★★★★★
Kukan da nake ya dawo hankalin mutane wajen, da sauri wani makocin mu daya shaida ni ya karasa gida ya kira Baba Altine, a kideme ta fito babu ko mayafi, tana gani na ta hau salati tana kuka. Zuwa lokacin radadin da nake ji ba kadan bane a idanuwa na, kama ni aka yi da taimakon wani Alhaji ya bada aron motar sa aka dauke ni zuwa asibitin.
Kamal a rude ya fito daga dakin sa, part din Iyayen sa ya nufa riga a hannu yana kokarin sakawa, Ammi na zaune ta tallafe fuskarta da hannun ta ya shigo a kid'ime.
"Ammi ina Daddy?" Yace a rude yana kallon ta.
"Menene?" Tace tana tashi tunanin ta wani abun ne ya faru.
"Kano zan tafi, akwai matsala."
Yayi hanyar fita daga falon, da sauri ta riko shi, tana kallon yanayin sa
"Kana da hankali kuwa? A daren nan? Wai menene ma ya faru?"
"Ban sani ba wallahi, kawai muna magana da Aminatun, naji ihu sai kuma na daina jin komai, ina ta kira kuma wayar bata shiga."
"Yarinyar da ka bani labari? Har yanzu kuna tare kenan."
"Ammi pleaseeeeee, suna bukatar taimako wallahi, bari kawai naje wajen Old Woman nasan ita zata fuskance ni."
"Tsaya." Tace tana daukar wayar ta, Alhaji Marwan ta kira, bai dauka ba har ta katse, ta sake kira sai ya biyo ta da text message suna wani meeting ne zai kira. Ajiye wayar tayi tana kallon dan nata
"Ka yi hakuri mahaifin ka ya dawo kamal, yanzu dare yayi."
"Amma..."
"Dan Allah, I can't risk loosing u, kasan dai yadda tafiyar dare take, ka bari kaje by flight idan Allah ya kaimu, yanzu ka duba available flight da time."
Kamar zaiyi kuka amma dole ya hakura ya koma dakin sa, tsawon daren kiran wayar ta kawai yake amma bata amsawa, haka dai ya hakura yana ta Allah Allah gari ya waye ya je ya gani, ya rasa dalilin daya sa ya damu da ita sosai da al'amuran ta.
***
Idan nace muku na runtsa tsawon daren toh nayi karya, kafin safiya idanuwan sun haye sunyi suntum, bana ko iya bude su ga bakar azaba, duk da wannan tunani na na wajen yata, waye wannan da zai sace ta, wai me nayi wa mutane ne har haka da ba zasu barni nayi rayuwa ta ba, iya sani ba bani da wani abokin gaba ko fada, amma me yasa hakan ke kasancewa dani.
Shigowar Anas dakin tare da yan sanda yasa nayi shiru daga kukan da nake na zuci, dan likita ya hanani kuka saboda idon nawa zai kara rikicewa.
Tambayoyi sukayi min suka fita, kamshin turaren sa daya sake kusantoni yasa na gane ya matso sosai
"Sannu." Yace yana dora hannun shi saman goshi na. Bance komai ba,zuciya ta ta riga ta karye, ina ji kamar numfashi na zai yanke na bar rayuwar baki daya. Shiru ne ya biyo baya, ina jin motsin sa yana taba abu a jikin gadon, kafin yace
"Ina zuwa."
Yana fita Baba Altine ta shigo Kamal na biye da ita, kamar wadda wani dangi ko dan uwanta ne yazo haka naji, duk sai naji komai na sake bijiro min, mantawa nayi da kashe din likita na shiga rera kuka sosai suna bani baki, shigowar likitan ya katse min kukan da nake, tare suke da Anas, ganin Kamal a dakin ya dan sha jinin jikin sa kafin ya basar yana sauraron bayanin likitan.
Aiki za'a shiga dani na gaggawa, saboda haka aka wuce dakin gwaje gwaje, babu wanda ya matsa nan da can a cikin su har zuwa lokacin da sakamakon ya fito. Daga nan aka wuce dani zuwa dakin theatre domin gudanar da aikin.
****
Daki ta shiga da sauri ta hau harhada kayan ta, har lokacin kuka take, yaran na tsaye bakin kofa kowa yayi shiru jiki a matukar sanyaye suke duban mahaifiyar tasu, idan da sabo sun saba duk lokacin da abin ya motsa sai anyi da gaske take hakura, sai dai yau zuwan wannan bakon ya so saka su a tunani, iya sanin su babu wanda yake zuwa musu da sunan dan uwa ko wani dangi, haka nan suke rayuwar su daga su sai iyayen nasu biyu.
Shigowar Abban nasu dakin hannun sa rike dana Farouk yasa suka matsa gefe suna jiran suji mai zai faru.
Anty Safiyya na ganin sun shigo tayi saurin rufe akwatin kayan ta tahau jan ta da sauri tana nufo su, kama hannun Farouk tayi cikin kuka tace
"Wuce mu tafi, ba zan sake zaman ko da awa biyu bane a garin nan na gaji!"
Gam ya rike hannun mata idanun sa na kadawa, duk da har lokacin ya kasa tunanin abubuwan da yadda suke sai dai tsantsar tashin hankalin da yake gani a idanun uncle Aliyu kadai ya isa ya gane akwai gagarumar matsala. Mai yasa tsawon wannan lokacin babu wanda ya nemu su?"
A gefen gadon ya zaunar da ita, ya rike mata hannu yana durkusawa a gaban ta, ganin taki daina kukan yasa hannu ya shiga share mata hawayen kafin yace
"Dan Aallah ki daina kuka, idan kina kuka mu fa? Dukkan mu zaki saka muyi kuka."
"Ina Ja'afar?" Tace tana share hawayen nata
"Ja'afar yana nan cikin koshin lafiya."
Girgiza kanta tayi
"An min adalci kenan? A rabani da d'ana tsawon wannan shekarun ba tare da ya ganni ba Farouk?"
"Kiyi hakuri."
Uncle Aliyu ne ya matso jikin gadon yana rike mata hannu
"Safiyya... Nasan kina dauka ta a cikin mutane mara sa adalci da son kansu ko? Kina tunanin na rabo ki da kowa naki na kawo ki nan, ki sani bani da zaɓi da ya wuce hakan, ba'a son raina hakan ta faru ba."
"Kullum magana daya kake, baka da zaɓi, baka taba zaunar dani ka sanar dani abinda ya kamata na sani ba, taya kake tunanin zan yadda da kai?"
"Bani da ikon sanar dake ne, sai dai a yanzu komai ya wuce, ni kaina ina bukatar ganin dangi na, dana kasa kare su na tsaya musu sanda suke da bukata ta, musamman Anty Abidah."
Cikin zumudi tace
"Kana nufin zamu koma gida?"
Daga mata kai yayi
"Tsawon lokacin nan ina jiran wannan ranar ne, duk yayi min ikirarin ba zan taba ganin ranar ba, sai dai ban fitar da rai ba, ina ta addu'a Allah ya kawo min karshen halin da nake ciki, Safiyya ba haka kawai na zauna anan ba, akwai babban dalilin da ya rike ni har wannan lokacin."
Juyawa yayi yana duban Farouk
"Ya akayi kazo nan, ga dukkan alamu ba yanzu kazo ba,yanayin ka ya nuna ka jima a kasar, menene ya faru?"
Ajiyar zuciya Farouk ya sauke yana jin an tabo masa tsohon mikin zuciyarsa, sai dai dole zai sanar musu komai saboda ga dukkan alamu Uncle Aliyu ya san wani abu dasu basu sani ba , sai dai kafin nan yana bukatar amsar tambayar dake nukurkusar zuciyar sa
"Ina da dalili babba na barin kowa na dawo nan da zama, sai dai na kasa auna fahimta ta a sanda na ganka, tun zuwa na farko kasar nan na fara haduwa dakai Allah be sa zamuyi magana ba, me yasa tun bayan tafiyar ku, babu wanda ya kuma neman ku, yasan inda kuke ko yayi maganar ku?"
Murmushi Uncle Aliiyu yayi ba tare da ya amsa ba ya jeho masa wata tambayar
"Tun tasowar ku ka taba ji ance maka yau ga Kawun ka Adam yazo?"
"Ina tunanin Uncle Adam ya rasu tun muna yara ai ko?"
"Eh ya rasu a idon duniya sai dai be rasu a idanun Aliyu ba, yana nan da rai yana yawo a doran kasa."
Zaro ido sukayi a tare da Anty Safiyya, ta tashi tsaye tana kallon mijin nata cikin rawar murya tace
"Ya akayi hakan ta kasance?"
"Babu amsar wannan tambayar taki sai a gaban mutanen da hakkin sanin hakan ya wajaba akan su, dole sai mun tabbatar da hakan ta hanya gamshashiya ba ta fatar baki ba, ƙaryata labarin mutuwar da ya dauki tsawon lokaci da wucewa ba abu bane me sauki. Musamman a wajen mutane irin su Adam wanda babu digo na imani a ransu."
"Tabbas akwai rudani a cikin wannan maganar Uncle Aliiyu, sai dai hakan yasa na fara wani tunani da hasashen wasu abubuwa ciki har da abinda ya faru dani, ina so zan sanar maka da komai da ya faru bayan tafiyar ku, ina nufin abinda ni ɗin zan iya dorarwa akai ba wanda ban sani ba, daga nan zan baka labarin abinda ya sa na dawo nan ɗin, ina fatan hakan ya bani haske a abun da na jima ina tunani da hasashen wanda yake da hannu a ciki."
"Madallah da kai, hakan ne zai taimaka mana kwarai wajen sanin ta ina zamu tabbatarwa da duniya abinda ya jima yana boye."
"Ina fatan haduwar mu ta zama warwawar manyan daurukan da suka dade a daure, ina fatan ya zama silar wanzuwar farin ciki a zukatan mutane da suka dade da mantawa da yadda farin ciki yake."
Madaidaicin study room din sa suka nufa, daga shi sai Farouk da Anty Safiyya, yaran na falo kowannen su ya samu abin tattaunawa da zuciyar sa, cikin gamsasshen bayani Farouk ya warware musu komai na abubuwa da zai iya sanar dasu, har zuwa lokacin da yayi bankwana da kowa.
Babu digon mamaki ko tashin hankali a tattare da uncle Aliyu bayan ya gama sanar dasu komai, a yadda ya nuna ma kamar dama yana da masaniya da dukkan abinda ya faru ɗin.
Da kyar suka barshi ya koma gida da niyyar zai dauko abubuwan bukatuwar sa ya dawo nan ɗin, sai a sannan ya tuna da maganar supervisor din sa daya ke kiran sa, a gaggauce ya tura masa mail na ban hakuri da bayanin uzurin daya riƙe shi, babu komai yace masa ya kuma sake bashi lokaci akan yazo ya ganshi gobe idan Allah ya kaimu.
Kwanan sa biyu ya gama tattare komai ya dawo gidan nasu, Anty Safiyya da duk ta tashi hankalin ta ta dauka ba zai dawo ba, sai data ganshi sannan hankalin ta ya kwanta.
Karatun sa daya zo gangara ya bada himma wajen hattama shi, shi kanshi a yanzu hankalin sa ya soma komawa gida, yana ji a ransa wannan lokacin zai hadu da Aminatu, duk da babu wani labari daya samu tun bayan zuwan sa game da komawar ta Shagari, amma kowanne lokaci cikin bibiya yake yana fatan Allah yasa ta koma.
Shirye shiryen komawar su ya kankama, gefe guda yana cigaba da zuwa shagon dan ba karamin sabo yayi da mutanen wajen ba, tun da suka ji zai tafi suka shiga tashin hankali, barin ma Mr John daya sakar masa kusan dukka ragamar wajen shi sai dai ya dan duba abinda yake ganin zai iya amma komai a wajen Farouk ke kula dashi cikin kwarewa da kaffa-kaffa.
***
Tsawon kwanaki hudu kenan tun bayan da akayi min aikin, sai dai ba'a cire ba sai zuwa karshen sati idan mai duka ya kaimu.
Kowacce uwa zata fuskanci yanayin tashin hankalin da nake ciki, batan d'a ba abu bane mai sauki, na rasa inda zan saka kaina, babu wani labari game da batan Iman, duk da kwantar min da hankalin da suke hakan bai saka hankalin nawa kwanciya ba, ji nake kamar na gudu daga asibitn na tafi neman ta da kaina,sai dai nasan daga Anas har Kamal suna iya kar kokarin su wajen ganin an samu ko da wani hint ne akan haka, kullum cikin jiran kiran su muke amma shiru kake ji kamar malam yaci shirwa, babu wani bayani gamsashe. Addu'a muka dukufa yi babu dare babu rana, ba ta kaina nake ba, buri na kawai naga yata, ita kadai ce dangin da nake dashi na kusa, duk wani da zai rabe mu da sunan kauna ba kamar ni da itan ba.
***
Ranar da za'a cire min abinda aka saka aka nannade idon dashi duk jikina yayi sanyi da tunanin abinda zan tarar. Dishi-dishi na soma ganin komai, nayi saurin runtse idon ina jin kamar sun sake kankancewa akan yadda suke a dah, a hankali na sake bude su ina duban mutanen da ke dakin daya bayan daya, har lokacin bana ganin su tar sai dai ina iya banbance komai da kowa, glass likitaan ya saka min hakan ya taimaka wajen kara karfin ganin nawa, sai dai babu kaso hamsin ciki dari na gani na adah.
Kuka nake so nayi amma babu hawayen ma balle har na saka ran zasu zubo, da zuciya ta na shiga kokawa cikin yanayi mara misaltuwa, an cuce ni an lalata min rayuwa yanzu kuma an kashe min baban jigo na rayuwar mutum, idan aka taba maka ganin ka an gama da kai, makanta babbar musiba ce sai wanda ya sami kansa a ciki ne kawai zai gane. Kai tsaye na yanke wa kaina hukunci na kira kaina da Makauniya, eh makauniya mana tunda menene banbanci na da wanda basa gani gaba daya, illar ido daga ranar da ya riga ya tabu toh daga lokacin sai dai hakuri saboda yadda zai tayin gaba.
***
Kai tsaye gida muka wuce bayan an sallame ni, babu Anas babu Kamal sai keke napep muka samu ya kaimu dauke da kayan mu, waya ta dake saman cinyata tayi kara, na dauka ina duban screen din, bazan iya karanta rubutun ba, dole na jawo glass din na saka na shiga bin rubutun a hankali ina kokarin karantawa, ji nayi idon ya fara ruwa, dole na rufe na kira shi kai tsaye ina manna wayar da kunne na
" Kina ji? Gamu nan tare da Daddy da Uncle Kabir, zasu duba ki sai kuma yayi miki maganar Iman, ina tunanin zai iya taimakawa idan yasa baki a kara tsaro sosai wajen neman nata, sai mun ƙaraso."
"Ai an sallame mu ma, muna gida."
"Kash, shikenan bari na fada musu, zan kira ki."
Kashe wayar yayi ya juyo baya
"Daddy Ashe an sallame su ma, wai suna gida."
"Toh, babu damuwa sai muje station din da kace case din na hannun su, idan yaso sai muji yadda za'a yi."
Kallon Daddyn su Farouk yayi yace
"Friend ban taba ganin Kamal ya zama so serious akan abu irin wannan lokacin ba, shiyasa nake so nayi supporting nasa with all I can."
"Hakan nada kyau, ban taba tunanin yara na bukatar support dinmu ba sai bayan na rasa Farouk, ban taba bashi dama yayi wani abu da kansa ba, i always find fault a kansa bansan me yasa ba, sai da kuma ya matsa nake dana sani."
"Suna bukata sosai, idan yaro yazo ma da abu ka fara bawa abun big thought,idan kaga akwai fault a ciki sai ka zaunar dashi ta cikin hikima ka fahimtar dashi illar abin, amma idan kace zaka zama tough toh yaran ka zasu na tsoron ka, ba kuma zaka taba sanin halin da suke ciki ba, komai a boye zasu dinga yin sa sai abu ya kwabe kuma sai kaji ana wallahi wallahi."
"Haka ne." Yace yana girgiza kansa.
Hirarrakin su suka cigaba har suka isa station din, waya Daddy ya daga ya kira commissioner of police na gaba daya Kano state ɗin ya sanar masa abinda yake so ayi, kai tsaye ya amince ya kuma hada su da head na station din da case din ke hannun su, a take aka chanja case din zuwa Babbar headquater su.
Dukkanin su a gajiye suke dan ba karamin yawo suka sha ba akan case din da kuma wasu harkoki na bussiness da suka shigo dasu garin na Kano, a gidan Dadah suka yada zango la'asar likis, zarewa Kamal yayi ya nufi gidan Aminatu dan tare zasu koma da Daddy sablda yadda ya ke kokarin ganin ya dora kamal ɗin akan komai na kasuwancin sa.
Har dare suna gidan sai da suka ci tuwo sannan suka tafi driver ya ajiye su a airport, abin ka da tafiyar manya cikin yan mintuna suka isa Abujan.
Dukkan abubuwan daya saba gabatar dasu sai daya kammala su kafin yayi shirin kwanciya, be iya zuwa ganin mahaifiyar sa ba yau kamar yadda ya saba idan ya dawo yakan je suyi hira yaji bukatar ta, har ya kwanta ya tuna da wani mail da wani abokin cinikayyar sa dake birnin London yayi masa tun rana, ya kuma kirashi akan lallai ya duba a yau din dan abin nada muhimmanci.
Tsam ya mike Ammi dake kwance ta bishi da ido tana gyara kwanciyar ta, hutun sa koda yaushe kadan ne, daren da yake samu ya huta ma sau tari yana kwanciya zai mike ya shiga wata sabgar kuma da na'ura mai ƙwaƙwalwa.
Shiyasa wani lokacin akan ce mara arziki yafi mai shi kwanciyar hankali da nutsuwa.
Zama yayi yana dora computer a saman dan karamin table din dake cike da tarkacen takardun sa, kunna tayi ya runtse idon sa yana jin kansa a cunkushe. Email ɗin sa ya shiga ya fara dubawa a hankali yana nazarin komai.
Tsawon lokaci ya dauka yana dubawa kafin ya kashe komai, wayar sa dake ajiye saman bedside drawaer ya dauka yana kokarin sata a flight mood sakon dake yawo a saman notification bar din sa yaja hankalin sa, budewa yayi ya soma karantawa
_"Cikar buri shine samun abinda zuciya ta kwadaitu dashi. Haka ma abu mai matukar muhimmanci na faruwa na da mutane masu muhimmanci.Kunyi tarayya akan abu guda, ba tare da sanin ku ba, saboda ku ɗin wawaye ne mayaudara. A yau abinda yafi komai muhimmanci a gareku kai da wanda kake kira aminin ka na hannu na. Ina fatan ku samu karfin zuciyar iya fuskantar abinda ke tunkaro ku!"_
Be fuskanci abu daya da sakon ke nufi ba, sake karantawa yayi ko zai samu wata amsa aciki, sai dai a yadda sakon yazo babu wani abu da zai iya fassarawaa ciki har ya gane inda maganganun suka dosa.
Menene sukayi tarayya da aminin sa akai? Abu kuma mai muhimmanci gare su? Dole yasa a bibiyar masa number sakon da safe idan Allah ya kaimu.
Gaba daya sai yaji dan guntun baccin dake idon sa ya kaurace masa, dole ya nufi toilet ya dauro alwala ya shiga nafilfili yana rokon ALLAH ya kare su daga sharrin masu sharri.
*Rano**DG*
*32*
★★★
Da safe ya tashi yana shiryawa sakon na cigaba da yi masa yawo a kwakwalwa, be wani tsaya karya wa ba ya karasa ya gaida Hajiya Turai a tsaitsaye ya fita.
Daddy shirye yake shima tun bayan da sukayi waya saboda haka yana fita suka hadu suka dau hanya, wayar sa ya ciro ya mika masa ya duba sakon, shi din ma bai wani gane komai ba, sai ya kashe ya mika masa yana kallon sa
"MD ban gane komai akan sakon nan ba."
"Nima hakan ce, kuma iya tunani na na kasa gane waye zai tura dashi?"
"Shine, hanya mafi sauki ayi tracing sakon,daga nan sai mu san yadda zamuyi."
"Shikenan." Yace yana lumshe idon sa, daren jiya bai wani runtsa ba, ba wannan ne karo na farko daya fara cin karo da irin wannan sakwannin ba, sai dai na yanzu yasha banban da sauran, idan har ya fahimta komene yana da alaka da abokin sa, hakan ya kara saka shi a taraddadin waye zai masa wannan?
Lokacin da PA d'insa ya bashi statement din dake kan sim card din yayi mamaki kwarai, suna da duk wani information da akayi register sim din dashi bashi da alaka da wanda ya rubuto sakon, ga dukkan alamu ma irin sim card masu register akan su ne sai dai kawai ka siye su a haka.
Shafa kansa yayi ya mikawa Daddy result din yana sake resting sosai akan kujerar office din nasa, dogon nazari Daddy yayi kafin yace
"Ina ganin so ake ayi wasa da hankalin mu, a shagaltar damu da abinda yake mai muhimmanci, karka damu zan san yadda za'ayi."
"Ok duk yadda kace haka za'a yi."
Wayar sa ce ta hau burari, duba wa yayi ganin KAMAL ne yasa ya dan tura hular sa baya
"Kamal ba zai barni na huta ba idan ban tashi tsaye akan case din nan ba."
"Da gaskiyar sa, atleast he's willing to help."
"Haka ne."
Yace yana bin kiran, magana sukayi kadan ya ajiye wayar ya cigaba da duba abubuwan da zai duba suna hira jefi jefi.
***
Duk motsin Farouk na kan idon Anty Safiyya, gani take kamar zata sake rasa babbar damar da take ganin ita kadai ce zata sata komawa ƙasar ta, ta gaji ainun, tana bukatar wani dangi a kusa da ita, ace rayuwa daga kai sai miji sai yaya. Tunanin da kachokam ya tafi akan Ja'afar, kullum kwanan duniya da tunanin sa take kwana take tashi, ba abu bane mai sauki a raba uwa da danta tun be san waye shi ba,tana bukatar ji daga gareshi, tasan matsalar sa, abinda yake so da wanda baya so.
Karatun Farouk ya kare, saboda haka uncle Aliyu ya shiga shirye shiryen dawowar su a boye ba tare da sanin kowa ba sai shi Farouk din.
Sai da komai ya kankama sannan ya sanar ma Anty Safiyya, ranar bata iya runtsawa ba kwana tayi tana duban ticket din tana hawayen farin ciki
Jirgin karfe sha biyun dare zasu hau, saboda haka sai bayan sun gabatar da sallar isha sannan suka fito, yaran duk basu da walwala idan ka cire mahaifiyar su da har nema take ta manta wasu abubuwan nata sai da Uncle Aliiyu ya ankarar da ita.
Duk da Farouk ba a wannan lokacin yaso ya koma ba, amma shima yana bukatar jin amsoshin dake dan kare a zuciyar sa.
***
Kuka nake na zuci na rasa wanda zan fadawa damuwa ta, yau tsawon mako guda kenan da kwanaki biyu babu labarin ta, Hajiyar su Anas sunzo sun duba ni ita da Ramlah da wata kanwarta sai dai yadda naga Hajiyar tayi min sai nake jin kamar akwai lauje cikin nad'i, ina kyautata zaton ba a son ranta ta amince wa Anas ba. Hakan kuwa be dame ni ba, dan ni yanzu ba ta aure nake ba, buri na daya shine naga yata na kuma san wanda yake kokarin kassara mana rayuwa ba tare da mun aikata masa komai ba.
Duk da Kamal ya bani tabbacin maganar tana hannu manya amma na kasa aiwatar da komai, magana ma idan ba Baba Altine tayi da gaske ba sai na wuni bance komai ba, daga uhum sai um um.
Murmushi na saki me matukar ciwo, bayan na dawo daga dogon zangon dana tafi na tunanin rayuwa ta,tun daga lokacin dana budi ido na na ganni a wannan duniyar me cike da mutane marasa tausayi da imani.
Mutane biyu masu matukar muhimmanci a rayuwa ta a yau na rasa su, ciwon da zuciya ta ke ciki ba zai misaltu ba, da kyar na mike daga kwanciyar da nayi,waya ta dake yashe a saman gado ta dau ruri a karo na uku, karamin tsaki naja kafin na mika hannu na dauka, kamar yadda na zata shi din ne kuwa, *Kamal*. Murmushi nayi daya fi kuka ciwo na katse kiran ina jingina da jikin dan madaidaicin fridge din dake daura da kofar shigowa dakin.
Sake shigowa kiran yayi na daidai ta zaman glass din ido na ina dagawa cikin muryar data fi kama da wadda bata da gata ko galihu nayi masa sallama cikakkiya kamar yadda manzon Allah (SAW) ya koyar damu.
"Ina ta kiran ki tun dazu."
Yace kai tsaye bayan ya amsa sallamar tawa.
"Sorry na tafi wani dogon tunani ne kamal."
"Zaki fara ko? Gani nan zanzo na dauke ki muzo nan station din, Daddy ma sun kusa ƙaraso wa shida Uncle Kabir."
Dan dum naji gaba na ya fadi nan da nan, dakewa nayi na amsa masa da toh na fito falon, Baba Altine na zaune tana tunani gefen ta karamar jikar tace data dauko ta tun zuwan da tayi ganin gida zaune tana barar gyada.
Zama nayi a gefe ina juya wayar hannu na, tunanin haduwar da zanyi da mahaifin kamal nake, duk sai naji na damu, kasan zuciya ta cike take da tsoron haduwar mu, ina jin karar tsayawar mota a kofar gida duk sai naji kamar an tsaida gudun jinin jiki na, a kasalance na mike ina kallon kiran sa ba tare dana daga ba na yi hanyar wajen.
Yana zaune ya zuro kafuwan sa wajen motar ya dago jin fitowa ta, bai tsaye wata doguwar magana ba ya tada motar muka bar layin.
Mun riga su isa station din saboda haka muka samu waje muka zauna zaman jiran su, basu iso da wuri ba sai bayan mun dade da isa, a waje Daddy ya tsaya yana amsa waya baban su Kamal ne kawai ya shigo, kaina a kasa ina kara jin abu mai kamar tsoro tsoro na fizgata, wuce mu yayi kai tsaye ya shige office din DPo ɗin, a dan rada rada nace ma Kamal
"I'm nervous."
Dariya ya saka yana duba na
"Kin cika tsoro."
Shiru nayi ina tunanin abinda yasa nake jin hakan, takun tafiya muka ji nayi saurin sake nutsuwa har suka ƙaraso gaban mu, a hankali na dago yayi daidai da duba na, kura min ido yayi cikin wani irin yanayi me kama da kallon sani, da sauri na furta
"Ina wuni?"
Kada kansa yayi a kajarce ya amsa yana maida hankalin sa kan Kamal
"Itace?"
"Eh itace Daddy."
"Ina iyayenki?" Ya wurgo min tambayar a bazata, da sauri Kamal yayi karaf yace
"Sun rasu ai Daddy."
Boyayyiyar ajiyar zuciya na sauke, ina jin dadin yadda Kamal ya cece ni, bansan amsar da zan bayar ba hakan kuma na iya jefa shakku a zuciyar sa, ina ji suka cigaba da magana da Dpo akan yadda za'a yi.
Daidai lokacin Daddy ya gama wayar da yake ya shigo ciki, dukkan su suka mike cike da girmamawa suka sara masa, hannu ya daga musu ya ƙaraso inda muke yana kokarin fahimtar maganar da suke.
"Ina fatan akwai wani improvement akan batar yarinyar?"
Da sauri na dago jin irin maganar Farouk, sai dai wannan girma ya yi mata rufi sosai inda kai tsaye zaka gane mamallakin muryar Baba ne, yawun bakina ne ya kafe a diririce nace
"Daddy?!" Sai a lokacin ya lura dani, ware idanun sa sosai yayi akaina cikin tsananin mamaki yace
"Kamar Aminatu ko?"
Sai na fashe da kuka da karfi ina daga mishi kai
"Ikon Allah." Ya furta yana dubana duban tsanaki
"Ko zuwan mu wajen Dadah sai data yi min maganar ki, ina kika shiga tsawon wannan lokaci?"
Ban iya bude baki nayi magana ba, sai kuka na daya karu sosai, ganin duk mutanen wajen sun juyo suna kallon mu yasa Dpo yace mu koma office din sa. Alhaji Marwan da Kamal sun shiga tunanin abinda ya hada mu, saboda haka muna shiga ciki Alhaji Marwan yace
"Me yake faruwa ne Kb? Ka santa ne? Ko shi yasa nake ji kamar na taba ganin ta tun shigowa ta wajen nan."
"Matar Farouk fa, wadda muke maganar ta ranar da Dadah."
"Ikon Allah."
Yace yana bi na da kallon tausayi, kamar an mintsini Daddy yayi saurin cewa
"Yarinyar da ta bata... Menene alakar ki da ita?"
" 'Yata ce!"
Na amsa kai tsaye ina sake sakin wani sabon kukan, tashi yayi yana zagaye dakin hankalin sa a matukar tashi, kenan da gaske bayan rabuwar su Da Farouk ta haifi abinda ke cikin ta har ma ta girma, idan haka ne yarinya ce wani tsani na warwarar wasu daurukan da har yanzu ya gaza warware su.
Da wani irin sauri ya mika hannu ya karbi wayar dake hannun Alhaji Marwan, kai tsaye ya shiga jerin sakonni ya fara dubawa, a kan sakon ya tsaya yana sake dubawa duban tsanaki, "abin da sukayi tarayya akai, ba tare da sanin su ba..."
"MD!" Ya kira shi da d'an karfi
"Yarinyar Farouk ce, ita ce ake magana a wannan text message ɗin, waye shi? Me mukayi masa da yake son ganin bayan mu?"
"Kana nufin abinda text ɗin ke nufi kenan?"
"Eh duba kaga, ya zama dole mu nemo shi ko waye, shine yake da amsar dukkannin tambayoyin mu."
Shiru nayi lokaci daya naji kukan ya dauke min, nauyin dake lullube a zuciya ta naji ya soma raguwa a hankali, sai dai ido na daya ke min wani irin zugi kamar na zuba masa yaji, su kadai yanzu suke maganar su sai Kamal daya zuba ido baya fuskantar komai, ni ɗin ma ba wani fuskanta nake ba, sai dai tabbas akwai wata kullaliya da ta saka aka sace min yata, kenan akwai me bibiyar rayuwa ta har bayan barin kauyanmu. Amal ce ta fado min, da ita kadai na taba haduwa har ta nuna min babu wata alaƙa tsakanin mu, ance zato zunubi sai dai a take zuciya ta ta shiga ayyana min ko tana da hannu a cikin batan Iman?
***
A kofar gidan Driver ya ajiye ta, fuskar ta sanye da bakin glass, ta sakala earpiece a kunnenta da alama waya take amsawa, sai data gama amsa wayar sannan taja jakar kayan ta ta shiga gidan, da mai aikin Dadah suka fara karo, bata ko bi ta kanta ba tayi hanyar falon tana yatsine, da gudu da fada jikin Dadah tayi saurin ture ta tana matsawa gefe
"Yar nema karki karya ni."
"Nayi missing dinki ne Dadah."
"Naji, tare kuke da Baban naku ne? Yayi min waya sun shigo garin tun dazu nake baza ido."
"Wai Daddy, ban masan yana nan ba, sai anjima kila idan ya gama abubuwan da ya kawo shi."
"Haka ne, ya mutanen gidan ya kowa da kowa?"
"Lafiya wallahi, bari n huta nazo naci abinci dan yunwa nake ji."
Ta mike tana jan jakar ta ta nufi daki.
***
Sai da suka gama komai sannan muka fito, Daddy ne ya dubi Farouk yace
"Kasan gidan Dadah ko?"
Soso kai ya hau yi yana kallon Alhaji Marwan, da sauri yace
"Yanzu duk zaman ka garin nan baka taba zuwa ba?"
"I'm sorry Dad." Yace yana matsawa dan yasan sauran bayanin
"Toh sai ku biyo mu a baya, chan zamu wuce Aminatu, ba zan iya bawa Dadah labarin da nake so na bata ba tare da ta ganki ba."
Amsawa nayi da toh muka bi bayansu zuciya ta na wani irin bugawa ina jin tsoron abinda zan tarar.
****
Sanye yake da dogon wando da riga longsleeve ya nade wuyan sa da abu mai kauri, hannun sa rike da Amir karamin dan uncle Aliiyu, bayan sa rataye da Jacket ɗin sa daya zare tun da suka ido Nigeria, cikin kankanin lokaci suka gama komai a airport dib suka tari cab kai tsaye suka nufi gidan Dadah bisa umarnin Uncle Aliiyu.
Kallon ko ina yake babu abinda ya sauya a dan tafiyar da yayi, kai tsaye unguwar suka shigo daidai lokacin da motar su Daddy ta tsaya a kofar gidan, runtse idon sa Farouk yayi yana tuno abinda yasa shi barin kasar gashi ya dawo dashi ba tare da sanin yadda zai tunkari mutanen da suka zama masa wani jigo na rayuwa ba.
Two hearts are about to reunite🏌️🏌️🏌️🏌️🏌️🏌️🏌️🏌️
idan kun shirya nima na shirya, let the game begins 🏇🏇🏇🚴
Idan na samu chargy zaku jini anjima. Manage dis wayata 3%*DG*
*33*
★★★★★
Tun kafin su k'arasa suka fito, Daddy ne a gaba Alhaji Marwan na biye dashi, sai kuma motar Kamal da ke tsaye a bayan tasu Daddyn, wani irin farin ciki ne ya lullube Uncle Aliiyu ganin mutanen da yake da muradin gani tsawon lokaci.
Rufe ido Farouk yayi ya kwanta sosai a jikin kujerar motar, a daidai lokacin Kamal da Aminatu suka nufi cikin gidan, har suka gama fita daga motar be dago ba sai da Uncle Aliiyu ya tab'a shi, kamar ba zai sauko ba sai kuma ya saki ajiyar zuciya ya fito yana kallon sararin samaniya.
Anty Safiyya ce a gaba yaran na binta sai Uncle Aliiyu da suka jera da Farouk yana mishi bayanin sauye-sauyen da ya gani.
A daidai lokacin Dadah na tsaye gaban fanfo tana daura alwala, da fara'a ta tarbe su maganar da take kokarin yi ta makale ganin wadda bata taba tunanin gani ba.
"Wa nake gani kamar Aminatu?"
Tace a dan kideme, tana matsowa inda nake tsaye kamar an dasa, tsananin farin cikin da nake ciki bazai misaltu ba.
Murmushi Daddy yayi
"Yau sai a bani tukwuici na ga Aminatu na kawo miki har gida."
Kukan farin ciki ta saka ta rungume ni jikin ta, kukan da nake kokarin rikewa ya kwace min muka shiga yi a tare, a yau na kara tabbatar da kaunar da matar take min, kenan sun koma nema na bayan na bar kauyanmu, wannan shine soyayya ta gaskiya ba tare da wani abu ba.
Sallamar Anty Safiyya ta katse dukkan me shirin magana, duk suka zuba mata ido cike da tsantsar mamaki, takawa take kamar wadda take tsoron yadda zasu karbe ta. Har ta tsaya a gaban Dadah babu wanda ya iya furta komai, shigowar Uncle Aliyu, Farouk biye dashi kansa a kasa kamar baya son ganin kowa ya kara jefa su cikin rudani, saki na Dadah tayi tayi wajen Anty Safiyya bakin ta a bude, yaran dake gefen ta, ta shiga bi da kallo daya bayan ɗaya tana kallon fuskar mahaifiyar tasu.
"Kabiru me yake faruwa, wa nake gani kamar Aliyu, Safiyya da Babana? Ban gama dawowa daga mamakin ganin Aminatu..."
A rikice Farouk ya dago jin an ambaci Aminatu, a lokaci daya ya dira a gabana, idon sa cikin nawa yake duba na, cikin wani irin yanayi da bazan iya misalta shi ba, rawa bakin sa ya soma kafin da kyar ya samu nasarar furta kalmomin a rarrabe,
"De..s...ti..ny."
Sai ya rike hannu na da sauri ya shiga jana yana kokarin barin gidan, Alhaji Marwan ne ya dakatar dashi ta hanyar rike shi, ya kuma bata rai sosai yana nuna masa ciki, daya bayan daya ya shiga bin mutanen dake tsaye a wajen kowa da kalar kallon da yake mana, sai kuma ya sauke idon sa akan Dadah dake kuka sosai, kukan daya sanyaya jikin kowa har aka rasa wanda zai iya cewa komai.
"Mu shiga ciki."
Alhaji Marwan daya fi kowa karfin hali yace yana nuna masa hanyar falon, mai aikin Dadah ce ta rike ta muka dunguma zuwa cikin falon har lokacin hannun sa sarke yake da nawa, kaina a kasa na gaza kallon sa, wani irin yanayi ne ke shiga ta yana bin kowanne lungu da sako na magudanar jinin jikina.
A kasa muka zube tare yaki saki na kuma, idon sa akaina baya tuna duk mutanen dake falon da matsayin su gareshi.
Kan Uncle Aliiyu na saman cinyar Dadah yana share hawayen dake faman reto a saman fuskar sa, girma da shekarun sa basu hanashi zubar da hawaye a wannnan lokacin ba, domin yana bukatar hakan. Saboda haka babu wanda yayi yunkurin tsaida shi sai daya gaji dan kanshi ya zauna sosai yana duban dukkan yan falon.
"Na tabbata duk wanda yake gurin nan yayi mamaki ganin mu, bayan shudewar lokaci da ina kyautata zaton babu wanda ya sake tunawa da Aliyu da matar sa Safiyya, sai dai mu bamu taba kwana ba tare da mun tuna da ku ba, duk da ba wai ina tuhumar ku bane, hakan ya faru ba tare da sanin daya daga cikin ku ba, haduwar mu da Farouk shine silar dawowar mu, wanda dama abinda muke jira kenan tsawon wannan lokaci da muka kasa dawowa din."
"Kamar yadda kuka sani, ni Aliyu na bar gida ba tare da sanin daya daga cikin ku ba, sai dai bani da zabi illa na tafi, dan a lokacin da na tafi bana cikin hayyaci na, ji nayi ba zan iya zama ba dole sai na tafi, da fari jihar fatakwal na fara yada zango duk da ba a bisa son raina ba, so nake kawai na bar kasar a lokacin, daga bisani Allah ya taimake ni na nemi gurbin karatu a jami'ar Cranfield dake birnin London, na samu, hakan ya saka na tattara na bar kasar ba tare da tunanin sake waiwayar kowa ba.
"Tafiyar da nayi da Safiyya ita ta taimaka min wajen tuna wanene ni, sanda na dawo hayyaci na hankali na yayi matukar tashi naji bana son sake kwana a kasar, bayan mun gama shirye shiryen komai ranar da zamu tawo na dan fita ina karasa siyan abinda zamu bukata na hadu da Adam, nayi mamakin ganin sa a kasar kuma ga dukkan alamu ba bakon kasar bane, take abinda ya faru ya dawo min, rai bace na tare shi zan soma magana yace
"Sako nazo baka, ka tabbata kai da barin kasar nan sai bayan cikar buri na, duk ranar da ka hadu da wani cikin mutanen dake da kusanci dakai, a rana zaka iya komai, sai dai ina maka albishir kai da haduwa da wani sai bayan ranka, kamar yadda kaso ka tona min asiri haka zaka kare rayuwar ka cikin kunci da dana sani."
Juyawa yayi ya bar wajen ban iya ce masa komai ba, kiran daya shigo wayata na maida hankali wajen dauka, kukan dana ji Safiyya nayi yasa jikina ya hau rawa, a nan take sanar min da an shigo an kwashe komai da zamu bukata wajen barin kasar, hatta yan kudaden da suka rage mana an kwashe komai, tun daga lokacin bamu sake samun damar barin kasar ba, haka muka cigaba da zama a kasar muna addu'ar Allah ya kawo mana karshen wannan musibar.
Toh kamar yadda kowa ya sani, Adam ya mutu a idon duniya, amma yana nan yana yawo a doran kasa yana aikata mugayen abubuwa, ina fatan wannan bayanin nawa zai saka Dadah ta sanar da kowa wani boyayyen sirri da ta sani, wanda sanin dana yi ya jefa ni a matsala, amma kafin nan ina neman alfarma ya zama a gaban Anty Abidah, domin a lokacin nake so komai ya warware, ina son na cika mata burin alkawarin dana yi mata na wanke ta daga zargin da ake mata."
"Kana nufin Adam yana raye?"
Daddy ya jeho masa tambayar kansa a daure cike da mamakin abinda Aliyun yace,
"Yana nan da ransa." Ya amsa kai tsaye
"Ikon Allah."
Ya dora
"Sai dai nasan yarda da hakan ba mai yiwu wa bane lokaci daya, ina bukatar lokaci dan tabbatar da haka."
"Me akayi masa haka mai zafi da yake kokarin ganin bayan mu?"
Yace yana duban Dadah data sauke kanta kasa, murmushi Uncle Aliiyu yayi, ya kalli Dadah ya kama hannun ta ya rike cikin nasa
"Ki taimaka ki sanar da kowa abinda kika sani, ke ce mahaifiyar mu dukka, ke kika haife mu saboda haka karki ji tsoron komai babu abinda ya isa yayi miki sai abinda Allah ya ƙaddara miki."
Kuka ta saka tana tuna abubuwan da suka faru, wanda take ganin kamar a lokacin suke faruwa ko kuma taso da maganar na iya saka komai ya kara tabarbarewa.
"Zan neme ku, kuyi hakuri yanzu." Tace tana goge fuskar ta
"Shikenan Allah ya kaimu."
Suka hada baki a lokaci daya, kallon Farouk Daddy ke tayi ganin yayi biris da kowa na falon kamar be san da zaman su ba, idanun Dadah na kansa haka ma Uncle Aliiyu na lura dashi tun zuwan su.
"Farouk!" Ya kirashi
Dagowa yayi yana duban sa cikin girmamawa yace
"Na'am."
"Baka gaida kowa a falon nan ba, ina fatan baka manta su waye a zaune a gaban ka ba ko?"
Kwarjini yaji yayi masa, idan ba haka ba bashi da niyyar tanka kowa a cikin su, musamman Daddy Da Dadah, wanda yake ganin sun fi kowa rashin son shi bayan yana da yakinin su suke fi kusanci dashi. Bai manta abinda Dadah tayi masa ba, ya kuma kasa tantance a wanne matsayi zai ajiye ta, ganin da yayi mata a yanzu kawai yaji yana bukatar tuntubar ta akan abinda ta aikata masa, yana so yaji dalilin ta na yin haka, a darare kamar wani bako yace
"Fatan na sami kowa lafiya."
Tsananin mamaki ya kama Daddy, ya gaza cewa komai sai Dadah ce da Alhaji Marwan suka amsa masa.
****Kiran sallar magriba yasa kowa ya mike domin gabatar da sallah, daki Dadah ta nuna min tace naje na yi alwala nayi sallah, ban mata musu ba sai dai ina so na tafi gida, nasan duk inda hankalin Baba Altine yake ya tashi yanzu, dan ma na sanar da ita in da na tafi ne.
Tana kwance na shiga dakin, ta ɗora kanta a saman pillow da alama bacci take kuma tana jin dadin baccin nata, kofar dana gani dake nuna alamun toilet na wuce ina tuna ranar dana hadu da ita da abubuwan data fada min.
Mik'ewa tayi jin wayar ta dake gefen ta nata vibration, ba tare da sanin ina ciki ba ta daga,
"Kina jina? Tashi maza ki duba min bakin da akayi a gidan, ki gani idan akwai Namiji Babba da matar sa da yara uku, yi maza ina jiran ki."
"Toh..." Tace tana mik'a, mikewa tayi ta tsaya tana duba fuskar ta a gaban mudubi kafin ta fita, babu kowa a falon sai Amir da Amrah babban yabi su Daddy masallaci, kallon su tayi kallon su waye ku kafin ta wuce dakin Dadah ta leka, Anty Safiyya na kan sallaya tana sallah dake gefe Dadah na gabatar da tata sallar ita ma, dan jim tayi kafin ta juya zuwa dakin nata, bata lura dani akan abin sallah ba, ta dauki wayar ta ta kira shi
"Na duba, naga yara biyu a falo sai wata mata a dakin Dadah tana sallah."
"What!" Yace cikin k'araji
"Da gaske kenan Aliyu ya dawo, Amma how comes?"
"Waye shi?" Tace tana zama
"Shine wanda ya raba ki da mahaifin ki tun kina tsumma, yanzu ma kuma zai sake wargaza min aikin dana jima ina yi, Amal so yake ya kashe miki uba ki zama marainiya gaba da baya, will you allow that?"
Da sauri ta girgiza kai
"Ba zan taba barin shi ba, nima ina bukatar uba kamar kowacce 'ya."
"Then zaki yi yadda nace?"
"Zanyi." Tace kai tsaye
"Good girl, zan kiraki anjima."
"Ok." Ta ajiye wayar, wayun bakin tane ya makale ta hau murza idon ta da sauri, kallo na tayi, nima na zuba mata ido babu ko daukewa bayan na gama sauraron wayar da tayi zan iya alakanta hakan da maganganun da naji anayi dazu.
"Me kike yi anan, yaushe kika zo gidan nan, waye ya kawo ki gidan nan?"
"Wanne kike so na amsa miki aciki?"
Nace mata ina murmushi
"Ni na kawo ta!" Ya shiga takowa cikin dakin yana kallon ta, sake shiga rudu tayi da sauri tace
"Ya Farouk!"
Daga mata hannu yayi
"Karki kuskura, kinji na fada miki."
Kasa nayi da kaina, ya iso gaban sallayar ya zauna yana tankwashe kafar sa, leka fuskata ya shiga yi, ganin naki yarda na kalle shi yasa shi sa hannu ya daga min fuskar.
"Gudu na kike Aminene? Nine Farouk dinki fa."
Gefe na kauda fuskata ina jin zafin abinda yayi min a baya, na farko saki na biyu ƙaryata abinda yake tsakani na dashi, wanda shine Ummul aba'isin jefa ni cikin gararin rayuwa.
"Please dan Allah kiyi min magana, shekara nawa? Kinsan yadda na azabtu da rashin ki? Kinsan wacce irin rayuwa nayi bayan na rasa ki? Dan Allah kiyi min magana."
Kamar tatsuniya haka nake jin maganar tasa, idan har abinda yake fada gaskiya ne me yasa ya rabu dani, yunkurawa nayi da nufin tashi ya sa hannu ya maida ni baya
"Wallahi baki isa ba, duk tsawon lokacin nan dana yi ba tare dake ba amma kiki cewa komai, haushi na kike ji? Me nayi miki?"
A zafafe nace
"Baka san abinda kayi min ba Ya Farouk? Baka sani ba? All this while ni kasan irin rayuwar da nayi? Why are you selfish? Shikenan nice me laifi saboda bani da gata balle galihu, daka tafi ka barni da ciki ka taba tunanin halin da zan shiga? Ka taba? Ka sake ni bayan ka koya min sonka, na shaku da kai na soka,amma nice abar tuhuma ko..."
Kuka ne ya taso min, na sake shi ina saka fuskata cikin cinyoyi na, be hanani ba, ina jin yadda numfashin sa yake kai kawo a saman kaina, tashi naji yayi, ya isa wajen da Amal ke zaune tana sharar kwalla yasa hannu ya fizgota ya dire ta a gabana
"Ki faɗa mata, ki faɗa mata komai da kula kulla ke da munafukan da suka tayaki, kin fi kowa sanin bani da laifi akan abinda take tuhuma ta, ki faɗa mata ko na kakkaryaki a wajen nan wallahi Allah."
"Ni...ni bansan komai ba." Tace cikin kuka, shaka ya kai mata ta shiga kakari, da sauri na shiga tsakani ina masa kallon mamaki
"Me kake yi haka? Dukan mace ya Farouk!"
Jin haka yasa shi sakin ta da sauri yana zama gefen gadon hannun sa rike gam da kansa, juyawa nayi na bar dakin da sauri, lokacin duk sun dawo suna zaune a falon, a gaban su Daddy na durkusa Ina share fuskata
"Zan tafi Daddy, dare yanayi."
"Eh kuma haka ne, na manta shaf Aminatu, ina farouk sai ya maidake, duk da zanso ki dawo nan ɗin amma for now tunda munsan inda kike shikenan."
"Aminatu." Dadah ta kira sunana, matsawa nayi gaban ta ta kamo hannu na
"Naji abinda ya faru, in Sha Allah za'a ganta, ki cigaba da addu'a kinji, sannan zaki dawo waje na zanzo da kaina har inda kike, kiyi hakuri kinga abinda kika tarar karki ga ban baki lokaci ba."
"Babu komai." Nace ina musu sallama, har waje ta rako ni kafin ta koma ciki.
"Wai kinsan matsalar idon ki amma kike ta kuka haka, me yasa?"
"Kamal dole nayi kuka, yanzu muje kawai zan maka bayanin komai ko a waya ne, Baba Altine na chan na jira na."
"Shikenan." Yace yana bude min motar, shiga nayi ya tayar muka tafi. Muna zuwa kofar gida na ga motar Ya Anas a ajiye da alama yana ciki kenan, fitowa nayi na masa sallama ina shirin shiga gidan najii yace
"Kinyi mantawa fa a bayan mota."
"Mantuwa?" Nace ina kallon shi
"Zo ki duba ki gani."
"Ni da ba idon kirki ba, duba min menene?"
"Ki zo dai ki duba." Yace yana kunshe dariyar sa, hararar sa nayi na dawo na bude bayan motar na zura jikina sosai a ciki, ji nayi an jawo ni gaba daya ciki, har glass din idona na nemam faduwa nayi saurin rike shi, fuskata daf da tashi har ina iya jin sautin fitar numfashin sa
"Kina tunanin zaki guje min ko?"
Kokarin kwace wa na hau yi ya rik'e ni gam, baki na bude zan sa kuka yayi saurin sa hannu a saman bakin nawa
"Kina kuka sai na baki mamaki wallahi."
Da sauri na hadiye kukan, ya sake ni nayi saurin fita daga motar, fitowa yayi shima ya leka yace
"Kanina zaka iya wucewa ni sai gobe."
Dariya Kamal ya saka yaja motar sa ya bar layin
"Muje ko?" Yace yana kallo na, kasa daga kafata nayi saboda tunowa da nayi Anas na ciki, ganin naki motsi yasa shi kama hannu na ya shiga jana har cikin zauren gidan
"Shiga zakayi?" Nace ina tsayawa ganin da gaske ciki yake son tura kansa
"I want to see my daughter dan jikina ya bani baby girl kika haifa min, baki da right na hanani ganin gudan jinina kuma."
Ya cigaba da jana, da karfi nasa na fizge hannu na ina sa masa kuka
"Ohh shit.!" Ya dawo baya yana duba na
"Kina so idon ki ya kara ciwo? Naji kamal na miki maganar ido."
Cikin shassheka nace
"Anyi kidnapping Iman, an kuma bata min ido na, bansan inda take ba."
"Me!!!!!" Yace yana zaro ido waje, girgiza ni ya hau yi da karfi
"Tell me wasa kike min dan Allah."
Sai kuma yasa hannu ya shiga shafa saman ido na
"Me yasa na tafi? Me yasa ban kara jira ba, menene amfanin rayuwa ta!"
Yace a rikice yana jawo ni jikin sa, da sauri na fada ya saka hannu ya rungume ni sosai yana kokarin boye hawayen sa.
"Waye Anan?" Yace yana haske mu da torchlight ɗin wayar sa.
****
Hello mutanen arziki, I'm sorry for yesterday duk da dama nace idan na samu chargy zaku jini.
Ga wata yar tambaya zuwa ga malaman zafafa
"Wai shin idan namiji ya saki matar sa ba tare da sanin sa ba, shin ta saku ko kuwa? Menene hukuncin sakin da Farouk yayi wa Aminatu a littafin DG? Shin ta saku tun da da kansa ya rubuta sakin duk da baya cikin hayyacin sa, kuma ba da gangan ya sha abinda ya gusar masa da hankalin ba, ko kuma bata saku ba?menene hukuncin hakan a musulunce. Nasan muna da manyan malamai cikin mu.
I ll be reading ur comments.
NagodeDG*
*34*
★★★★★
"Waye anan?"
Yace yana haske mu da torchlight ɗin wayar sa, da sauri nayi kokarin janye wa daga cikin sa amma sai yaki, ya sake kankame ni yana duban Ya Anas
"Baka iya sallama bane ko me?"
Wani banzan kallo Ya Anas yayi masa yana matsowa ransa na matukar suya da abinda ya gani, Aminatu rungume jikin wannan gardin, be taba tunanin ta a irin wannan yanayi ba, yana zuwa yasa hannu zai raba su Farouk ya nuna shi da yatsa yana maida ni gefe
"Karka kuskura kasa hannun ka jikin matata wallahi."
"Matar ka? Idan naki fa? Iskancin ya kai har ka biyo ta cikin gida saboda tsabar rashin mutunci ko?"
"Waye wannan?" Yace cikin bacin rai
"Ya Anas ne!" Na furta a dan tsorace dan duk na gama tsorata da yanayin sa
"Ya Anas, me yake anan? Me ya kawo shi?"
"Baka da bukatar sanin abinda ya kawo ni." Yace yana duban shi, sai kuma ya dube ni rai a bace yace
"Zo ki wuce ciki."
Ina kokarin daga kafata naji Ya Farouk ya rike ni
"Don't you dare, idan kika daga kafarki anan wallahi sai ranki yayi mugun ɓaci."
"Idan kai ka haife ta ba? Sai ka hanata, zo ki wuce kafin kiga fushi na."
A hasale na dakatar dasu ganin suna neman charja min kai, cikin kuka nace
"Dan Allah ku kyale ni da abinda yake damu na, ku dukka kuna da dama a kaina, dan haka babu wanda zan wa abun da yake so na bar daya."
"Ya Farouk wannan shine Ya Anas, mutumin da ya tallafi rayuwa ta ya dubi maraici na ya rik'e ni tsakani da Allah dani da 'yata."
"Ya Anas wannan shine Ya Farouk, tsohon miji na kuma mahaifin Iman."
Tana kaiwa nan tayi saurin fadawa ciki tana rufe kofar da zata sadaka da zauren gidan, da sauri Anas ya fice daga gidan ba tare da ya sake duban inda Farouk yake tsaye ba kamar an dasa shi.
Iska me matukar zafi ya furzar yana sake kallon gidan maganganun ta na masa yawo a tsakar ka, kenan tana nufin bata da alaka dashi a yanzu kenan? Da kyar ya iya jan kafafun sa ya kai kansa bakin titi ya tari abin hawa ya wuce gida.
A zaune ya tarar dasu dukan su, magana suke a tsakanin su, kai tsaye dakin daya saba sauka ya wuce yana jin kansa na matukar sarawa.
Har ya kwanta ya tuno da Kamal, dakin daya san zai same shi ya wuce kai tsaye, yana kwance yana kallon wani video a wayar sa yaji an turo,tashi yayi ganin Ya Farouk yasa shi dan sosa kai yana murmushi
"First time na kwanan ka gidan nan right?"
Daga mishi kai yayi yana dariya
"I see."
Sai ya mika masa waya
"I need her number please."
"An gama." Yace yana dariya, karba yayi ya saka masa, yayi godia ya juya ya koma in da ya fito.
Sai daya fara duba jakar sa ya ɗan samu cookies yaci sannan ya kuskure bakin sa ya kwanta yana kashe komai na dakin.
Aminatu na kwance ta rasa me yake mata dadi kiran sa ya shigo, kamar kar ta tashi haka take ji saboda yadda ko ina na jikin ta ke mata ciwo, ga wani irin ciwon kai me tsanani daya addabe ta tun ranar da aka rasa iman, duk da tana ji a ranta yarinyar ta na nan da rai sai dai hankalin ta ya gaza kwanciya musamman data fuskanci kamar akwai wata rigima data shafi Daddy da wanda ya dauke tan, da tunanin ta masu garkuwa da mutane ne su nemi kudi, sai dai a yanzu ta tabbatar wani game ne ake so a buga da rayuwar yar ta.
Tun tana kuka da hawaye ta dawo na zuci, ta dukufa fadawa Allah dan shine kadai zai iya kawo mata dauki a cikin halin da take ciki.
Ganin me kiran da gaske yake yasa ta lallaba da kyar ta jawo wayar, bata iya ganin me kiran ba saboda babu glass a idon ta, saboda haka daga kawai tayi tana maida kanta saman filon data tashi.
"Assalamu alaikum."
Tayi sallama a hankali, shiru ya biyo baya ta sake maimaita sallamar karo na biyu, jin babu alamun amsawa yasa tayi yunkurin kashe kiran yayi saurin katse ta
"Karki kuskura ki kashen waya wallahi."
Zare wayar tayi daga kunnen ta, ta kalli saman screen din kafin, kafin ta maida kunne ta
"Tell me, me ya sami 'yata,wanne progress aka samu neman ta "
"Ban sani ba nima, su Daddy ne akan case din."
"Yasan yarmu ce?"
"Ya sani jiya."
Ajiyar zuciya ya sauke da karfi
"Me yasa kika ki jin magana a gaban trash din nan, kinsan yadda maganganun ki sukayi hurting din na?"
"Uhum "
"Kiyi hakuri." Yace murya a kasa, bata amsa ba ya sake cewa
"I'm sorry for everything."
"Uhum."
"Talk to me Dan Allah, ki min masifa ma if you like, in ma duka na zakiyi ki dake ni idan zai sa ki hakura."
"Iman." Tace muryar ta na rawa
"Taci abinci? An mata wanka? Lafiyar ta lau, She's just a child ya kake tunanin zata iya coping without her mother,abinda ya damen kenan Please Farouk!"
Ta fadi sunan sa kai tsaye, tashi yayi zaune zuciyar sa na zafi yace
"Nayi miki alƙawarin dawo miki da ita sound and in a good health, karki manta 'yata ce nima, responsibility nace ba tasu Daddy ba, zanyi duk yadda zanyi."
Kukan ta na ya kara tsananta ya dafa kansa yana daidai ta zaman sa sosai
"Tell me anything da kike tunanin zai bani hint wajen neman yata, fada min komai."
Shiru tayi tana nazari, chan Amal ta fado mata da wayar data ji tana yi dazu
"Adam, shine first suspect yanzu duk da bansan takamaimai alakar su da Daddy ba, Ina tunanin game ne yake so yayi playing da su, yasan wace ni yasan alaƙa ta daku tsawon lokaci yana bibiyata."
"Sannan..." Sai kuma tayi shiru
"Sannan me?" Yace
"Amal, naji jiya tana waya, ban yarda da wayar da take ba."
"Will you be my personal lawyer?" Yace yana murmushi
Murmushin tayi kadan tana runtse idon ta
"I love everything about Aminene ta."
Yace yana jan numfashi, wani iri taji ta sake danna kanta sosai a saman filon data ke kai, tana jin sautin fitar numfashin sa a hankali.
"Goodnight, kiyi mafarki na da Iman mun saki a tsakiya kinji?."
Daga kai tayi kamar yana ganin ta ta ajiye wayar tana lumshe idon ta.
File din ta dake kusa da ita ta daga filon tasa ba tare da ta buda shi ba kamar yadda tayi niyy.
***
Yana ajiye wayar ya shiga zagaye a dakin, badan dare ba sai yaje dakin Amal. System ɗin sa ya ciro cikin kayan sa ya kunna ta, e-mail ɗin da akayi masa wajen 3days back yaja hankalin sa sosai, a tsanake yake bin komai yana gid'a kansa cike da tsananin farin ciki
***
Kukan da take ne ya katse sakamakon wayar ta data dauki suwwa,da bayan hannun ta ta goge fuskar sannan ta daga tana karawa a kunnen ta.
"Baby kina jina? Karki bari asan muna waya dake, zan dan daina kiran ki kwana biyu amma ina so kizo address din da zan turo miki akwai abinda nake so na baki kiyi min wani aiki akai kinji?"
"Toh." Ta amsa a cunkushe
"Me ya faru?" Yace jin muryar ta a shake
"Ba komai."
Tace tana kashe wayar, ba'a jima ba text message ya shigo, bata bude ba ta cillar da wayar tana kwanciya a kasa, babu abinda yanzu take bukata face ace auren ta da Ya Farouk na nan, ganin Aminatu da tayi yau ya kara dagula mata lissafi. Kishin ta take sosai kamar zata mutu. Da kyar ta samu bacci barawo ya sace ta ba tare da ta shirya ba.
Da safe ta tashi a makare idon nan duk ya kumbure, tana jin maganganu a falon tayi tsaki ta fada toilet, wanka tayo tazo ta gyara fuskar ta kafin ta duba text message ɗin da yayi mata, duba address din tayi ta ajiye ta karasa shiryawa ta fito falon.
"Idon ki kenan Amal? Duk jiya baki ji alamun akwai baki gidan nan ba?"
Dadah ta tuhume ta cike da mamaki
"Na shigo da magriba kuna sallah, bacci nayi da wuri kinsan na kwaso gajiya."
"Okey yayi kyau, baki ga bakuwa ba?"
"Ina kwana?" Tace a gajarce
"Lafiya lou." Anty Safiyya ta amsa kafin tace
"Girma ba wuya Amal an zama yan mata."
Haushi ne ya kama Amal ta tashi ta koma daki ta zauna tana tunanin yadda zata fita ba tare da kowa ya gane ba.
Duk tunanin ta ya tsaya ta rasa ya zatayi gashi daga ganin alamun zaman da Dadah tayi a falon babu ranar tashi.
Curtains ta yaye jin alamun za'a ta da mota, Kamal ne tsaye suna magana da Farouk, jingina tayi da bangon tana kare masa kallon tsaf, zuciyar ta bata san komai ba sai soyayyar sa, yayi kyau ya sake mirjewa kamar bashi ba. Ganin ya juyo yasa tayi saurin sakin labulen tana sauke ajiyar zuciya.
Cigaba tayi da tunanin mafita har zuwa sanda ta sake jin maganganu sun sake karuwa a falon
Alamun taba kofar dakin taji kafin tace wani abu ya budo ya shigo kai tsaye.
"Come out!"
Yace daga bakin kofar kafin ya juya, hadiye yawu tayi da k'yar ta tashi kamar wadda kwai ya fashe wa a ciki ta fito falon. Daya bayan daya ta shiga raba idanun ta tana binsu d kallo, kafin ta shiga jan kafar ta isa gaban su tana zama kasa. Daya Daya ta gaishe dasu Daddy zuciyarta na cike da tsoron kiran da aka mata
"Ina wayar ki?"
Ya Farouk ya mika mata hannu alamun ta bashi, gaban tane ya fadi ta hau rawar jiki. Daka mata tsawa yayi data firgita ta tayi saurin miƙa masa wayar, kai tsaye call log dinta ya fara shiga ya duba numbers din datayi waya da call duration kafin ya fita ya shiga messages, da sakon shi ya fara cin karo ya yi shiru yana karanta sakon, tabbas hasashen da Aminatu take gaskiya ne, Amal nada masaniya akan komai, number ya dauka akan wayar shi da message ɗin ya isa gaban Alhaji Marwan ya mika masa wayar yana komawa wajen zaman sa.
"Menene dalilin tara mu da kayi anan Farouk?"
Alhaji Marwan yace yana kallon wayar Amal din ba tare da ya duba ba.
"Daddy ka rike wayar ko da za'a kira, ina da maganar da zanyi kafin a gangaro maganar wayar."
"Toh muna jinka."
"Da farko dai ina neman yafiya a bisa laifin dana aikata na tafiya na bar kasar,hakan ya faru ne a bisa dalilai na da nake ganin sun kai na zartar da komai. Sai dai ni kaina bani da masaniyar takamaimai abinda ya faru, tun bayan da ƙaddara ta haɗa ni da Aminatu har aure ya shiga tsakanin mu zuwa sanda na bar gari zuwa wani aiki da dawowar da nayi na tarar da mugun labari da bani da masaniya akai."
"Naso kwarai Daddy ya bani dama ko sau daya na kare kaina amma hakan be samu ba, a dole na tsananta bincike anan ne na gano akwai hannun Amal a cikin abinda ya faru daya jawo rabuwa ta da Aminatu."
"Na kirata na tuhume ta da laifin dana kamata dumu dumu na kuma bukaci na ji wanda ya sakataa, to my surprise sai gashi ta kira sunan mutanen da nafi kusanci dasu, Dadah da Ja'afar wanda duk duniya ina ganin idan akwai wanda na yarda dasu toh su biyo bayan su,wannan dalilin shi yasa ni tafiyar dole dan bazan iya zama ina kallon su da abun ba."
"Innalillah wa inna ilaihi raji'un."
Dada tace tana kallon Amal kallon tsantsar mamaki.
"Muna sauraron ka." Uncle Aliiyu yace
"Na tafi da clip din da aka dauka lokacin da nake rubuta sakin da kuma voice recording din da akayi lokacin da aka kirani a gaban kowa dan a tambaye ni dalilin abinda na aikata. Da fari na shiga rudani sosai dan bani da hujja da zan ƙaryata hakan, na farko dai murya ta ce gata nan, na biyu ni ne zaune ina rike da takarda da biro."
"Tsawon lokacin nan nayi shi ne cikin binciken yadda akayi hakan ta faru, ban samu ba, haka na hakura na bar wa Allah komai. Sai gashi jiya cikin hukuncin Ubangiji mutumin da ya taimaka min kwarai wajen bincike na yayi min e-mail inda yake tabbatar min da duk abin da yake cikin clip din da kuma abinda yake a recording din nan shiryayye ne anyi amfani da lastest technology da wasu set of intelligent agencies dake ƙasar Amurika ke amfani dashi wajen sauya abin, yana so na tsananta tunani na gano abinda ya faru a rana makamanciyar da abin ya faru."
"Tsawon daren jiya ban runtsa ba ina tunanin abubuwan da suka faru, tunani na ya dawo nan take sanda nake tuna tabbas Amal ta kawo min abu nasha a ranar sannan munyi hira data shafi Aminatu tana min tambayoyi ina amsawa sannan tabbas ranar ina rubutu ne ta tarar dani, wannan abubuwan su aka juya aka sauya zuwa komai, ba dani aka yi waya ba sai dai tabbas murya ta ce,magana ta ce aka hada yayi daidai da abinda Daddy zaku tuhume ni akai."
Murmushi yayi me ciwo yana janyo system ɗin sa ya tura ta gaban Daddy kafin ya dora
"Ina fatan wannan shaidar kadai ta isa ta wanke ni daga zargin da ake min sannan ina so ta fada a gaban kowa gaskiyar abinda yake faruwa. Me yasa lokacin dana tuhume ta ta nuna min tabbas na rubuta takardar kuma bana hayyacina, me yasa ta boye min gaskiya ta sake nisanta ni da matata da yata, me nayi mata haka mai zafi ta na chanchanci wannan?"
"Annamimiyar Allah!" Dadah tace tana saka kuka, kukan Amal take sosai itama ta kasa cewa komai, girgiza kai Daddy yayi cikin yanayi mara daɗi yace
"Adam yayi amfani da yarintar ta ya bata mata tunani."
Wayar ta Alhaji Marwan ya duba kafin ya mika wa Daddy shima yaga text message ɗin
"Amal me yasa ki aikata haka?"
"Daddy kayi hakuri."
"Tell me, zan saurare ki, me yasa? Saki yayi ko? Me yace miki?"
"Daddy ni tausayin sa nakeji, babana ne, ina son sa yace kuma kashe shi zakuyi tunda kai soja ne."
"Haka yace miki?"
"Eh."
"Shikenan daina kuka, mesa zamu kashe shi, ba haka bane kinji? Shiryawa zamuyi dashi mu nemi gafarar sa laifin da mukayi masa, can you help us?"
Shiru tayi tana tunani, kallon fuskar Daddy take, babu alamun karya a maganar sa, bayan haka ma be taba musu alkawari ya saba musu ba komai shi yake musu, sai ta samu kanta da daga mishi kai.
"That's my girl, bata wayar ta MD, text him kice kina hanya kinji? Kije ki gan shi babu damuwa."
Kallon sa tayi ya dage mata kai cike da gamsar wa
"Kije Allah yayi miki albarka, karki sanar dashi munyi maganar nan a waya sai kinje yanzu text kawai zakiyi masa."
Tashi tayi tana goge fuskar ta ta wuce daki.
"Me hakan ke nufi?"
A cewar Uncle Aliyu
"Shine kawai mafita, bin ta zamuyi dole sai an kama Adam a hannu komai zai warware."
"Lallai akwai banbanci, na kara tabbatar da kai din jami'in tsaro ne, kudos."
Duk sukayi murmushi banda Farouk da yake kallon su kawai.
****
Kiran wayar ta ya fara yi bata daga ba, kai tsaye ya shiga gidan bakin sa dauke da sallama, shiru gidan lokacin Baba Altine ta shiga makota siyo koko, Aminatu na toilet tana wanka saboda haka bata ji shigowar sa ba, sakon da Ya Farouk ya bashi ya ajiye a gefe yana kallon falon, idon sa ne ya sauka akan file din dake yashe a kasa, garin sauri ta manta ta dauke filon bata dauke shi ba, kamar kar ya taba sai kuma yaji yana son ganin date of birth din ta ganin file ne na asibiti.
Kai tsaye yasa hannu ya dauka, sunan asibitin dake rubuce a saman file din dayayi daidai da irin sunan dake jikin birth certificate d'insa shi ya kara jan hankalin sa, murmushi ya saki yana jin dadin ganin ashe ma asibiti daya aka haife su,yana budewa yan kananun passport din dake ciki suka fado be bi takansu burin sa kawai ya ga date ɗin ta dan suna yawan musun ta girme shi sanda suna makaranta.
Mamaki ne ya kamashi ganin hatta date da time na haihuwar su daya ne, be kula da sunan ba yana dariya ya rufe ya tsuguna ya tattaro hotunan guda biyu, cikin tsananin mamaki yake kallon hoton yana sake kalla, hoton Ammi ne da Daddy, duk da dadewar da akayi da daukar hoton wanda idan ba sanin su kayi sosai ba ba lallai ka gane su ba, a birkice ya sake bude file din ya shiga bin sunan ta dake rubuce cikin babban harafi
"AMINATU MD"
Sakin file din yayi ya fadi a wajen daidai lokacin da Aminatu ta fito daga dakin a shirye tana kiran Baba Altine, ganin shi tsaye cikin wani irin yanayi yasa ta ƙaraso da sauri tana tambayar sa menene, be tsaya bata amsa ba ya juya da sauri ya fice daga gidan zuciyar sa na wani irin harbawa.
Masha Allah...
Duk naga bayanan ku, kuma zanzo insha Allah da hukuncin hakan a musulunce, Nagode kwarai Allah saka da Alkhairi. Allah ya taimaka ya bamu Sa'a baki daya.
RanoDG*
*35*
★★★★★
Tsaye tayi cikin tarardadin abinda ya faru, sai kuma ta bi file din nata dake yashe kasa da kallo kafin ta tsuguna ta tattara komai tana sake dubawa.
Ledar daya ajiye gefe me tambarin Shoprite ta dauka ta bubbbude breakfast ne me rai da lafiya sai yar karamar red rose me kyau sosai, dan karamin note din dake ciki ya fado, murmushi ta saka
"I love you"
Aka rubuta da wani irin rubuth me matukar birgewa, wato ya zama baturen karfi da yaji kenan, wani iri ta dinga ji kamar tana tafiya akan gajimare.
***Yana fita ya shiga motar sa ya kifa kansa saman sitiyari, fuskar Aminatu da bata da maraba da ta Ammin sa ta shiga yi masa yawo a saman ƙwaƙwalwar sa, tsawon wannan lokaci ashe da Ammi take masa kama ya kasa ganewa sai yanzu, hoton fuskokin iyayen nasa ya dinga kokarin haɗawa da nasa dana Aminatu sai dai ko kusa babu digon kama da sukayi dashi, sau tari yakan tambaya kansa da wa yake kama cikin iyayen nasa ganin babu yasa ya bawa kansa amsar kila wasu ya biyo a cikin dangin nasu tunda dama hakan na faruwa.
Tunanin sa ne ya tsaya chak, idan har Aminatu diyar Daddy da Ammin sa ce, shi kuma fa da yake da shekaru da komai irin nata ballantana yace ko kanwar sa ce, ji yayi zuciyr shi ta sake karaya da kyar ya lallaba ya bar kofar gidan ba tare da sanin kowa ba ya bar garin domin yana da bukatar sanin komai.
***
Ammi na zaune tana kallon talabijin cikin daya daga cikin jerin kujerun alfarmar dake zagaye da babban falon nata, rashin yara na matukar damun ta, tun tana yawon asibiti har ta hakura ta daina, babu wata matsala ta kai tsaye da za'a kira ta dashi daya hanata haihuwa.
Yanayin yadda ya shigo mata a firgice yasa tayi saurin ta tashi zaune tana kallon sa.
"Kamal!" Ta Kira sunan sa, kallon ta yayi sai kuma yayi saurin tattaro nutsuwar, tunowa da yayi bazai bari kowa ya san komai ba har sai ya gano ainihin abinda yake faruwa yasa shi sakin fuskar sa sosai ya zauna kusa da ita yana dora kansa a saman kafadar ta
"Ammi nah."
"Karka cemin dogon tuki kayi, ina Daddyn ya na ganka kai kadai?"
"Ammi ji nayi ina so nazo gida, ga Old Woman ta matsa shisa kawai na gudo gida Daddy ma be san na taho ba."
"Maganar yarinyar ce har yanzu Kamal?"
"Ki taya mu da addu'a Ammi, komai zai daidaita."
"Shikenan, amma gaskiya na soma gajiya da zaryar da kake tsakanin nan da chan, hanyar nan da babu kyau akwai risky."
"Babu abinda zai faru In Sha Allah."
"Allah yasa." Ta amsa ba don taso ba.
Bedroom d'inta ya shiga, ya dubo dukkan takardun sa masu muhimmanci, ciki har da birth certificate d'insa original din, da address din asibitin da aka haife shi ya wuce dasu dakin sa.
Be zauna ba ya tafi wajen Hajiya Turai, har dare yana chan suna hirar su gwanin sha'awa sai dai rabi da kwatan hankalin sa baya wajen yana tunanin yadda zai soma binciken kansa ba tare da sanin kowa ba.
***
Sai data fara sauya shigar jikin ta sannan tayi masa text message gata nan ta fito, handbag dinta dake ajiye saman drawaer tayi nufin dauka bata ganta ba, dubawa ta hau yi kafin da kyar ta gano ta, ta kusa shigewa karkashin gado, ba tare da tunanin abinda ya kai jakar wajen ba ta tura wayar ta fito, duk basa falon hakan yasa tayi ficewar ta kai tsaye, bata bi takan driver dake gidan ba ta fita titi ta tari abin hawa ta fada masa inda zai kaita.
Motoci biyu ne masu tsaron lafiyar Daddy sai motar da suke ciki su hudu wadda Farouk yake tukawa sai Uncle Aliiyu a gefen sa, Daddy da Alhaji Marwan na baya, tracker da Farouk ya sa mata a jikin jakar ta suke bi har zuwa sanda ta isa gaban building din da yake incomplete, saukowa tayi ta sallami me napep ɗin kai tsaye ta kutsa kanta ciki tana kokarin kiran number tasa.
A daidai lokacin ya saka Iman a gaba ta ƙatuwar wayar charger, ko ina na jikin ta duka ne beyi la'akari da kankantar shekarun ta ba, duk da yana bata abinci amma idan tayi mishi kuka dukan ta yake kamar ya samu babba, shigowar Amal wajen ya saki wayar hannun nasa yana dora hannun sa a saman bakin sa
"Shissh." Da sauri ta hadiye kukan ta saka dukkan hannayen ta biyu ta rike saman bakin ta
"Daddy, yarinya ce fa." Amal tace tana matsowa kusa da su
"Bani da time na tabbata by now Ali ya sanar dasu ina raye, ina so ki bawa Hajara wannan sakon, zata san yadda zatayi dashi."
"Toh yarinyar fa?"
"Itace makamin da zan yi amfani na yaki Kabir da MD, ina bukatar dukiya ta, ina so komai ya dawo waje na, na maida su abin kwatance kamar yadda suka zalunce ni."
"Idan har kana da damar hakan ba?"
Farouk ya shigo kai tsaye fuskar sa babu digon Rahma ko sassauci,kallon Amal gyatumin nata yayi cikin yanayi na tuhuma,
"Amal yaudara ta kikayi? Duk abinda nake ba saboda ke nake ba?"
"Bansan zai zo ba ai." Tace tana matsawa gefe gami da riƙe hannun Iman
"Idan bake kika fada musu ba, ya akayi suka san nan?"
"Duk yadda kake kafkaf tsawon wannan lokaci baka taba tunani wannan ranar ba?"
Zai yi magana sai kuma hankalin sa ya kai kan jakar hannun ta
"You are good as nothing Amal."
Yace ganin abinda ke jiki ba tare da ta sani ba.
Sosai hankalin sa ya tafi kan yar karamar kyakkyawar yarinyar dake tsaye tana raba ido, fuskar ta har dan tashi tayi saboda marin da take sha wajen Adam, babu tantama itace yar sa, yar da bata san mahaifin ta ba, very cute and innocent soul kamar Aminatun sa, takowa ya shiga yi yana zaro bindigar dake jikin gefen wandon sa daya karba wajen Daddy, kafin ya karasa Adam ya ciro tasa cikin zafin nama yayi kokarin riko hannun Iman, da sauri Amal ta hankad'a ta wajen Farouk yayi saurin riƙe ta yana sake dagowa.
"Amal!"
Ya ambaci sunan ta da dan karfi ganin abinda tayi masa, cikin zafin nama ya fizgota ya saita bindigar sosai a kanta
"Karka kuskura ka matso, idan ka matso zan saka bindiga na harbe ta har lahira."
Kuka Amal ta saka cike da mamakin abinda mahaifin nata ke shirin aikatawa. Dariyar rainin hankali Farouk ya saka kafin yace
"Wa zakayi fooling? Yar ka ce fa. Idan ka ga dama ka kashe ta yanzu waya damu?"
"Ok." Yace yana saita bindigar sosai yana kokarin jan kunamar bindigar Daddy ya dakatar dashi.
"Me kake bukata? Me kake so damu Adam? Me muka yi maka haka?"
"Ita tsohuwar bata fada muku abinda tayi min ba?"
"Yanzu me kake so?"
"Duk abinda kuka dade kuna tarawa, ina nufin dukiyar ka baki daya data MD, shine kadai zai fanshi duk abinda kukayi min ."
"Kazo muje gida a zauna sai a san yadda za'a bullo wa al'amarin, hannun ka baya rubewa ka yanke ka yar Adam."
"Ni na dade da sa gatari na yanke nawa, bani da alakar komai daku, babu abinda nake so fiye dana ga kun wulakanta, wulakanta mafi kaskanci."
"Daddy wanda yayi nisa baya jin kira, koma me akayi masa ya kamata ya zama mai yafiya, ka daina lallaba shi ba zai taba fahimta ba."
"Farouk kai yaro ne, Adam zaka karbi tayina kazo muje gida mu yi sulhu?"
"Har abadah." Yace yana sake riƙe bindigar sa sosai akan Amal dake kuka sosai har da majina.
"Well then, bani da zabi face na yake ka."
Yace yana nuna wa yaran sa hannu, kafin kace me sun zagaye Adam sun saka tsakiya,
"Retreat or die!"
Dariya ya saka
"Ka zata bani da cover, baka taba mamakin yadda na iya surviving this long years ba tare da na taba haduwa da wani ba, while I'm leaving right under ur noses? Ba kayi tunanin hakan ba? Adam bazai taba kamuwa cikin sauki ba, hatsibibine ni fiye da yadda kake tunani, sannan yanzu zamu fara wasa, best of luck Gen!"
Daga sama aka rufe su da kasa, nan da nan idon su ya rufe ruf kowa ya hau kici-kicin yadda zai ya kare idon sa, a lokacin ya samu ya gudu ba tare da sun ankara ba, sai da komai ya lafa suka neme shi suka rasa ya gudu.
***
A mota Farouk be iya tuki ba dole daya daga cikin sojojin suka karbi tukin ya rike Iman da ta galabaita sosai, Amal na gefen sa ta cusa kanta tsakiyar kafar ta tana faman shassheka, haushi da bacin rai kukan nata ke kara masa,ji yake kamar ya ce su tsaya a sauke ta.
Kai tsaye asibiti suka wuce da ita, domin tana bukatar a duba lafiyar ta. Sosai ta galabaita da yawan kukan da take sai rashin abinci ne suka haɗar mata, gashi da alama sauro yayi mata mugun cizo da har ya saukar mata da zazzaɓi me zafin gaske. Drip aka daura mata da allurai sannan aka gyara mata wajen da duk taji ciwo. A gefe Amal ta rakube bayan su Daddy sun tafi, Farouk be sake bin ta kanta ba ya shige dakin da aka kwantar da Iman din yaja kujera ya zauna ya zuba mata ido, babu abu daya daya raba ta dashi har duhun fatar shi dauka, idanun ta ne kawai irin na Aminatu da dan karamin bakin da zakayi tunanin karamin chokalin tea ne kaɗai zai iya samun sukuni shiga ciki.
Sosai ya shagala da kallon ta yana jin farin ciki mara misaltuwa, da zarar ta dawo daidai zai kwashe su su bar kasar ba zai iya zama ba, dan ya lura fadan na su Daddy me karfi ne dan haka bazai yarda a kara involving rayuwar aaminatu ko Iman ba.
Wayar sa ya ciro ya lalubo number ta, tana bukatar sanin halin da ake ciki ko dan lafiyar ta ita ma.
A lokacin zaune Aminatu take ta kunna karatun suratul Bagra tana saurara, sau uku kenan tana kiran Kamal baya picking sai ta hakura ta bari ta sake gwadawa anjima, saboda haka data ji karatun ya tsaya alamun shigowar kira ta zata shine. Number data gani a saman screen din ta sakata komawa ta lafe sosai a jikin katitar kafin ta daga
"Ina miki albishir da na cika alkawari, gani ga Iman."
A zabure ta mike
"Dan Aallah!"
"Allah." Yace cike da gamsarwa
Sai ta saka kuka
"Kukan me? Ke da zaki gode wa Allah."
Da sauri ta kai goshin ta k'asa cike da farin ciki tayi wa Allah godiya kafin tace
"Kuna ina yanzu? Lafiyar ta kalou? Me ya sameta?
"Duk wannan tambayoyin? Muna nan premier clinic an sa mata ruwa."
"Owk gani nan." Tace da sauri tana kashe wayar.
"Baba!" Ta kwala Kira
"An ga Iman."
"Alhamdulillah, Alhamdulillah."
"Dauko hijabin ki muje suna asibiti."
"Ina jiran ku a mota." Yace yana juyawa.
"Yaushe Ya Anas yazo?"
"Sanda kika fara waya, yana tsaye nace ma ya shigo falon yaki yace na miki magana."
"Ok." Tace tana yin gaba.
****
Da kallo yabi motar kafin ya kada kansa yana kara waya a kunnen sa
"Itace?"
"Ok done!"
Yaja motar ya bar layin.
***Kamar kurame babu wanda yayi wa wani magana har suka isa Asibitin, tambaya sukayi aka nuna musu dakin, da Amal suka fara gamuwa tana daga kofar dakin akan wani benci ta kasa shiga ciki, sallama sukayi mata ta dago tana kallon su, amsawa tayi ta maida kanta gefe.
Idon sa akan kofa yaji an turo, idanun su ne suka hadu waje daya, tayi saurin janye nata ta isa gaban gadon da sassarfa, kuka ne ya taso mata tayi kokarin tsaida shi sai dai duk da haka sai da ya zobo, Baba Altine ce ta karasa cike da jimami take kallon Iman din
"Allah sarki."
Cikin takun kasaita ya shiga takowa har ya iso gaban su, kallon kallo sukayi wa juna kafin Farouk ya dauke kansa yana jan karamin tsaki, hannu Anas yasa ya dafa kan Iman din akayi saa kuwa ta bude idon ta,tana ganin shi ta saka kuka tana kiran Abba tana mika masa hannu.
"Yi shiru kinji my angel." Yace yana shafa kanta
Riko hannun Aminatu tayi dana Anas tace
"Karku tafi ku barni kai da Ummi, kullum sai nayi kuka yayi ta min masifa kuka ki zuwa ku tafi dani."
"Karki damu kinji? Ba zamu kuma barin ki ba."
Sosai ran Farouk ya bci, ya hade girar sama data kasa ya shiga watsa ma Anas harara, ita kanta Aminatu bata bi ta kansa ba kamar ma ta manta dashi a wajen, murya ya shak'e yace
"Ba'a wa yaro hayaniya aka musamman wanda ba lafiya ce dashi ba, tana bukatar hutu an gode da dubiya."
Sarai Anas ya gane dashi yake, be kula shi ba ya sake shafa kan Iman din
"Baby Bari na dauko miki chocolate a mota ?"
"Uhum uhum..Karka ki dawowa."
"Zan dawo yanzu kinji?"
Daga mishi kai tayi tana lumshe ido
"Ina so muyi magana." Yace yana duban Aminatu, kallon Farouk tayi da sauri taga yadda yayi, fuskar nan tasa kamar wuta haka ya tamke ta.
"Baki ji bane Aminatu, yayanki Anas yana so kuyi magana."
Baba Altine tayi tsagal, yaki Aminatu tayi ta tashi da nufin bin sa dan tuni yayi hanyar fita Farouk yasa hannu ya finciko ta da karfi har sai da glass din idon ta ya cire ta fado jikin sa. Da hannu ya nuna ta cikin bacin rai yace
"Karki manta akwai igiyar aure na akan ki, ke idan ma babu ban yarda ki kebe da wani gardi ba wallahi, zan baki mamaki idan kikayi gigin aikata haka."
"Idan kai ne ka haife ta sai ka hana, dame kake takama ne wai?"
Anas ya katse shi a hasale, da hannu Farouk yayi masa nuni da Iman dake kwance
"Kaga abar da nake takama da, ba kuma zaka taba samun irin ta ba har abadah sai dai abi wani sarkin."
Cikin bacin rai Anas ya bar dakin, ko motsi Aminatu batayi ba, ita mamakin yadda Farouk ya zama take, kamar ba Farouk dinta na baya ba me saukin kai da son mutane ba.
***
Duk tsare tsaren da zaiyi ya gama shi, hatta address din asibitin da komai ya gama haɗawa waje guda, baya so Ammi tasan shirinsa saboda haka sai yayi mata karyar Kano zashi akan wasu harkokin Daddy da yake so ya fara duba wa, sosai taji dadi ta bishi da addu'a.
Kai tsaye tasha ya nufa karo na farko a rayuwar sa daya shiga motar haya, kamar akan kaya haka yake jin sa, sai dai bashi da wata hanya sai hakan. Kano suka fara zuwa kafin ya kuma samun wata motar zuwa Katsina.
Madam Inno😂 na zaune ta zabga uban tagumi tunanin rayuwar baki daya take, abubuwa da yawa sun faru, wasu ma nakan faruwa ciki har da yanayin da suke ciki yanzu na matsi da babu, duk jarin nata ya kare, ta dawo ta tsuguna sauran mazan gidan ne ke kokarin taimaka musu wani zubin da abinda zasu ci.
Nan da chan bata iya zuwa saboda yadda abinda ya faru ya gama zagaye ko ina na kauyen hatta ƙananan yara sau tari idan ta fita sai dai taji suna maganar hakan yasa ta tattara fitar baki daya ta watsar ta zauna ta fawwala Allah komai tana cigaba da jinyar Baba da ke cikin mawuyacin hali tsawon wannnan shekarun babu wani sauki sai godiyar Allah.
****
Yinin yau baki daya be duba wayar sa ba, aiki suke sosai akan wani kamfanin man gyada da yake son budewa a Niger, rabon da su hadu da Daddy yau kwana biyu kenan, shima ya zama busy sosai yana shirye shiryen ritaya ma saboda ya tattara hankalin sa waje guda, tun bayan abinda ya faru basu sake maganar Adam ba, sun barshi a matsayin ihu bayan hari ne kawai amma babu abinda zai iya, sun tuntubi Dadah da maganar tace su sake nata lokaci dole suka tattara suka ajiye komai.
Bayan ya gama duba komai ya tattare su waje guda, sakatariyar sa ya kira ya bawa ta kai office din Admin human resources sabida yana so komai ya kankama.
Babbar rigar dake jikin sa ya cire ya rataye ta a saman hanger kafin ya isa gaban dispenser ya tsiyayi ruwa ya sha sosai, sannan ya koma ya zauna yana jawo wayar tasa domin suba sakonni. Karon farko daya ji zuciyar sa tayi wani irin bugawa da karfin gaske, yasa hannu ya dafe ta yana kara bude idaon sa sosai akan sakon.
_"50million na dan ka dake amsa sunan ka KAMAL MARWAN DIKKO , 100million kuma na yar da baka san tana rayuwa ba, wadda jinin ka ke yawo a cikin jijiyoyin jikin ta, bata san kanta ba, bata san wacece ita ba,tayi rayuwar kunci da bakin ciki duk ta sanadi na."_
_"Dukkan wannan zabi ne ya rage naka ka zaba, idan kuma ba zaka iya sadaukar da million 150 ga yayanka ba, ina fatan zaka iya sadaukar da matar ka ba tare da sisin ka tayi kuka ba. Zabi ya rage ga shiga rijiya!"_ Adam
Rano 😍😍💯DG*
*36*
★★★★★
Number ya kira da sauri, ringing d'aya aka daga
"Adam, kana jina?" Yace jikin sa na rawa
"Ina jinka." Ya amsa a gadarance
"Yawwa, me kake nufi da sakon nan? Ban gane komai ba, me hakan ke nufi."
"Ina da tabbacin kai cikakken bahaushe ne ko? Lokacin boye boye ya kare ina so kaje kayi bitar abinda ka karanta da kyau zaka gane inda maganganun suka dosa, sai dai ka sani rayuwar Kamal na cikin hatsari, haka ma rayuwar yar ka da ni kadai zan iya tabbatar da hakan."
"Ya..." Katse kiran yayi ba tare da ya jira abinda zai ce ba, hanyar fita daga office din Alhaji Marwan yayi yana kokarin neman number Kamal, a kashe take cikin tsananin tashin hankali ya juya akalar kiran zuwa ga Ammi, fitowar ta kenan daga banɗaki taji wayar ta dake saman mirror na neman agaji, karasa wa tayi ta dauka
"Ina Kamal?" Yace a kid'ime
"Be dade da tafiya ba ai, na zata kunyi magana dashi kafin ya tafi, wani aiki ka bashi?."
"Ina ya tafi? Ban aike shi ko ina ba, be kuma fada min inda zashi ba, subhanallah!"
"Me ya faru?"
"Ina zuwa." Yayi saurin katse kiran yana neman layin Daddy
Hankalin ta ne ya tashi ta hau kiran layin Kamal din sai dai duk a kashe, tunanin Aminatu ne ya fado mata, bata raba daya biyu yarinyar ce tasa shi tafiya ba tare da izinin mahaifin shi ba, sannan yayi mata karya akan aikin Daddy xai je yayi, take tsanar yarinyar ya shiga zuciyar ta, ta hau zagaye a dakin tana tunanin mafita, alk'awari tayi ma kanta idan wani abu ya samu danta ba zata taba barin ta ba.
Gaba daya Alhaji Marwan ya birkice wa Daddy, tunanin sa kar wani abu ya samu Kamal d'insa, dan be san yadda zai iya dauka ba, a gefe guda kuma tunanin wacce yar tashi Adam yake nufi, iya sanin sa bashi da wata 'ya kawai Adam naso yayi wasa da hankalin sa ne tunda ya riga yasan tun bayan haihuwar Kamal din Ammi bata sake ko da batan wata bane, shiyasa kawai ya share maganar fatan sa kawai ya samu Kamal a waya yaji inda yake dan kwarai ya fara tsorata da lamarin Adam,ya soma tunanin komene akayi masa haka toh me girma ne a wajen sa.
****
Isar su Katsina ana ta kiraye kirayen sallar isha'i, hotel ya samu ya sauka da nufin da safe ya karasa garin na Shagari, baya jin dadin komai burin sa ya gano wani abu da yake da alaka dashi da Aminatu.
Be wani iya baccin kirki ba da sassafe ya shirya ya fita, asibitin ya fara zuwa da yake shi ba a cikin garin yake ba, ya tarar da wani mutum a reception, sallama yayi masa gami da mika masa hannu sukayi musabiha kafin yace
"Wani muhimmin abu ne ya kawo ni, takanas daga Abuja, ina fatan zan samu information din da nazo nema."
"Ok me kake bukata?"
"A asibitin nan aka haife ni, ga date nan da komai a jikin birth certificate d'ina, idan babu damuwa ina so ka binciko min file din da mukayi amfani dashi sanda muke zuwa Asibitin."
"Menene file number din?"
"0023."
"Ok ka dan zauna mu binciko shi, an kwana biyu zai danyi wuya."
"Owk." Yace yana samun waje.
Yana zaune mutumin ya dawo, hannun sa ya kalla ganin babu file din yasa shi cewa
"Ba'a samu ba ko?"
"Wallahi ba'a samu ba, abin mamaki duk daadewa ba'a rasa file amma wannan babu shi kwata-kwata."
"Dama nasan ba za'a samu ba. Amma dan Aallah ko zan iya sanin adadin mutanen da aka haifa a asibitin nan ranar da aka haife ni?"
"Da kamar wuya gaskiya, kaga an jima kuma mu ba wai muna da record bane cikin computer, manually ake komai dan haka gaskia ba zai yiwu ba."
"Idris ina aka ajiye file din Samira ne?"
Maganar ta ta riga ta ƙarasowa wajen, babba ce a kalla zatayi kusan sa'ar Ammi, kallon kamal tayi kadan kafin ta maida hankalin ta wajen wanda ta kira da Idris din tana masa magana,
"Wallahi Sister Asibi bansan inda aka sashi ba, ko yana wajen Lawal a tambaye shi."
"Sister Asibi?"
Sunan ya shiga masa yawo aka, idan har be manta ba shine sunan da ya gani akan file din Aminatu, sannan shine same sunan dake jikin nasa takardar, da sauri ya ciro ta ya duba, hakan kuwa ne, murmushi yayi ya bita da sauri ganin har ta kusa shiga wani office
"Dan Allah tambaya ce dani."
Ja tayi ta tsaya tana duban sa
"Ya akayi ɗan saurayi?"
"Am nidai sunana Kamal Marwan Dikko..."
"Anan aka haife ni, ranar 5 ga watan February, 1996."
"Kaga akwai ayyuka da yawa kaina, ina ganin ka nemi wani sai kayi masa bayani."
Tayi gaba da sauri, shan gabanta yayi yana bata rai sosai ganin da gaske so take ta gujewa maganar dan tun sanda ya ambaci sunan sa ta nuna alamun tsoro a idon ta
"Ki tsaya muyi magana ta fahimta kafin na sanar da hukumar asibitin, kece kika karbi haihuwa ta ko? Dan sunan ki ne a rubuce jikin takardar haihuwa ta."
"Shigo ciki."
Tace tana yin gaba, bin bayan ta yayi har wani office, suna shiga ta rufe kofar tana kallon shi
"Me kake so?"
"Ina son sanin waye ni? Me yasa sunana yayi daidai da na wadda aka haife mu rana daya, lokaci daya da ita, me hakan ke nufi?"
"Kai zan tambaya dan ban gane me kake nufi ba." Tace tana juya masa baya, murmushi yayi me ciwo kafin yace
"Ina bukatar sanin gaskiya, karki boye mun komai ki sanar dani, idan kuma ba haka ba..."
"Me kake so ka sani?"
"Waye ni? Wacece Aminatu? Ko ana so ace min mistake akayi wajen rubuta mana sunan mahaifi daya bayan an haife mu a lokaci daya a rana daya kuma asibiti daya? Ko ana so a cemin mu ɗin yan biyu ne, nasan ana iya samun suna iri daya, sai dai ba irin namu ba, hoton Daddy da Ammi dake jikin file dinta fa? Shima kuskure ne? Ba zai taɓa yiwuwav ba."
Hadiye yawu tayi me kauri ganin yadda yaron yake so lallai sai ya tono abinda ya dade da shudewa, abinda ta aikata wanda ta jima tana dana sanin amincewa zuciyar ta da tayi, kwanakin baya Inno da kanta tazo mata da rokon ta sanar da ita ko da address din inda aka kai mata dane, amma ita kanta bata sani ba.
Idon sa ne yayi ja sosai, ya sake duban ta a karo na ba adadi
"Shirun ki na nufin wani mummunan al'amari ya faru a ranar da aka haife mu, shirun ki ya tabbatar min da..."
"Tabbas nayi kuskure wajen amincewa zuciya ta, nayi dana sani mara amfani, ban taba tunanin wannan ranar zata zo ba."
"Kayi hakuri Kamal, tabbas mun zalunce ka zalunci me yawa, sai dai akan Aminatu kai gata mukayi maka, tun bayan lokacin ban sake haduwa dasu ba, sai dai har zuwa yanzu ina rayuwa ne da tunanin makomata."
"Me kike nufi?" Yace cike da dauriya dan zuwa lokacin zuciyar sa ta fara shiga mawuyacin hali
"Nice na chanja ka da Aminatu, nice sanadiyyar zaman ka duk abinda ka zama a yanzu, kuma nice sanadiyyar saka Aminatu a cikin mawuyacin hali, ba tare da sanin mahaifanta ba,son zuciyar mahaifiyar ka shine mafarin komai, da bata amince ba babu yadda zatayi hakan ta yiwu tunda ita lafiya lau ta haife ka tasan me ta haifa."
Dip ya daina ji kwata kwata, tsawon dakika biyar tana cigaba da jera masa bayanin da baya iya jin komai, a hankali jin sa ya soma dawowa, jiri ne ya kwashe shi yayi saurin dafa bangon office din, da sauri ta sa hannu zata tare shi ta dakatar da ita
"Menene kwatancen gidan?"
"Idan kaje ka tambayi gidan Inno babu wanda be santa ba."
"Waye ya saki aikata mana wannan mummunan aiki?"
"Bansan shi ba, sai dai na san sunan sa a lokacin da naji matar ta fada masa, Adam idan har ban manta ba, shi ya bamu kudi domin mu yi masa wannan aiki, ni, harira da mahaifiyar ka sai mace daya da suka zo tare, wadda ta zama wakiliyar sa dan ita muka sani bashi ba ."
Girgiza kansa yayi cikin sarkewar murya wanda yake jin numfashin shi na kokawa da gangar jikin shi ya soma magana
"Allah ya isa tsakanin mu daku, bazamu taba yafe muku abinda kukayi mana ba, ina rokon Allah ya wulakanta ku tun a duniya, ya bi mana hakkin zaluncin da kukayi mana."
Kofa ya nufa yana layi, kafin ya juyo yace
"Ki jira abinda zai biyo baya dan ba zan yafe miki ba, Shari'a ce zata raba mu."
"Dan girman Allah ka tsaya ka saurare ni."
Bugo kofar yayi da karfi, ta zauna dabas a kasa tana rike kanta, ina zata kama? Shari'a da Marwan Dikko ba abu ne me sauki ba tasan tabbas zai iya sakawa a rufe kaf dangin ta. Da sauri ta mike ta zari jakar ta ta fita da kofar baya.
***Da taimakon wani direbab mota daya dauka shata suka isa cikin garin, duk da dauriya kawai yake yi amma bashi da karfi da kuzarin tunkarar abinda yake tunkaro shi din. Tambaya sukayi aka nuna musu gidan, da ido ya shiga duban gidan da ya sake lalacewa ainun, yanzu mutane ne ke rayuwa a ciki? Ya tambayi zuciyar sa, a take ta bashi amsa da mutanen ma iyayen da suka kawo ka duniya, chije bakin sa ya yi ya fitar da iska mai zafi yana tuna girma da kyawun gidan su na Abuja, tabbas Aminatu ita aka cuta, aka sata rayuwa a muhallin da har ta bar duniya ba zata taba rayuwa a cikin sa ba, kwalla ce ta zubo masa yasa hannu ya goge.
"Sannu da zuwa."
Nura yace yana fitowa daga cikin gidan, saurin daidai ta kansa yayi ya mika masa hannu,tunanin Abinda zai ce mishi yake, sai yaji yace
"Wa ake nema?"
"Nan ne gidan su Aminatu?" Yace
"Nan ne, kana da labarin inda take ne dan Allah?" Ya amsa cike da zumudi,
"Zan iya ganin mahaifiyar ta?" Yace yana dauke wanchan maganar
"Bismillah shigo ciki." Yayi gaba da sauri, dan jim yayi kadan kafin ya kutsa kansa cikin makeken zauren gidan daya cika da yana.
"Inna, inna fito ga wani yazo ganin ki kuma da alama yasan inda Aminatu take."
"Yana ina?"
Ta tashi a zabure, tsaye yayi a bakin kofar ya kasa karasowa ciki, wannan itace mahaifiyar sa data zabi kudi akan sa, mahaifiyar data raini Aminatu a cikin kaskanci da tozarci bayan nata dan na cikin gata da jin dadi
Sararo tayi tana kallon sa, cikin sakannin da basu gaza biyar ba, ta kare masa kallo, kallon daya tabbatar mata da zargin ta, da sauri tayi kansa tana duban damtsen hannun sa dake bude cikin riga me gajeren hannun daya sa, katon tabon da aka haife shi dashi wanda shine abu na farko data fara gani sanda yazo duniya ta shiga bi da kallo, da hannu ta shiga nuna shi sai dai ta gaza furta kalma daya, tana kokarin riko hannun nasa yaja baya da sauri
"Kamal MD kamar yadda kike hasashe! Ina fatan kina cikin koshin lafiya bayan abinda kika aikata."
"Na shiga uku Nura, wallahi tallahi dana ne, shine dana wallahi shine, wallahi shine."
"Inno me kike fad'a, ni ban fahimci komai ba fa."
Cigaba da matsowa tayi tana kokarin riko shi yayi saurin ja baya yana bata fuska sosai
"Karki taba ni, karki fara! Ba abinda ya kawo ni kenan ba, ina so naga kalar rayuwar da kike yi, alhamdulillah na gani, yanzu zan koma inda na fito."
Yana kaiwa nan yayi waje da sauri, biyo bayan shi tayi tana kwala kiran sunan shi amma ko waiwayowa bai yi ba, motar ya fada da sauri ya umarci me motar su tafi.
"Na shiga uku Nura, wallahi tallahi dana ne, kana gani ya tafi amma baka tsayar dashi ba."
"Idan har da gaske shine, kina zaune zai dawo da kafafun sa, waye ya kawo shi yanzu? Ra'ayin kansa ko? Toh shi zai dawo dashi kiyi shiru karki tara mutane."
"Shikenan nayi shiru."
Tace tana kama bakin ta kamar yarinya karama. Ciki suka koma duk ta kasa komai data rufe idon ta hoton fuskar sa kawai take gani, ta girma sosai ya zama babban saurayi me ji da kyau da gayu, shigar sa kadai ta tabbatar mata da shi din waye, anya zai karbe ta a matsayin mahaifiyar sa kuwa? Yanzu da bata da maraba da mahaukaciya duba da yadda duk ta lalace ta koma kamar wadda tayi jinya ga babu suturar arziki.
***
Ganin an kwana babu labarin Kamal yasa Alhaji Marwan baza jami'an tsaro sosai aka shiga neman sa, banda kuka babu abinda Ammi take, hakan ya karawa mishi damuwa sosai dan ba Hajiya Turai bata san wainar da ake toyawa ba.
Dakin sa ta shiga ta tarar dashi yana waya, zama tayi a gefen sa idon ta duk ya ɓaci saboda kukan dataa sha, ajiye wayar yayi bayan ya gama ya dube ta cikin kulawa yace
"Ki kwantar da hankalin ki in Sha Allah za'a ganshi."
"An kira yarinyar da yake zuwa gani a Kano? Ina zargin ta dama ni chan hankali na be kwanta da ita ba."
"Sirikar Aminini ce ashe, yarinyar da muke ta fafutukar nema ashe jikarmu ce, dan haka bani da matsala da yarinyar, idan kika ganta ma nasan kema irin ta Kamal din zakiyi, ki ji ta kwanta miki."
"Bana son ta gaskiya, karo na farko dana fara jin mijina yana yabon wata bani ba."
"Kishi?" Yace yana murmushi, gefe ta kawar da kanta tana bata fuska.
"Kinsan Adam yana raye?" Yace yana duban ta, duburburce wa tayi tace
"Ban gane ba?"
"Hello inspector." Yace yana daga wayar
"What!!!" Ya mike tsaye da sauri
"Gani nan zuwa." Ya katse kiran yayi hanya da sauri*DG*
*37*
©️Hafsat Rano
★★★
Tafiya yake ba tare da yasan inda yake taka ƙafarsa ba, so yake yayi kuka ko zaiji sauƙin zuciyar shi, sai dai ashe kukan ma samu ne, tsawon shekarun nan yana rayuwa ne da mutanen da bashi da alaƙa takusa ko ma ta nesa dasu, mahaifiyar data kawo shi duniya na rayuwa a wani waje cikin tsananin talauci, da kunci, tabbas ba'a kyauta masa ba, sai dai akan Aminatu kusan shi gata akayi masa, rayuwa ce yayi ta cikin tsananin gata da dadi, ita kuwa aka dora mata rayuwar da bata dace da ko da me aikin gidan ba balle ita, ya ɗaya tilo da take buƙatar dukkan gata, gata mace me rauni.
Tunanin ta yadda zai fara sanar da kowa komai yake, idan har ya cigaba da boye gaskiyar abinda ya sani be kyauta wa Aminatu ba, haka be yi adalci ga iyayen da suke rikeshi bisa amana ba, suna bukatar yar su, itama tana bukatar iyayen da zasu nuna mata gatan data rasa.
Idon sa ya runtse tuno labarin rayuwar ta data bashi, da irin abubuwan data fuskanta, ya tausaya mata kwarai sai dai a yanzu shine abin a tausaya wa, rashin sa'ar iyayen k'warai masu nagarta.
"Baka gaji da tafiyar kasan bane?"
Ya tsinkayi wata murya a saman kansa, juyowa yayi ya kalli mutumin
"Ya kamata ace ka dan huta ai, bayan ka gano komai me ya kamata kayi?"
"Me kake nufi?" Ya katse shi yana duban shi
"Ina biye dakai tun barin ka gida, na kuma san abinda ya kawo ka, ina fatan bayyanar gaskiya be saka ka yanke hukunci da rayuwa ba."
"Me yasa kake bina, ina kuma ruwan ka da rayuwa ta, waye kai ma a takaice.?"
"Wanda ya chanja maka rayuwa daga ta tsantsar talauci zuwa mafi kuloluwar daraja."
"Adam!" Yace yana zaro ido
"Nine, Ina fata haduwar mu ba zata zamar wani babban al'amari ba."
"Me nayi maka? Me yasa ka zabi da kayi wasa da rayuwa ta?"
"Idan kace wasa da rayuwa kana nufin ban kyauta maka ba, dubi suturar jikin ka, ka dubi kanka, kana tunanin ban maka gata ba? Toh ka bude kunnen ka kaji.."
"Ina so abin da ka binciko ya zama tarihi a ranka, wajibi ne ka boye komai ka cigaba da rayuwar dana zaba maka, idan baka sani ba, MD ne ya zabarwa yarsa irin rayuwar da take, shine silar komai, ya rabani da abubuwa guda biyu mafi soyuwa a gareni, shiyasa na zabar wa abinda zai haifa rayuwa mafi kaskanci."
"Karya kake wa Daddy, babu abinda yayi maka karya kake, kuma wallahi sai na tona komai ko da zan dawo rayuwa ta ta asali."
Murmushi yayi gami da cije lebensa na kasa
"Idan har na bar maka damar yin hakan ko? Yaro kenan, sunana kawai kake ji amma na wuce tunanin ka."
"Ta Allah ba taka ba, duk abinda kake kullawa sai ya koma kanka."
Hannu Adam ya harde yana duban shi, tafiya Kamal ya cigaba da sauri da sauri ba tare da ya sake waiwayo wa ba.
A wani irin yanayi iska ta dauki karar motar ta kai masa kunnuwan sa,da sauri ya juyo kafin ya iya tantance komai tayi sama dashi. Ƙarar daya kwalla ita ta jawo hankalin mutanen dake wucewa ta wurin jefi jefi.
*****
A kid'ime yayi waje yana kwala wa Driver sa kira, kuka Ammi tasa tana binsa ganin kamar baya hayyacin sa
"Dan Allah ka sanar min abinda ya faru."
"Kamal ne ya hadu da accident a Katsina."
Abinda kawai ya iya cewa kenan ya fada mota, kuka ta saka me karfi ta fado motar.
Wani irin gudu driver yake kamar zai tashi sama, babu abin da kake ji sai sautin kukan Ammi, ikon Allah ne kawai ya kaisu, direct asibitn da aka kai shi suka wuce suna zuwa kasar tsaye suka nufi accident and emergency unit.
A lokacin ya riga ya zama unconscious be san wanda yake kansa ba, dukkannin fuskar sa an rufe ta da bandage sai karaya a hannun sa na haggu.
Tsananin tashin hankalin da suka shiga ba zai misaltu ba, sai ga Alhaji Marwan na share hawayen tsananin tausayin dan nasa, ba'a ta Ammi da kowa yasan yadda uwa kan shiga tashin idan abu ya samu danta.
Isowar Daddy ya d'an saukaka abun, kwarai ya tausaya wa aminin nasa yadda yaga ya koma a lokaci daya kamar wanda yayi kwanciyar shekara.
*****
Tun bayan fitar Anas babu wanda ya sake magana a cikin su, kamar kurame sai dai idon sa na kanta duk sanda ta dago sukan hada ido sai yayi saurin basarwa yana maida kallon sa kan yar sa. Fita Baba Altine tayi ta basu waje dan sam bata ji dadin yadda akayi wa Anas ɗin ba, gefn Amal tayi zaman ta tana kallon yadda mutanen asibitin ke kaiwa da komowa.
Kiran wayar Farouk din akayi, kamar bazai daga ba ganin Iman na kokarin farkawa yasa shi dagawa dan kar a tashe ta, Ja'afar ne, baya kasar shima ya tafi karatu sai yanzu yake samun labarin dawowar Farouk din a wajen Dadah da sukayi waya shine ya gwada kiran tsohon layin sa na Mtn aikuwa sai gashi ya shigo.
"Da gaske ka dawo? Wow nayi mamaki wallahi."
"Uhum... Na dawo, kana lafiya?" ya amsa masa
"Lafiya lou, sai dai banji dadin tafiyar ka ba Allah, ina tunanin baka san halin da Mummy ta shiga ba bayan tafiyar ka."
"Ja'afar, kana ji? Ina wani abu yanzu very important, muyi magana anjima."
Be jira amsar sa ba ya katse kiran yana jan dan karamin tsaki. Kallon ta yayi yaga shi take kallo, harara ya sakar mata
"Dan na kori dan iskan chan kike share ni ko?"
Yace yana baro kujerar da yake kai
"Ba haka bane..."
"Yaya ne? Ina lura dake har wani tasowa kikayi da ya kiraki."
Ya zauna kusa da ita sosai a gefen gadon kafadarsa na gogar ta ta, wani iri taji tayi kokarin matsawa ya sake matso ta sosai.
"Ni ba haka bane." Tace tana tashi tsaye, saurin chapko hannun ta yayi ya maida ita ya maida ita wajen da ta tashi yana dora kafadarsa a saman ta ta
"Mesa kike gudu na, bakiyi missing d'ina bane?"
"Ya Farouk?" Ta kira sunan shi
"Ehen ina jinki."
"Dan Allah ka daina wa Ya Anas haka, kaga babu dadi, yayi min kokari sosai a lokacin da na fitar da tsammani da samun wani jin dadi ko cigaba a rayuwa, shine ya rike mu tamkar nasa, ya kula da dukkan al'amuran mu, ya tsaya tsayin daka wajen ganin na samu ilimi me amfani, wanda idan babu shi da tuni rayuwar mu ta lalace, watakila ma da tuni na zama mabaraciya ko na mutu saboda wahala."
Tashi yayi sosai ya kalle ta idon sa na kankancewa
"Kina nufin dai yanzu ya fini wajenki ko? Saboda ya kashe muku kudi ke da Iman, shikenan, Ina so ki tambaye shi nawa ya kashe akan ku tun daga ranar farko zuwa yanzu sai na biya shi, tun da abin ya zama gori..."
"Subhanallah, kar kayi misunderstanding d'ina, ba abinda nake nufi ba kenan."
"Me kike nufi? Shikenan dan yayi wahala daku sai ya bashi damar shiga hurumin da bana saba? Nayi magana kuma kin juya min magana ta, alamun ma ni yanzu bani da wani amfani wajenki."
"Ya Salam!" Tace tana kallon shi,
"Wannan ba Ya Farouk d'ina bane, Ya Farouk d'ina me saurin fahimtar rayuwa ne kuma me yiwa mutum uzuri ne ko da yayi ba dai-dai ba."
Kin tankawa yayi ya sake hade rai shi a dole an bata masa rai, ganin haka yasa tayi shiru itama saboda ta lura neman rigima kawai yake, ba kuma zata biye masa ba balle har ya samu galaba akanta.
Dogon zango suka dauka ba tare da kowa ya sake magana ba, sosai ranta ya ɓaci, dan bata ga abinda tayi masa da zai sashi reacting haka ba, ganin zaman ya ishe ta yasa ta mike don zuwa waje dan ba zata iya cigaba da zama dashi haka yana share ta ba
"Zan koma gida." Tace tana mik'ewa, da sauri ya kalle ta
"Iman din fa?" Yace cike da mamaki
Idon ta ne ya ciko da kwalla tayi saurin sa hannu ta goge
"Ba kana nan ba?" Ta amsa masa kai tsaye
"Akan nace masa dan iska ko?"
Yace yana kura mata ido, kin amsa masa tayi saboda yadda ranta ya ɓaci, ya gaza fuskantar ta s ranaram kishi ya rufe masa ido, gaba tayi kawai tana ji Iman din na kokarin tashi ta bude kofa tayi ficewar ta.
"Ya jikin nata?" Baba Altine tace
"Da sauki, ina ga idan drip din ya kare su sallame ta, muje gida."
"Kamar ya? Muje gida ko naje gida? Na zata zaki zauna a sallame tan ne ko?"
"A ah, zai iya kula da ita ai, muje kawai."
"Fada kukayi?" Baban tace
Gefen da Amal ke zaune Aminatu tayi saurin kallo ganin hankalin ta na wani wajen daban yasa tace
"Ya kasa fahimta ta."
"Shikenan sai kuma kiyi zuciya da yarki? Wannan ai shashanci ne."
"Toh ya zanyi? Tsawon lokaci ina zaman jiran dawowar sa, ya dawo kuma amma ba da halin da na sanshi ba."
"Aminatu ita fa rayuwa da kika gani ba zaki ce mutum ya zama yadda kike sanshi a koyaushe ba, mutane na iya chanjawa, Sai dai chanjawar su ba zai sa kema ki chanja ba."
Jikin ta ne yayi sanyi, ta zauna tana tunanin mafita, suna zaune likita yazo ya wuce su, ya shiga ciki, jim kadan ya fito yayi nasa wuri. Ba'a wani jima ba sai ga Farouk ya fito rike da Iman a kafadarsa ya wuce su, ido Aminatu ta zubawa bayan sa ganin be ko bi ta kansu ba, ji tayi kamar ta tashi tabi bayan sa sai dai bata da wannan karfin halin, tsam Amal ta tashi tabi bayan sa, Baba Altine ta yanka mata harara cikin bacin rai tace
"Me kikayi kenan?"
"Ya zanyi toh?"
"Muje." Tace tana mik'ewa
Fitowa sukayi reception babu alamar su, suna fitowa parking lot suna fita daga asibitin. Wani iri taji ta rasa dalilin da Ya Farouk zai mata haka. Gida suka wuce Baba Altine nata yi mata fada akan abinda tayi, ko gaba kar ta sake irin wannan wautar. Ita dai jin ta kawai take bata iya cewa komai ba.
****Kwata-kwata ta kasa sukuni, tana yi tana duba wayar ta ko zata ga ya kira ta amma shiru kake ji, gashi kwarai tana so taji lafiyar yar ta, wannan shi ake kira a dakeka a hanaka kuka, yayi mata laifi amma ya fita daukar zafi.
Ganin wankin hula na neman kaita dare yasa ta ajiye komai ta kirashi, lokacin ya gama shirya Iman cikin sabon kaya ya bata abinci da chocolate ta gama rigimar ya kaita wajen Ummin ta ya samu tayi shiru bayan ya bata wayar shi yayi mata downloading wani cartoon, shigowar kiran ya katse mata kallon ta, kuka ta saka masa hakan yasa shi saurin rejecting kiran.
Sororo tayi rike da wayar a hannu, mamaki ne ya cika ta , dan son sake tabbatar wa ta kuma kira a take akayi rejecting, Sosai zuciyar ta ta sosu, ta zame ta kwanta ranta na mugun suya.
Shigowar Dadah dakin uku tana son daukar Iman din Amma sam taki yarda, a shigowar ta na karshe ne take ce masa ina Aminatun bata bukatar yarta ne? Duba da rashin ta da tayi kwana biyu? Da yake har yanzu be gama sakin jiki da ita ba yasa yace mata yanzu zai zo ya kai mata ita.
****Ja'afar na ajiye wayar yayi saurin kiran Mummy dan yasan bata san da dawowar Farouk din ba, lokacin tana tsaka da aiki a system ɗin ta, da sauri ta ture komai ta shiga kiran layin Farouk din.
Kura wa kiran ido yayi, a hankali ya zare wayar daga hannun ta ganin har tayi bacci wajen kallon, katse wa kiran yayi ya cigaba da bin wayar da ido har sanda wani kiran ya sake shigowa.
"Farouk!"
"Na'am."
"Yanzu Farouk ka bar kasar nan tsawon lokaci sannan ka dawo duk ban sani ba? Ka kyauta min kenan? Kasan yadda naji dana samu labarin tafiyar ka? Amma shine har ka dawo baka neme Ni ba?"
Shiru yayi duk sai yaji babu dadi, kallon tasa yar yayi ya tuna yanzu shima fa uba ne, idan tasa yar tayi masa haka ya zaiji? Cikin kankan da murya yace
"I'm very sorry, kiyi min afuwa."
Share hawayen fuskar ta tayi cikin dakewa tace
"Ina son ganin ka yaushe zaka zo?"
"Gobe ko jibi in Sha Allah."
"Kazo gobe."
"In sha Allah."
Ajiye wayar yayi yana sauke ajiyar zuciya, kura wa Iman ido yayi yana jin soyayyar ta na bin kowanne lungu da sako na jikin sa. Tunanin abinda ya faru tsakanin shi da Aminatu yayi, sai yaji duk be ji dadi ba, atleast idan bazai bi ta a yadda ta ke tunani ba kada ya kuma bata mata rai.
****
Duk sunyi jigum babu wanda yake iya magana da dan uwan sa, gashi har an kwana babu alamun zai farka, dakin likitan ALHAJI Marwan ya shiga ya nemi a basu transfer,zai tsaya yi masa dogon bayani yace shi sam be yarda ba, dole ya amince ya sallame su suka dauke shi suka yi Abuja dashi ba tare da yasan me yake faruwa ba.
A chan gidan kuwa Hajiya Turai ta tada bori bayan ta samu labarin abinda ya faru, gaba daya masu aikin gidan sun taru a kanta tana ta kuka da kururuwa a kaita wajen jikanta, duk sunyi jigum jigum motar su ta shigo gidan, da sauri ta tashi daga zaman dirshan din da tayi ta nufi kan motar tana kuka.
Duk wanda ya ga Kamal a lokacin sai ya masa kuka, tuni Alhaji Marwan yayi nisa a shirye shiryen fitar dashi waje.
Cikin dare ya farka, duk suna kansa, da wani irin abu ya soma kafin ya fara magana da k'yar irin ta wanda ya galabaitu da wahala. Babu wanda yaji me yake cewa saboda yadda maganar tayi kasa, Ammi na kuka Hajiya Turai na yi, cikin yanayin kamar an fuzgo maganar ya furta
"Dad..dy.. A...mm..i.. itace."
"Karka takura ma kanka da magana, dan Allah."
Ammi tace tana kuka sosai, kukan shima yasa yana mika mata hannu, da sauri Daddy ya isa gareshi yana riko hannun sji
"Kamal, look at me, menene? Kayi shiru kaji?"
"Daddy... Ami...natu."
"A kira maka ita?" Yace yana shafa kansa, daga kansa yayi alamun eh
"Toh shikenan, kayi hakuri gobe zatazo kaji?"
Daga kansa yayi yana maida idon sa ya rufe.
"Kaga ni? Yarinyar nan me tayi masa? Yana wannan halin yana kiran sunan ta? Wannan wacce irin masifa ce? Wallahi bazan yarda ta lalata min rayuwar yaro ba."
"Ya kamata ki duba lafiyar shi kafin ki tsaya tunanin komai, ni yanzu ta lafiyar sa nake, ba ta komai ba."
Ran ammi ne ya ɓaci, ta kara jin haushi ta tsanar yarinyar da bata taba gani ba.
Rashin Sani!!!! Yafi dare duhu
Rano 😍*DG*
0 comments:
Post a Comment