Zaune ya iske su suna mgana yayi sallama suka amsa ya cire takalmi ya kariso ciki kusa da Momma ya zauna yana gaisheta ta amsa tana mika masa Adil Haj.Mama dake kan kujera zaune tayi gyaran murya tace"Mgnar dana ce zamuyi mganace data shafemu dukkanmu shiyasa naga yakamata na taraku mu tattauna
Kai Sufiyanu mganar duk akankane yadago yana kallonta bai yi ba mgana tacigaba da cewa"kwarai da gaske ni wacece agareka? tafada tana kallonsa Da sigar tambaya cikin daure kai yace"ke kakatace wacce ta haifi mahaifina ammh hajiya mai yakawo wannan m....."Daga masa hannu tayi kan tace tana kallon momma"Na isa in zartar da hukunci a gidan nan"momma tace"haba hajiya ai dani da babana a karkashin ikon ki muke...Kifadi bukatarki umarni kawai zaki bada insha Allahu zaki samemu masu biyayyah".
Haj.Mama ta rausayar dakai cikin farinciki tace"Masha Allahu naji dadi dama nasanki Hadiza bazan samu mtsala dake ba,zuwana Safana dalinlinkane Sufiyanu"Ta fada tana kallonshi shima dagowa yayi yana kallonta kan yayi mgana ta rigasa dacewa"Matarka tafadamun mganar daya zaburar dani na farka daga barcin daya kwasheni,na tabbata in sakina tafi karfin iyayenta da mijinta to mu danmu bai fi karfin mu ba"
tayi shuru kan taci gaba da cewa"Naje da Niyyar Neman Aure ne"Arazane Dr Safwan yadago yana fadin"Neman aure kuma hajiya"yafada da sigar maimaitawa Haj.Mama tamike tsaye tace"Kwarai kuma sai kayi sa'a gidan dattako,ne daga Neman aure kuma aka Dauro Aure"Ras gaban Dr Safwan ya buga momma tace cikin mamaki"aure...Kina Nufin yanzu Babana mata biyu garesa kenan"Haj.Mama tace"ya wuce wai Hadiza ina fatan wannan aure shi zai kawo chanji arayuwar yaron nan" Nan tashiga labarta musu daga farko har karshen abunda ya Faru takareshe da cewa"Ka shirya ranar sati Attahiru ya raka ka kaje ku ga juna ina so ayi ayi tatare ne cikin lokaci"tafada da bada umarni.
Ajiyar zuciya momma ta sauke tana kallon Dr Safwan dayake kallon Hajiya cikin al"ajabi na abunda take Fada cikin sanyin murya yace"Hajiya wannan tatsuniyace ko kuwa dai wasan da kika sabane"Harara ta zabgamai kan tace"kai ashe shashashane ban sani ba ana nema maka mafita da yanci ammh kana sakarci ko"to babu wasa matarka SAFINA ta na chan tana jiranka"zai sake mgana Momma ta girgiza masa kai tayi saurin cewa"Alhamdulillah...Hajiya Allah ubangiji ya sa alkhairi aka kullah....Nasan Safina yarinyar kirkice kwarai matuka"
Haj.Mama tawashe baki tace"kwarai da gaske Safina itace daidai da tsarin Rayuwarka,ayanzu haka tana chan ibadan ita ta wakilci jahar su ta zamfara a gasar alqur'ani ta kasa gabadaya"Momma ta washe baki tace"Kai hajiya alkhairi ya shigomana gida wlh....Allah yasa mu amfana da ilimin nata"hajiya ta amsa da Amin
Dr Safwan mutuwar zaune yayi yashiga rudu gani yake kamar amafarki wai ya sake auren wata bayan Sakina abunda bai taba zato ba ko a mafarki baida sha'awar auren mace fiye da daya to dayanma ya yakare da ita balle har yayi Tunanin kari,Haj.Mama ta katsemai Tunani dacewa"baka ce komai ba,ko bakayi murna da alheri dana maka bane"cikin sanyin murya yace'na isa Hajiya...Allah yasaka da alheri"ta amsa cikin Farinciki dacewa"ko kaifa dan Albarka,Allah yama rayuwarka Albarka ya Sanya Safina abokiyar zamankace"momma ta amsa da Amin mika maka mata Adil yayi kan ya mike ya musu sai da Safe.
Asanyaye ya isa shashensu kai tsaye bedroom din shi ya shiga kan royal bed din dayaji kayataccen zanin gado,yafada zubewa yayi yana sauke Numfashi yakurama saman dakin ido yana tunanin makomar Rayuwarsa basan dawani ido zai kalli wata mace amatsayin matarshi ba,bawai don yana matukar son sakina ba a"a sai dan gasamasa aya Ahannu da Sakina tayi shiyasa ya cire kowacce mace a lissafi bai ko tunanin kallo mata mace da sunan kallo sha'awa duk halinsu daya yake gani yadade kwance kan ya yunkura yafada toilet,yayo wanka ya dauro al"awala yazo yagabatar da Nafila yadade yana addu',oi kafin ya koma ya kwanta wanda har barci ya kwasheshi bai tantance wani hali yake ciki ba shi dai ba haushi yake ji ba kuma ba murna yakeyi ba
Asuba tagari Dr S S Safana
_*TEAM SAFINA_π
_*TEAM SAKINAπ_
commet
and
share
*Janaf*✍
π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀
*NA TAFKA KUSKURE!!*
ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀
*NA*
*Janaf ce*✍✍
DEDICATED TO *My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*
I so much luvs u my mommaππ
*INTERLLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*{onward together}*
*{we give the the Reader's of ours the best out of the bests,,,Our inks are melodious and dropping a kinda light to reader's}*""""
*THE PEN OF LOVE*π
*HEART OF TOUCHING*❤ *TEARS OF SORROWS*π *CURDLES*π, *GIGGLES*π, *AND MARRIEGE THINKS*π
*JUST GIVES US A FOLLOW*✔
_wow....I so much happy wlh kunga ruwan commet bansan haka na tafka kuskure keda dimbin masoya ba sai jiya..I make sure baku yi Danasani ba tanque so much bbys for u lov support and care_
ππππππ
_*Hohoho ur Durling Safeena Aliyu zurmi tace karkuji komai,kawai ku bata lokaci tayi alkwarin chanza Rayuwar Dr S S Safana....iz juz d begining guyzs*_
*14*
----Koda garin Allah yawaye har saida Dr Safwan ya makara kafin ya tashi shima Dr Tahir ne ya ishesa da kiran kan ankawo musu emergency ,yayi mamakin barcin daya sha wanda rabonsa da irinshi wlh bazai iya tunawaba( lalle Safeena ke haskece arayuwar Dr S S Safana)cikin gaggawa yayi wanka ya shirya cikin suit masu rowan toka samfarin DKNY agurguje ya shiga shashen su momma ya musu sallama suka rakasa da sa albarka.
wata matace aka kawo zata haifi yan uku to biyu sun danne daya kuma suna kokarin turo kai atare gashi karfin uwar yafara karewa zuwan Dr Safwan cikin kwarewa da taimakon Allah ta haifi yaranta cikin salama da kwanciyar Hankali yan"uwan matan sun matukar jinjinama Dr Safwan ganin yadda tun dazu likitoci ke kara kaina akanta bata haihu ba ammh yana zuwa cikin mintin da bai gaza gomaba ta haihu hakika sun yaba da jajircewa irinta Dr Safwan Sale Safana wanda har sai da suka Furtamai.
Aranar Dr Safwan ya wuni aiki a asibiti operation uku yayi duk agajiye yake komawarsa office ya bude karamin fridge din dake office din ya ciro ruwan faro ya kafa kai sai daya sha fiye da Rabi kana ya ijiye kan kujeran office din yafada yana maida Numfashi.
Dr Tahir ne ya turo kofar office ya shigo ya kariso yana kallon Dr Safwan dake kwance idanunsa a lumshe duk da yasan ba barci yake yi ba file din daya shigo dashi ya ijiye kan yace"Dr Safana wai meke Faruwa ne yaudin nan naganka kana wani annushuwane"Dr Safwan yanajinsa yayi masa shuru sai chan yace"Kai fa mugun dan sa"ido ne wlh Tahir"Yafada still bai bude ido ba.
Dr Tahir ya kyalkyace da dariya kan yace"My man...ai indai kaine to momma ce kawai zata Fini saninka common gist me "Mirmishi Dr Safwan yayi kan ya Mike Zaune yana Fadin"Zan yi gisting dinka ammh ba yanzu ba but it only i know yau ina jin yanayi yana canzawa i dont know may be wani abu something zai Faru dani ne"Dr Tahir yayi galala yana kallonsa cikin farinciki kafin yace"Ko dana ji Dr Safana Dan Allah shafamin nasan komiye yasakaka Annuri yau iz sometin special".
Mikewa Dr Safwan yayi kan ya isa kan teburin dayama office din kwanya yana Fadin"Tsiyana dakai wutar ciki,ba ni nace ba"yafada yana kallonsa tare da dagemai gira guda daya Dr Tahir yace"Sure my Dr nakosa ne"Dr Safwan ya zari wani fayal yana wucewa yace"Nafasa kasan ban san damu"Da sauri yace"Srry..Nadaina damunka but karkajamin rai"Tsaki Dr Safwan yaja kan yace"in kafito ka rufemin office din Aku"Dariya dr Tahir yayi kan yace"Bakomai indai za"a bani lbr,daga haka ya fada toilet din office din shikuma Dr Safwan ya Fice.
Hmmm Su Dr Safwan tun yanzu tunma baku hadu da Safinar ba kafara zakewaπ€π€π€π€
*************************
*ZURMI*
---Masha Allahu kwanansu Safeena hudu suka dawo jaharsu ayayinda jahar Zamfara tazo na biyu,Hakika Safeena ta godema Allah dayasa iyayenta suka tsaya akanta tasamu limi yau dalilin ilimi tasamu kujerar makka harda motar hawa golf da zunzuruntun kudi har dubu dar biyar tayi kuka,kukan Farinciki da zamowarta wurin dabakowa ke takowa ba sai wanda Allah yabama limi da basira,haka suka dawo cikin Farin ciki kudi dai mkrantansu ta mallakamawa kujerar makka kuma Abbanta ayayinda motar tace Abbanta yabada adinga mishi haya,Hakika Ummi taga Ranar Haihuwa domin makota da yan"uwa da abokan arzika sai shigowa suke tayasu murna,suna cikin amsan baki shyasa Abbah bai samu kebewa da Safeena ba sai da tadawo da kwana uku kana.
Cikin dakinshi yakirata bayan ya yi godiya ga Allah subuhanahu wata'ala daya azurtasa da samun ya irita,yayi mata Nasiha mai kashe jiki har sai da ta Fitar da kwallah kan ya gangaro kan zence yace'Safeena kinsan dai bazan cutar dake bako"Yafada yana kallonta gyada kai tayi kawai jikinta yagama Sanyi fatanta Allah yasa bawani abu yafaru ba bayan batanan ba.
Yacigaba da cewa"to duk abunda zan Fada miki ki daukesa matsayin kaddara..Kina gabda tafiya gasar nan na daura miki aure"Dam!dam!gabam Safina ya buga tadago da sauri cikin Rawar murya tace'Aure kuma Abbah'kai tsaye yace'Kwarai Safina...Na daura miki aure sati biyu da suka wuce da jikan Hajiyar Safana"yafada yana ciro sadakinta ya kama Hannunta ya Damkamata,Safina taji hawaye ya wanke mata Fuska tana so tayi mgana ammh kuka yaci karfinta mallam Aliyu ya kalleta yaji tsausayinta ya tsirgamasa yace cikin taushin murya"karki ce komai yata Allah yayi miki albarka Safina Ubangiji ya jibanci lamarinki yakuma zaunar dake lafiya agidan aurenki"yafada yana kauda kai kwallah tataru a idanunsa,Safina tayi karfin halin cewa"Hakika Abbah kai yafi chanchanta daka zabamin mijin daya dace dani,na karbi auren nan hannu bibbiyu sai dai ina rokonka dan Allah Abbah kutayani da addu'a Allah ya bani juriya da hakuri"takareshe fada tana kara tsananta kukanta Abbah yace"tashi kije yar albarka da izinin lahi bazaki tabe ba Safina"cikin sanyi ta mike rike da kudin tace" Abbah karike kudin"girgiza kai yayi kan yace"A'a Safeena Hakkinki ne ki mikama Ummanki ta adana miki kan muji daga mijin naki.Kada kai tayi kan tafice tana sharan hawaye.Runtse ido Abbah yayi yanaji har aransa bai kyauta ba sam.
Commet
And
Share
*Janaf*✍
π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀
*NA TAFKA KUSKURE!!*
ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀
*NA*
*Janaf ce*✍✍
DEDICATED TO *My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*
I so much luvs u my mommaππ
*INTERLLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*{onward together}*
*{we give the the Reader's of ours the best out of the bests,,,Our inks are melodious and dropping a kinda light to reader's}*""""
*THE PEN OF LOVE*π
*HEART OF TOUCHING*❤ *TEARS OF SORROWS*π *CURDLES*π, *GIGGLES*π, *AND MARRIEGE THINKS*π
*JUST GIVES US A FOLLOW*✔
_i dedicated dis page to u INTERLLIGENT WRITER'S ASSOCIATION Soyayyarku agareni mai girmace,karku damu kowani bugawan numfashina kuna raina janaf namuku son so_
πππππππ
*16*
••••••Ranar lahadi tun Safe Dr tahir yayi ma Dr Safwan sammako,Shima Dr din yasan Halin Tahir din da wutar ciki dat why ya shirYa da wuri,Dama gashi jiya da daddare kwana sakina tayi bala'i haka kawai yana Zaune adakinsa yana wani aiki a laptop dinsa ta shigo ta sameshi tace tana son mgana dashi don Sakina bata da kunya wai tafaramai complain yana wulakantata yadaina kulata kana yadaina bata Hakkinta na Aure abun haushi abun takaichi yaji wani bakinciki yayimin shar arai yaso yamata mgama ammh sai ya tuna Neman shiri take shikuwa yayi alkwari nuna ma Sakina shi cikakken Namiji ne _yauwa Namijina_
Kwashe laptop dinsa yayi ya fice ya barmata daki dayan bedroom din ya shige dayake 3 bedroom ne yasaka key cos yasanta yar hayaniyace sai ta samai ciwon kai,aikuwa taita bala'i hartana Fadin dole dai Azauna da ita don babu yadda aka iya da'ita mirmishi yayi aransa yana auna girman rainin da Sakina tayimin lalle kuwa tayi kuskure inhar take Tunanin tafi karfin shi ne kawai kyaleta yakeyi cos darajar mahaifinta ammh shi tuni tagama Siremai da munanan halayyanta shifa baida darajar da Sakina zata fita tafadamai sai dai yazo yaga bata baida kimar da zatayimai abinci balle sauran abunda ba'a rasa ba, ji bi yadda Adil yarasa gatan ta ammh ko ajikinta ko nono sai tagama dama in momma ta roketa ta bashi,to har wannan macece,shiyasa yadau ma kansa Nuna mata _*TA TAFKA KUSKURE*
Ciki Wata shadda gezner deep blue ya shirya jamface zanna bukar ce bisa kansa itama da zaren blue akayita takalmin kafansa rufaffene na fatar Damisa,baki yafeshe jikinsa da turarensa Azzaro visit Kansa yadau gyara abunka ka mai kyau sai yafito yabada wani sirrin kyau wanda ba kowa ke ganewa ba sai wanda akayi dominshi.
Ko takan Sakina bai bi tana dakinta ta kwana da takaichin wulakancin Da Dr Safwan yamata kuma tayi alkwari kafin ya Fita sai yagayamata meye matsayinta agidan dayakemata halin ko inkula _Topha lalle Sakina kunya bai ishe ki ba_π€
Sashen Momma ya tarar Da Dr Tahir shima ya Shirya cikin shadda fara wagambari shima cikin dikin muhammd shima zannah bukar din yadora kafarsa shima cikin sawu ciki bakake Sororo yayi yana kallonsa tun shigowarsa momma Dake zaune gefe ita ta tsurama danta ido tana kallon yadda danta yau yake Fitar dawani hasken Annuri na dabam Haj.Mama dake tsaye gefe tasaki guda" Ayyiriri.....!!!!Masha Allahu Safiyanu lalle kanunamin kai jinin justice Habule.ne
Dr Safwan yayi mirmishi kan ya karisa ya duka yana gaida momma ta amsa tana Dafa kansa tace cikin farinciki"Babana nadade ban ganka cikin Annuri irin na yau ba'sunkuyar dakai yayi kan yace"Momma...Bbu komai wlh'tace"unhum...Fadamin gaskiya ko duk murnan zuwa ganin surukar tawace"tafada tana dago kansa da hannunta,Mirmishi kawai yamata baice komai ba domin shima mamakin farincikin daya tsinci kansa yakeyi ayau din.
Adil dake Hannun Dr Tahir ya amsa yana cillasa sama yana Fadin"Bawan Allah damo sarki hakuri...Zaka bini ne"yafada kamar yana jinsa Haj.Mama tace"Bawan Allah yakusa samin uwata gari ba wacce tambadaddiyar ba"Tafada tana nuna shashenta da Baki Dr Tahir"Yayi dariya yace"Allah barmana Hajiyarmu"Tace"eh...Kona ga karshen tazurancinka ba" tafada harda mele masa baki,dariya yayi kan yace"Haba Hajiyarmu verry soon za'ayi"tace"kai kasan wani vari san ince dai ba zagina kayi baπππYace yana Rike baki"Wane ni Tahir"tace"Au na'aza zagina kayi wlh in ci ubanka domin ni ban yadda da wannan gwarancin naku ba"Tafada tana harare harare dariya sukayi gabadayansu
Har wurin mota suka rakosu Haj.Mama na jaddadamusu cewa su fara bi Safana Iyami ta hadasu da wanda zai kaisu zurmin kar suje su bace ko yan kiddappers su sace suππ.
Koda tara tayi suna Safana dayake da benz din Dr akayi Tafiyan sai da suka fara biyawa gun kawu bala suka gaishesu yayi murna da ganin Dr yayi mai Nasiha sosai kan yarike wannan aure da hannu bibbiyu saboda yarinyace data Fito yar babba gida,Jikinsu yayi Sanyi da Nasihar kawu kuma daman shi baija da wannan aure cos har aransa baiji Haushi ba saima wani Annushuwa.
Iyami sai dai taga su Dr Safwan kwatsam taita ina tasaka dasu basu wani jima ba tahadasu da dan kishiyarta manu tace yakaisu gashi anyi ta neman mallam Aliyu awaya Afadamai ba'a sameshi ba gashi ita Ummi bata da waya balle Safina.
Karfe10:30 suka Dau hanyar Zamfara sai muyi Fatan isarsu lafiya.
•••••••••••••••••
*ZURMI*
Yau tun Safe Safeena taji gabanta na Faduwa bata kawo komai ba tayi addu'a taci gaba da sabgoginta,tana kammallah aiyikanta tayi wanka ta shirya cikin bakar doguwar riga da farin hijabinta har kasa da safa ta daura Nikabinta ta Fito tana Ma Ummi sallama kan zata ta Duba Aisha bata jin dadi Ummi tamata adawo lafiya.saboda taji dakyar Abbanta yabarta fita dan tunda tadawo bata sake fita ko'ina ba saboda akwai Hakkin wani akanta.
Tafita badadewa Ummi tana bakin kichen tana tsinkan zogale domin shi yau mallam yace yana sha'awa wato tuwo shinkafa miyar zogale kawai taga Manu ya fado da gudu manu dai bazai wuce shekara tara aduniya ba sa'an Usman ne Ummi ta saki tsigan zogale tana Fadin"Kai Manu daga ina? kuma kai dawane? ajere ta jefamai tambayoyin haki yakeyi kan yace'goggo Iyami ce tace na kawo wasu baki"Ummi tace"Baki..Kuma"Ta maimata da sigar tambaya.
Manu yace'eh...Tace mijim yaya Safeena ne"Ummi ta mike dafe da kirji tace mijin wa"tafada tana zaro ido yace"Mijin Yaya Safeena tace"Ummi tayi daki da Sauri tana fadin"na shiga Uku ni zainabu zuwa ba shiriππUmmi ta rude taji zuwan siriki.
Hijabi ta yaya tasanya kan tajawo tabarma ta Shimfida kan shararran simintin dake tsakar gidan tana Fadin",Maza manu ce su shigo.Yako ruga da gudu ya fice yana murna yasha dadin mota.
Suna tsaye ajikin motar Dr Safwan yana bin dan gidan su Safeena da kallo aransa yana fadin"wai daman akwai masu rayuwa a irin gidan nan" _Tab...Lallenema Dr to dankai kana gida mai kyau sai yazamana kowama hakane_
Shiko Dr Tahir anguwan yake bi da kallo dagani dai anguwan ta masu rufin asiri ce ba'a fadi dayan ba kofar gidansu Safeenar agyare tsaf dashi aransa yace"Tab....Nan gidan kuma Hajiya mama takawomu" _Kaniyarka Tahir Gidansu Safeenar kake zagewa_π
Suna zencen zucci ne manu yafito da gudu yana fadin"ance ku shigo"Dr Tahir yakalli D Safwan yace"to bismillah...Kaine maigidan aie"yafada yana dariya kasa kasa Harara ya wurgamasa kafin ya wuce ya rufamasa baya da sallama suka shiga abakinsu Ummi dake kofar daki ta amsa kanta na kasa tana masu maraba dukkansu zubewa sukayi suna kwasan gaisuwa Ummi ta amsa tana tambayan su Hajiya Dr Tahir ya amsa da "Suna gaisheku"
Shuru ya biyo baya Ummi kunya yahanata daga kai shikuma Dr Safwan tagefen ido yake bin gidan da kallon duk da dai talakawane ammh suna da tsafta ko'ina ashare shima Dr Tahir hakane ammh aransa fadi yake"Kar dai ace Wannan babar itace Safeenarπππ,cikin kunya Ummi tace"Ku zauna kan tabarma bari insa asiyo muku ruwan sanyu' ciccire takalma Sukayi suka zazzauna kai aduke Dr Tahir sai dariya yakema Dr Safwan kasakasa shikuwa yanajinsa yama sa banza.
Ummi ta shga daki takwalama Manu kira yazo tabashi kudi tana fadin"Kasan gidan su Gaddafi ya amsa da eh tace to maza hanzarta kaje yaya Safeena na gidan kace ta yi hanzari tadawo inzaka dawo ka biya shagon basiru kasiyo min ruwan gora guda biyu.
Commet
And
Share
*Janaf*✍
π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀
*NA TAFKA KUSKURE!!*
ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀
*NA*
*Janaf ce*✍✍
DEDICATED TO *My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*
I so much luvs u my mommaππ
*INTERLLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*{onward together}*
*{we give the the Reader's of ours the best out of the bests,,,Our inks are melodious and dropping a kinda light to reader's}*""""
*THE PEN OF LOVE*π
*HEART OF TOUCHING*❤ *TEARS OF SORROWS*π *CURDLES*π, *GIGGLES*π, *AND MARRIEGE THINKS*π
*JUST GIVES US A FOLLOW*✔
_*chai chai chai wlh commet dinku Anty sainah,my sahiba and my lovel esha ,yana sumar dani over ina rokon Allah ya iya muku abunda kuka gaza janaf na muku son kauna*_
*17*
****Yako zura da gudu ya fita Ummi tace'oh ni Zainabu Allah dai yakai lpy,gashi tana so tamusu bayanin Safeenar tadan fita zuwa gaida kawarta,ammh kunya ya hanata uwa uba tana son komawa kichen domin tadora miya aranta tace bari Safeenar ta shigo su dawo daki inba haka ba Takurani zasuyi oh ni Ummi kunyaπ€
Manu kuwa da gudu ya shiga gidansu Aisha mamansu Aisha tace'kai daga ina"yace"Ummi ce tace Yaya Safeena tazo yanzu"Maman Aisha tace"Tom gatanan zuwa kara fice yayi yanufi shago siyan ruwa,itakuwa maman Aisha lekawa tayi dakin da su Aishan ke ciki tace"To iyayan daka kufito kusha iska ke Safeena Ummi ta aiko kije yanzu"Safeena ta mike da sauri tana Fadin"To lafiya...Dan Ummi bata taba aikomin ba"Maman Aisha tace"Nima dai..Ki hanzarta komeye mai mahimmacine kam"Hijabinta ta sanya saboda sauri Nikabin ahannu ta rikoshi.
Tana tafe ahanya tana zencen zucci Allah yasa lafiya domin yadda gabanta ke faduwa tun safe nan da nan ta kawo dayake babu tazara taga mota akofar gidansu ammh ko alama bata kawo gidansu tazo ba tasan dai bawani mai zuwa amota balle tasa rai _Allah sarki Safeena to yau gashi mai motarma mallakinkine_
Da siririyar muryanta tayi sallama tasawo kai cikin gidan,kanta na duke shiyaasa bata lura dasu ba ammh kamshin Turaren Dr Safwan ya cika tsakar gidan,da hadaddun takalman tafara cin karo binsu da kallo take cikin Mamaki,har zuwa mamallakan takalmi idonta yafara Sauka kan wani hadadden Namiji fari mai cikar zati da kamala da haiba mai dauke da doguwar fuskar sajensa ya zagayen bakinsa wanda yakaramasa kwarjini hakiki Allah yayi Halitta Anan gurin sai akayi sa'a tun lokacin da Dr Safwan yaji muryan Safeena cikin sanyi da natsuwa tayi sallama yaji muryan tadakesa yayi saurin dagowa ya zuramata ido yana binta da kallo daga sama har kasa yakasa dauke idanunsa daga kanta duk da babu abunda zai dora da kamanninta ammh zuciyarsa da gangar jikinsa sun Fada masa cewa wanna ce _*SAFEENARSA_ kaji Dr S S Safana wai Safeenarsaπ€
lokacin da idanuwansu suka hadu wani marganet ne yajasu dukkansu Safeena ta tsinci kanta awani yanayi na mutuwar jiki da sauri ta sadda kanta kasa jikinta ya cigaba da rawa kafafunta Sun kasa daukanta Dr Tahir ne yayi gyaran murya saboda yaga yadda Safinar ke gabda faduwa.
Waskewa Dr Safwan yayi yacigaba da latsa wayarsa ammh zuciyarsa na fat Fat kamar wanda yayi gudun famfalakiπππDrTahir yayi karfin halin cewa"kari so mana malama Safeena"cikin rashin kuzari Safeena tadaga kafa ta karisa sai data danganta da kofar dakin Ummi kana tace cikin rawar murya"Sa....sannunku da....Da zuwa"Yauwa Sannu Dr Tahir ya bata amsa yana kara kallonta yadda Hijabin yake wani zumbudede dashi harda Safa duk da kanta na duke adan kallon dayamata yafahimci yarinta karara atare da ita.
Tana cewa haka tafada daki da gudu tana Haki Ummi tayi Saurin mikewa tajawo hannunta suka shige kuryan daki tace"Safeenar mijinkine fa suka zo"sororo Safeena tayi gabanta na tsananta Faduwa tace"mi...Mi...Mijina kuma Ummi"Ummi tace"Eh....Nima kwatsam na gansu kinga bbu lokaci na aiki Manu siyo ruwa shuru bai dawo ba bari ni in je ji da abinci da za"a musu,kekuma ki koma gurinsu"Safeena tace"Ammh..Ummi"Ke wai wata irin shashashace ko bakiji menace miki bane,"Ummi tafada ranta ya baci"Safeena tace"yi Hakuri Ummi zanyi yadda kikace daga haka tafice tayi tsaye afalo hannunta dafe da kirji tanajin zuciyarta nawani harbawa.
Sukuwa tana shigewa Dr Tahir ya zunguri Dr Safwan yana Fadin"Kai mijin malama kako ga malamartaka i think fa itace Safeenar"Banza dashi Dr Safwan yamai sai dannan wayansa yakeyi,ganin haka yasa Dr Tahir kama kansa agurguje Safeena tadan kara gyara falon ta shimfida musu darduma kan ledar dake tsakar dakin,cikin sanyin jiki ta leko da kanta tace"ku shigo ciki kuna zaune awaje"Dr Tahir yace"a"a ayi Haka ranki yadade"mirmishi tayi kawai atare suka mike Dr Tahir ne yafara shiga da sallama kana Dr Safwan wanda Safeena ke tsaye akofar dakin har yanzu suka zauna,ita dai Safina kanta aduke takasa motsi Dr Tahir yazauna yana Fadin"Masha Allahu..Amarya baki tambayi wanene angon naki ba"yafada yana kallon Dr Safwan dashima yawani sadda kai
Wuf ta fice tana Rufe fuska dukkansu suka bita da kallo Safwan yanajin wani iri aransa kunya tab to shi ina ma Sakina takeda kunya balle ayi mgana taji kunya,mirmishin gefen baki yayi yana bin inda tabi da kallo.Dr Tahir sai kallonshi yake yana mai dariya kasa kasa.
Ummi ta fito itama cikin kunya suka kara gaisawa kana tafice ta tararda Safeena zaune a kichen tayi tagumi Ummi ta kalleta tace"Ke kam Allah yayi miki Sauki...'Safeena tayi saurin mikewa tana rufe fuskar Ummi tayi dariya kan tace"Allah ya shiryeki..Kinga nifa tuwon shinkafa nakeyi miyar zogale ya kike gani za'a sake yi musu wani ne"Safeena tace"Ki barshi Ummi wlh sai kiga sunfi son tuwon ma "Ummi tace"ok sai na namusu zobe maza ki koma gurinsu niban ma gane surikin nawa ba duka yaran masha Allah.
Ummi tafada tana dariya mirmishi Safeena tayi kan tafice tana fita manu yakawo ruwan swan din guda biyu ta amsa ta sanya cikin faranti tahado da kofuna da sallama tashiga suka amsa,ta durkusa ta ijiye Tahir na mata sannu da aiki yadauki kofi tana tsiyaya musu Dr Safwan yana kallon ta ta wutsiyar idanunsa aransa yana jinjinama Hajiya mama ita aganinta wanna ficilar yarinya ne zata iya dauke Nauyinshi tab shi atunaninshi duk randa ya haikemata zata iya Mutuwa _see dis guy to ka gwadane_π€
Gefe takoma bayan ta zuba musu ta zaune akasa kanta a duke tana wasa da yatsun hannunta kowani dakika na mintina zuciyarta na bugawa,Dr Tahir yasha ruwa yana fadin"Munsha ruwan Amarya.."Yafada yana mirmishi kan ya cigaba da cewa"an dawo lpy kuma nanawa aka ciyo mana"ta gefen ido take kallon Tahir kan tace cikin sanyin muryanta"Na biyu nayi...Lafiya kalau"Yace"Wow..Masha Allahu lallai kin cika Hafiza"Mirmishi kawai tayi Tahir ne keta janta da mgana tana bashi amsa da umh a"a shikuwa Dr Safwan yana ta danne danne awayarsa ammh hankalinshi kaf akansu yake lokaci kankani yaji yarinyar ta burgesa yadda takeda aji da kamun kai.
Mikewa DR Tahir yayi yana Fadin"Bari na baku guri ku zanta.."yafada yana ficewa Safwan yarakasa da Harara,yana waigowa karaf suka hada ido tayi saurin sadda kai kasa mirmishi yayi yasamu kansa da kuramata ido kur yana kallonta jikinta yabata ana kallonta tana dagowa idanunwansu suka sarke ma juna,wani miracle ne ke aiki atare dasu kamar ansa super glue an manne musu sun kasa daina kallon juna.
Safeena taji jikinta na saki da wannan azababban kalon da Dr Safwan ke binta dashi ita tayi saurin jaye idanunta saboda bazata jure wannan kallon daga Dr ba,jikinta yana rawa takara dukar dakai tana kara jin bugawar zuciya.
Dr Safwan kawai yaji yasamu kansa da cewa"An dawo lafiya...Allah yasa albarka"cikin husky vioce dinsa ya furta haka tadago tana kallonsa aranta tana fadin"So sweet.."Tace"Alhamdulillah nagode..Daganan shuru ya biyo baya Ammh lokaci bayan lokaci suna satan kallon juna,sai suyi mirmishi atare.
Shikuwa D Tahir yana chan yatasa Ummi da hira ita kuwa haka takeso mutum mara bakunta tana bashi lbrin amintar Haj.Mama da iyami shikuwa yanata jinjina girman Amintansu.
Abun Mamaki saiga Dr Safwan yana abunda bai sababa wato mgana sai gashi wai Safeena Ta chanzashi da surutu yana tambayanta kan matakin karatunta tundaga na boko har na arabi yayi mamaki na yadda karamar yarinya kamar Safeena take da ilimin sanin littafan addini haka gaskiya ya jinjinama iyayanta matuka,tadan Sake dashi sama sama ammh ita aranta mamaki take wai yau itace ta mallaki miji iri Dr Safwan miji na Nuna sa'a wanda ko wacce mace take fata ta mallaka amtsayin miji duk ko takamarta da nasabarta da ikonta kallon daya zatamai taji ta raina kanta da duk abunda ta mallaka kuwa.
salla kawai ke tadasu.
Tabbas su Tahir basu Nuna bakunta ba suka zage suka ci tuwonsu Dr Safwan yaji dadin cimar saboda abincinsa duk miyar da akayita da ganye masoyiyarsa ce ga lafiyayyah zobonsu wanda tas suka shanye suna hamdala da wannan gidan irin albarka,saboda dadin Hira basu ankara ba sai da Tahir yaga shida Saura yaleka su Safeena yana cewa"plz amarya ama na hakuri hakanan kada muyi dare a hanya"Safeena tayi yar dariya tace"To ni na rikesa"Dr Tahir yace"kece mana to inbake ba To waye"Yafada yana kallonta hannu tasa ta rufe fuskarta Dr Safwan ya tsuramata ido yanajin wani shauki na dibansa domin wannan sa hannun datake tana rufe fuska shike burgesa yakesamasa shauki wanda yarasa ko na menene.
Minti biyar minti goma shuru D Safwan yaki fitowa yana chan kawai ya zurama Safeena ido yana kallonta so yake ya fahimci wani yanayi yake tsintar kansa in yana kallonta ammh yagaza fahimta sam,dakyar ya yakice abunda yakeji ya mike yana kallonta yace"to madam mukam munyi harama"Da wutsiyar ido ta kallesa kan tace"daman ba kwana zakuyi ba"tafada da wani salo wanda ita batama san ta iya ba,mirmishi yayi kawai yana kallonta kasa mikewa tayi saboda idon daya zuramata yana kallonta yana wani shafa sajensa yana cizan lebensa na kasa yunkurawa tayi tamike tayi gaba tana Fadin"Allah yammh tayi kUkoma kaduna yanzu"tafada tana isa kofar dakin da sauri ya isa ya cimmata tana kokarin fita ya bangaji kafardarta atare sukaji wani shock kamar wuta yaja su dagowa tayi tana kallonsa kawai sai yasamu kansa da dagamata gira daya yanajin wani farinciki na shigarsa,sunkuyar dakai tayi ta fice da sauri.Akasalance ya fito yana ma Ummi sallama.
Ummi tace"A"a Tahir dare bai yi ba yanzu fa za'a kira magarib'Dr Safwan yace"Babu komai Ummi mun Aiyuka gobe asibitine infact ma bamuyi shirin kwana ba"Safeena dake gefe tsaye jikinta duk yayi sanyi yanzu shikenan mr handsome zai tafi ya barta _topha safeena har Dr Safwan din yazama mr handsome_π
Ana haka saiga Abba yayo sallama yashigo hannunsa rike da manu da usman ummi tace"Shikenan ma ga Abbanta nan yadawo, Ummi tanamai Sannu da zuwa tana fadin"Allah yasa zaku hadu mijin Safeena ne sukazo shine wai yanzu zasu tafi"Abbah ya kariso yana fadin"Masha Allah...Sannunku da zuwa' zubewa sukayi suna kwaasan gaisuwa ya amsa yana tambayansu yasuka barosu suka ce suna gaishesu.
.Abbah yace"to masha Allahu...Ammh dai zaku fasa tafiyarnan dan magariba ma ake kira'Dr safwan zaiyi mgana Dr Tahir yayi saurin cewa"Toh Abbah matsalar bamuyi buking din gurin kwana na bane"Abbah yace'Haba dan wannan babu matsala akaba na wajema balle ku nagida kuyi sallah Safeena tarakaku nan gidan su baffanta isuhu su kwana"Ummi tace Shikenan kuwa"Abbah yace akawo musu ruwa abuta Safeena tazuba musu ta mikama kowanne tana Zuwan kan Dr Safwan sai da duka kana ta mikamasa zuru yamata domin a iya tsawon rayuwarsa Sakina bata taba bashi ruwan alwala ba balle har ta rankwafa karba yayi yana fadin"weldon..yanmatana"yafada ahankali da sauri ta wuce tana rufe fuska,tare sukayi alwala da Abbah dasu usman suka rankaya massallaci abun ya matukar burge su Safwan yadda Abbah yasake jiki dasu yana ta tambayansu aiyukansu abunda Safwan ya fahimta su Safeena talakawane ammh masu wadatar zuciya kaf da kanta har iyayenta lokaci daya yaji sun kwantamai arai,sai sukayi issha'i kana suka dawo suka dawo Safeena ta musu jallof din shinkafa da kifi sai kunun aya ta fesa wanka cikin riga da sikat tasauya hijabi humra ta shafa ajikinta tana fitar dawani sirrin kamshi Su Ummi dakin Abbah suka yada zango suka bar Su Safeena dakin Ummi.
Itama shinkafa sunci badayawa ba kunun ayan dai suka sha bil haqqi da gaskiyansuπtahir gurinsu Abbah yakoma ya bar mata da miji su kebe,to banda kallon juna suna aikin aikama juna mirmishi babu abunda sukeyi kowanne zuciyarsa tab farinciki.anan ne yake Nuna mata hoton dansa hakika kallo daya Safeena tama Adil ahoto taji yashiga aranta duk da lokacin da Ummi tafada mata yanada mata ko ajikinta ammh haduwarta da Dr sai taji dama ita kadai ta mallaki wannan hot guy dinπ€π€
sai after ten Safeena ta rakasu gidan Baba isuhu wa yake ga Abbah gidansu na gaba kadan danasu yafi Abbah abun duniya kuma yanada manya ya"ya maza dat gidansa keda dakunan kofar gida to daman dayake Abbah yamai bayani dasuka hadu a massallaci har suka gaisa da su Safwan din nan suka bar motarsu kofar gidansu safeena koda sukaje anygra musu daya daga cikin dakunan mai dauke da katifa wacce ke kasa sai sai kafet dake dakin sai toilet dakin tsaf dashi gwanin shawa'a Safeena bata wani tsayawa ba ta musu sai da Safe ammh sam Dr Safwan yaki barinta tatafi ita kadai sai da yarakata har kofar gida shima din tsayawa yayi yana kallon fuskarta cikin hasken farin wata daya haske garin..shigewa tayi gida tana masa dariya.
sai da ya koma yasamu sukunin kiran momma yake Fadamata halin da'ake ciki tayi musu fatan dawowa lafiya Haj.Mama na gefe take fadamata abunda Safwan din yacemata haj.Mama tayi tafi tace"Allahu akbar oh ni Maryamu Allah na gode maka kingani ko Hadiza yaushene safiyanu zashi wani guri har ya kwana"tafada harda rike haba kan ta cigaba dacewa"lalle Nasan yayaba da zabina kenan..Allah na godemaka.Itama momma murna take tana kara rumgume adil tanaji aranta komai yakusa zuwa karshe.
Dr Tahir yanata tsokanan Dr Safwan kin tankasa musa yayi wanka yayi yabaje a katifa daga shi sai boxer ya rumgume filo yana wani lumshe ido kamar wani tsohon maye sororo Dr Tahir ke kallonsa kan yadauki filo ya wurga akasa yana Fadin"Bari na barmaka katifan saboda tsaf cikin dare zaka ita turmusheni kazata Safeenar ce"Tunda na lura jaraba ce fal aranka.Tsaki Dr Safwan yayi kan yace"gwanda dani nasan dadin abun kai kuwa har yanzu kana kasa ne...Banza dan sa ido kawai,Dariya kawai yayi ya juyamasa baya.
Itama Safeena anata bangaren kasa barci tayi tana juye juye data juya ta rufe ido sai taga Dr yana mata wannan tsadaddan mirmishin nashi mai kashemata jiki,dataga barcin yaki zuwa tashi tayi ta dauro alwala tafara Nafila tana godema Allah daya mallakamata Dr safwan amtsayin miji aurenta.Tadade tana addu'a kafin takoma ta kwanta tana mirmishi ita kadai.
Commet
And
Share
*Janaf*✍
π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀
*NA TAFKA KUSKURE!!*
ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀
*NA*
*Janaf ce*✍✍
DEDICATED TO *My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*
I so much luvs u my mommaππ
*INTERLLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*{onward together}*
*{we give the the Reader's of ours the best out of the bests,,,Our inks are melodious and dropping a kinda light to reader's}*""""
*THE PEN OF LOVE*π
*HEART OF TOUCHING*❤ *TEARS OF SORROWS*π *CURDLES*π, *GIGGLES*π, *AND MARRIEGE THINKS*π
*JUST GIVES US A FOLLOW*✔
_18_
----- Dukkansu barcinsu rabi da rabine domin kowani dakika zuciyoyinsu suna bugawa da sunan juna,amassallaci kusa da gidan su Safeena suka yi sallah sun gaisa da Abbah sundade tare suna mgana har Dr Safwan yafadamsa zai koma ammh insha Allahu yana komawa zai tanadarma Safeena inda zata zauna sai susa lokacin da za'a ayi bikin Abbah yafadamasa kar ya takura kansa Safeena kanwa take agurinsa.
suna dawowa sukayi wanka domin yau monday tushen aiki suna da aiyuka a hospital,shiyasa Allah yasa shi Dr yana ijiye kaya amota kamar yasani dinkinsa daya amso wajen kala uku su ya dauko ya sanya daya yabama Tahir daya kafin karfe bakwai sun zama ready.
itakuwa Safeena tana idar da sallar asuba bata komaba,fita tayi ta share gida tagyara dakunan tazo ta musu abun karyawa kunun tsamiya tamusu da kosai daman tana tashi waken tafara wankewa,sai ruwan zafi wanda yaji citta da na'ana'a tashirya cikin riga da sikat na leshi milk and green kayan fiteed ne sun amsheta sun mata das da ita green din hijabinta ta tasaka,dogo har kasa ta dauki kayan akwando tama Ummi Sallama hakika Ummi taji dadin ganin yadda yarta bata Nuna wani damuwa ba duk da dai tasani aurene kawai ammh Dr Safwan ba ajin yarta bane _Abun Allah kenan_
Koda ta isa da kaya niki niki ta iske daga cikin gidan ankawomusu soyayyen arish da kwai harda kayan tea ta iske shirye ta duka har kasa tana gaishesu Tahir ne ya amsa yana dariya kan yace"Tashi mana amarya mun amsa gaisuwar aie"Shikuwa Dr Safwan tunda Safeena ta shigo kamshim humran data sa yashakeshi yarasa Natsuwarshi kallonta yake cikin wani yanayi wanda ya kasa gane kanshi Dr Tahir daya Fahimci haka ya fice ya basu wuri.
Tana nan durkushen kanta na kasa tana wasa da gefen hijabinta gaban na tsananta faduwa domim tasan wannan kallon nashi mai kadamata yayan Hanji yake mata ahankaki tadago caraf suka hada ido yana tsaye sanye cikin wani farin yadi milk mai sansti bayi da kauri tunda har ana hangan farar vest din dake jikinsa hulan kasan zannah bukar ce fuskarsa tayi fayau da ita yana furta da Annuri Kamar daren sha tara duka hannuwansa ya rumgume akirjinshi,kasa jaye idanunta tayi jitayi kamar kasa baza ta iya daukanta ba saboda wani kasala ke rufeta tsigar jikinta na tashi yarr!!!
saurin jaye idanunta tayi saboda tana gab da zubewa agurin mirmishi yayi kawai ya jawo kwandon data shigo dashi ransa yamasa dadi dayaga kunun tsamiya da kosai,masha Allahu yasha sosai kosan ma yaci sai ruwan na'ana'a shima yasha kadan ammh kowani lokaci tadago idanunsa na kanta,yana kammalawa yasa tissue yagoge baki ya mike yana fadin"Alhamdulillah...Yafada yana kallonta kai tsaye ya isa kusa da ita bata ankara ba shima ya durkusa har gwiwansu na gogan juna da Hanzari taja baya kallonta yayi kan yace'yan matana yakamata amin ramgwame naga wannan kwalliyar kan in Tafi"Yafada yanawani lumshe idanunwanshi tuni jikin Safeena yafara rawa takasa dagowa sai ma kara dunkule data keyi cikin hijabi wani yanayi keJan Safwan yayi saurin mikewa kada yabi shawaran zuciyarsa na Rumguman yar mutane.
Wayoyinsa ya Dauka yayi Hanyar ficewa yana fadin"Shikenan tunda kin Hanani ganin Halas dina"yafada muryansa kamar zai yi kuka,taga da gasken ficewa zaiyi da sauri ta mike cikin rawan murya"Am.... _*UNKU*_"cak ya tsaya kafin ya waigo yana kallonta so yake ya tabbatar da itace takirasa da Unku kai verry interresting.
Cikin kunya matsananci ta yaye hijabinta ta rike hannunta kanta na duke tace"kayi hakuri…"tafada dajan Numfashi kamewa Dr Safwan yayi yana kallon Safeena tun daga sama har kasa yake kallonta idanunsa na yawo ko'ina ajikinta Safeena doguwace mai dauke da doguwar fuskar gashin idanunta sun matukar burgeshi structure din jikinta shi ya tafi dashi uwa uba Nonuwanta dasuke cike tab atsaye suna masa maraba cikin mutuwar jiki da wata irin fitinanniyar murya ya Furta'Tsarki ya tabbata ga ubangijin dayayi wannan Halittar...."Yafada still idanunsa kyam akanta ita kuwa yadda idanunsa ke yawo ajikinta haka takejin wani sanyi na ratsata kamar wacce zata yi masassara,cikin tafiyar kasaita ya karisa kusa da ita yasa hannunsa ya tallabo habanta yana fadin"Baki kyautamin ba Sam Safeena daki hanani ganin wannan kyakyawan suran taki da wuri"Ya fada yana kokarin sa idanunsa anata itakuma taki saima runtse ido da tayi zuciyarta na bugawa tsuru yamata da ido yanajin wani magnet najansa wanda baisan sadda yasa Hannunsa duka biyu ya rumgumota ba yamata kyakyawan tarba afaffadan kirjinsa.
Ya salam Safeena ta furta akasa makoshi saboda wani schock dayajata kamar ta wutar lantarki tunda take arayuwarta babu Namijin daya taba rike mata hannu balle har ya rumgumeta sai gashi tafada cikin wani yanayi wanda kwKwalwarta tagaza hasaso mata komeye shi,shikuwa Dr wani chemistery ne ke aiki ajikinsa wani dumi mai hadi sanyi dadi ke ratsasa hannunwansa yasa duka yakara matseta gam yana Fidda Numfashi sama tuni hijabin Hannun Safeena ya Sulale ya fadi dankwalin kanta yafadi gashinta data dunkule yawarware yarufemata fuska"wow..Shine abunda Safwan ya Furta yayin dayayi tozali da gashin Safeena haka yasanya hannuwansu duka biyu yana lailashi idanunsa arufe yanaji kWakwalwarshi na wani amsawa zut,zut kamar zai shida.
Sun dade ahaka Dr Safwan yakasa sakin ta Saida karar wayarsa ya fargar dashi cikin kasala ya sausautamata rikon yazaro wayar a aljihu yana dubawa yaga Tahir ne yana Dauka Tahir yafara cewa"Kai Dallah mallam kafa shanyani bakasan tafiya ke gabanmu ba"saurin katse wayar yayi saboda bazai iya mgana ahalin daya ke ciko ba so yake su hada ido Safeena taki yarda sai wani sunne kai take kan kirjinsa wayyo Dadi Dr Safwan suma kadai baiyi ba shi yaushe Sakina tatabamai shagwaba juz hug da kiss sai tace duk salon takurane.Mirmishi yayi kawai ya dauko dankwalinta yadora mata bisa kai yana Fadin"Sarkin kunya...Mu zamu wuce Tahir ne yakirani,yana fadar haka yana mika mata hijabinta ta amsa ta sanya tana dukar dakai kallonta yakeyi yanajin wani bakon lamari na ziyartashi kardai ace in yakoma gida wanka yakamasa _Wanka fa Dr Tab koda yake andade ba'a hadu ba_π
Tare suka fito yana gaba tana binshi baya sai da suka shiga cikin gidan ya musu sallama 2000th yabasu suka amsa suna godiya,haka dasuka shiga yima Ummi sallama 50k yabata tace bazata amsa ba ya marairaice yace"Ummi...In baki amsa to kin Nuna min Safeena ce kadai yarki"Ummi tace"Kaima Danane duniya wa lahira Safwan nagode Allah yamuku albarka ya kaiku lapy"Suka amsa Da Amin Abbah kuwa daya bashi 30k kin amsa yayi sukayi sukayi yace'bazai amsa ba shidai burinshi ya rikemai Safeena da Amana"Hakika Mahaifan Safeena sun burge Su Dr Safwan matuka wanda har hakan yayi tasiri aransu.
Abun mamaki sai gashi kawai sun bude boot yara na jidan kayan abinci suna shiga dashi buhun shimkafa,katan din taliya katan din makaroni dadai sauransu narike baki cos nikaina bansan yaushe akasa kayan ba,sai dai Ummi su sukaga kaya kawai,Abbah baice komai ba saboda wannan karon in yace bazai amsa ba to surikin nasa bazai ji dadi ba.
Tabbas soyayyah gaskiya Safeena da Dr Safwan zukatansu sun aminta da juna domin daga ita harshi jikinsu yayi sanyi lokaci dasuka shiga mota zasu tafi Safeena na kofar gidansu tana kallonsu batasan sadda hawaye ya gangaro mata ba har Tahir ya tada mota D Safwan ya dakatar dashi ya bude mota ya fice sai dai ta ganshi agabanta kama hannunta yayi yana fadin'Kukan mekikeyi yanmatana"kallonsa tayi idanunta tab hawaye tace tana turamasa baki"Yaushe zaka dawo"tafada da shagwaba tab wlh badon mutane na wucewa ba abunda zai hanasa rumgumeta ya sumbaci bakin nan daya kusa zautar dashi ammh duk da haka sai da yakara matse hannunta yace"Yaushe kike so nadawo'kallonsa tayi ido cikin ido kawai sai tasamu kanta da furta"Ko gobene inaso"Mirmishi ya subucemai baisan sadda yace'Gobe. fa kikace,tagyada mai kai mirmishin yasake yi mata kan yace" Am srry bazai yuyi in dawo gobe ba,saboda in nadawo wazai kula da patient din "yafada yana kallonta kafin ya cigaba da cewa"kiyi hakuri verry soon zan dawo" yanzu tunda baki da waya ga wannan ki rike kan inzan dawo in siyo miki taki ko"yafada yana mikamata dayar wayarsa da hannu biyu ta amsa tace"Na gode Allah ya saka da alkhairi",wow....Shi wai she Sakina yataba bata abu tagodemai ai gani take dolema yabata ta amsa tana wani bude hanci kamar ta bashi ajiya,kura mata ido kawai yayi yana kallonta zuciyarsa yaji tana zafi in ya tuna Tafiya zai yi Tahir ne yaga abun bana karewa bane yadinga zabgamusu hon,Safeena ce tayi karfin juyawa tana Fadin"ka tafi....Kagaida hajiya da momma harda Adil Allah ubangiji yakaiku lpy"Tafada wasu hawaye na gangaro mata dagudu ta ruga gida wani kuka ya kwacemata.
.jikinsa sa babu laka yakoma mota yana Shiga Tahir ya kallesa kawai ya girgiza kai ya tada mota suka dau hanya,sun Fita garin gusau jefi jefi yana kallon shashen Dr Safwan yake wanda yamaida kansa jikin kujera ya lumshe idanunsa kamar mai barci ammh hakika ba barci yakeyi ba gabadaya ransa da tunaninsa naga Safeena kwana daya kacal ammh tasamu wani gurbi mai girma azuciyarsa wanda baisan sanda tasameshi ba,ji yake tamkar yasakota cikin mota yazo kaduna da ita kallonta kawai da yanayinta kansashi nishadi balle yangarta da salon kunyarta.
Dr Tahir yakara kallonsa kan yace"Duk wannan Damuwar ta mecece Dr Safana"yafada kansa tsaye shuru yayi masa wanda har ya fitar da rai da zai yi mgana yace cikim sanyim murya"Bai shafeka ba plz Tahir karabu dani bana son damu"yafada still idanunsa suna rufe shuru Tahir yayi kan ya jinjina kai yace"I can belive my Dr fall in luv wit Safeena....Any why ta cancanta saboda kyawawan halayyata congratulation mr man wlh kadace ta ko'ina"Abun mamaki sai ga Dr Safwa yayi mirmishi yace'Thanks u mr Tahir bello suraj.
_to ya kuka gani kunga yadda soyayyar Allah take ko,sai Allah yabaka wanda ko a mafarki baka taba tsammani ba,juz imaging Dr Safwan yafada tarkon son Safeena konace sun fadama Juna,kuna ganin salon Safeena bakwa ganin lokaci kadan za'a Shafe babim Sakina arayuwaR Safwan ba_
_*juz commet if i say commet i mean a verry touch one*
_love u so much my dearest fans_❣❣❣❣❣
*Janaf*✍
π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀
*NA TAFKA KUSKURE!!*
ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀
*NA*
*Janaf ce*✍✍
DEDICATED TO *My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*
I so much luvs u my mommaππ
*INTERLLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*{onward together}*
*{we give the the Reader's of ours the best out of the bests,,,Our inks are melodious and dropping a kinda light to reader's}*""""
*THE PEN OF LOVE*π
*HEART OF TOUCHING*❤ *TEARS OF SORROWS*π *CURDLES*π, *GIGGLES*π, *AND MARRIEGE THINKS*π
*JUST GIVES US A FOLLOW*✔
*19*
------Karfe sha biyu na rana ta musu akaduna,duk Da sun sharara gudu ko ahanyama haka Dr Safwan yake sukuku dashi bayi da kuzari lokaci bayan lokaci yana sakin ajiyar zuciya shikadai daga karshe kuma yayi mirmishi shi kadai,Dr Tahir yayita kallonsa yana girgiza kai cos yasani tunda yacemai bayasan damu ko ya mai mgana tsiya zasu tafka dat why yakyalesa akwai lokaci.
Asibiti suka wuce saboda sunsan aikwai tarin aiyuka illai kuwa aiki ya rike su sai dare kana,yamaida Dr Tahir gida yamasa godiya da bangajiya,kana ya Nufo gida hon yayima habu maigadi yataso da gudu ya budemai yana mai maraba Abun mamaki yana sulala motar tasa parking space kawai yaga Hajiya mama tafito da sauri zani ahannu tana Fadin"Oyoyo....Safiyanu angon Safeenatu"tafada tana budemasa murfin mota cikin kasala da mamaki ya fito fuskarsa na nuna almar gajiya yace"Hajiya...Wai baki kwanta ba",ta rike hannunsa tana fadin"inkwanta banga dan jikalle na guda daya aduniya ba,to ina lbrin Amarya Safeena yaka ganta tayi ko"Tafada harda dagamai giraππdariya takusa kubcemai yace"oh...My god hajiya dawowata fa kenan wlh am tired"yafada yana yamutsa fuska rikosa tayi tana fadin"Koma u taya neπwlh alqur"an baka isa ba sai kabani lbri daga farko har karshe karyan tsiya ke dawani turancinka na karya'tana fada tana jansa shi saboda mamaki ma yasa yakasa kwatar kansa jaye dashi har falo tana kwalama momma kira"Ke Hadiza ki fito ga danki yadawo dan nasan shigewa cikin duk na kewarsa ne"tafada tana dankwarar dashi akan kujera.
Momma tafito sabe da Adil tana Fadin"Oyoyo....Babana mutanen Zurmi andawo"Ya sauko yana gaida momma ta amsa da fara'a tana tambayan ya ya barosu da kuma Safeenar ya amsa da suna lpy Allah sarki hajiya ashe kichen ta shiga ta zubomai sauran alqubus din da momma ta musu dazu da miyar alaiyahu taji naman rago da man shanu,tahadomai da furarsa masoyiyarsa tana kawowa Adil na hannunsa tace"Maza ijiye yaron nan kazo kaci abinci dan nasan ka kwaso yunwa'baiyi gaddama ba ya mikama momma shi ammh kiri kiri Adil ya noke shi yasan ubanshi Haj.Mama tace"Kai kaci batar ubanka zonan...Inbanda kana butulu Hadizar zakayima kiyawa"Tafada tana rikosa harda dunkurinsa yayi nakwa nakwa yana kallon babansa zai yi kuka Haj.Mama tace"kul kamin kuka wlh in ci ballagazar uwarka"Ashhh....Dr Ya furta kan yace"plz hajiya stop it....Adil iz juzt 6 month fa mai yasani"yafada yananuna rashin jin dadinsa"Haj.Mama tagyara zama ta sunkuyar da kanta tace"Gani dakeni habule ko in kwantama ne"tafada harda rusunawa,banza da ita yayi kan yayi bismillah yafara cin abincinsa Haj.Mama Tace"Au dan batan uba kawai wlh sufiyanu kafita idona wai tun yaushe nake cema kadaina zagina da wannan yaren eye"tafada da karfi,banza yayi da ita cos baisan hayaniya sam itakuwa ta kulu tadinga masifa tanayi tana hadawa da Adil oh ni jami ko meye ruwan Adil anan oho.
yana kammalla ci ya wanke hannu ya mike yadauko kwanon furar yana cewa"momma zan je na kwanta wlh gabadaya agajiye nake..But tomorrow zan yi mgana daku"Daga haka yafice momma tanamishi fatan tashi lpy ita kuwa Haj.Mama binsa tayi da tsaki mteswwww tace"Aikin banza da wofi yo harni za'a ma gorin da' dan ubanka inda ban haifi ubanka ba za'a haifekane kuma in kayi zuciya zo kadauki dan kamaida ma uwarsa dama mungaji da reno wlh"Tafada tana dunkurar da Adil akasa ta mike tawuce fuu tana fadin"Ni za'ayima iskanci da bura uba.muda mukaga jiya mukaga yau muna shirin ganin gobe kuma da izinin Allahπ€£π€£π€£
Adil kuwa ya fashe dakuka momma tayi saurin daukansa tana jijjiga sa ba daman ta taka haj.Mama tadawo kanta ta lallaba ta kwashe kayan da Dr yaci ta kai kichen,takoma daki tana lallamin Adil shikuwa yayi luf a kirjin momma yana ajiyar zuciya _ho yahadu da fushin haj.Mama wo_ππππ
Yana zuwa sashensa abun mamaki Sakina na hakimce kan kujera tadora kafa daya kan daya sanye take dawata doguwar riga ta kamfanin armani baka rigar ta matseta kannan babu dankwali gashi yaji gashin doki abun haushi abun takaichi yan aikinta guda biyu ke durkushe gabanta daya na mata tsausa daya na sama jan kumba wa'iyazubillah tana yar musulma tana salla tana komai kumbanan zaro zaro kamar ta horo tayi wani shame shame kamar sakarya kallon daya yayi musu yayi saurin kauda kai ,ko gaisuwansu bai amsa ba yayi gaggawan shigewa master bedroom dinsa domin jiyayi wani karni karni na tasomai yanaji kamar zaiyi amai.
Sakina tabishi da harara kofin dayake hannunta cike da madarar hollandian ta kurba kan ta furta afili"Rubbish.....Tana kallon yan aikinta dasuka zuramata ido tadaka musu tsawa dole kowacce ta shiga taitayinta.
Yana shiga ya maida kofa Ya rufe fridge yafara isa ya sanya furarsa ciki kafin yafada toilet yayo wanka tareda dauro al'wala daure da tawul ya fito daya akansa yana tsane ruwan kan dressing mirror ya isa yana shafama jikinsa mai sai daya kammallah ya feshe jikinsa da body spry kana ya zura jallabiyan blue ya shimfida sallaya ya data sallah.
sai da yayi shafa'i da wutiri yadade yana addu'a wa kanshi da zuru'arshi gabadaya sai ga _*Dr Safwan sale Safana durkushe gaban rabbil izzati yana rokonma kanshi da Safeena rayuwa mai dorewa ta har Abada*_ yana kammallawa ya ninke sallaya ya ijeye saman stool ya koma ya kwanta kan gado hannu ya mika ya jawo wayarsa dake a ajiye a side drower din gadon kenan ta bude kofa ta shigo babu ko sallama wani kamshi ne mai tare da kwauri kwauri ne yadake hancinsa shyasa yayi saurin dagowa,baki bude yake bin Sakina da kallo sanye cikin wata uban night gwon pick colour kafinka tsirara saboda gabadaya surar jikinta ta bayyana rigar batada hannu daya gareta,tana wani takun yanga adole ita zataja hankali miji ammh kash bata iya abun ba kwata kwata bai mata kyau ba.
Bakinsa abude ta kariso kusa dashi ta zauna tare da cewa"Dr nah...Rufe bakin"Tab.....Lalle yarinyarnan yar tasha ne wato Dr na haka yafada aransa,binta yayi da kallo aransa yana ayyana tabbas tana bukatar wani abu ne ammh matar da yadawo ko kallonsa bata yi bane yanzu zata wani kwaso jiki miya miya tanawani fadin wai Dr nah. _kai Dr Safana wai miya miya kamar wata mage_π€£π€£
Shafa sajensa tayi tana fadin"Brk da hutawa likitar zuciyata..."tafada tana wani fari da ido daure fuska yayi yasa hannu ya cire hannunta yana fadin"quickly ask wht u want.....Zan kwanta ne"yafada yana kallon idanunta tsam tayi domin taga yana neman harbo jirginta kanta maze ta yi wuf ta fada jikinsa tana mai kukan kisss biye mata yayi cos yana so yaga inata dosa bakinta tasanya anashi tana sumbatarshi hannunwanta na shafa kwantattacen gashin kirjinsa cikin wani salo yayi kokarin kar ya biyemata ammh ina zuciya da gangan jiki na bukata tuni ya tallabeta yayi saurin birkitata tadawo kasan sa yafara aikamata da nashi zafafan wasannin itama tana maida masa.
Shudewar awanni biyu ya fito daga toilet kansa na digan ruwa Ya kalli Sakina datayi share share kamar jaka yayi tsaki yana duba kirjinsa yace"Sakina kewai wata irin mai kunni kashin ne...Har saunawa zance miki kidaina pixsing din kumbunan kina yar musulma infact ma kina jimin rauni look out"yafada yana nunamata yadda ta karceshi a kirji tayi wani lum da ido kan tace cikin sakarci"Haba my Dr kai komai nayi banyi daidai ba"Tsaki ya sake ja mtsweee kan yace"kinga don Allah ki tashi kiyi wanka kinsan ban hada gado dake da najasa and kuma ki tabbata wlh kin zubar da wannan turaran aljanun nan"Yafada da serious matter Tasan Halinshi dole yasa ta mike tafada toilet tana tuna turaren dayace na aljanune hajiyarta ta kawomanata kan tayi amfani dashi ko me tace Safwan yamata jiki narawa zai mata ammh gashi bata ma kai ga tambayaba ya kushe abun.
Koda ta fito har yakoma ya kwanta ita agurguje tasanya jallabiyansa tahayo gadon tadora kansa akirjinsa tana wasa da gashin daya kwanta da dashin ruwa tafara mgana cikin sanyin murya"My Dr.....Tafada tana dagowa" umhmmm"yace mata kan taciga ba da cewa"ammmh.....Ammmmh....Dama game da businees dina ne"sai kuma tayi shuru yace"inajinki business women zaki kara bude wani reshe ne aturai"yafada da yar dariya tace'No.....Kudi zaka bani 2million ina so na shigo da wasu bags ne zuwa nigeria kuma duka kudaden hannuna in na hada baza su isheni ba shine nake bukatar taimakonka amatsayinka na mijina"Ta fada wit full comfident.
Mikewa yayi yana tuntsuran dariya harda rike ciki zuru tamai da ido tana kallon sa domin batace tataba ganin Safwan na dariya haka ba daure fuska tayi ta mike tana fadin"Am not a fool....Safwan stop"tafada tana kokarin ficewa,saurin mikewa yayi yasha gabanta yana Nuna ta da yatsa yafara mgana"SAKINA KABIR KANKI....gaskiya saiyau na yarda baki da kunya do u think am fool dazan dauki kudi har 2million na baki"yafada yana nuna kanshi kan yadaure fuska yace"oh kin manta sanda keda uwarki kukacemin banida kudin zan iya dawainiyarki sai dai ke kiyi dawainyata to nikuma har abun zuwa anemi wani abu aguna ne ai nazata ke kin isa kima kanki komai"yadakata kan yadaure fuska yace"Yanzu ne nakeda daraja irinta miji agurinki....To bari kji wlh tallahi indai ni Dan Hadiza ne da Sale bazan taba baki kudina ba koda rance ne kuwa",yafada da kakkausan murya sororo tayi idanunta sun ciko da kwallah kam tanuna kanta tace"Baza ka bani ba"kai tsaye yace"yes...Ko kudin kine ai kudi yana gurin bussiness women so kiyi amfani da abunda ke hannunki cos Kudin Dr Safwan bana ci bane abi"yafada yana zakuda kafada alamar ko ajikinsa .
Idanuwanta yakawo ruwa ta nuna kanta tana fadin"Ni safwan kaci ma mutumci ko....Ya amsa da "eh....Ko zaki ramane"girgiza kai kawai tayi kan tafice tana kukan tsaki yaja yace"shashasha kawai gobema kidawo ni dake muga wanda zaiyi laushi yana fadar haka yayi swith off din light din ya kunna dumlight ya fada gado yana addu'an kwanciya barci.
sakina nakomawa daki tafada kan gado ta fashe da kuka wayarta tadauka da tsohon daren tadinga kiran hajiya kari no answer dole tayi wurgi da wayar tana shure shure kan katifa maganganun Safwan nakara dafamata zuciya,aranta tanaji kamar takoma tamaidamai martanin mganansa _chai...Daga baya kenan meyasa lokacin dayake miki mganan baki mayar mai stupid kawai_π€¨
*************************
Koda garin Allah ya waye cikin farin ciki Dr ya tashi domin yayima kansa alkwarin daina damuwa da al'amarin Sakina domin ya shirya tsaf don fito na fito da ita don ya nuna mata kuskurenta dan yasan sakina da taurin kai bata bari aga gazawarta.
Tun 7 ya fita domin yasamu emergency cll daga asibiti ko sashen su momma bai shiga ba bai samu kansa ba sai after 12 office din DR Tahir ya biya suka gaisa kan ya komo nasa isa yayi kan kujerar office din nashi yazauna yana jingina kansa alamar gajiya idanunsa na lumshe cikin sakan uku ya mike firgigit yana fadin"oh my god......Na manta yayi saurin zaro wayarsa yana latsa wasu nombobi kan ya kara akunne.
Safeena dake cikin dakin Ummi tana muraji'a cikin suratul yusuf taji wayar da Dr safwan yabata tadau tsuwa zumbur ta mike ta ijeye qur'anin tadauki wayan jikinta na rawa taja inda taga kamar nanne wurin dauka cikin sa'a kuwa tana karawa akunno muryashi ta dakin dodon kunnenta"yanmatane.....Badai aji ake jamin ba" rufe ido tayi kamar tana ganinshi kan tace"Assalamu Alaika...Ina yini"ta fada da siririyar muryanta cikin kasala yace'oh...Srry wa'alaikas salam...Lpy kalau yan matana shine ko ki nemi ko"Tura baki tayi kafin tace"to ka nuna min yadda ake bude wayarne"tafada da shagwaba tsam yayi wani abu na zirgamasa kafin yace"oh......Am srry na sha'afane kece kika mantar dani kina ta kuka"la....Ni yaushe nayi kuka"yace"la...Akofar gidan Abbah kin tuna"yafada yana kwaikwayonta tsuntsurewa tayi da dariya kan tace"kai ko....Yace"ke ko....Yafada yana siririyar dariya"rufe fuska tayi tana mirmishi shima mirmshin yakeyi yana fadin"Yan matane sarkin kunya...Ya Ummi na da Abbana ina usman"ta amsa suna lpy ,yace'me kikeyi ne yanzu"tace"muraji'a nake tunda yanzu bazuwa mkrantan nake ba kada kada haddan ta gudu"tafada tana mirmishi da sauri yace"af...Meyasa kika daina zuwa mkrantan"tura baki tayi kamar yana ganinta tace"ba Abbah bane yace nadaina zuwa ba wai yanzu ina karkashin ikon kane"farinciki ya cikamasa da ciki ko bakomai an nunamai yanada matsayi rausayawa yayi kan yace"Hakane mganar Abbah don mkranta kigayamasa kicigaba da xuwa kafin nazo nayi caraf dake"yakareshe fada harda kanne ido daya kamar tana ganinsa saurin rufe fuska tayi tana siririyar dariya cikin shagwababbiyar murya"Ni....Kabari bani so"shikuma ya amsa da cewa"Nikuma inaso yaza ayi kenan"Yafada yana dariya itama dariyar take tana rufe fuska janta ya cigaba dayi da hira tun bata saki jiki dashi ba har ta saki jiki suna hira suna dariya sunfi awa suna waya sai da wata Nurse ta shigo tana fadin"Sir....Emergency .....Ok yanmatana i u clll u later daga haka ya ktse kiran ya fice da sassarfa.
Itakuwa Safeena rumgume wayar tayi tana jin wani abu na fitowa daga kasan kirjinta yana kwarara asassan jikinta tafada kan gadon ummi tana fadin"I miss u Unku.....sai da tafada kana ta rufe baki tana kallon kofa sai da tattabar da bakowa kana jawo wayar tana kwatanta yadda dr yafada mata zata bude code illai kuwa yabude batasan sadda tace eyyyyyyyye...... ba.
Commet
And
Share
*Janaf*✍
π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀π€¦♀
*NA TAFKA KUSKURE!!*
ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀ππ½♀
*NA*
*Janaf ce*✍✍
DEDICATED TO *My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*
I so much luvs u my mommaππ
*INTERLLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*{onward together}*
*{we give the the Reader's of ours the best out of the bests,,,Our inks are melodious and dropping a kinda light to reader's}*""""
*THE PEN OF LOVE*π
*HEART OF TOUCHING*❤ *TEARS OF SORROWS*π *CURDLES*π, *GIGGLES*π, *AND MARRIEGE THINKS*π
*JUST GIVES US A FOLLOW*✔
*20*
••••••Wurin ma'ajiyar hotunan tafara shiga domin tadan san kan waya domin Aisha yayanta yataba bata wata tecno D3 _my first phone wo...Ammh sai da akasamu barawo ya saceta_π‘abun mamaki hotunan Dr ne dana Adil kawai aciki kala kala iya kallonta wani suna kwance wani suna zaune wani yagoyasa gasunan dai sai iya kallanta,abun da yaba Safeena mamaki shine shin uwar yaron nan basu tare da dr ne domin taga koda sau daya bata ganta acikin hoton ba sai dai shi da Dr to kodai ta rasu ne tayi saurin rufe baki aranta tana cewa"da ta rasu da Ummi ta fadamin"haka dai taita kallon hotunan babu hoton daya burgeta sai wani hoton Dr yana sanye da american suit,black and white ya daure wuyansa da tektie baki kansa yasha gyara yana maiko hannunsa sabe da rigar likitocinsa yana mikama Dr Tahir abu abakinn wani office ya juyo da gilashin dayake karamasa da kwarjini yana dariya aka dau hoton hakoransa farare reras suka bayyana hakika yayi kyau matuka a hoton wanda har Safeena tayi serving dinshi a Fuskar wayar saboda kyan dayayimata.
tana cikin daki taji sallamar Aisha suna gaisawa da Ummi kafin tatambayi Safeena Ummi tace mata tana ciki da Sallama Aisha ta shigo Safeena ta amsa tana fitowa daga uwardakan hannunta rike da waya tace"Yar halak yanzu nake zencencenki araina"Harara ta sakarmata kan tace tana zama kan kujera"Bawani nan ai ni wlh baruwana dake yanzuma zuwa nayi naji lpy baki zuwa mkranta kwana biyu"Zama Safeena tayi kusa da ita tana fadin"Allah sarki kawar arziki...Dalilin dazai kawoni kenan"Tafada tana dafata mikewa tayi ta isa ga botikin dake dakin tasanya kofi ta debo ruwa tana juyowa taga Aisha rike da wayar tana juyawa cike da mamaki gabanta ta ijiye ruwan tana fadin"Sha ruwa Aisha kafin muyi mgana"Shuru Aisha tamata tana bin wayar da kallo chan ta shafa saiga hoton Dr ya bayyana wow...Shine abunda Aisha ta Furta tana bin hotonn Dr da kalon kafin tadago tana kallon Safeena datake kallonta tace"Kawata waye wannan gayen...Ke wayarma tawaye wai? Safeena tayi mirmishi ammh aranta taji zafin yadda Aisha take kallon hoton Dr tana Shafawa cike da shawa'a da burgewa _ho kishiπ€ tashi tayi ta isa ga windo kafin tace _*MIJINA NE*_ da saurin Aisha tace"Mijinki kuma? tafada da sigar tambaya da mamaki juyowa Safeena tayi tana mirmishi tace"Eh...Mijina ne Aisha wanda Abbah yadauramin aure dashi kusan wata daya dawani abu da suka wuce"Sororo Aisha tayi kan ta mike tsam ta ijiye wayar takama hanyar ficewa tana fadin"Kinga nidai nayi gaba don aiki nake na fito ban iyawa da shirmenki Safeena"Safeena tayi mirmishi tace"Wlh da gaske nake Aisha nima yadda kikaji haka naji lokacin da Abbah ke fadamun"cak Aisha ta tsaya kan ta waiwayo tace"Wai da gaske kike Safeena"Karasowa tayi tadafata kan tace"Da gaske nake Aisha dama shine abunda zai kaini gidanku kenan".
Tsuru tamata da ido kafin tazame hannun Safeena ta isa ga wayar tashafa hoton Dr ya bayyana ta nuna ma Safeena tace"Kina Nufin wannan balarabe ko ince bature shine mijin naki"Dariya Safeena tayi kan ta isa ta amshi wayar ta kurama Dr ido tace"Kema kina tamtama ko Aisha"tafada tana kallonta kan taja hannunta su isa kan kujera tacigaba dacewa"Nima haka naji lokacin dana fara tozali dashi amatsayin mijina Aisha wlh babu karya Dr Safwan sale Safana shine mijina"Aisha tayi shuru tana kallon Safeena kan tayi wuf ta rumgumeta tana fadin"Kawata u ar so lucky wlh....Nayi murna sosai lalle kin tabbata mai sa'a
Nan Safeena ta warwarema Aisha komai tundaga farko har karshe Aisha ta jinjina kai tace"Ikon Allah kenan Safeena wlh in Allah yaso ka da Ni'imarsa bbu mai hanawa...Kinga abun Allah ko"Safeena tace"wlh ko amafarki bantaba tsammani ba Aisha sai gashi Allah da ikonsa ya zartar da komai"Aisha ta jinjina kai tana kara tabbatarma da Safeena ita mai Sa'ace.
Haka Aisha takoma gida tafadama mamanta ita kin yarda tayi sai da tasawo hijabi tazo ta tambayi ummi,Ummi tace"da gaskene kana ta yarda tasa albarka tareda da addu'an zaman lpy.
**************•••••••••
Itakuwa Sakina tun da tatashi ko takan Dr bata bi ba tashirya kayanta a trolley dinta tafito ta shige motarta ta dinga zabga hon habu mai gadi yana kewaye shikuma iliya bayanan hakanan ta jira domin jin kanta bazai barta ta fito ta bude ba, aikwai Habu yasha tsinuwa kamar itace uwarsa harda cewa zata sallameshi tunda yagaji da aikin tana cikin mai tijaran sai ga Haj.Mama ta fito dama tunda taji hon din namarasa hankali tasan jakarce,aikuwa tana zuwa sakina tayi shuru haj.Mama tana kallonta sama da kasa kafin kafin tace"Ikon Allah ke inbanda rashin kunya da fitsara kitsaya gaban sa'an ubanki kina zagesa harda cewa zai bar gidan ko"Takareshe fada ta tana rike kugu Sakina tace"plz hajiya niban saki cikin shirgina ba plz stay out"Haj.Mama tace"kinci ubanki nikike cema pulazπ€£hala nayi kama da sakaryan uwarki ce to wlh bari kiji ke kanki inbakiyi hankali dani ba to sai kin bar gidanan don banga uwar dakike tsinana mana ba"Sakina tayi tsaki mtseswwww tashige motar ta kirar vibe tana fadin"Inkin isa in yadawo kisa ya rubutamin saki uku,sai na tabbatar da kin isa uselless kawai"Tafada tana kokarin zuge gilass,Haji.Mama takarisa jikin motar tana fadin"Ahayyye....Tayaro kyau take bata karfo ai ni maryamu bazan taba yarda Safiyanu ya sakeki ba so nake ki kirbi abunda kika shuka da hannunki kuma Alhamdulillah abun da namiki tanadi yakusa isowa gareki wlh sai kin raina kanki tunda ke ballagazar macece wacce batasan darajan kanta ba"Tana gama fadar haka tawuce tana fadin kai megida wuce kakama harkan gabanka tunda ba ita ta daukeka aikin ba aikuwa da gudu ya wuce itama Hajiya ta shigewarta sashensu tana wake wakenta.
Sakina tayi turus acikin mota bakincikin kalaman Hajiya dana Safwan suka taru suka sata fitar da kwallah kamar ita Sakina mai aji da daraja ake cema ballagaza dama jiya Dr yace mata shashasha,tashare hawayenta tace afili wlh both of dem they will pay 4it kafin ta kwarara hon habu yazo da sauri ya budemata saura kadan ta takeshi sai da ya kauce ya rike baki yayi yace"Kai wannan mata baki kyale kowa ba shikanshi yallabai baki kyaleshi ba balle uwarsa da kakarsa balle mu yan aiki,tab...Ubangiji yamana maganinki"yafada da karfinsa kan ya rufe get ya koma kan bencensa.
Katsina ta dikko dakin kara ta nufa saidai haj.Kari taganta kwatsam tana mata kuka dakyar tasamu tafadamata duk abunda ke faruwa Haj.Kari ta mike ta lailayo ashar tace"babban bura ubanchan har ni za'a kawoma iskanci....Shi Safwan din harwani tsiyane balle uwarsa da wannan yamutsatsan tsohuwar har ta isa ta saki kuka, ita din banza to wlh bari Abbanku yazo Sakina nagaji dawannan auren yazo yasan yadda zai yi dashi"tafada tana huci kamar mayunwacin zaki _chau chau Haj.Kari Allah dai ya biya_ Sakeena tayi saurin cewa"a"a Hajiya wannan ba mafita bane kema kinsan wlh in Abbah yaji zai iya tsinemin kema kinsani"haj.Kari tayi shuru kan tace"eh...Kuma hakane shima sun asirceshi ji yake in aka taba yaron nan kamar antaba ubansa"Tafada harda yamutsa fuska Sakeena ta jingina da kujera tace'kyalesu hajiya so suke suga na ijiye kasuwancina indawo ina kula dashi da uwarsa inzamarmusu jaka"Haj.Kari tace"Ina har abada wannan bazai taba faruwa ba domin ni ban haifi malalatan ya"ya ba kudine zan hada na hannuna laila ma zan mata waya takawo abunda take dashi ki wuce kikama hanyar ki tafi ki saro kayanki kizo ki dasa daga inda kika tsaya kibarmin komai ahannuna ninasan matakin da zan dauka"Sakeena ta saki dariya tana fadin"Dat iz my hajiya shiyasa nake sonki"haj.kari tace'karki damu in ban tallafa muku ba wazai muku tunda irin uban da Allah ya baku kenan solobiyo"Sakina tasaki dariya tace"Hajiya Abbane solobiyo kuma tace"kona yi karya"Sakina tace"A"a Hajiya da gaskiyarki"Atare suka sheke da dariya harda tafawa
_oh ni jami Duniya harta kaimu ga haka_π€
°°°°°°°°°°°°°°°°
bayan la'asar Dr yadawo agajiye yake dat why yafara isa shashensu sai da yayi wanka ya huta kana ya fito baiji duriyar Sakeena ba bai damu ba dama kuma ba motsinta yakeji ba har zai fita sai yasamu kansa da tambayan daya daga cikin yan aikinta ina take kai tsaye tacemai tun safe ta fice bai damu ba illa zakuda kafada yayi yafice zuwa massallaci sallar mangariba kana yadawo ya wuce shashen su momma chan ya tarar da haj.Mama da momma suna hira,hajiya dai batai fushi ba saida ta tsaitsayeshi yafada musu yadda sukayi da mahaifin Safeena ya kareshe da cewa"Yanzu na yanke shawarar Safeena zata zauna gidana dake anguwan sarki tunda nan wurin babu inda zata zauna.
Haj.Mama tamike tace"kul...Karma ka fara Acikin gidan nan Safeena zata zauna anyi ba'ayi ba kenan ai inhar Safeena tabar gidan nan ban Nunama ballagazan matarka na amsa sunana maryamu ba"Dr Safwan yace"To hajiya ina gun da zaki sata"Kai tsaye hajiya mama tace"dakuna uku ke shashenka ko?tafada tana kallonsa da kai ya amsa tace"To ka gayamata ta kwashe kayanta adaya ka saka Safeena aciki tunda duk kaine mijinsu in lokacin da Safeena zata koma chan yayi nida kaina zan fada maka"Tana fadar haka tatashi tawuce har takai kofar bedroom din tajuyo tace"Umarnine ba shawara ba kafara shiri cikin sati biyu nakeso Safeena tatare,tana fadar haka tashige daki Dr Safwan yayi ajiyar zuciya aransa yace"Hajiya daru....Ita kuma momma tana ta jinjina kai kafin tace"kaji abunda hajiya tace ko"Ya gyada kai tace"to kabi umarninta kazauna lafiya"itama daga haka tashige kichen zata kawomai abinci shikuwa Dr Safwan yayi shuru yana so yagane dalilin hajiya na zartar da wannan hukunci ammh ya kasa.
_hoho hajiya mama kinayi muna jin dadi Jamuje Allah ja da mulikinki haj tamu_✋✋✋
"Commet and share domin kwarin gwiwata
0 comments:
Post a Comment