_I already left, ga wnn kiyi hidiman biki, take care of your self and baby. I luv you_
"Wani hawayen ta kuma sharewa, tana bude envelope din taga bandir din 'yan 'dubu dubu ne wato hundred thousand, sababbi fil fil dasu. "Note din ta kuma karantawa Allah sarki yaHaidar he loves her with all of his heart, what she does to him is unfair. Wayanta ta ciro ta shiga neman layinsa yayita ringing ba'a 'daga ba, 'karshe taji an kashe. 'Kirjinta ne yayi mugun bugawa, shikenn yaHaidar yayi fushi da ita sosai, take taji wani sabon hawaye na zubota, she loves him without a limit..... Tana zaune mamy ta turo 'kofa, tayi saurin share hawayen idonta ta 'dan saita kanta ta soma gaida mamy.
"Kallonta mamy keyi kaman me son gano wani abu tace daughter lafiya de ko, gyda kanta tayi tace lafiya mamy,
"Haidar ya wuce ya shigo kina barci, mamy ta fadi sanda take bude sip.
"Murmushin karfin hali Hanifa tayi tace "eh munyi sallama mamy, ta dauki kudin ta mikawa mamy tana fadin" ga wnn ma ya bani wai nayi hidiman biki nikuma bana bu'kata mamy.
"Mamy ta dubeta bata amshi kudin ba tace" keep it with you daughter, you might need it ko ba yanzu ba, kinji. ALLAH yayi Albarka, a sanyaye Hanifa ta amsa da ameen. Mamy tace maza ki sauko downstairs breakfast dinki is ready, ko kinfi son a kawo maki nan. Girgiza kai tayi tace a'a zan sauko mamy. Daga haka ta mike daga zaunen da take.
"Gaba daya haka ta wuni ranan babu walwala, ta alakanta rashin kunna wayan yaHaidar da maybe yana jirgi ne, toh amma har yamma bai kunna ba, duk sai taji ta damu.
"Haidar kuwa yana isa wayan mamy ya kira ya sanar da ita ya sauka lafiya, Hanifa da akayi wayan a gabanta mikewa tayi ta shige daki tana matsan hawaye, ta kuma kira amma saijinta tayi a kashe, kwanciya tayi a wajen ta rika kuka maras sauti, gaba daya ranan haka ta wuni ta kwana kaman maras lafiya, koda mamy da sumy suka tambayeta sai ce masu tayi kawai bata jin dadi ne, babu yanda mamy batayi su tafi asibiti ba amma ta 'ki.
"Wasawasa saida Haidar ya shafe sama da sati beko kirata, kullum yayi waya da mamy sai ya tambayi lafiyan Hanee da unborn dinsu, Hanifa kuwa kullum cikin tunaninsa take, bata da burin da wuce ta ganta kusa dashi yana nuna mata soyayyansa me class.
"A 'bangaren Haidar ma duk sai yaji kaman be kyauta wa beautiful dinsa ba, at least he needs to be much more understanding with her, ya kamata yayi considering situation dinta, he shouldn't have judged her the way he did, pic dinta na saman screen din wayansa yaketa bi da kallo, yana sonta yana son kasancewa da ita, amma hukumcin da ya dauka ne kawai zai tabbatar masa matsayinsa a zuciyan Haneefah. Kissing pic din yayi ya furta "I love you Beautiful.
"A satin bikin Aisar da Sameer suka iso Kano, Aisar da kansa ya tafi Zariya dauko Queen dinsa, yana isa waya ya mata ya sanar da ita ya iso, aiko su Fadila da Rashida suka sakata gaba da zolaya,
"Fadila tace "Oh ashede ashede shine angon, sojan da aka gama masifewa, Rashida tasa dariya tace ni dama tun a lokacin na gane they both had a crush..... " tsaki Sady tayi tace dan Allah kuzo mu tafi banson King yayi ta zama jira, dariya sukayi suka dauki luggage dinsu suka wuce, dan dukansu ko wacce an barta daga gida taje bikin kasancewar bikin aminiyansu ne, snn sunyi covering yawancin syllables dinsu dashike semester taja, sun kusa soma examz.
"Haka Fadila da Rashida sukata dariyan fa'dan Aisar da Sadiya cikin motan nan, yanzu za'ayi fada kowa ya juyar da kansa anjima kadan kuma sai a shirya yace my Queen tace my King.lol.....
"Gidan ya soma cika da jama'a, su Anty Hiba ma sun samu isowa tareda me gyaran amare, su Sady na isowa Anty Hiba ta wuce da ita yanda ake masu gyara ita da Sumy, already su Fadila sun sauka gidan wata Antyn ta dake nan Kano.
"Shema ta lura da yanayin Hanifa, dan haka saida ta bari babu kowa ya rage saura su biyu a dakin Inna ta soma tambayanta meke faruwa.
"Kuka Hanifa ta soma tana fa'din" Shema I just couldn't help it anymore, I really need someone to talk to..... "jiki sanyaye Shema ta matso ta ri'ke hannayenta tace" I'm here for you Hany, pls tell me what's bordering you.
"Hanifa ta goge hawayen idonta" kafin ta fa'dawa Shema duk abunda ke faruwa tsakaninta da yaHaidar, da mugun mamaki kawai Shema ke binta da kallo....." Hanifa ta katse shirun da fa'din" I luv him Shema, I luv him with all of my heart I don't wanna loose him.... "Shema ta sau'ke ajiyan zuciya kafin tace " What on earth could possibly make you do that Hanifah, haba haba that was crazy, da iliminki da komanki kiyi irin wnn shirme, it just doesn't fit in head.
"Shema pls yanzu ba lokacin dawo da zance bane, I want my husband, I need him.... "Shema tece" alright fine, ina wayarki sake kiransa...
"He won't pick up, na sani ne.
"Karki damu just call. Jiki a sanyaye tayi dialing.....
"Da sauri Haidar ya matsaya baya dan kar suji karan wayarsa. Saida ya fice daga sashen Inna kafin ya soma amsa wayan.
"Hello Beautiful,.....
"Mamaki ne ya kamata jin ya amsa mata... "yaHaidar kawai sai ta soma kuka, Haidar hankali a tashe ya soma fadin" Oh am sorry Beautiful, pls stop, kafin ki fa'da mun laifina I admitted, nayi laifi, all these while we didn't heard from each other, and this is all my fault, Beautiful kiyi ha'kuri aiki ne ya min yawa, pls forgive me I promise that will never happen again kinji Soulmate,..
"Sau'ke ajiyan zuciya tayi wani sanyi na shiga zuciyanta Shema ta kashe mata ido ta dau wayanta ta ci gaba da charting dinta,
"Hanifa tace" yaHaidar ka yafe mun.
"Beautiful na jima da yafe maki, remember I luv you very much.
"Toh yaushe zaka zo.....
"Murmushi yayi kafin yace" Ai nazo tun jiya, na sauka can gidanmu ne tare da amaryanki..... "Ai kaman wacce aka zabura haka ta mi'ke, amaryata kuma.
"Yes Beautiful amaryarki na maki amarya a lag na taho da ita kuga juna, yanzu haka tana nan tana jiran isowarki...... jifa da wayan Hanifa tayi ta sake sabin kuka, Shema ta mike tana tambayanta lafiya inaaa ta fice tayi side din mamy.
"Anty Hiba da mamy na zaune na tattaunawa Hanifa ta shigo tana kuka ta fa'da kan mamy tana kuka, gaba dayansu hankali a tashe suke tambayanta lafiya.... "cikin kuka take fadin "mamy wai yaHaidar amarya ya min, mamy wllhi ina sonsa dan Allah kice danyi duk abunda yake so mamy...... "mamy ta soma rarrashinta tana fadin " wasa yake maki Hanifa, Haidar babu wata amaryan da yayi..... mamy wllhi da gaske ne tana can gidansa haka yace mun...."Anty Hiba me zatyi inbanda dariya tana kallon Haidar dake tsaye bayansu shima dariyan yake...." kallonsu mamy tayi shida Anty Hiba yanda suke dariya..."wani mugun kallo mamy ta watsa wa Haidar kafin tace" tashi abinki daughter idan baki son amarya ai sai ya sakar min ke yaje can ya 'karata da amaryarsa... " A zabure ta dago tana duban mamy tace " mamy wllhi ni ina son shi bazan iya rayuwa babu shi ba saidai ya saki amaryar...." Caraf Haidar yace" Nima ina sonki Beautiful dina bazan iya rayuwa babu ke ba, ya 'karaso yana 'kunshe dariyar sa yace taso abunki yau zamu tafi gidanmu 'yan biki duk zasu ta'kura ki a nan, tinda baki son amaryar zan saketa idan muka isa gidanmu kinji..." wani kunya ne ya lullu'be Hanifa jin yanda ya wani 'dagota ya rungume gaban su mamy, Anty Hiba kuwa sai dariya take tana fa'din " kai 'dan gidana dama haka ake sonka lallai ka cire tuta. Mamy kuwa harara ta narka wa Haidar tace" zaka zo ka sameni ne kukan da ka daughter na tayi sai na rama mata. Anty Hiba tace mamy zane shi za'ayi, mamy tace shima ya sani idan ta kama a zanesan tsaf za'a zanesa akan daughter...... gaba daya suka sa dariya, mamy da Anty Hiba suka wuce sama suka barsu nan tsaye.
"Dago kai tayi baki a ture zata masa magana ya saka bakinsa cikin nata sun jima a haka kafin ya saketa, a ranar mamy ta Anty Hiba suka shirya mata komai nata Anty Hiba dasu Shema suka rakata can sabon gidanta, da farko mamy taki aminta ta tafi can saida Haidar yata magiya ya shaida mata sati biyu zaiyi kafin ya koma, karshe saida Abba yasa baki mamy ta yarda Hanifa ta koma.
"Da daddare misalin 'karfe tara ta gama shirinta na bacci tana zaune tana shafa turarruka na jiki da Anty Hiba ta bata wayanta ya soma ringing" My Handsome ne ya bayyana jikin screen din" tana murmushi ta 'daga wayan " Hello Handsome,
"Hello Beautiful shima ya fadi, ina fata yau kin shirya tarban mijinki dan yau musabaha sosai nake so muyi da Champ and Princess.
"Murmushi Hanifa tayi tace "kai Handsome, wai ina ka tsaya ne,
"Murmushi shima yayi yace aw kin dauka wasa nake, am serious nasan suma sunyi missing dina suna son jin 'dumin daddynsu, dariya tayi sosai kafin ta dan turo baki tace" Handsome nifa ban son kana kaiwa this hours a waje.
"Haidar yayi daeiya ya juyo yana duban su Sameer da suke can gefe yace yace" am sorry Beautiful wllhi su Aisar ne suka ri'ke ni kan shirye shiryen dinner dinsu, but am on my way now, wai suna gaida maman en 4.
"Hanifa ta zaro ido tace wai dama gabansu kake wnn maganganun... sai ka iso kawai tace gamida katse kiran.
"Dariya Haidar yayi ya 'karasa yanda su Sameer suke ya masu sallama, sai zolayansa suke ya wuce ya barsu.
"Tana jin 'karan bu'de gate gabanta ya wani fa'di, ta sake duban kanta a mirror rigar baccin dake jikinta yayi matu'kar mata kyau dukda cikinta da ya 'dan turo, ja ne rigar me kaman shimi, komai na jikinta kana iya gani dan very transparent haka rigar take. Ta dau na saman ta dan rufa kafin ta nufo downstairs. Shigiwansa knn yana kokarin rufe 'kofa ya hangota tsaye jikin staircase......"God have Mercy" abinda ya iya fadi knn, bude hannayensa yayi ta 'karaso ta shige cike, take 'kanshin turarrrukanta suka soma tafiya da Haidar wata duniya, a hankali ya masu sau'ki kan kujera yana shinshin wuyanta, kankace me ya soma kissing dinta ta ko ina, " a kunnenta yake ra'da mata I luv you beautiful. Ya ri'ko hannunta yace oya tashi muje kiga amaryarki kar ta gaji da jira....." A zabure ta mi'ke tana dubansa kafin tace" joke aside yaHaidar, peck ya manna mata a kumatu yace " kar ki damu Beautiful nafi sonki fiye da amaryar... kaman ra'kumi da akala haka ta bisa waje tana addu'an samu sau'ki cikin zuciyanta.
"Suna isowa waje juye juye ta soma ta ina zata hangi amarya..... " mayafin dake rufe da wata mita ya bu'de mata, kafin yace here is your amarya Beautiful, I hope you will like her.....
"Gana daya she's speechless, kallon motan take 'kirar Benz fara kal me shegen kyau.... Tsalle tayi ko nauyin cikinjikinta bataji ba ta ru gumesa tana fadin" I lobe you yaHaidar, I luv you soo much, Hanidar kaman a mafarki haka yaji zancen, shima ya dada matseta cikin jikinsa yace" I luv you too Haneefah. Hawayenta yaji a 'kirjinsa, ya dagota yana fadin" Beautiful me ya faru, ko baki son mota ne ko bata maki bane...." Girgiza kai ta soma kafin tace" yayi min sosai na gode yaHaidar, share mata hawayen yayi ya sureta suka shige cikin gida.
"A daren ranan sosai suka tausayawa juna, tausayinsa take sosai tasan yayi kewanta yayi 'ko'kari, shiko Haidar tausayinta yake yasan tayi 'ko'karin faranta masa a wnn dare dukda lalurar dake jikinta, wani kulawa na musamman yake bata, motsi ba motsi ba sai ya tambayi me take so ayi. A wnn dare Hanifa taga gata da soyayya wajen mijinta maras misaltuwa, har saida taji haushin kanta na hanasa kanta da tayi tuntuni. Haidar ya tabbatar mata shi'din me 'kaunarta ne.
"Washi gari ake kamun su Sumy, ji yake kaman kar ta fita su zauna a gida suci soyayyarsu, sai wani shagwa'ba yake zuba mata shi bai son ta fita wajen bikin nan, yana zaune yana kallonta tana shiryawa, kayan ya mata kyau sai tafiti das da ita.
"Mi'kewa yayi ya rungumeta ta baya suna fuskantan fuskokinsu a madubi yace" Beautiful kinyi kyau, nifa banson aje ana kalle mun ke, murmushi tayi tace " Kai Handsome wazai tsaya kallon mata me 'katon ciki kkwa yasan ni matar aurece, Haidar ya turo kansa cikin wuyanta yace" whatever nasan matata tafi kowa kyau a wajen dole na damu, ya danja hancinta yace 'karasa shirin mu tafi, I'll be waiting for you downstairs, kallo ta bisa dashi har ya fice, wani sonsa da 'kaunarsa ne zalla ke azalzalnta.
"Haka akayi kamu aka gama, duk wanda yaga Haidar yau zai gane tsantsan fari cikin da yake ciki, shi kansa jinsa yake kaman wani sabin ango. Washe gari mamy ta ha'da gagarumun walima, the next day aka daura aure da daddare angwaye suka ha'da Spectacular dinner na gani na fada, biki yayi da'di sai Allah son barka, ranar Sunday aka wuce da amare Lagos by flight, hakan yasa mutane 'kalilan ne suka raka su ciki harda Inna da Anty Hiba.
"Haidar kuwa sallama sukayi da angwaye dan yana nan sai nan da sati biyu ya koma, musamman da Beautiful dinsa da unborn Champ and Princess ya dauki hutu.
"Kulawa sosai suke bawa junansu ita da Haidar, wuni suke suna makale da juna, idan kaga ya fice toh gidan mamy ya taho, a haka suka shafe sati biyun su suna kwasan soyayya. Koda Haidar zai tafi sosai tayi kuka, tun ana washe gari zai tafi ya kusan kwana aikin lallashi, washe gari har airport ta raka sa, kaman kar su rabu da juna. Inna da kanta ta koma gidan Hanifa dan kula da ita....
*************************
"Kwanci tashi babu wuya wajen Allah yau gashi Hanifa ta shiga watan haihuwanta, tana zaune suna drama da Inna sai ta shanye wani ji'ko nasu na tsofi wai maganin za'ki.... sai ture turen baki take ita bazata sha ba" ana haka wayanta ya soma ringing ganin Handsome dinta ne yasa ta saurin daga wayan" cike da shagwa'ba suka gaisa,
"Haidar yace" Beautiful ya jiki haka, akwai wani abu ne.....
"Turo baki ta kuma yi tana hararan inna tace ba Inna ce wai sai nasha wani magani baka gani ba gaba daya ma is not hygienic bansan dame akayi ba....." A zabure Haidar ya mike yana fa'din" What! No way, saka wayan a hands free let me talk to her.... Hanifa tayi yanda yace, Inna kuwa sai sababi take mata, " ki tsaya biyewa namiji shi me yasani kuma shane dole kiyi....
"Muryan Haidar ne ya katse ta, " pls inna all those gargajiya things banso ana bata, it is not good for her and the baby...." Tabe baki Inna tayi tace yo ni nasan me kake fada, kai Zaki bari kaji dole tasha maganin zaki, ta mike tana gyara daurin kwali ta dubi Hanifa tace ku gama iyayinku ki zo ki sameni.
"Handsome kajita ko.. tayi magann cike da shagwa'ba.
"Kar ki damu Beautiful I'll be on my way gobe insha Allah, babu me ta'kura maki idan na dawo kinji. Da haka Haidar yayita lallashinta suka sha soyayyansu kadin sukayi sallama.
"Washe gari kuwa Haidar ya dira a garin Kano, haka sukata ya'ki da Inna a gidan duk wani shirgin maganin za'kin dake gidan Haidar ya zubar dasu Inna kuwa ta saka gaba da sababi. Da yamma lis suka shirya suka tafi akayi scanning aka duba lafiyan baby, nan Dr ya shaida masu babys uku ne a cikin Hanifa, ya'ki fa'da masu ne ya bari ya tabbatar, wai zakaga murna wajen Haidar, saida ya cika Dr Kasim da kyauta. Inna ma sosai tayi murna, Suna tafe a mota Haidae ya dubeta yace" Beautiful kinga Allah ya amshi addu'a ta, kin gado mamy, Allah ya raba lafiya, gaba daya ita da Inna suka amsa da ameen, kai tsaye gidan mamy suka wuce, Haidar ko kunya shi da kansa ya isar da wnn labari ga iyayen nasa wato Abba da Mamy.
"Wayyo Allah zo kaga murna wajen wa'an nan bayin Allah. Addu'ansu 'daya Allah ya sauketa lafiya.
👸🏻Queen Samy😍💄💋..........
[5/21, 10:33 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
80
"Satin Haidar guda a Kano, Hanifa kuwa har ta shige edd dinta da sati guda. Haidar ya'ki komawa Lag a cewarsa yafiso sai ta haihu ya koma, wani kulawa na misamman yake bata, kullum sai sumyi drama shida Inna gaba daya ya hana bawa Hanifa ko wanr irin magani sai na asibiti.
"Mislin 'karfe 9:30pm, ta gama duk wani 'dabi'un ta na bacci ta nufi 'dakinsa, zaume ta samesa saman gado laptop ne a gabansa yana duba mail 'dinsa. Yana ganinta ya sakar mata murmushi gamida bu'de mata hannayensa alamun ta 'karaso,
"Murmushin itama tayi kafin ta 'karaso ta zauna da 'kyar gefensa, hannunsa yasa ya tallafo bayanta gamida kissing gashinta yasan 'ko'kari kawai take amma cikin nan nata na mata nauyi.
"Handsome, ta kira sunansa gamida ri'ko yatsunsa.
"Juyowa yayi yana fuskantan ta kafin yace" yes my Beautiful.
"Yakamata ka koma bakin aikinka, kaga gaskiyan ka da ri'kon amanarka ya kaika maysayin da kake a yanzu. Zamanka a nan it will affect your work, you need to go back.
"Matse 'yan yatsunta yayi kafin yace" Beautiful family over everything, I can't leave you a situation din da kike yanzu, bazan ta'ba samun peace of mind ba ko na tafi, na sani sarai dauriya kawai kike but da alama cikin nan na baki wahala, I can't leave Beautiful, kinfi mun komai balle wani so called job. Ya rungumeta cikin jikinsa kafin yaci gaba da fa'din" am here for you Beautiful, together we will go through this, fatana Allah ya sau'keki lafiya.
"Hawayene ya ciko idonta bata san wani irin so yaHaidar ke mata ba, ha'kika tayi DACE samun miji irin yaHaidar sai an darje...... 'dumin hawayenta dayaji ne yasa hankalinsa mugun tashi, da sauri ya dago face dinta yana kallo.
"Oh no, what's wrong Beautiful, why those tears..... "Tell me kin fara jin ciwo ne.... ganin bata amsa sa baba kukan na 'karuwa yasa sa saurin mi'kewa yana shirin zura jallabiya....." Ri'ko hannunsa tayi ta mi'ke tsaye ha'de da rungumesa cikin jikinta tace" am fine yaHaidar, hawayen farin ciki nake, ha'ki'ka inajina tamkar nafi ko wace mace sa'a, you mean the world to me yaHaidar, sunan maraici nake amma ko ka'dan banta'ba experiencing bitterness na maraici ba, na taso cikin so da 'kauna daga wajen mahaifanka wanda ko iyayena iyakacin son da zasu nuna mun knn, snn na samu miji kaman kai me sona me 'kaunata wanda duk burin mace knn, yaHaidar ka ha'da abubuwa da dama, you and your parents means everything to me, Abba da mamy sun ri'ke amanan 'kannensu wanda da suna duniya a yau da sunfi kowa farin ciki, thank you for everything yaHaidar....... bai bari ta gama fa'da ba yasaka bakinsa cikin nata sun jima a haka wanda shima saida ya zubda 'kwalla.... rungumeta yayi cikin jikinsa tausayinta da tsananin 'kaunarta na shigansa. A hankali ya masu masau'ki kan wani resting chair dake can gefe cikin 'dakin,
"Murmushi yake yana duban face dinta ya saka 'dan yatsansa ya mayar mata da kitsonta da ya sakko guda daya kafin yace" Beautiful I should be the one thanking you, in spite of everything I have done to you but you still love me, you give me another chance, the only thing da zan maki shine na mallaka maki kaina completely.... yana murza 'yan yatsunsa cikin nata yake fa'din" Ni Aliyu Haidar *Mijin Haneefah* ne ita ka'danta tol nan duniya...... you're like an Angel to me, you're a great gift to me from our Lord. Ido cikin ido suke kallon juna hannunsu ri'ke dana juna kafim Haidar yaci gaba da fa'din " You are my Inspiration Haneefah, I love you.... "Rungumesa tayi tana cusa kai cikin 'kirjinsa. Ta jima cikin 'kirjinsa ko wannensu farin ciki yakeji maras misaltuwa kafin ta 'dago kai a shagwa'be tace"Handsome pls ka koma bakin aikinka kajifa Dr yace zan iya kaiwa 3weeks ma ban haihu ba... "Haidar ya da'da kwantar da kanta kan kafa'dunsa yana wasa da kitson kanta kafin ya kwaikwayi miryanta yace" kuma yace ai any moment from now labour na iya zuwa maki, ta yaya zan tafu na barki Beautiful, ya wani girgiza kai yana ta'be baki yace" no way I can't possibly do that...."Yanda yayi maganan saida ya bata dariya.
"Ta 'dan shnaye dariyan tana turo baki tace "but am not alone here, akwai Inna snn gasu mamy harma da Abba, idan ka'ki tafiya su Abba zasu ga kaman ka raina efforts dinsu akaina ne, I beg of you pls yaHaidar ka koma bakin aikinka.
"Murmushi Haidar yayi kafin yaja hancinta yace" wai kema har kin iya tsara zance ko, ok fine naji tunda korata kike, but nasan " my Champions da princess suna son na zauna, barin tambayesu idan sun yarda na tafi sai na tafi but idan suka 'ki, toh am not leaving.... "sunkuyowa yayi yana facing cikin yace" Champs princess do you guys want daddy to leave?.... "Yanda ya wani kafse yana maganan sosai ya bawa Hanifa dariya, itakam tana shan dariya idan taga yaHaidar ya dage da gaske yana magana da cikinta. 'Dago kai Haidar yayi yana kallonta yanda yaga sai dariya take " kashe mata ido 'daya yayi yace" kinji sunce basu so na tafi, sunfi so a haifosu daddy na nan..... sosai Hanifa ke dariya harda kwanciya bisa gado, mirginowa shima yayi ya rungumeta ta baya yana sha'kan ni'imtaccen 'kamshinta.
"Waswasa Haidar ya'ki tafiya gashi har ya share wajen sati biyu, saida Hanifa ta ha'dasa da Abba da mamy sukayi da gaske kafin ya koma Lag. Inna ma dama ba son zamansa take ba, dan tunda ya dawo kullum basu da aiki shida matarsa sai cin kayan fulawa a cewarta (pizza hot). Itako tafi son Hanifa taci tuwo yaranta suyi 'kwari.
"Tunda Haidar ya tafi kullum suna ma'kale a waya, cikinta ya kuma girma sosai gashi har yanzu bata haihu ba, gaba 'daya Haidar ya rasa samun kwanciyan hankali, kullum bayan sunyi waya da Hanifa sai sunyi da mamy ma yaji ko akwai wani abu ne, hankalinsa duk ya gaza kwanciya. Ga tafiya Turkey a gabansa duk ya rasa wanne zeyi gashi shine me jahorantar tafiyan. Idan kaga Haidar dole ka lira da raman da yayi. Ana gobe zaiyi tafiyan ya kirs wayan Hanifa. Tana ganin my handsome ne ta dauka cike da murna.
"Hello, Beautiful.
"Hello Handsome.
"Beautiful how you and our unborn doing .
"Am doing great, ya aiki.
"Alhamdulillah, but am damn missing you, I just couldn't help it.
"Murmushi tayi tace" same here yaHaidar, ina missing sweet luv dinka.
"Kar ki damu Beautiful we will soon be together, zan tafi Turkey gobe but ba jimawa zanyi ba just a couple of days kawai zanyi na dawo, bazanfi 5 days ba at most. Kin yarda naje Beautiful.
"Dariys me sauti tayi kafin tace" don't be ridiculous Handsome,Allah ya kaiku lafiya ya dawo mun da kai lafiya. promise me da zaran ka dawo zaka zo mun.
"Murmushi shima yayi kafin yace "you have my word ina dawowa ke zan fars zuwa na gani insha Allah. Kisses to you..... ya fadi kafin sukayi sallama.....
_Manage this ba yawa_
*Sorry for the late post, you guys should bear with me pls, am quite busy ne this dayz insha Allah book yazo 'karshe, Taku har kullum Queen Samy🌹💋.*
👸🏻Queen Samy😍💄💋......
[5/21, 10:33 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
81
"Tunda Haidar ya tafi sau biyu sukayi waya, kasancewar island 'din dasuke gudanar da Exercise 'din a 'kasar Turkey birnin Izmir babu enough service a wajen an ke'be wajen ne kawai mussaman dan horar da 'kwararrun sojoji musamman sojin ruwa.
"Hankalin Haidar duk baya jikinsa ya 'kagu su gama gudanar da wnn Exercise din su koma gida, Aisar ne ya hangosa zaune saman wani reshen wata bishiya data sau'ko 'kasa, 'karasowa Aisar yayi gamida sara masa kafin yace" Sir may I seat.... "Kallonsa kawai Haidar yayi dan gaba 'daya baya fahimtarsa, gajeren tsaki Haidar yayi yace" Whatever kana iya zama, wai wnn girman da kake wani bani fah, nifa banson haka...."Dariya Aisar yayi kafin yace" you deserved it Our Admiral the youngest Naval Chief Of Staff ever, mutumina zakayi breaking record ba'a ta'ba samun wanda ya 'kure Rank na Navy a shekarunka ba early 30's fa kake.... "Kanna wutanka Admiral ka duba fah duk tawagan nan are under your command..... "Stop talking ridiculous Aisar, ni Acting Naval chief of staff ne, snn bana fata na samu wnn mu'kami da wanne zanji da family koda aiki, I valued my Family more than anything else, Kasancewa da Beautiful yafi mun komai..... Dariya Aisar yasa yana fa'din kaji Romieo ba *Mijin Haneefah*.
"Tsaki Haidar ya kuma yi yace " You know what am damin tired of this place, kai nifa Nija nake son komawa, I need to see my Beautiful.
"Uhum , muma de naga munda matan nan haka muka tafi muka barsu.... "Hararan da Haidar ya narka masa ya hanasa 'karasa maganar wani navy ne ya 'karasi wajen ya sara masu kafin yace da Haidar" Sir we're done with exercise *Crocodile Smile* Haidar ya gya'da kansa yace good, ya juyo ya dubi Aisar yace Captain takeover, ka nuna masu exercise *Harbin kunama* A kifa jirgin kowa ya zube cikin tekun let them rescued their selves....Sara masa Aisar yayi ya dubi daya Captain din dake gefensa yace let's get going...... da poppoti suka karasa wajen sojojin.... nan suka ci gaba da horass dasu.
"Washe gari suka tafi Capital dinsu wato Istanbul dan ganawa da me girma shugaban 'kasan Turkey, sosai yaji da'din yanda Haidar ya jagoranci tawagar ake basu horaswa na 'kwararrun soji, take ya mi'ka 'ko'kon baransa dan a horas da Navys dinsu nacan, babu hali Haidar yayi rejecting dinsa kodan tarban da suka masu a 'kasarsu, dole suka 'kara kwana biyu suna horas da sojin ruwa na kasar Turkey.....
"Zaune suke a Maharas Hotel bayan sun gama ganawa na mussaman shida Kwamanda Hafsin rundunar sojin ruwa na 'kasar Turkey, ganawa ce sukayi 'yar sirri na dabarun ya'ki da abunda ya shafi Naval. Sosai Admiral. Saral Karem yaji da'din zuwan su Haidar 'kasarsu dan haka ne ya ha'da masu gagarumin dinner da daddare a farfajiyan Maharas Hotel. Duk yanda ka wuce sojin ruwa kawai kake gani kowa cikin Uniform 'dinsa gwanin ban sha'awa,....." Haidar ya 'dan matsa gefe nata faman neman layin Beautiful amma baya shiga, ya kira na mamy yafi sau nawa ba'a 'daga ba, ya kira na Inna ma same abu ba'a 'daga ba, sosai hankalinsa ya tashi, kana ganimsa kasan akwai abunda ke damunsa. "Aisar nata lura dashi ya bisa da kallo yaga ya mi'ke ya nufi restroom, shima mi'kewa yayi yabi bayan Haidar yana jiransa a 'kofar restroom, wayan aisar ne ya soma ringing ganin My Queen yasa saurin dauka yana fadin "Queen darling...... muryansa ne ya sar'ke jin muryan Sady na rawa... King I just couldn't help it, am so terrified.... "Aisar hankali a tashe yake fa'din" Queen put your self together and spell it out, meke faruwa...
"Ta 'dan share hawayen idonta tace "King tun jiya muka zo Kano nida mum, and mun tarar Hany na labour, toh tun jiyan bata haihu ba gashi har yanzu... likitocin sunata kai komo wai baby 'daya ya fita daga mahaifa kuma akwai risk na rasa maman babys din idan akayi Cs,..... kuka ya kuma kufce mata tana fadin Aisar bada son raina na kiraka ba dan basu so yaHaidar ya sani dan Allah kar ka fa'da masa nima na kasa samun nutsuwa ne shiyasa na kiraka to calm me down.....
"Innalillahi kawai Aisar ke nanatawa a zuciyansa kafin yace" Ki kwantar da hankalinki komai zai zama normal insha Allah, Hanifa zata haihu lafiya da izinin Allah, Allah zai sau'keta lafiya...... muryansa ne ya sar'ke sanda ya 'dago ido sukayi ido hu'du da Haidar... take Aisar ya juya zancen yana fa'din" Ok ok eh ai mun kusa dawowa yawwa queen will call you later.... ai beko jira cewa Sadiya ba ya katse kiran,
"Kallonsa kawai Haidar keyi yana son gano wani abu, Murmushin ya'ke Aisar keyi ya soma fa'din " I was waiting for you, I I also want to use the restroom..... "Kallon mamaki Haidar ke masa kafin yace" what do you mean Aisar, nanne kawai restroom gaba daya Hotel din nan, wait a second, are you hiding something from me...." Da sauri Aisar ya soma girguza kai kaman wanda yayi wa sarki 'karya yace" no no am not hiding anything, besides why would I do that.
"Haidar ya kafesa da ido kafin yace" who just called you on the phone? Girgiza kai Aisar ya kuma ya dagi yana kallon Haidar snn yace" stop being ridiculous Haidar,.... "karasowa Haidar yayi ya fizge wayan yana duba last call, Wueen ya gani wato Sadiya knn ta kirasa, harara kawai ya narkawa Aisar kafin yayi dialing....
"Sadiya kuwa tana gani ta daga da sauri a zatonta Aisar ne, nan ta soma fa'din" King 'dazu yaHaidar ne ya zo yanda kake ko, nasan shiyasa ka canza subject, pls king yaHaidar must not know about that....." Cikin hasala Haidar ya soma fa'din Sadiya fa'da mun meke faruwa, what happened to Beautiful?..... Innalillahi wa inna ilaihirraji'un haka Sadiya tace a zuciyanta shiknn yaji komai.... "Tasawan da ya kuma daka mata ne ya razana ta.... ta daburce tana 'kokarin kashe wayan Haidar yace" Are you deaf or what, don't you dear hang the phone, ki fa'da mun what's goin on there.
"Aisar ya 'karaso rai 'bace yana fadin " haba Haidar you need to calm down, why must you yelled at her, Ok fine bani wayata ni zan fa'da maka.... Sady kam kuka kawau tasa ta daura hannu aka.
"Haidar ya fizgo hannun Aisar suka bar wajen kafin yace oya inajinka meke faruwa,.. da kalamai masu 'karfafa gwiwa da tawakkali Aisar ya soma magana wa Haidar....."Look Aisar just get straight to the point, me Sadiya take cewa kar a fa'da mun..... "tunkan Aisar ya soma magana yaji zuciyansa ta karaya, fuskan nasa tayi jazur, a guje ya fice yana fa'din " now I get itm it's Haneefah, Aisar ma a guje yabi bayansa yana fa'din Haidar Haidar pls ka tsaya is not what you think.... Inaa bai samu Haidar ba sai cikin room dinsa, fizgo kaya kawai yake daga sip yana fa'din, I need to go and see her, Aisar ya soma fadin Haidar calm down first, pls don't panic, Ba abunda kake tunani bane.
"A hasale Haidar ya dago gamida jifa da rigar hannunsa yace " then what, mutuwa tayi, yes ta mutu ko Aisar.... take yaji kuka na shirin kufce masa. Girgiza kai ya soma yana fa'din I can't loose her, she's all I have, she's my happiness she's my inspiration..... "Rungumesa Aisar yayi gaba daya shima jikinsa yayu sanyi, I need to go there, am leaving this place first thing tomorrow morning...
"Aisar yayita bawa Haidar baki, gaba daya Haidar gani yake daren ya masa tsawo. Wnn dare ma iya cewa babu baccin da Haidae yayi, gari na wayewa yayu handling komai wa Aisar ya nufo Nigeria.....
"Flight dinsa a Lagos ta sauka, yana sauka ya shige na Kano ko gida beje ba ya nufi asibitin dayasan nan take awu. Su Abba duk suna reception sukaga Haidar kaman diran yeso, Haidar na ganinsu jigum jigum yaji kwalla yaciko idanunsa ko 'kafarsa ya gagara dagawa kafin ya 'kara step 'daya, cikinsu babu wanda ya iya masa magana, sai Abba da ya mi'ke ya ri'kosa. Mamy kam a hankali ta kauda kanta gefe hawaye na kokarin ambaliya a fuskanta.....
👸🏻Queen Samy😍💄💋....
[5/21, 10:33 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
82
"A hankali Abba yaja Haidar suka fice haraban asibitin, kaman ra'kumi da akala haka Haidar ke bin Abba, kafa'dun Haidar Abba ya dafa yace" Son don't panic, Dr suna iya bakin 'ko'karinsu, snn kai musulmi ne nasan kayi imani da 'kaddar me kyau da maras kyau, da sannu Allah zai raba matarka da abunda ke cikinta lafiya, so I want to you to be very strong, save your strength remain a soldier, Allah na jin ro'kon bayinsa koda yaushe dan baya gyanga'di balle barci.
"Kalaman Abba sun 'karfafa wa Haidar gwiwa, gya'da kansa yayi kafin yace" haka ne Abba, insha Allah zanyi yanda kace, but Abba idan da hali inaso a fita da ita waje koda States ne ko wata 'kasa masu 'kwararrun likitoci sai a kaita... " girgiza kai Abba ya soma kafin yace " Haidar wnn duk me yuwuwa bane, ta riga ta fara labour snn suma likitocin nan sunada nasu 'kwarewan duk yanda mutum yaje idan Allah ya 'kaddara faruwan abu tofah sai ya faru dan haka fawalla wa Allah komai shine mafi alkhairi.
"Haidar ya gya'da kansa yace hakane Abba..... daidai nan Dr Kasim ya fito ya nufosu.... A tar suka nufesa suma.
"Haidar baki na rawa yace" How is she, how is my wife Dr, tell me pls how is she doing...... "Dr Kasim ya dafa kafa'dun Haidar yace" Navy you need to calm down everything is gonna be alright.
"Can I see her pls, I really want to see her, Haidar ya fa'di kaman me shirin sa kuka. Gaba 'daya yabawa Dr Kasim tausayi, ko jira sauraren amsan da Dr Kasim zai bashi beyi ba ya nufi cikin asibitin.
"Dr da Abba suka bisa da kallo cike da tausaywa, Dr ya maida dubansa ga Abba yace" Alhaji we need to talk mu 'karasa office dina, ba musu Abba yabi bayan Dr suka wuce.
"Abba ya jigum yana sauraren Dr sanda yake fa'din" Alhaji the truth is that, her condition is getting critical, we have no other option dole mu mata aiki dan ta riga ta galabaita, though aikin akwai ha'dari babba a ciki kashi 'daya ne cikin 'dari akasari suke tashi idan masu, she doesn't have any strength, she can't even breath yanzu haka oxygen ne a bakinta. So we need her husband to sign here tunda ya riga yazo.
"Inna lillahi wa inna'ilahiraji'un kawai Abba keta nanatawa a zuciyansa, duk sanyin dake Office din saida yaji zufa na karyo masa, tunowa yayi da 'kaninsa da kuma 'kanwar matarsa wato iyayen Hanifa, ya kuma tuna sanda suka kawota gidansa yaye wanda zuwan nata knn har ranar da ya aurar da ita ma Haidar, ya kasance yafi sonta fiye da 'ya'yansa na cikinsa, wasu hawayene suka zubo daga idon Abba, girgiza kai ya soma yana fa'din" Haidar bazai iya signing takardan nan ba na sani, jikin Dr yayi sanyi sosai ganin babban mutum kaman Abba na hawaye.... basu ankara ba sa ganin Hannun Haidar sukayi yana 'ko'karin kar'ban takardan daga hannun Abba, Abba ya 'dago kai yana kallonsa shima hawayene kwance a fuskansa, da kyar ya iya furta" I can do this Abba, if that's the only way... rungumesa Abba yayi suna matsan hawaye. Haidar da kansa yayi signing... Dr Kasim ya wuce aka soma preparation.
"Ana shirin shiga da ita Haidar ya ri'ko hannun Dr Kasim yace "let me see her pls even for a while, I won't take long..... "Dr ya gya'da masa kai ya uamarci sauran likitocin da nurses din su fito.
"Tun daga nesa ya hangota cikin ya girma sosai oxygen na manne a face 'dinta, idonta a lumshe tamkar me bacci, ji yayi 'kafarsa sun kasa 'daukansa, rayuwansu da ita kawai yake tunowa tun tashinta da kuma aurenta da yayi, da irin azaba da wahalan da ya bata a baya, har I zuwa lokcin da suka zama cikakkun ma'aurata masoya junansu..yana tafe yana tunanin har ya 'karaso jikin gadon da take, hawaye kuwa nata faman ambaliya a fuskan sa, shafa fuskanta ya shigayi yana hawaye yake fa'din" hey I know you can go through this, you're a fighter..... kwantar da kansa yayi gefen gadon yana ri'ke da hannunta maras cannula yake fa'din" don't leave me Hanee, you're the luv of my life, I luv you with all of my heart, I can't loose you..... kuka me sauti yake sosai kansa na bisa gadon a gefenta, saida nurses suka shigo tura gadon Haidar ya mi'ke har lokacin na ri'ke da hannunta, Dr Kasim yana 'ko'karin jansa inaa yana rike gam da hannunta har suka fito zasu wuce theater room, su Abba mamy Inna duk suka nufosu, da kyar Abba ya zare hannun Haidar daga na Hanifa, gana daya kuka suke idan ka 'dauke Abba dake rarrashinsu, Haidar ya kamo hannun mamy suka zauna waje daya mamy ta kwantar da kansa bisa cinyarta tana share masa nawayensa tana fa'din" kuka ba namu ba Haidar let's pray for her okay.
"I luv her mamy, ya fa'di yana me dago kai yana duban mamy, gyada kanta mamy tayi tace" I knw Son, na sani she'll be fine kaji insha Allah. Juyawa yayi ya kalli Inna duk ta ji'ka bakin zaninta tana share hawaye ya mi'ke ya 'karasa wajenta ya zauna a gefenta" hannun Inna ya ri'ko cikin nasa yace " addu'a zamu mata kinji Inna Allah yasa ayi a sa'a, Inna ta amsa da ameen Zaki, ta rungumosa cikin jikinta tana goge ragowar hawayen.
"Su Hajiyan Saif, Mum 'din Aisar, Shema da kuma Sady harma da Saif ne suka shigo, Haidar na hango Saif ya mi'ke ya nufesa suka rungume juna.
"Asibiti ta cika dam kowa da kalan addu'an da yake yi, lallai Hanifa 'yar dangi ce inji Queen Samy.
"Mintoci suka shu'de haka awanni ma, Dr ne ya fito yana since abin rufe hanci, gaba daya suka mi'ke suka nufesa.... A tare suka hau tambayansa meke faruwa. "Kallonsu yake cike da tausayawa kafin yace" Alhamdulillah the operation was quite good, take kaga annuri ya bayyana a fuskokinsu banda hamdala ga rabbil izza basa komai....."muryan Dr ne ya katse su sanda yake fa'din" but unfortunately we couldn't save...... Ai Haidar be gama ji ba ya soma fa'din" no no that's not true..... "Dr yace calm down Soldier, let me finish my statement first, babyn da ya fice daga placenta ya riga ya mutu, and Furtunately the remaining two babies and their mother are still alive.... "Haidar kam besan sanda ya zube yayi sujidi shukri ba, ya dago ya rungume Abba yana fadin" Abba Hanee is alive, my wife is alive..... "murmushi kawai Abba keyi ganin duk yanda Haidar ya daburce sabida murna, yace" Son mun gode Allah, Allah ya 'kara mata lafiya, gaba 'daya jama'an wajen bazan iya kwatanta maku irin farin cikin da suka shiga ba tareda mi'ka godiyansu ga ubangijin talikai.
"Su Sady suka soma fa'din Dr can we see the babies, Dr yace sure yanzu za'a fito dasu bayan an gama shiryasu..... aiko bai gama rufe baki ba nurses biyu suka fito dasu ri'ke a hannunsu, gaba daya mutanen wajen hankalinsu ya koma kan babies idan ka 'dauke Haidar da ko kulawa beyi ba, shi haushima suka basa, ya galla ma Sady harara a zuciyans yayi tsaki yace sarkin 'yan rawan kai.
"Bayan Dr Kasim yabi yana tambayansa, " Dr zan iya ganin matata, murmushi Dr Kasim ya danyi kafin yace" Soldier naga alama sunanka zai koma romieo fah irin wnn soyayya haka, Haidar yace pls Dr may I,
"Dr ya dan dara kafin yace" muna son ta 'dan sami hutu, snn ba yanzu zata farka ba ko ka shigama bacci take.... " yeah koma me take yi nide kawai son ganinta nake, Haidar ya katsesa.
"Ok fine zaka iya shiga but pls navy don't take long,.... gyada kansa yayi yace " yeah sure, Dr yayi directing Haidar room din da aka kwantar da Hanee, ji yake kaman ya maidata cikinsa dan so da 'kauna haka yayita kallonta yana shafa mata addu'o'i 'karshe ya manna mata peck a kumatunta kafin ya fice.
"Inna na ri'ke da macen ta mi'kawa Haidar tana fa'din" ungo kar'beta ka ganta mana, a yatsine ya kalli Inna kafin yace" wato duk baku damu da halin da Beautiful ke ciki ba duk kun maida hankalinku kan babies. ?..... "Baki sake Inna ke kallonsa kafin tace "toh sannu tsuntsun soyayya, kai zaki ban son iyayi baka fimu sonta ba ehe, idan baka son 'ya'yan kuma toh,... "Haidar ko saurarenta beyiba ya soma kallon yarinyar yana murmushi ya kai hannu ya kar'beta yana fa'din" welcome princess ya manna maya kiss a goshi, mamy ce ta 'karaso da namijin Haidar ya ha'desu duka biyu ya kar'besu tareda yi masu kiran sallah a kunnuwansu na dama.
"Sai lokacin Haidar ya samu zarafin zuwa gida yayi wanka ya wuce gidan mamy ya 'dan sami wani abun yaci.
"Sanda ya dawo asibiti mamy ya samu a tareda Inna ta wuce gida dan kintsawa.
"Beautiful ya fa'di yana riko hannunta, mamy ta mi'ke tana duba yaran dake kwance bisa gadonsu....
"A hankali ta bu'de idonta fuskan Haidar ta gani yana mata murmushi. Murmushin itama ta 'danyi, Haidar ya sunkuyo ya manna mata kiss goshi yace sannu Beautiful 'dina, how you feeling. "A hanakali tace" da sau'ki Handsome, jawo kujera yayi ya zauna gefenta hannunsu cikin na juna.
"Handsome yaushe kazo.
"Kissing hannunta yayi kafin yace" ai na fa'da maki zanzo,
"Toh aikin...... "shiii ya daura hannu bisa lips dinta kafin" yace Dr yace babu yawan surutu, keep calm ok, I luv you...."Murmushi ta 'danyi tare da gya'da kanta a hankali.
"Sosai Haidar da Haneefah suka burge mamy tana jin sonsu har cikin ranta fatanta Allah ya barsu tare. Sun jima a haka yana ri'ke da hannunta har bacci ya kuma yin gaba da ita.
"Namijin ne ya soma kuka yana wutsil wustil, mamy ta mi'ke da sauri ta 'dagosa.... "A hanakli Haidar ya ajiye hannun Hanifa ya nufo mamy. "Mamy me yake so ko yunwa yake ji, yayi magana cike da kulawa.
"Yunwa yakeji daga gani zaiyi tsotso, gashi bata fara basu nono ba. "Mamy ko madara za'a basu,. "Eh toh amma gwara idan ta dawo hayyacinta ta fara basu nono kafin a basu wani madara.... "Haidar ya mi'ka hannu ya kar'besa yana jijjiga sa yana fa'din" it's Okay Champ daddy is here, zaka tashi momy da princess, sai sunbatu yake da jariri, mamy kam har dariya abun ya bata.... "'Karshe Haidar ya'dan saka masa le'ben bakinsa na 'kasa nan da nan kuwa ya kama yana ja.... da haka har yayi shiru ya koma bacci.
"Mamy tayi murmushi tace" Son ka iya raino fah, lallai daughter ta huta, murmushi Haidar yayi cike da kunya....
"Gaba 'daya Haidar ya tare a asibiti idan kaga ya tafi toh darene, a haka har tayu kwana biyar a asibiti kafin aka sallame ta, sosai Inna da mamy ke bata kulawa, Haidar yaso a wuce da ita gidanta amma fir Inna ta'ki tace gwara su tafi can gida, mamy ma ta goyi bayan haka, babu yanda Haidar ya iya dole ya ha'kura. Amma kullum na gidan mamy yana tareda Beautiful dinsa da Champion da kuma princess dinsa.
Su Sumy harma da momma sun samu isowa, kowa sai sha'awan yaran yake, Shema ma kusan kullum sai tazo duba Hany, Su Sady da Mum kuma sun wuce Zariya duba dangin mum kafin zuwa ran suna su zagayo.
"Hanifa ta sami 'karfi sosai, kamarba cs aka mata ba, ta warware sosai tana samun kulawa na mussaman daga masoyanta, bama kaman Haidar baijin kunya agaban kowa yake nuna mata tsantsan soyayyansa.
👸🏻Queen Samy😍💄💋......
[5/21, 10:33 PM] 🌹 Muhammad🌺kabeer🌹: 🌹🌹🌹 *Mijin Haneefah*🌹🌹🌹
83
"Gidan cike yake da mutane kai kace biki ake, yara sunci sunan Umar (Farouq) da kuma Khadeejah( Deena). Gata da soyayya kam wa'en nan yara sun ganshi tareda mamansu, tun safe Haidar be sakata a idanunsa ba dan kuwa ta ko ina mutane ne ma'kil a gidan, da yamma misalin 'karfe 5:00pm ya shirya tsaf cikin sky blue jampa da hula dark blue zanna bukar yayi kyau sosai kaman ka sace ka gudu, gidan ya nufa a tunaninsa tunda yamma tayi 'kila an 'dan ragu 'yan suna tinda waliman da rana akayi.
"Kai tsaye cikin gidan ya nufa sashen mamy, su Inna da wasu gwaggwanayen su zaune a parlorn ana ciye ciye an ta'ba hira anga dangi. Aiko yana kutso kai suka soma ga angon 'karni, Haidar gaba daya kunya ya kullu'besa, ya'dan tsuguna yana gaishesu, duk suka amsa masa da sakin fuska tare da masa barka, ya mi'ka yana 'ko'karin juyawa" goggo Rabi tace" tashi abinka ka shiga kaga yaranka. Inna ta ya'be baki tace" wa yace maki yaran yazo kallo, shi yasan wacce yazo gani uwar yaran yazo gani, ni mero ban ta'ba ganin soyyaya irin na Zaki da Hanifa ba, wai kunsan basa kiran juna da sunansu sede kiji yace mata bintiful(Beautiful) itakuma kiji tace Haso( Handsome)..... "Gaba daya suka sa dariya, Inna larai tace yo ai gaskiyansu haka muke so gwara suso junansu, kode kishi kike ne yaya mero. Dariya Inna tayi tace wa ni ai na sallama wa Hanifa suje can suci soyayyansu ita da taga zata iya rayuwan saman ruwa, ni mero ina zan iya salon kifi ta cinyeni... aka kuma saka dariya gaba 'daya..." Haidar ya mi'ke yana sunne kai..." caraf Inna tace" meye kake 'ko'karin juyawa mun san wajenta kazo, maza 'karasa nasan itama yau seta kusa zazza'bi tinda ta yini bata ganka ba.." kallon zamu ha'du Haidar ya mata kafin ya haye sama.
"Sallama yayi a 'kofan 'dakin kafin ya shigo, tana zaune saman stool gaban dressing mirror Anty Hiba na shiryata da alama wanka ta fito, su Sady suna zube saman gado ana zuba surutu. Gaba daya suka soma gaishesa yana satan kallon Hanee yake amsa gaisuwansu. Nan suka soma gaisawa da Anty Hiba sai tsiya take masa, wayan Anty Hiba ne ya soma ringing ta 'dauka ta nufi downstairs dan mamy ce ke kiranta.
" kai tsaye gadon babys ya wuce ya shiga masu wasa sai wutsil wutsil suke... Su Shema kuwa mi'kewa sukayi da niyyan fita Hany ta tsaresu da ido ina zaku, Sady ta 'karaso kusa da ita ta ra'da mata" Romeo is here you guys need some space nasani, harara Hanifa ta watsa mata, dariya Sady tace a hankali" King yana hanya, any moment from now zai iya isowa, so I need to go and check if his abinci is ready, Hanifata dubi su Shema da har sun isa 'kofa tace " and you ina zaku, Sumy tace zamuje gidan Hajiya dauko Amal da Ajmal... daga haka suka fice gaba 'dayansu.
"Haidar se kallonta yake yanda tayi kaman bata san yana 'dakin ba, har ta gama saka sar'kanta, 'karasowa yayi yanda take ya rungumota ta baya yana fa'din" Beautiful why the long face, you know this face doesn't fit you at all, ya 'karashe maganan yana sunbatan wuyanta, "'kala bata ce masa ba ta shiga saka enkunnaye, hannu yasa ya kar'bi 'yan kunnen yana sa mata yake fa'din" Beautiful you look Spectacular I luv you, ya 'karasa saka mata 'yan kunnen ha'de da manna mata kiss a wuya..... jin ya fara wuce gina da iri yasata saurin turesa tana fa'din" ni babu ruwana da kai baki a ture. Mi'kar da ita tsaye yayi yana ri'ke da kunkuminta yace" I admit nayi laifi banzo ba tun safe, am sorry Beautiful..... "Zatayi magana ya saka bakinsa cikin nata ya shiga kissing nata, sun jima a haka saida sukaji kukan Deena kafin ya saketa nan suka nufeta dukansu, Haidar ya 'dauketa yana jijjigata amma kaman cewa ake ta 'kara, da sauri ya mi'kata ma Hanifa yana fa'din" what's wrong with her, maybe she's hungry, oya feed her.... "Kallonsa kawai Hanifa keyi yanda duk ya daburce, aiko kaman ha'din baki nan Farouq ma ya soma, Hanifa na bawa Deena nono dole Haidar yayita jijjiga sa, ana haka mamy ta shigo da sauri tana fa'din lafiya de ko... "Ai da sauri Haidar ya mi'ka mata Farouq yana fa'din mamy at the same time suke jin yunwa, kinga Deena ta fara first gashi shima yanzu yana yi. Mamy ta kar'besa ta shiga basa madara.
"Kallon abincin da aka shigo ma Hanifa dashi tayu da alamu bata ci ba, ta gama bawa Farouq madara ta mi'ke ta shiga duba abincin, aiko ko ta'bawa ba'ayi ba.. "Tunkan mamy tayi magana gaban Hanifa ya shiga fa'di tasan bazasu wanye da mamy lafiya ba dole ta sata cin na dole.Haidar na ri'ke da Champion dinsa bayan mamy ta gama basa madara.
"Mamy bata ce 'kala ba ta shiga zubawa Hanifa tuwon dawa miyan kuka da yaji man shanu da pepper soup din kayan ciki, ta 'karasa ta kar'bi Deena kafin ta saka mata abincin a gabanta tace "oya eat up..... "Marairaice fuska Hanifa tayi tana fa'din mamy am not hungry, pls mamy... " Com on maza ki cinye abincin nan ban son wani magana, you haven't eaten anything since morning, and yet kina cewa baki jin yunwa... "Haidar ya 'karaso ya saka mata pillow a kan rug kaman yanda yaga ana mata ya ri'ko hannunta ya sau'kota 'kasa yana fa'din "is okay Beautiful zo na tayaki ci..."Muryansa ne ya sar'ke sanda yaga ba'kin tuwon, ya 'dago kai yana kallon mamy kafin yace" mamy what's this, haba haba mamy she can't eat this for heaven sake. This is irritating mamy.... Harara mamy ta galla masa kafin tace" zaka min shiru kokuwa, idan bataci tuwo taji 'karfi ba ina ruwan nono zaizo kana gani yaran tsosto garesu... "jinhaka yasa Haidar fa'din aah toh barun tayaki Beautiful, ya 'dauki spoon yana ci yana bata ashe tuwin da da'di, mamy ta shimfida Farouq dan yayi barci, daidai nan Anty Hiba ta shigo tana fa'din" Mezan gani Admiral da cin tuwo.... dariya Haidar yayi kafin yace" ba dolena na ci ba tunda Beautiful zataci. Dariya Anyy Hiba tayi tace lallai soyayya be bar komai ba snn zai iya canza kowa tunda ya canza *Mijin Haneefah* harta mamy saida ta dara. Anty Hiba tace yawwa idan kun gama Abba naso ayi family pics gaba 'daya a parlonsa,.
"Haka akayita yin pics gaba daya, iri da kala, iayayen yara kakkani da kuma su inna tatta'ba kunne lol.
"Zuwa washe gari gidan ya watse, sati 'daya Haidar ya 'kara ya koma bakin aiki, tinda ya tafi saidai waya kawai suke dan gaba 'daya aiki ya ri'kesa, baya samun zama at all.
"Hanifa kuwa wata biyi tayi ta koma gidanta, Mamy ta sama mata wata 'yar uwa daga 'kauye tana tayata rainon twins.
"Watan twins hu'du a duniya, yara sun girma masu shiga rai sun 'kara kyau gonin sha'awa, idan ka gansu sai ka zata 'yan wata tara ne. Yau tana zaune tasha wankanta cikin red gown na material , e ba'ka'ken duwatsu kaman daga sama taji sallaman Haidar. Baki sake take kallonsa shi kuwa ya 'karaso gamida 'dagata sama yana fa'din" I miss you Beautiful, kallon yanda ta 'kara kayu kawai Haidar keyi, ita ko ta kasa ce masa 'kala sai kallon yanda ya 'kara girma da kyau take, his personal Charisma ya fitowa sosai. Zunewa sukayi kan kujera ta shige cikin 'kirjinsa tana sha'kan 'kamshinsa da tayi missing. "Dago kai tayi tana kallonsa kafin tace" Handsome wato bazaka daina min zuwan bazata ba ko, murmushi yayi ya 'dan ja hancinta kafin yace" because I luv you ultimately, I always wanted to surprise you, nasan hakan will always make you happy. " Rungumesa ta da'da yi cikin jikinta kafin tace" I love you Handsome, you're the best. Kissing din goshinta yayi yace" I love you more Beautiful. Whare are my Champion and Princess, ta mi'ke tana fa'din barin dubosu suna can tareda Samira, Haidar ya mi'ke yana fa'din barin 'karasa ciki toh..
"Yana shiga wanka ya fa'da, tsaftan Beautiful 'dinsa na burgesa, dakin tsaf tsaf haka bathroom din, kaman yana nan, ko ina tidy very need.
"Yana fitowa yayi tozali da yaransa sun girma sosai. Far yayi da idanuwansa kafin ya 'karaso yana fa'din" I just couldn't believe it, my Champion and Princess are growing faster. Ya rungumesu yana masu wasa yana fa'din" daddy is here kids, you guyz are growing up very fast, oya tell me, me momy take baku,.... Hanifa me zatayi banda dariya. "Haidar ya shiga wulla su sama yana masu wasa 'karshe ya jawo Hanifa ma aka ci gaba da wasan gwanin ban sha'awa, saida Hanifa tayi da gaske kafin Haidar ya mi'ke ya shirya suka sau'ka downstairs, zata mi'ka su ma Samira Haidar ce " ina zaki kaisu, "Zan mi'kasu wa Samira ne ka samu kaci abinci..." Girgiza kai ya soma kafin yace" no kawosu yau full house ne ai, suma tare za'ayi dinner din, playing mat dinsu ta dauko ta zubasu akai, ta zuba ma Haidar abinci bisa dinning sai gani tayi ya sau'ko da abincin 'kasa yana fa'di" let's eat here. Yana kallon yaransa yana ci, Hanifa kuwa sai binsu da kallo take ganin yanda yaran suka shiga ran Haidar.
"Satin sa Biyu a Kano ya koma Port Hercot dan yanzu a can yake be faye zaman Lagos ba. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya cikin jin da'di da kwanciyan hankali..
*******************************
*Some years later*
"Sady ta dubi Aisar tace" pls king you need to let go of your past, ka mance komai ka kai Saadiq yaga kakansa Allah ma muna masa laifi ya yafe mana,... "kallonta kawai Aisar yayi kafin yace" idan kin gama ki haura ki haura ki fito da Saadiq kice wa mum zamu wuce...." marairaice fuska ta kuma yi tace" please King I beg of you, ka tunafah he's your father no matter what, you carries his blood, you can't change the fact that he's your Dad you can't deny that...."Enough! Ya daka mata tsawa, don't call that worthless disgusting man my father, he's coward and invincible, what he does was unforgivable. Sady ta kuma marairaice fuska ta ri'ko hannunsa tace" King if you really do luv me, then you need to let go of that hatred pls. Ka nuna masa jikansa and forgive him pls....."Mum ce ta 'karaso ta dafasa kafin tace" Sadiya is right Aisar, ni kaina da Hashim ya mun laifi na yafe masa, kaima ka yafe masa ka kai masa Saadiq ya gansa." 'Dago idonsa da yayi jazur yayi yana kallon mum zaiyi magana mum ta girgiza masa kai tace" Pls Son do this for us, me sady and Saadiq....." Saadiq ne ya sau'ko daga stirs yaron 'dan shekara biyar ya ri'ke hannun mum yayi kissing kafin yace" mum bazaki bimu Kano ba, murmushi mum tayi tace lil soldier zanzo amma sai kum dawo mu sake zuwa tare Okay... gyada mata kai yayi kafin ya ri'ko hannun Aisar yace" Dad let's get going, I can't wait to see mamy and Abbada maganarsa da be gama 'kwari ba.... murmushi Aisar ya masa kafin yace Ok my soldier. Sady ta 'dau mayafinta ta yafa ha'de da 'daukan handbag 'dinta ta dubi mum tace toh mum mun wuce, mum tace toh daughter Allah ya tsare ko ku gaishesu da kyau, toh mum zasu ji.
"Aisar sukayi sallama da Mum, har ya kofa ta kira sunansa, amsawa yayi ha'de da juyowa kafin tace" pls son don't forget to visit him first. Kai kawai Aisar ya gya'da kafin ya fice...
"Suna fita Cimon driver dinsa ya sara masu gamida bu'de masu 'kofa, Aisar na gaba Saadiq da Sady na baya. Nan Aisar yace da Cimon Prison suka fara nufa kafin airport.
"Zama yayi a wajen ganawa da mutane yana jiran fitowan Dad dinsa..... tunaninsa ne ya yanke sanda yaga an turo Dad bisa keken guragu...Dad kuwa hawayene kawai ke bin fuskansa, dan gaba 'daya ya cire ran zai sake ganin Aisar. "Kauda kansa gefe Aisar yayi sanda Dad ya 'karaso yana ri'ke hannunsa yana fa'din" Son is that really you, rungume Aisar Dad yayi hawaye na bin 'kuncinsa. Saida yayi mai isansa kafin ya 'dago.
"Aisar ya dubesa kafin yace" Dad when did you became a cripple? What happened to your legs..." Dad ya kuma share hawayen idonsa kafin yace" Aisar kaga yanda Allah ya maidani, akan na ara wayan wani da befi wayan dubu 'daya ba shine suka lakka'da min duka suka jefoni daga sama, tin daga lokacin na zama gurgu....kuka ya kuma kufce masa.
"Aisar ya sau'ke ajiyan zuciya kafin yace" wnn shine abin da nake ji maka tsoro a can baya, gashi billonia kaman kai kaga yanda ka 'kare, akan wayan nera dubu 'daya an nakasa ka, 'karya fure take bata 'ya'ya. And you'll end up here in prison, your life became so miserable dad, what you did to us was unforgettable. Idon Aisar ya kawo ruwa sanda yake fa'din" ka cuce mu nida mum, ka yaudare mu, you never loved us, at the end you manipulated us..... tun tasowata kullum hantaran mum dina kake kana tozarta ta, ni da nake danka baka ta'ba sona ba. In spite of everything mum had never stop loving you.... kuka ya kufcewa Aisar sanda yake fadin" Dad 'karshe ka mi'katawa tsinannun mutane wanda suka tashi raping dinta.... kuka sosai aisar keyi haka Dad ma...."Aisar pls forgive me, nasan ban kyautawa Hannatu ba amma wllhi ina sonta, I wish I've another chance dana nuna mata irin son da nake mata and to you too son..."Dago idonsa Aisar yayi ya share hawayensa kafin yace" but you know what Dad, mum has forgiven you, saboda tanada good heart..nima na yafe maka.
"Dad ya rungumesa yana kuka yake fadin" na gode Aisar na gode son, Aisar ya mike yana fadin, "don't thank me, thank my wife instead....."Dad yace Son kayi aure, Alhamdulillah, gyada kansa Aisar yayi kafin yayi alama wa Sady dake tsaye akan ta shigo... shigowa tayi tana hawaye... Dad ya bude mata hannayensa yace "come here daughter, karasowa tayi ta mika hannunta ma Dad ya ri'ke cikin nasa yace" Allah maki albarka, Allah ya albarkaci rayuwanku da Aisar, thank you for being a good wife to my son
"Girgiza kai Sady ta soma tana fa'din" pls Dad ka dena fa'din haka, nida Aisar abu guda ne, Allah ya baka ikon cin jarabawan da kake ciki.. Dad yana murmushi yace" Allah bless you both...suka amsa da ameen.
"Aisar ya fice ya shigo da Saadiq wanda suka barsa wajen Cimon.
"Kallonsa dad keyi ko ba'a fa'da masa ba wnn jininsa ne.... baki sake yake fa'din " is that your son? Kai Aisar ya gya'da, dad wani da'di da hawaye na bin 'kuncinsa ya bude hannu wa Saadiq yace "come here Hero.... "Da sauri Saadiq ya tafi ya rungumesa jin ya kirasa da Hero. Saadiq ya dagi yana kallonsa yace " are you a cripple, where are your legs.... " Aisar yace " behave son... "rufe baki Saadiq yayi yace sorry Grandpa. Sosai Dad yaji da'din kiransa Grandpa da Saadiq yayi yace " good Hero, nan suka soma hira da Dad, Saaiq yace why are you here anyway, meyasa ka bar mum a gida kaje ka tayata zama kaga mu zamu tafi Kano wajen mamy da Abba, you know what suna sona sosai me and my cousins..... "Jin surutun Saadiq yayi yawa yasa Aisar cewa" Soldier My Dad is here because he's sick, idan yaji sau'ki zai dawo gida, ku tafi mota kaida momy yanzu I'll catch you up okay... kai ya gyada Sady tayi sallama da Dad haka Sadiq ma suka wuce mota.
"Aisar ya kalli Dad yace, na tattara duk dukiyanka da nasan na sata ne na mi'kasu ma EFCC, snn dukiyanka na halal mun rabarsu wa marayu da marssa galiho dan nida mum bamuda bu'katan komai naka, abunda nake earning is enough for us. we're living a happy life now, remember I've forgiven you Dad and I still luv you, may Allah have mercy on you. Ya rungume Dad kafin yace" this is the last time we will see each other, bazan sake dawowa ba. Sosai Dad ke kuka kaman kar ya rabu da tilon 'dansa haka yaji....
"A airport suka ha'du dasu Sumy Sameer da 'ya'yansu Amal da Islam. Nan Saadiq ya wuce ya rungume cousins dinsa, su Amal irin itace Adda sai cewa take" you guyz should behave your selves kunsan ba'a wasa cikin jirgi... " turo baki Islam tayi tace kai Adda Amal, Sumy ta rungumosu gaba 'daya tace" Ok kids shall we.... gaba daya suka ce yeeees suka fara shigewa jirgi.
"Waya Haidar ya mata tana tsaka da rabin fa'dan Farouq da Deena, ta dauka tana ci gaba da fa'din" you guyz are boring...... dariya Haidar yayi yace " Beautifuuuuuul I apologies on behalf of them, besides daddy na hanya, na sauka yanzun nan a airport ki shirya tarban *Naval Chief Of Staff. Admiral Aliyu Abubakar (Mijin Haneefah)* dariya Hanifa tayi tace" Handsome I can't wait to see you, su Sady ma duk sun iso, kai kawai ake jira a soma shagali. Allah ya tayaka ri'ko my Handsome. Kiss ya manna mata daga cikin wayan yace ameen my Beautiful.
"Gidan mamy ya cika damm da jikoki da 'ya'ya Haidar da matarsa Haneefah tareda 'ya'yansu Farouq da Deena, Shema'u da mijinta Saifullah tare da 'ya'yansu Nisreen da Abdullah, Sadiya da mijinta Aisar tareda 'dansu Saadiq sai Sumayya da mijinta Sameer tarda 'ya'yansu Amal da Islam. Sai godiyan Allah zuri'a tayi albarka.
"Mamy ne ke sau'kowa daga stirs tana fa'din" ina kuke kuzo ku rabani da jarababbun 'ya'yanku, su kuwa yaran sai hayewa jikin mamy suke, su Hany kuwa me zasuyi banda dariya.... Inna ce ta shigo taci kwalliya take fadin" ina shugaban sojojin ruwan yake gwara a fara patin dan ni na gaji da jira ehe ga sosjoji ta ko ina a gidanmu, mun zama 'yan gata sojoji ke gadinmu... Su sameer sai dariya suke, Aisar yace Inna akwai harba bindiga fah....Inna tayi kicinkicin da fuska tace" ai kaji irin tsiyanku na sojojin,... aka kuma sa dariya.
"'Danmasani ne ya shigo ya zama cikekken saurayi meji da swags..... gaisawa sukayi da 'yan uwan nasa da mazajensu kafin ya wuce wajen yaran yana fa'din" Hi Kids.... "Gaba 'daya suka nufosa suna fa'din "Uncle Deee suka haye jikinsa... 'daukansu 'daya bayan 'daya ya soma yana fa'din" wanna have some Chocolates..... "Ganaki 'daya suka ha'da baki suna fa'din yeeessss..." Ok fine, let's go then..... "Nan duka suka hau bin 'Danmasani wasu na kama 'kafansa wasu na jan rigarsa suka fice......
ALHAMDULILLAH, Nan nima na kawo 'karshen wnn littafi nawa me suna *Mijin Haneefah* kuskuren da nayi cikinsa ina ro'kon Allah ya yafe mani, fa'dakarwan dake cikinsa Allah sa mu amfana dashi baki 'daya.
Kuna raina Queen Samy novel group.
Feesaty
Hanifa waziri
Islah luv
Mum Nazir..... and others luv you all.
Novels Only group.....
Aisha Maid
Kifdiya
Rally Garba
Pherty
Aisha
Maman khairat
HGU........dama wa'danda ban ban ambatosu ba.. lots of luv.
Sameena Aliyu Queen Samy ke maku ftan alkhairi.😅😏❤
Muna Matuƙar Godiya sosai agareki
Da fatan alkhairi, bisa wannan namijin ƙoƙari Allah ya ƙara basira ameen
Saƙon muhammad kabeer zuwa gareki
08160112181
👸🏻Queen Samy😍💄💋.......
0 comments:
Post a Comment