*NA TAFKA KUSKURE!!*
π♀π♀π♀π♀π♀π♀π♀π♀
*NA*
*Janaf ce*✍✍
DEDICATED TO *My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*
I so much luvs u my mommaππ
*INTERLLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*{onward together}*
*{we give the the Reader's of ours the best out of the bests,,,Our inks are melodious and dropping a kinda light to reader's}*""""
*THE PEN OF LOVE*π
*HEART OF TOUCHING*❤ *TEARS OF SORROW*π *CURDLE*π, *GIGGLES*π,
*AND MARRIEGE THINKS.*π
*JUST GIVES US A FOLLOW*✔
*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*
*AM BACK AGAINπ*
*SABUWAR SHEKARA SABUWAR RAYUWA....Happy New yearπππππ*
*01*
---------Da gudu wata motar kirar corrolla X kirar toyota,ta shiga cikin wani private hospital *S&S SAFANA SPECIALIST HOSPITAL* Cikin Hanzari matar tabude motar tafito tayi cikin asibitin da gudu tana fadin"ku taimakamin kada yata ta mutu ku taimaka" Nurses suka biyota aguje da abun daukan marasa lafiya,wata matashiyar budurwa ce aka fito da ita daga cikin mota tareda wata dattijuwan mata,tsirtsetsen cikin keta wutsul wutsul alamar yana gab da Fitowa Ihu take zabgawa iya karfinta tareda wasu maganganu marasa ma'ana Da Hanzari suka gungurata sai labour room,Hajiya karima takalli Momma tace"To ai sai kira danki shafaffe da mai ya taho ya girbi abunda ya shuka" tafada dawani irin izgilanci,Momma tayi murmishi irin nata kan tace"Ayyah Hajiya zai zo ba"a gabanki namai waya ba kan mufito,insha yanxu zai zo kila wani abun ne ya tsaidashi"Tafada tana duban Hajiyar yamutsa fuska tayi zata magana kenan Kamshin turaren azzaro visit yafara musu maraba ko ba'a fada musu ba sunsan mamallakin kamshin.
Momma takara fadada fara'arta daidai lokacin da suka kariso maza biyu ne cikin shigar suit Black and ash,rigar likitancine saye acikin su,Daya daga cikinsu ya Karisa yana Fadin"Momma Har kun iso"cikin fara"a tace"mun iso Babana kashiga sun shiga da ita ciki"mtswssss tsakin daya katsesu kenan suka juya atare suna kallon Hajiya kari datake zabgamusu Harara,tace cikin kallon raini"Kaga mallam ba mgana zaka tsaya yi ba yata nakeson nasan Halin data cike,tundazu anshiga da ita bawani labari"Tsam dukkansu sukayi da rai kafin momma tayi karfin halin zame Hannunta tana Fadin"Babana Hanzarta kashiga ga Hadin da *SAKINATU* take ciki,cikin takaici da bakin ciki ya juyo wow!! abunda na Furta kena dogon bufullatani mai cikar zati da kamala,yanada tsawon da dan kibam murjewa,dogon Hanci ya mallaka tareda madaidaitan dan bakinsa pick kamar yana shafa janbaki idanunsa,bakin gashin kansa yakwanta ye luf dashi,zagayayyen sajensa yakaramasa kwarjini Fari ne tas mai jaja din nan abun burgewa goshinsa dauke da tabon salla wanda yake kara masa kima a idon mutane,wani siririn gilashine mai karama Fuskarsa kyau sanye a idanunsa,kallo daya zakamai ka fahimci tsayayyan Namiji mai cikar zati da Haiba *DR SAFWAN SALE SAFANA* kenan likitan daya kware gurin kula daduk abunda yashafi mata wanda ke tare dashi *DR TAHIR* kenan Abokine kuma Amini garesa kuma abokin aikinsa dasuke aiki akarkashin asibitin shi Dr safwan din.
Sai da ya isa kusa da ita yadan ramkwafa yace cikin dakakkiyar murya"Barka da zuwa Haji......."wai shi na tambayeka"ta katseshi "yata nake bukatar jin Halin datake ciki anshiga da ita tundazu naji shuru'takareshe fada tana wani jijjiga kamar wata yar daba,yadade tsugunne kafin yamike cikin sanyin jiki,ya Nufi kofar labour room din yasa Hannu a handle din kenan Wata murya cikin karaji"Allah ya isa tsakani na dakai safwan,kayi min ciki kabarni da wahala,kacemin Haihuwa babu wuya...Gashi....Gashi kabarni da wahala kai babu abunda kasani sai ciπkamar tuwo wlh bazan sake yadda dakai ba" cikin bakin ciki da Nadama yasaki Hannun kofar ya juya ya Fara Tafiya duk suka bishi da kallo Hajiya kari tace cikin daga murya"Kai safwan ina zaka ko bakajin ihun da sakina takeyi bane.....Ina ko waiwayowa baiyiba saima kara sauri dayayi har yabace daga gurin.
Cikin Takaici Hajiya kari tadaga Hannu sama tana Fadin"wayyo ni karima nashga uku"kan ta isa kusa Da momma tana Fadin"ke wata irin uwace kinaganin wulakancin da danki yayi ma yata ammh kin gagara mai magana,saboda yagama cin moriyar ganga ya dirkamata ciki ko"Takareshe Fada Tana zaremata ido,Momma tayi mirimishi daya zaman mata jiki kam tayi magana Dr Tahir yarigata dacewa"Am....Hajiya kiyi Hakuri i promise u sakina Zata Haihu lafy"yana gama fadar haka ya shiga labour room. din
Dakyar Dr safwan ya karisa office dinshi cikin kunan rai,toilet yafada yasakarma kansa shower ko kayan jikinsa bai cireba Haka ruwan keta kwararamai yafi minti talati so yake yarage radadin dake addabansa,Haka ya Fito ruwa na diga ta ko'ina ajikinsa kan kujrerar dake office din yafada yana maida Numfashi.
Har abada baisan yaushe zai zama mutum a idanun sakina da mahaifiyarta ba,baisan yaushe sakina da Mahaifiyarta zasu daina cimai mutumci ba shida mahaifiyarsa ba,baisan sai yaushene zata darajasa ta kallesa amtsayin miji ba bai sani ba,bai sani ba,yafada da karfi idanuwansa sun canza launi.
Runte idanunsa yayi yana ajiyar zuciya kafin komai ya dinga dawomai daki daki kamar yanzu akeyi.
commet
And
Share
Janaf✍
π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀
*NA TAFKA KUSKURE!!*
π♀π♀π♀π♀π♀π♀π♀π♀
*NA*
*Janaf ce*✍✍
DEDICATED TO *My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*
I so much luvs u my mommaππ
*INTERLLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*{onward together}*
*{we give the the Reader's of ours the best out of the bests,,,Our inks are melodious and dropping a kinda light to reader's}*""""
*THE PEN OF LOVE*π
*HEART OF TOUCHING*❤ *TEARS OF SORROW*π *CURDLE*π, *GIGGLES*π,
*AND MARRIEGE THINKS.*π
*JUST GIVES US A FOLLOW*✔
*02*
*WASU SHEKARU ACHAN BAYA*
------DR SALE HABULE SAFANA shine cikakken sunan mahaifinsa wanda dane ga marigayi Justice Habule safana kafin Allah yamai Rasuwa,yayi gwagwarmaya agwannati har kawo mutuwarsa,Dr sale habule safana Haifaffan safana ne dake jihar katsina,yada shekara bakwai aduniya Allah yadauki ran mahaifinsa,Mahaifiyarsa Hajiya Maryam wacce suke kirada Hajiya mama ita tadinga kula da danta har yagirma,Yayi sakandiri sch dinsa a barewa college dake zaria anan kuma yahadu da Aminsa kabir kankia ganin sun fito daga jaha daya yasanya abotarsu tafi tafiya daidai.
Bayan sun kamallah amakaranta suka Fada ABU ZARIA a inda Sale ke karantan medicine shikuma kabir political science,ammh duk da haka suna Haduwa inbasuda lectures,Haka rayuwa tacigada da tafiya Har kabir ya kammala digirin dinsa ya dora masters dinshi shikuma alokacin sale yatafi Bautar kasa.
Sale a adamawa yatafi bautar kasa kuma achan Allah ne yahadasa da mahaifiyar Safwan Hadiza,Hadiza mahaifaffiyar Adawamane ce bafullatanan asali, marainiya bata uwa ba da uba sai kanin mahaifinta wanda yariketa mai suna Baffa Sani Hadiz bata zurfafa lilimi ba iyakarta sakandiri ammh masaniya littafan Addinin muslunci tana da ilimi fiye da tunanin mai karatu bai kammala bautar kasa ba Allah ya kulla aurensu tareda jajircewan Hajiya mama.
Lokacin da'akayi bikin kabir kankia na kasar spain yaje yin phd dinsa,sai da yadawo yaji amininsa yayi aure hakika ya tayasa murna kwarai matuka samun mace irin Hadiza.Macece kyakyawa dogowa mai dogon Hanci da gashi,Bayan kammala bautar kasarsa yafara aiki da Aminu kano,Yaso dauki iyalansa sukoma Hajiya mama taki amincewa dole yasa yabarsu nan safana yana zuwa musu weeked
Bayan kammala karatun kabir kankia yafada siyasa kadangadan akuma lokacin iyayensa suka masa aure da yar uwarsa Karimatu,karimatu tun tana karimar shegiyar makirace,gata bawani kyau ba bakace mummuna ga gajarta,tun tana yarinyanta take bala'in son auren mai kudi bata shiri da takala,gata da kyashi da hassada ga bariki kala kala dan dai babu yadda zai yine yasa yahakura ya amshi karima.
Yafara rike mukamin sakataren gwannatin janar katsina akuma lokacin Hadiza ta haifi Safwan Hakika tunganin Farko da karima tama Hadiza taji ta tsaneta saboda tafita kyau uwa uba hankali Natsuwa da tarbiya kai akomai tadarata shiyasa lokaci guda kyashi ya shigeta,batawani sakarmata sai kiga tawani yamutse yamutse kamar taga kashi shiyasa Hajiya mama ganin Farko tace"Kabiru ina karoro wannnan ruwan yan Duniyan"kai tsaye agabanta mirmishi kawai yayi itakuma karima tadago tana karema Hajiya kallo ta kasan ido.
safwan yazo cikin gata,badewa mahaifinsa ya tafi london karo karatu sai da ya shekara uku kana yadawo lokacin yazama consultand,Safwan nada shekara biyar iyayensa suka kaisa Nigeria turkish.tunda Hadiza ta haifi safwan bata kara Haihuwa.
Haka dai Rayuwan ta cigada juyawa cikin nasara da kwanciyar Hankali lokacin da Safwan ya kammala secondry sch dinsa lokacin Da Allah ya karbi ran Mahafinsa hatsari yayi ahanyarsa tadawowa daga kano hakika matuwar Dr sale Habu safasa ta girgiza yan'uwa da abokan arzika,Alhaji kabir yaji mutuwar Amininsa matuka sai dai Hakuri
Hajiya da Hadiza wacce Safwan kekira da Momma suka dau dangana suka maida Hankalinsu wurin kula da safwan,Lafawar abun yasa yadage kasar malesia zuwa karatun medicine sai da ya shafe shekara sha kana yadawo lokacin yazama cikakken likitan mata.
Shima din da Aminun kanon ya fara aikin kan chukun chukun bude asibitinsa ya kammala da taimakon Dady Alhaji Kabir kanki wanda yake matsayin kwashinan ilimi ta jahar katsina.
Koda bude asibitin ya kammala baida na aiki da Aminu kano ba Saida ya tattaro Su Hajiya suka dawo garin kaduna kana ya maida Hankalinsa kan asibintinsa,Dr tahir Aminsane wanda suka Hadu a malesia course daya suka karanta,kuma yan kasa daya shiyasa abotarsu tayi karfo Shiyasa bayan ya kammala asibitin ya Nemosa don Atafi tare
Alhaji kabir bai yada iyalan Dr sale ba yana kokarin ziyartarsu in yasamu dama,duk abunda suke bukatu tunkan suyi mgana yake kawo musu Hakika shi mutumin kirkine sai dai Karima tanajin bakincikin abunda yake musu dan dai bayya zatayi duk da yanxu ta mallakeshi sai abunda tace yakeyi
*WACECE SAKINATU*
SAKINAT KABIR KANKIA shine cikakken sunanta yace ga kwamishina Alhaji Kabir kankia da Hajiya karima wacce ake kira Hajiya kari,yayansu hudu salmace babba tana aure a portharcort wani controller ne sai laila dake auren wani dan kasuwa a kano,sai Sakina daga ita sai Ummi.
Gabadaya ya"yan Hajiya kari laila da sakina,sune suka dauko halayyanta wanda ma harsun gyasheta Salma ce da Ummi kadai suka fita dabam,dukkansu suna da degree sakina business admistration takaranta Tana son taga tazama yar kasuwa tana juya kudi ahannunta shiyasa tana dawo daga london bayan ta kammala masters dinta Mahaifinta ya tallafamata,tafara odar kaya daga dubai zuwa Nigeria irinsu dogayen riguna da takalma da jaka,kayan maza kai duk abunda yadanganci sawa da kwalliya,cikin lokaci Allah yasa abun albarka cikin shekara biyu sakina ta bunkasa tayi kudi tuni takeda dankara dankara shaguna a kano,kaduna,katsina,zamfara,da gombe,Sakina boutique and costimetics,sakinat shoes,etc.
Gabadaya Hajiy Kari bata kula da tarbiyan yaran ba kwamishina baya zama so komai na Hannunta,shiyasa sakina tataso tun tana karama bata kunya ga raina na gaba da ita bata da kunya ko kadan bata iya girmama nagabada da ita ba.
Sakina bawata kyakyawa bace ta azo agani bakace gajera ammh saboda shafen nan na yaran zamani yasa takoma Fara,Wani gajeran hanci gareta tana da dan tudun baki,kan nan kamar Hammatar dan iska kullum cikin gashin doki take,tanason mu'amala da abun mai kyau duk da ita din bamai kyau bace,Sakina bata kaunar talaka ko kadan shiyasa danginsu na kanki kowa yasanta da rainin arziki shiyasa kaf suka fita harkansu sboda Hajiya kari inrin matan nan ne masu kyashi arziki daga ita sai mjinta da yayanta.
Sakina yar gayuce ta karshe kullum cikin shigar alfarma zaka ganta,to tazo kaduna duba shop dinta taji zazzabi ya rufeta tana Hanya shine tafada asibitin Dr safwan ganin farko tamai yasace zuciyarta wanda dagashi har ita basusan juna ba saboda kowa ba kasar nan yayi karatunsa ba,Ada ta dauka wasane sai da takoma gida kana ta tabbatar da takamu da son Dr safwan,tayi kokarin tayakiceshi ammh hakan ya faskara,abinciken da'aka matane tagano dane gun Aminin Abbanta.
Da tama hajiya kari magnar kin bada goyan baya acewarta baida qualities din auren yarta,ammh sakinat taki hakura,taci gaba da shisshigemai da kissa da kisisina,Da hajiya taga yarta taki hakura yasa tashiga tafita har soyayyah mai zafi ta kullu atsakaninsu,Lokacin da kwamishina yaji labari yayi matukar farinciki dasamun suriki irin Dr safwan,kuma yakara zumunci tsakaninsa da amininsa duk da baya raye.
Da Hajiya mama taji lbr tadaga tsalle tace bata yarda ba saboda sanin mugun halin Hajiya kari ammh Dr safwan ya tubure dole tasa ta amince ita daman momma batada matsala cikin lokaci kankanin komai ya kammallah Amarya tatare a gidanshi dake kaduna,mai dauke da shashi biyu daya na momma da Hajiya daya shine mallakin sakina
Sunkwashi amarci na tsawon wata guda kafin halayyan,Sakina sufara bayyana.
Commet
And
Share
Janaf✍
π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀
*NA TAFKA KUSKURE!!*
π♀π♀π♀π♀π♀π♀π♀π♀
*NA*
*Janaf ce*✍✍
DEDICATED TO *My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*
I so much luvs u my mommaππ
*INTERLLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*{onward together}*
*{we give the the Reader's of ours the best out of the bests,,,Our inks are melodious and dropping a kinda light to reader's}*""""
*THE PEN OF LOVE*π
*HEART OF TOUCHING*❤ *TEARS OF SORROW*π *CURDLE*π, *GIGGLES*π,
*AND MARRIEGE THINKS.*π
*JUST GIVES US A FOLLOW*✔
*03*
------Hallaya ta farko data fara bayyana shine kazanta da lalaci,kafin Hajiyarta tasamo mata masu aiki Sai dai shi inyagaji da ganin kazanta ranar karshen mako yazage ya tsaftace gidan tun yana mgana har ya zuramata ido.
Girkuwa baida darajar da sakina zata girkamai abinci to tama iyane banda indomie bata iya dafa komai ba,kullum sai dai masu aiki su jagwagwala su ijeye sai da kullum yana rabawa sashin momma yanacin abinci, gashi batason zaman gidan kullum tana Hanyar katsina ko kano,Ko yamata mgana baji takeyi ba shiyasa ya zuramata ido.
Raininta har momma bata kyaleka ba yimata take dayake momma macece mai Hakuri da kawaichi momma irin matannan ne masu mugun Hakuri ko zaginka kayi sai dai tama mirmishi,ashekaru bata wuce43 ba,shiyasa sakina tayi bala'in rainata tadinga daka mata tsawa,Hajiya mama ce take shakkar domin itace big problem dinta agidan Safwan.
...Hajiya mama Dattijuwa ce yar kimanin shekara sitti aduniya,Bata daukan raini ko kadan irin tsofaffun nan ne wanda komai ke ransu gameda kai saisun fada maka sai dai kamutu tanada faran faran da jama'a dason mutane tun tana safana macece takowa makotanta kuwa kamar yan'uwanta Haka ta daukesu,tanada fada in aka tabota gata wani lokacin da ashisshigi koba"ayi da"ita saita tsoma kanta,shiyasa Sakina ta tsaneta saboda tana mata katsalandan a al"amarinta game da Mijinta Safwan.
Wani lokacin Hajiya ke tarema momma tacima sakinar,inkuwa dukkansu suka bata haushi tasharesu,Safwan yarasa yadda zaiyi da sakina daya tashi daukan mataki momma tahanasa.
Ranshi bai kara baci da Sakina ba saida tayi Rashin lafiya tafara,rashin lafy tana zubar jinin,Dubar farko ya fahimci taje anrufemata bakin mahaifa dayake Allah ba'a mai dabara sai ga ciki ya bulla agefen mahaifa,bai mata mgana sai da yayimata operation yamaida cikin jikin mahaifa ya sallamota suka koma gida,Sakina taga bacin ran Safwan wanda mgana har kunnin kwamishina wanda yacimata mutumci ba'a son ran sakina tacigaba da renon cikin jikinta ba domin ita atsarinta babu Hawaye Allah shi kyauta,Shawaran Hajiyarta da laila ne sunfada mata karta yarda yamaida ita akuya tadinga zazzagamai ya"ya karshen tadurkushe shikuma ya aure wata.
SAFWAN yaci sunan mahaifin momma ne shiyasa bata iya fadar sunansa sai dai da babana, Mutum ne mai Hakuri saboda Nonon Momma ya tsotsa,shekararsa ta haihuwa 32 yanada kawaichi da dattako mutum ne mai Nagarta kallo daya zakamai kakirasa ustaz ammh social ne yana da zurfafan bincike a bangaren ilimin addini duk matsayinsa na likita yahaddacce Qur'ani tun yana shekara sha hudu aduniya saboda jajircewan momma agaresa, da sauran littafai irinsu,muwadda malik,sahihul bukhari,iziya,sira,fiqhu,dadai sauransu,yana da tsantsane da addinsa matuka mutum ne mai yalwar fara"a,yana bala"in kaunar mommansa saboda itace ginshikinsa da kakarsa Hajiya mama.
Abangaren kaya yafison manyan kaya atsarinsa yafison yasanya shadda gezner da yadi mai stantsi ammh saboda yanayin aikinsa yasanya yake surkawa da suite ammh duk Ranar jumma"a ko yasani shigar manyan kayan ne atsararinsa.Yana da zuciya da fushi wanda yakan dade kafin yayi irinsa fushin kuma in yayi fushi da abu na har abada yakeyi,bangaren abinci yafison abincin gargajiya,irinsu dambu,fate,fankasau,tuwo miya kubewa da dai sauransu.
Aurensa da sakina babu abunda yakaru dashi sai ci baya tunbayan aurensu matsaloli suka dunga kunno kai saboda sanyinsa yasa ta rainasa bai isa yamata mgana taji ba shikuma baisan hayaniya da kwakwazo dat why yake yakyaleta uwa uba yana ganin mutumci mahaifinta,A yan"uwanta kaf bamai darajashi sai salma da ummi Hajiya kuwa da laila dama sune aminan sakina duk abunda sukace shi takeyi,ko bangaren auratayyah bazai iya dora komai ba domin sai inyarasa yadda zaiyi ne yake neman sakina,saboda baya samun gamsuwa bata iya komai na fanni bama miji kulawa ba,gashi bata rabo dama kanta pixsing kullum sugama saduwa da juna sai yakoma yana jinyar kansa saboda tsabar yakusan dayake sha,ita bata damu danashi bukatan ba nata kawai tadamu dashi tayimai sharf kamar kayan wanki yaci yatashi bawani salo balle kukan kissa,ita ba abunda tasani sai ci ta kwanta sai gayun kawai awaje ammh aciki sai takaichi.
Ko Rainan cikin sai abunda yagani sai yayi sati bai nemata ba ammh duk ranar daya nemata bada son ranta ba sai yakusa kuka saboda takaichi itadai sakina ba abunda tasani sai harkan kasuwanci ko dan kayan gyaran jiki bata damu dasha ba dan tagyara kanta ba a"a ita abunda tasama gaba shine agabanta.shiyasa bai rabo da azumin litini da alhamis Domin kare kansa daga halaka.
Kullum ta kalli cikin sai ta zageshi aranta,Haka tacigaba da renon cikin,cikin bakinciki da danasani saboda mahaifinta yace wlh yaji lbrin wani abu yasamun ciki kashinta ya bushe,ga bakincikin tadaina fita ko'ina tunda cikin ya tsufa,kullum cikin zuwa Hajiya take tana duba yarta acewarta,babu mai kula da ita,gashi ta ranma momma basaboda sunganta bamai karamniya bace.
Ranar da Sakina tafara naguda tun Safe Dr safwan yatafi asibiti,kuma da safe yadekata yaga tana barci,itakuwa Hajiya daman sunyi waya,da ita tafadamata batajin dadin jikinta shiyasa tun safe,tasa dereba ya daukota suka kamo Hanya koda ta iso ta iske sakina tafara jigata,shita da Hanzari tafito da ita zasu wuce asibiti,Itakuma momma tafito tazo taduba sakinar sai taci karo dasu,cikin azama ta isa tana tambayan lafiya"harara kawai Hajiya kari ke zabgama momma takasa bata amsa,da sauri Momma tace Hajiya bari in dauko mayafi insanar da hajiya muje"Ko kallonta batayi ba koda ta isa,shashensu ta iske Hajiya cikin daki take fada mata"Tabe baki hajiya tayi kan tace"Allah raba lfy nikingama barci nakeji in kinfita kirufemin kofar daga haka tashige ta barta nan momma takira Dr safwan take fadamai gasunan zuwa da sakina zata Haihu,yashiga rudu yace su hanzarta,Koda tafito Hajiya na kokarin sanyata cikin mota tataimakamata suka sanya suka nufi asibitin tanaji Hajiya kari takira yarta tanafadamata abunda ke faruwa tana zagin Momma din da danta sai dai kawai tayi mirmishi ta kauda kai.
Shine dalilin kawota asbiti da abunda yafaru.
WANNAN KENAN
Commet
And
Share
Janaf✍
π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀
*NA TAFKA KUSKURE!!*
ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀
*NA*
*Janaf ce*✍✍
DEDICATED TO *My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*
I so much luvs u my mommaππ
*INTERLLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*{onward together}*
*{we give the the Reader's of ours the best out of the bests,,,Our inks are melodious and dropping a kinda light to reader's}*""""
*THE PEN OF LOVE*π
*HEART OF TOUCHING*❤ *TEARS OF SORROW*π *CURDLE*π, *GIGGLES*π, *AND MARRIEGE THINKS*π
*JUST GIVES US A FOLLOW*✔
*04*
-----Tura kofar office din akayi tareda shigowa,Dr tahir ya kariso yana mai karewa Dr safwan kallo wanda ke kwance ruwa nadiga ajikinsa duk ya jika kujeran kwaya dayan datake office din,cikin azama Dr Tahir ya isa garesa yana Fadin"Dr Safana wht wrong with u"yafada yana mai dafasa,ajiyar zuciya Dr safwan ya sauke yana mai sauke gwaron numfashi bayan tsawon lokacin daya dauka yana tuna iya tsawon lokacin daYa dauka yana kunsan bakincikin sakina da uwarta.
Ya dago idanunsa jajir kamar garwashi yana bin Dr Tahir da kallo,kallo daya Dr Tahir yama safwan yaji mugun tsausayinsa ya tsirgamasa hannu yasanya yana jijjiga kafadarsa yana fadin"Dr Safwan Dan Allah Dan Annabi kayi....."Nagaji Nagaji Tahir wlh Nagaji"ya katsesa cikin kunar rai da kosawa"koda yaushe kaida momma kalmarku daya inyi hakuri shin bakuda wani abunda zaku iya gayamin sai kalmar Hakuri eye"yafada yanawani zaremai ido idanunsa sun tara kwallah,cikin sanyin jiki tahir ya karisa kusa dashi yana riko hannunsa,yana fadin"Babu...Babu safwan babu wata kalma data dace dakai bayan Hakuri,nasanka kacigabada da hakurin daka saba Allah nasane dakai"shuru Dr safwan yamai yana kallonsa kamar yana karantan wani abu atareda shi,kara damke hannunsa yayi yana jijjigawa alamar lallashi cikin kasala ya zare hannunsa ya isa ga wata durowa dake cikin office akafe ya bude sai ga wasu jeren kayan sun bayyana kai tsaye ya ciro su yakama Hanyan toilet Dr Tahir yayi zuru yana kallonsa sai dayaga yana shirin shiga toilet kana yace"ta sauka an sami DR SALE SAFWAN SAFANA Da sauri ya juyo yana kallonsa kan mirmishi ya subuce masa zaiyi mgana kenan Dr Tahir ya rigasa dacewa"Both momma da bby are in good Health yanxu ma zan basu sallama su koma gida" gyada kai yayi kafin yace"thanks so much Dr....."Zan maidasu gida"Abunda tahir ya katsesa dacewa kenan kafin yafice mirmishi kawai Dr safwan yayi kafin ya girgiza kai yafada toilet.
Dr Tahir ya tura kai Dakin da"a ka kawo sakina bayan angyarata,ita da bbyn nata,Momma ta amsa sallaman tana Fadin"Attahiru sannu da kokari "Yauwa mommanmu Barkanmu fa"Yafada shima yana mirmishi karisawa yayi yana mai kara kallon babyn wanda kamar Dr yayi kaki,momma tadago tana Fadin"kaga danku ko,kungirma yanxu inashi baban nawa yazo yaga dansa mana"Tahir yace zaizo yanxu momma bari nadubata in babu matsala inmai daku gida"Momma tace"Alhamdulillah..."Gurin sakina ya karisa wacce ka zaune kan gado tana shan ruwan shayi yayinda Hajiya kari ke gefenta tana faman buge bugen waya"cikin mirmishi yace"Sannu madam munfa gode"Kallon raini ta watsama Tahir kan tace"Dole kace kungode kun hadani da aiki kun gudu"Yasan da wanda take shiyasa yace mata"is ur duty ai madam kema kinsani Haihuwa na matane ba maza ba kuma meye ribar auren soyayyah,A Haifi ya'yan soyayyah"yakareshe Fada yana dariya kasa kasa tunda yafara mgana Hajiya kari dake waya take zagmai Harara yana kallonta ta kasan ido aransa yace'oho dai bazan dakuba dai" kasa bashi amsa sakina tayi saboda tasan waye Tahir gurin maida magana kamar dan Hausa bakwai.
..Ya rubuta mata maganin karin jini kafin yabata sallama saboda ta haihu lafy ko kari ba'a mata tana haihuwa kaji kwakwazo tsit tamike ras kamar ba ita ba yana tsokananta yasan ya kunnota shiyasa yaketa dariya,ita kuwa Hajiya kari jitake kamar ta shakeshi yacika iyayi ga tsinannan tadi kamar wani aku,momma tana ta zunduma ma Tahir Albarka har suka fito,har mota yarakasu momma dai ita ke rike da jikanta,har sunshiga mota Hajiya kari ta lego tace"Shi wanchan fa koda dan shege aka Haifa ai yazo yaganshi balle dan Sunnah ne kuma shi yadigasa"Tafada kanta tsaye Dr Tahir yagyara tsayuwa sanin matan bata da kunya ko kadan yasa kai tsaye yace mata"Wlh aikine yarikesa ammh kema kinsa bakasha wahalar diga abu da kanka ba,kuma ka banzarta dashi ba"Yafada yana kallonta ido cikin ido kasa bashi amsa tayi har dereba yajasu suka bar asibitin yana kallon motan yana killer smile kafin yace'kunyan mara kunya asara.
**********************
Hajiya mama dake zaune a farfajiyar flat dinsu tana tsinkan zogalanta datazo dashi daga safana radio tane takure kara tana jin gidan radion freedom ansa wakar sangaya ta daddage, tana bin abinta Mallam Ilaya mai baWa fulawa ruwane agidan,shine aikinsa shike zaune kusa da Hajiya tana zubamai labarin zamanta a safana sukaji hon din motan Mallan Habu mai gadi yayi gaggawan zuwa ya wangale get motar tasu tasawo kai zuwa parking space Momma ce tafara fitowa rike da baby a hannunta kafin Hajiya da sakina wacce tafito tana wani hura hanci kamar wata sakarya,Hajiya mama tai galala tana kallonsu Tunda Hajiya kari tafito taga Hajiya mama tawani hade rai,momma cikin farinciki ta nufi Hajiya mama tana fadin"Hajiya kiyi barka kinyi sabon maigida"Tsuramata ido Hajiya tayi tana kallonta sama da kasa kafin tace"Au....Wai tasauka ne na"aza bazata iya Haihuwa da kanta ba"tafada tana bin sakinar dawani kallon raini"jikin Momma yayi sanyi kafin tayi mgana Hajiya mama taci gaba da cewa'au ke kika koma mai renon kuma saboda sunmaidake wata sha katafi ko"tafada ranta abace Momma tadago zatayi magana taga mallam iliyasu ya tsuramusu ido da sauri tace"Mallam ilaya kunyi da fa "yana washe baki yazo ya amasheshi yana sa masa albarka shima mallam Habu yakariso yana sa albarka.
Hajiya mama tamike tawuce tana fadin"bari naje naji ubanwa zai mata renon dan"tana fada tawuce fuu sashen sakina wacce tun fitowarsu suka shige ciki,koda ta isa basu afalo cikin bedroom ta samesu sakina kwance share share Akan gado Hajiya kari nagefen suna mgana Hajiya mama tafado dakin,sororo suke binta da kallon Hajiya kari tayi karfin halin cewa"Haba hajiya da girmanki kina shigowa guri babu sallama"tafada tawani cin mgani Hajiya mama ta kallesu a wulakance kan tace"Ana sallama inda akasan darajan sallamane ba inda ba'asan darajarta ba"Cikin kunan rai sakina tace"gaskiya hajiya wlh kija girmanki,kan mene gaskia kija girmanki tunkan na tunkudesa"takareshe fada da rashin kunya Hajiya mama tace"Kin ma uwarki bani ba wlh da ita kikeyi don banace kinma ubanki ba don Kabiru yaron arziki ne, nikam nafi karfinki fitsararriya kawai,kuma wlh kinemi mai miki reno hadizar baiwar uwarkice dazaki barmata rikon jika tareni d'a kuma ta reni jika bazai yuyuba tunda kika iya bin miji kikai ciki to kin ko san yadda ake reno"Tana gama fadar haka ta buga musu tsaki tafice.
Hajiya kari takalli sakinar tana fadin"wai wannan tsohuwar anya kanta daya"Sakina tace"lafiyarta kalau Hajiya tsabar iskanci ne wlh,kuma shi safwan din ke dauremata gindi"Cikin takaichi Hajiya kari tace"shegiyar tsohuwa mai shisshigin bala'i"Sakina ta karbe da cewa"ta karshe wlh Hajiya tshohuwarnan tana shigan hanci wlh"Tafada tana bayyana takaichinta.
Hajiya tace"barta mugama da jikanta tukunnah ita karamar alhakice.
Koda Hajiya takoma ta iske momma na tsaye tana jiranta kallonta tayi tana rumgume da baby kan tace"sai ki wuce ki kaimusu dan'su saura kizauna kina musu bauta tunda nasan ki zuciyarki kamar ruwan sanyi take"tana fadar haka ta tattara shimfidanta ta shige ciki,koda momma takai shi itace tamasa wanka tasama sakina nata,ko wankanma saboda lalacewa dakanta tashiga hajiya na kallonta ko ajikinta momma taga abun mamaki ammh sanin halinsu yasa taja bakinta ta tsuke.
.Commet
And
Share
Janaf✍
π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀
*NA TAFKA KUSKURE!!*
ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀
*NA*
*Janaf ce*✍✍
DEDICATED TO *My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*
I so much luvs u my mommaππ
*INTERLLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*{onward together}*
*{we give the the Reader's of ours the best out of the bests,,,Our inks are melodious and dropping a kinda light to reader's}*""""
*THE PEN OF LOVE*π
*HEART OF TOUCHING*❤ *TEARS OF SORROW*π *CURDLE*π, *GIGGLES*π, *AND MARRIEGE THINKS*π
*JUST GIVES US A FOLLOW*✔
*I DEDICATED DIS PAGE TO U MY ANTY,SIS NARJA'ART MATAZU I CAN EXPLAIN MY ANTY BUT D ONLY THING I KNOW I REALLY CARE ABOUNT U,I LOVE U MY ANTYππ*
*05*
-----Karfe goma da wani abu Safwan yabaro asibitin sa dake anguwan rimi kaduna daura da iyali hospital kai tsaye anguwan sarki yana nufa cikin motarsa kirar benz baka,cikin slow yake tafe har ya kariso get din gidan nasa yana hon da hanzari mallam habu ya wangalemasa get yana masa barka da dawowa tareda masa barkan karuwan da'aka samu.
Kai tsaye part din momma yadosa cikin takun isa sanye cikin suit masu ruwan toka rigar likitancinsa sabe a kafadarsa wayarsa ke rike ahannunsa daya kuma yana sanye cikin aljihu,da sallama yashiga falon momma kadaice,afalon zaune kan darduma alamar sallah tagama tana lazimi cikin fara'a ta amsa sallanma tana cigaba da laziminta takalminsa sawu ciki na fatar damusa ya cire kafin ya kariso gabanta ya zauna yana fadin"Momma......"Tadago tana kallonsa cikin Annuri da farinciki,kansa yadora kan cinyanta data tankwashe yagyara kwanciyarsa,itakuma tasanya hannu tana shafa kansa lumshe ido yahau yi yanajin wani farinciki na ratsashi cikin kasala da gajiya yace"momma...Yunwa nakeji"mirmishi tayi kan tashafa addu"an shima yashafa yana fadin "Allah ya karba mommanmu"Allah ya maka albarka babana yajagoranci lamarinka yasama zuru"arka albarka"Atare suka Amsa gabadayansu da Amin harda hajiya mama data fito daga daki tana kallonsu.
Kichen tashiga tadaukomasa dambun zogalan datayimai saboda tasani masoyinshine,ruwa ta hadomai dashi sai furan data damamai don shinema basa rabo da furar'gabansa ta ijeyi tana fadin"kin cikasa da tadi....Maza ci abinci sufiyanu nasan kana jin yunwa"Mikewa yayi yana fadin"kai i so much luvs u Hajiyata kinaji dani"yafada yanajan kulan gabansa fara'arsa takarune dayaci karo da abunda ke ciki yadago cikin Annuri yana kallon momma da Hajiya dasuke kallonsa cike da so da kauna yana fadin"thanks so much hajiyata Allah biyaki da Aljannah"Amin...SufiyanuAllah yayi maka albarka"bata rai yayi yace"kinga hajiya wlh zamu bata basunana sufiyanu ba am Safwan sale safana by name"
Hajiya tace"kai kasan wani Safawaπ€£π€£ nibansanshi ba sufiyanu nasani Ato"Tafada harda da jaddawa kara bata rai yayi yamata banza yayi bismillah yafara cin abincinsa,har ya kammala bai sake mgana ba sai daya wanke hannunwansa kana yamike zai kwashe kwanukan momma tayi saurin amsa tana fadin"A'a barshi babana,kaje kahuta kuma kaga masu jego da safe ma hadu"Tafada tana amsa farantin ajiyar zuciyar ya sauke yana juyawa yace"Sai Allah ya kaimu momma"ta amsa da"Allah ya tashemu lafy"Hajiya tamike tayi hanyar dakinta tana fadin"muda ba'a son mukwana lafiyan sai mun tashi da izinin Allah ehe"tafada harda buga kafa dariya takusa subucema momma da Safwan sukayi saurin shanyewa saboda sunsan Halin Hajiya yanzunan takara harzuka.
Mirmishi kwance afuskar sa ya isa part dinsu koda ya shiga falon yadau shuru ga wata katuwar plasma tana yi ita kadai,kashewa Yayi kafin ya nufa bedroom din daya zama mallakinsa kan doruwar gadon ya ijeye wayoyinsa guda biyu kirar i phone8+ da lapcoat dinsa ya fada toile wanka yayi kafin ya dauro alwala,daure da tawul ya fito a kugunsa daya kuma yana goge jikinsa kan dressing mirror dake shake da kyan kwalliya kamar za'a bude shago ya isa kan yahau goga jikinsa da man detol,turaren avon yahau fesawa jikinsa sai da ya feshe ko'ina kana ya zura jallabiya ash colour yashimfida sallaya yadata sallah raka'a hudu yayi kafin yayi sallama yadade yana kwararo kirari ga sarki Allah daya bashi wannan kyauta haihuwa tareda addu'an Allah yakarasa masa juriya da hakurin akan sakina.
Kai tsaye bedroom din sakina ya isa ya tura da yar siririyar sallamarsa sakina na kishingide akan gado wayace ahannunta tana latsawa yasani baiwuce chart takeyi da kawayenta ba Hajiya kari na gefe ta baje sai kwasan barci take harda munshari dariya takusa kubcemai ya waske,kai tsaye ya isa ga jaririn dake kan dan gadonsa yaduka yasa hannu yadaukesa yana mai kare masa kallon cikin kauna,tsantsan kamar da yaron yake dashi yake kallo,hatta da yatsunsu iri dayace,sonsa da kaunarsa mai zurfi,yakamashi lokaci daya,rumgumesa yayi cikin shauki.da soyayyah ta har abada
Sakina dake kwance ta tsuramai ido tana kallon kyakyawan mijinta dogon dan safana tasani har abada bazata daina,son mijinta tana sonshi har gobe kuma tana kishinsa batasan sanda tatashi ta isa kusa dashi inda yake tsaye tadafa kafadarsa ahankali ya waiwayo kwallah tataru a idanunwansa da azama yahada ta da yaron ya rumgume yana fadin"Thank u Sakina....thanks so much sakina"yafada yanajin kamar kwalla zata zubo mai.
Jikin sakina yadan yi sanyi shiyasa tayi huging dinsa back,na tsawon lokaci suna rumgume da juna kafin su saki juna suna bin juna da kallon cikin ido itace tayi saurin sadda kanta kasa saboda kar ya sata cikin wani yanayi.
Hannunta kawai yaja kiii.....Tana biye dashi har bedroom dinshi kana ya sake ya haura gadon ya ijiye yaron yana kallon sakina cikin ido kan yace"Kinga kyautar da Allah yamana ko" kallonsa kawai tayi batace komai ba,yacigada da cewa"Sai wanda Allah yaso da rabon yake basa ammh kinaso kimana wasa da damar da Allah ya bamu"yakareshe fada yana sa idonsa anata,Hamma tayi kan tahaye gadon blanket taja tarufe jikinta tana fadin"Kabarni na huta Dr haihuwa fa nayi ko barci bansamu ba"tafada tana runtse ido alaman bata son damu.
Girgiza kai kawai yayi yacigada da kallon dansa har barci ya daukesa yana kan kirjinsa,koda yatashi daddare yana tsala kuka yatashi sakina tabashi nono tsaki ta buga tana fadin"Don Allah kabarni nayi barci mana"tana gama fadar haka takara jan bargo dama tunda yazo duniya bata bashi nono ba,sai ruwa da aka bashi,shi yayi ta girgizasa asaman kafada har yayi barci saman kujerar dake bedroom din yakwanta yadora bisa cikinsa hannunsa zagaye dashi har gari ya waye.
Gari na waye momma ta iso part din nasu,ta iske basu tashi ba kichen tashiga tasa ruwa a kittle tazo tazauna tana jiran tashinsu,Dr Safwan ya fito sabe da yaron yana lallashinsa yatashi sai yaga momma da sauri takarisa ta amsheshi tana fadin"Yaya kuma,kuka yakeyi ne"Sakarmata shi yayi yana fadin"Wlh momma tun jiya yake rigima"momma tace"to yasha mama kuwa"tsuru yayi mata kan yace"indai ba'a asibiti ba to bata bashi ba momma"ajiyar zuciya ta sauke kan tasabaashi tana aikin jijjiga har yayi shuru.
Yana zaune momma tamasa wanka tashiryasa cikin kayan sanyin masu kyau yafito ras dashi momma tamika ma safwan tana cewa"nono yake bukata ka roketa ta duba wannan yaron karta dau alhakinsa"cikin mutuwar jiki da kunan zuciya ya amsheshi ya rumgumesa yanajin tsausayinsu har cikin ransa itama momma shi take kallo cikin tsausaya aranta tana fadin"insha allahu HASKE yakusa shigowa rayuwarka Safwan".
Huduba yayi mai kan ya mikama momma yana fadin"Sunan dady nasa masa momma"yafada da raunin murya washe baki tayi tana fadin"kai masha allahu da zuwan sabon megida Allah yaraya ka SALISU"..
WHAT....""
Sakina ta furta da karfi wacce fitowarta kenan daga bedromm cikin rigar barci kai a hargitse,.
Tacigada cewa cikin karaji"me kace sunan dan sali wa"tafada da renin wayau galala momma tayi tana kallonta yayinda mamaki da al'ajabi ya daskarar da Dr safwan,ashe iskancin Sakina ya wuce inda yake tsammani.
Rike kugu tayi kan ta kariso falon tana cewa"tabdijam da sake an ba mai kaza kai,dan kunga nayi banza bawai ina nufun banason abunda na haifa bane balle awani roro sunan yan da na tsoffi a sama y.......SAKINA....!!! Safwan yakatseta da tsawa wanda ya firgitata har momma dake rike da jinjiri balle shi yaron daya yanka ihu tsawar ita ta data Hajiya kari, wacce take sharar barci cikin tashin hankali ta fito falo, dai dai lokacin da Safwan yace cikin bacin rai"na rantse har ga Allah inkika karisa abunda zaki fada sakina sai na baki mamaki inkin musa kuma"yafada yana kadamata hannu
Tadan tsorata ammh tsabar rashin kunya yasa tace"me zaka iya eye " tafada tanamasa wani kalon sama da kasa juyawa yayi zai koma daki tabishi tana fadin" Wlh ba wanda ya isa yasama dana wani rubabban suna wai sal...."jika ke tas!tas! ya wanketa da mari sai da ta kifa yace cikin bacin rai "wlh tallahi babu wanda ya isa ya sauyama yaro suna nine ubansa kuma nace sunan dana SALISU inga uban da isa yachanza masa suna shashasha kawai wacce batason darajan mijinta ba"yana fadar haka ya shige daki harda bango kofa jikake bam!!!!
Kasa Sakina ta zube tana kuka tana fadin"wlh Allah ya isa,kuma zakasan waka mara sai kayi nadama kuma suna baka isa ba kasama dana wannan sunan ba"tafada tana gunjin kuka,momma tadake rike da jariri ta isa kusa da Sakina zata rikota "tayi saurin dagowa tana ballamata Harara kafin ta mike ta shige daki da gudu tana cigaba da kuka,Hajiya kari tabi bayanta.
...Momma ta koma ta zauna asanyaye Hajiya mama dake bakin kofa tace tana tafa hannuwa"yayi daidai....abun yayimin dadai wlh dahaka yakema shegiya da tashiga taitayinta"momma tayi shuru tana kallon Hajiya dake ta fada tana habaice habaice amsan dan tayi tana jijjigasa tana fadin"wai shin anbashi nono kuwa,momma tace"ina fa taki bashi...."kutumar ubancan yau ga yar iska"ba'a bada nono uwarta ta bata"tafada ahasale kan ta mika mata dan tana ficewa da sauri.
Kai tsaye dakinta takoma ta dauko wayarta kirar Nokia da Safwan ya siyamata to dayake badamuwa tayi da wayan ba shiyasa bata cika amfani da ita ba,kai tsaye gun Habu mai gadi ta nufa tana fadin"mai sunan megida dan Allah duba ko zaka ga ansa kabiru,ya amsa yana duba mata yace"eh Hajiya gashi...Tace yauwa bugamai "tafada tana bubbuga kafa kamar wacce zatayi dambe
Bugu uku kwamishina ya dauka don yana da Nombar Hajiya maman da sallama yadauka yana gaisheta ta katsesa cikin masifa"kabiru kazo kaci ma yar iskan yarka da tsohuwar kilakin matarka mutumci"cikin al'ajabi kwashima ya mike yace cikin rawar murya"wani....Wani abun ne yafaru Haji...."kwarai zata kashe min jika kuma ta kashe dan data haifa dan taki bashi nono"tafada kit wayar ta mutu ba chaji Hajiya mama tayi kayfci tace"kazo ayi ta kare ko ta gyara ko tabika kutafi tare ina dalili"mallam Habu dake kallonta yace"Hajiya lafiya mai yafaru"Harara ta zabgamai kan tace"idon matambayi "Tafada tana wani harararsa afusacen ta wuce takoma part din sakina.
ho hajiya mama daru wayyo cikinaπ€£π€£π€£π€£
Kucigaba da bina cikinku zai kulle saboda darun Hajiya mama na gabaπππ
Commet
And
Share
Janaf✍
π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀
*NA TAFKA KUSKURE!!*
ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀
*NA*
*Janaf ce*✍✍
DEDICATED TO *My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*
I so much luvs u my mommaππ
*INTERLLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*{onward together}*
*{we give the the Reader's of ours the best out of the bests,,,Our inks are melodious and dropping a kinda light to reader's}*""""
*THE PEN OF LOVE*π
*HEART OF TOUCHING*❤ *TEARS OF SORROW*π *CURDLE*π, *GIGGLES*π, *AND MARRIEGE THINKS*π
*JUST GIVES US A FOLLOW*✔
*Ina kike my one and only HAFNAN marubuciyar SHIN SO DAYANE,Hakika kin chanchanci fiye da haka alkhairinki agareni bazai fadu ba,kin wuce yadda kike tsammani a zuciyata tanque for u luv support and care....Janaf luvs u more my Hafnan*πππππππ
*06*
-----Aikuwa hankalin kwamishina ya tashi dama meeting suke dashi da gwamnah,suna kammallawa,direba ya wuce dashi,kaduna koda ya isa sashen Hajiya mama yafara isa,aikuwa ta lissafamai kaf abunda sakina tayi,Hajiya mama takareshe da cewa"kaduba kabiru duk tsufana bai isa sakina ta ragamin ba,to wlh tsaf take zageni balle Hadiza ai marainiyarta ce.
Hohoho Sakina taga ta kanta don marika biyu kwamishina ya saukemata sai da momma taita bashi hakuri,yayi mata gargadi da kakkausan murya kan tashiga taitayinta inba haka ba wlh tallahi sai yasa da kanshi safwan ya sauwakemata tadawo gidan,kuma taci ubanta,yasa ta dole taba yaron nono agabanshi yakuma ce inta isa ta sauyama yaron sunan,Hajiya kari ba yadda zaiyi da ita illar sata agaba suka wuce katsina,har ya tafi basu hadu da Safwan ba domin kiran gaggawa yasamesa daga asibiti.
Washegari sai ga,laila tazo daga lagos ai kwamishina yace tayi maza takoma don ya haramtamata zuwa gidan sakina tunda yagane itace shedan din itada uwarsu,dole laila takoma da tarin takaichinta,salma ce kawai da ummi suka je sunnan Salisu wanda akama alkunya da Adil,sai kawayenta da yan uwa da abokan arziki,Sakina tashaka matuka shiyasa tayi alkwarin gasama Safwan aya Ahannunsa,badai haihuwa ba to ta haifa masa sai ya rena kayansa kuma haihuwa wlh har abadaπ³π³domin tuni tasa an juyamata mahaifa ita da haihuwa sai sadda tayi ra"ayi,anya Sakina baki *TAFKA DA KUSKURE BA*
Kwamishina da kanshi ya dauko mai zama da Sakina goggo Ramatu daga kanki taxo tana kula da Sakina da Adil hakika goggo Ramatu taga duniya agidan sakina rashin arziki kiri kiri yimata takeyi da rashin kunya duk dan tana kokarin gyarata shiyasa datagama abunda zatayi take komawa shashin Hajiya mama su barke da Hira dama zamuce ta tarar da mujemu.
Su sakina nayin arba'in goggo Ramatu,takoma tareda shatara na arzikin da Dr Safwan ya hadamata hakika tayi kewar mutanen kirki hajiya mama da momma tatabbatar da Sakina tana kokarin Tafka kuskure matukar tabari suka sallamata.
kamar jira take tayi arba'in tacigaba daga inda ta tsaya washegarin ranar tatafi kano wai anyo mata odar kaya,haka take kullum cikin yawo,kuma Adil agida take barinshi sai dai kaganshi bayan Hajiya ko bayan Momma suna aikin jijjiga in dare yayi Safwan ya amshesu wlh har kwallah sukemai aboye saboda tsausayin Dr safwan bai huta asibiti ba kuma agida ba Hutu,shidai kawai yabarma Allah komai ya yarda cewa wannan itace KADDARARSA.
**************************
*KARAMAR HUKUMAR ZURMI DAKE JAHAR ZAMFARA*
Tafe suke su biyu sanye da dogayen hijabai marun colour har kasa da nikabi kafafunsu sanye cikin safa baka ganin komai sai tafin hannunsu,littafaine a hannunsu sun rumgume alamar daga mkrantan islamia suke.
Aisha ce takauda shirun dacewa'Nikuwa *SAFEENA* ina so in tambayeki"
wacce aka kira da Safina tajuyo tana kallonta ta cikin nikabin tace cikin siririyar muryanta"Nasani daman zaki tambayeni....Nasan mganan bata wuce ta mallam yahuza ko"
Aisha tace"oh ashe ma kinsani....Niwai meke tsakaninku anya ba sonki yake ba"
Dariya Safeena tayi mai ban sha'awa kan tace"Nima ban sani ba Aisha....Kawai dai inajin wani iri in ina tare dashi"
Duka Aisha tadakamata kan tace"Yar iska ashe dama kina sonsa"
mirmishi kawai tayi batayi mgana ba har suka iso kofar gidan Safina taja ta tsaya tana kara rumgume littafanta tace"To sai gobe Aisha ki gaida mama"
"ALLAH yakaimu nima kigaidamin da Ummi yammah tayi shiyasa bazan shigaba.
Mikewa Aisha tayi,ita kuma Safina tashiga wani dan madaidaichin gidan bulo,da sallama tashiga,Ummi dake kichen ta fito tana amsawa,
Safina tace "Sannu da aiki Ummi" amsawa tayi cikin farinciki yauwa"Safinatu baiwar Allah andawo" tace"eh Ummi ina Abbah,tace"Yanzu ya fita zuwa massallachi shida Usman.
Shiga daki tayi ta kware hijabin jikinta da Safa da nikabin,sanye take da riga sikat na atamfa sunmata das da ita fitowa tayi tazari buta tashiga ta kama ruwa kan tafito tayi al"wala tashiga ta gabatar da sallar tadade tana azkar kafin ta mike ta fice ta iske Ummi na kwashe tuwo ta taimakamata suka kwashe suna Hira.
.Ta idar da isha'i kenan taji sallama Abbanta da shi da Usman kaninta,da sauri ta fito sanye da hijabi tana fadin"Sannu dadawowa ABBAH"
Yadago cikin annuri yace"Yauwa HAFIZA SAFINA brkan ki da gida"
Mirmishi tayi kan ta sunkuyar da kanta tana dariya saboda haka Abbanta ke kiranta saboda zamowarta Hafiza abangaren Alqur'ani mai girma.
da sauri takoma daki ta dauko tabarma ta shimfidamai tare da kawomai abincinsa da roban wanke hannu tana kammallah tana zaune gefe tana fadin"Abbah yau aka fadama amkranta zamu jigawa gasan alqur"ani kuma dani aciki"
"Masha Allahu....Yasa albarka Allah ya albarkaci Rayuwarki ta amsa da Amin ta na mai jin farinciki bismillah yayi kafin yafaraci shida usman ya kalleta yace"Sako hannunki Safina muci tare ko masamu albarkan ci cikin taro"cike da zumudi ta wanke Hannu ta tsoma suna ci Hira.
Ummi Data sallame sallah ta fito tazo tazauna tafadin"Au abun na ya"ya ne kenan "kai tsaye yace mata"eh na ya"yane iyaye sai su koma baya"
..Safina tace"La Ummi kema fa kinsan tare muke ci da Abbah kema kinso kiyi mgana ne"
.Allah miki albarka,tasani jan magana ne kawai"
Ummi tayi mirmishi tace tana zama"Ni ne maijan mgana yace"to waye,rigimarki nada yawa Zainabu ko safina bazatayi abunda kikeyi ba"
Kai tsaye tace'Me nakeyi tafada tana kallonsa shima kallonta yakeyi kafin yace"Kinfini sani"saurin sunkuyar dakai tayi tana dariya Safina tayi dariya Ummi ta dungureta mata kai tana fadin"Baki da kunya ko"
Yace"kyalemin yata itama tasan gaskiya.Haka suka kammallah cin tuwonsu cikin farinciki da annushuwa.
Commet
And
Share
Janaf✍
π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀
*NA TAFKA KUSKURE!!*
ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀
*NA*
*Janaf ce*✍✍
DEDICATED TO *My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*
I so much luvs u my mommaππ
*INTERLLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*{onward together}*
*{we give the the Reader's of ours the best out of the bests,,,Our inks are melodious and dropping a kinda light to reader's}*""""
*THE PEN OF LOVE*π
*HEART OF TOUCHING*❤ *TEARS OF SORROW*π *CURDLE*π, *GIGGLES*π, *AND MARRIEGE THINKS*π
*JUST GIVES US A FOLLOW*✔
*Wannan shafin nakine Anty sainah Ummi meenal hakika commet dinki nasani nishadi ubangiji yasaka miki da mafificin alkhairinsa...Janaf nasanki Sainah*
*07*
WACECE SAFINA
*SAFINA ALIYU ZURMI* shine cikakken sunanta,mahaifinta mallam Aliyu zurmi dan asalin garin zurmi ce dake jahar zamfara malamine wanda ya shahara abangaren limin addinin islama,yada matar aura guda daya wacce ta kasance diyar malaminsane dayayi karatu awurinsa agarin jalingo bafullatanan chan to dayake yakasance na hannu daman mallam alokacin shiyasa ya dauki yarsa zainabu abu ya aura masa batareda yayi duba da shidin marayane wanda baida komai,hakika zainab tacika ya tama mahaifinta biyayyah,su biyu iyayansu suka haifa ita da yayarta iyami,tare akayi bikinsu da iyamin wacce ta auri wani dan kasuwa a safana ita kuma Aliyu yadaukota suka dawo zurmi da zama.sana'ar saida hatsi yake a kasuwa Allah yasama abun albarka sunada rufin asirinsu.
Aurensu da wata biyu suka samu,lbrin rasuwar mahaifansu,sakamakon gobara takamasu cikin dare hakika snyi matukar rashi,rashi ma mai girma daga baya suka fauwalama Allah komai suka rumgume mazajensu.
sai da Zainab ta shekara,uku kana ta haifi yarta mace wacce aka samata Safina hakika safina tazo dawani al"amari domin soyayyata tuni tayi katutu azuciyar iyayanta,tun tasowarta yarinyace mai hankali da Natsuwa,ga hazaka mahaifinta yazage gurin koyamata ilimin addini tana shekara,goma sha biyu aduniya ta sauke alqur"ani,tana bitan sauran littafai.alokacin ne kuma ta sake haihuwan Usman daganan haihuwa ta tsayamata.
Tana da shekara sha biyar da aduniya ta kammallah sakandiri sch dinta sakamakon yarinyace da duk,garin zurmi ansan da kazanta,da baiwan da Allah ya bata,tana aji biyu a sakandiri akamata jumping taje ss1,Safina tahaddace sahihul bukhari da muwadda malik tana da sanin kan hadisi sosai gasan alqur"ani kuwa na gari gari ba inda batazo kuma tayi na daya,hatta mkrantansu suna alfahari da ita tuni ta kammallah aji shida yanzu suna ajin manyane.
Iyami wacce suke kira inna bata taba haihuwa ba har Allah ya karbi ran mijinsu to dayake kishiyarta nada yaya suke rike dasu har kwanan gobe,Safina tana bala"in son innanta iyami saboda har hutu take zuwan mata,da kuma Aminyarta Hajiyar safana wacce wanchan zuwan datayi inna iyami ke fadamata,jikanta yadauketa sun koma kaduna duk bataji dadi ba shiyasa safanar tafita ranta.
Samari dadama suna kawoma safina kai ammh bata basu dama saboda burin mahaifinta na zamowarta wacce al"ummah zasuyi alfahari da ita tareda kasarta Nageria,tana son iyayenta saboda suna da kyakyawan alaqa atare dasu inkagansu suna raHa da yayansu kace kannensune.
Safina yanzu tana da shekara goma sha bakwai ne aduniya yarinyace doguwa,bakace domin mahaifinta ta dauko sak doguwar fuska gareta tareda dogon hanci tana bakinta dan daidai matsakaitan idanuwa gareta Safina bawata kyakyawan azo aka gani bane ammh kyanta mai tattare da baiwane,tana da dogon gashi har baya baki silik wanda saboda yawansa yasa take kitso biyu ta rabu dashi.
Dirinta mai tsayawa arai ne domin daga kasanta a tsuke take samanta shima atsuke ba kallo daya zakamata kafahimci ta mallaki baiwa mai tarin yawana sai ka zauna da ita,miskilace ta karshe bamai wayan haniya ba tanada zurfafa bincike kullum agida in bata komai to zaka ganta cikin Nazari ne shiyasa iyayanta ke alfahari da ita matuka.
Bata jin wani namiji ya burgeta ba saboda kaf masu cewa suna sonta bbu wanda yadace da tsarinta,tana son Namiji yakasance mai aji ne kuma yakansance yanada fukafukai guda biyu wato ilimin addini dana zamani yakuma kasance yafi zurfafa ana addini,sosai yakuma zamonto mai alkunya,kawaichi,da dattako,kuma bamai yawan kwaranniya ba kuma wanda yaba duniya baya wanda yafi fuskantan lahirarsa yakuma kasance mahaifiyarsa na raye saboda tasamu makwafin Umminta,Nikuwa nace tab anya Safina zaki samu kuwaπ€
Mallam yahuza ne yakusa hada wannan abubuwan duk da baigama hadawa duka ba ammh taji ta natsu dashi duk da bai furta yana sonta ba ammh alamu sun nuna haka,mallam yahuza malaminsu ne amkrantan dasuke karatu wanda ko yasan matashine jajirtattace mai ilimi da hangen nesa,shiyasa dashi kadai zakaga Safina na mgana harda mirmishi.
WANNAN KENAN.
*********************
KADUNA
----Yau din ma Sakina kano ta kama Hanya tatafi tabarma shazeey Adil shazeey wata kedarace mara sallah Sakina ta dauko a mtsayin Nanny wacce zata reni Adil sai da takwana buyi da zuwa kana Dr safwan ya ganta bakinciki kamar yakasheshi yanzu ace arasa wacce zata renin mai da sai,kafura mara sallah kuma ace har yakoyi wasu abubuwa atareda da'ita,dawannan bakinciki ya isa shashen momma Adil na sabe akafadarsa wanda yanzu kimanin watansu uku yayi bulbul dashi sai wutsul wutsul yakeyi ahannunsa.
Momma na zaune cikin dakin Hajiya tana shafamata man zafi akafa saboda tace yau kafan ta matsamata,chan kasan makoshi yayi sallaman wanda momma ce kawai taji shi,kai tsaye ya shigo ya zauna kan stool din gadon yana rumgume da Adil momma takallesa tsausayinshi na tsirgamata.
Hajiya mama taja tsaki"mtwssss...Kai wai da girmanka kashigo ma mutane daki babu sallama" banza ya mata bai tankataba takara harzuka tace"Kai tashi kafita tunda ba dakinka bane haba ina dalili kazo kama mutane zaune kamar kabasu ajiya"
A Harzuke yace"Haba Hajiya kewai baki gane yanayin da mutum ke ciki ne eye"yafada dadan karfi galala tayi tana kallonsa kan ta kwace kafarta tagyara zama tace"To Habule gani dakeni kaji tunda wuyanka ya isa yanka"tsaki yaja kawai ya mike yana gaida momma kan ya mikamata Adil yana fadin"momma ki rikesa agurinki zan tafi asibiti," tasa hannu ta amsheshi kan tace"Adawo lafy Allah yabada sa"a" ya amsa da Amin
Hajiya mama tafara salallami tana fadin"yau anyi tsinanna yau din ma ficewa tayi tabar dan oh ni maryama naga takaina"tafada harda dora hannu akai,Dr Safwan ya isa bakin kofar yana fadin"Momma ko anzo karbarsa kar kibada shi.. Wai sakina arniya ta dauko wai ita zata renanmim da,dan Allah momma ki rike adil agurinki nasan bazaki gazaba"Ai da sauri Hajiya ta sauko daga kan gado tana fadin"Ar....Me lalle sakina yar tasha ce yanxu haka ta raina mutane to wlh billahil azim sai tabar gidannan bazan zauna da kedara ba agidannan ba wlh"Tana fadar haka tabi bayan Dr safwan tafice fuu.
Yana kokarin shiga mota yaga ta shige sashensa,kada kai kawai yayi ya shige mota yabata wuta don ahalin dayake ciki baida lokacin hajiya mama.
Shazeey taga bala"i domin hajiya mama tadunga mata watsii da kaya bayan tagama tasa yan aikin Sakina sujata sufitar da ita dagan gidan,fadi take"kuja shegiya kafurar banza agidan nan wlh baki isa kizauna ki koyamana kafurci ba kuja shegiya naceπ€£π€£π€£sukuwa suna janta tana kuka tana rokon hajiya mama tana fadin"Madam plz help me....Srrry ho..."sorin uwarki inkika kara kirana madam sai kinci ubanki"waje suka watsata sai da kanta yabugu da kasa da sauri tace"jesus ai da wani gudu Hajiya tabita tana fadin"mun shiga uku zata konamu jejesas din babankiπ agidannan,Ai da gudu shazeey ta rarimi kayanta megadi yabude mata get tayi waje,Hajiya tace"tsinanniya kawai da ki tsaya dasaina na fasa katon kanki kamar na kwakwaπ€£π€£π€£π€£kowa na kunshe dariyarsa sabida in Hajiya taganka wlh sai kasani.
.Momma tana gani ammh batayi mgana ba saboda sanin halin hajiya yanzunan ta dawo kanta Ranar hajiya wuni tayi tsinema sakina da uwarta daga karshe akace"ai ba shegen d'a irin sufiyanu sai da na hanasa daukoma yarinyannan saboda nasan arina ko ganin uwarta kamar wata tsohuwar kilaki amma dayake kunnen
kashi gareshi ya kwasomana bala'i har gida,daga baya kuma aka hau share hawaye tana fadin"Allah ya jikanka salisu dakana nan a raye dabai auromana tsinanniyan yar"nan baπ€£π€£π€£π€£Haka hajiya ta wuni ashar.
*Hoho sakina kinga ta kanki tunda Hajiya mama ta tsaneki*πππ
0 comments:
Post a Comment