Page 21
...............Kallonsa nai ya zubamin harara, babu shiri na ɗauke idanuna na zauna kamar yanda ya buƙata a lallausar kujerar tasa dariya nazomin a cikin rai, danni mamakin yanda ya iya harara wa mutane nake, sai kace wani mace. Da ƙyar na iya riƙe dariyar daketa son fallasa na saka flash ɗin a jiki, duk abinda nake yana tsayene a kaina harna kunna video ɗin. Har ya kai karshe ya sake komawa baya baice komaiba, ganin mun maimaitashi sau uku yaƙi magana saina juyo dan inga koma dai nikaɗai nake kallon. Mamaki ya kamani ganinsa tsaye a bayana hannayensa duka biyu cikin aljihun wandonsa, idanunsa akan Computer alamar duk yana kallona. “Idan kin gama kallon nawa saiki nuna inda baki ganeba”. Ya faɗa ƙasa-ƙasa, kamar wani mai tsoron a jisa.
Fuska na kumbura tare da ɗauke kaina, a raina nace, ‘Kai wama ya kaika iya kallon mutane’. hannuna na ɗaura saman mouse ɗin nai zumin dai-dai wajen mai faci ina faɗin, “Akan mai facin nan ne dama, kamar akwai alamar tambaya dangane da shi, dan......” kasa ƙarasa maganar nai saboda kusancin da muka samu, a dalilin ranƙwafowar da yay har munajin saukar numfashin junanmu, ya ɗaura hannun hanggunsa saman table ɗin, na damar kuwa saman nawa dake kan mouse. Da sauri na rumtse idanuna, tare dayin azamar janye hannuna dake ƙasan nasa, saboda wani mugun harbawa da zuciyata tai. Baice komaiba, shikam ko a jikinsa, saima ƙoƙarin maida video slowly da yay. Nayi matuƙar takura da tsorata da wannan kusancin namu da yay matuƙar yawa, har takai jikina ya fara rawa, idanuna suka ciko da ƙwalla, sam bana fahimtar bayanin da yakemin ma, dan sama-sama nake jin sautin muryarsa.
Jawaad da duk abinda yake akan sani yayisa ya juyo yana kallonta, ta rumtse idanu zufa dukta tsatstsafo mata a goshi tamkar babu ac a office ɗin. “Hummm” ya faɗa acan ƙasan maƙoshi ya janye jikinsa. A mamakinsa sai yaji ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi, hawaye sun silalo saman kumatunta, saurin ɗauke kansa yay tamkar bai ganiba.
Har bigewa nake da shi wajen rawar jikin miƙewa daga kujerar jin ya matsa, na goge hawayen dake bin kumatuna batare da na bari ya ganiba, gefen tebirin na koma na tsaya kaina a ƙasa nace, “Sir, bara kawai naje can dashi saina ƙarasa tattara bayanan”. Jawaad da har yanzu yake binta da kallo yaɗan lumshe idanu ya buɗe yana ƙoƙarin danne dariyar dake son kufce masa, murya a daƙile yace, “Barshi zan ƙarasa, ɗauka waɗanan files ɗin ki kaima Hafiz, zuwa anjima ki dawo zamu fita”. Bawani fahimtarsa nakeba, kai kawai na ɗaga masa na ɗiba files ɗin na fice cikin sassarfa. A raina banda takaici babu abinda nakeji, miyasa halin mazan wannan zamanin kusan duk ɗayane? Burinsu kawai su taɓa macen da ba muharramarsu ba a matsayin wayewa, ashe shima mutumin nan haka yake ban saniba?, “Aikam na daina sakar masa fuska wlhy” na faɗa a fili cike da takaici.
★★★★
Ƙarfe biyu muka fita cin abinci ni da Ummie, sai da muka gama nai ƙoƙarin biya sai nagama kuɗin dake jikkar tawa bazasu isaba, kusan koda yaushe Ummie ke biya mana inhar bada Yah Qaseem mukazo ba, sai naga da kunya hakan tacigaba da faruwa ai, ATM ɗina na shiga lalube dan na basu su cire, amma sai shima ɗin dai ban gansaba, gabanane ya shiga faɗuwa, dan bama shi kaɗaiba duk cards ɗina basa ciki kenan tunda a tare nake ajiyesu waje guda, kuma inada tabbacin itace jikkar danasan na fita da ita daga gida last. “Wai mikiketa lalube hakane kamar wata makauniya?” Ummie dake shan ruwa ta faɗa bayan ta ajiye kofin. Guntun tsaki naja ina mai bata amsa da, “Ai namafi makauniya yau Ummie, wlhy banga duk Cards ɗinaba, kuma inada tabbacin anan ciki suke”. Tasowa tai tana tayani, sai dai kumafa da gaske babu ɗin, hankalina yayi matuƙar tashi, “Ummie na shiga uku, a ina na jefar nikam?”. “Bily bazan saniba, amma nasan baki da mantuwa, yaushene rabonki dasu?”. “Ummie A ranar lahadi fa da hannuna na sakasu cikin nan dazan fita”. Tace, “Ai da sauƙima, ki tuna ranar ina da ina kikaje tunda kin tabbatar a ciki suke?”. Zama nai idona cike da kwalla ina tunano dukkan abinda ya wakana a wannan yinin, da sauri na kalli Ummie, “Ummie idanma har yardawa nai to
bazai wuce wajaje biyu ba wlhy”. Ummie tace, “Ina da ina ne?”. “Saloon da wani garden, amma bara na bincika a saloon ɗin dan inada Number ma'aikaciyarsu ɗaya”.
Ummie ta biya kuɗin muka fito a wajen, sai da muka koma office sannan nai kiran Number danai saving da Ladies mirror, bugu biyu kuwa aka ɗaga, bayan mun gaisa nace, “Dan ALLAH kiyi haƙuri, na kiraki maybe ba'a lokacin daya daceba”. Daga can tai dariya da faɗin, “lah babu komai”. Nace, “Okey ngd, ranar danazo wajen nan naku ina tunanin na yarda wallet ɗina, sam hankalina bai kaiba sai yanzu, ina fatan anan na yardar ɗin?”. tai ɗan jimm na wasu sakanni kafin tace, “Eh tabbas anan kika yarda, amma bata wajenmu, tana masarauta wajen su aunty Amaturrahman, dama sunbar saƙo akan idan kinzo nema a baki card ɗinsu, yanzu yaya za'ai kenan?”. Wani sanyi naji ya ratsani, na sauke numfashi da cewa, “Babu damuwa, idan na tashi aiki zan biyo na amsa, nagode sosai”. ta amsa da “Babu damuwa, sai kinzo”. Bayan mun kashe wayarne na faɗama Ummie duk yanda mukai, daga ni har ita mamaki muketayi na cewar wallet ɗin na masarauta.
Ban samu kiran boss ba kamar yanda yace zamu fita har lokacin tashi yayi, zuwa nai na sanarma yah Qaseem ya wuce gida ni zamuje nida Ummie wajen wanke kai, yanzunma da damuwa na iskesa, dan haka bai wani jamin zanceba yace mu haɗu a gida. Nidai al'amarin nasa sake ɗauremin kai yay yanzunma, har muka isa Ladies mirror banbar mamakin wannan canjin nasaba. Sosai Ummie ta rikice da haɗuwar wajen, harda ma kanta alƙawarin zuwa wannan weekend ɗin su mata aiki, bamusha wata wahalaba muka samu wadda na kira ɗin, ta bani card ɗin da suka bari. bamu daɗeba muka fito dan magriba ta gabato.
Ummie ta ajiyeni a gida ta wuce, koda na shiga saina iske an sallamo auntu Shahudah, falon cike da dangin Momy, da sukazo dubata, nidai na gaishesu itama nai mata yaya jiki na wuce, saboda a rayuwata na tsani kallon wilaƙanci, sukuma naga alamar indai ba nasuba to kowa banzane. Wanka na farayi harda wankan tsarki saboda baƙona ya gudu, na fito na gabatar da sallar magriba nai azkar, ina zaune a wajen har aka kira isha'i, har lokacin inajiyo hayaniyar ƴan gidansu Momy, dukda yunwar da nakeji saina zaɓi haƙura na kwanta a haka, ɗan kayan maƙulashen da yah Qaseem ke yawan siyamin nakan ajiye a ɗaki su nai zamanci, gefe guda kuma ina ƙoƙarin kiran Number jikin card ɗin da aka bani, saida ta kusa tsinkewa aka ɗaga, munyi gaisuwa da wadda ta ɗagaɗin a mutunce dukda bansan wacece ba, kafin na mata bayanin kaina. Nayi mamakin yanda tai saurin ganewa, kai tsaye tace na tura mata address ɗin inda nake kawai, zasuzo su kawomin har gida. Sosai na ƙara mamaki da jinjina ƙyaƙyƙyawar tarbiyyarsu gaskiya, sam basuda girman kai tamkar ba waɗanda suka fito daga babban gidaba. Godiya nai mata mukai sallama, ban zauna ɓata lokaciba na tura mata number dan inada buƙatar cards ɗina su dawo hannuna da gaggawa.
Jin gidan yayi shiru yasa na miƙe, dan fitar motoci da naji ya bani tabbacin duk sun wuce, ƙaramin hijjab na saka saman wando da rigar kayan barcina kalar ruwan hoda na fito, wata irin muguwar yunwa nakeji wlhy, rabona da abinci tun wanda mukaci da Ummie da rana. Babu kowa a falon duk sun tafi, na wuce kicin hankalina kwance, plates kawai nagani zube wanda sukaci abinci, sai dai babu komai a kulolin duk an cinye, cike da haushi na fara ƙoƙarin ɗora noodles dan bazan iya haƙurin kwanciya banci komai ba, dan danan na kammala dafawa na fito, mamaki ya kamani jin ƙamshin turaren da banyi zatoba, zuciyata sai harbawa take da sauri-sauri, waige-waige na shigayi a falon, saiko idona ya sauka akan wanda zuciyar tawa ke rayamin, tsaye yake dafe da ƙarfen benen dake falon waya a kan kunnensa, kamar koda yaushe ƙananun kayane a jikinsa, ido cikin ido muka kalli juna, nai azamar janye nawa ina damƙe plate ɗin indomie ɗina daketa tururi, inaji a jikina har yanzu kallona yake, hakan saiya haifarmin da tafiya a hankali kamar wata hawainiya harna shige lungun ɗakinmu ni da aunty Aamilah.
Jawaad daya kasa ɗauke idanunsa a kanta har saida ta shige sannan ya sauke ajiyar zu
ciya yana lumshe ido da cije lip ɗinsa na ƙasa, sannan ya cigaba da wayarsa, bai wani jimaba sukai sallama ya maida wayar aljihu idanunsa akan lungun da bily ta shiga, cike da kasalar data saukar masa yanzun ya haye saman ya koma wajensu Dad da Alhaji baba da Uncle Nasir da sukazo tare suke tattaunawa.
Ban kawo komai a rainaba dangane da ganin boss gidanmu, tunda ai dama yayma Dad alƙawarin zuwa, sannan kuma ga aunty Shahudah ta dawo gida itama, abincina naci hankali kwance nai brush na kwanta domin na hutama raina.
ALLAH YAY DARE.
Washe gari safiyar alhamis, koda na tashi sai naci karo da abubuwa uku na farin ciki sun samemu, na farko samun sauƙin aunty Shahudah da har aka sallamo daga asibiti a daren jiya, na biyu maganar aurenta da Boss bayan ansha gumurzu ya amince da ƙyar saboda saka baki da kakansa yay a maganar, na uku tsaida maganar aurena da Yah Qaseem bayan Dad yaje wajen dangin mahaifina ya samesu ashe a jiya da rana, an tsaida aurenmu rana ɗaya dasu aunty Shahudah bayan salla ƙarama da sati biyu. Koba komai na samu kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya, dan nikam abubuwan dake faruwa na wannan lokacin suna matuƙar tsoratar dani da sakani firgici.
Ban ƙara tabbatar da ina son Yah Qaseem ba sai da aka tsaida ranar auren nan namu, shi kansa wani sake lallaɓani yake da ji dani a yau, dukkan abinda zai saka a gidansa kuma sanda muke tafiya wajen aiki ya nema shawarata, hakama kayan lefe saida yace na faɗi duk abinda nake buƙata, nidai kunyace ta kamani nace kawai na bashi zaɓi.
Sai dai abu mafi bani mamaki sune jama'ar gidanmu, musamman ma Momy, koda wasa ban taɓa tunanin zata goyi bayan aurena da Yah Qaseem ba, amma sai gashi koda a fuska bata nuna komaiba, saima shirye-shiryen gagarumin biki take na nunama sa'a akan babban ɗanta namiji da zata fara aurarwa. Yah Salman ne kawai da aunty Aamilah sun shafema idanunsu toka suna ƙara faɗaɗa hantarata da muguwar tsana akan ban cancanci zama matar ɗan uwansuba, ƙiri-ƙiri suke nuna hakan babu ko kara a wannan safiya, su Dad dai basu tsawatar musu ba, sannan basu goya musu bayansu ba, Yah Qaseem ne daifa da yay kansu da masifa har saida na roƙesa yayi haƙuri kafin yay shiru muka fito.
Tom nidai lamarinsu bai ɓatan rai, Alhmdllh tunda wanda zan zauna dashi yana sona, sannan iyayensama suna sona, dansu ƙannensa sunce basayi miye a ciki. A dangima dai akwai ƴan adawa, dan harda inna zainabu faɗa taitama Dad akan haɗani aure da ɗansa da yay kamar yanda Aunty Aamilah take faɗamin cikin gori da tsana, wai acewar inna Zainabu duk ƴaƴan manyan mutane masu kuɗi abokan Dad Qaseem ya rasa wadda zaiso saini? Haka taita jaraba tamkar itace ta haifi Dad ko yah Qaseem ɗin.
Duk wanda ya kalleni a office yau yasan banda wata damuwa tattare dani, dan waɗandama suke faɗin basa ganin dariyata yau sun gani harma da haƙorana, sai dai abinda ya ɗaure kaina da mamaki rai a ɓace naga Boss yau, dan koda nakai masa saƙo office baiko amsa gaisuwataba bayan sallama, sannan harna fito baice dani uffanba, idanunsa jajur, hakama jijiyar kansa duk sunyi ruɗu-ruɗu, duk sai naji babu daɗi, dan koba komai nima ranar danai ciwon mara ya bani kulawa da nuna damuwarsa a kaina, da alama kuma yau shima baida lafiyarne. Kasa zama nai waje guda nakoma office ɗinsa wai naji mike damunsa?, ‘kuji ƙarfin halifa irin nawa’ to aiko dai ban jiyota da daɗiba, dan fatattakoni yay tamakr zai gaggallamin marukama, ALLAH dai ya taimakeni na gudo. A ƙofar office ɗin mukaci karo da gimba kamar a rikice yake, nidai na bashi hanya ya shige ko gaisuwa bamuyiba, sauka nai ƙasa abina ina ƙunƙunai, ban sakebi takansaba har aka tashi aiki kuwa, sai a wajen Ummie nakejin gulmar wai taga boss ya fita ɗazun ransa a ɓace kamar zai tashi sama, ban kulataba ita da zancen nata, dan haushinsa nakeji akan abinda yaymin ɗazun..
Mamaki yay matuƙar kamani da muka isa gida na iske aunty Shahudahr data kwana biyu a asibiti rai a hannun ALLAH zaune suna hira mai nuni da tsare-tsaren biki, a raina nace, ‘Dama ciwon so ke damunta ashe, ta samu yanzu kunga ta miƙe harda tsara
biki kamar wani auren farko mtsoww’ na ƙare zancen cike da takaicin da bansan dalilinsaba nima. koda nai sallama basu amsaminba sai Momy kaɗai, sannunma ita kaɗai taimin hakama amsa gaisuwata, jikina duk sai yay sanyi, na wucesu ƙwalla na cikamin idanu, nasan dolene saina sake ɗaura ɗammarar haƙuri kam, dan matsalolin dama sukafi haka zasu biyo baya akan aurena da Yah Qaseem, har nai wanka na fito hawaye basu daina gudu a idanunaba, bayan sallar isha'i saima naji gidan tsitt, koda na leƙo iskewa nai duk fita sukai, daga ni sai Yah Qaseem dana iske a d/table yanacin abinci aka bari gidan da alama, zama nai mukaci tare muna ƴar hira, bayan mun kammala ya fita sashensu ni kuma na koma ɗaki nai shirin kwanciya dan barci nakeji kuma. Ina kwance har tara na dare barcin bai ɗaukeniba bankumaji motsin dawowar su Momy ba, sai naji wani tsoro na shigata a hankali, addu'a nai na kwanta ina fatan barci ya ɗaukeni mai nauyi kozan samu nutsuwa, UBANGIJI kuwa sai ya amsa roƙona barcin yay gaba dani babu zato.
‘Innalillahi...’ na ambata cikin farkin barci lokacin da abinda ya faru kwanaki huɗun da suka shuɗe dana manta shi gaba ɗaya a raina yake neman maimaita kansa a wannan daren tamkar ranarma a yau, a matuƙar gigice na farka jikina na mazarin rawa haɗe da bugawar zuciya tamkar zata faso ƙirjina ta fito, na fashe da kuka ina mutsu-mutsun fita daga jikinsa, sai dai hakan ta gagara a yau, dan yaymin riƙo bana wasaba, ga bakina an ɗaureshi da yanda bazan iya maganaba . Wata irin siririyar dariya ya saki a cikin kunnena, yauma dai muryar tamkar irin ta wancan ce, “Hhhh sannu Jaruma, yauma na dawo gareki, ranar kinyi nasarar korata ko, to kisa a ranki yau duk gudunki bazaki iya tsereminba, harke wacece da kika isa ruguzani? Nazo miki da lallami ranar amma kikaƙi saurarata, hhhhhh ke baki isa zama matar aureba yarinya saina karɓi abinda yake nawa, gashi kina a cikin yanayin danafi buƙata ma kina haila, kina bani shikenan, dan samunsa bada igiyar aure a kankiba shine yafi komai muhimmanci, bakuma zan sake bibiyarkiba dana samu cikar burina, hhhh bilkisu kece kammaluwar nasarata, kece ƙarashen nasarorina, da dukkan wahalhaluna na tsawon shekaru zan cika nasarata! Hhhh taya kike tunanin zan bari ki kufcemin, ɗaura miki igiyoyin aure tamkar ni aka ɗaure da igiyoyinne, taya zan bari hakan ta kasance ban amshi abinda yake cikamakin nasarorina ba?, abinda naketa bibiya tsahon shekaru kenan, karki yaudari kanki da tunanin ranar kin tsira yauma zaki tsiran, namiki shiri sosai a yau bilkisu, na shiryama wannan ranar, dan tana cikin damammakin da idan na rasasu babbar asarace a gareni, bana asara yarinya sai dai nasara! hhhhhhh!........”
Duk wannan maganganun da yakemin a cikin kunne na zama tamkar wata gawace a kwance, gangar jikina ne kawai a duniya amma numfashina da tunanina basa tare da duniyar, ba'a maganar zubar hawaye ma dan waɗanan dama ke sakasu fitowa, wata irin hasala zuciyata keyi da kumburar ɓacinrai irin wanda ban taɓa tunanin inada shiba, haka kawai yau nakejin zuciyata ta bushe dukda inajin tsoron ya samu nasarar da yake fatan kuwa, sai dai ban fasa gayama UBANGIJINA ba, addu'a nake kawai ina ƙiyasta tunanin shaidar dazan iya barma koma wanene wannan shaiɗanin, bazanyi sake irin na wancan darenba a yau insha ALLAHU, koda ace zaici galaba a kaina nima saina ribantu dashi da izinin UBANGIJINA.
Lokacin da naji ya sassauta min riƙon da yaymin yana shirin hawa kaina saina samu damar bada dukkan ƙarfina da yazomin daga mahaliccina wajen ƙoƙarin son tureshi, sam hakan bamai sauƙine a gareni, dan da alama ba ƙaramin mutum bane, danni sam kusani bana kawoshi a jerin aljanu, inada tabbacin mutum ne tamkar ni da rigar shaiɗanu. Wata sassanyar dariya maicin rai da nuna tsantsar mugunta da bushewar zuciya ya saki, tare da komawa gefena ya kwanta da faɗin, “Bara na baki damarki, kafin nai yaga-yaga dake yanda bazaki taɓa ganuwaba a safiyar gobe, na kula tausayin banza nake miki, tsaurin idonki yayi matuƙar yawa yarinyarnan”. Ya ƙare maganar da cire abinda ya ɗauremin bakina. Kukan zuci nake da babu hawaye ina kai masa du
ka ta ko ina da masa gargaɗi cikin zafin rai, “Karka cutar dani dan ALLAH, minai maka kake ƙoƙarin ɓatamin rayuwa?, kaji tausayin maraicina dan ALLAH, kobaka tsoron mahaliccinka ne? ina buƙatar zuwa da martabata gidan mijina tamkar kowacce mace mai mutunci, idan ka ketamin haddi wlhy ALLAH bazai barkaba, zan ƙare rayuwata ne wajen jifanka da munanan addu'oin da koka samu cikar burin naka saiya zame maka musiba, mugu azzalumi, ALLAH ya gagauta tona asirinka dama kosu waye kuke aikatama ƴaƴan mutane ɓarna, ALLAH ya ruguzaku sheɗanu, insha ALLAHU wutar jahannamace makomarku inhar baku tuba kun koma ga ALLAH ba tare da neman yafiyar bayin da kuke cutarwa, la'anannu masu ado da rigar musulunci suna cin dunduniyar bayin ALLAH, insha ALLAH bazaka cika burin nan nakaba koda kuwa kasamu nasara a kaina.........
Shiiiiii!!!! Ya faɗa yana dannemin baki tare da birkiceni ƙasa ya fallamin wani gigitaccen marin da komaina yay tsaye cak na wucin gadi kafin na ƙwalla ƙara, yasa hannu ya dannemin baki tare da kaina da azabar ƙarfi, kiciniya na fara dan harda hancina ya haɗa gaba ɗaya, tako ina yakushinsa nake dukda babu farce a hannuna sosai, hannunane ya sauka akan wuyansa, jin wani abu a ɗaure kamar sarƙan bit na samu damar fincikarsa da masifar ƙarfi saboda fita a hayyacina da nayi lokacin da numfashina ke gab da barin jikina................✍
Ƴan WhatsApp kuma ga naku saƙon, gaisuwa da fatan alkairi gareku baki ɗaya. Saura kuma yau naji wani yacema Yah Qaseem ko Dad kwarto🙄🚴🏼🚴🏼😍😍😍😘😘😘😍😍.
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻
Billyn Abdul:
Page 22
...............“Bazai yuwuba, Ka gaggauta fita!! Ka gaggauta fita!!!” na jiyo wata murya mai amo sama-sama tana amsa kuwwa a cikin ɗakin lokacin da numfashin ke gab da barin gangar jikina. Daga haka ban sake fahimtar komaiba dake a cikin duniya sai wayar gari nai na ganni kwance a ɗakin Momy.
A hankali na shiga buɗe idanuna da sukaimin nauyi, na shiga bin ɗakin da kallo daki-daki, dan bamma fahimci inda nakeba da farko saboda zan iya irga shigowata ɗakin Momy a tsawon zama gidan, da ƙyar na tashi zaune ina sake mamakin abinda ya kawo ni nan ɗin, hakan yayi dai-dai da shigowar Momy ɗakin.
“Yauwa kin tashi Bilkisu?”. Kaina na ɗaga mata a hankali, saboda jikina yaymin wani masifar nauyo, na buɗe baki da ƙyar nace, “Momy miya faru na ganni anan?”. Hankalinta nakan ciro abu a cikin drawer ta bani amsa, “Za'a gaya miki daga baya, tashi kije ɗakinki kiyi wanka”. Da “to” kawai na amsa mata na sauka jikina duk yana wani masifar ciwo, ga tunani fal raina, wani abin mamakinma na sake tararwa a folon ƙasa, dan kuwa cike yake da dangin Momy, na gaisar da waɗanda zasu iya jina na wuce ɗaki kaina na kuma ɗaurewa. Akan gadona dake mugun yamutse na fara sauke ido, ‘Kowaye yay masa haka kuma?’ na ayyana a cikin raina, dukda banajin daɗin jikin sai nai tunani bara na fara share ɗakin, gadon na shiga kakkaɓewa, ƙarar faɗuwar abu naji kamar ƙwandala a ƙasa lokacin dana ɗaga zanin gadon, dube-dube na fara, sai dai banga komaiba, sharewa nai kawai na gyarashi tsaf, nakoma shara. A wajen shararne na sharo abinda ya faɗi ɗazun ashe wajen gado ya shige, Wuri ne kalar ja, sai dai wannan yafi wurin dana sani girma, haka kawai na samu kaina daƙin maidashi a sharar, saima na jefashi cikin jikkar islamiyya ta dake kusa dani, na cigaba da sharata. Da ƙyar na kammala aikin na lallaɓa bayi nai wanka, ganin baƙona ya tafi saina haɗa da wankan tsarki. Ina shiri ina mamakin barcin danai daga daren jiya zuwa safiyar yau ace bamma farkaba kamar yanda na saba a lokacin sallar asubahi dukda bana salla, yanzu hakafa sha biyu ma, ni saima yanzu maganar zuwa aiki tazomin a rai, gaba ɗaya wani iri nakejin kaina tamkar birkitacciya, wayata na shiga dubawa, sai dai kuma ban gantaba, ƙarasa shirin nai da tunanin naje ɗakin Momy na duba ko tana can idan na gama. Sallamar Momyn ce ta kacemin tunani na juya ina kallonta. taci kwalliya cikin rantsatstsen lase ɗan ubansu sai walƙiya yake, ga gwalagwalai ta zuba a wuya da hannu, taimin murmushi irin wanda tsahon zamana da ita ban taɓa cin karo da shiba sai yau, “Bilkisu irin wannan kallo haka” kunya naɗanji, dan haka na murmusa ina mai duƙar da kaina, nace, “Kinyi ƙyaune Momy”. “To nagode sosai” tafaɗa tana zama a bakin gadona da ajiye ledan data shigo dashi a hannu. takai dubanta gareni, “Kinga cire waɗannan kayan waɗanan zaki saka, nasan akwai tambayoyi fal ranki, karki damu zamu baki dukkan amsoshinsu zuwa dare idan baƙi sun tafi, fatanmu dai kizama maiyin biyayya a garemu kamar yanda kika saba, batun zuwa aiki kuma yau bazaki jeba”. Shiru nai kawai ina kallonta, sai kuma nace mata, “To momy, wayata fa?”. Miƙamin tayi tana faɗin “kin ganta nan, dama anata kirankima kuwa tun ɗazun”. Amsa nayi, itakuma ta miƙe ta fita. Da kallo na bita kaina na sake ɗaurewa da abubuwan da ban saba ganinsuba sai a mafarki, ganin ta ɓacema ganina saina sauke nannauyar ajiyar zuciya, wayar na duba, miss calls kam da yawa harma bansan dawa zan faraba, Yah Qaseem, Ummie, Amina, harma da Numbers ɗin da bansan na wanene ba, kafin nayi wani yunƙuri kira ya shigo, sunan Masarauta danai saving ne ya fito ɓaro-ɓaro a jiki, ɗagawa nai muka gaisa a mutunce kamar ranar, daga ƙarshe take sanarmin bayan an sakko massalaci zasuzo kawomin cards ɗina, murmushi nayi ina mata godiya, kafin mu yanke wayar. tunanin yaya zanyi na shigayi, dan yakamata ace koba komai nai musu tarba ta girmamawa ko badan gidan da suka fitoba, to amma yanda gidannan ke cike ta ina zanma fara nikam? Wlhy gaba ɗaya yau kaina ya ɗauki zafi, sam tunanina baya tafiya dai-dai dana sauran mutane. Kasa yin komai daya dace nayi, nai zaune a inda Momy ta barni, niba
n canja kayan datace ba, bankuma miƙe na nemawa baƙin abinda zasuciba idan sunzo balle kuma cikina dake Masifaffen ƙugin yunwa kamar zanci babu. Ina a wajen har ƙarfe ɗaya ta buga, tashi nai jiki a sanyaye na ɗauro alwala, gabana sai wata iriyar muguwar faɗuwa yake wadda ban taɓa jiba, idan girata ta haggu ta harba sai ta dama ma ta harba, sai kuma inji wata faɗuwar gaba ta biyo bayansu. Haka nai sallar azuhur batare dana fahimci abinda nama karanta a sallarba, dan wasu irin mugayen halittu na rinƙa gani suna zuwa gabana, haka dai na dake raina na cigaba da sallar inata faman kwarar da zufa tamkar wadda take a cikin ruwan zafi, a sujidar ƙarshema sai naji wata iriyar muguwar dariya a ɗakin tamkar za'a fasashi, sai kuma aka fashe da kuka, zuwa can aka kuma saka dariyar datafi ta farko. Na kasa ɗagowa daga sujidar ma gaba ɗaya tsahon lokaci, saida naji an taɓani ne a baya da magana kamar muryar Ummie sannan ALLAH ya bani ikon ɗagowa. Shiru naji ɗakin ya ɗauka sannan bana ganin komai a gabana harna kammala na shafa addu'a. Na sauke idanuna akan Ummie dake zaune da a bakin gadona tana latsa waya, sai dai na kasa cemata komai saboda wani irin yanayi da nakejin kaina mai masifar tashin hankali, jina nake tamkar ana kunnamin garwashin wuta a jiki........
“Bily! Bilyy!!” na tsinkayi muryar Ummie na faɗa tana girgizani. Kallonta nai na amsa da ƙyar, dan bansanma tazo kainaba, bana gane komai a yanzu bana kuma fahimtar komai hatta da kaina neman suɓucemin ya keyi. Tace, “Na shiga uku, Bilkisu lafiya kike kuwa? Wai mike faruwane haka?”. “Ban saniba nima Ummie” nai maganar hawaye na ziraromin akan kumatu. Kafin ta samu damar jehomin wata tambayar muka jiyo matsananciyar hayaniya ta kaure illahirin gidan tamkar ana faɗa. Mu duka kallon ƙofa mukai, hakan yay dai-dai da bugo ƙofar da aunty Shahudah tai hannunta ɗauke da wuƙa tana kuka.
A tare muka miƙe da Ummie, dan lokaci ɗaya wani ƙarfi yazomin da bansan daga inaba kuma, ganin kaina tayo da wuƙar saina zaro idanu waje ina faɗin, “Au...aunt...aunty Shahudah lafiya? kuw....” bankai ga ƙarasawaba ta kawomin suka tana faɗin, “Wlhy kasheki zanyi, tsinanniya jinin asara jinin masifa, jinin tsafi....” wani mugun tsalle nai na kauce mata, amma dukda haka saida taɗan yankeni a damtsen hannuna. Ɗakin ya cika sai ƙoƙarin janyeta ake tana ihu da tabbacin yaufa ita saita halakani.
Bansan hawaba bansan saukaba kawai naji aunty Aamilah da wasu ƴammata sun rufeni da duka sukuma, tun ina ƙoƙarin kare kaina harna gaza dan sunfini yawa, gashi kuma bayan Ummie babu mai yunƙurin karɓata.
Tun Bilkisu na fahimtar abinda ke faruwa harta sume, amma idanunsu ya rufe bama su fahimci bata numfashiba, haka suka jawota ƙiyyy!! waje har tsakar gida suna duka, abinda zai baka mamaki babu wanda ya hanasu acikin manyan iyaye irinsu Momy, suma kansu ruɗanin abinda yazo musu babu zato baisa sun kula da abin ƴaƴansu sukeba na yunƙurin kisan kai, Ummie ce kawai ke kuka da Amina da mama da suka shigo gidan saboda jin matsananciyar hayaniyar dake tashi.
Shahudah kuwa tun tana kuka da iƙirarin kashe Bilkisu har itama ta yanke jiki ta faɗi ƙasa babu numfashi, nanfa gidan ya kuma harmutsewa, babu mai iya fahimtar yaren wani balle ka samu tabbacin abinda ke faruwa dahar ya kawo wannan tashin hankalin.
____________________________
Abinda ya faru shine, a daren jiya su Mom sun dawo misalin ƙarfe sha ɗaya da wasu mintuna sai sukaci karo da wani irin ihu maiban tashin hankali da saka firgici a gidan, babu wanda bai tsoraba a cikinsu dan Aamilah harda fitsari ta jiƙe jikinta, sai bayan wasu mintuna komai ya lafa sannan suka fahimci daga ɗakin Bily wannan ƙara ta fito, sai dai a cikinsu babu wanda ya iya jarumtar shiga ɗakin. Mom ce ta ɗaga waya ta kira Dad hankalinta a tashe ta sanar masa komai, shima hankalin nasa a tashe ya tabbatar mata gashinan zuwa gidan dama ya fita rakkiyar su Alhaji baba ne da sukazo.
Duk wannan ihu yau Yah Qaseem bai jisaba sam, yana ɗakinsa yana barci, saida Shahudah taje ta tasoshi bisa umarnin Momy. Kafin isowar Dad Yah Qase
em ne ya fara shiga ɗakin, sai ya tadda bily a sume, ga ɗaki a hargitse tamkar anyi sukuwar salla a cikinsa. Babu wanda abun bai taɓa zuciyarsaba a gidan har Dad daya iso yanzun, sun shiga yayyafama Bilkisu ruwa amma ko motsi bataiba. sunkuma bi duk wasu dabaru shima bata farfaɗoba, hakan yasa Dad bada shawarar a maidata ɗakin Mom ta kwana a can, shikuma zuwa safiya zai ɗauki mataki akan wannan abun dake faruwa.
Daga Aamilah har Shahudah suma a ɗakin Mom suka kwana, da ita kanta Mom ɗin harma da Dad kansa saboda a firgice suke yaran da Mom. Har ALLAH ya wayi gari lafiya Bily kam bata dawo hayyacintaba sai kusan ƙarfe sha ɗaya da wasu mintuna ko nace sha biyu saura na rana.
Abinda ya farunne ya saka Dad yanke shawarar ɗaura auren Bily da Qaseem a wannan safiya ta juma'a dan kowa ya huta duk da basusan ainahin abindama ake bibiyar Bilkisu da shiba, ɗari bisa ɗari Mom ta bashi goyon baya. Ana idar da sallar asuba Dad ya nufi gidan Alhaji baba ya sanar masa halin da ake ciki tare da neman alfarmar haɗawa dana Shahudah da Jawaad, zuwa bayan salla idan ALLAH ya kaimu a cewar Dad sai ayi biki su tare. Alhaji baba bai musaba, dan yana fatan jikan nasa matsalarsa ta zama babu aure tazo ƙarshe. Daga gidan Alhaji baba gidansu Jawaad Dad ya wuce, a canma sun tattauna dasu Uncle Nasir kafin ai kiran Jawaad dake shirin tafiya Office.
Koda suka sanar masa shirinsu shima babu musu ya amsa musu, harma amincewar tasa da gaggawa ya basu ɗunbin mamaki, amma shi saiya fuske abinsa tamkar baiga mamakin nasuba sam ko bai fahimtaba, ya kuma fiddo kuɗin sadaki a take ya direma Uncle Nasir har dubu ɗari biyar. Kasa haƙuri kam sukai saida suka tanka akan hakan, batare daya kallesuba yace ai Alhaji baba ne ya kirasa ya sanar masa kafin su sukirashi, cikin gamsuwa da maganarsa Dad yace to ya rage kuɗin sunyi yawa, dubu ɗari sun isa. Murmushi Jay yayi yana wani susar ƙeya, kansa a ƙasa yace, “Karka damu Dad nariga na fidda kuɗin matsayin sadakin, Uncle kuje dasu wajen ɗaurin auren kawai please. Albarka suka saka masa tare da sallamarsa, yay musu sallama ya tafi fuskarsa ɗauke da wani shegen murmushi daya tsayama Uncle Nasir da Dad a ƙahon zukata. Dad ya dawo gida, yayinda Jay yanufi office ya nema alfarma tare da gayama Sir Ahmad abinda ake ciki. Sannan ya sanarma su Hafiz ma, sunyi matuƙar mamaki, amma ganinsa a wani yanayin da suka kasa yima fassara sai basuja zancen da nisaba suka shiga faɗama mutanensu nanan office da waɗanda suke kusa irinsu Abbati ta waya.
Maza nata haramar tafiya massallaci, inda daga canne za'a ɗauro auren bayan idar da sallar juma'a, yayinda ahalin gidansu Momy keta tururuwar zuwa gidan harma da tsiraru na ɓangarensu Dad kamar su inna Zainabu. Duk wannan abunda ke faruwa babu sanin bily, tanacan tanata barci abinta.
Massallaci ya cika tab da al'ummar musulmi yara da manya da matasa da tsoffi harma da mata dakanje sallar juma'a kasancewar wannan ranar ranace ta musamman a garemu, bayan an idar da sallar juma'a kamar yanda aka saba akai sanarwar ɗaure-ɗauren aure daza'ayi daban-daban wanda harda nasu Qaseem a ciki. Duk wanda yaga Qaseem a yau zai tabbatar yana cikin farin ciki, dan kuwa yaci ado da wata ɗanyar shadda fara ƙal da Dad ya bashi ya sanya, sai walƙiya da walwalin angwanci yakeyi kamar ka sacesa ka gudu, ga haƙoransa farare tas sun kasa rufuwa. Sai dai nayi iya dubana da waige-waige bangano ko mai kama da Jawaad ba balle shiɗin kansa, saisu Aliyu da suma duk suke sanye da shaddoji a yau, da alama dai gida suka koma bayan zancen ya riskesu suka canja shiri.
An fara ɗaura aure guda biyu da baida alaƙa dasu Dady, kafin a ɗaura wani da yaso bama kowa mamaki, wato dai Sabira da wani waishi Habib, ankuma roƙi Uncle Nasir dake kusa ya zama wakilinsu saboda wai wakilan amarya masu isoba har lokacin, wannan shine ya gogema mutane da yawa abinda ya taɓa musu zukata, ɗaurin aure na huɗu daya biyo baya shima bashi da alaƙa dasu Qaseem ɗin, saida akai kusan na mutum uku kafin a ɗaura na Qaseem da Azeema, jikin Qaseem har rawa yake ya miƙe zaiyi magana amma sai Uncle Uwaisu ya maida
shi ya zaunar yana mai sanar masa bafashi ake nufiba maybe wasune daban, ajiyar zuciya Qaseem ya sauke dukda dai hankalinsa bai kwantaba, gashi iya dubansa baimaga Dad a wajenba, bayan kuma tare dashi sukazo masallaci, ɗaurin aure na ƙarshe baki ɗaya shine ya tada hankalin dukkan mai alaƙa dashi, wato Jawaad Abdul-aziz da amaryarsa Bilkisu Adam, Alhaji Baba wakilin amarya Uncle Nasir da yay zaton da Shahudah ya kasance wakilin Ango, saida aka ambatanefa yaji wasan ya canja salo. Qaseem yama manta a ina suke, take yanke yaci kwalar imam da masa tambayar yaya haka ta faru?. Da ƙyar ƴan agaji suka ɓanɓare imam a hannun Yah Qaseem, cikin tsagwaron tashin hankali Dad da Qaseem ya gaza gani ɗazun a masallacin ya shiga jeroma imam tambayoyi shima. imam da duk bai fahimcesuba yace shifa a haka aka kawo masa sunayen anguna da amaren da za'a ɗaurama aure a yau, kuma iyakarsu kenan ya kammala gama takardar. Yay maganar yana nuna musu.
Ganinfa za'a iya bama hammata iska a massalacine ya saka ƴan agaji sallamar kowa akace su Dad su fito a shiga inda ya dace ayi magana, sannan ana neman dukkan angunan da aka ɗaura aurensu ba dai-dai ba.
Yah Qaseem kawai aka gani a cikin anguna, amma babu Jawaad babu Habibu da aka ɗaurama Shahudah, kuma kowa yayi imanin yaga Jawaad a massallaci kafin a tada sallah, yanzukam an nemesa ƙasa da sama tamkar allurar mayya an rasa. Kowa ƙoƙarinsa ya kira wayar Jawaad amma sam taƙi shigama, gefe kuma ana jajen wanene habib ɗin da aka ɗaurama aure da Shahudah?.
Lokacin da ake waccan dambarwar a lokacinne shikuma Salman ya kira Shahudah ya sanar mata komai, kafin ya kira Momy itama, yana tsaka da sanar mata abinda ke faruwa Shahudah ta nufi ɗakin Bilkisu da wuƙar data ɗakko daga kicin tsirara tana iƙirarin yaufa saita kasheta.
A masallaci komai ya hargitse, imam ya tara dukkanin ƴan agajin massallacin dake da alhakin rubuta sunayen waɗanan anguna da amare anata jera musu tambayoyi, dan kuwa dai Dad da kansa shine ya kawo list ɗin farko kuma an tabbatar yanada banbanci da wanda yake a hannun imam a yanzu. Sudai ƴan agajin dakeda wannan alhaki sun tabbatar abinda suka gani kenan, sannan kuma ga takardar farko da Dad ya kawo an samo kuma bata da alaƙa data yanzun. Abun ya ɗaurema kowa kai hatta da imam ɗin kansa, dan shidai yanada yaƙinin babu yanda za'ai ƴan agajin su bada abinda ba haka yakeba, dan invitations ake kawo musu na ma'auratan da duk za'a ɗaurama aure a satin, sukuma saisu rubuta sunayensu a takarda gabaki ɗaya domin samun sauƙi, nasu Jawaad kuma a rubuce Dad ya kawo tunda ba'a buga invitation card ba abin yazo a ƙure. TO A INA MATSALAR TAKE?.
Wannan itace tambayar dake a bakin kowa a wajen musamman lokacin da Yah Qaseem ya yanke jiki ya faɗi a sume shima. Dai-dai kuma da kiran da akaima Dad akan tashin hankalin dake faruwa a cikin gidansa. Abin tausayi sai kawai Dad ya fashe da kuka shima yana neman faɗuwar, cikin amincin ALLAH Uncle Sulaiman ya samu damar tarosa da faɗin, “Haba Alhaji Ali, ka kwantar da hankalinka mana, na tabbata saɓani aka samu ko kuskure, kuma abune mai sauƙi da nake ganin zamu warwaresa da gaggawa, Jawaad ya sakima Qaseem matarsa, haka shima wannan da bama asan ko wanenen ba ya sakema Jawaad matarsa”. Kasa magana Dad yayi, dan babu abinda yake fahimta daga kalaman Uncle Sulaiman, gaba ɗayama numfashinsa neman barin gangar jikinsa yakeyi.
Shugabannin massallacin dai nata ƙoƙarin binciken tushen wannan matsala da basu taɓa cin karo da itaba a tsahon rayuwarsu, anɗaura auren da babu adadi a shekarun wanzuwar massallacin amma hakan bai taɓa faruwaba koda da kuskure kuwa, babban tashin hankalinsu ma shine wanene Habib da aka ɗaurama Shahudah aure dashi?, dan kuwa dai an nema wakilan nasama an rasa balleshi kansa, matsalar Qaseem da Jawaad kam kowa yana ganin tanada mafita tunda su an rigada an sansu gasu kuma ƴan uwan juna.
Imam da kansa ya gama ɗaukar zafi gaba ɗaya ya cire rawanin kansa yana sharce gumi da faɗin, “Wannan wace irin matsalace haka? Tayaya za'ace an ɗaura auren da sam bashi da alaƙa da juna?”. Qaseem shi
ne mijin Bilkisu, an ɗaurama Jawaad, Shahudah itace matar Jawaad an bama Habib, Habib shine mijin Azeema, an bama Qaseem, Qaseem da Jawaad ahali ɗaya suka fito, a tare kuma aka kawo sunayensu, to yaya akai shi Habib mai mata azeema suka shiga cikin wannan sarƙaƙiyar? Idanma ance wajen haɗe sunayen waje ɗayane dan a sauƙaƙama liman wahala to tayaya abin ya kasance haka? Kenan suk yandama akai aka dawo akwai saka hanun hadiman masallacin kenan?. hakan bazai kasance mai yuwaba dan gashi dukkan bincike anyi babu wani baƙon al'amari daya shigo har aka bama imam ainahin takardar amare da angwayen wannan satin, wadda kuma kowane ɓangare suke nuna ba ita bace imam yay amfani da ita, kenan dukkan matsalar a yanzu tadawo ta tattarane gama shi imam ɗin dan kowa shi yake zargi.
★★★★★★
Ganin babu wata mafita anan Alhaji baba ya shawarcesu da tafiya gida kawai aje a samu nustuwa kafin a fuskanci matsalar cikin kwanciyar hankali a nema masalaha a kanta.
Kowa yay na'am da batun Alhaji baba, dan haka aka ɗunguma zuwa gidan Dad da tushen matsalar take.
Isowar motocin su Dad yay dai-dai da isowar motar gidan Sarki Sameer Saifudden dake ɗauke da ƴaƴansa ƴanmata a ciki, waɗanda suke cikin farin cikin samun fita yawo a wajen da basu saniba. Babu wanda ya fahimci su wanene su ɗin?, saboda kowa baya cikin hayyacinsa, ga matsananciyar hayaniyar data fiddo ƴan anguwa gaba ɗaya dake tashi daga gidan Dad.
Su Amaturrahman da kansu ke a kulle sunbi ayarin masu shiga gidan ganin shine gidan da Bilkisu ta tura musu address ɗinsa, sai dai gidan a harmutse yake har basu da damar fahimtar komaima. Isowar su Dad kuma ya sake harmutse gidan saboda ganin halin da Bilkisu da Shahudah ke ciki, ita kanta Momy bata cikin hayyacinta, ga Yah Qaseem can an wuce dashi asibiti shima, sai kawai Dad ya yanke jiki ya faɗi shima ganin ƴaƴan nasa biyu ga Qaseem kwance tamkar sun mutu.
Tashin hankali wanda ba'a saka maka rana kenan ke wanzuwa a wannan lokaci, a take aka kwashesu su uku aka fita dasu daga gidan zuwa asibiti domin ceto rayukansu, tuni suma sauran jama'a suka bisu a motoci, ƴan anguwa kuma suka shiga tattaunawa, danma anguwace ta manya kowa yana harkar dake gabansa babu ruwan wani da wani, amma a yanda lamarin yazo duk rashin shiga harkar junansu yazama dole a tattauna.
A wannan kace nace na ƴan anguwa su Amaturrahman suka fahimci wasu abubuwan, ciki kuwa harda fahimtar wadda sukazo gurintama tana cikin waɗanda aka fita dasu tamkar gawa daga gidan. Jikinsu a sanyaye suka koma mota driver ya jasu sukabar anguwar, Safah sai kuka take akan itafa subi suga wane asibiti aka kai Bilkisu, saida Amaturrahman tai kamar zata bugeta sannan ta nutsu tai musu shiru.
★★★★★
A ɓangaren su Jabeer kuwa tun dambarwar farko ta massallaci suka shiga ayarin ƴan neman Jawaad, sai dai komai kama dashima basu ganiba, bayan kuma a tare suka shigo dashi massallacin har aka tada salla, bayan an idarne suka nemesa suka rasa gaba ɗaya, a lokacin basu kawo komai a ransuba saboda ba'akai ga ɗaura aurenba, sai bayan an ɗaurane tsoro ya kamasu da tunanin kodai yanada masaniyar komai, to amma mizaisa yayi hakan kuma? Tunda sunsan halinsa sarai, suk son da yakema Bilkisu inhar babu wani dalili bazai zama mai aikata wannan abunda dake faruwaba domin kawai ya aureta, dolene su nemesa domin jin minene ke faruwa? Shine? Kokuwa shima bai saniba.
Sun fara da station, sai dai bai koma canɗinba kamar yanda kowa ya tabbatar, sannan gidansuma bai komaba, gidansa dake Abdul-aziz Yusif street nanma dai baima jeba, gaba ɗaya kuma sai kansu ya kulle ɓam akan komai.
Suna tsaitsaye a ƙofar gidansa na A.Y street ɗin saƙo ya shigo a wayar Jabeer. Jikinsa har rawa yake ya buɗe saƙon ganin Jawaad ɗinne ya turo.
“Kubar wahal da kanku wajen nemana, zuwa safiya idan ALLAH ya kaimu zan bayyana, akwai aikin dana tafi yine, sannan karku zargeni akan abinda ya faru kamar yanda nasan rashin ganina anjima kaɗan zai ɗarsama wasu daga cikin ahalina, sam bani da hannu a ciki, akwai ɓoyayyen al'amarin danima ban sanshiba, lokacine ka
wai zai warwareshi. Inason kuyi duk yanda zakuyi kafin nan da awa uku a canjama Miemaa asibiti, dan nasamu labari yanzunan akwai matsalar data faru gidansu, karku barta ta kwana a asibitin da aka kaisu, karkuma wanda yasan kun ɗauketa daga asibitin har Alhaji baba”.
Kallan kallo aka komayi tsakanin Jabeer da Hafiz da Aliyu akan wannan saƙo na Jawaad da ya kuma ɗaure kansu akan wannan al'marin............✍
Yau dai gashinan na muku words 3700😲 kuci ku ƙoshi har safiyar litinin.😉👌🏼
Barkanku da juma'a, kar a manta da saka bayin ALLAH a addu'a dan ALLAH.
Ƴan facebook kuma ga naku saƙon, gaisuwa da fatan alkairi a gareku a duk duniyar da kuke.
Asha weekend lafiya my sweet fans, banda taƙaddama kuma.😂😂😘😘😘😍👍🏻👌🏼
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻
Billyn Abdul:
Page 23
...............Tunkan su isa asibiti Dad ya farfaɗo, lokacin kuma da suka iso sun iske shima Qaseem ya farfaɗo, duk yanda Doctor yaso yayma Qaseem ɗin allurar barci danya huta yaƙi yarda, hakama Dad bai yarda ko dubashi ayiba, cayay babu damuwa su barshi. Bilkisu da Shahudah kawai aka shiga bama taimakon gaggawa, wanda daga farko Momy da catai baza'a duba Bilkisu ba, sai da Dad ya nuna mata ɓacin ransa a fili sannan ta nutsu, sai dai tanata ƙananun magana akan hakan.
Haka suma sauran family dake harabar asibitin saboda yawan da suke dashi aka tsaidasu nan kowa nata tofa albarkacin bakinsa, saidai mafi yawan kalamansu suna ɗora laifinne akan Bilkisu ce tai asiri. Yanda suke jifanta da mugayen kalamai dolene kaji tausayin Bilkisu, dan zaka ɗauka akan wata uwar mata suke maida yanda akayin. Hayaniyarsu ce ta saka Uncle Nasir cewa duk su wuce gida domin zamansu anan ɗin bashi da wani amfani. Badan sunso hakanba sukabi umarninsa.
Motocinsu na cikin fita su Jabeer suka iso asibitin suma domin cika umarnin Jawaad, mamakine yay masifar kamasu ganin wannan uwar gayya tamkar anan ake bikin. Shi Hafiz ma abin haushi ya bashi, ya buga tsaki cikin magana ƙasa-ƙasa yace, “Mutanen nan suna bani mamaki da al'amarinsu, to wannan gayyar kuma ta miye?”. Aliyu dake jinsa yace, “Kaima dai ka faɗa”.
Fitowa sukai a motar suka isa inda su Uncle Nasir ke tsaitsaye shi da Dad, da Uncle Sulaiman, sai Qaseem dake zaune cikin mota, Salman kuma yana zaune a saman motarne yanata latse-latse a waya tamkar baida wata damuwa a duniya. Gaishesu suka shigayi cikin girmamawa, tare da musu jajen abinda ya faru. Cike da kulawa suma suka amsa musu, Uncle Sulaiman yace, “Ina Jawaad ɗin shi yake? Tun ɗazun sai neman wayarsa muke taƙi shiga”. Duk kasa cewa komai sukai, dan kuwa suma dai basusan amsar daya dace ace sun basuba akan inda Jay yake, tunda suma basu saniba.
Uncle Nasir ya buɗe baki zaiyi magana ya fasa saboda shigowar motar Jawaad harabar asibitin, duk bin motar sukai da kallo harsu Jabeer, cike da mamaki suka tsatstsareshi da idanu lokacin daya fito a motar, yana sanye cikin wata dakakkiyar shadda ƴar ubansu ruwan zuma, sai maiƙo take, sosai ɗinkin ya zauna masa a jiki cif. Kosu kansu su Uncle Nasir ɗin ya musu ƙyau, dan kafin kaga Jawaad da manyan kaya akan daɗe saboda yanayin aiki, shiyyasa idan ya saka ɗin sai ya zama na musamman. Nufowa yay inda suke fuskarsa sam babu walwala, Qaseem da babu wanda ya lura da fitowarsa a mota yasha gabansa.
Kallonsa kawai Jay ya tsayayi batare daya iya cewa dashi komaiba, cike da ɓacin rai Qaseem yakai hannu zai shaƙosa, da sauri Jawaad ya ɗaga masa hannu, da watsa masa wani irin kallo mai razani dake gauraye da ɓacin rai, “Qaseem bani hanya”. “Anƙi a baka ɗin” Qaseem ya faɗa a zafafe. Jawaad baice komaiba ya raɓashi zai wuce, sake shan gabansa Qaseem yayi, Jawaad yay wani murmushi mai ciwo idanunsa na sake ƙanƙancewa tsabar masifar dake cin zuciyarsa, cikin wata irin muryar data bama Qaseem mamaki Jawaad yace, “Qassem ka riƙe girmanka, banason ka kaini bangon da zan sakaka dana sani mara amfani”. Kafin Qaseem yace wani Abu Uncle Sadiq ya ƙaraso wajen. “Ku wane irin shashancine haka kukem mutane anan?”. Jawaad baice komaiba, sai Qaseem ne ya bama Uncle Sadiq amsa da, “Uncle bazaka ganeba, wannan yaron munafukine, wlhy ko rantsuwa nai babu kaffara nasan yanada hannu akan wannan abun daya faru, kuma wlhy dolene ka saki Bilkisu a yau ɗin nan basai gobeba”. Murmushi Jawaad yay cikin taɓe baki ya raɓasu ya wuce batare da yace komaiba.
Ƙarasawa yay wajen su Uncle Nasir ya gaishesu, Uncle Nasir yace, “Kaikuwa ina kaje anta nemanka tun ɗazun Jawaad?”. “Amin afuwa Uncle, naje wani wajene”. “To amma saika kashe wayarka? Minene amfanin hakan?”. Jawaad dai baice komaiba.
Uncle Uwaisu yace, “Amma dai kasan miya faru a wajen ɗaurin aure ko?”. Cikin nuna halin ko in kula Jawaad yace, “Uhmmm na sani”. Ran Uncle Nasir a ɓace yace, “Ka sani? Amma shine dan wulaƙanci katafi wani waje ka barmu da nemanka?”.
Kafin Jawaad yace wani abu Uncle Sadiq yace, “Ya
ya nikam inaga wannan ba maganar nan bace, kamata yay muyi haƙuri yaranan su dawo cikin hayyacinsu sai ayi maganar a nutse a gida kamar zaifi, sannan kuma mu maida hankali wajen neman shi wancan angon da aka ɗaurama Shahudah aure dashi da ita Azeema take kowa”. Duk sunyi na'am da hakan, Jay ya kalli Uncle Nasir a wani yanayi, kamar zaiyi magana sai kuma yay shiru kawai.
Bayan sallar la'asar su Uncle Nasir suka wuce gida harda Dad da Qaseem da aka tilastama dole akan yadace suje su watsa ruwa kodan suji ƙarfin jikinsu, anbar momy kawai wajen Shahudah, Ummie da maman Amina kuma suna tare da Bilkisu, Jawaad bai shiga duba kowaba a cikinsu.
Suna isa gida ya shige sashensa, wanka yay yasha magani saboda kansa ciwo yake masa sosai, duk yanda yaso ya kwanta ya huta hakan ya gagara, ya shiga zagaye bedroom ɗinsa cikin faɗawa wani dogon tunani akan wannan dambarwar da suka wayi gari da ita yau, tabbas yasan kaso mafi yawa na abinda ya faru, musamman akan sarƙaƙiyar ɗaurin auren, sai dai akwai wani al'amarin daya ɗaure masa kai sam ya kasa samun amsa akai, kuma yazama dole ya nemo wannan amsar, Tabbas saiya nemota, itace zata zama tsanin buɗe masa hanyar fahimtar abinda ya kasa fahimta a yanzu da duk sauran jama'a ma. Ya sauke numfashi mai zafi tare da kwanciya a kan gadonsa ƙafafunsa a ƙasa.
Shi da kansa shine ya canja list ɗin ɗaurin aure a masallaci, sai dai daliline mai ƙarfi ya sakashi aikata hakan, kuma duk wanda zaiji dalilinsa anan gaba zai tabbatar abinda yayi shine dai-dai kuma shine ya dace, to amma tayaya zai fahimtar da mutane sukuma su fahimta batare da ya fito da ainahin maganar filiba?. Wannan tambayar itace keta cin ransa da sukarsa a ƙahon zuciya. Barci ɓarawo shine ya sacesa a wannan lokacin batare daya shiryama hakanba, bai farkaba sai gab da magriba, wasu massallatanma har sun fara kiran sallar. Wanka yay a gaggauce yay shiri cikin ƙanan kaya ya fita riƙe da key ɗin mota da wayoyonsa, mota ya buɗe ya zubasu sannan ya nufi massallacin ƙofar gidansu sukai sallar magriba.
Koda ya dawo bayan an idar mota ya shiga ya fice daga gidan.
★★★
MASARAUTAR GAGARA BADAU
Koda su Amaturrahman suka iso masarauta sai suka iske gimbiya Munaya tana sashen mai martaba, haƙura sukai akan idan ta fito saisu sanar mata da duk abinda ke faruwa. Safah dai batace komaiba, tana ganin yayun nata sun nufi ɗakinsu ta zare jiki zuwa sashen mai-martaban batare da sun saniba. Sai dai koda ta nema Jakadiya tai mata iso saitace mata gimbiya na tare da takawa, tasan kuma babu mai shiga ganinsa inhar yana tare da matansa. Tarbiyyar da su Safah suka tashi ciki akwai girmama hadiman gidan, dan koda wasa Gimbiya Munaya bata yarda yaranta suce zasu taka koda bawa na gidan yanda suke soba, tsaye take kan tarbiyyarsu daga ita har mai martaba da Mommah. Safah sai ta kwantar da kai cike da shagwaɓa tana lallaɓa jakadiya, harda bata ƙyautar dubu biyar. Baki Jakadiya ta washe, tace, “A uwar masu gida ai dolene nai miki iso, ammafa inhar basa falon farko to saidai kiyi haƙuri anjima saiki dawo.
Safah tace, “Na yarda, amma dai ba falon farko kawai ba, dan ALLAH harna biyu, dan kinsan inhar Ummu na tare da Abbu bazasu zauna a falon farko ba, nikuma maganace mai muhimmanci zanma Ummu”. Rigimar Safah da Jakadiya ta sani yasa ta amince zataje har falo na biyun. Safah na nan tsaye a ƙofar ƙatafaren falon mai-martaba Jakadiya ta shiga domin mata iso. Iyakarta falon farko tai kira ta wayar landline kamar yanda tsarin Sarki Sameer yake. Munaya ce dake masa tausa ta ɗaga, cike da girmamawa Jakadiya ta isar da saƙon Safah. Daga can Munaya zata fara faɗa akan Safah ta jirata saita fito Sarki Sameer yaymata nuni data bari Safah'n tazo, badan tasoba tabi umarninsa.
Cike da ɗoki Safah ta shiga kamar yanda Jakadiya ta sanar mata anbata izini, tun daga falon farko har zuwa na uku bata iske kowaba, hakan yasata wucewa ƙaramin falon da bakowa keda lasisin shigarsaba saisu da iyayensu. Tai sallama a bakin ƙofa suka amsa mata kafin a bata izinin shiga. Sarki Sameer na kishingiɗe a ƙasan lallausar daddumar da
aka ƙawata falon da ita, ya zubama ɗiyar tasa da bazata gaza shekaru sha uku ba ido yana murmushi, itama murmushi take masa tana satar kallon Ummu dake zuba mata harara ta gefen ido. Ganin tayi tsaye taƙi ƙarasowa garesu mai-martaba yakai dubansa ga gimbiya Munaya, hannu yakai yanda Safah bazata ganiba ya Mintsineta, gimbiya Munaya ta ɓata fuska irin taji zafinnan, gira ɗaya ya ɗaga mata yana murmushi da cewar, “Kin tsaremin yarinya da ido takasa ƙarasowa, Ummuna kinga zo naji mike tafe dake?”. Da sanɗa Safah ta raɓa gefe taje ga mai-martaba daya tashi zaune sosai, hannunta ya kamo ya zaunar da ita kusa dashi. Safah akwai shagwaɓa da ƙulafucin iyaye, gashi tsiwarta data gada ga Munaya yasa Sarki Sameer ke tsananin sonta sosai, danshi idan tana abu Munaya kawai yake gani a zamanin ƙurciya. A jikinsa ta lafe tana kumbura fuska, cikin raɗa tace, “Abbu dan ALLAH kacema Ummu tabar hararata ni tsoron idanunta nakeyi, kumafa abu mai muhimmanci zan faɗa”. Murmushi mai-martaba yayi, ya maida dubansa ga Ummu data tsume fuska. “Ummu Please kiɗan saki fuska mana, kinga dai tsoron idanunki mukeji”. Yanda yay maganar cikin marairaice fuska ya sakata yin murmushi ta ɗauke kanta daga garesu.
Safah ta gyara zama ganin Ummu tabar harararta tace, “Abbu kasan miya faru a inda mukaje kuwa?”. “Saikin faɗa Ummuna”. duk abinda suka iske na rikici a gidansu Bilkisu shi Safah ta zauna tsaf ta zayyanema mai-martaba da Ummu, sosai abin ya basu mamaki, sai dai basuce komai akan batunba Ummu tace, “Tunda kin gama faɗa tashi kije idan na fito zanyi magana dasu Amaturrahman”. Sosai Safah ta kumbura harda hawaye, tace, “Abbu kajifa ni bandani za'ayi maganar bayan aunty nace”. Murmushi takawa yay yana mai girgiza kansa, ya shafa kanta yana faɗin, “Ai dolenema ayi magana da magajiyar Ummu, bayan ma kece kika kawo zancen”. Cikin ɗoki tace, “Yauwa Abbunmu shiyyasa nake sonka, bara naje na faɗama Mommah itama”. Kafin wani cikinsu yay magana ta fice da gudunta.
Ummu tace, “ALLAH dai ya shiryeki Safah, nikam bansan irinkiba”. Murmushi takawa yay tare da ɗora kansa saman cinyarta, yakai hannu ya shafi kumatunta yana mai lumshe idanu, “Dukfa rawan kan Safah a wajenki ta gada, kinsan kawai dai shi ɗan gado idan ya gaji abu saiya zarta mai shine”. Murmushi gimbiya Munaya tayi itama tana shafa kansa, tace, “Kaikuma gashi baka mantuwa yallaɓai”. Sosai ya buɗe idanunsa a kanta yana mata wani sassanyan kallo, cije lips ɗinsa da yay tare dayin ƙasa-ƙasa da murya kamar mai tsoron ajisu yace, “Yallaɓiya ai Sameer bai cancanci mantawa da ƙuruciyarki ba, kin bani wahalafa da yawa madam”. “Kamar yanda nima ka baniba”. Dariya sukayi a tare. Saida suka tsagaita takawa ya tashi zaune sosai idanunsa akan gimbiyar tashi. Yace, “Ban fahimci zancen Safah ba, mike faruwane?”. Cikin nutsuwa gimbiya munaya ta zayyane masa komai akan farkon haɗuwar Bilkisu dasu Safah ɗin a wajen Saloon ɗinta, har tafiyarsu yau domin kaimata l'd cards ɗin da Safah ta zama sanadin ɗakkosu. Shiru baice komaiba tsahon wasu mintuna, itama Ummu bata sake cewa komaiba. Harma ta sakin zancen sai y jeho mata tambaya akai “Toke yanzu mi kika fahimta a zancen nata kenan?”. “Eh to inason nasamu ƙarin bayani wajensu Amaturrahman ne, daga nan sainaga idan maganar nada muhimmancin da zamu shiga ciki, dan na lura a zancen Safah kamar ita yarinyar ba ƴar gidan bace”. Kansa ya jinjina mata kawai, daga nan suka saki zancen suka cigaba da hirarsu.
_________________________________
Kai tsaye asibiti Jawaad ya nufa, Ummie ta wuce gida tun ɗazun bayan zuwansu Batool da Jawaad ya kira Ummah babba ɗazun yace taje asibiti ta kwana a can wajen Bilkisun, babu musu batool ta amsa sukazo tare dasu Ummah suka duba Shahudah da bilkisu, su su Ummah sai suka koma gida akabar batool din anan, da Nabeelah ma ta tubure nan zata kwana tana ta hawaye ganin halin da Bilkisu ke ciki, harda rantsuwar saita rama mata, saida ummah ta lallabata saboda sunyi yawa, kuma Jawaad tunda ba ita yaceba idan yazo ya sameta tasan kaniyarta zaici ne..
Batool na zaune suna ɗan hira itada maman Amina aka
n abinda ya faru yay knocking ƙofar, a zatonsu Doctor ne ya dawo. Ganin Jawaad ya saka Batool mamaki, dan cayayma Umma sai da safe zai dawo daga inda yaje, zatai magana yay saurin saka yatsansa saman baki alamar tai shiru, shirun kuwa tayi. Ya gaida Maman Amina cikin girmamawa dan dama sunsan juna tun lokacin da take aiki gidansu Shahudah kafin ta barma Amina saboda matsalar ciwon ƙafa data isheta. Takawa yay zuwa gaban gadon da Bilkisu ke kwance dama tunda ya shigo idanunsa a kanta yake, baya ganin fuskarta saboda ta juyama ƙofar baya. Cikin dabara maman Amina ta fita daga ɗakin.
Ta inda bily ta juya fuska Jay ya zagaya, tsaye kawai yay ya zuba mata manyan idanunsa da sukai jazur da ɓacin rai, tsawon mintuna uku kafin ya kalli Batool dake tsaye itama tana kallon bilyn. Cikin ɗacin murya yace, “Waye yay mata wannan dukan?”. Itama Batool muryarta da alamun baƙin ciki ta bashi amsa da cewar, “Su Aamilah ne akace, inason dan ALLAH kaci uban yarannan Brother, saboda wannan abin da sukai tsabar cin zaline ai da hauka, yaran gidannan naku sam tarbiyya bata ishesuba na lura, mtsoww!”.
Baice da Batool komaiba, sai dai yanda fuskarsa ta ƙara tsukewa zakasan lallai ran ƴan maza sun ɓaci, tsahonsa ya rage tare da ranƙwafowa akan bily da duk batasan anaiba, yakai hannun damarsa a hankali gefen kumatunta da yafi ko ina kumbura, motsawa tai tare da yatsine fuska alamar taji zafin taɓawar da yay ɗin, ya sauke nannauyar ajiyar zuciya yana mai janye hannunnasa. Tsaye ya miƙe idonsa har yanzu akan Bilkisun yace, “Mi Doctor yace yanzun?”. “Sunyi magana da Ummah, bansan miyace mataba gaskiya”. Bai sake cewa komaiba ya cigaba da kallon Bilkisu na tsahon lokaci, kafin ya sauke numfashi da zare hannunsa ɗaya daga aljihun wandonsa ya ɗauki file ɗin daya gani a drawer gefen gadon, saida yagama dube-dubensa sannan ya ajiye yay ficewarsa batare da yacema Batool komaiba. Itama da kallo kawai ta bisa, haka kawai yau takejin matsanancin tausayin ɗan uwan nata da ya kasance shi ɗaya tilo, babu wa babu ƙani, babu iyaye baki ɗaya sai dangi.
Magana yaje sukai da Doctor, ko kallon ɗakin da aka kwantar da Shahudah baiyiba yay ficewarsa daga asibitin, daga nan gidan Alhaji baba ya nufa.
Kiraye-kirayen sallar isha'i da akeyine ya sakashi shiga massallaci, saida aka idar ya shiga gidan. Shima Alhaji baban shigowarsa kenan babu jimawa, Jawaad ya zauna ya gaishesa, amsawa Alhaji baba yay idonsa akan jikam nasa. fuskar Alhaji a ɗaure baba yace, “Daga ina?”. Batare da Jawaad ya kallesaba yace, “Gida”. “Ɗazun kumafa da akaita nemanka a wajen ɗaurin aure?”. “Aiki naje”. Alhaji baba yace, “Humm aiki? Kenan bakasan miya faru a wajen ɗaurin aureba ma?”. Kan Jawaad a ƙasa dan yaƙi yarda su haɗa ido da kakan nasa yace, “Na sani, ninema na canja list ɗin ai”. Idanu Alhaji baba ya ɗago daga littafin addu'oin dake hannunsa ya kafe Jawaad ɗin da kallo, cikin sake ɗaure fuska yace, “Ai nasan bazai wuce kaiɗinbane daman, miyasa kai hakan?”. Kallonsa Jawaad ya ɗago yayi sai kuma ya ɗauke kansa yana wani ɓata fuska, dama yasan ko kowa bai gano shi bane da wuri Alhaji baba sai ya gane.
Alhaji baba yay ƙwafa yana maida kansa ga littafin da faɗin, “A hatsabibancinka dana sani hakan ƙaramin abune a gareka Jawaad, amma ince tun randa mukaje gidan Alhaji Ali akan maganarnan ya tabbatar mana da ɗansa zai aurama yarinyarnan kace ka haƙura?”. “Hakane baba, kamar yanda na faɗa a gabanku na haƙura na barmasa da gasken na haƙuran, sai dai kuma dalilin daya biyo bayane yasa na canja shawara”. Ran Alhaji baba ya fara ɓaci, dan haka cikin zafi yace, “Kasan zan iya saɓa maka ko Muhammad? Har wane irin banzan dalili ka riƙe da bazakazo ka sanar minba kafin ka yanke masa hukunci? Banason wannan shegen taurin kan nakafa kaima ka sani”. Sosai idanun Jawaad suka sake kaɗawa sukai jajur, jijiyar kansa dukta fito ruɗu-ruɗu, yasan duk sanda zaiyi abu saiya zo ya sanarma Alhaji baba, dan a halin yanzu shine kawai ke iya nuna masa ɓacin rai idan ya aikata ba dai-daiba kuma ya tsawatar masa akan ya kiyaye gaba, to amma akan wannan shi kansa baisan miyasa zuciyar
sa taƙi aminta da ya nema sharar kowaba akan batun har sai bayan ya aiwatar..........
“Ina maka magana ka tafi tunani”. Jawaad da maganar Alhaji baba ta maido hayyacinsa yay ajiyar zuciya, cikin sanyin murya yace, “Nayi laifi kayi haƙuri, amma zuwa nan gaba kaɗan zaka fahimci hakan danai shine dai-dai baba......”
“Dai-dai ɗin ƙaniyarka, ka sakar musu yarinya ta auri wanda suka zaɓa mata, shikuma wancan habibun halan shima kaine ka kawosu shi da Azeemar? Tunda kasan har cikin ranka bakason maida yarinyarnan miyasa ka amincemin zaka maidatan?”.
“Baba nifa bani na kawosuba, su Uncle Nasir pretending kawai suke akan maganar suma, dan sunsan wacece Azeema, tunda da saninsu aka ƙulla aurama shi Qaseem ɗin ita, sannan sakin yarinyar zai zama babban kuskurene, akwai wani abu da suke ɓoyewa akan yarinyar, ka bani damar bincikosa sanan, na yarda inhar nine banda gaskiya ka ɗauki kowane hukunci”. Shiru Alhaji baba yay yana kallon Jawaad da nazarin kalamansa a ƙwaƙwalwa, kusan mintuna biyu suna a haka shiru kafin Alhaji baba ya ɗauke kansa daga kallon Jawaad ɗin ya maida ga littafinsa, “Ka dainamin ɓoye-ɓoye, ka fito fili kasanar min abinda ke faruwa?”. Ajiyar zuciya Jay ya sauke da faɗin, “Duk abinda zan faɗa a yanzun zai iya zama kuskuren abinda yake a zahirin gaskiya ne, nima a yanzu bakomai na saniba baba, sai dai insha ALLAH zan binciko duk abinda yake a binne nanda ƙanƙanin lokaci insha ALLAHU”. Tsagwaron gaskiya Alhaji baba ya hango a kalaman Jawaad, hakan yasa bai sake cewa komaiba.
Miƙewa Jay yay ya nufi bedroom ɗin kakan nasa yay kwanciyarsa.
Alhaji baba ya bisa da kallo har saida ya shige, tabbas ya fahimci akwai abinda Jawaad ke ɓoyewa, kuma da alama yanada alaƙa da Uncles ɗin nasa, bazai matsa masaba akan sai yaji komai a yau, dan yasan idan yana fushi takura masa akan abu sake busar masa da zuciya yake, sai dai yasan duk abinda Jawaad ya dage a kansa to lallai akwai abinda ya hango a cikinsa, shi kansa akwai mafarkan da yake a kwanakinnan suna damunsa, ya kuma rasa ina suka dosa?, abin mamakin shine kullum mafarkin maimaita kansa yakeyi, kayi mafarki sau ɗaya sannan ka sake maimaitashi gobe, har tsahon wasu kwanani dolene kasaka masa alamar tambaya koda kaso tureshi a ranka. Tsahon lokaci yana zaune a falon yana tunani bai shiga ɗakinba sai kusan sha ɗaya, lokacin tuni Jawaad yay barcima shi. Shirin barcin yay shima ya hau gadon, idanu ya tairama Jawaad dake barci fuska a ɗaure alamun cikin ɓacin rai yay barcin, Alhaji baba ya sauke numfashi tare da shafa kan jikan nasa, a ƙasan ransa yanajin tausayinsa, gefe kuma yana jin matuƙar tsoron irin hatsabibancin Jawaad da rashin tsoro, yana tsoron kar wani yay amfani da wannan halayyar tasa ya cutar dashi wataran. Da waɗanan tunane-tunanen fal ransa yay barci shima.
★★★★★★
Bayan tafiyar Jawaad Maman Amina ta dawo ɗakin, macece ita mai yawan ibada dama, bata wasa da ibada ko kaɗan, dan haka koda ta dawo saita ɗauro alwala takoma gefen bilkisu ta zauna a kujera dan ganin wata irin zufa da Bilkisu keyi mara dalili, gashi sai mutsu-mutsu take kamar wadda aka saka cikin wuta, Batool kuwa tana gadon mara lafiya ɗaya daya rage a ɗakin tai kwanciyarta itama. Addu'oi maman Amina taita tofama bilkisu dan zufar ta bata mamaki da tsoro, gashi akwai fanka a ɗakin tana aiki kuma, bakuma wani uban zafi akeba a garin balle ace, da alama dai mafarki Bilkisun keyi. Ahankali-ahankali gumin ya fara tsanewa daga goshin bilkisu, ta koma sauke numfashi ahankali saɓanin da datake yinsa da sauri-sauri, takuma nutsu waje ɗaya. Tajima tana mata addu'ar har kusan ƙarfe ɗaya kafin ta miƙe ta shimfiɗa abin salla ta fara nafilfilinta data saba a zaune saboda ƙafarta bata jimirin tsaiwa.
Wani irin sukur-sukur maman Amina keji a ɗakin, tun tana ɗaukar motse-motsen da takejin a wasa hartakai ta fara waige-waige, tabbas tanaji a ranta akwai wani abu a ɗakin da itama bata iya hasasowa ba, tashi tai ta ɗakko jikkarta datazo asibitin da ita ta ciro Qur'anin da tazo da shi, karatu ta fara cikin suratul baƙara, sai motsin da takeji ya ƙara ƙarfi, ɗa
ga kan da zatai sai idanunta yaci karo da wata irin halitta mai kama da ƙadangare yana fitowa daga ƙarƙashin gadon da bilkisu ke kwance, sai dai kuma shi wannan farine fat tamkar babu jini jikinsa, sannan ƙaton gaske kamar kada ta cikin ruwa, jikinsa sai wata iriyar muguwar walƙiya yake tamkar ruwan dake kwance cikin teku, dukda zuciyarta ta girgiza da kallon wannan halitta mai ban tsoro dake nufota sai bakinta bai daina karanto ayoyin alƙur'anin ba kasancewarta jaruma mai dakakkiyar zuciya, tsayawa yay cak a tsakkiyar ɗakin batare da ya ƙaraso gareta ba, ya shiga goga kansa a ƙasan ɗakin kamar wanda ake duka, kafin kuma ya juya bindinsa har gab da ita ya fuskanci ƙofar fita, da gudu ya fice tamkar an masa umarni. Cigaba tai da karatunta har lokacin ta gaza ɗauke idanunta daga ƙofar. Sam Batool batasan wainar da ake toyawaba, barci take kashirɓan, bily ce dai bazamuce ga halin da take cikiba. Sautin karatun alkur'anin da Mmn Amina keyine ya tada Batool, itama samun kanta tai da shiga bayi tayo alwala, ta idar kenan ta miƙe tana gyara ɗan kwalinta zata fito taga wani ƙaton maciji jajur dashi yana silalawa ta Window toilet ɗin zai fita, ƙara ta ƙwalla tare da fitowa a guje jikinta na masifar rawa. Tazo ta ƙanƙame maman Amina dake cigaba da karatu dukda hankalinta yayi masifar tashi da ƙarar Batool ɗin, tanaji a ranta itama wani gamon tai a bayin................✍
Sannu sannu bata hana zuwa saidai a daɗe ba'a zoba. to aljanin daya canja takarda ya bayyana😂, sai muje zuwa domin jin dalilin Jawaad na canjawar da kuma tayaya ya canja ɗin, da alama kuma ya fara bankaɗo wani sirrine da zai bamu hasken sanin ina muka dosa🚴🏼. ALLAH ya daidaita sahun Jawaad akan lokaci😂, bara na fece nidai kafin ya karyani🚴🏼🚴🏼🚴🏼.
Barkanmu da dawowa, ina fatan kunsha weekend lafiya?.
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
Page 24
Godiya ta musamman ga UMMINRASHIDA CARE FOUNDATION, saƙo ya iso gareni, ina muku fatan alkairin nima, tare da godiyan bangirma da jinjina, alkairin ALLAH yakai gareku aduk inda kuke. Nagode da wannan girmamawa taku a gareni, duk da har yazu dai bilyn Abdull rarrafe takeyi, Inai muku so irin trillions ɗinnan😍😍😘😘👍🏻
................Jin Alhaji baba ya fara sauke numfashi Jawaad ya buɗe idanu a hankali, juyi yay domin ya tabbatar barcin baba yay nisa tamkar a cikin barci yake, shiru baiji Alhaji baba ya motsaba, yay murmushi tare da sauka daga gadon a hankali, cikin sanɗa ya fito daga bedroom ɗin, a falonma yanayi yana waiwaye harya fice, gudun matsala yasa yabar motarsa anan ya fice daga gidan baki ɗaya, wayarsa ya ciro a aljihu ya duba time, sha biyu saura kwata, ya maida wayar a aljihu yana furzar da iska. Daga gidan zuwa titi babu nisa sosai, hakan yasa ya taka da ƙafa ya samu napep. Saida suka fara tafiya ya sake fiddo wayarsa ya duba saƙon su Jabeer daya shigo tun ɗazun, ɗan typing yayi kaɗan ya tura musu cewar gashinan a hanya.
Cikin mintuna kaɗan suka iso gidansa na A.Y, sai dai bai bari sun ƙarasa gidanba ya sauka, dubu guda ya miƙama mai napep, yana ya tsaya ga canji amma Jawaad bai saurareshiba yay wucewarsa. Mai napep ya cusa kuɗinsa a aljihu yana faɗin “gaba ta kaini inma bakasan ka baniba”.
Oho Jawaad baisan yanaiba, tunima ya shige gidan. A falo ya iske su Aliyu, kowa da hidimar da yakeyi, ya zauna cikin kujera yana faɗin, “Kuyi haƙuri na rikeku anan ga madams suna jiranku a gida”. Hafiz dake aiki a lap-top yace, “Babu damuwa ango, yanzu dai mike faruwa?”.
Ajiyar zuciya Jawaad ya sauke yana faɗin, “Akan abinda ya farune yau, nasan kuma duk a ƙage kuke da sonjin yadda akayi?”.
Hakane boss. Suka faɗa a tare idanunsu na akansa.
Bayansa ya jingina da kujera yana mai ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, cikin ɗacin murya yace, “Kamar yanda nasan tunaniku na akan nine na canja komai hakane, nayi ne saboda labari dana samu daga majiya mai ƙarfi akan abinda Momy ta ƙulla ita dasu mama Atika. A zahiri sun tsaida bikin Qaseem ne da yarinyarnan Miemaa, sai dai a baɗini sun tanadarma Qaseem mata batare dashi kansa ya saniba. Azeemar da aka ɗaura aurensa dashi ɗiyace ga Gwaggo Hajarah ƙanwar Momy da suke ɗaki ɗaya”.
Sosai mamaki ya cika zukatan su Jabeer, Hafiz yace, “To amma miyasa sukai hakan?”.
“Wannan itace amsar da nakeson mu nemo nima Hafiz, har yanzu mamaki baibar ɗawainiya da zuciyataba akan wannan al'amarin, miyasa zasu aurama Qaseem Azeema bayan sunsan ga wadda yace yanaso?”. Jabeer yace, “Nidai a nawa ganin kamar dama basason aurensa da Mami ne, sunsan kuma kosun hanashi bazai hanuba, shine suka zaɓi bi ta bayan fage su haɗa masa guda biyu, zaɓinsu da kuma nashi zaɓin”. Hafiz yace, “Maganarka akwai ƙamshin gaskiya Jabeer, to amma idan hakane shi Habib ɗinan miya kawosa cikin wannan al'amarin, sannan wanene shiɗin kuma?”.
Aliyu datun ɗazun baice komaiba yay ƙwafa, “Ni wlhy kusan kawai minake saƙawa a wannan lamarin kuwa; Duk kallonsa sukayi suna jiran ƙarin bayani. ya cigaba da faɗin, “Inagafa su sun tsara al'amarinne akan boss ya auri Shahudah, Qaseem a bashi Azeema, ita kuma Mami su aura mata Habib ɗin, inhar ba hakanne tsarinsuba miya kawo shi habib ɗin a zancen tunda alama ta nuna babu matarsa a cikin list ɗin ɗaurin auren?”. Zaune sosai Jawaad ya tashi idanunsa akan Aliyu, yace, “Aliy wannan maganar taka haka take, abinda yake cin raina anan inhar hakanne to kenan shi Dad bai fahimci Mom batason aure Miemaa da Qaseem ba kenan? Kokuwa shima ta shirya cin dunduniyarsa ne? Tunda ɗiyar ƴar uwarsa ce”. Hafiz yace, “To nima dai abin yasani wannan hasashen, amma kuma idan mukai dubi da yanda ya tada hankalinsa bayan faruwar abun harda suma hakan na nufin baisan su Momyn Shahudah sun shirya hakanba?”.
Shiru duk sukai suna nazarin maganar Hafiz ɗin, Jawaad ya miƙe tsaye hanayensa duka cikin aljihun wandonsa, kallo , hardasu Uncle Nasir, abinda yasa abin ya tsayamin
arai shine, miyasa shi Uncle Nasir zai zama munafuki a tsakaninmu? Shinefa ya jagorancemu wajen Dad ni da Alhaji baba akan maganar Miemaa ɗin, saboda Ummah ta matsa akan sai dai Alhaji baba ya nemamin aurenta tare da Hudah kodan hakan ya zama gargaɗi gareta, kenan yasan shirinsu da Momy, amma kuma ya amsama Alhaji baba cewar muje muyima Dad ɗin maganar a haɗamin auren Miemaa da Hudah? Sannan sarai yasan Qaseem an tsaida masa ranar aure da Miemaa! ɗin kuma?”.
“To tabbas kam wannan matsalar daga nan take boss, Uncle Nasir yasan komai, amma kam bai ƙyautaba, dan nikam ina bala'in ganin girmansa wlhy saboda yanda ya riƙeka, ashe ba har zuciya bane, wannan wane irin zumincine muke fama dashi a wannan zamanin?, kaga yanda aka cukurkuɗe abu saboda kawai buƙatun wasu dason faranta musu, kuma duk idan kaje ka dawo zaka fahimci ita Mami itace akai shirin sakawa a tsaka mai wuya, miyasa sukaso mata wannan mugun ƙullin to?”.
Duk hankalinsu suka maida ga Jawaad da yay shiru yana nazarin kalaman Jabeer na ƙarshe akan uncle Nasir da maganar ƙullin da akaso yima Bilkisu. Cikin son maidosa hankalinsa Hafiz ya zunguresa, kallonsa yay. Hafiz yace, “Mi muke ciki yanzun? Dan ko game da Mami muna buƙatar bincike mugano gaskiyar maganar Jabeer, mizaisa suyi shirin cutar da ita?”.
Guntun Murmushi kawai Jawaad yay ya koma cikin kujera ya zana, kwantar da bayansa a kujeran yana mai lumshe idanunsa, a hankali ya furta, “Wannan shine dalilin zamanmu anan, dan inaji a raina wannan ƙiyayyar da sukaso nuna mata tawuce naƙin son aurenta da Qaseem kawai, akwai wani abu da bamu saniba, dan haka inason sanin anahinma alaƙarta da mutanen gidan”.
Jabeer ya ajiye cokali yana faɗin, “Kamar ta taɓa gayamin Dad yayan mahaifiyartane ubansu ɗaya, kaga kuwa bazai wuce Momy ta ƙitaba akan ƴan ubancin dake tsakanin Dad da mamata, sai dai kuma zata iya yiwuwa ɗin akwai wani abu a ƙasa damu bamu saniba harsai mun bincika tukunna”.
“Kai lamarinfa akwai ɗaurekai, sannan akwai lauje cikin naɗi, aganina tunda basa sonta da ɗansu su rabasu kawai basai sun zalinceta sun haɗata aure da wanda bata saniba”. Hafiz yay maganar cikin takaici.
Aliyu yace, “Kai dai bar son zuciya Hafiz, amma harma nawa Mami take da za'a mata irin wannan muguntar? Yanzu dai boss mikace kai akan batun? Tunda dai ALLAH yasa ta fita daga tarkonsu, yanzu aikin farko dake gabanmu shine Qaseem da Shahudah, baƙaramin yaƙi zasuyi a kankaba da Mami tunda. Shin Ka sanar musu kaine ka canja sunayen ne?”.
Jawaad da duk yake saurarensu cike da nazari yace, “Eh na sanarma Alhaji baba ɗazun, na nuna masa nine na canja, nakuma saka masa zancen Azeema ciki, na tabbatar zuwa safiya zai nema su Uncles da maganar, mukuma sai muyi amfani da wannan damar”.
“Amma Boss baka ganin ka ɗaure kanka da yawa? Taya za'ai ka amshi laifin kai tsaye bayan bamusan mike a ransuba game da batun?”. .
Muryarsa cike da damuwa yace, “Jabeer hakan shine kawai hanya mai sauƙi da zamu bama koma waye ƙafa, sannan Bazaka ganeba, rikicin tsohon nan ya wuce dukkan tunaninka, gara nafito na faɗa masa gaskiyar maganar, harfa ya kafamin sharaɗin saina saki Miemaa, yanzu dai nagama da matsalarsa”.
Dariya sukayi a tare, cike da tsokana Jabeer yace, “To tsakani da ALLAH gaskiya Alhaji baba ya faɗa, ka bama Qaseem matarsa”. Banza yayma Jabeer ɗin, ya miƙe yana kallon agogon hanunsa, “Kunga ɗaya harta wuce, mu tsaida maganar iya haka, zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu nasan Alhaji baba zaisa ai zama akan batun, anan zan fahimci yaren kowa, daga nan saimu ɗora da abinda ya dace kawai”.
Duk sunyi na'am da jawabinsa, kowa ya miƙe yana tattare kayansa kafin su fito, Jawaad tare suka tafi da Hafiz zai ajiyeshi gidan Alhaji baba saboda hanyarsa ce shi, su kuma su Aliyu kowa ya shiga motarsa.
★★★★★
Da sanɗa Jawaad ya shigo bedroom ɗin duk dan karyay motsin da zai tada Alhaji baba, a bazata yaji yace, “Daga ina?”. Tsam Jawaad yay ya kasa ƙarasawa, cikin sauke ajiyar zuciya yace, “Nafita akan wani aikine”. Alhaji baba baice komaiba, hakan yasa Jawaad
ɗago kai, cikin ɗacin rai yace, “Mafita itace wannan yaron ya sakarmin mata tunkafin rayuka suyi ɓacin da yafi na yanzu”.
Miƙewa Jawaad yay cike da takun ƙasaita ya ƙarasa gaban Qaseem sunama juna kalon kallo tamkar wasu zakuna, baki ya taɓe yana binsa da wani banzan kallo, cikin kakkausan furuci yace, “Gurɓataccen tunani kenan Qaseem, domin kuwa wannan shine abinda bazai taɓa faruwaba koda a cikin mafarki, kayi wani tunanin amma ba wannanba” Yaƙare maganar da ɗan buga kafaɗar Qaseem ya raɓashi ya fice daga falon.
Babu wanda ya iya yunƙurin hana Jawaad ɗin fita har Alhaji baba, dan a ganinsu garama ya tafi kar abin ya kuma ƙwaɓewa tsakaninsa da Qaseem. Asibiti Jawaad ya nufa domin ganin yaya su Bilkisu suka tashi. Saida ya tsaya ya sai abubuwa a hanya dukda yasan za'a kai abinci daga gidan Ummah, mintuna kaɗan ya shigo asibitin, da Nabeelah yaci karo ta fito sayama Ummah kati, ta amshi kayan hannunsa tana masa sannu da zuwa da gaishesa. Bai amsaba saboda waya yakeyi, hannu kawai ya ɗaga mata yay gaba, tabi bayansa tana gulmarsa a zuciya batare daya saniba, hardasu kwaikwayon tafiyarsa.
A ƙofar ɗakin ya tsaya yayma Nabeelah nuni akan ta shiga domin sanar dasu. Da “to” ta amsa, shikuma ya cigaba da wayarsa a nutse, baifi minti biyu da shigartaba tafito tace ya shigo.............✍
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
n amsoshinnan a wajenka.......”
Murmushi Jay yayi, sai dai baice komaiba, hasalima kansa a duƙe yake bai kalli kowaba har yanzun. Alhaji baba ne ya tsaida Momy jin tanata aibanta masa jika, “A'ishatu, inaga mubashi dama muji ina maganganunsa suka dosa kafin mu yanke hukunci koda na furucin bakine, mudukanmu nan a ƙage muke dason jin amsa, yakamata muji yaya akai aka kwana a ragaya bayan munsan shirinmu a tandun mai ne”. Magana Momy zata sakeyi Qaseem yace, “Momy Please ki zauna miji munafurcin dazai faɗa”. Ƙwafa Momy tayi ta koma ta zauna saboda gargaɗin da Uncle Uwaisu yay mata da idanu.
Shirun da akaine ya saka Jawaad ɗagowa, yace, “Inaga kafin warware dukkan sarƙaƙiyar massallaci yakama musan wacece Azeema da aka ɗaurama Qaseem aure da ita? Domin wannan shine kawai zai zama mabuɗin buɗe mana gaskiyar abinda muke son sani baki ɗaya”. Tsit falon yay saboda bugawar da zukatansu sukai a lokaci ɗaya babu zato ko tsammani da zuwa furucin Jawaad ɗin a garesu. Alhaji baba ya katse shirun da cewar, “Banda abunka Muhammad Jawaad muma ai duk amsar da muke nema kenan akan Habib da Azeema?”.
Jawaad yace, “Hakane Alhaji baba, amma ina ganin karmu jata da nisa, domin su Uncle duk sunsan wacece Azeema da Habib, idan ka cire Imam da jama'arsa, kai da Uncle Sulaiman, Uncle Sadiq, Qaseem, kune kaɗai kuke neman ƙarin bayani”. Uncle Sulaiman yace, “To mukam saiku amsa mana kunata sake dilmiyar damu a hasashe”. Fuskar Uncle Nasir a matuƙar ɗaure cikin kafe Jawaad da idanu yace, “Mikake nufi da waɗanan kalaman naka?”.
Jawaad yace, “Babu abinda nake nufi Uncle, kawai dai ina son kowa ya fahimci daga ina matsalar take harshi Qaseem ɗin da aka ɗaurama aure.......”
Cike da masifa Momy ta sake katse Jawaad da faɗin, “Inma wani munafurci ka ƙulla kai zai ƙaremawa, inace dai sokake kace mune muka haɗa auren Azeema da Qaseem batare daya saniba, to ai mun isane, yarinyar da ya kawo yanason zai aura batai manaba, tayaya idan shi baisan ciwon kansaba mu zamu biye masa duk muzama mahaukatan?”.
Cikin ɓacin rai Jay yace, “Amma miyasa ni da nazo neman a bani na aura kukace Qaseem shi zai aureta?”. Yanzukam tamkar Momy zata mari Jawaad ta bashi amsa a matuƙar zafafe “Saboda Shahudah tafi ƙarfin yin kishi da ita, bandama rashin mutunci da raini irin naka Jawaad, bakaji kunyar zuwa a gaban idanunmuba kace mu haɗa maka ƴar cikinmu da wadda mukema alfarma mu aura maka”. Sosai zuciyar Jawaad take sake hasala, sai dai ƙoƙarin dannewa yake dan koba komai Momy yayar mahaifinsa ce ita, cikin ƙoƙarin danne fushinsa yace, “Amma Momy dan kawai baƙwa ɓuƙatar marainiyar ALLAH ta jingini da jininku sai kuje ku biya wani kuɗi dan ya aureta bayan kunsan shiɗin ba mutumin kirki baneba? Wai shin nawa ita wannan duniyar take da har muke tunanin wanda muka tseramawa bazai taɓa taddomu ba? Baƙwason ta auri ɗanku, baƙwason tayi kishi da ƴarku, tominene fa'idar biyan wani ya aureta? Saiku barta ALLAH ya kawo mata wani mijin, shi kuma Qaseem ku sanar masa bakwason alaƙarsa da ita bawai saikun cutar da itaba ta hanyar da batajiba bata ganiba.......”
Qaseem ya miƙe a fusace zaiyi magana Uncle Sulaiman da baƙin ciki ya lulluɓe yay saurin katseshi daga shi har Jawaad ɗin, yace “Kai Qaseem kaga zauna, ku kuma Kunga kudaina mana magana a cuɗe daga kai har Humaira, shin minene ya faru?”.
Sosai zuwa yanzu fushin Jawaad ya kasa dannuwa, cikin zafin zuciya da kowa yasanshi da ita idan aka kaisa bango yace, “Wato Uncle yarinyace suke riƙo a gidansu, har takai maganar aure ya shiga tsakaninta da Qaseem, kuma sune suka amince masa, amma kuma sai suka koma ta bayan fage suka nema masa auren Azeemar gwaggo Hajarah. Bayan kuma Alhaji baba yaje akan su bani auren yarinyar amma suka nuna min cewar shi Qaseem ɗinne zai aureta. Abinda kuma zai baka mamaki ita kuma yarinyar suka samu wani da sam ba mutumin kirki bane suka biyashi akan zasu aura masa ita yarinyar batare datasan da shirinsu ba, kuma sun nuna masa duk badaƙalar da za'ayi karya sake ya saketa, wannan shine dalilin dayasa na koma nima ta hanyar da sukabi na canja nasu shirin
da nawa, tabbas nine na canja takardar da akaba Imam da tawa a lokacin da yake ƙoƙarin shiga massallaci.. Bayan duk an kawomin bayanai akan shirin da sukai na cutar da yarinyar saina shiga nazarin neman hanyar daya dace na hana faruwar mummunan ƙudirinsu, a kaf hanyar danake gani zata zama yarinyar za'a sake cutarwa, dan haka daga ƙarshe sai na yanke shawarar bin hanyar da suma sukabi, wato ta ƙarƙashin ƙasa. Imam idan har baka mantaba bayan isowarka massallaci wani yazo ya sameka akan batun wani aure, har ya roƙi afuwa akan rashin kawowa da wuri, kaikuma ka amshi uzirinsa tare da bashi takardar list ɗin sunayen waɗanda za'a ɗaurama aure a ranar kace ya rubuta sunayen waɗanda yazo dasu a gurin, to ba kowa bane face ni, da wannan damar nai amfani na canja takardarma baki ɗaya bayan na kwafe sunayen dake can nakuma canja namu a yanda naso”.
Salati manyan suka sanya da wannan al'amari, yayinda Cikin ƙaraji Qaseem yace, “ Momy!!!, mikuke nufi da hakan da kukayi to? Minai muku da zafi haka kuka zaɓi zalintata ni da Bilkisu?!, to wlhy, na rantse da ALLAH, ku kwana da sanin...........” da sauri Momy ta rufe masa baki, sauran ƙarfinsa da wanda ɓacinrai ya kawo masa yanzu ya tattara ya hankaɗe Momy gefe ta faɗi. Jawaad ne yay saurin miƙewa yana faɗin, “Qaseem minene haka? Baka da hankaline?”.
“Eh bani dashi kaikuma? Idan kai haƙuri kaima ina tafe kanka, garama kayi gaggawar sakarmin mata kafin kanema numfashinka a ƙirji ka rasa”.
Wani banzan kallo Jawaad yay masa, kafin ya bashi amsa Shahudah ta katsesu da jehoma duk wanda ke falon tambaya cike da rashin kunya. “Kai broth kamaji munafukan da suka ƙulla maka naka makircin, nikuma saiku faɗamin wanene Habib yake koma wane oho muku, kaikuma Bb kai gaggawar sakin waccan ƴar iskar yarinyar tamaje ta auri Uban Qaseem a yanzu wannan bai dameniba dan kaina kawai na sani, gwarama kowa yasan abinda zanyi sai yafi naka ɗaga hankalin kowa dake gidanan wlhy”.
Jin komai ya warware Imam da tawagarsa suka miƙe domin tafiya, a ganinsu wannan matsalace ta cikin gida, sukam tunda sun fita gara su kama gabansu. Godiya su Alhaji baba sukai musu sannan suka fice.
A take falon ya kaure da hayaniya har babu maijin maganar ɗan uwansa, Jawaad na shirin ficewarsa Shahudah dake kuka tana zubama mutane rashin kunya tai saurin riƙoshi, “Wlhy bazaka fitaba saika saki tsinanniyarnan bb”. Bai tanka mataba, sannan kuma bai juyoba, sai ƙoƙarin fisgar jikinsa da yay zai fice abinsa. Ƙara Shahudah ta ƙwalla wadda ta dawo da duk hankalin ƴan falon kansu, sosai ran Jawaad ke tafasa, ji yake badan wani daliliba da sai yayma Hudah dukan mutuwa yau, saida kuma shi a tsarinsa babu bugun mace. Alhaji babane yace, “Jawaad dawo ka zauna”. Umarnin Alhaji baba yabi, ya juyo tare da zubama Shahudah wani mugun kallo daya sakata sakar masa riga ta durƙushe a wajen tana kuka, kota kanta baibi ba ya koma inda ya taso ya zauna. Ran Alhaji baba a ɓace yace, “Wanene Habib ɗin to dakasa ya aurar musu yarinya?”.
Shima Jawaad ɗin ran nasa a ɓace yake, amma dai sai ya danne cikin ladabtaccen harshe ya bama kakan nasa amsa, “Alhaji baba shine wanda suka biya ya auri yarinyar”.
Kuka Momy ta saka mai ƙarfima kuwa tana zagin Jawaad da ja masa ALLAH ya isa.
Cikin rawar baki Uncle Nasir ke faɗin, “Yanzu nan Jawaad ɗan fir'auna ka aurama Shahudahr?.........”
Uncle Sadiq yace, “Wane irin sunane haka kuma Yayah?”. Kasa magana Uncle Nasir.
Dad kam ai hawaye kawai yakeyi kashirɓan, saboda wani irin ruɗani da wautarsa akan sakarma Momy ragamar gidansa yake hangowa. Falon yay tsit kowa na jiran ƙarin bayani daga garesu, yayinda Shahudah dake jikin Momy keta ribzar kuka. Qaseem kansa kawai ya dafe saboda tafasar da zuciyarsa ke masa da matsananciyar ƙuna.
Kowa dai ya fahimci su Mom sune suka gina ramin mugunta wa marainiyar ALLAH daga ƙarshe ya rufta dasu batare dasun fargaba, Alhaji baba ya katse shirun da faɗin, “Bin ƙwaƙwƙwafin komai a yanda yake baida amfani, tunda su bamusan manufarsu ba, a ganina yanzu mafita kawai ya dace mu nema kamardai....”
Qaseem ya
nufar toilet dan ya watsa ruwa.
_________________________________
A asibiti kam daƙyar mama ta kwantarma Batool hankali, Cikin sarƙewar numfashi da tsananin tsoro tai mata bayanin abinda ta gani a toilet, shiru maman Amina tai tana nazari da haɗa komai a mizanin daya dace, a fili kuma sai tayi murmushi tana mai girgiza kanta, cikin bama Batool ƙwarin gwiwa ta umarceta akan ta tashi tai sallarta koma minene ALLAH zaiyi maganinsa. Jiki a sanyaye Batool tabi umarnin Mama.
Haka suka kusan kwana akan abin salla suna gayama UBANGIJI damuwarsu, gabannin asuba bilkisu ta farka tana ambaton a bata ruwa. Fita Batool tai ta kira Doctor'n daya kwana duty, babu jimawa suka dawo tare. saida ya tabbatar babu wata matsala tare da Bilkisun sannan yace su bata ruwan tasha.
Tunda ta kafa kai a babban goran ruwan da Batool ta saka mata a baki sai da ta shanyesa tas sannan ta ɗauke kanta, dukansu kallon mamaki suke mata hatta da Doctor ɗin kansa, sai dai babu wanda yace komai.
murya a sanyaye tace, “Mama zanyi sallah”.
Taimaka mata batool tai ta sakko a gadon, mama ta rakasu har toilet ɗin ta sirkama bilkisu ruwan wanka da ruwan dake cikin flask, fita batool tai, mama ta taimakama bilkisu tai waka da gasa jikinta dukda tana ta noƙewa saboda kunya. Itako mama sai tayi kamarma bata gantaba. Bikisu taji daɗin wankan sosai, takumaji karifin jikinta, sallolin dake kanta ta shiga ramawa harda sallar zuhur ɗin jiya data tabbatar batayita cikin nutsuwaba.
★★★★★★
Zuwa 10:30am na safe dukkan mai alhakin tofa albarkacin baki akan wannan matsalar ya hallara a gidan Dady, bisa umarnin Alhaji baba daya buƙaci hakan, dan yanason jin gaskiyar magan akan abinda Jawaad ya faɗa masa gameda zancen Azeema da yace sunsani. Jawaad yana jerin waɗanda sukazo a farko-farko dan tare yake da Alhaji baba, hakan kuwa yaso bama kowa mamaki dan sunsan halinsa sarai da iya ƙin zuwa wajen meeting akan lokaci saiya gama shanya jama'a, amma yau abin mamaki sai gashi cikin masu sakkon zuwa.
Bayan isowar Imam da wasu daga cikin manyan massallacin da aka ɗaura auren Salman da Qaseem daya rame sosai tamkar wanda ya kwana biyu yana jiyya suka shigo suma, ya ƙara haske da tsayi abin tausayi, Jawaad dai baiko kalli inda Qaseem yakeba, amma shi Qaseem sai binsa yake da wani irin mugun kallo tunda suka shigo.
Imam ne ya buɗe taro da addu'a, a kuma dai-dai lokacinne Shahudah da Mom da suka taho daga asibiti bisa matsawar Shahudahn suka shigo suma, wajen zama suka samu idon Shahudah akan Jawaad tana mai kwarar da hawaye, itama harta rame kwana ɗaya kacal. Bayan imam ya kammala addu'oi ya ɗaura bayani da cewar, “Nasan kowa dake nan yana neman amsar tambayarsane a gareni, wadda yinin jiya har zuwa dare na ɓata lokacine wajen nemota nima amma har safiyar yau ban samo amsarba, narasa wannan wane irin cuɗaɗɗen al'amarine mai sarƙaƙiya, a hasashena har junnu saida na kawo dukda bani da tabbacin haka balle hujja, ban saniba shin ko a cikinku wani nada amsar da nima nake cikin ruɗani da bulayin nemanta?”.
Shiru falon yayi babu wanda ya iyayin koda tari, sai shashshekar kukan Shahudah kawai ke tashi. Uncle Nasir ne yay ƙarfin halin bama Shahudah umarni akan ta tashi ta fita. kafaɗa ta maƙe alamar bazata tashinba, ta koma jikin Momy ta lafe tana masa kallon harara dukda kasancewarsa wan uwarta. Babu wanda ya iya sake cewa komai game da tashin Shahudah, dan kuwa anga iyayenta basu tankaba alamar basu da damuwa da zaman nata su. Jawaad yay gyaran muryar da kowa ya maida hankali kansa, batare da ya kalli kowaba yace, “Imam kayi haƙuri, babu ta inda zaka iya samo amsar sarƙaƙiyar jiya kaida duk wanda keda alhakin sanin sirrin massallacin nan. Ni dasu Momy mune kawai masu wannan amsar, dukda inada tabbaci da yaƙinin bayanmu wasu sunsan komai koda ba duka ba”. kaf falon babu wanda bai sagade yana kallon Jawaad ba, yayinda Momy ta miƙe zumbur tana nunashi, “Amma kai dai Jawaad anyi shaiɗanin yaro, a gidan ubanwa nake da amsar? Ni dama tun jiya da akace an nemeka an rasa nasan kaine shaiɗanin daya dace a nema dukka
Billyn Abdul:
Page 25
.............Na daɗe banji irin wannan matsanancin bugun zuciyarba idan na samu kusanci dashi.
Tunda Nabeelah ta sanar da shigowarsa duk sai na nema nutsuwata na rasa, farfesun da Ummah ma ta tsareni naci sai naji ya fitarmin a rai, ƙasa-ƙasa nake kallon ƙofar ta gefen ido harya shigo da sallama, Sanye yake cikin ƙananun kayan nasa na fama, sai dai sun masa ƙyau kamar ko yaushe. Da hannu yake amsama kowa sannun da yake masa saboda waya yakeyi. Ummah ta tura masa kujerar da take zaune a kai ita kuma ta koma kusa dani a bakin gado.
Gaba ɗaya na kasa cigaba da shan farfesun har sai da Ummah taimin magana, “Saifa kin cinye abincin nan tas dota, garama ki dage kafin nasa a riƙeminke namiki ɗura”. Murmushi nai ina satar kallon boss da ƙamshin turarensa ya addabi hancinanmu, kasancewar turaren maza yafi na mata ƙarfi duk sai ya danne namu. A bazata muka haɗa ido, saurin janye nawa nayi dan banyi tunanin kallona yakeba. Farfesun na cigaba da tsakura kaɗan-kaɗan, har yanzu inajin idanunsa na yawo a kaina ko kunyar su Ummah bayaji.
Kusan mintuna biyar ya ɗauka kafin ya ajiye wayar yana faɗin, “Am sorry Ummana nazo ina waya”. Murmushi Ummah tai masa, tace, “Babu komai Son”. Guntun murmushi yayi yana mai risinar da kansa ya gaisheta ita da Mama, kafin ya ɗorama mama da godiya. Mama tace, “Babu komai Jawaad, ai yima kaine, Bilkisu ta cancanci ai mata abindama yafi haka dan yarinyar kirkice mai tarbiyya, mu saidai muce ALLAH ya sanya alkairi a wannan al'amari ya kuma baku zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba”.
Gaba ɗaya ban fahimci kalaman mamaba, dan dama Nabeelah ta shigo ɗazu tana cemin amaryar yayansu, kallonsa naɗan sata sai naga ya amsa da “Amin” akan laɓɓansa. Tunanin ko da aunty Shahudah aka ɗaura masa aurene yasa naɗanji nutsuwa. Ganin ya gama gaisawa da aunty Batool nima nace, “Ina kwana sir”.
Amsamin yay da “Lafiya, ya jikin naki?”. “Alhmdllh naji sauƙi”. Bai sake cemin komaiba ya juya sukai magana da Ummah, sai naga sun miƙe sun fita. Numfashi na sauke a hankali ina rumtse idona, dan fitar tasa yasa naji kamar an saukemin kaya. Babu abinda nake buƙata a halin yanzu kamar ƙarin bayani akan abinda ya faru jiya tsakanina da ƴan gidanmu, banga kowa a cikinsu ba kuma yau tunda na farka, sannan kuma miya faru har aunty Shahudah ta nemi jimin ciwo su aunty Aamilah kuma sukaimin wannan bugun da gashi ya kaini da kwana a asibiti?........
Ring ɗin wayatane da Ummie ta kawo ɗazun ya katsemin tunani, Nabeelah dake kusa da wayar ta miƙomin tana ƴar dariya, “Matar Yayanmu waye kuma masarauta?”. Wayar na amsa dan karta tsinke batare dana bata amsaba, bayan mun gaisa daga can Amaturrahman ke tambayata a ɗakin da nake?. Mamaki ne ya kamani sosai, ta yaya akai sukasan banda lafiya to? Kodai jiya sunzo ana wannan rikicin da bansan tshensa ba? Tunanin ƙila Ummie ce ta sanar musu ya sakani amsa mata da cewar bara na turo a shigo dasu. Da ga haka muka ajiye wayar, Nabeelah na kalla cikin marairaicewa nace, “Sorry dear, dan ALLAH ki shigo da baƙi wai suna waje”. Cikin dariya tace, “Karki damu matar yayanmu, girmankine ai”. Kasa haƙuri nayi nace mata, “Wai nikam wannan sunan daga ina haka?”. Sosai ta kwashe da dariya tana nufar hanyar fita da faɗin, “A wannan ba hurumina bane, yayanmu zai baki bayani”.
Aunty Batool ce tace, “Fitsararriya ALLAH yasa ya jiki dai”. “Ba amin ba” ta faɗa tana ficewa fuska a kumbure.
Murmushi mukai ni da mama, danni taɓarar Nabeelah dariya take bani, na lura gatane kawai yay mata yawa, ga uwa ga uba ga yayu ga dangi gata auta kuma. Mintuna baifi goma ba sai ga Nabeelah ta shigo dasu Amaturrahman bakinta fal magana da ganin jama'ar kamar jinin sarauta, dan tare suke da hadimai mata uku tare da wani dattijo, sai hadimai maza suma guda biyu.
Tun a waje Jawaad da Ummah dake zaune suna magana akan yanda za'ai da bilkisu kafin lokacin tarewar sukaga Nabeelah dasu Amaturrahman, cike da mamaki suka bisu da kallo, ganin da gaske ɗakin da bily take suka shiga yasasu tasowa suka biyo bayansu.
A waje suka iske hadiman su duka biyar, basuce dasu komaiba suka sh
iga.
Amaturrahman na zaune a bakin gadon da babu kowa a kai tare da aunty Batool, Marwah tsaye kusa da mama dake a ɗayar farar kujerar ta wancan gadon. sai dattijon kuma a kujerar da Jawaad ya tashi, , sai Safah data ɗane gadon kusa da bily tana taɓa kumburin fuskarta kamar zatai kuka, Bilkisu dai murmushi take mata, dan har cikin ranta takejin ƙaunar yarinyar da wannan shine haɗuwarsu ta biyu.
Jawaad ya ƙaraso suka gaisa da dattijon cikin mutuntawa, fuskar dattijo da murmushi yace, “Ina fatan kaine mijin nata?”.
Wani irin muguwar bugawa ƙirjina yayi, babu shiri na zubama boss ido dan naji amsar da zai bada, saiko naji yace, “Eh nine ranka ya daɗe”. Idanun mamaki na zaro dan nama manta akwai mutane a ɗakin, wata ƴar harara naga ya zubamin ya ɗauke kansa, yayinda shi kuma dattijon ke faɗin yazo zasuyi magana a waje. Binsa yay suka fita. Cikin dawo dani hankalina Safah tace, “Aunty B mijinki mai ƙyau, zaki yarda na zauna gidanku?”. Dariya duk ƴan ɗakin sukayi, bandani dana kasa koda motsi, sai ɗan kaɗama Safah kai nayi kaɗan dan nikaɗai nasan a kalar ruɗanin da nake ciki. Buɗe ƙofar da aka sakeyine yasa duk muka kalli can, shine ya leƙo yay kiran mama da Ummah.
Suna fita naji hawaye sun silalomin, da sauri nai ƙoƙarin gogewa dan banason kowa ya gani, sai dai na makaro dan Safah tarigada ta gani, da sauri tace, “Aunty B miyasaki kuka?”. “Ba kuka nakeba Safah, abune ya shigarmin ido” nai maganar da sauri. Tace, “Aunty B wai kema kina ɗaukata ƴar yarinyane? Nafasan kuka”. Tsawa Amaturrahman ta daka mata da faɗin, “Safah wai miye haka? Ke duk inda kika zauna saikin takurama mutane ne?........” Aunty Batool ce tai saurin katse Amaturrahman ɗin da faɗin, “Minene abin takura anan ɗin? Ai kulawama take bata”.
Marwah datun ɗazun bayan gaisuwa bata sake maganaba ta harari Safah ɗin da faɗin, “Aunty bakin yarinyarnan ne kamar bai gasuba”. Itama Safah ɗin harar Marwah tayi, tace, “Halan tarene ba'a gasa manaba, manya na magana kina wani tsoma musu baki mtsoww!”. Ƙwafa Marwah tai ta ɗauke kanta bata sake maganaba. Nai murmushi da riƙo hanun Safah nace, “A'a banda faɗa to, Marwah kema zo”. Babu musu ta bufoni, na kamo hanunta na zauna da ita ɗayan ɓangaren itama suka sakani tsakkiya.
A waje kuwa dattijo ya miƙama Jawaad takarda yana faɗin, “Saƙone daga Sarauniyar gagara badau, tace na miƙa wannan takardar ga mijin Bilkisu Adam makaho, ka karanta sannan ka bada amsar da za'a koma mata dashi”. Cike da mamaki Jawaad ya amshi takardar dake nannaɗe an ɗaureta da zare ruwan gwal, yace, “Sarauniyar gagara badau kuma? Ni kaina ya sake kullewa”. Dattijo dai baice komaiba sai murmushi da yayi. Jawaad ya buɗe takarda tareda karantawa a fili domin Ummah da Mama suji abinda ta ƙunsa.
Saida yakai har ƙarshe sannan suka shiga kallon-kallo, dan tayi bayanine a taƙaice gameda sanin Bilkisu da sukai har zuwan su Amaturrahman jiya da sukai tsozali da ruguntsumin da ya faru, a ƙarshe ta nuna buƙatar ganin shi Jawaad a yau zuwa masarauta domin suyi magana.
Jawaad ya kasa cewa komai, sai kallon inda dattijon ya koma gefe danya basu damar tattaunawa yayi, mamace ta katsesa da faɗin, “Jawaad nikam ina ganin kaje ɗin sai kaji minene takeson ji ɗin”. A sanyaye Jawaad yace, “Shikenan Mama zanje, bara na kira Alhaji babba shima na sanar masa”. “Hakan yayi” cewar mama, Ummah dai tama kasa cewa komai dan mamaki, saida mama tace, “Hajiya Mariya bakice komaiba”. Murmushi Ummah tayi, tace, “Abinne aini ya ɗauremin kai, daga tsintar Cards sai kusanci har irin haka ya shigo? Lamarin manyan nanne baka musu gaggawa, amma nima nagoyi bayan maganarki akan yajeɗin sai muji mitakeson su tattauna ɗin”. shidai Jawaad gefe ya koma yayma Alhaji baba bayani ta waya, shi kansa saida ya jinjina abin a ransa, kafin yace to Jawaad ɗin ya jirasa gasunan zuwa asibitin shi dasu Dad zasu duba Bilkisu.
Ciki Ummah da mama suka koma akabar Jawaad tare da dattijo anan waje suna tsumayen zuwansu Alhaji baba.
★★★★★★★
Kasancewar su Alhaji baba a hanya suke lokacin da Jay ya kira sai gasu babu jimawa sun iso, gais
uwa sukai da dattijon da babu wanda yasan daga ina yake sai Alhaji baba, da ido yayma Jawaad nuni dasu jirashi. Jawaad ya ɗaga kansa alamar amsawa. Shikuma yabi bayansu Uncle Sulaiman ciki domin duba Bilkisu.
Dole su Ummah suka fito waje suka bama su Alhaji baba ɗakin dan yamusu kaɗan, Safah da Marwah kaɗai aka bari tare da Bilkisu daketa faman gaishesu kanta a duƙe, dan bata yarda ta kalli kowaba sai da Dad yake matsawa kusa da ita ya ɗago fuskarta yana duba kumburin daya fara sauka da jera mata kalamun ban haƙuri tamkar zai ari baki sannan ne ta ɗago tana ɗan murmushi. “Dan ALLAH Dad kabar damuwa, wlhy ni kawai na ɗauki hakan matsayin ƙaddara da kuskure kawai, kuma nama yafe musu”. Babu wanda bily bata birgeba da kalamanta, wata irin faɗuwar gabace ta riski Alhaji baba lokacin da yay tozali da fuskar Bilkisu, ya kafeta da ido ko ƙyaftawa bayayi, dukda kuwa a kumbure take kaɗan ta gefen haggu saboda duka hakan bai hanashi hango wani abu tattare da itaba. Sam yama daina fahimtar sauran maganar data biyo baya tsakanin Bily dasu Dad, haka kawai ya tafi wani bahagon tunani da shi kansa yasan akwai kuskure a cikinsa. Saurin ture abin yay a ransa suka fito, saida ya kuma waiwayawa ya kalli Bilkisu da batasan yanayiba sannan ya fice.
Dad wajen likita ya nufa dan yaji yaya ake ciki? Su Uncle Sulaiman kuma suka fita domin tafiya gida, a wajen su Jawaad suka bar Alhaji baba shima.
Takardar Jay ya bama Alhaji baba, bayan ya karanta ya kalli dattijon, “Ƙanina zance ko ɗana yaushene akesan ganin nasa?”. Dattijo yay murmuahi da faɗin, “Baba yanzuma zamu iya tafiya, dan zanbar yaran anan muje mu dawo”. Kallon Jay baba yayi, yace, “Shikenan kabisa Muhammad”. Jawaad ya kaɗa kansa da faɗin, “To baba, amma zan koma gida na canja kaya tukunna”. Alhaji baba yace, “Ato ai maganinku kenan, ƙiri-ƙiri kun ajiye suturar mutunci kun biyema ta yahudu, saboda irin haka muke muku faɗa akan kuna tunawa da naku suturar kuma, dan sune kayan da zakuje gaban ko wanene batare da kunji nauyin hakanba”. Shidai Jawaad baice komaiba, sai dattijon masarautane keta murmushi da faɗin, “Wannan gaskiyane baba”.
★★★★★★
Sosai nake a cikin ruɗani da neman mai min ƙarin bayani akan wannan rikiɗaɗɗen al'amari, ina Yah Qaseem ɗina ya shiga da har ake jinginani matsayin matar boss?, shin wai mike faruwa hakane ni bilkisu? Mizaisa aitamin magana a curkuɗe?, a rasa maimin bayanin dazan fahimta. Koda su Oga Hafiz ma sukazo dubani harda matansu, matan sai faman yimin addu'ar fatan alkairi suke da faɗin, wai boss ya dace da matar da suka dace da juna, hakama da Ummie ta dawo tare da ƴan gidansu Momynta da Dady sunata min addu'ar ALLAH yasa hakan shine mafi alkairi, musamman ma Daddyn Ummie danaga tsantsar farin cikin hakan a garesa har suka tafi. Amina ma da Yayansu sunzo sunyi nasu kalar farin cikin, hakama Ummah ƙarama da naji suna faɗi da yaranta da tazo, sai murna suke da kasancewata wai matar ɗan uwansu. ‘Oh ALLAH! wannn wane irin ruɗanine haka?; Ina ƴan gidanmu suke? Dad kawai na gani, amma ko Yah Qaseem ban ganiba, shin ina ya shigane??. Haka naita juya wannan tunanin a raina, yawan jama'a da keta shiga da fici ya hanani sakat ɗin dazan samu na tambaya. A gefe kuma inajin daɗin ganin nima ashe mai mutanece? Ashe inada gatan dazan kwanta ciwo har mutane irin haka suyita tururuwar dubani?. ban sake ganin boss ba har sai bayan sallar zuhur.
★★★★★★
A ɓangaren Jawaad kam kamar yanda ya roƙa alfarma ga dattijo saida suka biya ta gida ya shiga ya sauya kayansa da ɗanyar shadda fara tas da tasha ɗinkin zamani, yaukam hardasu hularsa zannah ainahin nutsatstsiyar saƙar barnawa ta asali sai ƙyalli take, duk wanda ya gansa yaga sabon ango dukda bai shiga daga cikiba😂, shi kansa dattijon tunda Jawaad yafito daga gate ɗin gidan kasa ɗauke ido yay daga kallonsa, a fili ya furta ‘Masha ALLAH ’. Drivern dake jan motarma bai iya ɗauke idanunsaba har Jawaad ya shigo.
Sun isa katafariyar masarauta mai daɗaɗɗen tarihi da gininta na ɗaya daga cikin manyan gine-ginen da ake lissafasu a sahun farko na yankin masarau
tun afirika baki ɗaya saboda ƙawatuwarsa da gini mai nagarta data samu, gashi a koda yaushe cikin sake fidda masa wasu tsare-tsaren akeyi masu matuƙar sake ƙawatata. Wannan shine zuwa na biyu da Jawaad yayi cikinta, dan sun taɓa zuwa gaisuwar salla wa sarki Sameer tare da tawagar Gwamna a shekaru uku kenan da suka shuɗe. Sai dai a wannan karon sosai yaga sabbin tsare-tsare da tarin cigaban da yafi na wancan lokacin, bayi sai zubewa suke suna gaisuwa a garesu saboda wanda suke tare, shi kansa Jawaad ɗin kallon wani jinin sarauta suke masa saboda kama yake dasu ta siffofi da dama.
Jawaad mutumne shi mai nutsuwa da aji, sanan yanada tsari, bai damu da abinda babu ruwansaba komai ƙawarsa da abubuwan kallon cikinsa, wannan halin nasa na yima abu kallon ko in kula yasa sam bai zama ya rikice wajen kalle-jalleba a masarautar dukda ta cancanci a tsaya ƙare mata kallo harda son yin hotunama a cikinta. Tafiyarsa yake kai tsaye tamkar ko yaushe a kuma ko ina ya tainci kansa, bajinta, nutsuwa, da tarin ƙasaita kawai zaka hanga a takun nasa, waɗanda basu da fahimta akan halayyarsa harma zasu iya haɗawa da Izza da girman kai, sai dai kuma sam ba haka baneba, tun asali haka ALLAH yayisa tamkar wani jinin mulki wajen girmama nutsuwa a dukkanin al'amuransa koda akwai ruɗarwa a cikinsu kuwa.
An saukesa a katafaren falo mai cike da abubuwan ƙawa da birgewa, cikin mintuna ƙalilan aka cika masa gabansa da kayan ciye-ciye da har yake tsogumi a ransa wai ‘Kamar wani mai cikin zani’ (😂kujifa daga abun arziƙi. Lol🤣)
Bai taɓa komaiba bayan ruwa a kayan da aka jibge masa, dan shi ba ko ina yake sakin jiki yaci abuba (Yau naga mai irin halin babana a iya fulako😍, ALLAH ya gafarta maka baba😥🙏🏻). Cikin nutsuwa yake ɗanbin falon da kallo da jinjina daular dake ciki tamkar babu talaka mai buƙatar abinci da rigar sawa da kuɗin magani a duniya, yaɗan taɓe baki yana gyara zamansa, sam shi fariyya bata birgesa, dukda kasancewarsa mutum mai tarin dukiya bai taɓa sha'awar yin abinda ya fice hankaliba a hidimar rayuwarsa, dai-dai da motar hawansa guda biyuce kacal a duniya, hakama suturar sakawarsa akwai adadin da yake ajiyewa, ya gwammace duk sanda zai ɗinka wasu kayan ko ya saya to ya fidda tsoffin ya bada kafin ya ajiye wasu, baya sha'awar tsube sutura a drawer harya mance randa ya sake maimaita wata.........
Tunaninsane ya katse saboda sallamar da akayi a ƙofar falon, ya amsa yana gyara zama da tsumewa cike da kame kai. Hadimai mata guda biyune suka shigo, cikin girmama suka gaidashi kafin su sanar masa zai iya tasowa gimbiya ta fito.
Kansa kawai ya iya jinjina musu, ya miƙe tare da jefa wayarsa cikin aljihu yabi bayansu. Ƙaramin falone madaidaici, sai daifa ya haɗu harma ya gaji da haɗuwar, Hamshaƙiyar mace mai cike da tarin kamala da kwarjini da bazata gaza shekaru arba'in da biyar ba a duniya tana zaune, sai ƙamshi da walwali take cikin alƙyabbar da kallo ɗaya zakai mata kasan an sayeta da kuɗaɗe masu daraja. Gimbiya Munaya Awwal fharok kenan, sarauniyar gagara badau mai lokaci da amfani da damarta tana damawa yanda ya kamata, matar sarki Sameer saifudden Abubakar adalin sarki mai mulkin dake tafiya da koyarwar addinin islama da zamani, cikakken sarki mai iko da ƙasaita, adali mai tarin ilimin addini dana zamani, wanda yasha gwagwarmayar rayuwa tunkan rayuwar tagama sanin shiɗin wanene.
Da hannu gimbiya munaya taima matashin saurayi Jawaad nuni da wajen zama, bata haifi kamarsaba, amma kuma ta girmesa a shekarun haihuwa. Cike da nutsuwarsa ya zauna, kafin ya risina cikin girmamawa ya shiga gaidata. Gimbiya munaya tai murmushi mai ƙayatarwa dan Jawaad ya birgeta ainun, daganinsa zakasan yajiƙu da tarbiyya tsaftatacciya. Cike da ƙasaita tace, “Kana lafiya?”.
Jawaad ya amsa da “Alhmdllh ranki ya daɗe”. Murmushin ta sakeyi, kafin ta cigaba da faɗin, “Kana tare da Uwargidan Sakin gagara badau Sameer Saifudden, nasan kana cikin ɗunbin mamakin kiran gaggawa da nai maka wanda ni kaina bansan dalilin hakanba, kawai dai ina danganta lamarinne da tsantsar ƙaunar danaga gudan jinina tanama wadda banmm
a taɓa ganiba mai suna Bilkisu da a jiya nake samun labarin an ɗaura maka aure da ita, hakan kuma yazo da rikicin da ita Bilkisun ke buƙatar taimako”.
Jin tayi shiru Jawaad ya jinjina mata kai, cike da girmamawa yace, “Hakane ranki ya daɗe”. “Idan ban shiga hurumin daba nawaba inasonjin wani abu koda zan iya bada gudunmawa ta, dan a yanda yarana suka bani labarin abinda ya faru da Bilkisu hakan ya matuƙar tsayamin a zuciya a daren jiya”.
Murmushi Jawaad yayi, dan haka kawai yaji ƙaunar gimbiya munaya har cikin ransa, batare da tunanin komaiba ya buɗe mata cikinsa gameda abinda ya faru akan auren nashi da Bilkisu. Shiru gimbiya munaya tai tana nazarin maganganun nasa kafin ta sauke numfashi, cike da ƙasaitarta tace, “Jawaad!, a ɗan guntun hangena na fahimci akwai matsala babba dai dake a ƙasa wadda kaima kanka kakeson bincikowa? Hakan ya birgeni, dan inason jarumin namiji mara tsoro mai ƙwazo tamkar mai martaba na, zan baka gudunmawa akan dukkanin shirinka ɗari bisa ɗari, dan bansan mi UBANGIJI ke nufi da wannan haɗin namuba ta dalilin Safah da kullum bakinta bai gajiyawa da ambaton Aunty B”.
“Godiya muke ranki ya daɗe da wannan karamci, ALLAH ya ƙara lafiya da nisan kwana mai amfani”. Murmushi gimbaya Munaya tai tana maijin daɗin karamarwar Jawaad a gareta, sannan ɗabi'unsa sunyi matuƙar birgeta, idan badan ya faɗaba babu yanda za'ai kai tunanin yafitone daga tsatson tsohon shugaban ƙasa Marigayi Abdul-aziz yusif tafida, adalin shugaba da su kansu masarautarsu tayi ƙyaƙyƙyawar alaƙa dashi a lokacin mulkinsa na shekara huɗu a gwamna ɗaya a shugaban ƙasa, a yanzu haka kuma dukkan kayan itatuwa da kaji dawasu abubuwan da suka shafi gona ana kawomusu shine daga gidan gonarsa......... Kauda tunanin nata tai Tace, “Shikenan Jawaad, yanzu mataki na farko da zamu farabi shine ina buƙatar Bilkisu ta dawo masarauta da zama, dan komawarta gidansu bazai haifar da ɗa mai idoba kodan dalilin ita tsohuwar matar taka da tsohon saurayinta da kuma mahaifiyarsu, zata zaunane na gajeran lokaci daganan zuwa bayan sallar kamar yanda kuka tsaida tarewarta, dan itama tana buƙatar ai mata auren gata tamkar kowane mace mai iyaye kodan hakan yazama izina ga masu irin halin Gwaggonka dake tunanin su kaɗaine a sama babu mai taddosu, inason susan babu wani bawa ƙasƙantacce sai wanda ya ƙasƙantar da kansa ga barin bautar ALLAH saboda son zuciya..............✍
Ina godiya gareku akan addu'oin da akaita zubami harda masu kira da masu turo saƙo, naji sauƙi Alhmdllh sai dai inajinran manyan ledojin kayan dubiya😆😋.
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻
0 comments:
Post a Comment