Bayani yayima Salim yace "zamuyi wannan gwaje-gwaje dakuma hoton cikin nata inshaAllah zamu gano kowace irin matsalace ke damunta".
"To Doctor nagode" Salim yafad'a, Nan aka dibi jinin Fauziyya, dakuma fitsari sannan sukaje akayimata scanning,
Dawowa sukayi d'akin suka zauna suna jiran sakamako.
Bangaren sani Kuma, kamar yanda yasaba karfe takwas yake zuwa aikinsa gidan Fauziyya, sai dai yau Yana zuwa ya tararda 'kofar gidan gar'kame, tsayawa yayi Yana mamakin Ina Fauziyya tatafi, haka tunda safe, iya saninshi da tsawon zaman dayayi agidan Fauziyya bata tafiya unguwa bata gayamashiba Dan karyazo ya tarda batanan, "to ikon Allah" yafad'a afili, sannan yasamu wuri ya zauna kusada gidan zuciyarshi cike da tunani barkatai.
Wayarshi ya fiddo yafara shafawa, hotunan Fauziyya yake kallo daya bayan daya, kan wani hoto yazo Wanda Fauziyya tayi da mini skirt da wata Yar yaloluwar riga wacce ko hannuwan kirki batadu, ga wuyan rigar Mai fadine, shara-shara rigar take, hatta kalar bireziyar datasaka ana gani, Wanda Salim ne yayimata hoton da kanshi lokacinda tayi kwalliyar yake yaba kyanta, tanayimashi musu shine yace Bari yayimata hoto taga irin kyawun datayi shinefa akayi hoton, tagani Kuma saita barshi awarta har Sani yasamu damar turashi awayarta, Kuma duk cikin hotunanta yafison wannan, idan Yana kallonshi har wani nishadi yakeyi.
Zooming din hoton yarikayi Yana karema ko'ina najikinta kallo, Yana fad'in "Fauziyya Ina sonki Ina kaunarki, inason kasancewa da wannan kyakkyawar fuskar taki, da dirarriyar surar jikinki wacce bakowace mace Allah yayima irintaba, Fauziyya inaso inji fatar jikina ta hadu da lallausar fatar jikinki, Fauziyya kisoni Mana, kisoni yanda nake sonki....
Saurin fita yayi daga folder picture din Fauziyya, dan folder guda yayima hotunanta a wayarshi Wanda idan yashiga su kadai zaita gani.
Contact yashiga, sunan Fauziyya ya lalubo sannan ya danna Kira, riggin 2 Fauziyya tad'aga "Hello sani" "Hellow Aunty gani nazo gidanki na iske akulle lafiya kuwa?"
"Ba lafiya sani, Ina asibiti"
"Asibiti Kuma aunty,miya faru, waye bashida lafiya?"
"Wlh sani nice banida lpy asibiti muka kwana, tun jiya 'karfe 12 nadare mukataho" "innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, Aunty bakida lpy ashe, Kuna wane asibitin?" Nan Fauziyya tagayamashi asibitin dasuke, cikin zakuwa sani yace "ganinan zuwa aunty zanzo indubaki, wlh duk hankalina yatashi, bazansamu nutsuwaba sainaga yanayin jikin naki"
Murmushi Fauziyya tayi tace "kada kadamu sani nasamu sauki inasaranma asallameni anjima inshaAllah, yanzuma muna jiran results ne nawasu gwaje-gwaje da akayimin"
"To Aunty Allah baki lpy" "ameen" Fauziyya tace sannan takashe wayar, dukda talura da irin kallonda Salim kemata tunda tafara waya da sanin, hakan baisa ta daina wayarba saida suka gama, Salim kuwa duk yabi yahada girar sama data kasa, wani mugun takaici yakeji dangane da wayar da Fauziyya tayi da Sani, kawai kyaleta yayi Dan yasan yanzu yanamata magana zata 6ata rai, shikuma ba abunda yatsana irin fushinta, Kuma gashi batada lpy.
Sani kuwa suna gama waya da Fauziyya ya tsaida mashin yafadamashi asibitin dazai kaishi, cikin mintuna goma ya isa asibitin, batare da Bata lokaciba yagano d'akinda Fauziyya take dayake tagayamashi number d'akin,
Dai-dai Yana zuwa likita nashiga d'akin, lokacin Kuma maman Salim ta iso asibitin Dan itama waya Salim yayimata yagayamata rashin lafiyar Fauziyya, Kuma ya gayamata anasaran cikine gareta dukda basu tabbatarba, Amma sunanan suna jiran sakamkon gwajin da'akayi.
Da sallama mama tashiga, mamar Fauziyya ce ta amsa sallamar, wacce itama bata Dade dazuwa ba, waya sukayi da Fauziyyar tagayamata tana asibiti shine tazo, gaisawa sukayi itada mamar Salim ba yabo ba fallasa, sannan likitan ya gaishesu, ya kalli Salim yace "ga sakamakon gwaje-gwajen da'akayi Nan duka, yami'kama Salim yace kabiyoni office, sai nayima bayani ko" mamar Salim ce tayi karaf tace a'a likita kafad'a anan ai Babu bare anan cikinmu, nice mahaifiyarshi, wannan Kuma mahaifiyartace, tafad'a tana nuna maman Fauziyya.
Duk abunnan sani Yana bakin window d'akin Yana jiyo duk abunda ke faruwa, dan tunda yazo yaga mamar Salim da mamar Fauziyya, ga Kuma Salim adakin yasa baishigaba, dukda yasan bayada matsala dakowa acikinsu sai mamar Salim din.
Murmushi likita yayi yace, "amma kunsan wani abun Yana bukatar sirri" murmushi maman Fauziyya tayi tace "kada kadamu Doctor kafad'a kawai ai duk dayane"
Murmushi Salim yayi yace "fada kawai doctor Nan ai duk iyayenmu ne"
"Ok" doctor din yafad'a, sannan yafiddo wani farin siririn glass yasakama idonshi yace "sakamakon gwaje-gwajen damukayi mungano Fauziyya tasamu matsala amahifarta sakamakon amafani datayi da maganin zubar daciki ba bisa ka'ida ba Wanda hakanne ke haifarmata da ciwon mara lokaci zuwa lokaci....." wani mahaukacin fad'uwar gaba Fauziyya tayi tare da mi'kewa tsaye tadafe 'kirjinta Wanda zuciyrta ke barazanar fashewa saboda tsabar firgici, bangaren Salim ma hakane, kallon-kallo sukashigayi shida Fauziyya batareda kowannensu yayi maganaba, mamar Salim da mamar Fauziyya ma mi'kewa sukayi tsaye cike da mamakin abunda doctor din yafad'a, sani kuwa dayake la6e bayan window, gumine yagama jikeshi kamar Wanda aka shekama ruwa,
Shiru d'akin yayi bakajin 'karar kome saina fankar dake juyawa wacce duk tsananin juyawarta Bai hana Fauziyya hada zufa ba.
doctor ne yakatsemasu shirun dasukayi yace "Amma kada kudamu Naga kamar Kun daga hankalinku sosai matsalar ba Babba bace, ga magungunan Nan sai asiya indai takikaye tanasha kan ka'ida kome zai Koma normal inshaAllah Kuma inasaran tana gama shansu zata Kuma samun wani cikin da yardar Allah.
Wani irin kuka Mai 'karfine ya kwacema Fauziyya tace "karya kake Doctor, wlh 'karya kakeyi nibansha maganin zubar dacikiba akanme zansha maganin zubarda ciki, bayan abunda muka Dade muna nema kenan.... Nashiga ukku dama akwai likitoci masu jama mutum sharri, tokasani Allah bazai barkaba, inshaAllah sai kaga sakayya tun anan Duniya na wannan mummunan 'kazafin dakayim...."
"Dakata Fauziyya" Salim yafad'a cikin d'aga murya "Bakida wani sauran borin kunyar dazakiyimin, Ashe dama kece musabbabin zubewar farincikina, Kika zubarmin da gudan jinina, Fauziyya baki kyautaminba" ya karasa maganar murya 'kasa-'kasa hawaye nabin kumatunsa,
Maman Fauziyya tace "kada muyi saurin yarda da maganar da likitannan yafad'a...."
"Ke dakata malama Babu wata magana dazaki fad'a, ai tunda likita yace maganin zubar da ciki tasha, to wlh tasha, dan wlh kozaku hadiye kur'ani keda d'iyarki kice batasha maganin zubarda cikiba bazan taba yardaba, Allah yatona asirinku, dama ansaba zubarwa tun agida shine ananma za'ayi, idan banda dabbanci, waye kezubarda cikin Sunnah, ai idan kikaga anzubarda ciki tona rariya ne.
Juyawa tayi kan Salim "to kaikuma shanyayye, ga abunda nake gayamaka nan, nagayama wannan yarinyar Bata nemanka da Alkhairi, Dan duk Wanda bayason ganin kwanka duniya ai bamai kaunarka bane, saboda haka Ina umartarka daka rubuta takardar saki yanzu kabaiwa Fauziyya..."
Saurin dago Kai Salim yayi ya kalli mama, yace "haba mama plz, kibari abi kome ahankali mana"
Likita dai tunda suka Fara hayaniya yabar d'akin Dan Yanada aikin yi.
Sani Kuma Yana Nan dai inda yake yanaji Kuma Yana ganin duk takaddamar dake faruwa,
"Salim kasaketa nace, wane ahankali? Bawani ahanakli kasaketa kawai"
Tashi yayi yafita daga d'akin, sani naganin haka yaruga dagudu ya boye bayan wasu flowers,
Salim kuwa mashin dinsa yahau yabar asibitin Ranshi amatukar bace.
Mamar Salim kuwa, kallon mamar Fauziyya tayi tace "Bari kiji ingayamaki, daga Nan kiwuce da d'iyarki gidanki za'a aikomata da takardarta"
"Haba mamar Salim, idan Rai yabaci ai hankali baya gushewa, baikamata ace kinzama almakashin datse igiyar aure ba, Allah bayason haka, kibari abi kome a sannu har asamu a warware matsalar" mamar Fauziyya tafad'a asanyaye.
"Bawani ahanakli daza'abi, kitafi da mayaudariyar diyarki can ku karata". Tana gama fad'in haka itama tafita daga d'akin fuuuuu tanata bambamin fada.
Duk sani yaga fitowarsu jiki asanyaye yabar asibitin, duk yarasa abunda kemashi dadi, wani kunci da takaici suka ziyarci zuciyarshi Wanda shi kanshi baisan dalilin hakaba, farinciki yakamata yayi awannan lokacin ganin igiyar auren Fauziyya tana lilo, Amma Kuma saiya tsinci kanshi a Sabanin haka *to miye dalili,?*
*washh gajiyar sallah Bata sakeniba wlh, Ina typing Ina Gyan-gyadi*
.
*Mmn khady ce* 🤪
[8/20, 7:25 AM] Hayat: 🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* 🤦🏻♀
*Writing By*
*Zee Elkasim (Mmn khady)* 🥰
*Daga Marubuciyar* 📝
*Siyasa ko soyayya*
*Alhini*
*Gidan Asali*
*Halin Girma*
*Autar Hajiya*
*Zanen Zuciya*
*Yarinyar Baba*
*Auren tagwaye*
*Wata Uwar mijin*
*Ke Duniya*
And now 👇🏻
*ALMAJIRIN GIDANA* 🏠
Page 10
*JINJINA GAREKU YAN GROUP DIN ALMAJIRIN GIDANA NOVEL INA YINKU IRIN SOSAI DINNAN IYA WUYA ANA TARE, INA MATUKAR JIN DADIN YANDA KUKE COMMENT KUMA KUKE BANI KWARIN GWIWA AKAN WANNAN LITTAFIN NAWA*
*Dukda wasu shaid'an da hassada kan rufe ganinsu su gaza gane wannan k'yautatawar taki, hakan kan faru akan surukai, dangin miji, makwafta, ke harma daga cikin danginki, wani komi zaki masa bazai fasa aibantakiba, amma wlhy watan watarana koda bayan babukene saiya ambaceki koya tunaki cikin mutane Na kwarai, shiyyasa akace muguji ranar yabo.*
Tafiya sani yake Yana rangaji, duk abubuwa sun jagule mashi, wani bangaren na zuciyarshi Yana cikin farinciki saboda Yana ganin kome yazo cikin sauki, dan yasan yanzu lokacin rabuwar Salim da Fauziyya yayi, Abu dayane ke batamashi rai yakesashi takaici shine yanda Fauziyya tashiga cikin matsanancin tashin hankali, bayason ganin bacin ranta Koda dai-dai da second dayane.
Ahaka ya isa gidan kwanansu na Almajirai, gogaggiyar katifarka ya haye ya kwanta rigingine ya kurama rufin dakin ido, tunani barkatai acikin kwalwarshi.
Bangaren Fauziyya Kuma kuka takeyi sosai kamar ranta zai fita, tashin hankali tashi marar misaltuwa, wanda tunda take arayuwa ta Bata taba tunanin zata shiga irinsaba, kallin mamanta tayi da runannun idanuwata Wanda suka kumbura saboda tsabar kuka tace "nashiga ukku Mama, wlhy tallahi narantse harda Allah bansha maganin zubarda cikiba, kawai wannan likitan dai Yanada wata manufa tayimin wannan kazafin".
Hararta mamar tayi fuskarta a d'aure ba Alamar wasa, tace "wace manufa gareshi dazai kagamaki sharri, mutumin dabai sankiba bai taba ganinkiba miye ribarsa idan yajamaki sharri, Fauziyya inaso kigayamin gaskiya tsakaninki da Allah miye yafaru akan zubewar cikinnan naki?"
"Ki yarda dani mama, wlh bansan komeba akai, Allah shine shaidata" tafad'a tana Kara goge hawayen daketa zarya kan kumatunta.
"Fauziyya banason muyita jayayya dake, kigayamin gaskiya Dan insan yanda za'a shawo kan abun tun kafin yayi nisa"
"Mama kema kin yarda kenan, kin yarda da 'kazafin da'akayimin, shikenan mama, nasan duk yanda zanyi ba Wanda zai yarda dani tunda kema gashi kinki yarda dani, Allah kadaine shedata shine Kuma zai war-ware wannan matsalar"
Kallonta mama tayi, "Hmm Fauziyya kituna nice mahaifiyarki, bakida tamkarni duk fadi'n Duniya, idan bakigayaminba waye Zaki gayamawa, Amma tunda kinki gayamin gaskiya bari in kyaleki, saiki tashi mutafi gida ko, ai kinsan dai bazaki koma gidankiba kina ganin wannan Uwar mijin taki yanda take cika tana batsewa itada d'an nata, na tabbatar idan kikakoma gidan Salim kome na iya faruwa, Kara mutafi gida idan zuciyarshi tayi sanyi dakanshi zai nemeki"
"A'a mama kada muyi haka, idan Natafi gida kamar Karin wani laifine akan wannan da ake zargina akai, Kara inkoma gidan, zanyima Salim bayani Kuma nasan zai fahimceni"
"To naji, Amma yazakiyi da mahaifiyarshi?"
"Mama wannan ba matsala bace, indai Salim ya yarda ya amince ban aikata laifinda ake zarginaba wlh duk na mahaifiyarshi Mai saukine"
"To shikenan Allah rufa asiri" mama tafad'a duk itama tayi sukuku jitake kamar itama tafashe dakuka ganin yanda diyarta tashiga matsanancin tashin hankali "Ameen" Fauziyya tafad'a.
Tattara kaynsu sukayi suka fito harabar asibitin, saida suka Fara zuwa pharmacy suka siyo magungunan da aka rubutama Fauziyyar sannan suka tari adai-daita, har kofar gidan Fauziyya ya saukesu, saida mama tashigar da ita har gidan tayimata nasiha tare da kara bata hakuri akan duk abunda Salim din zaiyimata, Dan yanzu Yana cikin matsanancin bacin Rai zai iyayin kome, haka tatafi gidanta tabar Fauziyya cikin tsananin fargabar yanda zasu kwashe itada Salim.
Maman Fauziyya tana zuwa gida ta iske maigidan, sannu da dawowa yayimata sannan yatambayeta jikin Fauziyyar, Nan takwashe duk matsalar dake faruwa tagayamashi,
Yashiga cikin damuwa sosai dajin abunda yafaru, yace "wannan Al'amari akwai rud'ani aciki"
"Wlh kuwa, itadai tayi rantsuwa ta mai-maita akan batasha maganin zubarda cikiba"
"To Allah bayyana gaskiya" "ameen" mamar Fauziyya tafad'a.
Tun bayan tafiyar mama Fauziyya tarasa inda zata sanya kanta, tsananin fargaba da fad'uwar gaba.
Tun bayan azahar takesa ran shigowar Salim amma baidawoba, har la'asar shiru, ga wata irin yunwa dake addabarta, tashi tayi tanufi kitchen jikinta duk ba kwari, tattasai ta jajjaga tadora tukunya, indomie jallouf tadafa, da kwai mintuna Sha biyar tagama ta sauke, kula ta d'auko tana Shirin juyewa aciki tajiyo sallamar Sani, ansawa tayi tare dafitowa daga kitchen.
Murmushi ta kakaro Wanda Bai kai cikiba tace "a'a sani Kaine"
"Eh nine aunty, Ina wuni"
"Lpy lao"
"Yanzu daga asibiti nake akace an sallameku"
"Eh wlh tun wurin azahar muka dawo"
"Allah sarki, Aunty ya jikin"
"Da sauki sani"
"Allah karo sauki, Kinga kuwa yanda Kika rame aunty Kika Kara fari, gsky kinsha ciwo, waima miye ke damunki?"
"Wlh kuwa sani, zazzabi ne da Dan ciwon Kai, Amma yanzu na warke, bari inzubama indomie ce nadafa"
"Kai aunty daga dawowarki keda bakida lpy har Kika samu damar dafa wani abu"
"Dole indafa sani Dan nasan duk inda Salim yake idan yadawo zai nemi abinci, kasan baisaba cin abinci awajeba" d'aure fuska Sani yayi dan Fauziyya ta ambaci sunan Salim, cikin zuciyarshi yace "akwai sauran aiki agabana dole nasaka tsanar Salim azuciyarki Fauziyya, dan Salim yanzu banida matsala dashi tunda ya yarda da kece Kika zubar masa da ciki nasan dole son dayakemaki yaragu da kaso sittin bisa dari......
"Sani... Wai tunanin me kakeyi haka... Firgici ya kalleta hannunta d'auke da plate din indomie, yace "wlh aunty rashin lafiyar kice ke damuna shiyasa duk nashiga wani hali, Allah dai yakaramaki lpy aunty" "Ameen" tace ta ajiyeminshi plate din gabanshi Wanda bayada niyyar amsa tawuce d'aki.
Haka sani yafaracin indomie, Yana yaba iya girki irinna Fauziyya, Wanda komiye tadafa sai yayi dadi idan kanaci kamar kunneka zai tsinke.
Daga Nan inda yake yaketa faman zubama Fauziyya surutu amma yau bai samu yanda yakesoba Dan bata biyemashi kome yace batabashi wata cikakkiyar amsa daga eh sai a'a sune kawai abunda take iya fad'a.
Duk yanda sani yaso suyi fira da Fauziyya yau dai bai samuba, dan ita hankalinta nakan Salim Wanda tunda tadawo bai dawo gidanba gashi har andade dagama sallar isha'i.
Mi'kewa sani yayi yace aunty Bari inwuce saida safe, Allah sauwake "ameen" ta amsa daga cikin d'aki.
Sallama Salim yayi yashigo gidan, gaisheshi sani yayi sannan yayimashi sannu dazuwa, ba Wanda Salim din ya amsa sai wani mugun kallon tsana dayabi sanin dashi kafin yawuce d'akin.
Tabe baki Sani yayi yace "Nina kashe zomon Kuma nine zan ratayeshi, babu yanda zakayi dani Salim, danni yanzu jina nake dai-dai dakai indai akan Fauziyya ne,
da kamar ya labe yanda yasaba sai yaga koya labe bayada amafani dan bazai iya jiyo komeba tunda suna d'aki.
Dole yabar gidan zuciyarshi cike da farinciki da Kuma haushin Salim, da tsantsar kaunar Fauziyya.
*(Oh ni yasu, sani a daiji tsoron Allah)*
~kira garemu mata masu d'aukar 'katon Almajiri dasunan aiki wlh kalubale agaremu, Dan kwana ukku danaje gida, wani kanina yake bani labarin Almajirin gidan wata mata Wanda yayimasu asiri, saboda abun duniya, saboda haka wlh mata da maza magidanta kusan irin almajiran dazaku rika dauka sanamaku aiki agida, idanma yazama dole adauki alamajirin kenan, Amma idan sonsamune wlh sister kidaure kiyi aikinki da kanki zaifimaki kwanciyar hankali~
[8/23, 6:47 AM] Hayat: 🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* 🤦🏻♀
*Writing By*
*Zee Elkasim (Mmn khady)* 🥰
*Daga Marubuciyar* 📝
*Siyasa ko soyayya*
*Alhini*
*Gidan Asali*
*Halin Girma*
*Autar Hajiya*
*Zanen Zuciya*
*Yarinyar Baba*
*Auren tagwaye*
*Wata Uwar mijin*
*Ke Duniya*
And now 👇🏻
*ALMAJIRIN GIDANA* 🏠
Page 13
Kuka Fauziyya tafashe dashi, kafin tatashi tafito falo, ido biyu tayi da kud'i dakuma takardar da Salim ya ajiye kan kujera, ahankali ta Isa wurin tasa hannu ta d'auki takardar, budewa tayi tafara karantawa.
*Anyimani transfer wurin aiki anmaidani wani kauye, saboda haka natafi ga kudi nan nasan sun isheki har lokacinda zandawo, dan bazan rika dawowaba sai weekend* tana gama karanta takardar wasu sabbin hawaye suka ganagaro bisa kumatunta, cikin matsanancin bakin ciki tace "Haba Hubby ya isa haka, hukuncin ya isa, Koda dagaske na aikata wannan laifin ai hukuncin dakayimin ya hukuntani, yakamata kahakura mucigaba da rayuwarmu yanda muke ada.
Daukar kudin tayi ta had'a da takardar ta rike tacigaba da kuka, jitake kamar tahada kudin da takardar ta 'kone, sai-dai hakan ba dacewa bane.
Wayartace tayi Kara alamar shigowar Kira, amma ko kallon inda wayar take batayiba barantana ta dauka, harta tsinke aka Kara Kira nanma batada niyyar dagawa, saida aka Kuma Kira karo na ukku sannan tasa hannu ta dauka, sunan sani tagani akan wayar, saida tagoge hawayen idanunta ta dai-daita nutsuwarta sannan ta danna Alamar Kore tare da karawa a kunne, sani yace "Hello aunty ya kike"
"Lpy lao sani, ya safiyar"
"Safiya ba dad'i Aunty, kina ganin yanda oga Salim yayimin cin mutunci ya koreni batareda nayimashi wani laifiba"
"Kayi hakuri Sani, dama kobaka kiraba inada niyyar inkiraka, ingayama kadawo dan Allah kacigaba da aikinka kayi hakuri da abunda Hubby yayima"
Wani balai'itaccen kishine yatasoma sani jin fauziyya takira Salim da Hubby, jiyake kamar ya aza hannu bisa Kai yace wayyo, amma saiya daure yace "amma kina ganin hakan ba matsala, idan yaganni Kuma fa?"
"Kada kadamu baya garin, an canjamashi wurin aiki yanzu idan yatafi baya dawowa sai 'karshen mako"
Wani irin farincikine ya ziyarci zuciyar sani, dan yanzu yakeda damar tarewa gidan Fauziyya yaci karenshi ba babbaka.
Ko mintuna goma ba'a karaba dagama wayarsu saigashi yazo gidan, cikin farinciki yashiga kitchen ya tattaro kayan wanke-wanke cikin yan mintoci ya wankesu tass, dayake dama bawani yawane dasuba.
Yana gamawa Fauziyya tabashi kudin cefane yafita zuwa kasuwa, yana fita fauziyya tace "da Salim daya Kori sani nice zanrika fita inyo cefanen, Hmm ai maganar korar sanima daga nan gidanma bata tasoba".
Ruwan wanka tahada tashiga toilet tasheka wanka, tafito tashafa mai batawaniyi kwalliyaba dan rabonta da kwalliya tun kafin Salim yajuyamata baya, wasu riga da zani na atamfa ta sanya, tayi mamakin yanda tasanya rigar cikin sauki Kuma batareda tazage zif ba, rigarda ta masifar matsarta Amma yanzu jinta take wata sakwa-sakwa ajikinta, me hakan ke nufi ta tambayi kanta, Wanda bata bukatar abata amsa dan tasan amsar.
Kitchen tashiga ta silala indomie, tazuba nata a plate, sanan tajuyema sani nashi, tashige d'aki tana faraci sani yadawo, ajiye cefanen yayi kitchen sannan yashigo d'akin yami'kamata canjin, 'karba tayi sannan tace ya d'auki abincinsa nanan kitchen din.
"To" Sani yace, tareda sha'kar 'kamshin turarenta ya sauke wata ajiyar Zuciya, sannan yafita d'akin, abincin nashi yadauka sannan ya zauna yafaraci Yana zubama Fauziyya shegen surutun daya Saba, yauma dai bata biyemashiba dan batada kwanciyar hankalin zama tayi surutu dashi.
Haka Fauziyya ta zauna jugum cikin d'aki, shikuma Sani Yana tsakar gida, duk iya kokarinsa na ganin yaja Fauziyya da surutu abun yaci tura, haka yahakura yaja bakinshi yayi shiru, wayarshi ya fiddo yafara buga Game.
Sallamar Sadiya tasa yad'ago kanshi tareda amsamata sallamar, wani mugun kallo sady ta watsamashi dan taganeshi shine *ALMAJIRIN GIDAN* Fauzy, kenan har yanzu bata rabu dashiba dukda girman daya karayi, gaskiya Fauziyya tanada matsala.
Gaisheta Sani yayi, ko amsa gaisuwarshi batayiba tace "Fauziyya naciki?" "Tananan" yabata amsa ataikace.
Sallama tayi tareda daga labulen d'akin, zaune ta hango Fauziyya tsakiyar carpet ta buga uban tagumi da hannu biyu, kallo d'aya sady tayimata tagane tana cikin matsananciyar damuwa, ga wata irin rama datayi, duk tabi ta kod'e takara fari idanunta sunfad'a,
Juyowa Fauziyya tayi dan ganin waye tsaye bakin kofar, ido hud'u sukayi da sady tayi saurin tasowa tafad'a jikinta tasaki wani marayan kuka,
"Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, Fauziyya lafiya miye ke damunki, shiru Fauziyya tayi tacigaba da kuka, tambayar duniya sady tayimata amma taki bata amsa sai kuka dayaci 'karfinta, tun Sadiya na rarrashinta harta Fara bata haushi tace "wannan kuka Fauziyya bana lafiya bane, ko Salim ne yamutu? Girgiza mata Kai Sadiya tayi, to ko Mama da baba aka aikomaki basuda lpy? Nanma girgiza Kai Fauziyya tayi, "towai miye dan Allah, haba Fauziyya kefa ba karamar yarinya bace dazanta fama akanki, kigayamin abunda ke damunki idan inada maganin abun zanyimaki, idan Wanda zanbaki shawarane inbaki, idan Kuma yafi 'karfina intayaki da addu'a" goge hawayen fuskarta tafarayi Wanda basuda niyyar tsayawa, sannan ta zauna kan kujera sady ma zama tayi kusa da ita tace Ina jinki 'kawata gayamin damuwarki.
Goge hawaye Fauziyya tayi tafara gayama Sadiya duk abunda ke faruwa tsakaninta da mamar Salim dakuma cikin datasamu da yanda yazube, da rashin lafiyar datayi likita ya tabbatarmasu musabbabin rashin lafiyar Wai akan tasha maganin zubarda cikine Wanda ita batasan da wannan zancenba, dakuma yanda Salim yajuyamata baya, ko magana bata had'asu yanzu sai dai yarubutamata ya ajiye,
Goge hawaye Fauziyya tayi tace "yanzuma maganar damuke yau yayi tafiya wani kauye, Wanda akayimashi transfer daga wurin aikinshi, amma banci arzikin dazai gayaminba sai dai yarubutamin ya ajiye, Kuma bazai dawoba sai weekend, Kinga takardar daya rubuta"
Amsar takardar sady tayi ta karanta, wata irin ajiyar Zuciya ta sauke sannan tamaida dubanta ga Fauziyya tace "kawata ki gayamin tsakaninki da Allah kece Kika zubar masa da ciki"
"Haba sady kinsanni kinsan halina, kinsan abunda zan iya aikatawa da Wanda bazan iya aikatawaba, tun muna yara muke tare ba abunda ke rabamu nidake sai bacci, yakamata ace Koda wani kikaji yafad'i wannan maganar kizama mai bada kyakkyawar sheda akaina"
Dafa kafadarta Sadiya tayi tace "na yarda dake kawata dari bisa dari, amma wannan al'amarin akwai rikitarwa acikinsa"
Shuru sukayi suduka, kowace da abunda take ayyanawa aranta.
Wani munafikin murmushi Sani yayi, dan yaji duk abubuwan da Sadiya da Fauziyya suka tattauna dukda yasan abubuwa da dama afirar tasu, Amma yasamu Karin haske sosai, Kuma yanzu burinshi yakusa cika Yana gab da mallakar Fauziyya.
Sadiya ce takatse shirun tace "Fauziyya inaga yakamata su mama Susan da wannan maganar, sai asamu iyayenshi Salim din ayi magana inaga haka kad'ai shine solution, kawai ki shirya kije gida ki gayamasu"
"Kina ganin hakan ba matsala"
"Babu wata matsala inshaAllah"
"To nagode 'kawata, amma zanbari saiya dawo sai inje yanda za'ayi maganar yana gari" "eh haka yakamata, Ni bari inwuce dama hanyace tabiyo dani wlh da kamar kada inshigo, saikuma naji kamar ana ingizoni ashe rabon inzo inji abu marar dadi"
"Hmm kedai Bari kawata wlh ina cikin matsananciyar damuwa"
"Aiba saikin fadaba Fauziyya, dan duk wanda yasanki ada yaganki yanzu yasan akwai matsala, kinga yanda kikayi wata muguwar rama"
"Koni nasan narame wlh"
"To Allah ya kyauta" Sadiya tafad'a tare da fitowa daga d'akin tasanya takalminta, idanunta kan Sani wata irin muguwar tsana takemashi Wanda ita kanta idan za'a tsareta tafad'i dalili batadashi.
Rakota Fauziyya tayi har zaure, kallonta sady tayi tace "Fauziyya dama har yanzu akwai *ALMAJIRI GIDANKI*? murmushi Fauziyya tayi tace "Wai Sani, dama sani ai yananan, yaufa Salim saboda ya kuntatamin har korarshi yayi"
Sadiya tace "shine Kuma yadawo saboda tsabar rashin Zuciya"
Fauziyya tace "nice nace yadawo saboda idan yatafi waye zaiyimani aikin dayakemin, maganar yo cefane, ko nice zanrika fita dakaina Ina siyowa"
"Hmm kawata kidaiyi tunani mai kyau, wlh zama da Almajiri ba karamin hadari bane Koda kuwa yarone, barantana Kuma wannan kasurgumin 'katon, yazo yayimaka zaune cikin gida, wlh akwai matsala"
"Bawata matsala kawata, sani bayada matsala ko kad'an" Fauziyya tafad'a tana murmushi.
_niko nace sani kau shikeda manyan matsaloli, bama matsala dayaba_ 😡
Da haka sukayi sallama Sadiya tatafi, Fauziyya takoma ciki,
Tunda tagayama Sadiya matsalarta yau saitaji kamar an saukemata wasu manyan Kaya data dade tana dakonsu akanta, saitaji duk wani 'kunci da damuwa dake cikin zuciyarta yaragu da kaso sittin bisa dari.
Mmn khady ce 👌🏻
[8/24, 9:29 AM] Hayat: 🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* 🤦🏻♀
*Writing By*
*Zee Elkasim (Mmn khady)* 🥰
*Daga Marubuciyar* 📝
*Siyasa ko soyayya*
*Alhini*
*Gidan Asali*
*Halin Girma*
*Autar Hajiya*
*Zanen Zuciya*
*Yarinyar Baba*
*Auren tagwaye*
*Wata Uwar mijin*
*Ke Duniya*
And now 👇🏻
*ALMAJIRIN GIDANA* 🏠
page 14
Bayan kwana biyu, Fauziyya tasamu saukin damuwar data sanya aranta, tunda sady tabata shwara, dan harta dan fara murmujewa, bakaramin jin dadin haka Sani yayi ba, dan ko kad'an bayaso abinda zai taba ran Fauziyya.
Yauma kamar kullum Sani ne zaune kan kujera wacce ake Kira tayani gulma, Fauziyya na nesa dashi suna fuskantar juna, fira sukeyi cikin jin dadi, Babu abunda yadamesu, kwata-kwata Fauziyya tamanta da zancen Salim yakori sani daga gidan itace ta maidoshi, ko d'ar bataji a zuciyarta dangane da abunda tayi.
Ada Sanin shima yanadan jin tsoro, Amma yanzu ya sake baya tunanin kome, aishi bayada matsala tunda matar gidance tanemi yadawo bashine yamaido kanshiba.
Fad'owa tayi tsakar gidan bako sallama kamar wadda aka jeho, zumbur Fauziyya da sani suka mi'ke tsaye afirgice kamar wadanda aka Kama suna aikata wani mummunan laifi.
Jiki na bari Fauziyya tadurkusa gabanta "Sannu da zuwa mama, Ina wuni....
"Daban wuniba kinganni, nace daban wuniba kin ganni, sakarai shashasha, wacce batasan annabi ya faku ba, zuwa nayi inji yaya, kinsake samun wani cikin kokouwa har yanzu babu wani labari"
Shiru Fauziyya tayi kanta sadde, hawaye na diga daga idanunta, Sani Kuma dake tsaye gefe guda kurama Fauziyya Ido yayi Yana jiran amsar dazata bada dan shima Yana matukar bukatar jin amsar dazata bada.
Girgiza Kai tayi tace "kiyi hakuri Mama, komi lokacine, idan Allah yakawo lokacin sai kome yazama tarihi....
"Tariho, nace tariho, ni zaki gayama lokaci, ai lokacin yadad'e dayi, tun yaushema ya wuce, kinriga kinyi watsi da damarki, kinsamu ciki, kinje kinsa likita ya markadeshi yabi rariya, yaushe Kuma zakisa ran samun wani, Allah aiba abokin wasankibane dazaya baki kyautarda bamai iya bada irinta saishi Kuma kisa kafa ki Shure."
Wani irin kallo sani yayima Mama, jiyake kamar yarufeta da bugu, a rayuwarshi daka batama Fauziyya rai 'kara kakamashi kayimashi mahaukacin bugu.
Cigaba da ruwan bala'i mama tayi, "to zuwa nayi in gayamaki d'ana yasamu cigaba, Kuma yakara samun budi wlh dole ki sakarmashi mara yayi fitsari, Yana dawowa zai sallameki kisan inda dare yayimaki, sabon aure zai sake budurwa zai aura danya sharaf, wacce tasan arziki Yar gidan mutunci ba irinkiba mai yima arziki kulli"
Kuka Fauziyya keyi tana ba mamar Salim hakuri,
Hannu tasa ta hankadeta tafad'i zaune tace "tafi can sha_sha_sha Munafika kawai.....
Haba Babaa, idan anayin Abu ari'ka Sara ana dubar bakin gatari, iya biyayya Aunty nayimaki, amma baki gani, bakyau cin mutunci.....
"Kai dakata, kai-kuma uban waye Kai, miye matsayinka a gidannan Wanda yawuce *ALMAJIRIN GIDAN* to katsaya iya matsayinka idan Kuma kanemi ka wuce wlh zakaci kwal ubanka, shege mai idanu kamar na mujiya"
tana gama cin uban sani tafita daga gidan tana gyara zaman mayafinta Wanda yake sauka saboda tsabar bala'i.
Daga Nan gidan aminiyarta tawuce, Hajiya Habi, da sallama tashiga gidan, Hajiya Habi ta amsa, "a'ah kaji manyan mata, daga Ina Kuma haka?"
Murmushi maman Salim tayi tace daga gidan Salim nake, naje wurin wacce marar mutuncin matar, maiyima arziki kulli"
D'aure fuska Hajiya Habi tayi, tace "kada ki Kuma yimin maganar Nan, tun yaushe nakemaki tayin diyata khairat akan ahad'a aurensu da Salim Amma kika watsamin kasa a ido"
"bahaka bane, Hajiya wlh yaran yanzune ka haifesu baka haife halinsuba, kafin khairat saida nanemama Salim auren wata yarinya Nan kusadamu amma yaki ko saurarena barantana yajema yaga yarinyar, Amma yanzu nayimaki Al'kawarin koyanaso kobayaso saiya auri khairat indai nice na haifeshi.
*(Tofah reader's ana wata gawata)*
A 6angaren Salim Kuma tunda yatafi wurin aikinsa, hankalinshi bai kwantaba da halinda yabar Fauziyya, kullum daya kwanta da dare ba abunda yake sai tunaninta, anya yayimata adalci kuwa, gaskiya Bai kyautamataba, kowane irin laifi tayimashi yakamata ya hakura yabarta haka, ai tagane kuskurenta Kuma yasan bazata Kara gigin aikata laifi makamincin irin Wanda ta aikataba, da wannan tunanin ya yanke shawarar zaikoma gida yaga ya Fauziyyar take, Dan bazai iya hakurin zuwa wani weekend ba.
Washe gari tunda safe Salim yadauko hanya, dan yamatsu yaga halinda Fauziyya take ciki, haka kawai yakejin rashin kyautawarshi akan abunda yayimata.
Kamar yanda Sani yasaba yauma yayi wanke, wankensa yagama zuwa yayi bakin 'kofar d'akin Fauziyya yace "nagama abada kud'in cefanen"
"Shigo ka karba mana" ba musu Sani yacire takalminshi yashiga d'akin, dama abunda yake nema, barantana yasamu, mi'kamashi kudin tayi tana lissafamashi abubuwan dazai siyomata, bazato ba tsammani sai ganin Salim sukayi a gabansu, bakaramin razana sukayiba suduka, Salim kuwa wata irin Zuciya ta kuloshi wani mahaukacin Mari ya d'auke sani dashi, sannan yakaimashi naushi a hanci, Nan take hancinsa yafara zubarda jini, jikinsa har tsuma yake saboda tsabar bala'i cikin d'aga murya yace "ubanwa yamaidoka gidannan bayan nakoreka" cin kwalarshi Salim yayi yace yau sainasan kowaye abanka a 'kasar nan dahar zanyima iyaka da gidana saboda ka rainani kakiji, to idan kakiji ai bakaki ganiba" hannu yasa cikin Aljihu ya fiddo wayarshi yanacewa "Dan ubanka yau hukumace kawai zata rabani dakai"
Ai sani najin anyi maganar "yan'sanda Hantar cikinsa takad'a kad'an yahana yasaki fitsari a wando, hakuri yafara baiwa Salim Yana kuka, "Dan Allah kayi hakuri, karufamin asiri wlh bazankara zuwaba, dan Allah kada kahadani da police wlh banida Kowa a garinnan saiku, Koda wani nayima laifi ya kulleni ku kadai nakesaran zaku tsayamin, Dan Allah ka taimakmin kada kahadani da hukuma"
Sanyi jikin Salim yayi yasaki sani, ya zauna kan kujera yahada hannuwanshi duka biyu ya rike kanshi.
Fauziyya Kuma kuka take, tarasa me zatayi, itakau yau tabani, yazatayi da rayuwarta.
Abubuwa duk sunbi sun rincabemata daga wannan sai wannan,
Tasowa tayi tazo gaban Salim ta durkusa "Hubby Dan Allah kayi hakuri kada kahada sani da hukuma, nayima Alkawari tunda bakason aikinsa agidannan nahakura, zan sanya asamomin wani Almajirin, amma dan Allah ka kyaleshi yatafi, dukan dakayimashima kadai ya isa.
Shiru Salim yayi baitankaba, kusan mintuna goma sannan ya kalli sani cikin tsawa yace "ficemin daga gida" da sauri Sani yatashi ya dauki takalminshi a hannu yafita daga gidan, ga gaban rigarshi duk ya baci da jini.
*Hhhh su sani antabo ran maza yabaci* 🤣🤣🤣
Kai tsaye sansaninsu na Almajirai ya nufa, Yana zuwa yanufi dakinsu, yakoyi sa'a bakowa duk suntafi karatu Wanda shi yama manta rabon dayaje.
Ruwa yazuba abuta ya wanke jikinshi, acire rigarshi wacce tabaci da jini ya wanke, sannan yayi wanka yadanji karfin jikinshi, dawowa yayi kan gurzajjiyar katifarshi ya kwanta, ya kalli sama,
Azuciyarshi yace lallai Salim kadebo ruwan dafa kanka, wlh Kowa yaci tuwo dani Miya yasha, wlh tallahi sainasaka kuka da idanunka, sainasaka zubarda hawayenka, tashi yayi zaune yasa hannunshi yadafe kanshi daketa faman yimashi ciwo.
Fauziyya Kuma saida, iyaye suka shiga cikin maganar sannan kome ya dai-daita Kuma Salim dakanshi yaje wata makarntar yasamoma Fauziyya wani Almajirin yarone Dan shekara Sha biyu.
*Wannan kenan*
[8/25, 7:55 AM] Hayat: 🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* 🤦🏻♀
*Writing By*
*Zee Elkasim (Mmn khady)* 🥰
*Daga Marubuciyar* 📝
*Siyasa ko soyayya*
*Alhini*
*Gidan Asali*
*Halin Girma*
*Autar Hajiya*
*Zanen Zuciya*
*Yarinyar Baba*
*Auren tagwaye*
*Wata Uwar mijin*
*Ke Duniya*
And now 👇🏻
*ALMAJIRIN GIDANA* 🏠
Page 15
Shehu shine almajirin da Fauziyya ta canja, tun karfe bakwai na safe yazo gidan ko bud'e gida basuyiba yahau bugun 'kofa, cikin bacci Fauziyya tajiyo bugun 'kofa kamar za'a balla kyauren.
Sallim ta kalla Wanda ke bacci cikin kwanciyar hankali, tabashi tayi tace "Hubby naji kamar ana bugun kofa"
Saurarawa yayi yace "bari nafita nagani waye haka da wannan safiyar" Fauziyya tace "Allah sa dai lafiya" Salim yace "Ameen" jallabiya yasanya sannan yanufi zaure yabude, shehu yagani tsaye rike da robarshi irinta almajirai, ga wasu dangalalllun Kaya dayasa, sunyi muguwar dauda har wani maiko suke, gashi duk sun gama yayyagewa.
Kallonshi Salim yayi a kyamace yace "lpy kake bugamana gida da wannan farar safiyar" majinar data leko daga hancin shehu ya janye sannan yace "aiki nazoyi" "what" Salim yafad'a da karfi har saida shehu ya razana, yace "kaine dama *ALMAJIRIN GIDANA*" daga Kai shehu yayi tareda sa bayan hannunshi ya goge sauran majinar dake hancinsa"
A matukar kyamace Salim yace "kaje kaji munsamu wani Almajirin, dama namu yaje ganin gidane tokuma jiya da yamma yadawo" "to" shehu yafad'a Yana kokarin barin 'kofar gidan, kauda Kai Salim yayi Dan wani mugun zaurin fitsari daya ziyarci hancinsa.
"Dan dakata Ina zuwa" Salim yafad'a tareda komawa cikin gida, d'aki yanufa ya tarar da Fauziyya harta dawo falo, tarbar Salim din tayi tace "Hubby lafiya, waye Kuma haka tunda safe?'
"Ina zuwa Salim yace, wucewa yayi bedroom ya d'auko dari biyu sannan yanufi kitchen ya dauko wani sauran bread yafita, inda yabar shehu Nan yatarar dashi mi'kamashi bread din yayi yace "amshi wannan" jiki na kyarma shehu ya amsa, sannan Salim yamikamashi dari biyu yace "wannan kasiyi omo da sabulu kari'ka yin wanka da wanki" godiya shehu yayi yatafi Yana waiwayen gidan, Yana takaici dabaiyyi aiki cikinsaba, dan da alama za'a samu abun arziki a gidan.
Komawa Salim yayi duk a kyamace, zuciyarshi sai tashi take, dan Salim mutum ne Mai tsananin kyankwami, inda yabar Fauziyya Nan yatarar da ita zama yayi kusada ita, tareda jawota jikinshi ya rungumeta.
Shagwabewa Fauziyya takarayi jikin Salim tace "Hubby Wai waye dan Allah"
Hannunshi yakai kanta Yana shafa lallausar gashin kanta yace "Almajirinkine" dago Kai tayi ta kalleshi tace "Yana ina?" Salim yace "Nakoreshi" zumbur Fauziyya tayi tazauna tace "kakoreshifa kace, habba Hubby to waye zairika yimani wanke-wanke da shara, gakuma yo cefane kasuwa, haba Hubby dan Allah ka tausayamin, so kake aiki yakasheni"
Kallonta Salim yayi Yana jin matu'kar kaunarta a zuciyarshi, gsky Yana matukar 'kaunar Fauziyya, bayason abunda zai taba zuciyarta, mace ce managarciya, Mai hakuri, sannan uwa uba tana bashi hakkinsa na aure yanda yakamata, ga tsantsar juriya da......
'kara jawota yayi jikinshi yace "look my wife, kada kisa damuwa aranki zanje da kaina nasake duba wani Almajirin, Amma wannan 'kazantarshi tayi yawa, na tabbatar Koda kece Kika ganshi wlh bazakiso yayimaki aikiba, dan Koda yayi hankalinki bazai kwantaba, ke kibarma batun wannan, Bari ingayamaki gaskiya muddin wannan Almajirin zaiyi aiki gidannan nagama cin abincin gidan"
Zaro Ido Fauziyya tayi, arazane tace "Amma Hubby Mai zai hana uhm....umm
"Fad'a mana my wife minene kiketa wani in-ina"
"Kamin Al'kawarin idan nafad'a bazakace a'a ba"
"Namiki Al'kawarin matata, farincikinki shine farincikina, kome kikeso inaso Wanda bakiso Kuma kome sonda nakemashi zan iya hakura dashi"
Cikin fargaba da inda-inda Fauziyya tace "Hubby mai zai hana mu maido sani tunda kagashi da hankalinsa, Kuma Yanada tsafta, Kuma kaga munsaba dashi shekara nawa muna tar.........
"Ke......dakata, yafad'a a tswace yace Fauziyya Ina gargadinki da...
Wata irin Zuciya ta 'kuloshi yatashi fuuuu yashige bedroom, zama Fauziyya tayi falo tarasa miyema zatayi tashawo kan Salim.
***. ***. ***
Zaune yake kan d'aya daga kujerun d'akin yayi shiru Yana sauraren sababinda mama kemashi.
"Salim ka saurareni, wannan umarni nake baka ba shawara ba, kaje gidan Hajiya Habi, ku gaisa da khairat" arazane Salim ya dago ya kalli mama, Dan yasan khairat kamar yunwar cikinsa batada kamun Kai, tasha kawo tallar kanta gareshi rashin samun fuska yasa tashafamashi lafiya, watako yanzu tanan ta bullo, "aiko zanyi maganinta" yafad'a aranshi.
Cigaba tayi da magana, "inaso ku dai-daita kanku sonike ayi auren Nanda wata daya"
Wata irin fad'uwar gaba Salim yayi, yace "Amma mama...
"Dakata banison wani dogon bayani, amma me? nagayama umarni nakebaka Kuma dole kabi, Kuma wlh idan kaje naji labarin kayimata wani mugun kallo ko kagayamata wata magana marar dadi wlh Allah ya'isa tsakanina dakai"
dafe Kai Salim yayi da hannu biyu yace "innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un, mama....
***. ***. ***
.
Hajiya Habi gogaggiyar Yar duniyace, tayi zaman saudiyya (kano to jidda) daga can ta haifi khairat, ubanta balarabe ne Yana can 'kasar saudiyya, rabuwar wulakanci sukayi da Hajiya Habi, saboda yakamata da maigadin gidanshi sunacin amanarshi.
Dukda haka yaso tabarmashi khairat amma takiya, haka yabari tataho da ita badan ranshi yasoba, Yana masifar son khairat saboda ita kadaice diya mace cikin yayanshi.
Tunda Hajiya Habi tadawo Nigeria tasayi gida tana zaman kanta, gidanta babu control banza da wofi dashara da bola Kowa shiga yake gidanta, khairat Kuma haka tataso ba tarbiyya, sai yawon gidan party, da bin maza, dan farkon wandayafara lalatamata rayuwa shine Alhji shitu bazawarin Hajiya Habi ne wand suke sheke ayarsu shine Kuma ya lallaba ta bayan kasa ya yaudari khairat din, dayimata ruwan kudi.
*Reader's kuyi hakuri wlh banida lafiya ina fama da masassara da ciwon Kai Dan Allah kusanyani addu'a Idan naji sauki zakujini idan Kuma akasin haka to sai dai yanda yakama.*
Mmn khady ce 🙏🏻
[8/26, 7:34 AM] Hayat: 🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* 🤦🏻♀
*Writing By*
*Zee Elkasim (Mmn khady)* 🥰
*Daga Marubuciyar* 📝
*Siyasa ko soyayya*
*Alhini*
*Gidan Asali*
*Halin Girma*
*Autar Hajiya*
*Zanen Zuciya*
*Yarinyar Baba*
*Auren tagwaye*
*Wata Uwar mijin*
*Ke Duniya*
And now 👇🏻
*ALMAJIRIN GIDANA* 🏠
Page 16
"Hubby kada kasama ranka tunanin wani abu, wlh sani bayada matsala, kaga gashi da tsafta da sanin yakamata, babu wani abun 'ki tattare dashi, wlh duk wani Almajiri dazamuyi bazayakai Sani ba"
Shiru Salim yayi na tsawon wani lokaci, sannan yace shikenan yadawo d'in, Amma da sharadin Koda wasa kada inga kafarshi cikin dakinki, ya tsaya iyakar aikinsa"
"Kada kadamu Hubby, indai wannan ne inshaAllah zan kiyaye" "to shikenan, akiyaye"
6angaren sani Kuma tunda Salim ya koreshi daga gidanshi yarasa mikemashi dad'i, abubuwa duk sunbi sun jagulemashi, ga missing din Fauziyya da yayi, idanuwanshi na mararin ganinta, kunnuwanshi na tsananin son jin zazzakar sautin muryarta.
"Yanzu yazanyi" yafad'a Yana share hawayen dasuka gangaro kan fuskarshi, "yazanyi da rashinki Fauziyya, kitaimakeni nashiga wani hali sakamakon yin nesa dake" wayarshi ya fiddo, hotunanta yafara kallo d'aya bayan d'aya, baya gajiya da kallon hotunan kullum sabbi suke koma mashi idan yana kallonsu.
Yakai kimanin awa daya darabi yana kallon hotunan, saida wayarshi tabuga low battery sannan yamaidata aljihu.
Tashi yayi jiki a sanyaye yafito wurin abokaninsa Almajirai daketa hidimar gabansu a harabar gidan nasu.
Basiru ya hango can zaune bisa wani dutsi Yana wanki, karasowa yayi wurinsa ya zauna gefensa.
kallonshi Basiru yayi yace "abokina narasa mike damunka nayi juyin duniyarnan kaki gayamin damuwarka Kuma naga kwana biyu bakaje gidan Fauziyya ba ko lafiya?"
"Lafiya kau" sani yafad'a dan bayaso Kowa yasan maganar korar da Salim yayimashi, shiyasa ko maganar bayaso.
"Ba dai lafiya ba abokina, dan nasan lafiya-lafiya hakanan bazakabar aiki gidan Fauziyya ba, kadai gayamin gaskiya"
Basar da zancen Sani yayi yace "nifa ba wannan maganarce takawoniba, dama wata shawara nazo muyi nidakai muduka nasan zata amafanemu"
"Ina jinka" Basiru yafad'a tareda maida hankalinshi kan sanin Dan sauraran abunda zaifada.
Kaga jiya naduba kudina Wanda nake tarawa, yanzu sunkai kimanin naira dubu ishirin da shidda, shine nace mai zai hana muhada nidakai musamu wani karamin shago mufara siyarda kayan kwalliya, idan Allah yasanya Mana Albarka saikaga muna samun wani abu.
Shiru Basiru yayi na wasu mintittika sannan yadafa kafad'ar Sani yayi dariya yace "abokina kace kadawo daga rakiyar shiririta, kagane gaskiya kenan, shikenan ba matsala kasan dama akwai wani d'an karamin shago dana kama dubu bakawaine kud'in dana biya na haya, shikenan saimuyi amfani dashi, yanzu kabada dubu ishirin da biyar Nima inbada ishirin da biyar, saimu Fara mugani"
"To shikenan Allah yashigemana gaba" "Ameen"
Wayar Sani ce tafara tsuwwa da sauri yafiddo daga Aljihu yaduba, sunan Fauziyya yagani, wani mummunan fad'uwar gaba yaji, dai baisan dalilin dayasa takirashiba. saurin tashi yayi daga wurin yakoma gefe nesa kad'an da inda Basiru yake sannan yad'aga wayar yakara a kunne, shiru yayi Yana jiran abunda zata fada.
"Hellow sani, ya kake ya kwana biyu" shiru sani yayi yakasa magana, "Hello.....hello....... Sani kanajina kuwa?" Inajinki aunty "Ina wuni"
"lpy lao"
"Dama Kira nayi ingayama, Salim yace inbaka hakuri akan abunda yafaru Kuma yace kadawo kacigaba dayimani aiki"
Wayyo Allah dad'i, saboda murna Sani rasa inda zaisa kanshi yayi, koba komai zaicigaba da kallon kyakkyawar fuskar Fauziyya yanajin dad'i.
***. ***. ***
Kallon khairat Hajiya Habi tayi tace "Kai amma kinyi kyau wannan kwalliya haka, Ni nasan dole Salim ya amince da soyayyarki a wannan karon, Kinga kuwa yanda kikayi kyau kamar wata India"
Wani kallo khairat tawatsama Hajiya Habi tace "kinmanta Hajiya aini nafi India, kohar kinmanta waye babana"
"Ban mantaba khairat, watarana ai zankaiki saudia kigano babanki da 'yan'uwanki"
Wayar khairat dake ajiye kan mirror kirar camon 11, ce tayi ringing, da sauri ta dauka ta kalli Hajiya Habi tace "Salim ne" dagawa tayi takara a kunnenta tace "eh kashigo kawai
Jiki a sanyaye Salim yashiga gidan, gawani mugun bacin rai dake addabarshi, Hajiya Habi da kanta ta tarbeshi tayimashi iso awani madai-daicin d'aki Wanda yasha kujeru masu kyau da carpet tsakiyar d'akin sai karamin center table na glass, zama yayi sannan suka gaisa da Hajiya Habi din, Nan take tambayarshi mamarshi yace tana lfy.
Komawa Hajiya Habi tayi wurin khairat tace kiyi sauri kije kina batamashi lokaci, ni bari infita Nan gidan Hajiya Asabe muje wurin maganar kayan damukayi da ita" "to saikin dawo"
Feshi jikinta tayi da kalaluwan turare, sannan tanufi fridge ta dauko ruwan roba da lemu tadora kan tire da cup din glass tanufi d'akin da Salim din yake.
Ajiye tire din tayi kan table dinda ke gaban Salim din sanan tamatso kan kujerar dayake zaune two seater zata zauna gaf dashi idan kaganima saikace kan cinyarshi tayi niyyar zama.
Mi'kewa Salim yayi da sauri yace "ke miye haka, bakida hankaline"
Cikin nuna rashin jin haushin abinda Salim din yayimata tayi murmushi tace "nice ko keda hankali, ai natabbata da banida hankali bazaka amince da aurenaba"
"Wayagayamki amincewa nayi da aurenki, kawai zan aurekine dan bin umarnin mahaifiyata Amma banisonki, ko kad'an bani kaunar mace marar kamun Kai, khairat bakida tarbiyya ko kad'an babu namijin dazaiso ki kasance uwar yayanshi"
Tunda yafara magana khairat ke kallonshi tana wani lumshe Ido yanda kasan Yana zubamata wasu kalaman soyayya, ko kad'an bai bata haushiba, saima burgeta dayakeyi, tadade tana son Salim, amma ya'ki saurarenta, yanzu Kuma tunda tasamu wannan damar bazatayi wasa da itaba, Koda Salim duk zuwa zai kamata yayimata duka bazata nuna taji haushiba barantana har yakawo rugujewar maganar auren nasu.
Wani matsiyacin kallo Salim ya watsamata ganin yanda taketa wannan karairaya a gabanshi kamar macijiya, kasancewarta batada jiki ko kad'an kamar tsinke haka take Babu wata kwana single tatafi sai dai akwai tsananin kyawun fuska Mai d'aukar hankali, ga gashin kanta na asalin larabawa.
Wani dogon tsaki Salim yaja, sannan yafice daga gidan, ko sallama basuyiba.
Kai tsaye masallaci Salim yanufa yagabatarda sallar isha'i sannan yawuce gida, ranshi amatu'kar bace, Wai ace mama da kanta takeso tahad'shi aure da khairat kawai saboda tsanar dayayima Fauziyya,
Tunda yashigo Fauziyya takula da halinda yake ciki, haka tafara kokarin kwantarmashi da hankali dukda batasan miye musabbabin bacin ran nashiba,
Shiru Salim din yayimata, hakan ba karamin dagamata hankali yayiba, kuka tafashe dashi tace "shikenan Hubby nasan banida matsayinda zanbaka hakuri akan bacin ranka ka hakura, kanuna damuwarka ba dakuwata bace, nagode Hubby" mi'kewa tayi tana goge hawayen idonta,
Wani irin tausayi tabashi, jawota yayi tafad'a jikinshi ya rungumeta tsam ajikinshi, tunaninshi daya shine yanda zai tunkareta da maganar aurenshi, gaskiya mama batayimashi adalciba.
*Alhmdlh naji sauki, nagode da adu'oinku gareni, Naga dumbun masoya masu kirana a waya damasu yimin text massage damasu mun magana a chat duka Ina godiya, sai dai har yanzu jikina ba karfi,*
Mmn khady ce 🤩
[8/28, 6:43 AM] Hayat: 🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* 🤦🏻♀
*Writing By*
*Zee Elkasim (Mmn khady)* 🥰
*Daga Marubuciyar* 📝
*Siyasa ko soyayya*
*Alhini*
*Gidan Asali*
*Halin Girma*
*Autar Hajiya*
*Zanen Zuciya*
*Yarinyar Baba*
*Auren tagwaye*
*Wata Uwar mijin*
*Ke Duniya*
And now 👇🏻
*ALMAJIRIN GIDANA* 🏠
17
Dare mahutar bawa inji Hausawa, kowace rai tanason hutu, Amma lokacin wasu ke cikin kunci da tashin hankali, kamar yanda Fauziyya ta kasance a wannan daren, misalin karfe 1:37am Fauziyya kwance gefen gado, ajiyar Zuciya kawai taketa saukewa saboda kukan datasha tun lokacinda Salim yagayamata maganar 'karin auren dazaiyi.
Cikin bacci Salim yake jiyo sheshshekar kukanta, ahankali yabude idonshi ya saukesu kan Fauziyyar wacce takoma can karshe gado nesa dashi, tashi yayi zaune, jiki a sanyaye ya iso inda take yadafata, "kiyi hakuri Fauziyya, nagayamaki wannan auren wallahi bada son Raina zanyishiba, mamace ta tilastamin, Kuma wlh yarinyar nan banisonta ko kad'an, nifa duk wata mace indai bake bace wlh daya take da namiji a wurina, Dan Allah ki kwantar da hankalinki, ni Ina tare dake kome wuya kome tsanani"
Bayan hannu Fauziyya tasa ta goge hawayen dake bin kumatunta tace "Salim ba wannan bane damuwata, bansan yanda zamana zai kasance a gidannan ba idan ka Kara aure, nasan watarana mama saita watsamin kayana waje takoreni.....
Hannu yasa yarufemata baki "dan Allah kada kisa wannan tunanin aranki, Fauziyya Ina sonki bazan iya rabuwa dakeba, babu kuma Wanda ya isa yarabani dake, mutuwace kawai zata rabamu"
Ahakadai Salim yasamu yashawo kan Fauziyya, rungumeta tsam yayi ajikinshi suka kwanta, kowane zuciyarshi cike da tunani barkatai.
Bangaren sani kuma sun bud'e shago shida Basiru, anzuba Kaya, Kuma alhmdlh suna samun ciniki sosai, bakaramin dad'i sani yajiba Dan Yana ganin tanan zaitara kudinda zaisamu ya auri Fauziyya, tunda amatsayin zawara zai aureta bawai wani makudan kud'i ake kashewaba, dan koda yaushe jikinshi na gayamashi Fauziyya saitazama mallakishi komin daren dadewa.
Bangaren khairat da Hajiya Habi shirye-shiryen biki sukeyi sosai, dan anriga an sanya rana yau saura sati biyu bikin.
Salim Kuma tun zuwan dayayi wurin khairat bai'kara zuwaba, Amma wannan bai dametaba itada Hajiya Habi sudai burinsu ayi auren Koda bayaso daga baya sun San yanda zasu bulloma al'amarin.
Ko kad'an Salim Bai d'auki hidima yadorama kanshiba, bama zaka ganshi kace Yanada wata hidima gabanshiba, kullum dai Yana kan hanyar zuwa wurin aikinsa Yana fafutukar yanda za'a Kuma maidoshi wurin aikinsa, dan ko kad'an bayajin dadin kauyen dasuka maidashi.
Sati daya yanata shige da fice, cikin ikon Allah yau dai yasamu abuda yake nema an maidoshi garinshi.
Hakan bakaramin dad'i yayimashiba, Dan zai kasance da Fauziyyar shi Koda yaushe, zai Rika rarrashinta Yana kwantarmata da hankali Dan har yanzu tana cikin damuwa sosai.
Maman Salim dakanta ta tsare Salim ta amshi kud'i masu yawa taje kasuwa tahado kayan lefe set din akwati, tacika kowane da Kaya bayabo ba fallasa, kayan sunyi bakin gwargwado.
Salim Kuma dakanshi yashiga kasuwa yasiyoma Fauziyya tsaddaun Kaya less guda ukku, sai shadda guda biyu, sai atamafa kala biyar, sai dogayen riguna Dubai, suma kala hud'u, jikka da takalimi set hud'u, sai sauran tarkacen kayan make'up da turarruka, da sauran abubuwan dayakamata irinsu sarka passion da Yan hannu da sauransu.
Hidima dai yinta akeyi ba Kama Hannun yaro, Maman Salim itace ke karbar kudi wurin Salim ko ransa besoba tayima khairat duk abunda akeyi, dan yauma khairat din tazo amsar kudin dinkunan data Kai Wanda zatasanya wurin bikin, dubu goma mamar Salim tabata ta amsa a wulakance Dan khairat ta bala'in raina mamar Salim.
Salim kuma hidimar Shi kan Fauziyya yakeyinta dan itace damuwarshi, bayaso taga rashin adalcinsa.
Fauziyya Kuma kallo d'aya zakayimata kasan tana cikin damuwa, amma haka take daurewa dan tana samun tsananin kulawa wurin Salim, shiyasa batason nuna damuwarta afili.
Yau tun 'karfe bakwai Salim yabar gida saboda neman da akemasu wurin aikinsu sakamakon wani aiki da za'a turasu awata jiha, Wanda federal government ke neman hazikan malamai, na makarantun secondary shine makarantarsu tabada Salim saboda kwazonshi da Kuma jajircewa a wurin aiki, baya fashi saida wani kwakkwaran dalili, kuma Yana koyawa yanda za'a Gane sosai dalibai kejin dadinsa.
tunda yafita Fauziyya tatashi tashiga kitchen ta fiddo duk kayan wanke-wanke, tashare kitchen din, sannan tafera doya tasa atukunya tadora a wuta, sannan takoma d'aki tagyara ko'ina tsaf tashare ta goge, tafesa freshner, tsakar gida tafito ta dauki tsintsiya tafara sharewa,
Lokacin Sani yashigo da sallama, amsa sallamar tayi batare data dagoba, kallonta sani yayi ya hadiye wani miyau, kamar wani tsohon maye yace Dan wani mugun kyau yaga takara kwana biyun dayayi Bai gantaba, takara fari sai dai Kuma tarame "aunty Ina kwana" "lpy lao" ta amsa batareda tadago ta kalleshiba.
Matsowa yayi kusa da ita yaduka yasa hannu yari'ke tsintsiyar har Yana had'awa da hannunta, yace "haba aunty saboda me zaki wahalar da kanki bazaki Bari inzo in shareba"
Kallonshi Fauziyya tayi, sannan ta sakarmashi tsintsiyar batareda tayi maganaba, aranta Kuma tana yabonshi saboda sani akwai kirki da sanin yakamata.
Cigaba sani yayi da sharar itakuma takoma kitchen Dan hada abun Kari, Yana gamawa yahau wanke-wanke shima ba Bata lokaci yagama saboda bawasu kwanuka bane masu yawa.
Toilet Fauziyya tashiga tashe'ko wanka tafito, yauma kamar kullum wani shu'umin kallo sani yarikayimata wanda batasan yanayiba.
D'aki tawuce tashafa mai da kwalli sannan tasaka wata doguwar riga marar nauyi, tafito tanufi kitchen, tea tahada 2cups taba sani daya ta d'auki daya, tazumabashi doya data soya da kwai tabashi sannan tadauki nata tawuce d'aki.
Kallonta sani yayi azuciyarshi yace " waini Kam miye ke damun aunty, tunda nadawo gidannan nalura Bata cikin nutsuwa, ga wata irin rama datayi, to kodai tasake samun wani cikinne.
Kai beyiyuwa, aiko indai tunanina yazama gaskiya dole nasake d'aukar mataki, muddin Ina numfashi Fauziyya bazata haihu a gidannan ba, Kuma idan na tabbatar da cikine da ita saina zubardashi Koda yakai wata tara.
Wannan mugun tunanin da Sani keyi yasa yaji tea din da doyar duka sunfice aranshi, tashi yayi rai abace yabar gidan batareda sanin Fauziyya ba.
Saida Fauziyya tagama tafito taga sani bayanan, ga Kuma tea da doya yabari, dauka tayi cikeda mamaki takai kitchen tace ko lafiya Sani yabar tea dinanan, Almajiri taji yayi bara takirashi ta juyemashi, yayi godiya yafita Yana murna.
Sani Kuma gindin wata bishiya ya zauna yanata tunani aranshi, tun yanayi azuciyarshi haryafito fili "Fauziyya yazakiyimin haka, yaushe Zaki yarda ki Kuma samun wani cikin tareda Salim, haba Fauziyya, miyasa kikemin haka, nine yakamata ace kinsake d'aukar cikina bana Salim ba"
Wani shu'umin murmushi yayi yace Fauziyya kin tafka babban kuskure, amma zakiji ajikinki, dan wlh wannan karonma sainayi sanadiyyar zubewar wannan tsinannen cikin naki.
Kamar Wanda aka tsikara yatashi, komawa yayi gidan Fauziyya.
*"Kuyi manage da wannan kunsan jikin nawa sai a slow"*
*Mmn khady ce*
Mmn khady ce 😘
*Mmn khady ce* 🥰
[8/31, 8:03 AM] Hayat: 🏠 *ALMAJIRIN GIDANA* 🤦🏻♀
*Writing By*
*Zee Elkasim (Mmn khady)* 🥰
*Daga Marubuciyar* 📝
*Siyasa ko soyayya*
*Alhini*
*Gidan Asali*
*Halin Girma*
*Autar Hajiya*
*Zanen Zuciya*
*Yarinyar Baba*
*Auren tagwaye*
*Wata Uwar mijin*
*Ke Duniya*
And now 👇🏻
*ALMAJIRIN GIDANA* 🏠
Page 18
Kamar Wanda aka tsikara yatashizumbur.
Hanyar gidan Fauziyya yanufa yanata surutai kamar wani mahaukaci sabon kamu, "to wlh bazan taba yarda haka ta kasanceba, ciki....ciki Fauziyya nizakiyima haka, wlh kind'ebo ruwan dafa kanki dan wlh bazanbarki ki haife abinda ke cikinkiba, dole inyo waje dashi tunkafin lokaci yakuremin"...... Haka yayita surutai Yana tafiya baisan inda yake jefa k'afarshiba, bayama kallon gabanshi harya iso gidan.
Saida yazo zaure Yana gaf dashiga gidan yatsaya Yana tunani, "idan nashiga gidan haka tabbass dole Fauziyya ta fahimci Ina cikin wani hali,.... Dafe 'kirjinsa yayi na wasu Yan mintittika, sannan ya dai-daita nutsuwarshi, da sallama yashiga gidan, lokacin Fauziyya na zaune kan kujera tana wanke inners dinta Dana Salim, amsa sallamar tayi tareda juyowa ta kalli sani tayi guntun murmushi tace "Mal Sani kud'ifa sun zaunama da alama"
Shima murmushin yayi yace saboda me kikace haka aunty ?"
"Naga yau bakasha tea ba dasafe, saida nafito naganshi najuyema wani Almajiri"
"Eh wlh aunty banajin yunwane shiyasa"
"Ainasani angayamin anganka teburin Mai shayi anyima hadin kakkaura, da bread da wainar kwai......
Dariya sani yayi sosai, itama Fauziyyar dariyar take, yace "Kai aunty waya gayamaki Ni gaskiya kowaye 'karya yakemin, yoni aunty Fauzy inadake ainafi 'karfin zaman teburin Mai shayi"
"Hmm" Fauziyya tayi murmushinta Wanda yake Kara bayyana kyawunta, Wanda yakara Jan hankalin Sani gareta, jiyake kamar yaje ya rungumeta saboda wani sabon shauk'in soyayyarta daya dira a zuciyarshi.
Shiru yaratsa na kimanin minti biyar, sannan sani yakatsemasu shirun "nikam aunty intamabyeki Mana"
"Ina jinka sani Allah yasa nasani, tafad'a tanacigaba da wankinta batareda ta kalleshiba"
Shiru sani yayi Dan yarasa ta inama zaifara...
Jin yayi shiru yasa Fauziyya juyowa tazubamashi kyawawan idanunta, taga ya Lula wata duniyar yayi nisa cikin tunani,
Ruwan kumfan datake wanki tad'an d'ebo a hannu ta watsamashi afuska, wata razana Sani yayi Wanda yaba Fauziyya dariya,
Dariya take sosai, sani Kuma kallo kawai yabita dashi cikin ranshi tana matukar burgeshi.
"Wai Sani lafiya kuwa Naga kayi nisa cikin tunani kodai kasamu wacce takama zuciyarka ne?
"Sosaima Aunty, wlh wata kyakkyawar yarinyace tatafi da duka imanina, narasa tayanda zan fuskanceta da maganar soyayya.....
"Hhhhhh, wayyo cikina Fauziyya tafad'a tana dafe cikinta "ohni su sani amfada tarkon Love, wannan wace wayrinyace haka, wacce tayima zuciyarka kamun kazar kuku"
"Bakisaniba aunty nadad'e Ina dakon soyayyarta, kusan shekara biyu da wasu wattanni kenan, amma narasa taya zan tunkareta na yad'amata manufata, amma dukda Ina sonta batasan inayiba, hakan bai hanani bibiyar al'amurrantaba, dan duk wani taku nata insane dashi, yanzuma abunda yasa kikaga nafad'a tunani haka wanine yakeson yimin shigar sauri, to narasa ta inda zan bulloma al'amarin, aunty Fauzy kibani shawara mana........
Tunda yafara magana fauziyya ke kallonshi cikeda mamaki, Dan ita wlh cikin wasa tayima Sani wannan maganar Amma taga shi dagaske yake koramata bayani.
Ajiyar Zuciya tayi tace "abunda kawai nakega zaifi shine kadake amatsayinka na namiji ka fidda tsoro ka tunkareta kagayamata sirrin zuciyarka, inaji ajikina zata aminta dakai.
"Ammafa aunty kinsanfa matsayina, niba Kowa bane sai *Almajiri* kinaga zansamu soyayyarta ayanda nake"
"inshaAllah zakasamu zantayaka addu'a" "to shikenan nagode aunty, Amma aunty nikam sainaga kinrame wlh kodai bakida lafiyane?"
"Eh banajin dadi" tabashi amsa atakaice Dan surutunshi yafara isarta sakamakon ciwon mara datafaraji sama-sama.
Kallon Sani tayi tace sani kanada labarin "Salim zaikara aure kuwa?" zaro Ido sani yayi tareda dafe 'kirji Alamar razana yace "Aure Kuma aunty"
"Hmm" kawai tafad'a tad'auki buta tashige toilet Dan ciwon marar yanadan karuwa, tana shiga abunda take zato kuwa shine tagani bakon watanta ne yazo,
D'aki takoma taduba pad batada saura Ashe, rubutawa tayi atakarda sannan tafito taba sani, "Dan Allah sani kaje chemist yanzu kasiyomin wannan"
"To" kawai sani yafad'a yakarba yatafi.
Kai tsaye sani shagon kolo yanufa, yabashi takardar yace "bani wannan maganin" duba takardar kolo yayi yadauko pad din yasaka aleda yamik'ama sani yace kud'in 350 ne, juya ledar sani yashigayi, Dan yaga abun him cikin Leda kamar wani bread, kallon kolo yayi yace wannan Kuma namiye?"
Dariya kolo yayi yace "babyn Bata gayamaba tana period ne, wannan ai audigane na mata" sani bin kolo yayi da kallo danshi yakara tunzurashi a duhu, "miye Kuma period? Sani ya tambaya Kuma miye audigar mata?
Dariya kolo yayi yace "abokina duk yanda kake harka da mata amma bakasan wannan ba" danshi kolo atunaninsa sani wata mace ya ajiye suke sheke ayarsu, saboda haka zama yayi yayima sani bayani dalla-dallah harya gane kome.
Cikeda farin ciki sani yanufi gidan Fauziyya yakaimata part din Dan kolo ya gayamashi idan mace tayi period to batada ciki, idan Kuma wata yazo batayiba to tanada ciki kenan.
Godiya yayima Allah dayasa Fauziyya batada ciki.
***. ***. ***
Bangaren khairat Kuma duk wani shirye-shiryen dazasuyi sundade dagamawa ranar aure kawai suke jira tazo, khairat tadage Shan kayan mata rarumo wannan yayo wancan, duk inda taji wani maganin mata da'akace Yana maida mace kamar budurwa saita siyeshi komin tsadarshi, itadai burinta idan tashiga gidan tazama itace Yar gaban goshin Salim yazama sai abunda tace za'ayi.
Dan tanajin labarin yanda Salim d'in ke mutuwar son Fauziyya itakuma haka yasa talashi takobin shiga tafita, Koda ta kissa da kisisina har saitaga ta maida Fauziyyar Yar bayan goshin Salim ('keya).
Ana saura kwana goma bikin masu aiki sukazo cikin sati daya an canja samfarin gidan, Dan wani karamin gidane Salim yasiya kusadashi yahade danashi kowace akayimata falo da 2 bedroom kowane da toilet aciki, da kitchen, Amma tsakar gidan dayane, sai d'akin Salim din Wanda yakasnnce Yana kallon d'akunan nasu, daga can gefe Kuma kewayen tsakar gidane.
Gidafa yafito Shar gwanin sha'awa, Fauziyya daga gidansu aka kawomata sabbin set din kujeru Dana gado, saboda haka tsohon gadonta saitasashi bedroom dinta gudan,
Guda Kuma tasanya sabon, sai falonta tajera sabbin kujerun kome nata gwanin kyau kamar itace amaryar, tsoffin kujerunta Kuma d'akin salin tajerasu, shima yayi gado medium mai kyau d'akin nashi yatsaru dukda falan dayane, sai toilet dake ciki.
Khairat anyi kamu, Babu ango Dan dama tasan Salim bazaitaba zuwaba, daga ita sai abokanta da alhazanta Wanda suke sheke ayarsune sukayimata Kara sukazo, amma ta kudire aranta ran dinner kobayaso sai yaje, dan tanaso friend dinta suga handsome d'inta, dan susan itamafa babbar yarinyace, dan bakowace mace zata iya samun kalar Salim ba sai mai sa'a.
*Washe gari* ana gobe d'aurin aure akazo akayi jeren khairat, itama Alhmdlh an tsara sashenta kome yaji, bedroom dinta duka ansa gado, falontama yasha royal chairs, abun dai Shar kitchen dinta babuce kawai ba'a sakaba Dan saida ta wanki kud'ad'e wurin alhazanta sosai
tayima kanta hidima.
0 comments:
Post a Comment