Page 16
...............Napep na samu na tare nai tafiyata gidan Inna zainabu. Can nai zamana mukasha hira da Lawusa da a yanzu muke ɗasawa har bayan sallar isha'i sannan na nufo gida.
★★★★★
Bayan an buɗe taro da addu'a Uncle Nasir ya fara jawabi kamar haka. “Kamar yanda kowa ya sani mun fara tattaunawa akan maganar zaman Jawaad babu aure a kwanakin baya, har takai mukai masa tayin cikin yaran gidannan ko akwai wadda ya keso, sai dai ya nuna a lokacin zaiyi tunani, tun daga wancan lokacin ban sakeji daga gareshiba, to magana ta gaskiya mun gaji da ganinsa yana yawo a gari haka ana zaginmu, shi kansa bama girmansa bane, ƙannen-ƙannen bayansa ma gasunan duk da iyalansu har da ƴaƴa, yakamata Jawaad kaima kanka faɗa, dan lokaci bawai zai zauna jiranka baneba, kai kaɗai Abdul-aziz ya haifa, zamuso ganin ƴaƴanka a duniya kamar yanda mukasan da yanada rai zai ɗokantu da haka shima. A wannan karon ba shawara muke bakaba, umarnine, shiyyasama mukazo da Alhaji Baba domin ya zama shaida, tare da iyayenka, dolene a wannan karon kayi aure, ka zaɓi mace ɗaya a cikin ƴaƴan gidannan koma fiye da ɗayar mukuma zamu aura maka”.
Jawaad da kansa ke ƙasa yay guntun murmushi domin son ɓoye ɓacin ransa, batare da ya ɗagoba yace, “Uncle ku gafarceni, bazan jaku da nisaba, duk cikin yaran gidannan bazan iya auren kowaba, dan kallon ƙannena nake musu tamkar ciki ɗaya...” da sauri Uncle Uwaisu yace, “Ai tamkar kace, bawai hakan bane, tunda babu ta inda ALLAH ya haramta maka, Jawaad bamason shirme, garama ka zaɓa komu mu zaɓa maka, kokuma ka ɗauki zaɓi na biyu, wato ka maida matarka ɗakinta kuje kuyi haƙuru da juna tunda yarinyarnan ta horu kuma tana sonka”. Yanzu kam kasa daurewa yay saida ya ɗago kansa ya kalli Uncle Uwaisu, kamar zaiyi magana sai kuma yay shiru saboda gargaɗi da Alhaji Baba yay masa da ido, kansa ya maida ƙasa yana sauke ajiyar zuciya.
Uncle Sulaiman yace, “Son!” ɗago kai Jawaad yay ya kalli Uncle ɗin nasa da yake matuƙar so saboda ƙyawun halinsa, yace, “Na'am Uncle”. “Ko Kanada wadda kake sone?”. Ƙasa Jay ya maida kansa yana motsa laɓɓansa, sai dai babu maijin mi yake cewa, Uncle Taheer ya katsesa da faɗin, “Kai muke saurare Jawaad”. Batare daya ɗagoba ya girgiza musu kai alamar a'a. Shiru falon ya ɗauka kowa ya zuba masa idonu, shi kuma yaƙi kallonsu. Mama Zuhurah da bata da yawan magana tace, “To Jawaad ya kakeso ayi kenan? Yanzu kai kafijin daɗin kullum aita zaman meeting akanka akan maganar kaƙi aure, ka rufa mana asiri ka fidda kanka damu iyayenka daga zargi da zunɗen al'umma kaji, ƴar uwarka na sonka, tayi nadamar kuskuren datai a baya, kayi haƙuri a maida aurenku kaji”.
Ɗagowa yay zaiyi magana fitowar Shahudah ta katse masa hanzari, gabansa taje ta durƙusa tamkar yanda Mama Atika da Mom suka kitsa mata, ta fashe da kuka tare da kama ƙafafunsa, cikin gurɓatacciyar hausarta da harshen turancin da tafi ƙwarewa ya cinye tace, “Bb dan ALLAH ka gafarceni, wlhy nayi nadamar abinda na aikata, nakumayi alƙawrin bazan sakeba, na yarda zan haihu maka yara komai yawan da kake buƙata yanzun, idan ka barni mutuwa zanyi wlhy, dan ALLAH ka ceci rayuwata Bb...” hannunta ya ture daga saman ƙafarsa yana hararta, “Kima daina ɓata lokacinki, indai haihuwace bana buƙata daga gareki Hudah, karki damu kije kicigaba da cin moriyar ƙuruciyarki kinji, indai nine kima saka a ranki baki taɓa sanin mai kama daniba dan mun rabu kenan”. Fashewa tai da matsanancin kuka yanzunkam fiye da da, dan har ƙasan ranta kalamansa sun masifar sosa mata zuciya, ta dafe kanta dake juya mata, babu zato sai kawai ganinta ƙasa sukai ta yanke jiki ta faɗi. Gaba ɗaya ƴan falon da suka zuba musu ido suka miƙe, shi kansa Jawaad ɗin kallonta yake, dan ya zata salon iskancinta ne, sai daga baya da aketa jijjigata babu alamar rai tattare da itane ya fuskanci babu wasa a lamarinta, gaba ɗaya falon ya rikice, dan iya ƙoƙari anyi Shahudah taƙi farfaɗowa, Mom sai kuka take da sambatu.
Dole aka kwashi Shahudah zuwa asibiti da gaggawa kuwa, dan wasunsu harsu fidda ran da gaske ta mutu.
★★★★★★★
Tun a gate baba maigadi yake sanarmi
n ai babu kowa a gidan duk suna asibiti aunty Shahudah babu lafiya, hankalina ya tashi sosai, dan haka nai azamar tsayar da mai napep ɗin dake shirin juyawa dan harma ya fara tafiya, shiga nayi na sanar masa asibitin da baba magadi ya sanarmin an kaita. Asibitine mai ƙyau dan na kuɗine, kasancewar bansan ina zan nufaba sai nai kiran aunty Aamilah, saidai bata amsa ba, na sake kira nanma babu amsa, maida kiran nai kan Yah Qaseem, sai da ta kusan tsinkewa sannan ya ɗaga, faɗa masa nai gani a asibitin a ina suke?. Muryarsa a sanyaye yace na jirasa yazo ya shiga dani.
A yanda na gansa kawai na tabbatar akwai babbar damuwa dangane da aunty Shahudah, kasa daurewa nai na shiga jera masa tambayoyi. Amsa ɗaya na samu daga garesa, shine ta farfaɗo, sai dai sun mata allurar barci, sun kuma hana kowa ganinta sai banzan Jawaad ɗin da taketa sambatun kira. Ta bani tausayi matuƙa, dan na sake fahimtar tsananin son da takema Boss.
Duk sai da na gaida waɗanda na tarar a wajen, sannan na tambayesu ya mai jiki, sai dai babu Boss babu dalilinsa a wajen, zama nai kamar yanda suke zaune jigum-jigum, kusan mintuna biyar sai naji ƙamshin turarensa. Ɗago kai nai dan tabbatarwa, karaf kuwa muka haɗa ido dashi, ya dalla mani harara sannan ya ɗauke kansa tamkar baiyiba. Nima janye nawa nai, dan nasan laifina dai bai wuce tafiya bada izininsa ba. Cikin nutsatstsiyar muryarsa dake tattare da alamun gajiya naji yana faɗima Uncles nasa da matansu ya kamata su tafi gida su huta, tunda dai Doctor yace bazasu bari a gantaba har sai zuwa safiya.
Cike da nazari nake satar kallon yanda wasu suke masa kallon harara dajin haushi a kaikaice, amma a zahiri suna amsashi cike da kulawa, sai al'amarin nasu yay masifar ɗaure min kaina, to amma abinda babu ruwanka ai daɗin kallo garesa, dan haka nai ƙasa da kaina kawai ina sauraren mahawarar da suke akan wanda zai zauna ya kwana, ance Mom taje gida Aamilah ta zauna, sai dai ita aunty Aamilah ta tubure akan tsoro takeji ta kwana asibiti, da sauri Salman yace, “Kedai wawuyace Aamilah, to sai wannan yarinyar tazauna ku kwana ai”. Yay maganar yana nunanu. Da sauri Yah Qaseem yace, “Itakuma aikin tafa? Itadai Aamilah da babu inda take zuwa itace ta cancanci kwana da itan”. Shiru kowa yay, sai kuma daga baya wasu sukai na'am da batun Yah Qaseem ɗin, na saci kallon Boss da uffan baiceba, yama ɗauke kansa daga garemu tamkar baisan mimukeyiba, nikam lamarinsa kan bani mamaki wani lokacin gaskiya.
Wata mata da nake ƙyautata zaton cikin matan Uncles ɗin nasune ta kawo shawaran haɗa Aunty Aamilah da ɗaya daga cikin yaran gidansu ɗin da wata dattijuwar mai aiki, akan wannan shawarar aka zauna, dan haka duk sai muka fara shirin tafiya. Har mun fito baki ɗaya Mom tace gaskiya bazata iya tafiyaba, itama anan zata kwana, duk kallonta mukai da mamaki, sai kuma naga tsoro akan fuskokin wasu, dan koni naji wani iri saboda ganin Mom na sharar ƙwalla, nasan yanda ƴan gidanmu ke masifar son aunty Shahudah, hakan ya samo asaline saboda so mai tsanani da Dad ke nunamata kasancewar sunan Mahaifiyarsa taci, sai naji a raina kamar zamu iya rasa aunty Shahudah, duk yanda aka lallashi Mom taƙi aminta da hakan, sai kawai aka barta. jinai wani iri, dan tundafa Mom zata zauna nikaɗaice mace zan kwana a gidan, nima da sauri nace to zan zauna a asibitin, da sassafe sai naje gida.
Harara Yah Qaseem ya dallamin da cewar bazan zaunaba gida zani. Niko na fara roƙonsa akan ya barni, shikuma yaƙi saurarena, kowa kuma yaƙi saka mana baki. Na kalli inda Boss yake tsaye a jikin mota hawaye na gangaromin akan fuska, sarai nasan duk yanajinmu, amma yayi kunnen uwar shegu da kowa, harna yanke ƙauna daga taimakon kowa na tsinkayi muryarsa yana faɗin,
“Ita Aamilah ta fito ku wuce gidan tare mana, dan sunmayi yawa anan tunda Mom zata zauna, na tabbata sai ma'aikatan asibitin sunyi ƙorafi”. Harararsa Yah Qaseem yayi, sai dai baiyi maganaba.
Uncle Nasir ne yay na'am da shawarar Jawaad, dan haka ya aika aka kira Aamilah. Naji daɗin hakan da samun nutsuwa sosai. Daɗin da najine ya sakani matsawa inda yake
nace, “Thanks you Sir”. Banza yaymin tamkar bai jiniba, sai daƙilar waya yake abinsa, na ɗaga ƙafafuna zanbar wajen naji yace, “Uhm”. Kallonsa kawai nai sau ɗaya nabar wajen zuwa motar Yah Qaseem daketa antayomin harara tamkar idanunsa zasu zubo ƙasa.
Tunda muka tafi yah Qaseem keta zabga jarabar da babu wanda yasan kanta, daga ni har Aunty Aamilah da Yah Salman babu wanda ya kulashi, yana gama fakin kowa yay ficewarsa, dama nice farkon fitama nai cikin falo dan banaso ya tsaidani, nayi masifar gajiya wajen hutu kawai nake buƙata. Ina shiga ɗakina na murza key, na zaresu na ajiye saman mirror tare da jikkata dana cire a kafaɗa. Idanuna har lumshewa suke saboda gajiya, haka na daure nayo wanka da alwala na fito, daƙyar na iyayin shafa'i da wutiri na faɗa saman gado, sama-sama ma nai addu'a sai barci.
Cikin barci na ringajin saukar numfashin mutum a jikina, na buɗe idanu a razane ina ambaton ‘Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un’ tabbas a jikin mutum nake, na buɗe baki zan ƙwalla ƙara aka dafe bakin da hannu, cikin wata irin murya da bantaɓa jin mai itaba a gidan ake magana da shafamin jiki, “Bazan iya saduwa dake baƙya cikin hankalinkiba kamar sauran, shiyyasa na zaɓi baki damar farkawa, kiyi haƙuri ki bani haɗinkai cikin sauƙi bilkisu, samunkine kaɗai ya ragema cikar burina yanzun, karki lalatamin tanadina na tsahon shekaru, nai miki alƙawarin zan biki a sannu bazan cutar dakeba kodan son da nake miki, sannan zaki moru da tagomashi mai yawa a gareni saɓanin sauran da basu sami komaiba sai baƙin ciki, tun farko kece tsanin nasarata da na ɗauku dakon jira tsahon lokaci”.
Tsabar tashin hankalin da nake ciki sai zufa nake kwararwa dukda ac dake aiki a ɗakin, jikina wata irin muguwar rawa yake da ɗaukar azababben zafi lokaci ɗaya, gashi ya rufemin baki, hawayenma sunƙi fita daga idona sai zuciyata ke kukan, duk addu'ar da tazomin bakina yi nake da taimakon UBANGIJI na.
اَللَّهُمَّ إِنَّا نَجْعَلُكَ فِي نُحُورِهِمْ، وَنَعُوذُ بِكَ مِنْ شُرورِهِمْ .
“Allahumma inna naj'aluka fee nuhoorihim wana'oothu bika min shuroorihim”.
Ya ALLAH! Mu mun sanya ka a gabansu, kuma muna neman tsarinka daga sharrace-sharracensu.
اَللَّهُمَّ أَنْتَ عَضُدِي، وَأَنْتَ نَصِيرِي، بِكَ أَجُولُ وَبِكَ أَصُولُ وَبِكَ أُقَاتِلُ.
“Allahumma anta 'adudee, wa-anta naseeree, bika ajoolu wabika asoolu wabika oqatil”.
Ya ALLAH kai ne mai karfafa ni, kuma kai ne mataimakina, da karfinka ne nake yin dabarun yaki, kuma da karfinka ne nake kai hari, kuma da karfinka ne nake yin yaki.
حَسْبُنَا اللهُ وَنِعْمَ الْوَكِيلُ.
“Hasbunal-lahu wani'mal-wakeel”.
ALLAH ne mai isar mana, kuma madalla da shi abin dogaro.
اَللَّهُمَّ رَبِّ السَّمَوَاتِ السَّبْعِ، وَرَبِّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ، كُنْ لِي جَارًا مِنْ (فُلاَنٍ)، وَأَحْزَابِهِ مِنْ خَلاَئِقِكَ؛ أَنْ يَفْرُطَ عَلَيَّ أَحَدٌ مِنْهُمْ أَوْ يَطْغَى، عَزَّ جَارُكَ، وَجَلَّ ثَنَاؤُكَ، وَلاَ إِلَهَ إِلاَّ أَنْتَ.
“Allahumma rabba s-mawati s-sab'i wa rabba-l-'arshi-l-'azimi. Kun li jaran min (fulanin) wa ahzabihi min khala'iqika, an yafruta 'alayya ahadun minhum aw yatgha. 'Azza jaruka, wa jalla thana'uka, wa la ilaha illa anta”.
Ya Ubangijin sammai bakwai, kuma Ubangijin Al'arshi mai girma, ka kasance mai tsari gare ni daga wane dan wane, da dukkan rundunarsa daga cikin halittunka kar wani daga cikinsu ya yi gaggawar azaba a gare ni, ko ya ketare haddi, kariyarka ta buwaya, kuma babu abin bautawa da gaskiya sai kai.
اَللهُ أَكْبَرْ، اَللهُ أَعَزُّ مِنْ خَلْقِهِ جَمِيعاً ، اَللهُ أَعَزُّ مِمَّا أَخَافُ وَأَحْذَرُ، أَعُوذُ بِاللهِ الَّذِي لاَ إِلَهَ إِلاَّ هُوَ، الْمُمْسِكِ السَّمَوَاتِ السَّبْعِ أَنْ يَقَعْنَ عَلَى اْلأَرْضِ إِلاَّ بِإِذْنِهِ، مِنْ شَرِّ عَبْدِكَ فُلاَنٌ، وَجُنُودِهِ وَأَتْبَاعِهِ وَأَشْيَاعِهِ، مِنَ الْجِنِّ وَاْلإِنْسِ، اَللَّهُمَّ كُنْ لِي جَاراً مِنْ شَرِّهِمْ، جَلَّ ثَنَاؤُكَ وَعَزَّ جَارُكَ، وَتَبَارَكَ اِسْمُكَ، وَلاَ إِلَهَ غَيْرُكَ " ثَلاَثَ مَرَّاتٍ.
“ALLAHU akbaru. ALLAHU a'azzu min khalqihi jami'an. ALLAHU a'azzu mimma akhfu wa ahdharu. A'udhu billahi lazee la ilaha illa huwal mumsikis samawatis s
ab'i an yaqa'na 'alal-ardi illa bi'izinihi, min sharri 'abdika (fulanin) wa junudihi wa atba'ihi wa ashya'ihi minal-jinni wal-insi. Allahumma kun li jaran min sharrihim Jalla thana'uka wa 'azza jaruka, wa tabaraka smuka, wa la ilaha ghayruka”.
ALLAH shi ne mafi girma, ALLAH shi ne mafi buwaya daga dukkanin halittarsa, shi ne mafi buwaya daga abin da nake jin tsoronsa kuma nake shayinsa. Ina neman tsarin ALLAH, wanda babu abin bautawa da gaskiya sai shi, mai rike sammai daga su ruguzo a kan kasa sai da izininsa, daga sharrin bawanka (ya ambai sunansa), Ya ALLAH! Ka zamo mai tsari gare ni daga sharrinsu. Yabonka ya girma, kuma kaiyarka ta buwaya, kuma alherin sunanka ya yawaita, kuma babu abin bautawa da gaskiya ba kai ba”.
Duk da na rigada na sadaƙar tawa ta ƙare ban fasa karanto addu'oinba ina faɗama ALLAH kukana, koda a wani wajen bana haɗa kalmomin dai-dai saboda ruɗani karantowa nake, wata razananniyar ƙara mukaji a dukkanin illahirin gidan, hakan ya saka koma waye sakarmin baki ya miƙe a firgice kamar yanda nima na samu damar ƙwalla tawa ƙarar saboda firgita da nayi, ɗif naji kunnuwana sun daɗe banajin motsin komai, dukda ɗakin a duhu yake dunɗum, jinai an sake rungumeni an fashe da kuka, yanzunkam a tare muka ƙwala ihu da koma wanene duk da naji jikin ya banbanta dana wancan, ɗakin sai naga yana wani irin juyamin tamkar ina cikin hajijiya, rumtse idanuna nai da ƙarfi na sake ƙwalla ƙarar da ni kaina bansan iyakar ina muryata ta tsaya ba a gidan, daga nan ban sake sanin mi duniyar ke cikiba kuma.
Duk wanda yake a cikin gidan kunnensa saida ya jiye masa ƙara maiban tashin hankali da tsoratarwa da aka ƙwala da farko a wannan dare, wadda taɗauki adadin mintuna biyar kafin ta gushe ihun bilkisu ya biyo bayanta, Aamilah da ɗakinta ke kusa dana Bilkisu ce ta fara fitowa a razane saboda kiɗimar data shiga na tsoro itama, cikin lalube ta afko ɗakin bilkisu batare data saniba itama tana ihun, fitar sautin ihun bilkisu ne ya bata damar isa inda take suka ƙanƙame juna suna kuka maiban tashin hankali. A daidai lokacin da Qaseem da Salman harma da kuku suka shigo sashen suma a razane, dan duk wanda yake gidan yaji ƙarar farko, sannan a yanzu yana jiyo ihun su Aamilah dake nuna alamar tsoratar da sukaice ta gusar musu da hankali suka tsinci kansu a yanayin. Kuku ne ya samu damar kunna fitilar ɗakin haske ya gauraye ko'ina, dukansu kansu Bilkisu sukayi, dan hakan yayi daidai da ɗaukewar numfashinta daga gangar jikinta.
Babu mai iya musalta tashin hankalin da suke ciki a wannan dare, kan kowa ya kulle daga abinda ya faru, cikin ƙarfin hali Salman ya ɗakko ruwa ya miƙama Qaseem dake taya Aamilah jijjiga Bilkisu, bai tsaya yayyafa mataba ya bulbule matashi kawai a fuska, wani nannauyan numfashi Bily ta kawo, sai dai jikinta babu alamun ƙarfi, ta buɗe idanu a hankali ta kalli kowa sai kuma ta maida ta lumshesu hawayen da bata samu yiba ɗazun suna ziraro mata a kumatu masu ɗumi.
Sama-sama nake iya jiyo muryar yah Qaseem daketa jeramin sannu shida Aamilah da Kuku, bandaiji muryar Salman ba sai daga baya, tsahon wasu mintuna muna a haka kafin barci yaɗan fara fisgata, addu'a nake buƙatar ko yaya wani ya dinga karantowa yana tofamin kozanji sauƙin abinda nakeji a jikina tamkar ana kunna garwashin wuta, sai dai nasan ba samu zanba, dan duk waɗanda suke a kaina babu mai irin wannan tunanin. nesa-nesa nake jiyo maganar Yah Qaseem dake cewa Aunty Aamilah mutashi muje mu kwanta, da taimakonta na koma saman gado, sai daifa tace itama anan zata kwana bazata koma ɗakintaba, sannan suma dan ALLAH su kwanta anan ɓangaren basai sun koma nasuba. Bansan amsar da suka bataba saboda idona ya rufe ruf da barci.
★★★
Kiran sallar farko na asubahi na farka, sai dai abin mamaki da al'ajabi na mance kaso mafi yawa na abinda ya faru jiya a gidan, na tashi zaune ina kallon Aunty Aamilah dake mamuƙe dani alamar a tsorace tai barci, ajiyar zuciya na sauke a hankali inason tuno koda wani abune kaɗan, sai dai sam ƙwaƙwalwata ta gaza aiki, tamkar ansa murfi an toshe bututun dake kai saƙo tsaka
nin ƙwaƙwalwa da zuciyata, addu'a na shiga karantowa kozan sami sassaucin da nakeji dangane da ƙuncin da zuciyata ta shiga da zafin da nakeji a cikinta.
اَللَّهُمَّ رَحْمَتَكَ أَرْجُوفَلا تَكِلْنِي إِلَى نَفْسِي طَرْفَةَ عَيْن، وَأَصْلِحْ لِي شَأْنِي كُلَّهُ لاَ إِلَهَ إِلاَّ أنْتَ.
“Allahumma rahmataka arjoo fala takilnee ila nafsee tarfata 'ayn, wa-aslih lee sha'nee kullah, la ilaha illa ant”.
Ya ALLAH! Rahamarka nake kauna, don haka kar ka kyale ni da kaina ko da kiftawar ido ne, kuma ka kyautata mini sha'ainina dukkansa; babu abin bautawa da gaskiya sai kai.
Sai da aka fara kiran salla ta biyu sannan na samu ƙarfin sakkowa daga gadon, banda ƙuncin zuciya babu abinda nakeji a jikina, sai kaina dake ɗan ciwo kaɗan-kaɗan da marata, ban ɗauki hakan komaiba, dan nasan hakan alamun zuwan period ɗinane, da sam bana ciwon mara idan zanyi al'ada, amma a shekararnan gaba ɗaya haka nake fama dukda bawai yanamin tsanani baneba. Saida na duba na tabbatar babu alamar zuwansa ciwon mararne kawai sannan nai wanka dan na samu ƙwarin jikina, daga nan nayo alwala na fito. Nayi ƙoƙarin tada aunty Aamilah amma sam taƙi koda motsi, haka na haƙura na barta nai sallata ganin nima lokaci na neman ƙwace mani. Bayan nayi azkar karatun alkur'ani nayi har zuwa 7am sannan na tashi, shirin office nayi abina, harna kammala aunty Aamilah batako motsaba har lokacin, nakuma ƙoƙarin tadata salla amma taƙi tashi, ƙyaleta nayi na fita kicin danna samu koɗan tea na sha dukda banajin cin komai.
★★★★★★★
Tunda suka shigo gidan daga asibiti daƙyar ya iya dauriyar yin wanka saboda barcin da yakeji, ya samu yay shafa'i da wutiri a daddafe ya haye gadonsa, ya fara addu'a, amma bashi da tabbacin ya kammalata barci yay awan gaba dashi. Can tsakkiyar dare ya farka a matuƙar razane saboda mummunan mafarkin da yayi.
‘Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un’.
أَعُوذُ بِكَلِمَاتِ اللَّهِ التَّامَّاتِ مِنْ غَضَبِهِ وَعِقَابِهِ، وَشَرِّ عِبَادِهِ وَمِنْ هَمَزَاتِ الشَّيَاطِينِ وَأَنْ يَحْضُرُونَ.
“A'oozu bikalimatil-lahit-tammat min ghadabih,wa'iqabih, washarri 'ibadih, wamin hamazatish-shayateen, wa-an yahduroon”.
Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku daga fushinsa, da ukubarsa, da sharrin bayinsa, da kuma wasuwasin shaidanu, da kuma kada su zo mini (a cikin al'amurana).
أَعُوذُ بِاللهِ مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ ثَلاَثٍ مَرَّاتٍ.
a'uzu bi-l-lahi mina shaytani r-rajeem’. ya faɗa sau uku, yay addu'a ya tofa gefen haggunsa da dama sau uku, sannan ya sauka a gadon, alwala yayo yazo yay salla raka'a biyu saboda idonsa cike yake da barci, yay addu'a sama-sama ya koma saman gadon ya kwanta, sai dai ya canja sashen da yay mafarkin dashi ɗazun. Babu jimawa barcin ya sake awan gaba dashi.
Ana kiran sallar shiga massalaci ya farka, hakan ya sakashi ɗaura al'wala ya fita massalaci dan har an tada sallah. Koda aka idar bai wuce motsa jikiba yau sai ya shigo gida duk da yana buƙata saboda jikinsa yayi nauyi, gyara ɗakinsa yay ya shiga wanka, bayan ya fito yay shirin office. Ƙarfe bakwai da kwata Gimba ya ɗaukesa suka fice daga gidan..............✍
Gaskiya an fara sakama boss ido a gidannan fa😑, yana koyama yarinya aiki anacewa yayi🤐🙄 nayi nan, karkuma ace na koma team Beejay ne🚴🏼.
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
Typing📲
ƘWAI cikin ƘAYA!!
Bilyn Abdull ce🤙🏻
BOOK TWO
Page 17
................Bayan na kammala shan tea ɗin dana sakama suga kaɗan sai na fito daga kicin ɗin, a falo na iske Yah Qaseem zaune yana waya da Dad, da alama abinda ya faru a daren jiya yake bashi labari, sai dai yanda naji yana faɗama Dad ɗin shima wai ba komai zai iya tunawaba, shidai kawai an bamu tsoro jiya a gidan. Bansan mi Dad ya faɗa masaba, nadaiji ya amsa masa da cewar, “To Dad ALLAH ya kawoka lafiya, itama yanzu zamuje asibitin muji yaya jikin nata”. Yaɗanyi shiru yana sauraren mi Dad ɗin ke faɗa daga can, sai yace, ”Okey gata”. Wayan ya bani, muka gaisa da Dad, daga can yace, “Ɗiyata yaya jikin naki?”. Muryata a sanyaye da har yanzu nakejin jikina wani iri nace, “Alhmdllh Dad, banajin ciwon komai sai na kai, gashima nayi shirin Office ”. “To ALLAH ya kiyaye gaba ya ƙara sauƙi kinji, nima insha ALLAHU ina tafe, anjima kaɗan zan iso”. Nace, “To Dad ALLAH ya kawoka lafiya”. “Amin” ya faɗa mukai sallama, na miƙama Yah Qaseem wayarsa. Miƙewa yay yana faɗin, “Muje dan mu samu mubiya asibitin”. Kaina na jinjina masa, har mun fara tafiya nace, “Yah Qaseem bazakasha ko tea ba?”. Kansa ya girgizamin a sanyaye, haka kawai na samu kaina da tsura masa idanu, gani nai fuskarsa tai jazur kasancewarsa farin mutum, idanunsama haka, duk ya wani fita hayyacinsa, gashi tamkar a firgice yake. Cikin katseni yace, “Bilkisu lafiya?”. Firgigit na dawo hayyacina, saina girgiza masa kai kawai nai gaba ya biyoni a baya.
Tunda muka fice daga gidan babu mai iya cema ɗan uwansa komai, yau ko redio bai kunnaba, sannan sam baya gudu kamar yanda ya saba, duk yanda naso tuno wani abu na daren jiya na kasa hakan a yanzunma, iyakar firgitar da mukai kadaice ban mantaba da abinda ya biyo bayanta, amma miye musabbabin hakan? Amsar itace ban saniba ba, tamkar anma ƙwaƙwalwarta formatting ɗin komai lokaci ɗaya, haƙura nai dason tunawar na cigaba da maimaita ‘Hasbinallahu wa ni'imal wakil’ a cikin zuciyata.
Motar Jawaad na fita daga asibitin bayan yasa gimba ya biyo sun duba Shahudah su Bilkisu na shigowa, shi Qaseem yaga fitarsu Jawaad, amma bily bata luraba dan hankalinta baya tare da duniyar mutane.
Shiga suma sukai suka duba Shahudah, har yanzu barci take, sundai leƙata ta Window suka fito, gudun karsu makara yasa sukaima Mom sallama suka wuce office.
★★★★★★
Koda muka iso yau ban samu damar yima Yah Qaseem rakkiyaba, shima bai nema hakanba, da kansa ya kwashi kayansa ya wuce office nima na wuce. Sama-sama nai gaisuwa da kowa na zauna a mazaunina, Ummie kanta yau takula bani da walwala, koda ta dameni da tambaya sai nace mata aunty Shahudah ce bata da lafiya tana asibiti. “ALLAH ya bata lafiya” kawai tace cikin rashin ɗaukar abun da muhimmanci.
Ban iya cewa da ita komaiba na cigaba da aikin gabana, kusan sha ɗaya akai kiran wayar landline ɗin office ɗin namu, Ada dake kusa ta ɗaga, da hannu taimin nuni nazo. Na ajiye biron hannuna na nufeta, miƙamin kan wayar tayi tabar wajen, na saka a kunne nace, “Hello”. “Ki sameni a office” kawai akace aka yanke. kamar nayi kuka haka naji, da inada dama dana roƙesa ya ɗagan ƙafa zuwa ɗan anjima, dan marata a ƙulle take tamau ga wani azababben ciwon kai dake cina tamkar jijiyoyin kan zasu katse. Mazaunina na koma na ɗauki ATM ɗinsa dana manta jiya ban bashiba na saka a aljihu na fita, ina kallon su Ada na gulmata, na girgiza kai kawai na fice abina dan banida lokacinsu.
Halin da nake ciki ya sake haddasama tafiyata sanyi, ga fuskata a cinkushe sosai, wadda harni kaina nasan bana cikin yanayin farin ciki gaba ɗaya yau, abinne ya haɗemin da yawa, zuwan period kan sakama mace ɓacin rai na babu gaira babu sabar, tausayin aunty Shahudah da ganinta yau ya sake ɗagan hankali, damuwar abinda ya faru a daren jiya dason tuna koda ƙanƙanin abune amma hakan ya gagara, ciwon kai ga mara dakan saka mutum takura yaji baya buƙatar yin koda magana ma.
Nai knocking ƙofar a hankali tamkar banaso, shirun da naji ya sakani sake ƙwanƙwasawa, umarnin shigowar da aka bani daga cikine ya sakani tura ƙofar na shiga.
Ƙamshin dana shaƙa a office ɗin ya sakani jin ɗan sanyi a raina, na ƙarasa inda yake ina mai satar kallonsa, sanye yake da suit yau, sun masa ƙyau sosai kamar koda yaushe, bai ɗagoba tunda na shigo, yanata rubuce-rubuce a takarda. nace, “Ina kwana sir” bai amsa minba, hakanne ya sakani kallonsa da haushi, sai da na kalli abinda ke a kunnensa na fahimci waya yakeyi, yaɗan ɗago ido ya kalleni yana faɗin, “Okey Sir” cikin jinjina kai. Da hannu yaymin nuni da kujera, kaina na gyaɗa masa kawai na zauna, cigaba da abinda yakeyi yayi. Bawani sauraren abinda yake nakeba balle na fahimta saboda halin da nake ciki, kusan mintuna bakwai kafin suyi sallama ya cigaba da rubuce-rubucensa baice dani uffanba.
Cikin dauriya na kumace masa “Ina kwana”. “Lafiya” kawai yacemin yana cigaba da sabgarsa. Ɓoyayyen numfashi na sauke ina ƙoƙarin son daidaita gudun zuciyata, na ɗora masa ATM ɗinsa saman table ɗin nace, “Gashi nagode, ALLAH ya ƙara buɗi mai albarka”.
Karon farko da tunda bilkisu ta shigo office ɗin Jawaad ya ɗago ya kalleta.
Yanda ya zubamin idanun ne ya sakani saurin duƙar da kaina, baiyi maganaba ya maida kansa ga abinda yakeyi yana ɗan lumshe idanu. sai kuma ya ɗago kansa, takardun dake gefen hannun damarsa ya ɗakko, buɗesu ya shigayi na wasu mintuna sannan ya miƙomin yana kafeni da muggan idanunsa, “Ki fara tattare dukanin bayanan wannan case ɗin a file ɗinnan, komai dake aka farashi, ki nutsu kiyi abinda ya dace”. Kaina na jinjina masa, ya sake miƙomin hotuna guda biyu, batare da ya kalleni ba yace, “Ki sakasu a ciki” suma amsar nai na buɗe na saka a farkon takardun ina cije lip saboda wani mugun katsawa da marata tayi. Babu shiri na ajiyesu na kwantar da kaina jikin tebirin ina ambaton sunan ALLAH da ɗaura hannuna na haggu bisa cikina.
Idanu Jawaad ya zuba mata na wasu sakanni, sai kuma ya ɗauke kansa, duk yanda yaso basarwar sai ya kasa, a hankali yace, “Miemaa” shiru Bilkisu bata amsaba, bakuma ta motsaba, ya zuba mata ido a karo na biyu, ganin taƙi ɗagowa sai ya miƙe ya zagaya inda take. Kujerar dake kallon wadda take zaune yaja baya kaɗan ya zauna, nanma idanunsa a kanta, dan yarasa kuma mizai mata, sunanta ya kuma kira yanzunma a hankali.
Ƙwallan da suka cikamin ido na share sannan na ɗago kaina ina amsawa da “Na'am” Ganin idonsa a kaina suke ya sakani maida nawa na risinar ƙasa. yace,
“Lafiya?”
Kaina na jinjina masa alamar eh babu komai, dan ko giyar wake nasha bazan iya cemasa marata ke ciwoba, fatana kawai ya sallameni na koma.
Ƙaramin tsaki naji yayi, cikin ɗan kausasa murya yace, “K kalleni”. Ɗagowa nai na kallesa danjin babu wasa a furucinsa, yanda ya zuba idanunsa cikin nawa bazan iya jurewaba, naɗan risinar da nawa ina haɗiye busashshen yawun dana tattaro daga bakina da ƙyar.
“Ni zakima ƙarya?”
Da sauri na girgiza kaina. Ya sake cewa ”Mi akai miki?”. Saboda ya barni nace, “Kaina ke ciwo”. Shiru yay baice komaiba, hakan yasa na ɗago kaina a tunanina bani yake kalloba. Sai dai anyi rashin sa'a idanunsa ƙyam suke a kaina. Ɗauke nawa nai ina kumbura fuska danni banason wannan kallon takuramin yakeyi.
Huci naji yaɗan fitar kaɗan mai kama da ajiyar zuciya, yace, “Tashi kije ki kwanta”. Kallonsa nai da mamakin maganarsa, ni ina zani na kwanta to?. Doguwar kujerar dake rukunin kujerun office ɗin a gefe ya nunamin fuskarsa a matuƙar ɗaure babu wasa.. Gabana ya faɗi, na kallesa cikin waro idanu da rawar baki dan nakasa cewa komai. Harara ya zubamin, a ɗan tsawace yace, “Na fara wasa da kene?”. Saurin girgiza kaina nayi na miƙe.
Kasancewar dama kwanciyar nake buƙata saina shiga sauke tagwayen ajiyar zuciya lokacin dana kwanta, na takure waje ɗaya saboda azabar da nakeji, bammasan hawaye nabin kumatunaba, kusan mintuna uku kafin ta lafamin, na buɗe idanuna a hankali na saukesu akan Boss dake zaune saman centre table ɗin rukunin kujerar ya zubamin idanu, saurin maidawa nai na rufe ina ƙoƙarin haɗiye kukana. Baice dani komaiba, amma inajin yanda idanunsa ke yawo a jikina har yanzun. Yunƙurawa nai zan tashi yace, “Koma ki kwanta”. cikin marairaice fuska nace, “Ya daina ai, zan koma nacigaba da aikina”. Yanda yay kicin-kicin da fuska ya tilasta min komawa na kwanta yanda yake buƙata. “Mike miki ciwo?” ya jehomin tambayar a kausashe. Bansan sanda na tura baki gaba ba nace, “Nifa kainane kawai sir”. Bai tanka minba yamiƙe yabar wajen, ban sake sanin mi yakeyiba saboda ciwon ya dawo. Saida ya lafamin ne na buɗe ido naga Ummie durƙushe a gabana tanamin sannu, hannunta na kama na riƙe ina hawaye, “Ummie ki taimakeni kiyi masa dabara mubar office ɗin nan dan ALLAH”. Kanta ta jinjinamin tana gogen hawayen, tace, “Mararki ke ciwo ne?” da sauri na ɗaga mata kaina ina cije baki. Nace, “Koda yaushe zai iya fitowa wlhy Ummie”. Cikin ƙara rage murya ƙasa Ummie tace karki damu bara nai masa magana”.
Jawaad da duk ke saurarensu daga inda yake zaune ya girgiza kai kawai. Mutum ne shi da ALLAH yayma baiwar jii, dukda ahankali suke maganar yana jiyosu batare da sunyi tunanin hakanba. Koda Ummie ta miƙe zuwa inda yake domin ta tsarashi kamar yanda Bilyn ta buƙata sai yace ta tafi. Babu ƙofar yimasa musu, dan haka tabi umarni ta fice tana waigen bilyn. Waya ya ɗauka shikuma ya tura saƙo. Cigaba yay da aikinsa kamar ya manta da Bilkisu a office ɗin, lokaci-lokaci yakan amsa waya koshi ya kira. Kusan mintuna ashirin da tura saƙonsa aka kawo masa abinda ya buƙata, Gimba ne ya shigo ya ajiye ledan hannunsa bayan ya gaishesa.
Sama-sama nake jin muryar gimba a office ɗin, kafin kuma naji alamar fitarsa. Ƙamshin turaren Boss da naji a akaina ya sakani buɗe idanu, yace, “Tashi zaune” babu musu na tashi, a raina ina murna zai barni na tafi, abinda ke cikin ledar ya fiddo sai naga magunguna ne, batare da ya kalleniba yace, “Kinci abinci?”. A hankali nace, “Nasha tea tun a gida”. Baice komaiba ya miƙe. Naɗan bisa da kallo sai kuma na janye idanuna ganin ba fita zaiyi daga office ɗinba, bansan mi yakeyiba saboda ya juyamin baya, a ɗan ƙanƙanin lokaci ya juyo ɗauke da kofi, ya zauna a table ɗin tamkar ɗazun yana miƙomin tea ɗin daketa turiri, sai cake, yanda yay da fuskane ya tabbatarmin babu wasa, ya miƙe yana faɗin, “minti biyar na baki kuma”. Bance komaiba nidai sai fuska dana kumbura. Dayake yunwar nakeji kuma tea ɗin ya haɗashi dai-dai yanda zan iyasha gashi babu suga sai gashi na shanye naci cake ɗin, ina ajiye kofin yana dawowa wajen hannunsa ɗauke da ruwa, nidai kaina a ƙasa naƙi kallonsa, dan dauriya kawai nakeyi kar yaga na cika raki, sai haɗiye kukan dake tahomin nakeyi da sauri-sauri, da kansa ya ɓalla maganin ya miƙamin. Amsa nai babu musu na zuba a baki, ya miƙamin ruwan shima, na kammala sha ya amsa yana min nuni dana kwanta. Ban musaba dan babuma damar yin musun na koma na kwanta kamar ɗazun, shikuma ya miƙe zaibar wajen. Bansan lokacin da harshena ya suɓuce nace, “Sir dan ALLAH kai min addu'a a ruwa ka bani nasha, sannan ka tofamin, jinake jikina kamar ana kunna garwashin wuta”. Cak ya tsaya, sai kuma ya juyo a hankali tamkar mai ciwon wuya ya zuba min idanu. Lumshe nawa nai hawayen da nake maƙalewa suka silalo.
Wani irin bugu ƙirjin Jawaad yake da sauri-sauri, ga wani irin sanyi na ratsashi daga saman kai har yatsan ƙafa tamkar wanda ake tsundumawa cikin ƙanƙara, mafarkinsane na daren jiya yake rige-rigen dawo masa a kwaƙwalwa. Bayan gushewar kuwwar halittu masu ban tsoro da ya samu damar yin addu'a ta koresu, sai furucin ƙarshe na cikin mafarkin daya fito daga bakin wata murya mai amo da baisan daga ina ta ɓulloba ita kuma, yay masa tsaye cak a zuciya yakuma kasa fashin baƙi a kai harya iso office ɗin nan, {Ƙaddarar haɗuwar Jini a cikin jini da zai zama jini ta tabbata, rashin gaggawa zai tabbatar da zubewar jinane, hhhhhhhhh karku manta! Karku manta!! Karku manta!! Hhhhhhhhhhh!!!!}......... “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un” ya shiga ambata lokacin da yaji gilmawar abu shuuu ta bayan kunnensa, da dawowar maganar tamkar a yanzu ake mai ambatonta ke faɗinta, hankalinsa ne ya dawo jikinsa. ya kalli inda bilkisu take kwance har barci ya fara fisgarta, samun kansa yay da tsira mata idanu a zahiri, a baɗini kuma taurarin cikin mafarkinsa ne daya koma barci bayan yayi addu'a da nafila ne suke masa kaikawo, yay ƙoƙarin tuno furicin mahaifinsa aka taurari huɗu da sukafi kowaɗanne haske acikin taurarin da ya gani, sai guda ɗaya shima mai tsananin haske amma ya matsa nesa dasu sosai, ya kasa tuna komai da Abba ya faɗa masa akan taurarin, kansa ya shiga yamutsawa cikin wani irin yanayi, a fili ya furta, “Jiya wace irin ranace?”. “Ranar da zata zama cikin ranakun tunawa daga nan har ƙarshen numfashi”. Bily da idanunta ke rufe har tana sauke numfashin tabbatuwar barci ta faɗa cikin motsa labɓanta da sauti mai sanyi, badan ALLAH ya yisa mai jii ba da bazai taɓa fahimta ba. Dukda yaji wani abu a ransa game da amsar tata sai ya tureshi da tunanin ai a fili yay magana shima, tajisane shiyyasa ta bashi wannan amsar, to amma abin tambaya anan miyasa ta bashi amsar a haka?. Ƙirjimsa yay wani irin motsawa, kiran sunata ya shigayi amma ko motsi bataiba alamar barcinta yayi ƙarfi. Ƙwaƙwalwarsa ma saita gaza tunanin komai, samun kansa yay da fara mata addu'ar data buƙata kawai ya shiga tofa mata akan fuska, gani yay ta saki wani lallausan murmushi tana motsa laɓɓanta, yay saurin kai kunnensa amma bayajin komai, ɗagowa yay ya kalleta sai kuma yaga ta yamutsa fusaka ta maida fuskarta ta haɗe. Yay shiru yana kallonta kafin ya miƙe yabar wajen.
Cikin ƙanƙanin lokaci barcin Bilkisu yay ƙarfi sosai saboda maganin na saka barci, gashi dama bawani isashen barci ta samu a daren jiyaba, Jawaad kam ya cigaba da ayyukansa har akai kiran sallar zuhur. Tashi yay ya shiga toilet yay alwala ya fito, idanunsa suka sauka akan bily dake takure cikin kujera alamar sanyi takeji. Takawa yay a hankali wajen zamansa, rigar suit ɗinsa dake jikin kujerar a rataye ya cire ya nufeta, lulluɓa mata yay dukda bata rufe har ƙafafuba, cikin barci ta sauke ajiyar zuciya jin ɗumi ya ratsata, ya ɗan lumshe ido ya buɗe yana girgiza kai, sai kuma ya kalli agogo ya nufi hanyar fita da hanzari ganin zai makara salla.
Koda aka fito salla bai dawo office ɗinba ya amsa kiran da Sir Ahmad ke masa a office ɗinsa.
★★-:-:-:-★★★-:-:-:-:-:-★★★-:-:-:-★★
Ƙarfe biyu da wasu mintuna Dad ya isa asibiti, daga airport bai zarce ko gidaba yasa driver ya wuto dashi dan ya matsu yaga jikin mamansa, zuwa lokacin Shahudah ta farfaɗo, sai dai daka ganta kasan tanajin jiki, tayi zuru-zuru, farar fatarta tai jajur musamman fuskarta ma, Dad ya zauna a bakin gadon kusa da ita yana mai shafa gashin kanta fuskarsa a ƙwaɓe tamkar zaiyi kuka dan tausayinta. “Sannu kinji mamana, ALLAH ya baki lafiya”. Hawayene suka ziraro a kumatun Shahudah, ta kama hannun Dad ta riƙe tana magana a hankali saboda nauyin da ƙirjinta yay mata, “Dad bazan samu lafiyaba, mutuwa zanyi, tunda Bb baya buƙatata gara na mutu, Dad cayayfa mun rabu kenan har abada, ya daina sona Dad, Dad mut......” saurin ɗora hannunsa yay akan bakinta yana girgiza kansa, “Mamana bazaki mutuba, ni da kaina zan roƙesa, ko durƙusa masa ta kama zanyi Mamana danki samu farin ciki, indai ina raye a duniya babu ɗayanku da zai nema abu ya rasashi ko menene shi, danku kawai nake neman arziƙi, nai miki alƙawarin saikin koma wajen Jawaad kinji, zaku sake rayuwarku ta jin daɗi fiyema da da har ki haifamin jikoki, nidai abinda nakeso dake ki kwantarmin da hankalinki ki samu lafiya, namiki alƙawarin daga nan ko gida bazaniba office ɗin Jawaad zanje kinji”. Kanta ta ɗaga tana zubda hawaye, tace, “Kaje dan ALLAH Dad, ka faɗa masa ina sonsa, idan ya barni mutuwa zanyi, wlhy namasa alƙawarin ko a daren yau yakeso yamin ciki na haihu gobe, na kuma samin wani jibi, ko ƴaƴa ɗarine zan haifa masa indai zamu kasance tare har abada”. Wata irin kunya ce ta tsargama Doctor jin furucin Shahudah wai ko yau ai mata ciki ta haihu gobe, a ransa yace anya kuwa wannan ƴa da ubane? ‘to irin wannan manya-manyan zance haka babu risinawa’ yaɗan girgiza kansa yana mamakin yanda tarbiyyar yaran hausa fulani keta ƙara ƙuɓucewa a hannun iyayen wannan zamanin, a ganin ko uwa mace ya dace ƴa taji nauyin buɗe wani lafazin a gabanta inba doleba balle uba namiji, gashi ya kula shi Dad ɗinma ko a jikinsa, saima biyema Shahudah da yake sakeyi yana lallashinta da alƙawarta mata samun duk abinda takeso, anya kuwa wannan hanyar ɓullewace iyaye ke ginama ƴaƴansu?, a yanzu tarbiyya da al'adun kunyar da aka sanmu dashi na tangal-tangal ɗin ɓarewa a hannayenmu tamkar kwale-kwale a ƙaton kogi inaga ƴaƴan dake tasowa waɗanda suke jiran amsar tarbiyya a hannun ƴaƴanmu, anya kuwa zamu girbi abinda iyayenmu suka shuka a garemu na alkairi?......
Maganar Dad ta katsema Doctor tunaninsa, ya miƙe yana mai ranƙwafawa ya sumbaci koshin Shahudah da kumatunta, sannan ya shafa kanta cikin sigar lallashi da nuna tsagwaron soyayya da ƙaunar da yake mata yace, “Ki kwantar da hankalinki Mamana, yanzun nan zanje na isar ga saƙonki ga bb'n ki kinji, ki cire komai a ranki indai Jawaad ne kamar kin samu”. Kaita gyaɗa masa, murya a sanyaye tace, “I love you so much my Daddyna, duniyata, farincikina”. Cikin jin daɗin kalamanta Dad ya sake shafa kanta yana murmushi, yace, “I love you more mamana sanyin idaniyata, ki bani awa ɗaya kacal zan dawo miki da zance mai daɗin gaske”. Kanta ta ɗaga masa tana lumshe idanu tare da murmushi.
Dad ya matsa daga gaban gadon tare da kamo hannun Aamilah dake tsaye jikin Window tana kallonsu, “My autana zo mana”. Baki taɗan tura gaba tana ƙoƙarin ƙwace hannunta, tace, “Bayan bakama kulaniba sai mamanka”. Jawota yay jikinsa ya rungume yana murmushi, “Waneni da ƙin kula autar Mom, ayi haƙuri bazan sakeba ihuyim”. Kanta ta jinjina masa kafin ta taso daga jikinsa tana kallon fuskarsa, cikin magana a hankali dankar Shahudah taji tace, “Dad dan ALLAH kasaka mai shegen taurin kan nan yay sanyi, kaga sister tana cikin damuwa, son da take masa yayi yawa tausayi take bani”. Murmushi Dad yayi ya shafa fuskarta, “Karki damu autana, insha ALLAH komai yazo ƙarshe kinji, bara naje na dawo kafin Mom ɗinku ta dawo”. Kanta ta jinjina masa, shikuma ya saketa ya fice.
★★★★★★
A station kuwa, bayan an fito salla Rose ce ta nufi Office ɗin Jay domin kai masa wasu takardu, tai knocking dan batai tunanin bai dawoba, jin babu amsa kusan sau uku saita tura ta shiga, dan sarai tasan randa yakejin wulaƙancinsa haka yakeyi, takuma tabbatar yana kallonta ta cctv. Babu kowa a office ɗin sai ƙamshinsa, saita shiga waige-waige, hangen kamar mutum a kwance a kujera ya sata takawa ta nufi wajen, ƙirjinta yay masifar bugawa saboda yin tozali da fuskar bily dake barci tana sauke numfashi a hankali tabbacin lafiya ta samu, ga rigar boss lilliɓe a jikinta. Cikin gurɓataccen hausanta ta lailayi ashariya ta direta tana kaɗa jiki da hura hanci, kafin takai hannu da nufin finciko bilkisu ƙasa, dan ta rantse yau sai tayi maganin shegiyar baƙar yarinyarnan koda boss zaiyi markaɗenta ya murza a turmi jininta ya zama mai, tsokarta da ƙashinta da fatarta su zama tunkuzar ƙuli-ƙuli.............✍
To baza'ai tankaɗe da rairaya a gabanaba Rose nayi nana🚴🏼. Yau words dubu uku harda ɗari uku da hansin da hida nayi yanda zaku karanta har lahadi🤭🤫🤥🤐.
Barkanmu da juma'a, kar'a manta da saka bayin ALLAH a addu'ar juma'a😥🙏🏻.
Musha weekend lafiya😍😘🚴🏼
ALLAH ka gafartama iyayenmu🙏🏻😭
Bilyn Abdull 📚:
Page 18
...............“Wannan shine kuskure mafi girman da zaki aikata a rayuwarki inhar hannunki ya sauka kanta!!”.
Kakkausan furuci daya karaɗe illahirin office ɗin da kunnuwan Rose kenan a lokacin da hannunta ke gab da kaiwa jikin Bilkisu da batasan Rose ɗin na kantaba ma, dan barci take cikin kwanciyar hankali da jin daɗi, harma ta manta a inda take kwance.
A firgice Rose ta janye hannunta tare da ɗago idanunta da juyowa domin tabbatar da abinda take zato, ilai kuwa shine fuska a murtuke babu alamar wasa tattare dashi balle sassauci, ya saki hannunsa dake harɗe a ƙirjinsa yana cigaba da watsa mata wani mugun kallon daketa tsitstsinke jijiyoyin jikinta da hanjin cikinta, “Mi kike shirin yi da?” ya faɗa muryarsa cike da tsanarta irin wadda bata taɓa ganiba a gareshi. Da ƙyar Rose ta haɗiye ɗan yawun data tattaro a maƙoshinta, tace, “Ni babu abinda zanyi, kawai dai na shigone na ganta anan kwance____” “Shine zaki tada ita saboda a kanki take kwance?”. Yay saurin ƙarasa mata zancen data ɗakko yana tsatstsareta da idanu. Fuska ta sake tsukewa cikin tsananin kishi tace, “Ni wlhy yarinyarnan batai minba”. Wani banzan kallo sama da ƙasa yay mata ya ɗauke kansa yana faɗin, “Saiki kasheta ai”. Kamar zatai kuka tace, “Amma boss wai miye haɗinka da ƙwailar yarinyarnan? dako mace bata gama zamaba ma”. Tsaki yayi ya juya zaibar wajen yana faɗin, “Duk abinda ke ranki shine tsakaninmu, kozaki hana?”. Tamkar rose zata fasa kuka tabishi da kallo, yana zama Su Hafiz na shigowa da sallama, hannun Aliyu ɗauke da leda mai tambarin gidan abinci, duk kallon Rose sukai ganinta tsaye tamkar gunki tana kallon Jawaad da tamkarma baisan da itaba, ga fuskarsa a matuƙar ɗaure alamun zuciyar na kusa, mai tsautsayi ya taɓa a fashe masa ita. Hafiz ne ya fara janye idanunsa daga kan Rose ya sauke akan Bilkisu dake kwance tana barcinta lulluɓe da rigar Jay, har yanzu ko motsi bataiba dukda ihun da yayma Rose ɗazun, kafin suma su Jabeer su lura da ita. Babu wanda yace komai a cikinsu, shi kuma Jay baiko ɗago yama kallesuba balle su saran zai tanka.
Aliyu ya matsa inda Jay yake ya ajiye ledar yana faɗin, “Ga abinci, kasa munje munata jiranka a wajen ashe kai kanama nan ka manta damu Boss”. Ɗago ido Jay yay fuska a yatsine ya harari Aliyu batare da yace komaiba, shi dai Aliyu zama yay abinsa bai kulashiba, Jabeer ma yaja kujerar kusa da Aliyu ya zauna yana haɗiye dariyarsa, dan ya lura Rose suman tsaye tayi a wajen kokuma ta samu gushewar hankaline na wasu mintoci.
Hafiz yay guntun tsaki yana harar Rose, “Ke kuma lafiya kika wani tsaya ƙiƙam kamar wata dogariya?”. Numfashi Rose ta kawo cikin dawowa hayyacinta, ta watsama Hafiz harara kafin ta nufi ƙofar fita batare data tankama kowa a cikinsu ba, jikinta sai rawa yakeyi. Tana fita Jabeer ya kwashe da dariya, duka Hafiz yakai masa ya duƙe, Jay ya galla masa harara da faɗin, “Dilla malam miye haka?”. “Me nayi ni?” cewar Jabeer dake rama harar da Jay yay masa, ya cigaba da faɗin, “Kai ka dace da wannan tambayar baniba boss, sai neman haukatar da yaran mutane kake kana wani cijewa, gwara idan son yarinyarnan kake kafito ka sanarma duniya ka kuma shiga cikin ƴan takara ko Rose ta dawo hankalinta, kuma ka kwana da sanin Qaseem son yarinyarnan yake, yasin ka tsaya kallon ruwa ƙwaɗone zaima ƙafa, saboda gida ɗaya suke kwana suna tashi, dan a ruwa kake kusa da kada malam”. A fusace Jay da dama kaɗan yake jira ya miƙe, ƙofa ya nunama Jabeer yana huci, “Tashi ka fita a office ɗinan Jabeer kafin nama rashin mutuncin da bazaka taɓa mantawaba, banason wasan banza kaima ka sani ko”. Miƙewa Jabeer yay yana taɓe baki, yasan fitar tasa shine mafi alkairi dan Jawaad a wuya yake, shikuma idan yay zuciyar da har ɓacinta ya fito a muryarsa kai nesa dashi yafi komai alkairi, idan ya huce da kansa zai nemeka yay maka bayani harma daban haƙuri idan yasan yamaka abinda bai daceba. Ficewa Jabeer yay yana murmushi da girgiza kai. Jawaad ya koma ya zauna yana ƙwafa, sai kuma ya miƙe ya nufi toilet yabar su Hafiz dake binsa da kallo.
A sanyaye Aliyu yace, “Sonta yake amma kamar shima bai fahi
mci hakaba Hafiz”. Cikin damuwa Hafiz ya bama Aliyu amsa da cewar, “Na daɗe da fahimtar haka Aliy, ba fahimtace baiyiba kuma shima, sarƙaƙiyar dake cikin al'amarin yarinyarne yake sakashi ƙoƙarin haɗiyewa, sai dai kuskuren daya kasa tunawa shine, ba kowanne irin SO bane yake haɗiyuwa lokacin da ake buƙata, wani koda ka korashi da ruwan haƙuri dana juriya a maƙoshi yake tsayawa ya tsaida dukkanin muhimman al'amuranka wucewa cikin zuciya da ƙwaƙwalwa, ni kaina na waiga ta kowacce kusurwa bashi da wani magoyin baya akan al'amarin yarinyarnan sai sashe ɗaya, shi kuma baida wani ƙarfin iko akan hakan”. ajiyar zuciya Aliyu ya sauke mai ƙarfi yana dafe kansa, sai kuma ya ɗago ya kalli Hafiz dake kallon inda Bilkisu take, yace, “Minene mafita yanzu Hafiz? Jay yana buƙatar mace a kusa dashi sosai ta kowanne ɓangarema kuwa, yarinyarnan kuma tanada mafi yawan nagartar data dace ta zame masa abokiyar rayuwa, mizai hana mu bashi shawarar ya sanar mata ABINDA KE RANSA”. Numfashi Hafiz ya sauke yay shiru na wasu sakkani yana nazari da bubbuga yatsansa akan baki, ya kalli Aliyu yana kaɗa kai, “Aliyu ita kanta yarinyarfa bamuda wani ƙwarin gwiwar samun goyon bayanta, dan tayi nisa wajen son ɗan uwanta, sannan bana tunanin zata iya barin Qaseem kodan halaccin mahaifinsa a rayuwarta ta ɗauki waninsa, shiyyasa nace maka akwai sarƙaƙiya takowacce kusurwa, Kasan Jabeer yanada fiƙira akan irin waɗannan al'amuran, sai dai shi matsalarsa saka wasa a dukkan lamarinsa, bansan lokacin da zai dinga kallon abu mai muhimmanci a muhallin daya dace ba, amma mubari zuwa weekend sai muyi zamana musamman akan maganar”. Cikin gamsuwa Aliyu yace, “Shikenan ALLAH ya kaimu”. Fitowar Jay daga bayi fuskarsa jiƙe da ruwa ya sakasu yin shiru, babu wanda yace dashi komai yazo ya zauna a kujerarsa, Hafiz ne ya fara miƙewa yana faɗin, “Bara muje zuwa anjima ma dawo muyi maganar idan ka samu lokaci”. Kai kawai jay ya ɗaga amma baice uffanba.
Fitar su Aliyu babu jimawa Dad ya iso station ɗin su Jawaad, ba'a bashi damar shigaba saida ya kira Jawaad a waya, tamkarma Jawaad bazai ɗauka wayarba sai wani tunani yazo masa a rai, hakan yasa bayan wayar ta katse yabi bayan kiran Dad shi ya kirashi. Koda ya sanarmasa yana gate sosai mamaki ya kasheshi, amma sai yabama securitys ɗin umarnin a rako Dad office ɗinsa, shaf ya manta da Bilkisu dake kwance tana barci.
Bai nunama Dad komaiba yay masa tarba ta mutuntawa, bayan sun gaisa ya bashi ruwa Dad ya fara magana cikin karyar da murya. “Jawaad”. Yanda ya kira sunansane ya sakashi ɗaga kai ya kallesa, ya amsa da “Na'am”. “Jawaad wajenka nazo gwiwoyina a ƙasa da tarin magiya da roƙon da idan kamawa tai na duƙa a gabanka zanyi hakan. Dan ALLAH ka tausayama Mamana ka dubi al'amarinta, bazan musamaka ba akan ita mai laifice damu kanmu, sai dai ince dan ALLAH mu manta da baya domin ta shuɗe, wlhy ina mai tabbatar maka duk wautar dake kan Mamana a yanzu babu ita, dan ta gurzu da horonka, ka tausayamin kodan ciwon dake tare da ita na hawan jini da likita ya sanar mana, badan tanada sauran shan ruwaba faɗuwar da tai jiya a gidanku likita ya tabbatar mana da sai ta kamu da paralysis, wlhy yarinyarnan tana sonka fiye da yanda kake zato ko tsammani........” Jawaad da kansa ke ƙasa yace, “Kayi haƙuri Dad ban katsekaba, da Huda na min irin wannan son da bazata guji haɗa zuri'a daniba, yakamata mu fahimci Hudah ta huce sahun ƙuruciya yanzun, bai kamata ace duk abinda yazo zuciyarta tai tunanin aikatashi shine mafi dai-dai a rayuwarta ba, sannan kuma abinda takeso ace dole saita samesa, dolene duk inda akwai take wataran za'a samu babu. batason haihuwa yanzun miyasa ta yarda tai aure? Bata shirya zama kamar kowacce macen aureba miyasa ta zaɓi muyi aure? A ganina da sai ta bari sai lokacin da duk ta shirya waɗan nan, Dady ni bahaushene, uwata bahaushiyace, mahaifina bahaushene, dukkanin dangina hausawane sai fulani, addinina shine musulunci, addinin iyayena da dangina duk musuluncine, tayaya Hudah take tunanin zan biye mata na ajiye dokokin UBANGIJINA na ɗauki son zuciyarta?, tayaya take tunani zan ajiye al'adun yarena dana tashi
cikinsu na ɗauki ra'ayinta data aro a wajen wasu?, ai duk duniyar da zan shiga dady ina alfahari da abubuwannan guda biyu, YARENA ADDININAH, banajin kunyar nuna kaina a gaban kowanne mahaluki da tambari kasancewata musulmi, dan rahamace babba a gareni da wofantar da ita babbar asarace da bata da madadi duniya da lahira, a duk duniyar dana shiga zan kira kaina bahaushe, koda wanda nake tare dashi baitaɓa jin sunan yaren hausa ba ma zan tabbatar masa da yaren ya fara saninsa a lokacin kuma nai masa AlFAHARI dashi saboda yarena ne, shine harshen da UBANGIJINA yafi ganin ya cancanta na fito a ciki ya zama abin maganata, to mizaisa na ƙyamacesa saboda yaren wasu da ko za'a kashesuma basusan nawa ba, wlhy Dady idan ka cire LARABCI daya kasance yaren MANZON ALLAH (S.A.W) to babu wani yare da yakai muhimmancin dazan fifitashi sama da yarena na HAUSA, duk yaren da kaji yafita a harshena saɓanin LARABCI da HAUSA to inayinsane saboda lalurar mu'amulla da mutane badan ina kallonsa a saman nawaba. Kayi haƙuri Dad mubar wannan maganar kawai, ku tayamu addu'ar ALLAH ya bama kowa dai-dai da ra'ayinsa ni da ita, dan nikam Hudah tafi ƙarfina”.
Jikin Dad duk yayi sanyi da maganganun Jawaad, dan kuwa dukkan abinda ya lissafa matsalace mai tushe da shima yanada kaso mafi yawa wajen ƙirƙirarta ga ahalinsa, to amma yanzu bata wannan akeba, matsalar mamansa itace gaba da komai. Ya nisa cikin girgiza kai da raunana murya fiye da farko yace, “A karo na babu adadi Jawaad zan kuma cewa kayi haƙuri, ina mai tabbatar maka a yanzu zaka sami mamana a yanda kakeso kuma kake buƙata”.
Shiru Jawaad yay yana mai kallon Dad cike da tausayi, dan yasan shine ginshiƙin ruguza gidansa wajen sakaci, gashi a yanzu abinda ya raina yayi gawurtar da al'amarinsa yafi ƙarfinsa amma shi baima fahimtaba, cike da girmamawa yace, “Kayi haƙuri Dad zanzo gida na sameka idan na tashi aiki insha ALLAH, wannan maganar bata nan baceba, ALLAH ya zaɓa mana abinda yafi alkairi”. Shiru Dad yay ya kasa tashi, dan gani yake tamkar Jay yawo da hankali zai masa, saboda yasan taurin kan yaron da kafiya idan ya juyama abu baya, tun yana yaro ya fahimci wannan shegiyar halayyar tattare dashi, shiko buƙatar ƴaƴansa bai haɗata da komai a wannan duniyar ba. A bazata Jawaad kawai sai yaga Dad tsuggunne gabansa yana faɗin, “Jawaad dan girman ALLAH karka wofantar da maganar n....” da sauri Jawaad ya miƙe jikinsa har rawa yake ya tanƙwaɓe wayarsa dake kan desk ɗinsa ta faɗi ƙasa, baibi takantaba ya kama hannun Dad yana faɗin, “Ya ilahi, Dad dan ALLAH ka tashi, minene kakeyi haka? Wlhy na tabbatar maka zanzo muyi magana a gida” da ƙyar Jawaad ya samu Dad ya tashi tsaye, gaba ɗaya al'amarin yana neman birkita masa ƙwaƙwalwa, wane irin ubane Dad? Wane irin kalar mugun so ne wannan yakema ƴaƴansa? Abin yayi yawa matuƙa, kowanne iyaye nason ƴaƴansu amma na Dad yana neman wuce hankali. Shidai Jawaad sai ya koma lallashin Dad ɗin ya samu suka fita yay masa rakkiya ya tafi, gaba ɗaya kansa a cinkushe yake, harma ya fara masa wani masiffen ciwo tacan ciki.
Koda ya dawo office da shashshekar kukan Bilkisu ya fara cin karo, tun shigowar Dad ta farka, dukkan maganganun da Dad sukai da Jawaad kaf ta jisu, takuma fahimci kaso mafi yawa na dangane da matsalar data raba aunty Shahudah da mijinta, Dad ya bata tausayi matuƙa gaya yau, babban mutum kamarsa da ya haifi ɗan da yafi Jawaad amma yake tsugunawa a gabansa domin kawai farin cikin ƴarsa, wanne irin makahon so ne haka Uncle ɗin nata kema zuri'arsa?, a ganinta lokaci yayi da zata bada gudunmawarta ga Dad ko ƴar kaɗance......
Jawaad tsaye yay a ƙofa hannunsa duka biyu cikin aljihun wandonsa ya zuba mata ido, ransa a dagule yake, sannan ita kuma baisan ma'anar kukan nataba balle inda ya dosa, hakanne ya sakashi jan wani shegen tsaki ya cigaba da takowa cikin office ɗin batare daya sake kallonta ba. Har cikin zuciya da ruhi tsakinsa ya taɓa Bily, hakan ya sake jawo gudun ruwan hawayenta babu ƙaƙƙautawa, ta cigaba da kukanta na tsawon wasu mintuna shi kuma yana cigaba da aikinsa tamkarma baisan da zamanta a office ɗinba. Dan
kanta taji kukan ya isheta ta share hawayenta ta tashi ɗauke da rigarsa a hannu ta nufesa. A tsorace zuciyarta take, amma wani sashe na bata ƙwarin gwiwa akan abinda take shirin yi. Gaban Jawaad taje ta durƙusa kanta a ƙasa. Jawaad da yaƙi ɗagowa ya kalleta dukda yanajin motsinta ya cigaba da aikinsa.
Karan farko a rayuwar Bilkisu data shirya ambaton sunan Jay a harshenta harma da ƙarfin halin furtawa a gabansa, sai dai tayi imanin bazata iya ambaton sunansa da kallonsaba a yau, dan haka ta duƙar da kanta tana durƙushe akan gwiwoyinta, rigarsa riƙe a hannunta ajiye akan cinya, tace, “Yah Jawaad!.…….”
Cak Jay dake rubutu a wasu takardu ya tsaya tamkar wanda aka tsaida da remote, shi bai kalleta ba, kuma bai cigaba da abinda yakeba, saima lumshe idanunsa da yay yana sauraren sarawar da kansa ke masa da harbawar jijiyoyinsa harma da gudun jininsa daya tsinke a lokaci ɗaya. Bilkisu daba kallonsa takeba ta cigaba da faɗin “Dan girman ALLAH Yah Jawaad kayi haƙuri karka wofantar da magiyar Dadynmu, wlhy ni shaidace aunty Shahudah na matuƙar sonka, duk da bansan ainahin matsalarkuba inada yaƙinin zaka iya amfani da son da take maka ka canjata, matsalar da duk kake ganinta da ita ƙirƙirarriyar matsalace dakeda tushe a gareta tun tana tsumman haihuwa, ba laifinta bane ita kaɗai haka ta tashi taga kanta itama, bata isa banbance baƙi ko fariba a buƙatar jin zafi saboda an nuna mata hakan shine dai-dai da rayuwarta kuma nasararta, Mahaifina yasha faɗamin, {Bilkisu, aduk lokacin da zama ya haɗaki da mutane ki fara nutsuwa ki fuskanci halayyarsu da tsarin rayuwar da suka rayu, dan babu wata zuciya dake gogayya da ƴar uwarta akan hallayya iri ɗaya, lokacin da k tarbiyyarki ta baki dai-dai a wajen wani shi kuskurene, abinda yake kuskure a yaƙininki a wajen wani dai-dai ne, idan har kika kasance cikin mutane masu fahimtar ilimin duniya ina mai tabbatar miki zaki zama nasararki sama data kowa koda ace ke kaɗai kike kallon kanki a wannan nasarar, daga lokacinda ilimin sanin hallayar ɗan adam ya dawo tafin hannunki inada yaƙinin zaki gyara ɓarna da yawa, domin zakibi mutum da halinsa ki ɗorashi akan hanyarki mai nagarta batare dashi yasan ya afkaba ma, munzo zamanin da halin ɗan adam dashi ake cinsa da yaƙi bada takobiba, zauna dame ƙinki da zuciya ɗaya, ƙyautata masa kuma da yaƙinin neman sakamo wajen mai badawa ba ga shiba, koda shi a kullum zai kasance mai bibiyar bayanki da sharri, karki zama mai damuwa da zama gwana a duniya, dan wani lokacin nasarar duniya faɗuwace gamai ita, koda idanun duniya na kallonsa a saman kowa, mai kuma sa'a fiye da kowa}, Yah Jawaad ba soyayyarka kawai aunty Shahudah ke buƙataba, a yanzu tafi buƙatar ka jingina da soyayyar tata ka ɗorata a hanyar tsira domin kaikaɗaine zata iya saurara, saboda girmamaka a matsayin gwaninta, na yarda dakai ta kowanne fanni koda banida ilimin sanin ɓoyayyun halayenka, ina sake roƙonka a matsayin Yaya ba shugabana a wajen aikiba, dan ALLAH ka ceto rayukan bayin da zukatansu suke a rufe ruf akan sanin gaskiya da makomar bin hanyarta, yahudanci da nasaranci duhune, wannan duhun kuma shike mamaye da jama'ar gidanmu, sai dai hasken ruɗani da gushewar banbance mai tsafta ya hana ijiyarsu ganin kowanne tsani sai wanda suka hau, kullum fatana ALLAH ya kawo musu drivern dazai fidda rayukansu a kwale-kwale saboda ni nayi ƙanƙanta ƙarancin matsayin yin wannan jagorancin, kaiko inada yaƙinin zaka iya, domin son da sukema aunty Shahudah gyaruwarta tamkar gyaruwar kaso mafi yawane daga ahalin gidan, ciki kuwa harda Dad da tuni ya fahimci gaskiya, sai dai ƙarfin riƙonta a garesa da tafi ya hanashi nunawa ko a fuska, ya gwammaci ya haɗiyeta a rai yacigaba da rainon ƴaƴansa tamkar ƴaƴan agwagi da basa bin uwa sai dai ita ta bisu” na ɗago kai a karo na farko tunda na fara maganar na kallesa, sai dai a mamakinna shi ba ni yake kalloba, gashi yayi kicin-kicin da fuska irin yanda ban taɓa ganiba a tun sanina dashi, na raya a raina saitna dire abinda na fara, dan haka nace, “Dan ALLAH Yaya Jawaad ka yarda a maida aurenku da aunty Shahudah a karo na b....i...y...u.”
A yanda y
a juyo ya sauke rikitattun idanunsa a kainane yay masifar hargitsani na ƙarasa kalmar ƙarshe da ɗai-ɗai.............✍
Tab wlhy badaniba nayi nan, idan ya huce na dawo na ƙarasa muku yanda aka ƙare🚴🏼🚴🏼🚴🏼🚴🏼🚴🏼kuma bily addu'ar fitowa lafiya itama, dan inaga ba'a taɓa karyata ba😂🤣.
Barkanmu da dawowa, inafatan kowa yayi weekend cikin ƙoshin lafiya?.😍😍
Billyn Abdul:
Page 20
.................“Ya salam” Jawaad ya faɗa tare da ranƙwafawa ya ɗaga frame ɗin da hoton ke ciki, a bisa tsautsayi ya ɗaura hannunsa kan glass ɗin da ya maƙale kaɗan bai ida fitaba, yay tsini siriri, “ouch!!” ya faɗa yana yarfe hannunsa saboda shigar zafin bazata. Alhaji baba ya taso da hanzari garesa, hannun da yake yarfewar ya kama, abinka da jiki babu wahala tuni jini sai rige-rigen fita yake, abin mamaki har yana neman wuce girman ciwon da yajin. Daga Alhaji baba har Jawaad sai fitar jinin da yawa ta basu mamaki, dan sosai yake ɗiga a ƙasan tiles ɗin tamkar wanda yay wani uban yanka, Jawaad yay ƙoƙarin ajiye hoton saman drawer batare da ya kallesa ba sai kawai ya sake ɗora ƙafarsa akan glasess ɗin dake zube ƙasa. Da sauri ya ɗaga ƙafar tare da sake damƙe hoton a hannunsa yaja da baya yana faɗin, “Yah ALLAH”.
Alhaji baba yace, “Subahanallahi sake takawa kayi?, to kaga zauna ina zuwa”. Zama Jawaad yayi ya ɗora fasashshen frime ɗin da ya rage katako da katin hoton kawai a cinyarsa yana tarbe ɗigar jinin hannunsa da ɗayan hannun wanda tuni jinin ya ɗiɗɗiga a hoton ma. Sai dai hankalinsa bai kaiba, har Alhaji baba ya dawo ɗauke da ruwan ɗumi a roba mai ɗan faɗi da guntun towel, a hannun kujerar ya ɗora ya kama hannun Jawaad ya saka a robar tare da jiƙo towel ɗin da ruwan zafi ya goge masa hannun tas dukda dai jinin yaƙi tsayawa har yanzu yana ɗiga, kamar yanda sukai hasashen ɗan yankan bawani mai yawa baneba, tissue ya warwaro ya ɗora masa dai-dai yankan yana mai tsokanarsa da cewar, “Lallai cin kayan daɗinka yay yawa na wajena, kaga ɗan yanka kaɗan amma jini yayi rabin botiki”. Babu shiri Jawaad ya ƙyalƙyale da dariya, “Oh ALLAH, tsohon nan kana hawa kaina da yawa wlhy, idan yakai rabin botiki ai saidai a ɗiba naka a ƙaramin kenan”. Dariyar alhaji baba yake shima, ya durƙusa tare da kamo ƙafar Jawaad ɗin itama dake jinjin ya saka a robar, kwalbar data sokesa anan tana ciki, hakan yasa Alhaji baba shammatarsa ya cirota, “Ouch!!” Jawaad ya faɗa yana rintse ido dan yaji zafi, ciwon ƙafar yanada ɗan girma, Alhaji baba ya ɗaure masa dan su samu jinin ya tsaya.
Batool ce ta shigo da sallama ɗauke da abincin kakan nasu. A tsorace take kallon jinin da ƙafar Jawaad ɗin, “Ɗan uwa garin yaya haka?”. Fuska yaɗan yamutsa yana kallonta, yace, “Tsautsayi mana”. Sannu ta shiga jero masa, ta ajiye basket ɗin ta ƙaraso ta amshi tsintsiyar hannun Alhaji baba danta share kwalban kamar yanda taga yana niyyaryi. Jawaad ya sake kai hannu zai ɗauke hoton daga cinyarsa dan yanason ya tashi yaje yay wanka, sai idanunsa suka sauka akan waɗanda ke jikin hoton, dukda jininsa dukya ɗan ɗiɗɗiga a jiki, hakan bai hanashi ganin fuskar mahaifiyarsaba ras a jiki, tayi ƙyau sosai tana murmushinta mai birgewa, ya maida idonsa akan ta kusa da ita, autarsuce da suke kira aunty Mammah, itama ALLAH yay mata rasuwa shekaru masu tazara bayan ɓatan mahaifiyarsa, haka kawai ya samu kansa da tsura musu ido harna tsahon lokaci, sai da Batool ta ɗauke hoton daga hannunsane ya dawo hayyacinsa. Ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauke yana miƙewa. Batool dake kallon hoton tai murmushi da share guntayen hawayen da suka cika mata ido saboda tuno da Gwaggonnin nata guda biyu da suka rasa a ƙaddarar mutuwa da ƙaddarar taɓin hankali.
Koda Jawaad yay wanka ya kimtsa ya fito bai zauna cin abincin da Batool ta kawoba, sai ya ɗauki hoton daya fasa zai tafi dashi akan zai sabunta masa glass, babu yanda Alhaji baba baiyiba amma yaƙi ya ajiye. Cikin tsokana Batool tace, “ALLAH yasa ba sace maka zaiyiba Alhaji baba”. Harararta Jawaad yay ya fice, batare da ya jira amsar da Alhaji baban zaiba Batool ba.
Maimakon ya nufi gida kamar yanda yay niyya sai kawai ya wuce office, ta waya ya kira Gimba yasanar masa shi yana office anjima yazo ya samesa zasu fita. Cike da girmamawa gimban ya amsa masa sannan suka ajiye wayar.
Koda Jawaad ya shiga station kai tsaye office ɗin Jabeer ya nufa, shima da alama bai jima da isowarba, ya ɗago yana kallon Jawaad daya shigo office ɗin da sallama, murmushi yay masa, shikuma Jay ya hararesa yana ƙarasowa ya z
auna a kujerar dake gaban tebirin ɗin. Hannu ya miƙa masa sukai musabaha, murɗe hannu Jay yay har saida Jabeer yay ƴar ƙara, ya fisge yana hararsa da faɗin, “ALLAH kai mugune na bugawa a takarda, ciremin hannun zakayi boss”. Murmushi Jawaad yayi yana miƙa masa key ɗin motarsa da faɗin, “Gobema ka sake yin gulma”,. Jabeer ya sake hararsa yana juya hannunsa, “Kasan ALLAH Jay, yau da ace ba sunan momine da itaba da akanta zan rama, ALLAH ya ceceta kuwa”. Murmushi Jay yayi yana taɓe baki, yace, “Kaje ka rama mana ina ruwana, Am sorry jiya na maka tsawa, rainane duk a jagule kaikuma kazo zaka sake cazamin kai da naka shiriritan”.
Murmushi Jabeer yay yana shafa kansa dajin ƙaunar abokin nasa cikin rai, “Ni dama ban ɗaukesa komaiba, nasan wanene Jay ɗinmu idan yay fushi, ina fatandai itama Momin tamu ka bata haƙuri, dan na koma office ɗinka kusan 3:45 na isketa tana kuka”. Haɗe fuska da lumshe idanu Jay yayi yana sauke numfashi, “Ai yarinyarnan bata da kunya. manta da zancenta, ina fatan su Hafiz sun iso, dan inason muyi magana”. Kamar yanda ya buƙata sai Jabeer ya bar zancen bily, ya amsa masa da, “Okey bara na kirasu to, nasan duk sun iso yanzun”. Gyara zama Jay yay, yayi shiru har Jabeer ya gama kiransu. Babu wani jimawa sai gasu duk sun shigo, saida suka gaggaisa sannan kowa ya nema wajen zama, Aliyu da idonsa ya sauka akan yatsan Jawaad dake naɗe da bandage yace, “Boss miya samu hannun kuma haka?”. Hannun Jawaad ya kalla yana ƙaramin tsaki, “Wlhy Aliy wani ɗan ciwo naji, shinefa Alhaji baba yaymin wannan naɗin”. Dariya duk sukayi, Hafiz yace, “Shi ka kaima fushin jiya kenan?”. Hararsa Jay yayi amma baice komaiba.
“Kunga ku ajiye shiritarnan taku muyi magana yau inada aiki a office saboda jiya banyi komaiba”. Duk hankalinsu suka maida gareshi, Jabeer ya direma kowa kofin coffee daya haɗo, “Thanks ” Jawaad ya faɗa yana ɗaukar kofin, suma su Hafiz sukai masa godiya, Jawaad yakai kofin bakinsa sanan ya janye idonsa a kansu, sai dai yay matuƙar canja fuska saboda maganar da zaiyi tana zafarsa a cikin rai, “Guys dolene yarinyarnan tabar cikinmu a wannan karon, bazan iya cigaba da zama da itaba ta isheni haka nan”. Kallon juna suka shigayi kowa da tsoro akan fuskarsa, Aliyu yay ƙarfin halin faɗin, “Wa kake nufi a cikinsu boss? Kasan yanzu sun zama su biyu”. Kallon Aliyu yayi tamkar bazaice komaiba, sai kuma cikin takaici yace, “Rose nake nufi”. Shiru sukai duk suna jinjina zancen a ransu, kafin Hafiz yace, “Banƙi ta takaba Boss, sai dai hakan zai iya zama wata matsala daban, duk da bansan ainahin abinda tai makaba na kula tanason takurama rayuwar mami ne, abinda kuma na fahimta itafa gani take son Mami kake gaskiya shiyyasa take duk waɗanan abubuwan”. Tsaki Jawaad yaja yana yamitse fuska cike da takaici amma baice komaiba. Suma shirun sukai basu damu da rashin bada amsarba, dan a ganinsu idan son Bilkisu yake wataran ai dole ta fito fili ko. Jabeer ne ya katse shirun nasu da faɗin, “Gaskiya boss hakan ba shine mafitaba, na farko Rose tasan sirrikanmu da yawa, yaƙi take akan soyayyarka a yanzu, idan kace ta barmu zaitai amfani da wannan fushin ta koma cin dunduniyarmu, munada muhimman ayyuka a ƙasa waɗanda munyi zurfi sosai na kaiwa ga nasara, sune zata fara harin ɓatawa, karka manta zagaye muke da maƙiya, ƙaramar ƙofar da za'a kutsa cikin mutuncinmu kawai ake nema dama, magana ta ƙarshe kuma Rose zatabi duk hanyar da zuciyarta ta ƙawata mata ta cutar da mai sunan mom batare da munsan tayaya ta shirya hakanba, kaga kuwa tako ina korarta ba mafita zata bamuba, domin iyakar gudunmu dai bai wuce kabi ta ƙasa kasa aimata transfer ba, duk nisan da kake tunanin zatayi damu ALLAH saita dawo koda ta hanyar saka wanine yay mata aiki kuwa”.
Dukansu sun gamsu da maganar Jabeer. Aliyu yace, “Maganar Jabeer fa gaskiyace Jay, sawa tabar cikinmu ba mafita bace, gara ace muna ganin duk motsinta, sannan ni a ganin idan kanason Mami ɗin miza hana ka fito ka bayyana mata kawai a wuce wajen, da zafi-zafi ake bugun ƙarfefa a wannan zamanin”. Fuska sosai Jawaad ya haɗe, cikin nuna halin ko in kula ya wani taɓe baki yaƙi cewa
komai a karo na biyu kan maganar Bilkisu. Duk idanu suka zuba masa na mamaki, sun rasa miyake ɓoyewa. Sai da ya shaƙi iska dan kansa sannan yay magana, “Kuna ɓatamin rai da shirmennan naku, kunefa dalilin shigowar wannan yarinyar cikin tawagarnan, amma miyasa kuke son maida zancenta wani abu daban, to inagama ba rose bace ta cancanci yin nesa damu, Miemaa zansa aima transfer, ince dai shikenan”.
Da sauri Hafiz yace, “Ba shikenanba, yarinyarnan yanzune ta fara aiki, ƙwazon data fara nunawa yana buƙatar a cigaba da horar da ita akan gaskiya, munji ba sonta kakeba, kuma insha ALLAH babu mai sake maka wannan maganar, inaga kawai mu zauna dasu ita da Rose kajama Rose dogon gargaɗi akan wannan haukar tata mara tushe, domin munutsu mu fuskanci sauran ayyukan dake gabanmu, yanzu aikinan da muke wlhy yanada matuƙar sarƙaƙiya da haɗari, amma gashi muna wasa dashi, sai dau ku yaya kuka gani?”. Jabeer dake wani shegen murmushi yana satar kallon Jay yace, “Hakan yayi nidai a wajena, gara a bar mana Miemaar mu muyita kwasar albarkacin sunanta”. Hafiz da Aliyu sukai dariya, dan sunsan shaƙiyancin Jabeer ne ya motsa, Jawaad kam uffan baiceba, saima miƙewa da yayi yay musu sallama ya fita.
Yana fita duk sukayi dariya, Aliyu yace, “ALLAH Jabeer kasama boss ido da yawa, nakula son ƙureshi kake kawai,, ka barshi yasha iskar duniya malam”. Nanma dariyar sukayi, Hafiz yace, “kunga nima bara na koma Office, gayenan addu'armu kawai yafi buƙata”. “Hakane kam” cewar Aliyu dake miƙewa shima.
Fitowar Jay daga office ɗin Jabeer yay dai-dai da fitowar Bilkisu daga motar Qaseem suna murmushi ma juna, dukda a sama yake kuma ta glass yake ganinsu hakan bai hanashi ganin murmushin yamata ƙyauba, dayake ba yawan ganin murmushin nata yakeba sai yazam idan tayi yakan kasance na musamman, ya taɓe bakinsa yana barin wajen.
Bilkisu kam da batasan yanayiba rakkiya tayoma Qaseem dake bata labarin maganar da sukai akan aurensu jiya da Dad.
hakan sai yasani jin daɗi da raguwar nauyin da zuciyarta tayi tun a daren shekaran jiya, a ganina garama nai auren na huta, dan na kula zamanmu a haka haɗarine babba a gareni, maganganun Dad na jiya akan fyaɗen mai aikin su Nazifa ya mugun tsaya mani a rai, inada yaƙinin irin wannan ƙaddarar ta afka tsakanin ni da ƴaƴansa to wlhy nikaɗai zanyi kukana, dan tabbas zai goya musu bayane, a yanda kuwa Yah Qaseem ke kaima jikina hari da halayyar Salman da batai minba komai zai iya faruwan, to maganin ayi kar a fara kawai.
Saida nai masa rakkiya har office ɗinsa sannan na juya na sauka namu, saida na gaisa da kowa sannan na zauna mazaunina, Computer ɗin gabana na kunna domin duba gajeren video da boss ya bani nai sharhi akan abinda na fahimta ciki, gaba ɗaya hankalina na maida akan aikin har Ummie data makara yau ta shigo, gaisuwa tayi da sauran sannan ta matso inda nake ta bani hannu muka gaisa idonmu akan video mu duka. “Bily jiya wai miyasa kika gudu bayan kinsan magana mai muhimmanci muke tattaunawa a group?”. Murmushi nai mata ina cigaba da control ɗin mouse ɗin Computer a hannuna na haggu, na damar kuma ina riƙe da pen ina rubutu a takarda. “Hankalina ne yay masifar tashi Ummie, al'amarinne akwai ruɗani a ciki, dan na fara zargin mai aikata ɓarnarnan ba mutum ɗaya bane sai dai ƙungiya garesu”. Kujera ta jawo ta zauna saɓanin da da take tsaye ta ranƙwafo jikin tebirina, tace, “Miyasa kikai wannan tunanin bily?”. Kallonta naɗanyi na ɗauke kaina ina cigaba da aikin gabana, nace, “Saboda Amina mana, kinga su su Nazifa a gida ɗaya akai musu ita da marigayiyya, sai kuma na yarinyar jiya, amma ita Amina ai a gidanmu akai mata, yanda ake salon fyaɗen duk iri ɗayane, sai an bugar dasu ake cutar dasu, sannan babu wandda ta taɓa ɗaukar ciki a cikinsu, zuwa yanzu ina buƙatar mu haɗu waje ɗaya mu duka biyar ɗin, dan yadace mushiga binciken neman sauran waɗanda hakan ta faru garesu, inaji a jikina Ummie basu kaɗai bane akwai wasu”. Na ƙare maganar da kallonta idanuna cike da ƙwalla. Kanta ta girgizamin a hankali alamar karnai kuka, na ɗauke kaina ina haɗiye abinda ya tokaremin maƙoshi mai nauyi d
a ƙyar.
Nuna mata Computer ɗin nayi ina zooming ɗin wani waje cikin video ɗin da faɗin, “Ummie kalla dan ALLAH mikika fahimta a wajen nan?”. Matsowa tayi sosai tana kallon wajen cike da nazari, kafin ta amshi mouse ɗin hannuna ta maida video'n slowly, “Kai bily kilura da ƙyau wani kasuwancin kurame akeyi a wajen nan fa, ki kalli zuwan yarinyarnan wajen da ƙyau, kafin ta ƙarasa wajen shi wannan mai kifin saida suka kalli juna da mai raken can sukaima juna wata inkiya da idonu, sannan bakin mai kifin ya motsa alamar magana yayi”. Kaina na shiga jinjina mata, nace, “Haka nima duk na fahimta Ummie, to amma sam na kasa fahimtar mi mai kifin ya faɗa, na maimaita wajen yafi sau goma wlhy, amma kuma abin lura anan shi wacan mai facin minene ya ɗauka cikin tayoyi ya bama gurgun yaron can almajiri?”. Baya ummie ta dawo da video dai-dai wajen, da alama mai ɗaukar video bai saka da mai facinba a ɗaukar, dan acan gefe yake yana harkokinsa shi kaɗai, hakan yasa ba komai ake iya fahimta dangane da shiba. “Bily kinsan mizakiyi?” nace, “A'a saikin faɗa”. kije office ɗin boss kimasa bayani, inba hakaba zamu iya rikita komai anan”.
Gabana ne ya faɗi jin ta ambaci boss, abinda ya faru jiya ya shiga mani kaikawo, gashi yau yanda na lura baije duba aunty Shahudah bama tun jiya da safe kamar yanda naji iyayenmu na tsogumi a asibitin, ALLAH dai yasa ba maganata bace ta jawo hakan, dan yakamata ace ya cika alƙawarin daya ɗaukama Dad na zuwa gidanmu a daren jiya......... “Lafiya kuwa? Ina magana kin tafi tunani”. Numfashi na kawo ina dafe kai, nace, “Babu komai, bara nakai masan”. Nasan yanda nai maganarne a sanyaye ya sakata bina da kallo, ban yarda mun haɗa idoba na cire flash ɗin daga Computer'n na ɗauki takardun danake rubuta bayanan na tattare cikin file ɗin daya bani jiya na fita. Maimakon na nufi office ɗin nashi saina tafi office ɗin Oga Aliyu. knocking nai aka bani izinin shiga, su biyu na iske a ciki, hakan yasani gaishesu na tsaya gefe su kammala, dan naga magana suke. Basu wani ɗauki lokaciba wancan ya miƙe ya fita, oga Aliyu ya nunamin kujera alamar na zauna, sake gaidashi nayi sannan na zauna ina ɗora takardun hannuna a tebirin gabansa. “Mami ta samune?” yay maganar cikin zolaya. Murmushi nayi nima na bashi amsa da “Sosai ma”. Yay ƙaramar dariya yana amsar takardun, “To ALLAH yasa mai washa-washa ne da zamuci mu more”. Yanzunkam saida naɗan dara kaɗan, dan bansan yana magana mai tsaho hakaba, yaɗan duba takardun sannan ya kalleni, “Mami ban fahimci komaiba anan, na minene?”. Hannuna naɗan matsa kaɗan sukai ƙara, na muskuta zamana, “Oga Aliyu bayanan daga wani video suke” nai maganar ina miƙa masa flash ɗin hannuna da cigaba da faɗin, “Nice na haɗasu anan, to kuma na cije a wani waje shine nazo neman haske”. shiru yay na sakanni batare daya amshi abin hannunaba, kafin yace, “Okey, wanene ya baki aikin a cikinmu?”. Nace, “Boss ne”. Takardun ya miƙomin, “Kinga to kije wajensa, dan bansan case ɗin miye ba, nasan zai miki bayanin duk da zaki fahimta”. Shiru nayi na kasa amsar takardun.
Aliyu dake kallonta yace, “Da matsalane?”.
Kaina na ɗago na kallesa, sai kuma na sauke idanuna ƙasa, “ALLAH oga shi ya cika faɗan tsiya, yaytama mutane mazurai”. Dariya sosai Aliyu yayi da wannan magana tawa, saida ya gaji dan kansa yay shiru, sake miƙomin takardun yayi har yanzu fuskarsa da murmushi, “Ai sai an masa ba daidaiba yake mazurai, tunda akan aikine zai fahimceki bazaiyi faɗaba kinji”. Kaina na jinjina masa, badan nasoba na amshi takardun na fita. Jinake kamar karnaje, amma wani sashe na zuciyata na bani shawarar naje dan akan aikine, bai kamata kuma na sanya wasa akan aikinaba, nidai na kiyaye duk wata hanya da zata sake haɗani dashi harnaga fushinsa kamar na jiya kawai. Da wannan ƙwarin gwiwar na nufi office ɗin, knocking nai aka bani izinin shiga, gabana sai faman faɗuwa yake na tura ƙofar da sallama a ƙasan maƙoshi na shiga.
Tarin aikine jibge a gaban Jawaad, ko buƙatar shigowar wanima babayi office ɗin, hakan yasa koda Bily ta shigo sallamarta kawai ya amsa amma bai ɗagoba, ƙarasowarta gabansa ƙamshinta
ya tabbatar masa itace, sake ɗaure fuska yay sosai fiye da yanda ta shigo ta sameshi.
Kallo ɗaya naima fuskarsa na ɗauke kaina, a ɗaure take fiye da kullum ma dana sani, gaba ɗaya ƴar jarumtar dana shigo da ita saita gudu itama, gashi yaƙi kallon ko inda nakema dukda inada tabbacin yasan nice na shigo. Da ƙyar na iya daurewa nace, “Ina kwana Sir”. Batare daya kalleniba yanzunma yace, “Lafiya”. Shiru nai nakasa cigaba da magana, dan yanda ya amsa gaisuwar tawa a daƙile ya sake sanyayamin jiki sosai, ganin tsayuwar tawa bata da amfani na daure nace, “Sir dama akan aikin daka bani ranar monday ne”. Harna fidda rai da samun amsa sai naga ya nunamin kujera batare daya ɗagoba. Ɓoyayyen nunfashi na sauke ina ƙara ƙoƙarin ƙarfafa kaina. Na ajiye takardun hannuna a gabansa kafin naje na zauna a kujerar, shiru muka sakeyi na mintuna, saida ya tattare wasu takardun gabansa waje guda ya ajiyesu gefe kafin ya kalleni. Saurin nuna masa takardun dana ajiye nayi. Janye idanunsa yay daga tsatstsarenin da yay dasu ya ɗauki takardun, shiru tsawon wasu mintuna yana dubasu kafin ya ɗago, yace, “Kin gama ne?”.
Sau ɗaya na kallesa na ɗauke idanuna ganin ni yake kallo, na girgiza kaina, “A'a ban gamaba, akwai wani wajene a video'n to sai nakeson ka gani kafin na shigar da bayanansa” na ƙare maganar da miƙa masa flash drive ɗin, bai amsaba ya ɗauke kansa daga gareni ya maida ga Computer ɗin gabansa, “Taso kisa”. kamar nai kuka haka naji, sai dai bani da wata mafitar daya wuce bin umarninsa, inda yake naje, a mamakina sai naga ya tashi daga kujerar tasa ya nunamin alamar na zauna, batare da yace uffanba............✍
Yau shafin nakune ƴan telegram, kuma ku warwasa da wannan, alkairin ALLAH yakai gareku aduk inda kuke, ammafa babu canji mun ƴan hud-jay team ne😜😂😂😂😍😍😘😘😘.
ALLAH ka gafartama iyayenmu🙏🏻😭.
Bilyn Abdull 📚:
Telegram link group ɗinmu kenan, dan wasu sunata tambaya cewa ya zasu shiga, indai kana tele to kawai ka antaya MASARAUTAR BILYN ABDULL tanan.
https://t.me/joinchat/TIsXYRvhtri2kQ9E4x7w6g
Page 19
................Idanunsa sunyi masifar kaɗawa sunyi jajur, batare da yace dani komaiba yaymin nuni da ƙofa alamar in fita, kasa koda motsi nayi, sai hawaye dake cigaba da ambaliya a kumatuna tamkar an buɗe fanfo.
Cikin matuƙar kaushin murya da tsawa na tsinkayi furucinsa cikin kunnuwana, “Miemaa! niɗin sa'anki ne ko?!”. Da sauri na shiga girgiza masa kai jikina na rawa saboda harga ALLAH na matuƙar tsorata da yanayinsa. Ya sake faɗin, “Tashi kifita a office ɗinan kafin naimiki duk abinda yazomin kai, Yanzunan har idonki yakai tsaurin kallona ki faɗamin abinda ya dace dani?!, ki fitar min anan kona sauya miki kamanni!!”. Kuka na sake fashewa dashi ina saurin jan jikina nai baya gudun karya makeni, dan harga ALLAH tausayin Dad na tsaga dukkan jijiyoyin jikina harda aunty Shahudah, na tabbatar samun boss ga aunty Shahudah shine farin cikin gidanmu, Hawayen dake ziraromin na share tare da faɗin “Kayi haƙuri dan ALLAH, bazan sakeba”. Cikin faɗan dana rasa abinda ya fusatashi irin haka yace..... “Baki jiniba ko?!” yay maganar a hasale yana tasowa kaina, Baya na shiga jan gwiwoyina batare dana tashiba, matsanancin fushin dana gani akan fuskarsa ya bani tsoro matuƙa, bantaɓa tunanin yanada zafin zuciya irin hakaba, ya nunani da ɗanyatsa yana faɗin, “Badai kece kika buƙata da kanki ba, to duk abinda ya biyo baya kiyi kuka da kanki ba daniba Miemaa, zan aureta tamkar yanda kike buƙata, amma wlhy ko sau ɗaya kikai ƙorafin hakan wataran saina hukuntaki da mafi girman hukunci, indai Hudah ce gaki ga tanan shashashar banza”. Ya ƙare maganar yana ranƙwafowa kaina ya fisge rigarsa dake hannuna ya fice daga office ɗin”.
Ɗif naji komai na ya ɗauke wuta yabar aiki, sam narasa awane mizani zan ɗora ruɗaɗɗun kalamansa marasa tushe balle makama, man kaina gaba ɗaya ya tsiyaye, babu wata jijiya dake ɗaukar saƙon ƙwaƙwalwa zuwa zuciya dake aiki a jikina har tsahon wasu mintuna da naji saukar abu mai ɗumi a jikina. Zumbur na miƙe domin samun dawowar hankalina daya gushe na wucin gadi. Ban sami damar gama tattaro abinda ya shuɗeba idona ya sauka akan Oga Jabeer dake bakin ƙofa a tsaye yana kallona. murmushi yaymin kafin ya ƙarasa shigowa office ɗin, “Tashi ki shiga toilet ki wanke fuskarki kinji” Ya faɗa yanamin nuni da hannu. Ban musa masaba na miƙe, dan koba komai ina buƙatar duba halin da nake a ciki.
Bani da isashen lokacin fashin baƙi akan ruɗaɗɗun kalamansa, dan kaina tsaye ina dangantasune kawai da rufewar ido ga mamallakin furtasu, to danmima zuciyata kesan rikitani da hasashen abinda bazai taɓa zama hakaba, na ƙurama kaina ido a madubin dake cikin toilet ɗin ina mai tariyo kalaman dallah-dallah yanda zasu bani fassarar da nake buƙata, “{Duk abinda ya biyo baya kiyi kuka da kanki badaniba Miemaa, zan aureta tamkar yanda kike buƙata, amma wlhy ko sau ɗaya kikai ƙorafin hakan wataran saina hukuntaki da mafi girman hukunci, indai Hudah ce gaki ga tanan shashashar banza}”. ‘Kenan yana nufin inhar aunty Shahudah ta sake koma masa da halinta na baya akwai hannuna wajen cutar dashi? Kuma nizai kuhunta ba itaba? To miyasa? Miyasa zan zama laifi akan ƙoƙarin ganin na inganta auren sunna, na haɗa zukata biyu masu ƙaunar junansu, na tabbata shima yana sonta kawai halayyarta yake ƙyamata, to miyasa ni laifin zai tattara a kaina kuma?’ “Saboda kalamanki ne suka tursasashi yarda ta koma” wata zuciya ta ayyanamin daga can ƙasan rai, ‘To miyasa zai amince da abinda bai zama wajibiba? Ni shawara na bashi da nuna masa ƙwaɗayin samun lada ai ba tilasba, sannan na ceto zuciyar Dad daga ɓacin ran tashin hankalin gudan jininsa, kenan hakan yana nufin kuskure nayi?, ni wacece da har zai amshi roƙona ya wajabtama kansa?, nasake tambayar kaina hawaye na silalomin. Nima kaina sai yanzu naga ƙarfin halina da wautata akan taryarsa, banyi tsammanin zan iya hakanba koda a cikin mafarkine kuwa, zan cigaba da roƙon ALLAH ya hana faruwar mat
salar da yake hangowar, insha ALLAHU lafiya zasu zauna abinsu. Haƙura nai da tunanin na kimtsa jikina da tissue ɗin dana gani a toilet ɗin dan inada tabbacin zai riƙeni har zuwa a tashi insha ALLAHU, na sake ɗauraye fuskata na fito. Zaune na iske oga Jabeer, yana ganina yay ƙaramar dariya da faɗin, “Anya maman nan tamu ba raguwa baceba?” murmushin da ban niyyaba ya suɓucemin, na girgiza masa kai ina faɗin “a'a sir”. Dariyar ya sakeyi da cewar, “To ALLAH yasa, yanzu daga nan sai ina kuma?”. Nace, “Zan koma Office ne, akwai aikin da boss ma ya sani tun ranar waccan monday ɗin ban kammalaba”. Ya miƙe yana faɗin, “To masha ALLAH, nima bara na koma office, amma daga yau idan kikaga Jay a irin wannan matsanancin fushin ki daina masa naci akan koma wane irin maganace, dan idan yay fushi irin haka akwai matsala, ALLAH ne ya taimakeki ya zaɓi ya fita yabar miki office ɗin, amma dabai fitanba ke kuma kika cigaba da taurinkan kin fita komai zai iya biyo baya, ki kiyaye kinji, boss ya wuce duk yanda kike zatonsa, mutumne murɗaɗɗe mai wahalar sha'ani matuƙa, idan yaso kaji dadinsa baka taɓa fahimtar tsaurinsa, idan baiso hakanba wahala zakasha ta gaske”.
Nace, “Insha Allah zan kiyaye nagode sosai”.
“Hakan shine dai-dai, ALLAH ya kiyaye gaba”.
Tare muka fita, shi ya nufi office nikuma na sauka ƙasa, harna fara tafiya sai naji ina buƙatar ganin yah Qaseem, dan tunda mukazo yau ban gansaba kuma bai nemeniba, ko a waya.
Nayi knocking kusan sau uku babu amsa, hakan yasani tura ƙofar office ɗin a hankali na shiga, zaune na sameshi a kujerarsa, ya kwantar da bayansa jikinta idanunsa a lumshe, na sake maimaita sallamar tawa idona kafe a kansa. A hankali ya buɗe idonu yana kallona, sai kuma ya tsashi zaune sosai yana murmushi damin alamar nazo da hannu. Takawa nai a hankali zuwa garesa, na zauna a ɗaya daga kujerar gaban tebirinsa idona har yanzu a kansa. Wani murmushin ya sakemin, kafin ya buɗe baki a hankali cikin sanyin murya yace, “Har yanzu jikin dai bilkisu?”. “A'a Yah Qaseem naji sauƙi, mike damunka? Tunda muka baro gida baka da walwala, gashi har yanzu ina ganinta a saman fuskarka kuma, mike faruwane?”.
“Humm” ya faɗa yana cije baki, kafin yace, “Babu komai, kawai dai banajin ƙarfin jikinane”. Numfashi na sauke a hankali fuskata na nuna tausayinsa, nace, “To ko zamu tafi gida kaga likita”. Nanma kansa ya girgiza mani, cikin kauda maganar yace, “Kinci abinci ko?”. Kaina kawai na iya ɗaga masa, dan jinai dukna damu da halin da yake a ciki, shiru mukai na wasu mintuna kafin na miƙe nace, “bara na wuce dama leƙoka nayi dan naji shiru”.
Baice komaiba saida na doshi hanyar fita daga office ɗin, “Ki ƙoƙarin gama abinda kikeyi, da anyi la'asar zamu wuce dan yanzu Mom ta kirani jikin Shahudah ya sake rikicewa”. Sosai naji gabana ya faɗi, na kaɗa masa kai kawai ina haɗiye ƙwallar data cika mani ido, “ALLAH ya bata lafiya” “Amin”. ya amsa mini akan laɓɓa.
★★★★★★★
A ɓangaren Jay kuwa gaba ɗaya yarasa gane kansa, haka kawai ya tsinci zuciyarsa da fushi mai tsanani, koda ya fita daga station rasa ina zai dosa yayi, yata zagaye gari daga wannan titi zuwa wannan har ƙarfe biyar na yamma, sallar la'asar kawai ya tsaya yayi da lokacinta yayi, ganin yamma tayi saiya juya kan motar Jabeer daya ɗakko daga office ya nufi gidan Alhaji baba kakansa.
A ƙofar gida ya iske Alhaji baba da tsaaffin anguwar a bishiyar dalbejiyar dake ƙofar gidansa, inda yake zama duk yamma yasha iska koda hantsi, sai yazam tsaffin dake anguwa sukanzo suma su zauna suyita hira, a kusa dasu yay parking, yaja kusan mintuna uku bai fito a motarba, tsoffin nata magana akan wanene? Amma bai tankaba balle ya fita, shiko Alhaji baba bai tankaba, dan yaji a ransa Jawaad ne dukda yasan ba motarsa bace, kuma glass ɗin motar nada duhu ba'a ganin na ciki.
Sai da ya mula dan kansa ya buɗe ya fito. Alhaji Baba ya bisa da kallo kawai batare da yace komaiba. Jawaad ya rissina ya gaida tsoffin kafin ya miƙe ya nufi hanyar gate ɗin gidan batare da yacema Alhaji baba komaiba. A falo ya zube saman doguwar kujera ko takalmi bai cir
eba, ya lumshe idanunsa yana maijin kewar iyayensa na tsarga masa da zafi-zafi, a yau babu abinda yake tsananin buƙata sama da ɗumin mahaifiyarsa, burinsa kawai ya ɗora kansa a cinyarta tana shafawa da tambayar damuwarsa, shiko ya juye mata duk abinda ke ransa ta bashi shawara da masa addu'a. Sai dai kuma gashi ƙaddara ta daɗe da hana hakan a jerin farin cikin rayuwarsa, ƙilama tuna tabar masa duniyar bai saniba, kokuma ta fita hayyacinta fiye da yanda zata iya tuna ita wacecema balle abinda shi ta haifa, amma duk yanda take yanason abinsa, zaiyi farin ciki da maraba da ganinta a duk yanda take.
Buɗe idanunsa yay saboda saukar hannun Alhaji baba a saman fuskarsa yana share masa ƙwalla, Alhaji baba yay murmushi cikin zolaya yace, “Kullum kai saika kwaso ragwantakarka ka kawomin gida, ina namijin dake filin daga ina kuka Muhammadu”. Murmushi Jay yayi tareda lumshe ido yana rungume hannun kakan nasa a cikin wuyansa, baidaice komaiba, hakan yasa Alhaji baba ɗaga kansa ya zauna sannan ya maida kan saman cinyarsa ya ɗora, ahankali ya shiga shafa kan Jay dake cinyar tasa, hannunsa ɗaya kuma na shafa fuskarsa da ƙananun gashin saje da bai askeba ke kwance a jiki. Shiru sukai gaba ɗaya, Jawaad yay lamo a jikin kakansa yana sauke numfashi a hankali, tuni kaso mafi yawa na damuwarsa yaji ya gudu, tsahon lokaci suka ɗauka a haka babu wanda yay magana, ganin lokacin salla ya gabato Alhaji baba ya shafa fuskar Jay yana faɗin, “Muhammadu tashi kaje kai wanka kayo alwala muje masallaci”. Buɗe idanu Jawaad yay a hankali, sun ƙanƙance sosai alamar yanajin barci, tashi yay ya nufi ɗakin kakansa dan baida matsalar kaya tunda yana ajiyewa anan. Cike da tausayawa Alhaji baba ya bisa da kallo, yana tsananin son jikan nasa tilo namiji da tausayinsa matuƙa, a kullum baya gazawa da yimasa addu'ar kariya daga dukkanin abin ƙi da maƙiya.
Ana ƙoƙarin shiga sallah Jawaad ya fito a gaggauce cikin jallabiya ruwan siminti, sai ƙamshin turaren kakansa yake mai sanyin daɗi, tare suka tafi massalaci dan Alhaji Baba yayi alwala a toilet ɗin falo. Koda aka idar sai sukai zamansu acan har isha'i, bayan sun fitone Alhaji baba yay sallama da mutane da neman gafara ga wanda ya ɓatamawa bisaga al'adarsa, dan acewarsa bai zama lallai yana cikin jerin masu tashi suga safiyar gobe ba, shiyyasa duk bayan kowacce sallar isha'i yakanyi sallama da maƙwaftansa da neman gafararsu kafin ya shige gida. Sun iske Nabeelah ta kawo masa abinci kamar kullum, tunda ta gaida Jay sau ɗaya ya amsa yay kwanciyarsa a doguwar kujera, sai hira suke ita da Alhaji Baba, zuwa takwas da rabi tai musu sallama ta tafi dan tare suke da driver dama. Tana fita Jawaad ya sakko ya shiga buɗe kulolin da aka jero cikin kwandon mai ƙyau daga gidan Ummah, tuwone kamar kullum dare da Alhaji baba ya wajabtama kansa, jay ya miƙe zuwa kicin ya ɗakko filet da cokali, tuwon alkamar ya dawo ya ɗiba da miyar ɗanyar kuɓewa, shidai Alhaji baba nata tsokanarsa da gwauro kafi tuzuru. Wani ya tanka wani yay shiru, sai kuma a hankali ya saki jikinsa sukai hira sosai kamar yanda Alhaji baba ya buƙata, cikin hikima kuma yake masa nasiha, sai wajen sha ɗaya suka kwanta, dan Jay yace anan zai kwana yau, da yayi sallar asuba sai ya wuce gida.
★★★★★★
Ƙarfe huɗu da rabi muka bar office, daga nan asibiti muka nufa, mun iske jikin aunty Shahudah kan babu daɗi, dan yanzunma dai saida tasha allurar barci. Anan muka zauna har magriba saboda kowa yana nan sannan muka tafi kamar yanda Dad ya bamu umarni. Har zuwa yanzun dai Yah Qaseem bashi da wata walwala, muna isa gida kuma kowa yay ɗakinsa, naji haushin ganin ɗakina kaca-kaca, yanda Aunty Aamilah ta tashi haka ta barminshi uwa turken jakai, gadon na fara gyarawa nai shara sannan na shiga wanka, dama gaba ɗaya a takure nake, saidai maganin da boss ya bani ya mugun taimaka mani, dan jina nake sakayau babu ciwon marar sai abinda ba'a rasaba. Kamar yanda na saba har alwala saida na ɗaura dukda ina fashin salla, sannan na fito nai shirin barci, gado na haye na buɗe data, dan munada meeting dasu Ummie akan bikin Nazifa, munyi nisa a firarmu
sosai Nazifa tai wata maganar data saka zuciyata bugawa lokaci guda, “Sisters wlhy akwai matsala, ko kunsan a daren jiya anyima jikar marka mai aikinmu fyaɗe, kuma kamar dai namu ne itama saida aka bugar da ita”. Ina gama karanta abinda Nazifa ta rubuta na saki wayar a kan gado jikina na wata irin rawa, a wani irin firgici maiban tsoro na tsinci kaina a ciki, na shiga waige-waige a cikin ɗakin tamkar mai tsoron ganin wani abu, a wani irin matsanancin ihu na shiga faɗin, “Ya isa!! Nace ya isa!!! Ya isa haka nan Pleaseeeeeee” na ƙarashe faɗa da sanyin murya ina fashewa da kuka, Aamilah Da Dad ne sukai rige-rigen shigowa ɗakin saboda jiyo sambatun Bilkisu.
Dad ya riƙo hannunta data tattare bedsheet ta matse a ciki yana faɗin, “Daughter! K daughter miya faru??”. Bilkisu ta kuma fashewa da kuka tana kallon Dad dake riƙe da hannunta, Aamilah a gefensa, “Dad dan ALLAH kuce dasu ya isa haka, su bari hakanan” ta cije baki tana zazzaro idanu cikin ficewar hayyaci ta fisge hannunta ta tashi zaune a kan gadon, ta bubbugashi da ƙarfi na alamun ɗaukar alwashi, kafin tacigaba da magana cikin kaushin murya, “Wlhy wlhy Dad, inhar basu dainaba, ni da hannuna saina kakkashesu, gunduwa-gunduwa zanyi da namansu naba karnukan office ɗinmu su cinye, kamar yanda suke bibiyarmu wlhy nima zan cigaba da bibiyarsu, subar ganina mace, duk mai hannu a ciki sai ya shiga uku a hannuna, wlhy halakashi zanyi Dad, saina halakashi” ta ƙare maganar da fashewa da kuka tana faɗawa jikin Aamilah.
Sam Dad bai fahimci komai daga zantukan Bilkisu ba dake fita a murɗe, yama fara tunanin yarinyarnan ko aljanune da ita, jiba jiya yanda suka bashi labarin an basu tsoro a gidan, kuma ita tafi kowa firgita da shiga ruɗani, ahankali ya juya ga ƙofa saboda jin motsi, Salman ne da Qaseem, Qaseem ya jiƙe sharkaf da zufa dukda fanka dake aiki a ɗakin, gashi idanunsa sun kaɗa sunyi jazur har ana iya hango yanda jijiyoyin kansa sukai ruɗu-ruɗu.
“Qaseem kaikuma mike damunka?” Dad ya faɗa da tsagwaron mamaki, Salman da shima dai jikin nasa a sanyaye yake ya kalli Qaseem tare da dafa kafaɗarsa, kallonsa Qaseem yayi shima, sai dai babu wanda ya iya cema ɗan uwansa komai, saima Qaseem ya zame hannun Salman a jikinsa ya juya ya fita daga ɗakin.
Dad ya sauke nannauyan numfashi, dan shifa al'amarin ƴaƴan nasa ya fara bashi matsanancin tsoro, shin mike faruwane haka wai?. Babu mai bashi amsa dan haka yay shiru kawai ya zubama Bilkisu dake shashshekar kuka a hankali idanu. Ita kanta Aamilah duk iskancin nan nata yau a firgice take, dan tsaf bata manta tsoratasun da akai jiyaba, hakan yasa Bilkisu na fara sambatu itace farkon jiyota.
Dad ya kamo hannun Bilkisu yana rabota da jikin Aamilah, “Bilkisu tashi ki faɗamin mike faruwa?”. Babu musu Bily ta tashi zaune, Dad ya sake cewa, “Miya farune? Jiya ance an tsorataku musamma k, yau kuma gashi mun jiyoki kinata sambatu?”. Hawayen daketa faman ziraro mata ta share.
Naɗan kalli Dad ƙaɗan na maida kaina ƙasa, cikin muryata data dishashe a yinin yau gaba ɗaya nace, “Dad fyaɗe akaima ƴar mai aikin gidansu Nazifa” shiru yay kawai yana kallona har nakusan sakanni ashirin, kafin ya girgiza kansa cikin wani yanayi yace, “To Bilkisu shine kuma kike irin wannan mahaukacin kukan?, ƴar gidan waye a cikin ƙawayen naki abin ya faru a gidansu?”. “Gidan Alhaji Sufyan magashi”. “To ALLAH ya kiyaye, ki kwantar da hankalinki shima ai zai ɗauki mataki, inake ina shiga irin wannan maganar ƴar ƙaramarki dake, sannan kuma ma k miye naki a ciki? Ai can matsalar family ɗinsuce, muma muji da tamu gatanan kinji”. Kaina kawai na ɗaga masa cikin tsantsar takaicin furucinsa, yaukam na sake girmama al'amarin Dad fiye da tunanina, miyasa shi kansa kawai ya sani sai ƴaƴansa? Yanzu da ace Aamilah ko aunty Shahudah akaimawa ai da bazaice hakaba ko, anya kuwa koda a kaina wannan abun ya faru Dad zai nuna damuwarsa kuwa?. Sosai gabana ya faɗi da zuwan wannan tunanin a cikin raina, nayi nisa sosai a tunanina har bansan lokacin dasu Dad suka bar ɗakinba, kawai juyawa nai na jini kwance a gado har an lulluɓeni da bargoma, a
unty Aamila na kwance a gefena da alama ta jima dayin barci ma, nasan badan tsoron da takejiba bazata taɓa zuwa ta raɓeniba.
Dad kam koda suka fita a falonsa na sama ya iske Qaseem zaune yana jiransa, da mamaki ya kallesa. “Kana nufin dama ba zuwa kai ka kwantaba?”. Kai Yah Qaseem ya jinjina alamar eh. Dad ya zauna kusa dashi cikin kulawa yace, “Mike faruwa?”. Kallonsa Qaseem yayi, murya a sanyaye yace, “Dad inason a saka ranar aurenmu ni da Bilkisu”. Shiru Dad yay kawai yana kallon Qaseem tamkar yaune ya fara ganinsa, kusan mintuna biyu kafin ya jinjina kansa, yace, “Shikenan za'ayi hakan, to amma ita kaji ra'ayinta akan ta shirya aure yanzun?”. Kai Qaseem ya jinjina, yace, “Munyi magana da ita ranar, dama dawowarka nake jira Dad, banason asa bikin da nisa kuma, karya wuce wata ɗaya”. Dad yay murmushi cike da tsokana yace, “A lallai wannan angon a shirye yake, yanzu dai kaga Ramadan baifi saura kwana goma sha uku ba ya rage mana, lokaci yazo a ƙure kenan, saimu saka bikin bayan salla kenan kamar da sati biyu, zan fara nemar dangin mahaifinta muyi magana dan wannan huruminsune dukda sun wofantar da al'amarinta, kaga sai a haɗa tare dana mamana kawai ayi a huta”. Fuskar Qaseem ɗauke da murmushi yace, “Shikenan Dad nagode sosai, ALLAH ya ƙara lafiya da nisan kwana”. “Amin ya rabbi” Dad ya faɗa yana mamaki a ransa yau Qaseem ya masa godiya akan abu, lallai kusanci da Bilkisu ya kawo cigaba a wani ɓangare na rayuwar yaransa, dan shikam bazai iya tuna randa yayma Qaseem abu yaymasa godiyaba balle akai ga addu'a ma baki ɗaya. Sallama Qaseem yay masa ya sakko, sai da ya leƙa ɗakin Bilkisu yaga sunyi barci ita da Aamilah sannan ya wuce sashensu zuciyarsa najin daɗin ya kusa mallakar bilynsa.
★★★★★★
A ɓangaren Jawaad kuwa bayan an idar da sallar asuba yanayin azkar ya fita daga massalacin, motsa jiki yaɗan zagayo ya koma gidan Alhaji baba, a falo ya iske tsohon zaune yana duba wani littafin addini, Jay ya gaidashi da girmamawa kafin su koma tsokanar juna, ganin lokaci yaja ya miƙe yana faɗin, “Bara nai wanka nazo naje gida na shirya daga can na wuce office”. Cikin zolaya Alhaji baba yace, “To agogo sarkin aiki”. Dariya Jay yayi yana miƙewa da faɗin, “Nikam sunayen da kake jeramin sun isa hakanan”. Alhaji baba yace, “To gwauro na daina”. Juyowa Jawaad yay zai bashi amsa hannunsa ya tanƙwaɓi ɗaya daga cikin hotunan da Alhaji baba ya jera saman wata ƙyaƙyƙyawar drawer dake hanyar shiga bedroom. A take hoton ya kifo ƙasa ya shiga bada ƙarar fashewa................✍
Gaisuwa da tarin fatan alkairi a gareku ƴan wattpad, wannan page ɗin yau nakune ku kaɗai, kuyi birgima a ciki ku more😂😘😘😘😍😍😍.
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻
0 comments:
Post a Comment