"Yah Farouk, dama kana tsaye?"
"Umm. Ina tsaye ina jinki kina waya da siriki na."
"Ni?" Ta zaro ido tana dafe kirjin ta
"Da fa Ilham muke magana."
"Ahaap, idan ma dai boye min shi kike shikenan, anyway zo muje ina son magana dake."
Gaba yayi ta bi bayan shi cikin tarardadin abinda zai ce mata ɗin, part dinsu ya shiga, ya zauna saman kujera cikin sanyin jiki ta zauna gefen sa tana kallon sa.
"Kina da wanda kike so?"
Tayi saurin dagowa,
"Yes... Idan har akwai wanda kuke magana dashi, let me know, ni kuma zan yiwa Daddy maganar."
Marairaice wa tayi kamar zatayi kuka tace
"Ni dai babu kowa Allah."
'Dan jim yayi kafin yace
"Kin tabbata?"
Daga mishi kai tayi tana sake kwabe fuskar ta, girgiza kansa yayi ya furta
"Shikenan ba damuwa, kije kawai."
"Ya Farouk!" Ta kira sunan sa ba tare da ta tashin ba, maida kallon sa yayi kanta yana jiran yaji me zata ce, wasa ta soma da hannun ta kafin ta daure tace
"Mamaa tace min zaka aure ni, shiyasa bana kula kowa."
A mamakan ce ya bita da ido har ta bar dakin da sauri, janye hannun rigar sa yayi cikin rashin sanin madafa ya jingina kansa da jikin kujerar yana lumshe idon sa.
Kwana uku a tsakani yana ta tunanin mafita, ya rasa yadda zai ɓullo wa al'amarin, idan har yace ba zai aure ta ba, toh tabbas kamar ya dasa wani babban abu ne tsakanin sa da mahaifinsa, wanda bashi da wani buri sai na ganin ya faranta masan.
Muskutawa yayi yana sake kiran Number a karo na ba adadi,magana d'aya ce babu wani sabon bayani game da neman nata, tsaki yaja yana ajiye wayar, chan ya sake dauka ya danna wa Dadah kira, bata daga ba har ta gama ringing, zamewa yayi a wajen ya mike kafar sa yana fatan komai ya zama masa da sauki.
Yayi nisa cikin tunanin da yake na kokarin ganin ya samu mafita, ganin yana kara bata lokaci yasa shi mik'ewa ya sauya shigar sa zuwa kayan motsa jiki, mota ya fada ya nufi wajen motsa jiki. A chan ya dade ba tare da ya dawo gida ba, sai daya ji ya gaji sosai sannan ya juyo gidan.
Part dinsu ya wuce kai tsaye, Ja'afar ne zaune da sauran yaran gidan suna buga game d'in wot, idanun sa ne suka sauka akan Amal dake zaune cikin su ana yi tare da ita, ransa ne ya ɓaci, ya daka mata tsawar data saka dukkan su firgita, hannu ya nuna mata kofa yana jin kamar ya kikkifa mata mari, gaba daya wannan wani sabon hali ne da be san ta dashi ba, duk da sukan yi hakan a lokacin yarinta, amma yabzu fa? Sam ba zai yarda da wannan shashancin ba, dole ya taka wa Ja'afar birki dan shine babban banza, idan ba haka ba ace duk cikin su basu san abinda ya dace ba,yadda zamanin nan ya sauya, yan uwan da suke uwa daya uba daya ma shaidan na iya tasiri akan su, ballantana ita da take ba muharramar su ba, ya lura kanta na rawa sosai da yadda suke shige wa juna tsakanin su. Dole yayi wa tufkar hanci ba zai yarda su kara masa wani ciwon kan aakan wanda yake fama dashi ba.
A kufule yayi hanyar daki wanda tun kafin ya kai ga yi musu magana duk kowa ya dare ya kama gaban sa.
★★★
Idan nace ina da matsala ta zamantakewa ta da wadannan bayin Allah nayi karya, duk wani abu da zamu bukata nida Iman sai dai mu ganshi.
Sai dai har yanzu zuciya ta ta gaza daukar nauyin abubuwan da ke cunkushe a cikin ta, duk da ina kokarin dauke damuwa ta ko dan yawan fadan Hajiya a gareni, Amma Tabbas ba karamin abu bane a gareni, mutanen da ka sani a matsayin dangin ka, rana daya a tabbatar maka da babu wata alaƙa tsakanin ku, mesa tun da ta kasa daukar haske a kan hakan duba da yadda Inno take mata, sai a yanzu wata maganar da Babarsu Harira ta taɓa fada mata ke dawo mata, Inno bata taɓa shayar da ita ba, a lokacin ta dauki hakan a matsayin wata lalura kila data hana hakan, sai gashi yanzu ta gane babban dalilin ta nayin haka, ba zata ce ta cuce ta ba, amma tabbas bata kyauta mata ba, bata yi mata adalci da d'an data haifa ba.
Bata da wata hanya ta neman mutanen dake da muhimmanci a rayuwar ta, Farouk, Dadah, da mahaifanta. Yaushe zata gansu? Ta riga tayi ma manta alƙawarin ba zata sake komawa garin na Shagari ba har sai sanda ta tabbatar wa kanta shine daidai lokacin daya kamata ta koma din.
Turo kofar akayi aka shigo hade da sallama, dan gyarawa tayi tana kallon sa, a saman kujerar dakin yayi wa kansa masauki cikin kamala yace
"Ya jikin naki?"
"Alhamdulillah." Na maida nasa
"Allah ya saka da Alkhairi." Na dora, nasan abinda yazo gani, tsam na mike na dauki Iman na isa gareshi, hannu ya mika da nufin daukar ta hannayen mu suka hadu waje daya, da sauri na janye nawa ina sauke kaina kasa, kallo na yayi na yan dakiku kafin yayi murmushi yana maida hankalin sa wajen ta, hanyar fita nayi daga dakin bakin daya saboda ba zan iya zama ni dashi kadai ba, yau ne ma rana ta farko daya taddani a dakin ni kadai, ban kai ga fitar ba ya dakatar dani da maganar sa
"Dawo magana zamuyi."
Da baya na dawo na koma inda na tashi na zauna, shiru ne ya biyo baya, ya cigaba da rikon Iman ba tare da yace komai ba, duk sai naji na takura, dagowa nayi da niyyar ganin abinda ya hana shi maganar, idanun sa a kaina suna yawo, da sauri nayi kasa da kan ina ji na a matukar takure.
"Akwai abinda kike bukata ne?"
Kai tsaye nace
"A'ah..." Sai kuma na tuno da maganar kudin nan, tashi nayi na bude inda na ajiye su, na dauko na dire a gaban sa.
"Dama... Dama idan ba damuwa ina so ko zaka ajiye min kudin nan, idan yaso duk abinda za'a bukata sai ayi a ciki."
Da wani irin kallo ya bini
"Kamar me za'a yi dashi?" Ya tambaya yana kallo na, kin yarda nayi mu hada ido nace
"Amm.. ko za'a siya ragon da za'a yi mata hakika wai dama."
"Aka ce miki ban siya ba? Bana bukatar kudin ki, nayi niyya ne ba wai dan wani dalili ba, nayi ne saboda Allah da ya halicce mu, kuma ya umarce mu da mu taimaka wa wanda yake bukatar taimakon."
Daga kaina sama nayi, sai naga kamar ransa ya ɓaci, ajiye Iman din yayi a saman gadon ya juya zai bar dakin, sai kuma yaja ya tsaya yana juyowa
"Idan kina bukatar inda zaki ajiye ne, zaki iya bude account sai kisa a ciki duk abinda kike bukata sai kiyi a ciki."
Daga haka yasa kai ya fice, shiru nayi ina tunani, ni banga abin fushi a magana ta ba, sai dai dukkan alamun sa sun nuna haushi yaji, ya zanyi toh ni? Me laifin abinda nace?
Ko da Hajiya ta shigo, sai ta hau min fada, kar na sake maganar duk abinda za'a yi wa Iman din, dan shi mutum ne mai saurin harzuk'a, na bata hakuri tace ya wuce. Tun daga lokacin bana taba cewa komai har idan bashi ne ya yanke ba, sati ya zagayo aka yanka mata abin yanka kamar yadda addini yace.
Sosai muke zaman mu lafiya da Ramlah, kasancewar ta mutum me faran faran da son mutane, Iman kuwa dukkan dawainiyar ta a wajen su take, idan tana makaranta Hajiya amma da zarar ta dawo shikenan ita zata dora.
Slip dina na ciro na post Utme d'ina na duba, date da komai, Ramlah na bawa ta gani kafin tace zata je ta kaiwa Ya Anas, har ta tafi kai masan ina tunanin amincewar sa, ina zaune ta dawo da fara'ar ta,
"Ya kukayi?"
"Yace kije da kanki wallahi, dama nasan haka zai ce wallahi."
"Na shiga uku, wallahi kunyar sa nake ji Allah."
"Toh kuwa sai ki hakura wallahi."
Tsaki naja na tashi ina daukar mayafi na, baki daya sun kasa gane yanayin da zuciya ta take ciki, kokarin su na son ganin lallai sai na sake dasu, bani da yadda zanyi, haka na fito falon ina wara ido, a hakimce yake a saman kujera ya ajiye laptop a gaban sa yana aiki, be dago ba duk da yaji sallamar danayi masa, a ciki ya amsa yana cigaba da danne dannen sa hankali kwance, rasa ta ina zan fara masa magana, sai dana juya iya kalmomin da zan iya fada masa sannan na soma magana a hankali, har na kai aya be fasa abinda yake ba, be kuma kalle ni ba, sai kawai ya ture laptop din yana daukar slip ɗin nawa, dubawa yayi ya ajiye, ya sake jawo laptop din sa ya cigaba da aikin gaban sa. Mik'ewa nayi tsam nayi hanyar dakin zan koma naji yace
"Allah ya kaimu, best of luck."
Cigaba da tafiya ta kawai nayi ba tare da na tsaya ba, nayi shigewa ta ina turo kofar, Ramlah na riƙe da Iman tana jijjigen ta, ba laifi akwai rigima idan ta fara kuka har sai kan mutum yayi ciwo, karbar ta nayi na yi mata abinda nasan zai sata shiru, da haka na dora sabon tunanin mutum daya tamkar da dubu wanda ya zama min kamar wata al'adah ta yau da kullum.
****
Daddy be sake neman sa ba, kamar ma ya bar maganar gaba daya, har aka soma kiran sa na gaggawa a wajen aiki, ranar yana hanyar Kano kiran ya riskeshi, ba tare da sanin madafa ba ya isa gidan na Dadah. Sai daya ci abinci ya huta sannan ya sanar da ita halin da ake ciki, ta jinjina lamarin duk da ta fara cire rai akan ganin Aminatu nan kusa, sai dai ba zata taba hanashi auren Amal ba, da shi da ita dukkannin su nata ne, babu wanda zata zaba sama da wani, dadin dadawar maraicin yarinyar, duk da babu laifi Maman na kokarin kula dasu, sai dai rashin uwa tun kana d'an karami ba abu bane me sauki.
Abu daya ta dogara dashi a halin yanzu shine Exams d'in da Aminatun zatayi wanda tabbas tasan idan har tana da rai da lafiya ba zata kasa zuwa ba, idan kuwa haka ne zatayi amfani da wannan damar wajen ganin ko za'a dace.
Sanda ta sanar masa da kudurin ta, murna ya hau yi, kamar ance an ga Aminatun ne an gama, duk da babu sanin takamaimai ranar da zata je ɗin, sai dai a hakan zasu duba ko Allah zai sa a dace d'in.
Bincikowa yayi ya samu date ɗin da za'a yi dukka Exams din da venue, ya had'a komai intact yana jiran ranar.
★★★
Ranar labari shine ranar da zatayi ta ta Exams din, tun ranar Monday suka fara jelar zuwa makarantar, daga nan suyi nan har la'asar babu alamun ta, haka suka koma gida washegari ya komo shi kadai ba tare da Dadan ba, nan ma haka ya gama zagayen sa daga nan zuwa nan har aka gama baki daya, ya sha wuya matuka sosai haka ya hakura babu komai a cikin sa ya koma gida yana fatan samun dacewa.
Karfe 9 zamu shiga hall saboda haka da wuri na shirya, Ramlah ma ta shirya don dama sunyi hutun makaranta, shirya Iman akayi saboda zamu biya ta banki daga makarantar, tare muka fito suna zaune da Hajiya yana shan tea, kallo daya yayi mana ya maida hankalin sa kan abinda yake yi, zama mukayi ya karasa Hajiya na dan jana da hira, tashi yayi yana mika min kofin kafin yayi hanyar fita
"Sai mun dawo Hajiya."
"Allah ya bada sa'a, sai kun dawo."
Kitchen na nufa na ajiye kofin na dawo mukayi mata sallama Ramlah na rungume da Iman muka fita.
Yana zaune cikin mota ya kunna ta,muka shiga ya ja muka bar gidan. Karo na farko dana fito kenan tun bayan zuwa na, kallon unguwar nake babu hayaniya, layi ne Babba me dauke da shinfidaddiyar kwalta, daidai kofar wani madadaicin gida me kyau da tsari gate din gidan ya bude a hankali, wata bakar mota me bakin glass ta fito, da wani irin gudu ya hau kan dan karamin titin ba tare da ya kula da motar mu ba. Tsaki naji Anas yaja cikin kuluwa yace
"Sojan nan yazo kenan!"
Ramlah ce tayi tsagal tace
"Jiya ma da Hajiya ta aike ni naga motar tasa, ba yau yazo ba."
"Na tambaye ki?" Yace yana zare mata ido
"Bana son gulma da sa ido kinji, ni da nake da grudges dashi daban, mind ur bussiness."
K'us tayi tana turo baki, ya sake jan tsakin yana kallon mirror din dake saman motar, hada ido mukayi ya harare ni nayi saurin sauke kaina k'asa. Zuciya ta na tsananta bugu jin ambatar sojan da yayi, tunanin Farouk d'ina ne ya dawo min, shi kadai na sani da hakan. Tun daga lokacin na daina sauraron komai, na fada kundin tunanin sa.
Rano😊🙏🏼 DAURIN GORO
21
Gudu yake sosai muna biye dashi har makarantar, a wajen shiga suka tsaida shi ba'a barin me tinted glass shiga, kamar zai yi musu dasu sai kuma ya dawo da baya yayi wajen da aka tanadarwa masu irin glass din, shiga mukayi still Anas na ta mita, mitar yasan dokar kawai dan shi force ne zai taka, mu dai babu wanda ya tanka masa har muka isa gaban Hall d'in, fita mukayi ya nemi wajen parking mu kuma mukayi wajen gungun mutanen dake jiran zuwan examinars ɗin, zaman mu da kadan suka iso, nan dana aka soma screening ana shiga hall din, ba'a dau wani dogon lokaci ba aka fara, addu'a kawai nake duk wadda tazo baki na, saboda ba kowacce na sani ba, ba kowacce na iya ba, dama Farouk ne yamin alƙawarin sani a islamiyya da zarar ya dawo, ashe hakan ba mai yiwu wa bane.
Na gefe na ne muka hada ido dashi, ya bini da wani irin kallo kamar ya ga kashi, mamaki ne ya kamani ganin ba wai sanin sa nayi ba, shigar jikin sa kadai ta nuna waye shi, da inda ya fito. Ban sake kallon sa ba, dan na lura dan zafin kai ne, na shiga abinda ya kawo ni. Har muka gama ban sake kallon ko in da yake ba, hanyar fita nayi ina sauri sauri, ya cimmini yana tsaida ni, kamar bazan tsaya ba sai kuma na tsaya, cikin isa da kasaita ya tsaya a gabana yana min kallon up and down
"Na sanki?" Ya tambaye ni looking as if ya taba gani na
"Kamar ya?"
Wani iri yayi da bakin sa, yana sake ware idanun sa a kaina, sai kuma yce
"May be, may be."
"Ban fa gane ba ."
"Shit!, Kin tab'a attending birthday party haka or kinsan wani a abuja"
Juyawa nayi da nufin barin wajen dan na lura bashi da abun fada sam, sai ya sake biyo ni da sauri,
"I'm Kamal Marwan Dikko by name."
"Baku gama bane?" Muryar Ya Anas ta kawo mana ziyara har inda muke, juyawa nayi na bar wajen da sauri ina tunanin yanayin da fuskar tasa ta nuna, inda na bar Ramlah na sameta, tana rik'e da Iman dake ta faman kuka, tana zagaye a wajen, tausayi ta bani ganin yadda tayi wujiga wujiga.
"Kar dai kuka take tayi miki tun da muka shiga."
Nace ina karbar ta,
"Kuma kinsan batayi kuka ba sai yanzu, wannan da muka gani sojan nan dazu, har nan yazo, da yaji kukan ta har da karbar ta, yana da kirki na rasa me yasa basa shiri da Ya Anas wallahi, kinsan yana zuwa ya ganmu tsaye tare, ya haɗa rai ya karbe ta a hannun shi, dalilin barin wajen nan kenan da yayi, kuma dan mugunta irin ta Ya Anas yana tafiya ya dawo min da ita lokacin ta soma kuka,shine fa take tayi har yanzu, taki shiru."
Dariya kawai na saka muna nufar motar
"Kika san me ya hada su, kinsan ance wasu masu khakhi akwai iya shege, duk da ba dukka ba, Ya Farouk ba haka yake ba sam."
"Toh wannan din ma bashi da damuwa wallahi, zafin rai ne irin na ya Anas."
"Maza ya jiki wallahi, ba ruwana."
Dariya ta saka
"Nima wallahi ba ruwana nayi shiru."
"Atoh, yafi dai."
Jikin motar muka tsaya, tsawon lokaci sannan ya zo ya bude mana muka shiga, rannan nasa a jagule, kamar wanda akayi rigima dashi, banki muka wuce direct ya karbar min Form, na cike komai, wajen sa marital status ne har na zabi wajen Married, naga yayi min wani kallo, da sauri na gyara ina yak'e, na mika masa ya karba yana sake sakarmin harara. Dariya ma ya bani, na dan murmusa kawai, shi sam abin bacin rai baya masa kadan, komai abin ayi fushi ne, sai dai duk inda mutum me nutsuwa da kamala yake ya cika, bashi da hayaniya balle baragada, komai yana yinsa ne gently cikin tsantseni da takatsantsan.
Yana ajiye mu a gida be ko shiga ba ya ja motar ya tafi, Hajiya bata nan taje Barka, Baba Altine ce kawai a gidan ta gama aiki tana kishingid'e tana jin radio, sai a lokacin muka samu muka ci abinci sannan muka zauna muna d'an tayata hira.
★★★
Daya bayan daya mutanen dake cunkushe a harabar makaranta suka dinga yayewa, har ya zama na babu kowa sai yan tsirarin mutane, ran Farouk babu dadi ganin da gaske har ana neman gama wa babu alamar ta, hakan na nufin ta hakura da duk wasu muhimman abubuwan da suka dace da rayuwar ta kenan ko me? Baya so zuciyar sa tana raya masa wani abu mummuna ya faru da da ita, yana ji a ransa tana nan da ranta, kuma koman daren dadewa zata dawo gareshi. Amma yaushe? Yau? Gobe ko jibi? Babu rana balle wata, a duk sanda ya kira Shagari jikin sa kara mutuwa yake, a tunanin sa zata dawo baya, duk da yasan ba lallai bane tunanin ta ya kawo mata hakan, duba da yadda komai ya zo mata a lokaci daya.
Da kyar ya bar makaranta zuciyar sa babu dadi, yana zuwa ya rufe kansa a daki ya kwanta kawai, ba zai taba yafe wa Inno ba, da kuma duk wanda yake da hannu a ciki.
Sakon text message ɗin Ja'afar ne ya iso masa, ya bude yana karantawa
"Daddy na neman ka, idan da hali ka baro komai ka dawo Please."
Ajiye wayar yayi ya koma ya kwanta yana yanke hukuncin amsar tayin na Daddy. Saboda haka yana tashi da safe ya sanar wa da Dadah kudurin sa, addu'a kawai tayi masa tare da sake karfafa masa gwuiwar yayi wa mahaifin sa biyayya.
Haka ya tattaro koman sa ya dawo, ya kuma jewa da Daddyn da albishir ɗin karbar tayin nasa, tsabar farin ciki a take ya kira waya ya nemi alfarmar barin sa ya tafi karatu na tsawon wasu shekaru ba tare da ya bar aikin nasa ba, babu bata lokaci aka gama komai aka hau shirye-shiryen biki na alfarma.
Shi dai sai ya koma gefe ya zuba musu ido kawai dan bashi da katabus akan komai zasu aiwatar.
Da yake abun na gida ne sati biyu aka saka, tun daga lokacin Mama ta soma aikin gyaran amarya, aka shiga hidima sosai tun da wannan su shine karon farko da za'a yi aure a cikin gidan, auren kuma na mutum biyu.
Wednesday suka fara events, dama sam babu wanda yasa ran Farouk din zai halarci abu ko daya a ciki, a harabar gidan dake manne da nasu da ya zama gidan shikiki kuma aminin Daddyn suke yin komai saboda girman sa.
★★★
Sanye take da takalmi me kamar slipers rigar jikin ta doguwa ce me budewa sosai, sai d'an karami mayafi data dora saman kanta, a hankali cike da farin ciki take taka harabar gidan har ta dangana da part din Mama, yan uwa ne cike kowa na zaune ana hada-hada, cike da karsashi ta karasa garesu, suka hau yi mata kirarin ga amarya ga amarya, bakin ta ya kasa rufuwa saboda tsabar farin cikin da take ciki, kan wata Anty ɗin su ta faɗa tana kunshe fuskar ta.
Tsokanar ta suka cigaba da yi, ta zame da kyar ta fada bedroom din su, sauran yan uwan su sa'annin ta ne da manyan ma da suka girme mata a zazzaune ana shafta, cikin su ta shige aka cigaba da yi dakin ya kaure da hayaniyar su.
Wayar tace tayi k'ara, ta daga da sauri, ganin sunan Yah Farouk yasa ta mike tayi saurin fadawa toilet tana saka key, shikiyanci suka hau yi mata tana jinsu ta daga wayar tana karawa a kunnenta
"Kizo side dinmu yanzu ina jiran ki."
Fitowa tayi ta fice tana ji su sake tsokanar ta, har ta isa bangaren nasu babu kowa,tura kofar tayi ta jita a bude, ta tura kanta kai tsaye, yana kwance akan cusion ya daga kansa sama sanye da farar singlet da dogon wando fari, wajen sa ta nufa yasa hannu ya dakatar da ita
"Zauna a saman kujerar nan magana zamuyi."
Jikin ta ne yayi sanyi ta zauna tana mamakin yadda yayi mata, tashi yayi zaune , idon sa sun kada sunyi ja sosai, gaban ta ya fadi da suka hada ido.
Takawa ya shiga yi yana kai komo tsakanin farkon falon da karshen shi ya gaza furta kalma daya, duk in da yayi sai ta bishi da kallo, har ya isa gaban system ɗin dake ajiye tana fitar da sautin suratul munafikun cikin kira'ar Ghamid'i. Kashe karatun yayi ya dauko d'an karamin Flash ya jona a jiki, hoton bidiyon da aka turo masa ne ya bayyana a saman screen din, dan zabura tayi, har ya iso gaban ta ya tsaya kusa da ita daf, ya kura wa videon ido yana masa kallon ssoai, hadiye yawu tayi cikin wani irin yanayi ta kalli fuskar sa, hankalin sa kachokam ya tafi kan kallon video, pause ya saka ya juyo yana hade hannayen sa suka bada sauti me dan karfi. Cikin shakakkiyar murya yace
"Ina kika samu Flash ɗin nan?"
"Ni... Ni? Na'am!"
"Kinji me nace, bazan sake maimaitawa ba."
"Ni ba nawa bane, bansan nawa ye ba."
Wani irin kallo yayi mata shakeke, kafin ya tashi yana matsawa baya
"Tun ranar da abin ya faru, ban taba hutawa daga binciken wanda zai min haka ba, I tried very hard na gano ranar da ni da kaina na zauna na rubuta takardar, sai dai na kasa."
Dan sunkuyowa yayi daidai fuskar ta
"Kin tuna ranar da kika zo kika kawo min juice Ina aiki, ranar dana fada miki zanyi tafiya ina so kuje wajen ta, kin tuna?"
Daga kai tayi da sauri don har ta fara digar hawaye,
"Bude baki kiyi min magana!" Ya daka mata tsawa
"Na tuna."
"Good, what did you do? I trust you the most, na kula dake na baki dukkan gata, kinsan komai nawa, what did you do?"
Ya fad'a cikin daga murya
"Ya Farouk, dan Allah."
"Shissshhhhhhh..." Yasa hannu a saman leban sa
"Don't say a word, bayan na amince miki, you betrayed me, kika bani juice da akayi mixing da abun da zai dauke min hankali, and you gave me this na rubuta same abinda ke jiki."
Ya dago takardar yana nuna mata a fuskar ta da ita da kanta ta rubuta, karfin kukan ta ya karu sosai, wani irin harbawa jijiyoyin kansa suke, ba zai taba yarda idan aka ce masa Amal zata cuceshi haka ba, me yayi mata da yayi deserving wannan sakamakon? Tabbas abinda ya faru kenan ranar, amma yayi imani ba zata taba aikatawa ita kadai ba, dole sai dai idan da hannu wani babba,amma wa?
Kokarin saita kansa yayi dan yana son jin komai.
"Ki daina kuka, ina son sanin dalilin da yasa kika yi min wannan hukuncin, me nayi miki? Soyayyar dana nuna miki tun kina tsumma? Shine sakamako na?"
"Ya Farouk dan Allah kayi hakuri."
"Amal hakuri, is that all? Kinsan halin da kika samu dukka? Dalilin haka yanzu ba'a san inda take ba, and kice nayi hakuri?"
Girgiza kai kawai take tana kuka sosai, tsugunawa yayi a gaban ta yana jin dama shima ya samu damar yin kuka, hannun sa ya dora a saman bakin sa, da sauri ta hadiye kukan da take tana ajiyar zuciya.
"Waye ya saki?" Ya zare mata ido sosai yana sake hada ransa
"Yaaahh..."
"Waye ya saki!!!" Ya daka mata tsawa da karfn da ta kusa sakin fitsari a wando, babu bata lokaci ta shiga sanar mishi komai tana kuka sosai.
Kansa ne ya hau juyawa, ya soma ganin dishi-dishi, bayan samun evidence din da yayi a jakar ta da yadda abin ya dawo masa kamar Flash back, duk da ya shiga kaduwa, sai dai bai taba tunanin zasu aikata masa hakan ba, mutane uku masu matukar muhimmanci a rayuwar sa, wanda ya aminta dasu, yake ganin su a matsayin wanda suka fi kowa a wajen sa, su suka taimaka wajen tarwatsewar rayuwar sa, da baya da baya ya shiga takawa har ya dangana da daki, ganin haka yasa ta fita da gudu tana kuka sosai kamar ranta zai fita.
Daki ya fada ya saka kuka, kukan da ya jima yana neman sa, sai a yau ya samu damar yin sa, lallai ya chanchanci yayi kuka. Ya jima yana yi, sai da yaji kamar zai fita hayyacin sa, sannan ya tashi ya dauro alwala ya shiga gaya wa Allah kukan sa, yana sallar yana hawaye sosai, hawayen zallar bakin ciki yadda suka ci amanar sa.
Asubar fari ya tattara komai nasa yayi wa gidan kallon karshe, ya dau hanya ba tare da tunanin zai sake waiwayo wa ba har abadah.
Ranar data kasance ranar da za'a daura auren, a rana yayi bankwana da kowa nasa da dukkan memory d'insa da yayi tare dasu.
Karfe sha daya kamar yadda aka tsara, dubunnan mutane suka shaida daurin auren Amal Adam Shagari, Da Farouk Kabir Shagari. A daidai lokacin yana kwance a dakin hotel din daya sauka, ya rasa inda zai saka kansa yaji dadi,ya san daga lokacin da Daddy zai gane yayi nisa, duk da yasan zai yi fada ssoai, zai kuma yi fushi dashi me tsanani, amma ba zai iya ba, ba zai iya zama ba, zai bi abinda zuciyar sa ta riga ta saka masa, ko da hakan na nufin zare shi daga cikin ahalinsa ne.
Rano😍
Manage 🙋🚴
Ido baya son takura 🙏💔😢 DG
22
★★★
Kuka take sosai ta kudundune kanta cikin katon bargo, tana jin lokacin da aka sanar da daurin auren, amma bata da katabus, tana ji suka shigo baki dayan su, kowa na kokarin tsokanar ta, da sauri duk suka yo kanta ganin yadda jikinta ke faman rawa, suka shiga tambayar abinda yake damunta, kayan jikin ta ne tun na jiya, idanun ta sun kumbura sosai alamun kwana tayi bata runtsa ba, da sauri daya daga cikin su ta fita dan kiran Mama. A tare suka dawo dakin, ta dago ta tana karata jikin ta
"Baki da lafiya ne dama aamal?"
Kasa magana tayi, sai wani iri da take kamar zata shid'e, riko ta sosai Maman tayi suka fita daga dakin, dakin ta ta kaita babu kowa ciki, ta kwantar da ita tana kokarin kiran ko Ja'afar ne tun da tasan Daddy na cikin Jama'a. Be d'aga ba shi din ma, alamun shi ma ya shiga busy. Jawo mata kofar tayi ta dawo falon, daidai lokacin da Uncle Buhari ya shigo yana gyara zaman Babbar rigar sa.
"Ina Amal?" Ya tambaya bayan ya amsa gaisuwar matan dake falon
"Tana daki na, bata jin dadi ne."
"Ok Ina son ganin ta. "
"Lafiya dai ko?"
"Eh kalou, magana zamuyi."
Ganin da mutane wajen yasa tace ya biyo ta dakin nata,suna shiga ya matsa jikin gadon, ya duba ta kadan kafin yace
"Kunyi magana da Farouk daga jiya zuwa yau?"
Gaban ta ne ya fadi, tayi saurin girgiza kanta tana fatan ba wani abu yace ba, d'an jim Uncle Buhari yayi kamin yace
"Farouk fa ya tafi, ya ajiye letter a dakin su, yanzu haka Yaya bai san inda zai sa kansa ba, matsalar ma ba'a ga letter tasa ba sai bayan aure ya dauro.
"Innalillah wa inna ilaihi raji'un, mun shiga uku."
Mama tace tana sallallami, karfin kukan Amal din ne ya karu, ta mike zaune tana sake bude muryar ta sosai, girgiza kai Uncle B yayi yace
"Kinga yi shiru kar ki ankarar da mutane halin da ake ciki."
Da sauri ta rage kukan nata, sai dai bata daina ba, dan ita kadai tasan dalilin faruwar komai, a yau da tana da iko da kanta, data sanar wa kowa komai, sai dai bata da wannan damar, kenan a haka zata kare rayuwar ta? Ko akwai sauyin da zai zo bayan nan? Kiyayyar Aminatu ce ta shiga ninkuwa a zuciyar ta, duk itace dalilin komai, ta raba ta da Ya Farouk dinta, mai sonta da kaunar ta tun bata san kanta ba.
Cigaba da bayani Uncle B yayi, bata dauki komai a maganar tasa ba, sai data dawo daga tunanin da ta tafi taji yana yiwa Maman bayani
"Abinda nake tunani ko menene akayi wa yaron nan me girma ne, da zai sa shi yanke wannan danyen hukuncin, idan akwai abinda ya haɗa ku ki sanar mana, idan yaso sai asan yadda za'a bullo wa al'amarin."
Ya kalle ta yana sake tambayar ta a karo na biyu, sake girgiza masa kai tayi tana goge hawayen fuskarta
"Bansan komai ba Uncle B, ni jiya ma tun bayan la'asar rabo na dashi."
"Shikenan, ku kwantar da hankalin ku, kar a bari mutane su sani, idan kowa ya watse sai musan ta ina zamu ɓullo wa al'amarin."
Fita yayi ya koma Falon da su Daddyn suke, waya ce a hannun sa yana ta making calls, babu wani information akai, yanke hukuncin kiran Dadah yayi duk da baya son d'aga mata hankali, amma yana tunanin xata iya sanin wani abu.
Yana gama mata bayani ta saki salati, sai kawai tasa kuka sosai, ta gaji da wannan abubuwan dake ta tasowa, ace daga wannan sai wannan? Idan fa wani ciwon ya kamashi? Ba taga ta zama ba.
Sosai maganar ta firgitata, iya sanin ta Farouk ba zai taba aikata abinda zai wargaza ahalin nasu ba, shiri ta soma yi, a yau bayan shekaru masu yawan gaske, zata sake taka garin na Abuja, garin da tayi wa kanta iyaka dashi saboda babban dalilin ta, tana shiryawa tana addu'ar komai yazo musu cikin sauki, dan ba zata juri wani abu ya sake bullowa a ahalin nata ba.
Driver ne ya iso, ya dauke ta da dukkan abubuwan bukatar ta, suka dauki hanyar birnin na abuja.
Tasbah ne ya hannun ta tana ja, bata jin dadin jikin ta kwana biyu, haka dai take daurewa tana yin komai, sai dai a yanzu yadda take jin jikin nata na neman rinjayar ta, addu'a take tayi tana rokon Allah ya daidaita al'amarin ya kare su daga sharrin masu sharri.
****
Mummy na zaune suna meeting da clients dinta kiran Ja'afar ya risketa, message ta tura masa tana meeting ta kashe wayar baki daya.
A gajiye ta fito bayan sun gama, takardu ne masu yawa a hannun messenger ta, hannun ta rike da yar karamar jakar hannun ta suka nufi motarta, sai data zauna a ciki gami da cilla jakar tata gefe sannan ta daga wayar ta kira shi tana kishingida a bayan motar.
"Mummy, akwai matsala wallahi, Ya Farouk ya tafi, babu wanda yasan ina yake, bayan an gama daura auren shi da Amal na shiga daki duboshi na tarar da letter daya ajiye, dan Allah Mummy ko ya fada miki ina zaije? Hankalin kowa ya tashi."
Tuni taji gajiyar da take ciki ta warware, tashi tayi zaune sosai tace ma driver ta ya rage gudn motar,
"Kana jina Ja'afar? Ina yace ya tafi?"
"Be fada ba, yace dai yayi nisa kada a neme shi."
"Dama aure Daddyn naku zai masa? Bani da masaniya akai?"
"Na zata kin sani naga yazo wajen ki before yayi accepting maganar ,shiyasa ma ban sanar miki ba."
"Shikenan, ka kwantar da hankalin ka, bansan ina yake ba amma i ll try my very best naga na same shi, ka kwantar da hankalin ka."
"Ok shikenan, sai anjjima."
Ranta ne ya ɓaci, mamakin girman kiyayyar da Daddy yake mata har ta kai hakan, a karo na biyu ya sake aurar da dan nata ba tare da sanin ta ba, kwafa tayi tana lumshe idon ta, ta gaji da komai, dauriya ce kawai da karfin zuciya, amma wannan karon ya kamata ta nuna masa da gaske ita ta haifi Farouk ba wai shi kadai ɗin bane kamar yadda yake mata iko da gadara akan dukkan abin da ya shafe shi.
Maimakon ta wuce gida kamar yadda ta saba, sai ta sauya akalar motar zuwa gidan su, dan tabbas ba zata bar komai ba, zata nemo danta ta dawo dashi gaban ta, ta bashi dukkan kulawar da ta kamata. Dauriyar ta ta kare!
∞∞∞
Dadah basu isa Abuja ba sai daf da magriba, lokacin kowa ya watse sai yan tsirarin da suka zama dole, Daddy na zaune a masallacin gidan Aminin sa, tun bayan da aka idar da sallar la'asar suke ciki ba tare da sun fito ba, sosai tafiyar Farouk ta bige shi har yana jin kamar bashi da lafiya, zuciyar shi tayi sanyi, tabbas yana tsaurara wa a duk abinda ya shafi Farouk din, ya rasa dalilin da yasa baya iya tsayawa ya saurare shi, ko ya bashi damar kare kansa.
Sai da aka yi magriba da isha'i sannan ya fito, ya nufi cikin gidan nasa yana takawa a hankali, da motar dasu Dadah suka zo ya fara tozali, da dan saurin sa ya nufi shashen nata da zama mallakin ta a dah, Wanda yake a rufe tun bayan tafiyar ta, taron biki yasa aka bude shi saboda mutane, bakin sa dauke da sallama ya shiga, suna zaune dukkan su, Mama na daga kasa wajen kafarta, sai Amal datayi matashin kai da kafarta tana kuka k'asa-k'asa.
Waje ya nema ya zauna, cike da girmamawa ya gaishe ta, ta amsa masa kafin su fara zamewa daya bayan daya suna barin falon, su biyu sukayi saura, daga ita sai shi, kallon sa tayi a tsanake, da hango tsantsar ramar da yayi, wadda ba zata wuce a wunin yau ta same shi ba, Tabbas ba abu bane mai sauki ba tafiyar Farouk din, sai dai a yau zata nuna ma Daddy kuskuren sa, zata sanar dashi abinda ya gaza fuskanta.
"Kabiru..." Ta kira shi da sunan shi kai tsaye, sai yaji zuciyar sa ta kara karyewa, tabbas ko menene zata fada masa yasan me girma ne, cikin girmamawa yace
"Ina neman gafarar ki Dadah, idan na bata miki dan Allah."
Gyara zaman ta tayi, cikin jan hankali tace
"Idan nace kamin laifi nayi karya, tsakani na dakai, babu abinda zance maka sai Allah yayi maka albarka, ka zama baya goya marayu, ka rike kowa naka, ya'yan yan uwanka ka kula da su da al'amarin su, ba tare da ka duba abinda ya faru a baya ba, sai dai kayi kuskuren wofintar da naka duk da sunan son hukunta mahaifiyar sa, menene laifin sa a ciki abinda bashi da masaniya akai..?"
"Baka taba bashi damar jin ta bakin sa ba, komai yayi laifi ne wajen ka, baka taba damuwa da halin da yake ciki ba, halin da zai shiga, duk da haka yana kokarin yi maka abinda kake so."
"Ina ji a jikina a duk inda yake ba a dadi yake ba, akwai babban dalilin da yasa shi barin mu."
"Nayi kuskure, ban taba jin abinda nake aikata masa laifi bane, sai yau, sai dana samu wanda zai fahimtar dani, tun safe maganar da muke kenan da MD, me yasa na kasa gane haka? Sai da lokaci ya kure min, ya zanyi da auren da ke kan Amal? Na rasa ina zan saka raina naji dadi Dadah, komai ya tsaya min."
"Hakuri zamuyi, mu bar wa Allah komai, mu bashi lokaci muga yadda abubuwan zasu sauya, watakila ya waiwayo mu, idan ransa ya saki."
"Allah yasa, bana son matsala ta sake faruwa, ina son yadda muka binne komai, kada wannan matsalar ta tono shi, zuciya ta ba zata iya daukar maimaituwar abinda ya shud'e ba."
"In Sha Allah hakan ba zata faru ba."
Cigaba sukayi da tattaunawa, a hankali cikin hikima Dadah ke kara nuna wa Daddy laifin sa, sosai jikin sa yayi sanyi, yaji tsoron abinda zai je ya dawo. Duk a dalilin rufe sirrin gidan nasu, ya bata wa d'an sa komai, da hannun sa ba tare da ya ankara ba. Tsaki yaja yana tuna shi,ba zai taba yafe mishi ba, duk kuwa da k'asa ta riga da ta rufe idanun shi a yanzu, amma tabbas ya bar musa tabo babba a zuciyar sa da ba zai taba iya goguwa ba.
Kwana Dada uku a daddafe ta tabbatar da komai ya lafa, ta hau shirin juyowa, rokon da suka dinga yi akan ta zauna dasu, ki tayi dan hakan shine abu na karshe da ba zata iya ba. Amal ce ta roki alfarmar zata bita, kai tsaye Daddy ya amince , ta haɗa kayan ta ta bita don samun nutsuwar zuciya.
****
Hakimce take saman kujerar ta ta gado, me samfurin karagar mulki, farar tsohuwa wadda a ƙalla ta doshi shekaru tamanin da yan kai, bata da Abu mafi soyuwa a rayuwar ta fiye da jikin nata wanda ya kasance d'a kwaya d'aya tak.
Hajiya Turai kamar yadda sunan ta yake, wadda tsabar farin ta yasa aka saka mata sunan, gashi har tsufan ta tana nan da farin nata da ya sake haduwa da hutu da jin dadi.
Sanye yake da rigar sa marar nauyi da gajeren wando da be wuce masa guiwa ba, hannun sa rike da football yana dokata a hankali ya isa falon.
Fara'ar fuskarta ce ta dadu, ganin abinda yafi komai soyuwa a gareta, dukkan soyayyar da take wa mahaifin sa ce ta dawo kansa, da ya zama da d'aya tilo da ta haifa a duniya, bayan ta cire dai ta fitar da tsammanin samun sa.
Zama yayi yana cigaba da doka ball ɗin yana kamawa, ransa a bace babu walwala, tasan kwanan zancen,saboda haka ta shiga yi masa kirarin data saba masa a kodayaushe, biris yayi da ita kamar bai san tana yi ba,
"Wanane ya taba min kai wai?"
"Haba Old Woman kinsan fa dalilin fushi na, nace ku fada masa bana son karatun a Nigeriar ma baki daya kunki, ace a rasa ina zanyi University kamar ni sai a Kano, a Kanon ma ba Private Uni ba, chan ta kowa da kowa har da ya'yan talakawa, Allah ya gani an cuceni walalhi."
"Ka kwantar da hankalin ka, ka fara chan ɗin tunda ya kafe, idan yaso a hankali sai na sashi dole ya fitar da kai wajen, amma sai ka fara rage rawar kan naka ya tabbatar ka nutsu sosai."
"Ni wai wacce rawar kai nake, haka kullum Ammi sai faɗa take min, ke kadai ke sona sai Anty, ni na gaji da gidan nan ma baki daya duk babu dadi ayi ta yimin iyaka da abinda ya zama mallaki na."
"Yo dama uwar ka ai ba sonka take ba, ka rabu dasu duk zanyi maganin su dan uban su, kaji shalele na, ka daure ka fara chan din tunda ya kafe."
"Old Woman..." Ya kafe ta da ido
"Wai bake kika haifi Dad bane?"
"Nice mana, me ka gani."
"Kawai ki tilasta masa kice kin gama magana ya kaini waje nayi karatu."
"Ba za'a kai ka ba, dan gidan ku."
Da sauri ya mike yana sosa kai, yayi wuri wuri da ido yana neman hanyar fecewa daga falon, matsowa yayi har gaban sa kafin ya sakar mishi rankwashi a tsakiyar kai, da karfi yasa ka ihu kamar karamin yaro, hakan yasa Hajiya Turai yin salati tana tafa hannu
"Karka kashe min shi, rankwashin nan sai ya juya masa kwakwalwa ai."
Kunkuni ya saka ya bar falon da sauri.
"Hajiya duk ke kike biye masa wallahi, yanzu Kamal shekara nawa yake? Amma bai san abinda ya dace da wanda be dace ba, gashi kinga ni shekaru na kara hawa suke, yaushe zai yi hankalin da zai kular min da dukiya? Ya kula da mahaifiyar sa dani? Lokaci fa tafiya yake."
"Ka kaishi wajen daya ke kulafuci mana, chan anfi saurin karatun nan danan sai yayi ya gama ya dawo."
Girgiza kansa yayi
"Hajiya dan Allah, mu bar wannan maganar, Kamal zan dauka na kai waje? A gaban mu ma ya yakare? No bazan taba wannan gangancin ba."
Juya masa baya tayi, tana magana kasa-kasa, sallama yayi mata ya fita dan yasan idan ya biye mata rigimar da zata sashi a gaba tayi ba kadan bace. Bayan motar sa ya fada yana addu'ar shiriya ga tilon dan nasa, duk kuwa da yasan laifin na mahaifiyar sa ne, taki barin su sam suyi masa nagartacciyar tarbiyyar data dace dashi.
Niko Nace hmm, Allah sarki su malam Kamalu an zake da yawa😂😂
***
Gaisuwa ta musamman gareki Oum Iman me comment da readmore😍😍 Allah ya bar kauna. Muna gani kuma muna godia.
Sannu sannu dai bata hana zuwa sai dai a dade baje ba, kuyi hakuri a hankali zamu warware komai, *Daurin Goro* labari ne me rassa da zaruruka da yawa. A hankali zamu kawo inda muke son zuwa.🙋
Comments dinku na kara mana kwarin guiwa sosai, mungode.DG
23
★★★
Tun daga kan zauren gidan zaka tabbatar da san samu chanji ta kowanne bangare, tana zaune gaban kofar dakin ta, ta yi tagumi tana tunanin rayuwar baki daya, idan aka ce mata komai zai chanja rayuwar ta juya mata baya cikin dan kankanin lokaci zata musa.
Tun bayan fitowar su daga police station bata sake samun nutsuwa ba, magana ta zagaye kowanne lungu da sako na kauyen nasu, bata da damar fita nan da chan, sai kaji ana yar mata da magana. Dalilin haka ta hana kanta fita, gashi komai ya tsaya mata na abinda ya danganci sana'ar ta.
Jikin Baba ya sake matsawa sosai, haka dai suke jinyarsa ita da yalwati duk da karfin jinyar ma ta Yalwatin ce, ita kanta tana bukatar a kula da ita dan kuwa ba isashiyar lafiyar ce da ita ba.
Karime ce ke dan lekowa lokaci zuwa lokaci tana duba su, ta tafi, da haka ake rayuwar cikin kankanin lokaci dan jarin nata ya kare sai yan dabbobin da suka rage mata. Tabbas ko a haka aka barta ta gane kuskurenta, tana ji a ranta bata kyauta wa Aminatu ba, duk da a tunanin ta ta aikata hakan ne don taimaka mata, amma tabbbas tayi kuskure, ta ina ma zata fara neman ta, ta haifi abinda yake cikin ta ko yaya! Wannan tunanin biyu ke sata sake shiga cikin matsanancin tashin hankali.
Cikin dare jikin Baba ya sake rikicewa, babu wanda ya runtsa a gidan, wani irin abu yake fitar wa daga bakin sa, ala tilis da safe suka nufi asibiti bayan ta barwa Nura sallawun daukar guda cikin dabbobin ta ya kai kasuwa wajen mahauta su siya saboda kudin asibitin da za'a bukata.
Ba'a karbe shi ba, har sai da Nuran ya kawo kudin,sannan aka bude masa file aka karbe shi, kafin kuma asan abun da za'a bukata a gaba.
***
Duk hanyar da take tunanin zata same shi ta bi, tayi dukkan kokarin ta amma babu wani labari. Sosai zuciya da ruhin ta suka kosa da abubuwan, tana bukatar wanda zata fadawa damuwar ta, tun bayan rabuwar su da Daddy ta zama mace me matukar tsauri, bata barin kowa ya rabe ta, bata sabo da kowa balle ta saki jiki , agogo ta mayar da kanta,ko yaushe cikin aiki take ba dare ba rana, duk don son ganin ta manta komai. Sai dai a halin yanzu ta karaya, zuciyar ta tayi laushi ainun, tana son wani a kusa da ita, da zai jibanci al'amuran ta, ya saurari kukan ta, amma waye? Bata da kowa a halin yanzu sai babbar yayarsu data rage dake zaune a cikin garin na Kaduna, wadda itama girma da dawainiyar yaya da jikokinta kadai ya ishe ta, ranar data bar wajen meeting dinsu chan ta nufa, da niyyar ta sanar da ita kukan ta, sai kuma ta tarar da ita ma da tata matsalar, dole ta hakura ta boye natan har ta baro gidan.
Kwanan ta kusan hudu bata sake leka waje ba, jinya take sosai, jiki da ruhi, komai baya mata dadi, tana jin ta kamar a yanzu komai yake faruwa, duk abubuwan data shafe su a babin rayuwar ta a baya, yanzu sun dawo mata suna mata amsa kuwwa a kanta.
Rashin uzurin Daddy da yadda yake rufe idon sa ya kasa gano gaskiya komai,ya sake jefa rayuwar d'an su a wani hali. Ba zata taba bari rayuwar dan nata ta salwanta kamar yadda komai ya chanja mata a rana daya tak!
****
Bai taba tunanin zai shiga damuwa kamar haka ba, sai gashi komai ya kakare masa, tafiyar Dadah ta kara sashi a wani yanayi, maganganun ta ne ke kai kawo a cikin ransa, babu abu daya data fada masa da bai zama gaskiya ba, sai gashi yana jin son sanin abinda ya faru a bayan, duk da ya rufe babin nan a rayuwar sa, amma kuma wani bangare na zuciyar sa na son sanin komai, watakila hakan zai taimaka wajen samun haske a wannan sabuwar matsalar data same su.
Ita kadai ce zata sanar dashi komai, sai dai yasan ba zata taba sauraran sa ba, duk da kasan zuciyar shi na nan akan bakan sa na abinda ya aikata mata shine daidai da ita, amma kuma yana jin kamar bai mata adalci ba, kamar yayi tsauri wajen yanke mata hukunci, duk da abu ne daya shafi mahaifiyar sa da d'an uwan sa shakikinsa, amma kuma da ya bata dama, yaji wani bangare na labarin ta, sai dai kash, bai yi hakan ba, a lokacin ma sam baijin zai iya bata wannan damar, yadda zuciya da ruhin sa suka azabtu da abinda ta aikata masa. Bata kyauta masa ba, bata kyauta ba!
Mirginawa yayi yana gyara kwanciyar sa, zai dora tunanin sa Mama ta turo kofar dauke da wayoyin sa da ya baro su yashe a saman teburin falon sa. Mika masa tayi ya duba kiran, misscals ɗin MD ne, shaf ya manta sunyi zasu hadu a yau din, tashi yayi ya shirya kansa ya sauya shigar sa daga doguwar jallabiya zuwa farar shadda da hula ya fita. Kai tsaye gidan sa ya nufa, ya shiga ya nufi babban Falon sa da yake ajiye duk wani bako mai muhimmanci a wajen sa.
★★★
Rayuwa ta a gidan bayin Allah nan rayuwa ce me cike da kyautatawa da mutuntawa. Na gama gane halin kowa a gidan naci kuma alwashin zama da su da halin su, zuwa ranar da zamu rabu, tunda nasan ba zamu taba dawwama a haka ba, dole watarana xan tafi.
Iman bata da matsalar komai, girma da wayo kawai take karawa abin ta, duk wani abinda za'a bukata nata Anas na samar mata shi tun kafin a nema. Kunsan ance me d'a wawa, hakan ya kara mishi matsayi babba a zuciya ta, ina jin sa kamar wani uba ko babban wa a garemu, ina jin sa kamar wanda aka aiko shi dan ya taimaka wa maraicin mu nida ita a lokacin da muka rasa madafa.
Ina zaune ina ninke kayan ta da na wanke da rana Ramlah ta shigo a gajiya ta fada saman gado tana sakin nishin gajiya
"Makaranta akwai wahala wallahi."
"Bayan wuya?" Nace mata ina dariya
"Kafin dadin fa? Aiko kinga naji labarin ance Post Utme ta fito fa."
"Innalillah, kinji yadda naji, Allah sa muna da rabo, karatun nan shine kadai hope d'ina."
Na faɗa a sanyaye,
"In Sha Allah zaki samu, akwai abokin Baban mu wani professor kuma nasan Ya Anas yayi masa magana, nima dan cut-off mark d'ina na jamb be kai na buk ba shiyasa na chanja northwest."
"Toh Allah yasa,kinga har naji kamar bani da lafiya wallahi."
"Allah sa muji Alkhairi."
Amin nace ina cigaba da aikin da nake, sauya kayan jikin ta tayi ta nufi Kitchen dan samo abinda zata ci.
Da daddare kamar yadda muka tsara Ramlah na koya min karatun daya shafi addini, ba laifi ina karuwa sosai da ita, duk abinda kake da interest akai kana tsayawa ka koya sosai, hakan ce ta faru dani, zama na dasu na gane bansan komai daya danganci addinin ba, daga karatun sallah sai dan abinda ba za'a rasa ba, bana mantawa a makaranta na koyi yadda zan kula da kaina yayin lokacin al'adah. Shiyasa na dage nake takura ta a kullum tana karamin sani a abinda ya shige min duhu.
Da hannun sa rataye a bayansa abinda ya zama masa dabi'a ya shigo dakin namu da sallama, kusan sati guda kenan baya zama sosai a gidan aiki ya masa yawa kamar yadda naji Ramlah na fada, daina karatun mukayi muka maida hankalin mu wajen sa, be ƙaraso ciki ba ya tsaya yana kallon mu, a tare muka hada baki muka gaishe shi, ya amsa a sake kafin yace
"Congratulations, sai jiran admission kinci postutme."
"Alhamdulillah." Na shiga jerantawa, cikin tsananin farin ciki na hau yi masa godiya, rana ta farko dana ga babu wannan cunkushewar a fuskar sa, a sake yake amsa min yana yi yana min wani kallo.
Yana fita muka rufe karatun muka yi dakin Hajiya, dan sanar mata, tayi murna sosai ta saka albarka. Daren ranar ban iya runtsawa ba, tunanin Farouk da yadda zaiji idan yana tare dani kawai nake, tun bayan tsawon lokaci yau naji alamun ina da rabo a rayuwar nan.
Haka na tashi da safe cike da farin ciki da walwala, tsokana ta su Hajiya da Altine sukayi tayi ina dariya. Da wuri muka gama aikin mu da zamuyi ranar na bi Altine kitchen ina kara koyon abubuwan da ban taba sanin ma suna existing ba sai yanzun.
Cikin hukuncin Allah Admission ya fito, sunana na jerin sunayen farko da suka samu, nayi farin ciki ranar nayi kuka sosai na kuma godewa Allah, saboda nasan ba wayo na bane ko dabara ta. Tun daga lokacin na tattara dukkAn damuwa ta na watsa ta a bayana na shiga shirye shiryen sabuwar rayuwar makaranta.
Yadda Ya Anas ya soma chanja min ne ya shiga daure min kai, duk lokacin da yake gida ya kan tabbata da ina falon a zaune, duk hirar da za'a yi sai ya sako ni a ciki, ta karfi da yaji yake kokarin ganin sai na sake dashi, ina lura da yanayin Hajiya kamar bata son hakan, duk sanda zai min wata magana sai ta kawo abinda zai sauya akalar maganar zuwa wata daban da bata shafe ni ba. A haka aka fara registration da screening, shine dai wannan karon ma ya shige min gaba akan komai, sannan duk kudin da aka bukata shi ne ya bada su, duk da naso yin wani abun da kaina sai dai sanin halin sa yasa na hakura na zuba masa ido.
Kwana wajen uku sannan na samu nayi screening din, na gama ina zaune karkashin wata bishiya me dauke da zagayayyun kujeru naji an zauna a gefe na, dagowa nayi da nufin ganin waye, hannu yasa ya nuna ni cike da mamaki yace
"You!" Sai nayi kamar ban gane shi ba na juya kaina gefe. Gefen dana koma ya dawo ya sake zama yana leken fuska ta.
"Ji mana."
"Wa kake nema ne Please?" Na watsa mishi wani kallo, dan tsaf na karance shi dan rainin wayo ne na ajin karshe, sosa kansa yayi kafin yace
"Shit! Kin iya rainin wayo wannan beb ɗin wallahi, kece dai ta ranar Exams din nan na gane ki."
"And so?"
"And so? And so?"
Ya shiga nanatawa kamar karatu , sai kuma ya bigi gefen kujerar yana fitar da yar karamar iska daga bakin sa, sai kuma yayi murmushi m d'an sauti
"Can we be friends?" Yace yana miko min hannun sa,bin hannun nayi da kallo, kafin na girgiza kaina ina sake matsawa kadan
"Bana ƙawance da maza, infact ban ma tab'a ganin ka ba sai yanzu, sai kawai na saki jiki da kai?"
"Kaji matsalar yan matan garin nan kenan, kauyancin masifa. Go to hell!!."
Yace yana mik'ewa, da ido na rakashi har ya bar wajen cikin tafiyar sa ta ya'yan da suka jiku da hutu, murmushi na saki kadan ina mamakin sa. Gefe na kalla ina sake sakin murmushi, ido na ya sauka a cikin na Ya Anas, yana tsaye ya harde hannun sa, fuskar nan tasa a gimtse, da sauri na dauki tarkacen kaya na na nufi wajen sa, bansan tsawon lokacin daya dauka a wajen ba, ina karasawa yaja dan karamin tsaki yayi gaba, na bishi.
Tada motar yayi muka fita daga makarantar, gefen window nake kallo ina ganin yanayin garin, tsaki yake tayi tun da muka fito, ban kulashi ba, haka ban kalli inda yake ba ma balle na san halin da fuskar sa take ciki. Murya a cunkushe ya soma magana
"Idan har kinsan irin wannan ƙananan yaran zaki tsaya kulawa ba karatu ba, sai ki sanar dani tun farko na daina wahalar da kaina."
Juyowa nayi da mamaki na kalle shi, idon sa na kan titi ya hade girar sama da ta k'asa, sai nayi shiru kawai na maida kaina waje ina mamakin fushin sa. Har muka isa gida be sake magana ba, fita nayi na barshi a motar don naga bashi da niyyar fitowa.
Ina shiga na tarar da Altine na ta faman zagaye goye da iman, murmushi nayi na gaishe ta, ba karamin girman matar nake gani ba, kunto min ita tayi na karbe ta na shige ciki.
Dakin Hajiya na leka, na sanar da ita mun dawo, kadaran kadahan ta amsa ta cigaba da abinda take, kwana biyu akwai chanji sosai a yadda take min, sai dai na dau hakan a matsayin wani ɓangare na dan adam, ba lallai ne koyaushe ya zama kamar yadda ka san shi ba, idan ma babu wata matsala ai akwai lalura, zata iya yiwuwa bata jin dadi ne. Sai ban wani damu ba, na cigaba da al'amura na yadda na saba su.
***
*Bayan wata biyu*
Cikin nasara na soma zuwa makaranta, bani da matsala da iman dan lokacin ta fara shan ceareal, wajen Altine nake barin ta bayan na tabbatar da tasha ta koshi, sauƙin ta ma babu ranar da muke wuni a makarantar, duk inda azahar tayi mun dawo, hakan shi yasa nake jin dadin karatun ina kokarin ganin na samu abinda naje nema.
Bangaren Hajiya bani da wata matsala tun bayan rage shige min ɗin da Anas yake, sai ta sake muka koma kamar da, duk ban kawo komai ba.
Ranar wata talata na sauka a titi na shigo layin namu ina tafiya a nutse, nazo daidai wajen wani me dan kiaosk na saida katin waya naji maganar ta, bazan taba mantawa da muryar ba,muryar da zan iya cewa na daya daga cikin abinda ke makale a raina na yarinta ta, da sauri na isa wajen, ido bude nake kallon ta da tsantsar mamaki, idan har idona ba gizo yake min ba, kunnuwa na ba karya suke min ba,toh tabbas Amal ce. A bayan ta na tsaya cikin tsananin farin ciki ina jiran su gama, juyowa tayi da nufin barin wajen, taci karo dani, da wani irin tashin hankali ta ja baya, kamar zata koma cikin kiaosk ɗin
"Amal." Na kira sunan ta cike da farin ciki sai naga ta hau jujjuyawa kamar me neman wani abu
"Amal baki gane ni ba? Aminatu ce fa."
Gaba tayi da sauri har kamar zata fadi, nabi ta da sauri na cimmata ina kwala kiran sunan ta, ja tayi ta tsaya tana juyowa a fusace tace
"Wai lafiya kike bina?"
"Nice fa Amal, baki gane ni ba?"
"Na gane ki, sai akayi yaya?"
Washe baki na nayi ina tunanin matsala ta tazo karshe nace
"Nasan dama zaki gane ni ai, ina su Dadah da Ya Farouk, Allah Nagode ma daka hada mu."
Dariya ta tuntsire da, kafin ta hade fuskar ta cikin isa tace
"Ke wai har yanzu baki manta da su ba, bayan sun manta da kina existing a duniyar nan, kinga karki takura min dan Allah, kar ma ki kuma nuna kinsan ni wallahi, ke da su kuma sai dai idan ana haduwa a lahira."
"Me kike cewa Amal, kina nufin Ya Farouk ya manta dani, Dadah ma haka, idan kowa zai manta dani nasan su ba zasu taba mantawa dani ba,dan Allah ina Ya Farouk ina son haduwa dashi ko dan yar sa dake tsakaninmu?"
Na fada murya ta na rawa, daga min kai tayi, sosai naga yanayin fuskar ta ya sake sauyawa, ambaton yar sa da nayi, ja baya tayi
"Ya manta dake mana, tun da har ya aure ni, nice matar sa a yanzu saboda haka bana bukatar ki kusa da mijina da yan'uwa na, batun ya kuwa ke da kanki kinsan ya ƙaryata tun lokacin rabuwar ku, sai kije can ki nemi uban yar ki, idan kuma shegiya ce sai mu sani."
Jiri ne ya soma dauka ta, na kalle ta ido na na ciccikowa nace
"Amal?"
"Abinda kunnuwanki suka ji haka yake, saboda haka karki bata min lokaci, kinga tafiya ta."
Ina kallon ta ta juya tayi hanyar fita daga layin, kuka nasa sosai, na kasa daga kafata daga wajen, ina kallo ta haura daga layin, tun ina hango ta har na daina, durkushe wa nayi a wajen na saki kuka sosai kamar raina zai fita.
RanoDG
24
★★★
Da kyar na mike kafata da tayi nauyi na karasa gida, a waja na tsaya na goge hawayen fuskata na shiga gidan, da kallo Altine ta bini tana karantar yanayin fuskar tawa, ciki nayi ba tare da na tsaya yar hirar dana saba mata ba.
Ina shiga daki na sake sakin kuka, kuka me cike da ma'anoni da yawa, a yau komai ya dawo min sabo, ina ji kamar a yanzu komai yake faruwa dani, idan har da gaske Amal take, Farouk ya aure ta, to tabbas ya manta dani, ya rufe ni a cikin babin rayuwar sa kenan, idan ko haka ne bai kyauta min ba, bai min adalci ba, bayan ya koyo min yadda zan rayu da son sa, ya tafi ya barni a sanda nafi bukatar sa.
Amal yar uwar sa ce, nasan shakuwar da ke tsakanin su, ban taba kawo hakan a nufin soyayya suke ba, sai yanzu nake hango wasu abubuwan da suka dangance ta din, ta yadda yake yake bata lokacin sa.
Har Ramlah ta dawo daga makaranta ban bar kukan da nake ba, ina ji a raina ina bukatar nayi kukan, ko naji sauƙin zuciya ta, yadda ta tarar dani ne ya sa duk ta rikice, a dan zamana da ita na shaku da ita da har bana iya boye mata damuwa ta, ko ba haka ba ma ina bukatar wanda zai fada ma kuka na ko da ba da nufin a share min kukan ba, sai dai ko yaya na zanji sauƙin abinda ke damuna.
Yanzun ma ban boye mata ba, na sanar da ita komai, girgiza kanta ta hau yi tana dawowa kusa sani sosai kafin tace
"Aminatu har yanzu baki san wasu matan ba, ya zaki yanke masa hukunci da abinda ta fada miki, ina kyautata zaton babu masaniyar sa a komai, a yaya kika ganta? A nutse take alamar wadda take cikin kwanciyar hankali tayi sabon aure, ko kuwa? Kuma baki yi tunanin abinda yasa ta yi miki haka ba? Bayan ko ni nasan yadda kika daukake ta a zuciyar ki? Abu daya ne, kishi take ko dai tayi kokarin samun abinda yake mallakinki bata samu din ba, ko kuma ta samu amma babu kwanciyar hankali."
"Kin batar dani Ramlah, kina nufin Amal nada hannu a komai?"
"Eh haka tunani na ya bani, ko da ba komai ba, amma a wannan lokacin akwai ayar tambaya akan, akwai babban dalilin da yasa tayi miki hakan."
"Taki bani damar da zan san inda take, ballantana na rok'i alfarmar ta hadani dashi ko da na dan sakanni ne, akwai tambayoyin da nake son yi masa ne, sannan na nuna masa abinda ya tafi ya barni dashi, shine kawai buri na."
"Shiyasa nace miki abinda tayi nada alaka da hakan, tabbas bata son haduwar ku dashi ne, idan har ya cire ki a ransa, ba zai ji shakkar haduwa dake ba, ita kuma kai tsaye zata hada ku dan tasan bashi da alaka dake, amma me? Sai taki ta hauki da cin mutunci, Allah ma yaso ta ba tare dani bane, wallahi da sai na saki shegiya na yar a wajen."
Murmushi nayi ganin yadda ta hakikance, sai na zame na kwanta a wajen ina jin kamar wata dama na samu mai muhimmanci a rayuwa ta ta kuma kubce min. Yin ranar haka nayi shi sukuku, abincin kirki ma ban iya ci ba, daren wuri na lallaba Iman tayi barci ni kuma na hau kogin tunani.
Dan buga gadon tayi tana harara ta, sai a lokacin na lura da tsaiwar ta akai na
"Allah ki rage tunanin nan, is not good for ur health,ki taso Ya Anas na kira."
"Bacci fa na fara, Please kice masa nayi bacci kaina ke ciwo kinga kuma ina bukatar hutu."
"Kinsan shi sarai, sai ya zo har dakin, babu ruwana wallahi ki taso ni nayi gaba."
Ganin da gaske tayi ficewar ta yasa na mike da kyar na dauraye fuskata na zura dogon Hijabi na fito, idon sa kur akan kofar dakin namu, ina kallon yadda ya sauke ajiyar zuciya a boye ba tare da sun ankara ba, dauke kaina nayi na karasa na zauna a gefen Amal,.
"Bak'ya gajiya da zaman daki?"
Yace yana kallo na, da sauri Hajiya tace
"Bata fa dade da tafiya dakin ba, kaine dai zuwan ka kenan shiyasa."
"Duk da haka Hajiya, ta fiya takura kanta a daki, ya kamata ki dinga fitowa ana hira dan an riga an zama daya kin gane?"
Daga kaina nayi bance komai ba, maida hankalin sa kan Hajiya yayi
"Ina ganin shawarar siyan adaidaita sahun (babur mai kafa uku) ita kawai zamu dauka kawai, ko hudu ne a samu a siya sai a dinga kawo balance duk sati."
"Hakan yayi, Allah ya taimaka."
"Nace ba, idan tana da ra'ayin hakan sai a hada da ita, idan yaso ita ma sai a dinga kawo mata wani abu duk sati..."
Ya karashe yana kallo na,
"Kina da ra'ayin siyan abin hawa ana miki haya? Kudin ki zai isa ki sai guda daya ko ba sabuwa bace, idan Allah yasa miki albarka sai kiga kin maida kudin kin sayi wata."
Dadi ne ya kamani, dama ina ta tunanin abin yi, tunda zaman ba zai yiwu haka ba, ko ba dan Iman ba ko dan makaranta ta, da sauri na amince, dan shine kawai abinda nasan za'a yi min ɗin ba tare da ya shiga lokacin makaranta ta ba.
Murmushi yayi, daga ganin yadda na amince din yayi masa dad'i, dan shi mutum ne mai son a yarda shi, kuma kai tsaye yake nuna maka yadda yaji game da kai.
"Shikenan, Nagode da damar da kika bani, sai a hada a siya dukka Hajiya, hakan ina ganin yayi ko?"
"Yayi." Tace Muryar ta a dan ciki
"Yauwa Anas, wai ya maganar da mukayi ne tun ranar? Shiru fa nake ji ya kamata kasan abinda kake ciki, shekarun ka kara ja suke."
"Hajiya kenan, ai ina ganin lokaci kawai nake jira na bayyana miki komai, ki tayani da addu'a kawai ta karbi tayi na, dan nasan zaki yi farin ciki sosai da zabi na."
"Ah masha Allah, shine tuni baka sanar dani ba? Ka barni ina ta tunanin wa zan binciko maka a dangi."
"Na hutassheki Hajiya, ke zaki fara sani bayan ita, kuma nasan zaki yi farin ciki sosai dan yarki ce ma."
"Toh madallah, Allah ya tabbatar mana da Alkhairi."
"Amin ya ALLAH."
"Naji kamar kuka ko? Jeki duba ko tashi tayi."
Mikewa nayi na musu sallama, kallon k'asan ido naga yayi min, nayi gaba da sauri ina jin faduwar gaba.
****
Kamar wadda aka koro haka ta shiga gidan tana waiwaye, ajiyar zuciya ta sauke da karfi ganin bata biyo ta ba, lock ta saka wa kofar ta shige ciki. Kallon tuhuma Dadah ta bita dashi kafin tace
"Ina kika je ne nake ta neman ki, baki fada min zaki fita ba kuma."
"Kati naje na siyo, ina so nayi waya na kasa siya ta bank shiyasa."
"Shine kike abu kamar baki da gaskiya?"
"Ni ba abinda nake kece kika ga hakan."
Tayi cikin dakin ta, tana shiga ta murda dan key din jiki ta cire mayafin ta ta haye gadon tana kiran number. Kasancewar akwai rata da tazara me yawa tsakanin su, sannan akwai banbancin lokaci yasa suka tsara sanda zasu dinga magana a waya, tun da tazo gidan sau biyu kawai sukayi waya. Kamar ba za'a daga ba, dan har ta fara cire rai, sai kuma taji an daga ɗin, cikin magana k'asa-k'asa ta shiga bayanin komai, bata wani dau tsawon lokaci ba ta ajiye wayar tana murmushi.
Duk ranar da Farouk ya gama boye-boyen sa zai fito, daga lokacin zai karbe ta a matsayin matar sa, dolen sa ne, tilas ɗin sane hakan,da shi kadai zata iya rayuwa.
Sam tafiyar sa bata dame ta ba tun bayan da aka tabbatar mata da ita din matar sa ce, aure ya dauro, zata jira shi komai daren dadewa, sai dai ba zata taba gangancin barin sa ya hadu da Aminatu ba, wannan Alk'awari ne tayi wa kanta, tunanin yadda akayi ma har Aminatu tazo nan ɗin, ayi sanin ta bata da wasu data sani a garin na Kano, sai gashi ta hadu da ita a lokacin da haduwar tasu tamkar yankewar farin cikin tane, kuma a unguwa daya da wadda take rayuwa a yanzu, shin dama tasan inda Dadahn take zaune ne ko kuwa co-incidense ne? Amma ta yaya? Idan har ta sani ba zata nemi ta kawo ta ba ai, toh amma? Kanta ya cunkushe ta rasa kalar tunanin da zata saka.
Koma dai menene, ba zata taba barin ta ba, ko da kuwa hakan na nufin tonuwar asirin dake rufe shekaru masu yawa ne!
★★★
Riga ce karama da dogon wando a jikinsa ya dora doguwar Jacket a sama, kansa ruf da woody cap sai bakin glass me matukar duhu daya rufe ilahirin kwayar idon sa, tun sanda abin ya faru yake cikin garin na Lagos, bai taka ko nan da chan ba sai a yau da zai bar k'asar, bolt ya kira suka zo har gaban hotel din daya sauka ya fito suka dauki hanyar filin jirgi.
Sai da ya daidai ta a cikin jirgin sannan ya ciro wayar sa ya kunna, sakonni suka fara shigowa, sai daya tabbatar sun gama shigowa tsaf,sannan ya saka wayar a airplane mode ya shiga duba sakonnin.
Daga na Daddy, Mummy, Ja'afar, Amal sai Dadah ne kowanne da abinda yake cewa, kai tsaye ya goge dukka baya son jin komai daga gare su, idan ba so suke su k'arasa shi ba, dan a yadda yake jin zuciyar sa yasan tabbas ba daidai take ba.
Gyara kujerar sa yayi sosai ya kwanta, sakonnin su kadai sun sashi ya tuna da komai. Zuciyar sa ba zata taba daukar cin amana daga mutane uku ba, Ja'afar, Amal da Dadah! Sune mutanen da ya yarda dasu fiye da kowa a duniya, fiye da iyayen da suka kawo shi duniya. Amma ta yaya hakan ta kasance? A lokacin daya gane akwai sa hannun Amal bai shiga tashin hankali ba kamar sanda take sanar masa da komai, Dadah! Why? Ya kasa gasgata hakan, gashi ya gaza samun hujjar da zata kare daya daga cikin su, shiyasa ya gaza hakuri, ya kasa juriya, ya bar su, bari na har abadah, duk kuwa da yana sa ran haduwa da Aminatu komai daren dadewa, sai dai akwai lokaci, kafin sannan, yana fatan Allah ya bashi aron rai da lafiyar da zai iya fuskantar ta, ya kuma nuna masa gaskiyar komai.
A hankali sanda jirgin su ya lula sama sosai ya furta!
"Sai wata ranah!"
★★★★★
Kullum idan na dawo daga makaranta sai nabi hanyar ko zan sake ganin ta, sai dai ko mai kama da ita ban sake haduwa da ba, tun ina saka rai har na hakura na cire na barwa Allah komai na rungumi karatu na, duk bayan sati biyu ake kawo mana balance, da su nake amfani wajen hidimar makaranta ta da abinda ba za'a rasa ba, tun Anas na fada har ya daina ya zuba min ido, daidai gwargwado yana kokarin sa a kaina duk da hakan, tun da mafiya yawancin lokuta shine yake ajiye ni a makaranta,bana cin komai har naje na dawo shiyasa ba wani kudi nake kashewa ba, nidai burina nayi karatun na taimaki kaina da yata.
Tun bayan fara zuwa na makaranta haduwar mu wajen bakwai da Kamal d'an gayu, duk sanda ya ganni sai yayi kokarin min magana a haka har na saki jiki dashi muke gaisawa, anan na gane course din da yake business adminstration. Na lura kwarai ba karamin dan masu kudi bane duba da yadda mutane keyi masa a duk lokacin da suka ganshi, bashi da girman kai ko kadan sai dai dan gayu ne na ajin farko, kullum cikin sabuwar shiga yake komai masa abin kallo ne tun daga kayan sawar sa har zuwa takalman da yake sawa.
A hankali sabo ya shiga tsakanin mu, har mu kan zauna muyi hira duk da bata fita tsawo ba, kullum maganar sa guda daya ce Kakar sa, ko da zaman mintuna biyu kayi dashi zaka tabbatar da irin shakuwar da ke tsakanin su, tabara da tsantsar gata take nuna masa fiye da tunanin mai tunani.
A off-campus yake zaune, gida guda ne yake zaune a cikin sa, duk da ba karamin takura yayi ba a yadda ya saba, amma hakan yake zaune ala dole bisa tursasawa mahaifan sa, duk weekend a gida yake yi, sai Monday da safe yake dawowa wani lokacin ma sai Tuesday, bashi da matsalar komai duk abinda yake so shi yake yi.
Ina ta sauri zan fita daga makarantar ganin yau har la'asar ta taho ban isa gida ba, mota ce ta tsaya a gabana,na daga ido na dubeshi, daman nasan sai shi, fitowa yayi ya tako har wajen da nake, ina sanye da dogon Hijabi maroon har k'asa, sai jakata dake makale jikin sangalalin hannu na.
"Gida kikayi ne irin wannan sauri Meena?"
"Wallahi yau na dade, shiyasa nake ta sauri."
"Lemme drop you mana idan ba damuwa."
"A ah Ina, bashi na samu bus ta fita dani, see you."
Nayi gaba ina nufar wajen da cincirindon mutane suka kowa na jiran abin hawa, dage kafadar sa yayi ya jingina jikin motar sa yana kallon mu, mota daya ce tazo, aka hau rububin hawa, kasa shiga nayi ina kallo aka cika ta, na sake matsawa gaba. Tsawon lokaci muka dauka shiru babu alamar zuwan wata motar, gashi ranar kudi na kenan, idan nace zan fita titi na hau normal abin hawa ba zai ishe ni ba, waigawa nayi gefe na hange shi still yana inda na barshi, muna hada ido ya saka dariya yana turo bakin sa alamar gwalo, da sauri na dauke kaina na yi gaba ina sauri ganin wata motar ta tawo, ita dinma hakan ce ta kasance, ina kallo aka gama shigewa aka barni, dafe kaina nayi dake ciwo na sake kallon sa, gani nayi ya fada motar sa ya bata wuta, yazo ya wuce ni, duk sai naji babu dadi, na hau takawa a kafa, ga yunwa gashi rashin nawa Iman abincin ta da banyi ba yasa duk sun cika sosai har na fara jin zazzaɓi na neman rufeni.
Tafiya nayi mai nisa kafin na isa gate ina yi ina haki, a wajen gate din na hangi motar sa a fake a gafen titi, an bud'e kofar mai zaman banza daidai inda zan wuce, har zan dauke kaina muryar sa ta iso min tun kafin na karasa
"Miss... da kin cire komai kinzo na ajiye ki, after all ba cinye ki zan ba, idan ma na cinye ki, za'a iya kamani ai tunda nasan za'a ce an ganni tare dake last."
Bani da zabi, ila na shigan, a hankali na ja kafafuwana na zauna ina cin magani, dariya ya sa ya ja muka tafi yana yan kananan wake-waken sa da harshen turanci.
Hanya na dinga nuna masa har muka isa, sosa kansa yayi yana kallon unguwar,
"Kinga fa akwai gidan da Daddy yaso na zauna anan unguwar naki, babu nisa daga gidan ku."
"Kafi so ka zauna Off-k kaci karanka ba babbaka ko?"
"No ban saba squatting bane a rayuwa ta, kinga ba zan fara yanzu da girma na ba."
"Yayi, nagode sosai, sai Monday idan Allah ya kaimu."
Nace ina balle murfin motar. Daga min hannu yayi ya bar unguwar, na juya da nufin shiga gida, gabana ya fadi ganin shi a tsaye yau ma kamar ranar, ya harde hannayen sa a kirjin sa, fuskar nan tasa kamar wuta. Dakewa nayi naje zan wuce ta kusa dashi, hannun sa ya sauka a cikin hannu na, da wani irin karfi yasa ya fizgoni, ya tura ni cikin gidan, kamar zan fadi nayi saurin tsayawa a kafata fuska ta dauke da madaukakin mamaki.
Da hannu ya nuna ni, cikin tsananin bacin rai ya soma magana
"Baki isa ba wallahi,kinyi kadan kina kawo mana samari kofar gidan, samarin ma na jami'a, kanana yara wanda basu mallaki hankalin kansu ba, uban me wannan dan yaron zai baki, shiyasa kika yi zaman ki a makarantar bayan yau da wuri kuke gama lecture ko?"
"Ban gane ba." Nace ina matsawa baya ganin yadda yake matso ni
"Dama ba zaki gane ba,haka zaki ce kullum akayi miki magana, U act as if baki san me mutum yake ciki ba..."
Dukan kirjin sa yayi da hannun sa biyu
"Can't you see how much I love you? Nace baki gane ba? Ke makauniya ce? Baki da ido? Ko baki da wayo? Ba zan dauka ba, ke tawa ce, mine and mine alone! Kin gane? Get it straight to your filthy head, ni zan aureki saboda haka bazan dauki ganin ki da kowanne kazami ba."
Daya bayan daya na hau kokarin fahimtar maganganun sa, kamar ya zare haka ya cigaba da magana yana sake nufo ni, yaki bari na sam na gama digesting kalaman nasa, wasu yake kara min akan wasu, a bayan mu muka ji salati, muka juya da sauri gaba daya
"Na shiga uku,Anas mai zan gani? Tsintasshiyar magen zaka aura? Innalillah wa inna ilaihi raji'un, abinda nake gudu ya faru."
RanoDG
25
★★★
Jingina nayi da jikin bangon, cikin tsananin mamaki naga ya kalli hajiyan, kafin ya soma magana a hankali kamar ba shine ya gama min ihu aka ba yanzu
"Hajiya? Aminah ce fa? Nayi tunanin duk daya kika dauke ta da Ramlah."
"Dah kenan kafin ka fara nuna alamun soyayyar ta, karka manta hausawa sunce tsintasshiyar mage bata mage ko? Shikenan daga taimako sai aure? Baka san kowa nata ba? Ta yaya kake tunanin ni mahaifiyar ka da dangin mahaifin ku zasu amince? Ina ba zai yiwu ba."
"Amma Hajiya d'a na kowa ne, kuma ƙaddara babu wanda ba zata iya fadawa ba, dan Allah karki ce haka."
"Na fika sani ai, ko zaka sake maimaita min ne?"
"Ba haka bane Hajiya, iya dan zaman da kikayi da ita, kinsan bata da matsala, dan Allah karki hana abinda Allah bai haramta shi ba dan Allah Hajiya."
"Duk nasan wannan Anas, inji dai nice na takura aka taimaka mata? Ko banyi mutunci anan ba? Shikenan dan nace ba zaka aure ta ba zaka nemi gayan magana ko?"
Dafe kansa yayi idanun sa na komawa ciki, bai sake magana ba, sai ya juya da sauri ya bar gidan baki daya, kaina ta juyo,ta sakar min harara kafin ta juya ta koma ciki, tana maganganu k'asa kasa
Mai yake faruwa dani ne? Mai nayi haka mai zafi da kowa yake k'yamatata? Shikenan a haka zan kare? Daga na soma farin ciki sai wani al'amari ya gifta. Da kyar na iya kai kaina dakin Ramlah, da nake jin tabbas zamana a cikin sa ya kusa zuwa karshe, chan kuryar gado na makure kaina, na shiga kuka a hankali ina jin kamar na kare rayuwata na huta da komai.
Tsawon lokacin dana dauka a dakin babu wanda ya leko ni, tun bayan da Altine ta miko min Iman nake zaune a lungun, da kyar na lallaba nayi sallah na goya Iman na shiga hada kayanmu. Ina yi ina kukan inda zan kama nida yarinta ta.
A hautsine ya shigo dakin tana wara idon sa, da sassarfa ya ƙaraso gareni, ya sa hannu ya fincike jakar hannu na
"Me kike shirin yi?"
Bance komai ba, ya sa hannu ya cire komai na jakar ya ajiye a gefe, karo na biyu da ya sake kama hannu na, ya shiga jana muka fito daga dakin, dakin Hajiya naga ya nufa zuciya ta ta sake tsinkewa, tura kofar yayi ta dago tana kallon mu, kasa tayi da kanta zuwa hannayen mu dake makale kafin ta juyar da kanta gefe, a k'asa naga ya tsuguna, nayi saurin durkusawa nima.
"Ina neman yafiyar ki idan har abinda nayi dazu ya bata miki, banyi da nufin na saba miki ba, dan Allah kiyi hakuri, kar kice zaki yi fushi damu akan hakan, ko kice ta bar gidan dan Allah."
Sake juyar da kanta tayi bata ce komai ba, sai ya dora da
"Na janye maganar da nayi dazu, na hakura da komai dan Allah Hajiya ki koma kamar da, taimakon da kika yi niyya ki karasa Allah zai baki lada."
"Kana nufin ka ajiye batun auren ta."
"Na janye, Allah ya baki hakuri."
"Shikenan, da har ina tunanin ko ka zaɓe ta ne akaina, tunda haka ne babu matsala zanyi kokarin ganin komai ya wuce, sai dai kaima tilas kayi min alƙawarin babu wani abu da zai sake shiga tsakanin ku da sunan soyayya."
"Nayi Alk'awari!"
"Tashi ka je zanyi magana da ita."
Kallo na tayi kallon tsaf, ta kalli Iman dake goye a bayana ta murmusa kadan
"Karki yi tunanin ko akwai wani mugun hali da kike dashi, duk da ance mugu baida kama, ki daura kanki a matsayina, ke uwa ce tunda kin haifa."
Gid'a mata kai nayi ba tare da nace komai ba,
"Ki koma dakin ku, komai ya wuce, sai dai duk ranar dana sake samun abu makamancin wanann, toh kiyi hakuri gaskiya sai dai ki tafi."
"Nagode hakan ma ba zata faru ba."
"Yayi."
Guiwa a sake na fita, maimakon na koma dakin, sai nayi harabar gidan, na samu wani lungu na zauna ina kuka na, kukan rashin gata da rashin yanci, a yau da ina da inda zanje, ba zan kara ko da sakan bane a gidan nan, sai dai zama na anan ɗin shine kawai rufin asiri na, ya zanyi da rayuwa ta.?"
****
Tun daga lokacin Hajiya ta koma kamar da, kadaran kadahan, bangaren Anas kuwa baya shiga harka ta, magana ma baya iya yimin, hakan sai yafi min dadi dan na lura Hajiya na ankare da komai.
Sosai na chanja da yadda na d'an saba da a gidan, komai nake kaf-kaf dashi, zaman falo sai ya zama dole nake yin sa, rayuwa ta gaba daya a makaranta nake, dan ma akwai nauyin Iman, haka dai aka gurgurawa tsakanin chan da nan ɗin.
Sabo sosai ya sake shiga tsakani na da kamal, ni kaina ina mamakin yadda na saba dashi din, sai dai duk da sabon da mukayi akwai limit din da bana yarda yayi crossing, Ina kokarin ganin na kare mutunci na, wanda na lura hakan na kara min kima da daraja a idanun sa.
Ranar muna hira nake sanar mishi ina da 'ya, sosai yayi mamaki dan bai taba tunanin hakan ba, damuna ya hau yi akan lallai sai nazo da ita makaranta, k'i nayi ganin ya dage yasa na masa alkawarin zuwa da ita ranar da nake da lecture gajeriya.
Haka kuwa akayi, na cika masa alƙawarin nazo da ita, ranar kuwa naga tsantsar kulawa da soyayya kamar ya kwace ta ya gudu, ba inda bai zagaya da ita a makarantar ba,hakan da yayi kuwa ba karamin faranta min yayi ba, mai d'a wawa inji hausawa, sai na k'ara masa babban matsayi a zuciya ta.
Rayuwa ta cigaba da garawa, a kullum zuciya ta a matse take da tunanin abinda zai je ya dawo.
Bangaren karatun mu komai yana tafiya yadda ya kamata, tuni muka cinye zango na daya dana biyu na karatun shekarar farko, hutun da aka tafi ne ya sani zaman gidan dole, zuwa lokacin Iman tayi wayo sosai, dan har ta fara takawa abin ta, Altine, Ramlah sune kadai nake sakewa dasu, sai Kamal, shima hutun nan ya saka na bar ji daka gareshi, dama bani da yawa kuma bani da muradin ta a yanzu, kudin da ake kawo min balance na cigaba da ajiye abuna sai idan zanyi wata bukata tawa. A haka har muka cinye hutun muka koma makaranta
Watarana muna zaune nida Ramlah, tana tsefe wa Iman kai, Hajiya na kwalo mata kira, karbar kibiyar nayi na cigaba da yi mata ita kuma ta fita zuwa kiran, jim kadan sai gata ta dawo da sauri tana dafe da kirjin ta.
"Aminatu, kinsan me?" Tace tana zama a gefe na jiki a sanyaye
"Menene?"
"Akwai matsala, Yaya Anas an masa transfer daga Kano zuwa Abuja..."
"Ah Masha Allah." Na katse ta ina murna
"Shine kuma zaki shigo kamar anyi mutuwa, ai abin farin ciki ne."
"Hmm." Tace tana girgiza min kai
"Ba wannan ba, kinsan wai Hajiya garin mu zata koma da zama yan uwanta sun ce ta koma, tunda shi Yaya Anas ɗin barin Kanon zai, ni kuma wai tunda saura shekara daya sai na k'arasa a hostel."
Yadda naji maganar sai da na saki kibiyar hannu na, sai na duburburce, na kasa magana, da kyar na tattara natsuwa ta nace
"Allah sarki, toh shine me?"
"Wai baki gane ba? Idan Hajiya ta tafi aina zaki zauna? Ashe shiyasa tun jiya nake ta jin suna maganganu da Ya Anas, ina ga ma shiyasa yau yayi asubanci ya tafi chan garin nasu Hajiya, nasan ba zai yarda ba."
"Karki damu, Allah na tare dani, duk yadda ya tsara min rayuwa ta ina maraba da hakan, so karki damu Allah, karki kuma ce zaki yi wa Hajiya maganar."
Bina tayi da kallo ganin na mike sabe da Iman na dora ta saman gado, ajiye kibiyar nayi na fada toilet ina jin wani tashin hankali na ziyarta ta.
Kwana biyu tsakani ina lura da yadda mutanen gidan ke mu'amala, tabbas akwai matsala dan har na kan jiyo muryar Hajiyan wani lokacin a sama, da alama fada take masa.
Da daddare na shirya bayan kowa yayi bacci, na zura dogon Hijabi na, na fito a hankali na nufi bangaren sa, yana zaune system a gaban sa yana aike kamar kowanne lokaci, ta windon dakin sa na hango shi, zuciya ta na bugawa nasa hannu na kwankwasa, sai daya fara duba agogon dake manne a jikin bangon dakin kafin yace
"Waye!"
A hankali cikin magana k'asa nace
"Nice."
Matsar da komai yayi daga gabansa ya taso, ya janye kofar, da kallo ya bini cike da mamaki, sai naga yaja baya yana nuna min kofar, girgiza kai na nayi, na nuna masa dan dandamalin dake daura da wajen wanke wanken su ina nufar wajen, sakin kofar yayi ya biyo bayana muka zauna.
"Lafiya ? Ko Iman ce bata jin dadi?"
"A ah,alfarma nazo nema,bana son Hajiya ta ganmu na jawo maka fushin ta shiyasa nazo yanzu, kayi hakuri dan Allah."
"Ina jin ki, mai ya faru?"
Dan matsawa nayi ina juya maganar kafin nace
"Dan Allah so nake dama a siyar da adaidaita sahun a kama min haya."
"Haya kuma?"
"Eh."
"Me yasa? Kinsan illar zaman mace ita kadai? Beside ma at your age zaman ki kadai akwai matsala, me ma ya kawo wannan maganar ne ma wai ni?"
"Nasan zama na ni kadai akwai hatsari, sai dai dama ba gida ni kadai ba, gidan da akwai mutane a ciki, wanda zan iya zama tare dasu."
"Ba zai yiwu ba, nan gidan fa? Ko wani abun akayi miki?"
"A ah, kawai nasan halin da ake ciki ne, bana so ku cigaba da jayayya da mahaifiyar ka, shiyasa na yanke wannan shawarar."
Ido ya zuba min, har sai dana ji nauyi, na dora kaina a saman cinyata, ajiyar zuciya naji ya sauke da karfi, kafin yace
"Shikenan zanyi yadda kika ce, sai dai ba yana nufin kin bar idona bane, zan cigaba da dukkan yadda na fara, zan saka ido akanki, karki yi tunanin rayuwar ki ce zakiyi yadda kike so, ina nan ina kallon ki."
Murmushi nayi, sai naga shima ya sakar min murmushin, kasan makoshinsa ne naga yana motsi alamun akwai abinda yake son fada ya kasa, sai na mike da sauri ina kokarin barin wajen, kamar an fuzgo maganar haka ta fito
"Zuciya ta ta kasa sukuni daga lokacin dana dora ido na akan ki, ina fatan sakkowar Hajiya anan kusa, ina jin kamar numfashi na zai yanke a duk sanda nayi tunanin hakan zai iya daukar lokaci."
Ban juya ba nayi saurin shigewa, ina dora hannu na a saman zuciya ta, tsoro ne fal a cikin ta da tunanin makomata. Ya Farouk! Ya ambata a hankali ina jin kamar zanyi kuka
"Daga ina kike?" Tace tana tsaye a dokin kofar dakin ta, hanunta goye a bayan ta, fuskar ta babu walwala ko kadan
Dan zubura nayi dan banyi tunanin akwai mutum ba, sai na hau in-da-in-da kamar mara gaskiya, kwafa naga tayi ta nufi hanyar fita daga falon, da sauri na nemi hanyar dakin Ramlah na fada ina saka mukulli.
****
Da safe na dauka zatayi min magana, sai naji bata ce komai ba, tun ina nokewa har na share na cigaba da sabgogi na, kwana uku a tsakani naga suna ta haɗa kaya waje daya, babu wanda yace min komai, sai kawai nima na shiga hade kayana waje daya ina tunanin ko ya nema min inda zan zauna ɗin kamar yadda na roka.
Kiran Hajiya ya riske ni har daki, zuwa nayi na russuna a gabanta nace gani, bayani ta shiga kwararo min, wanda na riga na shirya musu dama chan, maganar dai akan abinda Ramlah ta fada min ne, sam banji haushi ko bacin rai ba, da ace ma sai lokacin ne na sani dole na damu, amma na riga na yanke wa kaina hukuncin da nake ganin shine daidai ta rayuwarta, dan babu wani da zai kuma tsaya min dole na koyi tsayawa da ƙafafuwa nah.
Har ta gama jawabin ta ban chanja daga yadda yanayi na yake ba tun farko, ina kallon yadda take mamakin rashin ganin tashin hankali a tare dani, sai ma godiya da na shiga kwarara nata ina rokon Allah ya saka mata da alkhairi. Duk sai naga jikin ta yayi sanyi, ban bi ta kai ba na koma daki na cigaba da tattare abinda nasan nawa ne.
Ransa a bace yake saka min kayan a bayan motar, Ramlah banda kuka babu abinda take yi, ni kuwa zuciya ta k'ek'ashe ko kukan ma bana ji, gwara na tafi tun da sauran mutunci na kafin na rasa tudun dafawa, Altine ce ta fito rike da kayanta, kallon mamaki na bita dashi, ta saka kayan nata itama sannan ta dawo wajen da muke tsaye ta karbi Iman, sake jingina nayi sosai da motar ina duban gidan. Hajiya ce ta fito, ta tsaya a jikin kofa tana kallon mu, babu wanda tayi wa magana har muka shiga motar, Ramlah ta shiga gaba nida Altine muka zauna a baya ya ja motar. Hannu naga ta daga mana, sai a lokacin naji wani iri, tabbas ko ba komai ta taimaka min, fiye da Inno dana dauka a matsayin mahaifiya amma ta rufe idon ta, ta koreni a cikin yanayin da ko makiyina bana fatan ya riski irin sa.
Gidana madaidaici, mai dauke da zaure da dan karamin daki, sai farfajiyar tsakar gida da daki ciki da falo da toilet sai kitchen, akwai ruwan fanfo a gidan sannan akwai yar karamar rijiya daga gefe, kayan mu muka shigar ina karewa ko ina kallo, dan karamin gida ne sosai da bai fi rayuwar mutum guda ba. Babu komai a falon sai tiles, dakin kuwa katifa ce katuwa a kasa sai yar karamar kujerar katako daga gefe. Kitchen ma haka yake, daga yan tuk'wane guda biyu sai plate da spoons sai yan kofuna da abinda ba za'a rasa ba. Sai kayan abinci
Sosai tsarin yayi min, har bansan sanda nayi murmushi ba, Ramlah na lura dani, taki sakin jikin ta sai faman goge fuska take ta kasa zama ma.
A tsakiyar falon ya tsaya, bai zauna ba ya kira sunana a kausashe
"Kamar yadda kika nema, a gida nan an samu,amma ban saida miki abin sana'ar ki ba dan tabbas nasan zai taimaka miki, na riga na biya kudin shekara biyu, zuwa lokacin muka abinda Allah zaiyi, ki riƙe mutuncin ki, ki riƙe mutuncin ki, zan cigaba da bibiyar dukkan al'amarin ki koda bana nan, ga Baba Altine nan, ita zata zauna daki, ki girmama ta kamar yadda zaki girmama mahaifiyar ki."
Kuka ne ya taso min, na shiga yin sa babu kakkautawa, bansan me zance masa ba, bansan da wanne bakin zan gode masa ba, bani da abinda zan saka masa kokarin sa, sai dai zan cigaba da yi masa addu'a har karshen rayuwa ta, tabbas Anas mutum ne, mai daraja da kima a idanun Aminatu.
Ina kallo suka tafi suka barmu da kewar su, munsha kuka sosai nida Ramlah, sai da yayi mana alkawarin zumunci da juna sannan muka sarara
Wayar da ya bani sanda zasu tafi na cigaba da jujjuyawa a hannu na, numbobin mutane biyu ne kawai a ciki, tasa da ta Ramlah, ajiyewaa nayi na kwanta lamo a bisa katifar ina jin sabon yanayi na shiga ta.
*****
*FAROUK*
Haka yake jikin sa babu dadi tun zuwan sa k'asar, a yau ya tirsasa kansa zuwa ganin likita, saboda haka ya shirya ya nufi dan karamin asibitin dake kusa dashi, bayan dukkan tsare tsaren da suka kamata ya shiga dakin likita, mace ce wadda a ƙalla zatayi shekaru arba'in, da fara'a ta karbe shi, duk da banbancin fata da kuma addini, kai tsaye yaji ya sake sake da ita ya sanar mata abinda yake ji, dubawa shi tayi, sannan ta bashi magunguna da shawarwari, godiya yayi mata ya fito.
A kafa yake takawa rike da ledar magungunan sa, hankalin sa gaba daya baya tare dashi, ji yayi sunyi karo da mutum ledar hannun sa ta watse a kasa.
Fuskar sa fiye rabi a rufe take da doguwar hular sanyi wacce ke cike da zare, a tare suka tsuguna da niyyar kwashe magungunan mutumin ya riga shi kai hannu ya shiga tattare wa, tashi Farouk yayi ya tsaya yana kallon sa, bakin fata ne daga yanayin hannun sa, sai dai ya kasa ganin fuskar sa,miko masa ledar yayi ba tare ta ya bari sun hada ido ba yace
"Sannu, ka dinga dubawa idan kana tafiya."
Yayi gaba da sauri, da hanzari Farouk yayi nufin binsa, sai yaji kamar an rike shi, zubawa bayan sa ido yayi yana tunanin dalilin da ya sashi jin wani iri game da mutumin.
****
Gaba daya Daddy ya zama wani iri, bashi da walwala, komai yana yinsa ne amma ba a cikin kwanciyar hankali ba, haduwar da sukayi da Mummy a wani waje ya saka zuciyar shi sake karyewa da komai, maganganun data gasa masa masu zafi ne, sun kasa barin zuciyar sa, tilas yake binsu ko da yaushe yana sake nazarin su.
Shawara ya yanke da zuciyar sa, abu daya ne yake ganin shine mafita, idan ya tuna abubuwan da suka faru da Farouk da yadda yake nuna bashi da masaniya akan komai, ya sake tabbatar masa da akwai babbar matsala a cikin ahalin nasu, a tunanin sa komai ya riga ya wuce ne tun bayan da ya aiwatar da kudurin zuciyar sa, sai dai ya kasa yarda da hukuncin nasa, musamman da yake ganin abinda hakan ya haifar a yanzu.
Waye kuma yake son ganin bayan su? Shin akwai alaka da abinda ya faru a baya da na yanzu? Lallai akwai bukatar komawa baya domin bin diddigin komai! Ya zama dolen sa, ko dan samarwa sauran yaran sa na baya ingantacciyar rayuwa. Diary d'insa ya ciro daga cikin jerin tsofaffin littafan sa, ya bude ya shiga bin shafukan daya bayan daya, har zuwa sanda komai ya soma.
★★★
Shekarun Baya!
****
Oya kowa ya daura belt din sa.🚵🚵🚵🚵🚵🚵
Kun shirya??????
Idan kun shirya zamu shiga ainihin labarin na Daurin Goro. Shin ko zamu fara warware wasu zararrukan labarin ne? Ko kuwa wani daurin zamu k'ara yi? Muje zuwa.🚵🚵🚵
Rano[8/6, 2:43 PM] +234 808 540 5215: DG
26
BARKA DA SALLAH!
★★★
Asalin su shine jihar ta Katsina, tun yarinta shakuwar su babba ce tunda daya baya iya komai ba tare da daya ba, sun shaku matuka har zuwa girman su babu abinda ya chanja na daga yadda suke.
Asalin amintar su ta fara ne daga kusancin iyayen su maza, kar kawo yanzu.
Kabir Aliyu Shagari kenan da aminin sa Marwan Muhammad Dikko. Duk inda kake neman shakuwa da yarda da juna toh sun hada, tare suke komai tun daga matakin farko na rayuwa har zuwa shigar su jami'a.
Tafiyar su jami'a bisa mabanbantan ra'ayi be sa sun chanja ba, Kabir ya zabi bangaren aiki soji inda ya tafi makarantar horar wa dake garin na Kaduna, inda Marwan ya zabi tafiya jami'ar ta Ahmadu Bello dake garin na Zaria. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya cikin nasara.
Kasancewar shi Marwan d'a daya tilo wajen iyayen sa yasa shi kara shakuwa sosai da aminin nasa, saboda babu wani wa ko k'ani da zasuyi shawara sosai. Masu arziki ne na gaske, abun kwatance a kaf fadin yankin su .
Kabir su uku ne wajen iyayen su duk maza, shi ne na farko sai kannen sa Adamu da Ahmadu. Mahaifiyar su da suke kira da Dadah mace ce mai kirki da sanin ya kamata. Tana da abokiyar zama guda daya sai dai Allah bai sa ta haihu a gidan ba har zuwa lokacin da maigidan ya rasu ta tattara ta kama gaban ta, duk da hakan har yanzu suna gaisawa da juna.
Bayan rasuwar mahaifin su komai ya dawo hannun Kabir, shine ya tsaya tsayin daka wajen ganin ya kula da abinda mahaifin su ya bar musu, ya kuma cigaba da kula da yan uwan sa.
Cikin hukuncin Allah komai ya dinga tafiya musu cikin nasara da daukaka.
***
A gaggauce ya shirya yana yi yana duba agogon dake daure a tsintsiyar hannun sa, karo na shida kenan da yake faman kiran sa akan an fara baya wajen, cikin sa'a ya gama shirya wa ya dauki hanyar jami'ar.
Yana isa yayi saurin dukawa kansa a k'asa yace
"Tuba nake ranka ya dade."
Harara ya sakar masa, ya bigi saman kafadar sa cikin jin haushi yace
"Allah ka iya jirga mutane, da ban azalzala ka ba da shikenan sai ayi babu kai."
"I'm deeply sorry oga."
Ya sara masa yana kokarin cire hular kansa, da wani irin shock ya tsaya yana kallon su, yan mata ne su biyu cikin shiga iri d'aya sai dai d'aya ta girmi daya duba da yanayin shekarun su
"Kb!"
Ya kira shi da d'an ƙarfi ganin yadda ya bada attention d'insa gaba daya wajen su.
"Man nayi farin zuwa, wallahi naganta, no wonder naji sai na tsaya na tsara kwalliya ta ashe yau zan hadu da future d'ina."
Dariya Marwan yasa ya kama hannun sa.
"In dai Abidah ce kamar yadda naji ana fada ba sauraran ka zatayi ba, amma wacce kake so cikin su? Karamar ko babbar?"
"Babbar, itace Abidah?"
"Wai, toh ka gwada sa'ar ka, nidai babu ruwana idan ta wulakanta ka."
Gyara wa ya shiga yi sosai
"Aiko zan gwada, nasan nafi karfin wulakanci wallahi."
"Owk best of luck, bari na matsa ciki kafin a fara, kuma wallahi ka zama kusa dan zan neme ka."
"An gama my guy."
A chan nesa ya hange su, suna tsaye gefe suna kallon yadda ake gabatar da taron convacation ɗin, magana suke kasa kasa da juna, kai tsaye ya isa wajen cikin gwarewa ya shiga introducing kansa, duk suka zuba masa ido suna kallon sa, dan murmushi tayi kawai bata ce komai ba, karamar ce ta amsa masa suka shiga hira kamar sun saba, da haka ya hilace su har ta saki jiki dashi, cikin dan kankanin lokaci suka saba, ta ware sosai tana amsa masa,tun daga lokacin shikenan suka saba, soyayya ta shiga tsakanin su.
***
Bayan Aure!
Part uku ne sai na Dadah dake gefe, baya zama saboda yanayin aikin sa, hakan yasa ka shakuwa mai karfi shakanin ta da Adam da Aliyu, bata da matsalar komai duk sanda yazo yakan yi two weeks sai kuma wani dogon lokacin. Kasancewar Dadah mace wadda tasan ya kamata yasa suke zaune lafiya kowa yana mutunta kowa.
A lokacin ne Marwan yayi aure ya auri wata yar zaria, basu wani dade ba auren ya mutu tun da ya ji tana waya akan yadda take so dukiyar sa ta dawo hannun ta, ya tattara ya watsar da duk wata maganar aure ya cigaba da zaman sa haka nan.
Rayuwar ahalin Dadah rayuwa ce mai dadi da kaunar juna.
Shekaru biyar da auren Kabir da Abidah Allah ya azurta su da samun d'a namiji, wanda take Dadah ta zaba masa sunan mahaifin ta Umar Farouk, dukkan soyayyar da d'a yake nema wajen mahaifin sa Uncle Aliyu kamar yadda Abidah take ce masa ya karbe ta, shine yake masa komai na uba saboda rashin zaman mahaifin sa.
A lokacin Marwan ya sake auren har mata biyu suma duk abu daya ne ke kawo su data farkon, gashi duk cikin su babu wadda ta haihu sai dai suzo su tafi.
Kanwar Abidah mai suna Safiyya ta gama karatun ta, ashe dama soyayya suke da Aliyun babu wanda ya sani, hakan ya kara faranta ma Dadah dan ta gamsu da Abidah saboda haka zata so su kara hada zuri'a.
Rikon Farouk ya koma kachokam wajen Aliyu da Safiyya bayan auren, su ka cigaba da zaman lafiyar su cikin kauna da kwanciyar hankali.
***
Cikin kankanin lokaci dukiyar Marwan Muhammad Dikko ta bunkasa. Samun aikin sa a PTDF ya sa dole suka tattara suka koma garin na Abuja, kasuwanci ya cigaba yana juya dukiyar su, daga shi sai mahaifiyar sa har lokacin baya maganar aure, babu yadda aminin sa bai masa ba amma sam yaki maganar auren da uzurin har lokacin bai samu wadda tayi masa ba.
Gini ya fara a hade da juna guda biyu, komai iri daya sai dan banbancin girma, abun da akwai kudi ba'a wani dau lokaci ba ya kammala. Yanayin aikin Kabir yasa har aka gama ginin be san komai akai ba, mukullin gida kawai ya damka masa a matsayin kyauta ya zauna har karshen rayuwar sa. Ba karamin murna yayi ba, saboda bai taba zato ko tsammani ba, nan suka hau shirin tariya suka tattara komai suka koma garin na Abuja har Dadah, duk da Safiyya da Aliyu basu ji dadin tafiyar tasu ba, amma sun san hakan wani cigaba ne, dole suka bisu da fatan alkhairi suka rabu cike da kewar Farouk da ya zama tamkar d'an su.
****
Shekaru sun ja, abubuwa da yawa sun faru, ciki har da haihuwa da Allah ya azurta Aliyu da Safiyya ta d'a namiji, suka sa masa suna Ja'afar, lokacin Farouk na da shekara biyar a duniya. Har lokacin Alhaji Marwan Dikko bai yi aure ba, kuma bashi da niyyar yi, takanas Hajiya Turai ta aika aka kira mata Kabir (Daddy) ta sasu a gaba da fadan lallai ya matsa masa ya fitar da mata, dan zaman shi haka ya ishe ta babu da balle jika, hakuri suka hada baki suka bata, suna fitowa Kabir ya sake dora masa da nasa fadan, haka dai yayi masa alƙawarin zai yi kwanan nan babu jimawa.
***
*Bakaken Ranaku*
Yanayin aikin soja da rashin lokacin su ya kara saka shakuwa mai karfi tsakanin Adam da Abidah, a bangaren ta yake zama har dare ayi kallo ayi hira da wasa da dariya, wani lokacin ma har sai ta tafi ta kwanta ta barshi idan ya gama ya rufe mata kofa.
Watarana da daddare bayan ta tafi daki ta kwanta sai taji tana buƙatar dauko ruwa, kanta tsaye ta nufo falon, tun daga nesa take jin alamun magana a cikin fushi, d'an dakatawa tayi tana sauraron shi,
"Kinsan Allah, kije chan ki nemi uban da yayi miki ciki, dan kin rainan wayo shine zaki kwaso cikin ki kizo ki na na min."
"Eh nasan wannan amma sau daya shikenan sai kice ni, tab ai wallahi uban da yayi miki kije can ki neme shi, dan tsabar iskanci sai da kike gab da haihuwa sannan zaki kirani kina min wani banzan zance, karki kara kirana wallahi kinsan ni kinsan me zan iya."
Tsaki yaja da karfi ya kashe wayar yana bugata saman kujera, rai a bace Abidah ta ƙaraso falon
"Anty!" Ya fada cikin alamun tsoro tsoron ko taji, bata amsa ba sai ma zama da tayi kujerar dake kallon sa tana tallafe cikin ta dake wata takwas.
"Adam, me naji kana cewa?"
Ta watso masa tambayar tana kallon yanayin sa. Zai yi magana tayi saurin daga masa hannu
"Ciki kayi ma wata Adam?"
Juyar da kansa yayi gefe a ciki ciki yace
"Tun da kin riga kinji, bani da damar boye miki, mistake ne ba wai hali na bane."
A cikin tsananin mamaki take kallon sa, bata taɓa tunanin Adam da aikata abu makamancin hakan ba, fada ta hau yi masa ta inda take shiga bata nan take fita ba, tayi masa tas kuma tace tabbbas dole yan uwan sa da mahaifiyar sa su sani, da sauri ya zamo kasa ya haɗa hannun sa ya hau yi mata magiya, bata saurare shi ba tayi wucewar ta daki ta rufe da key.
Tsawon kwanaki uku yana mata ziryar ta rufa masa asiri, kin bashi fuska tayi, ta daina sakar masa fuska ko kadan, tunanin yadda zata sanar wa Dadah take, bata son abinda zai daga wa matar hankali, haka tayi ta fama da abin a ranta ta rasa wanda zata faɗa wa.
Kwatsam sai ga Safiyya da Aliyu sun zo, hakan ba karamin dad'i yayi mata ba, bayan sun huta ne ta samu damar sanar musu abinda yake faruwa, sosai Aliyu ya dau zafi ya kirashi ya ci masa mutunci sannan ya ce dole ne Dadah ta sani sannan dole Kabir ma ya sani, shawarar yadda zasu fara fad'a wa ita Dadah sukayi musamman suka je har dakin ta, tare da Adam ɗin yana sunkuyar da kansa kamar munafiki, tun da taga yadda suke nuku-nuku ta gane akwai matsala, kafin su samu damar fada mata ta jefe su da tambayar,ala dole Aliyu ya daure ya sanar da ita, iya kar rudewa ta rude, bata san sanda ta rufe shi da duka ba, tana yi tana kukan ya cuce ta, da kyar suka lallaba ta, ta yi shiru suka shiga tunanin yadda za'a bullo wa al'amarin tun da dai ya tabbatar musu ba halin yarinyar bane shine ya yaudara ta da dadin bakin zai aure ta ita kuma ta amince masa.
Tunanin zuwan Daddy kowa ya shiga yi dan yasan ba karamin artabu za'a sha dashi ba, ranar da ya kira kuwa yace yana hanya duk jikin su a sanyaye, haka ya zo ya tarar dasu sukuku kamar wanda akayi ma mutuwa.
Wanka yayi ya fara hutawa kafin ya nufi bangaren Dadah, bayan sun gaisa ne suna d'an taba hira Alhaji Marwan ya shigo, yana zama aka shiga yin sallama a ɓangaren, Dadah ce ta yunkura ta leko, mata ne guda biyu cikin yanayin tashin hankali da rashin nutsuwa, hannun su tabi da kallo a take tasha jinin jikin ta jiri-jiri ne ya soma daukar ta, tayi saurin dafe bangon tana yi musu iso ciki, a d'arare suka bita, falon suka koma suka samu waje suka zauna. Hakan yasa suka katse hirar da suke suna kokarin mik'ewa Dadah ta dakatar dasu
"Ku tsaya ayi komai a gaban ku, dan kuma ta shafe ku."
Komawa sukayi suka zauna da tunanin abinda yasa tace hakan,
"Sannun ku da zuwa."
Tace tana mika hannu dan karbar jaririyar hannun su.
"Gata nan, tabbas bamuyi tunanin ganin ku haka nan ba, ranmu a bace muka tawo sai dai a yadda kika yi mana yasa muka ji nauyi da kunya, gata nan, yar ku ce dan dukkan bincike ya nuna yaron gidan nan ne yayi mata cikin, sai dai ita Allah yayi mata rasuwa wajen haihuwar shiyasa ma muka jinkirta kawo ta har zuwa sanda akayi sadakar bakwai."
"Allahu Akbar, Allah ya jikan ta, Allah ya raya mana, kuyi hakuri dan Allah, d'a ne ka haife shi, amma baka haifi halin shi ba, kuyi hakuri kuyi hakuri."
"Me ya faru Dadah.?"
"Kira min Adamu a waya, yazo nan bangaren sai kuji komai."
Daga waya yayi ya kirashi, ya ajiye yana jin zuciyar sa kamar zata faso kirjin sa. Kan sa tsaye ya shigo falon, da kallo duk suka raka shi har ya samu waje ya zauna yana kallon matan. Tashi Dadah tayi ta mika masa jaririyar tana buɗe rufin da akayi mata da abin daukar yara
"Ko da ace zaka ƙaryata, ka dube ta, babu abu daya data bari naka sanda kana karami, babu abu ɗaya, kaga ikon Allah ko? Toh haka rayuwa take, duk wanda yayi da kyau zai gani."
Sai ta juya wajen su Daddy
"Gashi nan ya ce aka kawo muku, sai yayi muku bayanin yadda akayi aka haihu a ragaya, sai dai wannan tsantsar kamar ta isa ta tabbatar da komai."
"Ku kuma dan Allah kuyi hakuri akan abinda ya faru, bani da bakin da zan iya baku hakurin rashin kyautawar da akayi wa yarku, sanadiyar da har ta rasa ranta, Allah ya baku hakurin rashin ta."
Mik'ewa sukayi a tare, sukayi sallama suka tafi. Suna fita Dadah ta karbi jaririyar tayi dakin ta tana jin kamar ta yi kuka, yau itace zata goya yar da ba ta hanyar sunna aka same ta ba, sai dai dole laifin iyayen ba zai shafe ta ba, zatayi kokarin ganin hakan bai shafi rayuwar ta nan gaba ba.
***Wata irin shaka Daddy ya kai masa, ya shiga bugun sa da dukkan karfin sa, da kyar Alhaji Marwan ya kwace shi dan tuni ya sauya masa halitta, da rarrafe ya fita daga falon saboda tsabar yadda ya daku.
Saman kujera ya fada yana dafe kansa, idan akwai abinda ya tsana take kyama a rayuwar sa ya kasance zina, abu ne da duk wanda zai iya aikatata to tabbas bashi da sauran mutunci a idon sa.
Idan ya tuno yar jaririyar sai yaji kansa ya sake sarawa, komai daren dadewa dole ne gaskia ta fito. Ya zatayi da abinda bata da masaniyar komai akai? Shigowar matar dake dan taimakawa Abidah da aiki a guje ya maida hankalin su gareta
"Alhaji ina tunanin haihuwar tazo."
A kid'ime suka bi bayan ta, aka nufi asibiti da ita, lokacin ta riga ta gama galabaita sosai, har bata gane wanda ke kanta sosai. Sai data dau tsawon lokaci dan har an soma shirye-shirye shiga da ita theatre ta haihu sai dai abinda ta haifa bai zo da rai ba. Kwanan ta biyu a asibitin aka sallame ta.
***
Bangaren Abidah Dadah ta nufa dauke da jaririyar a hannun ta, Abidah na zaune tana shan tea a kofi duk jikin ta babu dadi aka shigo, ajiye kofin tayi tana kokarin mik'ewa ta dakatar da ita
"Zauna dan Allah. Ke da ba lafiya ba."
"Ai da sauki Dadah, ashe sun zo ranar." Tace tana mai kallon hannun nata
"Hmmm sun kawo ta gata nan, gashi sam taki karbar madara wallahi, kwana biyun nan kuka kawai take sai dai idan taji uwar bari ta karba tasha kadan, na rasa yadda zan."
"Allah sarki."
Tace tana kallon yarinyar, da sauri Farouk ya taso yana leka fuskar ta, daidai lokacin ta saka kuka sosai, da sauri ya kalli Abidah
"Mummy kuka take, sabuwar bbyn da kika haifa mana ce?"
Daga masa kai tayi, ta mika hannu ta karɓe ta daga hannun Dadah ta soma jijjigen ta.
"Bari na dauko madarar a sake gwada mata, kukan ya soma yawa wallahi."
"Mummy ya sunan ta? Itama kanwata ce kamar Ja'afar?"
"Kanwar ka ce Farouk."
"Yess!" Yace yana murna, yana kama dan karamin hannun ta, Dadah ce ta dawo dauke da madarar ta bata ta koma wajen bakin da tayi, karbar ta tayi suka shiga daki, ta sake hada mata madarar ta bata, kadan tasha ta yi bacci, shiru tayi tana tunanin taimakon yar jaririyar da bata san abinda duniyar ke ciki ba. Ba tare da shawara da kowa ba ta yanke abinda take ganin zai taimaka mata ya kuma farantawa Dadah.
***
[8/6, 2:43 PM] +234 808 540 5215: *DG*
27
Adam duk ya fita hayyacin sa, babu wanda ke bashi fuska a gidan, zaman daki ne ya zama abin yin sa tunda idan ma ya fito babu wanda ke kulashi, gefe daya yarinyar da yake mutuwar so da kauna, kwana wajen nawa kenan yana sintirin kiran ta a waya amma bata daga wa, daga karshe ma sai tayi blocking kiran sa baki daya, abin yayi masa zafi ssoai, dole ya shirya ya tafi gidan su, tun da ya hango motar yaji jikin sa ya soma rawa, ganin an bude gate din gidan yasa shi labewa a baya, itace tayi kyau ainun, cikin shigar ta kamar ko yaushe, ta nufi motar. Motar Alhaji Marwan ce, ji yayi numfashin sa ya soma ja da kyar, be kara shiga tashin hankali ba sai daya ga ya zuro kafafun sa ya fito, shi din ne kowa, fuskarsa dauke da madaukakin farin ciki, yadda tayi masa jagora zuwa cikin gidan yasa gama tabbatar da komai ya kare masa. Wayar sa ya sake kira yana son sake tabbatar wa, sai dai kamar ko yaushe ne, ba zai taba iya kiran nata.
Da kyar ya kai kansa gida, zuciyar sa na zafi, zafi irin na rabuwa da masoyin daka kwallafa rai akan sa, ka dora dukkan buri akan sa, shin me hakan ke nufi? Ta san abinda ya faru dashi ne yasa ta juya masa baya? Ko kuwa dai Alhaji Marwn...
Tuni zuciyar sa ta hau tururi, yaji kamar ana zare masa sauran tausayin da ya rage masa a zuciyar sa, sai da ya zama babu digo ko sauran tausayin kowa a ransa, a take ya yanke wa kansa shawarar abinda yake ganin shine daidai.
***
Zagayen dakin yake yana dan shafa saman kansa, tunanin sa ya tsaya tsak daga lokacin da ya tuna tabbas Abidah ta shayar da Amal nono, eh duk da ba wai ta shayar da ita bane har zuwa sanda ta isa yaye, amma tabbbas ta zama mahaifiyar ta ta shayarwa kamar yadda musulunci yace,ya akayi dukka suka manta da wannan? Duk da a lokacin ya hane ta ya gargade ta akan kadda ta shayar da ita bayan ya gano take taken ta, sai dai a yanzu yana hasaso hakan a matsayin wani ɓangare da yake bukatar dubawa. Da sauri ya jawo wayar sa, number ta da har lokacin ke ajiye a wayar sa, har ya danna kiran sai kuma yayi saurin katsewa, akwai sauran abubuwan da yake son ganowa, dan haka dole ya gama bitar komai daki-daki kafin ya kira ta.
***Babu bata lokaci aka shiga hidimar bikin Alhaji Marwan Dikko, zuwa lokacin Adam ya zama kamar wani tsohon mahaukaci, komai ya tsaya masa, babu kuma wanda ke bin takansa, kowa sabgar gaban sa yake akan abinda yake ganin wani kuskure ne da ya aikata da ya kamata su sassauta masa, idan yaje dakin Dadah bata wani sauraron sa, balle kuma Abidah da taso tafi kowa daukar zafi ita da mijin ta Uncle Aliyu da Safiyya na tayasu, sai yaji duk ya sake tsangwamar kansa.
Haka akayi biki aka watse aka kawo amarya, ranar bai iya baccin kirki ba, atleast yaso yaji ta bakin ta akan dalilin daya sa tayi masa hakan, sai dai duk cikin su babu wanda yake da niyyar sauraron sa. Hakan kuwa ya taimaka wajen dasa mummunar kiyayyar su a zuciyar sa. Zuciya bata da kashi, tuni ta shiga ingiza shi, da sunan daukar fansa wanda yake ganin haka ne kawai mafita.
***BAKAR RANA!***
Tana kwance ta bubbbude curtains din dakin ta saboda yanayin da ake ciki na zafi, gashi ranar babu wuta sai zafin ya kara yawa. Motsi taji kamar ana taba kofar ta, ta dan cire kanta ta dubi kofar na dan wani lokaci, maida kanta tayi ta rufe idon ta dan yadda baccin ke fizgar ta, ba zata iya hakura ba.
Yamma ce wajen karfe hudu da rabi, a ka'ida ba'a son baccin na rana, sai dai ita ta rasa dalilin jin nasa yau sosai, shiyasa ma ta kora Farouk da Ja'afar wajen Dadah tayi kwanciyar ta. Nan da nan bacci ya dauke ta me karfin gaske.
***Yau ranar daban take da dukkan ranakun da yake zuwa ganin gida, yau yana jin shi cike da son kasancewa da ita, yadda yayi kewar ta ba kadan bace shiyasa ma bai sanar da kowa zuwan nasa ba. A matukar gajiye ya shigo gidan, ya kalle bangaren Dadah sai ya wuce kai tsaye zuwa nasu bangaren, ta sallama ciki ciki ya tura kofar, yana son bata mamaki, shiru ko ina baka jin motsin komai. Ajiye kayan hannun sa yayi kai tsaye ya nufi dakin baccin su, da karsashi ya tura kofar ba tare da tunanin komai ba.
Runtse idon sa yayi ganin komai na dawo masa a ƙwaƙwalwar sa, hoton da ya riga ya zama permanent a cikin zuciyar sa ya shiga dawo masa, numfashi ya soma ja cikin fitar hayyaci jikin sa ya soma rawa, kokarin tashi yake daga wajen bayan ya saki diary din hannun sa ya kasa, sai ya koma yaraf ya zauna yana kokarin saita kansa yana bawa kansa k'warin guiwar tsayawa yabi komai.
Mugun gani kamar yadda ya kamata ya kira wannan rana, Abidan sa da kaninsa, a dakin sa na sunna cikin yanayin da zuciya da ruhi ba zasu iya dauka ba, da wani irin tashin hankali ya hau dukan su a tare dukka su biyun, duka irin na wanda yake jin kamar za'a zare masa numfashi ya bar duniyar.
Kallon cikin ido Adam ke yi masa, kwatankwacin kallon tsanar da Daddyn ke masa, jifa yayi dashi ya bugu da bango kansa ya fashe, a take jini ya shiga malala a wajen babu alamun rai a jikin sa.
Daidai lokacin ta kwalla ƙara tana kokarin neman abun da zata kare jikin ta, nufo ta yayi bayan ta samu nasarar jan dogon Hijabi ta zura ya shak'e ta, kakare ta hau yi kamar zata mutu, da kyar ta bude baki cikin galabaita tace
"Ka... Tsaya.. ka saurare ni, wallahi ba abinda kake tunani bane."
Wurgi yayi da ita ta fada a saman drower ya shiga kokarin zare belt din jikin sa, daidai lokacin Dadah ta fado dakin a hargitse, abinda ta gani ya firgita ta, bata san sanda tayi kan shi tana kiran sunan sa ba
"Kabir!!! Zaka yi kisa, innalillah wa inna ilaihi raji'un."
Sakin belt din hannun sa yayi yana ja da baya ya fita daga dakin da sauri, rudewa Hajiya tayi ganin jinin dake fita akan Adam, da sauri ta yo waje tana kiran Kabir ɗin. Chak ya tsaya lokacin har ya kusa fita daga gida, a gaban sa ta tsaya tana kuka sosai
"Dan Allah karka tafi, kar ya mutu ka taimaka wa uwar da bata san komai ba sai lafiyar d'an ta, dan Allah."
Hannun ta ya kama, ya rike gam yana sauke ajiyar zuciya, sakin ta yayi ya koma ciki da sauri, yana zuwa ya daga shi ya fito dashi, ya saka shi a mota yaja ya fita daga gidan.
***Da rarrafe ta isa gaban ta muryar ta ta dashe saboda tsabar kuka, ta rike kafarta
"Dadah dan Allah kiyi min rai, ban aikata ba wallahi bansan komai ba, bansan mai ya faru ba, nasan kin yarda dani, nasan zaki fahimce ni."
Ga mamakin ta sai gani tayi ta janye kafarta, ta bar wajen da sauri ba tare da tace komai ba.
Daki ta koma ta fada toilet ta sakar wa kanta ruwa, kuka take a cikin ruwan tana tunanin abinda ya faru, wannan wacce irin bakar rana ce? Waye zai saurare ta ya yarda da abinda zata ce? Tana nan zaune jigum har suka dawo daga asibitin, da sauri ta mike jikin ta na rawa ta yo wajen, tun kafin ta k'arasa ya dakatar da ita
"Karki ƙaraso nan, na sake ki saki uku! Keji ban yafe miki cin amanar da kikayi min ba."
"Yaya!"
Aliyu ya fada da karfi yana shigowa ciki, da sauri Safiyya tayi wajen ta ganin yadda take layi kamar zata fadi
"Babu ruwan ka Aliyu, ta chanchanci fiye da haka ma, dan dai hakan shine karshen hukuncin da zan mata, taje na barta da Allah!"
"Amma Yaya da ka tsaya kaji uzurin ta, haba yaya, Anty Abidah ce karka manta kafi kowa sanin halin ta, ya ba zaka bata damar kare kanta ba?"
A zafafe Dadah ta kalle shi
"Kayi min shiru Aliyu, babu ruwan ka."
"Dadah kema baki yarda dani ba? Baki san abinda zan iya aikatawa ba? Iya zaman da mukayi?"
Ta tambaya tana kuka sosai, girgiza kanta tayi
"Bani da sauran zama a inda ba'a san daraja ta ba, ba'a taba tsayawa a saurari uzurin ka balle kasa ran samun sauki, tir daku nayi dana sanin shigowa rayuwar ku, a yau ni Abidah na yanke dukkan wata alaƙa tsakani na daku, babu sauran komai tsakanin mu sai ta yarana guda biyu, dan yar uwata da Farouk, wanda su kuwa kamar dole na ne duk da haka zan tafi na bar su tunda ba dasu nazo ba!"
Tana kaiwa nan taja hannun Safiyya dake kuka sosai ta fita daga dakin fita ta har a abadah.!
*** *DG*
28
****
Da sauri ya rufa musu baya yana kwala mata kira, bangaren ta suka nufa, tana zuwa ta haɗa dukkan abinda tasan mallakinta ne, Farouk ne da Ja'afar suka shiga kuka ganin yadda iyayen su biyu ke kukan, tsaye uncle Aliyu yayi a dokin kofar ransa na mugun suya, mai yasa sam yayan nasu baya tsaya wa yayi bincike ne? Komai sai ya yanke hukunci a cikin fushi da bacin rai bayan ba haka Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya koyar damu ba, lallai duk wanda zai biye wa zuciya yayin da ransa ya ɓaci zai iya aikata komai, ciki kuwa har da aikin da mutumin da ya fita daga hayyacin sa.
Gashi yanzu ya aikata abinda har ya bar duniya ba zai taba daina dana sani ba, saki uku, a lokaci daya? Saki da aka ce idan akayi shi al'arshi ce take girgiza. Anty Abidah bata chanchanci hakan daga gare su ba, matar data tsaya da dukkan karfin ta wajen ganin ta kyautata ma kowa.
Zuwa tayi zata wuce ta gefen sa yayi saurin tare kofar yana jin kamar alamun kukan shima
"Anty yanzu tafiya zakiyi? Dan Allah karki tafi."
"Uncle Aliyu kenan, zamana ya kare a gidan nan, karka manta da babu igiyar auren yayan ka yanzu akaina. Alfarma daya zakayi min, ka taimaka min ka kular min da Farouk da Ja'afar, yayana ne dukkan su saboda haka amanar su na hannun ku ku biyu."
Girgiza kansa yake ya rasa ina zai tsoma kansa, gaba yayi ya sake baya ganin yadda yaran ke kukan fitar hayyaci, hannu yaga ta bude musu suka tawo jikin ta gaba dayan su. Runtse idon ta tayi hawayen da take kokarin makalewa suka shiga saukowa.
"Allah yayi muku albarka!"
Sai ta janye su tayi hanyar barin gate din Safiyya na take mata baya.
***
A zafafe ya fada falon, wurga idon sa ya shiga yi har ya sauke su akan Adam dake jingine da kujera kansa na kallon kasa. Da sauri ya isa gareshi ya ci kwalar rigar sa, idon sa daya rine yayi ja ya sauke masa aka cikin matsanancin fushi yace
"Me yasa zakayi mata haka? Me yasa zaka manta alkhairin ta gareka musamman, baka san halacci ba?"
Kwace wa yayi daga rikon daya yi masa, cikin fushin shima ya taso masa
"Just stay out of this idan ba so kake kaima ka shiga lissafi ba."
"Idan naki fa? Me zakayi?"
Murmushi yayi ta gefen bakin sa ya juyar da kansa
"Ka shiga taitayin ka, na wuce yadda kake tunani wallahi, zan iya yin komai."
Dukan kirjin sa yayi ya tura shi baya,
"Babu abinda ka isa kayi sai abinda Allah ya ƙaddara akaina."
Yana kaiwa nan ya juya ya bar masa dakin.
Bangaren Dadah yayi yana riƙe da hannun yaran, tana zaune ta rasa ina zata saka kanta, da sauri ta dago tana ganin shine ta mike
"Aliyu, dan Allah karka ce zakayi bincike akan abinda ya faru yanzu akan yayar matar ka, karka ce zaka tsaurara bincike na roke ka."
Durkusawa yayi a k'asa ya kaskantar da kansa yace
"Ke mahaifiya tace, idan har kike bani umarni dole nabi ko da hakan zai zamar min matsala, wajibi ne nayi idan har bai sabawa Allah ba, sai dai a wannan karon zan nemi afuwar ki tun kafin àbinda zai kasance ya kasance, zan tsaya wa Anty Abidah na bi mata hakkin ta, ba zan hakura ba har sai sanda gaskiya tayi halin ta. Ki yafe min."
Kuka ta saka ta shiga yi mishi magiya ya bar komai kar ya tsaiwata bincike, babu alamun zai saurare ta, tashi yayi da nufin barin dakin tayi saurin rike shi tana kuka sosai.
Yana tsaye kyam a bakin kofar dakin ya harde hannun sa a saman kirjin sa, cikin isa da gadara yacw
"Barshi, wanda bai ji bari ba, shine zaiji hoho."
Juyowa Aliyu yayi a fusace ya bar dakin da sauri, kukan yaran dana Dadah ya hautsina dakin, be bi ta kansu ba ya wuce uwar dakin ta, yar jaririyar sa na kwance tana jujjuya kafarta da alamun ta jima da tashi har tayi kuka ta gaji, yau ne karo na farko daya mata kallon tsaf tun ranar da aka kawo ta gidan, babu maraba tsakanin ta dashi sai ta banbancin jinsi. Shafa kanta yayi makogaron sa na kaiwa da komowa yace
"I ll come back for you one day!"
***
Tsawon sati kenan Daddy na rufe a bangaren sa, baya zuwa ko ina ko sallah ma a daki yake yin ta, sosai abin ya taba shi, yana ganin kiran Alhaji Marwan amma sam yaki dagawa, duk sanda ya runtse idon sa su yake gani, sun cutar da zuciyar sa, sun dasa masa wani babban al'amari da zai ta bibiyar tunanin sa.
Tsawon satin nan babu wanda ya leko tsakanin Aliyu da Adam, yaran uku dake gaban ta su kadai take kalla taji hankalin ta ya tashi, bata taɓa fatan ko tunanin abinda zai zo ya wargatsa musu kwanciyar hankali ba cikin d'an kankanin lokaci, gaba daya gidan ya fita daga kanta bata fatan cigaba da zama cikin sa, zaman da zai cigaba da yi mata famin abinda ya faru.
Sai da Alhaji Marwan yayi da gasken gaske sannan ya samu Daddy ya fito, yayi muguwar rama da baki, fada yayi ta masa amma bai sanar dashi abinda ya faru ba, labarin yafi gaban a bada shi ba, duk kuwa da yadda suke da karfin abota amma ba zai iya ba.
Tubure musu Dadah tayi akan lallai sai ta bar gidan, ba kuma Katsina zata koma ba, bata son duk wani abu da zai tuna mata komai, ganin ba zata amince da kokarin kwantar mata da hankalin da suke kokarin yi ba yasa suka yanke shawarar sama mata gida a Kano, wannan shine asalin komawar Dadah Kano tare da Farouk, Amal da Ja'afar.
***
Daddy na rurrufe ko ina na gidan dan komawa aiki Adam ya shigo, har lokacin kansa rufe yake da bandage, dauke kai Daddy yayi kamar bai ganshi ba, ya wurga masa keys din bangaren sa
"Ka duba komai naka ka kwashe ka bar min gida."
Dage kafadar sa yayi ya tsuguna ya dau keys din, bud'e dakin yayi ya dauke abinda zai dauka ya fito,kamar yadda ya wurga masa keys din shima hakan yayi, ya gefe shi dashi cikin keta yace
"Sai watarana!"
A kusan tare suka bar gidan, sai da Daddy ya fara biya wa ta Kano ya duba Dadah, kafin ya wuce wajen aikin daya dauki lokaci mai matukar tsawo kafin ya sake waiwayar gida.
Samun babban matsayin da yayi shi ya rage masa nauyin abubuwan da yake, ya tattara hankalin sa waje daya yayo gida, Dadah na ganin shi tasa masa kuka, kukan dake nuna tsantsar halin da take ciki, sai a sannan take sanar mishi ta mutuwar Adam din, hatsarin mota ne ya rutsa dashi daga Lagos zuwa Kano ko gawar sa ba'a kawo ba.
Babban tashin hankalin ta bai wuce daina ji daga Aliyu da Safiyya ba, tun bayan rasuwar, taje gidan yafi a kirga amma magana daya take samu daga makotansu shine sun yi tafiya.
Takanas Daddy yaje da kansa har wajen aikin Aliyun, sai a sannan ne ma yake jin labarin ai ya bar aiki tun da jimawa, abun ya matukar daure masa kai, haka ya dawo a sanyaye gida ya sanar wa Dadah, wadda hakan ba karamin sake gigitata yayi ba,tun daga nan basu sake k'ara ji daga gare su ba, a hankali suka manta, kamar an cire musu su da abinda ya shafe su daga ƙwaƙwalwar su, babu wani daga cikin su daya sake yin maganar sa har kawo yanzu!
****
Sake shiri yayi, ya fito a cikakken mutum mai cikar zati da haiba, sai dai yanayin fuskar sa kadai zata tabbatar maka da ba daidai yake jin jikin sa ba, bayan mota ya fada ya d'an kishingida kadan yana lumshe idon shi, tabbas yana bukatar ji daga gareta, yana so yaji komai daga bakin ta ko da kuwa ba zata saurare shi ba zai gwada sa'ar sa.
Su biyu ne kaɗai daga shi sai driver sa, yau baya jin zai iya yin wannan tafiyar da masu kula dashi, bayan haka ma baya bukatar hayaniya yana so yaje mata a Kabir ɗin sa, Kabir ɗin data sani shekarun baya ba na yanzu ba..
"Ina zamu je ranka ya dade?"
"Kaduna." Ya amsa mishi a gajarce yana sake mikewa sosai.
***
Duk nauyin dake cunkushe a zuciyar sa yau yayi sauki har yana jin bukatar fara aiwatar da abinda ya kawo shi. Shigar manyan kaya yayi kamar ba a k'asar masu jajayen kunne ba, ya dora hula ya fito a cikakken bahaushe bakar fata, kai tsaye inda sukayi zasu hadu ya nufa da taimakon address din daya bashi.
Daga d'an nesa ya hango shi, tabbas shine mutumin nan na ranar nan, ya akayi suka sake haduwa? Daga kafar shi yayi cikin sauri ya nufe shi, daf da zai isa gareshi yaga ya bude wata mota dake ajiye wajen ya shiga, bai iya ganin fuskar sa sosai ba sai rabi kamar wanchan lokacin, kamar an dasa shi a wajen haka ya tsaya yana kallon motar har ta bar wajen, jan ƙafarsa yayi zuwa shagon yana kokarin ganin ya yakice shi daga zuciyar sa, ya rasa dalilin ma da yasa yake jin wani abu game da mutumin. Ganin zai bata wa kansa lokaci yasa yayi saurin shigewa ciki yana duba agogon hannun sa, yasan baturen mutam da ka'ida, baya so ka saba masa alkawari.
Tambaya yayi aka nuna masa inda zai same shi. Cikin aiki ya tarar dashi kacha-kacha, yana ganin shi yayi dariya, yana tura masa takardun gaban sa, da mamaki Farouk ya kalle shi amma kafin yayi magana ya riga shi
"No time to waste."
Gid'a kansa yayi a hankali ya furta
"Nima bani da lokacin batawar ai, I'm here for it"
Aikin ya shiga nuna masa,da yadda yake so komai ya kasance, babu wani bata lokaci ya fuskanci abubuwa da yawa sai dan abin da baza'a rasa ba wanda sai a hankali dama.
Ranar a gajiye likis ya koma gida cike da farin cikin fara aikin da yayi da shugaban shagon wanda dalilin social media suka hadu tun da dadewa, sai gashi yayi masa rana a lokacin da bai taba tunani ba.
Wanka kawai ya iya yi yasha tea ya kwanta dan sosai yake jin bacci, yana kwanciya kuwa baccin ya dauke shi wanda rabon da yayi irin sa ba zai iya tunawa ba. Gashi dama duk sanda yayi yunkurin baccin sai tunanin ta ya shigo masa, daga nan sai yaji sam baccin ya fita daga kansa, daga nan sai ya dasa sabon tunani har zuwa sanda baccin zai dauke shi ta karfin gaske ba tare da ya shirya ba.
*** *AMINATU*
Na cigaba da zuwa makaranta da taimakon Allah dana Baba Altine data zama wata babbar bangare na sabuwar rayuwa ta.
Bani da matsalar komai gefe ga Kamal daya zama abokin shawara ta. Ban yi watsi da duk abinda Anas ya ce min ba ina matukar kokari wajen ganin na kare mutunci na.
Lokuta da dama nakan tuna Baba, Inna da Karime, Yalwati da sauran mutanen da suka fi kowa kusanci dani a da amma babu ko daya cikin su yanzu a rayuwa ta, hakan ba karamin sani yake na kara tuna wacece ni ba, mara asali da tushe abar kyama ga kowa.*DG*
*29*
★★★★
Dukkan abubuwan bukatuwa na makaranta ta Kamal ya dauke min shi, tun ina fada har na kyale shi na zuba masa ido, ranar ina tsaka da duba wani handout ya iske ni wajen da muka saba haduwa, a dan gefe ya zauna yana leken cikin handout din
"Kaga yan allazi boko."
Yace yana dariya, harara na sakar masa ina janye handout din.
"Wai dan Allah yaushe zaki kawo min Iman ne, I'm dying to see her kinsan abinki da hanta da jini, daga zuwa sau daya shikenan nasan ma ta kara wayo."
"Sai dai ka shirya kaje da kanka, ni bazan iya dauko ta makaranta ba,dame zanji?"
"Toh ai ni hakan ma zaifi min farin ciki, yaushe zaki gama da school?"
"Lecture daya ya rage, nan da 30min zamu shiga."
"Shikenan ki kirani idan kin gama."
Yace yana mik'ewa, waya ta dake cikin jakata tayi k'ara, tsayawa yayi ya harde hannu yana jiran yaga mai kiran. Ina ciro ta naga ya kwashe da dariya
"Yanzu zata nutsu kamar wani maka'ika." Yace yana bata fuska, ban bi ta kan shi ba na kara wayar a kunne na gami da sallama. A nutse na shiga amsa masa har ya ajiye wayar, ajiyar zuciya na sauke ina duban KAMAL da shi ma nidin yake kallo
"Ya Anas ne fa."
"Na sani, ai naga sunan, ki rage tsoro kamar zai yanka ki idan ya kira."
"Kai ka sani, aka ce ma tsoron sa nake? Kawai ina respecting d'insa ne."
"Daga baya kenan, ki cigaba da nuna masa tsoro, idan kika aure shi kisha wuya yarinya."
Da sauri na ware ido ina murmushi
"Yanzu Kamal har kasan wani aure? Inyeee."
Dariyar shima yasa yana yin gaba abin sa, sai daya dan d'ara wajen kafin ya ce
"Kinci sa'a ke sirikace zaki bani Iman amma da kinji magana gabza gabza wallahi."
Murmushi kawai nayi ban kuma ce masa uffan ba na hau tattare kayan karatu na ganin lokacin shiga ajin ma ya kusa.
A gaban Hall d'in na tarar dashi tsaye yana jira na, ni har na manta ma munyi maganar zamu tafi tare, babu yadda na iya haka na bishi muka dau hanya, sai dai kamar yadda ya san gidan a dah yau sai yaga mun chanja akalar tafiyar tamu, kallo na yayi yace
"Kun chanja gida ne?"
"Eh." Na amsa mishi a takaice, muna zuwa na shiga na sanar wa Baba Altine zai shigo, cikin daki ta koma na rik'e hannun Iman muka fito, da mamaki yake kallon mu, sai kuma ya ƙaraso ya daga ta sama yana dariya sosai
"Baki da kirki Meena, haka matar tawa ta girma amma baki fada min ba?"
"Shigo ciki dai sarkin zance, sai muyi maganar."
Cikin muka koma, ya zauna a kan dardumar dana shinfida masa, ruwa na dauko masa na ajiye sannan na shiga daki na ajiye jakata na sake fitowa, yana zaune yana wa Iman wasa ita kuma tana ta dariya kamar ta sanshi, Kitchen na wuce na duba, shinkafa da wake Baba tayi, sai salak da tumatir dake yanke an tsaftace shi a cikin mazubi, hadowa nayi na jera komai na kawo masa ina zama.
"Ga abincin gidan talakawa sai kasa albarka."
"Kinci bashi wallahi."
Murmushi kawai nayi, a gefen sa ya ajiye Iman ya bude flask din, ya dauki plate ya zuba abincin sosai ya shiga ci muna hira, sosai yaci dan banyi tunanin zai ci haka ba, ganin yadda yake d'an gayu sai na dauka a komai ma hakan ne, shiyasa Bature yace never judge a book by it's cover, tabbas haka ne, kar kayi saurin yanke wa mutum hukunci ba tare da sanin ainihin waye shi din ba.
Kiran wayar sa akayi, da murna ya daga yana sawa a handfree
"Old Woman kinyi missing d'ina ne hala shisa kika biyo baya."
"Sosai kuwa, sati nawa rabon dana saka ido na? Kana cewa baka son Kano sai gashi kayi luf har kana mancewa dani, ko kayi sabuwar mata ne?"
Dariya ya tuntsire da yace
"Aikuwa dai kin iya saurin gano abu, yanzu ma kin ganni wajen ta, nazo mamanta ta cika min ciki da Rice and beans me shegen dadi."
"Da gaske kake yaron kirki?"
"In bata ku gaisa ne?"
"Eh bata naji."
A kunne ya kara wa Iman wayar yana kunshe dariyar sa
"Oya say hi to my boring Grandma kinji baby."
Gwaranci ta soma yi, kamar yadda ta saba duk sanda Anas ya kira a bata wayar, dariya muka hau yi gaba dayan mu har granny din dake kan waya,
"Ja'iri zaka zo har inda nake ka same ni." Tace tana katse wayar, tallafe fuskata nayi da hannu biyu ina kallon sa
"Baka da dama kamal, Allah shirye ka."
"Amin, naji, itama da gulmar tsiya ai maganin ta."
Mik'ewa yayi ya mana sallama ya tafi, bayan tafiyar sa ina kokarin tattare komai na abincin ya shigo, bakin sa dauke da sallama, ido na cikin nasa nayi saurin yin kasa ina jin faduwar gaba, bai sanar dani zuwan sa ba dazu da mukayi waya, da gudu Iman ta rungume shi tana masa oyoyo, daga ta yayi ya manna ta a jikinshi har lokacin idanun sa na kaina yana yawo dasu.
"Sannu da zuwa." Nace ina cigaba da tattare kayan, da hannu ya amsa min yana nazarin wajen zaman da kayan da nake kwashewa, sallayar na gyara masa ya zauna yana tankwashe kafar sa.
"Bako kikayi ne?"
Yace yana karanta ta, ban amsa na gaishe shi, a gajarce ya amsa daidai lokacin Baba Altine ta fito tana masa sannu da zuwa, da fara'a ya amsa mata ba kamar yadda yayi min ba, ta zauna tana tambayar su Hajiya, tashi nayi na kawo masa ruwa da ragowar abincin na wuce daki, ina jin sa ya jeho ma Baba Altine tambayar da yayi min ɗin, maimakon tace masa eh sai naji tace
"Wata kawarta ce tazo bata jima da tafiya ba ma, ko kun hadu a hanya?"
"No shikenan."
Girgiza kai na nayi ina mamakin halin shi, kayan na sauya na fito na koma kitchen din na dora indomie dan ba karamar yunwa nake ji ba, zama na nayi a Kitchen din ba tare da na koma Falon ba, ina jiyo hirar su ya ware sosai yana wasa da Iman, wannan na daya daga cikin dalilan daya saka nake sake bashi girma, da gasken gaske yake kula damu kamar wanda muka zama masa dolen sa.
Zama na nayi bayan na gama dafa indomie na ci a Kitchen din na zuba ma Iman da Baba Altine tasu a dan flask na fitar da kwanukan na daureye sannan na koma ciki.
"Mu baza'a bamu indomie ɗin ba ne?"
"Za'a baku." Nace ina kokarin komawa kitchen din
"Barshi sai da muka roka, dauko hijabin ki rakani unguwa."
"Baba dauko nake kema kar mu barki ke kadai a gida."
"A ah wallahi, shikenan kuma sai na biku godai godai dani, Aallah kiyaye sai kun dawo."
Murmushi yayi kawai ya rike hannun Iman sukayi waje, ciki na koma na zura hijabin na fito.
A jingine jikin motar na tarar dashi, yana gani na ya bud'e min bangaren mai zaman banza, shiga nayi sannan ya miko min Iman ya rufe mana kofar, zagaya wa yayi yaja muka tafi.
Zagaye ya dinga yi damu daga wannan titin zuwa wannan har zuwa lokacin magriba, tsayawa yayi a wani masallaci yayi Sallah sannan ya kaimu wani wajen cin abinci, nidai duk a takure nake haka yayi mana takeaway muka fito, shopping mall din dake manne da wajen abincin ya shiga, ya ɗan dade a ciki sannan ya dawo hannun sa dauke da manyan ledoji ya zuba a baya muka dau hanya.
Muna zuwa gida ya tsaya jikin motar yana nuna min kayan ciki
"Kwashe kayan ki shiga dasu kizo muyi magana, dare ya fara yi."
Kwashe wa nayi na dawo, na karbi Iman data fara bacci na kaita itama na sake dawowa na tsaya.
"Ya karatun?" Ya tambaye ni
"Alhamdulillah, yasu Hajiya? Kwana biyu bamuyi waya da Raudah ba nasan suna shirye shiryen finals."
"Lafiya lou."
"Ya maganar mu?"
"Na'am?"
"Kinji ai, ina so mu fara fuskantar juna, idan yaso sai nayi kokarin shawo kan Hajiya."
Girgiza kai na nayi a nutse nace
"Maganar iyaye magana ce mai matukar girma, kayi hakuri mu yi abinda tace, bana so ka sami matsala da mahaifiyar ka."
"Zaki jirani zuwa lokacin da zata amince? Zaki jirani?"
"Bani da zabi da rayuwa ta sai abinda Allah ya zaba min, idan kai din Alkhairi ne gare ni, nima kuma alkhairi ce a gareka, Allah ya sa ta amince, idan har ta amince ni bani da zabi."
"Shikenan, in sha Allah zata amince, ki bani lokaci."
Daga masa kai nayi, ya sakar min murmushi ya fada motar yana daga min hannu, sai dana ga fitar sa daga layin sannan na shige ciki ina saka key a kofar.
Da daddare nayi ta juyi ina tunanin maganganun, bani da zabi face amince masa, wacece ni ma da har zai tsaya bata lokacin sa akai na, bani da asali bare tushe, bayan haka wannan ce hanya kawai mafi sauki da zan saka masa da dukkan alkhairin sa.
Sake juyawa nayi zuwa dayan barin ina tuna Farouk, mutum na farko daya so ni duk da karancin shekaru na, ban taba tunanin shi ma zai guje ni ba, haka dama rayuwa take shiyasa na bar wa Allah zabin komai na rayuwa ta, sau tari tunanin sa kan hanani sukuni har naji zuciya ta na zafi, tun ina sa ran haduwa dashi har na hakura na barwa Allah.
Ban cire rai ba amma, kila watarana ya waiwaye mu, ko ba dan ni ba, ko dan yarinyar sa, duk da yace babu komai tsakanin mu, amma ina fatan ganin da zai mata kadai ya isa ya gamsar dashi yar sa ce,shafa kanta nayi ganin yadda yake bacci cike da kwanciyar hankali, bata da damuwa ko matsala, tsoro na daya ranar da zata tambaye ni mahaifin ta, duk da ina fatan kafin ranar na samo gamsasshiyar amsar da zan bata.
***
Shirin fita take taji ana mata knocking, ajiye abinda take tayi ta nufi kofar kai tsaye tana tunanin waye, turus tayi ganin shi, tayi saurin ja baya tana kokarin maida kofar
"Karki rufe min kofa."
Wani kallo tayi masa kafin tayi dariya
"A matsayin ka nawa?"
"A matsayi na na wanda kike jira tsawon shekaru."
"Jira?"
Tayi dariyar rainin hankali
"Karka manta babu auren tsakanin mu."
"Kema karki manta nasan kinyi auren kin fito, kin zata bani da labari?"
Juyawa tayi kawai ciki ya bi bayan ta yana murmushi, falon yabi da ido, yadda aka kawata shi da kayan kawa da komai, sanyin Ac hade da kamshin turaren ta tun na fil'azal ne manne a falon, iska ya shaka ya fesar yana zama cikin jerin manya manyan kujerun da suka kara wa falon kawa.
Ciki tayi ta barshi zaune, sai data dau tsawon lokaci sannan ta dawo ta sauya shigar ta zuwa simple gown ta rufe kanta, zama tayi chan nesa dashi tana kallon screen din wayar ta.
"Me kake bukata?" Ta tambaya kai tsaye kuma a gajarce
"Nazo ne nayi miki wasu yan tambayoyi, nasan tabbas kinsan amsar su."
"Then..." Ta kalle shi cikin ido sosai
"Kin shayar da Amal?" Yayi mata tambayar kai tsayen, kai tsayen itama ta amsa masa
"Eh akwai wani abu ne?"
"Akwai, kinsan auren Farouk dake kanta ko? Kuma kinsan musulunci ya hana auren wanda suka sha nono daya, amma ban manta ba tun a lokacin dana ga take taken ki na hana, saboda irin wannan ranar."
"Na shayar da ita tun kafin kayi min magana, haka zalika na bari daga lokacin da ka hana."
"Mesa baki fada min ba?"
"Me yasa baka fada min da zaka hada auren ba? What is my fault anan? Wait saboda nice karkatacciyar kuka mai dadin hawa ko? Shine bayan komai ya kwabe muku zaka zo wajena."
"Why are you like this? Kin chanja sosai."
Dariya ta shiga yi sosai kafin tace
"Mutane na chanjawa ne daga lokacin da wanda suke tare dasu suka chanja, baka ga komai ba indai nice."
Mik'ewa tayi tana duban agogo
"Ina da abin yi, can you please excuse me?"
"I'm not done yet, ina son sanin ina d'ana?"
"Shine tambayar da ya kamata nayi maka tun zuwan ka, ka sani ba wai nayi shiru bane, ina baka time ne kayi gaggawar fito min dashi duk inda kasa shi ya tafi."
Ransa ne ya ɓaci, ya tashi tsayen shima zai maida mata martani wayar ta dake gefen sa tayi kara, kura wa wayar ido yayi da kuma sunan dake rubuce akan screen din kamar mai nazari, da sauri ta sa hannu ta dauke wayar tana sakata a silent. Shiru ne ya biyo baya ya kasa tantance abinda yake ji game da sunan da ya gani. Ganin ya kasa tunawa yasa ya share yana kokarin tausar zuciyar sa, sai daya dan ja lokaci yana tunanin yadda zai yi maganar kafin ya daure kamar an fuzgo maganar yace
"Abinda ya faru shekarun baya, menene gaskiya? Menene tsakanin ki dashi? Me ya faru a ranar?"
Dagowa tayi a dan zabure, sai kuma tayi saurin saita kanta tana sakin murmushi
"Duk abinda zuciyar ka ta tsara maka, shine abinda ya faru,kuma ya riga ya wuce babu amfanin dawo dashi baya, bani da lokacin wannan maganar."
Tana kaiwa nan tayi shigewar ta daki tana rufo kofar da sauri, kamar wanda aka dasa haka ya kame a wajen yana ayyana abun a ransa, yanayin ta da yadda ya hangi tsantsar tsoro a idanun ta bayan ya kawo mata maganar ta sashi shakku, ko dai ya aikata abu cikin fushi? Ya biye wa dokin zuciya? Yayi mata adalci kuwa a lokacin? Me yasa yanzu yake jin son jin gaskiya duk da tsawon lokacin da aka dauka? Bashi da amsar tambayoyin. Da kyar ya kai kansa mota yana shiga yace
"Kano zamu je."
****
Basu suka isa Kanon ba sai dare, Dadah na zaune saman abin sallah tana karatun Alkur'ani, ya shigo, da kallon mamaki ta bishi har ya dire a gabanta yana jin kamar ana sassara masa kasusuwan jikin sa. Da kyar ya bude baki ya amsa sannu da zuwan da take masa, shiru ne ya biyo baya sai kuma ya tuna yana bukatar suyi magana
"Dadah kinsan Abidah ta shayar da Amal kuwa?"
Kai tsaye tace
"Na sani, amma ina ga ai ta daina tun lokacin daka hanata."
Dafe kansa yayi da dukkan hannayen sa
"Ya akayi duk ban san da haka ba? Kinsan musulunci ya hana aure tsakanin wanda aka shayar dasu nono daya, duk da malamai sunyi sabani, wasu sunce idan har an shayar da nonon sau uku, toh ta haramta ga duk wasu da suke muharraman wadda ta shayar da ita din, wasu suka ce ko sau daya ne idan har an bata tasha ta koshi, toh an haramta auren tsakanin ya'yan matar data shayar da ita, ko kannenta da suke uwa daya, ko uba daya, ko uwa daya uba daya, ko yayyenta da suke uwa daya, ko uba daya, ko uwa daya uba daya,ko mahaifinta. Duk dai wasu muharraman da babu aure tsakanin su da ya'yan matar data shayar da ita, toh sun haramta ga wannan wadda aka shayar ɗin.
Wasu malaman suna ganin sai idan har ta shayar da ita na tsawon lokaci ne hakan zai kasance, toh amma dai ko yaya ne, nasan tabbas ta shayar da ita, na tsawon wata guda koma fiye, kinga kenan ta haramta ga Farouk."
"Allahu Akbar, ilimi fadi ne dashi, ban taba sani ko ji ba wallahi, shiyasa ban kawo komai a kaina ba, bayan haka ko da ace na sani,bana ma tunawa da ta shayar da ita din."
Ajiyar zuciya ya sauke yana jingina kansa da saman kujerar, komai ya chanja masa daga yan da yaso ya kuma tsara.
***
Da baya da baya ta koma ta fada saman gadon ta tana sakin kuka, idan har abinda taji Daddy na fad'a gaskia ne, kenan ita da Ya Farouk shikenan? Kai ina bazai yiwu ba, yadda ta kwallafa ran nan dashi, ace kuma shikenan? Sai ta kara sautin kukan ta sosai.
Da ido tabi wayar da kallo kafin ta shiga share hawayen fuskarta da sauri da sauri, dagawa tayi ta shige toilet bayan ta sawa kofar dakin key.
Tsawon lokaci ta dauka suna magana kafin ta ajiye wayar ta fito, lamo ta kwanta tana tunanin mafita.
***Babu wanda yayi mata maganar daga Dadah har Daddy. Taso tayi ma Dadah maganar taji me zatace amma bata so ta tabbatar mata da gaskiyar hakan, duk abin duniya yabi ya dame ta, gashi ana maganar komawar ta makaranta saboda lokaci na kara tafiya, kamar marainiya haka ta zama, duk farin ciki da take dah idan ta tuno da auren dake kanta yanzu ya kau, tunanin ta yadda za'a samu mafita ace akwai aure tsakaninsu kawai take, idan haka ne Mummy ta cuce ta wallahi. Bata da aiki sai kuka, ranar da sukayi waya da Mama ta fada mata abinda ya faru, kwantar mata da hankali tayi, ta dan ji dama dama kuwa, har ta dan saki ranta.
****
Tun ranar da ta fada mishi abinda ya faru be sake kiran ta ba, ya dai tabbatar mata da yana nan zai san yadda za'a yi.
Sati guda ya dire a kasar, ya wuce kai tsaye Abuja, Daddy na zaune wajen daya saba shan iska ya shigo gidan.
"Saukar yaushe?" Daddy yace yana fadada fara'ar sa, zama yayi kan katon carpet din yana mika masa hannu
"Mun same ku lafiya?"
"Lafiya lou mutanen Turai, Azeema kuwa tasan da zuwan ka?"
"Ina bata sani ba ai, zuwan nawa kenan."
"Lallai sannu da zuwa, ka shiga ciki toh nima yanzu zan shigo ai."
"Ok." Yace kai tsaye ya shiga ciki, tana ganin sa ta rufe baki da hannun ta.
"Ya akayi haka?" Tace tana zaro ido
"Zuwan dole ne, akwai abinda zan duba ne ba jimawa zan koma."
Ajiyar zuciya ta sauke
"Na zata ai ko lokacin da muke jira ne yazo."
"Saura kiris." Yace yana nuna mata hannun sa, dariya ta saka.
Shigowar Daddy yasa su yin shiru, zama yayi suka sake sabuwar gaisuwa,kafin a gabatar masa da abubuwa ci da sha, kadan yaci ya yi musu sallama ya tafi.
Yana fita ya tsura wa gidajen guda biyu ido kafin ya fashe da da dariya, motar sa ya shiga wadda ta kasance a rufe ruf da bakin glass, da karfi yasa hannu ya zare mask din fuskar sa, a razane na saki alkalami na ina sake duban sa da kyau
"Adam!!!" Na furta baki na na rawa.
Murmushin gefen baki ya saki kafin ya maida fuskar ta zama ta wani mutum daban ya ja motar ya bar kofar gidan da mugun gudu.
Rano[8/12, 12:03 PM] Nadady: *DG*
*30*
Kai tsaye garin na Kano ya wuce, yana isa ya mata text kafin ya karasa wajen da zasu haɗu. Tana zaune tana jira sakon ya risketa, dama a shirye take saboda haka mayafi kawai tasa ta fita.
Kafin tazo ya cire mask din fuskar sa ya fito a ainihin kamar sa. Tana zuwa tayi saurin fad'awa jikin sa ta saka mishi kuka, shafa bayan ta ya shiga yi a hankali har ta tsagaita da kukan nata, tissue ya ciro ya mika mata
"Menene matsalar ki?"
Ya tambaya yana dago ta,
"Ya Farouk." Tace cikin muryar kuka. Murmushi yayi mata yana jingina ta jikin kujerar motar
"Karki damu, ki koma karatun ki, zan san yadda zanyi."
"Yaushe? Daddy fa ya gama sanin komai, kuma ya fada wa Dadah."
"Akwai lokaci, akwai lokaci."
Yace yana tada motar.
Shiru tayi tana tuna abubuwan da ya jima yana fada mata, haushin kowa take ji, babu wanda zatayi wa uzuri a cikin su, duk kuwa da sun yi mata sosai a rayuwa amma ba kamar mahaifin daya kawo ta duniya ba. Idan bata tsaya masa ba bayan kowa ya juya masa baya wa zai taimaka masa? Ita kenan daya mallaka a duniya dolen tane ta share masa hawayen sa.
***Tsawon makwanni biyu ya dauka a garin kafin ya tattara ya koma inda ya fito, itama Amal sai ta koma can Abuja don karatun ta ta cigaba da rayuwar ta kamar babu komai. Duk da lokaci zuwa lokaci sukan yi waya amma babu wanda ya san da hakan sai Mama kawai, shiyasa ma bata da matsalar komai dan kanta tsaye take abubuwan ta tun da sau tari ma a wayar Maman zai kira bayan sun gama magana sai ta bata.
Alaka ce mai karfi tsakanin su, sai dai ta gaza gane wacce irin alaka ce hakan da har tasan sirrin sa.
***
Dukkan kokarin Daddy na son ganin ya samu wani bayani ta wajen Mummy sam ta ki bashi fuska, rashin sanin yadda zai ɓullo mata ne da yadda yake mata gadara yasa ta kafe itama, zuciyar ta, ta riga ta k'ek'ashe shiyasa bata wani jin shakku ko wani abu game da hakan.
Tun yana tunanin jan aji ne irin na mata har ya gane da gaske take ba zata saurare shi ba, duk baya jin dadin komai, tun bayan rabuwar su da auren da yayi bayan lokacin da kadan bai taba jin wani abu game da ita ba sai yanzu da girma yazo.
Duk da Mama na kokari sosai wajen kula dashi amma ya kasa yakice ta daga ransa. Mai yasa ya kasa mata uzuri a wancan lokacin? Ya kasa gane dalilin sa na yin hakan, gashi yanzu ya fada kogin nadama da dana sani mara amfani.
****
*Farouk*
Aiki yake sosai babu kama hannun yaro, sosai yake jin dadin aiki da Mr Johnson shiyasa bashi da wata matsala da kasar.
Zuwa lokacin da ya fara karatun sa ya riga ya tara kudade masu yawan gaske, duk da haka duk weekend yana zuwa ya zauna a wajen hakan kuwa ba karamin dad'i yake ma Mr John ba dan shi a rayuwa yana son mutum mai kwazon aiki.
Da gangan Farouk ya zamar da kansa agogo baya bada lokacin sa a komai sai neman halal dan yayi wa kansa alkawarin ko zai koma gida ba zai taba bari ya rabi da kowa ba balle har ayi masa wata alfarma.
Batun mutumin nan kuwa, tun ranar bai sake haduwa dashi ba, sai ya tattara shi ya watsar ya rungumi sana'ar sa da karatun sa.
***A gurguje ya sauko kasan shagon tun bayan daya samu sakon supervisor din sa akan yana son ganin sa, dole ya tattare aikin da yake waje daya ya nufi makarantar.
A daidai gate din shiga ya hange shi, da motar sa ya fara gane shi, sai dai yau ba shi kadai bane hadda mace da yara, da sauri ya tsallaka bangaren su yana tsaida su, kamar ba zai tsaya ba sai kuma yaga yaja ya tsaya dage gefe, karasawa yayi cikin sassarfa yana kokarin ganin fuskar sa.
"Assalamu alaikum."
Yayi sallama kai tsaye, a tare suka amsa dukkan su, kafin namijin ya juyo da dukkan fuskar sa yana duban shi, duba na tsanaki.
A wani irin yanayi suka hada baki a tare kamar wanda maganar tazo wa a lokaci daya cikin yanayin dake kama da an fuzgota suka ce
"Farouk!"
Ware idanun sa yayi, duk da karancin shekarun sa ba zai taba mantawa dasu ba, mutane biyu masu kusanci dashi, daya kani ne ga mahaifin sa, daya kuwa kanwa ce ga mahaifiyar sa. Mai suke anan? Me yasa babu wanda yake tunawa dasu? Babu wanda yake maganar su. Bayan har da d'an da suka tafi suka bari. Ja'afar! Mai yasa suka manta da kowa suka zo nan suka kafa sabuwar rayuwa. Bashi da amsar ko daya daga cikin wadannan tambayoyin, shaf ya manta da abinda ya kawo shi makarantar, da sauri ya fada motar yana kallon yaran guda uku dake zaune a bayan motar suma suna kallon sa.
Sautin kukan Anty Safiyya ne ya sake dagula masa lissafi, kuka take sosai sai dai babu wanda yace uffan har suka isa gida. Daga kai yayi yana karewa gidan kallo, tsawon wannan shekarun suna rayuwar su su kadai ba tare da dangi ba. Mai yasa?
★★★★
Rayuwa ta cigaba da garawa cikin hukuncin Ubangiji, idan baku manta kuduri na ba, ba zai wuce na cikar buri na ba, karatu na nasa a gaba babu wani abu daya sauya na daga yadda rayuwar tawa take
Yadda komai yake wanzuwa cikin hukuncin Allah, zaka tabbatar da babu mai tsara bawa ƙaddarar sa face Allah SWA.
Hakan ce ta kasance dani, a yau na rubuta jarabawar karshe ta makarantar horar da lauyoyi dake garin bagauda (law school). Idan na tuna matsayin karatun da nayi a daya daga cikin manyan jami'oin Nijeriya (BUK), na kan ji wani nishadi mara misaltuwa, ban taba hasashen hakan ba, sai gashi Allah ya hukunta min cikin manyan kaddarorin rayuwa ta.
Anas ya zama wani babban jigo a karatu da rayuwa ta, sannan Kamal daya zama mafi kusanci dani da yarinyata
Tun ina tunani ko hasashen zan hadu da wani daga cikin ahalin su Farouk har na daina sai dai har lokacin yana makale a kahon zuciya ta. Duk sanda na kalli Iman na kan tuna dashi da komai nashi.
**Sanda sakamakon jarabawar ya fito sai dana yi kuka, kukan farin ciki saboda yadda result din yayi kyau ainun, wai yau nice rike da shaidar zama cikakkiyar lawyer, Anas yaso yafi ni farin ciki saboda a daidai lokacin ne Hajiya ta amince masa da aure na, duk da abin yazo min a wani irin yanayi amma nayi kokarin boyewa na biye masa wajen nuna farin ciki na, y'an kwarya kwaryar walima ya shirya min daga ni sai shi sai Iman, Baba Altine da Ramlah sai kawayen ta biyu, ban gayyaci kowa ba a yan makarantar mu, duk dama babu wata shakuwa tsakanin mu sai abinda ya shafi karatu.
Kamal tun daya koma ban sake saka shi ido na ba sai dai muna waya sosai dashi.
Komai ya sake chanjawa bayan gama karatu na, kai tsaye Anas yake zuwa a matsayin zance. Mutum ne shi da yake bin komai a tsare, dan haka bai taba ketare iyakar sa ba, komai yanayin sa ne a addinance babu jahilci. Hakan na kara birgeni dashi, yadda yake tafiyar da rayuwar sa cikin tsari abin so ne.
****
*Waye Shi!*
Hannu na sakale dana Iman muke zagaye supermarket din, Alk'awari nayi mata idan har ta iya wasu surori zan kai ta, ta zabi abinda take so, da kanta ta fada wa Anas aikuwa sai ga kudi ya aiko mana dashi.
Doguwar riga ce bud'addiya a jikina, na yane kaina da madaidaicin mayafi, takalmin kafata irin flat shoe ne, babu yadda za'a yi daga kallo daya ka gane wacece ni ko daga ina na fito, jikina ya murje sosai na zama cikakkiyar mace ta kowanne fanni. Bamu da matsalar komai saboda Anas ya tsaya mana.
Mun bata lokaci sosai kafin mu gama saboda yadda Iman ta tsaya ruwan ido,sai dana gaji nace tafiya zanyi sannan ta hakura, napep muka tara muka nufi gida lokacin duhu ya fara sauka.
Muna cikin tafiya wayata tayi kara, ciro ta nayi ganin Kamal ne yasa na daga.
Magana muke wanda ta dauke hankali na har muka kusa wuce inda zamu sauka, da sauri na tsaida me napep din muka sauko na mika masa kudin har lokacin wayar na makale da kunne na.
Kasancewar har anyi magriba tasa layin babu kowa, da hannu daya na rike wayar da kayan dayan hannu na rike Iman dake min mitar na bata wayar su gaisa, tafiya muke a kafa ina cigaba da amsa wayata ban bi ta kanta ba.
Kamar walkiya haka naji an fizge hannu na dake hade da nata, kafin nayi wani yunkuri an watsa min wani abu mai matukar yaji da radadi a idanuwa na, bansan lokacin dana saki kara mai karfi ba cikin tsananin azaba na durkushe a wajen.
Ina jin sahun digadigan su, ina jin ihun Iman mai haɗe da kiran sunana, a birkice na tashi ina laluben ta, tsananin duhun daya mamaye ido naa yasa na kasa aiwatar da komai.
Ƙarar tashin motar su kawai naji, na sake yunkura wa da dukkan karfi na, sai dai ban yi ko da taku daya ba naji an shaka min wani abu da yasa na daina gane komai.
Rano
Manage 🚴🚴🚴🚴🚴🏇🏇🏇
0 comments:
Post a Comment