A hankali take ware manya manyan idanunta da suka kaɗa suka zama jajur dasu, ba tun yanzu ta farka ba, kawai dai Allah ne be bata daman buɗe idanun nata ba sai yanzu. Tun farkawarta kuwa take cikin tsanani da kuma mamakin mutum mai taurin zuciya irin Zaid, lallai shiɗin yacika ɗan iska kuma shu'umi, duk da irin girman laifin da ya aika ta mata, hakan baisanya yaji ɗar ko kuma shakkan tunkarar ta ba, lallai shiɗin acikin ƴan iska ma daban yake,, haka nan taji gaba ɗaya zuciyarta ta ƙeƙashe takuma bushe, lallai tunda ya nuna mata shiɗin babban ɗan iska ne yakamata ace itama ta nuna masa iyakar iskancinsa, tunda har baiji kunyar tako ƙafa yazo gareta ba, to tabbas itama yakamata tacire kunya, wajen ganin ta koya masa hankali... Sai dai kuma kome zatayi bazata huce ba, saboda iyaka kuma maƙurar cuta Zaid yayi mata, ya mata illa dakuma tabon da bazata taɓa mantawa ba, harta koma ga mahaliccinta kuwa, Zaid ne ya surka mata farincikinta da wani irin mummunan baƙin duhu, ya katse mata jin daɗi da kuma walwalanta, ya lalata mata rayuwa a rana ɗaya, ya ruguza duk wani buri da fatanta, ya gwada mata ƙarfi ya amshi budurcinta cikin yanayi na tozarci, me yafi wan nan ciwo a rayuwar ƴa mace? tasan ƙiyayya amma kuma zafin ƙiyayyar da takeyi mawa Zaid na daban ne, tabbas idan da kisan kai yana da kyau a addinance to haƙiƙa ba abun da zai hanata kashe Zaid san nan kuma itama ta kashe kanta, saboda ƙuncin da ya mamaye zuciyarta ba'irin ƙuncin nan bane da yake fita, lallai ƙuncin zuciyarta dawwa memme ne, sai dai kawai ta roƙi Allah daya sassauta mata.....
Hawayen da suka fito daga cikin idanunta suka gangaro ta gefen kumatunta ta sanya hanu ta share haɗe da miƙewa zaune, babu amfanin ɓata hawayenta wajen fiddasu, yanzu lokaci yayi da shine yakamata yayi kuka ba ita ba. Kayan jikinta tashiga cirewa, haɗe da ɗaura zani akan ƙirjinta kana ta sanya lufaya....
Tana fitowa daga cikin ɗakin nata, Inna ta kalleta haɗe da cewa.
"Yauwa Zahrah kintashi ko? ya ƙarfin jikin naki de?" alokaci ɗaya Inna tajero mata duka waƴan nan tambayoyin..
"Eh Inna na tashi, ko zan samu ruwan zafi inaso nayi wanka ne, gaba ɗaya banajin daɗin jikina, gashi ina so naje gidan su Husnah" tafaɗi maganar tana me ɗan rumtse idanun ta, saboda wani juwa da taji yana ƙoƙarin ɗibanta..
"Kinkuwa ci sa'a yanzu na ɗaura ruwan abincin rana, gashi can inaga yama tafasa saiki ɗiba, amma idan kin ɗiba ki ƙaramin ruwa acikin tukunyar" Inna tafaɗi haka tana meyi mata nuni da tukunyar abincin dake ɗaure kan murhu...
Sosai taji daɗin jikinta sakamakon wanka da ruwan zafi da tayi, bayan ta idar da Sallan Azahar ne, tayi mawa kanta mazauni akan katifarta haɗe da ɗaukan jakar kayan kwalliyanta, mai kawai tashafa sai kwalli da ta zizara a cikin idanunta, ko powder bata shafa ba...
Doguwar rigar atamfa irin me sauƙin kuɗin nan tasanya ajikinta, haɗih da ɗaura hijab akan kayan nata mai kalar blue, yakumayi shige da atamfarta saboda shima atamfar kalan blue ne dashi (shuɗi). Me kyau de me kyaune ko a yaya kuwa, duk da batayi kwalliya ba kuma fuskarta a kumbure take saboda kuka, amma hakan bai hana kyawun fuskarta bayyana ba....
Kallon Inna dake ƙoƙarin sauƙe tukunyar abinci Zahrah tayi, tana me gyara zaman lufayar jikinta tace.
"Inna ni zan je gidansu Husnah, zuwa yamma zandawo insha Allah"
"Wani irin maganar zuwa gidansu Husnah kuma Zahrah? inace ɗazu ɗazun nan muka dawo dake daga asibiti, har kin yi sauƙin da zaki soma fita yawo?"
(Su Inna anfara soyayya da Zahrah fans, lol)
"Kada ki damu Inna yazama dole ne naje, amma bazan jima ba zandawo, dan Allah kada ki hanani zuwa Inna!" Zahrah ta faɗi haka cikin yanayi na nuna zaƙuwa.
"Shikenan tunda kin matsa, ai de kya tsaya kici abinci, idan yaso saiki tafi"
"A'a Inna banajin yunwa yanzu, idan nadawo zanci" takai ƙarshen zancen nata tana me nufar hanyar fita daga cikin gidan. Da kallo kawai Inna tabita harta fice daga gidan...
Tsayawa tayi tana kallonsa cike da mamaki, yayinda shima kallon nata yake cikin yanayi na mamaki...
Giransa ɗaya ya ɗage haɗe dayin murmushi.... "Ashe ma kinyi sauƙi, dana sani da ban bar aikin da nakeyi nazo duba kiba ae" Dr.Sadeeq yafaɗi haka yana me takowa zuwa wajen da take tsaye.
Kunyarsa ne taji yakamata, sakamakon abun da yafaru ɗazu a tsakaninsu, wato rungumarsa da tayi, wanda tasan hakan ba abu bane me kyau haramunne, mace ko namiji su taɓa mutumin da ba muharrami'n su ba, duk da cewa ba'acikin hayyacin ta ta rungumeshi ba, amma tabbas hakan bai dace ba...
"Yade naga kina wani sunkuyar dakai kamar amaryar da aka kaita ɗakin mijinta" Dr.Sadeeq ƴafaɗi haka cike da zolaya.
Sai alokacin ta'iya ɗago kanta ta aika masa da
hararan wasa,,,,, " Yaushe kazo? kuma me yasa ka tsaya anan baka shiga cikin gida ba?"
"Ummm banjima da zuwa ba, dama inaso amin sallama dake ne, kinga bai dace ace koda yaushe ina shiga cikin gidanku kai tsaye ba, amma sai kuma naga kamar keɗin sauri kike zaki unguwa ko?"
Yaƙare maganar yana me leƙa fuskarta wanda ta sunkuyar da ita ƙasa.
Wasa da yatsun hanunta tashiga yi, haɗe da sanya haƙorinta na sama taɗan datse leɓenta na ƙasa..
"Yajikin naki?" yatambayeta don yaga bata daniyar basa amsan abun da yatambaya.
"Dasauƙi, dama ni lafiyata ƙalau" tabasa amsa a ta ƙaice..
"Eh hakane kuma dama kinsan wani lokacin, idan lafiya tayi mawa mutum yawa, takan iya sawa ya kwanta a gadon asibiti"
Saurin kallonsa tayi sakamakon jin abun da yace, "Lafiyan?" ta tambaya cike da mamaki.
"Eh itafa lafiyan, to baga example akan ki ba" yanayin yanda yayi maganar kaɗai ya'isa ya tabbatar maka cewa zolaya ne kawai ke damunsa..
"Hmm" kawai Zahrah tace haɗi da ɗan satan kallonsa, aikuwa karab suka haɗa idanu, saurin ɗauke nata idon tayi.
Hmm yalura sarai kunyarsa takeji, kuma shiɗin ma kusan hakanne, kawai de dauriya dakuma shariya yafita, shiyasa ya share abun, amma shikansa yasan cewa ya aikata ba dai dai ba, saboda da ta rungumesa baikamata ace yabiye mata ba, kamata yayi ace ya ɓanɓareta daga jikinsa, sai de kuma babu yanda ya'iya saboda alokacin tana cikin halin buƙatar taimako, kum san nan shi be rungumeta don yaji daɗi ba.
"Inazakije ne haka, da rana tsaka?" yajefo mata tambaya.....
"Gidan su Husnah zani" ta basa amsa a taƙaice, saboda ba da kowani lokaci tacika son dogon magana ba...
"Shikenan muje saina kaiki, domin kinsan samun abun hawa zaimiki wahala, saboda rana tayi sosai"
Kallonsa tayi naɗan sakanni, kafun ta rausayar da kanta gefe cikin yanayi na shagwaɓa tace "Dama kabarni, koda ƙafana ai zan iya zuwa, idan har bansamu abun hawa ba, balle ma nasan zan samu"
"Da gaske zaki iya takawa da ƙafa daga nan har gidansu Husnah? to shikenan tunda zaki iya, zaimafi kyau ki taka da ƙafan, saboda kisamu ki ɗan rage wan nan ƙiban dakika haɗa, gaba ɗaya duk yasa kin yi muni, kin zama wata super mama dake" yafaɗi haka yana me ƙare mata kallo.
Waro idanu Zahrah tayi haɗi da soma kallon kanta, wai tayi ƙiba, takuma zama super mama.
Take idanunta suka yi raurau dasu, yayinda ruwan hawaye ya soma cika cikin su, "ashe da gaske tayi ƙiba bata sani ba? gashi harya fara goranta mata, to me yasa ita bataganin ƙibanta?" tatambayi kanta...
Dariya Dr.Sadeeq yasanya domin kuwa yalura tayarda da maganarsa, shikuwa wasa yake mata, bawai dagaske tayi ƙiban bane, gashi har tana ƙoƙarin yin kuka, shikam ya lura gaba ɗaya kuka baya bata wahalar yi, hawayenta a maƙale suke, mintuna kaɗan saikaga sun tsiyayo"
"Kintsorata ne dan nace kinyi ƙiba? hmmm nan gaba kaɗan zakiyi bindiga ki fashe saboda tsabar ƙiba"
Sake waro manya manyan idanunta tayi zuwa yanzu kam har ƙwallan cikin idanunta sun gangaro akan fuskarta....
"Au kinfiso ki kumbura ki fashe ɗin kenan?" yatambayeta yana me danne dariyar da ta taso masa...
Kai ta girgiza masa alaman "A'a"
"To kinaso na faɗamiki me zakiyi wanda zaisa bazaki fashe ba?"
Dasauri ta ƙaɗa kai alamar tanaso yafaɗa mata...
"Yauwa ƴar gari ashe de kema bakyaso ki fashe, to abu ɗaya zakiyi wanda shizai hanaki fashewa, kinga de ni likita ne ko? nakumayi zurfi cikin karatun likitanci, saboda tsabar zurfin da nayi ina karatune ma yasanya nagano cewa idan mutum yacika matsantawa kansa da damuwa da kuma yawan koke koke to yakan iya kumbura kamar de yanda kikayi yanzu, daga nan kuma bayan kamar 1 week shikenan sai dai yayi bindiga yafashe fush, shikenan kuma sai de wani bashi ba, kinaso haka ta faru dake?" yafaɗi haka yana me zura mata manya manyan idanunsa.
"A'a" tabashi amsa cikin murya me sanyi, domin kuwa a haƙiƙanin gaskiya ta yarda da kalamansa, ko kaɗan bata gano cewa shiya shirya abunsa ba. take fargaba ya ɗarsu a zuciyarta....
Wata irin dariyane takama Dr.Sadeeq amma kuma ba halin yasaki dariyar tasa, dolensa ya danne ta matuƙar yanaso Zahrah ta gamsu da bayanan sa hundred percent,,, lallai yau yaƙara tabbatarwa kansa cewa Zahrah yarinyace kuma yarinta na damunta, amma inbanda haka ta'ina ta taɓa jin ance mutum ya yayi bindiga yakuma fashe da ransa.
Gyara tsayuwarsa yayi haɗe da cewa "To yanzu de zaɓi ya rage gareki Yarinya, ko ki daina kuka ko kuma ki fashe, saboda haka zaki biyoni muje ne ko kuwa a'a nayi tafiyata?"
"Zanbika" tafaɗa cikin muryar tsoro saboda gaba ɗaya kalaman likita sun rikitata...
Murmushin gefen baki Dr.Sadeeq yayi haɗe da juyawa yanufi wajen motarsa, yana me danne dariyarsa...
Zahrah kuwa tamkar wacce ƙwai yafashewa haka ta bi bayansa.
Saida suka hau titi kafun yajuyo da kallonsa gareta, gani yayi tayi jigum da'ita, da'alama tunani takeyi....
"Amma nace miki yawan sakai a damuwa shike sa mutum ya fashe ko? hala don ba ɓangaren likitanci kike karanta ba shiyasa bakisan da hakan ba"
Kallonsa tayi haɗe da ƙwaɓe fuska, cikin murya me sanyi tace "Ni ae yanzu bawai a damuwa nake ba, kawai de ina kallon hanya ne" ....
Kansa ya jinjina haɗe da cewa tayi masa kwatancen gidansu Husnah'n domin shi basani yayi ba....
A dai dai ƙofar gidan su Husnah ya tsaida motar tasa, haɗe da dawo da kallonsa ga Zahrah wacce ke ƙoƙarin buɗe murfin motar tayi ficewarta...
"Da yaushe zaki koma gida?"
Ɗan jim tayi kana tace "Ko zuwa bayan la'asar ma, irin ƙarfe biyar ɗin nan haka" yanayin yanda taƙai ƙarshen zancen nata tana me juya kyawawan idanunta, shi ya shagaltar dashi har ya tsaida idanunsa akan ta, sosai takeyi masa kyau idan tana juya idanunta, ya kuma lura cewa hakan al'adarta ne, idan hartana magana, to takan juya idanunta masu kyawun gani, musamman idan maganar tazo ƙarshe..
"Ya de?" Zahrah ta tambayeshi sakamakon ganin da tayi yakafeta da idanunsa..
"Babu, kikulamin da kanki kinji, zan zo na ɗaukeki idan 5 ɗin tayi, inafata babu wata matsala?" yatambayeta cike da nuna kulawa.
Murmushinta me kyau tayi masa haɗe da cewa
"Babu wata matsala"
Yana kallonta tabuɗe ƙaramar ƙofar dake jikin gate ɗin gidan su Husnah tashige... Yana tabbatar da shigewarta yayiwa motarsa key haɗe dayin reverse yaɗauki hanyar asibitinsu, saboda dama aiki yabaro yazo gareta, to yazaiyi tunda tazama wani ɓangare na jikinsa...
Da matuƙar farinciki Husnah ta rungume Zahrah tana mejin daɗin ziyarar bazata da Zahrah'n takawo mata, saboda bata faɗa mata zata zoba. Bayan Zahrah ta gaisa da Momyn Husnah ne, suka rankaya zuwa ɗakin Husna'n,,, ba ɓata lokaci Husnah ta cikawa Zahrah gabanta da kayan ciye ciye dasu drinks.
"Naji daɗin zuwanki sosai ƙawata, kamar kuwa kinsan ina kewarki, jiyafa har mafarkin ki nayi, da safe naƙira wayarki kuma najita switch off, ina fata dai kina lafiya?"
Hijabin dake jikinta ta cire haɗe da cewa "Lafiya amma ba sosai ba"
Da sauri Husnah ta dawo da kallonta ga Zahrah
"Meyafaru dear?" Husnah tatambaya cike da kulawa.
Kallon Husnah Zahrah tayi na tsawon minti guda....
"Babuƙatar tuna abun da yafaru Husnah, saboda kinsan inada raunin zuciya, tuna abun zai iya sake jefani cikin wani hali"
Damuwane ya bayyana ƙarara akan fuskar Husnah haƙiƙa tamkar ƴar uwa ta jini take kallon Zahrah saboda haka duk wata damuwa ta Zahrah damuwar tace itama.
"Zaki iya ɓoyewa kowa damuwarki amma bandani Zahrah, sai de kuma babu amfanin takuraki akan cewa lallai sai kin sanar dani, saboda bansan wani hali zaki samu kanki aciki ba bayan kin faɗamin"
Dafa kaɗan Husnah Zahrah tayi haɗi da daure zuciyarta...
"Nasake haɗuwa da.... da....wanda ya yimin fya......." kasa ƙarasawa tayi saikawai tafashe da kuka.
Ko bata ƙarasaba Husnah tafahimci me Zahrah take nufi.
Cike da tashin hankali Husnah tasoma salati...
Sake jawo Zahrah jikinta tayi haɗi da rungumeta...."Ki daina kuka, yanzu ba lokacin kuka bane Zahrah, kinmaci abinci kuwa ?" Husnah ta tambayi Zahrah cikin kulawa...
"Banajin yunwa Husnah!" Zahrah tafaɗi haka cikin shaƙewar murya, wani yunwa zataji ita da take cikin bala'in sake ganin Zaid...
"Kinsan de ba kyau zama da yunwa ko, kinga yau ni namayi abincin dakaina, bana zuba mana muci tare, kuma dan Allah kada kicemin a'a"
Babu yanda Zahrah ta'iya dole tabiyewa Husnah taci abinci, gaba ɗaya Husnah se zuba take tamkar kurna, takasa yin shiru koda na minti biyu ne, tayi hakanne kuma saboda ta gusarwa da Zahrah da muwarta, daga ƙarshe de har game, Husnah ta jona musu a tv suka buga, sosai kuma hakan ya ɗebewa Zahrah kewa....
Tare sukayi sallan la'asar daga nan kuma Husnah ta ɗebi Zahrah, suka tafi shoprite, dangin su ice cream da chocolate suka jida, daga nan sukayo gida.
Kamar yanda yafaɗa ƙarfe biyar da minti ɗaya dai dai ya ƙaraso ƙofar gidansu Husnah.. Ƙiran Zahrah yayi a waya ya tabbatar mata cewa yana ƙofar gidan su Husnah....
Zahrah na ajiye wayarta Husnah ta kalleta haɗe da kashe mata ido ɗaya.
"Ƙawata tazama ƴar soyayya, sosai yanayin soyayyarku da Man ɗin nan yake kasheni, kinfasan gayen naki ya haɗu over, da badan ke bace danayi snatching ɗin sa!" cike da zolaya Husnah ta faɗi maganar...
Dariya suka sanya su dukansu, haɗe da rungume juna.
Har bakin motar Dr.Sadeeq Husnah ta raka Zahrah, bayan Momyn Husnah ta cikawa Zahrah leda da dangin su turare dakuma kayan shafa hadda kyautar wani haɗaɗɗen leshi, sosai Zahrah tayi godia, hakan kuma yana ɗaya daga cikin abubuwan daya sanya bata son zuwa gidansu Husnah, saboda idan dai tazo tofa sai mahaifiyar Husnah tayi ɗawainiya da'ita wajen bata kyautan kayayyaki masu kyau da tsada...
Harsaida Husnah taga tashin motar su Zahrah kafun takoma cikin gida...
"Kinsamo abun daɗi shine kokimin tayi ko?" Dr.Sadeeq yafaɗi haka ga Zahrah wacce ta ɗaura ledan sayayyar da sukayi a shoprite ita da Husnah akan cinyarta...
"Murmushi me sauti tayi haɗe da cewa "Ba'abun daɗi bane, kayan shafa ne"
"Um um ni banyarda ba, kitaimaka kiban ko chocolate ɗaya ne, naci yunwa nakeji, yau duk banci abinci ba" yaƙare maganar yana me shagwaɓe fuska, sai kace wani ƙaramin yaro...
Dariya Zahrah tayi haɗe da satar kallonsa "wai ma ya'akayi yasan cewa acikin ledar hanunta akwai chocolate?" ta tambayi kanta.
"Kina mamakin ya'akayi nasan cewa a ledarki akwai chocolate ko?, ai ba abun mamaki bane, tunda nasan shiɗin favorite ɗin ki ne" yafaɗi haka cikin yanayin shauƙi, amma still idanunsa naga titi..
Buɗe ledar tayi taciro wani chocolate mai kyau da daɗi kusan yafi kowanne ma daɗi acikin sauran chocolate ɗin da ta saya, ta miƙa masa haɗi da cewa "Ga wan nan amma bazan iya baka kyautarsa duka ba, saboda haka kaci rabi kabarmin rabi"
Saurin kallonta yayi fuskar sa ɗauke da murmushi... " Naƙi wayon, idan har kinaso na karɓa saide kibani kyautansa duka"
Turo ɗan ƙaramin bakinta tayi gaba, haɗe da noƙe kai alamar hakan bazai yiwuba, kallon bakin nata yayi, harsai da yaji tsikar jikinsa ƴa zuba, hmmm lallai idan ya auri Zahrah, zai tsotse wan nan ɗan ƙaramin bakin nata ne yanda ya kamata🙈...
"Kici chocolate ɗinki ke kaɗai nikam na gode" yafaɗi haka a taƙaice domin dama wasa yake mata baci zaiyi ba, shi da yake fama da ciwon ciki idan yaci chocolate kuma yake nan?
Lokacin da suka iso gida biyar da rabi har ta gota... kallon Zahrah Dr.Sadeeq yayi haɗe da ɗan nisawa.
"Nagama haɗa miki kayan lefe da kuma sauran abun da suka dace, wace rana kikeso a kawo?"
Saurin ɗaga idanu tayi ta kallesa jin abun da yace.
Idanunsa ɗaya ya kashe mata, wanda yasanya taji gabanta yafaɗi, saboda a wajen mutum ɗaya ta saba ganin irin wan nan kashe idon, kuma shi hakan yazame masa al'adarsa ne, bakowa bane kuma face ZAID.
"Zamuyi waya" Zahrah tafaɗi haka don son kawar da tambayar tasa, saboda a yanzu bata da amsar da zata basa..
Ajiyar zuciya ya sauƙe haɗe da dafa steering motar da duka hannayensa biyu. "Shikenan idan kin nutsu zan ƙiraki" yafaɗi haka cikin sanyin murya..
Murmushi tayi masa irin me tsayawa a rai ɗin nan, kana tabuɗe murfin motar tayi ficewarta, sai de batare da yasani ba, ta aje masa wan nan chocolate ɗin...
Bayan kamar 2 minute da shiganta cikin gida yaja motarsa shima yayi tafiyarsa...
*ZAID*
Tunda yasha wan nan ƙwayoyin baisan inda kansa yake ba harsai ƙarfe uku na yammaci,, ko da ya buɗe idanunsa ji yayi duniyar na juya masa, amma haka adaddafe ya shiga bathroom yayi wanka haɗe da ɗauro alwala, sai yanzu zaiyi sallan Azahar don tsabar asara, gashi har la'asar ma takawo kai....
Yana idar da sallan azahar ya miƙe daga kan sallaya haɗe da zura slipper ɗinsa yafice daga ɗakin... Kai tsaye masallacin jikin gidansu yanufa don gudanar da sallan la'asar wanda ake ƙira yanzu.. Ko a cikin masallacin mutane sai mamakin ganinsa suke saboda abune mawuyaci ka gansa a masallacin da wan nan time ɗin, yafi yawan zuwa sallan isha ko asuba, amma banda azahar da la'asar saboda a wan nan lokacin ma kwata kwata baya gida, sai de yayi sallah a wani wajen. Baidamu da kallon da mutane suke masa ba, yana idar da sallan sa yatashi yayi shigewarsa cikin gida...
Tsab yagama shirya kansa cikin ƙananan kaya, riga da wando na blue jeans wanda suka matuƙar amsar jikinsa. Ba abun da yake sai tashin ƙamshi.
Zama yayi abakin gadonsa haɗe da sanya hanunsa duka biyu ya dafe kansa dake yi masa ciwo kaɗan kaɗan,, wani irin sabon al'amari yakeji a cikin zuciyarsa, baisan da wani suna ze ƙira abun ba, amma tabbas jiyake zuciyarsa na azalzalarsa akan Zahrah, san nan yanajin cewa itace muradinsa, saurin buɗe idanunsa da ke lumshe yayi sakamakon hasko masa marukan da Zahrah ta sharara masa akan fuskarsa da sukayi, hanunsa yakai kan ƙuncinsa ya shafa haɗe da sakin murmushi, tunda yake a a rayuwarsa wata mace banda mahaifiyarsa bata taɓa kai hanunta jikinsa da sunan duka ba ballan tana har akai ga mari, sai gashi yau, Zahrah ta shararamasa lafiyayyun maruka harguda biyu akan fuskarsa, takuma haɗa masa hadda duka, amma ko kaɗan baiji zafin abun ba, anya kuwa shine? kodai an musanyashine bai sani ba? meke damun ƙwaƙwalwa da zuciyarsa ne? shine Zaid kuwa? Yajerowa kansa waƴan nan tambayoyin....
*(Team Zaid saiku basa amsa, shi ɗin ne koba shiɗin bane?)*
*27/December/2019*
*Follow me on Whatsapp and Wattpad*
*Wattpad user name fatymasardauna*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SHU'UMIN NAMIJI !!*
*Written By*
*Phatymasardauna*
*Dedicated To My Brother KHABIER*
*🌈 Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
*Editing is not allowed📵*
*CHAPTER 70 to 71*
Yajima zaune a kan gadon nasa, gaba ɗaya kansa ya kulle yarasa meke damunsa, wai shin da gaske SO yake ko kuwa? anya kuwa yanaga zaman sa haka zai yi wu? zaifi masa kyau yanemi Abid domin shi ne kaɗai zai iya fayyace masa halin da yake ciki, tabbas shi koda son Zahrah Abid ɗin yace masa yanayi yanzu bazai musa masaba, idan kuwa har haka so yake to yana mawa Zahrah so me tsanani, saurin laluɓar wayarsa ƙirar Samsung dake kusa dashi yayi. Numbern Abid ya dannawa ƙira, bugu biyu Abid ya ɗaga ƙiran cikin muryan kasala yace "Mutumin ya akayi ne, ka katseni ina cikin holewata"
"mcheeww aikin ka kenan cin ƴaƴan mutane, kana ina yanzu inaso muyi serious magana da kai" Zaid yafaɗi haka cike da zaƙuwa.
Miƙa Abid dake kwance shame shame a gado yayi haɗe da sakin daria, wai yau shi Zaid ke cewa baida wani aiki se cin ƴaƴan mutane, hmm ai duk iskancinsa shikansa yasan a ƙarƙashin Zaid yake, domin kuwa Iskancin Zaid me lasisi ne.
Cike da ƙuluwa Zaid yace " Nifa bana ƙira ka kamin iskanci bane, da zaka tsaya kanamin dariya"
"Yi haƙuri mana nawan, maganartaka ce tabani dariya, zuwa anjima mu haɗu a Millinion Park ina fata de bawata matsala bace ta afku?"
Ɗan yamutsa fuska Zaid yayi haɗe da duban agogon Rolex ɗin dake ɗaure a tsintsiyar hanunsa. "Shikenan to muhaɗu ƙarfe 5 na yamma banakumason kamin african time, 5 nacika idan bakazoba, bazan tsaya ɓata time ɗina wajen jiranka ba" yayi maganar cikin yanayi da yake nuna cewa ba wasa yake ba..
"Okay" kawai Abid yace haɗe da aje wayartasa yajawo babe ɗin dake kusa dashi, suka ci gaba da watsewarsu ko kunyar Allah dayake ganinsu basayi, Allah karabamu da ƙeƙashewar zuciya Ameen.
Zaid yana aje wayartasa yasanya hanu yashafi cikinsa, sai alokacin yake tuna rabonsa da yasanya abinci acikin cikinsa tun jiya da yammaci, amma saboda tsabar yashiga tension ko yunwarma bayaji, murmushi yayi tunowa da yayi da yanda yaji muryan Abid, dagajin yanda yaji yanayin muryartasa yatabbatar masa cewa holewa da mace Abid ɗin keyi, "hmmm Abid ba dama wajen iya latsa mace" yafaɗi haka a fili, shikamma rabonsa daya kusanci wata mace harya manta, shi yanzu ko mace ma yagani bata wani burgesa, yanzu idan zaiyi sex to badakowacce mace yakeso yayi ba, face Zahrah ita kaɗai yakejin cewa zai iya sauƙewa damuwarsa yanzu, itakuma kaɗaice zata iya basa gamsuwa ɗari bisa ɗari. Miƙewa yayi yanufi wajen fridge ɗin dake ɗakin nasa, fresh milk ya ɗauka haɗe da tsiyayawa a cikin glass cup, zama yayi yasoma sipping fresh milk ɗin a hankali, gaba ɗaya hankali da tunaninsa sunaga Zahrah, ko yanzu wani hali take ciki? Allah masani...
***
Sake narke masa murya tayi cikin shagwaɓa tace "Nide bance bana sonka ba, aikaima kasan inasonka, kawai de nakasa sakewa da kai ne har yau!" taƙare maganar tana me rausayar dakanta gefe tamkar yana ganinta..
Dr.Sadeeq dake zaune cikin luntsumemiyar kujeransa na office ya lumshe idanunsa haɗe da gyara zaman wayar akan kunnensa, sosai shagwaɓan Zahrah ke sauƙar mai da kasala acikin jikinsa, yayinda idan yaji muryarta yake samun nutsuwa a cikin zuciya da ruhinsa...
"To meyasa bakya iya sakewa dani ne My Princess, kinkuwa san irin sonda nake miki? inasonki Zahrah fiye da tunaninki, amma bazaki gane hakan ba, sai idan nasameki a matsayin matata, na tabbata nan da 3 weeks kinzamo mallakina daganan kuma zaki gaskata soyayyata a gareki!" yafaɗi maganar tasa cikin yanayi na shauƙi..
Saurin kulle idanunta tayi haɗe da sanya hanu tarufe fuskarta, saikace wanda take aga banshi, sosai maganarsa yasa taji kunya,, ta lura haka Dr.Sadeeq ɗin yake watarana baruwansa kansa tsaye yake faɗar maganar da zaisanya taji kunya.
"My Princess kinyi shiru" Dr.Sadeeq yafaɗi haka a kasalance.
Numfashi Zahrah ta fesar haɗe da sake yin ƙasa da muryarta cikin shagwaɓan daya zamemata sabo tace "Munyi magana da Baffa, yace ku kawo kayan lefen duk sanda kuka shirya kawai"
Daɗi ne yakama Dr.Sadeeq harsaida yakasa ɓoye murnarsa idan kuwa hakane to tabbas acikin satin nan zai sanar da ƴan uwansa saisu shirya rananda zasu kawo kayan, shida zasuce yauma to tabbas da zaiso hakan.
"Naji daɗin maganarki My princess saboda haka kincancanci nabaki kyauta ta musamman, idan banzo da dare ba gobe zanzo insha Allah"
Murmushi kawai Zahrah tayi haɗi da cewa "Nagode amma kariƙe kyautarka bayanzuba"
"Meyasa?" yatambayeta cikin yanayi na ɓata fuska.
"Saboda hidiman da kakeyi yayi yawa, dan Allah kabari haka kaji!" taƙare maganar cikin yanayin shagwaɓa.
"Inde akan kine Zahrah bazan taɓa gajiyawa ba, zanyi wani aiki yanzu zanƙiraki anjima kinji princess ɗina!" yafaɗi haka cike da lallashi.....
Haka sukayi sallama cike da kulawa ga junansu, yanzu kam tagama aminta da Dr.Sadeeq insha Allah kuma idan ta auresa zata basa farinciki me ɗorewa, iyaka iyawarta.....
Sosai Zaid yashaƙa da irin yanda Abid yasanyasa agaba yaketa yi masa dariya,, tsuka Zaid yaja me tsayi haɗe da kawar da kansa gefe jiyake tamkar ya tashi ya rufe Abid da duka, idan banda iskanci taya zai sanyasa gaba yayi ta masa dariya bayan yagama jin matsalarsa...
Wani mugun kallo Zaid yajefawa Abid me ɗauke da tarin ma'anoni da yawa, ganin haka yasanya Abid saurin gimtse dariyarsa haɗe da kama hanun Zaid ɗin...
"Yi haƙuri Abokina, maganar ce tabani dariya"
Tsuka Zaid yakuma ja batare da yace komai ba.....
"Nafuskanci inda matsalanka ta dosa Zaid amma kuma nasan abune me wahala ka yarda da abun dazan faɗa ma"
"Bazaka gane yanda nakeji agame da'ita ba ne Abid, dakasan yanda nakeji a zuciyata da ka tausaya kasanar dani maganin matsala ta, kodai shine so ɗin da kake cewa?" Zaid yatambayi Abid cike da damuwa...
"Ƙwarai kuwa Zaid wan nan shine SO, sai de naka SO'n ya banbanta da sauran soyayya'n, kai naka soyayya'r me tsanani kakeyi, wanda tariga da tajima acikin jikin ka batare da ka sani ba, ina da yaƙinin cewa tun farko Son Zahrah kake bawai sha'awarta ba kamar yanda ka ɗauka!" Abid yafaɗi haka da iyaka gaskiyarsa...
Nannauyar ajiyar zuciya Zaid ya sauƙe haɗe da sanya duka hannayensa ya dafe kansa wanda yake ɗan sara masa a hankali.. Tabbas yanzu kam ko yaso ko yaƙi dolensa ya yarda da maganan da Abid yafaɗa masa, domin kuwa idan har ba soyayya ba menene ke damunsa dayake sawa yakejin zafi a zuciyarsa? idan ba soyayya ba menene yake sanya tunaninsa hargitsewa da zaran yatuno Zahrah? idan ba soyayya ba menene yake sanya sa rasa sukuni da nutsuwarsa aduk sanda yatunanota kokuma yaganta? lallai kuwa soyayya baimasa adalci ba da bai sanar dashi kansa ba tun sanda yafarasa batare da yasani ba..
Idanunsa da sukayi jajur dasu ya ɗaga haɗe da maida kallonsa ga Abid "Inasonta Abid inasonta sosai!"
Waro idanu Abid yayi yana me kallon Zaid idan da ba Zaid ɗin ne da gaske a gabansa ba, to tabbas da sai yace badaga bakin Zaid wa ƴan nan kalaman suka fitoba, yau Zaid da kansa yake cewa yakamu da son wata? lallai kuwa rayuwa tana shirin juyawa abokin nasa baya.
Miƙewa Zaid yayi daga zaunen da yake haɗe da sanya hanu ya kwashe wayoyinsa dake kan ɗan ƙaramin table ɗin dake aje gabansu.
Kallonsa Abid yayi cike da mamakin ganin yanda lokaci ɗaya yanayin Zaid ɗin ya sauya.
"Inakuma zaka?" Abid yatambaya..
"Zanje gidansu Zahrah Abid, idanuna sun matsamin zuciyata har bugawa take Abid, ita kawai nakeson gani, idan har zata amince inaso ayau base gobeba koda ƙarfe ɗaya ne na dare a ɗaura mana aure da'ita" yanakai wa nan a zancensa yayi tafiyarsa.. Hangame baki Abid yayi yana kallonsa harya ɓacewa ganin idanunsa. Anyakuwa Zaid yana cikin hankalinsa? Kodai asiri yarinyar talakawan nan tayi masa ne? Abid yajerowa kansa waƴan nan tambayoyin, bayan yasan baida amsa bai kuma da me basa amasar...
Zahrah dake zaune tana gudanar da assigment ɗinta, wani yaro yashigo cikin gidan nasu haɗe da kwaɗa sallama.. Amsa masa Zahrah tayi batare da taɗago kanta takalli yaron ba..
"Wai ana ƙiran Zahrah a waje" yaron yafaɗa yana me kallon Zahrah domin kuwa yasan cewa itace wacce aka aikosa yayi ƙiranta..
Sai alokacin Zahrah taɗago kanta ta kalli yaron, haka nan taji gabanta yafaɗi, to waye kenan yake sallama da'ita? ta tambayi kanta, wayarta dake kusa da'ita ta ɗauka haɗe da dubawa, 1 missed call tagani na Dr.Sadeeq, dayake wayartata a silent tasanyata shi yasa bataji ƙiran nasa ba, kenan shine yazo yaƙira wayarta bata ɗauka ba shiasa yaturo yaro. "Jekace inazuwa" ta bawa yaron amsa a taƙaice..
Miƙewa tayi haɗe da tattara takardunta tayi ɗaki. Mayafi taɗauka ta yafa akan kayan dake jikinta...
Tsaye yake ajikin motarsa yayinda yakifa kansa asaman motar yana me kaɗa key ɗin motarsa dake riƙe a hanunsa..
Kanta a ƙasa tafito daga cikin gidan tana me duba wayar dake hanunta. Tsayawa tayi cak bayan ta haɗe wani miyau dayazo me ɗaci ya maƙale mata a maƙoshinta.
Murmushi yasakarmata haɗe da soma takowa zuwa gareta..
Lokaci ɗaya idanun Zahrah suka sauya kala daga fari zuwa ja, juyawa tayi a fusace tanufi hanyar shiga gida, da sauri Zaid yasha gabanta haɗe da marairaice fuska cike da tashin hankali yasoma cewa....
"Dan Allah Zahrah kitsaya ki saurareni, dan Allah kada kimin haka Zahrah, inaso ki saurare....." kasa ƙare maganar nasa yayi sakamakon kyakkyawan marin da Zahrah ta shimfiɗa masa akan kyakkyawar fuskarsa...
Cikin ƙuna da kuma zafin zuciya haɗi da raɗaɗi Zahrah ta haɗa yatsanta na tsakiya dakuma babbar yatsarta, ta kaɗa ade de fuskar Zaid duk da kuwa cewa yakerema tsayinta..
"Natsaneka tsana mafi muni, natsani jin kowani irin kalma ce da zata fito daga bakinka, wlh wlh nayi rantsuwa sau biyu, idan har ka sake naƙara ganin fuskar ka to zanyi maka abun da baka taɓa tunani ba!" cikin matsanancin ɓacin rai taƙare maganar tana me raɓan gefensa zata wuce, Zaid da zuciyarsa tariga da ta karye baiyi ƙasa a guiwa ba yasake shan gabanta.
"Kimin duk abun da kikeso Zahrah, zanfi jin daɗima idan akace kece zakiyi silan mutuwa ta, dan Allah ki saurareni mana Zahrah!!" yaƙare maganar cikin rawan murya...
Kuka ne ya ƙwacewa Zahrah me tsanani cikin muryan kukan tasoma cewa.....
"Miye laifina Zaid? Menene aibuna? shin wani abu na aikata maka da ka zaɓi cutar da rayuwata? ashe de ganganci ne don na ɗau soyayyata na baka? me yasa ka yaudareni Zaid? meyasa dole saini kazaɓi ka tozarta? Kacutar da rayuwata ka dasamin ƙunci a cikin zuciyata, wlh natsaneka Zaid, Idan har yaudara zata zamemaka abun ado mezaka amfana dashi acikin rayuwarka? Miye ribar aikata zina da fasiƙanci? Natsaneka Zaid! Natsaneka!! Bana fata Allah yaƙara haɗa fuskata da taka fuskar har gaban abada! Dan Allah kafita a rayuwata Zaid!!!" cikin matsanancin kuka taƙare maganar tana me durƙushewa ƙasa domin kuwa zuwa yanzu tsayuwa ya gagarewa ƙafafunta...
Idanun Zaid ne suka kaɗa suka zama jajur dasu tamkar wanda aka zuba musu jan barkono. gaba ɗaya jikinsane yasoma ɓari, shi ɗin ma durƙusawa yayi agabanta cikin murya me tsananin rauni yaƙira sunanta,, saurin ɗaga masa hanu Zahrah tayi alaman batason jin komai daga garesa..
"Banason nasake koda jin muryarkane Zaid, kafita a rayuwata, wai mekake nema dani ne? ko kana tunanin zan sake aminta da kai ne? hmmm kayi babban kuskure Zaid idan kuwa har haka kake tunani, zaifi maka kyau, kamanta dani kakuma manta da wacece ni, ni na barwa Allah cutarwan da kayi agareni, kuma insha Allah nasan zai ɗaukarmin fansa,, sai de inaso kasani cewa har abada bazan taɓa yafe maka ba, inaso kuma kada kamanta da cewar natsaneka !" a fusace ta faɗa cikin gida haɗe da banko ƙofar gidan nasu.
Tashi yayi daga durƙuson da yake haɗe da bin bayanta da kallo, gaba ɗaya zuciyarsa tagama karaya, wani irin abu yakeji ajikinsa yayinda kansa yayi masa wani irin masifaffen nauyi, zafi yakeji azuciyarsa irin sosai ɗin nan.
Zahrah kuwa zamewa tayi jikin ƙofar gidan nasu tasaki wani irin kuka me tsuma zuciya. Se yaushene zata warke daga raɗaɗi dakuma ciwon abun da Zaid yayi mata? ganinsa yasake tasomata da mikin daya ƙi warkewa tsawon lokaci acikin zuciyarta, maiyasa Zaid yazame mata bala'i acikin rayuwarta? kuka tashiga yi sosai da sosai...
Zaid kuwa daƙyar ya iya jan ƙafafunsa yanufi motarsa, kasa tuƙa motar tasa yayi, gaba ɗaya idanunsa duhu suke gane masa, tabbas bazai taɓa iya tuƙa mota yana a irin wan nan halin ba,, da ƙyar ya'iya laluɓa wayarsa yaƙira driver'nsa... Mintuna kaɗan drivern Zaid yazo ya wuce dashi....
Saida tayi kukanta son ranta har sai da taji kanta yasoma ciwo kafun ta tsagaita, haɗe da miƙewa daga jikin ƙofar tashige cikin gida, direct ɗakinta ta wuce ta kwanta numfarfashi kawai take sauƙewa, lokaci ɗaya zazzaɓi yarufeta, harsaida tajawo mayafi ta lulluɓi jikinta....
Sanda yashiga falonsa ko gani bayayi sosai, wani irin ciwo kansa ke masa me tsanani wanda yasanya idanunsa sukayi nauyi, da ƙyar ya'iya jan ƙafansa yashiga ɗaki, kalaman Zahrah ne sukeyi masa yawo acikin kansa,, yatsani jin kalmar tatsaneshi da take yawan faɗa ɗin nan, wlhy a gurinshi da ta faɗi wan nan kalman gwamma ta sharara masa maruka koda kuwa guda biyarne akan ƙuncinsa.. Ya yanke shawara da de yakasance a irin wan nan yanayin ya gwammace yafita daga cikin hayyacinsa idan yaso bayan wasu tsawon lokaci yadawo cikin hayyacin nasa,, wasu ƙwayoyin magani yaɗauko harkala biyu, wanda suke gusarwa mutum da hankalinsa, maganin suna da hatsari sosai hakan nema yasanya ba'a sai dasu a bayyane sai de a ɓoye, kuma suna mugun sa bacci sosai... Saida ya ɓalli guda uku uku daga jikin kowani sachet, kafun ya watsa maganin cikin bakinsa, wan nan karon ko ruwa baisha ba haka ya haɗiye magungunan, yanda kalaman Zahrah ke dawowa cikin kunnensa yafi komai ɗaga masa hankali, kwanciya yayi lamo akan gado yayinda yake ƙwato numfashinsa dake ƙoƙarin ƙwace masa da ƙyar. wani irin fusga numfashinsa yayi lokaci ɗaya kuma komai najikinsa ya sake...
Zahrah kuwa zazzaɓine ya dirarmata me zafin gaske, wanda yasanya lokaci ɗaya jikinta yasoma ɓari ta fara rawan ɗari, har zuwa yanzu hawayenta bai tsaya ba. Zaid ya cuceta itakam duk irin ƙuncin daya jefata a baya bai ishe saba saida yakuma da wowa gareta, sai yaushene hawayenta zasu tsaya? sai yaushene zata samu farinciki ingantacce wanda babu algus acikinsa? tunda ta haɗu da Zaid ƙuncin rayuwarta yasoma, wani irin annoba Zaid yazame mata ne?.....
*(Kuyi haƙuri kuyi manage da wan nan, headache ke damuna, nida Zaid duk cutarmu ɗaya😜 banyi posting da wuri ba wlh network ɗin sim ɗi nane gaba ɗaya ya ɗauke😥)*
*29/December/2019*
*Follow me on Whatsapp and Wattpad*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SHU'UMIN NAMIJI !!*
*Written By*
*Phatymasardauna*
*Dedicated To My Brother KHABIER*
*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
*(💗Wannan page ɗin baki ɗayansa kyautane agareku my wattpadi'ans inagodiya sosai a gareku💗)*
*Editing is not allowed📵*
*CHAPTER 72 to 73*
Baki Labisat dake tsaye taturo gaba haɗe da ɓata fuskarta duk wai akan don Mom ɗinsu tace taƙira mata Zaid a ɓangarensa ne yasa take wan nan abun...
"Tsayuwan uban me kike bacewa nayi ki ƙiramin yayanki ba!" Mom tafaɗi haka cike da faɗa, ganin Labisat ɗin bata da niyar zuwa aiken datayi mata.
"Mom wlhy tsoro nakeji kada naje ya masifance ni!" Labisat tafaɗi haka cikin shagwaɓa.
Harara Mom tawurga mata bashiri Labisat takama hanyar fita daga cikin falon...
Aranta kuwa roƙon Allah take yasa idan taje kada ya masifanceta saboda shi abun faɗa baya masa kaɗan ko kaɗan, jiya jiya dawowanta daga boarding school amma Mom zata haɗata da masifan Yaya Zaid (Su yaya manya😂)
Kusan sau huɗu Labisat tana knocking ƙofar daze kaita cikin falonsa, amma shiru ba amsa, hakan yasanya tatura ƙofar tashiga,, bakowa acikin falon sai daddaɗan ƙamshinsa dake tashi.. Direct ƙofar bedroom ɗinsa tanufa haɗe da soma knocking ƙofar,, jin shiru ne yasanya tashiga ƙiran sunan sa...
"Brother! Brother!" ko gyaran murya bataji yayiba balle tasa ran zai amsa mata, batama tabbatar yana cikin ɗakin ko baya ciki ba..
Gajiya tayi da knocking ƙofar ta juya tayi tafiyarta...
"Mom inaga fa kamar Bro bayanan domin nayita knocking door ɗinsa amma bai amsa ba"
"Tabbas yana cikin gidan nan Labisat domin kuwa tunjiya daya shigo baifita ba, har me gadi na tambaya naji ko yaga fitarsa amma yacemin tunjiya daya shigo bai fita ba, miskilancin nasa ne ya motsa, banaje dakaina nasa mesa nikam ae be isa yanunamin halin ƙyaliya ba" Mom tafaɗi haka tana me miƙewa tsaye daga zaunen da take..
Itama ɗin de knocking tayi masa haɗe da ƙiran sunansa amma shiru bai amsata ba, hakan yasa ta murɗa handle ɗin ƙofar ta kutsa kanta ciki bakinta ɗauke da sallama..
Tsuka Mom taja sakamakon ganinsa da tayi kwance akan gado yayi ruf da ciki, lallai ma wato iskancine ya hanasa amsa mata, da fari hartayi zaton ko baya gidan ne..
"Zaid!" taƙira sunansa cikin kakkausar murya... Ko motsawa baiyi ba balle tasaran ze amsa mata..
Kafeshi da idanu tayi tana me nazartarsa, a iya saninta da Zaid baya bacci a irin wan nan lokacin, impact ma shiba mutum bane ma'abocin yawan bacci ba'a bisa ƙa'ida ba, idan kuwa harda gaske baccin yake to baya rasa ɗayan biyu kodai baida lafiya ko kuma yayi halin nasa nashan ƙwayoyi, "Sai yaushene Zaid ze san ya girma? sai yau shene zai dena nuna rashin damuwa da lafiyarsa?" tajeromawa kanta waƴan nan tambayoyin, "Haƙiƙa Zaid ɗanta ne amma ita kanta har yau batasan wani irin haline da shi ba, shi mutum ne me nuƙu nuƙu bakoda wani lokaci ne kake sanin gaba da bayansa ba, haka nan yake bakomai ne zaka masa ƙa burgesa ba yanada wani shegen shu'umin hali saide kawai Allah yashirya mata shi"...
A hankali tashiga takawa zuwa gaban gadon nasa..
Idanu Mom tasake warowa waje, tabbas idan de idanunta de de suka gane mata to kuwa Zaid baya numfashi, domin babu wata alamar da take nuna akwai nunfashi a tattare dashi saboda ko cikin sa baya motsawa, alama ta baya shaƙan numfashi kenan..
Hanunta takai setin hancinsa ko da zataji ɗumin numfashin sa.
Salati Mom tasa haɗe da dafe ƙirjinta, sakamakon wani irin bugawa da taji zuciyarta tayi.
"Zaid!Zaid!" Mom tashiga ƙiran sunansa cikin tashin hankali haɗe da soma jijjigasa.
Hawayene suka shiga bin ƙuncin Mom bashiri ta fita daga ɗakin, direct ɓangaren Alhaji Ma'aruf ta nufa saboda yana gida baikai ga fita office ba..
"Alhaji! Alhaji! katemaka wlhy Zaid baya numfashi zo muje ka gani, katemakeni kada na rasa ɗana mafi soyuwa a gareni!!" gaba ɗaya cikin tashin hankali Mom keyimawa Dad bayani..
Mamaki haɗi da al'ajabi ne yakama Alhaji Ma'aruf amma de yanzu balokacin tambaya bane gwamma yabita yaga meke faruwa da Zaid ɗin....
Shima sosai ya tsorita kuma hankalinsa yatashi daganin Zaid yashe a gado baya numfashi sai kace gawa...
Da ƙyar Abba ya'iya sungumarsa yasanyasa a mota, abunka da ƙaƙƙarfa kuma ma'abocin yin gym shiasa jikinsa yake ko ina a murɗe, san nan kuma me ƙaramin ƙarfi bazai iya ɗaga sa ba, Dad ɗin ma saida temakon Mom ya iya ɗagasa... Daga Mom har Labisat hankalinsu amatuƙar tashe yake haka suka shiga mota suka rankaya zuwa asibiti...
Direct Emergency aka kai Zaid cikin gaggawa likitoti suka shiga basa temakon gaggawa...
Jigum jigum haka Abba da Mom sukayi a wani ɗan corridor dake kusa da ɗakin da aka kai Zaid, iya ƙololuwar tashin hankali sun shigesa, kuka kawai Mom da Labisat keyi, kasa koda rarrashinsu Alhaji Ma'aruf yayi domin shima da akwai hali da kukan ze sanya ko da zaiji sassauci a cikin zuciyarsa...
Likitotin nan sunci baƙar wahala kafun da taimakon Allah suka samu suka daidai ta numfashin Zaid. Haka suka fito suna sharce gumi.... Kallon Alhaji Ma'aruf ɗaya daga cikin Doctors ɗin yayi haɗe da cewa "Ranka ya daɗe muje office" ƙoƙarin binsu Mom tasomayi Alhaji Ma'aruf yaɗaga mata hanu alamar tajirasu....
Handkerchief likitan nan yaɗauka ya ƙare share gumin dake tsatstsafawo akan goshin sa..
Ganin haka yasa Abba cike da tashin hankali yace "Yade Dr.Bilal meke faruwa ne, dan Allah kada kafaɗamin wani mummunan labari!"
Jinjina kai Dr.Bilal yayi haɗe da kallon Dad. "Kwakwantar da hankalinka Alhaji zuwa yanzu komai ya daidaita munshawo kan matsalan"
Nannauyar ajiyar zuciya Dad yasauƙe haɗe dayin hamdala acikin ransa...
Sake gyara zama Dr.Bilal yayi haɗi da cewa "Sai de kuma agaskia bazan ɓoye maka ba Alhaji ɗan ka yana cikin matsala wanda yake gab da rasa rayuwarsa matuƙar baikiyayewa kansa shan ƙwayoyi masu mugun haɗari ba, baya ga haka kuma idan har ya cigaba dashan giya nan da ƴan kwanaki tofa sai de kuma abun da Allah yayi!"
Yanzukam Dad ne yashare gumi ba Dr.Bilal ba, domin kuwa a iya tsawon rayuwarsa baitaɓa sanin Zaid nashan wasu ƙwayoyi masu bugarwa ba, yade san da ya nashan giya amma kuma atunaninsa yajima da dena shan giyan.
"Bangama fahimtarka ba likita, naji kace ƙwayoyi na bugarwa, kana nufin shiɗin ne yakeshan ƙwayoyin bugarwa?" Dad yatambayi Dr.Bilal cike da son sanin ƙarin haske akan batun..
"Wato a iya bincikenmu mungano cewa akwai wata ƙwaya me haɗarin gaske da yakesha lokaci zuwa lokaci, wanda kuma haɗarin ƙwayar yana da matuƙar yawa, bazanyi mamakin a ina yasamu ƙwayan ba, saboda nasan shiɗin isashshene, saboda ƙwayar ba ako ina ake samunta ba, a ƙa'ida ma anhana shigo da ƙwayar nan gida Nigeria, kawai de rayuwar yanzune da ta zama sai a hankali, zai iya yuwuwa kuma ba anan yake sayan ƙwayan ba daga can waje yake shigowa da abarsa, sai de kuma wan nan duk bashine damuwar ba, idan har ya cigaba da shan wan nan ƙwaya to ina me tabbatar maka da cewa zai iya rasa ransa ako da yaushe, duk da kuwa dama munsan mutuwa tana kan kowa yanzu ko anjima, amma tabbas kiyayewan shine yafi, san nan kuma giya tayi masa mummunan illa saboda tasamu mafaka acikin cikinsa, wataƙila yamai da ita ruwan shansa ne, amma kuma duk hakan ba wani babban matsala bane idan har ze kiyaye to da taimakon Allah komai zezo masa cikin sauƙi!"
Salati Alhaji Ma'aruf yayi a bayyane haɗe da sanya hanu yazame hular dake kansa, ashe bayan giya hadda wata tsinanniyar ƙwaya me haɗari Zaid yake sha? anya kuwa Zaid yanada cikakken hankali? shin wani irin haline haka da Zaid? amma babban abun tambayar shine laifin waye acikinsu, laifinsune su iyayensa kokuwa laifinsa ne shi kansa Zaid ɗin?
"Haƙiƙa dukansu suna da laifi, amatsayinsu na iyaye basu wani tsaya sunbawa Zaid kyakkyawar kulawa ba, kuɗi kawai suka sake masa haɗe da turasa makaranta har wata uwa duniya, amma duk da haka bekamata ace yakasance haka ba, idan su basa lura da al'amuransa shi ɗin mahaukaci ne da be san dede ba? tabbas yasan shiyake da alhakin kulawa da tarbiyan Zaid tunda shine yaɗaukosa daga wajen Mahaifiyarsa yadawo dashi America kusa dashi, tunda suke America bai taɓa tsayawa da kyau yakula da wani irin rayuwa Zaid ɗin keyi ba, shide kawai yabuɗe masa bakin aljihu yana ganin hakan shine gata, ƙwarai mafiyawancin iyaye ayanzu sunfi bada kulawarsune ga Ƴaƴa mata, yayinda ƴaƴansu maza kuwa ko oho, duk wata kyakkyawar tarbiya Ƴaƴa mata ake ƙoƙarin koyawa, yayinda Ƴaƴa maza kuwa suka zama hoto, aganin iyaye komiye ɗa namiji yayi adone bakamar ƴa mace ba, tabbas hakane duk abun da ɗa namiji yayi adone bakamar mace ba, amma hakan bawai yananufin shi ɗa namiji abarsa sakaka haka bane batare da annuna masa kulawa ba, shi namiji a koda yaushe ana ganin zai iya kula da kansa, amma yana da kyau ana nuna masa kulawa ana kuma jansa ajiki kodan yasamu inda zena faɗan damuwarsa, kowafa yanason yasamu tarbiya me kyau daga Namiji har mace, saboda haka yazama lalle iyaye su tashi tsaye wajen kulawa da ƴaƴansu maza saboda ba mata ne kaɗai suke buƙatan kulawa ba harsuma maza suna buƙata......
Dr.Bilal ne yakatse Dad daga tunanin da yafaɗa me zurfi tahanyar cewa da yayi dashi. "Zaid yana buƙatar hutu saboda haka sai nan da 4 hours kafun su samu ganinsa"
Jiki ba ƙwari haka Dad yafito daga office ɗin yanufo inda su Mom ke tsaye suna sharce hawaye..
"Yaya de Alhaji me likitan yacema?" Mom tatambaya cike da damuwar son sanin wani hali ɗanta yake ciki..
"Kada kidamu, ku kwantar da hankalinku jikinsa da sauƙi zuwa anjima kuma insha Allah zamu samu ganinsa yanzu likita yace yana buƙatar hutu ne, to dole zamu barsa yaɗan huta" Dad yaƙare maganar yana me kamo duka hannayen mom alamun rarrashi..
Hamdala Mom tayi haɗe da sauƙe ajiyar zuciya
Sake kallon Dad tayi cikin yanayi na tuhuma tace "Meyasanya naga fuskarka ɗauke da tashin hankali me tsanani Alhaji?"
Murmushin dole Dad yanemo ya ara akan fuskarsa bayason faɗa mata wan nan maganar yanzu yafiso saisun samu nutsuwa sunkoma gida tukunna, sai de kuma abun da shi besani ba shine tafikowa sanin cewa Zaid yanashan giya, saboda tasha kamasa acikin maye yayi mankas, san nan kuma tajima da sanin cewa yanashan ƙwayoyi, sede abun da bata sani ba shine haɗarin da ƙwayoyin suke ɗauke dashi....
********
Haka Zahrah tawayi gari yau da zazzaɓi sede duk da haka bata nunawa kowa cewa bata da lafiya ba, sede kuma idanunta sun kunbura sakamakon kukan da taci ta ƙoshi a daren jiya..
Haka de tashirya kanta tsab don zuwa makaranta amma kowa yaganta yasan bata da wani isashshen kuzari a tattare da'ita,, ko abun kari bata tsaya taci ba haka ta fice a gidan nasu....
********
"Kuka bazai taɓa yimiki maganin komai ba Zahrah, tabbas nasan kinajin raɗaɗi a cikin zuciyarki amma zuwa yanzu yakamata ace kimanta da baya kifuskanci gaba, aure zakiyi yanzu babu amfani kicigaba da sanya kanki cikin ƙunci!" Husnah tafaɗi haka ga Zahrah cikin yanayi na tausasawa, kasancewar duk wunin yau ɗin da sukayi amakaranta bata gane kan ƙawarta ta ba...
Hannayen Husnah duka Zahrah takama haɗe da kallonta. Cikin murya me rauni tasoma cewa.....
"Ni kaina inaso naganni cikin farinciki Husnah, amma nasan hakan bazai samu ba matuƙar Zaid yana raye a doron ƙasa, koda ma ace baya raye nasan bazanyi farinciki ba Husnah saboda yariga daya gama lalatamin rayuwa, bana tunanin cewa akwai wani namiji da zaiyi ɗokina idan ya aureni? Shifa budurci wani abune me matuƙar mahaimmanci a rayuwar ƴa mace Husnah, babu wani mutumci dakuma karamci wanda ya wuce mace takai budurcinta ɗakin mijinta, mafi ganganci da kuskure da mace zata aikata kafun aurenta shine ta yarda ta bawa wani kyautar budurcinta, mata irina suna da yawa Husnah wa ƴanda aka mawa fyaɗe aka ƙwaci budurcinsu da ƙarfin tsiya, san nan kuma akwai waƴanda maza suke ruɗansu da kuɗi ko kuma da soyayya harsu yi nasaran rabasu da budurcinsu, san nan akwai kuma wanda dan kansu suke bada kyautar nasu budurcin ga wani daban, rasa budurci abune me matuƙar ciwo Husnah musamman ma ga iri na wanda aka mawa fyaɗe, Yawancin maza suna fatan idan sunyi aure su samu matansu da cikekken mutumcinsu, inde kuwa har a matsayin budurwa suka aureta, haƙiƙa akwai wata soyayya dakuma girmamawa dake shiga tsakanin mace da mijinta matuƙar takawomasa budurcinta ɗakinsa, saɓanin haka kuwa shike hargitsa tunanin namiji, shike jagulawa mace zaman aure'nta, koda ace ya yarda ƙaddarane hakan amma tabbas wani lokaci abun zaina masa ciwo, duk da nasan cewa Dr.Sadeeq yasan komai daya faru dani, amma duk da haka tabbas nasan duk randa yakusanceni saiyaji ciwo acikin ransa, saikuma yaji wani abu saɓanin tunaninsa, shi a yanzu yana ganin cewa hakan bakomai bane, amma kuma hakan komai ne bakuma ze gane hakan ba sai randa ya aureni yakuma nemi dana basa haƙƙinsa na aure,, wan nan ranan nake gujewa kaina Husnah bansan ina zan tsoma kai da zuciyata ba amma nabarwa Allah komai!!" gaba ɗaya hawaye sungama wankewa Zahrah da Husnah fuska, lalle kuwa wan nan itace mummunar ƙaddara wand ba'a taɓa mantawa da'ita,, rungume Zahrah Husnah tayi cike da tsananin tausayin ƙawarta ta,,, tabbas duk abun da Zahrah tafaɗa gaskiya ne kai budurci ɗakin miji yafi komai daɗi a rayuwa saboda ko ba komai zaiƙara muku danƙon soyayya dakuma mutunta juna, duk da cewa Zahrah ba'asonta tarasa budurcinta ba amma kuma tabbas kamar yanda Zahrah ta faɗa hakan yake dolene Dr.Sadeeq zaiji zafin abun sosai aduk ranarda kusantar farko tashiga tsakaninsu, amma kuma babu wanda ya isa ya tsallakewa ƙaddararsa.....
Hawayenta tasanya hanu tashare kafun tashiga sharewa Zahrah ma nata hawayen,,,,
"Ki kwantar da hankalinki Zahrah komai zai zo cikin sauƙi insha Allah taso muje musamu ruwa muwanke fuskarmu ko"
Ba musu Zahrah ta tashi tsaye Husnah takama hanunta suka nufi wajen da sukasan zasu samu ruwa......
***********
Jigum haka su Dad dake tsaye agefen gadon Zaid sukayi, yanzu awa 5 kenan suna irgawa batare daya buɗe idanunsa ba, gashi kuma 4 hours likita yace musu zaiyi....
Babban yatsar ƙafansane tasoma motsawa kafun idanunsa da sukayi nauyi suka soma buɗewa a hankali,, da sauri Dad ɗinsa yaƙaraso jikin gadon yanayi masa sannu...
Ƙoƙarin tashi zaune yasomayi da sauri Dad ɗinsa yamaidasa ya kwanta "Ba sai ka tashi ba Zaid yakamata kabari kaɗan wastsake tukunna kafun kasoma yunƙurin tashi"
Ɗan yamutsa fuska Zaid yayi haɗe dabin ledar ruwan da aka ɗaura masa da kallo.
Dai de lokacin Labisat suka shigo ita da Dr.Bilal domin dama Mom naganin Zaid ɗin yabuɗe ido tace da Labisat tayi mata ƙiran Doctor...
Ƴan gwaje gwaje Dr.Bilal yayi masa haɗe dayi masa wasu ƴan tambayoyi, ko motsawa bakin Zaid beyiba balle Dr.Bilal yasa ran samun amsa, ganin haka yasa Dr.Bilal yin murmushi batun yauba yasan Zaid ɗin saboda haka shirun da Zaid ɗin yayi masa bawani abu bane daya kamata ace yadamu ba,, kallon Dad Dr.Bilal yayi haɗe da cewa
"Ko yanzu idan kuna buƙatar sallama se a baku saboda babu wata damuwa, se daifa a kiyaye kamar yanda na faɗa"
Kai Dad yajinjina haɗe da cewa "Shikenan Doctor insha Allah za'a kiyaye, muje sai nakarɓi takardan sallaman ko" Dad da Dr.Bilal suna fita Zaid yatattaro duka wani kuzarinsa dayayi masa saura yamiƙe tsaye, kafaɗun Labisat dake tsaye kusa dashi ya kamo haɗe da ɗaura hanunsa akan kafaɗan nata suka nufi hanyar fita daga ɗakin, domin kuwa koda Dr.Bilal be basu sallama ba tabbas bazai ƙara 1 hour a cikin asibitin ba...
Yana riƙe da kafaɗan Labisat harzuwa cikin mota, shida Labisat mota ɗaya suka shiga, yayinda su Dad da Mom suka shiga wata motar wanda duk su sukazo da ita... Direct gida suka nufa
Idanunsa gaba ɗaya suna a lumshe yayinda yajingina bayansa a jikin kujeran motar wanda yake zaune akai.
Ɗan satan kallonsa Labisat tayi hakanan taji wani irin mugun tausayin ɗan uwan nata ya kamata, tabbas basuyi wani shaƙuwa da yayan nata ba amma tafuskanci cewa yanacikin damuwa, takuma tabbatar da cewa sanadin damuwarne ma har ya kaisa ga kwanciya a asibiti, to wan nan wace irin damuwace yayanta yake ciki haka? tabbas zataso sanin damuwar dake damunsa saboda tana matuƙar son ɗan uwan nata bandashi batada wani ɗan uwa dasuke uwa ɗaya uba ɗaya shikaɗaine yayanta kuma garkuwanta......
Koda suka isa gidama Labisat ce tarakasa har ɓangarensa,, zama yayi akan kujera haɗe da jawo wani ɗan ƙaramin table ɗin dake tsakiyar falon yaɗaura ƙafafunsa akai..
"Yaya mezan kawo maka, yakamata kasa wani abu acikin ka!" cike da ɗar ɗar Labisar tafaɗi maganar saboda tasansa sarai ba'a iyarmasa yanzu saiya saceka..
"Friedrice" yafaɗa a taƙaice batare kuma daya buɗe kyawawan idanunsa dasuke a lumshe ba..
Jiki na mazari haka Labisat ta tafi kawo masa friedrice ɗin dayace, domin kuwa dama agidan nasu ba a rasa friedrice..
Mintuna kaɗan tadawo hanunta ɗauke da ƙaton tire hadda plate ɗin yankakkun kayan marmari akan tire ɗin,, adede gabansa ta ajiye tire ɗin haɗe da ɗaukan plate ta buɗe kulan da friedrice ɗin ke ciki ta zuba masa.
"Yaya gashinan na kawo" tafaɗa tana me tura masa plate ɗin friedrice ɗin gabansa.
Ganin da tayi bece da ita komai ba yasanyata miƙewa sumu sumu tafice daga falon nasa...
Jawo plate ɗin yayi gabansa yasoma tsakuran abincin yanaci kaɗan kaɗan duk da kuwa bawai buƙatar abincin yakeyi ba adole kawai yakeci... Lomansa huɗu ya aje spoon ɗin dake hanunsa haɗe da jawo plate ɗin yankakkun kayan marmarin dake gabansa yasoma sha, sai alokacin yasoma jin daɗin bakinsa, amma da kwata kwata bayajin ɗanɗanon komai,, fruits ɗinma baiwani sha me yawaba haka yature yakuma maidakansa yajingina da kujera,, idan akwai abun dayake ƙauna dakuma muradin gani yanzu arayuwarsa baiwuce Zahrah ba, dole yaje gidansu ayau ɗin koda kuwa idan yaje zata ɗauki wuƙa ne taluma masa a cikinsa.....
Yauma de kamar kullum Zaune take a tsakar gidan nasu, kwanon abincine aje agabanta tana tsakura da kaɗan kaɗan tana kaiwa bakinta domin kuwa haryanzu bata wani jin daɗin jikinta..
Inna ce zaune daga gefenta tana ta ƙoƙari wajen ganin ta seta tashan radion ta..
Wani yarone yayi sallama yace wai ana ƙiran Zahrah,, "Jekace tanazuwa" Inna tahanzarta faɗa, har yaron yakama hanyar fita daga gidan, Zahrah ta tsaidasa haɗe da cewa "Kace bazata zo ba"
Hangame baki Inna tayi tana kallon Zahrah "Bazakijeba fa kikace?"
"Eh Inna dan Allah kuma kada kitambayeni dalili" tayi maganar tana me langwaɓar da kanta gefe.
Harara Inna ta watsa mata haɗe dayin tsuka baƙin ciki kawai Zahrah'n takeyi mata wayasani ma ko wanda ke ƙiran nata da alkhairi yazo...
"Wai Bazata zoba" yaron nan yafaɗawa wanda ya aikosa.
Waro idanu Zaid yayi maganar ma shi dariya taso basa, amma a irin wan nan yanayin dayake ciki bayatunanin zai iyayin dariya...
"Wayene yacema bazata zo ba?" Zaid yatambayi yaron.
"Ita da kanta" yaron yabasa amsa domin kuwa shiɗin ɗan maƙotansu ne saboda haka yasan Zahrah'n.
Kai Zaid yajinjina haɗe da cije laɓɓansa,, Allah sarki rayuwa babu yanda bata juyawa mutum, amma in banda haka wai yau shine a wata ƙasƙantacciyar unguwa kuma ƙofar gidan su mace yakuma aika tace bazata zo ba, shine fa Zaid ɗin da har gobe ƴan mata suke rushing akan sa, to amma meyasa haka takasance dashi?" ganin da yayi yaron nashirin tafiya ne yasanya yace "Kaje kace injini nace tayi haƙuri tafito" bamusu yaron yakoma yakuma faɗi saƙon da akabasa umarnin yafaɗa..
Tsuka Zahrah taja haɗe da tashi tsaye "Kaje kace wai inji Zahrah kozai mutu a tsaye baza ta zoba" tanakaiwa nan azancenta tayi wucewarta ɗaki..
Abunda Zahrah tafaɗa shi yaron nan yazo ya sanarwa Zaid, kuɗi Zaid yaciro a aljihunsa 1k yabawa yaron dafari yaron yatsorita yaƙi amsa, amma Zaid yatilasta masa saida ya amsa, haka yaron yatafi yana murna...
Motarsa yabuɗe yashiga yayinda yakifa kansa a steering motar meyasa soyayya zata masa haka, idanunsa Zahrah kawai suke son gane masa tabbas yau bazai taɓa iya runtsawaba matuƙar baiga Zahrah ba, yana mawa Zahrah wani irin mugun so me tsananin zafi.. Jan motarsa yayi yakoma ƙarƙashin wata bishiya tayanda bakowa zai lura da cewa yana wajen ba, yaƙudurta aransa cewa koda zai kwana a wajen ne bazai gusa ba harsai idanunsa sun mai tozali da Zahrah....
Bayan awa ɗaya
Zahrah ce tafito daga cikin gidan nasu sanye da wani siririn mayafi wayarta ce riƙe a hanunta se kuma wani littafi. Zaid dake zaune cikin motarsa yana ganinta ya sake waro idanu haɗe da sauƙe ajiyar zuciya me ƙarfi, jiyakeyi tamkar yaje ya ɗauƙota can caɗak yatafi da ita... Yana kallonta tayi shigewarta wani gida dake kusa da nasu gidan.. Bayan kamar mintuna 8 da shiganta gidan yaga takuma fitowa da sauri yabuɗe murfin motarsa daniyar ƙarasawa gareta sai de kuma ko taku biyu baiyiba tashige cikin gida ko ganinsa ma ita batayi ba, haushine yasanyashi buga tayar motarsa da ƙafarsa, haka yakoma yayiwa motarsa key haɗe dayin reverse yabar unguwar tasu cike da ƙuncin rashin samun daman yi mata magana da be yiba, amma de yaji sanyi sosai a zuciyarsa daya ganta...
*********
Yau tunsafe Zahrah tashiga busy hidama kawai sukeyi ita da Husnah domin kuwa yaune ranar da Dr.Sadeeq yace mata za'a kawo lefenta,, yanzuma daga shopping suke sunje sun sayo kayan drinks da kuma su snacks wanda za'abawa baƙi. Zama sukayi akan tabarma suna me da numfashi saboda sungaji sosai,,, kallon Zahrah Husnah tayi haɗe da sakin murmushi.
"Ƙawata nifa yau daɗi nakeji jinake tamkar ma nice za'a kawowa lefen" dariya Zahrah tayi haɗe dacewa "To aike kince bayanzu zakiyi aure ba saikin gama school gashi Nuruddeen yana tsananin son kuyi aure amma ke kinƙi"
"Hmm ai zan masa maganane yaturo kawai domin ni mafa yanzu dagaske auren nakeso nagaji da rungumar pillow idan nazo bacci" Dariya suka sanya su dukansu hadda tafawa, "Allah yashiryeki Husnah" Zahrah tafaɗa tana dariya.. Haka de sukaci gaba da ƴan hirarrakinsu irin na ƙawaye..........
Ƙarfe biyar dai dai wasu rantsa rantsan motoci suka soma tsayuwa a ƙofar gidan su Zahrah duk macen da tafito acikin motar sai kaga tana yatsuna fuska haɗe da soma ƙarewa wajen gidansu Zahrah kallo, motocine kusan guda goma sha biyu suka kawo kayan lefen ahankali aka shiga fito da akwatuna ana shiga dashi cikin gidan su Zahrah.. Fuska babu yabo ba fallasa haka matan nan suka soma shiga cikin gidansu Zahrah,,,,, da fari'a Inna da tawagarta suka tarɓi mutanen haɗe da basu wajen zama, haka suka zauna wasu daga cikinsu suna yatsuna fuska kamar wanda akace su zauna akan kashi...
"Sannunku da zuwa lale marhaba" Wata mata maƙociyar su Zahrah tafaɗa ga matan da suka kawo lefen. Amma kuma daƙyar aka samu biyu daga cikinsu suka amsa mata..
Akwatuna ne harguda shabiyu aka jibge akan wata tabarma dake shimfuɗe,, su Inna ne suka fara ɗagawa matan da suka kawo lefen gaisuwa ciki ciki suka amsa musu cike da isa,,,,, Aunty Raliya ce ma tayi ƙarfin halin cewa "Ga kayanan munkawo Allah yasa ayi bikin a sa'a, Allah kuma yasa asamu kyakkyawar zuri'a" dagajin yanda tayi maganar kaɗai ya isa ya tabbatarmaka cewa kalaman ba anyi su bane cikin daɗin rai,,, da Ameen kawai su Inna suka amsa musu,,, kuɗi Aunty Raliya taciro acikin jakarta bandir ɗin ƴan dubu dubu har na dubu ɗari ta ɗaura akan wani akwati haɗe da kallon ƴan uwanta tace "Muje ko" dukansu miƙewa sukayi suka nufi hanyar waje,,, yayinda Inna tasa yaran maƙotansu suka kwashi kayan tarban baƙin da suka musu aka kai musu cikin mota, maman Badi'a ɗaya daga cikin maƙotan su Zahrah ita tazari dubu hamsin daga cikin kuɗin da suka aje tabawa ƴarta Badi'a tace takaiwa matan dasuka kawo lefen,,, dawowa da kuɗin Badi'a tayi tace ae sun riga da sun tafi koda tafita ƙurar motarsu kawai tagani,,, "To suko wasu irin mutanene haka ae ba haka akeyi ba, ko fa kayan basu tsaya sun nuna mana ba saikace wanda suke akan ƙaya" Maman Badi'a tafaɗi haka cike da mamakin hali irin na matan da suka kawo lefen,,, washe da baki wata mata daga cikin gayyar Inna tace "Kai amma kuwa Zahrah tayi goshi kuga kayafa kamar wanda za a buɗe kanti" ae kuwa basusan cewa Zahrah tayi goshi ba saida suka soma buɗe akwatunan,, kowanni akwati shaƙe yake da kaya nagani na faɗa,, take Inna tasoma rangaɗa guɗa hadda rawan murna.......
(Team Dr.Sadeeq da Zahrah saiku wanke ƙafa don zuwa gano kayan lefen Zahrah🤗)
*31/December/2019*
*Follow me on Whatsapp and Wattpad*
*Wattpad user name fatymasardauna*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SHU'UMIN NAMIJI !!*
*Written By*
*Phatymasardauna*
*Dedicated To My Brother KHABIER*
*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed: our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
*Editing is not allowed📵*
(Kutayani jaje wlh sau biyu kenan typing ɗina yana gogewa😨😨 yanzu saida nayi 2000 words wlh ya kuma gogewa maganan danake wlh yanzu haka ina rubutun nan ina kuka😭😭 wlh abun da ciwo sosai😭😭)
*CHAPTER 74 to 75*
Hayaniya haɗi da guɗan da su Inna keyi shiyayi sanadiyar janyo hankalin Zahrah dakuma Husnah da suke zaune a ɗakin Zahrah sunyi muƙus,,,,
"Ke nifa tashi zanyi naje nabawa idanuna abinci, dan wlh bazan iya zama aɗaki kamar wata sabuwar amarya ba, ke dai da zaman yazamemiki dole saiki ta fama" Husnah tafaɗi haka tana me miƙewa tsaye daga zaunen da take,,, murmushi kawai Zahrah tayi mata haɗe da binta da kallo hartafice daga cikin ɗakin...
Hamdala Husnah tayi haɗe da nunatsantsar farincikinta alokacin da idanunta sukai mata tozali da kayan lefen ƙawartata,,,, lallai Dr.Sadeeq yayi ƙoƙari domin kuwa naira tayi kuka, koda kyawun akwatunan aka barka sun isa sanyaya maka rai, balle kuma aje ga kayan ciki masu kyau da tsadar gaske, wan nan shiyasake tabbatar mata da cewa Zahrah bazatayi kuka ba idan ta auri Dr.Sadeeq, saboda me sonkane kaɗai zai iyayin komai dayasan zai faranta maka rai....
Duk yawan atamfofin dake cikin akwatunan nan saida su Inna suka irgesu kaf, turame hamsin banda su laces haɗi da shaddodi dakuma dangin su materials,, ɓangaren dogin riguna ma akwati guda aka cika dasu, sosai kuma yasaki bakin aljihunsa wajen zaɓo masu kyau da tsada,, haka ɓangaren sarƙokima komai yaji domin kuwa kaf cikin sarƙoƙi da ɗan kunnayenta babu wani mai sauƙin kuɗi acikinsu gwala gwalanta har guda uku,, san nan kuma ɓanagaren jaka da takalma ma yayi ƙoƙari sosai, domin kuwa kusan kowani kaya yanada jaka da takalmi hadda mayafinsa,, wajen kayan shafa ma yayi ƙoƙari sosai wajen fidda naira yasai kayan shafa ƴan yayi masu kyau duk da kuwa yasan cewa ita ba gwanar kwalliyan fuska bace...
"Gaskiya kaya yayi kyau yarinya tayi goshi, ai wan nan kayan ko ɗiyar babban attijiri sai haka" Maman Badi'a tafaɗi haka bayan taƙarewa wani haɗaɗɗen leshi dake riƙe a hanunta kallo wanda a ƙalla kuɗinsa zai kai 50k,,,
"Ƙwarai kuwa yarinya tayi goshi Maman Badi'a ai dama tuntuni nasan fiye da haka ma sai yafaru, ga kaya kan nan harda nasadakarwa!" Inna tafaɗi haka cikin murna...
Wata dake zaune kusa da Inna tace "wan nan haka yake muma dai Allah yabawa namu ƴaƴan mazajen aure masu ƙashin arziki"
Duka matan suka haɗa baki wajen cewa Ameen domin kuwa babu wacce zataƙi ace ƴarta ce tasamu wan nan kayan more rayuwan....
Sai kusan magriba matan dasuka karɓi lefen Zahrah suka soma tafiya, bayan Inna ta yaga musu wani abu daga cikin dubu hamsin ɗin daya rage,, haka suka tafi suna mata godiya suna kuma zuba santin kayan domin kuwa koda maƙiyin Zahrah ne yaga wan nan uban kaya da Dr.Sadeeq yayi mata tabbas dole sai ya jinjina abun.....
Lokacin da Zahrah taga irin yawan kayan lefen da Dr yayi mata kasacewa komai tayi, sosai abun yabata mamaki domin kuwa bata taɓa zaton zai ɓarnata dukiya mai yawa harhaka wajen yi mata lefe ba, bayan kuma yasan cewa ita ba cikakkiyar budurwa bace,,, sai de taƙudura aranta cewa zata faɗa masa kayan sunyi yawa......
Gidansu Doctor...
"Gaskiya da sake Hajiya, yakamata a dakatar da wan nan batun auren na Sadeeq da yarinyar nan, kinkuwa ga gidansu Hajiya? wlhy ko suminti babu a tsakar gidansu zallan turbuɗin yashine, kallo ɗaya zakai musu kafuskanci cewa suɗin faƙara'une basu da komai, kwata kwata ma Sadeeq baisan inda zaije ya nemo aure ba domin a wan nan gidan bana tunanin akwai wata halitta da zata burge wani ɗa namiji acikinsa, kawai dai ni inaga ma asiri sukayi masa wlhy, amma bacin haka banjin dakansa zaije neman aure wan nan gidan!" Auntie Raliya ce ke faɗan haka cikin ɓacin rai.....
Ajiyar zuciya Hajiya tayi cikin ɗacin rai tace "Hmmm Raliya kenan aeni ban isa hana wan nan auren ba ko kinmanta cewa har ƙarana wajen Baffan ku Sadeeq yakai akan naƙi amincewa da aurensa, ni yanzu baruwana acikin lamarin aurensa ko mai ya jajiɓowa kansa shiya sani"
Ƙwafa Auntie Raliya tayi haɗe da sakai tafice daga cikin ɗakin Hajiyar, harga Allah ita sam batason wan nan auren da Sadeeq zaiyi, yarasa ma wacce zai kwaso musu sai wacce wani ya haiƙewa a waje san nan kuma ƴar talakawa futuk...
Auntie Raliya tana fita falo ƙawayenta da ta gaiyato suka kai lefe tare, sukayi caaa akanta kowacce tana ingizata akan cewa tasa afasa auren domin kuwa sam ajin Sadeeq yagirmewa neman aure a wan nan gidan matsiyatan,,, take kuwa Auntie Raliya tahau kan zancen tazauna dabas, takuma ƙuduri aniyar lalata zancen auren abune me sauƙi kuma dakanta zataje ta kwaso kayan lefen ƙanin nata........
Ɓata fuska Zahrah tayi haɗe da tunzuro ɗan ƙaramin bakinta gaba cike da shagwaɓa tace "Dagaske nake faɗa maka kayan lefen nan sunyi yawa, ko ɗazu dawowan Baffa daya gani shima haka yace, kuma kafasan ba kyau yin wasa da dukiya" taƙare maganar tana me langwaɓar da kanta gefe.
Murmushi Dr.Sadeeq yayi haɗe da kwantar da bayansa ajikin kujeran motar dayake zaune akai kana ya lumshe gajiyayyun idanunsa, sautin muryarta nayi masa daɗi sosai...
Shirune yashiga tsakaninsu har na tsawon minti ɗaya.
"Duk abun da mayi miki kin can can ci haka daga gareni ne Zahrah, dan Allah kibar maganar yawan lefen nan, ni banga wani yawa da sukayi ba, naso ma nayi miki wanda yafi wan nan to abubuwane sukai min yawa, amma kin wuce haka a wajena, kuma kinsan ku biyu ne" yafaɗi haka yana me kafeta da idanunsa..
Murmushi kawai Zahrah tayi haɗe da kawar da kanta gefe, sam bataso idan yana kallonta itama ta kalleshi saboda takanjin nauyinsa awasu lokutan,, amma kuma hakanan taji kalmar dayace su biyu ne yaɗan sosa mata rai, wato idan ma ta manta to yatuna mata...
Wani murmushin Dr.Sadeeq yakumayi sakamakon ganin yanda fuskarta ya ɗan sauya lokaci ɗaya yakuma san maganarsa ce batai mata daɗi ba, dama kuma yafaɗi hakanne don yagane cewa tana kishinsa ne ko a'a....
"Bansan wani irin daɗi da kuma farinciki zan tsinci kaina ciki ba aduk sanda wannan ranar taruskeni, amma kuma da zanfi kowa jin daɗi idan har Allah ya gwadamin wannan rana!" yafaɗi haka cikin shauƙi, dason kawar da wancen zancen nasu..
Cike da mamaki Zahrah taɗan saci kallonsa haɗi da cewa "Wace rana ce wan nan?"
"Ranar da zaki zamo mallakina, ranarda za'akawomin ke ɗakina amatsayin matata ta sunna, ranar da zan kwana ina kallon wannan kyakkyawar fuskar taki babuko ƙyafta ido"
Kunyane yakama Zahrah wanda haryakaita ga cusa kanta tsakankanun cinyoyinta, sautari Dr.Sadeeq yakan faɗi abubuwan da suke sanyawa takejin kunyarsa sosai...
Murmushi Dr.Sadeeq yayi haɗe da sake kwantar da jikinsa akan kujeran motar,,,, yana matuƙar son komai na Zahrah ciki kuwa hadda wan nan kunyar nata, tun asalinsa yanason mace me kunya, sai gashi kuma yanzu Allah yabasa, sai de kuma yasan nan gaba kaɗan zaisha fama da'ita saboda idan sunyi aure yasan wan nan halin nata na kunya zatai ta gwadamasa.
Kallon agogon dake ɗaure a hanunsa na dama yayi.
"8:30pm" yafaɗa a bayyane kana yadawo da kallonsa ga Zahrah wacce har yanzu bata ɗago kanta ba.
"Shikenan to tunda dai kunyana kikeji ni zantafi naga dare yasoma yi" yafaɗi haka adai dai lokacin da yake ƙoƙarin ɗaura sit belt ajikinsa..
Sai alokacin taɗago kanta amma bata yadda ta kallesa ba,, "Sai da safe" tafaɗi haka tana me ƙoƙarin fita daga cikin motar domin dama taƙosa yace mata zaitafi saboda tagaji da zaman motan gashi tana da assigment kuma gobe zasuyi submit ɗinshi, san nan kuma tana buƙatar kasancewa ita kaɗai domin tattaunawa da zuciyarta a game da sabon al'amarin dayake shirin kunnu mata kai....
Kansa yajinjina haɗe da cewa "Dama so kike natafi ko?"
Murmushi tayi masa kana taɗan girgiza kan ta alamar a'a, cikin murya me sanyi tace "Bahaka bane kawai de nafara jin bacci ne"
Kansa yakuma jinjinawa cike da gamsuwa haɗe da juyawa baya yaɗauƙo wata farar leda dake aje kan kujeran gidan baya na motar.
"Idan Allah yakaimu da safe zanƙiraki ina fata zakiyi bacci me daɗi" yafaɗi maganar yana me miƙomata ledan dake riƙe a hanunsa...
Shagwaɓe fuska Zahrah tayi haɗe da marairaice manya manyan idanunta da suke sauƙar masa da kasala aduk sanda ya kallesu,, "Gaskiya ni dai a'a nagaji da wayon da kakemin, kuma tun ba yauba na faɗa ma hidiman dakakemin yana yawa!"
Lumshe idanunsa yayi haɗi da buɗesu alokaci guda, idan yanaganin irin wan nan shagwaɓan nata to tabbas zata iya zautar dashi lokaci ɗaya, yafice a hayyacinsa, domin shi shagwaɓan mace nasanyawa yaji feeling ajikinsa sosai,, cikin murya me sanyi yace "Kiyi haƙuri ki ƙarɓa kinji princess ɗina, kinga ba kyu maida hanun kyauta baya!"
Sake turo baki tayi haɗe da kwaɓe fuska, abun mamaki sai taga shima ya marairaice mata fuska kamar wani ƙaramin yaro,, "Please!" yafaɗa cikin muryarsa da tayi ƙasa sosai..
Dole babu yanda ta'iya haka tasanya hanu takarɓi ledan haɗe dayi masa saida safe tafice daga cikin motar,,, yanaganin shigewarta cikin gida yasaki murmushi haɗe da sanya hanu yashafi sajen dake kwance akan ƙuncinsa, key yayi mawa motar haɗe dayin reverse yabar unguwar tasu. Yana tuƙi amma shikaɗai yaketa zuba murmushi, aduk sanda yake tare da Zahrah yakansamun kansa cikin farinciki da nishaɗi, tabbas yanayimawa Zahrah so me tsanani.....
Zahrah kuwa tana shiga cikin gida direct wajen da Inna ke zaune tanufa, ƙoƙarin zama tasomayi haɗi dayimawa Inna sannu da gida.
Washe da baki Inna ta amsa mata bayan ta kafe Zahrah da'ido, Allah Allah take taga menene acikin ledan da Zahrah ta shigo dashi..
Dariyane ya ƙwace mawa Zahrah sakamakon ganin yanda Inna ta tsareta da'idanu tamkar wata mayya.
"Dariyan uban me kike? banson shashanci wallahi" Inna tafaɗi haka ga Zahrah a hasale, ganin bata da shirin buɗe ledan...
Hannayenta tasanya ta toshe bakinta haɗe dasoma ƙoƙarin shanye dariyar ta.
Ledan da tashigo dashi ta buɗe tasoma dubawa gasassun kajine manya guda biyu sai kuma sauran kayan ciye ciye kamar su snacks dakuma chocolate,,
Ledan da kajin ke ciki ta ciro ta miƙamawa Inna ae kuwa hanun Inna har rawa yake lokacin da tazo karɓan ledan tsabar kwaɗayi.
Fari'ar Inna ne yasake yawaita sakamakon ganin kaji da tayi, babu wani ɓata lokaci ta yago cinyar kaza ɗaya takai bakinta,, tsabar daɗin kazar saiga Inna tana lumshe idanu haɗi da jijjiga kai.
Murmushi kawai Zahrah tayi haɗe da ɗaukan sauran kayan tawuce ɗakinta yayinda tabar Inna tayi pieces tana cin kaza hadda rausayar da kai gefe alamar daɗinta takeji....
Jigum tayi haɗe da sake takurewa waje ɗaya akan ƴar katifartata,,, tabbas Dr.Sadeeq yacancanci ta sadaukar masa da duka soyayyarta ko dan saboda halaccin da yayi mata a rayuwa, bazatace batasan menene so ba, itacema zata ba da labari akan so, domin ta ɗanɗana zafinsa me matuƙar ɗaci da dafi,, idan tace Dr.Sadeeq baya burgeta tayi ƙarya, haka kuma idan tace Dr.Sadeeq baida abubuwan burgewa ajikinsa da zasu sa mace tasosa nan ma tayi ƙarya? tabbas Dr.Sadeeq baida wani makusa daga halayya ɗabi'a harma da surarsa yacika cikakken namiji, amma babban abun dake damunta shine batajin tsananin soyayyarsa acikin zuciyarta, bawai tana ƙinsa bane, kawai de zafin soyayyar tasa ne bataji a jiki da zuciyarta, ba kamar yanda taji na Zaid ba,, ada batajin soyayyar Dr.Sadeeq acikin zuciyarta amma ayanzu tayi ƙoƙari wajen ganin takoyawa zuciyarta sonsa, takuma yarda cewa zata iya zaman aure dashi domin baida wani makusa atattare dashi wanda zaisa a ƙisa, murmushine yasuɓuce mata sakamakon tunowa da tayi da irin kallon dayakeyi mata ɗazu, tabbas ya iya nuna soyayyarsa a fili, abu ɗaya ne ajikinsa wanda yake ɗaukar hankalinta, shine ƙwayar idanunsa, duk da cewa shi ɗin namiji ne amma yanada idanu masu kyau wanda zasu sanya maka nutsuwa aduk sanda ka kallesu, hakan yasa ako da yaushe takeson kallon cikin idanunsa amma bata iyawa saboda kunya..... Tunanin Zaid ne yakutso kansa cikin zuciyarta harsai da taji faɗuwar gaba,, "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!" shine abun da tashiga nanatawa acikin zuciyarta,, wannan wani irin bala'i ne? tunda Zaid yashigo cikin rayuwarta shikenan kuma komai nata ya ruguje, lallai itakam taɗaukeshi amatsayin annoba wanda gani da jinsa babu alkhairi .....
Yau Kwanansa ɗaya da wuni ɗaya cur baisanya ko wani irin abinci abakinsa ba, sai ruwan giya dayake ta kwankwaɗa ba dare ba rana,, damuwa ce tayi masa mugun yawa abubuwa gaba ɗaya sun caɓemasa, kallo ɗaya zakai masa kafuskanci cewa yanacikin halin damuwa, domin kuwa lokaci ɗaya ya zabge rama ta bayyana kanta ajikinsa, yayinda manya manyan idanunsa suka sake fitowa waje,, wani irin zafi zuciyarsa keyi masa, baisan da yaushene kuma ta yaya yakamu da soyayyar Zahrah me tsanani haka ba, tunjiya yarasa nutsuwarsa a sakamon labari dayaji daga bakin wanda yasanya yana kulamasa da shiga da ficen Zahrah, inda yasanar masa cewa ankawowa Zahrah kayan lefe, iya ƙololuwar tashin hankali Zaid yashiga dajin wannan magana, sam be shirya wa rasa Zahrah ba saboda rasata dai dai yake da rasa rayuwarsa gaba ɗaya, akuma yanda yakejin matsanancin sonta a cikin zuciyarsa zai iya sadaukar da komai nasa gareta, ko da kuwa ransa ne...
Yanzuma zaune yake yatusa wani ƙaton hoton zanen fuskarta daya zana a daren jiya a gaba yana kallo, saboda tsabar kyawun da zanen yayi idan kagani bazamakace zane bane...
Idanunsa dake kan idanunta na cikin zanen ne suka kaɗa sukai jajur dasu. Saiyanzu yakejin tsanar kansa dakuma tsanar wannan banzan halin nasa, sai yanzu yake tsananin danasanin abun daya aikatawa Zahrah, haƙiƙa yasan cewa ya zalunci Zahrah ya cutar da'ita ya lalata mata rayuwa, kuma hakan da yayi mata shiya nisan ta masa ita, wani irin tsana ne Zahrah tayi masa haka? shin tasan irin zafi dakuma raɗaɗin dayakeji akanta kuwa? yadaina cin abinci tasanadiyar ta, wannan yasa ulcer tayi masa mummunan kamu, gakuma soyayyarta da ta sanya masa ciwo a zuciya,, ta wani ɓangare kuma yana fama da wani matsanancin ciwon kai wanda dashi yake kwana yake kuma tashi, cikinsa kuwa tamkar anhura masa wuta haka yakeji aciki,, hanu yasanya yashafi zanen fuskartata, tabbas idan baisamu Zahrah ba bazai taɓa iya cigaba da rayuwa ba,,, abun da Zaid baisani ba shine tuni ruwan hawaye sun cika idanunsa gangarowa kan fuskarsane kawai da basuyi ba, zumbur haka yamiƙe tsaye haɗe da zura silifas ɗinsa ko wayoyinsa bai tsaya ɗauka ba, haka yafice daga cikin ɗakin nasa....
Yana fita compound ɗin gidan nasu driver'n sa yaƙaraso garesa da sauri,,,, "Oga fita zamuyi ne?" driver'n yatambaya cike da girmamawa,, kai kawai Zaid ya ɗaga masa alamar "eh" jikin driver'n na rawa yace "Oga da wacce motar zamu fita?"
Cike da ƙosawa Zaid yace "Kowacce"
Driver yayi mamaki sosai dajin maganar Zaid domin yasan idan dai har fita Zaid ɗin zaiyi to sai yazaɓi motar dayakeso amma kuma sai gashi yau yace kowacce.. Wata haɗaɗɗiyar baƙar benz driver'n yatuƙo daga cikin parking space zuwa inda Zaid ke tsaye ya harɗe hannayensa acikin aljihun wandon track suit ɗin dake jikinsa..
Zaid nashiga cikin motar driver yabawa motar wuta yayinda me gadi ya wangale musu gate suka fice daga cikin gidan.....
Baffa ne zaune akan dakalin ƙofar gidan yana me latsa ƴar ƙaramar wayarsa, zaman da yayi Zahrah yake jira ta dawo daga aiken da yayi mata,, daf dashi motar tayi parking, hakan yasa Baffa ya kafe motar da'ido don ganin wanene zai fito daga ciki...
A hankali Zaid yabuɗe murfin motar yafito, kallonsa Baffa yashigayi daga sama har ƙasa saboda sarai yagane shine ɗan iskan me kuɗin da yamawa Zahrah fyaɗe, saida Baffa yagama ƙaremasa kallo kafun yakawar da kansa gefe...
Da sallama Zaid yaƙarasa wajen Baffa,, ciki ciki Baffa ya amsa masa sallaman, durƙusawa Zaid yayi haɗe dayin ƙasa da kansa cikin murya me sanyi yace "Kagafarceni Baffa, nasan ban kyautaba amma dan Allah kada ka hanani auren Zahrah, wallahi a yanda nakeji idan bansamu Zahrah ba mutuwa zanyi!"
Baki Baffa yasake yana kallon Zaid, namiji har namiji amma wai yana cewa idan bai auri Zahrah ba mutuwa zaiyi kuji iskanci fa,,
Sake ɗago kansa Zaid yayi haɗe da watsawa Baffa jajayen idanunsa, "Wlh Baffa yanzu da gaske nake aurenta zanyi, kada kace zaka hanani ita dan Allah, wallahi Zahrah tana da matuƙar mahimmanci acikin rayuwata!"
Yanzukam kallon tsab Baffa yashiga yi masa saida yaɗauki kusan minti biyu yana kallon Zaid ɗin kafun yaɗan nisa haɗe da cewa "Bantaɓa tunanin kana da idanun da zaka dawo ka kallemuba, amma sai gashi kadawo kana kallona har kuma kana roƙona dana baka auren Zahrah, idan da kanasonta tunfarko mai yasa baka aureta ba kalalata mata rayuwa? ni bazance maka komai ba saide ince munbarka da Allah saboda bamu da yanda zamuyi dakai, amma kuma kasani bazan baka auren Zahrah ba harsai da amincewarta, idan har tace ta amince zata aureka shikenan nime iya baka aurenta ne" Baffa yana kaiwa nan a zancensa yatashi yayi shigewarsa cikin gida.. Da ƙyar Zaid ya'iya tashi ya zauna akan dakalin da Baffa yatashi hannayensa duka biyu yasanya ya dafe kansa dake yi masa nauyi kamar ze faɗo ƙasa.....
Da ɗan sauri take tafiya tana latsa wayanta burinta kawai shine taganta acikin gida, duk sanyin da akeyi yau yagama ratsata, saboda haka take Allah Allah ta'isa gida.. sam bata lura da akwai mutum a ƙofar gidan nasu ba dan hankalinta gaba ɗaya nakan wayartata...
"Zahrah!" taji anƙira sunanta da murya wacce bazata taɓa mantawa da'ita ba a iya tsawon rayuwarta...
Ja tayi ta tsaya haɗe da maida kallonta inda taji sautin muryar tafito,, tabbas kuwa ba gizo kunenta keyi mata ba shiɗinne dai, kallonta yashigayi da idanunsa wanda suka zama jajaye, itama tsayawa tayi tana kallonsa, a wannan karon kam babu alamar wasa kokuma tsoronsa akan fuskarta,, kallonsa takeyi ido cikin ido...
"Dan Allah Zahrah ki saurareni, wallahi inasonki inamiki so me tsanani, inamiki soyayyar da babu wani wanda zaiyi miki shi a duniyar nan, meyasa bazakisoni ba Zahrah? Inasonki, Inasonki, Inasonki da duka zuciyata, dan Allah kiyarda muyi aure Zahrah!" cikin rauni yaƙare maganartasa saikace ba jarumin namiji ba...
Kallonsa Zahrah tashigayi tundaga ƙasan sa harzuwa samansa, wani irin murmushi tayi masa wanda ita kaɗai tasan ma'anarsa,,, "Bantaɓa tunanin zaka iyayin wannan jarumtar ba, ƙwarai kayi ƙoƙari dahar ka iya tunkarana da wannan maganar, sai de kuma tun awancan lokacin na faɗamaka kafita a rayuwata, idan duka mazan duniya zasu ƙare na gwammace na mutu babu aure dana aureka, ka kalleni da kyau bancancanci zama matar mazinaci kuma ɗangiya ba, niba irin matan nan bane da yacancan ci fasiƙai irinka su samuba, natsaneka Zaid tsana me tsanani, wlhy danaga ranar da zan zamo matarka gwamma acemin naga ranar mutuwa ta, katafi kawai Zaid kaje nabarka da Allah, kuma inaso kasani cewa yau ɗin nan za'a tsaidamin ranar aurena da wanda zuciyata ta aminta dashi, wanda yake kamili me tsoron Allah, shi ba kamar kai bane ɗan giya!" tanakaiwa nan azancenta tajuya daniyar shigewa cikin gida...
Dasauri Zaid ya kamo hanunta haɗe da jawota da ƙarfi tafaɗa cikin jikinsa, dai dau lokacin ne kuma motar Dr.Sadeeq taƙaraso wajen....
*Happy New Year 💃*
*2/january/2020*
__________________________
*Follow me on Whatsapp and Wattpad*
*Fatymasardauna*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SHU'UMIN NAMIJI !!*
*Written By*
*Phatymasardauna*
*Dedicated To My Brother KHABIER*
*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
*Editing is not allowed📵*
*CHAPTER 76 to 77*
Saurin turesa tayi haɗe da hankaɗasa gefe da iya ƙarfinta ta ƙwace jikinta daga nasa, wani irin mugun kallo tashiga yimasa haɗe da tofar da yawu aƙasa, da ace wulaƙanta ɗan adam abune me kyau to tabbas da akan fuskarsa zata tofa wan nan yawun ko hakan zai sanya ya gamsu da irin tsantsar tsanar da takeyi masa.
"Banafatan na sake haɗa jikina da wan nan ƙazamemmen jikin naka mai ɗauke da tarin najasa!" cike da tsananin ƙyamata Zahrah ta faɗi haka ga Zaid haɗe da juyawa tanufi hanyar shiga gida..
"Koda kuwa na daina aikata zina nakuma daina shan giya?" Zaid yafaɗi haka cikin dakakkiyar muryarsa...
Cak ta tsayawa daga tafiyan dakeyi, sosai maganar tasa ta daki zuciyarta..
A hankali yashiga takowa zuwa inda take saida yazo gaf da'ita kafun ya tsaya....... " I promise to leave all my bad habit if you wish to marry me, I love you Zahrah, trust me for the sake of God, i will not hurt you!" gaba ɗaya muryarsa tayi rauni dagajin muryartasa kasan cewa yana cikin matsanancin damuwa...
Idanunta da suka kawo ruwa ta ɗago ta watsa masa su,,,,, Shi ɗin ma kallon ta yakeyi da idanunsa wanda suka zama tamkar an watsa musu garin barkono,, sun ɗauki tsawon mintuna biyu suna kallon juna kafun da ga bisani Zahrah tajuya ta shige cikin gida, ko sake waiwayosa batayi ba yayinda yashiga ƙiran sunanta amma bata amsa masa ba harta shige cikin gida, because tagaji da wannan ɗan iskan yaudaran nasa, yanzukam bazata iya ɗauka ba....
Iskan dake cikin bakinsa ya fesar haɗe da meda duka hannayensa cikin aljihun wandonsa, cikin sanyin jiki haka yakoma cikin motarsa driver yayimawa motar key suka ɗauki hanyar fita unguwar batare da sun kula da Dr.Sadeeq dake zaune cikin motarsa ba...
Haƙoransa ya sanya ya danne laɓɓansa na ƙasa komai daya faru akan idanunsa ya wakana sai de baijiyo magan ganun da suka shiga tsakaninsu ba,, wani irin ɗaci yaji maƙoshinsa nayi, iya matuƙa ɓacin rai yashigesa, bakomaine yafi komai ƙona masa ransa ba kamar yanda yaga Zaid yajawo Zahrah jikinsa, hakanan yaji wani irin mugun kishi ya turnuƙe masa zuciya,, babban abun dayafi ɗaga masa hankali shine yanayin daya hango fuskar Zahrah, tabbas yafuskanci wani ɓoyayyen abu daga gareta,,, key yayi mawa motarsa cikin ƙunan rai yayi reverse haɗe da barin ƙofar gidan nasu batare da ya aika ayi masa ƙiranta ba..
Zahrah na shiga cikin ɗakinta ta durƙusa a ƙasa haɗe da fashewa da wani irin kuka me tsuma zuciya kaicon zuciyarta da ta so mata namiji irin Zaid, ashe da gaske shiɗin mazinaci ne tunda gashi da bakinsa yafaɗa, kuka tashiga yi tamkar wacce aka sanarmawa da ranar mutuwarta, yayinda wani abu yataso ya tokare mata ƙirji wanda batasan komenene shi ba kamar yanda batasan kukan me takeyi ba...
Driver yana parking motar Zaid yace yafita ya bashi waje, aikuwa babu musu driver'n yafita daga cikin motar..... Kansa ya kafa ajikin kujera haɗe da fidda wani irin zazzafan numfashi ta bakinsa, zuwa yanzu kam bazai iya jurewa ba, sam bazai iya jure raɗaɗi dakuma azaban soyayyar Zahrah dake damunsa ba, tabbas da ace zai iya to da yayi iya ka ƙoƙarinsa wajen ganin ya yakice soyayyarta acikin zuciyarsa amma hakan bazai yiwuba domin kuwa duk kowani kwanan duniya soyayyarta ƙara ninkuwa takeyi acikin zuciyarsa, zuwa yanzu soyayyar Zahrah babu inda bata ratsa acikin jikinsa ba,,,, a ƙalla yakai kusan 30 minute acikin motar yana saƙawa da kuncewa, da ƙyar ya'iya fitowa daga cikin motar kai tsaye yanufi babban parlour'nsa dake cikin guest house ɗin nasa, domin kuwa daga gidan su Zahrah guest house ɗinsa suka yiyo....
Yana shiga cikin falon ya faɗa kan doguwar kujera haɗe da lumshe kyawawan idanunsa, kansa ne ke saramasa yayinda juwa ke ɗibansa, lallai yazame masa dole yasamawa kansa mafita, yazama dole yafarka daga wannan mafarkin daya keyi tabbas al'amuransa a yanzu suna masa kama da al'amara,, tabbas yana buƙatar samun relief daga damuwar dayake ciki, amma sai dai babu amfanin shangiya a yanzu domin kuwa koda yashama bata basa wani relief ɗin da ya kamata, miƙewa yayi yashiga cikin ɗakinsa, kai tsaye wani ɗan drower yanufa haɗe da buɗewa, hanu yasanya ya ɗauko wata wayarsa ƙirar techno phantom 9 wanda dama yana ajewane saboda rana irin haka, kasancewar baifito da wayoyinsa ba duk yabarsu a gida,, yana kunna wayar ya laluɓo wata lamba haɗe da turawa lambar text message, yana ganin alamar saƙon ya isa inda yakeson yaje yayi switch off ɗin wayar haɗe da maidata inda ya ɗaukota kwanciya yayi akan makeken gadonsa wanda yasha shumfuɗa ta alfarma, cusa kansa yayi cikin pillow haɗe da soma fitar da numfarfashi akai akai....
A hankali taturo ƙofar ɗakin wanda kafun ma tashigo tuni ƙamshinta yarigata shigowa, sanye take da jan wando pencil wanda yayi matuƙar bayyana kyakkyawar surar jikinta yayinda rigarta yakasance baƙa me kyau, rigan irin masu faɗin wuyan nan ne hakan ne yasanya manya manyan breast ɗinta bayyana kansu tasaman rigar,, takalmine me uban tsini a ƙafarta yayinda ta tufke dogon gashin kanta da jan ribbon kalan wandonta,, kallo ɗaya zakayi mata kafahimci cewa wayayyar macece ƴar duma, shigarta kaɗai ya isa yabayyana maka ainihin ko wacece ita, saboda bashigane da mata masu mutumci sukeyi su fita ba kamar yanda ita tayi, domin kuwa ko ɗan kwali babu akanta, wani irin murmushine kwance akan fuskarta dake nuna alamar cewa tana cikin farinciki,, lumshe idanunta tayi haɗe da buɗesu alokaci guda, kallon surarsa kaɗai ya isa sanya mata nutsuwa, tajima tana tsumayi da kuma fatan Allah ya sake ɗaurata akansa, harta cire rai saikuma gashi yau shi da kansa ya gayyatota, lallai zata iya cewa a rana irin ta yau tafi kowa sa'a..
Duk da yaji ƙamshin turarenta acikin hancinsa hakan baisanya yaɗago kansa ba,,
Cikin taku irin na matan da suka goge wajen iya ɗaukar hankalin ɗa namiji tashiga takowa har zuwa inda yake kwance ya yinda juyawa ƙofa baya...
Hanunta tasanya a bayan wuyansa haɗe da soma shafawa a hankali,, cikin wata murya me sanyi dajan hankali tace "Man!"
Shiru yayi bai amsa mata ba, duk da kuwa cewa yanajinta,,, ganin bai amsa taba yasanya tayi murmushi haɗe da cire takalman dake ƙafarta ta hawo kan gadon,, bakinta ta sanya adai dai saitin tsakiyar bayansa tashiga tsotsa haɗe da shafa bayan wuyansa a hankali,,,, wani irin zubawa Zaid yaji tsikar jikinsa tayi, adai dai sanda take ƙoƙarin nuna masa wani sabon salo.... "Meenal!" yaƙira sunanta da wata irin murya wacce ta riga da ta cushe..
Murmushi Meenal tayi haɗe da mirginowa ta dawo gabansa suna fuskantar juna, lumshe idanunta tayi alokacin da tayi arba da kyakkyawar fuskarsa, wallahi tana matuƙar son Zaid komai nasa me kyaune daga ciki har waje, ba abunda yake ɗaukar hankalinta akan fuskarsa kamar wannan kyakkyawan sajen nasa dayake shan gyara da mayuka masu kyaun gaske..
"Nayi kewarka Man, ashe de kaima kayi kewata? katafi ka barni da tunanin daɗin da kajiyar dani, wanda har rana me kamar ta yau babu wani ɗa namiji da yajiyar dani kwatan kwacin wannan" Meenal taƙare maganar cikin yanayi na shagwaɓa haɗe da sake matsowa tashige cikin jikinsa,, ɗan guntun murmushi yasakar mata haɗe da soma ƙarewa fuskarta kallo, Meenal kyakkyawar yarinyace wanda kyawun nata kuma yazama na ɗan maciji, domin kuwa Meenal tantiriyar ƴar iska ce kuma cikakkiyar mazinaciya wanda idan ta kafamawa namiji ƙahon zuƙa duk nuƙu nuƙunsa sai ta jefasa cikin raminta, sai dai idan kuma shiɗin ya kasance gwaska na gasken gasken, tofa nan ne zasu dai dai ta, kamar dai Zaid da ta buga ta rawa yaƙi faɗowa raminta, domin kuwa shi ɗin ma ɗan iskane me lasisi san nan kuma gwaska ne me zaman kansa, wannan yasa Meenal takasa turasa a cikin raminta..
Hanu Meenal tasanya akan faffaɗan ƙirjinsa tashiga shafawa haɗe da cusa kanta acikin wuyansa cike da ƙwarewa take manna masa kiss,, tamkar wata mayya haka take sake shigewa cikin jikinsa..
Lumshe idanunsa yayi haɗe da cusa hanunsa cikin sumar kanta,, take yasoma sauƙe ajiyar zuciya akai akai domin kuwa gani yake tamkar Zahrah ce kwance haka a jikinsa,, idanu Meenal ta kafesa dashi cike da mamakin irin sauyawan da yayi, nafarko ta hango tarin damuwa acikin idanunsa yayinda na biyu kuma ta hango wani abu mai ɗaure kai acikin idanunsa,,, "Man!" taƙira sunansa cikin wata irin murya, idanunsa kawai ya jefa acikin nata idanun batare da yace da'ita komai ba,, dama haka takeso burinta shine yaɗaga kyawawan idanunsa ya kalleta,, take ta sauya salon nata kallon ta marairaice idanunta,, fuskarta ta matso daf da tashi fuskar lokaci ɗaya tasoma ƙoƙarin haɗe bakinsu waje ɗaya, kamar koda yaushe ƙin aminta da hakan yayi da sauri ya kawar da kansa gefe, saboda hakan baya daga cikin tsarinsa haɗa miyau da matan bariki, domin babu abu mafi saurin sanya shaƙuwa kamar haɗakar yawun baki, sosai kiss yake sanya shaƙuwa a tsakanin masu yinsa, domin haɗuwar yawun bakuna biyu wani sinadari ne na musamman,,,, bata damu ba domin dama tasansa bayawa mace kiss batakuma san dalilinsa na hakan ba, wan nan kuma ita duk ba damuwarta bane matuƙar zai kusanceta to zatafi kowa farinciki,,,,, hanunta ta sanya akan mararsa tashiga shafawa a hankali haɗe da ɗaura bakinta akan nipples ɗinsa, jawota yasakeyi jikinsa bayan ya cire mata ƴar ƙaramar rigar jikinta, kansa ya cusa acikin ƙirjinta yana me shaƙar ƙamshin turarenta, haɗe da sanya hannayensa a bayanta yasoma shafawa a hankali,, take Meenal tasoma sauƙe numfashi akai akai dama ƙiris take jira saboda akunne take ƙwarai... Lokaci ɗaya Meenal tarikice wasu irin salo take gwadawa Zaid masu sanya mutum ya fita a hayyacinsa, yayinda shima yagama ruɗata da nasa salon har saida yakusa sanyata shiɗewa,, amma kuma wani abun mamakin shine yanayin hakan ne cikin wani irin yanayi wanda baisan dame zai ƙira sunan yanayin ba, kwata kwata baijin wani abu mai suna sha'awa a jikinsa duk dakuwa irin romancing ɗinsa da Meenal keyi, lumshe idanunsa yayi haɗe da jawota yadawo da ita ƙasansa aniyarsa shine ya kusanceta amma kuma sai yaji zuciyarsa tashiga bugawa da sauri sauri yayinda Zahrah tashigo cikin ransa ta tsaya cak, take idanunsa suka haskomasa irin kallon tsanan da tayi masa ɗazu, nan danan yaji komai yafice masa arai, da sauri ya ture Meenal gefe haɗe da sanya hanu ya dafe kansa da yayi masa nauyi, da wani irin kallo Meenal da takai ƙololuwa wajen sha'awa ta bisa, meye haka yakeyi? badai halin nasa na wulaƙanci zai gwada mata ba? idan kuwa hakane Zaid yacuceta, saida yagama jefata acikin masifaffiyar sha'awarsa san nan yajuya mata baya, hanu tasanya ta rungumosa ta baya haɗe da soma goga masa breast ɗinta akan bayansa "Meke damunka Man? kada kabari damuwa ya hanaka jin daɗin rayuwa please" tafaɗi haka cikin narkakkiyar murya, hanunsa yasanya ya zameta daga jikinsa wani irin haushinta ma yake ji, miƙewa yayi direct ya wuce toilet ɗinsa ko waiwayota baiyi ba, baki sake haka Meenal tabisa da kallo harya shige cikin toilet ɗin,, kuka ta fashe dashi haɗe da matse cinyoyinta, tsakani da Allah take kuka domin kuwa iyaka cuta a wajenta shine abun da Zaid yayi mata...
Zaid kuwa yanashiga bathroom ya zame wandon dake jikinsa haɗe da nufar inda babban bathtub ɗin wankansa yake, ruwa ne me kyau da tsabta acikin bathtub ɗin, amma duk da haka saida ya zubar yakuma taran wani ruwan, turaren wankansa me daɗin ƙamshi ya sanya a cikin ruwan haɗe da shiga cikin ruwan ya kwanta a hankali,, lumshe idanunsa yayi haɗi da jingina kansa, zafi yakeji adai dai saitin zuciyarsa, tabbas yanaji ajikinsa cewa akwai abun da zai faru dashi bayan wanda yake faruwa dashi yanzu, "wace irin soyayya ce haka yake yiwa Zahrah me zafi?" tambayar da kullum sai yayimawa kansa kenan, lallai yau yasake tabbatar mawa kansa cewa yazama mutum me rauni, A she dama akwai wata rana da zai iya kasancewa haka? yaƙira Meenal ne don taɗebemasa kewa yakuma samu ya rage tarin sha'awar dake damunsa, domin kuwa har wani ciwo yakeji mararsa nayi masa, amma kuma sai gashi ya kasayin komai da Meenal, ashe ba Meenal ɗin bace muradinsa Zahrah ce, haƙiƙa yasake yardarwa kansa cewa abunda kake so shi yake wahalceka sannan kuma yasake tabbatar mawa kansa cewa ƘAUNA guda ɗayane tal aduniya, SO ne kawai yake da yawa, amma ƙauna ƙaunace,, kafun yaƙira Meenal yayi tunanin cewa idan tazo zata gusar masa da damuwarsa, sai kuma bayan tazo yaga ashe bazata iya ba, ashe yin sex da shan giya basune maganin damuwarsa ba, Zahrah har lau itace maganin damuwar sa,, anya kuwa zai warke daga damuwar nan tasa?
Yajima acikin bathroom kafun yayi wanka yafito jikinsa sanye da farar rigar wanka,, kallonsa ya maida kan gado inda yabar Meenal don ganin wani hali ta ke ciki domin kuwa sarai yaji kukanta lokacin dayake cikin bathroom,, dariyane taso ƙwacemai sakamakon ganin Meenal da yayi takure a can ƙarshen gado tana bacci, yayinda ta cusa hanunta na hagu a ƙasanta, sarai yasan Meenal jarabebbiya ce yanzu haka fingering tayi don samawa kanta relief, abun da yafi tsana kenan wato mutum yayi amfani da kansa don biyan buƙatarsa, amma kuma wannan halin Meenal ne,, kai kawai ya girgiza haɗe da nufan gaban dressing mirror ɗinsa, vaseline yashafa ajikinsa kasancewar garin ana ɗan yanayi na sanyi, saida ya feshe jikinsa da body spray kafun yasanya kayansa riga da wando na jeans masu kauri, sosai kayan sukai masa kyau, kuɗaɗe yaciro a cikin drower ɗinsa ya ajiye a kusa da Meenal daketa sharan bacci, kana yayi ficewarsa daga ɗakin, direct bai zarce ko inaba sai compound ɗin gidan, yanzu kam shida kansa yakeson yayi tuƙi, don hakane ma yazaɓi BMW blue colour amatsayin wacce zai fita da ita....
Dr.Sadeeq
Duk yanda Dr.Sadeeq yaso samawa kansa nutsuwa hakan yagagara domin kuwa sam zuciyarsa bata amince da zuwa wajen Zahrah da Zaid keyi ba, duk da yau yafara ganinsa aƙofar gidan su Zahrah'n amma jikinsa ya basa cewa ba yaune zuwansa na farko ba, amma bakomai zaiyi maganin abunne zai nisanta Zahrah da Zaid nisantawa me tsanani kuwa, da wannan tunanin bacci ya ɗaukesa...
Washe Gari.
Dasassafe Zahrah ta shirya tayi tafiyarta makaranta sai dai a ranta tana mamakin rashin ƙiranta da Dr.Sadeeq yayi, rabonta dashi tunjiya da yamma sunkuma rabu dashi akan cewa zai ƙirata sai gashi kuma har zuwa yanzu bai ƙirata ba, uzuri tayi masa akan cewa ko aikine yayi masa yawa domin tasan hakanan Dr.Sadeeq bazaiƙi ƙiranta ba...
Tana tafiya ba jimawa motar Dr.Sadeeq ta tsaya a ƙofar gidan nasu, fitowa yayi daga cikin motar yasha adonsa cikin blue ɗin shadda sosai kuma yayi kyau,, yaro ya aika cikin gidan yace yace ana sallama,, bajimawa yaron daya aika yadawo ya shaida masa ance me gidan yana fitowa.... Washe da baki Baffa yaƙaraso wajen Dr.Sadeeq dake tsaye " Maraba da Likita, dama kaine ai da kashigo ciki amma ka tsaya a waje sai kace wani baƙo"
Murmushi Dr.Sadeeq yayi cike da girmamawa ya sunne kansa ƙasa haɗe da durƙusawa ya gaishe da Baffa,, fuska cike da fari'a Baffa ya amsa gaisuwan,,,
"Aikuwa kayi rashin sa'a domin kuwa mutumiyar taka bata jima da fita a gidan ba, tatafi makaranta ko karyawa bata tsaya tayi ba, amma ina ga zaifi kyau mushiga daga ciki ko"
"A'a Baffa nan ɗin ma yayi, dama wajenka nazo ae"
"To to masha Allah, saimu zauna ae ko abisa dakalin nan" Baffa yaƙare maganar yana meyi mawa Dr.Sadeeq nuni da dakalin ƙofar gidan.
Duk yanda Baffa yaso Dr.Sadeeq ya hau kan dakalin su zauna ƙiyawa yayi, domin kuwa Baffa surikinsa ne baidace ace sun zauna gaf da juna ba kodan saboda kara da matuntawa,,
"Shikenan to tunda dae kaƙi zama, inajinka Allah yasa dai lafiya?"
Kansa yaɗan sosa haɗe da sakin murmushi "Lafiya ƙalau Baffa dama akan maganan aure nane da Zahrah..." sai kuma yayi shiru ya kasa ƙarasa maganar dake cikin bakinsa, gani yake tamkar idan yafaɗi maganar kai tsaye Baffa zaice masa yayi gaggawa ko kuma yace yayi rashin kunya...
"Ka kwantar da hankalinka Likita kafaɗi duk wani abu dake ranka" Baffa yafaɗi haka ga doctor ɗin..
"Am dama...dama inaso ne kabani izini nasake turo magabatana dan sukawo sadaki san nan kuma a tsaida ranar aure"
"Alhmdlh to ai wannan abun farinciki ne Likita, wannan ae bawani abun damuwa bane, nabaka dama ka turosu aduk sanda kakeso, sai de kuma zakaɗanyi haƙuri, saboda zansa lokacin da ɗan tsayi saboda kasan ba a yin aure kai tsaye haka dole sai anɗanyi mawa yarinya sayayya, ina fata hakan bazai sosa ranka ba?"
Murmushin jin daɗi Dr.Sadeeq yayi haɗe da cewa "Naji daɗi sosai Baffa, amma kuma maganar sayayya basai kun wahalar da kanku ba, domin zuwa yanzu gidan da zamu zauna baya buƙatan komai, saboda haka don Allah kada kusa kanku a wahala"
Murmushi Baffa yayi haɗe da cewa "Ƙwarai mungode da wannan ƙoƙarin naka, amma sai de nace kayi haƙuri, duk da cewa mahaifin Zahrah baya raye ni ƙaninsa ina raye kuma niɗin ma ubane a wajenta, zan yi amfani da ɗan abun da nake dasu wajen ganin namata kayan ɗaki iya dede ƙarfina, kamarde yanda kowani uba keyiwa ƴarsa, wannan shine kaɗai gatan da zamu iyayi mata a yanzu" Baffa yafaɗi haka da iyaka gaskiyarsa..
Ajiyar Zuciya Dr.Sadeeq ya sauƙe, haƙiƙa shi Zahrah kawai yakeso bawai wani abu na daban ba, kuma shi baiso akawota da komai, domin musamman ya ware mata ɓangarenta, kuma tuni yabawa wani abokinsa me saida furnitures a Dubai order akan akawomasa setin kujeru dakuma gado harma da duk wani abu wanda yasan zai ƙawata ɗaki,, amma tunda yaga Baffa yadage akan cewa shima zaiyi iya nasa ƙoƙarin shikenan zai ware wani ɗaki na da ban idan yaso sai a sanya kayan da Baffan yayi mata acan,,, cike da mutuntawa Baffa da Dr.Sadeeq sukayi sallama....
Baffa na shiga gida ya kalli Inna dake zaune,, "Salame inajin fa tafiyana yola yagabato idan banje jibi ba to zanje gata insha Allah"
Fuska ɗauke da mamaki Inna ke kallonsa, "Yola kuma Malam?"
"Ƙwarai kuwa, kinga fitana ɗin nan to yaron nan ne Sadeeq yazo min da maganar cewa inbasa dama yaturo magabatansa don sukawo sadaki akuma sa rana, to ni dai nace yaturosu duk sanda yakeso, yanzu dole zanje yola insanya fili dakuma gonan nan namu na gado a kasuwa idan aka siya intarkata kuɗin nan nasamu nasaiwa yarinyarnan kayan ɗaki dakuma kayan aikace aikace kamar de yanda kowani iyaye kemawa ƴarsu dan baiyiwuwa ace mu miƙata haka"
Ajiyar zuciya Inna tasauƙe haɗe da gyara zama " Duk naji batunka Malam, amma kuma mezai hana kabar shi mijin nata yayi mata komai, ae naga yana da halin da zai iyayi mata fiye da wannan ma"
Murmushi kawai Baffa yayi shi kam tun ba yau ba yasan cewa bakoda yaushe ne Inna take gane karatun da'ake biya mata ba, don haka baiƙara cewa da'ita komai ba yawuce ɗakinsa, domin yasan kozai shekara a wajen yanason ganar da'ita tofa bazata fahimcesa ba,,, Inna kuwa baƙin ciki ne yakamata ina ma laifin yace zaiƙara jari da kuɗin, sai yace wani wai zai siyawa Zahrah kayan ɗaki,, haka taita ƙananun maganganunta babu maijinta ma balle yatanka mata......
Da yamma Dr.Sadeeq yaƙira Baffa yasanar masa cewa Baffansa zaizo da dare donsu tsaida magana, duk da cewa Baffa yayi mamakin sauri irin na Dr.Sadeeq ɗin amma saiya share yace Allah yakawosu lafiya,,
Hargida Baffa yaje yasanarwa Alhaji Umar abun da Dr.Sadeeq yace, kuma dama Alhaji Umar ɗin tuni yasan da maganar saboda duk abun da yafaru Baffa yanazuwa ya sanarmasa har kawo lefen da akayi ma Baffa yasanar masa,, sosai Alhaji Umar yayi murna yakumace zaizo gidan Baffa'n da dare a ƙarɓi baƙin dashi......
Kamar yanda Dr.Sadeeq yafaɗa hakane yakasance domin ana idar da sallan Isha Baffa Amadu da wani shaƙiƙin amininsa suka zo gidansu Zahrah,, sosai Baffa da Alhaji Umar suka musu tarba na mutunci,, zama sukayi haɗe dayin magana ta fahimtar juna, nan Baffa Amadu ya miƙa sadakin Zahrah ga Baffa naira dubu ɗari (100,000) bawani ɓata lokaci Baffa yasanya lokacin aure wata ɗaya, aikuwa take kowannensu yacika da farinciki haka sukayi sallama cike da girmama juna.......
(Team Dr. Saiku fitarmana da ankon biki, nasan duk Baba Zaid ze saya mana auren Zahrah'nsa ne ae 🤣🤣😜)
*4/Junuary/2020*
*Follow me on Whatsapp and Wattpad*
~Fatymasardauna~
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SHU'UMIN NAMIJI !!*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Brother KHABIER*
*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
*Editing is not allowed📵*
*CHAPTER 78 to 79*
Zahrah na zaune a ɗakinta Inna takutso kanta cikin ɗakin.
"Idan kin gama rubuce rubucen banzan naki kije Baffan ki nanemanki!" Inna tafaɗi haka aƙufule, ko jiran amsan da Zahrah zata bata batayi ba tayi ficewarta acikin ɗakin,,, da kallon mamaki Zahrah tabi bayan Inna wai meke faruwane tun dawowarta amakaranta tafuskanci cewa ran Inna a matuƙar ɓace yake da'ita, domin kuwa ko abincin rana Inna batayi mata tayi ba, kamar yanda ta sabayi mata kullum, to koma dai menene Allah yasa bawani abu bane me zafi... Tattara books ɗin dake gabanta tayi haɗe da miƙewa ta sanya hijab a jikinta kana tafice daga cikin ɗakin.....
Da sallama ɗauke a bakinta takutsa kanta cikin ɗakin Baffan nata,, zama tayi akan tabarman dake shimfuɗe a tsakiyan ɗaki, haɗe dayi mawa Baffa barka da gida,, fuska ɗauke da fari'a Baffa ya amsa mata..
Gyara zama Baffa yayi haɗe da cewa "Bakomai yasa nayi ƙirankiba sai dan na sanar dake abun dayake faruwa sannan kuma na danƙamiki haƙƙin ki a hanunki, yau da safe yaron nan likita yazo yasameni akan cewa zaituro magabatansa don sukawo sadakin ki, nakuma bashi dama, to yanzu dai sun riga da sun danƙamin sadakin ki a hanuna saboda haka ga abunki naira dubu ɗari ne cus nakine halak malak" Baffa yaƙare maganar yana me miƙa ma Zahrah maƙudan kuɗin dake hanunsa....
Gaba ɗaya jitayi jikinta yayi sanyi laƙwas gaba ɗaya duk wani kuzarinta ya gudu, hakanan taji wani iri a cikin zuciyarta.
"Ki karɓa mana Zahrah" Baffa yafaɗi haka ganin da yayi ko ɗago kanta takasa yi.
Girgiza kanta ta shigayi a hankali cikin muryarta me sanyi tace "Duk abun da ka yanke a gareni Baffa dai dai ne, amma maganar sadaki ka riƙe a wajenka, saboda ko kabani babu abun da zanyi dasu!" taƙare maganar cikin ladabi.
"A'a Zahrah ki karɓi abunki haƙƙin kine, saboda haka nima babu abunda zanyi dashi ki karɓi abunki saiki adana a wajenki, idan kuma wani abu zaki saya saiki saya, amma kada kiyi almubazzaranci dasu, zaifi kyau kisaya abu me mahimmanci wanda zai amfaneki yanzu ko gaba" maganar da tafito daga bakin Baffa kenan.
Shiru Zahrah tayi ita tama rasa yanda zatayi gaba ɗaya yanayinta yasauya, cikin sanyin jiki Zahrah tasanya hanu ta karɓi sadakin nata a hanun Baffa bawai dan ranta yasoba sai dan Baffa ya matsa akan cewa saita karɓa..
"Yauwa kinga idan kika riƙe abunki a hanunki ae yafi ko, sai kuma maganar sa rana, nasa nanda wata ɗaya, ai inaganin hakan yayi domin kafun lokacin insha Allah mungama iya ƙoƙarin da zamuyi wajen sayan ƴan kayayyakin ɗaki"
Wannan magana ta sa rana yafi komai rugaza mata zuciya, fiye da maganan sadaki, haka nan taji faɗuwar gaban da takeji ya tsananta,, amma haka tayi mawa Baffa sallama cikin sanyin jiki tanufi ɗakinta...
Zama tayi akan katifarta haɗe da rumtse idanunta, take hawaye suka shiga fitowa daga cikin idanunta suna gudu akan fuskarta,, shikenan yanzu saura mata wata ɗaya tazamo matar aure? tambayar da tayiwa kanta kenan, bazata iya faɗan wani irin yanayi ta tsinci kanta aciki ba, fargaba ne ko kuma tsoro ne shine abun da bata sani ba,, idanunta ta buɗe haɗe da maida kallonta ga kuɗaɗen dake riƙe a hanunta,, tsurawa kuɗin idanu tayi tamkar mai son gano wani abu ajikin kuɗin,, hawayene suka kuma ɓalle mata, batasan dawani idanu zata kalli Dr.Sadeeq ba, shi wani irin mutum ne? yasani ƙwarai cewa ita ba cikakkiyar budurwa bace da ita da bazawara duk ɗaya suke, amma kuma shine ya cire maƙudan kuɗaɗensa yabada amatsayin sadakinta alhali kuma farashinta baikai haka ba, ita ba irin matan nan bane dasuka dace a sayesu da tsada har haka ba, domin kuwa acikin abubuwa goma da zasu ƙara farashinta babu kaso tara, saboda haka bata cancanci wannan sadaki ba,, hanu tasanya ta share hawayenta, haƙiƙa bazatace batason Dr.Sadeeq ba amma kuma batajin son nasa acikin jini da jikinta, amma hakan bawai wani abu ne da zaisanya taƙi aurensa ba, domin shi ne ma mutum na farko aduniya daya cancanci ta aura, kodan halaccin daya gwada mata a rayuwa.... Cikin wata jakarta tasanya kuɗin sadakin nata, haɗe da dawowa ta kwanta akan katifarta, bazama ta iya ƙarisa assigment ɗin nata ba domin kuwa gaba ɗaya yanayinta yasauya damuwa ta bayyana a tattare da'ita,, da ƙyar ta iya jawo wayarta taƙira Husnah ta sanar mata da duk wani abun daya faru,, daɗine ya kama Husnah sosai take ta hau farinciki haɗe da cewa gobe zatazo yakamata su fara shirye shiryen biki tunda wuri, domin wata ɗaya bawani lokaci ne me tsawo ba idan har darai da kuma lafiya...
*****
"Kiyi kuka da kyau Saleema amma kuma kozaki mutu bazaki auri Sadeeq ba matuƙar bai fasa auren da zaiyi da waccar ƴar ƙasƙantattun mutanen ba, ni bazan iya haɗa iri da jinsin matsiyata ba!" Abunda Hajiya Habiba take faɗa kenan cikin ɓacin rai.
Ɗago kai Saleema tayi takalli mahaifiyarta ta fuska caɓa caɓa da hawaye, cikin muryar kuka Saleema tasoma cewa " Wlhy inasonsa Mom kuma bazan taɓa iya auren wani bayan shiba, nidai na amince zan aureshi a haka, idan yaso bayan auren sai nasan yanda zanyi naƙori ita yarinyar"
Kallon ke shashasha ce Hajiya Habiba tashiga yi mawa Saleema, cike da baƙin ciki taja tsuka haɗe da watsawa Saleema'n harara "Nibansan yaushe zuciyarki ta mutuba wlhy Saleema, ashe ke baki da hankali? to nifa kisani nagama maganata aure da Sadeeq ne anfasa, kuma suzo su kwashe lefensu bama buƙata, domin kuwa kamarni Hajiya Habiba bazan lamunci cinfuskaba, saboda abunda suke shirin yi yanzu cin fuskane a gareni" fuuuu haka tayi wucewarta sama, tabar Saleema tana ta ruskar kuka, saikace wanda akace ubanta ya mutu....
****
Baffa na zaune a wajen sana'arsa wasu maka makan motoci guda biyu suka faka adaf dashi.. Sosai yayi mamakin ganin Alhaji Ma'aruf yakuma dawowa garesa a karo na biyu, wanda ko kusa baiyi tunanin haka ba..
Bayan sun gaisane Alhaji Ma'aruf ya nisa haɗe da cewa "Nasan zakayi mamakin dawowata gareka Malam Hayatu, sai de kuma me nema baikamata ya gajiya ba"
Ajiyar zuciya Baffa yasauƙe haɗe da tattaro duka nutsuwarsa yadubi Alhaji Ma'aruf...
"Bazan taɓa ɓoyemaka ba Alhaji, kamardai yanda nafaɗa maka afarko yanzu ma hakane, domin maganan da nakeyi maka yanzu ma jiya aka kawo sadakin yarinyar, saboda haka sedai nace kawai kuyi haƙuri"
Kai Alhaji Ma'aruf yashiga jinjinawa, zuwa yanzu dolensa zaibawa Zaid haƙuri akan cewa yayi haƙuri yacire yarinyar aransa, domin kuwa idan ba wani ikon Allah ba to babu alamun cewa Zaid zaisamu auren yarinyarnan Zahrah..
Haka Baffa da Alhaji Ma'aruf suka rabu, bayan Alhajin yayi mawa Baffa alkhairi maiyawa, amma sam wannan karon Baffa yaƙi karɓa yace bai buƙata, duk yanda Alhaji Ma'aruf yaso Baffa ya amshi kuɗin hakan bai samu ba,, haka Alhaji Ma'aruf yayimawa Baffa sallama shida tawagar body guard ɗinsa suka bar wajen, sam Alhaji Ma'aruf baiji daɗin hakan ba, yaso ace ɗansa yasamu abunda yakeso.....
Cike da tsananin damuwa Alhaji Ma'aruf ke kallon Zaid dake zaune a ƙasa yayi shiru, gaba ɗaya ya sanja, komai nasa yazama sanyi sanyi, ga alamomin damuwa da suka bayyana kansu a jikinsa, baisan wani irin masifaffen soyayya ɗannasa ya kamu dashi ba, baimasan taya ya Zaid zai ɗauki maganar da zai faɗa masa ba, amma dai yazama dole yafaɗa masa gaskiya amatsayinsa na mahaifinsa.
"Zaid!"
Alhaji Ma'aruf yaƙira sunan Zaid murya a tausashe.
"Na'am Dad" Zaid ya amsa murya ƙasa ƙasa.
"Inaso kabani hankali da nutsuwarka, dan Allah Zaid ka kwantar da hankalinka, nasani kuma kaima kasani nema cikin nema haramunne, kacire wannan yarinya acikin zuciyarka domin kuwa yau naje nasamu shi Baffan nata, yakuma shaidamin cewa a halin yanzu har ya karɓi sadakinta, saboda haka zaifi kyau kacireta a zuciyarka, kanemi wata nasan babu wata mace da zata ƙika"
Tamkar wanda Dad ɗin ya watsa masa ruwan zafi haka yaji sauƙar maganganun mahaifinsa acikin kunnuwansa, da sauri yaɗago jajayen idanunsa ya watsawa mahaifin nasa su,, bakinsa na rawa yace "Ankarɓi sadakinta kuma Dad?"
"ƙwarai kuwa Zaid abunda Baffan nata yafaɗamin kenan, shiyasa nace ka cireta a ranka"
Kai Zaid yashiga girgizawa,,,,, "Bazai taɓa yiwuwaba Dad, wlhy wani bazai taɓa auran Zahrah ba matuƙar ina numfashi acikin duniyar nan, inasonta fa Dad meyasa bazaku gane hakan ba? bazan iya cigaba da rayuwaba idan har babu Zahrah a gareni, nasan laifinane Dad, amma duk da haka bai dace a hanani Zahrah ba, saboda inasonta inamata wani irin so me tsanani please Dad niko yanzu dan Allah a ɗaura mana aure idan yaso daga baya ni na amince zan shawo kanta, nasanma tana sona har yanzu, kuma nasan daga baya zata yafemin abunda nayi mata!"
Cike da tsananin mamaki Dad ke kallon Zaid wanda gaba ɗaya ya ruɗe alokaci ɗaya, anya kuwa ba aljanune suka shiga jikinsa ba ? Dad yatambayi kansa cike da tsananin mamaki, domin kuwa sam Zaid ba haka yake ba, shi mutum ne me nuƙu nuƙu amma kuma wani babban abun mamaki shine yauga Zaid nan yana faɗin wai bazai iya rayuwa ba idan babu wata,,
"Zaid!" Dad yakuma ƙiran sunansa cike da tausayawa domin shikam baitaɓa ganin soyayya irin wannan ba...
Zaid bai iya amsawa mahaifinnasa ba, saide idanunsa daya ɗago ya kalli Dad ɗinnasa dasu.
"Zaid ka kwantar da hankalinka, ba ita kaɗai bace mace a duniyar nan akwai mata da yawa, kana da ƴancin da zaka zaɓi duk irin macen da kake so" Dad yafaɗi haka ga Zaid cikin lallami...
"Idan ni inada ƴanci ita kuma dana cuta fa? nacutar da ita Dad cuta mafi muni, na zalunceta, banda wata hanya dazanbi na goge laifina a wajenta, sai ta hanayar aurenta, dan Allah Dad kayi wani abu, bazan iya jure rashin Zahrah ba!" yanzu kam har ƙwalla suncika idanun Zaid batare daya sani ba. (hmm so mugun wasa)
Miƙewa Zaid yayi daga zaunen da yake haɗe da sa kai yafice daga cikin falon Dad ɗin nasa, da kallo kawai Dad yabisa dashi harya fice, baisan me yake shirin faruwa da ɗan nasa ba amma ae so ba hauka bane.....
Zaid yana fita daga ɓangaren Mahaifinsa direct part ɗinsa yanufa, idanunsa gaba ɗaya sun rufe yayinda kansa ke matuƙar sara masa, sam bazai iyaba, bazaitaɓa iya jure rashin Zahrah ba, lallai yazama dole yakuma yarda da shawaran da zuciyarsa ta basa,, tabbas yazama dole ya kusanto Zahrah zuwa garesa koda kuwa hakan zai jawo faruwar abubuwa masu tarin yawa...key ɗin motarsa ya ɗauka yafice daga cikin ɗakin, gaba ɗaya zuciyarsa ta bushe babu wani abun dayayi saura aciki banda tsananin soyayyar Zahrah.....
Da wani irin mahaukacin gudu Zaid yafigi motarsa yafice daga cikin gidan saura kaɗan yabitakan me gadi daya wangale masa gate, Allah ne ya ta ƙaita Me gadin yayi saurin matsawa gefe, domin kuwa ko gama buɗe gate ɗin baiyi ba Zaid yayi yo kansa....
Tuƙi yakeyi amma kuma kwalbar giya ne riƙe a ɗayan hanunsa yana sha, jinkansa yake gaba ɗaya yana juyawa, yayinda zuciyarsa keyi masa zafi, idanuwansa Zahrah kawai suke hango masa, batare da Zaid yakulaba motarsa tayi karo da wata babbar mota, take motar tasa ta ɗagu sama haɗe da faɗowa ƙasa sannan kuma tashiga gungurawa kan titi, batare da Zaid dake cikin motar ya tsira ba.....
*(Dan Allah ku daina min kutse acikin labarin nan, kudaina saurin yanke hukunci, haryau ban ce ga wanda zai auri Zahrah a tsakanin Zaid ko Dr.Sadeeq ba, kubarni ni kaina nasan abunda ya dace, zaifi kyau ku sanyamin idanu kukuma ci gaba da bina harzuwa ƙarshen labarin nan, amma abun da wasunku sukemin banajin daɗinsa, suna nunawa kamar ina shirin yin abun da bai dace ba, suna nunawa kamar bansan me nakeyiba, dan Allah kuyi haƙuri zancigaba da rubuta labarin nanne kamar yanda yazomin acikin kai dakuma zuciyata, idan kukayi haƙuri komai zaizo cikin sauƙi kuma ina da tabbacin cewa ƙarshen labarin zai muku daɗi, nasan dama dole zan fuskanci ƙalubale a wajen wasunku, amma banyi tunanin abun zaiyi tsanani har haka ba,, amma bakomai namuku uzuri my lovely fans nasan ƙaunace tajawo hakan😅... kuyi haƙuri nayau baida yawa wlhy gaba ɗaya banganewa kaina bane shiasa inafatan zakumin uzuri)*
*Fatymasardauna*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SHU'UMIN NAMIJI !!*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Brother KHABIER*
*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*
*WATTPAD*
fatymasardauna
*Editing is not allowed📵*
*(Wannan page ɗin baki ɗayansa kyautane agareki Masoyiyar asali MY SHALELE (marubuciyar RAGGON MIJI) kiji daɗinki Shalelena iya wuya munatare inakuma yi miki son so)*
*CHAPTER 84 to 85*
Kyakkyawan murmushinsa ne ɗauke akan fuskarsa still hannayensa a ware suke, alamar ta taho zuwa garesa.
Ahankali tashiga takawa tana nufar inda yake, ganin haka yasanya Zaid sakin ajiyar zuciya me ƙarfi, haɗe da sake sakin murmushi alokaci na ba adadi,, koda tazo gareshi yana shirin yaji ta rungumesa amma kuma sai yaji saɓanin haka, domin kuwa tana zuwa kusa dashi, sai gani yayi ta raɓa ta gefensa ta wuce batare dako kallonsa tayi ba. Cikin hanzari yasha gabanta haɗe da kamo hanunta. Cak ta tsaya daga tafiyan da takeyi haɗi da rumtse idanunta,, a hankali ya zame guiwowinsa ƙasa, ya durƙusa mata, duka hannayenta ya kama ya riƙe acikin nasa hanun....
Cikin murya me ɗauke da matuƙar rauni yace da'ita...... "Koda kalamaina baza suyi tasiri acikin zuciyarki ba, dan Allah inaso ki tsaya ki saurareni, ki dubi halin danake ciki Zahrah, banda wani sauran farinciki a duniyar nan idan har babuke a tare dani, haƙiƙa nayi nadama nakumayi dana sanin abun dana aikata a gareki, amma dan Allah Zahrah kiyi haƙuri kiji tausayina ki yarda muyi aure, wallahi namiki alƙawari zandaina duk wani abu danakeyi, zan baki farinciki me ɗorewa, zan mantar dake duk wani damuwa, me yasa bazaki cigaba da sona ba Zahrah? meyasa bazakiji tausayina ki yarda da tuban danayi ba, inasonki Zahrah so irin wanda bantaɓa yiwa kowa irinsa ba acikin wannan duniyar, zan iya fansar da komai nawa idan har zaki amince ki aureni, zan iya rayuwa babu komai babu kuma kowa, amma bazan iya rayuwa babu keba, zan iya sadaukar da duka dukiyata, dakuma duk wani abu nawa dana mallaka, matuƙar zansameki amatsayin matata, dan Allah Zahrah ki yarda dani mana, ninefa Zaid, nine mutumin da kika fara so acikin rayuwarki, shin mai yasa bazaki tausayamin ba, kikalli cikin idanuwa na Zahrah hakan kaɗai ya'isa bayyana miki irin tsananin ƙaunar danakeyi miki, inasonki, wallahi inasonki Zahrah!!.." gaba ɗaya zuciyarsa ta karye, sosai rauninsa ya bayyana... A kan fuskar Zahrah kuwa hawayene ke zuba tamkar anbuɗe famfo sannan kuma haryanzu idanunta akulle suke, yayinda harkawo yanzu hannayenta ke cikin nasa hanun. Bazatace yaushene ko kuma tayayane itama ta tsinci kanta da zamewa ƙasa ba, ta dai tsinci kanta da kafa guiwowinta a ƙasa. kukane yaci ƙarfinta bazata kuma iya cewa ga abu ɗaya dake damunta ba... Hanunta tashiga ƙoƙarin cirewa daga cikin nasa hanun, amma kwata kwata Zaid yaƙi bata daman hakan saima ƙara matsowa kusa da'ita da yakeyi...
"Zahrah!" yaƙira sunanta cikin wata irin murya da bata fita sosai...
Manyan manyan idanunta da suka cika da ruwan hawaye ta ɗago haɗe da waresu akansa, batare da tace dashi komai ba,, wani irin kallo yakeyi mata wanda yake ɗauke da tarin ma'anoni masu yawan gaske.. Hanunta dake cikin nasa hanun ya shiga murzawa haɗe da langwaɓar da kansa gefe yana me cigaba da kallon fuskarta. Hawayene yaziraro daga cikin idanun ta zuwa kan ƙuncinta, sam bata taɓayin zato ko tsammani ba, saijin sauƙar bakinsa tayi akan ƙuncinta, yayinda yasanya harshensa yana me lashe ruwan hawayen dake gudu akan ƙuncin nata. wani irin bugawa zuciyar Zahrah tashigayi da sauri, yayinda numfashinta keshirin ƙwace mata batare da tashiryawa hakan ba,, cikin ɗan kuzarin daya rage mata tayi saurin tureshi gefe haɗi da miƙewa tsaye, ƙoƙarin kama hanunta yakuma yi amma saidai baisamu daman hakan ba domin kuwa tuni harta fara tafiya. "Zahrah" yakuma ƙiran sunanta amma sai dai ko waiwayosa batayiba balle yasaran zata amsa masa.. Jefa ƙafarta kawai take batare dako da ganin gabanta tanayiba, gaba ɗaya ƙwalla suncika mata idanu, yayinda ƙirjinta ke mata luguden duka kanta kuwa tamkar anɗaura mata gungumen ice haka takeji yamata nauyi...
Cikin Hanzari Zaid yarufa mata baya, yana me ƙiran sunanta amma kuma bata amsa masaba, haka kuma bata tsayaba, dai dai lokacin wani me taxi yazo wucewa da sauri Zahrah taɗaga masa hanu, aikuwa take yatsaya,, ganin haka yasanya Zaid yaƙara sauri don yaga alamar tafiya zatayi batare da ta tsaya ta sauraresa ba,, amma ina yamakaro domin mai taxi ɗin yana tsayawa Zahrah ta buɗe murfin motar tashige haɗe da cewa mai taxi ɗin yatada motar sutafi.. Zaid na ƙarasowa wajen, me taxi ɗin kuma na figar motar ya cillata kan titi.. Wani irin iska me zafi Zaid ya fesar daga cikin bakinsa, sam baiso haka ba, yaso ace yaji koda kalma ɗayane daga bakinta, amma kuma duk da haka yamatuƙar jin daɗin ganinta, gashi kuma har kusa da'ita yasamu yazo, babban abun farincikin kuma shine har numfashinta ya shaƙa. Take yaji zuciyarsa tayi masa wani irin sanyi, yayinda daɗi da kuma nutsuwa suka cika masa ruhinsa.. Cike da farinciki haka yakoma inda yabar motarsa.....
Zahrah kuwa ko acikin taxi hawayenta kasa tsagaitawa sukayi, saima kara tuttulowa da suke tamkar ana hankaɗosu... Ahaka har mai taxi ɗin yakawota ƙofar gidansu. Kuɗinsa tabasa ko canji bata tsaya karɓa ba ta wuce cikin gida.. A zauren gidan nasu ta tsaya haɗe da sanya hanu ta share hawayenta, sam bataso kowa yasan halin da take ciki, ta barwa Allah dakuma zuciyarta...
Tana shiga cikin gida Inna tayo wajenta da sauri
"A'ina kika tsayane Zahrah? gaba ɗaya duk kinsa hankalinmu yatashi, munsan bakya kaiwa iwar haka baki dawo ba" Inna tafaɗi haka tana me ƙaremawa yanayin Zahrah'n kallo.
"Bansamu abun hawa bane Inna, yau Samad yana da wani uzuri shi yasa baisamu daman ɗaukoni ba" Zahrah tafaɗi haka tana me ƙwaƙulo murmushi ta aza akan fuskarta..
Da kallon tuhuma Inna tabi ta harta shige cikin ɗakinta, tana shiga cikin ɗakin ta dannawa ƙofarta sakata, a hankali tazame ƙasa haɗe da jingina bayanta da ƙofar, kana ta cusa kanta cikin cinyoyinta, wani irin kuka tashiga rerawa me tsananin bantausayi, Yazatayi da rayuwarta ne itakam, da badon kada tayi saɓo ba da sai tace wannan ƙaddaran nata yayi mata girma dayawa, amma sai dai kuma ba'aja da ikon Allah, haƙiƙa tayi imani cewa komai zaizo yawuce, domin kuwa komai yayi farko yana da ƙarshe, amma kuma sai dai tana da yaƙinin cewa kafun nan wataƙila zuciyarta tayi bindiga ta tarwatse,, "yazatayi da abun da takeji acikin zuciyarta?" tambayar da kullum saitayi mawa kanta kenan, amma kuma zancen ɗayane shine bata da amsar da zata bawa kanta.. Tana cikin kukan taji wayarta na ƙara, amma ko ɗago kanta batayiba haka wayar taƙaraci tsuwanta har ƙiran ya katse, wani ƙiran ne yakuma shigowa still har wayar ta katse batako ɗaga ido ta duba taga waye yake ƙiranta ba.. Kuka tayi sosai kafun tatashi daga durƙushen da take takoma kan katifarta,,,, kwanciya tayi luf tana me sauƙe ajiyar zuciya akai akai, yayinda tsikar jikinta ke yawanta tashi, idan tatuno kusancin da suka samu ɗazu ita da Zaid, bakomai ke dagula mata lissafi da kuma hautsina mata ƙwaƙwalwa ba kamar idan tatuna da yanda yasanya harshensa akan kumatunta yanashan hawayenta, yana me kuma yi mata wani irin kallo wanda yakasa ɓacewa daga cikin idanunta,,, batasan me Zaid yakeso a tattare da'ita ba, wataƙila rayuwarta yakeso, wataƙila kuma hauka yakeso yaga tayi, baisan yatakeji idan ta gansa ba, baisan metakeji agame dashi aduk sanda taɗaura idanuwanta akansa ba, sake gyara kwanciyarta tayi, tabbas tana da buƙatar samun wani wanda zata faɗawa gaba ɗaya damuwarta, tana da buƙatar wanda zai kwantar mata da hankali yakuma samamata nutsuwa, tana kuma buƙatar wanda zai fayyace mata abun dake cikin zuciyarta, koda hakan zaisanya tasamu sauƙi da salama,, haka dai Zahrah tayi bacci zuciyarta cike da tarin tambayoyi.....
Zaid ne kwance akan wata haɗɗɗiyar kujera mai kama da gado, wanda take aje cikin wani irin katafaren falo wanda aka ƙawatasa da kayan ƙyale ƙyale dakuma more rayuwa. Murmushine ɗauke akan fuskarsa, yayinda kyawawan idanunsa suke a lumshe, wani irin shauƙi me tsanani yakeji a tattare dashi, a iya ganinta da yayi jiyake tamkar anyaye masa gaba ɗaya damuwarsa ne, idanunsa yasake lumshewa haɗe da sake shaƙan daddaɗan ƙamshin da yakeyi masa yawo acikin hanci, ƙamshin da tun ɗazu yakasa barin hancinsa, "wani irin daddaɗan ƙamshine haka Zahrah'nsa keyi?" ya tambayi kansa,, tabbas zai so ace iyanzu Zahrah na kusa dashi, dakuwa kwana zaiyi manne da'ita yana shaƙan wannan daddaɗan ƙamshin nata, sannu ahankali wani irin muguwar kasala ke dirar masa, yayinda wani irin sha'awarta me tsanani ya kawo masa ziyara,, a hankali yasanya harshensa ya lashi laɓɓansa haɗe da sanya hanu yashafi ƙwantaccen beard ɗin sa wanda koda yaushe yake ƙara ƙawata masa fuskarsa,, a hanakali ya ware manyan idanunsa wanda suka soma sauya launi daga farare zuwa kalan bacci, wanda idan ka kallesu dole zasu sauƙar maka da kasala... Laptop ɗin dake kusa dashi ya ɗauka, haɗe da buɗewa, take hoton kyakkyawar fuskarta ya bayyana akan screen na laptop ɗin,, murmushi yayi haɗi da sanya hanu yashafi kan screen ɗin laptop ɗin..
"Inasonki Zahrah!"
ya faɗi haka cikin wata irin murya me ɗauke da matsanancin shauƙi. Take yaji yana matuƙar sha'awan kallon vedion dayayi mata ɗazu batare da tasani ba, lokacin fitowarta daga gidan Hajiya Shuwa. Wayarsa da vedion ke ciki ya ɗauka haɗe da kunnawa, kallon vedion yakeyi yana murmushi, amma kuma kwata kwata saƙonnin da suke shigowa ta Email ɗinsa sun hanasa sakat.. Kai tsaye fita daga ɓangaren vedion yayi ya kutsa cikin Email ɗin nasa, saƙonnin abokanan business ɗinsa ne, sama sama yakaranta saƙonnin, haryana shirin fita daga cikin Email ɗin sai kuma idanunsa suka sauƙa akan saƙon Jasheer wanda yaturo masa,, hakanan yaji gabansa yaɗan faɗi saboda yasan duk saƙon da zaizo daga Jasheer to akan Zahrah ne,, buɗe saƙon yayi haɗe da ƙurawa hoton da Jasheer yaturo masa idanu.. Wani irin abu ne yaji ya taso yatokare masa maƙoshi, yayinda idanunsa suka kaɗa sukai jajur dasu, take gashin jikinsa suka mimmiƙe, wani irin juyawa yaji kansa nayi masa,, shin dagaske katin ɗaurin auren Zahrah idanuwansa suke gane masa ko kuwa? sake waro manya manyan idanuwan nasa yayi aikuwa ba ƙarya idanun nasa keyi masa ba, sunan Zahrah ne rantaɓe ajikin katin dakuma sunan Dr.Sadeeq,, wani irin ƙara Zaid yayi haɗe da yin cilli da wayartasa, take ta bugi bango takuma faɗowa ƙasa lokaci ɗaya ta tarwatse.. Cikin matsanancin ɓacin rai jikin Zaid yasoma rawa take yaji wani irin matsancin zafi a dai dai saitin zuciyarsa, lokaci ɗaya wani irin tari ya tasomai, take yasoma tari babu ƙaƙƙautawa, sai ga jini na fita ta bakinsa abun mamaki, abun da bai taɓa gani ba arayuwarsa,, da ƙyar yasamu tarin ya tsagaita, amma kuma duk da haka ƙirjinsa bai daina yi masa ƙuna ba, yayinda zuciyarsa keyi masa zafi har cikin cikinsa kuwa yakejin zafin,, a hankali ya jingina bayansa da jikin bango, haɗe da rumtse jajayen idanunsa, numfashi yashiga fitarwa a hankali, daga ni kai kasan yana matuƙar jin ciwo,, cikin yanayi na wahaltuwa haka ya daddafa zuwa cikin ɗakinsa, ƙaramin drower'n dake gefen gadonsa ya jawo haɗe da ciro magungunansa, tsabar ɗacin da yakeji a maƙoshin sa da ƙyar ma ya iya haɗiye magungunan... Kwanciya yayi akan gado haɗi da rumtse idanunsa, baisan ina zai tsoma rayuwarsa ba, baisan tayaya zai fara jure rashin Zahrah akusa dashi ba... Kamar dai yanda Zaid yaga rana haka yaga dare, koda kuwa na minti guda ne baiji wani salama ko sanyi acikin zuciyarsa ba, haka ya share awanni masu yawa cikin ciwo,, sai da yayi sallan Asuba ƙafun wani irin bacci me nauyi ya sace sa batare daya shiryawa hakan ba......
*****
Zahrah kuwa yau da wani irin irin matsanancin ciwon kai ta tashi, gaba ɗaya idanunta sunyi luhu luhu dasu, da gani kai kasan cewa kuka tasha ta ƙoshi.
Yau ya kasance aurenta da Dr.Sadeeq saura kwanaki shida kenan tana ƙirgawa kuma acikin kwanakin nan ne zasu fara gudanar da shirye shiryen da suka tsara,, gaba ɗaya ji takeyi bata marmarin auren, sannan kuma ji takeyi komai yafice mata arai, bawai kuma don batason Dr.Sadeeq ɗin ba, tun shekaran jiya Dr.Sadeeq yakawo mata ɗinkunanta da kuma kayan da zata sanya a kamu da wajen diner, amma kuma ko duba kayan batayi ba balle taga ma ko sunyi mata ko basuyi mata ba, batasan meyake damunta ba, amma tabbas tasan akwai wani baƙon al'amari dayake ta kusanto rayuwarta aduk kwanan duniya. Yau hakanan tatashi taji ko gyaran jikin ma batason zuwa, amma kuma dazaran tace bazata jeba tasan Inna zata sanyata agaba da yawan tambayoyi, don haka ma gwamma kawai ta je ɗin zaifiye mata... Sauri sauri haka ta shirya tafito, saboda tasan cewa yanzu haka Samad na ƙofar gida yana jiranta... ai kuwa tana fitowa taga motar Dr.Sadeeq fake a ƙofar gidan nasu, murmushi kawai tayi haɗe da ƙarasawa wajen motar... "Allah sarki Samad yana da haƙurin jira, da Dr.Sadeeq ne da yanzun ya ƙirata a waya" tafaɗi haka a zuciyarta dai dai sanda taƙaraso gaf da motar, buɗe murfin motar tayi tashiga bakinta ɗauke da sallama, "Kayi haƙuri Samad nabarka kana ta jira" tafaɗi haka tana me ƙoƙarin rufe murfin motar, batare da takalli Inda Samad ɗin ke zaune ba.
Tana rufe murfin motar tadawo da kallonta wajen zaman driver fuskarta ɗauke da murmushi,, a maimakon taga Samad saitaga Dr.Sadeeq, mamakine ya bayyana akan fuskarta alokaci guda, sake ware idanu tayi tana kallonsa, da'alama dai ganinsa yabata mamaki sosai...
Murmushinsa me kyau yayi mata haɗe da kafeta da idanunsa wanda suke sauƙar mata da wani irin yanayi na kasala ajikinta.. Itama murmushin tayi masa haɗe da shagwaɓe fuska....
"Ni dai nayi fushi!" tafaɗi haka a shagwaɓe...
"Tuba nake"
Dr.Sadeeq yafaɗi haka yana me kama kunnuwansa da duka hannayensa.. alaman ban haƙuri.
"Ni dai naƙi wayon" tafaɗi haka tana me kaɗa idanunta.. Murmushi yayimata haɗe da kamo duka hannayenta yasanya acikin nasa hanun, lumshe idanunsa yayi alokaci guda haɗe da buɗewa
"Nayi kewarki sosai Zahrah na!" yafaɗi haka cikin wata murya me sanyi.
Ɗan guntun murmushi tayi haɗe da soma ƙoƙarin janye hanunta daga cikin nasa hanun, amma kuma bata samu daman hakan ba. "Meyasa jiya kika ƙi ɗaga wayana?" yatambayeta cike da kulawa bayan yagama karantar yanayin da take ciki. Sai alokacin ne ma Zahrah ta tuno da cewa jiya taga missed calls ɗinsa, sanann kuma bata bi bayaba,, ƙaƙalo murmushi tayi haɗe da cewa " Kayi haƙuri nayi bacci ne alokacin"
Kansa ya jinjina badon wai ya gamsu da abun da ta faɗa ba,, ta da motar yayi suka hau kan titi. Saida sukayi nisa a tafiyar kafun yadawo da kallonsa gareta, sosai tayimasa kyau komai nata ya canja, sai dai kuma kallo ɗaya yayimawa fuskarta yafuskanci cewa tayi kuka, dafari yaso tambayarta meke damunta, amma kuma sai kawai ya share,,, sama sama yake janta da hira harsuka iso gidan Hajiya Shuwa... Yana ganin shigewarta cikin gidan ya sauƙe ajiyar zuciya ƴaɗe da kifa kansa akan steering motar, "meke damun Zahrah ne?" ya yiwa kansa tambayar a bayyane, amma sai dai kuma bayida amsar da zai bawa kansa.... A jiyar zuciya yakuma sauƙewa akaro na barkatai, zuciyarsa cike da tunani kala kala yaja motarsa yabar ƙofar gidan....... Ɓangaren Zahrah kuwa kwana biyun nan wasu irin magunguna masu ƙarfin gaske Hajiya Shuwa take bata tanasha, hakan kuwa shike taimakawa wajen hautsina mata tunaninta, wani irin abu takeji acikin jikinta wanda kai tsaye za'a iya ƙiransa da suna sha'awa, ko da yaushe yanzu Zahrah cikin jin feelings take, hattakai ta kawo yanzu alwala ma baya daɗewa ajikinta yake karyewa saboda sosai sperm ke fita ajikinta, duk kuma ɗaya daga cikin aikin magungunan ƙarin ni'iman da Hajiya Shuwa ke bata ne, lallai ita kanta tasan cewa Hajiya Shuwa tayi mata babban haɗi me matuƙar kyau...... (su Doctor za'asha nice😜🙈)
Tunda bacci ya ɗaukeshi da asuba bashi yafarka ba sai ƙarfe 9:30 am, da wani irin zazzafan zazzaɓi yatashi, wanda ya zamana ko ɗaga kansa ba ya'iyawa hatta numfashima da ƙyar yake iya fitarwa. Yana a wannan halin ne yaji anturo ƙofar ɗakin nasa, bai iya ɗago kansa ya dubi ko waye ba amma kuma duk da haka ya gane waye ne yashigo cikin ɗakin... Dasauri Alhj Ma'aruf yaƙaraso garesa...
"Lafiya Zaid meke damunka?" Alhaji Ma'aruf yafaɗi haka yana me kai hanunsa jikin Zaid, da sauri yajanye hanunsa daga jikin Zaid ɗin domin kuwa jiyayi jikin Zaid ɗin yaɗau zafi rau kamar wuta. "Subahanallah, bana ƙira Doctor yanzu" Dad yafaɗi haka yana me ƙoƙarin ciro wayarsa daga cikin aljihu,, bugu biyu Dr.Bilal yaɗauki wayar, cike da damuwa Dad yace yanason ganinsa jikin Zaid ne yatashi. take Dr.Bilal yace gashinan zuwa..
Zama Dad yayi jigum agefen gadon Zaid ɗin, gaba ɗaya yarasa mekeyi masa daɗi, sosai matuƙa cutar Zaid ke damunsa, yana matuƙar ƙaunar Zaid sam bayaso wani abu ya samesa, musamman ma yanzu da Dr.Bilal yashaida masa cewa Zaid ɗin yana ɗauke da ciwon zuciya me tsanani... Mintuna kaɗan Dr.Bilal yaƙaraso gidan, babu wani ɓata lokaci kuwa yashiga yiwa Zaid wasu ƴan gwaje gwaje, drip yaɗaura masa bayan yayi masa wasu allurai guda biyu wanda zasu taimaka wajen kawar da zazzaɓi da kuma ciwon da kansa keyi masa uwa uba kuma su sanyasa bacci, saboda idan yana a cikin hayyacinsa bazai taɓa barin zuciyarsa ta huta ba, yin hakan kuma shike ƙara sawa ciwon yayi tsanani... Bayan sun fito compound ɗin gidan ne Dr.Bilal yagyara tsayuwarsa haɗe da duban Alhaji ma'aruf,, bayani yashiga yimawa Alhaji Ma'aruf ɗin sosai agame da ciwon Zaid ɗin. Bayan sun kammala maganan ne Alhj Ma'aruf yakoma wajen Zaid da tuni wani baccin wahala yasake ɗaukansa......
*****
Rana bata ƙarya, ranar yau takasance laraba kuma yautake kamun Amarya, tun da safe gidan su Zahrah yake acike ƴan uwan Inna sun tattaro ƙwansu da ƙwarƙwatansu sun garzayo, don haka tuni gida yaɗauki hargowa da hayaniyan mutane yayinda amarya kuwa tunsafe take ƙunshe a ɗaki acewarta cikinta ne keyi mata ciwo,, Husnah da Suhaima ne suka taimaka wajen ɗebe mata kewa ta hanyar zama da'ita.....
Ƙarfe uku na yammaci kenan amma tuni gidansu Zahrah ya ɗinke da mutane, ciki kuwa hadda ƴan matan school ɗinsu wanda Husnah ce ta gayyacesu, domin ita dai Zahrah bata da wasu ƙawaye Husnah ce kaɗai ƙawarta... Kowacce ka kalla acikin ƴan matan nan tasha kyau cikin kayan anko ɗinta. Husnah ce tsaye akan Zahrah tana ta faman ɓaɓatu akan cewa Zahrah'n ta tashi su tafi shagon meckup domin tuni Dr.Sadeeq yaturo freinds ɗinsa waƴanda zasu kaisu shagon yin meckup ɗin suna ma jiransu aƙofar gida,, ita dai Zahrah yau jitayi gaba ɗaya bakinta ya mutu sambatajin wani kuzari ajikinta. Kayan da zata sanya da duk wani abun da zatayi amfani dashi, Husnah ta ɗaukar mata haɗe da kama hanunta suka fice daga cikin gidan. Wasu haɗaɗɗun motoci suka shiga kai tsaye aka wuce dasu wani shahararren shagon meckup....
Kwalliya sosai shahararriyar meyin meckup ɗinnan ta tsantsarawa Zahrah akan fuskarta lokaci ɗaya saiga Zahrah ta sauya kamanni asalin kyawunta yasake bayyana tamkar wata balarabiya ita kanta Zahrah saida tayi mamakin ganin kanta, tabbas dabadan tasan ita ɗin ceba, to da sai tace sanja mata fuska akayi, kowa yaga kwalliyanta saiyayi santi saboda tasha kyau iya kyau.. Wani doguwar rigan leshi me kyau da tsada ta sanya ajikinta, take kyakkyawar surar jikinta ya bayyana kansa acikin kayan, sosai ɗinkin yayi kyau yakuma amshi jikinta, zama tayi aka tsantsara mata haɗaɗɗen ɗaurin ɗankwali akanta, yayinda aka nannaɗe mata dogon gashinta atsakiyar kanta, ita dai tsayawa tayi kamar wata statue tana mamakin irin baiwar kyawun da Allah yayi mata, daga riganta har zuwa kan takalminta dakuma ɗan karamin fos ɗin dake rike ahanunta kalarsu yakasance light peach ne, yayinda stones ɗin kayanta suka kasance farare, lokacin da su Husnah sukayi tozali da Zahrah ihu dakuma shewa suka sanya haɗe da tsantsar mamakin irin kyawun da Zahrah tayi, kowa dai yasan Zahrah kyakkyawace amma kuma basuyi tunanin kyawunnata har ya kai hakaba, lallai duk namijin daya samu Zahrah amatsayin mata yayi babban gamdakatar. Take su Husnah suka shiga ɗaukarta hotuna da kuma vedios suna watsawa a instagram dakuma whatsapp, suna cikin buga selfie abokan ango suka ƙaraso don ɗaukar ƙawayen amarya,, duka ƴan matan kowacce da motar da tashiga, yayinda aka bar Zahrah da Husnah sukaɗai saboda Ango yace shi dakansa zaizo yaɗauki amaryarsa... Ƙawaye basu jima da tafiya ba wayar Husnah tasoma ƙara,, murmushi tayi haɗe da kallon Zahrah adai dai lokacin da taɗaga wayar takara akan kunenta, "To ranka shi daɗe gamunan fitowa" abun da Husnah tafaɗa kenan haɗe da miƙewa tsaye hannuwan Zahrah takamo haɗe da miƙar da'ita tsaye..
"Angonki yaƙaraso yace nafito masa dake" murmushi kawai Zahrah tasakar mawa Husnah kana ta sunkuyar da kanta ƙasa.. A hankali Zahrah ke takawa yayinda rigar jikinta kejan ƙasa, babu abun dake tashi ajikinta sai daddaɗan ƙamshin turare,, gaskiya Zahrah tayi kyau sosai ayau ɗin..
Ware idanu Dr.Sadeeq dake zaune acikin motarsa yayi yana me kallon Zahrah, shima yasha ado cikin wata farar gezina me matuƙar kyau da tsada yayi kyau sosai da sosai, kwarjininsa yasake fitowa fili..... Har Husnah ta buɗe murfin motar ta tura Zahrah ciki bai rufe bakinsa ba haka kuma bai ɗauke idanunsa daga kallon da yakeyi wa Zahrah ba, lallai ne godiya ta tabbata ga ALLAH (S.W.A) daya tsara wannan kyakkyawar halitta, kullum kuma koda yaushe yana kallon kyawun Zahrah amma kuma yau saiyake ganin kyawun nata yafi na koyaushe ƙawatuwa.. A hankali ya sauƙe wata irin ajiyar zuciya haɗe da lumshe idanunsa,,, Zahrah kuwa tunda tashiga cikin motar ta sunkuyar da kanta ƙasa tana me wasa da yatsun hanunta,, Motar Habeeb dake bayan ta su Zahrah Husnah tashiga,,, atare motocin suka tashi tafiya sukeyi ahanakali akan titin...
"Zahrah!" Dr.Sadeeq yaƙira sunanta cikin wata irin murya me sanyi dakuma sauƙar da nutsuwa. Kasa amsa masa Zahrah tayi, hakanan taji wani irin nauyinsa ya lulluɓeta.
"Kinyi matuƙar kyau sosai, sai yanzu nasakejin cewa nayi babban sa'a dana sameki, inasonki sosai Zahrah na, ina fata watarana nima kisoni tamkar yanda nake sonki!"
Sai alokacin Zahrah ta ɗago kanta, haɗe da sakar masa ƙawataccen murmushi, jiyayi gaba ɗaya ta kashesa da salon murmushin nata, a hankali ya matso daf da'ita haɗe da kamo hannayenta duka biyu ya riƙesu gam acikin nasa, wani irin soyayyartane yaji yana ƙara shiga jikinsa, jiyakeyi tamkar ya jawota jikinsa ya rungumeta kozai sake samun nutsuwa acikin zuciyarsa.... Harsuka iso katafaren hall ɗin daya cika maƙil da jama'a zuwan amarya da ango kawai ake jira, amma Dr.Sadeeq bai ɗauke idanunsa akan abar ƙaunarsa ba, wani abun daya ƙara rikitar da Zahrah takasa cewa dashi komai shine yanayin yanda yake mata magana da wata irin murya me sanyi... Motarsu na'isowa wajen taron, mc yasoma shela cewa ga ango da amarya sun ƙaraso, take guri yasake ɗaukan shewa yayinda kowa yazura idanun ganin ango da amarya, waƴanda suka zo wajen dan gulma suka sake miƙa wuya musamman ma familyn Dr.Sadeeq wanda anriga da angama gayamusu cewa amaryan ƴar matsiyata ne saboda haka suka baza idanuwan ganin ta don kashewa idanuwansu ƙwarƙwata.... Habeeb ne ya buɗewa Dr.Sadeeq ƙofar motar yafito, yayinda shikuma Dr.Sadeeq da kansa yazagayo ya buɗe mawa Zahrah nata ƙofar,,, cikin nutsuwa ta zuro ƙafafunta waje, kafun daga bisani tafito daga cikin motar, hanunta ɗaya Dr.Sadeeq yakama suka soma taku cike da nutsuwa,, wajene yaɗauki shewa masu murna nayi masu baƙinciki ma sunayi, haka masu ɗaukar amarya da ango hoto da vedio's ma duk sunayi,, gaba ɗaya family'n Dr.Sadeeq ƙamewa sukayi ƙam ganin kyawun amarya ya tsoratasu sosai, saboda basu taɓa tunanin haka zasuga amaryan ba, sunyi tunanin zasu ganta wata almajira da'ita amma kuma sai suka ga saɓanin tunaninsu, lallai ba'abanza ba Dr.Sadeeq ya liƙe akan cewa shi dole sai'ita, takai takuma cancanci ayi mata fiye da haka ma... Har amarya da ango suka ƙarasa mazauninsu mutane basu daina yimusu vedio's ba, haka kuma idanu bai ɗauke daga kan suba.........
*(Bazan'iya cigaba da typing ɗinnan ba, saboda banaso ayi bandani domin nima yau zantaka rawa sosai💃💃💃💃 idan kamu ya kammala zan cigaba da typing😜🤣 Team Zaidu muna tare iya wuya😘, Team Dr.Sadeeq kuna cikin ƙalbina asahun farko ma kuwa🤗)*
*12/January/2020*
*Follow me on Whatsapp and Wattpad*
*Fatymasardauna*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SHU'UMIN NAMIJI !!*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Brother KHABIER*
*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
*Editing is not allowed📵*
*CHAPTER 86 to 87*
Sunkuyar dakai ƙasa Zahrah tayi gaba ɗaya ita kunyar mutanen dake tare a wajen takeyi, tunda take bata taɓa shiga irin wannan taron ba, sai gashi yau akanta ma akeyin taron, ba abun dake damunta kamar yanda idan taɗaga idanunta take ganin idanuwan mutane akanta kowa ita yake kallo da waƴanda suka santa haddama waƴanda basu santa ba,, matso da kansa yayi kusa da'ita haɗe da kawo bakinsa wajen kunnenta "Anan ma kunya zaki nuna?" ƙasa ƙasa yayi maganar. satan kallonsa tayi haɗe da ɗan sakin murmushi amma kuma batace dashi komai ba, haka dai masu yin vedio suka ci gaba da ɗauka yayinda..... Hmmmm kamu dai yayi kamu yakuma ƙawatar amma kuma sai dai sam amarya Zahrah ta kasa sakewa komai a ɗari ɗari takeyinsa, abu biyune suka haɗe mata kunya dakuma rashin sabo, saboda bata taɓa zuwa irin waƴannan wajen ba, wannan ne karonta na farko, gashi kuma kamun yatara mutane sosai, su Husnah sunyi rawa sosai sun raƙashe Amarya kuwa ae ko taka kafarta bata'iya ba gaba ɗaya nauyi da kunya sun hanata sakat.... sai gab da magrib aka tashi daga kamu kowa yasamu abun arziƙi ankuma cika ciki da abinci na musamman da kuma lemuka... Yanzu kam mota ɗaya Zahrah da Husnah harma da Suhaima suka shiga, yayinda Dr.Sadeeq shikuma yashiga wata motar ta daban... Jingina bayanta tayi da kujera haɗe da kwantar da kanta akan kafaɗan Husnah, duk hiran da Husnah da Suhaima keyi jinsu kawai takeyi, sosai sanyin AC'n dake cikin motar yake ratsata har hakan yaso sanyamata zazzaɓi, haka dama ita take matuƙar ta shiga hayaniya to kanta sai ya ɗanyi mata ciwo, uwa uba kuma idan sanyi yayimata yawa saita ɗanyi zazzaɓi.. Harsuka isa gida Zahrah ko uffan batace ba duk da kuwa yanda su Husnah kejanta da hira, amma iya abun da take iyayimusu shine murmushi... Fitowarta a wanka kenan, sauri sauri ta zura wata doguwar riga me kauri ajikinta,,, kallon ta ta mayar ga Husnah wacce taketa faman chatting a wayarta sai nurmushi kawai take zubawa..
"Wai ke da waye ne haka? a iya sanina dake ke ba mutum bace me yawan chatting da'alama dai munsamu ƙaruwa" Zahrah tafaɗi maganar cikin sigar tsokana... Dariya Husnah tayi haɗe da ɗage giranta sama. "Ƙwarai kuwa tawan, wallahi ɗazu na haɗu da wani guy a wajen kamunki, ina tunanin ya kwantamin arai"
Dariya Zahrah ta sanya haɗe da neman guri ta zauna akusa da Husnah haɗi da kwantar da kanta akan kafaɗan Husna'n....
"Husnah kinsan ya so yake?" tambayar da ta fito daga bakin Zahrah kenan..
Mamaki tambayar da Zahrah tayi mata ya bata amma kuma batasan menene dalilin dayasanya Zahrah tayi mata wannan tambayar ba...
"Eh zan iyacewa nasansa zankuma iya cewa bansan saba, saboda banyi wani zurfi acikinsa ba, amma kuma ke kinsan bana yaudaran kaina Zahrah, duk wasu alamomin so nasansu, saboda hakane ma nayardarwa kaina cewa nakamu da soyayyar Yazeed so matsananci!" Husnah tafaɗi haka tana me wasa da wayar hanunta, da'alama sunan Yazeed kaɗai da ta ambata yasanyata cikin shauƙi..
Ajiyar zuciya me ƙarfi Zahrah ta sauƙe haɗe da ɗago kanta daga kan kafaɗar Husnah, hannayen Husnah takama cikin murya me sanyi tace da Husnah "Wasu irin alamomi ne kesanyawa mutum yagane cewa yakamu da so? sannan kuma inaso ki sanar dani menene hukuncin zuciyar da ta makance har take ƙoƙarin sake son wanda yacutar da'ita, wanda kuma baida wani amfani a wajenta"
Kallon mamaki haɗe da ɗaurewar kai Husnah tashiga yi mawa Zahrah, ƙwarai itakam maganganun Zahrah sun sanyata a duhu me Zahrah take nufi?
"Banfahimci inda kalamanki suka dosa ba Zahrah, zanfi fahimta idan har kika warware maganar tazama abu guda, amma kuma ni a ganina babu amfanin zuciyar da zata so wanda baida amfani a wajenta, sai dai kuma amma kinsan shi so wani zubin yakan makantar da komai naka ne tahanyar da baka isa kayi yaƙi dashi ba, amma kuma shi so kala kala ne, kowani so da'irin ƙarfinsa haka kuma da irin rauninsa, wani son yana fita, wani kuma sai ahankali zai fita, wani kuwa baya taɓa fita har gaban abada, amma shi wanda baya fita har abada shi ake ƙira da ƙauna, ita ƙauna kuma idan zafinta yatashi ƙona ka, to ƙunan yakan kasance me tsananin zafi da raɗaɗi bakamar na so ba, ina fata dai Ƙaunar Doctor ce tasanya kikamin wannan tambayar?" Husnah tafaɗi haka tana murmushi.. Wasu siraran hawayene suka silalo daga cikin idanun Zahrah zuwa kan ƙuncinta.
"Zahrah kuka kuma?" Husnah tatambaya cike da mamaki domin ita sam bataga abun kuka acikin maganar da sukeyi ba, hasalima ita Zahrah'n ce tafara ɗago maganar ba wai ita ba.
Hanu tasanya ta share hawayenta haɗe da sakin murmushi, "Bakomai Husnah kawai dai idanuna ne tunɗazu sukeyimin zafi, kinsan ban saba da irin wannan kwalliyar da akamin ba, bacci ma nakeji bana ɗan kwanta, idan kingama ki rufe mana ƙofa" Zahrah tafaɗi haka fuskarta ɗauke da murmushin dole..
Har Zahrah ta kwanta Husnah bata ɗauke idanunta daga kanta ba, sosai ganin hawayen Zahrah'n yabata mamaki duk da kuwa cewa tana lure da'ita a ƴan kwanakinnan gaba ɗaya acikin damuwa take wuni, amma gudun kada ta dameta da tambaya yasanyata sharewa bata tambayeta ba, amma tasan damuwa kam akwai shi jingim acikin zuciyar Zahrah...
Kusan mintuna talatin hawaye na gangarowa daga cikin idanunta, amma kuma ko kyakkyawan motsi taƙi tayi gudun kada Husnah ta fuskanci cewa batayi bacci ba,, bazata taɓa bari kowa yasan damuwarta ba, ta yarda ta amince zata haɗiye duk wani damuwarta acikin rai da zuciyarta ita kaɗai, koda kuwa damuwartata zata kasheta, tabbas wannan abun da takeji ba abu bane wanda zai ɓoyu ba, amma kuma zatayi iyaka ƙoƙarinta wajen ganin ta maidashi ɓoyayyen sirrinta a haka har baccin gajiya ya ɗauketa, tana bacci babu jimawa kuwa ƙiran Dr.Sadeeq yashigo cikin wayarta, ganin ya nace da ƙiran ne yasanya Husnah ɗaga wayar ta shaida masa cewa Zahrah tayi bacci, to kawai yace haɗe da ajiye wayar..
Wani irin tausayinta ne yaji ya dirar masa acikin zuciyarsa, hakanan yaji yau soyayyarta yasake shiga zuciyarsa fiye da ko yaushe yayinda tausayinta yakuma ɗarsuwa acikin zuciyarsa, yaso jin muryarta acikin wannan daren amma kuma hakan baisamu ba, haka yashare yashiga cikin abokansa suka cigaba da sabgoginsu......
Kafe cak idanunsa suke akan haɗaɗɗen zanen POP'n dake mamaye saman ɗakin wanda aka ƙawatasa da ado me matuƙar burgewa, a hankali yake fitar da numfashi me zafi daga cikin hancinsa,, ahalin yanzu ba ciwon da yakeji bane damuwarsa, yafi damuwa da ganin Zahrah'nsa fiye da komai, yanzu kenan saura kwana uku a ɗaura mawa Zahrah'nsa aure da wani bashi ba, rumtse idanunsa yayi da sauri haɗe da haɗiye wani irin yawu me ɗaci daya tsaya masa a maƙoshi, abu kamar wasa saiga ƙwalla suna gangarowa daga cikin idanun Zaid, hanu yasanya yashafa gefen fuskarsa inda yaji sauƙar ɗumin wani abu kamar ruwa,, ruwan hawayen daya fito daga cikin idanunsa ya lakato ahanunsa koda yaga cewa hawayene ke fita daga cikin idanunsa sai yasaki wani irin murmushi me matuƙar ciwo, rayuwa kenan babu yanda bata juyawa bawa, watarana kaga me kyau watarana kuwa kaga mummuna, ƙaddara kenan babu tayanda bata zuwarwa bawa, haƙiƙa SO babban cutane ga bawa musamman idan baka samu abun da kakeso ɗin ba, tabbas ya jarabtu domin ko a iya haka Allah yabarsa ya horasa horo mafi tsanani ma kuwa, tabbas Zahrah itace rauninsa, rasata kuma shine abu wanda zaifiye masa komai ciwo acikin rayuwarsa, baisan wani irin zazzafar soyayya yakeyiwa Zahrah ba, ashe tun dama yaudaran kansa yayi ba sha'awarta yake ba sonta yake, amma kuma saboda wani banzan tunani da kuma banzar hujjan sa yasanya ya kasa yarda da hakan, idan yace zai misalta irin tarin yawan nadaman da yayi kawo daga randa ya yiwa Zahrah fyaɗe zuwa yau to tabbas yayi ƙarya, ya cutar da'ita, ya zalunceta, tabbas yasan bai kyauta mata ba, sannan kuma baiga laifinta da ta ƙishi ba tabbas shida kansa ya san cewa bai cancanci ta sake yarda dashi ba, saurin rumtse idanunsa yayi haɗe da dunƙule hannayensa da ƙarfi, bakomai ne yasanyasa yin hakan ba face tunowa da yayi lokacin da idanunsa suka rufe ya shigeta da ƙarfin gaske yanajin wani irin ihun da tayi amma saboda bushewar zuciya irin tasa haka bai saurara mata ba,, kansa yashiga duka da hannayensa biyu kamar mahaukaci, ihun da Zahrah keyi masa alokacin da zai keta mata haddine yashiga dawowa cikin kunnuwansa ji yake tamkar alokacin ne abubuwan suke faruwa,,, ihu yashiga yi batare daya sani ba, gaba ɗaya idanunsa sun kaɗa sunyi jajur dasu, Mum da shigowarta falon nasa kenan taji ihun Zaid na tashi daga cikin bedroom ɗinsa, cikin sauri hartana haɗawa da tuntuɓe tanufi ɗakin nasa,, kwance tagansa akan gado yaɗaura duka hannayensa akansa yana wani irin ƙara tamkar wani wanda aljanunsa suka tashi..
"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un, Zaid! Zaid!!" Mom taƙira sunansa cikin matuƙar ruɗewa,, girgiza sa Mum tashiga yi cike da ruɗewa sunansa kawai take ƙira, a tunaninta Zaid ɗin nata ya haukace ne, yanajin muryar Mom ɗinsa acikin kunnensa yatashi a zabure haɗe da faɗawa cikin jikin mahaifiyartasa, abun mamaki saiga Zaid nan na kuka tamkar wani ƙaramin yaro, ita kanta Mum kasa motsi tayi haka ta tsaya kamar statue, wai da gaske Zaid ɗin tane wannan, kuka fa yake, anya kuwa ba aljanune suka shiga mata jikin ɗa ba?.
"Zaid" Mum takuma ƙiran sunansa cikin murya me sanyi domin kuwa itama tuni ƙwalla harsun cika mata ido... "Please help me Mum, i don't want to lost her!" abun da Zaid ke faɗa kenan yana kuka,, mamaki marar misaltuwa ne yakuma kama Mum wannan wace irin masifa ne ya ruski Zaid wace irin tsinanniyar soyayyace wannan datake shirin haukata mata yaro? lallai yazama dole tayi wani abu, bazata taɓa bari tanaji tana gani ɗanta ya rasa ransa akan wata ba, wai dama ashe haka so yake? idan kuwa haka so yake to sai dai muyi fatan Allah yarabamu dayin so me tsanani....
Kansa mum tashiga shafawa ahankali cike da tausayawa tace "Ka kwantar da hankalinka Zaid, kayi haƙuri kasamawa kanka nutsuwa, badai kana sonta ba?"
Kai Zaid ya kaɗa tamkar wani ƙaramin yaro.
"Insha Allahu zata zamo taka, zaku rayu da'ita rayuwa ta har abada, kadaina damun kanka kaji my son!"
Mum ta ƙare maganar cike da lallashi..
Kansa ya kwantar akan kafaɗan mahaifiyartasa lokaci ɗaya yashiga sauƙe ajiyar zuciya irin dai yaro ƙarami yayi kuka ya ƙoshin nan.... Bayansa Mum take shafawa a hankali sai gashi cikin mintunan da basufi 10 ba Zaid yasoma fidda numfashi a hankali cike da nutsuwa da'alama dai bacci ne ya ɗaukesa, Mum tana tabbatar da cewa Zaid ɗin yayi bacci ta tattaro duka ƙarfinta haɗe da zameshi akan kafaɗanta ta kwantar da kansa bisa kan pillow'n sa haɗe da ja masa bargo ta rufeshi, kallon fuskarsa Mum tashigayi cike da tsananin tausayinsa, tajima tana kallonsa kafun daga bisani tayi masa addu'a ta shafa masa akan fuskarsa, cikin sanyin jiki ta tashi tafice daga cikin ɗakin, gaba ɗaya zuciyarta tayi rauni......
*Washe Gari*
Tun safe kwararriyar me zanen lalle wanda Dr.Sadeeq ya ɗaukarwa su Zahrah bayan yabiyata maƙudan ƙuɗaɗe tazo gidan,, zanen jan lalle me matuƙar kyau aka tsantsarawa Zahrah akan hanu da ƙafarta, abunka da farar fata take zanen jan lallen yafito akan fatarta yayi kyau sosai,,, lokacin da ta wanke zanen lallen nata hakanan ta tsinci kanta da sakin murmushi ita kanta sosai zanen yayi mata kyau gashi ya ƙara ƙawata farar fatarta gwanin sha'awa. Wayarta dake ringing ta ɗauka haɗe da karawa akan kunnenta, cikin wata irin kasalalliyar murya taji yace "Amaryata" murmushi tasakar masa me sauti haɗe da cewa "Umm" Dr.Sadeeq dake zaune cikin motarsa yagyara zama haɗe da cewa "Ki ɗan bani aron minti 10 daga cikin lokutanki na yanzu inason ganinki" ya ƙare maganar yana wani lullumshe ido kamar wanda yake a gabanta. Ajiyar zuciya Zahrah tayi haɗe da cewa "Gani nan zuwa" tana aje wayar ta ɗauki wani haɗaɗɗen mayafi wanda aka masa ado da fararen duwatsu ta yafa ajikinta yayinda haɗaɗɗen gashinta dayasha saloon ya bayyana kansa ta cikin mayafin..
Tana fitowa tsakar gida ta kalli Husnah wacce yanzu ake zana mata nata lallen, murmushi tayi mata haɗe da kashe mata ido ɗaya, dariya suka sanya su duka domin sukaɗai suka san ma'anar hakan.... Murmushi yayi haɗe da sauƙe ajiyar zuciya alokacin dayaga fitowarta daga cikin gida,,, buɗe murfin motar tasa tayi tashiga bakinta ɗauke da sallama,, cikin murya me ɗauke da kasala ya amsa mata sallaman haɗe da maida kallonsa gareta. Murmushinta dake ƙara mata kyau akoda yaushe tayi masa haɗe da ɗan tsaida idanunta akansa,,,, shiɗinma kallonta yake batare dayace komai ba, azuciyarsa kuwa mamakinta yake ta yanda ta'iya tsaida idanunta akan sa a yau ɗin, bayan kuma yasani sarai batayi masa dogon kallo.
"Namiki kyau ne ƴan mata?" yatambayeta yana me duban kansa,, dariya ne ya kwace mata amma kuma saitayi saurin sanya hanu ta toshe bakinta,
"Wow! gaskiya wannan zanen lallen yayi kyau sosai!" yafaɗi haka yana me ƙoƙarin kamo hanunta, sam shi bai lura da zanen bama sai yanzu,, saurin maida hannayenta cikin mayafin dake jikinta tayi haɗi da cewa "Sai an biya kuɗi me yawa sannan ake kallon wannan zanen" murmushi yayi me sauti, ba ɓata lokaci ya sanya hanu acikin aljihunsa, kuɗi yaciro wanda baisan ko nawa bane, ya ɗaura mata akan cinyarta.
"Karki hanani gani please" yafaɗi maganar yana me marairaice fuska,
"Naƙi wayon kuma ni wannan kuɗin sunmin kaɗan" tafaɗi haka cikin sigar wasa.
"Laluma aljihunsa yayi dama da hagu amma kuma yaji babu ko sisi, kawai saiya marairaice idanunsa yana kallonta, dariya yanzu kam tashigayi, sai da tayi dariyarta ta ƙoshi sannan tace "Kasan baka da kuɗi kuma kakeson ganin zanen lallena?"
Jin shiru bai bata amasa ba yasanyata saurin ɗago kanta ta kalleshi, gani tayi ya zuba mata idanu kamar wani wanda bai taɓa ganinta ba, murmushi kawai tayi haɗe da kawar da kanta gefe, sosai takejin wani iri ajikinta idan yana kallonta.
"Zahrah na!" yaƙira sunanta cikin wata irin murya me sanyi. Zahrah bata iya amsa masa ba, sai dai ta dawo da kallonta gareshi..
Yabuɗe baki zaikumayin magana kenan wayarsa tasoma ƙara,,
"Hajiya"
shine sunan dake yawo akan screen ɗin wayar, dakatawa da maganar yayi haɗe da ɗaukan wayar yakara akan kunnensa.. Hajiya dake zaune akan kujera cikin yanayi na ɓacin rai tace
"Kana'ina ne?"
"Ina wajen Zahrah Hajiya" yabata amsa cike da girmamawa.
"Kabar duk abun da kake kazo gida inason ganinka" tana kaiwa nan azancenta ta kashe wayar.
A hankali ya zame wayar daga kan kunnensa haɗe da sauƙe ajiyar zuciya kallon Zahrah yakumayi haɗe da ɗan sakin murmushi.
"Hajiya nason ganina yanzu, ki riƙe wannan saboda hidimar walimanki na gobe, maybe bazaki sake ganina ba sai bayan na angonce!" yafaɗi haka yana me miƙa mata wasu kuɗaɗe masu yawa daya ciro daga cikin wata ƴar loka dake cikin motar.
"A'a ae bana buƙatar komai don mungama duk wani abun da zamuyi, kuma komai na walima yazama ready, sannan kuma inada kuɗi a wajena ka...."
"Shiiii kinsan banason yawan musu please ki karɓa kinji baby na, ki ajiye kobazakiyi komai dasu ba nasan zasu miki amfani wani lokaci" yafaɗi haka ta hanyar katseta daga maganar da takeyi batare daya bari ta ƙarisa ba,, badon ranta yasoba ta amshi kuɗin haɗe dayi masa godiya kana ta buɗe murfin motar ta fice, shima tada motar nasa yayi yabar ƙofar gidan, zuciyarsa cike da mamakin ƙiran da Hajiya tayi masa, Allah dai yasa ba wata matsalan ne takuma kunnu kai ba, idan dai har akan aurensa da Zahrah ne tofa shikam gaskiya sai dai kowama yayi haƙuri saboda ayanzu baijin zai iya sanja muradin sa...
Fuska ɗauke da mamaki Dr.Sadeeq ke cewa "tafasa aurena kuma Hajiya?"
"Badole tafasa aurenka ba, wace uwa ce zata yarda da irin abun da katsiro dashi? tun ma ba'aje ko inaba kana nuna banbanci ƙarara, gashi abanza ka jawo zubewar mutumcin dake tsakanina da Hajiya Furaira, yanzu da wani ido kakeso nasake kallonta!" Hajiya tafaɗi haka cikin ɓacin rai.
Sunkuyar dakai ƙasa Dr.Sadeeq yayi yana me hamdala acikin zuciyarsa da aka soke batun aurensa da Saleema, dama shi Allah yasani ko ya auri Saleema ba lallaine yakamanta mata adalci ba, saboda abun a bayyane yake yafi ƙaunar Zahrah fiye da kowacce mace a yanzu idan aka cire mahaifiyarsa dakuma ƴar uwarsa ta jini.
"Dama haka kakeso ai shikenan burinka yacika, gakuma kayan lefe dakuma kuɗin auren da kakai can sun dawo maka dashi, sai kaje kayi ta fama da wacce zuciyarka ta zaɓa ma ni tashi kabani waje !"
Sumi sumi haka Dr.Sadeeq yatashi daga gaban mahaifiyartasa cikin sanyin jiki yafice daga cikin falon...
Yana shiga ɗakinsa yasaki wani irin ajiyar zuciya, wayyo Allah shikam daɗi kasheshi, dama yafi kowa tunanin yanda zaman nasu zai kasance saboda shi a tsarin rayuwarsa bai da niyar auren mace sama da ɗaya bare yanzu daya samu Zahrah yasan cewa ita kaɗaima ta'ishesa rayuwa, yaji daɗin fasa wannan auren ƙwarai...
*Zaid*
Gaba ɗaya jikinsa yaƙi daɗi duk yanda yaso koda a daddafene yaje yaga Zahrah hakan yagagara, saboda wunin yau ma gaba ɗaya baiyishi cikin daɗi ba, kasancewar ciwon zuciyarsa yatashi yasanya Dr.Bilal ya dinga basa magani masu sanyasa bacci gudun kada ya matsantawa kansa da tunani, haka dai yanaji yana gani tashi zaune ma yagagaresa, haka ya kwana yana begen ganin Zahrah....
*Friday*
Kowa dake gidansu Zahrah shirin zuwa wajen walima kawai yakeyi, yayinda amarya Zahrah tasha kyau cikin wani haɗaɗɗen sari da aka ɓata lokaci wajen naɗa mata shi ajikinta, yauma dai meckup aka tsantsara mata akan fuskarta nagani na faɗa, take fuskar amarya Zahrah yaci gaba da walwali,, motoci Dr.Sadeeq yaturo suka kwashesu har zuwa inda za'a gudanar da walima,,, walima fa ya ƙayatar saboda Malami aka ɗauko na musamman yagudanar da wa'azi akan yanda ake zamantakewar aure, sanan kuma yaƙara da wa'azi me ratsa jiki harsaida amarya tayi kuka,, bayan anƙare walima ne kuma aka soma rabon abinci haɗe da kyaututtuka kamar su memo da kuma jaka wanda Dr.Sadeeq ne duk yayi su, sai dai babu hoton amarya da ango ajiki sai dai sunansu kawai. Walima fa yaƙayatar kowa sai dai yace Alhmdlh haka aka tashi a taron walima kowa yanacikin farinciki,, yayinda gobe asabar kuma take ɗaurin aure💃.
*(Maza kuzo fa, mata kuma ku faɗawa Mazajenku su je ɗaurin auren😂 🙊Nidai baruwana Team Zaid kada kuga laifina Dr.Sadeeq ne yace ingayyaci kowa da kowa 😂💃😜)*
*Fatymasardauna*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*SHU'UMIN NAMIJI !!*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Brother KHABIER*
*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed; our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*
*WATTPAD*
@fatymasardauna
*(Wannan fejin baki ɗayansa nakine My KHAIR74 kinasani nishaɗi sosai, kiyi farinciki marar iyaka kiji daɗinki akullum inayinki sosai KHAIR74)*
*Editing is not allowed📵*
*NOTE: Masoyana masu cece kuce inagaisuwa agareku, sannan ina mai baku haƙuri, idan akwai wacce wannan hukuncin baiyi mata daɗi ba tayi haƙuri dama shi Aure nufine na Allah, kuma ance matar mutum ƙabarinsa, abun danakeso ku fahimta shine, balallai ne koda yaushe mutum yasamu abun da rai dakuma zuciyarsa keso ba, SO baƙarya bane haƙiƙa so gaskiya ne, amma kuma bako da yaushe bane burin so ɗin ke cika ba, ita rayuwa dama haka take tana iya sauyawa ako da yaushe akuma kowani lokaci.....*
*CHAPTER 88 to 89*
Yauma dai kamar jiya agajiye take matuƙa, suna komawa gida ta yi wanka da ruwa me zafi sai alokacin ta ɗanji ta samu nutsuwa a jikinta. Kwanciya tayi luf akan katifarta haɗe da jawo wayarta tasoma buga game, tayi hakanne gudun kada tunani ya samu daman bijiro mta acikin zuciya...
"Kinada baƙo a waje fa Zahrah" maganar da tafito daga bakin Husnah wacce shigowarta ɗakin kenan..
"Baƙo kuma Husnah?" Zahrah tatambaya cike da mamaki.
"Ƙwarai kuwa amma sai dai gaskiya inaga ba ya ɗaya daga cikin abokan Doctor, yakamata kije ki gansa dan naga kamar yamatsu dason ganinki" Husnah tafaɗi haka bayan tayi mawa kanta masauƙi akan katifar da Zahrah take kwance...
Cike da mamaki Zahrah tamiƙe tsaye haɗe da ɗaukar mayafi ta rufa ajikinta, hakanan taji tamatsu da taga waye ne ke neman nata.....
Tana fita waje tasoma raba idanu ko zata hango wanda akace yana ƙiranta, sai dai kuma bata ga kowa ba...
"Zahrah" taji anƙira sunanta daga bayanta,, da sauri ta juya don ganin kowaye.
Wani kyakkyawan saurayi handsome guy tagani tsaye a bayanta yana ta zuba murmushi, kallo ɗaya zakayi masa kafahimci cewa shiɗin cikekken ɗan gaye ne, kuma ɗan hutu, domin kuwa fatar jikinsa da kuma kayan dake sanye ajikinsa kaɗai sun isa tabbatar maka da hakan..
Takowa yashigayi gareta, har saida yazo kusa da'ita kafun ya ja ya tsaya, kallon kallo suka shiga yiwa juna, Zahrah kallon mamaki da kuma al'ajabin me ya kawosa wajenta take yayinda shikuma yakeyi mata kallon ƙurilla,, wani yawu ya haɗiya a maƙoshinsa bayan yagama ƙare mata kallo daga samanta har ƙasanta... "Zahrah ko?" yafaɗi haka yana me nuna ta da yatsarsa...
Kai kawai Zahrah ta'iya jinjina masa alamar "Eh" still amma kuma idanunta nakansa..
Murmushi yakuma yi mata haɗe da gyara tsayuwarsa "Naji daɗin ganinki ƴan mata, sunana Abid, nasan baki sanni ba amma kuma idan babu damuwa me zai hana muje mota sai muyi maganan, saboda nazomiki da wata magana ce me mahimmanci" yafaɗi haka yana me sake dubanta da kyau...
Kallon sa itama ta sakeyi sosai kafun ta ce. "Kafaɗi duk abun da zaka faɗa anan inaji, amma bana buƙatar shiga cikin motarka" ta ƙare maganar tana me ɗage kanta sama.
Murmushi Abid yakumayi akaro na barkatai "lallai ba'a banza ba Zaid yakasa magance matsalarsa yarinyar akwai taurin kai" yafaɗi haka acikin zuciyarsa...
"I'm sorry bacutar dake zanyi ba, kada kiji tsorona, nazo miki da magana ne me matuƙar mahimmanci, nasan abune me wahala amma kuma keda kanki zakiso ace kinzamo silar ceto rayuwar da take shirin gushewa, nasan bazakiso ace ta sanadiyarki Zaid ya rasa rayuwarsa ba, kina da tausayi Zahrah, me yasa bazaki yarda ki aure sa ba?" abunda ya fito daga bakin Abid kenan..
Kallon baka da hankali Zahrah tashiga bin Abid dashi, da ƙyar ta'iya cewa "Bansan maganar Zaid bace takawoka wajena ba, da bantsaya ɓata lokacina wajen saurararka ba, don bazan ɓata lokacina abanza ba, dan Allah kufita a rayuwata, kacewa Zaid ya ƙyaleni na huta, domin kuwa ko maza sun ƙare a duniya bazan taɓa auren Zaid ba!" Zahrah tafaɗi haka cikin dakiya dakuma ɓacin rai...
"Ba gaskiya bane Zahrah, wannan maganar da kika faɗa ba daga cikin zuciyarki tafito ba daga bakinki tafito, kobaki furta ba raunin kalamanki sunnuna cewa kinason Zaid har yanzu, me yasa bazaki yafe masa ba? Allah ma muna masa laifi ya yafe mana, dan Allah Zahrah ki taimaka ki auri Zaid, haƙiƙa nida Zaid muna biyewa zuciyarmu muna aikata abunda baidace ba, amma kuma ina me tabbatar miki da Zaid ɗin dakika sani a yanzu bashine wanda kika sani ada ba, soyayyarki ta sanjawa Zaid tunani, soyayyarki ta juyamasa ƙwaƙwalwa, wallahi ke kaɗaice muradinsa acikin duniyar nan, Zaid baisan damuwa ba sai akanki Zahrah, yayi nadama me tsanani akan abun daya aikata miki, akan ki Zaid yafara sanin menene ƙunci, akanki yafara sanin menene ɗacin soyayya dakuma zaƙinta, haka akanki Zaid ya kasa fuskantar gabansa dakuma bayansa, akan kine kuma dalilinkine Zaid yakamu da ciwon zuciya me tsanani, ahalin yanzu Zaid yana acikin wani hali, Zahrah ke kaɗaice zaki iya sanjasa ki kuma ceto rayuwarsa please koba don nida Zaid ba kodan ceton rayuwarsa ki taimaka ki auresa!" Abid yaƙare maganar cike da raunin murya sosai yake matuƙar tausayin Zaid musamman ma dayaje yagansa yau, gaba ɗaya yafita hayyacinsa...
Murmushi me tsananin ciwo Zahrah tayi haɗe da sanya haƙoranta tacije lips ɗinta, kallon Abid tayi kana ta girgiza kanta
"Meyasa ku kazamanto mutane masu tsananin son kansu? Zaid rayuwarsa kawai zai rasa, amma ni gani da raina ta sanadiyarsa ne kuma narasa farinciki na, rayuwata tazamo marar amfani a gareni, ya katsemin farinciki dajin daɗi na, yakawo kansa gareni alokacin dayaga dama, yakuma sanyamin soyayyarsa alokacin dayaga dama, sannan yakuma ketamin haddina alokacin da yaga dama, yayimini duk wani abu da ransa keso alokacin dayaga dama, nima kuma yanzu nadawo mutum zankumayi duk wani abun daya dace alokacin dana ga dama, idan shi ne ya aikoka da waƴannan yaudararrun kalaman to kaje kasanar masa cewa kalaman naku basuyi aiki akai na ba, zaifi kyau kubarni nayi rayuwar aurena cikin farinciki da salama, domin kuwa gobe iwarhaka najima da zama matar wani insha Allah, inaso kuma kasani cewa najima da barin Zaid da Allah, haƙiƙa ya cutar dani, amma kuma dama hakan yakasance rubutaccen ƙaddarata ne wanda Allah ya rubuta, kaje kawai Abid bana tunanin sake burin haɗa rayuwata da ta Zaid!" hanu tasanya ta sharce hawayen da suka silalo daga cikin idanunta haɗe da juyawa tasoma tafiya...
"Komai yana hanunki Zahrah idan har kikace afasa aurenki da wanda zaki aura aɗaura da Zaid nasan iyayenki zasu amince, shin maiyasa bazaki cika muku burinku ba? kinasonsa shima kuma yana sonki, ki amince ki aure sa, wallahi namiki alƙawari ko nawa kikeso aduniyar nan zan mallakamiki shi koda kuwa duka dukiyata kika buƙata nabaki zan baki, amma bazan tilastaki ba sai dai inaso kisani idan Zaid ya rasa rayuwarsa a yanzu kece SANADI" Abid yana kaiwa nan azancensa yabuɗe murfin motarsa, wata ƴar madaidai ciyar jaka ya ɗauko, takawa yashigayi harsai da yazo kusa da'ita kafun ya tsaya... "Ki amshi wannan jakan idan kika buɗe laptop ɗin dake ciki zakiga yanda Zaid ya koma A SANADI'N SONKI" Abid yafaɗi haka yana me miƙa mata jakar.. Tsintar kanta tayi da kasa ƙin karɓan jakar, yana bata jakar ya juya yayi tafiyarsa,,, har motar Abid ta ɓule Zahrah na tsaye sororo hanunta riƙe da jaka,,, saurin share hawayenta tayi, haɗe da nufar cikin gidan su,,, sumi sumi haka ta shige cikin ɗakinta, abun yayi mata daɗi sosai data iske Husnah hartayi bacci,, mayafinta ta cire haɗe da neman waje ta zauna, kanta ta kifa akan guiwowinta, damuwane cike azuciyarta, takasa sanin wani hali take ciki, kanta ta ɗago takalli jakar da tashigo dashi, da sauri tajawo jakar haɗe da buɗeta, a hankali ta zaro laptop ɗin dake cikin jakar, saida ta ƙarewa laptop ɗin kallo kafun ta buɗeta, tana danna wani madanni laptop ɗin takawo haske take kyakkyawan hoton fuskarta ya bayyana akan screen na laptop ɗin, mamakine yakamata ganin hotonta wanda batasan ma dashi aduniya ba, balle tasan yaushe ko wace ranace aka ɗauketa hoton ba, ƙurawa hoton nata idanu tayi tamakasa yin komai, bata ɗauke idanunta akan hoton ba har saida hasken screen ɗin laptop ɗin ya gaji dan kansa ya ɗauke.. Ajiyar zuciya me ƙarfi ta sauƙe haɗe da sake kunna laptop ɗin, batasan inazata shiga ba, bata kuma san mezata fara dubawa ba, hakanan ta ji zuciyarta ta ingizata da tashiga ɓangaren hotuna,, tana kutsawa ɓangaren hotuna, hotunantane suka farayi mata wellcome, mamakine yasake kasheta ganin hotunanta kaca kaca babu adadi acikin laptop ɗin, wanda ita a iya tsawon tarihin rayuwarta ma bata kasance mace meyawan sonyin hoto ba, yanzu haka ko hotonta ƙwaya ɗaya bata dashi acikin wayarta,,,, bata da me amsamata tarin tambayoyin dake ranta dan haka kawai saita shiga wuce hotunan nata, hotunan Zaid takuma cin karo dasu wanda saida gabanta yayi wani irin faɗuwa yayinda ƙirjinta yashiga dokawa da sauri.. da ƙyar ta'iya view ɗaya daga cikin tarin hotunan nasa, sanye yake da wandon jeans baƙi dakuma wata farar riga saikuma hular sanyi daya sanya akanshi yayinda kunnensa ke sanye da farin earpiece, yayi kyau matuƙa a hoton domin kuwa fuskarsa ɗauke take da wannan ƙawataccen murmushin nasa wanda yake ƙara masa kyau ako da yaushe... Ƙura mawa hoton nasa idanu tayi, saitaga tamkar shiɗinne da kansa agabanta, batasan sanda wasu hawaye suka silalo daga cikin idanunta zuwa kan ƙuncinta ba,, tajima tana kallon hoton nasa, haka kuma hawaye na tsiyaya daga cikin idanunta, ɓangaren vedios takuma kutsawa, sai dai vedion farko da ta gani shine wanda yakusa tarwatsa mata zuciya, yakuma ɗaga mata hankali,, Zaid tagani kwance akan gadon asibiti ansanya masa oxygen, yayinda aka dasa masa wasu ƙarafan na'urori akan ƙirjinsa dai dai saitin zuciyarsa, da badon ɗan abu kamar computer'n dake gefensa wanda shike nuna alama yana da rai ba, to tabbas da saidai ace dashi gawa,,, wani irin sarawa taji kanta yayi, yayinda wani irin kuka yazo mata alokaci guda, saurin sanya hanu tayi ta toshe bakinta haɗe da rumtse idanunta, a hankali ta jingina bayanta da bango,,, hawayene suka shiga gudu wani na koran wani akan fuskarta,, duk yanda taso daurewa kasawa tayi saikawai tafashe da wani irin kuka me sauti, kuka take sosai yayinda ta rungume wannan laptop ɗin akan ƙirjinta,,,, kamar amafarki Husnah kejin gunjin kuka natashi acikin ɗakin, dayake ita ba me nauyin bacci bace yasanyata buɗe idanunta ahankali, aikuwa dagaske ba amafarki bane, kukan Zahrah taji raɗau acikin kunnenta, da sauri ta tashi zaune haɗe da dawo da kallonta inda sautin kukan ke fitowa,, sake waro idanunta tayi ganin da tayiwa Zahrah na kuka tsakaninta da Allah. "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un! Zahrah meyafaru kike irin wannan kukan?" Husnah ta tambaya cikin ruɗewa... Jin muryar Husnah acikin kunnenta yasanya, tataso daga inda take da sauri ta faɗa jikin Husnah ae kuma saita ƙara volume ɗin kukan nata,, kai Husnah ta dafe cike da tashin hankali, "Allah yasa dai bawani gagarumin abubane yafaru" Husnah tafaɗi haka acikin zuciyarta.
"Kiyi shiru dan Allah Zahrah, kinga dai yanzu dare ne sokike kowa saiyaji gunjin kukan ki? kiyi shiru kisanar dani meke faruwa" Husnah tafaɗi haka ga Zahrah cike da damuwa... Yau Zahrah tsintar kanta tayi da kasa daina kuka, ji ma take tamkar Husnah ingizata take da ta ƙara volume,, sororo haka Husnah tayi ganin Zahrah taƙi daina kukan, zame ta tayi daga jikinta haɗe da nufar inda aka aje musu ledan ruwa na pure water, guda ɗaya ta zaro acikin ledan haɗe da fasawa ta tsiyaya acikin cup,, dawowa tayi ta zauna haɗi dakai kofin ruwan bakin Zahrah, babu musu Zahrah ta amshi kofin takai bakinta, gaba ɗaya ruwan dake cikin kofin tashanye tas haɗe da aje kofin agefe, ajiyar zuciya tasoma sauƙewa akai akai amma na kuka,,, kwanciya tayi luf haɗe da sanya hanu ta dafe kanta dake matuƙar sara mata,,, idanu kawai Husnah ta zuba mata tana me mamakinta, gaba ɗaya aƴan kwanakinnan talura Zahrah ta maida kuka abinci da kuma ruwan shanta, ita yanzu hartama fara tunanin ko aljanune suka shiga jikin Zahrah'n,, bayan kamar minti goma Husnah taƙira sunan Zahrah,, amma kuma saitaji shiru Zahrah bata amasa mata ba, hakan ne yasanya tayi tunanin cewa Zahrah'n tayi bacci, raɓawa gefen Zahrah'n itama tayi ta kwanta, mintuna kaɗan bacci yakuma surarta, Zahrah na jin sauƙar numfashin Husnah nafita a hankali ta tabbatar da cewa Husna'n tayi bacci, ahankali ta ware idanunta dasuka cika tab da ƙwalla, sarai tanaji sanda Husnah taƙira sunanta, taƙi amsawa ne gudun kada ta tonawa kanta asiri, saboda batason wannan sirrin yafita daga cikin zuciyarta, har abada tafiso ta bunneshi ita kaɗai batare dakowa yaji koya gani ba, ada tana ganin cewa ita mahaukaciya ce datakeson wanda ya zalunceta, sai ayanzu ta sake tabbatarwa kanta cewa shi so babu ruwansa, idan zai shiga jikinka baya duba wani cancanta ko matsayi haka nan yake faɗa ma, ashe da fari tayi ƙarya da tace zatayi yaƙi da soyayyar Zaid a zuciyarta, ashe ba'a iya yaƙi da soyayyar da take acikin jini da tsoka,, ada tana tunanin cewa zuciyarta bata kyauta mata ba, ashe itace bata kyautawa kanta ba, yanzu ta gamsu cewa so ne ya lalata mata rayuwa ba wai Zaid ba, ashe so shine ya yaudareta, ashe so shine yaci amanarta, ashe Zaid bai aikata mata wani babban laifi ba So ne ya aikata mata laifi me girma, inama da ana ganin so, to da tayi masa roƙo takuma yi masa magiya akan cutarwar da yayi mata daya barta haka,, itakuma SO shine ƙaddaranta, ada ta ɗauka idan tafaɗawa mutane cewa tanason mutumin dayayi sanadiyar rugujewar rayuwarta, kowa zai ɗauketa mahaukaciya wacce batasan me takeyi ba, amma kuma ayanzu tagane cewa wanda duk ya mata kallon mahaukaciya akan soyayyar da takeyia Zaid, to ko kaɗan baisan menene SO ba, SO shine wanda ke sauyawa mutum tunani alokaci ƙanƙani batare daya shiryawa hakan ba, SO shine wanda ke makantar da idanun mutum yazamanto bayaji baya gani, haka kuma tasanadiyar SO wasu ke salwantar da rayuwarsu, SO shike sawa kabi wanda baidace dakai ba, SO shike sawa amaka wulaƙanci amma kuma gobe ka koma inda aka wulaƙanta ka, SO shike sawa mutum yazalunceka amma kuma bazakaga laifinsa ba,kuma koda ma kagani bazaka iya juya masa bayaba, SO yana da matuƙar haɗari sannan yafi kowani abu saurin ɗaiɗaita tunanin meyinsa, SO shikaɗaine abun da zafinsa ke narkar da zuciya,,,,SO shine babban jagoran zuciya haka kuma shine raunin ta,, hanu ta sanya takuma dafe kanta wanda takeji kamar zai zazzago ƙasa,, hmmm kamar dai yanda Zahrah taga rana haka taga dare bacci sam yaƙauracemawa idanunta.....
(Kada kuga laifin Zahrah dan ta ci gaba da son Zaid, haƙiƙa Zaid ya cancanci Zahrah taƙisa mugun ƙi mawa kuwa, amma kuma SO bazai taɓa barin haka yafaru ba, wallahi Soyayya tawuce gaban kwatance, so babu ruwanshi da wai ancutar dakai ko ba a cutar dakai ba, shi so kaitsaye yake abunsa batare da yatambayeka shawara ba, nikam bana ganin laifin Zahrah dan taso Zaid domin shi so baya fita acikin sauƙi, sannan kuma zafinsa yanada matuƙar illa, ba'akanta aka fara ba, sau da dama zakuga namiji yana zagi dakuma dukan matarsa amma kuma duk da haka tanazaune dashi saboda tana sonsa, haka kuma saudadama zakuga Saurayi yayi amfani da soyayyar da budurwarsa takeyi masa ya yaudareta sun aikata zina, daga baya kuma idan ciki yashiga jikinta sai kuga yagujeta, saboda yasamu abun dayakeso daga wajenta, amma kuma idan harson gaskiya takeyi masa saikuga bata daina sonsaba duk dakuwa irin girman abun dayayi mata,, wallahi soyayyar gaskiya bata taɓa gushewa koda kuwa girman laifin da mutum ya aikata maka bazai misaltu ba, haƙiƙa idan banda sharrin SO babu wata mace da namiji zaiyi mata fyaɗe kuma ta dawo tacigaba da sonsa, wannan sharrin SO ne kawai wanda bashida magani😭 nidai nace ko guba baikai so hatsari ba, wallahi so mugune, inkun ganshi kukamaminshi kumai duka😰)
Ƙarfe 2 na dare ciwon Zaid yatashi sosai, abun gwanin ban tausayi, zuwa yanzu kam ciwon nasa yasoma fin ƙarfin tunanin Doctor's domin kuwa sai anyi tunanin cuta tayi sauƙi saikuma tadawo, yanzu haka bincikensu yanuna musu cewa zuciyarsa ce takumbura, gaba ɗaya hankalin Alhj Ma'aruf yakai ƙololuwa wajen tashi, Mum kuwa yanzu bata da aiki saina kuka dare da rana, hakanne ma yasanya Alhj Ma'aruf yanke hukuncin tattara Zaid ɗin sutafi Jermany, saboda ya ga abun yana nema yafi ƙarfin likitotinmu na nan, saboda koda yaushe Zaid cikin aman jini yake, lokaci ɗaya ya lalace yayi wani irin rama, kamar ma ba
Zaid ba.....
Washe Gari (Asabar)
*ƊAURIN AURE*
Tun ƙarfe 8 na safe gidansu Zahrah yake acike yayinda ƴan uwansu na nesa suka soma hallara don ɗaurin aure,, hayaniya ne ke tashi kota ina acikin gidan...
Ɗakin Zahrah na garzaya don inga awani hali take ciki...
Kwance take akan katifarta yayinda duka jikinta ke rufe da bargo, amma duk da haka bargon bai ɓoye rawan da jikin nata keyi ba, karkarwa kawai takeyi acikin bargon yayinda jikinta yaɗauki zafin zazzaɓi zau..
"Kitashi kisha maganin nan dan Allah Zahrah, kinga fa babu amfanin zama da ciwo batare da kinsha magani ba" Husnah tafaɗi haka ga Zahrah cike da lallami..
Kai kawai Zahrah ta'iya kaɗawa alamar "A'a bazata sha ba" komagana ma yanzu bata iyayi saidai kawai ta kaɗa kai, hakan yafarune kuma saboda ciwon kai me tsanani da ta tashi dashi a safiyar yau ɗin,, duk yanda Husnah takaɗa ta buga akan Zahrah tatashi tasha magani ƙiyawa tayi, sai ruwan hawaye dake ta fita daga cikin idanunta, dole haka Husnah ta ƙyaleta..
10:30 tuni ƙofar gidansu Zahrah yasake cika da jama'a bamasaka tsinke, hayaniya ne kawai ke tashi tako ta ina, yayinda tsala tsalan motocin ango suka ƙaraso,, hmmm Dr.Sadeeq yasha kyau sosai cikin wata haɗaɗɗiyar gezina milk colour me matuƙar kyau da tsadar gaske, ɗinkin rigane da wando saikuma gare, amma kuma sunyi masa kyau sosai, yayinda ya ɗaura tsadadden agogo a hanunsa na dama, takalmin ƙafarsa kuwa ƙirar kamfanin GUCCI ne me matuƙar kyau,, ango fa yasha kyau iya kyau, sai yau nima nasake tabbatarda cewa shiɗin ma wani Handsome guy ne mezaman kansa, domin kuwa duk ƙwaƙwan mutum babu ta'inda zai kushesa, yahaɗu iya haɗuwa sonkowa ƙin wacce ta rasa😜, bakin ango fa yaƙi rufuwa sai murmushi kawai yake, yayinda abokansa keta tsokanansa,, shidai kawai murmushi yaketa zubawa, bazai taɓa iya misalta irin tarin farincikin dayake ciki ba, haƙiƙa yau yana cikin nishaɗi dakuma jin daɗi, yau takasance babban rana agareshi ranar da duk wani gauro da gauruwa suke jira, ranar da duk wani mai hankali da nutsuwa yake biɗar zuwanta wato RANAR AURE, shikam sai dai yace Alhmdlh yagodewa Allah mai kowa me komai daya nuna masa wanann rana... Baffa na hango shima yau cikin farinciki yake, yasha adonsa cikin farar shaddansa riga da wando dakuma gare, su uban amarya manya,,, 11:00 am dai dai dandazon jama'a suka shaida ɗaurin auren SADEEQ KHABEER SARDAUNA (Dr.Sadeeq) da amaryarsa FATIMA ADAM (Zahrah) akan sadaki naira dubu ɗari,, masha Allah ana kammala ɗaurin aure aka soma taya ango murna da Allah yasanya alkhairi, ae kuwa fuska asake haɗe da tarin annuri Dr.Sadeeq ke amsawa, hamdala kawai yakeyi acikin zuciyarsa shikenan Zahrah ta zama tasa mallakinsa halaliyarsa... Bayan angama musabahane kuma aka ɗunguma zuwa wani babban hotel wanda anan za'a gudanar da receiption....
Lokacin da labari ɗaurin auren ya'isa ga kunnen Amarya wani irin faɗuwar gaba wanda bata taɓa jin irinsa ba taji ya rusketa, shikenan yanzu tazama matar Doctor, zuciyar tane tashiga bugawa da sauri sauri yayinda har ƙirjinta yasoma amsawa, take taji wani abu maikama da tsananin tsoro ya lulluɓe mata jiki,ae kuwa sai neman ɗan kuzarinta tayi ta rasa,jitayi gaba ɗaya gaɓoɓinta sun mutu laƙwas kamar ansassare mata su,, sake duƙunƙunewa tayi acikin bargo tashiga rera kuka marar sauti, ita bata tsani Dr.Sadeeq ba ko kaɗan, amma kuma tarasa meke damun ƙwaƙwalwa da zuciyarta....
(Kuyi haƙuri Team Zaid wallahi nima Allah jikina gaba ɗaya yayi sanyi sai dai kuma kunsan ita ƙaddara bata taɓa sanjawa dole saitazo a yanda Allah ya aikota😭 yanzu haka jinake kamar ruwan jikina ya ƙare😥)
Ƙarfe 2 dai dai jirginsu Zaid yatashi daga cikin garin Lagos Nigeria zuwa Jermany saidai shi Zaid sam baisan wainar da ake toyawa ba saboda baya cikin hayyacinsa kwata kwata, tunda suka baro Abuja har suka iso Lagos baisan inda kansa yake ba....
Ɓangaren ango kuwa reception aka gudanar gangariya, anci kaji ansha fruits juice kowa cikin sa yayi haniƙan sai dai godiyar Allah da sanya albarka...
Amarya kuwa koda ruwane takasa sanyawa acikin cikinta, rashin lafiya sosai ya tsananta a gareta, zuwa yanzu kam hawayen ma sun kafe sundaina fitowa, sai numfashin wahala da take fitarwa ta bakinta kawai,, kasancewar anata hidima yasa babu wanda yadamu da cinta kokuma shanta, Husnah ce kaɗai ke tsaye akanta tana bata kulawa.
"Dan Allah Zahrah ba danniba kitashi inrakaki toilet kiyi wanka kizo kisamu koɗan sabon kayane kisanya kingafa zuwa anjima za'a zo ɗaukarki!" Husnah tafaɗi haka tana me ƙoƙarin tada Zahrah dake kwance zaune.
Da taimakon Husnah Zahrah taje banɗaki tayi wanka, koda tafito wata haɗaɗɗiyar doguwar rigar atamfa Husnah ta bata tace ta sanya, babu musu tasanya saigashi kuwa rigan tayi matuƙar yi mata kyau ajiki, da ƙyar Husnah ta lallaɓata tashafa mata powder haɗe da man leɓe, sai kace wata ƙaraman yarinya,,, komawa gefe Zahrah tayi ta takure bayan Husnah tagama shiryata, still Husnah maganar abinci tayi mata amma Zahrah tasake bushe idanunta tace ita sam bazataci abinci ba batajin yunwa (Ninaga jarfa saikace wanda aka mawa auren dole 😏)...
Ƙarfe 5 tsala tsalan motocin ɗaukar amarya suka shiga fakawa a ƙofar gidansu Zahrah motocine reras masu kyau har guda 15 suka zo don ɗaukar amarya yayinda motar da amarya zata shiga ta banbanta da duka sauran motocin don tafi duka sauran kyau..
Zahrah na zaune wata Aunty Ladi ƴar uwar mahaifiyarta wacce tazo daga Niger tashigo cikin ɗakin babban mayafi me kyau ta ɗauka haɗe da rufe Zahrah dashi, miƙar da'ita tsaye tayi cikin farinciki tace
"Allah yayi yauzaki tafi ɗakinki amarya muje ɗakin Inna'n taki aimiki nasiha"
aitun kan aƙarasa ɗakin Inna Zahrah ta ɓarke da kuka wiwi, (Wayyo Allah, wallahi duk rashin daɗin gidanku randa zaka barshi saikaji ciwo acikin ranka harna tuna da nawa ranan 😭🙈)
Nasiha Inna da sauran matan dake ɗakin suka shiga yi mawa Zahrah akan tabi mijinta sauda ƙafa inayi bari na bari, komin ƙanƙantan ɓacin ransa ta gujesa, duk kuma wani abu datasan bayaso kada ta aikata, sannan kuma taji taƙi ji tagani taƙi gani, takuma riƙi haƙuri don shine tubali kuma gini haka ƙinshiƙin zaman aure, bawai idan anyi aure kullum soyayya ake ci ba, a'a watarana dole sai kunɓatawa juna, dole sai kunyi haƙuri kundanni zuciyarku tukun zamanku zaiyi daɗi, sannan kuma idan tasan tayi masa laifi kada tayi girman kai, tasameshi har ƙasa ta duƙa tabasa haƙuri, domin kuwa har kullum shine sama da'ita, yanzu amatsayin uba yake agareta bata da wani wanda yafishi,, wayyo Allah Zahrah tayi kuka sosai harda shiɗewa, Allah sarki sabo turken wawa duk da cewa Inna watarana tana hantararta amma yau duk saitaji babu daɗi tafiyan Zahrah'n saiga Inna tana hawaye tana jan majina, shikenan Inna kuma fa cin kaza ya yanke mata lol 😂.
Su Inna suna gama nasu nasihar aka garzaya da'ita wajen Baffa,, wayyo Allah Zahrah tana ganin Baffanta ta faɗa jikinsa haɗe da sake ƙara volume ɗin kukanta, Allah sarki take Baffa shima yasoma hawaye, daƙyar ya'iya daure zuciyarsa yayi mata nasiha, duk dai maganar ɗayace shine tabi mijinta sau da ƙafa takumayi masa biyayya akan duk abun dayace, sannan kuma tazamo me haƙuri akan dukkan komai, sannan kuma yaroƙi yafiyarta akan abun dayayi mata baya, tana kuka tace tajima da yafe masa kuma ita baimata komai ba, itama tanemi yafiyarsa yakumace ya yafe mata😭
Haka Aunty Ladi da Husnah suka fita da Zahrah tana kuka Husnah kanta kuka take, yanzu itama haka watarana za'a zo a ɗauketa daga gaban Momynta akaita can cikin wasu dangin😭...
Anasa amarya acikin mota sauran ƙawaye da ƴan uwa ma kowa yashiga motar da ransa keso, bayan komai yakammalane motocinnan suka gangara kantiti, atare suke tafiya wani abayan wani, sannan kuma komai anitse akeyinsa babu wani hargowa...
Direct gidansu Dr.Sadeeq aka wuce da amarya, domin kuwa 8:00 pm nayi za a wuce wajen diner...
Abun mamaki tarba me kyau Hajiya tamawa amarya dakuma danginta, ko kaɗan bata nuna musu ɓacin rai kokuma tsana ba, sai dai su Aunty Raliya dasuketa binsu da wani irin kallo dake nuni da cewa baƙaunarsu sukeyi ba, ɗaki guda aka warewa amarya, balaifi ɗakin yayi kyau sosai, akan gado Aunty Ladi ta zaunar da Zahrah, mintuna kaɗan da shigowansu ɗakin wasu ƴan mata suka cika musu gabansu da kayan ciye ciye dakuma na sha abun gwanin burgewa, gaskiya sun samu tarba na mutumci daga Hajiyar Doctor......
Wayar Husnah ce tafara ruri ganin wanda ke ƙiran nata yasanya ta ɗaga wayar bawani ɓata lokaci
"Bestie'n mu how far?" abunda wanda yaƙirata acikin wayar yafaɗa kenan..
Dariyane yakamata amma saita taƙaita dariyan haɗe da cewa "I'am fine sai dai gaskiya na gaji"
Murmushi shima yayi haɗe da cewa "Ina Amaryata Allah yasa tana lafiya, nayi kewarta sosai rabona da'ita fa tun ranan alhamis" Dr.Sadeeq yafaɗi haka yana me gyara kwanciyar dayayi akan gadonsa...
"Kamar kuwa kasan kainaketa so kaƙira, wallahi yau tun safe Zahrah taƙicin komai kuka kawai takeyi, gashi bata da lafiya temperature ɗinta ya hau sosai" Husnah tafaɗi haka ga Dr.Sadeeq.
"Subahannallah, keda su waye aɗakin?" Dr. yatambayi Husnah cike da zaƙuwa..
Kallon waƴanda ke cikin ɗakin Husnah tashiga yi kafun tace
"Gaskiya munada ɗan yawa"
"Oh my God to shikenan, please anjima kikawomin ita ina cikin boys guaters kinji"
"To shikenan zan kawota insha Allah"
Daga haka suka kashe wayar murmushi kawai Husnah tayi bayan ta'ajiye wayar tata gaskiya azamaninnan idan mace tasamu wanda ke sonta kamar irin sonda Dr keyiwa Zahrah yakamata ta riƙeshi da kyau hanu tara tara domin samun irinsu wahalane dashi, saboda yanzu zuciyoyin yawancin mutane duk taɓaci da yaudara.........
*Inasonku masoyana na Wattpad irin sosai ɗinnan, ina yaba ƙoƙarin ku wajen min comment, Allah yabar ƙauna*
*Kuɗin ma ae nadabanne masoyana na Whatsapp inajin daɗinku sosai iya wuya muna jone Insha Allah*
0 comments:
Post a Comment