Zahra Muhammad Mahmud
*DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION*
*Bissimillahirrahmanirrahim*
Da sunan Allah Zan fara Da sunan shi zan gama insha Allahu.
Kada wani ko wata ya juyamin labarina ta kowacce siga in hakan tafaru nabar mutum da rabbil alamin.
Inkinji wani abu dayayi dede da rayuwarki arashi ne dan labarina ƙirƙirarrene.
*1*
Salma ƴa ce ga malam hadi me walda da faci,suna zaune a garin kaduna cikin wata unguwa da ake kira hayin rigasa.
Malam hadi mutum ne me taƙawa da tsoron Allah duk da talaucinshi kullum cikin yiwa Allah godiya yake,dan wata rana ko,abinda zasu ci gagararsu yake.
Matarshi ɗaya da ƴaƴa biyu,Rakiya shine sunan matar tashi,wacce ƴaƴan ke kira da Umma,se Sahabi wanda shine babban ɗansa,sannan Salma,wacce tazama ƴar auta sabida daga ita Allah be ƙara basu haihuwa ba.
Salma ƴar kimanin shekara Goma sha shida,ta kammala makarantar secondry da ƙyar sabida iyayanta ba masu ƙarfi bane,amman suna da zuciyar neman nakansu,tun tasowar Salma yarinyace da ta ɗauki ɗabi'ar ƙarya tasa a ranta,tana da rawar kai ga tsiwa da rashin kunya,bata da buri daya wuce ace gata a jami'a tana karatu uwa uba kuma ace ta zama ƳAR BAUTAR ƘASA,wannan shine fata da burin Salma
Da kyar tasamu tayi registration ɗin jam,kuma Allah ya taimaketa taci,tasamu Admission a Zaria,wato A,B,U,in kuka ga yadda kan Salma ke rawa zaku ɗauka har tashiga ma ta gama.
Duk wata kadara da iyayanta suka mallaka ita suka siyar,suka biya mata kuɗin registration,murna gurin Salma baa magana.
Tun shigar Salma jamia idonta ta ƙara buɗewa ta fahimci ba ƙaramin cutarwa bace data kasance ƴar talakawa,sam kalarta ba kalar talauci bace,sabida haɗuwa da tayi da ƙawaye ƴaƴan masu kuɗi.
Salma duk wani abu da ake kira kyan sura ba abinda Allah be bata ba,tana da kyau na bugawa a jarida sede wani ikon Allah duk da wannan kyau na,salma sam bata da farin jinin samari,dan ko saurayi bata dashi,wanda ita anata ganin talaucin data taso acikine yasa samarin basa kulata,hakanne yaƙara haddasa tsanar talauci a zuciyar Salma duk wani abu daze daidaitata da ƴaƴan masu kuɗi shi takeso kuma takeyi,matsalarta ɗaya bata da irin suturarsu,wannan shi ke kawo mata cikas a rayuwar datasa kanta aciki.
Abu dayakai abu Salma har sata tafarayi,kana sake da kayanka tuni zata gyara musu zama,in shaddace se takai a rina mata taci gaba da sawa ba me cewa tashice,inkuma atamfa ko materials ne se takai acanja mata ɗinki,yadda duk ƙwaƙwar mutum yasha Ƙarya yace tashi ce.
Satar takalmi da jaka kuwa ta jima dayin,degree a wannan fannin sede idan bata ganiba,shigar ta ce tasa ɗalibai ƴan uwanta ke ɗauka ƴar masu kuɗi ce.
Muje zuwa.
Surbajon kuce.
[8/8, 19:15] UMMU AYMANA CE: *👩🏻💼Y'AR BAUTAR K'ASA*
Zahra Muhammad Mahmud
DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION
*See yourself as a light and you will shine,there is no one without a past,Don't be a prisoner to your past,move on, Allah is your witness*
*2*
Haka rayuwar salma taci gaba da tafiya,acikin jamia,har zuwa lokacin data kammala aka turasu service.
Salma tafi kowa ƙosawa ayi posting ɗinsu,har addua take sunanta yafito a verge A, Allah kuma yataimaketa sunan nata yafito inda aka turata garin keffi,cikin jahar nasarawa domin gudanar da bautar ƙasarta acan.
Salma sam bataso aturata keffi ba,Abuja taso akaita inda idonta ze ƙara buɗewa ,sosai.
Zaune suke ita da wata Aminiyarta,me suna Firdausi,wacce aka fi sani da fee-fee,makwabciyarsu salma ce,yarinya me natsuwa da kamun kai,sam halinsu yasha bambam da salma Allah ne de kawai ya haɗa jininsu suke ƙawance tun daga yarinta,makarantarsu ɗaya,ko hutu akayi tare suke tafiya,sede ɓangaran da kowa ke karanta da bam,ita firdausi,business admin take karanta,yayin da salma take karantar medical doctor.
Hira suke game da tafiyarsu bautar ƙasa,inda dukansu gari ɗaya aka turasu cikin hukuncin Allah,wato keffin ɗan yamusa.
"mtssuu,nide fee-fee gaskiya keffin nan bataminba,wlh,nibanma taɓa jin,sunan garinba inbanda da aka turamu can"salma ta faɗi cikin yanayin damuwa.
Dariya feefee tayi sannan tace.
"In banda abinki,Salma meye abun damuwa aciki mude ba iyakarmu in mundawo daga inda muke service ɗin mu koma kamp ba,nide yamin wlh dan inason dama indunga zuwa garin da ban saniba"feefee ta ƙarasa zancan cikin dariya.
Tsaki salma ta ƙarayi,sannan tace.
"Ni wlh Abuja naso aturani,idonka zefi buɗewa".
"To inbanda abinki,ay tsakanin keffin da Abuja ba nisa,ɗari biyar ne kuɗin mota,sannan garin keffin fa,ance garin ƴan boko ne sosai,kuma babban garine,dan yawancin maaikatan garin ma a Abuja suke ayki,akwai manyan masu kuɗi a garin sosai,dan har ɗan takarar gwamna garesu agarin,sunan shi wadada,kinga ko in ace ƙaramin garine bazaa sami hakanba".
Murmushi salma tayi tace.
"feefee,duk wannan bayanin a ina kika sameshi,naga kema kince bakisan garinba?"
"hhhh kede akwai sokuwa, kinmanta yaya nasiru acan yayi service ɗinshi?ay duk shine yabani labari,kinsan ko ba halinshi bane ƙarya bare ince ita yamin"
Farin ciki ne ya mamaye zuciyar salma sabida ta gamsu da bayanan feefee,dan tasan yayan feefee nasiru ba maƙaryaci bane.
Da wannan hirar da sukayi da feefee ne salma ta samu ƙwarin guiwar,tunkarar garin na keffi.
Shiri iyayanta suka mata sosai,gamida dayi mata nasihar taji tsoron Allah,takama mutuncin kanta,salma harda kuka na munafunci kamar ta yarda da shawarar iyayan nata.
Haka,suka kamo hanyar keffi ita da sauran ɗaliban da aka turasu garin.
Sanda suka shigo garin Abuja salma ji tayi kamar tace a sauketa a garin,dan haɗuwar garin,haka tanaji tana gani aka wuce garin batare da an tsaya ba.
Da la'asar suka isa, NYSC camp dake garin keffi.
Ranar lahadi ne dan haka masauki aka basu kamin gobe monday su gana da mahukuntansu.
Da kyar salma ta yarda ta kwanta,da dare yayi dan ita burinta,tafita ta zaga garin taga yadda yake.
Feefee ce ta hanata fita,amman ranta be soba,haka ta kwanta tana mita dan ba haka tasoba.
Washe gari da safe duk suka hallara a inda zaa faɗawa kowa inda zeje yayi aykinsa.
Babban Asibitin gomnati na garin aka tura Salma,me suna.F,M,C.
Tun daga bakin gate ɗin Asibitin salma ta fahimci asibitin babba ne duba da yawan jamaar dataga suna shige da fice aciki.
Haka taje tayi clearing komai aka nuna mata ɓangaran dazata dunga wakilta,inda babban likitan gurin bayanan yana ƙasar jamus,inda yaje wata seminer da aka haɗa ta manyan likitoci.
Muje zuwa.
Maman yusuf.
[8/9, 11:33] UMMU AYMANA CE: *👩🏻💼Y'AR BAUTAR K'ASA*
Zahra Muhammad mahmud
DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION
*3*
Yau da wuri salma ta tashi tayi wanka ta tsuke acikin uniform ɗinta na nysc,kaisu tayi aka rage mata tsawo da faɗin wandon,hakan yasa intasaka,wandon baya sauka har ƙasa,daga sama kuma ya kamata inda hips ɗinta ya bayyana sosai acikin wandon,haka itama rigar ta kamata sosai,bata ɗora ta samanba,hular kawai tasaka ta saki gashinta baya,se wani uban glass data rufe idonta dashi.
Tana gama shiryawa ficewa tayi,a waje suka haɗu da feefee,cike da mamaki feefee take kallon shigar salma,wacce ita feefee ɗin harda ƙaramin hijabi tasaka,kamin tasaka hular.
"Salma kinada hankali kuwa,wannan wacce iri ɗabia ce don Allah,yanzu da kikayi wannan shigar meye marabarki da arniya?karfa bautar ƙasa tasa kimance da tarbiyar da iyayanmu suka bamu".
Dariya,salma tayi sannan tayi ƙasƙas da cingam ɗin dake bakinta,sannan tace.
"banga laifinki ba dan kin faɗi hakan,danke kinga kinada farin jinin samarine shiyasa,niko ko kare be taɓa tsayar dani yace yana sonaba,dan haka dole inyi shigar dazan bayyana kyawun,surata ko Allah zesa wani yaganni yace yana so,ni kinga tafiyata nakusa yin latti"
Tana kaiwa nan tasa kai tayi ficewarta tana juya mazaune gamida karkaɗa na shanunta.
Feefee binta tayi da ido gamida jin ƙyamar hali da ɗabiun salma,adduar shiriya taimata sannan itama tanufi gurin nata aykin.
Salma ko tafe take a ƙafa tana baza takunta,wanda duk inda tawuce seta bar maza da baki buɗe amman ba wanda Allah yaba ikon yimata magana.
tana isowa bakin titi tsayawa tayi jiran masu mashin dan garin na keffi babu napep sede ƴan achaɓa.
wata arniyar motace tazo tawuce tagabanta da gudu,miyau ɗin salma seda ya tsinke gameda haɗuwar motar,jitayi dama tatace, har motar ta ɓace salma bata dena binta da kallo ba.
Jiki asanyaye tahau mashin tanufi gurin aykin,koda tashiga asibitin gabanta taji yana faɗuwa haka ta daure ta ƙarasa ɓangaransu,ba ƙaramin gigicewa tayiba da ganin motar data wuceta ɗazu a parking space ɗin gurin.
Shiga ciki tayi sede tayi mamakin ganin kowanne maaikaci yamaida hankalinshi kan,aykinshi saɓanin da da kowa ke shagalinsa.
Gurin wata nurse ta nufa tace mata.
"mary lafiya kuwa naga duka kowa ya natsu?kode wani patient ɗinmune ya mutu?"
Jawota gefe mary tayi sannan ta raɗa mata akunne.
"oga,ne yadawo un expected ɗazu ya shigo"
"Waye oga kuma?dahar zesa kuyi irin wannan natsuwar waye shi?"
Toshe mata baki tayi sannan tace.
"Babban doctor ɗin gurinnan shine yadawo daga seminar daya tafi"
Ido salma taware sannan ta kaɗasu cikin wani yanayi,sannan tace.
"ok badamuwa,amman kuncika tsoronshi dayawa sekace mala'ika"
"Nide baruwana kije ki kwashi gaisuwa,ga office ɗinshi can,kuma wlh kitaka ahankali bayason raini ko kaɗan,kuma beson surutu,gashi ke kuma shegen surutu ne dake,kuma shine ze dunga kula dake har kigama abinda yakawoki"
Dariya salma tayi sannan tajuya tanufi office ɗin da mary ta nuna mata.
Da sallamarta ta tura ƙofar office ɗin tashiga,wani niimtaccen ƙamshine yadaki hancinta wanda ko baa faɗa mata ba turaren me tsadane.
idontane yasauka kan ɗan ƙarfen da ake rubuta suna dake,ajiye akan table ɗin dake gabanshi,wanda shi kuma yajuyawa table ɗin baya,yana jujjuyawa kan kujerar.
*Doctor Najeeb Hassan Alkanawi*
shine sunan data ga an rubuta ajiki.
a hankali ta furta,"Wow nice name".
Guri tasamu tazauna batare data jira ya amsa sallamar tata ba bare akai ga yabata izinin zama.
zamanta keda wuya taji wata murya wacce tunda take bata taɓa cin karo da namiji me daɗin murya irintaba.
"how dare you,to come to my office,and sit without my permission?get out right now,mtsssu useless"ya faɗi batare daya juyo yakalli koma wayeba,d ƙamshin turaran daya jine yas yagane macec ta shigo office ɗin,sabida turaran na matane.
Salma jikinta har ɓari yake tamiƙe tafice daga office ɗin zuciyarta namata zafi,kuka takeyi,sabida tunda take baa taɓa cin mutuncinta irin hakaba,take taji tsanar likitan tashiga zuciyarta me tsanani.
muje zuwa Surbajoce duk wuya duk runtsi.
[8/9, 22:49] UMMU AYMANA CE: 👩🏻💼Y'AR BAUTAR K'ASA
Zahra Muhammad Mahmud
DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION
*A jawo,A jawo,inde Ilahu ya riƙe farkon,wlh babu me iya tsinke zarena,zahra surbajo ce har abada#haka nake,aman wuta nake na ƙona kiɗa 🤷♀*
*4*
Guri tasamu a inda babu yawan mutane ta zauna tana share hawayenta,tsanar doctor ɗin naƙara shiga zuciyarta.
Mary ce tazo wucewa,taganta,da sauri ta ƙarasa gurinta.
"corper salma lafiya naganki zaune anan ko har doctor ya sallamekine?"ta tambayeta cike da kulawa.
Tsaki salma tayi sannan tace.
"wannan ɗan akuyar likitan bashida mutunci,karkiga irin korar dayamun ta wulaƙanci,kawai dan nashiga office ɗinshi batare daya bani izini ba harda cemin useless fa"
"kema salma me yakaiki,tun kamin kijefa seda na faɗamiki likitannan bayason raini kuma shi agurinshi abinda kikayi raini ne shiyasa yamiki hakan"marry ta faɗi fuskarta ɗauke da damuwa.
Wani tsakin salma tasaki sannan tace.
"can ta matse mishi,ni ze nunawa son girma uban waye beso a girmamashi,sallamafa nayi masa ma be amsaba".
Dariya mery tayi sannan tace.
"can ta matse mishi kode can tamatse miki,wlh kece zaki ɓata takardunki abanza,shiko aykinsa yake wahalarsa ta ƙare,yau inkika bari yatashi bakije kun ganaba wlh kin kaɗe".
Shuru salma tayi tana nazarin maganar mary,ita bawai karatun dazatayi asara bane yadametaba,babban tashin hankalinta ace yajawo an koreta a bautar ƙasa shine kawai tashin hankalinta.
jiki asanyaye ta juya takoma office ɗin,ta dunga sallama be amsaba seda takusa minti Ashirin atsaye sannan ya amsa yabata izinin shiga.
a ɗan tsorace ta shiga tasamu gefe ɗaya ta rakuɓe,bakinta na rawa tace.
"good morning sir".
ko kallonta beyiba yanata rubuce rubuce awani file sannan yace.
"who are you?"ya tambaya sanda ya ɗago ido yana kallonta.
wow ita salma ta faɗi,dan likitan kyanshi yakai kyau ta koina,duk da tanajin tsanarshi aranta amman hakan be hanata ganin shi da kyau ba,dan duk hassadarka ga wanda bakaso kasha ƙarya kace ɗuwawunshi ɗaya ne.
"am salma hadi,from A,b,u zariya".
ƙara ɗago ido yayi yana ƙaremata kallo,sannan ya yamutsa fuska yace.
"da kyau,amman ke ba musulma bace ko?"ya jeho mata tambayar batare daya kuma kallonta ba.
Ran salma inyayi dubu ya ɓaci,gameda rainin wayon da likitan yakeson yimata,amman dole tayi wani abu akai dan bazata barshi yaci bulus ba.
Murmushi tayi tana ɗan sosa kanta alamar jin kunya,sannan tace.
"Doctor kenan,ashe da gaskene da akace duk likitan daba musulmiba inyaga musulmi yana ganeshi,wlh se yanzu nayarda da hakan,da ban yardaba,se gashi naga misali akanka tunda gashi kallo ɗaya kamin ka gano ni musulmace,"takai ƙarshen zancan fuskarta ɗauke da keeler smile.
ko kallo bata isheshiba bare tasa ran,zenunamata ɓacin ranshi.
cugaba yayi da rubutunshi,seda yagama tsaf sannan yamiƙe ze fice,seda yakai bakin ƙofa sannan yace.
"Ƙarfe bakwai dot ake hallara agurin ayki,ko ranar sunday ne sede ki haƙura da zuwa service a ranar inkika kuskura kika ɓata lokaci koda minti ɗayane,zan koya miki hankali da yadda ake magana da manya,duk da cewa ranar friday ba zuwa nakeba sabida masallacin jummaa dazanje,ki yi hattara,am najeebullahi Alkanawi,bana ɗaukar raini".
yana kaiwa nan yafice yabarta a office ɗin se juye juye take tabbas ta lura seta nuna mishi kalarta ta aynihine ze kiyayeta.
Tajima a officr ɗin tana tunani,kamin daga bisani idonta ya sauka kan wasu kuɗi dake zube akan table ɗinshi ƴan dubu dubu,wanda da gani tasan mancewa yayi dasu agurin.
Cike da faraa ta ƙarasa gurin kuɗi ta kwashe ƙirgasu tayi taga ten thousands ne,da sauri ta turasu cikin bra ɗinta ta fice daga office ɗin tanajin yau take sallah agurinta dama kuɗinta ya ƙare.
Tofa🤔
Surbajo ce har abada ba fashi.
[8/10, 08:13] UMMU AYMANA CE: *👩🏻💼Y'AR BAUTAR K'ASA*
Zahra Muhammad Mahmud
DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION
*Gareku masoyana,don Allah,don Annabi,duk inda kukaga anzageni,karku ramamin,kubar mutum,da halin shi,kamar yadda kuka saba bani haɗin kai kuci gaba na in kunga sakon zagin kubarshi can inda kuka gano shi,karku damu da zagin nasu kamar yadda nima be dameniba,Sabida abun kunyane ga zaki ya tsaya musayar yawu da ɓera,surbajo ce#haka nake,atare abuge ba dama,abari in wuce ga haushi,Allah kaimin komai har Abada Alhamdulilahi*
*5*
Cike da farinciki salma takoma camp,tun a hanya ta tsaya ta sayi duk abinda bata dashi sannan ta ƙarasa.
Feefee tayi mamakin ganin salma da kudi wanda tasan bata dasu,dan haka tambayarta tayi.
"Salma ina kika samo kudi haka?"
Dariya tayi sannan tace.
"Tsinta nayi a gurin aykinmu"
"wacce irin tsuntuwace wannan,ta kuɗi me yawa,kuma waya faɗamiki,in ka cinci kuɗi ya zama naka ,ko cigiya nasan bakiyiba haba salma abun da kikeyifa be dace ba"
"To uwar ile,nide na tsinta kuma nakashe,karki dameni kuma,ke komai mutum yayi idonki nakai,pls kiɗan rage sa ido don Allah mtssuu"
Feefee bata sake magana ba,illah zuba mata ido da tayi.
Washe gari da asussuba salma ta shirya,ƙarfe shida tanufi gurin ayki,acan bakwai taimata.
A ɓangaransu ta riga kowa zuwa,dan haka office ta shige tayi zamanta.
Bata jimaba tafara jiyo hayaniyar mutane a waje,tana nan zaune marry ta shigo.
"Ah salma kene da sassafe haka kamar wacce ta kwana anan?"
Tsaki salma tayi sannan tace.
"Wannan ɗan balain ne yace kar in bari bakwai tayi banzo gurin Aykiba,shiyasa kika ganni anan da wuri"ta ƙarasa maganar cikin yanayin damuwa.
Dariya marry takeyi harda tuntsurawa sannan tace.
" kin faɗa tarkon doctor,kita addua Allah ya rabaku lfy,dan bashi da daɗin shaani sam".
Shuru salma tayi kawai tan nazari a zuciyarta.
Doctor Najeeb se ƙarfe takwas ya iso asibitin kai tsaye office ɗinshi ya shige,yana zama,ya kunna computer dake haɗe da cct camara,dan ganin abinda ya wakana kamin yazo,
Ba ƙaramin mamaki yayiba sanda ya hangi salma tana kwashe kuɗin daya bari akan table jiya,wanda shi inbanda yanzu daya gani yama manta da kuɗin,sosai yayi mamaki,aranshi yace.
"she is so beautifull,but ba hali me kyau,iwill make sure that i play with her intelligent"yayi want keeler smile ta gefen bakinshi.
Jin doctor yazone yasa salma miƙewa tanufi office ɗinnashi,sallama tayi baa jimaba ya amsa yabata izinin shiga.
Tana shiga taga ya ƙureta da ido,har tsarguwa tayi ta kama ƴan soshe soshe alamun rashin gaskiya.
"have a sit".
taji yace,jiki a sanyaye tazauna,ta gaisheshi ya amsa.
Daga haka bece mata komaiba yafara duba marasa lafiya,wainda suke matane,kasancewarshi, doctor,wasu tambayoyin in yana yiwa patient ɗin har kunya suke ba salma shiko ko ajikinshi,itade tana sauraronsu tana jorting a littafinta na abinda take ganin bazata iya riƙewaba.
be dakatar da duba marasa lafiyanba,se da azahar,dan haka miƙewa yayi yacire agogonshi yashiga toilet yayi alwala ya wuce masallaci,yana sane yayi kamar yamanta da ogogon,wanda kuɗinshi yafi dubu ɗari.
Yana fita salma ta ƙarasa haɗa Takardun gurin ta adana,har ta miƙe zata fita itama,se idonta ya sauka kan agogon,tsayawa tayi tana kallonshi,tana tunanin ɗauka,tana jin tsoro.
Ƙarasawa tayi gurin agogon,sede abinda ta hanga aƙasan table ɗin yafi mata agogon,amfani,kuɗine bunch bunch na one thousands guda huɗu.
jiki na ɓari tasa hannu ta ɗauki ɗauri ɗaya,harta tafi sekuma ta sake dawowa ta ɗauki ɗaya yazama dubu ɗari biyu kenan,cikin aljihunta ta zuba kuɗin,tafice daga office ɗin da sauri.
Jakarta taje ta zuba kuɗin aciki sannan tayi sallah,ta koma office ɗin doctor tana ta adduar Allah de yasa be duba kuɗinshiba.
Shiko doctor duk yana sane ya ajiye kuɗin dan yagani iya ƙananan sata ta iya koko harda manya ma,ilai kuwa koda yadawo daga masallaci,dubawa yayi yaga babu dan haka kunna computer yayi dan yaga yadda abun yafaru.
Sosai yasha mamaki,daga ƙarshe abun yabashi dariya,ba abinda yafi bashi dariya kamar yadda ta ɗauki na farko har ta tafi taga be ishetaba ta dawo ta ƙara na biyu.
Kashe computer yayi yashiga tunanin ta ina ze ɓullowa wannan me hannun ɓeran da aka haɗashi ayki da ita.
Sallamar salmace ta dawo dashi daga duniyar tunanin,izinin shigowa yabata.
Tana shiga yamiƙe afusace,yace.
"uban waye ya dau..."bata jira yagamaba jikinta narawa bakinta na karkarwa tace.
"wallahi doctor ban ɗaukar maka kuɗiba"
Dariyace taso kamashi,ganin yanayin da salma tashiga,dakewa yayi yasake dakamata tsawa yace.
"kinji nace miki,an ɗaukemin kuɗine?baki jira nagama maganaba kin katseni,to cewa zanyi waya ɗauke takardun danake ayki akansu".
Wata uwar ajiyar zuciya salma tasaki harda dafe ƙirji ta jingina da bango ta lumshe ido na ƴan mintuna.
Dariyace sosai cike da cikin doctor amman se yadanne.
Salma baki na rawa gumi na keto mata tace.
"nice na kwashe na zuba maka a loka,bari in ɗauko,maka"kamar mazari tanufi lokar ta ɗauko takardun ta bashi,suka ci gaba da duba patients,lokaci zuwa lokaci doctor na lura da yadda salma take ta faman sakin ajiyar zuciya.
haka sukai ta duba marasa lafiyan har zuwa sanda sukayi changen duty.
Jiki na ɓari salma tafice daga Asibitin,aƙafa take tafiya,dan gaba ɗaya a rikice take tama kasa tsaida mashine ta hau,dan tunda take sata bata taɓa yin babba kamar wannan ba.
Motar doctor taga yasha gabanta kaɗan yarage ta saki fitsari a wando,sabida tsoratar datayi,kasa ci gaba tayi da tafiyar,shiko duk yanayin data shiga yana observing, da ƙyar ta ƙaraso inda yake taɗan rusuna ta gaisheshi.
"shigo in rage miki hanya"doctor yace batare daya kalletaba.
Da cewa zatayi ta gode,sekuma taji tsoron kar rsnshi ya ɓaci wataƙila ma yagano,ita ta ɗaukarmasa kuɗi ya tozartata a gurin,danhaka ba musu tashiga motar suka tafi.
Se ƙara rungume jakar ta takeyi takasa sakinta.
"Hala de jakarnan taki akwai wani abu me muhimmanci acikine ko?"doctor ya wurga mata tambaya.
A kiɗime ta waigo tana kallonshi tace bakinta na rawa.
"Aa wlh ba kuɗi bane acikiba"ta bashi amsa tana ƙara riƙe jakar da kyau.
"ke ko kode kunnenki beji dakyaune a ina kikaji na ambaci kuɗi?".
Jan bakinta tayi tai shuru,har suka iso camp ɗin yasauketa,har ta sauka daga motar,se ya leƙo da kanshi ta window yace.
"To akashe lafiya".
yana faɗin hakan,yaja motarshi ya barta agurin tana nazarin kalmarshi.
"akashe lafiya,to me yake nufi kenan?"salma ta tambayi kanta,rashin amsane yasa ta juya tawuce ɗakinsu.
surbajo ce,for life.
[8/10, 18:11] UMMU AYMANA CE: *👩🏻💼Y'AR BAUTAR K'ASA*
Zahra Muhammad Mahmud
DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION
*i don't need everybody in my life,i just need few people who truly understand me,#be your own bossssss*
*6*
Tana shiga ɗakinsu tayi sauri taciro kuɗin ta ɓoye acikin kayanta,wanka ta shiga tafito tayi sallah.
Tana idar da sallar ne tasamu natsuwa,dan haka kwalliya ta tsara a fuskarta,kamar amarya,sannan ta ɗauki wasu arnayan english wears ta saka,iya kyau tayi kyau,amman babu me kallonta ya ɗauka tasan abinda ake kira musulunci.
Tana ɗaura takalmi feefee tashigo ɗakin,cike da mamaki take kallon salmar.
Miƙewa salma tayi tacewa feefee.
"ƙawa zani shopping ne pls,kimana girki kan nadawo".
"salma kina nufin wai dawannan shigar zaki fita?anya kinada hankali ƙuwa,wannan shigar mijinki ne yafi cancanta daya ganta fa,wlh inkina yin haka bazaki samu miji nagari dazece yana sonkiba".
"Aniyarki tabiki wlh,miji nagari kuma har se nazaɓa,sabida yadda kike taƙama ke virgin ce haka nima,da ace iskanci nakeyi sekice bazan samu ba,nifa feefee kinfara wuce gona da iri,wanne irin wulaƙanci ne wannan,nayi kwalliya ko ɗan cewa nayi kyau bakiyiba,amman kinzo kina cikamin kunne,da zancen banza,tonide daga yau karki sake yimin haka,jikinki ko jikina?".
Tana kaiwa nan tayi ficewarta tabar feefee atsaye kamar gunki.
Tana isa bakin titi ta fara sauya takunta,dama ga rigar datasa koya ta motsa cibiyarta na fitowa,daga saman wandin kuma jigidar dake jikinta itama tafito,tana tafiya kamar wata tarwaɗa.
Tana isowa bakin titin taja gefe ta tsaya,tana taunar cingum.
Wata venz 4matic ce ta faka agabanta,sannu a hankali glass din yasauka,wani mutumine aciki wanda a haife ya haifi salmar.
A zaton shi ba musulma bace dan haka da turanci yamata magana.
"sexy baby barka da yammaci"
Ɗago ido salma tayi ta haskeshi dasu,sannan tadan murmusa,tace.
"yauwa suger daddy"
amsar tata dariya tabashi,dan haka yace.
"in bazaki damuba muje in rage miki hanya mana"
Su salma abin nema ya samu amman dayake baby ce me class setace.
"Ayya nagode kawai nima nan daka ganni driver na nake jira".
Har ga Allah ya amince da batun nata,dan batayi kala da ƴar talakaba.
"ay daganinki nasan akwai dalilin dayasa kike tsaye anan,amman don Allah kishigo na rage miki hanya".
Dakyar de yasamu ta amince,koda zata shiga motar seda tayi wani juyi da mazaunanta sannan tashiga,wani miyau mutumin ya haɗiye ba shiri.
"Ni sunana Alhaji Adamu canji,ni maaikacine a CBN,ina zaune a Abuja ne,yanzu haka dakika ganni nazo wani meeting ne nan,kefa ya sunanki".
cikin salon ɗaukar hankali,tace.
"Sunana salma hadi medala,nazo nanne bautar ƙasa daga jihar kaduna".
"wow nice name,ashema ke musulmace?"
"sosai ni musulmace,ilove fation ne kawai shiyasa kaganni ahaka"
"thas good,ina kika nufa yanzu".
"zani shopping ne wlh kuma inason in sauya wayata ne,shiyasa kaganni nafito yanzu".
"Ok ba matsala bari nakaiki,ay kin cancanci amiki komai"
Wani haɗaɗɗen super market yakaita,nan tashiga jidar kaya,na kwalliya dana ci,bayan tagama da wannan fannin,sukaje ɓangaran wayoyi.
Alhajin dakanshi ya zaɓar mata,iphone7 da kuma samsung galaxy s6 edge,salma ware ido tayi kawai tana kallon ikon Allah koda sukaje gurin biyan kuɗi akayi total ɗin duka kayan data siya da wayoyin,dubu ɗari huɗu da hamsin.
numfashinta be kusa ɗaukewaba seda taga Alhaji Adamu yaciro kuɗin yabiya cash.
Kasa magana tayi,binsa kawai take da ido har aka gama zuba kayan a leda,aka kaimusu mota,ko tafiya ta kasa yi dan haka Alhaji adamu,hannunsa yasa yakamo ƙugunta،salma kasa hanashi taɓata tayi,ahaka yajata suka bi hanyar fita,suna kaiwa bakin ƙofa suka ci karo da doctor najeeb shima yazo shopping.
Ba ƙaramin mamaki yayi da ganin yarinyar ahakaba,kallon tsana yabita dashi,yayinda itama,ta wurga mishi nata.
Duk da bata ji daɗin ganinta da yayi rungume ajikin Alhajiba amman bazata bari ya gane hakanba.
Shigewa ciki yayi sukuma suka fice zuwa mota.
0 comments:
Post a Comment