Da sunan Allah Mai rahama Mai Jin 'kai.
Dan saurayine Wanda ashekaru bazai gazama Sha takwas zuwa Sha tara ba, zaune yake kan kujera 'yar tsugonno a wani madai-daicin tsakar gida gabansa Kuma 'yan kwarorin kwanonin wanke-wanke ne Wanda basu wuce kwara 7 ba, sai 'yan cokulla Wanda suma ba yawane dasuba,
Hannunsa cikin robar ruwan dayazubama clean Yana wankewa sannan ya dauraye cikin wani ruwan daban kafin yakife cikin kwandon da aka tanada dan kife kwanonin.
Sallamar Mai gidan tasashi juyowa daga aikin dayake tare da amsa sallamar, fauziyya dake daki tafito cikin farin ciki Jin dawowar mijin nata, sanye take cikin Riga da siket na atamfa Wanda kalar atamfar da dinkin ba karamin fiddo da kyawunta sukayiba, cikin murna da farinciki ta rungume Salim "sannu da zuwa hubby," tafada cikin nushadi yakara rungumeta tare da kissing kumatunta, yace "Nagode My wife"
Jikkar hannunsa ta karba sannan takama hannunsa suka nufi d'aki.
Sani Dake zaune Yana kallonsu duk abunda sukeyi kan idonshi, wani kululun bakinciki yazo yatokaremashi wuya,
Sauri yayi yanufi kofar fita daga gidan, zauren gidan yayi zaman dirshan yakalli kudu maso arewa yafara rizgar kuka kamar Wanda aka aikoma da sakon mutuwar uwarshi da ubanshi da duka danginshi lokaci daya.
Shikau abunda Salim da fauziyya keyi Yana bala'in batamashi rai, Yana masifar kishin fauziyya har cikin ranshi, baya kaunar yaga salim yayimata koda wani kallo Wanda yadanganci soyayya barantana Kuma akai ga yataba jikinta jiyake kamar ya had'iyi Zuciya yamutu,
Dafe kanshi yayi da hannu biyu dayakejin Yana barazanar tarwatsewa gida biyu saboda azabar ciwon dayake mashi,
Dagewa yayi iya karfinsa yabuga kanshi ga bango, Dan jiyakema kamar ba cikin hayyacinsa yakeba.
"Sani... Sani... Kusan sau ukku fauziyya tana kwalamashi Kira Amma bai amsaba, hanyar zauren tanufo tana Kara kwalamashi kira, sai lokacin yajiyota da sauri yanufi cikin gidan Yana goge hawayen dake kan fuskarsa, "gani aunty" yafada tare da saddar dakanshi kasa Dan bayaso su had'a ido da ita.
Kallonshi fauziyya tayi sannan tace "sani Wai meke damunka, kuka kayine?"
Saurin 'kakaro murmurshi yayi Wanda Bai Kai cikina yace 'yace "a'a aunty
Ruwan clean ne danake wanke-wanke- ya fallasamin a Ido shine nadan fita kofar gida ko yadan saki"
Tunda yafara magana fauziyya ke kallonshi tace "dama aikenka zanyi can shagon ka amsoma hubby lemu"
Wani kududun bakin ciki yaji yazo yamakalemashi a makoshi Dan jin fauziyya takira Salim da sunanda yatasana a rayuwarshi wato *Hubby* wlh dayanada Hali daya hanata fad'ar wannan sunan.
'karbar kudin lemun yayi Yana niyyar fita, fauziyya ta kira sunanshi "sani"
Juyowa yayi yakuramata mayun idanunshi masu kama dana mujiya.
"Meya sameka agoshi Naga ya kumbura" tajeho mashi tambayar idanunta akanshi.
"Uhe eh uhum dama lokacin da ruwan kumfa clean yashigarmin a ido Ina niyyar fita shine na buge da bango"
"To Allah ya sauwa'ke sani karika kula Dan Allah idan kana aiki, kullum Kai idan zakayi wanke-wanke sai ruwan clean yashigarma a ido kamar wani 'karamin yaro, kayi sauri Dan Allah kakawomin lemun hubby zaici abinci Yana bukatar lemu a kusa"
"To" yafad'a tare da ficewa daga gidan zuciyarshi na tafarfasa jiyake kamar yaje yarufe Salim da duka Dan duk fadi'n Duniya ba Wanda yatsana kamar Salim.
Bayan mintina dabasu wuce glbakwaiba sani yadawo da Leda d'auke da lemun Coca-Cola, sallama yaketa kwadawa Amma shiru ba amsa haka yasa yanufi dakin Kai tsaye ya yaye labulen, fauziyya ce zaune tad'an kwanto jikin Salim tanata zubamashi shagwaba, shikuma Yana aikin rarrashi kamar wata yarinyar goye,
Karar fad'uwar ledar lemunda sani yasawo yadawo dasu cikin hayyacinsu, saurin rabata da jikishi Salim yayi tareda bin sani da kallo Wanda shima su yake kallo zuciyarsa na tafarfasa, sunkai tsawon minti 2 haka kafin sani yasaki kabulen dakin da karfi yayi baya, yanufi wurin wanke-wankensa hawayenda ke makale a idonshi suka cigaba da zubowa, ahaka ya karasa wanke-wanken ranar ko abinci bai tsaya karba ba yabar gidan.
*Tofah Reader's Ina fatan kungane waye sani Kuma waye Salim, Kuma wane matsayi fauziyya take wurin Salim, kubiyoni Dan Jin yanda labarin zai kasance, idan Naga yasamu karbuwa gareku zancigaba idan Kuma Naga akasin haka zakuji shiru kawai*
Wannan somun tabine daga cikin labarin *ALMAJIRIN GIDANA*
[8/20, 7:23 AM] Hayat: đ *ALMAJIRIN GIDANA* đ¤Śđť♀
*Writing By*
*Zee Elkasim (Mmn khady)* đĽ°
*Daga Marubuciyar* đ
*Siyasa ko soyayya*
*Alhini*
*Gidan Asali*
*Halin Girma*
*Autar Hajiya*
*Zanen Zuciya*
*Yarinyar Baba*
*Auren tagwaye*
*Wata Uwar mijin*
*Ke Duniya*
And now đđť
*ALMAJIRIN GIDANA* đ
Page 2
~Tun daga page din farko Naga yanda aketa comment Kai naji dadi nagode masoyana ku kasance da wannan 'kagaggen labarin nawa domin amfana da abubuwan daya kunsa, fad'akarwa ilmantarwa gami da nishadantarwa~
Fauziyya da kanta tazo ta d'auki lemun da sani yasaki a kasa ta kalli Salim tace "hubby narasa mai ke damun sani, ace kusan tsawon wata biyu Yana aiki a gidannan amma kullum sai ruwan omon wanke-wanke yashigar masa a Ido, yaufa baka ganiba wlh yanda idanunsa sukayi ja, Kuma yaje fita ya buge da bango, bakaga yanda goshinsa ya kumbura ba, yanzu Kuma ji yanda ya saki lemunnan akasa ya gudu kamar Wanda yaga wani abun firgici"
Tunda fauziyya tafara magana salim ke kallonta saida takai Aya sannan yace "ba dole ruwan omo yashigar masa idoba, aikine yakeyi Wanda bana jinsinshiba, kyau ace namiji kamar sani Yana kasuwa Yana neman na kanshi, ga sana'a nan kala-kala ko dako yakeyi ai yafi zama cikin gidan mutane, ace mutum Yana namiji Amma yazuna yanama mata bauta"
"Haba hubby yanzu idan sani yabar gidannan yazanyi da aikace-aikacen dayake tayani, Kuma idan ba saniba banida d'an aike kariga kasani, ni wlh baniso kana maganar barin sani a gidannan, nan dinma meya nema yarasa, cidasha da sutura ba Wanda bamuyimashi, Kuma duk wata idan ka amshi salary kana bashi 500 meya manta"
Murmushi Salim yayi tare da shafa gefen fuskarta yace "to ai shikenan amaryata Kuma Uwar gidana, yanda kekeso haka za'ayi"
"Nagode hubby, bari nahad'ama ruwan wanka tunda kagama cin abincin". Daukar kular abincin tayi da plate din takai kitchen, robar abincin sani tagani ajiye yanda tazubashi ba'a taba ba, cike da mamaki tace "Sani baici abincinba, ko lafiya oho, hmm nasan zai dawo"
Inda ruwan gidan yake tanufa tacika bucket takai kewaye, sannan takoma d'aki tace "Hubby ga ruwan wankan can nahad'ama"
"To my wife sai muje ki tayani wankan dan kinsan yau na matukar kwaso gajiya"
Murmushi tayi tace "to muje Mana, ai sainayima wankanma duka dan banason abunda zai wahalarmin da Hubby na"
Da sallama Sani yashigo gidan saboda wata mashahuriyar yunwa data addabeshi, da dai baiyi niyyar Kara dawowa gidanba a yau saboda bayason ganin bakinciki, saikuma yaga yunwa na niyyar illatashi, Kuma yasan yanzu Salim yabar gidan saboda haka yadawo gidan cike da farinciki Dan yasan zasusha fira shida fauziyya saboda idan Salim bayanan shine abokin firarta, Kuma idan suna fira jiyake kamar ansakashi aljanna saboda tsananin farinciki har mantawa yake da duk wani bakin cikin rayuwa.
Ganin yayi sallama kusan sau 2 ba'a amsamashiba, sai karar ruwa yakeji a toilet ya tabbatarma kanshi da wanka takeyi, saboda haka ya nufi kitchen ya dauko robar abincinsa yafito da niyyar zuwa inda yasaba zama a gidan, dai-dai lokacin Kuma Salim yafito daga toilet shida fauziyya suduka d'aure da towel jikinsu da lema Alamar wanka sukayi, juyowa sani yayi Aiko idonshi ya sauka kan Fauziyya dake Daure da 'karamin towel Wanda baigama rufe cinyoyintaba, a matukar firgice Sani kebinsu da kallo da mayun idanunshi, Nan take zuciyarshi tarinka harbawa da sauri da sauri, wani abu mai Kama da madaci yataso yazo ya tokaremashi makoshi, miyan bakinshi gabaki daya yakafe, kanshi yarinka juyamashi duk illahirin jikinshi kyarma yake, hakan yayi sannadiyyar fad'uwar robar abincin dake hannunshi wacce Nan take ta tarwatse abincin Kuma ya zube a kasa.
Salim na ganin haka yakama Hannun fauziyya, baizame ko'ina da itaba sai bedroom ya zunar da ita gefen gado, sannan yasako jallabiya yadawo tsakar gidan da niyyar yayima sani rashin mutunci, dan baiji dadin yanda yaga sani ya zubama Fauziyya manyan idanunshi ba, Amma Yana fitowa sai ya iske Sanin baya tsakar gidan, har kofar gida ya leka amma baiga komai Kama dashiba.
Dawowa Salim yayi ranshi a matukar bace ya iske Fauziyya zaune inda ya zaunar da ita ta buga uban tagumi, kallonta yayi yace "Fauziyya korar sani zanyi daga gidannan".
Arazane ta juyo ta kalleshi "hubby, saboda me? Me yayimaka? Haba hubby gaskiya baikamata ka koreshiba Babu laifin zaune babu na tsaye"
"Dole yabar gidannan tunda ba gidan ubanshi bane"
"Haba Salim akanme zaka dage akan sai sani yabar gidannan Alhalin bayimaka wani laifiba" tafad'a a hasale, "Ni gaskiya hubby bazan yarda ka koreshiba, idan Kuma yazama dole saika koreshi to kagayamin laifin dayayima"
Banza Salim yayi da ita yacigaba da shirinsa, kananun Kaya yasanya wandon jeans sai shirt polo milk colour, kafarsa sanye da bakaken takalmi ba karamin kyau yayiba, makullin mashin dinsa roba-roba ya dauka, yafita yabar gidan batareda yakara Yima Fauziyya wata maganaba.
Jiki a sanyaye Fauziyya ta d'auko wani sassayan lotion akan mirror tashafama jikinta, sannan tashafa farar fowder da man lebe, wasu riga da siket ta sanya na English wears marassa nauyi sannan tabi jikinta da wani sassayan turare mai dadin kamshi, dan ana zafi garin dukda marece yayi,
Ba karamin kyau Fauziyya tayiba, dukda kasancewarta gwana a fagen makeup Amma yau batayiba, hakama kayan data sanya ba karamar muhimmiyar rawa suka takaba wurin fitoda illahirin surar jikinta, tabarma ta dauko da pillow ta shimfida tsakar gidan cikin inuwa ta kishingida duk jikinta a sanyaye.
Sani kuwa tun lokacin dayabar gidan da gudun tsiya yakoma gidansu, inda suke kwana shida 'yan'uwanshi Almajirai, kan sosashiyar katifarshi ya kwanta ya kalli rufin dakin idanunshi na zubar da zafafan hawaye, ya Lula cikin kololuwar tunani, ba abunda ke addabar zuciyarshi sai tsantsar So da 'Kaunar Fauziyya, sannan uwa uba Zazzafan kishinta dayake, baya 'kaunar yaganta tareda Salim, bayaso yaga Salim yakai hannunshi a jikin Fauziyya jiyake kamar yasa takobi mai kaifin bala'i ya yanke hannunshi, saigashi yau yayi mugun gani Wai Fauziyya ce take wanka tare da Salim a toilet daya da soso daya da sabulu daya acikin kuma bokiti daya.
_Zee Elkaseem (Mmn khady) ce_ đĽ°
[8/20, 7:24 AM] Hayat: đ *ALMAJIRIN GIDANA* đ¤Śđť♀
*Writing By*
*Zee Elkasim (Mmn khady)* đĽ°
*Daga Marubuciyar* đ
*Siyasa ko soyayya*
*Alhini*
*Gidan Asali*
*Halin Girma*
*Autar Hajiya*
*Zanen Zuciya*
*Yarinyar Baba*
*Auren tagwaye*
*Wata Uwar mijin*
*Ke Duniya*
And now đđť
*ALMAJIRIN GIDANA* đ
*Duk wacce tasan tana karanta wannan novel d'in tayi joining a wannan group din, Dan girman Allah idan ba karantawa kikeba Kuma baki comment kada kishiga Dan kokin shiga zan fiddaki, Kuma bamu bukatar kome sai Wanda yashafi book din idan Kuma bashi zai kawokiba plz kada kishiga*
https://chat.whatsapp.com/BbHG7kh5gZGDPuqodYetSO
Page 3
Hawaye yacigaba da zarya kan fusakarshi wani na bin wani, tashi yayi zaune daga kwancen dayake yace "Fauziyya Ina sonki Ina kaunarki Kuma kota wane hali sai kinzama mallakina"
"Sani... Sani... Sani Wai mike damunka? Tun d'azu nake Nan inatama magana Amma kaki kulani sai wasu surutai kakeyi Wanda ni banganeba....
Firgigi sani yadawo daga dogon tunanin dayake dakuma surutan dayaketa zubawa mararsa kan gado,
Kallon Basiru yayi sannan ya goge hawayen dake kan fusakarshi yace "uhum ba kome Basiru"
Dafa kafadarshi Basiru yayi yace "tayaya zan yarda da ba abunda ke damunka bayan ga damuwa Nan 'karara tare dakai, waini sani yaushe kafara boyemin abubuwan dasuka shafeka, nalura dakai tun ranar da kafara aiki gidan Fauziyya duk gaba daya kabi ka canja, narasa gane kanka"
Murmushi Sani yayi Wanda bai Kai cikiba, sannan yatashi ya dauki buta yazaga kewaye yafito yayi Alwala yayi sallar la'asar,
Wata tsohuwar jaka gana yajawo yafara fiddo kayan sakawarshi a ciki, wani wandon jeans ya jawo da wata Riga mai kalar wandon ya kallesu kamar Yana nazarin wani abu a jikin kayan minti 2 kafin yayi wani irin wurgi da kayan zuciyarshi na tafarfasa Natsaneka Salim natsaneka bana sonka natsani duk wani abu daya fito daga hannunka"
Wasu riga da wando na yadi ya sanya kalar ruwan hoda, dukda kayan sunji jiki duk sun kod'e Amma wanke suke fess, dan ba laifi sani Yanada tsafta bama zaka kalleshi kakirashi almajiri ba.
Basiru ne yasake zuwa inda yake yace "Ina zuwa Kuma mutumina?"
Kallonshi sani yayi yace inafa zanje inda yawuce gidan Fauziyya, kasan duk garinnan banida inda yawuce nan"
Murmushi Basiru yayi yace "adaibi sannu da shigema gidan mutane kada asamu matsala, danni wlh bama zan iya aiki gidajeba na kwammace naje kasuwa nayi dako na samu na kashewa"
Rab'awa sani yayi ta gefenshi ya wuce, batare daya cemashi kome ba, shima Basiru bayanshi yabi domin tafiya sabgar gabanshi, idonshine ya sauka kan kayanda Sani ya jefar, kwalama Sanin Kira yayi Wanda harya Kai bakin kofa ya juyo,
Basiru yace "wannan ba kayanka bane anan?"
"Nawane banaso ka d'auka idan kanaso" baijira abunda Basiru zaiceba yafice daga gidan.
Kai tsaye gidan Fauziyya yanufa da sallama yashiga gidan, Fauziyya dake kwance a inuwa ta amsa sallamar tare da tashi zaune "a'a sani Kaine?"
"Nine aunty fauzy, sannu da hutawa" "yauwa sani, Amma sani Wai yau mike damunkane d'azu kawanibi ka firgice?"
"Bakome aunty ni kaina d'azu narasa miye matslata, Amma yanzu Kinga lafiya Lau nakejina, ga wani farinciki da annashuwa danakeji yanda kikasan anyi mani bushara da gidan Aljannah"
"Kai sani baka gajiya, waini sani Ina abokinka?"
"Wane kike nufi Basiru ko Tukur,?
Dariya Fausiyya tayi sosai Dan tunowa datayi da drama da akasha tsakanin sani da tukur din Wanda ada shine almajirinta, kafin sanin.
"Aunty Fausiyya ai bakisan wani abuba, Tukur fa yanzu yazama abunda yazama dan naji labarin Wai kwaya yake siyarwa"
"Kai Dan Allah" Fauziyya tafad'a tare da dafe kirjinta Alamar maganar ta razanata.
"Wlh kuwa aunty, Dan kafinma yatafi wlh sata yafarayi, tunda yayo sata shagon wani mutum aka kamashi akayimashi mugun duka yakara gaba, sai kwanaki nakejin labarin Yana siyo kwaya Yana siyarwa"
"Oh kace Allah ya tarfama garina nono daya rabani dashi"
"Kedai Bari aunty Fausiyya..
Sallamar Sadiya kawar Fauziyya ce ta yankemasu firar dasukeyi, da murna Fauziyya ta tarbeta tanayimata oyoyo.
Kallon ta Sadiya tayi sannan ta kalli sani dake zaune kallo daya zakayimashi kasan Yana cikin annashuwa da farinciki.
"Shigo 'kawata" tafad'a tana nufar d'aki, Sadiya tabita tana waiwaye tana Kara kallon Sani,
Zama tayi kan kujera Fauziyya takwomata ruwa Mai sanyi daga cikin karamin fridge dinda ke dakin.
Kallon Fauziyya Sadiya tayi tace "kawata wanene wancan?"
Kallonta Fauziyya tayi tace *ALMAJIRIN GIDANA NE* dafe kirji Sadiya tayi tace "wancen katon shine Almajirinki Fauziyya, ko tsoro bakiji"
"Tsoron me zanji, iyakarsa shara da wanke-wanke sai aike idan yakama"
"Amma nikam gani nake kamar akwai ganganci d'aukar wannan katon amatsayin Almajiri, yo Fauziyya duka dame Kika girmeshi, Ni wlh danashigo zauren gidan naji firarku wlh nad'aukama Salim dinne, ke fauza ko rantsuwa nayi banzanyi kaffaraba nasan baki girmi wancan yaronba"
"Hmm ke nidai banison inskanci, wani Zaki dauka Salim ne, a'a kin manta, yanzu dai ya school?"
"Lpy lao wlh, nasameku lpy?" "Lpy lao" haka sukacigaba da firar yaushe gamo, sani Kuma ganin Fauziyya tayi bakuwa maimakon yatafi Amma saiya gyara zama Yana jiran tafiyarta sudasa firarsu, Dan ko Yana barin gidan sai Salim yadawo Shima badan ranshi yasoba.
*Mmn khady ce* đĽ°
[8/20, 7:24 AM] Hayat: đ *ALMAJIRIN GIDANA* đ¤Śđť♀
*Writing By*
*Zee Elkasim (Mmn khady)* đĽ°
*Daga Marubuciyar* đ
*Siyasa ko soyayya*
*Alhini*
*Gidan Asali*
*Halin Girma*
*Autar Hajiya*
*Zanen Zuciya*
*Yarinyar Baba*
*Auren tagwaye*
*Wata Uwar mijin*
*Ke Duniya*
And now đđť
*ALMAJIRIN GIDANA* đ
Page 4.
No editing đ¤Ş
*Ina mi'ka sa'kon gaisuwata ga masoya Allah bar 'kauna, inajin dadin yanda kuke nuna tsantsar kauna ga littafin, gaisuwata gareku 'yan group d'in ALMAJIRIN GIDANA Fans group, iya wuya ana tare* đđđ
Akwana atashi, hausawa sukace asarar mai rai, yau kimanin shekara guda kenan Sani Yana aiki gidan Fauziyya.
Ba'kin kishin da sani keyi akan Fauziyya kuwa sai abunda yayi gaba, soyayyarta ta 'kara girma acikin zuciyarshi, Amma yanzu yafara iya takunsa, Dan Yana kauda Ido akanta duk lokacinda Salim yake gida, wani lokacima baya zama gidan saiya tabbatar Salim din bayanan.
Yauma kamar kullum, da sallama Sani yashigo gidan Fauziyya ta amsamashi, wuri yasamu ya zauna itma Fauziyya tabarma ta shimfida nan tsakar gidan suka shiga firar Duniya,
Hannu sani yasaka cikin Aljihu ya fiddo waya kirar Vivo Yar makimanciya yace "Aunty Fauziyya kitayani murna nayi waya"
Dariya Fausiyya tayi har dimple d'inta ya bayyana, Wanda ba abunda ke Kara burge sani kamar dariyarta, kuramata Ido yayi Yana kissima abubuwa dayawa azuciyarshi dangane da tsantsar kyau da Allah yayima Fauziyya.
"Kai-kai-kai..... Ah Sani congrats Ashe dai kaji shawarar dana baka" tafad'a tana karbar wayar daga hannunshi, "Kai ammafa wayar yayi kyau, nawa kenan kasiya?"
"Wlh dubu hudu nasiyeta Aunty tayi tsada ko,"
'Dan Hararshi tayi tare da tamke fuska tace "kaifa Sani dadina dakai son banzar bala'i, ai danma tana vivo Amma yaushe zaka samu waya mai kyan wannan a dubu hudu, kaga yanzu nahuta tunda kayi waya idan Ina nemanka basaina tura an nemomin kaiba, Kuma Koda na aikeke kasuwa saboda mantuwa ko tambaya ga waya, Bari na d'auko wayata Nima saika sakamin no dinka"
Tunda tafara magani sani Bai d'auke idanunshi akantaba, harta tashi tanufi d'aki nanma bayanta yabi da kallo, hips d'inta na d'aya daga cikin abunda ke 'kara d'aukarmashi hankali, ga Kuma uwa uba yanda idan tana tafiya mazunanta ke juyawa, sanifa yashiga wani yanayi.
Dawowa tayi hannunta d'auke da wayarta Samsung Galaxy S7, tace amshe sakamin number dinka Nima Bari insama tawa sai kayi serving, anan sukayi musayar number,
Sani yace yauwa aunty Bari ind'anyi turi, Dan tun jiya nasayi memori 8 GB, Dariya Fausiyya tayi tace "Sanifa anzama babban yaro, ga waya anyi gashi cikin kwanakinnan naga sai wani d'aukar wanka kakeyi Wai miye sirrin? Kodai kafara zuwa zance ne banida labari"
"Ai Nan wurinki nake zuwa zancen Fauziyya ke nakeso, ke nake 'kauna, sha'awarki kullum da ita nake kwana da ita nake tashi" yafad'a a zuciyarshi, amma a zahiri murmushi kawai yayi tare da Sosa kwantacciyar sumarshi ta fulanin Asali.
Fina finai, da wa'koki video da audio sani yashiga turawa daga wayar Fauziyya zuwa wayarshi, maimakin yatsaya anan, sai yashiga tura picture din Fauziyya batare data saniba.
Da sallama matashiyar matar tashigo gidan, cikin farinciki Fauziyya ta amsa tare da girmamawa tamike tana fad'in "Mama sannu da zuwa"
Wani irin kallo shekeke matar tabita dashi batare data amsa sannu da zuwar datakemata ba,
Sani dake zaune kallon matar yayi shima yace "Ina wuni" shima wani matsiyacin kallo ta watsamashi tace "kaikuma waye, daga Ina haka zakazo gidan mutane ka zuna"
Fauziyya tabata amsa "Mama *ALMAJIRIN GIDANA ne*"
"Ke Fauziyya kigayamin gaskiya idan kinfara tara maza agidan d'ana, wannan gardin zakicemani Almajirinkine, Shi Salim din Yana Ina aka kawo wannan 'katon amatsayin Almajiri"
Sani dai sadda Kai yayi 'kasa Dan bayada bakin magana,
Matar tacigaba da masifa, "kekuma Fauziyya dama wurinki nazo, "kinbi kin mallakemin d'a kinhanashi sa'kat kin hanashi sukuni, gaki kekuma tunda ya aureki yau kimanin shekara 2 kenan Amma ko batan wata baki tabayiba, to wlh da sakal, danni ba abunda nafiso irin Inga jikikina, Salim Shi d'aya na Haifa amma Ina fatan yazama natara gari guda asanadiyyarshi, saboda haka idan kinsan baki Haihuwa, Kara ki Kama gabanki dan baki daya daga cikin jerin mata hud'u danake fata Salim ya aura"
Jin mamar Salim ta ambaci mata hud'u yasa Fauziyya saurin dagowa arazane ta kalleta, idanunta sharkaf da hawaye.
Sani kuwa jiyake kamar yakama mamar Salim yayita duka dan tabatama Fauziyya rai, ba abunda yatsana arayuwa irin yaga bacin ranta.
Juyawa mama tayi danufi barin gidan, harta Kai bakin 'kofa tajuyo tace "idan Salim din yadawo kice inason ganinshi" batajira amsa daga Fauziyya ba tafice daga gidan afusace.
"Dan Allah aunty Fauzy kiyi hakuri ki daina kuka, Haihuwa ai Allah ke badawa ga Wanda yaso, Kuma shike hanama bawansa badan baya sonshiba, kiyi hakuri ki daina kuka"..
Cikin muryar kuka Fauziyya tace "Sani Kaine kasan wannan, Amma dayawa mutane jahilci na rufe masu ido suna mantadawa da cewa komefa nufin Allah ne"
"Shikenan aunty fauza kada kisama kanki damuwa akan wannan abun daya faru inshaAllah kome zai wuce"
'karar mashin d'in Salim suakaji a zuare, yasa sani yace "aunty ni zan wuce sai Allah ya kaimu" dan lokacin anata kiraye-kirayen magrib.
"To sani gobe kazo da wuri dan Allah kayi aikinka da wuri dan Inaso infita unguwa"
"To" kawai yace yasa Kai yafita dan bayaso Salim yashigo yanacikin gidan saboda kada yaga kayan takaici,
A zaure suka had'e da Salim, sani yayimashi sannu da zuwa sannan yawuce, shikuma Salim yashigo gidan.
.
sallama Salim din yayi tare da shigowa gidan, Fauziyya a inda take zaune ko motsawa batayiba ta amsa sallamar ciki-ciki,
Mamakine yakama Salim ganin yau Fauziyya batayimashi irin tarbar data Saba yimashiba, da sauri yanufi inda take ya ajiye jikkar hannunsa ya tallafota yahad'ata da jikinshi, haba my wife yau laifin menayi aka kasa tarbata kamar yanda aka Saba" kuka Fauziyya tafashe dashi ta kwace jikinta daga rungumar da Salim yayimata tashige d'aki.
Sani dake la6e a zaure Yana lekensu wani irin farincikine ya cika zuciyarshi ganin Fauziyya tayi fushi sa Salim.
Rarrashinta Salim yashigayi dukda baisan laifin dayayimataba, Bata kulashiba sai kuka datakeyi, da kyar yasamu ta tsaigaita kukan sannan tacemashi "Mama tazo d'azu Kuma tace tananemanka"
Ajiyar Zuciya Salim yayi, yanzu yagano inda matsalar take, wato duk yanda yake tausasa mama yana mata nasiha ashe batajiba saida tazo tagayama Fauziyya ba dad'i, dafe kanshi yayi yace "oh my God, Fauziyya kiyi hakuri nasan mamace ta batamaki Rai Dan Allah kiyi hakuri kada kisa damuwa aranki, zanje Kiran datakemin inshaAllah Kuma zannunamata rashin dacewar abunda tayimaki.
Haka Salim yacigaba da rarrashinta har aka Kira sallar isha'i tare sukafita suka d'auro Al'wala, Salim ma agida yayi sallar, ranar haka suka kwana sukuku, Dan duk yanda Salim yaso yaja Fauziyya da magana amma taki sakin jikinta dashi, dan bakaramin batamata rai mamar Salim tayimataba, kanta taji Yana saramata, tashi tayi ta dauko paracetamol ta balli guda 2 tawatsa baki tabi da ruwa, sannan tanufi wadrope ta d'auko kayan bacci wata rigace maisharara marar nauyi da siririn hannu ta sanya, sannan tahaye gado jikinta duk yamata nauyi.
[8/20, 7:24 AM] Hayat: đ *ALMAJIRIN GIDANA* đ¤Śđť♀
*Writing By*
*Zee Elkasim (Mmn khady)* đĽ°
*Daga Marubuciyar* đ
*Siyasa ko soyayya*
*Alhini*
*Gidan Asali*
*Halin Girma*
*Autar Hajiya*
*Zanen Zuciya*
*Yarinyar Baba*
*Auren tagwaye*
*Wata Uwar mijin*
*Ke Duniya*
And now đđť
*ALMAJIRIN GIDANA* đ
Page 5
*Gareki SAMIRA YUSUF wannan shafin nakine, naji dadi sosai akan yanda Kika fahimce yanda labarina yake dakuma sakon danakeson isarwa garemu mata, Kai harma da mazajenmu, Ina fata wannan labari nawa yazama IZNAH agaremu baki daya*
Washe gari
Misalin karfe 9 na safiya Salim yayi sallama gidan mamarshi, bayan sun gaisa yasamu wuri ya zauna cikin d'aya daga cikin kujerun dake dakin, Bayan sun gaisa Salim yace "Mama jiya Dana dawo gida Fauziyya tace kina nemana,"
D'aure fuska tayi kamar bata taba dariyaba, tace "eh nemanka nakeyi dan in gayamaka kasan yanda zakayi da wannan juyar matar taka wacce bata Haihuwa, nifa jikoki nakeso ingani dagwai-dagwai bi da bi amma har yanzu shiru, ba wani labari, to wlh bazan lamuntaba dole kasan nayi"
"Haba mama, dan Allah kidaina irin wannan maganar, baikamata ace kina irin wannan tunanin ba, duka shekararmu nawa da aure ne, da har za'afara Kiran Fauziyya juya, duka-duka shekara biyu ne, wasufa har shekara goma sukeyi basu Haihuba, Kuma bayan tsawon wannan shekarun idan sunada rabo saikiga sun haihu....
"Dakata Salim" tafad'a cikin d'aga murya da 6acin rai "Nizaka gayama duka shekararku biyu da aure, to a wannan shekaru biyun idanda ba juya bace da yanzu tayi haramar aje yaro na biyu, amma idayake juya ce Bata Haihuwa har yanzu shiru kakeji,
duk tabi ta kanainayeka ta mallakeka sai abunda tace kakeyi, bakason laifinta ko kad'an, shiyasa wlh tunda kazomin da maganar aurenta raina baisoba, dan dai idan Allah ya kaddara ba yanda mutum zaiyi"
"Nagodema Allah Hajiya dakikasan Aurena da Fauziyya Allah ne ya kaddara, to hakama Haihuwa tsakanina da ita idan Allah ya kaddara zamuyi kome dad'ewa....
"Kai dakata, banison zancen banza zancen wofi, tashi kabani wuri shashasha Wanda baisan inda aka dosaba, to kasani nabaku wata ukku muddin banji wani bayaniba 'karshen zamanka yazo da Fauziyya, dan wlh saika saketa, ehe"
Tana gama fadin haka tashige bedroom tabarshi zaune, yama rasa miye zeyi,
Haka yatashi jiki duk ba kwari yabar gidan.
Koda yaje wurin aiki kasa aiwatar da kome yayi, duk abun duniya yabi ya hademashi, ga Fauziyya taki sakin jikinta dashi tunda Mama tazo gidan, gashi Kuma mama tazomashi dawata irin magana marar makama, "wohoho" yafad'a tare da dafe kanshi.
Bangaren Fauziyya kuwa tunda tatashi takejin jikinta ba dadi, bakinta yayimata d'aci, ga tashin Zuciya dake addabarta,
Sani Kuma tunda yazo yafara wanke-wanke har yakusa gamawa Amma Fauziyya bata leko tsakar gidanba,
Ba karamar damuwa yashigaba, Dan rashin ganin Fauziyya ba 'karamin tashin hankali bane taredashi,
Tunani yacigaba dayi "ko lafiya, kokuwa dai tun abunda mamar Salim tayimata jiyane har yanzu bata huceba,, wata zuciyar tace "kashiga dakin kadubata Mana, wani bangaren Kuma na zuciyarshi yace "a'a kada kayi haka tunda dai matar nan har yanzu bata baka fuskar shigarmata dakiba.
Yana cikin wannan tunanin yaga Fauziyya tafito daga d'akinta da sauri, bakin maguji kusada inda Sani ke wanke-wanke ta durkusa tafara kwaraya amai, "subhanallah" sani yafada "Aunty dama bakida lafiya ne? Kasa ko d'aga Ido tayi ta kalli sanin kakarin amai kawai takeyi, tun tana amayo abunda taci harya kasance bakome cikinta dukta amayar amma dukda haka kakarin amai kawai takeyi, cikin 'kan'kanin lokaci dukta galabaita,
Sani Kuma rasa yanda zeyi da'ita yayi, shiba abun yatabataba, gashi Kuma tayi kwance wurin datayi aman, da alama batada 'karfin dazata tashi tabar gun.
Hankalin sani inyayi dubu yatashi, jiyake dayanada hali daya cirema Fauziyya ciwon dake damunta,
Can murya 'kasa-'kasa Fauziyya tace "sani kaduba falo kan kujera wayata nanan ka d'aukomin"
Da sauri Sani yanufi d'akin Fauziyya, bakin kofa yacire takalminshi sannan yashiga d'akin tsayawa yayi yana 'karema d'akin kallo dan duk yanda yake da gidan zai iya k'irga shigarshi dakin Fauziyya, hannu yasa ya d'auki wayar harzai fita ya kaimata wayar, kamar Wanda yayi mantuwar wani muhimmin abu saiya koma d'akin, bedroom yanufa Kai tsaye, yafara bin ko'ina na d'akin da kallo, idanunshi suka sauka kan rigar baccin Fauziyya dake yashe kan gado, data cire dasafe saboda rashin karfin jiki yasa Bata d'aukeba, hannu yasa ya d'auko rigar ya d'orata akan fuskarshi Yana sha'kar 'kamshin turarenta, yakai kimanin minti 2 ahaka kafin ya sauketa zuwa kirjinshi ya rungumeta Yana fad'in "Ina sonki Fauziyya Ina 'kaunarki, Ina fatan kasancewa dake har 'karshen rayuwata, Fauziyya nayimaki Al'kawarin sai kinzama mallakina kome wuya kome tsanani, ko ana ha maza ha mata saina mallakeka, haka yari'ka surutai kamar wani zautacce maganar Salim ce tadawo dashi hayyacinshi, zaro Ido yayi cikin tsanain tashin hankali ya juyo.
đ
*Tofah reader's Anya sani Bai d'ebo da zafiba kuwa*
*Hmm muje dai zuwa ai Hausawa sunce, KOWA YA DEBO DA ZAFI BAKINSA* đ¤
[8/20, 7:24 AM] Hayat: đ *ALMAJIRIN GIDANA* đ¤Śđť♀
*Writing By*
*Zee Elkasim (Mmn khady)* đĽ°
*Daga Marubuciyar* đ
*Siyasa ko soyayya*
*Alhini*
*Gidan Asali*
*Halin Girma*
*Autar Hajiya*
*Zanen Zuciya*
*Yarinyar Baba*
*Auren tagwaye*
*Wata Uwar mijin*
*Ke Duniya*
And now đđť
*ALMAJIRIN GIDANA* đ
Page 6
*JINJINA GAREKU YAN GROUP DIN ALMAJIRIN GIDANA NOVEL INA YINKU IRIN SOSAI DINNAN, IYA WUYA ANA TARE*
Saurin fitowa yayi daga d'aki Yana fad'in "Aunty ga wayar" juyowa Salim yayi ya kalleshi a kidemi Dan hankalinshi yagama tashi da ganin yanda ya iske Fauziyyar, karbar wayar yayi daga Hannunshi yace "Sani yi sauri kashiga gidan sister Firdausi ka gayamata Fauziyya batada lpy tazo Dan Allah ta dubata"
Da gudu sani yabar gidan zuwa gidan Firdausin, wata nurse ce makociyar Fauziyya duka gida ukku ne tsakaninsu.
Salim kuwa sani natafiya yataimakama Fauziyya ta wanke jikinta sannan yakaikta d'aki yadawo ya wanke inda tayi amai,
Mintuna dabasu wuce bakwaiba Firdausi tashigo gidan itada Sani, Kai tsaye d'akin Fauziyya tanufa kwance ta isketa tana numfashi sama sama ga wani 'katon bargo data rufa dashi, dan wani masifaffen sanyi takeji sakamakon Zazzafan zazzabin daya saukomata.
Dubata fidausi tayi tare dayimata wasu tambayoyi,
fitsari tasa Fauziyyar tayi tayimata PT sanan tadawo d'akin fuskarta d'auke da murmushi, ta dauko biro da wani takarda tafara rubutu, bayan ta kammala tajuyo ta kalli Salim tace "congratulations Salim, kakusa zama Daddy, Dan Fauziyya tana d'auke da ciki"
Zaman dauri sani yayi a inda yake, sakamakon abunda kunnuwansa suka jiyomashi, Dan tunda fiddusi tashigo yake sauraren abunda ke wakana dangane da rashin lafiyar Fauziyya, inda akayi rashin sa'a yafad'a kan wata roba wacce Nan take ta tarwatse, daga d'aki faiddusi taleko ta window Jin karar abu na fashewa, gagnin sani tayi zaune duk ya had'a gumi Kuma yakasa tashi daga kan robar daya fadamawa dukda kwalleliyar ranar dake wurin, saboda tsananin firgicin dayake ciki.
Salim kuwa cike da farinciki yad'aga hannu sama Yana godema Allah, koba kome Allah yakawomashi 'karshen rigimar mamarshi, yauga Fauziyya d'auke da cikinshi.
Takarda fiddausi tami'kamashi tace "ayi hanzari asawo wannan magungunan tafara sha inshaAllah zata samu sauki"
Karbar takardar yayi yafito tsakar gidan da niyyar yaba sani yaje chemist yasiyo maganin danshi bayaso yayi nesa da Fauziyya saboda yanda dukta galabaita.
Inda sani yafad'i har yanzu Nan yake baitashiba, kallonshi Salim yayi yace "Kai sani, wai kai wane irin sakarai ne?"
Tashi yayi da kyar yace "wlh fad'uwarce najita shiyasa nakasa tashi, ya jikin auntyn? Yatambaya Yana gyara tsayuwarshi,
"Da sauki" Salim yafad'a, sannan yace "anshi wannan kaje chemist kasiyo wannan magungunan" yafada Yana mikamashi takarda da kudi,
Amsa sani yayi yafita daga gidan Yana layi kamar wani mashayi, haka yafara tafiya Yana tangadi kamar Wanda yasha yabugu, duk tsabar damuwace, Shi yanzu takaicinshi dayane ba biyuba, yanda zaiyi yaraba Fauziyya da cikin jikinta.
Gindin wata bushiya ya zauna Yana tunanin yanzu miye abunyi, "dole insan yanda zanyi da cikinnan yazama dole yazube, taya zanyi in zubar mata dashi?" Tamabayar dayayima kanshi kenan wacce yakasa bama kanshi amsarta.
Yakai kimanin mituna goma awurin kafin dubara tafad'o mashi, da sauri yatashi fuskarshi d'auke da murmurshi Dan tunowa dayayi da chemist din kolo, wani chemist ne na wani Christan Mai suna kolo, Wanda Almajirai masu shaye-shaye ke siyen kayan maye wurinsa, can yanufa Yana zuwa yayi sa'a bakowa a chemist din sai kolo Shi d'aya, bayan sun gaisa yace kolo dama wannan magungunan zaka bani yafad'a tare da mi'kamshi takardar, amsa yayi sannan yafara d'auko maganin, saida yagama hadawa yamikamashi yace "kud'inka 450"
Sani yace "inada bukatar maganin zubar da ciki, Mai 'karfi nakeso Sha yanzu magani yanzu, dariya kolo yayi yace "abokina ya akayi kabari haka yafaru, akwai Allura Wanda akeyi idan kana tare da girl bazata samu cikiba zaku iyayin shekara ukku babu wata matsala"
Dariya sani yayi yace "afara bani na zubarwa zanzo na karbi Allurar idan angama wannan"
Daukomashi kwayar maganin yayi kwara 2 cikin takarda yace "kaga wannan tanasha aikin gama yagama"
Dariya sani yayi sannan yabashi kud'i ya karb'i maganin yawuce.
Da sallama yashiga gidan, Kai tsaye d'akin Fauziyya yanufa daga bakin 'kofa yatsaya yace ga maganin" Salim yace shigo mana" daga labulen d'akin yayi yashiga, Fauziyyar na kwance tadora kanta kan cinyar sani, duk tabi tawani shagwabe.
Kallonta sani yayi cike da takaici jiyake kamar ya d'auke Fauziyya daga jikin Salim, azuciyarshi yace "Dani kk dace Fauziyya"
Sallamar maman Salim tasa yayi saurin fitowa daga d'akin, cikin zumud'i da fara'a da farinciki take magana, "Kai naji dadin wannan Albishir naji dad'i sosai Nima zansamu jika, sannu kinji sannu Allah raba lpy" tafad'a tana kallon Fauziyya wacce lokaci d'aya dukta kod'e ta kara fari.
*WAYE SANI*
Sani mutumin wani 'kauyene can kusada 'kasar Niger, irin Wanda basu Niger Basu Nageria, amma a ka'ida kauyensu Yana cikin yankin Nigeria, sani bafulatanine gaba da baya, farine Amma ba fayauba irin fari mai duhu-duhu, Yanada dogon hanci irinna fulani, bakinshi madai-daici sai manya idanunshi, sumar kanshi kwance take luf kamar ta yayan turawa, yataso cikin so da kulawar iyayenshi kasancewarshi shi dayane namiji a gidansu sauran 'yan'uwanshi duk matane, yayi makarantar primary Kuma yafara sencondary yana aji biyu ne suka billo dawata d'abi'a shida wani abokinshi dan 'kauyensu, ta tare yara a hanya suna tabamasu nono, kullum sai akai kararsu wurin iayayensu yafi a k'irga, ganin haka yasa iayeyen nasu suka yanke shawarar kaisu Almajiranci Kuma gari daban daban.
Yayinda akayo garin Katsina da sani, shikuma abokinshi mu'azu aka kaishi Kano,
Tun saukar sani a makarantarsu yahad'u da tukur Wanda suka kulla abota, Amma sai abotar tasu bata d'oreba kasancewar tukur Yana shaye-shaye, Kuma shine yakema Fauziyya aiki, suna zuwa gidan tare da sani lokaci zuwa lokaci, daga karshe tukur yafara sarin kayan maye Yana siyarwa ganin Yana Kama kud'i yasa yari'ka Sha ruwan tsuntsaye a gidan Fauziyya yau idan yaje gobe baya zuwa, Wanda Fauziyya da kanta tagaji da hakan tanemi da sani yacigaba dayimata aiki shikuma tukur takoreshi, sanadin haka tahada fada tsakanin Sani da tukur Wanda saida aka Kai ruwa rana kafin tukur yahakura yabar Sani yacigaba dayima Fauziyya aiki, shima saida malaminsu yasa baki, *wannan kenan*
*WACECE FAUZIYYA*
Fauziyya shehu shine asalin saunanta, mahifinta Alhj shehu Yanada rufin asiri Dan baya cikin jerin talakawa sannan Kuma baza'a kirashi hamshakin mai kudiba, Yanada mata daya Hajiya A'isha, yayansu biyar mata ukku maza 2, Fauziyya itace auta shiyasa duka gidan aka dauki son Duniya aka doramata yayunta duka hudun sunyi aure, Allah ya azurta Yan gidansu da wani irin kyau mai d'aukar hankali, Wanda yayyenta mata duka suke auren hamshakan masu kud'i ammafa dukansu sunada kishiyoyi saboda duk Wanda suka aura sunada mata.
Lokakacinda Fauziyya tataso cikin tsanain farinjini, masu kudine keta kawomata hari, yayinda Salim Shi kadaine saurayi cikin manemanta Kuma shine talaka yasa taji ba Wanda ya kwantamata saishi, ba yanda iyayenta basuyiba akan tarabu dashi ta auri wani Alhaji amma takiya, haka suka hakura suka amince mata saboda sunason duk abunda takeso.
Shikuwa Salim lokacinda yatunkari mahaifiyarshi da maganar auren Fauziyya kin amincewa tayi Dan tana ganin kamar yadebota da zafi duba da mutanen unguwar keyi Yan gidansu Fauziyya Basu aure sai masu kud'i, da kyar da sud'in goshi mahaifiyar Salim ta amince da aurenshi da Fauziyya shima saida kanin babanshi yasanya baki, kasancewar baban Salim yarasu tun salim Yana J's 2,
Mahaifiyarshice tacigaba da d'awainiya dashi da hidimar karatunshi haryayi degree inda yasamu aikin koyarwa a makarntar secondary ta maza anan cikin garin Katsina.
*Andawo labari NEXT PAGE* đ¤Ş
[8/20, 7:24 AM] Hayat: đ *ALMAJIRIN GIDANA* đ¤Śđť♀
*Writing By*
*Zee Elkasim (Mmn khady)* đĽ°
*Daga Marubuciyar* đ
*Siyasa ko soyayya*
*Alhini*
*Gidan Asali*
*Halin Girma*
*Autar Hajiya*
*Zanen Zuciya*
*Yarinyar Baba*
*Auren tagwaye*
*Wata Uwar mijin*
*Ke Duniya*
And now đđť
*ALMAJIRIN GIDANA* đ
Page 7
Mamar Salim tunda tazo taketa Nan nan da Fauziyya ko kuda bataso yatabata, sai jeramata sannu takeyi, "oh Allah mai iko yau nice zanga jikana a duniya"
"inshaAllah Mama ai dama haka Al'amarin ubangiji yake, mahakurci mawadaci, duk Wanda yayi hakuri tokuwa zaiga ribar hakuri" Salim yafad'a Yana kallon Mama.
Kirarye-kirayen sallar azahar yasa Salim d'auko maganin yace "Fauziyya yakamata kisha maganinnan" kad'a Kai Fauziyya tayi kamar mai shirin kuka Dan tatsani magani a rayuwarta, Koda tana gida sunsan halinta idan ita dakanta zata dauki magani tasha to kuwa sai dai ciwon ya kasheta.
Rarrashinta Salim yafarayi akan tasha maganin soyake yafita masallaci kada lokacin sallah ya wuce, juya Kai tafarayi Alamar bataso.
Duk abunnan mama na kallonsu tasowa tayi tazauna kusada Fauziyya tadafa kafad'arta "haba kekuwa ki daure Kisha maganin mana ko bakiso kiji 'karfin jikinki? Kallon Salim tayi tace "taci abincine?" Girgiza Kai Salim yayi yace "a'a tun dai Karin safe Kuma tayi amai"
"yauga sakarci, ashe dama ahaka kake kokarin duramata magani batare dataci komeba, bakasan hakan matsala bane, dakanta tashiga kitchen tadafa ruwan zafi Wanda yaji kayan kamshi citta da karamfani, sannan tahadamata tea kakkaura, dakanta takawomata tarinka rarrashinta hartasha tea din sannan ta d'aukomata magungunan tarika ballowa tana bata, Fauziyya dole tasa take 'karbar maganin tanasha Dan bazata iya musu da mamar Salim dinba, maganin sani ta d'auko kwara 2 cikin ledarsa tace "shikuma wannan kwara 2 ne duka Zaki shanyeshi" fiddoshi tayi tamikamata shima karba Fauziyya tayi ta shanye, sannan takoma ta kwanta dukda yanzu tanajin 'karfi-karfi ajikinta tunda tasha tea d'in, dama hada yunwa ke Kara galaibatar da ita.
Zama mamar Salim tayi tana kallon Fauziyya tana tausayamata ganin yanda ta canja lokaci guda tayi fari fat, gawata Uwar rama datayi, dama abu gamai d'an jiki.
Dawowar Salim daga masallaci yasa mama tayi haramar tafiya gida,
"Salim nizan wuce Allah sauwake sainasake zagayowa kuma"
"To mama mungode" tare suka fita zuren gidan yarakota, juyowa tayi ta kalleshi tace "Salim karika kula da yarinyarnan sosai, kaga yanzu tana bukatar kulawa, Kuma....
Wata irin 'kara Fauziyya tayi sakamakon wani balai'in ciwo dataji mararta nayi, "Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, take mai-maitawa da karfi, hakan yasa Salim saurin shigowa gidan Mama ma biyo bayanshi tayi tana fad'in "lafiya miye ke faruwa" durkushe suka iske Fauziyya tsakiyar d'akin tanata murkususu bakinta kuwa sai maimaita salati takeyi, gawani uban gumi data had'a,
Akidime suka nufi wurinta har rige rigen kamata sukeyi suna tambayarta "miye ke damunki?" Cikinta tanunamasu tana magana da kyar "cikina zanmutu Salim, wayyo mutuwa zanyi"
Kamata Salim yayi yace "yi ha'kuri Fauziyya bari nakira Ahmad yazo da mota muje asibiti, wayarshi ya fiddo yakira abokinshi Ahmad yagayamashi halinda ake ciki, kafin yakatse Kiran yaji mama tabuga wani uban salati, dago idonshi yayi dan ganin meke faruwa, jini ne kebin 'kafar Fauziyya kamar me, "Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un" yafad'a.
Cikin tsananin kidemewa Mama tace "kayi sauri kakira Ahmad din ya taho da sauri muje asibiti banaso murasa wannan cikin"
Karar mota sukaji a 'kofar gidan tareda horn, kodajin haka suka gane Ahmad ne ya iso, Kama Fauziyya sukayi akasata a mota sai asibiti.
Binciken farko da'akayima Fauziyya aka tabbatarmasu da lalacewar cikin jikinta na kimanin wata biyu da sati d'aya.
Saboda haka wankin ciki akayimata aka Ida cire cikin, tareda rubutamata magunguna, aranar aka sallameta suka koma gida cike da bakinciki da takaicin rasa cikin.
Salim har saida ya matse Yan kwallah batareda Kowa yasaniba, dan ganin yanda tunda aka tabbatarmasu da zubewar cikin Hajiya tashiga damuwa, yanzu Kuma baisan kowace irin matsalace zata sake kunno kaiba, "Allah gamu gareka" yafad'a a bayyane.
Bayan tafiyar mamar Salim, kuka Fauziyya tafashe dashi tare da fad'awa jikin Salim tace "Hubby yanzu shikenan munrasa wannan Babyn, Ni kaina a yanzu inason Haihuwa, kaduba kaga cikine kawai akace inadashi amma tarai-raya ba wacce mama bata nunaminba, yanzu gashi yazube..... Kara fashewa tayi da kuka.
Har cikin ranshi yakejin kukanta, rarrashinta yakeyi shima kamar yatayata kukan yakeji, amma hakan baidace dashiba amatsayinshi na namiji "kiyi hakuri inshaAllah Allah dayabamu wannan shine zaikuma bamu wani, Kuma wannan d'in ba alkahiri bane agaremu shiyasa Allah yazubardashi, dan duk lokacinda zanyi addu'a nakan roki Allah idan zai azurtamu da haihuwa yabamu d'a ko d'iya wacce zata zama Alkhairi arayuwarmu"
Shiru sukayi suduka bakajin komai sai ajiyar zuciyarda Fauziyya keyi.
Bangaren sani kuwa duk abunda ke faruwa yasani, yatausayama Fauziyya matuka ganin yanda ta galabaita Dan kan idonshi akafito da ita zuwa asibiti, Yana labe Yana kallonsu.
Yanzuma zaune yake nesa kad'an da gidan, Salim yagani yafito daga gidan yanufi hanyar masallaci kasancewar anata kirarye-kirayen sallar isha'i,
Tagabanshi Salim yabi yawuce kasancewar duhun dake akwai unguwar yasa Salim baiga Saninba.
Saboda haka Yana ganin wucewar Salim yayi saurin shiga gidan sallama yayi kusan sau ukku amma shiru ba'a amsaba, d'akin yanufa Kai tsaye kwance ya tarar da Fauziyya kan kujera 3seater tana bacci.
Kallonta yayi zuciyarshi cike da tausayinta ganin yanda ta canja lokaci guda, tarame gawani irin haske data Kara, "kiyi hakuri Fauziyya bada son Raina na aikatamaki hakaba, zuciyata bazata iya jurar ganinki da cikin wani namijiba, cikina yakamata ki dauka ki haifamin baby ba wani ba, Ina jiranki Fauziyya zakizo gareni"
Cikin bacci Fauziyya kejin maganganun sani kamar tana mafarki, Motsawa tayi, da sauri Sani yafita daga d'akin, takalminshi ya dauka a hannu yayi saurin fita daga gidan, Yana fita Salim na dawowa.
Zaune Fauziyya tatashi tana nazarin abunda taji, anya ba aljanu ke garetaba Wanda suka zubarmata da ciki, Dan itadai taji kamar ana fad'in *dani kad'ai yadace ki haihu bada waniba* "Kai wannan shirmen mafarkine, Allah tsaremu da sharrin shaid'an" tafad'a sannan tayi addu'oi tashafe jikinta.
*Mmn khady ce* đđť
[8/20, 7:24 AM] Hayat: đ *ALMAJIRIN GIDANA* đ¤Śđť♀
*Writing By*
*Zee Elkasim (Mmn khady)* đĽ°
*Daga Marubuciyar* đ
*Siyasa ko soyayya*
*Alhini*
*Gidan Asali*
*Halin Girma*
*Autar Hajiya*
*Zanen Zuciya*
*Yarinyar Baba*
*Auren tagwaye*
*Wata Uwar mijin*
*Ke Duniya*
And now đđť
*ALMAJIRIN GIDANA* đ
Page 8
Ba karamin bakinciki da takaici Salim da Fauziyya sukayiba dangane da zubewar cikin, amma yazasuyi dole suka hakura suka fauwalama Allah kome, dama shine yabasu Kuma shine zai sake basu wani.
Sai dai wata matsalar tunda Fauziyya tayi barin take fama da wani irin ciwon mara Wanda tarasa gane kanshi, amma bata taba fadama kowaba, ko Salim bata gayamawaba,
WATA SABUWA INJI YAN CACA,
Fauziyya ce zaune tsakar gida itada Salim, sanye take cikin wasu Riga da wando na Pakistan Wanda sukayi matukar karbar jikinta, kamar wata India, Salim Kuma sanye da wando three-quarter da riga body hug, kayan sun karbi jikinsa sunyimashi kyau sosai, Salim kyakkyawa ne ajin farko, dogo ne, idanunsa makimanta, bakinsa dai-dai nashi, ga saje dayabi fuskarsa yayi kwance luf, ba baki bane sannan Kuma bazaka kirashi fariba, tsaka tsakiya yake,
Kwance yake yadora kanshi kan cinyar Fauziyya, hannuwanshi kan fuskarta Yana wasa da dogon gashinta wanda yakasance kwance bisa kafadunta, murmurshi suke sakarma junansu lokaci zuwa lokaci, da alama yanayin yayimasu dadi,
Gangarowa Salim yayi da hannunshi kan cikin Fauziyya yadafa cikin yace "Wai yaushe Zaki sake samun wani baby ne, yaufa shekara daya kenan da zubewar wancan cikin Amma har yanzu shiru, murmushi Fauziyya tayi tace "Hubby, miye kakeci nabaka nazuba, ai idan natashi yan biyu, zan haifama masu Kama dakai"
"A'a ninafiso ki haifamin masu Kama dake, dan yakansance ko ina na juya a gidannan inrika kallon kyawawan fuskoki, data matata data 'ya'yana"
"Hubby ai kafini kyau nesa bakusaba"
"Inji waye yafad'amaki, to bari kiji in fasalatamaki yanda kyawunki yake, Na farko Fauziyya ke farace, kinsan mutane nacewa (Kowa yayi fari yagama kyau), na biyu keba gajera bace, Kuma baza'a saki layin dogayeba, dai-dai dai-dai yanda nakeso haka kike, sannan kinada manyan idanuwa masu d'aukar hankali, da dogon hanci, sannan kinada karamin baki, da tattausan labba, hakoranki farare tas ajere ga siriryar wushirya data Kara kawatasu, kinsan abunda kekaramaki kyau kuwa?" Girgiza Kai Fauziyya tayi tana murmushi, "idan kikayi dariya dimple dinki ya bayyana bakaramin kyau yake karamakiba, ga diri jiki Allah ya horemaki, Fauziyya kinada manyan breast" hannu tasa tarufe fuskarta dan maganar tabata kunya, "sannan kinada hips mai d'aukar hankali, Kai Fauziyya kin had'u kinada kyau matu'ka, inafata ko alahira Allah yabarminke amatsayin mata agareni Fauziyya......
Mama sukagani tsaye akansu, kamar an jehota tashigo gidan bako sallama tanata cika tana batsewa, batako damu da yanayin data iskesuba "to shanyayye Wanda mace tagama dashi, yanzu Kai Salim ka rainani bakajin maganata, ban Isa inbaka umarni kabiba, naje gidansu Rabi'atu ance bakajeba, tokasani ko kaje kaganta ku dai-daita kanku ko kada kaje Babu fashi aurenka da ita, dole kakara aure Salim, wacce zata haihu nakeso ka auro ba wacce bata haihuwaba"
Hawaye yagama wanke fuskar Fauziyya, wasu nabin wasu, tashi tayi tashige d'aki tana cigaba da kuka,
"Ina Zaki munafuka, wato kinshige d'aki kinbar karya tayi haushinta ita d'aya"
Dawowa Fauziyya tayi ta durkusa gaban Mama inda shima Salim yake durkushe gabanta tanata zazzaga ruwan bala'i.
Bud'e jikka mama tayi taciro biro da takarda ta watsama Salim a fuska, "amshi maza maza karubuta takardar saki kaba wannan yarinyar takoma gidan ubanta, dan nakula itace kehanaka bin umarnina"
Sai yanzu Salim ya iya bud'e baki yayi magana "a'a mama wlh baruwan Fauziyya da maganar damukayi dake, asalima ita batasan da maganar ba, Dan Allah Mama kiyi hakuri kada kirabani da matata wlh Ina sonta bazan iya rayuwa batare da it....
Tassss kakeji mama ta d'auke Salim da mari, arazane Fauziyya tadago ta kalli mama zuciyarta na Kuna, "ni kakegayama kanason wannan kodaddiyar yarinyar, Salim yaushe tamaidaka marar kunya, to wlh kayi gaggawar sakinta tun muna shaida juna nidakai"
"Mama kisani saki ba'ayinshi batareda wani kwakkwaran daliliba,Kuma....
"Kwakkwaran dalili gashi a bayyane bata Haihuwa, akwai wani dalili Wanda yafi wannan" mamar tatari numfashinsa tafad'a.
"To kiyi hakuri mama bazan iya sakin Fauziyya ba, danba laifin datayimani, kuma saki abune wanda Allah ya halatta amma bayasonshi, kinga bai kamata mama da girmanki da iliminki kisani in aikata abunda Allah bayaso ba, sannan Kuma mama malam Mai ahlari yace Babu bi ga abunn halitta wurin sabama umarnin ubangiji, Kinga yanzu idan nabi umarninki na saki Fauziyya nasabama mahaliccina, hakan Kuma ba dai-dai bane"
Bala'i mama tacigaba dayi tana fad'in Salim Ni zakayima wa'azi, nicefa na haifeka amma kanemi kagayamin Allah da annabi, lallai nayarda Salim nangaba kila ko wurina bazata barka karika zuwaba, to kasani kwana biyu nabaka kada ka kuskura indawo in iske Fauziyya agidannan, idan Kuma ba hakaba rayuka zasu baci" tana gama fadi tafice daga gidan kamar zata tashi sama.
Kusan Karo tayi da Sani Wanda yadade a zaure Yana jiyo badakalar da akeyi acikin gidan, har azuciyarshi yakejin farin ciki, yana cewa "yauwa mama kisa Salim yasaki Fauziyya in aureta dan dani tadace badashiba"
Durkusawa sani yayi har kasa yagaida mamar Salim, ko kallonshi batayiba barantana ta amsa gaisuwarshi tawuce fuuuu, bin bayanta yayi da kallo yace "masifaffiya jarababba" shima baya yayi batareda yashiga gidanba, amma zuciyarshi cike da farinciki.
Tunda Mama tafita Salim yaketa faman rarrashin Fauziyya, "kiyi hakuri Fauziyya , Ina tare dake komi wuya kome tsanani, bazan rabu dakeba, Ina sonki, rungumeta yayi ajikinshi yakai bakinshi saitin kunnenta Yana radamata wasu kalamai Wanda nikaina bansan kome yake fadaba, kunsan tsakanin mata da miji sai Allah Nan Naga Fauziyya na dariya harda kyakyatawa, dama abunda Salim kenema kenan, daukarta yayi yanufi bedroom da ita, kan gado yayimasu masauki nanfa sukacigaba da farantama junansu rai har suka samu ladar aure.
Yau sati biyu kenan mamar Salim bata Kara zuwa gidanba, Fauziyya da Salim Kuma sun manta da Al'amarinta, Salim kuwa tsawon wannan lokacin baije gidan mamaba, dan gani yake zuwanshi dai-dai yake da tunoma mama abunda takeso ya aikata na rabuwa da Fauziyya.
DARE MAHUTAR BAWA
Kwance suke kan gado Salim yabi ya kan'kame Fauziyya a 'kirjinsa kamar Wanda akace za'a kwacemashi ita.
Can cikin bacci Fauziyya takejin ciwon ciki, ahankali tabud'e idonta ta saukesu kan agogon bangon d'akin 'karfe 12 da rabi na dare, batayi niyyar tada Salim ba Amma sai taji ciwon sai Kara gaba yakeyi har abun nanema ya girmi tunaninta.
Taba Salim tayi tace "hubby, hubby cikina" saurin bude Ido Salim yayi yace meyasameki, "cikina ke ciwo tafad'a tana ciccije baki saboda tsananin azabar ciwon dake addabarta.
"Subhanallah, yafad'a yatashi yacanja Kaya itama ya taimakamata ta canja yace Zaki iya hawa mashin muje asibiti?" d'agamashi kai tayi Alamar e,
Haka suka fito unguwar tsit bakowa, Salim yatada mashin Fauziyya tahau suka d'au hanyar zuwa asibiti Fauziyya na kwance bayan Salim, idan cikin ya murdamata saita kan'kameshi har suka iso wani asibitin kudi dake nan kusada unguwarsu,
Sunyi rashin sa'a babu likita sai wasu nurse suka karbeta sukayimata allurar rage radadin ciwon tareda sanyamata 'karin ruwa, cikin ikon Allah kuwa saitaji sauki,
Nan suka tabbatar ma Salim Akan dasafe likita zaidubata yaga miye matsalar.
Nurse dinne suka umarci Salim daya koma gida dasafe yadawo, sune zasu rika kula da Fauziyyar.
Washe gari 'karfe bakwai asibitin tayima Salim, dakinda Fauziyya take yanufa Kai tsaye, bacci ya iske tanayi, yayi kusan minti goma dashiga kafin tafarka bakinta d'auke da salati, taimakamata yayi tashiga toilet tayo Alwala tazo tayi sallah, sannan yatambayeta karfin jikinta "da sauki sosai tabashi amsa" wayarta yamik'amata "ga wayarki natahomaki da ita Koda Zaki nemi wani kokuma anemeki" "Nagode hubby" tafad'a tareda karbar wayar.
0 comments:
Post a Comment