-----Tana isa kusa dashi ta rikosa tana fadin"Oyoyo safiyanu ango Safeenatu barka da zuwa tana fadar haka tana jansa zuwa filin rawa jama'a nata rangada guda suna isa tsakiyar Filin tace"Anchanza salon kida ga ango ya shigo flil baki safwan ya sake kan yayi mgana sunfara kida kwaryan tako ina yana tashi sunayi suna fadar sunanshi da safeena haj.Mama ta rikeshi tana rausayawa shidai binta kawai yakeyi guri yadau ihu da sowa shikuwa tahir manni yahau zuba musu yana yi yana daukansu video ana tafi kai yan kida sunkwashi naira dakyar Safwan ya yakice ya fice afilin yana zufa yana jinjinama hajiya mama daru to a ina tasan masu kidan kwarya _Niko nace kana wasa da hajiya mama_
sai alasar aka gama kda suka tafi suna godiya da tarin alkhairin dasuka samu suma yan biki suka fara shirin komawa yan zurmi mota guda Safwan yasamo aka maidaasu bayan Safeena tasha kukan rabuwa da yan'uwanta da Kawarta Aisha safwan yacikasu da kudi itakuma momma da hajiya mama sun cikasu da abun biki sun koma suna labarta karamcin yan kaduna,Yan safana kadai suka rage sai gobe zasu tafi Safeena momma ta rikota tun bayan tafiyar yan zurmi suka shga takaita har dakinta tana rike da Adli safeena tasa hannu ta amsheshi bai mata kiyuyaba yako je gunta ta tsuramasa ido kaunarshi na ratsata shima ita yake kallo yana bamgalamata dariya itama batasan sadda tayi dariyar ba ga guntun hawaye a idonta.
_KATSINA_
karfe bkwai da rabi Sakina ta isa gida saboda tayi gudu ahanya sosai shikanshi mai gadin gidan nasu sai da ya firgita da irin hon din da sakina ta dinga saki shiya fito da kwamishna daga daki wanda yaji abun yawuce misali yana saukowa falo yaci karo da sakina wurjajan bako mayafi kamar mahaukaciya tana kiran"Hajiya....Hajiya safwan ya kasheni"kwamishina yadakamata tsawa yace"KE.....Sakina"Yafada yana saukowa daga saman benen Hajiya kari dake daki taji kamar muryan sakina nakiranta kuma taji muryan Kwamishina ai da hanzari ta sauko kasa zani na neman faduwa abunda taganine yakusa sata faduwa sakina ce durkushe tana rafzan kuka ga kwamishina yana ta tambayanta taki mgana ai da sauri hajiya kari ta karisa tana fadin"nashiga uku ni karima sakina lpy meyake faruwane"Tafada tana rikota ai da gudu sakina tafada jikin hajiya kari tana fadin"Hajiya safwan ya cuceni yaci amanata yamin kishiya"Tafada tana fashewa dawani kuka haj kari ta zabura kamar taga abun tsoro tace Tana dafe kirji"na shiga uku wani safwan din ne yayi aure"tafada tana kallon Sakinar sakina tace cikin kuka "Hajiya aure dakika sani Safwan kishiyamin bansaniba"haj kari tace"kan bala'i ammh safwan anyi tsinanne wlh.....Kice tsinanniya mara tunani"Kwamishina yafada ransa abace hajiya kari tayi zuru tana kallin kwamishina kan tace"Ni ce tsinanniya kabiru"yace"Kwarai kece inbanda rashin ilimi mutum yayi aure kice masa tsinanne!Sakina ta shanye kukanta hawaye dai baidaina zubaba hajiya kari tayi tsam kawai tana kallon ikon Allah yajuya ga Sakina yana fadin"Ke shashasha mara tunani don ubanki me na fada miki kwanaki"Yafada rai bace sakina tace murya na rawa"kace karna sake dawowa gida da sunan amun wani abun"Yace"to me yazo dake"Tace"dady amanata fa yaci yayi aure bansani ba"Kwamishina yace"ungo naki yamata dakuwa kan yace dan gidanku ke amanarsa nawa kikaci to billayil lazim ki ka kuskura kika kaso aurenki na rantse sai dai kinemi wani uban bani ba"Yafada da kakkausan murya hajiya kari data daskare tun dazu tace"Haba Alhaji acuci yarinya kana ka hanata yin kuka ga dan iska chan.....shout up....!yakatseta da tsawa kan yace"Na rantse karima kika kara samin baki saina ci mutumcinki"Haj kari ta rike baki kawai tayi shuru saboda ganin yadda kwamishina ke huci.
Yajuya zai wuce yace"Ba wacce tatabamun yaji agidana sai ke saboda kece baki dauki aurenki da daraja ba wlh saboda abun kunyan dakikeyi gidan mijinki kunyan yaron nan nakeji duk sanda yakirani.....to kibde kunnu da kyau kjini kijirani yanzu zan shirya muje na maidaki wlh tallahi Allah daya ko inkika sake kika kashe aurenki sai kingane kurenki sakarya wacce batasan meyakemata ciwo ba"yana fadar haka ya haura sama.
Sakina ta fashe da kuka tace"Hajiya ki taimakeni kada daddy ya maidani wlh baran juri ganin safwan da wata mace ba"hajiya kari ta jawo ta jikinnta tace"Bar kukan nan sakina kada kisa nima nahau yi fa kimanta kece sakinar nan mai aji da kwalliya da dakiyar zuciya"!sakina takara fashewa da kuka tana jin zuciyarta ta kusa bugawa kamar zata mutu kan hajiya kari tasamu zarafin mgana Kwamishina ya fito cikin shirinshi shadda harda babban riga yace"oya taso mutafi....Ke karima samamata mayafi bazan maidake a haka ba!sum sum tashiga daki tadaukomata ta yafamata sakina na hawaye ta fice haj kari tace"Alhaji....ya waigo yace"Bakiji ba kenan"Jin haka yasa tayi shuru har suka fice sunisu direba ya tukasu suka kama hanyar kaduna.
Hajiya kari tayi tsuru zaune afalo kan tace"komai ya dagulemin lokaci daya na shiga uku ni karimatu.
_ai komai ya gama kwabemiki haj.Kari sai dai hakuri_
commet
And
Share
*Janaf*✍
🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀
*NA TAFKA KUSKURE!!*
🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀
*NA*
*Janaf ce*✍✍
DEDICATED TO *My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*
I so much luvs u my momma😍😍
*INTERLLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*{onward together}*
*{we give the the Reader's of ours the best out of the bests,,,Our inks are melodious and dropping a kinda light to reader's}*""""
*THE PEN OF LOVE*😘
*HEART OF TOUCHING*❤ *TEARS OF SORROWS*😭 *CURDLES*🙂, *GIGGLES*😁, *AND MARRIEGE THINKS*💑
*JUST GIVES US A FOLLOW*✔
_*wannan page din naka ne dan uwana rabin jikina rabin raina bugawar zuciyata da Numfashina murmishi da dariyata SCIENTICS JAMILU UMAR Hakika kai dan uwane mafi daraja agareni domin dama da'akayi jamilu ne akayi jamila kuma daman Jamilan ta jamilune*_
_Addu'ata agareka kullum bata yankewa Allah ya taimake ka yabaka nasara ga duk abunda kasa gaba yabada sa'ar rayuwa duniya da lahira_
*26*
-------Tafiyar yan zurmi ba dadewa su kwamishina suka iso wanda sakina tasha kuka a mota kamar ranta zai fita kai tsaye shashen su momma ya Nufa shine agaba kana sakinar abayansa haj.Mama na falo zaune itada iyami wacce sai gobe zasu tafi suna hira kwamishina yayi sallama ya shigo sakina na biye dashi a baya da mamaki hajiya ta mike tana mai maraba cikin mamaki sakina durkushewa tayi anan tana kuka mai tsuma wanda ke sauarare hajiya mama tace"kabiru lpy kuwa naganga a gaggauce"Kwamishina yace"Lpy kalau hajiya wannan yarinyarnan ce tazo gida tun safe tanama mutane kukan banza,ina fatan safwan na nan"Hajiya mama tarike baki tana kallon sakina kan tace"Ikon Allah kabiru kaga muko ko fitarta bamu sani ba,bashi gida sai dai ka kirasa awaya"Kwamishina ya ciro waya yana fadin"Iz ok hajiya yimin mgana da hadiza don Allah kuzo mgana zanyi daku yanzu ina saurine"Hajiya mama da iyami suka mike suka wuce cike da mamakin sakina wacce ke durkushe tana kuka momma ma tayi mamaki da hajiya ke fadamata zuwan kwamishina hakama safwan yaji lokacin da ya kirasa to daman bayan sungama sallaman bakine suka wuce asibiti ahanzarce ya shigo mota ya taho
Afalon su hajya aka zaune da momma da sakina da hajiya mama sai Safwan wanda ke gefe yana kallon yadda sakina tazama kamar tsohuwa saboda tashin hankali gyaran murya kwamishina yayi kan yace"Don Allah hajiya kuyi hakuri da halin yarinyarnan nasani tana bata muku sosai ammh kuyi hakuri mussanman kai Safwan don Allah kayi hakuri"Safwan ya sunkuyar da kai yace"Dady bbu komai wlh kaima kayi hakuri nayi aure baka sani ba abun ne yazo agurguje"Kwamishina yace"Masha Allahu wannan ai karuwace ubangiji Allah yatayaka rIko bbu komai safwan...Gatanan na dawo da ita hajiya ku shaida wlh in sakina tayi abunda safwan ya saketa wlh sai dai ta nemi wani uban bani ba gabadaya yarinyarnan tafita zakka a gidana halin uwarta kaf ta debe to billahil azim daga ke har ita inkukayi abunda kuka kashe auren nan wlh dukkanku sai kun raina kanku" yana gama fadar haka yace"Hajiya dake hadiza gatanan nadawo da ida don Allah ku kara hakuri don Allah"Hajiya mama tace"Bakomai kabiru Allah ya kyauta kawai"Yadakamata tsawa yace tashi kibani guri mutuniyar banza kawai"Da gudu sakina tatashi tana kuka ta fice hajiya suka bita da kallo tana tuna rabon dataga sakina cikin wannan yanayin lalle auren ya bugeta.
Kwamishina yasa aka kiramasa safeena ya hadasu da Safwan ya musu nasiha mai ratsa jiki kan su zauna lpy yana tashi tafiya ya ijiyema su momma dubu hamasin ya wuce direba yaja suka wuce ko takan sakina baibi ba.
Safwan yadade tsaye har motar kwamishina tabace mashi kafin jiki asanyaye ya shige barayinsu kai tsaye dakin sakina wacce ke kwance kan gado tana rafzan kuka mai tsaya azuciya yadade tsaye yana kallonta yauce rana ta farko da safwan yaji tsausayin sakina ya tsirgamai asanyaye ya karisa kusa da ita yasanya hannu ya rikota tadago tana kallonsa idanunta sunjajur dasu kurama juna ido sukayi na tsawon lokaci kafin ita ta jaye idanunta tayi saurin saukowa daga gado zata wuce yayi saurin riko hannunta tafada jikinsa ya rumgumeta tadinga dukan kirjunsa ammh yaki sakinta dole tagaji tadaina tayi lamo tana kuka shafa kanta kawai yake yana fadin"Srry....banyi wannan auren don na batamiki ba sakina kibar kuka hakanan"Ina saima kara volume take shdai sai aikin lallashinta yake ammh tatafasa batace maiba shiya yimata wanka ya shiryata saboda yadda tazama cikin kwana daya tal,Ita dai kukan ta kawai take ko kallonsa batayi shiyaje shashen su momma yataho da safeena bayan su hajiya sunkara musu Nasiha.
Dakyar da sodin goshi sakina tayarda ta fito falo inda safeena ke zaune tana jiranta tana zuwa tazame daga kan kujera tana gaisheta zuramata jajayen idanunta kawai tayi ammh tak batace mataba to shima kanshi Dr shirun Sakinar yafara batamasa rai haka dai ya musu nasihan su zauna lpy yakuma fadama safeena ceWa sakina yartace kada yaji ko yagani ta rainata ita kuma sakina yace takama girmanta itace babba kuma tasani in tazauna lpy to kamar ta taimakeshi ne mganar raba girki kuma yace tafada kwana nawa za"a raba shuru ta musu kawai idanunta na kallon kasa kwallah tataru a idonta kawai sai tatashi ta wuce dakinta wanda tayi hakane kada kukan datake boyewa ya bayyana.
Dr Safwan yabi bayanta da kallo kafin yayi ajiyar zuciya yadawo da kallonsa kan Safeena wacce ke durkushe kasa tana wasa da gefen hijabinta yayi shuru kawai yana kallonta jikinta ne yabata ana kallonta shiyasa tadago karaf suka hada ido ammh me sai taga kamar ma hankalinshi bai tareda shi sam tsuramasa ido kawai tayi tana jin badadi domin ta fahimci Antyna nata bata karbeta amatsayin kanwarta ba.
Hada ido sukayi da ita yayi saurin sakarmata mirmishi kafin ya mike yace"Yan matana don Allah ban minti biyu "yana fadar haka ya bi bayan sakina yana tura kofar yaganta zaune kan sofa ta chusa kai agwiwan kafafunta kai tsaye yakira sunanta tadago da sauri idanunta na fitar da ruwa tace"KA FITA SAFWAN KA FITA BANA SON GANINKA KA FITA NACE!!!tafada cikin karaji idanunta na zubar da kwallah Safwan yayi jagale yana kallonta yabude baki zai yi mgana kenan ta mike tace"KAFITA NACE KO!!!"tana zaremai ido kamar mayya ya lura tarasa natsuwarta dat why yace"iz ok zan fita shikenan ko"yafada yana kallonta juyamai baya tayi tana jin zuciyarta na zafi kamar zata fashe cikin tsausayama sakina ya fice yajamata kofa yadade tsaye kafin ya karisa kusa da Safeena yasa hannu yadagota kawai ya rumgume yana jin shima kamar ya kurma ihu Safeena tanajin yadda zuciyarsa ke fat fat kamar wanda yayi gudun tsere,ahaka yakarisa dasu har dakin safeena gafen gado ya zaunar da ita yana kallonta da shanyayun idanunwa wanda babukomai acikinsu sai zallah desire yace cikin wata murya"yanmatane kidan jirani kadan yanzu zan dawo"Yafada yana rikeda hannunta da kai ta amsa kan tace"Tom adawo lpy"Mirmishi yamata kan ya saketa yafice da sassarfa,bayansa da Safeena tabi da kallon tana jin tsausayinshi da wani sonshi na kara shigarta tayi alqawarin bashi dukkan goyin baya wurin yaye damuwarshi.
Commet
And
Share
*Janaf*✍
*NA TAFKA KUSKURE*
*NA*
_*Janaf ce*✍_
© _INTERLLIGENT WRITER'S ASSOCIATION_
_*ROMANTIC AND SEXY NIGTH*_
_plz duk wanda yaga abunda bai masa ba awannan page din yayafemin banda zabi ne gaskiya kunsan kuskuren dan Adam_
_27_
-Yana fita ya shiga mota sai yahuza suya ya siyo gasassun kaji guda biyu yakamo hanyar komawa gidane kiran tahir ya shigomai yana dagawa tahir yace"Sannu batulu shikenan mun gama ma wahala ko aneMemu ko"Tsaki safwan yaja yace"plz Tahir kakar matamin rai ina alfahari da wannan daren...Kunyi naku nikuma ku barni nayi nawa mana"Tahir yace"Rakiyar siyan bakin kai kadai zaka"Safwan yace"Kai wani irin nadawane yaushe kaga ana wannan kauyancin wai siyan baki to ni tuni na siya baki kayata bani bukata kasha zamanka kakula da asibiti kan ingama hutun amarci gwaro na"Yafada yana dariyar keta Tahir yace"Kan ubanchan Allah ya isa"Dr yace"× 2 nima wlh"Yana fadar haka ya kashe wayar yana dariya.
Tahir kuwa chilli yayi da wayar kangado yace"Na rantse nima auren nan zanyi kodan innuna ma gayen nan kuskurensa"Yafada yana fadawa kan katifa kan yace aransa"Gaskiyan Dr Safana yau Daren Alheri ne agaresa niko yaushe zan yi katari da wannan daren alhairin. _Niko nace ga Sahiba zan baka dama tuni take sonka_ wani dirty look yamin wanda tasani ficewa ba shiri _sorry sahiba nayi iya bakin kokarina ammh Tahir yaki amincewa kibari zan ma Mallam yahuza mgana ko yana ciki_😛😛😛
Yana adana motarsa a parking space ya shige ciki da sassarfa dakin sakina yadosa yajisa adatse shuru yayi yana jinjina abun kafin ya isa kichen ya bude fridge ya sanya leda daya dayan ledan kuma ya dauko faranti yadora akai tareda kofuna guda biyu ya wuce dakin Safeena inda ya barta nan ya sameta harta zame tadan kwanta karar bude kofan shi yadata ta mike da sauri tana masa sannu da zuwa cikin hanzari ta mike ta isa kusa da shi tana kokarin amsan faranti kallonta yakeyi mirmishi saman fuskarsa yaki bata farantin yanoke kafada yace"Amarya bata aiki koma ki zauna aikin ki na nan zuwa yan matana"Yafada yana kanne mata ido daya mirmishi tayi ta noke kai kan ta koma kan gado ta zauna shikowa ya ijiye faranti akasa ya isa ga fridge din dake dakin ya bude shake yake da madarar hollandian saboda daga shi har sakina abun shansu kenan dat why ko'ina kaduba agidan shi zaka dinga gani.
Dauko guda daya yayi yazo ya ijiye kan yahau bude ledar yana fadin"Sauko yan matana kici daga mijinki"kin tasowa tayi harsai da yagama juyewa acikin farantin kana yataso yazo ya mikar da ita tsaye kan yasa hannu ya zare hijabin jikinta yace yana kallonta"Daga yau na haramtami ki sanya hijabi mutukar muna tare"yafada yana kallonta sunne kai tayi yarikota har zuwa saman kafet din dake dakin ya zaunar da ita yana jawo farantin gabanta naman yayago ya nufe bakinta tayi saurin kauda kai yabata fuska yace"Bana son gaddama Safeena kinsani ko"Jin yafadi haka yasa tayi saurin bude baki ya samata yana fadin"good girl....Haka yadinga ciyar da ita ita kuma kunya yahanata sakewa bai matsa mata ba harsai da tace ya isa ya tsiyayamata madarar yabata tasha shima yaci ammh badayawa ba suna gamawa tamike zata kwashe kayan dasukai amfani da shi yayi saurin dakatar da ita yana fadin"Karki bari na sake maimatawa"Tanajin haka tayi saurin sakarmai shi ya kwashe ya kai kichen yana dawowa yace mata taje tayi wanka kai tsaye tace"Nayi fa dazu"Kallonta yayi yace"Bani son......Bai karisa ba tashige toilet juyawa yayi yana mirmishi.
Dakinshi yashiga shima yafada wankan alwala yadauro kana yafito yashafa mai yafeshe jikinsa da body spry kayan barci yaso yasanyawa sai kuma yafasa kawai jallabiya yasanya ko boxers bai sanya ba yafito yanufi dakin Safeena fuskarsa na fitar da Annuri.
Yana shiga ya isketa harta kwanta harda uban hijabi gyaran murya yayi kan yace"Kinyi alwala ta amsa da eh ya wuce ya shimfida darduma yana fadin"oya taso muyi sallar godiya ga Allah"tana so tace ai itayi nata ammh ganin yadda yahade rai yasa tatashi sum sum tawuce raka'a hudu sukayi kan yadade yana kwararo musu addu'an zaman lpy da juna da zuru'a dayyiba.yamata tambayoyi kan addininta baiyi mamakin amsoshinta ba cos yasan ko wacece ita suna kammalawa jikin safeena narawa ta haye gado tana fadin"Unku mu kwana lpy"Dariya ta kusa kwacemai yace"To yanmata asha barci lpy" tadade batayi barci ba tana tsoron kar ya hayo gadon hardai barci yasaceta shiyasa sai dayaga barcin yadan yi nisa kana yatashi ya kashe wutar dakin ya kunna dumlight kafin ya isa kan makeken gadon ya kwanta agefen safeena wacce ke sauke numfashi cikin kwanciyar hankali rumgumeta yayi numfashinta na sauka awuyansa shiyakara rikitasa lokaci daya ya zare mata hijabin jikinta harda dan kwalin yana shafa gashin kanta cikin jan Numfashi kara kamkameta yayi yana jin wani abu na mai yawo ajiki rumgumar da yayi mata shiya data ita tayi saurin bude ido bata ganinsa sai dai duhunsa bai bata zarafin mgana ba ya yadora harshensa kan lebenta yana mata yawo dashi tsam safeena taji tuni jikinta yafara rawa tabude baki kenan zatayi mgna yasamu nasarar tura harshensa cikin bakinta yana kissin din in romatic way wayyo safeena tashiga hannu manya duniya tuni ya rikitata shima ya rikita kanshi cikin zumudi ya jaye mata sikat din dake jikinnta rigar kuwa dayaga zata batamai lokaci yagata yayi ya yarda da ita yar bireziyan ya fincike nonuwanta suka bayyana wow....Ai safwan ya kusa zaucewa dayaji hannunsa kan na shanun Safeena ai arikice yadinga kai musu damka ita kuwa safeena taji wani dadi na kwaranyomata ai sai tadinga toromai kirjin shikuwa yasamu abun so kawai sai ya kifa kanshi yafara mata sucking cikin kwarewa ai nan safeena tafara nishi sama tana tura hannunta agashin kansa cikin fitar hayyaci yadade yana abu daya kafin yagangaro kan mararta yana shafawa a hankali bata fargaba sai da taga yana kokarin zame mata pant tafara matse cinya safwan yace cikin wata irin murya"karki hanani Safeena plz ki barni"Yafada yana wani jan Numfashi ai tuni safeena tafara kuka domin tanaji yadda joy tick dinshi take mata yawo ajiki domin tuni ya cire jallabiyan jikinshi yazama dukkansu sun hada fatarsu wuri daya dakyar ya fincike pant din yaturama hannu...Shiiii tace cikin azaba fingering yahau yi mata cikin zafi zafi ita kuwa safeena Abba take kira da Ummi domin taji abun ya girmeta gani yayi tana batamasa lokaci kawai sai yadanneta yadoramata Nauyinshi akanta yatura harshenshi cikin bakinta yadatseta kawai ya ware mata kafa yadau hanya dodar yana karanta addu'an da Annabi ya koyar damu in mutum zai sadu da iyalansa yana gamawa yadanna kai da karfinsa duk da yasan budurwace ammh baida zabi inaji Safeena tasaki kara daga nan kuma naji dif sai karan fitar Numfarfashi kake ji...Ni to amun afuwa domin naga abunda bai kamata dole nayo waje.
Ina fitowa naga sakina na safa da marwa bata kofar dakinta bata kofar dakin su Safeena tana kasa kunni hawaye yana mata ambaliya fadi take"Safwan kaci amanata kacuceni yanzu ina gidan nan kashiga dakin wata zaka kwana"Sai kuma chan Tazube kan kujera tana kuka mai cin rai duk ta rame lkaci daya....
Dr S AND S ASHA AMARCI LPY
_Allah sarki sakina kin bam tsausayi yauce rana ta farko tunda na fara rubuta book din nan tsausayinki ya tsirgamin...Srry haka kishi yake_
Commet and share domin kwarin gwiwata
*Jamilatee*✍
*NA TAFKA KUSKURE*
*NA*
_*Janaf ce*✍_
© _INTERLLIGENT WRITER'S ASSOCIATION_
_Na sadaukar da wannan page din gareka kani...Wato kamalu no love dan gombawa kulawarka akaina tamkar yadda yaya zai kula da kanwarsane bbu abunda zencema sai godiya ammh ina so kasani ni janaf ina girmamaka_
~gareki qawata sumayyah basheer kugu bby kina raina wallah...ina mugun ji dake qawar alkhairi~
*zamu yi sauri mu kammallah cos akwai wani aiki agabana kana ga sch plz ina neman addu'anku kan ya taimakeni kan abunda nasama gaba....Yasa Albarka aciki Amin*
~zaku dinga samun post sau biyu arana but banyi promise dinku ba~
*28*
---Shudewar awa biyu kafin Dr ya saurarama Safeena wacce tagama galabaita har kukanta yadaina fita sai dai na zuciya,kamkameta yayi na tsawon lokaci yana ji wani kwallah na ziraromai na farinciki bazai ce komai ba ammh safeena ya tabbata Ta dabamce acikin mata shidai baitaba mu'amala da wata macce ba illah sakina ammh bazai iya dora komai ba akan zamtakewarsu ba illah kawai yaji kuma yasani yau ce rana ta farko da yaji zam 100% yadade rumgume da ita yana mata addu'a tareda lallashi mai cike da soyayah da kauna ta har abada.
tashi yayi yafada toilet yayo wanka da alwala zuwa yayi ya shimfida darduma yahau sallar godiya ga Allah da Ni'imar da yayimasa na samu Safeena acikin dubban mata,yadade yana zuba addu'an kafin yakoma yakwanta kusa da ita yana shafa fuskarta yake fadin"Komai naki mai kyaune yan matane"Yafada yana manna mata kiss abaki.
_gareku yan matan wannan zamanin wlh kukiyaye kanku da biyema mazan wannan zamani to kinaji kuma kina gani mutumcinki shine kikai darajarki agidan mijinki domin samun soyayyah ta har abada wlh tallahi kika banzarta da kanki karema yafiki daraja agurinsa...Allah ya ganar damu Ameen_
Kiran sallar farko Safeena ta farka taga Dr yana kamkame da ita dakyar ta zame jikinta daya mata tsami tana kokarin mikewa azabar dataji ne yasa tasaki kara"ochhu....Shiya farkar da Dr dayake barci yayi saurin mikewa yana riketa yake fadin"ina zaki kiyi ahankali fa kinada rauni"Narke fuska tayi tana sunne kai tace"sallah zanyi..."Tafada cikin shagwaba yayi saurin mikewa yana fadin"Ok...Yanzu kuwa"Kan tayi mgana yana ciccibeta sai toilet cikin bath yadireta yahadamata ruwa masu zafi da kuka da komai yasamu Safeena ta shiga ruwan zafi ruwa biyu ya chanzamata kafin yabarta tayi wankan tsarki,fitowa yayi zashi dakin shi yaga sakina kwance akasa daga gani barcin yadauketane bata shiryaba turus yayi yana kallonta kan ya isa kusa da ita ya dan bubbugata yana kiran sunanta...Firgigit ta mike tana fadin"Don Allah Safwan karka kwanta da yarinyarnan.."Tafada azabure da alama da abun ta kwanta kuramata ido yayi yana kallanta kan yace"meya sameki kike barci anan"Saurin mikewa tayi tana kallonsa kallo na kurullah shima kallonta yake da mamaki afuskarsa cikin fitar hayyaci tace"Ka kwanta da ita ko"Tafada tana kamo hannusa Safwan galala yake kallonta kan yace"wa ..kenan"Tace"Amarya ka don Allah kace baka kwanta da ita ba"kallon cikin idanunta yake kan yaji dariya na neman subucemai yadda yaga tayi wani kalan tsausayi yace"Dama nayi miki alkwarin bazan kwanta da ita bane"Yafada yana hade rai kan ya fizge hannunsa yace"kinga wlh ki natsu sakina kada ciwon zuciya yakamaki don naga kina gab"Yana gama fadar haka ya wuce dakinsa ai sakina sai ta sulale tana fadin"shikenan wlh ya kwanta da ita...Shikenan wallahi safwan kagama kasheni"Haka take maimatawa kamar wata zararriya Kafin kuma tadiba tashige daki tana kuka kamar makauciya sabon kamu.
Wanka ya sake yi yayi alwala massallaci ya wuce saboda yaji an tada sallah koda ya fito baiga Sakina ba tsaki yaja yace"kawai mata kinsa kanki adamuwa kinason miji kika banzarta dashi.
sai da gari yayi sha kana yadawo daga massalaci saboda anyi wa'azi ne shiyasa yadan jima koda yashiga dakin Safeena har tayi wanka tasanya wata bakar doguwar riga kirar armani tana kwance akan gado karisawa yayi yana mata mirmishi kauda kai tayi tana tura baki fuskarta tayi fayau da ita dariya ya saki yana fadin"ok kari kikeso to gyara..In dada miki daman bai isheni ba'yafada yana haurowa gadon saurin dira tayi tana fadin"wash...Yadda taji zafi akasanTa saurin biyota yayi yana riketa yace"oh am srry....Kirinka bi ahankali fa kinsan kina da rauni"Tura baki tayi tace to ba kai bane kace zaka kara ba"Dariya yayi yace"To ai kene naga kinason kari"Tayi saurin cewa"Ni yaushe nace"yace yanzu kika fada'diddira kafa zatayi sai taji zafi sai tayi saurin fadawa jikinsa tana mai kukan shagwaba shikuwa yana mata dariya yana fadin"Zaki sanine...Inkika fama ciwonki baruwa na ni sai dai in kara famamiki shima.
Nan suka lalace tanamai shagwaba yana biyemata Momma ce takirasa tace"ga abun karyanwansu yazo ya amsam musu to yace dakyar ya yakiceta yaje ya amso masa hajiya mama sai wani kallonsa take tana fadin"Ango mijin amarya ansha maiko"kasa kallonta yayi saboda kunyan data basa dundu tabugamai abaya tana fadin"Dan nema sai yanzu kake jin kunyata ko"Mirmishi kawai yayi iyami ke karemai da matar kawu bala Adil ne ya makale masa dole yataho dashi Safeena ta amsheshi tana murna tace"Oyoyo....Dana dakai na kwana arai"Tafada tana chabesa Dr yace yana ijiye kwandon breakfast din"Ke dai fadi gaskiya dashi kika kwana koda baban yaron"Yafada yana wani kallonta hararar wasa ta mai kan tace ashagwabe"ai ni ba ruwa na da baban yaro tunda bai da tsausai"jagale yayi yana kallonta kan yace"To bari in maida yaro...Sai baban yaro yanuna miki ainihin kalan rashin tsausayin"Tana jin haka ta rumgume Adil tana fadin"a'a kana da tsausayi sosai ma kuwa ko yarona"Tafada tana kallon Adil shikuwa ya barke da dariya kamar yasan me ake yi Safwan yakuramusu ido kawai cikin sha'awa da burgewa zuciyarsa kamar zata zama takarda saboda fari.
Atare suka karya suna yi suna hirar kauna shikuma Adil daga yayi tsalle ajikin safwan sai yayi a jikin Safeena shikanshi Adil yasamu farinciki...Allah sarki yaroma kenan.
Sai zuwa yammah suka je shashen su momma lokaci yan Safana zasu tafi haka suka tafi kamar kar arabu Hajiya mama harda hawayenta da suka tafi sun dade shashen nasu shida safeena Hajiya mama tatasu da hirarta shidai danne danne yake awaya bai jinsu sai dai ita safeena ke samata baki sai da sukaci tuwon acchan da momma tayi da miyar kubewa kana suka koma barayinsu wanda dakyar aka bambare Adil ya makale shi sai ya bisu Hajiya ko ta amsheshi da karfin tana fadin"Kai kaga yaro da munafurci yana neman hana ubansa cin amarci"Ai sum sum suka fice da kunyar hajiya mama.
Sakina kuwa kuka ta wuni yi adaki gashi Anty laila ta kirata tana dura uban ashar tana fadamata ita ta zauna harshi safwan din wata tsiyace balle amaryansa da har zata zauna wata kishiya tadagamata hankali to tayi maza ta mike ga kanta tunkan ranar Nadama tazo mata...Kashe wayar kawai tayi tana kara fashewa da kukan ita Anty laila tana wani mgana batsan abunda takeji azuciyarta ba dabata fadamata hakaba ita yanzu bata da Natsuwar da zata gane menene yakamata tayi ita dai gatan nan ne dai bata da aiki sai kuka kullum abincinta hollandian sai ko in tasa yan aikinta sun dafamata indomie shima bada yawa take ci ba taji ya fita ranta kasuwancinta kuwa yayi kasa domin sai kranta ake kayan su yi kasa kuma gashi bata sake yo odar ba to inata ga kwanciyar hankaki tunda Safwan yayi auren nan gabadaya komai nata ya tsaya cak.
BAYAN SATI DAYA
Hakika acikn satin dayan da Safwan da Safeena suka kwashe atare sun gurji amarci iya son ransu wanda Dr ya zabura ya kusa cirema safeena kunya ammh har yanzu da saura sun murji juna wanda dukkansu suka murje sukayi kiba abunsu Hatta Adil yayi bul bul dashi kamar dan turawa,Tsakaninta da Sakeena gaisuwa in tafito falo ammh ko kallonta batayi itada bazata daina gaisheta ba domin ko amusulunci tafita hakkinta tun tana kwana uku agidan tacema Dr zata fara girki tahutar dasu momma haka nan yaso yahana ammh ta dage harda neman yin kuka dole ya barta kullum ita da danta zasu yi ta burumtunsu ita tana aiki shikuwa da rarrafe yaita barna inta kammallah aikinta tamai wanka ita tayi su shige sashen su momma sai kuma Dr yadawo wanda adaddafe yayi hutun kwana biyar yakoma asibiti.
Yau din kuma zai koma dakin Sakina wanda daga shi har safeenar kamar marasa lpy haka suka wuni sukuku dako yadawo bayan sungama taking dinner wasa yake da Adil ammh safeena tayi shuru kawai sai da Adil yayi barci kana yakaisa kan gadon yakwantar dashi kafin yazo inda safeena ke zaune kan stool din gadon ya mikar da ita yana kallonta itama shi take kallon kan kwallah datake boyewa ta gangaro saurin fadawa tayi jikinsa tana fadin"Unku...Shikenan nikadai zan kwana"tafada da sheshekan kuka runtse ido yayi kan yace yana rumgume da ita"Hakuri zakiyi yanmatane daga gobene zandawo mu kasance tare kuma ga danki nan yatayaki kwana"Matse hawayenta tayi dagota yayi yana kallon yadda hawayenta ke sauka harshensa yasa yana daukemata su kafin ya dora harshensa kan lebenta yana zagayawa dashi cikin kwarewa ta bude bakinta ta chafki harshensa ta rike kansa kam tana sumbatarsa cikin shauki da kauna mai dorewa shima kara hade kugunsu yayi wuri daya yana kara damke harshenta sun dade ahaka sai da taga hankalinshi na kokarin barin jikinshi kana tayi saurin fizge jikinta tafada toilet saboda jitayi wani abu ya tokaremata amakogaro yadade tsaye kan ya fice jiki asanyaye yacewa"Kar ki manta da addu"A inzaku kwanta,daga haka ya fice
Tadade abayin domin tagama kukanta wanka tayo da alwala tazo tayi shafa'i da wuturi ta sanya rigar barci tazo ta rumgume danta ta musu addu'a suka kwanta ammh bawai don barci zatayi ba a'a sai don bata da zabi ne.
Shikuwa dakinsa yayi direct sai da yayi wanka yayi sallar sa yasnya kayan barcinsa riga da wando masu ruwan toka masu taushi,ya feshe jikinsa da body spry kana ya nufi dakin sakina ammh sai da yataba dakin safeena yaji akulle kana ya murda na sakina yaji abude yasa kai yashiga da sallama.
Commet
And
Share
*Janaf*✍
🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀
*NA TAFKA KUSKURE!!*
🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀
*NA*
*Janaf ce*✍✍
DEDICATED TO *My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*
I so much luvs u my momma😍😍
*INTERLLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*{onward together}*
*{we give the the Reader's of ours the best out of the bests,,,Our inks are melodious and dropping a kinda light to reader's}*""""
*THE PEN OF LOVE*😘
*HEART OF TOUCHING*❤ *TEARS OF SORROWS*😭 *CURDLES*🙂, *GIGGLES*😁, *AND MARRIEGE THINKS*💑
*JUST GIVES US A FOLLOW*✔
_*wannan page din nakune MOM KHADIJA da MOM AMIRA dake kanki MMANSADDIQ DA FADILA TALBA u guyz kusani KUKARA SANI commet dinku nasani nishadi matuka walle sumar dani yake...Kusani ku kara sani kowani bugawan Numshina kuna raina,ina muku so mai tattare da Natsuwa*_
_INA KUKE YAN AISHA SADA MACHIKA NOVEL HERE IZ URS....KUJI DADINKU KU HUTA JANAF NA MUKU SON KAUNA MAI TATTARE DA NATSUWA_
*29*
-----Dakin yayi dumlum da duhu shiya sa hannu ya kunna makunni wutan abunda ya bashI mamaki yadda dakin yayi kaca kaca chan kaya chan plate din abinci akan gado harda su kofuna da ledojin bickut...Kuma abun takaichi Sakina na zaune atsakiyar gado ta tusa kanta atsakanin kafafunta cikin dakiya ya karisa kusa da ita yana fadin"Shin wai sakina kinyi haukane...Kiduba inda kike zaune fa"dagowa tayi tana kallonsa saida ya razana da ganin yadda idanunta yakoma jawur gashi kan nan dayaji attac duk yafara cirewa gayinan dai ba kyan gani jikin ta kuwa rga da dabam sikat dabam kallonsa take cikin fitan hayyaci kan tace cikin shakakkiyar murya"Bbu ruwan ka da muke damuna mallam ka fice min adaki don na tsaneka"daure fuska yayi kan yace"Bazan fita ba wai ke meke damunki kanki farau kishiya...Oho nazata bani da wani amfani agareki banzaci innayi aure zaki damu ba ai"Yafada yana wani zakuda kafada kukan kura tayi tadiro daga kan gadon ta chakumi wuyansa tace cikin karaji"Daman don kaga iyakata kayi ko safwan to wlh yadda ka ruguzamin rayuwa kaima saina ruguza naka"Ransa ya baci yasa hannu ya fizge rigarsa kafin ya tunkudata ta fadi kan gado yace rai bace"Nafi karfi inyi abu saboda ke Sakina..kina sona kikemin abunda kikemin kike banzarta dani kamar wani wawanki wani dama ne banbaki ba eye..Ammh kika kasa kafa kika shure kekina ganin kin isa kowa to wlh bari kiji infada miki in wani abu yasamu matata wlh tallahi kinji na rantse kotu ce zata rabamu ni dake kuma in kin musa ki kwatanta Nonsess kawai"Yana gama fadar haka yajawo blanket din dake kan gadon da filo ya jefa kasa yashimfida kashe wutar yayi yakoma ya kwanta ransa na masa kuna.
.
Daskarewa sakina tayi akwance kukanma ya kasa zuwa gyada kai kawai takeyi tanaji aranta zama mai ganta ba itace yau Safwan yama wannan bangazan yake kuma yabamata mgana son ransa harda kotuce ce zata rabasu in Tatabamai mata tabdijim wlh yadebo ruwan dafa kansa don kowa agidanan sai ya gane kuransa,kwanciya tayi tana sake saken zucci na yadda zata rama dukkankan abunda aka mata.
Kiran sallar farko ya farka dama akagare yake yatashi ya fice adakinsa yayi alwala kan yafice zuwa massallaci kotan sakina bai bi ba koda yadawo yasamu kira daga asibiti ashiryeshi ya iske Safeena ita da danta akichen suna soya wainar kwai Adil yadauka yana masa wasa ita kuma Safeena natsaye sanye da riga da sikat yan kati da hula akanta ta harde hannunta akirji tana kallonsu dagowa yayi suka hada ido tasakarmai murmishi,shima ya mayarmata sanye cikin american suit red and blck suit dinsun amsheshi matuka yar briefcase dinsa ke makale akafadarsa kallo daya tamai ta fahimci baida fara"a kallonsa tayi kan tace'ina kwana....Ya amsa da "Lpy kalau ummi Adil yakuka tashi ta amsa da lpy tana kallonsa saurin fita yayi yana fadin"Zan makara yanmatana zo ki karbi danki"kashe gas din tayi kan ta fito tana fadin"Unku baka fa karya ba zaka fita"Kallonta yayi kan yace"Na makara sai dai in nadawo....Yana fadar haka ya mikamata Adil ta amsheshi shikuma ya fice binsa tayi da kallo tana mamakin mai ya batamasa rai haka.
Ko achan hospital kowa ya fahimci baida walwala hatta tahir wanda bai ma tambayesa ba domin yasan duk sanda yaga Dr Safana awannan yanayin yasan mutum dayane ke sauya Dr Safana wato SAKINA.
Koda yadawo baiwani sake ba saida Safeena tadinga jansa da hira shiyasa yasaki ransa yau ma abun jiya aka maimata akasa ya kwana wanda ko mgana bata hadasu da sakina ba shi da badon yasan darajar aure da adalchi ba har Sakina ta wulakantasa never domin yanzu ba da bane.
***** ******* *******
Kwanchi tashi Asarar mai rai gashi yanzu watan su Safeena biyu da tarewa gabadaya rayuwarsu ta chanza ita da Safwan da Adil domin suna cikin farinciki da Annushuwa hatta su momma suma sun ga chanji saboda su yanzu girki sai sunga daman yi domin Safeena ta daukemusu komai ita keyi in tagama abunda zatayi sai takoma shashensu suta hira da dariya da hajiya mama.
Ga Adil yanzu watansa goma sha daya gudu ba inda baya zuwa mami kuwa abakinsa da Abbu da hajiya da momma radam abakinsa ya Iya fada safeena ta shaku da Adil matuka bata son abunda zai tabashi kwatakwata tana jin dadin zaman gidan fiye da komai gashi Dr ya siyamata sabon waya kullum sai sunyi waya Da Ummi tana kara bata shawarwari wa'inda zasu amfaneta.
Ada Sakina bata cika fitowa ba ammh yanzu tachanza taku domin afalo take wuni in ko Adil ya kuskura yayi gefenta wlh sai yadawo da kuka itakuwa Safeena ko kallo bata isheta ba domin har abada bata da lokacinta kawai tana gama basu dama ne saura kiris abunda ta dana musu yatashi dasu.
Commet
And
Share
*Janaf*✍
🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀🤦♀
*NA TAFKA KUSKURE!!*
🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀🙆🏽♀
*NA*
*Janaf ce*✍✍
DEDICATED TO *My Momma Hajja Hadiza muhammed Ba'are*
I so much luvs u my momma😍😍
*INTERLLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*{onward together}*
*{we give the the Reader's of ours the best out of the bests,,,Our inks are melodious and dropping a kinda light to reader's}*""""
*THE PEN OF LOVE*😘
*HEART OF TOUCHING*❤ *TEARS OF SORROWS*😭 *CURDLES*🙂, *GIGGLES*😁, *AND MARRIEGE THINKS*💑
*JUST GIVES US A FOLLOW*✔
*shafin kine sahiba Hafsart Hafnan tsakanina dake Allah ne kawai yasani ina miki kauna ta har abada*
*30*
----Mtsala ta farko da sakina tafara fuskanta shine na danta ADIL....wanda indai yana wasa afalo tashigo yanzu zai yanka ihu yatashi da gudu yabi safeena daki ko kichen inko tace zata daukeshi yadinga yanka ihu kenan kamar yaga dodo sai Safeena tazo ta daukeshi tana rarashi yana kuka yana fadin"Mami....Yana nuna sakina,saidai Safeena tasabasa su koma daki kana zaiyi shuru.
Abun yana damun Sakina matuka domin koda take rashin kula Adil bawai batason shibane yaza'ayi mutum yahaifi da da cikinsa yace bayason wannan mai ai karyane,tana son danta kawai abubuwane suka mata yawa ciwon abu biyu tahade mata ga na kwatar miji gana da domin yanzu Safwan tsakanin shi da Sakina ido ko kula da yadda take rayuwa bayayi saboda shi yanzu kwanciyar hankalinsa kwanciyar hankali Safeena da gudun jininsa.Hatta da su momma sai suyi sati basu sata a ido ba Hajiya mama ko aranar data shigo shashen ta iske zaune afalo dariya tahau tsintsurawa tana fadin agaida uwargida sarautar mata shiyasa bahaushe yace kada kayi wasa da damarka domin watarana matsayin daka ke adama rasashi kakeyi,babu shakka tasan da ita takeyi shiyaasa sum sum ta shige daki ranta na mata suya tana son tadawo Sakinarta tada ammh tarasa yazatayi.
Yau Tun safe Dr Safwan ya fice bayan yar rigiman sa Safeena tagama kukan Ita Umminta takeson gani tun yana lallashinta har yazo yana binta da ido domin kowani dakika kaunarta kara zurfi take aranshi,bawai bayason tafiyar nata bane A'a yadda Safeena tazama tallafinsu shida danshi yakeji kada suyi maraici,tana fushin yafice ya barta.
Sau wurin sha biyu tafito daga daknta Adil na biye da ita kamar jela yana mata gwarancinshi sanye take da wata atamfa milk and green riga da sikat kayan sun amsheta tayi daurin ture kaga tsiya ta daure gashinrta da band,tarasa mai zata dafa kawai sai ta soya musu doya tayi miyar kwai ta kammallah kenan taji ana sallama da sauri ta fito tana amsawa.
Wasu mata tagani guda biyu dayar tafi manyanta dayar kuma yarinyace dukkansu kallon banza suke binta dashi kamar sunga kashi Safeena taji gwiwarta ta sake tace cikin sanyi murya"Sannunku da zuwa...Ku....ke dallah rufema mutane baki"Anty laila kenan ta katseta tana binta dawani matsiyacin kallo Hajiya kari tace'yo kekuwa dole tamana sanabe mana anzo gidan daula anrabu da cin gabza"safeena taji wani abu ya tsayama amakogwaro kafin tace wani abu Adil ya fito daga daki dagudu da wayarta yana fadin"Mami....Mami...Abbu...Yana mikamata wayar alamar ana kira Amsa tayi tana shafa kanshi Dr ne ke kira shiyasa ta barshi.
Hajiya kari da laila suka hada ido suka futar lokaci daya"MAMI....."da mamaki afuskarsu kafin Laila tace"Hajiya kamar fa Adil ne fa yagirma hajiya kari tace"Shine Nima nayi mamakin girmansa rabona fa dashi tun haihuwarsa"Laila tace"Nima inaganin tun lokaci ammh naji yana cema watanan mami fa"Tafada tana kallon Safeena datake rumgume da Adil dake binsu da kallon rashin sani.
Hajiya kari tace'Ato sakarcin sakina ne baki sani ba"Tafada rai bace ai laila da hanzari ta ficikosa tana fadin"Bazai yuyuba kin asirce uba kuma ki asirce da"Yako tsandara ihu iya karfinsa hajiya kari ta dunguremasa kai tace"Kinganin mun munafukin yaro kaci gidanku ni nan daka ganni kakankace ita kuma wannan yar'uwarka ce"Tafada tana nuna laila kana ta nuna Safeena dake daskare awurin hawaye sun taru a idanunta tace"Ita kuma wannan kshiyar uwarkace ga uwarka chan wacce tayi nakudarta"tafada tana figan hannunshi ta wuce dakin Sakina laila ta marata baya shikuwa Adil kuka yake yana mika hannu yana ta kiran"Mami.....Mami...ita kuwa hajiya kari nakara jansa tana fadin"Ko zaka mutu sai kabar mamin don ubanka".
Safeena da kuka yakwacema tashige daki da sauri tana maida kuka gefen gado tazauna tana sharen hawaye aranta tana addu"an kada Allah yabasu ikon Rabata da Adil domin wlh bazata iya rayuwar gidannan ba yaron nan akusa da ita ba.
Sakina na kwance akan gado su laila suka shigo cikin mamaki ta mike tana kallonsu rike da adil dake ta kuka harda hawaye,cikin mamaki su hajiya ke kallon sakina tareda bin dakin da kallo laila tace"Sakina....Haka kika maida kanki ashe"Sakina ta tabe baki kafin tadiro daga kan gado sanye da breziya da under bako kaya tace"Eh....Haka Safwan ya maidani Anty"Tafada tana fashewa da kuka rumgumarta Anty laila tayi tana lallashinta hajiya kari ta damkafar da adil akasa tana fadin"Kama ma mutane baki wlh ko in mauje ka munafinki yaro"Sakina ta saki laila tana fadin"Hajiya kuma kungani ko wlh yaron nan in yaganni kamar yaga dodo"Tafada hawaye yana zubo mata hajiya kari tace"badole yamaidake dodo ba tunda kin zauna kin maida kanki sakarya mara wayo har ita waccan sillan kara wata abace dazaki zauna su ruguza miki rayuwa'Sakina ta tsananta kukanta tana fadin"Ya zanyi hajiya ya zanyi wlh narasa ma ni mai zanyi"Anty laila ta riko hannunta zuwa gefen gadon tazaunar da ita tana fadin"shine dalilin dakika bar kasuwancinki ya ruguje ayanzu haka shagonki na kano an rufesa coz bbu kaya why sakina zaki sakaci da rayuwarki ta tarwatse lokaci daya"Sakina ta share hawayenta tace"Ni bata shago nake ba ta yadda na zama bola agidan nan shi yafi damuna ku fadamun yazanyi"tafada hawaye na kwaranyomata Hajiya kari tace"Abunda zaki ki mike ga kanki kidawo sakinarki danki kuma da ake miki iko dashi ki karbi abunki domin ba uwar wani ya haifar miki ba wlh sakina in har baki mike kin kwaci yancinki agidan nan ba to na yarda ke ba nonon karimatu kika sha ba"Takareshe fada da bacin rai Sakina tace cikin kuka'zanyi hajiya zan nuna miki nidin yar karimace ta halas ma kuwa"Hajiya kari tace"ke kefa kici mutumci duk wanda yanemi yadakatar dake koda uwarsa ne"Laila tace"Ai sune munafukai baran wannan katafiriyar tsohuwar mai kalan yan duniya"Sakina tace"Ai itace ke juya safwan din inaji ko auren nan ita tayimai shi"Laila tace"Yar tasha ita lokacinta ubanwa yasa amata kishiya"Hajiya kari tace'ai karta aragama kowa harda ita tahada taci uban shegiya kota koma kauye inda aka fito tana wani ji da baki kamar fanteka🤣🤣🤣🤣gabadayansu dariya sukasa harda tafawa.
Koda suka waiga ba Adil ba dalinlinsa ashe suna chan suna mgana ya sulale yakoma gun Safeena wacce taci kuka ta koshi yana ko shigowa yatafi ya rumgumeta yana ajiyar zuciya alamar yasha kuka rumgumesa tayi tana dariyar farinciki.
gabda la'asar sukayi shirin tafiya bayan sun cika sakina da mugayan shawaransu wanda bazai bulle da ita ba saima karin jawoma kanta wata fitinar...kwamishina bayanan yaraka gwanna jgawa shiyasa sukasamu zuwa domin ido yasanya musu ko laila yace tadaina zuwa sai anyi wani abu kwakkwara tukun..
Sakina ta rakosu kenan suka ga hajiya mama zaune adan barandansu ta shimfida tabarma tana jin radio ta sai gasu sun fito sun yi tsam da suka ga hajiya mama ammh sai suka waske itakuwa hajiya mama harda cemusu bata gansu wurin biki ba adakile hajiya kari tace"Sunyi tafiyane shiyasa...Suka shige motarsu laila ke jan motar suka fice hajiya
mama tabisu da gwalo.
commet
And
Share
0 comments:
Post a Comment