maimaita jin ta mata banza, bata amsa mata ba, har suka isa charge office, fito dasu akayi aka watsa su cikin wani ɗan karamin cell kafin ya tura Garbati a cikin nasa shi kadai.
"Zan dawo, kar kuma ku bawa uban kowa belin su har sai sun bqyyana inda suka kai min matata da jariri na.
Da sauri suka amsa ya juya ya bar wajen, Ja'afar na bin sa haka suka koma gida, be kula takan maganar da Ja'afar din yake ta masa ba ya fada daki da sauri ya saka key, misscals ɗin Dadah ya tarar, sai yaji zuciyar sa ta karye, yasan yadda ta damu da Aminatu idan taji labarin nan hankalin ta ba karamin tashi zai ba, fasa kiran ta yayi ya ma kashe wayar baki daya yana bin dakin nasu da kallo, dakin da sukayi rayuwa a ciki, rayuwar da yake ganin ta cikin wasu muhimman lokutan da yayi masa matukar muhimmanci a rayuwar sa. Ji yayi zuciyar ta ta bushe, ta k'ek'ashe, ba zai taba kyale duk wanda yake da hannu ba, ko da kuwa mutanen dake da kusanci mafi rinjaye dashi. So yake yayi kuka da idanun sa, ko yaji dadi a zuciyar sa, sai dai yasan abu ne me matukar wuya a yanzu, lallai zubar da hawaye idan kana cikin damuwa ma Rahma ne.
Sai yamma likis ya tashi daga inda yake, istigfari yayi hade da dauro alwala ya gabatar da sallar azahar da la'asar. Jawo wayar sa yayi ya kuna, ya danna kiran wayar Dadah don yasan tabbas tana cikin son jin abinda yake faruwa. Bugu daya ta daga, da sauri tace
"Babana me yake faruwa? Kun barni cikin tashin hankali."
Share zufar kanshi yayi, murya a ciki-ciki ya soma mata magana, salati kawai take har ya kai karshe, zuwa lokacin gaba daya komai ya fara tsaya mai, yunwa, tashin hankali da wani abu daya tokare masa makoshi ne suke barazanar kaishi kasa, kiran sunan shi take sai dai baya jin komai sai chan a saman kanss, ya gaza amsawa, a hankali idanun sa ke rufewa, kadan-kadan kafin su rufe baki daya yana sakin wayar wadda karar faduwar ta, ta saka Ja'afar tasowa da gudu ya hau dukan kofar. Jin shiru yasa shi firgicewa yayi dakin Dadah da gudu ya nemo spare keys, a gaggauce yazo ya bude shi, da sauri ya k'arasa wajen sa yana jijjigashi, ganin da gaske baya hayyacin sa yayi saurin dauko ruwa ya shafa masa a fuska, ajiyar zuciya ya sauke da karfi yana bude idon sa da suka rine sosai, taimaka masa yayi ya dora shi saman gadon kafin ya fita don dauko wayar sa. Daddy ya fara kira no answer, sai ya kira Mummy ita din ma babu amsa, shiru yayi yana tunanin wanda zai kira kuma, daga karshe ya yanke shawarar kiran Dadah, a rikice ta daga kiran nasa dan dama suna magana da Farouk din ne taji shiru.
Dakin Ja'afar ya komo bayan sun gama wayar, har lokacin idanun sa na bude ya kura wa saman dakin ido.
"Ya Farouk!" Ya kira sunan shi,
"Dadah tace karka sa damuwa a ranka, da cewa tayi ma xatazo nace a'ah zamu taho ma gobe."
"Waye aka ce ya kawo takardar nan?" Ya jeho masa tambaya still idanun sa na kallon sama
"Wacce kenan?"
"Takardar dake rubuce da sakin, waye ya kaiwa Aminatu?"
"Ban sani ba gaskiya, a yadda naji,makaranta aka je aka kai mata."
Shiru yayi cikin dogon nazari kafin yace
"Shikenan, koma waye zan gano ai."
"Kabi komai a sannu Please."
"Karka damu, zaka iya wucewa kawai, zan dan zauna anan ko na sati daya ne."
"Babu matsala idan na Barka? Baka jin dadi naga."
Girgiza masa kai yayi kafin yace
"Idan ka fita ka jamin kofar Please ina son zama ni kadai."
Juyawa dayan barin yana sake gyara kwanciyar sa, dan jim Ja'afar din yayi kafin ya ja masa kofar kamar yadda ya bukata
Dare ya tsala sosai, yayi zurfi a cikin tunanin sa,duk kokarin sa nason ganin ya samu ko da wani haske ne a binciken sa abun ya faskara, juyi kawai yake yana tuna halin da Aminatun ke ciki.
Da safe ya shirya sukayi sallama da Ja'afar ya tafi, duk da baya jin dadin jikin sa da zuciyar sa, amma haka ya danne ya nufi station din don yana son magana da Inno. Fito da ita akayi yayi mata yan tambayoyin da suka shige masa duhu, game da wanda ya kawo takardar sakin. Yadda ta sanar masa yasa kansa ya k'ara daurewa, wacece wannan da zatayi masa haka? Menene tsakaninsu? Mutun daya ya ke tunanin zata aikata hakan, Mummy, sai dai ya kara shiga matukar damuwa daya nuna mata hoton Mummyn amma tace ba ita bace.
Gidan Maigari ya nufa, sai dai shima bayanin d'aya ne mata ne su biyu suka zo wajen sa, sai dai shi be nuna masa hoton na Mummy ba ya daiyi godiya kawai ya tafi.
Duk inda yake tunanin zai kai ga neman ta, yayi, ya sare sosai yana jin kamar rayuwar sa zata k'are. Gidajen Radio da talabijin duk ya kai musu cikiya hade da hoton ta, dan baya taba tunanin zatayi nisa da Katsina, duk binciken nasa a iyakar nan din ne.
Tsawon sati guda kenan yana bincike akai hade da neman ta, duk inda yake tunanin zai same ta har gidan principal yaje, gaba daya ya rame ya lalace kamar bashi ba.
Yana zaune kiran Daddy ya riske shi, a kasalance ya daga yana karawa a kunnen sa gami da sallama
"Farouk, me kaje ka aikata a gidan su yarinyar nan, maigari ya kirani akan kaje har gida kasa an kama mahaifiyar yarinya tsawon sati daya kenan, wai kai yaushe zakayi hankali ne ehe?"
"Daddy ba abinda kake tunani bane..."
"Kai kullum abinda zaka sani magana shi kake yi, ya kamat kasan kai ba yaro bane yanzu."
"Ba haka bane... Ayi hakuri dan Allah."
"Awa uku na baka, kaje ka fitar dasu sannan ka baro garin, kayi abu ya dame ka shine zaka je ka huce akan bayin Allah, Awa uku ka bar garin nan ka dai ji na fada ma."
Bin wayar yayi da ido, ya rasa me yasa har yanzu Daddyn ya gaza aminta dashi balle ya fahimce shi, har yanzu bashi da ikon kansa. Ba ya taba barin sa ya kare kansa, komai yayi bai iya ba, komai yayi sai fada. Mutum daya ke tsayawa ta saurare shi tun yana yaro har zuwa yau, mahaifiyar sa da ita da babu banbancin su kadan ne, bata san komai ba sai kasuwanci ta, bata da lokacin su tun ma kafin rabuwar su da Daddy balle yanzu da take ganin sun girma.
A gurguje ya shiga hada kayan sa, yana yi yana ayyana hukuncin da zai yanke wa kansa, hakan ne kawai mafita a garesa, baya jin zai iya sake zaman wasu awowin a cikin garin. Duk abinda yasan zai bukata ya tattare su, waya kawai ya daga ya kira sifetan yan sandan wajen yace ya sake su, loda koman sa yayi ya rurrufe ko ina ya damka wa Baba maigadi yan mukullayen gidan ya dauki hanyar Kano.
Shigar dare yayi, Dadah na cin tuwo ya turo kofar ya shigo yana jan kafar sa, da kallo ta bishi cike da tausaya wa, har ya zauna gefen ta yana tankwashe kafarsa
"Babu wani labari ko?"
Tace tana tsame hannun ta, girgiza mata kai yayi bakin sa ya gaza furta kalma daya, tashi tayi ta wanko hannun ta tazo ta zauna gefen sa, da sauri ya dora kansa a saman ƙafar ta. Tun yana yaro haka yake mata, idan baya jin dadi ko kuma ransa ya ɓaci, fasa tambayar sa komai tayi. Sai daya gaji dan kansa sannan ya mike ya nufi daki, bata hana shi ba, tasan lallai yana bukatar kadaici, addu'a ta bishi da ita kawai tana fatan komai ya warware cikin sauki.
Ko da ta tashi da safe tuni ya fita, sai gabannin azhar sannan ya dawo gidan, kwana uku yana jeran fita a rana ta hudu yace mata zai je Lagos, bai sanar da ita abinda zai je yayi ba, haka ya tattara ya tafi, a ranar ne ita kuma ta dauki hanyar Shagari don samun magana da Inno.
***
Satin sa biyu a Lagos ya dawo ya wuce Kaduna gidan Mummyn su, duk ya sake ramewa kamar ba Farouk ba, ita kanta data ganshi sai data ji babu dadi, ta shiga tambayar shi abinda ya same shi. Wanka yayi ya shirya kafin ya same ta a zaune a falon ta na alfarma. Tana zaune kafarta saman tuntu tana hutawa.
Maimakon ya zauna a kujerar data ke nuna masa sai ya zauna a k'asa, cikin yanayin da ta kasa ganewa ya soma mata magana
"Kiyi wa girman Allah Mummy, ki sanar dani gaskiya, ba zargin ki nake ba, sai dai zuciya ta, ta kasa nutsuwa, ina son sanin da hannun ki a duk wani abu daya danganci Aminatu? Dan Allah ki taimaka ki fadan gaskiya, kaina ya kule, na rasa waye zai aikata min hakan? Iya sani na ban sake ta ba, amma me yasa na kasa wanke kaina daga daurin da akayi min?"
Murmushi tayi kafin tace
"Farouk kenan, bani da masaniyar komai, haka zalika ban aikata abinda kake tunani ba, mesa zan boye kaina idan har ni ce na raba ku? Karka manta ni mahaifiyar ka ce, tsarin rayuwa ba zai sa na manta matsayi na ba, idan har ina son na raba ku, kai tsaye zan sa ka sake ta, bisa karfin iko na da matsayi na wajen ka."
"Kiyi hakuri, ba ina zargin ki bane, kiyi hakuri dan ALLAH."
"Karka damu, bani da masaniya akan ba kaine ka sake ta ba, bayan na samu labarin a wajen Ja'afar, ban yi niyyar zuwa ba, sai dai text message dana samu ne yasa ni zuwa dole, tun da sakon na nuna cewa ka saki yarinyar sannan Daddyn ku yaje domin ya maida auren, bayan kuma kace kai bakaa so, hakan yasa na tafi, a ganina hakan zai sa na hana abinda yake shirin aikata maka karo na biyu."
"Text?Waye ya aiko shi?"
"Ban sani ba, dan nima tun a ranar na kirkira number ba,tq shiga."
"Zan iya ganin number."
"Ok bari na duba, ina tunanin ban goge message ɗin ba ai."
Gyara zaman sa yayi ta dubo masa number, da sauri ya dauki Number ya kira, ringing daya biyu aka daga, sai dai muryar data bayyana a wayar ta sake sashi a wani rudanin, bayerabe ne ya daga, cikin harshen sa na yarabawa, dole ya kashe yana jingina da kujerar dakin.
Kwana ɗaya yayi mata yace zai tafi, taso ya d'an kara zama sai dai yace mata zai dawo nan kusa, haka ya tattara ya wuce Kano, nan dinma kwanan sa biyu, ya komo abuja.
Jiran Daddy yayi har ya dawo ya same shi a falon sa, gaishe shi yayi a mutunce ya amsa kafin ya nemi izinin sanar dashi abinda ya kawo shi.
"Na yanke shawarar ajiye aikina, zan koma karatu a karo na biyu, na nemi izinin ajiye aike, sai dai sam shugaban mu ya ki amince wa, shine nake rokon ka saka baki dan Allah."
"A wanne dalilin zaka ajiye aikin ka?"
"Akwai matsi da takura sosai, sannan ina son chanja akalar rayuwa ta ne, zuwa mutumin da zaka yi alfahari dashi a gaba."
Da sauri ya kalle shi, sai kuma yayi murmushi
"Kana tunanin yanzu bana alfahari da kai?"
Be ce komai ba, ya sunkuyar da kansa kasa,
"Shikenan, zan yi magana, duk abinda ka zaba wa rayuwar ka, ina fatan hakan ya zamo Alkhairi a gareka."
Sosai yaji dakin maganar, da sauri ya amsa da amin yana jaddada kansa a k'asa cikin tsananin farin ciki
"Sai dai akwai sharadi guda daya..."
"Ina so ka amince da auren kanwar ka Amal, hakan shine kadai buri na akan ka yanzu, idan kayi min shi nasan ka cika d'a nagari."
Da wani irin shock Farouk din yake kallon shi, daga mishi kai yayi cikin gasgata abinda yace ya dora
"Idan har kana son ka samu damar barin aikin ka, ka tafi duk inda kake son tafiya tun da nasan kudurin ka na barin k'asar ne, toh tabbas sai ka auri Amal, idan yaso sai ku tafi tare, daga nan har karshen duniya bani da matsala da kai."
Juyawa kansa ya hau yi, idan har shawarar sa ta kauracewa kowa na nufin auren sa da Amal, da kuwa ya sani be dauki wannan shawarar ba, sai dai ya sani Daddy ba zai taba kyale maganar ba, tun da har ya riga ya furta, idanun sa ne suka shiga dauko masa hoton Amal, duk da yana son ta, yana jin ta sosai a ransa, amma ba hakan na nufin zai iya auren ta ba, aure a irin wannan lokacin da bashi da nutsuwar zuciya, idan yayi haka be wa Aminatu adalci ba.
"Zaka iya zuwa kayi shawara sosai, zuwa nan da lokacin da zuciya ka zata zaba maka abu daya, sai dai ka sani, abu daya tak zan iya yi maka, in ma ka hakura da kudurin ka naa son nisanta kanka damu, ko kuma ka yarda da auren yar uwarka, zabin ya rage naka."
Tirkashi!!!
Shin za'a yi auren nan?
Yaya rayuwar Aminatu zata kasance a gidan data samu kanta?
Sai yaushe zasu hadu da Farouk?
Waye yake ma Farouk makarkashiya?
Ina labarin d'an Inno ne wai?
Yaushe a kuma wanne irin yanayi Aminatu zata hadu da iyayenta?
Leggo🚴🚴🚴🚴🚴🚴🚴🚴🚴🚴🚴🚵🚵🚵🚵🚵🚵Hansatu R
20
ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIKA GANI (DON GIRMAN ALLAH) KARKI SHARING,IDAN KINA BUQATAR SIYA ZAKI TUNTUBI WANNAN NUMBER*
0 comments:
Post a Comment