Wani babban gate hadadde naga an bude ai kuwa nan motocin suka shige ciki bayan sunyi parking ne wasu securities ne suka zo wurin motar tsakiya suka bude kofar motan wato gidane nagani a fada tsarin gidan kawai ko hmmm .. ba a magana domin kuwa bata baki ne ga gidan babba gashi hadadde wacce tafito cikin motar aikuwa ina ganinta saida na.......
Wata yar budurwace fara kyakkyawa batada jiki kuma bazaka kirata da slim girl ba ga hancinnan zir kamar pencir ga bakin madaidaici komai nata cip cip kamar ita ta halicci b abin sai wanda yagani ANEESa kenan yarinyar albarka ga kyau ga ilmi ga hankali mashaa Allah
Jallabiyace ajikinta sai mayafin jallabiyar da tayi hijab dashi yayi mata kyau sosai wasu mata ne suka fito suka durkusa har kasa suna mata sannu da zuwa Aneesa ta amsa sannan tayi masu umurni dasu mike tsaye ba musu suka mike ai kuwa kafin takuma cewa uffan wasu yan mata ne suka fito dauke da wasu kwanoni kyau ga daukan ido flowers ne suka fara zubawa a kasa suna wakoki Aneesa tace kudai wai bakwa gajiya ne ?
Duk dawowana sai kunmin irin wannan tarba.... ai sai ji tayi popospoossss kamar ana fasa baloons kamar kuma knockout kunnuwanta tayi da hannayenta bibbiyu kana tace wai me haka ne Allah ni banason haka wai inasu mom ne da murmushi suka fito dauke da cake a hannun mom din murmushi itama Aneesar tasakar mom dinta sannan taje ta hura candle din da ke saman cake din da baki takuma sa knife ta yanka tabama mom dinta sannan itama taci
Mom dinta ta mikawa wata mata kusa da ita sannan ta rungumi Aneesa cikeda so da kauna a haka suka shiga har cikin palo Aneesa tace...... ban tsaya ta fada ba niko in baku lbr ganin dukiyarda ke cikin palon ne yasa na kasa cigaba da ✍π» domin kuwa hannuna har nauyi yamin
Love u all ππ❤ππ»
π©π»⚖ANEESA YAR PRESIDENTπ©π»⚖
Na Hannatu Dada Kuta
π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬
UMMU SAFWAN HAUSA NOVELSπ
02
Aneesa ta rusuna har kasa ta gaida mominta sannan tagaida kawayen mommy bayan sun zaina ne aneesa ta kalli momminta tace wai mom dan Allah bazaku daina wannan kashe2 kudinba?
Da wannan kashe kudinda kukayi dan tarbata wallahi mom da sadaka kukaje kukayimin da ita da yafimin kuma danafi jin dadi wallahi mom bazan gaji da fada maki hakan ba waishin mom kinkosan adadin mutanenda ke cikin damuwarda idan kika basu wannan kudin cake kawai zai fiddasu cikin kuncin rayuwarsu kuwa?
Mom tace toh ustaziya ai kyabari ki huta kafin kifara wa azin naki da baki gajiya dayinshi koh?
Wata mata ce ta kalli Aneesa kana tace lallai ma Anee wallahi in bancin ina gari her excellency ta haifeki ko toh wallahi da babu abinda zai hanani tunanin ko daukoki tayi a gidan gajeyu
Yarinya da gatanki amma sam ga naira ga ga ..... amma sam baki damu da cinsu ba
Lallai ne kam bahaushe yayi gaskiya dayace Allah baiya baiwa mai wuka nama in da nice cikin wannan daular da sai na taki uban kowa inci mutuncin talaka kuma in kwana lfy amma kashhhh... sai gashi a lokacina babana teacher ne wanda hakan yasani a damuwa domin kuwa makarantar yan masu naira nake zuwa har kunyan gidanmu nake kuma ......
Hajiya Fatima tace habaa hajiya da kanta kibar bata yawunki indai akan ustaziya ce domin kuwa ko sauraranki bazatayi ba
Kinga da ace a Nigeria na haifeta kuma da ace tiyata akamin toh da bb abinda Zai hanani cewa an chanzamin yarinya
Aneesa kam sai jinsu take domin kuwa idan sabone tariga da ta saba dajin irin kalsamannan nasu mara dadi saidai babu yanda ta iya dasu tunda iyayenta ne a kullum addu'a take masu akan Alah shiryesu niko nace Ameen
Shin wacece ANEESA????
Kubiyoni don jin cikakken.......
Love u olπ
π©π»⚖ANEESA YAR PRESIDENTπ©π»⚖
Na Hannatu Dada Kuta
π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬
wannan page din nakune YAN GROUP DIN RAYUWAR LEEMAT Allah bar kauna πππππ
03
Wacece Aneesa?
Aneesa Abbas Abdullahi shine cikakken sunarta diyace a wurin Alhaji Abbas mutan Niger state amma a Abuja sukeda zama Alhaji Abbas hamshakin mai kudi ne wanda sunanshi ya shahara a kasashe da dama dan siyasa ne babba wanda aduk inda aka kira sunanshi sau 1 toh fa ba a kumawa domin kuwa sananne ne na karshe.....
matarshi 1 Hajiya Fatima Dada Kuta wacce akafi sani da TIMABBAS dukkansu gwarawa ne kuma gwarin shiroro ne soyayya ce mai karfi a tsakanin ma auratannan biyu wanda hakan ya sanyasu hada sunanyensu gu 1 Fatima da Abbas sai suka maidashi TIMABBAS babu wanda bai san masoyannan 2 ba
lokacinda suke koyarwa a wani makarantar matar aure dake SHIRORO LOCAL GOVERNMENT abu kamar wasa dai har manya suka shigo tsakani bayan an daura aurensu ne Allah ya albarkancesu da yaya 2 Abdul-Basit da Aneesa ana haka sai Alhaji Abbas yashiga siyasa Allah yabashi sa a yacinye zabenshi a karo na 1 inda yafito takarar House of Assembly daga nan ne yakuma fitowa na House of rep sai yanzu da yake neman shugaban kasa dukiya kam ba a magana domin kuwa ya tarasu abin sai wanda yagani ga boutique nan na gani a fada daya budema Hajja Fati wannan kenan
Cigaban Labari
Hajiya Fatima tace Ustaziya bismillah zo muci abinci sannan ki hau sama ki huta in yaso daga baya kyayi wa azin naki da kika saba ba musu Aneesa ta mike sai kan dinning wasu yan mata ne sunsha uniform jiki na rawa suka bubbude warmers dinda ke kan dinning table din Aneesa ta sakarwa da daya daga cikinsu smile kana tace da ita haba Aisha Aneesa ce ke zaune anan fa ba .... Hajiya Fatima ce ta iso da mukarrabanta hajiya Rahma ta kwashe Aisha da wani wawan mari wanda ya firgita kowa kana tace dan kutuman bu........ mu tsaranki ne ko kuwa Anee din tsararkice da zaki kura mata ido harda murmusawa dan Ubanki ko slippers din Anee ya isa ya ciyar da ke da danginku gabaki daya shegiya kawai nifa na tsaneki tun ranarda nasakaki a idanuwa Allah kadai yamasani ko me kika bawa diyarmu da take ji dake kamar wata class dinta Aneesa kam ji tayi ba dadi hakan yasata ta mike dan bazata iya jure ganin rashin mutuncinda Hajiya Rahma kema Aisha ba kawai saboda dan ta tsaneta ba sannan bazaka ce hajja Rahma tabaka kwakkwaran dalilin tsanan Aisha datayi ba tabaka ba sai dai kaji tana zubo maka lbrin da bakai ba gindi.......
Hajiya Fatima tace......
Love u allπππ
π©π»⚖ANEESA YAR PRESIDENTπ©π»⚖
Na Hannatu Dada Kuta
π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬
4
Hajiya Fatima tace haba hajja rahma meyasa kin kk ma Aisha haka ne ko kinsan munfi yarda da aisha acikin gidannan akan sauran yan aikin domin aisha ta daban ce dan Allah kirage tsanarda kike mata yanzu ji yanda kk sa anee dear tayi fushi taki cin ma abincinda na hana kowa ya hada mata nida kaina nashiga kitchen na hada mata dan welcomin dinta gaskiya hajja rahma banji dadin abinda kk yiba hajja rahma ko ko ajikinta sai gyara zama da tayi dan kwasan gara
Hajiya fatima ta maida kallonta gun Aisha da taketa zubda hawaye tace Aisha yi hkr kinji Aisha tayi murmushin karfin hali kana tace bakomai Hajiya sannan tajuya da nufin barin wurin hajja rahma tace ke dan uban.. wa kk so yayi servin dinmu? Nan da nan aisha ta juyo ta......
Hajiya fatima tace Aisha diba abinci ki kaima Anee Dear daki ki rarrasheta kuma ki nuna mata komai ya wuce Aisha tayi smile nan ta diba abinci ta dauki juice da cup a tray takama hanyar dakin Aneesa
Tana isa tayi sallama jin muryar Aisha yasa Aneesa ta saki smile kana amsa sannan tace shigo abinki sister Aisha tashiga Aneesa na kallonta suka hada ido sai smile suka sakarwa juna Aisha taje ta ijiye tray din a saman gadon Aneesa
Aneesa tace Sister kiyita hakuri da hajiya rahma domin kuwa..... Aisha ta katseta dacewar ai yariga ya wuce dan haka yanzu kici abinci Aneesa ta rungumi Aisha na wasu yan seconni sannan ta saketa kana tace wallahi Aisha ina matukar jinki ajikina kamar yar uwata ta jini Aisha ta murmusa tace nima haka nake jinki sister na ta kaina
Nan Aneesa tamike taje ta dauko spoon ta ce ma aisha suci tare ba musu suka fara ci idan ka gansu gwanin sha awa wannan kenan.....
Koda suka kammala Aneesa ta hana aisha fita tace saidai suyi fira ai kuwa haka akayi fira suketa yi har barci barawo ya kwashesu basu suka farka ba sai after 2 da sauri Aisha ta mike ta hau hada plates dinda sukaci abinci Aneesa tace sister ai kya bari kiyi sallah ko kafin ki fita Aisha tace toh shikenan tashiga bathroom ta dauro alwala tafito tana jiran aneesa dan suyi jam'i Aneesa na fitowa nan sukayi sallah bayan sun idar Aisha tace sister ina bakin ciki a duk lokacinda kika koma makaranta kinsan meyasa ?
Aneesa tace aa sai kin fada sai Aisha tafara hawaye tace saboda aduk lokacinda kk tare dani sai inji ni kamar ina aljanna amma idan bakya nan ina shiga damuwa har wani lokacinma sai inji inama ace mutuwa ta daukeni dan in huta........
Takarashe maganar tana kuka mai tsumar da zuciya Aneesar ma hawaye take batasan lokacinda ta rungumi Aisha ba sai kuka suketayi dukkansu biyu babu mai cema daya bari suna cikin hakane hajiya Fatima tashigo mutuwar tsaye tayi cen tace................
✍π»By LEEMAT
Love U Olπ❤ππ
π©π»⚖ANEESA YAR PRESIDENTπ©π»⚖
Na Hannatu Dada Kuta
π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬
UMMU SAFWAN HAUSA NOVELsπ
5
Cen tace wai ku kenan kullum bakuda aikinyi sai kuka kamar wayanda aka aikomawa da sakon mutuwa?
Aneesa tace mom ina tausayama Aisha mom dan Allah kimaida Aisha yarki kisota kamar yanda kk sonaππ»π
Shiru hajiya fatima tayi nadan wasu seconni kana tace Aisha maza kije ku kammala aikinku domin kuwa yanda ake biyanki haka suma ake biyansu
Aisha ta share hawayenta nan ta juya da niyyar fita har ta gifta hajiya fatima sai ji tayi anriko mata hannu chak ta tsaya bata juyo ba jin muryan hajiya fatima ne yasata juyowa dan ganema idanuwanta abinda kunnuwanta suka jiyo mata smile hajiya fatima ta sakar mata kana tace Aisha?
Aisha tace na am hajiya ta tsuguna a wurin hajiya tace mata Aisha sanin kanki ne duk fadin gidannan babu wanda na yarda da ita domin kuwa halayyanki daban yake dana saura aisha inaso kisani ina kaunarki sosai saidai hajja rahma ta tsaneki bansan dalili ba amma karki damu Allah zai sa tasoki wata rana
Kiyita hkr da halayyarta kinji sannan inason in sanar dake cewar zan maidaki makaranta Aisha kuka tafarayi na farin ciki tanata godiya da addu'oi hajiya ta dagotatana kada mata kai alamar aa dinnan ganin taki yin shiru ne yasa Aneesa tazo ta rungumeta nan hajiya fatima ta rungumesu su biyun tanata faman kwarara masu albarka cendai hajiya tace masu suje shan iska a waje ba musu suka fita Aisha kam dawowa tayi ta tsuguna kana tace hajiya wane aiki ma kk ce inje in kama?
Smile hajiyar tayi kana tace ni daga yau ki daina kirana da hajiya ki rika cemin mom kinji toh kawai aisha tace sannan hhajiya tace daga yau kin daina yin aiki makaranta kawai zaki rinka zuwa cikin kunya da jin dadi aisha tamike tana godiya sannan tace Allah dada budi mai albarka mom dina aguje tafita
Murmushi hajiya tayi dan har cikin kasan zuciyarta taji dadi ashe duk abinda suke yi duka a kunnen hajja rahma
Niko nace babban magana
Bayan 2days halayyan Aneesa ya fara canzawa kullum yakasance batada aikinyi sai wulakanci da musgunawa al'umma ga rashin kunya abin duk ya daurema kowa kai
Hatta mom dinta ta kasa gane kanta Aneesa abinnata sai cigaba yakeyi kullum abin mamaki kuwa shine tafi tsanar Aisha
Kwata2 bata kaunar ganin Aisha a rayuwarta ita kuwa Aisha kullum cikin damuwa take domin kuwa ta dauki Aneesa tamkar jininta ana cikin haka ne wata rana.......
✍π»by leemat
Love u allπππππ
π©π»⚖ANEESA YAR PRESIDENTπ©π»⚖
Na Hannatu Dada Kuta
π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬
UMMU SAFWAN HAUSA NOVELSπ
Wannan page din nakine HAJMA Dear nagode da addu'arki da fatan Alkhairi gareni kina raina Allah bar kauna ππ❤
6
Wata rana Aisha tashiga dakin Aneesa domin yi mata nasiha sannan ta tambayeta laifinda tamata dahar yasa tafi tsanarta acikin duk masu aikin gidan duk da Hajiya Fatima ta hana Aisha yin aikace2 amma bai sa ta daina kirga kanta acikin yan aiki ba
Tashiga dakin da sallamarta Aneesa na kallonta amma bata ce mata komai ba sai amsa sallamar datayi
Aneesa na kallonta harta zauna kana tace sister na takaina nazone in tambayeki laifinda namaki kike fushi dani kuma kika tsaneni haka kamar ba keba dan girman Allah ki sanar dani abinda namaki idan kuma bazaki iya sanar dani ba toh kiyi hakuri kiyafemin
Nayi maki alkawarin zan kiyaye koma menene indai bai sabawa mahaliccinmu ba sannan inaso inyi maki nasiha akan abinda kikewa mom agaban kowa kisanifa itace ta dauki cikinki wata 9 tayi nakuda batasani ba ko zata rayu ko zata mutuba a haka har Allah ya sauketa lfy har ta haifeki bayan kin fito duniya tayita shayar dake idan kk yi kuka batada nutsuwa idan kkyi barci tayita gadinki idan bakida lfy.....
Aneesa ce tayi maza ta katseta dacewa dalla malama ya isa hk kece uwata ko kuwa ubana da zaki tasani a gaba kina tofamin yawun bakinki maza kifita a dakina kafin in.....
Aisha tace kafin ki kasheni ko dan iya abinda zaki iyamin kenan amma inaso kisani wallahi bazan fita ba har sai naji dalilanki nayin hakan
Dariya aneesa tafarayi kamar wacce ta zauce Aisha kuka tafarayi ta tsuguna a gaban ta tana kuka tana fadin sister dan Allah kifadamin abinda nayi maki ok idan bazaki fada min ba dan Allah ki daina yima mom rashin da a Aneesa tayi shiru ganin Aisha tana kuka hakan ya karya mata zuciya ta tallabo Aisha ta rungumeta itama tana kukan tace sister yi hkr kibar zubda hawayennan haka wallahi nima bansan dalilina nayin wayannan munanan abubuwa ba wani lokacin saidai in tsinci kaina cikin aikata hakan Aisha kiyi hkr ina kaunarki ki yafemin bazan kara ba
Hajiya fatima da akai komai akan idonta ne tashigo tana smile tana tausayama diyarta kana tace Alhmdllh Allah nagode maka dukkansu suka juyo suna kallonta Aneesa tayi maza taje ta tsuguna a gaban mom tana kuka tana fadin mom ki gafaceni mom bansan meke damuna ba mom ina bukatar addu'arki Hajiya fatima ta dagota tashare mata hawayenta kana tace ni bakimin komai ba a kullum addu'ata shine Allah shiryeki ya karemin ku da al umman musulmi baki daya Anee dear na yafe maki
Godiya suka shiga yimata kana tace ki nemi yafiyar Aisha domin kuwa ita kikafi musgunamawa rannan har pp soup kika zuba mata a fuska saida aka kaita asibiti
Sannan bayan wannan kika shiga har dakinta kika hada mata electric sannan kika kirata akan tafito ta rakaki koda tafito tana sa hannunta akan kofa sai wutan yajata saida tasuma dan ma Allah yayi tanada karan kwana shima saida tayi kwana 2 a asibiti haka kika kone mata books dinta gabaki daya harda uniforms dinta sannan shekaran jiya jiyannan kika zazzageta harda iyayenta da suka rigayemu gidan gaskiya bata amsa ki ba hakan yasa kikaje kitchen tana aiki kika zuba mata ruwan omo ajiki koda tayi kokarin fitowa ta zame gashi har yanzu tana fama da kafarta na hagu Y Aneesa y????
Aneesa zubewa tayi a wurin tana kuka mai tsumar da zuciya kana tace acikin kukan mom wallahi bansan ma nayi ba mom sanin kanki ne ko makiyi na bazan iya aikata masa haka ba bare sister na wacce nake ji da ita fiye da kaina Aisha ta tsuguna tana goge mata hawayenta tana fadin nima nasani sister bayin kanki bane amma Karki damu Allah yana tare damu kuma babu wanda ya isa ya rabamu sai Allahn da ya hadamu
Dan haka ki daina kuka nina yafe maki Allah yafe mana baki daya Ameen mom ta amsa sannan tace Allah maku albarka ameen suka amsa nan Aisha tace sister tashi kiyi wanka sannan kifito inada suprise maki a palo
Ba musu ta tashi tashige bayin Aisha da Hajiya Fatima suka fito Aneesa ce tafito ta saka jallabiya brown ba karamin kyau yamata ba tana sakkowa Aisha tace wow mashaa Allah sister kinko kalli mirro kuwa?
Dan bugun wasa takaima Aishan nan suka shiga dariya Aisha taja hannunta har zuwa kan dinning tayima Aneesa nuni data zauna ba musu ta zauna nan tafara bude first warmer ganin favourite dinta yasa Aneesa darawa kana tace wowww sister Aisha Allah barmu tare ngode da kulawarki gareni wannan pp soup haka
Aisha tabude na 2 shima lafiyayyen fried rice ne aciki sai kamshi ke tashi duk ya gauraye palon ina gefe rike da ✍π» amma inata hadiyan yawu ina fadin inama ace zan iya ajiye ✍π» domin nima in taya Aneesa kwasan gara π
Hajiya sai kallonsu take cikeda so da kauna a haka suka zauna suka ci suka sha bayan sun kammala ne suka kintsa wurin tas sannan sukayi ma hajiya Fatima sallama cewar zasu fita shan iska addu a tamasu suka tashi suka fita motoci ne gudag 4 suka bi bayansu har suka je suka dawo a ranar kam shakuwa ne mai karfi tqshiga tsakaninsu abin sai wanda ya gani domin kuwa ranar a dakin Aneesa suka kwana
Bayan kwana biyu saiga hajja rahma ta kawoma Hajiya fatima ziyara nan tayita nuna farin cikin ganin Aneesa da Aisha saidai ita Aisha taki sakewa da ita domin abin har mamaki yake bata ganin yanda hqjja rahma take nuna mata so yau
Zuwa yamma hajja rahma tawuce dama tazo sallamar Aneesa ne dazata koma skul domin kuwa har sayayya tamata washe gari Aneesa takoma skul dama Abu zaria take tana karanta bio/chem Aisha har zaria taje rakata tayi kwana 1 sannan tadawo koda zata dawo saida sukaci kukan rabuwa da juna na wasu yan lokaci Aneesa ta dauki shawarda Aisha tabata kan ta bude shago a zaria ko a minna hakan kuwa akayi ta bude shago a minna babba na indian dress da designers bags harda classic shoes babban boutique ne ya hadu iya haduwa dama ana 2weeks zata koma skul sukaje itada Aisha suka ba wata kanwar Hajiya fatima kudi Hannatu da cewar ta tayata saro kayayyaki lfyayyu haka kuwa akayi nan tasa sunar shagon Tripple A classics & designers
Ma ana Aneesa Aisha Abbas AAA
Sannan tasa Aisha a managing director na shagon haka ta nemi tailors tazuba acikin shagon shago kam duk wanda yashiga bazaiso fita ba sbd tsabar haduwar sa domin kuwa ko kofar shiganta ma abin kallo ce
Aneesa ba wanda bai santa a makarantar ba domin kuwa tana taimako sosai hakan yasa kowa yasan da ita hatta estate din mahaifinta kowa ya santa kamila ce bata kula maza kuma mai gadin da matarshi ta daukesu kamar iyayenta ana haka bayan satinta 1 da komawa ne ..............
✍π»by Leemat
Love U Ol
π©π»⚖ANEESA YAR PRESIDENTπ©π»⚖
Na Hannatu Dada Kuta
π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬
UMMU SAFWAN HAUSA NOVELSπ
Wannan page din nakine Habibaty MUM MUHIBBAT π Allah bar zumunci da kauna jinjina da godiya agareki sweety I L U so dearly ππ❤ππ»ππ»ππ»ππ»
7
Wata rana taji kamar ana kiran sunanta lokacin tana cikin part dinta sai taki amsawa aka kuma kiran sunarta a karo na 2 nan ma taki amsawa a karo na 3 ne taji murya kamar na matan mai gadin estate din ai kuwa sai ta amsa da na am mama ina zuwa
Kamar da ta sani karta amsa ai kuwa nan taji kamar ance fita abinki da gudu tafito daga ita sai wando 3qrter da yar karamar riga ajikinta ko kan ta isa bakin gate baba mai gadi yariga ya hangota hakan yasashi mikewa yana fadin subhanalillahi yar Albarka lfy kk fito babu ko kayan kirki ajikinki......
Bata kobi ta kanshi ba tana kokarin bude kofa tafita ne dayaga da gaske take kuma baida karfin hanata hakan yasashi yi mata tsawa sannan ya dafata ai kuwa ihu ta sakar wanda yasa duk aka firfito gata sai wani huci take kamar kumurci sai hararan baba mai gadi take amma ba daman fita
Isowar mutane ne yaba baba mai gadi bakin magana yace ma matarshi da wata mata ku kaita ciki Aneesa tace kar wacce ta tabani mutane suka fara tambayar ko lfy yasa tayi ihu hk????
Aneesa tace lfy ta lau kuce yabarni in fita babu ruwanshi dani mama tace subhanalillahi yar albarka lfy hk wani wawan harara Aneesa tamata kana tace ina lfy fa mijinki ya hanani fita nan mama tagane da matsala kallon mijinta tayi shiko yace idan baki koma cikiba zan maki abinda bazaki manta daniba Aneesa tace kayi Allah kabarni in fita ai kuwa ya bude kofar sannan yace fita mugani kasa fita tayi jama'a sai kallon ikon Allah suke dan wannan ba dabi'un Aneesa bane sa insa dana gaba da ita ba
Baba mai gadi yace maza kafin in rufe idona in budi ki koma ciki inba haka ba ai bata tsaya jin abinda zai fada ba da gudu takuma komawa ciki mama ce tabita abaya sannan baba mai gadi yace kubarta kawai asiri aka mata ana son tabi duniya ne saidai duk wanda yake shirin kwasan alhakin baiwar Allah bazaiyi nasara ba kuma sai ya tozarta a idanun duniya
Ameen kowa ya amsa sannan wani daga ciki yace gaskiya yakamata muyita tayata da addu'a domin kuwa Aneesa ta daban ce
Allah yabata lfy ya mayarma duk wanda yake niyyar yimata hk Ameen suka amsa kowa ya koma yana jimamin irin wannan al amari sannan suna mamaki wai ace kamar Aneesa tanada makiya duk taimakonta ga al umma kuma gata bata da girman kai Allah sauwaka niko nace Ameen
Koda Aneesa tashiga ciki sai ta tsinci kanta da tsanar kanta nan tafara bubbuga kanta a bango ganin haka yasa mama ta kwallama baba mai gadi ihu akan yataho ba lfy aikuwa da gudu yataho shiganshi cikin palon Aneesa keda wuya ai kuwa sai ta tsaya chak tana huci ga jini nazuba a saman goshinta baba mai gadi yace ke wai bazaki fita kibar jikin yar talikar Allah bako saina saba maki .......
Aneesa tayi wata dariya sannan tace nifa ba mace bace kuma ma ai bani 1 aka aiko cutar da ita ba munada yawa
Baba yace kunkai ku nawa? Kuma me tayima wanda ya aikoku? Wani dariyar takuma yi kana ta tabe baki tace ina ruwanka da abinda tayi? Kuma waima kai me hadinka da ita ne eh dan bakin ciki
Smile baba mai gadi yayi kana yace lallai kam ina umurtanku da kusan inda dare yamaku in ba haka ba...... cikin sauri tace in ba hakaba sai me?
Me zaka iya yi?
Kaga mufa aikanmu akayi kuma mu 30 ne aka aiko mata kakoga idan kasan wata to bakasan wata ba hahahahhhh ........
Baba mai gadi yace haka kace koh? To muzuba nida ku shge kafasa.....
Tukunama me sunanka?
Cikin gadara yace sunana duna 6aleri subhanalillahi kaiba musulmi bane cikin fushi yace ban saniba dan rainin hankali kawai hannunshi ya daura kan Aneesa wani irin wahalallan ihu tayitayi cen tazube a kasa nan tafara atishawa
Mama kam banda kuka babu abinda takeyi duk tausayin aneesa ya kamata baba yafara bata hkr akan tayi shiru Allah zai kare masu Aneesarsu Ameen mama tayita amsawa da nan tamike taje ta debo ruwa mai dan zafi tazo ta gogema Aneesa jininda ya bata mata fuska bayan ta kammala ne ta daure mata wurin da bandeji baifi 10 mins ba Aneesa ta fara bude ido ganin mama tanata faman share kwalla ne yasata mikewa jin kanta namata zafi ne yasa tasaki yar kararda ya dawo da hankalin mama kanta Aneesa tace mama kaina zai fashe mama zan mutu .......
Rufe mata baki mama tayi kana tace Aneesa Allah yana tareda mai gaskiya kuma inshaa Allahu bazasuyi nasara akanki ba
Aneesa tace suwaye mama?
Mama ta bude baki kenan zatayi magana Aneesa ta..........
✍π»by Leemat
Love U allππ❤
π©π»⚖ANEESA YAR PRESIDENTπ©π»⚖
Na Hannatu Dada Kuta
π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬
UMMU SAFWAN HAUSA NOVELSπ
Wannan page din nakine my sweety MUNEERA na jinjina maki kuma ina mai alfahari da samun kamar ki a matsayin besty na Dear I ❤ U π
8
Aneesa tace mamana halan hauka nafara koh? Shiru mama tayi Aneesa ta mike ta dauko wayarta tazo ta zauna kusa da mama nan tashiga dialing number Hajiya Fatima ringin 2 yayi aka dauka Aneesa da sallamarta a dayan bangaren kuwa aka amsa sannan tace mom ina bukatar addu'arki fiye dana da hankalin Hajiya fatima ne ya tashi kana tace lfy?
Aneesa tace lfy ba lfy ba mom nidai kuyita tayani da addu'a mom tace toh shikenan Anee Dear inshaa Allahu zamuyita yimaki addu'a yanzu ma zan sanar da daddynku Aneesa tace ohhh dad yana gari ne eh mom tace mata nan Aneesa tace bashi mu gaisa daddynda tunda suka fara waya yake jinsu sai yace bazan karba ba kice mata nayi fushi tunda bata tunawa dani sai momminta jin haka yasa aneesa ta katse wayar tana smile nan tayi dialing number daddynta bayan ya dauka suka gaisa nan suka hau hira saida suka ci kusan 1hour sannan sukayi sallama kiran number yayanta tayi wato Abdul basit yana dagawa yace yar my queen, my precious little sister smile aneesa tayi kana suka gaisa nan shima take rokonsa daya taimaka mata da addu'a toh yace mata sannan suka hau hirar rayuwa
Saida sukayi mai isarsu sannan sukayi sallama bayan Aneesa tayi mashi alkawarin kai mashi ziyara a cen inda yake karatu a U.S.A next week yaji dadi yace mata Allah kawota domin kuwa yaji kewarta
Nan takira Aisha maganar dai duk 1 ne a tayata da addu'a Aisha ta shaida mata cewar tayi mummunar mafarki akanta saidai bata sanar da ita komai akan mafarkinba nan tacema Aneesa gobe monday su dau azumi sannan su rage barcin dare surika yin nafiloli Aneesa tace toh siater Allah shige mana gaba Ameen Aisha ta amsa nan sukayita hira mama kam na zaune sai faman binta da kallo taketayi sannan tana ayyanawa acikin ranta cewar hardani za ayi azuminnan da nafilan dare wallahi dan bazan taba bari a cutarmin dake ba Yar albarka nan tayi smile wanda yasa aneesa tambayarta nan tacema aneesa bkm kawai tana murnar ganinta cikin nishadi ne
Washe gari Aneesa,Aisha,Mama da Baba mai gadi suka dauki azumi Aneesa ce tafito daga part dinta Zuwa garage tana isa bayan ta bude motar ta tayi bismillahi kafin ta shiga ta zauna idonta ne yakai gun dayan motar ta wani layane baki wul dashi da sauri tafito tana kiran sunan Allah jikinta har kyarma yake tace Baba taho kagani baba mai gadi da wuri ya iso wurin harda matarshi da batason abinda zai taba lafiyar Aneesa ta biyo bayanshi
Yana isa Aneesa ta nuna mai layar nan yaje kusa da layar ayi addu'oi ya tofa nan layar tafara hayaki mama kam wannan al amari yafara bata tsoro sai tambayar kanta take waishin me Aneesa tayi ne da ake neman salwantar da rayuwarta haka yarinyarda babu ruwanta yarinyarda take girmama nagaba da ita.........
Aneesa ce ta rungumeta hakan ya dawo da ita daga tunanin da take Aneesa kamar zatayi kuka tace mama waishin wa na batawa rai ne da bazai sanar dani ba in rokeshi gafara ba sai dai yana kokarin.....
Baba mai gadi yace yar Albarka koma wayeshi toh hakika yana wasa ne da rayuwarshi domin kuwa Allah bazai taba bashi sa a akanki ba
Shiga motarki kiwuce makaranta abinki hankali kwance Allah natare dake mama takara dacewa indai har muna raye toh inshaa Allahu sai inda karfinmu ya kare
Aneesa tace nagode baba nagode mama Allah barmu tare suka amsa da ameen haka aneesa tashiga mota tawuce makranta bayan tafiyarta ne mama tace a gaskiya malam yakamata ................
✍π»Leemat
I L U olπππ
π©π»⚖ANEESA YAR PRESIDENTπ©π»⚖
Na Hannatu Dada Kuta
π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬
UMMU SAFWAN HAUSA NOVELSπ
Wannan page din nakune masoyan asali yan group din ANEESA YAR PRESIDENT ina ❤ ku irin sosai sosai dinnan Allah bar kaunaππππ»
9
Yakamata musan abinyi tun kafin a cutar mana da Aneesa domin kuwa wallahi nikam sai inda karfina ya kare indai akan Aneesa ce Baba mai gadi sai kallon matar naahi yake shakka babu yasan sun shaku da Aneesa sannan kuma shima yasani harga Allah sai jin aneesa yakeyi kamar jininshi shima kuwa koda zai rasa rayuwarshi ne dan taimakawa Aneesa he's ready kai kaji soyayyar gaakiya Allah hadamu da masoyan gaskiya
Ameen .........
Mama tacigaba da cewa malam kaga Allah bai taba bani diya macebako?
Sai gashi Allah ya albarkanceni da haduwa da Aneesa tun ranarda nasanyata a idanuna nafara jin dadi domin kuwa nasani Allah ne ya hadamu nakuma ci al washin maida Aneesa diyata tilo sai gashi Allah cikin ikonsa yasa Aneesa ta daukeni tamkar mahaifiyarta sai yau in wayi gari inga wani banza cen na kokarin salwantar min da rayuwarta sammmm.....Allah bazata sabu ba
Baba yace ki kwantar da hankalinki inshaa Allahu babu abinda zai sameta domin kuwa batada hakkin mai kokarin cutar da ita dan haka muci gaba dayimata addu'a Allah zai kareta Ameen mama ta amsa sannan ta mike tana fadin bari inje in debo kayayyakinta in goge mata su kafin ta dawo baba yace kedai ba kullum tana hanaki ke kuma baki bari bako?
Mama tace toh baji ikon Allah mutum da diyarshi ace wai kar ya taimaka mata bayan tanada ladabi da biyayya kaga nidai sai nayi mata gugan in kuma yi mata wanki in akwai masu dauda murmushi Baba ya sakar mata kana yace toh masu diya kardai ki manta nima dai diyata ce kuma yar albarka tace mama bata amsa mashiba tayi wucewarta
Aneesa ta isa makaranta tayi parkin amma taki fitowa sai faman tunani taketayi tana tambayar kanta dacewar ni Aneesa wa na batawa rai da har yake nemar cutar dani ni Aneesa wa..... bugun glass dinta da akeyi ne ya dawo da ita daga tunaninda take Adama ce tsaye tana smile itama Aneesar smile din ta mayar mata dashi nan tabude tafito Adama tace Dear yau kin danso kiyi latti fa Aneesa tace hmmm kedai bari kawai abin ba acewa komai
Haka dai sukayita hira har suka shiga class shin wacece Adama?
Adama Uwaisu shine cikakken sunanta yarinyace fara kyakkyawa ga hankali da nutsuwa tunda tazo makarantar bata taba yarda tayi kawa ba sbd yanda suke su talakawa ne hakan yasa tarike matsayinta bata shiga tsabgar kowa abinda yakaita makaranta shi kawai takeyi ta dawo gida dama su 5 ne a wurin iyayensu Rumaisa'u,Umar,jibrin wanda suke kiranshi da Abbati sai ita Adamar sai sharifullah
Duk da su talakawa ne hakan bai hanasu karatun boko ba mahaifinsu yana iyaka kokarinsa akansu haka ma mahaifiyarsu Amina itama tana nata kokarin dan ganin sun samu in gantacciyar rayuwa
Haduwarsu da Aneesa kuwa daga Allah ne domin kuwa ko kadan ba ajinsu daya ba saidai dayake Aneesa batada girman kai hakan yasa suka zama kawayen juna
Ranarda Aneesa taje ganin lecturer dinsu nan taga Adama a tsugune tanata kuka tana rokonshi akan ya kara mata lokaci zata biya kudin nan yayita mata koran kare hakan ya batawa Aneesa rai nan ta tallabo Adama take tambayarta bayan ta sanar da ita ne tace yanzu sir akan 3k kake mata wannan wulakancin
Shiru yayi dan yasan wacece Aneesa nan yashiga bata hakuri bude handbag dinta tayi taciro bandir din 1k tamikama Adama sannan ta zari kudi tamikamawa lecturer n yana kirgawa yaga 6k ne yace hajiya Aneesa 6k kika bani instead of 3k budan bakin aneesa sai tace sir ka rike sauran dan naga alamar....... kome ta tuna kuma oho sai tayi shiru nan taja hannun Adama suka fito har sunkai bakin kofa sai tajuyo tace saura kuma kaki yimata abinda yadace nan sukayi ficewarsu suka barshi cikin murna dama ranar ko sisi baida
Koda suka fito Adama tace yar uwa ga kudinki nagode tunda kin biyamin Aneesa tayi smile tace sister karki damu ki ajiyesu incase ko kinada bukatar wani abu
Tun daga ranar suka zama Aminan juna
Cigaban labari Aneesa da Adama sun maida hankulansu gun lecturer daya shigo dama basa wasa da karatunsu ko kadan karfe 11 su Aneesa ne zaune suna hirarsu sai jin ..........
✍π»by Leemat
Love u allππππ»
π©π»⚖ANEESA YAR PRESIDENTπ©π»⚖
Na Hannatu Dada Kuta
π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬
UMMU SAFWAN HAUSA NOVELsπ€
Wannan page din nakane kai 1 masoyina, abin al faharina,jinin jikina,rayuwana,farin cikina MUHAMMAD LAWAL BONSAYπ miji nagari Allah barmu tare,Allah karemu da sharrin makiya Allah dada hada kawunanmu da dankon soyayya, kaunarka ta mamayemin zuciya I ❤ U so dearly ππππ
10
Sai jin murya sukayi daga sama anyi masu sallama ai kuwa adama ta juyo itako Aneesa ko ajikinta saidai ta amsa sallamar batareda ta juya ba
Adama tace lfy haka mallam ta kanmu?
Shiko yace lfy amma ba lau ba dan Allah ina iya zama Adama ta bude baki kenan zatayi magana sai Aneesa tayi maza tace aa bazaka iya zama a nan ba sbd nan wurin mata ne smile yayi sannan yace haba beauty dan Allah fa nace Adama ce tace toh bismillah mana zo ka zauna kallon Aneesa yayi yace kin bani izinin in zauna tabe baki tayi abin dariya ma yabashi Aneesa tace kana iya zama amma da sharadi cikin kaguwa yaji sharadin yace me sharadin tace bazaka damemu ba
Smile yayi yace naji zan kiyaye dan haka ina iya zama?
Kada kai tamai alamun eh dinnan zama yayi nan Yake tambayar Adama yar kawarmu ya sunanki?
Adama tace sunana Adama Uwaisu nan yace wow nyc name tank u tace mai nan shima yace Sunana Ashraf Sudais nan Adama tace sunan da zan sama dana na farko kenan inshaa Allah smile yayi yace Allah baki iko ameen ta amsa
Sunata hirarsu da Adama amma yana satan kallon Aneesa da ko dagowa ta kalleshi batayiba sai faman latsa wayrta taketa yi ya lura tunda yazo gurin bata dago ta kalleshi ba acikin zuciyarshi yace wannan wace irin mutum ce haka nan ya furta gashi na kamu da sonta kullum saita hanani sukuni yau kuwa ga ...... Adama ce tace Ashraf kaida wa?
Ajiyan zuciya yayi yace bkw Adama tace ka kamu da sonta ko?
Ashraf yace kina nufin kinajin abinda nake fada a zuciyata?
Adama tace aa sai dai wanda ka furta a fili
Ashraf yace wallahi Adama na kamune da son wata kyakkyawar yarinya nan yafara describing din Aneesa yana gamawa Adama tace kuma ya sunanta nan yace ban san sunanta ba domin kuwa bata bani daman zuciyata tayi bincike akan sunantar ba amma muddin taba zuciyata izinin binciken sunanta to shakka babu zuciyata zai san sunanta kuma zai sanar dani
Aneesa da take jinsu batasan sanda dariya ya kufce mata ba nan tafara dariya shiko sai faman kallon yanda take dariyar yakeyi ushiryarta mai kyau gata da dimple kai mashaa Allah yarinyarnan tayi a rayuwa Adama ce tace Anee lfy? Bata kulata ba saida tayi mai isarta sannan tace kai amma wannan guy din koh nan ne ta dago idanuwanta ai kuwa karaf idanuwansu suka hade dana juna wani irin abu sukaji ajikinsu gabaki dayansu
Subhanallah aneesa ta furta a fili shima haka maida idanuwanta kasa tayi shiko yace meya baki dariya beauty?
Adama da tariga ta dagosu smile tayi nan tacema Aneesa eh meya baki dariya nan Aneesa tace jin wannan abokin naki daya fadin wai zuciyarshi zatayi searching sunar masoyiyarshi ne yabani dariya dan ban taba ji ba wani dariyar takuma yi
Shima dariyar yayi dan ya dagota tana so tace mai makaryaci amma kuma sbd ganin girman dan adam yasa ta kasa
Nan yace mata eh mana kuma idan kina ganin wasa ne sai inje inyi searching kuma tsab zan gano sunarta smile aneesa tayi kana tace toh bismillah je kayi nasan saidai kaje ka tambayi wasu
Ashraf yace idan kika ganta ko toh ko ke saikin bata sunarda zaiyi matchin da ita bare ni masoyinta
Aneesa tace toh kaje ka sanar mata abinda kk ji mana game da ita nan yace toh ai bazan iya ba sbd ban taba yin hakan ba
Wani kallon tuhuma Aneesa tabishi dashi Adama ce ta katsesu nan sukaci gba da hira har lokacin shiga lectures dinsu Aneesa yayi nan sukayi sallama da juna Ashraf sai ji yakeyi kamar yabisu amma ba dama karfe 4 daidai suka fito nan suka shiga motar Aneesa daman tunda suka hadu da juna itace ke dauko Adama tazo ta sauketa a gida wani lokacin ma tare suke zuwa makaranta A motar Aneesa
Aneesa takai Adama har kofar gidansu Ashraf kuwa na biye dasu nan Adama tafita tayi cikin gida sannan Aneesa ta juya tayi hanyar gida itama ganin kamar mota na binta a baya ne yasa taja burki ta tsaya Ashraf na ganin haka sai yayi kamar ba ita yake biba har yazo yawuceta kasancewar tint glass ne ya hana Aneesa ganin fuskar wanda ke ciki
Nan tafito ta sayi su fruits sannan taja motarta shiko ashraf koda yayi gaba kadan nan yayi parkin ganin wucewarta ne yasa shima tada motarshi yabita ganin ta tsaya a Alhaji Abbas Estate ne yasa yayi smile a zuciyarshi yace woww lallai dole yarinyarnan taja aji
Baba ya bude mata gate tashige bayan tayi parkin ne ta fito da su fruits dinda tasayo tazo ta mikawa mama bayan ta gaishesu kamar yanda ta saba nan tayi wucewarta part dinta dan yin ibada tana shiga ........
✍π»by LEEMAT
LOVE U OLπ❤πππ»
π©π»⚖ANEESA YAR PRESIDENTπ©π»⚖
Na Hannatu Dada Kuta
π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬π³π¬
UMMU SAFWAN HAUSA NOVELSπ€
Wannan page din nakune jinin jikina yan uwa nagari Aunty Fatima Dada Kuta ❤
Aunty Hasiya Antiwoπ
Aunty Safiya Dada Kutaπ
Aunty Aisha Dada Kutaπ
Aunty Hamida Dada Kuta π
Ina yinku irin sosai sosai dinnanπ❤
11
Tana shiga da sallamarta daki tanufa ta rage kayan jikinta shiga bathroom tayi ta watsa ruwa ajiki sannan ta dauro alwala tafito jallabiya tasaka da hijab tayi sallah a nutse
Tana idarwa tayi kira ar Al Qur'ani mai girma ba ita ta daga daga sallayarba sai 6pm nan tayi Addu'oi tashafa sannan tafito
A palo ta tarar da mama tana jera fruits a fridge murmushi tayi kana tace mama nida nake kokarin fitowa yin aiki ashe har kin kammala
Smile mama ta mayar mata kana tace yar arziki ai kiyi zamanki ki huta kinga mun saba da wannan aikace2 lokacinda muke aiki a cen gidan senator mansur ai yaranshi har...... Aneesa ce ta katseta dacewar habaa mama baki mantuwa ne? Kusan kullum sai kinyi maganar nan kiyi hkr ai yariga ya wuce yanzu baganinan ba diyar mama ita kadai yar tilon mama da baba murmushi mama tayi kana tace tabbas ina alfahari dake inaji ajikina kamar nina haifeki saboda komai daya kamata yaya suma iyayensu na kyautatawa kina mana kamar mu muka haifeki sannan kina mana hidima dagamu har yaranmu sannan.....
Aneesa ce ta rungumeta tana fadin dan Allah mama kibar fadin haka ku kuka haifeni nice diyarku tilo ina kaunarku sosai mama tace Allah maki albarka Ameen ta amsa
Mama ce tace bara naje na duba mana alala Aneesa tace laaa mama harda alala kika mana eh mama ta amsa mata Aneesa tace yauwa mama natuno yau na sawo maki awara nan ta bude jakarta taciro ta mikama mata mama tace inni sa imun habibaty
Wangale baki Aneesa tayi cikeda mamaki kana tace mama kema azumin kike?
Eh mama ta amsa mata Aneesa tace Allah karba ameen mama ta amsa mata mama tafito Aneesa kuwa na biye da ita a baya suna hira har suka isa part dinsu baba mai gadi suka shiga tare da mama bayan ta duba alalanda ke kan stove Aneesa tace mama........
0 comments:
Post a Comment