_KATSINA_
-----koda kwamishina yadawo ya tarar da Sakina agida fada yahau yi yace meya kawota sai ta shirgamasa karya da cewa da izinin Dr Safwan tataho aikuwa baiyi kasa agwiwa ba yakirashi yake tambayansa abun mamaki Dr ya amsa masa da hakane cos bayaso ta dalilin sa Sakina tarasa albarkar mahaifinta.
******************
Babu yarda Safwan ya iya da mganar haj.Mama domin ko momma bata tsallake umarninta daya fadama Tahir shima yayi na'am da batun na hajiya domin yace abunda babba ya hango yaro ko yahau rimi bazai hangoshiba.
kullum sai sunkusa raba dare suna waya sun maida abu kamar ibada shakuwarsu na kara ninkuwa atare da juna koda Dr Safwan bai budi baki yayi mgana ba shikansa yasani Safeena tana kokarin jan ragamar rayuwarsa agida ko office cikin waya suke kamar wasu tantabaru😛acikin satin yace tasa ido yana tafe saboda shirye shiryen Tarewarta.
Kamar wanchan xuwan wannan tare da Tahir suka tafi Ranar Asabar wanda tun adaren da Dr yafada mata suna tafe takasa zaune gari na wayewa taje akamata kitso dama tun adaren tasanyama kafarta sajen yayi ja sosai tana dawowa dama ta aikama Aisha suka zage suka musu alalan hanta da lemion kankana wanda Safeena tahada shi da hannunta,suna kamnallawa suka share gidan suka gyara dakuna Safeena tashiga wanka itakuma Aisha takoma gida ta shiryo.
Karfe 12 tamusu kofar gidansu Safeena wanda suna isowa yadaga waya Yakirata lokacin tagama shirywa cikin wata doguwar shadda light green taji aiki da Sallah Abbanta ya dinkamata turaren ta Wanda Humrace kanwar Abbah inna husai ta aikomata dashi ta shafa tuni tadau kamshi ba make up tayi ba hoda ta sanya liptick ammh ta fito ras da ita fitowa tayi tana sanya hijabi tace"Ummi sun iso"Ummi dake dakin Abbah tace"To Alhamdulillah...Ki shigo dasu".
Cikin takunta na natsuwa ta isa kofar gidan dukkansu suna jingine jikin motar Idanunta suka fara sauka kan Haskenta Yau kam sanye yake cikin wani farin yadi mai stantsi da yarari yana da ligo ligon zane a jikinshi ammh shararane domin hatta farar vest dinsa ana gani kafarsa sanye cikin bakin buddaden takalmin na fatar damisa hannunsa sanye da agogo na kamfanin rado,hularsa kansa kubece bakace idanunsa boye cikin gilashin dake karamasa kyau,cikin mutuwar jiki yake kallonta itama shi take kallo kasa kasa tana jifanshi da mirmIshi Dr Tahir ne yayi gyaran murya tace"To mr and mrs love kunbarni atsaye fa"Da sauri Safeena tace"La...ya Tahir yi hakuri barkanku da zuwa ku shigo"Tana fadar haka tajuyawa suka take mata baya da sallama suka shiga cikin gidan Ummi ta fito tana amsawa zubewa sukayi suna kwasan gaisuwa ta amsa cikin farin ciki tana tambayansu mutanen gida sukace suna gaishesu.
Daki suka shiga suka iske Safeena ta turare dakin da turaran wuta mai kamshin dadi ta shimfida musu darduma a inda zasu zauna suka zauna Dr Tahir na fadin"Gamu akaro na biyu amarya kuma insha Allahu na karshe"Da sauri ta dago tace"Na karshe kuma tafada da tashin hankali yar dariya yayi kan yace"Eh man daga wannan zuwa sai dai na zuwa daukanki zuwa kaduna ko"Yafada yana kallonta da sauri ta rufe fuska tayi waje tana mirmishi shukuwa Dr ba baka sai kunni domin duk inda Safeena tayi yana binta da ido ne yakasa mgana saboda jiyake kamar yana wayo a gajimare saboda farinciki.
Daya bayan daya tajera musu komai agabansu Dr Tahir na mata tsiyan ta shirya likitan nata ci ne dashi ta shirya mirmishi kawai tayi batace komai tabasu wuri su ci abinci kafin takoma tayi mamaki taga yadda suka ci alalan lemon ma sun kusa shanyewa🤣
Dukawa tayi kana tafara gaishesu Tahir ya amsa yana ta mata tsiya itadai batacewa komai sai mirmishi ana haka saiga Aisha ta shigo itama ta shirya cikin kayanta mai kyau Safeena ta gabatar da ita a matsayin kawarta suka Gaisa da Dr kana Tahir har yana cewa"Shine taki xuwa sai yau"Dariya tayi tace"Yau din aka gayyaceni"Harara safeena tazabgamata karaf a idanun Dr Safwan wanda ya mata kuri da ido yana cizan lebe ai su tahir sai suka fahimci sukadaine ke hirar Dr Safwan da Safeena hirarsu ta aikama juna sakonni ne ta idanunsa Dr Tahir ya mike yana fadin"Kinga kawarmu zo mu fita tunkafin mara kunyar nan yabamu kunya"Aisha ta mike tana fadin"Kwarai kuwa don itama ba kunyar ta isheta ba"mirmishi suka musu kafin su fice suna fita Safwan ya maida hankalinsa kachokan kan Safeena itama tanaji tasan kallonta yakeyi shiyasa taki dagowa ajiyar zaciya ya sauke tareda Numfashi da sauri tadago ta kalleshi yayi saurin langwabar da kai yace"Shine ko dan sannu da zuwa ko"Yafada idanunsa kyar akanta cikin sauri tace"la...Bana muku ba"Shima da saurin yace"NO...ke agarinku haka ake ma miji oyoyo"Tadago tana fadi cikin shagwaba"To yayane akeyi"Mirmishi yayi yace"Gud girl bari kigani....Ya mike tsam ya isa gabanta yasanya hannu yadagota ya zaremata hijabin jikinta yana karema kallo cikin sha"awa kafin Safeena tayi wani yunkuri yayi wuf ya rumgumeta tsam akirjinsa yana fidda Numfashi sama sama hannunsa tazagaye kugunta dashi ya matseta sosai hannunsa yadauko yakara azawa bisa hips dinta atare sukaja Numfahi shiii!!!kamar suna shan yaji tuni Dr yaji wani abu na mai yawo tudun hip din Safeena yagama rikitasa baisan sadda yake sanya hannu yana shafashi a hankali cikin kwarewa itakuwa Safeena neman shidewa takeyi saboda Dr yazomata da wani al'amari mai girma wanda kwakwalwarta baza ta iya dauka tafara mutsu mutsu dat why ya sausautamata rikon yadago yana kallonta idanunta arufe ya kurama ma lips dinta ido dayake wani maiko baisan sadda ya dora lebensa akai ba yafara wasa da harshenshi akan lebenta ba kara kamkame ido Safeena tayi tanajin wani abu na zirgamata sai da yagama lailaya lebenta kafin yatura harshenshi cikin bakinta topha anan wasan ya fara wani irin sumbata ne mai tsaya aran masoyi yake mata tare da shafa ko',ina na jikinta tabbas Dr yafara rasa control dinshi yafara nishi sama ya neman turamata hannu cikin riga gashi tana tsoron ashigo agansu batasan sadda ta fashe maida kuka ba jin kukanta yasa yayi saurin sakinta yakoma ya jingina da bango yana sauke Numfashi idanunsa a rufe yace cikin murya kamar ta mara lpy"Shiii!iz ok bazan kara ba"da sauri tasa hijabinta zuciyarta na bugawa yadade tsaye kafin ya koma ya zauna abunda ta lura dashi jikinsa gabadaya yayi sanyi yadukar dakai kawai Safeena taji gabadaya ranta ba dadi tayi sanadiyarta da mijinta yayi fushi da ita shiyasa tatashi a hankali ta isa kusa dashi ta zauna kanta akasa tace"Don Allah unku kayi hakuri baran kara ba"dagowa yayi yana kallonta idanunsa sunchanza kala mirmishi yamata kafin ya riko hannuta yace"Karki damu yanmatane dama nadade awannan yanayi kawai nidai fatane in kika tare bara ki dungamin rowa ba ko"Yafada yana kanne mata ido daya"saurin kauda kai tayi tana mirmishi yace"Common tashi kije kifadama Ummi ina son mgana da ita tunda Abbah bayanan kuma sauri mukeyi yanzu zamu koma",tayi lau da ido zata yi magana yayi saurin cewa "Yaushe kika fara gardama"da sauri ta mike ta fice ta iske babu Tahir balle Aisha Ummi ke fadamata wai ta kaishi zaga gari rike baki kawai tayi nan tafadama Ummi sakon Dr tako sanya hijabi ta shiga bayan sunkara gaisawa dr yace"Ummi dama mganar tarewar Safeena ce hajiya tace nan da sati biyu ina fatan babu matsala"Ummi tace'Sati biyu safwan gaskiya yayi kadan...Ina laifi wata biyu kan lokacin anfadama wanda yadace"mirmishi yayi yace"Duk don wannan ba mtsala sai a fadamusu yanzu ko"Ummi tayi shuru kafin tace"A'a Safwan abarshi ahakan kawai"Dr yayi shuru kafin yayi mirmishi yace"Ummi duk nagane meyasa kikace haka Safeena ko ba aure kanwatace nimai mata komai saboda haka Ummi karku tada hankalinku Safeena kadai na aura ita kuma zaku kaimun"Ummi tace"Ayi haka Safwan mahaifinta bazai yarda ba"Yace"Haba ummi in hajiya taji bazata ji dadi ba zata ga kamar kun waretane"Ummi tace to shikenan ubangiji Allah ya saka da aiheri yakuma bada zaman lpy,ya amsa da Amin.
Nan yayi sallama da Ummi kan tafito a waje suka hade da Safeena yacemata sauri sukeyi but komai kenan zasuyi mgana ta yawa Dr tahir kuwa sai da ya dinga kiransa kana yadawo safeena tasha tsaraba kayan makeup dana makulashe ya siyo mata jibge da kudu 2000k yabata itakuma Aisha 5000k yabata sun nuna bazasu amsa ba ranshi ya baci dole suka amsa wannan tafiyar ma sai da Safeena tayi kwallah shima Dr dai sai ahankali karfe 4 suka mika hanya suna daga musu hannu.
Koda Abbah yadawo yaji abunda Dr yace cewa yayi "bazai yuyu ba zainabu ba saboda komai ba sai saboda darajar yarmu zamuyi mata daidai karfinmu bazan janye lokacin dasuka sa ba saboda dama kyan aure mace tatare gidan mijinta zan ma yanuwana bayani akwai kudade ahannuna kome suka yanke shikenan.
_KADUNA_
Suna komawa yafara gyaran gida kuma har lokacin Sakina bata dawoba bai damu ba shiya bashi ikon yin gyaran gidan a tsanake kamfanin MAHARHABA Suka zo suka chanza tsarin dakunan bayan an shanza tsarin fentin, da kawatattun kayansu gabadaya sashen su dana su momma sai da aka chanza komai falon nasu an kawatashine da black and red shima bedroom dinshi an kawatashine da black and ash ita kuma Safeena pick and white na uwargida kuma daman kalan kenan blue and purple sukuwa su momma an kawata musu ne da kalan black and red ko'ina hakika gida yadau kyalli amarci kayan kaf habu da iliya yabamawa yace sukaima iyalansa sunrasa bakin godiya saboda alherin megidansu agaresu mai girma ce.
Kudi ya damkama momy mahaifiyar Dr Tahir itama yar kasuwa ce 4million yace tahadomai komai na bukatar aure na akwatin mace na Safeena kawai banda Sakeena ita kudi zai bata saboda sanin halinta ita yar tsarice.
Haj.Mama abu nasu mganin akwabesu tab ta shirya tatafi Safana tagayyaci yan'uwa da abokan arzuka na suzo su tayasu murnan tarewar matar jikanta sunyi sallama da iyami na sai sun hadu in sunkawo amarya,hakika Dr ya gwangwaje safeena akwati takwas shake da kyan alfarma momma da haj.Mama kowacce kala biyar biyar yayi musu bayan kayan abincin biki daya jibgemusu hatta Adil ma ba'a barshi abaya ba Dr ya gwangwajesa.
Ana saura Sati daya aka shirya kai kaya ai haj.Mama tabuga lamara tace da ita za'a dole kuwa akaje da ita sai matar kawu bala uwani sai momy sai wasu yan uwansu na Safana suka dunguma sai Zurmi wanda Tahir ya kaisu hakika mutanen zurmin sunga inda ake abun arziki domin kayan da'akawoma Safeena yazama abun yawo agari,su maman Aisha ne da matan baffa isuhu da su iyami da kanwar Abbahsu inna husai data zo daga cikin zamfara sai makota suka amshi kayan tare da kayan abinci buhu buhu na da kwalaye am amshesu cikin farinciki da karramawa to daman anzama kawai aka baje ana sa albarka Ummi sai da tayi kwallar farinciki domin ko a mafarki bata taba zato ba.
Shikuwa Tahir gidansu Aisha yasamesu Safeena ya basu sakon da yazo dashi kati na shaidar gayyata guda dari sai kwalayen cimgam da minti guda goma da tsabar kudi dubu Hamsi yace inji Dr in suna kuma bukatar wani abu samai mgana ta waya ai sunma kasa mgana saboda mamaki illar kawai godiya,sai wajen bayan la'asar sukayi haramar komawa cike da kyan soye soye irinsu dubulan cincin da alkaki cikin farin ciki aka rabu.
sunkoma suna bada lbrin karamcin mutanen zurmi wanda suka kasa boyewa ita kuwa Safeena washegari inna husai ta tara ta suka wuce zamfara ita da Aisha domin ta gyarata sai dai tama Dr text tafadamai dariya yayi yace"Allah ya kiyaye hanya ai ni za'a gyarawa mawa ko"Dariya kawai tayi ta shareshi.
Tabbbas inna husai tadage da gyara yarta magunguna masu inganci irinsu kumbar da take sha da nono da wanda akeci hakanan sai kayan fruit data hada mata sai wanka lalle mai hade da sinadarin turare mai tsayawa aran masoyi cikin kwana biyu Safeena ta chanza jikinta yadawo yana fitar da wani kamshi mai dadi gashi tayi wani haske da sulbi ita kanta ajikinta tanaji ta chanza domin kullum cikin zubar da ruwan Ni'ima take ko wayama basuyi inna husai ta kwace Dr yanaji yana gani Dole ya hakura har komai ya kare.
Ana saura kwana uku tarewar uwargida Sakina ta diro gidan bayan shafe sati uku batanan daga katsina kano taje daga chan ta wuce dubai kwananta goma ta dawo sai da tsaya tagama clearing din kayanta suka iso hannunta tukun ta dawo tayi mamakin ganin chanji agidan bata gama mamaki ba sai da tashi ga sashensu taga ikon Allah batawani damu ba ita duk azatonta Dr neman sulhu yake da ita shiyasa tana shiga daki tace"Hmmmm dama nasan zaka nemi ni wlh zaka gane kuranka indai sakina ce"Tafada tana shekewa da dariya.
_lalle sakina kin cika sauna inbanda sakarci ko ada bai baki hakuri ba sai yanzu stupid kawai_🤔
Commet
And
Share
*Janaf*✍
🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀
*NA TAFKA KUSKURE!!*
🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀
*NA*
*Janaf ce*✍✍
DEDICATED TO *My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*
I so much luvs u my momma😍😍
*INTERLLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*{onward together}*
*{we give the the Reader's of ours the best out of the bests,,,Our inks are melodious and dropping a kinda light to reader's}*""""
*THE PEN OF LOVE*😘
*HEART OF TOUCHING*❤ *TEARS OF SORROWS*😭 *CURDLES*🙂, *GIGGLES*😁, *AND MARRIEGE THINKS*💑
*JUST GIVES US A FOLLOW*✔
_*Sahiba ina kike wannan page din kacokan nakine Hafsart Almustapha Hafnan wlh soyayyarki araina tawuce duk kan tunaninki inaso kisani kowani bugawan Numfashina kina kokon qalbina*_
*22*
Koda Dr yadawo yaga Sakeena bai wani yi mamaki ba cos shiyanzu bata gabansa kokarin yadda zuwan amarya zai zama ready yake.
BaDa wuri yadawo ba shiyasa sai da yayi wanka yayi sallah kana yadauki check din daya rubatama sakina kudi yanufi dakinta da sallama abakinsa ya shiga illai kuwa Yar mulkin kwance kan gado tana zuba selfie tana daukan yanayin dakin dariya takusa kubcemai,saboda ganin yadda take wani ji dakai ita adole miji ya biyota dauke kai tayi kamar bata ganshi ba tacigaba abunda tajeyi mirmishi yayi kan ya isa ya zauna gefen gado yana fadin"Ashe andawo....Andawo lpy"kamar baza tayi mgana ba sai chan tace"Lafiya kalau aka dawo duk da akwai wanda baiso mutafi ba"Tafada tana wani girgiza dariya yayi har hakoransa suka fito yace"Ai wani baice kar mutum yaje ba iyaka yace mutum yaje da kudinsa ne hakan da yayi laifi ne"Yafada yana kallonta basarwa tayi domin tagane yagasa mata mganane mikamata check din yayi takalleshi a wulankance tace'Na miye kuma mallam"Yace"Ki karba nakine"amsa tayi awulakance tana dubawa check din 2000hud thousand ne arubuce dagowa tayi ta mika mai tana fadin"Kamakara ai ka rike tsiyarka domin ni yanzu nafi karfin taimakonka kodama tsautsayi ya kaini"bude baki yayi kan yace"Ke...abunda kike tunani kenan"Yafada hannunsa a haba Sakina tace"Bangane ba"Yace"Kudin nan hakkinkine fa aure zan kara shine nafita hakkinki na baki kudin saboda kisai Abunda kikeso ko"yafada yana kallonta kallonsa takeyi kan tasheke da dariya harda faduwa kasa kallonta yakeyi aranshi yana auna dabbancin sakina.
Mikewa yayi ya ijiyemata check din yanufi hanyar kofa yana cewa'Ki bar dariyarnan ina jiyemiki ranar da zaya koma kuka"Saurin mikewa tayi tasha gabansa tana cewa cikin shakiyanci"Tab...Wai aure zakayi kai bakaji kunya ba,ni zaka razana to ai bari kaji ni Sakina matar kaddarace mutuwace kadai zaisa kayi aure kai ko mutuwar nayi sai na ga dama balle da raina'Tafada tana nuna kanta kan takara shekewa dadariya,kallonta yayi kan ya girgiza kai yace"Kin Tafka kuskure sakina shiyasa har yanzu yake dawainiya dake kinyi kuskuren sawa aranki zan dauwama dake ke daya....watch and see"Yafada yana kada mata hannu kafin ya fice.
check din ta dauka kan tace"raba mugu da makami....Ibadane'tafada tareda fadawa kan gadon tana fadin"ji shi wai aure kamar auren banzane"Daga haka tajawo wayarta tacigaba daga inda ta tsaya
*Chai chai wlh kedai sakina anyi dabba wlh kin tabajin inda akayi wasan kishiya mtsssss mai kwakwalwar kifi kawai*😡
ko washegari tun safe Abuja tatafi saboda isar kayanta kotakan mganar Dr bata bi ba gani takeyi bazai taba iya kara aure ba sai da ta fito zata tafi yaganta shima zashi aiki yake cemata"Madam business sai ina kuma"Tayi mamaki ammh saita danganta haka da neman shiri yake a yatsine tacemai Abuja Mirmshi yayi mai kayatarwa yace"Allah ya kiyaye hanya madam busuness"Daga haka ya fice shashen momma ya barta nan itama daga nan tahaye motarta tayi gaba.
Ashashen momma daru suka sha da haj.Mama don yace tabari abincin sha'anin bikin yayimusu odar haj.Mama tace"Ina bazai yuyu ba tuka tuwon ne akafi su iyawa kokuwa miyar ne za'a nuna musu kukowa dafa shinkafanne za'a nuna musu to maza karya ya sake wannan ai barnan kudi ne yan'uwa zasu zo suzasu yi kada inji ka gayyatomana wasu kedararru suna bamu abinci"Dole ya hakura ammh yana jinjina karfin halin hajiya na fadar abunda bamai sauki bane gareta.
Tun aranar bakin Safana suka fara zuwa matar kawu bala uwani da abokiyar zamanta sai makotansu hakika haj.Mama tayi farincikin ganin baki sun fara hallata mussamman Haj.Mama tasa aka gayyatomata masu kidan kwarya daga zaria dushi _wayyo za'a tuka tuwon babban gida_ momma kuwa farinciki yagama cikata duk inda ka ganta bakin nan har kunni goye da bawan Allah Adil.
Washegari kuwa sai ga mota tahau sauke musu drinks kala kala da ruwa abun sai wanda yagani baki kuwa suncika gida harda yan garinsu momma Allah sarki aikin haj.Mama ce tace kowa yazo ataru anuna farinciki domin yanzu safiyanu yayi aure,koda Sakina tadawo daga Abuja taji hayaniya ashashen su momma ammh bata leka ba tunaninta yan kauyen nanne suka zo sucika ma mutane gida da hayaniya ko kallon shashen batayi ba tayi shigewarta shashenta agajiye take shiyasa wanka kawai tayi tafada gado sai barci yan aikinta naso suyi mata tsegumi domin gunsu habu maigadi sukaji yallabai zaiyi aure ammh ganin ba fuska yasa suka ja bakinsu sukayi shuru.
_ZURMI_
Sai ana gobe tarewar Safeena tadawo duk wanda ya ganta sai yakara kallonta saboda wani sheki data keyi kamar daren goma sha biyar Kda tadawo tayi gyaran kanta da lallenta kawayensu na mkranta sunyi mamakin jin tarewar safeena kuma wai andaura tuni harta Mallam yahuza takaimawa ya amsa yana sama mata albarka da aurenta gabadaya _Allah sarki loser_ batada wasu kawaye shiyasa daga ita sai Aisha suke gudanar da komai gashi daman Dr yace"Su zama cikin shiri karfe biyu za'a zo atafi dasu saboda kada suyi dare ahanya.
mganar kaya kuma hajiya ita tayi mgana Da Abbah tace kadama ya wahalar da kansa domin ko sunkawo zatasa amaidamai saboda safeena da safwan duk dayane agurinta ba bambamci to bbu yadda ya iya domin hajiya nada wata kima a idanunsa bbu abunda zaice sai godiya domin iyalan justice habule safana sun gamamai komai.
_YININ BIKIN TAREWA_
_*Both kaduna and zurmi*_
Tabbas inda ake dashi nan akeyi domin tuni takowani bangare shagali yakachame bari mu leka kaduna.
Haj.Mama tun asuba tasa aka dora tunkunya lamba talatin🤣🤣na tuwo da na miya aka shiga sha'ani atsakar gidan masu yanka alaiyahu nayi masu yanka albasa nayi wuri yahade sai hira ake ana shewa.
.Itakuwa momma tana ciki ita da bakinta mommy na tare da ita ga dan Amanar Adil shima yaci gayunsa yau takefa ranar itama momma taci gayunta cikin swice less dinta tadau dauri momna ta fito ras da ita ita kuwa hajiya mama doguwar rigar shadda taci taji aiki abunta harda daurin gwagwaro🤣🤣kan kice kwabo am kammallah tuwo an kwashe aleda an zuba a kuloli miyama tuni ta sauka wacce taji naman rago zubu zubu aciki ga jallop din shinkafa itama an kammallah ansa a kuloli ga alalen leda shima an kammallah abun gwanin sha'awa tuni aka tsabtace wurin kamar ba'ayi komai ba.
Itakuwa sakina sai wajen 12 tatashi tayi wanka tafito falo koda ta fito taji hayaniya ta leka har sungama komai sun shige ciki sai hayaniyarsu kawai takeji tabe baki tayi takoma tasanya tashar bollowood tana kallo ko ajikinta shidaman Dr tun Safe yayi wanka yafice suna chan suna tsara yadda za'a tafi dauko amarsu ta ango.
Azurmi ma shima abunda ya gudana kenan domin ana hada hadan saukewa da dorawa ita kuma Amarya Safeena tana gidansu Aisha ita da kawayenta suna sitting cirewa kawai take tana zurawa chan bayan sallar azahar iyami tazo tatafi da ita gidan baffanta usuhu aka kaita yamata nasiha wanda tuni Safeena tafara kuka sun kawo kofar gidansu kenan sai ga motocin daukan amarya guda goma sha biyu hadaddu domin ba motar banza tahir da taufiq da jabir da Gidado,da sauran abokansu dai sukazo Tahir ne shugabansu.
Cikin gida akayi da Safeena domin kaita gun Abbanta yamata Nasihan zuwa gidan miji.
Commet
And
share
*Janaf*✍
🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀
*NA TAFKA KUSKURE!!*
🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀
*NA*
*Janaf ce*✍✍
DEDICATED TO *My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*
I so much luvs u my momma😍😍
*INTERLLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*{onward together}*
*{we give the the Reader's of ours the best out of the bests,,,Our inks are melodious and dropping a kinda light to reader's}*""""
*THE PEN OF LOVE*😘
*HEART OF TOUCHING*❤ *TEARS OF SORROWS*😭 *CURDLES*🙂, *GIGGLES*😁, *AND MARRIEGE THINKS*💑
*JUST GIVES US A FOLLOW*✔
_ina kike kawata kawar arziki kawar mutumci kawar anguwace mai matukar muhimmanci,kunsan me kullum sai mun hadu ammh ji muke kamar bama haduwa,kinsan kanki maryam muhammd ce kisani jamila na miki son kauna_
*23*
------Kai tsaye dakin Abbanta aka kaita wanda yake ciki domin anfadamai za'a tafi da safeena ita kadai aka bari dashi tana durkushe agabanshi sanye cikin dogon farin hijabinta tana kuka.
Abbah yayi gyaran murya Yace"Safeena kibar kukan nan hakan ki saurari nasiha mafi daraja da tsada daga mahaifinki wanda rashin sauraran zai sa kirasa abubuwa dadama arayuwarki"Yadakata cak kuwa kukan safeena yadauke Abbah yacigaba da cewa"Rana bata karya sai dai uwar diya taji kunya hakika yau ranar da amanarki zai fita ahannunmu yakoma ahannun mijinki to nasihata agareki yake yata shine na farko kiyi biyayyah zuwa ga mijinki ki kasance baiwa agaresa shikuma yazammiki ubangida kibisa sau da kafa domin aljannarki tana karkashin kafansa ne yake yata kada kizama mai bijirema bukatar mijinki akoda yaushe kisance mai goyamasa baya aduk abunda yasa gaba kada kisance mai gardama agaresa kuma kar ki kasance mai saurin fushi agaresa ki koyi mu"amala da kowa ki kyautatama yan'uwa sai kema ya kyautata naki ki girrmama abokiyar zamanki sai itama ta girmamaki domin keki ka auran mata miji kina kasa da ita sannan abu na karshe ki girmama mahaifiyarsa da kakarsa kamar yadda zaki giramamu Safeena ki kaunaci Safwan da duk abunda yadanganceshi to inkikayi haka kin rabauta duniya wa lahira yata'yafada muryasa tayi rauni safeena ta fashe da kuka tace"insha Allahu Abbah namaka alkwarin baza kasameni mai saba umarninka ba'Abbah yace"Nasani Safeena bazaki bani kunya ba tashi tashi asada ki da dakin aureki na har abada"Yafada yana mikar da ita tana mikewa ta rumgumesa kam tana kuka hannunta yakama ya sanya mata karamin al'qur'ani izu sitti kafin ya kira iyami yace suzo su fita da ita shikanshi hawayene ya gangaromai na rabuwa da yarsa mafi soyuwa agaresu su iyami suka banbareta jikin Abbah da kyar sunkusa fita yadaga murya cikin rauni yace"abunda na baki ki rikesa da kyau duk halin kuncin dazaki shiga to karki manta dashi domin shi din haske da warakane ga duk wanda ya rikesa ku tafi ubangiji ya kaiku lpy yakuma sanya Albarka arayuwar rayuwanki"Yanagama fadar haka yajuya baya hawaye sun gangaro masa haka aka fice da ita tana kuka gun Ummi aka kaita wanda tun shigowarsu take kuka ana bata hakuri iyami tace',zainabu lokaci na tafiya kisama yarki albarka "Ummi tace cikin kuka tana dafa kan Safeena dake durkurkushe gabanta tace"Duk nasihar da zan miki yan uwana da mahaifinki sun miki nidai abu daya zan gayamiki kibi mijinki kibi mijinki ki mai biyayyah kada daga karshe ki kasance mai tsafta da kamshi akoda yaushe sannan ki girmama mahaifiyarsa da kakarsa in kika kuskura kika saba musu Safeena ban yafe miki"Maman Aisha tace"Ashsha maman Safeena"Ummi tatashi tadago safeena ta rumgumeta suka kamkame juna Ummi tace"ku tafi yata Allah yabaku zaman lpy yasa i gidanki kenan har mutuwa Allah ya miki albarka na yafemiki duniya da lahira"Allah sarki rayuwa duk mai tsausayi sai da yayi kwallah dakyar aka rabasu ummi na kuka safeena na yi haka Usman dakyar aka bambare ajikin safeenar aka sanyata cikin motar tahir wanda iyami da inna husai da maman Aisha suka sata a tsakiya sauran motocin kuma jama'a sukai ta shiga abu mamaki chan naga zugan Janaf novels and fans sunci ankosu na perper less blue and pick sundaura head pick su mom khadija mom Amira my xee Abi my juree name sake sahiba gun shiga mota harda faduwa😂😂😂 hakika sun bada kala domin kaf dinsu sun halarta ba wanda aka bari gadin gida wow.. Chan naga yan Na tafka kuskure fans suma sun kame awata jeep chan kuma na yan kungiyata Interlligent writers association suma da nasu gayyar suna sun kame awata bakar corrolla x hadaddiya na rike baki nace"Tab. To yaushe suka zo nibanma san zuwansu ba nima dai na lallaba na shige motar kawayen Amarya kada atafi bani.
Karfe 4:00 dai dai muka dau hanya sai fatan Allah yakaimu lpy.
_KADUNA_
Karfe 8:39 da muka shigo kaduna domin dai ba'ayi wani gudu ba domin Dr ya tsawartar yace"Kada ajamai asarar da baiyi niyya ba dole aka lallaba dasu ahankali ammh ina kallon yan janaf fans sai da suka ce atsula gudu dasu domin motarsuce akan gaba nidai nace to Allah yasa kada haj.Mama tace nayomata zuga😛.
Magadi najin hon yabude get motoci suka dunga sulalawa jiki aikuwa kikaji guda na tashi domin haj.Mama najin hon tayi waje matar kawu bala kuwa ta dinga sakin guda abun sai wanda yaji haj.Mama ta bude murfin motar amarya iyami ta fito da ita haj.Mama ta waiga tace wai ina matan ne banji guda na tashi bane ai kan hajiya tace me kuda ya kacame gidan domin yan janaf ma ba'a barsu abaya mussaman murya mom khadija data Name sake tafikowa murya sahiba kuwa muryanta kadai akeji gida ya hautsine da murnan isowar amarya hajiya ta rike Amarya tana fadin"Aminiya kin biyashe ni domin kin kawomin safeena har gida ina kara godiya"iyami tayi dariya tace"hajiya duk mu godema Allah domin shine abun godiya"Haj.Mama tace hakane kam bari tashiga shashen hadiza tukun kafin taje barayinta tako amarsu kinzo gidan karamci gidan mutumci da amana tako da bismillah Amaryan Safiyanu tako da izinin Allah aifa nan aka dau sowa da guda anayi har shashensu momma itadai Safeena tana dunkule cikin hijabi tana kukan rabuwa da iyayenta.
SAKINA Na daki taji dirin motoci zuwanchan kuma sai guda ta ko'ina taji abun yawuce misali shiyasa ta fito ta isa ga windon falo ta leka sai ko taga tawaga guda ga haj.Mama rike da wata lullube cikin hijabi ana ta guda gabanta yafadi ras'ras lokaci na farko tareda rawan jiki a idonta aka wuce shashen su mommah jikinta asanyaye ta saki labule takoma kan kujera ta fada yaraf tana auna abubuwa akwanyarta ta tuna kalaman Dr _kudinki ne aure zanyi nabaki ki siyi ra'ayinki_ tatuna kuma abubuwan da ake tayi daga jiya zuwa yau ana shagalin biki ta tuna sanda taji wata nacewa"Brka da zuwa amarsu ta ango"zuciyarta ta buga lokaci daya tareda mikewa tana dafe kirji tace afili"Kardai da gaske auren Safwan yayi..........
_topha karakara ga akuya ga kura.....Koya zata kasance muhadu a shafi na gaba_
commet
And
Share
*Janaf*✍
🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀
*NA TAFKA KUSKURE!!*
🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀
*NA*
*Janaf ce*✍✍
DEDICATED TO *My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*
I so much luvs u my momma😍😍
*INTERLLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*{onward together}*
*{we give the the Reader's of ours the best out of the bests,,,Our inks are melodious and dropping a kinda light to reader's}*""""
*THE PEN OF LOVE*😘
*HEART OF TOUCHING*❤ *TEARS OF SORROWS*😭 *CURDLES*🙂, *GIGGLES*😁, *AND MARRIEGE THINKS*💑
*JUST GIVES US A FOLLOW*✔
_*Congratulation for u completing ur amrzing special and educating Novels Naja'atou and Anty sainah Ummi meenal, DUK TSUNTSUN DAYAJA RUWA DA MUHIBBAT ina fata abunda kuka fada dai dai Allah yasa albarka kuskuren dake ciki Allah ya yafemaku hakika kun zuba dukkan basirarku da hazakarku wurin ilimatar damu da nishadar damu harda ma fadakarwa.ina So kusani kowani bugawan Numfashi na kuna cikin kalbina janaf na muku son kauna*_
*24*
Sai kuma takoma ta zauna tana cewa"Haba yama za'ayi safwan yayi aure haba nasan waye safwan mutum ne mai ra'ayin kanshi mace fiye da daya bata cikin tsarinsa"dariya tayi tace"Haba ni nasani"Kamar wata mahaukaciya tajawo waya tana dannawa ammh abun mamaki kowani dakika zuciyarta na bugawa takasa yarda da abunda kunnanta yajimata karfin hali kawai take.
Sukuwa tawagar Amarya suna shiga kai tsaye gaban momma aka direta haj.Mama tace"Samata Albarka Hadiza samata albarka da bakinki mai daraja"Momma tayi mirmishi tadafa kan safeena dake durkushe gabanta cikin hijabi tace"ina miki barka da zuwa ya ke yata ubangiji yasa albarka arayuwar aurenku da safwan"Tafada idanunta sunkawo kwallah anata amsawa da Amin cikin tsausayawa haj.Mama tace"Bar kuka hadiza da izinin Allah safeena haskece agaremu"Iyami ta amsa da "Insha Allahu maryamu sai ance gwara da akayi"Nan fa akayita addu'an zaman lfy agaresu gabakidaya sai ga haj.Mama tadauko turare ta hau fesema amarya ana sakin guda guri ya dau sowa kowa na fadin Allah barna ke Hajiya mama.
Sun dan jima ashashen su momma kafin hajiya ta musu jagora zuwa shashen Amarya suna tafe ana guda sakina na zaune taji hayaniyar na ta karuwa kuma kamar shashenta ake dosowa bata gama mamaki ba suka shigo haj.Mama agaba tana kwarara sallama Amarya da tawagarta suna baya Sakina dake rike da waya batasan sanda wayar ta subuce ba ta fadi kasan tayels din dake falon ba mike idanunta sun fito jikinta na rawa tana kallon jama'a dake shigowa da guda bata gama mamaki ba taga hajiya mama ta nufi dayan bedroom din dake kusa da nata tasa makulli zata bude Sakina bakinta na rawa tace"Am....Am....Nace ba'Tafada murya na rawa hajiya ta dakata ta juyo tana kallonta kan tace"oh...Na manta iyami ku fara isa da ita gun uwargida ku mika amana yadda ake na al'ada"Tafada harda dariya iyami tace"hakane tako ja hannu safeena dake rike da kawarta Aisha sai gaban sakina dake tsaye kamar mutum mutum aka dukar da ita inna husai ce tace"uwargida ga Amanar kanwarki nan ku hade kai ku zauna lpy da juna shine kwanciyar hankalin mijinku"tafada tana kallon Sakina,Sakina ta zura ma safeena dake durkushe gabanta ido tana so tababbatar da ba mafarki take ba Hajiya mama tace"Ta karba Allah ya tayamu rikewa ku karasa da ita ciki kunsan uwargidan akwai mulki"Tafada harda shewa jikin wasu yayi sanyi domin sudan fahimci cewa sakina bata cikin hayyacinta,haka suka mike suka rankaya dakin safeena iyami tace"Kishiga da kafar dama safeena kiyi addu"an mutuwa ce zata fitar dake"Gyada mata kai Safeena tayi hawaye na kwaranyomata.
Hajiya mama data tsaya abaya saida taga kowa yashige kana ta kalli sakina dake tsaye dafe da kirji tace"Ahayyyye....Rana bata karya sai dai uwar diya taji kunya,nasan kina tunanin mafarki kikeyi ko? to kibude idanunki da kyau ba mafarki kikeyi ba da gaske Safiyanu yayi aure da Amaryarsa safeena itace aka kawota yanzu wannan shine amsa abunda kika taba fadamun watannin baya,kin manta ko? to bari in tuna miki kince in zan iya yima jikana maganin matsalarsa nace miki bani da ikon yayesa masa mtsalarsa ammh ina da ikon kawo masa wacce zata iya yayemasa"Hajiya mama ta dakata kan tacigaba da cewa"To yau shine ya tabbata....Ni maryama duk wanda yaci tuwo dani miya sha Nasan ko ahaka na barki kingane kuranki"
Tana gama fadar haka tayi shigewarta dakin safeena tana fadin"ya banji guda na tashi bane kudaina daga kafa fa" Ai sakina lokaci daya taji wani abu ya dira bisa kirjinta ya gangara har sassan jikinta kafafunta suka hau rawa lokaci dayata zube akasa tana dafe kirji cikin karaji tace"Na shiga uku nalalace ni sakina aure"Tafada da karfi to dayake hayaniya yayi yawa ba wanda yajita sai yan aikinta dake kichen suka rugo suna tambayata lafiya abun mamaki sakina ce ke hawaye idanu biyu tana girgiza kai tace"Never wlh it can happen...Kai haba bazai yuyuba wlh sam"tana fadi hawaye na kwaranyomata masu zafi da radadi so take ta karyata abunda taji kuma ta ganine ammh saboda dakiyar zuciya takasa yarda din.
Suna ta mata sannu ko kallonsu batayi ba tamike dakyar tana dafa bango tashige daki tana fadin"Ina never 4ever wlh...Ni din kishiya tab wlh badai niba"tana fada tabuga kanta agaru ta fashe da kuka mai tsuma rai tana bubbuga hannunta agaru tana ta surutai"Na shiga uku ni sakina kardai ace da gaske ne sai kuma tayi shuru sai chan tace'kodai wasane wanine adanginsu yayi aure"Sai kuma chan tace'to ai hajiya bazata min karya ba "Sai kuma chan tace"Wlh da gaskene wayyo ni sakina na mutu na lalace tafada tana sulalewa akasa tana kuka mai cin rai.
_Ho ho chai chai diz girl kinada hauka taurin kan sakina na burgeni don ubanki kiga amarya da idanunki kiki yarda saboda muguwar taurin kai zaki yarda in kika ga Dr ya shige dakin amarya Addabun Arab inji mrs ibrahim_
Adakin amarya kuwa anata yaba dakin sabida yadda ya tsaru kowa sai san barka yake nan fa aka shiga shigowa da abinci kala kala da abunsha aka baje ana dibar girki ana hira safeena dai ko kadan bata ciba domin har yanzu kuka take muryanta ya dishe sai wuraren sha daya suka baro shashen safeena aka bar safeena da kawayenta sukuma iyaye suka koma barayin su momma.
Su kuwa su Dr tahir suna ijiye tawagar amarya suka juya gidansu tahir suka wuce domin chan suke daman suka iske ango na jiran dawowarsu sun tabbatar mai da amarya ta iso cikin aminci da salama ajiyar zuciya ya sauke kan yace"Ina ta kiran wayarta tana ringing but no answer tahir ne yace"To sai kayi hakuri gobe in mun kaika domin amarya harmuka zo kuka take"Kuka safwan yafada yananuna damuwa Tahir yace"Eh...kukan rabuwa da gidamana Dr safwan yakoma ya kwanta yana cewa"Allah yasa tabar kukan nan cos bani son ciwon kai yakamamin ita'!shekewa sukayi dadariya Gaddafi yace"Shege nawa karka wani damu gobe zaka fanshe kaji abokina"Kara fashewa sukayi dadariya shikuwa banza yayi dasu kusan kwana sukayi suna mai shakiyanci.
abangaren su hajiya mama sunkwana cikin farinciki da Annushuwa haka bangaren ango da abokansa bangaren Amarya ma sai dai muce Alhamdulillah domin kowa yakwana cikin murna safeena ce ta kwana da ciwon kai saboda kukan data sha bangaren Sakina kuwa kwanan zaune tayi domin barci sai da kwanciyar hankali gashi wayarta taki tashi balle takira hajiya kari a idanunta aka kira sallah asuba idanunta sunyi ja sun kumbura saboda kuka ana shiga sallar asuba tazare key din mota ko mayafi bata saba tafice tanajin hayaniya adakin amarya ammh ko kallon gurin batayi ba tafice da sauri motarta tafada ta bata wuta afusace take dannah hon habu megadi dake sallah sai da ya sallame saboda firgici ai yana ganin Sakina cikin halin kamar mahaukaciya yayi saurin budemata tafice dawani mahaukacin gudu tsaye yayi yana dafe kai kafin yarufe yakoma yakara tada sallah.
.Katsina ta nufa da asubahin nan tana ta zuga gudu ahanya domin sam bata cikin hayyaacinta itadai burinta ta isa ga mahaifiyarta ko ta fada mata cewa karyane safwa baiyi Aure ba.
Koda gari ya waye ba wanda yabi takan sakina balle yasan bata nan abun kari mai rai da lafiya akayima bakin zurmi dakyar inna husai ta mtsama safeena taci abinci tasha magani ta kwanta don ta huta karfe biyu nayi masu kidan kwaryan da hajiya ta hayo suka iso tuni suka baje atsakar wuri suka fara sakin kida nan wuri ta hautsine hajiya mama ta shge fili tana tikar rawa ana mata manni tayi shar cikin leshinta ciki da alaku🤣🤣🤣kai yan zurmi sunga rawan banjo ai hajiya da chashe iya chashewa momma na gefe tana dariya domin tasan yau ranar farincikin hajiya safeena da Aisha kadai aka bari adaki su kuwa sauran suna wurin kidan kwarya ana cikin kidan ne saiga motar Dr Safwan tasawo kai cikin gidan shida tahir wanda tunda suka doso get din gidan sukaji kida na tashi .
Da mamaki Dr Safwan ya bude murfin mota ya fito wuri ko yadau sowan ga ango nan ga ango nan jin haka yasa hajiya mama tafito cikin fili ta nufi Safwan tanamai dariya.
Commet
And
Share
0 comments:
Post a Comment