Page 36
.................Tabbas muryar iri ɗayace, kamanin ma ɗayane, sai dai wannan farine tas, shekarunsa kuma basu kai nasa ba, sannan muryarsa bata kai tasa kauriba, na sake lunshe idanu a hankali na sake buɗewa da tunanin kodai mafarki nake?, saukar goran ruwa a saman bakina ya sakani fahimtar komai yana faruwane a zahiri ba'a gaibun mafarki ba. Ruwan nasha sosai kozan samu sauƙin nauyin da ƙirjina yayi, matashiyar budurwar da bazamu wuce sa'anniba fara tas itama balarabiyar usul ta duƙa gabana tare da kamo hannuna cikin nata, ta narke fuska sosai tamkar zatai kuka, magana take cikin harshen larabcina da ban fahimta saboda tanada ɗan saurin baki, na kafeta da kallo, itakuma idanuntane kawai irin na Boss, amma kamaninta daban. Juyawa nai a hankali domin son ganin fuskar wadda nake a jikinata, sai akai sa'a itama niɗin take kallo. Wani irin faɗuwar gaba naji. Na lumshe idanu na sake buɗewa a kanta, kallona take babu ko ƙyaftawa itama tamkar mai ƙoƙarin gano wani abu akan fuskata.
A tare muka sauke ajiyar zuciya ni da ita, kafin nai yunƙurin tashi zaune tsigar jikina na wani irin tashi. Na sake kallon saurayin da sam hankalinsa baya kanmu yanata latsa waya abinsa, gabana ya sake faɗuwa dan kuwa yanda yake tsaye iri ɗayane da yanda Boss ke tsayuwarsa, sosai ruɗani ya sake bayyana a gareni, na kuma juyowa ga matar dattijuwa sosai mai tarin kamala, doguwar rigar jikinta mai adon fari tai masifar yima fatarta ƙyau, murmushi ta sakarmin, cikin harshen turanci tace, “Sannu, kiringa kula kinji?”. Nima murmushin nai mata na gyaɗa mata kaina. Miƙewa tai tsaye ta miƙomin lallausan hannunta da alamun girma ya bayyana a fatar, babu musu na miƙa mata nawa ta taimakamin na miƙe, budurwar ta miƙomin ƴar ƙaramar bag ɗina itama tana murmushin da sakemin sannu. Godiya nai musu, na juya zanbar wajan, taku biyu na juyo na sake kallonsu, sai naga suma duk niɗin suke kallo harda saurayin yanzuma, murmushi mukaima juna na sake juyawa na ciga da tafiya.
Naɗan ƙara juyawa na kallesu sai naga still suma dai idonsu na kaina har yanzun........
Riƙo hannuna da akai ya sakani saurin juyawa, lip ɗina daya bushe na ɗan lasa zuciyata na wata irin tsitstsinkewa.
Amaturrahman ta girgiza hanun Bilkisu data kula sam bata cikin hayyacinta, “Bily lafiya kuwa? Ina kika shiga munata nemanki?”.
Nannauyan numfashi na sake saukewa ina haɗiye abinda yaymin tsaye a maƙoshi tare da tattaro murmushin ƙarfin hali nace, “Babu komai Amaturrahman, kawai jinai inajin jiri shine naɗan samu waje na huta fa, inasu Safah?”. Cikin sauke ajiyar zuciya Amaturrahman tace, “Gasu can ke muketa nema dama mu wuce, muje ko”.
Hira suke tayi a motar amma nifa nakasa cewa ko uffan, abinda na gani ya kasa barin raina, shin da gaske dama akan samu mutum mai kama da wani koda basu da alaƙa kamar yanda ake faɗa? Wacece wannan mai kama da Boss haka? Shin mamansa ba rasuwa tayi ba dama kokuwa minene ke faruwa?... Da wannan tunanin a raina har muka iso gida, hankalin kowa nakan abinci.
Kowa na ƙoƙarin cin abincin da aka barbaje kala-kala domin farin cikin bikin salla amma bandani, kallonsu kawai nake tamkar wata sokuwa, Meenal dake kusa dani taɗan zungureni da hannu, “Wai nikam mike damunkine? Kodai kewar yayanmu kike ne?”. Harara na dalla mata nace, “Ashe...” dariya suka sanya min, shiru nai musu kamar bansan sunaiba.
A gaba ɗayan wannan yinin nayi sane zuciyata cike da tunanin waɗanan bayin ALLAH da ganinsu ya kasa barin raina, a dukkan motsina sai sun faɗomin a rai, munsha yawo sosai, an kaini wajaje daban-daban na tarihi da wajen hutawa, bamu dawo gidaba sai dare, a gajiye muke liɓis, dan haka wanka kawai mukai kowa ya nema makwancinsa.
Haƙurin dana kasayine ya sakani kallon Amaturrahman da keta lumshe idanun alamar barci nace, “Amaturrahman wai su Umm-Anum ɗin basu dawo daga ittiqafin bane?”. Kaɗan ta buɗe idanu ta kalleni ta maida ta lumshe tana murmushi, “Hajiyata kin ƙagarane a fara gyarama yayanmu ke ko? Kwantar da hankalinki nasan sun dawo, dan bama gidane shiyyasa bamu shigaba, Umm-Anum saita maidake
zinariya a idanun yayanmu saboda gyara”. Juya kwanciyata nai ina faɗin, “Masheranciya kawai, daga tambaya zakimin banzan fassara saida safe”. Ina jiyo ƴar dariyarta naƙi kulata, Meenal dama tana wankane.
★★★★★★★
Washe gari tunda safe saiga kira daga Ummu, bayan duk mun gaisa da ita tace a bani wayar. Daga can tace, “Yauwa ɗiyata ki shirya komai naki danke yau zaki koma wajen Aunty da zama, tun jiya da daddare ma taso shigowa ta ɗaukeki, ki nutsu ki kwantarmin da hankalinki ki fahimci dukkan abinda akeson ki fahimta kinji, kinga lokaci ya ƙure sosai, inason kidawo ƙasarnan da cikakken sunanki BILKEESU MAI GADON ZINARI ba Bilkisu kawai ba kinji”. Cike da jin nauyinta nace, “Insha ALLAHU Ummu zanyi duk yanda kikeso”. “Yauwa ƴar albarka ALLAH ya bada sa'a kinji, jibi su Amaturrahman zasu taho su saboda makaranta, ranar litinin su Safah zasu koma hutu”. Kamar zanyi kuka nace, “Wayyo Ummu ni kaɗai za'a bari anan kenan?”. Murmushi tayi har ina jiyo sautinsa, tace, “Ohni Munaya, anya kuwa randa zan miƙaki gidan miji baza'a sha daruba? Karki damu itama Anum ɗinta zakuyi sa'anni, nasan zata ɗauke miki kewarsu, kuma kedama zaki maida hankali ga abinda za'ai miki ai baƙya buƙatarsu Amaturrahman kusa dake, koma sun zauna na ganin juna zakuyiba, inason suzo domin shirye-shiye, ki basu duka numbers ɗin ƙawayenki karki manta”. Godiya nai mata mukai sallama.
Kamar yanda ta umarceni haka na shirya dukkan abinda yake nawa, duk ji nake babu daɗi, banso ace batare zamu koma dasu Safah ba, to amma yaya zanyi tunda haka Ummu ta tsara.
Atare muka fito cikin shiga ta kamala, Marwah jaye da ɗan ƙaramin akwatina. Gida baifi huɗu bane a tsakaninsu, dan haka tafiyar mintuna ƙalilan muka iso gidan, Aunty Mahfuzah tai knocking haɗaɗɗiyar ƙofar falon, babu jimawa akazo aka buɗe mana, wani irin tsammm naji jikina ya bada saboda cin karo da fuskar budurwar jiya. Ta rungume Aunty Mahfuzah tana magana cikin harshen larabci, kafin ta saketa ta rungume Amaturrahman da Meenal cikin tsalle irin na nayi kewarku, sai dariya suke da faɗin yanda sukai missing ɗin junansu. Ta sake rungume su Safah suma kafin ta juyi gareni, idanu taɗan waro tana nunani da faɗin, “Lah kece?” murmushi nai mata kawai dan nikaɗai nasan mi nakeji, rungumeni tayi nima, sannan muka ƙarasa falon daya gama jin kayan more rayuwa, ga sanyin AC da wani ƙamshi mai kashe zuciya, tuni ɗan gumin da mukai harya tsane, labarin haɗuwarmu ta jiya taketa bamasu Amaturrahman saboda tambayar da sukai na ina muka san juna?.
Fitowar matar gidan ya sakasu Safah miƙewa gaba ɗayansu harsu Amaturrahman sukai kanta suka rungume, ba kowa bace face matar jiya data taimakeni, bayan sun zauna ta gaisa da aunty Mahfuzah cikin salon gaisuwar larabawa, nima gaidata nai kamar yanda na iya a nawa al'adar da tarbiyyar, kallon mamaki tai min dan da'alama sai yanzune ta lura dani ma, da turanci take tambayata wai dama tare muke dasu Safah?. Amaturrahman ce ta bata amsar da take buƙata harma da ƙara mata wadda bata tambayaba. Murmushi taita saki da ƙaremin kallon da kowa yaketa mamakinsa, tana ta maimaita sunana tamkar karatu a bakinta, bansaniba daɗi yaymatane kokuwa yaya oho, dan nasan suna Bilkisu dai sunane sananne da zaka iya jinsa a kowacce duniyar musulmai balle tace yaune ta fara jinsa sabo.
Ranar dai anan muka yini, har yamma su Amaturrahman basu koma can gidanba, danni dai an tabbatarmin da nazo kenan bazan koma canba, acewartama a daren zata kaini can makarantar da Ummu ta faɗamin. Banga saurayin nanba sai yamma lis ya shigo sanye da farar jallabiya sol da mayafi irin wanda larabawa kansa akai su saka baƙin abunnan a sama tamkar gammo, fara'ar da bangansa da itaba jiya sai gata yau a fuskarsa yanamasu Amaturrahman magana da kulawa kamar yanda suma suke masa, shima dai sai da ya nuna mamakin sake ganin nawa anan, su Amaturrahman da basa hutawa sukai masa bayani dai-dai fahimtarsa, shima dai murmushin yayta saki kafin ya nufi ɗakinsa wai zaiyi wanka.
Ban tashi shiga damuwaba sai da su Amaturrahman zasu koma gidan aunty Mahfuzah su barni anan, hakan kuma na
nufin munyi sallama kenan dasu, sai naji ƙwalla ta cikamin idanu, sabo kenan turken wawa. Suma kansu na lura basuso hakanba, amma sai suketa dariyar ƙaramin ƙwarin gwiwa da tsokana. Haka mukai musu rakkiya har gidan sannan muka sake dawowa ni da Anwar da Anum mai shegen surutu, yanayin rawan kanta sai yakemin kamanceceniya da Nabeelah, gata da saurin magana saina nutsu sosai nake fahimtar magana idan tayi, dama dai maganar tamu sai da turanci. A falo muka sake zama, cikin son fidda abinda kecin raina na tambayi Anum da Anuwar da naga shima ya saki jiki dani yanzu kosun taɓa zuwa ƙasarmu?. Anuwar ne kaɗai yace ya taɓa zuwa shima sau ɗaya tare dasu Abdur-rahman, sunzo hajji wata shekara zasu koma ya bisu sukaje tare, satinsa biyu acan ya dawo daga nan bai sake komawaba har yanzun, amma yanada burin sake zuwa saboda ƙasar tai masa daɗi sosai.
Murmushin jin daɗi nayi sai dai a ƙasan raina ina mamakin to Mamansu fa? Ita bata taɓa kaisu wajen nata danginba kenan kokuwa?, da ƙyar na ture tunanin a raina muka cigaba da hira har sanda Umm-Anum ta fito cikin shiri, sanin inda zamuje ya saka duk muka miƙe, tana gaba muna biye da ita har inda Anuwar ya ajiye motar da zamu fita. Ni da ita baya muka shiga, Anuwar da Anum na gaba, dukda darene garin zirga-zirga aketayi tamkar rana, gashi ko'ina ƙwanyar da wuta abin birgewa.
Mun iso wani haɗaɗɗen gini babba da nake ƙyautata zaton makarantarce, Anuwar yay fakin duk muka fito, jin kamar ana kallona yasa na ɗago, Anuwar na kama idanunsa tsaye a kaina ƙyam, saida gabana ya faɗin dan wlhy sai naga tamkar Boss, murmushi yaymin. ɗauke kaina nai batare dana maida masa murtani ba, Umm-Anum dana fahimci tana kallonmu ta hararesa da kama hannuna mukai gaba. Ina jiyo dariyarsa shi da Anum, sai dai banajin mi suke faɗa cikin harshen larabci. Gaskiya ina sake jinjina wannan tsananin kama a cikin raina, kai gaskiya inason sanin wani abu dangane da mutanen nan, wannan kamar ta wuce kama kawai, anya kuwa babu wata alaƙa tsakanin...........
Shigarmu wajenne ya katsemin tunanina, Bansan yanda zan fasalta muku haɗuwar wannan makarantaba da tsarinta, na bama kowa dama ya ƙiyasta a cikin ransa kawai, dan idan nace zan lissafo komai shafin yau da gobe duk anan zamu ƙare. Tuni na zama baƙauya wajen kallon abubuwan birgewa, to lallai da ace munada irin waɗanan makarantun da mace-macen aure ya ragu muma a yankunanmu, da ansamu sauƙin rikin aurarraki a gidajenmu. Sashe na musamman aka buɗe mana mai madaidaicin falo guda da ɗakuna biyu a ciki.
Fuskar Umm-Anum ɗauke da murmushi ta kalleni, “Ɗiyata anan zaki zauna, dan da kaina zan miki aikinnan saboda ƙurewar lokaci, ga mamanki ɗinan sotake ta ganki tamkar zinare”. Murmushi nai mata kaina a ƙasa dan haka kawai nakejin nauyinta, nai mata godiya tare da addu'ar fatan alkairi. Batace komaiba sai murmushinta dake kasheni taketa sakarmin.
Ɗaya daga cikin ɗakunan muka shiga, kayayyakine ajiye da ban fahimci kona mineneba, ta umarceni dana cire kayana gaba ɗaya na shiga wani madaidaicin kwami dake cike da ruwa da bazamu kirashi normal ruwa ba, ita kuma ta fita. Dukkanin yanda ta umarceni nayi haka nayi babu musu, inayi ina ɗan waige-waige tamkar mai tsoron wani ya shigo, saida na cire komaina kafin na fara saka ƙafa cikin kwamin, ajiyar zuciya na sauke a hankali saboda ɗan ɗumi-ɗumin ruwan mai warware gajiyar jiki, na ida saka ɗayar ƙafar sannan na shige gaba ɗayana, sihirtaccen ƙamshin da ruwan keyine ya sakani lumshe idanu ina karanto addu'ar godiya ga ALLAH da ni'imominsa masu yalwata ta fuskoki da dama ga ɗan adam. Sai da nai kusan mintuna uku da zama sannan ta shigo da sallama, ta canja kayanta da wata doguwar riga mai kama da leda, hannayenta sanye da safar hannu ta leda itama, murmushi taimin ta tako inda nake. Ɗan kwalina daban cireba ta zame daga kaina, ta warware gashina da Alhmdllh yanzu ya cika sosai kuma yanada tsayi gwargwado saboda kulawar da naita bashi bisa koyarwar su Ummie tun muna boarding, wani ɗumi mai daɗi naji ya ratsa kan nawa, hakan yasani kallon madubin dake gabana da nake iya hango kaina da ita kanta.
Tace, “A cikin ruwannan zaki kwana, babu abinda zai sameki insha ALLAH karkiji tsoro, ruwane mai ɗauke da sirrika kala-kala da duk macen da aka gyara dasu dolene mijinta yasan ta isa mace, sirrikane na ƙamshi masu daraja a jikin ƴa mace, ƙa'idar makarantarmu watanni ukune domin mace ta samu damar koyon abubuwa masu yawa, ba sirrin gyaran jiki bane kawai mace tafi buƙata a rayuwar aure ɗiyata, zakiga wata macen komai ta iya ta kuma ƙware, amma idan batasan yanda zataima miji maganaba kawai sai ya rusa mata komai, dan wani namijin shi abinda ke ƙololuwar birgesa ga mace shine iya magana, wani kuma a kallo kawai zaki gama dashi, wani tafiya, wani girki, wani ƙamshi, wani shagwaɓa, wani kwalliya, wani kwanciya. Karki sakama ranki cewa tarayya da miji a gado shine kawai farin cikin aure ko shikaɗaine auren, hakan kuskurene, wani namijin ƙanƙanin abun da kika raina shike sakashi farin ciki. Karkiyi tunanin gyara kanki yana nufin kin mallaki namiji ya zama naki ke kaɗaine, macen data isa mace bata shakkar zama da kishiya ɗiyata, dan wani lokacin zama da kishiya nasake bayyana darajar macene a wajen mijinta. Karkuma kiyi tunanin babu wata mace data isa raɓar mijinki dan yana sonki ko kin iya komai, wani namijin badan baya sonki yake miki kishiyaba ko yake budurwa, a'a halayyar san mace fiye da ɗaya a jinin maza yake, ko bazasu ƙara aureba saisun kalla. kizama mai gyara aurenki ta kowanne ɓangare, idan nace kowane ɓangare ina nufin kowanne fanni hatta da ƴan uwansa da duk abinda ya shafesa. Inason ki cire komai a cikin ranki ki nutsu ki bani dukkanin hankalinki a kwanakinan goma sha biyu da zamuyi tare, sonake komai na cikinsa ya zama tamkar rubutu bisa dutse a cikin ƙwaƙwalwarki, ki ɗaukeni tamkar mahaifiyarki, kuma ƙawarki aminiya wadda zaki iya magana kowacce iri da ita batare da kinji kunya ba, inhar kika riƙe duk abinda zaki koya a kwanakinan ina mai tabbatar miki bazaki taɓa goguwa a zuciyat mijinki ba koda zai auri mata uku ku zama huɗu bayan ke”.
Idona a risine na ɗaga mata kai alamar to, inajiyo sautun murmushinta itama. Abu ta fara shafamin a fuska tana cigaba da min magana cikin nutsuwa, sosai kunya ta lulluɓeni, dan abubuwane masu matuƙar nauyi a gareni take faɗa a buɗe, ta haɗe fuska a yanzu babu wasa tattare da ita ko kaɗan. Saida ta gama tsaf sannan ta fita suka sake dawowa da wata mata. Matar ta nunamin da faɗin, “zata zauna dake anan, ni zan koma gida sai da safe idan ALLAH ya kaimu zan dawo”. Kaina na jinjina mata dan ta hanani magana tunda ta shafamin abin fuskarnan.
Duk yanda zan baku labarin abinda ya gudana a kwanakinan da wahala ku iya fahimtata, abubuwan dana koya kam ba'a magana, sam Umm-Anum bata wasa dani idan akazo ɓangaren abinda zan iya jin kunyarta balle naga fuskar yin sakaci da abinda ake koyamin, tsaye take kaina ɗari bisa ɗari, komai buɗemin shi take babu hijjabi, aduk lokacin da takemin bayani aka abinda yafi ƙarfin kaina tamke fuska take tamau babu wasa, kai jama'a hatta da salon tafiya ba'a barniba sai da aka koyan, komai a tsare yake. Matar da take bari ta kwana dani kasa haƙuri tayi ranar dai take tambayata wai kodai ni ƴar uwar Umm-Anum ce? Dan ita yanda take ganin tanamin ya ninka yanda takema ɗalibanta fiye da zato. An kawoni ɗaki na musamman, sannan komai ba'a sakani cikin ɗalibai ni kaɗai ake koyamashi a nutse, daɗin daɗawa da kanta take min komai bata yadda kowa yayminba sai abubuwan da ba'a rasaba, dan takance kowa a rayuwa da irin basirar da ALLAH yay masa, abinda suma sauran malaman makarantar suke koyamin zai amfanar dani ta fannoni da dama. Murmushi nayi nidai bance komaiba, dan nikaɗai nasan mi nakeji game da matar nan, ita kanta lokuta da dama nakan kamata ta shagala da kallona, kallo maiban mamaki, kallo irin na shagala da zurfi ason tunano wani abu, idan tai irin wannan zurfin kuma zakaga daga ƙarshe ta dafe kanta tamkar zata fita cikin hayyacinta. Akwai randa naga kallon har yaso yimin yawa, sannan ni kaina yanda takemin ɗin nasan ba kamar yanda takema kowa baneba, tana sakin jiki dani fiye da hasashen mai hasashe. Akwai randa tazo tana koyamin
girki sai muke ɗan hira kaɗan-kaɗan, cikin dabara nake tambayarta ko zasuje ƙasarmu nan kusa?. Shiru tai bata bani amsaba, na kasa daurewa dai na sake mata tambayar cike da ladabi. Yanda ta juyo ta kalleni fuska a haɗe saida naso firgita. Kaina na duƙar ƙasa ina faɗin, “Kiyi haƙuri dan ALLAH Ummu, bansan tambayar zata ɓata ranki ba”. Sautin murmushinta na jiyo, hakan yasa na ɗan ɗago na kalleta, ta ajiye cokalin hannunta tazo ta kama hannayena, murya a sanyaye tace, “Ɗiyata ba laifi kikayiminba, ƙasar takuma ni ban taɓa zuwantaba ai, duk amintakar dakika gani tsakanina da ƙanwata Gimbiya Munaya ban taɓa ziyartarta ba, sai dai ita idan tazo nan mu haɗu, duk lokacin danai yunƙurin zuwa nakan tsinci kainane a wani mummunan hali da baida fassara”. Tana gama faɗa ta saki hannuna ta juyamin baya, aikin da mukeyi ta cigaba dayi batare da ta sake min maganarba.
Ajiyar zuciya na ɗan sauke hawaye na ziraromin, haka kawai yanda tayi maganar sai naji abun daban, to amma ai Ummu ta sanarmin itaɗin ƴar ƙasarmu ce, sanadin neman magani ya kawota nan hartai aure, itakuma gashi yanzun tace bama ta taɓa zuwa canba, anya kuwa babu wani sirrin dake ɓoye?.......
Ajiyar zuciya na sauke da saurin kallonta jin ta taɓanu, tace, “Kinama fahimtar abinda nakeyi kuwa?”. Da sauri na ɗaga mata kai alamar eh na tattara hankalina gareta baki ɗaya.
____________________________
A ɓangaren Jawaad ma dai shirye-shirye sun kankama, an gama gyaran gida tsaf, ya canja kamanni gaba ɗaya tamkar bashiba, amarya kawai yake jira ta shigo cikinsa. Gaba ɗaya a tsakaninan a busy yake matuƙa, ga aiki ga shirye-shiryen biki dasu Jabeer ketayi naban mamaki, dan gayya suke ta gaske da gayya tamkar wannan shine auren farko da Jawaad ɗin zaiyi. Shidai ya zuba musu idone kawai yana kallon ikon ALLAH, dan dayay magana ca sukai babu ruwansa, kawai dai yama shirya dan bai isa cewa bazaije wajen abinda suke shiryawanba ehe. Bai sake musu maganarba kuwa ya cigaba da nasa harkokin, maganar kayan da za'a saka a gidan kuwa gimbiya Munaya tace Takawa yace zaiyi komai, kayan kicin kuwa itace zatayi. Da yay mata maganar lefe tace masa ya dakata, zasu nema Dady suyi magana, sai ana saura kwana biyu tarewar za'a kaisu can gidan Dad ɗin dan sune sukafi cancanta da amsar lefen, koyayane zasu bashi matsayinsa na uba kodan ɗawainiyar da yay da Bilkisun. Jawaad baice komaiba shi dai sai ALLAH ya kaimu.
A yau tunda safe Su Amaturrahman suka shirya yima Mami (Munubiya) rakkiya gidan kamar yanda Gimbiya da Takawa suka buƙata, zataje su haɗu da kamfanin da zasu shirya gidan. bayan sun duba saisu zaɓa mata kalar data dace a tsara komai yanda ya dace..............✍
Bara dai na baku hakanan, inata ƙoƙarin typing ɗin bayan tafiyar baƙi amma kiraye-kirayen waya ya hanani nutsuwar yi da yawa, takaima harna daina ɗaga wayoyin mutane wlhy🤦🏻😑😓.Bilyn Abdull 📚:
Page 36
.................Tabbas muryar iri ɗayace, kamanin ma ɗayane, sai dai wannan farine tas, shekarunsa kuma basu kai nasa ba, sannan muryarsa bata kai tasa kauriba, na sake lunshe idanu a hankali na sake buɗewa da tunanin kodai mafarki nake?, saukar goran ruwa a saman bakina ya sakani fahimtar komai yana faruwane a zahiri ba'a gaibun mafarki ba. Ruwan nasha sosai kozan samu sauƙin nauyin da ƙirjina yayi, matashiyar budurwar da bazamu wuce sa'anniba fara tas itama balarabiyar usul ta duƙa gabana tare da kamo hannuna cikin nata, ta narke fuska sosai tamkar zatai kuka, magana take cikin harshen larabcina da ban fahimta saboda tanada ɗan saurin baki, na kafeta da kallo, itakuma idanuntane kawai irin na Boss, amma kamaninta daban. Juyawa nai a hankali domin son ganin fuskar wadda nake a jikinata, sai akai sa'a itama niɗin take kallo. Wani irin faɗuwar gaba naji. Na lumshe idanu na sake buɗewa a kanta, kallona take babu ko ƙyaftawa itama tamkar mai ƙoƙarin gano wani abu akan fuskata.
A tare muka sauke ajiyar zuciya ni da ita, kafin nai yunƙurin tashi zaune tsigar jikina na wani irin tashi. Na sake kallon saurayin da sam hankalinsa baya kanmu yanata latsa waya abinsa, gabana ya sake faɗuwa dan kuwa yanda yake tsaye iri ɗayane da yanda Boss ke tsayuwarsa, sosai ruɗani ya sake bayyana a gareni, na kuma juyowa ga matar dattijuwa sosai mai tarin kamala, doguwar rigar jikinta mai adon fari tai masifar yima fatarta ƙyau, murmushi ta sakarmin, cikin harshen turanci tace, “Sannu, kiringa kula kinji?”. Nima murmushin nai mata na gyaɗa mata kaina. Miƙewa tai tsaye ta miƙomin lallausan hannunta da alamun girma ya bayyana a fatar, babu musu na miƙa mata nawa ta taimakamin na miƙe, budurwar ta miƙomin ƴar ƙaramar bag ɗina itama tana murmushin da sakemin sannu. Godiya nai musu, na juya zanbar wajan, taku biyu na juyo na sake kallonsu, sai naga suma duk niɗin suke kallo harda saurayin yanzuma, murmushi mukaima juna na sake juyawa na ciga da tafiya.
Naɗan ƙara juyawa na kallesu sai naga still suma dai idonsu na kaina har yanzun........
Riƙo hannuna da akai ya sakani saurin juyawa, lip ɗina daya bushe na ɗan lasa zuciyata na wata irin tsitstsinkewa.
Amaturrahman ta girgiza hanun Bilkisu data kula sam bata cikin hayyacinta, “Bily lafiya kuwa? Ina kika shiga munata nemanki?”.
Nannauyan numfashi na sake saukewa ina haɗiye abinda yaymin tsaye a maƙoshi tare da tattaro murmushin ƙarfin hali nace, “Babu komai Amaturrahman, kawai jinai inajin jiri shine naɗan samu waje na huta fa, inasu Safah?”. Cikin sauke ajiyar zuciya Amaturrahman tace, “Gasu can ke muketa nema dama mu wuce, muje ko”.
Hira suke tayi a motar amma nifa nakasa cewa ko uffan, abinda na gani ya kasa barin raina, shin da gaske dama akan samu mutum mai kama da wani koda basu da alaƙa kamar yanda ake faɗa? Wacece wannan mai kama da Boss haka? Shin mamansa ba rasuwa tayi ba dama kokuwa minene ke faruwa?... Da wannan tunanin a raina har muka iso gida, hankalin kowa nakan abinci.
Kowa na ƙoƙarin cin abincin da aka barbaje kala-kala domin farin cikin bikin salla amma bandani, kallonsu kawai nake tamkar wata sokuwa, Meenal dake kusa dani taɗan zungureni da hannu, “Wai nikam mike damunkine? Kodai kewar yayanmu kike ne?”. Harara na dalla mata nace, “Ashe...” dariya suka sanya min, shiru nai musu kamar bansan sunaiba.
A gaba ɗayan wannan yinin nayi sane zuciyata cike da tunanin waɗanan bayin ALLAH da ganinsu ya kasa barin raina, a dukkan motsina sai sun faɗomin a rai, munsha yawo sosai, an kaini wajaje daban-daban na tarihi da wajen hutawa, bamu dawo gidaba sai dare, a gajiye muke liɓis, dan haka wanka kawai mukai kowa ya nema makwancinsa.
Haƙurin dana kasayine ya sakani kallon Amaturrahman da keta lumshe idanun alamar barci nace, “Amaturrahman wai su Umm-Anum ɗin basu dawo daga ittiqafin bane?”. Kaɗan ta buɗe idanu ta kalleni ta maida ta lumshe tana murmushi, “Hajiyata kin ƙagarane a fara gyarama yayanmu ke ko? Kwantar da hankalinki nasan sun dawo, dan bama gidane shiyyasa bamu shigaba, Umm-Anum saita maidake
zinariya a idanun yayanmu saboda gyara”. Juya kwanciyata nai ina faɗin, “Masheranciya kawai, daga tambaya zakimin banzan fassara saida safe”. Ina jiyo ƴar dariyarta naƙi kulata, Meenal dama tana wankane.
★★★★★★★
Washe gari tunda safe saiga kira daga Ummu, bayan duk mun gaisa da ita tace a bani wayar. Daga can tace, “Yauwa ɗiyata ki shirya komai naki danke yau zaki koma wajen Aunty da zama, tun jiya da daddare ma taso shigowa ta ɗaukeki, ki nutsu ki kwantarmin da hankalinki ki fahimci dukkan abinda akeson ki fahimta kinji, kinga lokaci ya ƙure sosai, inason kidawo ƙasarnan da cikakken sunanki BILKEESU MAI GADON ZINARI ba Bilkisu kawai ba kinji”. Cike da jin nauyinta nace, “Insha ALLAHU Ummu zanyi duk yanda kikeso”. “Yauwa ƴar albarka ALLAH ya bada sa'a kinji, jibi su Amaturrahman zasu taho su saboda makaranta, ranar litinin su Safah zasu koma hutu”. Kamar zanyi kuka nace, “Wayyo Ummu ni kaɗai za'a bari anan kenan?”. Murmushi tayi har ina jiyo sautinsa, tace, “Ohni Munaya, anya kuwa randa zan miƙaki gidan miji baza'a sha daruba? Karki damu itama Anum ɗinta zakuyi sa'anni, nasan zata ɗauke miki kewarsu, kuma kedama zaki maida hankali ga abinda za'ai miki ai baƙya buƙatarsu Amaturrahman kusa dake, koma sun zauna na ganin juna zakuyiba, inason suzo domin shirye-shiye, ki basu duka numbers ɗin ƙawayenki karki manta”. Godiya nai mata mukai sallama.
Kamar yanda ta umarceni haka na shirya dukkan abinda yake nawa, duk ji nake babu daɗi, banso ace batare zamu koma dasu Safah ba, to amma yaya zanyi tunda haka Ummu ta tsara.
Atare muka fito cikin shiga ta kamala, Marwah jaye da ɗan ƙaramin akwatina. Gida baifi huɗu bane a tsakaninsu, dan haka tafiyar mintuna ƙalilan muka iso gidan, Aunty Mahfuzah tai knocking haɗaɗɗiyar ƙofar falon, babu jimawa akazo aka buɗe mana, wani irin tsammm naji jikina ya bada saboda cin karo da fuskar budurwar jiya. Ta rungume Aunty Mahfuzah tana magana cikin harshen larabci, kafin ta saketa ta rungume Amaturrahman da Meenal cikin tsalle irin na nayi kewarku, sai dariya suke da faɗin yanda sukai missing ɗin junansu. Ta sake rungume su Safah suma kafin ta juyi gareni, idanu taɗan waro tana nunani da faɗin, “Lah kece?” murmushi nai mata kawai dan nikaɗai nasan mi nakeji, rungumeni tayi nima, sannan muka ƙarasa falon daya gama jin kayan more rayuwa, ga sanyin AC da wani ƙamshi mai kashe zuciya, tuni ɗan gumin da mukai harya tsane, labarin haɗuwarmu ta jiya taketa bamasu Amaturrahman saboda tambayar da sukai na ina muka san juna?.
Fitowar matar gidan ya sakasu Safah miƙewa gaba ɗayansu harsu Amaturrahman sukai kanta suka rungume, ba kowa bace face matar jiya data taimakeni, bayan sun zauna ta gaisa da aunty Mahfuzah cikin salon gaisuwar larabawa, nima gaidata nai kamar yanda na iya a nawa al'adar da tarbiyyar, kallon mamaki tai min dan da'alama sai yanzune ta lura dani ma, da turanci take tambayata wai dama tare muke dasu Safah?. Amaturrahman ce ta bata amsar da take buƙata harma da ƙara mata wadda bata tambayaba. Murmushi taita saki da ƙaremin kallon da kowa yaketa mamakinsa, tana ta maimaita sunana tamkar karatu a bakinta, bansaniba daɗi yaymatane kokuwa yaya oho, dan nasan suna Bilkisu dai sunane sananne da zaka iya jinsa a kowacce duniyar musulmai balle tace yaune ta fara jinsa sabo.
Ranar dai anan muka yini, har yamma su Amaturrahman basu koma can gidanba, danni dai an tabbatarmin da nazo kenan bazan koma canba, acewartama a daren zata kaini can makarantar da Ummu ta faɗamin. Banga saurayin nanba sai yamma lis ya shigo sanye da farar jallabiya sol da mayafi irin wanda larabawa kansa akai su saka baƙin abunnan a sama tamkar gammo, fara'ar da bangansa da itaba jiya sai gata yau a fuskarsa yanamasu Amaturrahman magana da kulawa kamar yanda suma suke masa, shima dai sai da ya nuna mamakin sake ganin nawa anan, su Amaturrahman da basa hutawa sukai masa bayani dai-dai fahimtarsa, shima dai murmushin yayta saki kafin ya nufi ɗakinsa wai zaiyi wanka.
Ban tashi shiga damuwaba sai da su Amaturrahman zasu koma gidan aunty Mahfuzah su barni anan, hakan kuma na
nufin munyi sallama kenan dasu, sai naji ƙwalla ta cikamin idanu, sabo kenan turken wawa. Suma kansu na lura basuso hakanba, amma sai suketa dariyar ƙaramin ƙwarin gwiwa da tsokana. Haka mukai musu rakkiya har gidan sannan muka sake dawowa ni da Anwar da Anum mai shegen surutu, yanayin rawan kanta sai yakemin kamanceceniya da Nabeelah, gata da saurin magana saina nutsu sosai nake fahimtar magana idan tayi, dama dai maganar tamu sai da turanci. A falo muka sake zama, cikin son fidda abinda kecin raina na tambayi Anum da Anuwar da naga shima ya saki jiki dani yanzu kosun taɓa zuwa ƙasarmu?. Anuwar ne kaɗai yace ya taɓa zuwa shima sau ɗaya tare dasu Abdur-rahman, sunzo hajji wata shekara zasu koma ya bisu sukaje tare, satinsa biyu acan ya dawo daga nan bai sake komawaba har yanzun, amma yanada burin sake zuwa saboda ƙasar tai masa daɗi sosai.
Murmushin jin daɗi nayi sai dai a ƙasan raina ina mamakin to Mamansu fa? Ita bata taɓa kaisu wajen nata danginba kenan kokuwa?, da ƙyar na ture tunanin a raina muka cigaba da hira har sanda Umm-Anum ta fito cikin shiri, sanin inda zamuje ya saka duk muka miƙe, tana gaba muna biye da ita har inda Anuwar ya ajiye motar da zamu fita. Ni da ita baya muka shiga, Anuwar da Anum na gaba, dukda darene garin zirga-zirga aketayi tamkar rana, gashi ko'ina ƙwanyar da wuta abin birgewa.
Mun iso wani haɗaɗɗen gini babba da nake ƙyautata zaton makarantarce, Anuwar yay fakin duk muka fito, jin kamar ana kallona yasa na ɗago, Anuwar na kama idanunsa tsaye a kaina ƙyam, saida gabana ya faɗin dan wlhy sai naga tamkar Boss, murmushi yaymin. ɗauke kaina nai batare dana maida masa murtani ba, Umm-Anum dana fahimci tana kallonmu ta hararesa da kama hannuna mukai gaba. Ina jiyo dariyarsa shi da Anum, sai dai banajin mi suke faɗa cikin harshen larabci. Gaskiya ina sake jinjina wannan tsananin kama a cikin raina, kai gaskiya inason sanin wani abu dangane da mutanen nan, wannan kamar ta wuce kama kawai, anya kuwa babu wata alaƙa tsakanin...........
Shigarmu wajenne ya katsemin tunanina, Bansan yanda zan fasalta muku haɗuwar wannan makarantaba da tsarinta, na bama kowa dama ya ƙiyasta a cikin ransa kawai, dan idan nace zan lissafo komai shafin yau da gobe duk anan zamu ƙare. Tuni na zama baƙauya wajen kallon abubuwan birgewa, to lallai da ace munada irin waɗanan makarantun da mace-macen aure ya ragu muma a yankunanmu, da ansamu sauƙin rikin aurarraki a gidajenmu. Sashe na musamman aka buɗe mana mai madaidaicin falo guda da ɗakuna biyu a ciki.
Fuskar Umm-Anum ɗauke da murmushi ta kalleni, “Ɗiyata anan zaki zauna, dan da kaina zan miki aikinnan saboda ƙurewar lokaci, ga mamanki ɗinan sotake ta ganki tamkar zinare”. Murmushi nai mata kaina a ƙasa dan haka kawai nakejin nauyinta, nai mata godiya tare da addu'ar fatan alkairi. Batace komaiba sai murmushinta dake kasheni taketa sakarmin.
Ɗaya daga cikin ɗakunan muka shiga, kayayyakine ajiye da ban fahimci kona mineneba, ta umarceni dana cire kayana gaba ɗaya na shiga wani madaidaicin kwami dake cike da ruwa da bazamu kirashi normal ruwa ba, ita kuma ta fita. Dukkanin yanda ta umarceni nayi haka nayi babu musu, inayi ina ɗan waige-waige tamkar mai tsoron wani ya shigo, saida na cire komaina kafin na fara saka ƙafa cikin kwamin, ajiyar zuciya na sauke a hankali saboda ɗan ɗumi-ɗumin ruwan mai warware gajiyar jiki, na ida saka ɗayar ƙafar sannan na shige gaba ɗayana, sihirtaccen ƙamshin da ruwan keyine ya sakani lumshe idanu ina karanto addu'ar godiya ga ALLAH da ni'imominsa masu yalwata ta fuskoki da dama ga ɗan adam. Sai da nai kusan mintuna uku da zama sannan ta shigo da sallama, ta canja kayanta da wata doguwar riga mai kama da leda, hannayenta sanye da safar hannu ta leda itama, murmushi taimin ta tako inda nake. Ɗan kwalina daban cireba ta zame daga kaina, ta warware gashina da Alhmdllh yanzu ya cika sosai kuma yanada tsayi gwargwado saboda kulawar da naita bashi bisa koyarwar su Ummie tun muna boarding, wani ɗumi mai daɗi naji ya ratsa kan nawa, hakan yasani kallon madubin dake gabana da nake iya hango kaina da ita kanta.
Tace, “A cikin ruwannan zaki kwana, babu abinda zai sameki insha ALLAH karkiji tsoro, ruwane mai ɗauke da sirrika kala-kala da duk macen da aka gyara dasu dolene mijinta yasan ta isa mace, sirrikane na ƙamshi masu daraja a jikin ƴa mace, ƙa'idar makarantarmu watanni ukune domin mace ta samu damar koyon abubuwa masu yawa, ba sirrin gyaran jiki bane kawai mace tafi buƙata a rayuwar aure ɗiyata, zakiga wata macen komai ta iya ta kuma ƙware, amma idan batasan yanda zataima miji maganaba kawai sai ya rusa mata komai, dan wani namijin shi abinda ke ƙololuwar birgesa ga mace shine iya magana, wani kuma a kallo kawai zaki gama dashi, wani tafiya, wani girki, wani ƙamshi, wani shagwaɓa, wani kwalliya, wani kwanciya. Karki sakama ranki cewa tarayya da miji a gado shine kawai farin cikin aure ko shikaɗaine auren, hakan kuskurene, wani namijin ƙanƙanin abun da kika raina shike sakashi farin ciki. Karkiyi tunanin gyara kanki yana nufin kin mallaki namiji ya zama naki ke kaɗaine, macen data isa mace bata shakkar zama da kishiya ɗiyata, dan wani lokacin zama da kishiya nasake bayyana darajar macene a wajen mijinta. Karkuma kiyi tunanin babu wata mace data isa raɓar mijinki dan yana sonki ko kin iya komai, wani namijin badan baya sonki yake miki kishiyaba ko yake budurwa, a'a halayyar san mace fiye da ɗaya a jinin maza yake, ko bazasu ƙara aureba saisun kalla. kizama mai gyara aurenki ta kowanne ɓangare, idan nace kowane ɓangare ina nufin kowanne fanni hatta da ƴan uwansa da duk abinda ya shafesa. Inason ki cire komai a cikin ranki ki nutsu ki bani dukkanin hankalinki a kwanakinan goma sha biyu da zamuyi tare, sonake komai na cikinsa ya zama tamkar rubutu bisa dutse a cikin ƙwaƙwalwarki, ki ɗaukeni tamkar mahaifiyarki, kuma ƙawarki aminiya wadda zaki iya magana kowacce iri da ita batare da kinji kunya ba, inhar kika riƙe duk abinda zaki koya a kwanakinan ina mai tabbatar miki bazaki taɓa goguwa a zuciyat mijinki ba koda zai auri mata uku ku zama huɗu bayan ke”.
Idona a risine na ɗaga mata kai alamar to, inajiyo sautun murmushinta itama. Abu ta fara shafamin a fuska tana cigaba da min magana cikin nutsuwa, sosai kunya ta lulluɓeni, dan abubuwane masu matuƙar nauyi a gareni take faɗa a buɗe, ta haɗe fuska a yanzu babu wasa tattare da ita ko kaɗan. Saida ta gama tsaf sannan ta fita suka sake dawowa da wata mata. Matar ta nunamin da faɗin, “zata zauna dake anan, ni zan koma gida sai da safe idan ALLAH ya kaimu zan dawo”. Kaina na jinjina mata dan ta hanani magana tunda ta shafamin abin fuskarnan.
Duk yanda zan baku labarin abinda ya gudana a kwanakinan da wahala ku iya fahimtata, abubuwan dana koya kam ba'a magana, sam Umm-Anum bata wasa dani idan akazo ɓangaren abinda zan iya jin kunyarta balle naga fuskar yin sakaci da abinda ake koyamin, tsaye take kaina ɗari bisa ɗari, komai buɗemin shi take babu hijjabi, aduk lokacin da takemin bayani aka abinda yafi ƙarfin kaina tamke fuska take tamau babu wasa, kai jama'a hatta da salon tafiya ba'a barniba sai da aka koyan, komai a tsare yake. Matar da take bari ta kwana dani kasa haƙuri tayi ranar dai take tambayata wai kodai ni ƴar uwar Umm-Anum ce? Dan ita yanda take ganin tanamin ya ninka yanda takema ɗalibanta fiye da zato. An kawoni ɗaki na musamman, sannan komai ba'a sakani cikin ɗalibai ni kaɗai ake koyamashi a nutse, daɗin daɗawa da kanta take min komai bata yadda kowa yayminba sai abubuwan da ba'a rasaba, dan takance kowa a rayuwa da irin basirar da ALLAH yay masa, abinda suma sauran malaman makarantar suke koyamin zai amfanar dani ta fannoni da dama. Murmushi nayi nidai bance komaiba, dan nikaɗai nasan mi nakeji game da matar nan, ita kanta lokuta da dama nakan kamata ta shagala da kallona, kallo maiban mamaki, kallo irin na shagala da zurfi ason tunano wani abu, idan tai irin wannan zurfin kuma zakaga daga ƙarshe ta dafe kanta tamkar zata fita cikin hayyacinta. Akwai randa naga kallon har yaso yimin yawa, sannan ni kaina yanda takemin ɗin nasan ba kamar yanda takema kowa baneba, tana sakin jiki dani fiye da hasashen mai hasashe. Akwai randa tazo tana koyamin
girki sai muke ɗan hira kaɗan-kaɗan, cikin dabara nake tambayarta ko zasuje ƙasarmu nan kusa?. Shiru tai bata bani amsaba, na kasa daurewa dai na sake mata tambayar cike da ladabi. Yanda ta juyo ta kalleni fuska a haɗe saida naso firgita. Kaina na duƙar ƙasa ina faɗin, “Kiyi haƙuri dan ALLAH Ummu, bansan tambayar zata ɓata ranki ba”. Sautin murmushinta na jiyo, hakan yasa na ɗan ɗago na kalleta, ta ajiye cokalin hannunta tazo ta kama hannayena, murya a sanyaye tace, “Ɗiyata ba laifi kikayiminba, ƙasar takuma ni ban taɓa zuwantaba ai, duk amintakar dakika gani tsakanina da ƙanwata Gimbiya Munaya ban taɓa ziyartarta ba, sai dai ita idan tazo nan mu haɗu, duk lokacin danai yunƙurin zuwa nakan tsinci kainane a wani mummunan hali da baida fassara”. Tana gama faɗa ta saki hannuna ta juyamin baya, aikin da mukeyi ta cigaba dayi batare da ta sake min maganarba.
Ajiyar zuciya na ɗan sauke hawaye na ziraromin, haka kawai yanda tayi maganar sai naji abun daban, to amma ai Ummu ta sanarmin itaɗin ƴar ƙasarmu ce, sanadin neman magani ya kawota nan hartai aure, itakuma gashi yanzun tace bama ta taɓa zuwa canba, anya kuwa babu wani sirrin dake ɓoye?.......
Ajiyar zuciya na sauke da saurin kallonta jin ta taɓanu, tace, “Kinama fahimtar abinda nakeyi kuwa?”. Da sauri na ɗaga mata kai alamar eh na tattara hankalina gareta baki ɗaya.
____________________________
A ɓangaren Jawaad ma dai shirye-shirye sun kankama, an gama gyaran gida tsaf, ya canja kamanni gaba ɗaya tamkar bashiba, amarya kawai yake jira ta shigo cikinsa. Gaba ɗaya a tsakaninan a busy yake matuƙa, ga aiki ga shirye-shiryen biki dasu Jabeer ketayi naban mamaki, dan gayya suke ta gaske da gayya tamkar wannan shine auren farko da Jawaad ɗin zaiyi. Shidai ya zuba musu idone kawai yana kallon ikon ALLAH, dan dayay magana ca sukai babu ruwansa, kawai dai yama shirya dan bai isa cewa bazaije wajen abinda suke shiryawanba ehe. Bai sake musu maganarba kuwa ya cigaba da nasa harkokin, maganar kayan da za'a saka a gidan kuwa gimbiya Munaya tace Takawa yace zaiyi komai, kayan kicin kuwa itace zatayi. Da yay mata maganar lefe tace masa ya dakata, zasu nema Dady suyi magana, sai ana saura kwana biyu tarewar za'a kaisu can gidan Dad ɗin dan sune sukafi cancanta da amsar lefen, koyayane zasu bashi matsayinsa na uba kodan ɗawainiyar da yay da Bilkisun. Jawaad baice komaiba shi dai sai ALLAH ya kaimu.
A yau tunda safe Su Amaturrahman suka shirya yima Mami (Munubiya) rakkiya gidan kamar yanda Gimbiya da Takawa suka buƙata, zataje su haɗu da kamfanin da zasu shirya gidan. bayan sun duba saisu zaɓa mata kalar data dace a tsara komai yanda ya dace..............✍
Bara dai na baku hakanan, inata ƙoƙarin typing ɗin bayan tafiyar baƙi amma kiraye-kirayen waya ya hanani nutsuwar yi da yawa, takaima harna daina ɗaga wayoyin mutane wlhy🤦🏻😑😓.
Billyn Abdul:
BARKA DA JUMA'A
Page 37
..................Sosai su Amaturrahman ke santin gidan Jawaad na A.Y Street, badan yafi kowane gidaba, bakuma dan an cikasa da ƙawa ba, ginine dai tamkar kowanne gini da kowa yasani, sai dai yanda akai tsarin gyaran sai ya kuma fiddo da ƙyawun gidan fiye da yanda yake a da, (masu karatu karku manta wannan shine gidan da aka haifa Jawaad, a cikinsa iyayensa suka rayu, dan shine gidannan da turawannan suka bama Abba Abdul-aziz, shine kuma sanadin wannan arziƙi daya tsolema mutane ido). Sai da suka shiga ko'ina da ina dan babu komai cikinsa sai ƙamshin sabon fenti.
Suna tsaka da dubawa Jay ya iso gidan, zaune yake a bayan motar sai Sadiq sabon drivern sa dake tuƙi cikin nutsuwa, dan shima dai baida matsala, amma hakan bai hana Jay tuna Gimba ba a kowacce daƙiƙa ta rayuwarsa, yasan gimba bazai mantu a zuciyarsa ba, dan yawuce duk tunanin mai hasashe a zuciyar tasa. Yauma kamar kullum yana cikin gayunsa da ƙyamshi, sai dai ya ɗan rame, hakan yasakashi yin wani fayau dashi, (bamu saniba azumin da aka shane kokuma ɗokin amaryarne. lol😂).
waya yakeyi, hakan yasa har Sadiq ya fito ya buɗe masa bai fitoba, sai da yaja kusan mintuna huɗu sannan ya fito bayan ya ajiye wayar, Safah data dage sai anzo da ita da gudu tayo kansa, fuskarsa ɗauke da murmushi harta iso garesa, hannunsa ta kama tana gaishesa. Shidai kallonta yake kawai, dan sosai ƙiriniyarta ke bashi mamaki, ko gajiya batayi, girma take amma abun tamkar ƙaruwar mata yakeyi. (Hhhhh tunda Jinin Munaya na yawo a jikin Safah ai kaga abinda yafi hakama, sarki Sameer ne zai baka labari dalla-dalla😂🤐). Cikin ɗoki tace, “Yayanmu gidanka kaida aunty B ya haɗu sosai, nima harna zaɓi ɗakina dan kasanfa nan zan dawo. Murmushi yay mata mai sanyi ya jinjina mata kai amma baice komaiba.
Sosai mamaki ya kama Jay lokacin da suka shiga ciki shi da Safah yay arba da Munubiya, shi tunaninsa Gimbiyace da kanta, itama ɗindai kallon mamaki take masan sai dai ita bamusan kona minene ba. Su Amaturrahman ne suka katse tunaninsa da gaisuwar da suke masa, ya amsa musu da kulawa kafin shima ya gaida Munubiya cikin girmamawa. Kasa haƙuri yay dai yace, “Ummu da kanki? Su Amaturrahman ma aisun isa basai ke kinzoba”. Munubiya tai murmushinta mai kama dana Munaya, kafin ta bashi amsa Safah tace, “Lah Yayanmu bafa Ummu bace, wannan Mami ce sweetheart ɗin Ummu”. Cikin rashin fahimta yake kallon Safah amma baice komaiba. Amaturrahman tace, “Yayanmu ai Ummu ƴan biyune, Mami itace hassanarta”. Ɗan waro idanu Jay yayi waje sai kuma ya shafa kansa, “Sorry Mami ai wlhy ni duk ɗaukata Ummu ce, bansan ita ƴan biyu baneba nasan dai tanada yaya mace”. “Karka damu ƙanina, Gida yay ƙyau masha ALLAH, ALLAH yasa rai akaimawa, ALLAH yasa a cika manashi taf da ƴaƴa ko jikoki zance”. Cikin murna su Safah suka shiga faɗin, “Amin”. Shidai a saman laɓɓa ya amsa nasa amin ɗin.
Kasa jurewa Mami Munubiya tai ta koma gefe tai kiran Munaya, tana ɗagawa tace, “Sweetheart kingako mina gani ga angon nan?”. Daga can murmushi gimbiya Munaya tai tana gyara kanta a kafaɗar takawa, tace, “Nasan ina kika dosa sweetheart, tun randa na fara ganinsa nima naga abinda kika gani, wannan ne dalilin tura matarsa can ta ɗan zauna, sai dai bamu da tabbas, amma muna fatan ALLAH yasa ta kasance hakanne”. “Kai to amin kuwa, al'amarin akwai ruɗarwa, amma gaskiya bana tantamar alaƙa a tsakaninsa da Umm-Anum Sweetheart, nifa da farko na zata Anuwar ne wlhy, sai da nai masa kallon nutsuwa na fahimci yafi Anuwar cikar zati, Anuwar kuma ya fisa haske, hatta da maganarsu kumafa babu banbanci, bara sai dai mun dawo ma tattauna”. Daga haka Mami Munubiya ta yanke wayar ta koma ciki dan baƙin da suke jira har sun iso.
Sai da suka gama zagaye gidan tsaf kafin su basu hotunan kayan ɗakin da zasu dace da tsarin gidan akan su zaɓa. Shi dai Jawaad bai saka musu bakiba, Mami dai ta tambayesa kalar da yafi so, ya sanar musu, daga haka ya cigaba da danne-dannen waya Safah na gefensa tana zuba masa surutu, shidai nasa saurarenta dayin murmushi, sai jefi-jefi yake bata amsar wani abun koyay mata tamba
ya.
Kusan awa guda suka kammala komai dangane da zaɓin kayan, a take Mami ta kira Ummu ta sanar mata kuɗin da suka cajesu. Kafin kuwa subar gidan har ƙuɗaɗensu sun shiga accaunt. daga haka suka bar gidan akan sai zuwa jibi idan ALLAH ya kaimu zasu dawo suga yanda kamfanin suka shirya gidan. Jay yaymusu rakkiya har mota yanama Mami godiya, sai da suka wuce sannan shima ya shiga mota suka bar gidan.
Office Jay ya koma domin cigaba da tarin ayyukan dake gabansa, dama yana tsaka da aikinne Ummu ta kirasa akan yaje can gidan yanada baƙi, dole ya ajiye ya tashi ya tafi. Fatansa ya rage ayyukan sosai, gashi yanason ɗaukar hutu kona sati ɗayane, duk da dai Sir Ahmad yace bai isaba na sati biyu zai ɗauka shima yaje yasha angwanci da ƙyau.
Zamansa baifi da mintuna talatinba baƙon da yake jira ya iso, sai da akai masa iso sannan ya bada izinin a shigo dashi, ba kowa bane baƙon face Sulaiman yayan Amina, Jay ya ɗago daga abinda yake fuskarsa a sake dukda dai ba murmushi yake ba. hannu ya bashi suka gaisa kafin ya miƙe ya kawo masa abinsha baya. ya nuna masa wajen zama, yah Sule yay godiya. Ɗan murmushi kawai Jay yayi baice komaiba. Sai da ya ɗan sha ruwa sannan Jay yace, “Yaya ake ciki Sulaiman? ka gano ina yake?”. Numfashi yaya sule ya sauke yana gyara zama, “Wato ni abin nasu yanzu ya fara ruɗar dani oga, nama rasa wanene mara gaskiyar tsakanin Alhaji Alin da Hajiya Humairan? A yanda bincikena ya nunafa Qaseem baya ƙasarnan”. “Baya ƙasar kuma?” Jawaad ya faɗa yana tamke fuska cike da ɗunbin mamaki kuma. “Ƙwarai kuwa wannan itace magana ta gaskiya, saura kwana ɗaya a ɗauki azumi ya tafi, kuma abinda na fahimta lafiyarsa ƙalau ba kamar yanda ku anan office yace zaiyi zaman ganin likita a gidaba”. Shiru Jay yayi yana juya al'amarin a ransa, tun randa ya fiddo Qaseem a cell bai sake ganinsa ba, sai ana gobe za'a fara azumi, ya shigo station amma baifi awa uku ba ya tafi, Jawaad bai kawo komai a ransaba sai da aka sake ɗaukar tsahon sati ɗaya baiga yazo aikiba, shinefa yay bincike ya fahimci Qaseem ɗin hutu ya ɗauka akan baida lafiya zaiyi zaman ganin likita a gida. Aranar bai ƙasa a gwiwa ba ya nufi gidan Qaseem, amma sai ya iske bayanan daga bakin maigadinsa, yayi tunanin yana gidansu ne, saiya saka a bincika masa can, nanma an tabbatar masa baya nan, tunda yayma gidan yajin aiki ma bai sake waiwayensa ba. Shinefa yasa yaya Sule ya bincika masa.
Huci mai zafi Jay ya furzar daga bakinsa yana danna ƙasan pen ɗin hannunsa da ƙarfin gaske, ya ɗan kalli yaya Sule ya ɗauke kansa daɗan duka table ɗin, “Tabbas yanzu na sake fahimtar akwai abinda suke ɓoyewa, in babu rami miya kawo maganar rami? Sun fahimci ina bibiyar Qaseem shiyyasa suka turashi can, ammafa sunyi abanza, sugama zagaye-zagayensu saina gano komai, da izinin ALLAH sai na bankaɗo komai, idan nace ina nufin komaima Sulaiman!!”. Ya ƙare maganar cikin fushi da dukan tebirin da masifar ƙarfi. Shidai Yaya Sule har sai da yaɗan rumtse ido. Jay yace, “Wace ƙasa suka kaisa?”. Yaya Sule da yay ɗan shiru alamar tunani yace, “Idan dai ban mantaba China naji”. Karan farko Jay ya saki murmushi mai ma'anoni da dama, yaɗan ɗage kafaɗarsa da taɓe baki.
★★★★★
Da daddare bayan Jawaad ya koma gida ya samu kira daga su Uncle Nasir, saida ya kammala shirin barcinsa sannan ya nufi sashen mama Atika inda suke jiransa. Bai wani nuna mamakin ganinsuba gaba ɗaya ya gaishesu cikin girmamawa kamar yanda ya saba.
Uncle Nasir yace, “Alhaji Ali ya kirani jiya akan ankirashi daga gidan sarki za'a kai lefenka gidansa, Jawaad kana ganin kuwa wannan hanyar daka biyo mai ɓillewace? Karfa ka manta a yanda kasa akai ɗaurin aurannan?”. Shidai Jay baice komaiba kuma bai ɗago ya kallesa ba. Cikin fushi Uncle Uwaisu yace, “Wato ga ƴan iska na magana kayi kunnen uwar shegu damu ko?” Murmushi Jawaad yayi yaɗan girgiza kansa batare daya ɗago ɗinba, yace, “Uncle to nikam mi kukeso nace, idan maganar yanda aure ta kasancene tun a wancan karon na bada amsar da duk ake buƙata, a tunanina yanzun mun wuce wannan wajen, kai lefe kuwa daga can masarauta ne sukai t
unain akai lefen can saboda koba komai ubane shi ga yarinyar shine kuma mariƙinta har a yanzun..........”
“A wannan ganganne Jawaad, Shine mariƙinta ko kai daka ɗauketa ka maida gidan sarki saboda ka isa, karkuma a taɓa maka ƴar gwal?”. Uncle Bashir ne yay maganar a fusace. Jawaad da har yanzu yaƙi kallon kowa a cikinsu yace, “Nidai duk abinda kuke ganin na mukushi ba daidaiba akan wannan aure kuyi haƙuri ku kuma gafarceni”. Uncle Sulaiman da tun ɗazun baice komaiba yace, “Nima dai a ganina maimaita maganar baida amfani tunda abinda ya faru ya rigada ya faru, haka kuma ALLAH ya tsara dama zata kasance, kunga kenan bamu isa canja wannan ƙaddarar ba. Yanzu Jawaad ina zaka ajiye matarka? Dan bamuga kana ƙoƙarin gyara ɓangaren nakaba”. Karon farko Jay ya ɗago daɗan murmushi ya kalli Uncle Sulaiman, “Uncle ba anan zan ajiyeta ba, A.Y street zata zauna har an kammala gyaran”. Uncle Nasir yace, “A.Y kuma? Saboda karmu cinyeta anan?”. Jay da keta ƙoƙarin danne fushinsa yace, “Ba haka bane Uncle...........”
Da sauri Mama Atika ta ƙatseshi da faɗin, “Inma haka ɗinne kaidai ka sani fitsararre mai shegen taurin kai da raini, hakan dakai ni bai dameniba, dan ko kaƙi ko kaso dolene a maida aurenka da Sabira, dama shirin maka tsinannen mijin daka aura mata muke a kotu, sai gashi ya matu kuɗinmu sun huta, to wlhy kama tabbata aure kamar mun maidashi ne kai da Sabira”. Cikin fushi Jay ya kalleta zaiyi magana Uncle Sulaiman ya girgiza masa kai. Shiru yay ya maida kansa ƙasa, har sukaci jarabarsu suka tsire bai sake tankawaba, taron dai ya watse da sharaɗin sai ya maida aurensa da Shahudah.
Shidai bai tanka musuba tunda yasan ɗan fir'auna bai mutuba.
______________________________
SAUDIA
Gaba ɗaya wannan yinin na yau Umm-Anum ta yisane cikin yimin nasihohi da haɗamin kayan gyaran jiki da wasu littatafai masu muhimmanci kamar yanda tace, sai faifan cds da tace na kasance cikin kallonsu duk randa nake da lokaci zasumin amfani.
Gaba ɗaya raina a ɓace yake banason tafiya, basan yanda zan musalta muku yanda nakejinta a rainaba, tunda tafiyarnan ta gabato har kuka nakeyi idan na tuna zan tafi, baƙaramar shaƙuwace ta shiga tsakaninmu ba a kwanaki sha biyun nan, kodan ta jani jikintane oho.
A ɓangaren Umm-Anum ma dai cike take da damuwa, haka kawai takejin batason Bilkisu ta tafi, yinin yau komanta sukuku zaka gansa, da daddare tare suka dawo gida da bilkisu, anan zata kwana yau gobe idan ALLAH ya kaimu zasu wuce ita da Aunty Mahfuzah da Anum sai Anuwar daya dage shima zaije, da farko Umm-Anum catai bazaijeba, sai da Abie yasa baki sannan da ƙyar ta amince, dan haka kawai takeji batason suje da ga shi har Anum ɗin.
Abie bai taɓa ganin bilkisu ba sai yau bayan sun dawo, itama kuma yauɗin ta taɓa ganinsa, amma yanda ya karɓeta abin har mamaki ya bata, shikansa mamakin yanda yarinyar ta shiga ransa yakeyi, sannan badan kar ace yay ƙaryaba wasu abubuwa nata suna ɗan masa kama dana Umm-Anum ɗin, musamman tafiya da dai wasu ƙananun abubuwa da saika nutsu sosai kake fahimtarsu.
Sai da su Bilkisu suka shige suka kwanta sannan ya fuskanci matarsa, dan yanda take komai rai ɓace ne ya sakashi jinsa shima a damuwa. cike da kulawa yake tambayarta mike damunta?. Hawayen da taketa riƙewane suka zubo mata. Sake rikicewa yay ya jawota jikinsa, dan yanason wannan baiwar ALLAH shidai a rayuwarsa, dukda ba ita kaɗaice matarsaba kuwa, amma yanda take ƙyautata masa yasa tazama tauraruwa a garesa. Yanda yaketa jero mata tambaya wata kan watane ya sakata sakin murmushin ƙarfin hali, idonta a kansa tace, “Bafa komai baneba, yarinyarnan banason ta tafi wlhy, jinta nake cikin jinina fiye da yanda kake zato, ina mata ƙauna maiban mamaki har a ƙarƙashin zuciya, sannan sunanta duk sanda na ambacesa ko wani ya ambata sai naji matsananciyar faɗuwar gaba, bansan miya saba”. Abie dai kallonta ya keyi cike da nazari, sai da tagama ya sauke ajiyar zuciya tare da sake rungumeta, maganganunta na buƙatar ayi musu zama na musamman domin yin nazari, amma duk da haka bara ya gwadata ya gani, ko lokacin da suke fata
ne yazo. “To kodai zamu shirya muma muje bikin nata ne?”. da sauri Umm-Anum ta tashi daga jikin mijin nata tana girgiza kanta, fuskarta harta nuna ɓacin rai, tace, “Babu inda zani Annur, badanma ka takuraba kosu Anum bazasu jeba”. Da kallo shidai kawai yake binta, amma baice komaiba, baikuma sake cewa uffanba game da tafiyar har gari ya waye su Bilkisu suka tashi da shiri.
★★★★
Yau ta kasance ranar da zan koma ƙasata ta haihuwa tare da tarin alkairan Umm-Anum da mijinta da Aunty Mahfuzah, sai su Anum da nakejin ƙololuwar farin cikin tafiya tare da su, gefe guda kuma na zuciyata najin ɗacin rabuwa da Umm-Anum tare da matsananciyar kewa. Munfi awa uku zaune da ita tana sake tisamin abubuwa masu dama, daga ƙarshe ta roƙeni akan karna manta da ita, zata kuma ringa kirana akai-akai, idan kuma nasamu lokaci na daure muzo gareta wataran tare da mijina, haka kawai takeji a ranta tanason ganin mijin ƴarta. Murmushi kawai na iyayi ina share hawayena kaina a risine, ta rungumeni a jikinta tana jeromin addu'oin fatan alkairi da zaman lafiya a gidan aurena. Da ƙyar ta barni na fito, tana kuka nima inayi tamkar zan shiɗe, da ƙyar Aunty Mahfuzah taja hannuna ita da Anum.
Har jirginmu ya ɗaga ban daina kukan kewar Umm-Anum ba, ina ƙaunar matarnan matuƙa a cikin jinina da tsokar zuciya harma da ruhi.
Kasancewar tafiyar yamma mukayo dukda ba time ɗinmu ɗaya da nanba munyi saukar dare ne, inda mukaci karo dasu Amaturrahman ƴan tarba, sosai muke murnar ganin juna, sai santi suke wai na canja matuƙa, sunata zubamin shaƙiyanci nadaiƙi kulasu, dan bana cikin mood ɗin farin ciki sam.
Koda muka isa masarauta Ummu ma rungumeni tayi, sai taɓani take tana jerama Umm-Anum addu'oi na musamman, ga daɗin da taji na barin su Anuwar da akai suka biyomu. A ƙasan raina inata mamakin ganin yanda suketa shirye-shiryen bikin tamkar zasu aurar da ƴarsu ne ta cikinsu ko ƴar uwa ta jini, kai waɗanan mutane sun cancanci zama shugabbani, domin duk mai fuskantar al'umma da maida al'amarinsu nasa to lallai shine shugaban da yafi cancantar zama shugaba.
Ɗaki guda aka waremin dan Ummu tace bazan zauna ɗakinsu Amaturrahman ba wannan karon, akwaima sauran kayan gyara da Umm-Anum ta bayar a ƙarasa min a kwanaki biyun da suka rage mana. Babu wanda yaymin maganar Boss nima kuma bamma kowa ba, da yake darene bayan anɗan gaggaisa duk muka kwanta.
WASHE GARI.
A safiyar yau nakejin wai za'a kai lefena gidan Dad ne, haka kawai naji gabana ya faɗi, amma sai na danne zuciyata na cigaba da addu'oi, har yanzu Yah Qaseem na ƙasan raina, inason nasan halin da ya ke ciki shi da Dad fiye da kowa a gidanmu, sai dai hakan ta gagara dan boss ya toshe ko ina da ina da zan iya jinsu. Su Amaturrahman sunata shirin tafiya can gidan domin amsar lefen suma, sai a yau naga sauran manyan ƴaƴan Ummu ƴan uwan tagwaicin Amaturrahman. Abdul-Raheem da Abdur-rahman, sai Ameen ɗan uwan tagwaicin Meenal, sai Uncles ɗinsu huɗu, Sauban da matarsa ƙyaƙyƙyawa mai kirki da yaransu huɗu masha ALLAH, sai Aryaan shima da matarsa da yara biyu, Aiyaan ma matarsa da yarinyarsu ɗaya sai ciki ƙarami da matarsa keda shi, sai Khalil shima da tasa matar da yara biyu, dukansu suma a jiya suka iso daga India. Gida ya cika yanda akeso tamkar bikine daya shafesu na jini, washe gari sai ga wadda naji suna kira Aunty Samha itama da nata ƴaƴan, sai kuma babbar mace suna kiranta Aunty Mimi. Wlhy bansan sanda hawaye suka faramin gudu a kumatuba, duk wani kewar ahali sun toshemin ita ta ko ina, sun mayemin gurbin dangin da suka nisanceni.
A wajen Amaturrahman nakejin wai Boss yazo masarauta wajen Ummu yau da safe, bai nemi inda nakeba har ya wuce, banji komai a rainaba game da hakan, sai daga baya suke bani labarin Ummu ce tace an daina ganina har da shi kansa bazai ganniba. Ni saida abinma yaso bani dariya amma na kanne.
_______________
A gidan Dad kam shirye-shiryen karɓar lefe suke, duk da dai ran Momy a ɓace yake matuƙa tana dai ƙoƙarin dannewane, shi dai Dad baka gane yanayinsa, dan yamafi maida hankali ga lallashin ƴar lelensa da suka cikama zuciya
da alƙawarin komawarta gidan Jay nan bada jimawaba.
Kusan sha biyun rana su Amaturrahman suka iso gidansu Hudah, Hudah dai bata fitoba zamanta tai cikin ɗakinta, Aamilah kuma an fito ayi rainin wayo saita iske waɗanan sunci uwarta aduk iskancin da take taƙamar ta tara kota iya. Dole fa ta nutsu waje guda ta kama kanta, harta je ta ƙwanƙwasama Shahudah dake ɗaki gulma da cewar lallai Bily ta shahara a asirin nata har ƴan gidan sarki taimawa. Cikin takaici Shahudah tace, “Tsinanniya jikar matsafa, ai nayi alƙawarin randa na koma gidan Bb wlhy bazata kwana a gidanba, shi kansa saina sakashi yin nadama wlhy, kuma a banza zata shiga ta fito Hajiya (mama Atika) tamin alƙawarin ko hannunta bazai riƙeba dan Uban da ya haifeta”. Dariya Aamilah ta sanya da sake tunzurata akan hakan da zatai shine dai-dai, kuma taji daɗin matakin da mama Atika tace zata ɗauka akan kar Bilkisu ta raɓu Jawaad, (dan sufa har iyanzu tunaninsu nakan asiri Bilkisu taima Jay bawai sonta yakeba😂). “Mtsooww kamar kin manta da aikin matsafa kenan” cewar Shahudah cike da takaici. Haka dai sukaita aikin zagin Bilkisu da Alhaji Babba harda su Ummah basu tsiraba, kai gidan sarki ma saida suka samu rabonsu😂.
Oho su bama susan da zaman wata Hudah ba a duniya balle a cikin gidan, sun ɓararraje abinsu sunata harkokinsu tamkar gidansu (😂Wani aiki saisu Samha) hankalinsu kwancefa yake a gidan Dad dukda sunga cika da batsewar da Momy keyi basu nuna ta damesuba.
Ƙarfe biyu da wasu mintuna na rana matan Uncles ɗin Jawaad dasu Ummah suka iso da lefen Bilkisu. Kayane gwargwadon iko na gani na faɗa babu fariyya a ciki balle nuna anfi kowa. Sai dai fa tsarin kayan da nagartarsu dolene ta girgiza zukatan mahassada da masu ganin wadda akai dominta bata cancancesu ba. Inna zainabu sai haɗiyar zuciya akeyi, hatta da Lawisa da ayanzun basa faɗa da bilkisun kuma itama mijinta Alhmdllh sun sami sauyi saida taji ɗaci a ranta, hakama sauran dangin kowa dai ta ciki na ciki, su kansu matan Uncles ɗin Jawaad da suka kawo kayan kowa dai sai murmushin saman fuska tunda suma sai yaune suke ganin kayan tunda su Ummah ne suka haɗa abinsu. To kowa dai ya danne an gama komai lafiya, an kuma bar kayan anan sai Dad ya gani sai a kaisu masarauta zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu suma su Gimbiya su gani.
Tukuyci mai tsoka ƴan masarauta suka saukema su Ummah, wanda ya girgiza kowa hatta momy da take ganin wanda Dad ya bada a bayar yayi yawa da.
Aikam tunda su Safah suka koma masarauta babu abinda suke sai labarin lefe, suka addabama Bilkisu da tsokana musamman su Amaturrahman da matansu Aryaan da suke biye musu suma dayake mashiriritan ne. Sai da gimbiya ta fito da kanta ta korasu daga kan Bilkisu sannan suka sama mata lafiya.
_____________
Gayya taban mamaki su Jabeer sukayo a wannan biki, al'amarin har ba'a cewa komai, tun a yau baƙin nesa kuwa suka fara sauka, irin su Abbati ma duk yau suka kawo matansu gidan Ummah babba, su kuma suka yada zango a masaukin da su Hafiz suka tanada musu.
Ango kuwa yau alhamis yana zuwa office Sir Ahmad ya korosa akan ya tafi sun bashi hutu, karya ƙara ganin ƙafarsa sai nan da sati biyu ciff, shidai murmushi kawai yayi baice komaiba. Ƴan station ɗinsu ma dai zuwa yanzu sunsan boss ya auri Bilkisu, masu gulmar dama soyayya yake da ita sai bakuna suka buɗe aka samu nayi, yayinda masu goyama Rose baya suketa angizata da maganganun ɓatanci ga Bilkisu da Jay ɗin kansa, masoyansu na ƙwarai kuwa murna suke tayasu da ganin sun dace da juna.
MASARAUTA
Tunda garin ALLAH ya waye an tashine cikin shirye-shiryen kamu da aka haɗashi da Hausa fulani day baki ɗaya, su Ummie, Nazifa, Zuhrah, Rebecca, Amina, Nabeelah, duk suna can suma tare dasu Amaturrahman, abin birgewa kuma duk ƙawayensu na Boarding skull sai da su Ummie suka gayyatosu suma duk sunata isowa masarauta a safiyar yau, hakan saiya saka Bilkisu hawaye da tuno iyayenta, inama da ransu wannan rana tazo mata, inama suna jingine da ita har zuwa yau ɗinta, ina firdausin ta, ƙawar amana ko tace ƴar uwa rabin jiki, kullum addu'arta ALLAH ya
sadata da Firdausi da iyayenta kafin tabar duniya.
Tunda safe dama mai ƙunshi tazo muka shige cikin ɗaki daga ni sai ita ta shiga zanamin na nutsuwa, zuwa azhar ya bushe yay shar kamar ka cinye dan baƙi da jaa aka ɗaɗara mani, kasancewar fashin salla nike dama sai kawai aka shigamin gyaran kai a nan gida dan Gimbiya nada dukkan kayan gyaran kai a gida da takema kanta, bayan an kammala nai wanka lokacin ƙarfe kusan uku.
Kasancewar ba sallah zanyi ba sai ban damu da kwalliyar da ake shirin tsaramin ba, ni kaina basai an faɗaba nasan ina tsaruwa dai-dai gwargwadon iko, duk da ba'aimin kwalliyar dana canja kamanni baneba amma nayi ƙyau fiye da zato. Bayan an kammala kwalliyar aka shiryani cikin atamfa lass ƴar ubansu datasha stones work ɗan gaske, sket da riga akai da suka fidda ainahin tsarin jikina dukda basu matseni tsam ba, sundai zaunamin a jiki ɗas har ni kaina ban gaji da kallon kaina ba. An min naɗin ɗan kwali mai tsari aka ƙawata adon nawa da sauran kayan ƙawata kwalliya irinsu sarƙa da sauransu. Ƙamshina kam ai har hawa kan mutane yakeyi, daka ganni kaga cikakkaiyar bahaushiya jinin Fulani, tabbas a yau na sake yarda da babu mummuna a duniya sai wanda ya munana kansa, idan har zaka tashi ka gyara kanka tofa ka wuce a kiraka mai muni, dama can rashin gata da kulawane suka dadushe sihirtaccen ƙyawuna mai cike da kwarjini.
Taron iya matane, dan acikin masarauta ma za'a yisa, su Ummah da danginsu duk sun iso masarautar, hakama danginna na ɓangaren Uwa su Inna Zainabu dasu Momy harda Aamilah, Aunty Shahudah dai ban gantaba, ƴan gidansu Boss ma kam inada tabbacin ƙwai da kwarkwata ne a wajen nan. Babu abinda da dai za'a cema UBANGIJI sai godiya a wannan al'amari, amma tabbas Bilkisu tazo da farin jini mai ban mamaki da tarin alkairi. Iyayen ƙawayenta su Ummie, matansu Aliyu, abokan aikinsu ƴan station ɗinsu, ƙawayenta na makaranta harma da waɗanda sukazo dalilin wane da wane duk suna a wajen. Sai ƙarfe huɗu da rabi Gimbiya Sarauniyar gagara badau Munayatul-muna ta fito riƙe da hannun amarya Bilkisu mai gadon zinari.
Ai a take wajen ya ɗauki ƙannan magana musamman ma ƴan gidansu Jawaad da ada suke ɗaukar Bilkisu ba komaiba saboda yanda su Momy ke munanata da ƙasƙantar da ita a garesu. Wasu sunɗan santa sama-sama wasuko sai a yau suke ganinta.
Ganin yanda ɗunbin mutane suka taru danni sai kawai naji hawaye sun zubomin a kumatu, Zuhrah ce ta duƙa gabana inda ya kasance mazaunina ta shareminsu da handkherchief tana murmushi, “Haba amarsu ai lokacin kuka baiyiba kinji, sai gobe idan ALLAH ya kaimu kina kusa da Boss, da sun zubo ya lashe kayansa”. ta ƙare maganar da kashemin ido. Hararta nayi ban iya cewa komaiba, sai dai fa maganar datai sai da naji gabana yaɗan faɗi, dana tuna kuma ma ina period saina ɗanji sauƙi a raina.
Ba'a ɓata lokaci wajen fara gudanar da abinda ya tara mutane ba, komai kuma a nutse babu wata hayaniya, koda aka fara kiɗan ƙwarya ma a nutse ƴammata da matan aurenma masu jini a jika keyin rawa, ina tsakkiya nikam anata zubamin liƙi, Anum na liƙe dani wai tana gwagwaɗamin wai itama idan ta tashi aure zamuje Saudiyya da masu kiɗan su mat. Murmushi kawai nayi mata dan ta bani dariya.
komai ya tafi cikin burgewa da kwanciyar hankali, kafin a koma yin hotuna da kowa ke fatan yi da amarya da gimbiyar gagara badau. Zuwa magriba aka tashi.
Ni dai tunma kafin magriban muka bar wajen tare da Ummu da akoda yaushe tana kusa dani idanunta akan kowa da zai iya raɓata. Dan tace itafa bata wani yarda da kowa dake wajenba.
__________________
A ɓangaren su Jay suma sunacan suna nasu shagalin, sai dai su nasu sai bayan sallar isha'i suka fara, suma iyasune maza zalla a wajen abokansa, su Aryaan duk suna can dan kuwa dai sa'annine, sudai su Abdur-raheem, dasu Anuwar basu jeba kasancewar su Jay yayunsune wannan shigar ba tasu bace, suna buƙatar sakewa kuma, sunama can gidan Mami Munubiya suna shan shaftarsu hankali kwance.
Dauriya kawai Jay keyi, dan kansa ciwo yake masa matsanancin ciwo ma kuwa, amma kasancewar yasan duk ɗunbin mutanennan dan shi
suka taru sai ya daure har zuwa goma na dare kafin ya gudu ɗakin da zai kwana a hotel ɗin ya barsu, ko wanka baiyiba dan bai jima da yiba, kayansa kawai ya zame ya faɗa saman gadon ya kwanta yana sauke tagwayen ajiyar zuciya, cikin ransa ko mamakin Bilkisu ya keyi, ƙaramar yarinya da ita sai shegen jan aji da miskilanci, tunda ta tafi bata nemsaba, ta dawo ma haka. Wani ɓangare na zuciyarsa yace, ‘Kaida haƙƙin sanin lafiyarta ke a kanka ka nemeta ne?’. Kansa ya dafe kawai da lumshe idanu, kafin ya buɗe a hankali ya jawo wayarsa dan tunawa da saƙwanin da yasa a turo masa.
Kasancewar datarsa a buɗe take duk sunma buɗe kansu da kansu, harda videos. Ya sauki wani lallausan murmushi maiban mamaki daya sakani tunanin wai shin mi yake kallo hakane?................✍
Jiya kun haɗan zafi yasin, waɗanda ban ɗaga kiransu ba suyi haƙuri man kaina ne ya tsiyaye😂🚴🏼.
BARKA DA JUMA'A.
Musha weekend lafiya
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭😭🙏🏻
Billyn Abdul:
Page 38
..................Shagulgulan biki sun cigaba da gudana a washe gari tamkar yanda aka tsara, su Ummah babba sunyi yinin biki suma matsayin iyayen ango, kafin zuwa la'asar su ɗunguma zuwa masarauta domin halartar walima da gimbiya ta shirya itama. Walima kam ta ƙayatar fiye da zato, amarya tasha ƙyau cikin shadda pink mai duhu. Inda malamai magada annabawa suka gudanar da wa'azi mai kashe jiki da ɓargo, bilkisu kam dai ansha kuka, idanu sun ƙara girma. Tun su Zuhrah dake zaune kusa da ita suna mata dariya har dai suka koma lallashinta suma suna sharar hawayen dan jikinsu duk sai yay sanyi ƙalau. An tashine gab da magriba, dan haka kowa yana yin salla shirin tafiya dinner ya fara. Amarya ma wanka aka sakata ta shiga.
Gaba ɗaya jikina a sanyaye yake, tunani da fargaba duk sun cika zuciyata, yau ni Bilkisu nice za'a ɗauka akai gidan boss matsayin matarsa ta aure, aure ba yawo ba, idan naje shike nan natafi din din din, duk da nasan ba sonsa nakeba, shima kuma bason nawa ya keba na ɗaura ɗammarar masa biyyayya insha ALLAH, zanyi haƙuri tamkar yanda kowa ke faɗamin zaman aure haƙurine, zanyi biyayya a garesa matsayinsa na mijina shugabana, zanyi aiki da dukkan dabarun Umm-Anum da gambiya suka ɗorani akai domin samun zaman lafiya a gidana koda ace bazai soni ba. tausayinsa nakeji har cikin raina yanzun, dan a daren jiya munyi zama na musamman da Ummu inda muka tattauna game da kamanninsa da Anuwar harma da Umm-Anum ta abubuwa da dama. Ta tabbatar min nice ya dace nai wannan aikin na bincikar abinda ya shafesa ko tanan zasu iya fahimtar idan akwai alaƙar da duk muke zargi dan kamannin sun wuce kama akwai dangantakar jini dole, bansan komai na abinda ya shafi family nasa ba, sai ɗan abinda ba'a rasaba shima iyakarsa daga wajen su Mom ne da da rashin jituwa tsakaninsa da Yah Qaseem, amma a raina nima tunda muka haɗu da Umm-Anum nakeji abubuwa da dama nazomin a rai game da shi......... Da wannan tunane-tunanen na tsaftace jikina na fito, kasancewar ba salla zanyiba zaman min kwalliya akayi.
Tun ina jiyo hayaniyar ƙawayena dake ɗakin su Amaturrahman suna shiryawa har naji tsit, alamar dai sun fice dan zuwa yanzu har anyi sallar isha'i. Basan yaya zan musalta muku irin ƙyawun da nayiba yauma, amma na bama kowa damar ya hasasoni cikin zuciyarsa, kwalliyata ta yau ta kasance harda alƙyabar da Mommah ta bani matsayin ƙyautarta, basai an faɗaba, a gani da ido kaɗai ya isa amsa ga mai kallo cewar an sayeta da kuɗaɗe masu nauyi da darajar gaske. Suna cikin gyaramin alƙyabbar da santin ƙyawun da nayi aunty Samha ta shigo.
“Wow, masha ALLAH amaryar ƙamshi” ta faɗa tana rungumeni, ta ɗagoni tana kallona da cigaba da faɗin, “Wannan ai saiki rikita angon yace an fasa dinner ɗin”. Dariya waɗanda sukaimin kwalliyar sukayi, ni dai kaina a ƙasa ban yarda na kalleta bama dan tasa naji kunya, gashi kukane keta ƙoƙarin tasomin ina dannewa. Itace ta kama hannuna muka fice, ganin ba'a kaini wajen Ummu ba sai nayi tunanin za'a sake dawo dani nan kenan, ƙilama sai gobe idan ALLAH ya kaimu. A take naji farin ciki ya wani lulluɓeni. Ko ina ƙwanyar yake da haske a masarauta shiyyasa koda muka fito dukda kaina a ƙasa yake ina kallon inda muka nufa.
Mun tsaya dai-dai motar da na hango Oga Jabeer jingine yana waya tun fitowarmu, yana sanye da shadda ƴar ubansu ruwan madara. Yana ganin mun ƙaraso ya ajiye wayar yana murmushi da faɗin, “Aunty Samha aini da har ina shirin bin bayanku, dan naga baƙwa son bamu amaryarnan kamar”.
Murmushi tayi mai sauti tana gyaramin hular alƙyabar, “To gaskiya badan munasoba zamu baku, dan bamu gaji da ɗiyarmu ba, amma yaya muka iya, wannan shine girman”. Oga Jabeer na ƴar dariya ya buɗe ƙofar motar da cewa, “Aure yaƙin mata”. Tace, “Har mazan ma”.
Daddaɗan ƙamshin turarensa da na sani daine ya fara tarbata da sallama, na shaƙa na lumshe idanu ina ƙoƙarin dai-daita bugun zuciyata da kalato yawun da zan jiƙa maƙoshina da ya bushe, sai da na zauna da ƙyau Mah-mah ta gyaramin alƙyabar sannan na tsinkayi muryarsa yana gaisheta cike da mutun tawa, sai da suka gama gaisuwar s
annan Oga Jabeer ya rufe motar ya shigo shima, itama motar da zasu tafi a ciki ta nufa ta shiga.
“Ina yini?”. Na faɗa a hankali har banyi zaton zaima jini ba. Shiru banji ya amsaba, kuma tabbas inaji a jikina idonsa a kaina suke, dan ina jinsu har cikin ɓargona. kaɗan juya na kalli sashen da yake dan in tabbatar da bai jinin ba kokuwa ƴan wulaƙancinne a kusa.....
Ina ɗagowa idanuna na shigewa cikin nasa, saurin maida kaina ƙasa nai ina ɗan ƙunƙuni a cikin raina batare da nasan bakina naɗan motsawaba ashe, ‘mutum babu abinda ya iya sai kallo, har sai an hango maka muni’.
Jawaad dake kallon yanda bakinta dake ta shining na ɗan lipstick ɗin da aka sanya mata ya lumshe idanu a hankali yana sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya, maida kansa yay jikin sit ya kwantar yana maijin takaicin yarda da yay da zuwan wannan dinner ɗin banzar, yanzufa kowa sai yaga wannan ƙyawun da tai ko?. Ware idanunsa ya sakeyi a kanta yana binta da wani irin sassanyar kallo, gaba ɗaya ƙamshin turarenta ya saukarma gaɓɓansa da kasala.........
“Ehhgy egeehhmm!”. Jabeer yay gyaran murya. Haɗe fuska jay yayi ya balla masa harara tare da ɗauke kansa ya maida gefe bai dai ce komaiba. Jabeer ya haɗiye dariyar dake cinsa daƙyar sannan ya tada motar suka fice.
Shiru motar tayi bakajin motsin komai sai na ac da ƙamshin turarukanmu, tunda na gaida Oga Jabeer nima ban sake ko ɗaga kai na kalli inda sukeba, dodon nawa kam tun gaisuwarsa da aunty Samha ban sakejin ya firta komai ba shima, anata kiran wayarsama yayi kunnen uwar shegu tamkar ba yaji ana kiran. Mintuna ƙalilan muka iso wajen taron, inda muka taras da abokansa dasu Ummie tsaitsaye alamar isowarmu suke jira.
Jabeer da yay fakin ya juyo ya kalli Jay. “ku zama cikin shiri boss, bara na musu magana”. Kai kawai ya ɗaga masa, shi kuma ya fice. Kusan sakanni ashirin da fitar Oga Jabeer babu wanda ya motsa a cikinmu daga ni har shi, inata ɗan juya zoben yatsana ne dan gaba ɗaya a takure nakejin zaman namu kusa da juna.
“Bana son rawa” na tsinkayi muryarsa ƙasa-ƙasa saitin kunnena, da sauri na juya garesa dan a bazata maganar tazomin. A karo na biyu muka sake haɗa ido, sai dai yanzun duk yanda naso janye nawa kamar ɗazun hakan ya gagara, kallo yakemin irin na tsakkiyar idonnan tamkar zai haɗiyeni dasu, bazan iya jurewa ba, amma na kasa janyewa dan tamkar yamin ɗaurin goro ne da mayun idanun nasa da a yau suke farare tas babu sirkin ja alamar dai baya tattare da ɓacin rai. Da ƙyar na samu nai ƙoƙarin yin ƙasa da kaina zuciyata na wani tsitstsinkewa tare da jinin jikina. Amma a bazata saijin tattausan hannunsa nai ya taro haɓata ya sake ɗago fuskar, tuni zuciyata ta sake wani zallo tamjar zata faso ƙirji ta fito, Farfar na farayi da idanuna da suka cika taf da ƙwalla lokacin da ya matso da fuskarsa daf da tawa har munajin saukar numfashin juna, lumshe idanun kawai nayi ganin bani da wata mafita kuma, ya kawo bakinsa daf da nawa.
Yanda jikina ke tsuma zai tabbatar maka a matsanancin tsoro nake da yanayin, tsigar jikina duk ta miƙe.
Jay dake kallon yanda bily ta rikice ya saki lallausan murmushi tare da goga hancinsa kan nata, murya can ƙasan maƙoshi yace, “Matsoraciya kawai, darajar matata tafi ƙarfin nayi kissing ɗinta anan wajen yariya, hakan bazai taɓa yuwuba sai a fadata insha ALLAH. badan girman alƙawari ba da bazan taɓa bari ki shiga wajen nanba, ni kaɗai yafi cancanta na shaida wannan ƙyawu naki a cikin gidana. Ina ƙara maimaita miki bana son rawa”. Ya ƙare maganar da ɗaura yatsansa babba saman lips ɗina ya kwashe ɗan lipstick ɗin da aka samin.
Wata irin kunya naji ta lulluɓeni mai haɗe da tsoro da ɗan haushin gogen lipstick da yayi, nai ƙasa da kaina ina ɗan kumbura da faɗin, “Toni nama iya rawan ne ma.........”
Saukar ɗalli kawai naji a saman laɓɓana mai azabar zafin, na ɗago idanuna da suka cika da ƙwalla a kansa. sassanyan murmushin mugunta ya sakarmin har dimples ɗinsa duka biyu na loɓawa, ya ɗage kafaɗunsa yana ɗage gira ɗaya da taɓe baki alamar ni naja.
Kafin wani ya ƙara magana a ciki
nmu akai knocking glass ɗin motar, sauke gilas ɗin yayi, oga Hafiz ne yay masa magana akan mu fito. Banji amsar da ya bashiba, baice min komaiba nima ya fice, ina ƙoƙarin gyara alƙyabata nima na fita naji an buɗe ƙofar ɓangarena, na ɗago dan ganin wanene muka haɗa ido ashe shine ya zagayo tanan, hannunsa na dama ya miƙomin yana wani ɓata fuska da kallona ƙasa-ƙasa, a kunyace na ɗora nawa ya taimakamin na fita nima, hannunsa na haggu yasa yaja hular alƙyabar ya sake rufemin fuska da ƙyau.
Ina jiyo wani cikin baƙin abokansa na faɗin, “Sarakin kishi muma ba kalla zamuyiba ai bar wahalar rurrufe mata fuska”. banji ya bashi amsaba sai dariyar da sauran sukayi. Inajin irin zafin da nakeji a duk lokacin da ya raɓu jikina, sai dai yau kaɗan nakejinsa cikin amincin ALLAH, dan haka nai jarumtar daurewa tamkar banajin komai ina addu'a cikin raina har muka shige abokansa da ƙawayena na biye damu a baya cikin ƙyaƙyƙyawan tsari babu wata hayaniya.
Muna shiga da aunty Batool dake ƙofar tsaye tana jiranmu muka fara cin karo, ta shiga feso mana wani farin abu mai ƙyalƙyali da ƙamshi, masu hotuna kuwa nata ƙyalla mu.
Sauran mutanen duk suka miƙe idanun kowa na kan amarya da ango dake cike da birgewa, yayinda ƴanmatan family ɗin su Jay sukejin zafi a zukatansu dajin takaicin bilkisu da tazo daga sama tai musu wuf da shi, sai irinsu Rose da kallo ɗaya zakai musu ka hango tsagwaron kishi da tsanar bilkisun a cikin idanunsu. MC kuwa na zubama amarya da ango kirari. yayinda Ali jita ya sake gyara maƙogwaron nan nasa na zinari ya fara baitocin girma ga amaryar ƙamshi bilkisu mai gadon zinari cikin waƙarsa mai taken Bilkisu gimbiya.
(Bara naɗan raira muku kaɗan saura wani yace ban iyaba😣😚. lol)
🎸🎸🎶🎶BILKEESU zan faɗa dan ALLAH, mata ku bani dama duka.
bilkisu gimbiya.
BILKEESU mai gadon zinari waƙarki ta fita haka.🎸🎶🎶
BILKEESU sai gani sai nuni, kowa ya tabbata duka.🎸🎸🎸🎺🎺
BILKEESU gimbiya an baki, mata su dakata duka.🎸🎸🎺
BILKEESU sanya alƙyabar ki kaya mayalwata haka.🎸
Bilkisu gimbiya.
BILKEESU za'a yiwa fada, ai mata fifita haka. 🎸
Jita kaja muje nai waƙar Bilkisu masu girma haka.🎸
Mata ku rausaya Ali jita nine na baku dama haka🎸🎶🎶
Komai yanada rana a gane dama tanada dama haka, Bilkisu gimbiya.
Giwa ki rausaya BILKEESU ALLAH ya ƙara baiwa haka.🎸🎷🎷
Komai yaje ya dawo BILKEESU ku za'a tabbatarwa haka🎸
Ganga irin ta girma a miki waccan a mata garwa haka.🎸
BILKEESU za'a baiwa Number komai daren daɗewa duka
Bilkisu gimbiya
BILKEESU sannu mata irin na zamanin ɗebe kewa duka.🎸🎸
Kinsha aradu kinsha yasin, kin samu arziƙi duka.🎸🎷🎸🎷
Kin tsallakema tarkon maƙiya, ga ɗan abin biki haka.🎸
Kinzam sarauniya a cikin mata bar munafuka haka.
Bilkisu gimbiya🎸
Ga zamani da daɗi wannan al'amarinkine duka🎸🎸🎸
Tsarki na zuciya bilkisu ya baki ɗaukaka haka.
Kinsa kara a hanya BILKEESU wazata tsallakane🎸
Komai kina tunani Bilkisu baƙya abu daka haka🎸
Bilkisu gimbiya
Ga ilimi da halin girma, ALLAH ya ɗaukaka haka.........🎸🎷🎸🎷🎸🎺🎺🎺🎺
(Kunema sauran kuji na gaji😂😜)
“Mawaƙin nan dolene yaci ƙyautar mota”. Oga Aliyu dake bayanmu shida matarsa ya faɗa yana ƴar dariya.
Murmushi naga boss yayi a hankali lokacin da yake kama kafaɗuna yana zaunar da ni a ɗaya daga kujerar guda biyu da aka tanada danmu. Ni kaina waƙar tamin daɗi sosai, hakan ya sakani sakin murmushi da banyi niyyaba. Jay yaɗan lumshe idanu ya sake buɗewa a kanta sannan ya zauna a nashi mazaunin shima.
Babu ɓata lokaci aka fara gudanar da abinda ya tara mutane, an buɗe taro da addu'a kafin ai kiran Ummie tazo ta bada tarihin amarya a taƙaice, Hafiz ma ya bada tarihin ango tare da ɗorawa da shaƙiyancin randa suka fara gane Jawaad ya kamu da son amaryar tasa. Yanda yake faɗar wajen dole ya saka mutane dariya, masu baƙin ciki kuwa suka shiga zuba tsaki suna haɗiyar zuciya. Bily kanta sai da ta murmusa dukda tasan ba haka bane tunda ita
dai bai taɓa ce mata yana son nata ba, ɗagowa tai da nufin satar kallonsa sai suka haɗa ido, dan shima kallonta yake ƙasa-ƙasa idanu a narke.
Cike da salo ya wani ɗagemin girarsa ɗaya, maida kaina nai ƙasa zuciyata na motsawa. Ban sake gigin kallon sashen da yakeba nima na maida hankalina ga kallon mawaƙa da suketa baje fasaharsu cikin daɗaɗan waƙoƙi da duk an raira baitocinsune da sunayenmu. Umar m shariff, Ado gwanja, Nura m inuwa, Naziru Ahmad, Hamisu breaker, Isa ayagi, Abdul D one, kai abunfa ba'a magana, ƴan uwa da ƙawaye da abokan ango nata casar rawa, duk yanda mc keta magiya da roƙon amarya da ango su fito filin rawa ya hanani ko motsi, duk wanda ke buƙatar mana liƙi sai daifa yazo nan inda muke zaune ya liƙa mana ɗin, amma ko sau ɗaya bamu shiga filin rawarba.
Lokacin da Anum da Nabeelah suka hawo domin yima su Jay liƙi ba ƙaramin faɗuwa gabansa yayiba, itama ɗin dai sai da ta ɗora hannunta a ƙirji alamar gaban nata faɗuwar ya keyi, dama tun sanda su bilkisu suka shigo saida gabanta ya faɗi, jikinta a sanyaye ta liƙa masa kuɗin shi da bilyn suka sauka ko jin surutun da Nabeelah keyi bataiba. Duk bilkisu na kula da yanayin da boss da Anum ɗin suka shiga, dan harta sauka yana binta da kallone.
Tun ɗazun nake wuwwula idanu ko zanga Yah Anuwar, haka kawai nakeji a raina bana son su haɗu da boss yanzu anan, to bammaga su Abdur-raheem bama. Da hannu na yafito Anum, ta taso zuwa gareni. Cikin magana ƙasa-ƙasa nace, “Ina Yah Anuwar?”. Tace, “Tab aishi bayason bidi'a, da wahala idan zaizo wajen nan, amma bakiga yanda mijinki ke kama da Yah Anuwar ba? Nifa dana kallesa gabana sai ya faɗi wlhy bilkisu”. Murmushi na mata da cewa, “Karki damu zamuyi magana amma ba anan ba”. Kanta ta ɗagamin ta koma wajen zamanta. Ina kallon irin kallon tuhumar da boss kemin nai kamar ban ganiba, dan rashin zuwar Anuwat ɗin yasa naji hankalina ya kwanta.
An buƙaci mu fito domin yanka cake. Ganin bai motsaba nima nai zamana, Ina jiyo fitar guntun tsakinsa alamar bayason yi, ni kaina bason nakeba, dan duk a takure nake matuƙa. Sai da Jabeer yazo yayta roƙonsa da ƙyar ya amince muka miƙe zuwa gaban cake ɗin da yay masifar ƙyau.
Mun yanka cake tamkar yanda tsarin yake, ni na fara cira ɗan guntu da zan saka masa a baki cike da jin matsananciyar kunya, dan da ƙyar na iya control ɗin tsumar da jikina keyi nakai hannuna bakinsa, hannun nawa ya riƙe shima muka saka masa gaba ɗaya wanda na ciroɗin kasancewar ɗan ƙaramine a baki. Ina ƙoƙarin janye hannun ya maidashi cikin bakinsa ya tsotse yatsun biyu dana ɗauki cake ɗin dasu suka ɗan ɓaci kaɗan. tafi hall ɗin ya ɗauka. Jinai tamkar na nutse dan kunya.
Shi kam Maimakon ya ciro ya bani kamar yanda nai masa sai ya lakato ya samin a saman hanci kawai dan wulaƙanci, ban gama fita daga takaicin salon nasaba naji saukar numfashinsa kan fuskata, kafin na sami damar magana ya lashe wanda ya lakatamin ɗin da bakinsa. tafin yanzun kam har yafi na ɗazu, dan yanzu harda waƙar Ali jita aka sake saki ta Bilkisu gimbiya. Ƙasa nai niyyar duƙewa dan kunya yay azamar riƙoni jikinsa, sai kawai na ɗora kaina saman ƙirjinsa ina sakin murmushin jin kunya, shima ya ɗaura hannunsa ɗaya saman bayana yana ɗan bubbugawa.
Da ƙyar mc ya samu hayaniyar ta lafa, zamu koma wajen zamanmu aka dakatar damu. Jabeer ya fara bayani kamar haka....
“To jama'a kowa sai ya buɗe idanu domin dai zamuga wasan manya ne, kunsan daga amaryar har angon jarumaine a filin daga”. Ya nuna bindigu guda biyu dake saman wani table duk an buɗesu, “Kuna dai ganin bindiga guda biyu ajiye ko? To munason ango da amarya su haɗasu cikin minti ɗaya yanda suke, wanda ya fara gamawa yana da ƙyauta ta musamman”.
Ni abinma dariya ya bani, hakan yasa naɗan murmusa, batare da tunanin zanyi nasaraba muka ƙarasa, sai da oga Jabeer ya irga uku sannan duk muka fara ƙoƙarin haɗawar cikin hanzari, ina kammalawa nai saurin ɗagowa na nunasa da bindigar fuskata a ɗaure, dai-dai da shima ya nunani data hannunsa fusakarsa babu wasa. .
Wani irin ihu hall ɗin ya ɗauka da tafi. Murmushi ya saki tare da tanƙwa
ɓe hannuna bindigar tai ƙasa ya caɓe cikin hannunsa, nai ƙasa da kaina ina murmushin nima dan naji kunya.
Duk da kusan tare muka gama ni aka bama ƙyautar dai dan nina fara nunasa da bindigar, wajen zamanmu muka koma, muna zama mc ya fara sanar da babban saƙo daga ƙannen ango na musamman Princes, sunce a basu wannan filin su kaɗai, dan ga waƙa ta musamman daga garesu da suka tanada domin amarya da ango. tsit hall ɗin yayi kowa ya buɗe kunne yaji ya kuma ga waɗanan ƙannen ango na musman da kowa ke ƙyautata zaton ƴaƴane daga masarauta.
Matasan samari masu ji da jini a jika da wautar ƙuruciya, Abdul-Raheem, Abdur-rahman, Ameen, suka miƙe, dan da gaske Anuwar bai zoba (su ustazu🤐 lol). sunsha ƙyau harsun gaji cikin shadda kalar sararin samaniya, kansu tsaye mazaunin ango da amarya suka nufa, yayinda Hamisu breaker ya miƙe ya fara raira musu waƙar........
Ashe da rai yake sanki jaruma bada zuciyatai ba, komai ruwa da iska akanki jay baza ya daina kewa ba, tunda dai ya samu zarrar samunki baza ya tanka kowaba, shi baiga mai hararaba, balle ya waiwaya baya. Indai a kankine zaya jure wahalar zuwa garin nisa, da an taɓaki ajirasa danko tilas yazo ya ɗau fansa..........
(Man kaina ya tsiyaye dole mukoma wajen breaker ya ƙarisa🚶🏻😫)
Breaker na fara raira waka sukuma suka farke ƴan dubu-dubu suka fara zubama Jay da bily liƙi, gaba ɗaya hall ɗin ya yamutse da hayaniya, masu ɗaukar video nayi a waya masu hotuna nayi, masu yima breaker liƙi nayi masu yima ango da amarya dasu Abdur-raheem nayi. Daga hakafa aka tafi casun ƙarshe.
Alhmdllh taro ya tashi lafiya kowa cikin farin ciki, anci ansha kowa yayi haniƙan banda amarya da ango, dan ko ruwa bily batasha a wajen nanba har aka tashi, haka shima Jay ɗin.
★★★★★
Ana tashi aka fice dani daga wajen, ganin mun barsa acan ba'a mota ɗaya zamu tafiba kuma farin ciki ya kamani, dan nazata dai masarauta za'a maidani. Sai dai ana sakani mota naji suna faɗin daga nan gidan amarya za'a nufa, idan anje ana kaita mutane su fito dan ba zama za'aiba dare yayi shabiyu saura.
A take zuciyata ta shiga tsitstsinkewa, hawaye suka fara gudu a kumatuna, dan nama manta da wata kwalliyar fuskata, ALLAH bansan wannan shirin suka shirya ba, duk zatona sai gobe idan ALLAH ya kaimu ganin bamuyi sallama da Ummu ba a masarauta. Tun ina kuka a hankali har ya bayyana fili. Lallashina Mah-mah take tayi da sakemin nasiha ƙasa-ƙasa har muka isa, dazan fita a motarma sai da ta sakani nai addu'a, hakama da zan saka ƙafata a falon, kaina lulluɓe yake da alƙyabba banajin komai sai ƙamshin fenta da ya haɗe dana turare dana sabon kaya ya bada yanayi na musamman.
An miƙa amarya Bilkisu ɗakin mijinta, inda basu wani ɓata lokaciba dan basufi mintuna ashirinba aka saka kowa ya fita ya shiga mota, dama wasu sun wuce gida daga wajen dinner, acewarsu zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu sazo suga gidan amarya da ƙyau.
Cikin mintuna ƙalilan gidan yay tsit, motocin duk sun juya, Aunty Batool kawai aka bari, itama zata ɗan zaunane kar abar Bilkisu ita kaɗai kafin Jay ya shigo. Bayi ta shiga ta haɗa ruwan ɗumi da turaruka masu ƙamshi tazo ta tada bily da har yanzu take kuka. “Kukan ya isa haka amarsu, tashi ki daure ki watsa ruwa dan wannan kukan naki nasan ya ɓata kwalliyar”. Ban musa mataba dan inada buƙatar yin wankan kasancewar a yanayin da nake ciki. Alƙyabar ta taimakamin na cire kawai ta fita ta barni, ban zauna jan jikiba dan tace nai sauri boss zai iya shigowa koda yaushe, bai kuma dace ya iskeni a haka ba. Wanka na shiga nayo sauri-sauri na kimtsa jikina na fito, harta kwashe kayan dana cire ta ajiye min riga da zani na atanfa. Shiryawa nai a gurguje, ina kammala saka kayan tana shigowa. Tace, “Yauwa kinga ai hakan yafi, bara aɗan gyara fuskar”. Bance komaiba nidai taɗan shafamin fauda da lipsgloss a baki kaɗan sai turarurruka data fesheni dasu ta bani babban gyale na yafa tare da sake feshe ɗakin da Air Fresheners masu daɗin ƙamshi.
Inda ta zaunar dani ta matso tana murmushi, “To Amarsu angonki ya shigo, bara naje hasu Aliyu can na jirana zasu
saukeni a gida, mu kwana lafiya ALLAH ya huta gajiya”. Hawayen da suka ziraromin na share, nace, “Aunty Batool dan ALLAH ki kwana anan mana, kingafa dare yayi”. Murmushi tayi tana riƙe haɓa, “Inani ina kwana gidan amarya, kinga nayi nan”. Hawaye masu ɗumi ne suka sake gangaromin, na zame na kwanta inayin kayana dan jinake ma duk haushin kowa nakeji, ni banason auren a maidani gidan Dad kawai na cigaba da zamana hankalina kwance.
__________________________
Lokacin da shagali ke gudana a gidan Dad tashin hankali suke fuskanta, dan kuwa dai Salman ne ya gano hotunan biki na yawo a yanar gizo waɗanda ke wajen dinner nata ɗorawa, kunsan mutane da waya a hannu tamkar abu na cizonsune idan suka gani, tun fara dinner ɗin suketa ɗakar hotuna suna ɗorawa wasuma harda videos. Aiko Salman yaci karo da su, shigowa gida yay ya kunna tv dan son ganin wainar da ake toyawa a wajen kasancwwar babu wanda yaje a cikinsu Momy ta hana. Yana zama Aamilah na fitowa, zama tayi suna kallo tare da zagin Bilkisu da Jawaad, hayaniyarsu ta saka Shahudah dake kwance a ɗaki zazzaɓi ya rufe fitowa, aiko tai mummunan gani, dan kuwa dai-dai wajen da Jay ya lashe cake ɗinan daya saka a hancin Bilkisu taci karo dashi, idan ba kallon tsaf kaima wajenba zaka ɗauka kissing ɗin Bilkisu ya keyi. Ƙara kawai ta ƙwalla ta yanke jiki ta faɗi.
Duk kanta sukayi da ihu har Momy Da Dad dake sakkowa daga sama. Girgizawar duniya da sakama Shahudah ruwa taƙi koda motsi, a take hankalinsu ya ƙara kaiwa ƙololuwar tashi suka kwasheta zuwa asibiti likitoci suka rufu a kanta. Har zuwa yanzun dai babu wani bayanin farfaɗowarta kuma.............🤦🏻✍
Duk wanda suka kirani jiya ban ɗagaba suyi haƙuri, ngd sosai kuma da addu'oinku gareni na samu lafiya🤦🏻.
ALLAH ka gafartama iyayenmu🙏🏻😭
[12/30, 6:16 PM] Marsy😘: Page 39
.................Tsaye kawai Jawaad daya shigo yay yana kallon Bilkisu da keta faman shashashar kuka, ya ɗan sauke ajiyar zuciya yana girgiza kansa. Sai ya tuna da randa aka kai masa Shahudah, cikin kayan barci ya shiga ya sameta zaune hankalinta a kwance tana buga game a waya, amma ita jiba duk da ba daga ainahin iyayenta aka rabotaba ta kasa barin kuka. Idanunsa ya lumshe a hankali da ƙara sauke ajiyar zuciya. Ya cire hular da babbar rigan, daga shi sai wando da ƴar cikin da iyakarta rafin cinyarsa. Ƙarasawa yay gaban gadon ya zauna kusa da ita, dauriya kawai yake dan kansa ciwo yake masa shima, hannunta ya kamo batare da yayi magana ba.
Gaba na ne ya faɗi dan banji motsin shigowar kowa ba, gyalen dana rufe har fuskata da shi nai saurin janyewa dan naji tsoro, ya murza hannuna dake cikin nashi yana faɗin, “Tashi zaune, K baƙya gajiya da kukane?”. Yay maganar da kamoni sosai ya miƙar. Koda na tashi zaunen ban yarda na kallesa ba, ya sake murza hannuna da har yanzu yake a cikin nashin. Idanuna naɗan rumtse ina ƙoƙarin danne abinda nakeji.
Jay dake kallonta ya girgiza kansa kawai tare da kai hannu ya janye gyalen data rufe fuska “Jiba yanda wannan kukan ya saka miki zazzaɓi, amma bazaki tausayima kankiba ki barsa haka, indai danni akeyi a ya isa haka na yafe”. Kamar jira take yay magana wasu hawayen suka sake zubowa sharrr. Kai Jawaad ya dafe kawai yana lumshe ido da sake buɗewa a kanta, shi kukan natama ya fara bashi dariya, sudai mata a duniya suyi kuka shine jin daɗinsu, ya sauke numfashi kaɗan yana ƙoƙarin danne dariyarsa. “Tashi muje kici abinci kisha magani sai mu dawo ki cigaba da kukan kamar ƙyafi samun ruwan hawayen sosai ai”. Mamakin maganarsa yasa na ɗago na kallesa. Yace, “To miye na kallon nawa? Ba daɗi kukan yake miki ba?”. Ɓata fuska nayi nasa hannu na goge hawayen. Bai sake cewa komaiba ya miƙar dani tsaye, kunyace ta kamani nai azamar ɗaukar gyalena daya zame zan maida, amma sai ya riƙe, yana nunamin hanya alamar muje. Cikin rawar murya nai magana a karo na farko tun shigiwarsa, “To ka bani gyalen”. Matsowa yay gab dani sosai, hakan yasa naja baya idanuna na sake tara ƙwalla, Hannuna kawai ya kama batare da ya bani gyalenba bai kuma cemin komaiba muka fito falo.
Dukda kaina a ƙasa yake nasan falon nan ya haɗu, ga wani ƙamshi mai kwantar da zuciya na tashi a cikinsa. Cikin kujera ya zaunar dani shima ya zauna kusa dani, ya buɗe filet ɗin dake akan centre table ɗin falon, ƙamshi mai daɗi ya daki hancina, kajine guda biyu da suka sami gashi mai ƙyau da tsafta. Yace, “Kici abinci kisha magani jikinki yayi zafi da yawa”. “Nifa na ƙoshi”. Na faɗa murya na rawa. Banza yaymin ya ɗebo naman da hannunsa ya kawo min a baki. matsar da fuskata nai ina girgiza kaina da sake faɗin, “ALLAH da gaske nake na ƙoshi”.
Shiru yay na wasu sakanni baice komaiba yana kallona, kafin ya ajiye wanda ya ɗebo ɗin ya matsoni sosai, Hannunsa kawai naji saman haɓata ya ɗago fuskata, muryarsa babu alamar wasa yace, “Iyayi zakimin danma kinga zan baki kazan ƙyauta, ALLAH garama kici da arziƙi, bar ganin period kikeyi inada hanyoyin da zan sakaki kukan da kike sha'awar yi mai dalili, idan kuma kinji ƙarya kar kici na nuna miki ainahin kalata da baki saniba”. Tunda ya fara maganar idona ya cika da ƙwalla, na fara ƙyaƙyƙyaftasu.
Fuska Jawaad ya haɗe sosai, dan ya kula sai ya buɗe mata wuta zasu dai-daita, a ɗan kausashe yace, “Miemaa!”. Da sauri na ɗago na kallesa jin yanda ya kira sunan a daƙile. Ya tsatstsareni da idanunsa dake tattare da ɗumbin gajiya, duk yanda naso janye nawa ya hanani. “Na miki kama da abin wasanki?”. Kaina na girgiza masa da sauri. “Inhar kika bari waɗanan hawayen suka zubo ALLAH saikin gane kurenki”.
“Dan ALLAH kayi haƙuri, wlhy nima bada sona suke zubowa ba, wani irin tsoro nakeji a raina, saina dinga ganin kamar gilmawar inuwa kuma idanuna, sannan a ƙasan zuciyata wani irin zafi nakeji, kamin addu'a a cikin ruwa”. Kafeta yay kawai da idanu na wasu sakanni, ya ɗan ciza leɓensa na ƙasa yana jawota jikinsa ya rungume. “Ki daure kinji, ki dinga ƙarfafa zuciy
[12/30, 6:17 PM] Marsy😘: arki, insha ALLAHU babu abinda zai faru ALLAH na tare damu da duk al'amuranmu, kefa jarumace na sani, ko kinaso suci galaba a kanki?”. A hankali na girgiza masa kaina hawayen da nake maƙalewa na sauka masa saman ƙirji, nace, “Insha ALLAH zanyi kamar yanda kace”. Yace, “Yauwa my sweet princess, tashi kici abinci ki manta da komai dake zo miki a rai kinji”.
Munkai tsahon mintuna uku a haka kafin ya ɗagoni, addu'ar yaymin a cikin ruwa kamar yanda na buƙata ya bani na sha, a take na fara zufa duk da kuwa falon fanka na aiki, wata nutsuwace ta fara saukarmin a hankali har naji nauyin da kaina yayi ya ragu sosai, sai ajiyar zuciya kawai naketa saukewa. Da kansa ya bani naman, duk da a kunyace nake matuƙa haka na daure naci, sai dai banci da yawaba nace na ƙoshi, amma ƙin saurarena yayi ya cigaba damin ɗurar dole. Daƙyar na samu ya barni, tashi yay babu jimawa ya dawo ɗauke da ɗan box a hannu, ni dai harma na ɗan fara gyangyaɗi dan sosai naji nutsuwa a daga ruɗanin dana fara shiga ɗazun, dama ga yunwa kuma. magani ya bani na sha.
“Tashi kije ki kwanta dare na sake yi”. Kaina dake a ƙasa na ɗaga masa na miƙe, rashin gyalenan a jiki duk jina nake a matuƙar takure.
Jay ya bita da kallo harta shige, ajiyar zuciya ya sauke a hankali yana jingina da kujerar tare da lumshe idanunsa, tausayi take bashi sosai, kallo ɗaya zakai mata ka fahimci tanada damuwa sosai, yasan zafin rashin iyaye, dan haka yake tausayin duk wanda bai dasu, balle mace ma mai rauni irinta dake zagaye da ruɓaɓɓun dangi gaba ɗaya, garashi dangin uwa na ɗauke masa kewa da damuwa ma. Yanzukam ya samu kwanciyar hankali duk wani motsinta zai kasance a kan idanunsa, a yanzune zai binciko abinda ke binne da iznin ALLAH.
Da wannan tunanin ya tashi ya shiga ɗakinsa, wanka yayi da ruwa mai zafi yay shafa'i da wutiri, maganin shima yasha dan kansa ciwo yake masa sosai dauriya kawai yakeyi.
★★★★★★
Kasancewar maganin da ya bata harda na barci tuni barcin yay awan gaba da ita, kayantane a jikinta bata canjaba, hakan ya saka Jawaad daya shigo tsura mata idanu, komanta ya ƙara canjawa, musamman ma fatarta tai wani irin gogewa sai ƙyalli takeyi, a fuskarta kawai zaka karanci bata da son hayaniya, komai nata tsaka tsakine, hakan yasa ƙyawunta ya kasance mai sanyi, a kallo ɗaya bazaka taɓa ganin sirrin ƙyawunta ba dan batada cika ido irin na Shahudah, yanda take nutsatstsiya haka ƙyawuntama a hankali yake bayyana ga mai kallonta. Tanada kwarjini da cikar haiba na isassun mata masu kamun kai. Yaɗan lumshe ido ya sake buɗewa a kanta, a fili ya furta, ‘Sai jan ajin tsiya da miskilanci ga tsoro kuma ba’. Yay maganar yana nufar akwatinta da aka jiye alamar kayantane a ciki, buɗewa yay, a sama yaci karo da kayan barci har kala uku, doguwar riga da bazata wuce rabin cinyaba, sai riga da wando kala biyu. Riga da wandon ya ɗauka dan sun ɗanfi kauri da mutunci, yasan dai saka matasu akayi daga gani. Zama yay bakin gadon kusa da ita, ya janye bargon data rufama ƙafafunta zuwa ƙugu, zif ɗin rigar ya janye ƙasa bayan ya zame ɗan kwalinta gashinta da yasha gyara yanata ƙamshi ya bayyana.
Cikin barci naji ana ƙoƙarin ciremin kaya, da ƙyar na buɗe idanuna sai naci karo da shi, ai babu shiri na miƙe zaune duk da jikina babu wani ƙarfi, na dafe rigar da har ya ciren hannu guda batare da na yarda mun haɗa ido ba.
Kayan daya ɗakko mata ya ajiye saman cinyarta yana miƙewa, “Ki canja waɗanan kayan dan zasu takuraki sunyi nauyi da kwanciya barci”.
Da kallo kawai na iya bin bayansa ina haɗiye tsoron da saura kaɗan ya hudan zuciya, gaba ɗaya mamaki al'amarinsa ke bani, wai dama haka yake boss ɗinan ashe, yanzu daban farkaba nufinsa shine zai sauyan kayan? Tabɗi wlhy daya gama dani kuwa. Saida yaje ƙofa zai fita sannan ya juyo yana kallona, “Idan kika bari mintunan dana ɗiba miki ya cika baki tashi kin sauya kayan nanba, hummm..” yay maganar murya ƙasa-ƙasa amma daɗan karsashi sannan ya fice.
Kamar nayi kuka haka naji, na kalli kayan barcin da ya ajiyemin tare da ɗag
asu, riga ce ƙarama dan ko ɗuwawuna bazata saukaba, hannunta ɗan si
[12/30, 6:18 PM] Marsy😘: riri sai wando da nasan iyakar gwiwa zai tsaya min. Sanin halinsa ya sakani miƙewa ina sauke ajiyar zuciya, dan nasan zaiyi duk abinda yace ɗin, canja kayan nai ina addu'ar ALLAH yasa bazai dawo ba dai. Ina kammalawa na kwanta. sallamarsa ta daki dodon kunnena.
Sosai na waro idanu waje naja bargo na rufe duk jikina, ganin ya zagaya ya kwanta ta ɗayan gefen Cikin in ina nace, “A a..nan za.. ka kwanta?”. Ba tare daya kalleniba yace, “Uhmm”. Baki na tura ina lullumshe idanu, Cikin ɗan haushi-haushi nace “Ammafa kowa ance da ɗakinsa ai”. Ganin ya juyo yana kallona, nai saurin jan bargon na rufe har saman kaina da shi. Murmushin da baiyi niyyar yi bane ya suɓuce masa, ya matso inda take sosai tare da ɗaga bargon ya shiga shima, saka hannu yay ya yaye na saman fuskartata tare da ɗora kansa saman filon data kwanta suna fuskantar juna, tuni jikinta ya fara tsuma, ta kuma rumtse ido kam, fuskarta duk ta bayyana tsoronta a fili. Hannunsa ya ɗora saman kanta ya shafa gashinta dake kwance luf yasha gyara tun daga goshinta har inda yake ɗaure da ribbon, a hankali ya zame ribbon ɗin gashin ya warware. Ƙoƙarin danne dariyar dake neman kufce masa ya keyi. Tsabar yanda take a tsorace har bugun zuciyarta yanaji dan suna gab da junane sosai, hannunta data sakane ta matse ƙirjinta yay musu kantanga. Da biyu ya tura yatsun hannunsa cikin gashin nata da wani irin salo.
“Na shiga uku ni balki”. Ta faɗa babu shiri muryarta na rawa tamkar zata fashe da kuka tare da ware idanunta gaba ɗaya kansa. Jay daya kasa riƙe dariyarsa yanzun kam ya saki lallausan murmushi da ɗora goshinsa saman nata, “Kinsan baki da ƙarfi miyasa kika nemi faɗan?”. “To yi haƙuri dan ALLAH” ta faɗa tana son jan jikinta baya. “Daga baya kenan yarinya” ya bata amsa shima da sake matsota jikinsa sosai ya matse yanda tilas ta janye hannunta data kare ƙirji da shi dan taji numfashinta na neman barin ƙirjinta. Jawaad kam da yasan da biyu ya matsetan dama ya sake sakin murmushi da manna dukan fuskarsa akan tata har labbansa na gogar nasa. Cikin raɗa-raɗa yace, “Nifa idan aka takaloni faɗa banajin bari saina maida raddi”. Hawayen da bily ke maƙalewane suka zubo mata a kumatu, tace, “To ai na baka haƙuri ko”. “Ni kuma sai ban haƙura ba ai hajjaju” yay maganar da manne laɓɓansu yanda babu damar sake magana ma. Duk yanda take mutsu-mutsu ya hanata kowacce irin damar da take buƙata, karan farko a rayuwarta da hakan ta faru da ita, abinda takema kallon ƙazanta idan ta gani a film yau shine ake mata a zahiri, ba kowa ke matanba kuma sai boss, innalillahi...... itakam taga takanta dama haka mutuminnan yake.......?
(To nima dai bansan hakan yakeba bily sai yanzun, duk zatona waliyyine fa kamar yanda Jabeer ya faɗa😂🚴🏼🚴🏼😜).
★★★★★★★★★
Barcin da suka gaza samunyi da wurine ya ja musu makara, Jay ya janye bilkisu daga jikinsa da ƙyar ya tashi zaune bayan ya kunna fitilar ɗakin, hannunsa dafe da kansa da har yanzu yake jingim alamar ciwon bai saukaba gaba ɗaya, bargon ya gyara mata yana kallon fuskarta da duk hawayen da tai suka bushe, idanunsa yaɗan lumshe yana mai tunanin yanda zasu kwashe da wannan uwar tsoron randa yace mai gaba ɗaya zaiyi, a daren jiyanma ba wani abun kirki yay mataba amma tabi ta ishesa da kuka. Numfashi ya sauke da sauka a gadon. Yasan tilas ne yay wanka kafin yace zaiyi salla, dan haka ya fita zuwa ɗakinsa a gaggauce kafin a tada sallar.
A hankali na buɗe idanuna dake jingim da barci nabi bayansa da kallo harya fice, tunda ya motsa nima na farka, sai dai matsananciyar kunyarsa da nakeji bazata barni na nuna masa na farka ɗinba, abinda ya faru daren jiya ya shiga rige-rigen dawomin a zuciya, hannuna na ɗora saman laɓɓana da sukasha gurza a hannunsa, da wanine ya cemin abinda yay a daren jiya zai iya wlhy sai na ƙaryata, kamar ba boss ɗin nanba na office gwanin hayaƙi da mazurai, sai yaso kaga walwalarsa balle akai ga dariya, yanda yake mara hayaniya a zahiri haka yake a komaima nasa babu hayaniyar, ajiyar zuciya na sauke murmushi na suɓuce mani, tashi nai nima dan ina buƙatar gyara jikina dukda barcin da nakeji na fitar h
[12/30, 6:19 PM] Marsy😘: Billy Abdul:
ankali. Gadon na gyara sannan na nufi bayi, wanka nai da ruwa mai zafi ina addu'a a raina ALLAH yasa kar jinin nan ya ɗauke yau, dan nasan a ƙa'idar kwanakin da nakeyi zuwa rana zai ɗauke, dama yanzun kaɗanma na gani a jikin pad ɗin amma bai ɗaukeba, to na tabbata zuwa azhar bazan gansaba. Ina fitowa doguwar riga na zura na koma gadon dan har wani jiri-jiri nake gani saboda barci, yau ko azkar na kasayi, aiko kafin na farga na lula.
Ɓangaren Jawaad ma ana idar da salla da ƙyar ya daure yay azkar ɗin, yana kammalawa ya nufo gida, sama-sama suka gaisa da maigadi ya shigo gidan, yasan Bilkisu barci take tunda dai ba salla zata tashi yiba. Ɗakinsa ya shige, jallabiyar jikinsa kawai ya zare ya haye gadonsa shima sai barci.
_________________________________
Da ƙyar likitoci suka samu Shahudah ta farfaɗo kusan ƙarfe biyun dare, ba ita kanta dake cikin mawuyacin halinba harsu kansu sunyi matuƙar jigata, gasu Dad duk sunbi sun ruɗa musu asibiti sai kace ran ƴar tasu a hannunsu yake. Aiko koda ta farfaɗo allurar barci kawai sukai mata ta sake komawa, suna fitowa su Momy dake wujiga-wujiga suka yo musu caa da tambaya. A yanzu bazasu iya wani zaman musu bayaniba dan haka sukace kawai ta farfaɗo.
Koba komai su Dad sun sami kwanciyar hankali, dan shi kansa ɗazun harda hawaye yayi, baisan irin ƙaunar da yakema Shahudah ba a rayuwarsa, musamman ma a rin wannan lokacin da wani gagarumin abu mai taɓa zuciya da tashin hankali keson faruwa da ita, sam zuciyarsa bazata iya ɗaukaba gaskiya, bama zai yuwuba, dolene ya nema mafita kafin lokaci ya ƙure. Shahudah sa, ɗiya mafi soyuwa a zuciyarsa, kai ina bazai yuwuba, dolene yasan mai yuwuwa, ya yarda ya rasa komai akan Shahudah wlhy.
Haka suka kwana a asibiti hankalinsu tashe har ALLAH ya wayi gari lafiya.
Misalin takwas na safe Shahudah ta farfaɗo bakinta na kiran sunan Jawaad, kuka take rurus da roƙon a kira mata Jawaad ya saki Bilkisu inba hakaba zata kashe kanta.
Kasancewar har mama Atika da bama lafiyar ƙafane da itaba tazo asibitin itama tunda safe suka rufu kanta suna lallashi da bata baki akan cewar ai Bilkisu bata tareba wai, kuma ta kwantar da hankalin Jawaad zaizo anjima kaɗan. Sam taƙi sauraren kowa, daga ƙarshe dai dole Doctor ya sake zuwa yay mata allurar barci mai ƙarfi dan jininta yay masifar hawa.
Doctor ya kalli Dad da Momy dake zaune a gabansa bayan ya gama rubuce-rubuce a takarda. Momy ta sake share hawayen da tun ɗazu ke mata ambaliya a saman kumatunta, “Doctor ka sakamu a duhu, kace muzo kuma kaƙi kace mana komai, mike faruwa ne da yarinyarmu?”. Numfashi Doctor ya saki yana goga biron hannunsa saman gira, kafin ya sake ɗagowa ya kallesu. “Maganar gaskiya bazan ɓoye mukuba yarinyarku na cikin haɗari, jininta ya hau ƙololuwa kasancewar tana ɗaukar abu da girma fiye da kima, wannan shine karo na biyu datai irin faɗuwar da ba'ason duk mai hawan jini irin nata da yi, dan kai tsaye take kaisu ga paralysis, yakamata ku daure ku sama mata abinda ta keso koku ɗauki ɗammarar ƙwantar mata da hankali ta hanyar data dace. sannan akwai wani ciwo da muka gano tana dashi wanda ita kanta da wahala ace tasan a kwashi, dan baikai lokacin da har yanzu zai fara ciwon da zatajisa a jikinta ba”. Cikin matsanancin ruɗani Dad da Mom ke tambayarsa wane ciwo ne?. Kafaɗunsa yaɗan ɗage yana sauke numfashi, “Karku damu bamai ɗaga hankali bane can sosai, domin ko babu ciwon ai sai ALLAH ya ƙaddara mutum zai haihu a duniya dama. Alamu sun nuna yarinyarku ta taɓa cire ciki, bincikenmu da hasashenmu ya nuna mana kuma kamar wata allura tayi yayin zubarwar, a zahiri wannan allurar tana aiki fiye da zato ga mace mai son zubda ciki, dan a ƙanƙanin lokaci take rugurguje ɗan tayin dake mahaifa ta kuma ɓarosa waje, sai dai idan akai rashin sa'a da yanayin jinin mutum takan haifar da matsala a mahaifa daga baya musamman idan anyita babu ƙa'ida, sai bayan wasu shekaru kuma ake gani illar da taima mace, wata macen haihuwace bata sakewa kwata-kwata, wata kuwa ruɓarmata da mahaifar takeyi har sai an cire mata, to Alhmdllh ita duk hakan basu
kasance a gareta ba”. Ajiyar zuciyar Dad da Mom suka sauke lokaci guda, Doctor ya cigaba da faɗin, “Sai dai wani ƙari ya fito a bakin mahaifar, a hankali kuma zai rinƙa girma inhar ba'ai mata aiki ba, zaita girmane cikinta na girma kamar mai ciki, idan tsautsayi yasa ya fashe kuma sai ta ringa zubar da ruwa mai wari”. Idanu a waje cike da tsoro su Dad suke kalon Doctor, cikin rawar baki Dad yace, “Likita amma ai kace ana cirewa?”. “ƙwarai Alhaji ana cirewa, sai dai itamafa cirewar nada nata haɗarin, dan zaku iya rasata a dalilin cirewar, idan kuma an dace za'a cire lafiya ta tashi”. Kuka Mom ta fashe dashi iya ƙarfinta, shi kansa Dad dauriya kawai yakeyi, amma kallo ɗaya zakai masa ka fahimci tsagwaron tashin hankalinsa. Murya a sanyaye yace, “Wannan itace kaɗai mafitar Doctor?”. Doctor yace, “Eh to akwai wata mafitar bayan wannan”. Cikin rawar jiki Mom tace, “Wacece Doctor faɗa mana ita dan ALLAH”. “Hajiya mafitar ƙarshe itace shan magani, zamu iya bata maganin da zata shashi a sati sau ɗaya, ya kama a wata guda sau huɗu kenan, sai dai yanada matuƙar tsada, sannan zata cigaba da shansane har illa masha ALLAH, amfanin shansa anan bazai bar wannan ƙarin ya cigaba da girmaba, sannan bazata sake samun cikiba sai abinda ALLAH ya ƙaddara wannan ikonsane da rahamarsa idan yaso, nidai iya hasashena na faɗa sanin gaibu kuma sai ALLAH”.
________________________________
Knocking ƙofa da akeyine ya saka Jawaad farkawa, guntun tsaki yaja yana buɗe idanunsa akan agogon ɗakin nasa, ƙarfe goma harda mintuna sha bakwai, ya ɗan lumshe idanu ya sake buɗewa kafin ya tashi zaune da ƙyar. Lallai yasha barci sosai ashe. Sauka yay daga gadon ya nufi toilet, fuska ya wanko ya kuskure baki ya fito, jallabiyar da yaje masallaci ya ɗauka ya zira.
A falo suka haɗu da Bilkisu wadda itama bugun ƙofarne ya tasheta, nbatare da ita tama gansaba ta buɗe ƙofar. Nabeelah ce ɗauke da basket.
Murmushi nai mata ina matsawa na bata hanya ta shigo tana ƴar dariya damin shaƙiyanci. “Ta wajena naga duk kinyi wani laushi, ko Yayanmu ya angwanc..........”
Jin tayi shiru tare da jan biriki bata ƙarasaba ya sani maida ƙofar na rufe na juyo. zaune yake saman kujera ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya yay bala'in ɗaure fuska da tsatstsareta da idanunsa masu ban tsoro ga marajin magana. Ba itaba hatta ni saida na tsume, dan a bazata na gansa tunda sanda na wuce ban ganshi a wajenba.
Yaƙi cewa komai kuma yaƙi daina kallonta, a hankali takai ƙasa ta durƙusa kamar wata munafuka, muryarta har rawa take wajen faɗin, “Yayanmu ina kwana”. Bai amsa mataba, sai sake ɗaure fuska da yay yace, “Ƙarasa abinda kika fara”..................✍
ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.
SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.
HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO
MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.
MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.
BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....
abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.
Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899
sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.
Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300
Sai kunzo😍😍😍😘.
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
Typing📲
ƘWAI cikin ƘAYA!!
Bilyn Abdull ce🤙🏻
BOOK TWO
Page 40
...............Sosai Nabeelah ta waro idanunta da suka cika da hawaye tana haɗe hannayenta waje guda alamar roƙo, “ALLAH yayanmu ni babu abinda zan faɗa, dan ALLAH kayi haƙuri”.
“Kinsan ALLAH idan kika bari harna miƙe kanki sai jikinki yay masifar yin tsami”. Yay maganar muryarsa babu alamun wasa. A mamakina sai naga Nabeelah ta fashe da kuka tana ɗanja baya, na kallesa da nufin bashi haƙuri duk da nima a tsoracen nake sai na ga ya miƙe, ai kafinma nace wani abu sai hango Nabeelah nai ta kwasa da gudu ta fice. Yanda yaja birki tare da riƙe ƙugu yana kallontane ya sakani kasa danne dariyata, hannu nasaka na toshe bakina tare da saurin kauda idanuna ganin ya kalloni.
Jawaad yay ƙwafa yanabin Bilkisu da kallo, “Ke kuma dariyan na miye to?”. Kallonsa nai da sauri ina ƙoƙarin haɗiye kayata amma na kasan, dan fuskata kawai zaka kalla kasan dariyar taƙi haɗiyu wa, harar daya ballo mince tasa nai niyyar barin masa falon naje nai dariyata a ciki. Caraf naji an cafkomin hannu da faɗin, “Dariya ko? To bara na huce a kanki”. Tsaf na haɗiye dariyar na koma zare idanu, cikin marairaice fuska nace, “Nifa ba dariya nayiba”. “To mi kikayi?”. Yay maganar da tsatstsareni da mayun idanunsa. Sosai kunya ta lulluɓeni nai ƙasa da kaina ina ɗan waige-waige, nima na Nabeelah nake tsarawa na fece kawai. Kamar ya fahimci abinda nake tsarawa a raina yace, “Kema guduwar zakiyi? Itama ɗin ba ƙyaleta naiba zan sameta har gida sai naci ƙaniyarta na gasa mata baki tunda ita magananniyace”. Murmushin da ban shiryaba ne ya suɓucemin, nace, “Yi haƙuri to niba baƙuwar zafi bace wlhy”. Kafin yace wani abu wayarsa ta shiga ring, kallon wayar duk mukai da mamaki, da alama ma anan ya mantata ta kwana ko?, hannuna dake cikin nasa na janye na ɗakko masa wayar da rabinta ya shige ƙasan filon kujera. Ban tsaya kallon ko wanene ba na kawo masa cikin.
Amsa yayi yana zama, ni kuma na juya na ɗauki basket ɗin da Nabeelah ta kawo wanda ko ba'a faɗaba kasan breakfast ne a ciki. Harna nufi D/table naji ya kirayi sunana, juyowa nai ina amsawa da “Na'am”. Dai-dai zai saka wayar a kunnensa alamar wancan kiran ya katse shi ya sake kira. Yace, “Kawomin tea, karki saka suga da yawa”. Da “to” na amsa kawai na ƙarisa na ajiye basket ɗin saman dani. Kicin ɗin na nufa ina ɗan murmushi da yaba ƙoƙari da sadaukarwa irin ta waɗanan bayin ALLAH, babu dangin iya babu na baba suka kashemin waɗanan kuɗin? Ba ƙaramin mutsuwar tsaye naiba da ganin yanda kicin ɗinan yay mugu-mugun haɗuwa, ni balki ɗiyar baba makaho ce da wannan gidan matsayin matar cikinsa? Sai kawai naji ƙwalla sun cikamin idanu, na shiga maimaita kalomin Alhmdllh a zuciyata ina hawayen zuci. Fasalta muku yanda kicin ɗinan yake ai ɓata lokacine, abin mamaki da al'ajab harda kayan abinci da malam bahaushe ke kira da gara, dai-dai da magi wannan sakarai an ajiye min shi. Sai dai kuma babu kayan tea ɗin da yace na haɗa masa, iya dubana banga koda lipton ba sai kayan ƙamshi kawai da abinda ba a rasaba, komawa nai da niyyar faɗa masa ban ganiba amma na iske yana waya da ransa a ɓace. “Uncle Please ka ƙyalesu ni babu abinda zanzo na musu, ina ƙoƙarin danne duk abinda suke son takalata dashi kawai amma na kula neman kaini maƙura sukeyi akan shirmensu”. Yaɗanyi shiru alamar saurare, hakan yasa na juya zan koma dan na bashi damar gamawa amma sai naji takunsa a bayana, baimin maganaba yazo ya wuceni, ganin hakan yasani bin bayansa, drawer saitin fridge ya buɗe ya nunamin. Kaina na jinjina masa na ida shiga ciki shi kuma ya fice yana cigaba da wayarsa. Bani da matsala da kayan ƙamshi dan duk gasunan a robobi harma da ganyan shayi masu daɗi da Umm-Aban dama tace zata haɗa min saboda ta lura inason shayi. Tukunya na ciro da dama an fiddata a kwalinta na ɗauraye na zuba duk abinda zan buƙata na ɗora saman gas da dama an haɗashi shima. Komawa nai na ɗauki plate da flask da kofi na ɗaurayesu tsaf, cikin mintuna ƙalilan na kammala na fito da komai na ajiye a dani ɗin, sannan na koma na ɗakko tea ɗin dana haɗa a kofi na ɗaura saman ƙaramin tire na kai masa falon dan har yanzu wayar yakeyi. Yanda yake kallona harna ajiye tiren a centre table duk sai naji na takura, nuni yaymin da in bashi, ɗauka nai na miƙa masa, ya ɗan lumshemin idanu alamar “thanks”. Bance komaiba nabar wajen dan sonake nai wanka.
Saida na gyara gadon yay tsaf sannan na shiga wankan, wanka nai haɗe da wankan tsarki dan mai jar motama ya ɗauke tunkan azhar ɗin da nake hasashen, zaton babu mai shigominne ya sakani fitowa daga ni sai guntun towel ga gashi a jiƙe, sai dai inata ƙoƙarin tsanesa da ƙaramin towel dake a hannuna. Ina ƙarasawa gaban mirror yana shigowa da sallama ciki-ciki alamar ransa a ɓace yake har yanzun, saida naji tamkar na ƙwala ihu, na ɗan wawwaiga banga wani abu dazan iya ja na rufe jikina da shiba, haƙura nai kawai na ɗan ɗago na kallesa cikin dauriya ina faɗin, “Nazo na baka abincin ɗinne?”. Shirun da naji yayi bai amsaba yasa na ɗago kaina na dubesa, idanunsa nakan gashina ko ƙyaftawa bayayi. Sake maimaita masa tambayar nayi. Ya janye idonun nasa da juyawa zai fita yana faɗin, “Ki gama nima zanyi wankan ne”. Binsa kawai nayi da kallo dan na lura ransa a ɓace yake, ‘Komi akai masa kuma?’ na faɗa a fili batare da inada mai bani amsata ba. Gudun karya sake shigomin yasa nai shiri a gaggauce cikin sket da riga na shadda orange color. Ni kaina nasan sunyimin ƙyau dan kamar an haliccesune a jikina sunmin ɗam dan telan ya iya ɗinki, kaina nakeson busarwa amma abin haushi babu wuta, a haka na gyarashi bayan na tsanesa sosai babu ruwa, ɗauresa nai da tunanin ƙila su kawo wutar anjima tunda naga anguwar kamar suna samunta sosai. Bawata kwalliya nai da yawaba amma fuskata tayi fayau, na saka ƙaramar sarka sannan na feshe jikina da turare sosai, kowa ya ganni yaga amarya da gaske, farin gyale na ɗauka shima na saka turare sannan na yafa na fito falon. Gidan tsaf yake babu wani datti, hakan yasa kawai na ɗauki fresheners da turare mai ƙamshi haɗin gida na fesa iya falon nan kawai. Ina cikin fesawar ya fito.
Jin Motsinsa a bayana ya sakani waigawa, kwalliyar tasa ta sakani shagala a kallonsa batare dana fargaba, shaddace ƴar ubansu golden color ya saka, sai maiƙo take da ɗaukar ido, ta samu nutsatstsen ɗinki na zamani da ya fiddo cikar zatinsa mai tabbatar dashi jinin hausawan usul harda su hula......
Saukar iskar da naji a cikin idanuna da ƙamshi Mouth freshener ɗin da ya saka ya sani dawowa hayyacina daga sakin layin da nayi, nai ƙasa da kaina dan naji kunya.
“Gulmammiya kinaso kina kaiwa kasuwa, na miki ƙyaune?”.
Ɗan kallonsa nai na juya ƙeya nace, “Kaɗan”. Murmushi ya saki har inajin sautinsa, ya ɗaura hannunsa saman haɓata ya maido fuskata inda yake, “In har da gaske kike ki kaleni cikin ido kice kaɗan nai ƙyau”. Hannu nasa na rufe fusa da sake juya masa baya ina murmushi. “Baki da gaskiya kenan”. Yay maganar kusa da kunnena yana zame gyalen dana yafa. “Malama niba surukinki bane ai, muje kiga gidanki”.
Shine yaymin rakkiya lungu da saƙo na cikin gidan har ɗakinsa da harabar gidan, gaba ɗaya gidan ya canjamin tamkar ba wanda na taɓa zuwa ɗin nanba, an gyarashi sosai ya canja kamanni. Sai da muka gama zagaye ko ina muka yada zango a wajen cin abinci. Nidai kasa sakewa nai naci saboda yanda yay mugun tsatstsareni da idanu, duk sanda zan ɗago sai naga idonsa a kaina. Da dai na gaji saina kumbura masa fuska, “Nifa wlhy ba television bace ba”. Bakinsa ya taɓe baice dani komaiba bai kuma bar kallon nawaba har muka gama. Ɗakinsa ya koma nikuma na tattarr wajen, na fito masa da abincin maigadi da tunkan mu fara cin namu ya sakani na zuba shima ya fito, agogonsa da links ya miƙomin tare da miƙamin hannunsa. Dukda inajin kunya haka na saka masa links ɗin sannan na saka masa agogon. “Thanks” ya faɗa a hankali yana ɗagemin gira ɗaya.
Kafin nace wani abu maigadi ya doka sallama a ƙofa, kallon ƙofar mukai gaba ɗaya amma shi ya amsa masa, ya amshi kular hannuna tare da nufar ƙofar ya buɗe.
Maigadi ya gaidasa da faɗin, “Alhaji kanada baƙone”. Da ɗan mamaki Jawaad yace, “baƙo kuma malam gambo?”. “Eh Alhaji, harzan masa ƙaryar baka tashiba saina fahimci amatse yake da son ganinka gaskiya, kuma kamar baƙon mai muhimmanci ne”. “Okey, to ga abincinka ina zuwa”. Amsar kular yay dayi godiya ya koma, Jay kuma ya maida ƙofar ya rufe ya dawo inda yabar Bily tsaye tana kallonsu. Wuceta yay ya ɗauka key ɗin motar dake kan centre table, “Bara naje na gaida Alhaji Babba daga nan na leƙa asibi wai Hudah aka kwantar”. “Ya salam” na faɗa cikin damuwa, “Miya sameta kuma? Dan ALLAH kaje dani”. Kaɗan ya kalleni ya ɗauke kansa, “Kimata addu'a daga nan ya isa, kokin taɓa ganin amarya ta fita”. Cikin shagwaɓar da bansan inada itaba nace, “Toni tsoro nakeji wlhy”. “Tsoro kuma?” ya faɗa yana kallona. kaina na ɗaga masa batare dana yarda mun haɗa ido ba. Jin yaƙi magana yasa na sake kallonsa, sai naga niɗin yake kallo ashe shima. “ALLAH na kula kinma rainani” yay maganar yana matsoni, baya nai saurin ja, amma duk da haka saida ya riƙoni. Cikin magana raɗa-raɗa yace, “Ke komai abin tsorone a wajenki halan?”. Nace, “To inason naje naga aunty Shahudah ne”. “Uhhyim shine zakimin ƙarya? to babu inda zakije, ki jira ƙawayenki na nan zuwa zan dawo bazan jimaba dan zanyi magana da ku”. Saurin kallonsa nai da mamaki nace, “Su Ummie?”. Kansa ya ɗagamin. “Miya faru?”. “dan na dawo zakiji ai, ana jirana yanzun”. Ya ƙare maganar da ɗaura bakinsa saman nawa babu zato. ‘Ya salam’ na ambata a zuciyata tsigar jikina na tashi ga yanayin da nakeji na neman tasomin dukda dai yanzuma da sauƙi sosai ba kamar da ba. Sai da yaja kusan minti biyu kafin ya saki bakin ya sumbaci goshina. “Saina dawo”. Kaina kawai na jinjina masa dan na kasa kallonsa. A hankali na furta, ”ALLAH ya tsare”. Inajin yana murmushi. Nidai ban kallesanba har ya fice.
Sassanyar ajiyar zuciya na sauke tare zubewa a kujera daɓar na dafe kaina, wlhy abun mamaki yake ban, boss fa! Kai rayuwa bata rabo da abubuwan al'ajabi. Naja kusan mintuna biyar a haka kafin na miƙe naje ɗakinsa dan na gyara. Sosai ɗakin yake ƙamshin turarensa daya fesa yanzun, tsaf na gyarashi na saka fresheners sannan na koma kicin na ɗauraye kwankina da mukaci abinci shima naɗan gyara abinda bai minba.
Koda Jawaad ya fito sai ya iske baƙonsa cikin rumfar bunun dake harabar gidan maigadi ya kawosa, ƙarasawa yay yana faɗin, “Ai bammayi tunanin kai bane Munkaila”. Baƙo mai suna Munkaila daya miƙe domin girmamawa ga Jay yay murmushi, “Nine wlhy Oga barka da fitowa”. “Yauwa sannunka da zuwa” Jay ya faɗa yana zama tare da masa nuni daya zauna shima. Cikin girmamawa Munkaila ya gaishe da Jay kasancewarsa ogansa, file ɗin gabansa ya miƙa masa yana faɗin, “Oga dukkan abinda kake buƙata gashi, harma da abinda bakaceba dukna haɗo maka”. Kai Jay ya jinjina masa da faɗi, “Sannu da ƙoƙari” yana buɗe file ɗin. Da hotuna ya fara cin karo waɗanda sukai masifar ɗaure kansa dan harda Alhaji baba tare da mata biyu wadda ɗaya a ciki takasance kakarsace mahaifiyar su Ummah da shima a hoto ya santa, kallon Munkaila yay kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya maida file ɗin ya rufe.
Munkaila yace, “Oga akwai matsala ne?”. Kai Jay ya girgiza masa, “Babu matsalan komai, yaya maganar wancan aikin?”. “Shima ina gab da kammalawa oga, saboda naga ka matsu da wannan ma shiyyasa na dakata da wancan”. “Shikenan kayi ƙoƙari shima ka haɗamin shi a satin nan, ga wannan ka saka mai nima nayi aljihun nawa yay ƙasa”. Godiya Munkaila yayi sosai sannan suka fito a rumfar. Jay ya shiga mota shikuma ya fice dan mashin ɗinsa na daga waje bai shigo da shiba.
★★★★★
Fitar jawad babu jimawa su Ummie suka isa gidan amarya Bilkisu, Ummie, Zuhrah, Rebecca, Nazifa. Duk da jiya suka rabu da juna tuni suka haukace da ihun murnar ganin juna, suka saka bily tsakkiya da tsokana kala-kala, tun tana musu shiru dai harta koma ramawa itama dan taga shirun nata bazai sa su barta ba.
_________________________
Asibiti yay niyyar fara zuwa saboda Uncle Sulaiman daya tilasta masa yaje, to amma wannan bayanan da Munkaila ya kawo masa yanzun sun ruguza komai, burinsa kawai ya dangane da gidan Alhaji Babba. A waje yay fakin motarsa ya shiga shi kaɗai, Alhaji babba na zaune a falo hannunsa riƙe da Jarida Jay ya shiga da sallama. Ɗagowa yay yana kallonsa fuska ɗauke da murmushi, cikin tsokana yace, “A lallai wannan angon da gaske bahausa ya aura, ashe ba gidan jiya ya komaba”. Jay dake murmushi ya girgiza kai kawai yana zama, “Wannan itace tarbar da zakamin ma na baro matata na taho ganinka da farar safiyar nan”. Alhaji babba yay dariya irin tasu ta manya yana faɗin, “Ja'iri kenan bakifa ya buɗe”. Gaidashi Jay yayi yana murmushin tsokanar da kakan nasa ke masa. Sai da suka kammala gaisuwar da tambayar lafiyar juna da amarya Bilkisu kafin jay ya buɗe file ɗin da Munkaila ya kawo masa, hotunan ciki ya fiddo gaba ɗaya ya miƙama Alhaji Babba shi kuma ya maida hankali ga duba bayanan cikin file ɗin.
“Sa'adatu! kuma?”. Alhaji babba ya faɗa da alamun bazata. Kallonsa Jay yayi amma baice komaiba. Alhaji babba yace, “Jawaad kana nufin matarka nada alaƙa da wannan ta hoton?”. Zama Jawaad ya gyara sosai yana maida dukkan hankalinsa ga kakan nasa, “Baba abinda bincike ya nuna min kenan, sai dai nima kaina a kulle yake musamman da ganin hotonka a tsakkiyar mata biyu bayan mata ɗaya nasan kanada ita kafin Mama Maryam”. Shiru Alhaji babba yay na wasu mintuna kafin ya sauke ajiyar zuciya, yace, “minene sunan mahaifin nata?”. “Adam makaho” Jay ya bashi amsa a taƙaice. Nanma shiru Alhaji babba yay na wani ɗan lokaci yanata faman jinjina kai da murmushi a fuskarsa kafin yace, “Abin akwai ɗaure kai da ban al'ajabi”. Jawaad yace, “Miyasa zai ɗaure maka kai bayan na fahimci kasan wani abu”. Murmushi Alhaji babba yayi mai ciwo da sake maida hankalinsa ga hotunan guda biyar, ɗaya shine da mata biyu a jiki sai jaririn yaro da alamu suka nuna ranar sunansa aka ɗauki hoton ma ƙila, ɗaya kuma matane da miji matar gurguwa sai mijin da alamu suka nuna makaho ne, sai hoto na uku jaririyace nannaɗe cikin farin showal da gani kaga sabuwar haihuwa, hoto na huɗu, mata da minjin nan ne da jaririyar, na ƙarshema dai mata da mijinne sai bilkisu a tsakkiyarsu da bazata wuce shekaru goma sha biyarba. Ya ajiye hotunan yana kallon Jawaad da ƙyau. “Akwai abinda ku baku saniba Jawaad, mahaifiyarka cema kawai zata iya sanin wani abu itama ba duka ba dan a labari ta sani. Ba Amina da Maryam kawai na taɓa aureba, na taɓa auren wata matar mai suna Sa'adatu. Kafin aurena da Amina Sa'adatu itace yarinyar da naso aura dan itace muke soyayya amma iyayena suka ƙi, bakomai ne ya sakasu ƙinba sai kasancewar Sa'adatu batajin magana, duk da yarinyace da bata wuce shekaru goma sha biyarba a lokacin mutane kan jefeta da kalmar ƙarancin tarbiyya, Sa'adatu ta tashi a gidansu bata da uwa a hannun kakarta ta tashi, hakan yasa ta tashi sangartacciya da batajin ƙwaɓa, a dalilin ɗan karatun da aka sakata na boko wanda a wancan lokacin iyakamu maza kawai keyinsa yasa idanunta buɗewa dan ita kaɗaice mace a cikinmu, Sa'adatu ji take tafi kowa a ƴammatan yankinmu dama gata ƴar gata kuma babanta shine maigari, ALLAH ya jarabceni da sonta fiye da yanda kake tunani har takai naima iyayena maganar aurenta. Amma sai mahaiyata tace sam batasan wannan zanceba tama rigada tamin mata Amina, na ɗaga hankalina matuƙa a lokacin amma dole na haƙura muka rabu da Sa'a ina kuka tanayi. Hakan ya zafi kakarta har tayi alwashin sai nayi nadamar yaudarar jikarta da nayi. Babu wanda ya ɗauki alwashinta wani abu aka ɗauramin aure da Amina ta tare. Banason Amina amma ita tana sona kuma mace ce mai haƙuri da kawaici, a zamanmu tasha wahala kafin na ɗan fara fuskantarta, aurenmu da Amina yakai shekara shida amma bata taɓa ko ɓariba, a wancan lokacin dan mace takai shekara goma ma bata haihuba babu mai damuwa da hakan balle ya zama abin magana shiyyasa nima ban taɓa damuwaba. Zuwa lokacin Sa'a itama tayi aure amma ba a wannan garin namu ba, wani ɗan uwanta mai kuɗi aka aura mata, sai dai kuma hankalinta na kaina dan haka shekararta uku ta kashe auren ta fito da yarinyarta guda safara'u, a lokacinfa na tsaya kai da fata saina auri Sa'a dan sonta na nan daram a raina. Zakasha mamaki idan nace maka Amina itace taita kai kawo ga iyayena har mahaifiyata ta amince na auri Sa'a. A farkon shigowar Sa'a gidana ta kwantar da kanta tanama Amina biyayya kamar gaske, amma tunda muka wayi gari ta samu ciki sai abubuwa suka fara canja salo, raini da wulaƙanci babu wanda take ragewa bataima Amina shi ba a bayan idona, amma a gabana babu abinda ya sauya na ladabin da take mata da. Sam ban fahimci zaman kisan mummuƙen da akeyi a gidana ba dan Amina ko a fuska bata taɓa nunaminba har ALLAH ya sauki Sa'a lafiya ta haifi ɗa namiji wanda yaci sunan kakana Adamu. Bayan haihuwar Adamu ne na fara fuskantar akwai matsala a zaman nasu, dan wataran na shigo a bazata na iske Sa'a nama Amina gorin haihuwa. Ranar nayi tamkar bansan Sa'a ba saboda biji-biji nai mata tare da dogon gargaɗi na saki ɗaya. Kamar Sa'a ta nutsu bayan wani lokaci saita dawo da halinta na rashin arziƙi har ƙawaye take kawowa suna haɗuwa cin zarafin Amina. Cikin amincin ALLAH Sa'a bata yaye Adamu ba saiga Amina da ciki. Munyi murna sosai fiye da zato, ganin Amina itama ta samu cikin da ake mata gori sai Sa'a ta sake sabon salon iskanci, Amina dai bata kulata dan ta bama banza ajiyartane. Cikin ikon ALLAH itama cikinta yakai haihuwa ta haifi mace wadda taci suna Bilkisu (mamanka kenan) dariya Sa'a taitayi alokacin da faɗin ai dai itace a sama tunda namiji gareta, Amina dai bata kulatan, bata yaye Bilkisu ba sai ga wani ciki, Sa'a kuma shiru, hankalin Sa'a ya kuma tashi ainun da wannan ciki na Amina harta sake haihuwa bata barta ta hutaba, a wannan haihuwarma dai mace ta samu itace Wasila (Ummah babba). dukda Sa'a ta nuna bata damuba tunda Amina mace ta sake haihuwa saita kasa daurewa, tashiga ƙananun magana Amina tai mata asiri haihuwarta ta tsaya, tun ina tsawatarwa har al'amari yafi ƙarfina na saki Sa'a saki biyu ya zama uku dan al'amarinta ya isheni. Wannan saki yama dangina daɗi yama nata zafi dan dangina dama babu mai sonta sai ƙalilan a cikinsu. Nayi ƙoƙarin na amshi Adamu amma kakar Sa'a tace ban isaba, duk hanyar data dace nabi suka hanani ɗana, acewarsu kishiya bazata riƙe musu yaroba wataran ta kashesa. Rabuwarmu da Sa'a da shekara guda Amina ta sake haihuwar mace dai again, wadda taci sunan Rahamah (ɗiyar Alhaji babba wadda ta rasu) haihuwar Rahama babu jimawa kakar Sa'a ta rasu, alokacinne na shirya amshe yarona dan banaso ya tashi da kalar tarbiyyar gidansu, sai dai a randa naje nai magana da mahaifinta washe gari aka nema Sa'a aka rasa ta gudu da Adamu. Neman duniya anyi babu wanda yaga Sa'a, munɗauki tsahon lokaci muna nemanta amma babu Sa'a babu labarinta. Har kuma ALLAH yayma Amina rasuwa ta barni da ƴaƴa huɗu duk mata ban sakejin ko labarin Sa'a ba balle yarona, kullum yana a raina, dan harda Maryam mun taɓa yin labarinsa”.
Ajiyar zuciya Jawaad ya sauke yana mai jinjina al'amarin a ransa, yace, “to Amma baba miya nisantaka da danginta harmu bamu taɓa saninsu ba ballema shi labarin Uncle ɗin? Tunda gashi dai alamu sun nuna shi Uncle ɗin ya dawo gida har yay aurema kenan ya haifi Miemaa”.
“Kasan na faɗa maka dama akwai damuwa tun hanani aurenta da akai a farko, sannan koda mukai aure danginta sunajin zafin mahaifiyata dani kaina, badanma sunso Sa'a ta dawo ta aureni ba, bayan guduwarta kuma sai abubuwa suka sake ƙwaɓewa suka ɗaura laifin akan Amina ce tai mata kurciya tabar gari saboda ita ƴaƴanta matane Adamu kuma namijine, dalilin wannan sheɗancin nasu nema yasa nayo nesa dasu na dawo nan dan lokacin garin bai haɗe ya zama babba ba gaba ɗaya kamar yanzun, ahankali abubuwa sukaita canjawa dangi makusanta sunata ƙarewa, shiyyasa kusancin namu ya sake taɓarɓarewa ma baki ɗaya tunda wanda za'aiyi dominsa babu shi tare dasu”.
Kai kawai Jawaad ke iya jinjinawa amma ya kasa magana, Alhaji babba ya katse shirun nasu da faɗin, “Duk da na daɗe banga Adamu ba tun yana yaro amma ƴarsa sai ta ɗakko kamanin Rahamah sosai musamman tana yarinya fiye da nasa kamannin, dan ni randa na farama ganinta a asibiti kamannin Rahamah na gani tattare da ita bana Adamu kawai ba, hikimar UBANGIJI kenan mai tsara yanda yaso a lokacin da yaso, Jawaad yanzu kenan Adamu baya raye?”. Cikin damuwa Jay ya jinjinama Alhaji babba kai, “Ta faɗamin mahaifinta ya rasu bayan rasuwar mamanta kusan shekara bakwai kenan ana cikin na takwas, kuma a yanda bayanai suka nunama kenan anan ɗin ya rasu, to amma abinda yama ɗauremin kai sufa danginsa ma suna nuna tamkar bashi da wata alaƙa da ɗiyar tasane fa, wannanne dalilin daya raunana zumincinsu ya dawo gefe yana rayuwarsa shi da matarsa kawai da yarinyar, kuma ko bayan rasuwarsa abinda yasa sukai watsi da ita kenan sai dai batasaniba ita”.
“Jawaad ban gane basu da alaƙa ba, duk wanda ya kalli matarka aiko yaga jinin Adamu ai”. “Gaskiya ne Baba, a hoton dai kam daka gani kasan jinsa ce, nima inason zuwa da kaina garesu naji miyasa suke nisantashi da abinda alamomi suka nuna nasa ne?”. “Bakai kaɗai zakajeba Jawaad, tare zamuje ai, dan nima ina buƙatar amsoshi da yawa a garesun”. Sun daɗe suna tattaunawa akan batun kafin jay yayma Alhaji babb sallama ya tafi asibiti.
★★★★★★
Tunda ya shiga asibitin sukai masa caa da idanu, shiko ya fuske abinsa fuska a ɗaure ya gaidasu da tambayar jikin Shahudah, kafin ya shiga ya dubata tana barci har yanzun, dan data farka suke sake mata wata allurar barcin tunda taƙi kwantar da hankalinta ta saurari kowa, ta dage sai an kira mata Jay.
fitowa yay daga ɗakin ya dawo wajensu da nufin yimusu sallama ya kama gabansa, amma sai mama Atika ta dubesa cikin gadara fuska babu wasa tace, “Mun gama magana da ƙannen ubanka yau bayan sallar azhar za'a maida aurenka da Sabira, kuma gobe idan ALLAH ya kaimu zata tare koda ba'a sallameta daga asibitin ba”.
Wani lallausan murmushi Jay ya saki da ya bama kowa al'ajab da mamaki, dan ba murmushin sukai tunanin gani daga garesa ba. Ya kalli mama Atika da ƙyau yana tura hannayensa cikin aljihun wandon shaddarsa da gyara tsaiwa yace, “Shi kuma mijinta yaya zakuyi dashi”. Yay maganar da maida kallonsa ga ƙofar shigowa.
Gaba ɗaya suka maida kallonsu ga ƙofar inda ɗan-fir'auna ke tsaye akan ƙafafunsa ya warke sarai sai tabbunan raunikan da yaji waɗanda basu gama bajewa da ƙyauba.............✍
(Kana basu pepe da ginger ɗan bilkisu da Abdul-Aziz mijin bilkisu🤣😂🚴🏼)
______________________
ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.
SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.
HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO
MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.
MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.
BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....
abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.
Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899
sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.
Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300
Sai kunzo😍😍😍😘.
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
Billyn Abdul:
Page 41
.................A firgice Mama Atika, Dad, Mom, Uncle Nasir, Uncle Uwaisu, Aamilah, Salman duk suka miƙe baki hangame. Uncle Sulaiman da Uncle Sadiq da basusan komaiba illa cewar ɗan fir'auna ya mutu suka bisu da kallo dansu basusan ɗan fir'aunan ba a zahiri har yanzun. Cikin tsananin firgici da suɓutar baki Mama Atika tace, “Nasiru ba kunce sheɗanin nan ya mutu ba wai?”. Rasa mai bata amsa akai a cikinsu.
Ƙyalƙyalewa da dariya ɗan-fir'auna yay irin ta asalin tsagerun nan da suka gama gawurta a fitsara, ya nuna Mama Atika yana tsuke fuskar tamkar ba shine ya gama dariyar ba, “Ke dai tsohuwarnan anyi ƴar buƙulu, to idanma na mutu ban kwashi garaba ashe kanwa na kawo duniya, koda yake ashefa shirya kasheni akai ko? To anyi tabanza dan shegen taurin raine dani zanyi dogon zamani fiye da naki, a nunamin inda matata take malamai”. Jikin Aamilah na rawa tace, “Brother ga shi nan”. Harara ya zabga mata, “K dan tsohuwarki waye Brother ɗin? Yayah zaki ringa cemin dan gyatuminki hausa zakimin, kujimin faratun banza mai suffar yahudawan farkon ƙarni”. “Kayi haƙuri dan ALLAH yaya bazan sakeba” tai magana tana komawa bayan Jay da yay kunnen uwar shegu dasu kamar baisan wainar da ake toyawaba ta maƙale, Jay wayama yake latsawa abinsa hankali kwance kamar baya wajen. Dariya ɗan-fir'auna ya sake kecewa da ita yana faɗin, “Kaji bayani, da kikace ke tsagerace? Hegiya nifa bar ganinki ƙanwar matata billahillazi jinake kamarfa nai miki eyane dan zaki bada kala a garin maji daɗi. Amma kinci arziƙin musulunci ba'a wannan haɗin. Oga bara na shige daga ciki duk da fa inajin nauyinka fuska kawai zanyi aradun ALLAH na siɗaɗa”. Yay maganar da wani ɗora hannu ɗaya kan ɗaya irin salon nan na gaisuwar gayu ga na gaba dasu. (ALLAH ya daidaita sahunka akan lokaci habibullah😂🤣)
Jawaad da baiko ɗagoba ya jinjina masa kai kawai yana cigaba da aikin latsa wayarsa. Sai da ɗan fir'auna ya shige ɗakin da Shahudah ke kwance sannan Jay ya ɗago yana kallon Dad da yay sagade kamar wani gunkin hanya yana kallon ƙofar, firgigit ya dawo hayyacinsa saboda bugo ƙofar da ɗan-fir'auna yayi da masifar ƙarfi.
Inda Jay yake ya nufa da sauri-sauri yana baza babbar riga, Muryarsa da zafi ya furta, “Inason muyi magana”. Kallonsa kawai Jay yayi baice komaiba, sai dai fuskarsa shima a haɗen take, da ya kai maƙurar da ayanzu zai ɗauki matakin da bai ɗaukaba ada akan kowa. Guntun Murmushi yay da miƙewa yana ɗan kallonsu Uncle Nasir da suka zubo musu idanu. Rai a ɓace Dady yace, “Jawaad!!....” saurin ɗaga masa hannu Jay yayi batare daya kallesa ba. “Karkai saurin harzuƙa, muje waje muyi maganar”. Ɗauke kai Dady yayi kamar bazai sake tankawa ba sai kuma miya tuna oho ya nufi ƙofar fita yana jiyo kukan Momy dake sukar masa zuciya. Tashi Jay yay shima ya fice baiko kalli inda ƴan gidan nasu sukeba balle ya nuna yaji ihun kukan Momy dana Mama Atika.
A can gefe inda babu mutane ya hango Dad nata kai kawo ransa a ƙololuwar ɓace, Jay yay ɗan murmushi ya ƙarisa. Kallonsa Dad yay ya ɗauke kansa, “Jawaad!! Tun muna ƴar kunyar juna ka saka wannan ɗan iskan yaron ya sakarmin yarinya ta”. Murmushi Jay yayi da tura hannunsa ɗaya aljihu ɗaya kuma ya shafi kumatunsa da gashin saje ke kwance kaɗan saboda yana askewa, “Miyasa kukai tunanin kashesa ne zai baku mafita domin farin cikin ƴarku?. Irin wannan raɗaɗin da kakeji a yanzun, ita kuka shiryama taji mafiyisa Dad, Miye dalilinku na janta jikinku bayan baƙwa buƙatar ta raɓu jininku?........”
Dady ya kallesa da ɓacin rai sosai ya katsesa da faɗin, “Ya ina maka magana akan Mamana kanamin wata banzar magana taka mara tushe?”. Haɗe fuska Jawaad yayi da tura ɗayan hannunsa aljihu cikin ƙoƙarin danne nasa fushin yace, “Banason mu bama juna wahala, dan inhar muka kai ga haka komaima zan bankaɗo babu ruwana, dan haka mu tsaya iya haka ɗin kamar zaifi sauƙi. Batun Hudah na riga na gama da wannan matsalar yanzu tsakanin kune ku da sirikinku. Lokaci yayi da zaku nuna gajiyawar da baƙwaso a gareta na bakomai zaku iya bata ba, ALLAH shike bada komai ga wanda yaso a lokacin da yaso ba mutum ma
i barci, mai mutuwa, mai mantuwa ba. Koda yake, wannan bashi bane matsalata. Minene Ya kai Qaseem China kuma?!”.
“Kai Jawaad!! Tsagerancin naka da su Alhaji Nasiru ke faɗa har yazo kaina nima kenan? Minene matsalarka ko alaƙarka kuma da barin Qaseem ƙasar nan?, Qaseem fa ɗanane, babu kuma wanda ya isa ya sakani koya hanani a kansa, itama bilkisun ba tsoro yasa na bar maka itaba dan inada ikon hanaka auren nata tunda ɗiyar ƴar uwa tace, a hannuna kuma ka ganta. Niba sa'an yinka bane, ka kama kanka kajiki”. Ya ƙare maganar da fara tafiya zai bar wajen.
Jay dake binsa da kallo yay murmushi, “Tabbas kanada iko da ita fiyema da hakan, kuma har gobe ita kallon uba take maka dan ta baka dukkan yarda kai da ahalinka, babu wani laifinku da take kallo laifi sai dai kuskure. Haka take komai nata irin na masu ƙyaƙyƙyawar zuciya ne, tana ƙyautatama kowa zato musamman wanda ya nuna tausayinta saboda a irin rayuwar data tsinci kanta ciki, Dady ka daina tunanin har yanzu al'amarin a rufe yake, na tanadi hanyoyi masu yawa dazan bankaɗo komai harda na Qaseem da kukai ƙoƙarin rufewa dan ina bibiyarsa kuka turasa China”.
Juyowa Dad yay daga tsayuwar da yay tun fara maganar Jay. Idanu suka zubama juna na kusan mintuna biyu kafin Dady yay wani murmushi yana girgiza kansa. Batare da yace komaiba ya juya ya tafi.
Da kallo kawai Jay ya bisa har ya shige, ya lumshe idanu da furzar da huci mai zafi daga bakinsa, batare da yay ƙoƙarin sake komawa cikiba ya nufi motarsa ya bar asibitin
A ciki kuwa tunda ɗan fir'auna ya shiga da maida ƙofar ya rufe babu wanda ya sake jin ɗuriyarsa balle sanin mi yayi a ciki har saida Dad ya koma ciki da kusan mintuna biyar sannan ya fito yana wani ɗan iskan washe baki kamar gonar audiga. tsayuwa yay ya gama kallesu a ɗage sannan ya wuce batare da yacema kowa komaiba, sai wani rangaji yake irin na tsageru tamkar wani bishiyar giginya.
Babu wanda ya iya cewa uffan dan har ransu tsoronsa sukeji, sai da ya kai ƙofa sai kuma ya juyi da sauri, “Af kunga nayi mantuwa zan wuce, Surukina inafa da magana da kai a ina zamu haɗu mu tattauna ta?”. Kafin Dad yay magana Uncle Sulaiman yace, “Haba yarona, hakan duk bai kamataba kaji, koba k.......” Da sauri ɗan-fir'auna ya katse Uncle Sulaiman cikin ɗaga masa hannu da faɗin, “Nifa ka ganninan duk tsagerancina ina girmama masu mutunci, kai Uncle ɗin Ogane mai daraja babba, dan ALLAH na roƙeka ka zama ɗan kallo, dan ko takalmin Oga bazan so na takaba balle kai Uncle ɗinsa”. Uncle Sulaiman ya jinjina kansa kawai batare daya ƙarasa abinda ya faroba, sai dai a ransa yana mamaki. Juyawa ɗan fir'auna yay yana faɗin, “Duk da ni mutumne mai kunya da baya son yawan shiga gidan surukai Zanzo gida na sameka surukina”.
Kallo kawai suka iya binsa dashi harya fice tamkar wasu wawaye babu wanda ya iya sake tanka masa.
___________________________
Ɓangaren su Bilkisu kam sunsha firarsu cike da nishaɗi kasancewar sun daɗe basu sami damar irin wannan haɗuwar ba, abincin da driver ya kawo daga gidan Ummah babba suka ci, dan Nabeelah ƙin biyosa tayi dan tazata Jawaad na gidan. Sai dai batasanma yana tafe zuwa gidan nasu ba, dan bayan sallar azhar can ya nufa. Tana falo zaune tana kumburin fushin Ummah tace taje tai kitso yay sallama. Ai da wani shegen gudu ta kwasa sai ɗakinta ta garƙame ƙofa. Hakan datai ya saka kowa fahimtar laifi tai masa.
Zama yay suka gaisa da Ummah tare da musu godiyar hidima da gajiyar taro, Aunty Batool ma ta gaidashi da tambayarsa bilkisu. Anan yaci abincin rana suka ɗan tattauna da Ummah akan abinda ke faruwa, kuka rurus Ummah keyi na farin ciki da al'ajabi, kai ita kanta tana mamakin irin yanda takejin Bilkisu har cikin jinin jikinta da ɓargo, san nan tana hango abubuwa da yawa dake mata kamanceceniya da jininta tattare da Bilkisun amma tarasa wacece?, wato jini ya wuce gaban wasa duk inda yake. Tace, “Jawaad bazan iya haƙuri ba gobe idan ALLAH ya kaimu zaka ganni a gidanku”. Murmushi Jay yayi, “To ai Ummah itama bata saniba, bamason ta san komai yanzun har sai mun bincika sauran
abinda ke faruwar tukunna, dan kinga al'amarin yazo da ruɗani a ciki”. Shiru Ummah tai na wasu sakanni, cikin sauke ajiyar zuciya tace, “Hakane kuma Jawaad, rashin faɗa matan yanzu yanada amfani, dan ko ƴan gidanku karmu bari su sani yanzun sai mun gama sanin komai mu kanmu”. Jay yace, “Insha ALLAHU Ummah bazasu sani ba”.
Baibar gidan Ummah ba sai kusan ƙarfe uku na rana. Daga nan gida Ummah ƙarama yaje itama, itakam harma tafi Ummah Babba shiga ruɗani, saboda ita mutumce mai ƙarancin juriya akan farin ciki ko ɓacin rai, duk wanda ta tsinci kanta a ciki saika ganesa tattare da ita. itama dai ya jima anan suna tattaunawa, dan saida akai sallar la'asar sannan ya baro gidan.
Gida ya nufa dan a gajiye yake ga barci yanaji sosai cikin idanunsa. Dai-dai traffic light ta tsayar dashi idonsa ya hango masa ɓaleru cikin mota, wanda ke a bayan motar ya kalla ya ɗauke kansa, sai kuma yay saurin sake kallon motar. Abinda ya faɗo masa a raine ya sakashi saurin ɗaukar wayarsa ya shiga WhatsApp, saƙon gimba da har yanzu yana nan ya kunna, ya maimaita dai-dai inda gimba yake sanar masa sunan Alh...Alh..k......
Ganin an basu hanya ya harba motar gaba hankalinsa nakan motar su ɓalerun, gefen titi ya gangara yabi motar da kallo harta ɓacema ganinsa, a fili ya furta ‘Tabbas Alhaji Kokino Gimba kake nufi’ yay maganar da ɗan dukan sitiyarin motar yana cije lip ɗinsa na ƙasa da ƙarfi, kafin ya furzar da huci mai ƙarfi ya kife kansa a sitiyarin na kusan tsahon mintuna bakwai. Tabbas inhar tunaninsa nakan dai-dai matarnan ce, to minene alaƙarta da Gimba?. Bashi da mai bashi amsa, dan haka wayarsa ya ɗauka yay kira, bugu biyu kuwa aka ɗaga daga can cike da girmamawa. Bai tsaya sauraren gaisuwarba yace, “Hameed kana tare da ɓaleru ne yanzu haka?”. Daga can aka amsa masa da, “Yes Sir, ai da naga ma irin sabuwar motarka a traffic yanzu har na ɗauka kaine”. “Kaga manta da wannan, wa yake ja a motar?”. “Alhaji Sadi Kokino ne sir” “Ka tabbata shine?”. “Wlhy shine Sir”. Shiru Jay yayi yana murza goshinsa, ya sauke zazzafan numfashi da faɗin, “Amma kacemin Drivern Mr Gebrail ne ai?”. “Wlhy Sir tunda na fara aikin nan tare da shi nake ganinsa, ni kaina yau da naga ya ɗauki Alhaji Kokinon nasha mamaki, shiyyasa ban gazaba wajen bibiyarsu”. Sitiyari Jay ya sake daka da ƙarfi, “Hameed akwai matsala, kodai sun shirya bada ƙafane dama dankar a bibiyesu, kokuma sunada tabbacin akwai mai bibiyarsu, yanzu haka suna ina?”. “To Sir nikam ka sakani a ruɗani, amma gamu a anguwar Sanni zasu shiga wani gida mai farin gate”. “Maza kabar wajennan Hameed, kuma duk abinda ka gani bai makaba ka tabbatar ka kirani, gobe idan ALLAH ya kaimu kazo ka sameni a A.Y street”. Cikin mamakin da babu damar tambaya Hameed yace, “Okey Sire”. Yanke wayar Jay yayi ya maida akalar kiran ga Jabeer, yana ɗagawa shima bai saurari tsokanar da yake masaba ta ango ango yace, “Jabeer kuna Office ne?”. “Eh muna Office, lafiya naji muryarka haka?”. “Jabeer inason yanzun nan ku bincikamin Number da Gimba yay wayar ƙarshe da ita a randa aka ɗaukesa, a ina mai ita yake yanzu haka? Sannan macece ko namiji?”. “Okey boss ina zuwa”. Yanke kiran Jawaad yayi ya tada motarsa yabar wajen, kansa tsaye tashar da ake hawan motar garin su Gimba ya nufa. Nesa da wajen yay fakin tare da kiran Dattijon nan a waya. Mintuna uku kuwa basu cikaba sai gashi. Motar ya buɗe masa ya shiga sannan ya maida ya rufe. Saida suka gaisa Jay yace, “Ka tabbatar yarinyarnan tana mana aikin da muke buƙata?” “Sosai kuwa Alhaji, ai itama kanta batasan aiki take manaba a kansa, yanzu haka ɗazun take sanarmin wai yau zasuje wani gidan dirama wani mawaƙi zaiyi wasa na musamman akan soyayyarsu da ɓalerun”. Murmushi Jay dake ɗan wasa da yatsun hannunsa saman sitiyari yayi, “Address ɗin wajen, sunan mawaƙin, time ɗin da zai shiga wajen da tashinsa?”. Dattijo yay ƴar dariya da faɗin, “Ai Alhaji kamar dama nasan zaka tambaya duk sai da na samo waɗanan amsoshin kaf, gasu a rubuce”. Amasar takardar Jay yayi yana jinjina kai, ya ciro kuɗi ya miƙa masa yana faɗin, “Ga cikon kuɗin aikinka nagode”. Baki a washe dattijo yac
e, “Nine da godiya ai Alhaji, ALLAH ya ƙara buɗi na alkairi, idan wani aikinma ya taso wlhy a kawo zanyi”. Jawaad baice komaiba sai murmushi kawai.
Dattijo na fita kiran Jabeer na shigowa, ɗagawa yay yasa a kunne batare da yayi magana ba. Daga can Jabeer yace, “Tabbas Boss mace ce, sunan da tai register layin dashi shine Safara'u Hashimu, kakanta Bala, sunan mahaifiyarta Indo, kakaninta na wajen uwa Hassan da Baraka, shekarunta sittin da huɗu a duniya, asalinta ƴar garin Tsamiya ce, yanzu haka alama ta nuna ana amfani da layin a anguwar Habbun.........” Jay ya katsesa da faɗin, “Habbun kuma? Ba garin nan bafa kenan?”. “Kwarai hakane”. Baya Jay yay ya jingina da kujerar yana furzar da huci, kafin yace, “Hasashena ba dai-dai bane kenan?”. Daga can Jabeer yace, “Kai minene hasashen naka da?”. “Jabeer akwai wata mata lokacin case ɗin nan na Alhaji kokino mun haɗu da ita a gidansa idan baka mantaba itace ta taimakemu sosai har muka ɗauke mata yaro mai suna Yazeed, da ina zargin itace Gimba ke magana a gidan Alhajin nan da bai ƙarisa faɗaba”. “Tabbas Boss hasashenka ba kuskure bane, tun a wancan lokacin naso nace muku kodai Alhaji Kokino Gimba ke nufi, dan na taɓa ganinsa a ƙofar gidan farkon fara maka aiki lokacin bikinmu da Surayya, kasan matar Alhaji kokino ƙanwar maman tace, yanzu abinda za'ai shine kabani daga nan zuwa safiya insha ALLAHU zan bincika komai”. “Okey babu damuwa, shima yaron nan yau insha ALLAHU zan kamashi dan na kula akwai wani abu damu bamu saniba”. “A'a haba boss, ka bari wani a cikinmu ya kamashi mana, karka shigarma Mami lokacinta, amma mika hasaso mana”. “Da kaina zan kamashi Jabeer, dan akwai saƙon da nakeson bari a kamun nasa, abinda na hasaso kuma sai mun haɗu zamu tattauna”. Ya kashe ƙittt batare da ya jira amsar Jabeer ɗinba.
Wayar Bilkisu ya kira, sai da ta kusa tsinkewa ta ɗaga dan bata kawo a ranta shi bane, ba Number data sani bace. Shiru tai taƙi magana, dan haka shi yay sallama. Yanda ta amsa sallamar ne yasashi fahimtar ta gane wanene yanzun, zamansa ya gyara da ƙoƙarin dai-daita muryarsa dake cike da ɓacin rai, “Am sorry kicema ƙawayenki suje kawai zan haɗu dasu zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu, wani uziri yane ya riƙeni gaba ɗaya shiyyasa ban dawo ba”. Murya a sanyaye bily tace, “To zan faɗa musu, amma bakaci abinciba fa, haka kake yawo da yunwa?”. Idanun Jawaad ya lumshe yana murmushi, ji yay duk ɓacin ran da ya tarar masa a ƙirji yana guduwa, yace, “Karki damu da anyi magriba zan dawo isha ALLAH, jin muryarki kawai tasa nama ƙoshi, ke dai ki shirya amsar angonki kawai ƙanwar Jay.......” ƙittt ta yanke wayar daga can.
Jawaad ya girgiza kansa yana murmushi har kumatunsa na loɓawa, motar ya tada yay gaba har lokacin murmushi ya gaza barin fuskarsa.
___________________________
Tunda su Zuhrah suka wuce sai naji gidan duk babu daɗi, ga wani motse-motse da naketa famanji amma narasa takamaimai a ina nake jinsan, nai jarumtar dakewa dan bana son na ruɗar da kaina, sai kuma na koma ganin tamkar gittawar inuwoyi ta jikin Windows, da farko dai naso fita na leƙa waje, sai kuma wata zuciya ta gargaɗeni dayin hakan, yanda kaina ya farayin nauyine yasa na jawo wayata na kunna karatun Al-Qur'ani mai girma, a hankali nutsuwa ta fara saukarmin, naji kaina ya saki na koma normal, gidan kuma yay wani irin yin tsitt mai ban mamaki, babu motsin nan sam, ko ƙarar na'urorin dake aiki da wutar dake a kwai duk bakajin ƙararsu, ban ɗauki hakan komaiba na cigaba da zama a falon har aka fara kiraye-kirayen sallar magriba, Miƙewa nai da shirin sake wanka, dan ɗazun lokacin sallar azhar da zanyi salla ganin ɗingon jini yasa banyi ba, amma yanzu dana duba gab da su Ummie zasu wuce kuma ya sake ɗaukewa, dama nasan ɗazun nayi gaggawar yin wanka dan ƙa'idane sai bayan sallar azhar nake wanka ko la'asar duk da lokaci kan ɗan canja min wani watan.
Wayar na ɗauka na shige bedroom, Kayan da zan saka na fara cirowa a drawer na ajiye, dan waɗan nan dazan cire ɗin jini yaɗan ɗiga a sket ɗin kaɗan sai yanzu na kula ma. Batare dana kashe karatunba nabar wayar a saman gado na cire
kayan na shiga bayin, ban jimaba na fito gudun kar lokacin salla ya ƙwace min. Saida na farayin sallar magriba sannan. Saboda wutar dake akwai sai na jona hand dryer a soket kawai, nai zaman fara busar da gashina.
Karatun Al-Qur'anin dana sakane yasa sam banji motsin shigowarsa ɗakin ba, sai da yay sallama, da sauri na juyo dan banyi tunanin ganinsa ba.
Jay da tun ɗazun yaketa faman sallama ya ɗan tsura mata idanu, daya shigo baiga kowa a falo ba, har yay tunanin nufar nasa ɗakin sai kuma ya nufo nan saboda jiyo sautin karatu.
Towel ɗin dana tsane kai na ɗauka na ɗaura a kafaɗa ta ya ɗan rufemin ƙirji, wanda na ɗaura ɗin kuma sai faman jansa nake ƙasa dan cinyoyina duk a waje suƙe. Ganin ya ɗauke kansa tamkar baiga abinda nakeyinba ya sakani saurin cemasa, “Sannu da zuwa”. “Yauwa sannunki kema”. Ya faɗa yana ƙarasowa cikin ɗakin sosai. Zama yay a bakin gadon yana sauke numfashi alamar gajiya. Daurewa nai na tashi, na raɓa ta gefensa na ɗauka kayana dake saman gadon zan nufi bayi dan na saka sannan na dawo ɗauka masa ruwa da zaman busar da kan.
“Da miye na saurin yin wankan tunda kinsan bai tafiba?”. Maganarsa tazomin a bazata. Cak na tsaya tare dayin ƙasa da kaina dan ni bansan wace amsa zan bashi ba nikam, yaushe yasan nayi wankan to? Anya boss bai gani har hanji kuwa?.
Ganin yanda ta wani tsume waje guda ya sakashi miƙewa yana girgiza kansa, zare rigarsa yayi ya raɓata ya wuce batare da ya sake cewa komai ba.
Ganin ya shige bayi nai azamar saka kayan sauri-sauri sannan na fita na ɗaukko masa ruwa, zaman busar da kan na sakeyi yanzun kam hankalina kwance, saukar laimar ruwa da naji a kan hannuna ya sakani saurin ɗagowa na kalli mirror'n, shine tsaye a bayana, sakar masa hand dryern da yake ƙoƙarin amsa a hannuna nayi ina rumtse idanu, dan wani irin masifaffen harbawa zuciyata tayi, karan farko da naga namiji a tuɓe kamar haka a gabana bayan jazuga da baida wani fasalin kirki irin na zaratan maza. a raina rayawa nake, ‘Wai miyasa maza sam basu da kunya ne? Daga shi fa sai towel iya ƙugu zuwa gwiwa amma ya iya fitowa gabana ya tsaya’.
Jay da duk yana kallon yanda ta rikice ta cikin mirror'n yay guntun murmushi kawai yana ƙarasa busar mata da kan, sai da ya gama tsaf ya ɗauki ribbon ɗin da yaga ta ajiye ya ɗaure matashi tsaf fiyema da yanda zatayi, harda su mata wani ɗan style da brush. Kujerar ya juya ya maido fuskarta inda yake kafin ya miƙar da ita tsaye ya ɗaura duka hannayenta saman ƙirjinsa daketa raɓar ruwan wanka. “Buɗe idonki” ya faɗa babu wasa.
Hannunta dake ɗan rawa tai ƙoƙarin zamewa tana maƙe kafaɗa alamar “Ah-ah”. hannun nata ya maida da ƙyau, yana bin fuskarta da kallo. A bazata ya sumbaci inda batai zatoba duk da akwai riga a jikinta. A take ta waro idanu waje da masifar sauri tare da buɗe baki. Babu shiri Jay ya ƙyalƙyale da dariyar da bai niyyaba, dan yaga tsoron nata fiyye da yanda yake son gani.
Bilkisu tai saurin duƙewa tana matse hannayenta duka biyu a ƙirjinta tare da cusa kanta duka a cikin cinyoyinta tana murmushi, dan ita kanta tabama kanta dariyar abinda tayin. Ga kunya mai tsanani akan abinda yayi ta lulluɓeta. Kafaɗunta ya kama ya ɗagota yana murmushi, duk yanda yaso su haɗa ido taƙi, daga ƙarshema saita ɗora kanta a ƙirjinsa ta ɓoye fuskar. Rungumeta yay da duka hannayensa yana murmushi tare da shaƙar ƙamshin da gashinta keyi da jikinma nata ya lumshe idanu. Kusan mintuna biyu suna a haka sannan ya zauna a bakin gadon ya ɗaurata saman cinyarsa. Fuskarta ya ɗago yanda zata kallesa duk da dai tanata faman yin ƙasa da idanu amma tana ganin fuskar tashi. Laɓɓansa ya nuna mata da ɗan yatsa yana wani ƙanƙance idanunsa. Kafaɗa ta maƙe da sake maida kanta a ƙirjinsa.
“Ni ai sai nayi” yay maganar yana yin baya dasu a kan gadon ya birkiceta ta koma ƙasa. A take idanun bily sukayo waje, hanata dukkannin dama yay ya shiga yin yanda yaso da ita.
Kiran sallar isha'i ne ya ƙwaci Bilkisu a hannun Boss, shima da ƙyar, dan daga kiss sai salon ya nema canjawa. Tunda ta samu ya barta ta cusa kanta cikin filos. Baice da i
i buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.
Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899
sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.
Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300
Sai kunzo😍😍😍😘.
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
ta komaiba shima ya fice yana murmushi. Ɗakinsa ya nufa ya sake ɗaura alwala da canja kayansa zuwa blue jeans da t-shirt itama Blue, ya saka turare kaɗan da ɗaukar wata ƴar ƙaramar bindiga ya saka a gefen ƙugunsa sannan ya fito. Ɗakin Bilkisu ya koma. isketa yay ta fito daga toilet fuska a jiƙe alamar alwala tayo. Ruwan data ajiye masa ɗazun ya ɗauka yana sha idonsa a kanta. Kofin ya ajiye yana kallon agogon hannunsa, “Bara naje za'a shiga salla, idan an idar zan ɗan ƙarasa wani waje insha ALLAH kafin goma zan dawo.
Da sauri Bilkisu ta kallesa idanu cike da ƙwalla, “Dan ALLAH mu tafi tare, nidai tsoro nakeji”. Yanda ta kumbura baki taso bashi dariya, amma sai ya danne abinsa ya taka zuwa inda take tsaye, fuskarta data duƙar yasa hannu ya ɗago, acan ƙasan maƙoshi yace, “Kin taɓa ganin amaryar kwana ɗaya a gidan miji ta fita?”. “To ai babu wanda zaisan na fita tunda dare ne”. Fuskar tata ya saki yana ɗan ɗage kafaɗa, “Okey, ki shirya kafin na dawo salla saimu je”. Cike da murna ta amsa masa da to. Goshinta ya sumbata ya juya ya fice yana murmushi dan wayo kawai yay mata ba dawowa zaiyi ba.
Ana idar da salla Jay ya fito daga massallaci, motarsa da dama ya bari a waje bai shiga da ita gida ba ya shiga ya bar anguwar, kai tsaye address ɗin da dattijon nan ya bashi ya nufa, anguwace irin sabuwar anguwarnan da uncompleted building sukama fi yawa, sai dai inda gidan drama'n yake anɗan gaggama wasu gidajen dan wajen harya fidda santa ɗoɗar, bakajin hayaniyar komai saina Genretor ɗin da suka kunna da ƴar hayaniyarsu alamar basu gama zuwa ba, akwai ƙwayayen wuta a waje da suka haska kusan rabin layin, sai mai Nama daketa faman haɗa wuta, gefensa mutum biyune ɗaya mai ruwa ɗa kayan drinks, sai saurayi da budurwa dake can gefe suna hira, sai kuma masu shiga da fita cikin gidan ɗai-ɗai dan yanzu suke kan zuwa. Waya ya ɗauka yay kiran wani abokinsa da ya kasance ainahin police, saida suka gaisa ya gama tsokanarsa da ango-ango, sannan Jay yace, “Auwal kuna garin nan amma tsageru har suke da lasisin buɗe wuraren iskanci irin haka?”. Daga can Auwal yace, “Haba dai Jay, kaima kasan hakan bazai kasanceba”. “Gashi kuwa na gani da idona, akwai wani gidan Drama a sabuwar anguwar nan data kusa haɗewa da jan-ɓauna, inason ƙarfe goma da rabi kuzo wajen kuyi kamen kan mai uwa da wabi”. Bai jira cewar Auwal ba yace, “Mu kwana lafiya” ya yanke wayar. facemask ya ɗauka ya saka tare da facing cap, kallon kasan yayi a madubi ya tabbatar komai yayi kafin ya fito bayan ya kashe motar. Sai da ya tabbatar babu wanda yaga fitowarsa sannan ya nufi gidan.
★★★★★★
Ina idar da salla na koma bakin gado nai zaman jiransa, ganin shiru-shiru sai kawai nahau yin game a waya, hamma na farayi ɗai-ɗai alamun inajin barci, nayi guntun tsaki da kallon agogon ɗakin, tara saura minti ashirin, zamewa nai na kwanta tare da jan filo na ɗaura kaina na cigaba da game ɗin, tun ina ƙoƙarin damƙe wayar dake neman suɓuce min harna yaddata batare dana saniba.
A firgice na farka jikina na wani irin ƙyarma, ‘innalillahi wa'inna ilaihirraji'un’ na shiga ambata ganin ɗakin dunɗum da duhu bayan kuma nasan fitilar a kunne take, dariyar da aka tuntsure da ita ta sakani sake firgicewa nahau laluben gadon.....
“Bilkisu! Kenan mai gadon zinari, wato ke amarya ko? Azatonki zaki iya tsere minne? Ke da kina tunanin na barki? Wannan gurɓataccen tunanine bilkisa, na rantse miki yau saina amshi abinda ya kasance cikar burina dan bazan rasa komai a dalilinki ba wannan gangan ne hhhhhhhhhh!!!!!!!!.................✍
ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.
SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.
HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO
MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.
MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.
BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....
abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gama
+234 909 304 4460:
Page 42
..................Inda mai naman nan yake ya tsaya, batare da yayi magana ba ya miƙama mai-naman 1k tare da nuna masa naman. Kallonsa yay a ƙufule, “Haba malam, ya zakazo waje babu ko sallama ka miƙomin dubu wai na baka nama? An faɗa maka ni irin sakarkarun masu saida naman nan ne da kuke rainama hankali, nibanma taɓa ganinka a gidannan ba, kai wane?”. Jay ya danne takaicinsa cikin salon maganar kurame yay masa nuni wai shi bebe ne”. Mai nama yace, “Oh to yanzu naji batu, kasan rainin tsagerun gidannan ne bazan iya ɗaukaba shiyyasa kaima nai zaton kalarsu ne, na duka kake so?”. Kai Jay ya jinjina masa. Mai nama ya fara yankowa yana sawa a takarda da raira ƴar waƙarsa ta shata mai taken “Natsaya ga annabi Muhammadu.......” Jay dai kallonsa yake da nazarin wajen harya kammala yanka masa, amsa yay da masa godiya ya juya zai tafi, sai kuma ya juyo da sauri irin kamar yayi mantuwar nan. Ƴar takarda ya ciro a aljihun wandonsa ya miƙama mai nama. Mai nama ya amsa da faɗin, “Miye kuma wannan? Nifa kunsan ba wani boko nayiba amma kuyitamin wani lagude-laguden jaraba. Kai Hamusu zo duba mi ya keso kuma?”. Wanda aka kira Hamisu dake gaban lemuka ya amsa da “To baba”. Takardar ya amsa ya duba sannan ya kalli mai naman, “Baba wai gidan Ɗan Alhaji ya keson a nuna masa”. Shiru mai naman yay yana kallon Jawaad, mikuma ya tuna oho masa sai ya washe baki, “Af to inaga irin abokansa ne daya ɗan gayyato, kasan yau zaiyi ajo”. Jinjina da hannu Jay yayma Mai nama irin ka gane ɗinan. Mai-nama ya sake washe baki da nunama Jawaad wani gida dake can kusan ƙarshen layin. Cikin alamar maganar kurame yayma Jay yay masa godiya da nufar inda aka nuna masan.
Rufe gidan yake dan haka ya ƙwanƙwasa, sai da yay sau kusan baƙwai sannan akazo aka ɓuɗe cike da masifa.
“Wai wane shegene yake bugama mutane gida haka? Sai kace ya bada ajiya ko an ci masa bashi, idan akai haƙuri dai ai zan fito ba sai ansama lokacina ido b.....” hankaɗa shin da Jawaad yay ya koma baya ya hanashi ƙarasa maganar, zai sake magana Jay ya ɗaura hannunsa saman baki yace, “Shiiiiii”. yana ɗaga rigarsa bindiga ta bayyana, jiki na rawa ɓaleru ya saka hannu ya toshe bakinsa yana faman zare idanu. Ƙofar Jay ya maida ya kulle bayan yay wurgi da ledar naman daya shigo da ita, ya sake kaima ɓaleru wani bahagon bugu tare da damƙo wuyan rigarsa ya miƙar dashi tsaye. Batare da yay magana ba ya nuna masa hanyar cikin gidan. Jikin ɓaleru na rawa ya shiga kaɗa kai tamkar wani ƙadangare.
Gidane madaidai ci yasha tiles har a jikin bango, ga hasken wutar Genretor da alamu suka nuna na gidan drama ɗinne aka jawo masa har nan, ƙofar dake buɗe suka shiga, budurwar dake kwance saman katifa tsirara ta miƙe da sauri zaune tana jan bedsheet ɗin saman katifar ta ƙudundune kanta ciki zata zabga ihu.......
“Idan baki rufemin shegen bakin kiba saina ragargaza ƙasusuwanki wlhy!!”. Jay yay magana cikin kaushin muryar da ta saka budurwar cusama bakinta bedsheet ɗin tana zare idanu hawaye na ƙwarara, jikinta sai rawa yake.
Jawaad ya maida kallonsa ga ɓaleru da duk hankalinsa ke kan wayoyinsu dake zube a ɗan table na glass ƙarami dake gefe. Ƙafa Jawaad yasa ya taɗesa ya faɗi ƙasa tim, cikin zafin nama ya shiga sauke masa maruka a fuska da hannu bibbiyu. A take ji da ganin ɓaleru suka gushe, gashi babu damar yin ihu yana tsoron bindiga. Sai da Jay ya jigatashi da maruka ya tabbatar ya fita hayyacinsa sannan ya barshi. Budurwar daketa gunjun kuka da faman ɓoye fuska ya kalla, “K zoki kashemin duk wayoyin nan....”. Kafinma yakai ƙarshe harta miƙe zaram tana damƙe bedsheet ɗin da ƙyau jikinta na rawa, wayoyin uku manya ta kashe sai ƙarama ɗaya. Yace, “Ina taki?”. Nuna masa ɗaya daga cikin manyan tayi, ukun kuma tace, “N..na nashi ne sauran”. Ɗauke kai Jay yay batare da ya sake cemata uffan ba, ya ɗauki Coc dake ajiye yanata raɓar sanyi ya ɓalle murfin, saman fuskar ɓaleru daya suma ya juyeshi, a take ɓaleru ya kawo numfashi. Wani marin Jay ya sake sauke masa a fuska. Take ya dawo hayyacinsa ya fashe da kuka yana share jinin da yake fita daga hancinsa yana sauka masa kan baki, “
Dan ALLAH malam minai maka kake min irin wannan dukan? Idan kuɗi kakeso ko nawane zan baka, nidai karka kasheni dan girman ALLAH, kag.....” sake wanka masa wani marin Jawaad ya ƙarayi tare da ɗora ƙafarsa ɗaya kan katifar ya ranƙwafo kansa da nuna masa fuskar wayarsa. “Wanene wannan?”. Ɓaleru da jikinsa ke rawa ga jini nata fita masa ta hanci da gefen baki yace, “Ni...ni ban sanshi ba wlhy”. “Baka sanshi ba! Kace baka sanshi ba?!!”. “Eh wlhy oga bamma taɓa ganinsa ba”. “Yayi ƙyau” Jay ya faɗa yana miƙewa da tattare hannun rigarsa sosai yay sama. Har Ɓaleru ya fara murna an barsa sai kawai ji yay Jay ya cakumo masa wuya ya miƙar dashi tsaye da ƙyau. Mahaukacin duka ya shiga masa da babu algus, yanda yake bugun nasa zai tabbatar maka zuciyar ƴan mazan a wuya take. Sam baya sauraren roƙon da ɓaleru ke masa da kukan karuwarsa. Saida yay masa lilis sannan ya hankaɗashi ya faɗa saman katifar kansa ya daki bango Ƙummm!!!!. Dafe kan Ɓaleru yay da sakin wata wahalalliyar ƙara, saiga jini sharrrr. Jay ya sake cakumo wuyansa ya shaƙesa da ƙyau da hannu guda, ɗayan kuma ya sake nuna masa hoton Gimba dake tare dashi da suka ɗauka a gidan gonarsa wani zuwa da suka taɓayi tare. Yace, “Har yanzu dai baka sanshin ba?!”. “Dan ALLAH ka tausayamin oga ka daina dukana karka halakani na sanshi, Abokina ne sunanasa Gimba garinmu ɗaya”. Ɗauke fuskarsa Jay ya sakeyi da mari yana faɗin, “Ɗan iska kake son maidanine da?”. “Na tuba dan ALLAH kayi haƙuri bazan sake maka ƙarya ba”. Miƙewa Jay yay tsaye ya kaima Ɓaleru harbi a ƙafa da tofa masa yawu, sai faman huci yake, jiyake tamkar ya kashe banzan nan ko zaiji sauƙin raɗaɗin da zuciyarsa ke masa.
____________________
Bilkisu! Kenan mai gadon zinari, wato ke amarya ko? Azatonki zaki iya tsere min ne? Ke da kina tunanin na barki? Wannan gurɓataccen tunanine bilkisa, na rantse miki yau saina amshi abinda ya kasance cikar burina dan bazan rasa komai a dalilinki ba wannan gangan ne hhhhhhhhhh!!!!!!!!.
Hannu nasa na toshe kunnuwana domin nisanta jina daga shaiɗaniyar dariyarsa, na fashe da kuka ina jan jikina baya, “Kaji tsoron ALLAH bawan ALLAH, koda kai aljanine na tabbata kasan akwai hisabi tsakaninmu ƴan adam da ku, minai maka ne kakeson ganin bayana? Ka tunafa ni matar aurrece yanzun, dan ALLAH na roƙeka karka wulaƙantani, ka barni da mutuncina.............”
“Kima daina ɓata yawun bakinki madam, babu wani roƙonki dazan taɓa saurara, keɗin kaddarace mai girma a gareni, makullin cikar dukkanin burkana. Kinsan illa nawa kikaimin ne?!!” yay ƙare maganar a tsawace da cafke wuyana ya shaƙe. A take jikina ya fara rawa na fara ƙoƙarin fisgo numfashi cikin kakari. Hankaɗani yay na bigi fuskar gadon. Azaba ta sakani fashewa da kuka na riƙe wuyana da duka hannu biyu. Wani irin matsanancin fushine ya tasomin jin dariyar da yake sake ɓaɓɓakawa yanzu ma, nace, “Ƙarya kake azzalumi, idan ka isa ka daina ɓoyemin kanka, matsoracin banza da wofi kawai, Bazan sake roƙoka ka barni ba koda hakan na nufin zakai nasara a kaina ɗin, sai dai na ɗauki alwashin in ALLAH ya yarda, inhar ƙazamin jikinka ya kasance shine ƙaddarata, nima nice zan zama ƙaddarar mutuwarka, dan da hannuna zan kasheka a ɗakin nan, a wannan daren la'ananne ALLAH fasiƙi kawai!!!”.
“Hhhhhhh!!” ya shiga sake ɓaɓɓaka dariyarsa mara daɗin ji da tafa hannayensa. Gaba ɗaya ɗakin ya ɗauki sauti hakan yasa na kasa fahimtar taka maimai inda yake. “Da ƙyau Bilkisu, da ƙyau!, ashe kema kin fara koyon jarumtar mijin naki?, nine zaki kashe, ni ni ninan kikejin zaki iya ki kashe.....?!!!” naji an sake damƙar wuyana an shaƙe.
A take jikina ya fara rawa, nasa hannu na daki cikinsa cikin gushewar hankali, dukda alamu sun nuna yaji zafi bai sakeni ba, sai ma dannani da yay baya ya maƙureni jikin fuskar gadon ya haye kaina. “Zanyi abinda ya kawonin, ada nayi niyyar barinki a raye tamkar sauran kicigaba da rayuwa kema, to amma tunda kince ke tsagerace saina shayar dake gidauniyar azabar mutuwa, k har wacece? Nawa kike? Da zaki zamewa rayuwata matsala.......”
Yanda naima Jazuga ne ya shiga dawomin a rai, duk da
shaƙar da yaymin cikin rahamar UBANGIJI na samu damar lalubar bed side drawer da naji a kusa da hannuna, kofin da boss yasha ruwa ban fiddaba yana a kai na jiyo, ALLAH ya bani sa'a fisgosa na ɗaga hannuna dake rawa da ƙyar na maka masa a gefen kunnensa. A take ya sakarmin wuya yana huci na shigar zafi..... Kafin ya dawo hayyacinsa na caka masa sauran kofin dake riƙe a hannun nawa, sai dai bansa a inane ba dan a kwai duhu a ɗakin har yanzun. ƙara ya saki yana sake kaimin wawura sai dai na zille harma na dire a gadon. Cafkoni yay cikin zafin nama ya maidoni baya kan gadon har saida nai ƙara dan azaba nima. Na gallama hannunsa cizo tare da halbinsa da ƙafa cikin salon trianing ɗin da muka samu duk da ba ganinsa nake ba. kokawa ce ta kaure a tsakanina da shi dukda yafi ƙarfina nesa ba kusaba. Amma kasancewar akwai taimakon UBANGIJI da kuma kowa yasan mata ALLAH kan bamu ƙarfi a irin wannan yanayin koda ace bazamu iya ƙwatar kanmuba kuwa. Kokawa muke bil haƙƙi da gaskiya dukda nice keshan wahala ban yarda ya kaini ƙasa ba. Cikin sa'a na kama ɗan yatsan hannunsa da yake neman sake kaiwa wuyana na murɗesa da azabar ƙarfi nai baya dashi. Jikake ƙaraƙassss ƙasss ƙasss ƙashin na bada sauti. Wahalalliyar ƙarar daya saki yay baya ta bani damar jan hannuna baya nima, sai na saɓulo da zoben dake jikin yatsan.
A take Ɗakin ya ɗauki sautin wata murya mai ban tsoro da saka firgici, aka shiga faman faɗin, “Barmata shine kuskure mafi girma, ka karɓa maza ka fita karka tsaya akwai matsala!!”.
Wani irin ɗagowa yay a zabure ya fisgoni muka tafi ƙasa tare ya murɗe hannuna da zoben ke a ciki zai ƙwace. Hakan yasa na shiga ambaton,
حَسْبُنَا اللهُ وَنِعْمَ الْوَكِيلُ.
Hasbunal-lahu wani'mal-wakeel.
(ALLAH ne mai isar mana, kuma madalla da shi abin dogaro).
اَللَّهُمَّ اكْفِنِيهِمْ بِمَا شِئْتَ.
Allahummak finihim bima shi'ita.
(Ya ALLAH! Ka isar mini su da abin da Ka so).
اَللَّهُمَّ لاَ سَهْلَ إِلاَّ مَا جَعَلْتَهُ سَهْلاً وَأَنْتَ تَجْعَلُ الْحَزْنَ إِذَا شِئْتَ سَهْلاً.
Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahlan, wa anta taj'alu-l-hzana idha shi'ta sahlan.
(Ya ALLAH! Babu wani abu mai sauki sai abin da Ka sanya shi ya zama mai sauki, kuma Kai kana sanya tsanani idan Ka so ya zama sauki).
Ƙarar da aka ƙwallah ta sakashi Hankaɗani kaina ya daki gadon, ya fita da gudu, na fasa wani irin gigitaccen ihu jikina na ɗaukar wani irin rawa, a take komai yay min ɗifff.......
Fasa ƙarar Bilkisu tai dai-dai da ƙarasowar Jay jikin ƙofar falon zai buɗe dan isowarsa gidan kenan bayan yakai Ɓaleru ya ajiye a wani ɓoyayyen waje. cikin zafin nama ya faɗa falon batare da ya rufe ƙofar ba. Ledar dake hannunsa ma sakinta yay a falon. A gigice ya danna makunnar fitilar ɗakin ta kawo haske. Ya daka wani uban tsalle sai gashi gaban Bilkisu data sume. Da ƙarfi ya ƙwala kiran sunanta jikinsa na rawa dan har yanzu yana tattare da fushin ɓaleru ne, yay saurin maidata ya kwantar jin kamar gudun mutum ta bayan Windown ɗakin. Fita yay da gudu yana ƙwalama maigadi kira cikin matsanancin hargagi akan ya rufe masa gate. sosai maigadi dahar ya shiga ɗakinsa zai kwanta ya fito a gigice shima jin wannan mafaraucin kira, baƙaramin tashin hankali ya shigaba ganin yanda Jawaad yake nufosa tamkar mahaukacin zakin dake a yunwace. Ɗaukesa Jay yay da mahaukacin mari, “Waye ya shigomin gida? Ka gayamin wa kabama damar ya shigomin gida!!?”.
Maigadi daya gama ruɗewa da marin da yasha yace, “Wlhy oga babu wanda ya shigo gidannan tunda ka fita, narantse maka babu wanda ya shig........” bai gama saurarensaba ya bar wajen, ta bayan Windows ɗinsu ya nufa kasancewar akwai wuta ko ina da haske. Take masa baya mai gadi yay da sauri shima dan bai fahimci abinda ke faruwa ba. Jay yaja wani mahaukacin birki yana kallon tsanin dake tsaye jikin katanga alamar koma wanene tanan ya shigo, kuma tanan ya fita. Naushi ya kaima bango da azabar ƙarfi yana faɗin, “Noooo!!”. Da sauri maigadi dake cikin tsoro ya riƙe masa hannu, “Oga dan ALLAH karka jima kanka ciwo”. Fisge hannunsa yayi dayin wani Uban tsalle ya ɗane katangar cikin ƙwarewar training da su
ka samu batare da ya kalli inda tsanin ya keba. Dirarsa can baya kawai maigadin yaji. “Na shiga uku ni gambo, mike faruwa a gidan wai?” mai gadi ya faɗa hankali tashe.
Babu abinda Jay ya gani sai sayin takalmi kawai da wani tsanin a baya, wajen siririyar hanyace data fita ɗoɗar har babban titi, hanyar tana taimakawa ƴan anguwarne wajen fita titi basai sunbi ta titin layinba dake da nisa da babban titi, ya dafe kansa dake wani irin masifar sara masa. Halin daya bar bilkisu a cikine ya faɗo masa a rai. Ya fiddo wayarsa a aljihu ya shiga haske-haske harya zagaya ta ƙofar gate yay knocking. Koda aka buɗe baiko kalli maigadi dake neman ƙarin bayani ba ya nufi cikin gidan.
Yanda ya barta haka ya Koma ya sameta babu alamar numfashi tattare da ita. Tsugunnawa yay gabanta ya Rungumota da ƙarfi cikin ƙirjinsa jikinsa na wani irin tsuma na tsananin ɓacin rai, “Ubanwaye ya shigomin gida? Miyay miki?”. Yay maganar cikin raunin murya da ɗaci, jijiyoyin kansa na miƙewa ruɗu-ruɗu, zafafan hawayene ke kwarara a cikin zuciyarsa, a zahiri kam babu ko ɗigonsu sai idonsa daya kaɗa yay jazur. Ɗagata yay gaba ɗayanta ya ɗaura a kujerar dake ɗakin guda ɗaya ƴar doguwa, sai da ya gama bin ɗakin da kallo tsaf, ɗigon jini har a kan gadon ya gani, sai fasashen glass aƙasa zuwa gadon dake a yamutse alamar ansha dabbe a kansa. Kauda kansa yay yana rumtse ido da danne abinda ke yinƙuro masa tamkar zai faso ƙirjinsa ya fito mai alaƙa da Masifaffen kishi, sauran ruwan daya bari dake yashe a ƙasa ya ɗauka, a hannu ya zuba ya shafa mata a fuska. A take ta kawo wani nannauyan numfashi tare da miƙewa zumbur cikin zafin nama tana faɗin, “Saina kasheka, bazan barkaba yau, kasheka zanyi wlhy......” Saurin riƙe hannunta da take ƙoƙarin kaiwa wuyansa yayi da ƙarfi ya mannata jikinsa yana faɗin, “Kwantar da hankalinki ki nutsu nine”.
Ƙamshin turarensa da naji ya sakani fashewa da kuka na ƙanƙamesa, “Boss shine, wlhy shine ke bibiyata tun a gidan Dad wai sai yamin fyaɗe, ya ɗau alwashin saiya ketamin mutuncina, yace nice cikar burinsa, saiya yimin yanda yayma su Amina, na shiga y......” ɗagota yay da sauri jikinsa na kakkarwa ya manne bakinsa da nata, sam baya buƙatar ji, bayason yaji komai a yanzu, zuciyarsa zata iya tarwatsewa idan ta cigaba da faɗa bazai iya ɗauka ba, yanada kishi mai tsanani akan dukkan abunda ya kasance nasa. hawayen da tun ɗazun yake fatan yinsu sunƙi suka shiga silalo masa a kumatu yanzun, yanda yake matan kawai zai baka tabbacin ba'a hayyacinsa yake ba. Yaja kusan mintuna biyar yana kissing ɗinta, tun tana ƙoƙarin son ƙwacewa harta nutsu ta miƙa wuya, dan ta kula da fushi yake sumbatarta. hawayensu ne masu ɗumi ke sauka bisa fuskokin juna. Saida yaga tayi laƙwasa sannan ya zare bakinsa cikin nata da sake rungumeta yana haɗiyar zuciya tamkar numfashinsa zaibar ƙirjinsa. Yanda ƙirjinsa ke sama da ƙasa sosai ya firgita Bilkisu, sai dai tai luf a jikinsa tana kuka dan dukkan abinda ya faru a waɗancan ranakun a yanzu tsaf suke dawo mata tamkar yanzune komai ke faruwa. Ɗaukarta yay gaba ɗayanta ya nufa ɗakinsa da ita, kai tsaye bayi ya zarce. Tanason tai magana sai dai babu fuska, dan haka ta nutsu shiru tanata share hawaye da sauke ajiyar zuciya. Ruwa ya haɗa mai ɗumi sosai ya nuna mata alamar tai wanka ya fice.
Binsa nai da kallo harya fice sannan na maida idona ga hannuna dake a rumtse, zobene mai azabar ƙyau da ɗaukar ido dana samu zamewa hannun tsinannen nan. Na maida hannun na rumtse ina cigaba da zubar da hawayen, mamaki nake a raina miyasa wancan zuwan da yaymin a gidan Dad ban taɓa tunawabama balle na sanarma wani? Nida sam bani da mantuwa amma gashi wannan ban taɓa tunawaba sai yau? Ko yaya akai hakan ta faru?. Da wannan zoben rumtse cikin hannuna nai wankan, da gasa jikina kawai nayi da ruwan daya haɗamin kafin nai amfani da sosonsa sama-sama dan wani irin ƙyanƙyami da takaicin raɓar jikina da la'anannen can yayi nakeji.
Jay Ɗakinta ya sake komawa. Bai taɓa komaiba bayan kayan barci daya ɗauka mata ya kashe fitar ya rufo ɗakin. Ledar daya yasar a fali ya ɗauka ya koma ɗakinsa.
ina kammala
wankan yana shigowa, nai saurin komawa na duƙe dan bankai ga ɗaura towel ba, bai fasa shigowa cikin toilet ɗinba, sai dai kuma bani yake kallo ba, bathrobe dake ajiye ya ɗauka ya juyo inda nake, kafaɗuna kawai naji ya kamo ya miƙar dani, nai azamar rumtse idanuna dake cika da ƙwalla hannuna na naɗe a ƙirjina gaba ɗaya, ban buɗeba harya gama sakamin ya ɗaure igiyar sannan ya kama hannuna daga cikin bathtub ɗin ya fitar dani. Muryarsa a dakushe yace, “Yi alwala”. Juyawa nai naɗan kallesa, ganin shima ni yake kallo nai saurin maida kaina ƙasa tare da miƙa masa hannuna dake a dunƙule rumtse da zoben. A hankali ya tako inda nake ya kama hannun ya buɗe, jin bai ɗaukaba baikuma yi maganaba yasa na kallesa. Zoben ya kafe da idanu tamkar mai nazari, hakan ya bani damar ƙarema fuskrsa kallo dake a matuƙar ɗauren da ban taɓa ganiba nima. Ya ɗago jajayen idanunsa masu tsananin saka firgici ya kalleni. “Nashi ne?”. Kaina na ɗaga masa. Bai sake cewa komaiba ya ɗauke zoben yana sake nunamin nayi alwala. Nima ɗin bance komanba na barsa tsaye yana jujjuya zoben a hannunsa. Ina alwalar ya fita, babu jimawa ya dawo lokacin na kammala, fita nai na barsa, sai yanzuma nake tunawa banyi sallar isha'i ba ashe balle shafa'i da wutiri. Riga da hijjab dana gani a saman gadon na ɗauka na saka, na ɗauki abin salla dake ɗakin na shinfiɗa na tada sallar isha'i na miƙe nai shafa'i, bayan na idar na miƙe zan sake kawo shafa'i da wutiri na tsinkayi muryarsa yana dakatar dani. Dukda nayi mamaki haka nabi umarninsa, wani abin sallar ya shimfiɗa a gabana. Munyi salla raka'a biyu sannan mukai shafa'i da wutir. Juyowa yay ya dafa goshina bayan mun idar, a fili ya shiga karanto addu'arnan ga mai sabon aure,
اَللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ خَيْرَهَا، وَخَيْرَ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّهَا، وَشَرِّ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ.
Allahumma innee as-aluka khayraha wakhayra ma jabaltaha 'alayh, wa-a'oothu bika min sharriha washarri ma jabaltaha 'alayh.
(Ya ALLAH ina rokon Ka laherinta da alhrin da Ka dabi'antar da ita a kansa, kuma ina neman tsarinka daga sharrinta da shaarrin Da ka dabi'antar da ita a kansa).
Ya saki goshin nawa ya juya tare da ɗaga hannu yay doguwar addu'ar da banaji, dan haka nima nai tawa tareda yima iyayena addu'a da sauran musulmai baki ɗaya.
Batare da yace dani komaiba ya miƙe, ficewa yay, babu jimawa sai gashi da kofi a hannu da filet, ina a inda ya barni zaune nidai banko motsaba, ledar ya buɗe ya juye gasashen naman rago daketa tashin ƙamshi saboda yanda aka sarrafashi cikin filet ɗin, kofin kuma ya saka fresh milk a ciki. “Taso kici abinci” ya faɗa yana zama akan sofa. Duk da bazan cinba ban musaba na tashi zuwa garesa jikina duk babu ƙwari ga ciwo yanamin ta ko ina saboda damben da mukaci da azzalumin can, ƙasa naso zama amma sai ya riƙoni na zauna kusa da shi, murya a sanyaye nace, “Naƙoshi, da yamma mukaci abincin da Ummah ta aiko dashi da rana”. Baice dani komaiba ya miƙamin fresh milk ɗin cikin kofin, amsa nai ita na kafa kai na shanye gaba ɗaya badan tanamin daɗiba sai dan buƙatar samun sanyi a cikin ƙirjina da yaymin nauyi. Jikina ko ina ciwo yay tsamu ga barci dama inaji. Amsar kofin yayi ya sake zubawa ya miƙomin, kaina na girgiza masa cikin marairaicewa dan kar yace saina shaɗin tilas. shanyewa yay ya miƙe ɗauke da filet ɗin naman da kofin. “Ga kaya nan ki canja ki kwanta”. Kaina a ƙasa nace, “To”. Juyawa yay ya fita, harna kammala saka kayan bai dawoba, na zauna bakin gadon ina ƙara tariyo abinda ya faru awanni biyu da suka shuɗe tamkar film ko mafarki. Gittawar da akai ta gabana ya sakani saurin ɗagowa, ganin shine sai na sauke ajiyar zuciya a hankali. Kwantawa nai da sauri ganin zai cire jallabiyar jikinsa na juya masa baya. Kusan mintuna goma sannan ya hawo gadon shima ya kwanta bayan ya kashe fitilar yabar ta gefen gadon kawai. na lumshe idanuna hawayen da suka taru min na silalowa, ni kaɗai nasan irin raɗaɗin da nakeji a raina da ruɗanin abinda ya hanani tuna waɗancan kwanakin da wannan shaiɗanin yazomin. saukar tattausan hannunsa akan kumatuna ya sakani buɗe ido a hankali kan
sa, fuskarsa gab take da tawa har muna shaƙar numfashin juna, dan akan filon danake kwance ya ɗora kansa shima, idanunsa dake kallon fuskata ya lumshe a hankali cikin salon lallashi yana mai sharemin hawayen da hannunsa dake akan fuskar tawa, cikin muryar raɗa yace. “Miyasa baƙya gajiya da kuka?”. Wasu hawayen ne suka sake silalo min, nace, “Na tsaneshi ne fiye da yanda kowa zai iya tunani”. Murmushi naji yayi mai sauti, hakan yasa na buɗe idanuna ina kallonsa, kallona yake shima,, “Kinsan minene?” kaina na girgiza masa alamar a'a, yace, “Na fiki tsanarsa Miema”. Murmushin da ban niyya bane ya suɓuce min a bazata. Gani nai shima yay murmushin idanunsa da suka rine jaa na wani irin ƙyalli kamar hawaye ya taru a cikinsu. nai ƙoƙarin jan fuskata baya dan kusancinmu yayi yawa, sai yay saurin maidoni gab fiyema da farko, yace, “Faɗamin miya faru? Kozan sami nutsuwa”. Hawayen ne suka sake silalowa, na maida idanuna na lumshe inajin yanda yake murza yatsansa babba saman fuskata, sauran huɗun kuwa kan gashina daga ƙeyya zuwa gefen kunne “A wani daren daya shuɗe, wanda tunani ko hasashe bai sake dawo dashi ba gareni, ranar da ya fara zuwa gareni.........................”.
Na ƙare faɗa masa dukkan abinda ya faru har zuwa yau da fashewa da kuka mai cin rai, da ƙarfi ya jawoni jikinsa ya rungumeni tsam, jikinsa na wani irin rawar ɓacin rai, nima saina sake fashewa da kukan, dan koba komai na fahimci shima yanajin irin zafin da nakeji a cikin raina, nace, “Na rasa miyasa ban taɓa tunawa ba sai yau?, Inason nasan ko wanene shi? Miyasa duk waɗanan kalaman nasa a kaina? saina kasheshi, da hannuna zan kasheshi azzalummi maƙiyin ALLAH, sainai gunduwa gunduw.........”
Jawaad daya saki murmushin takaici mai ciwo ya ɗagota daga jikinsa, babban ɗan yatsansa da yake share mata hawaye ya ɗaura akan laɓɓanta da faɗin, “Shiiii!!. kisa a ranki zaki sanshi, bana buƙatar sake ganin kukanki, Ni Jawaad Abdul-aziz yusif insha ALLAHU zan gurfanar miki da shi a gabanki kan gwiyoyinsa, abinda yake bibiyar kuma zan tabbatar masa da yafi ƙarfinsa har abada a wannan daren”. Ya ƙare maganar da manna bakinsa saman nata batare da ya sake bata damar magana ba. Duk da yana tausayinta bazai iya barintaba, wani irin shauƙi da zumuɗin kasancewa da ita yakeji, ji yake tamkar ana ingiza zuciyarsane akanta, jiyake idan bai kasance da itaba a wannan daren kamar zai rasa komai ciki harda ita kanta, tun yana sarrafata da tunanin iya ƙaramin wasa ya barta har hakan yaji bazai yuwuba, zuciyarsa ingizashi kawai take na kaiwa ga ƙololuwar martabarta................✍
😜Saura kuma naji wani yay gulmar Jay ehe😣🤐🤣🚶🏻.
Barkanmu da dawowa.
A ranar asabar an samu kuskuren ɗakko page daga telegram zuwa WhatsApp, wadda tayo copy ɗinsa daga can bata ɗauka a jereba kamar yanda page ɗin yake, shiyyasa tallan zafafa goma ya koma tsakkiyar page, wasu sai sukai tunanin ƙwai cikin ƙaya ake talla wai. To ba haka baneba, dan ranar kam masu sai da zafafa goma saida kuka tsiyayar musu da man kansu tas🤦🏻😑 saboda kira. Waɗanan buks ɗin goma namu sune nake talla gasu ga mai buƙata dan karku bari a baku labari inhar kasan baka karantanba dan duk sunyi lagwadar daɗi aradu🚴🏼👇🏾 .
ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.
SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.
HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO
MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.
MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.
BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....
abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.
Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899
sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.
Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300
Sai kunzo😍😍😍😘.
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
Typing📲
ƘWAI cikin ƘAYA!!
Bilyn Abdull ce🤙🏻
BOOK TWO
Page 43
.....................A take salon wasan ya canja, bily da batai tunanin hakan daga garesaba a wannan daren duk da dai yau jinta take wani sakayau kamar an sauke mata kaya tuni jikinta ya fara tsuma, zuciyarta da jininta na wani irin tsitstsinkewa, gashi ya hanata dukkan damar da zatai ƙorafi ko magiya, juyata yake duk yanda yaso da zafafan salonsa masu rikita ƙwanya da zuciyar duk macen data mallakesa matsayin mahaɗin rayuwarta, ta rumtse idanunta da ƙarfi lokacin da yake karanto___
ﺑِﺴْﻢِ ﺍﻟﻠﻪِ ﺍﻟﻠّﻬُﻢَّ ﺟَﻨِّﺒْﻨَﺎ ﺍﻟﺸَّﻴْﻄَﺎﻥَ، ﻭَﺟَﻨِّﺐِ ﺍﻟﺸَّﻴْﻄَﺎﻥَ ﻣَﺎ ﺭَﺯَﻗْﺘَﻨَﺎ .
Bismil-lah, allahumma jannibnash-shaytan, wajannibish-shaytana ma razaqtana.
(Da sunan ALLAH. Ya ALLAH! Ka nisantar da shaidan daga garemu, kuma ka nisantar da shaidan daga abin da Ka azurta mu da shi).
Ƙanƙamesa tai da sauri jikinta na wani irin rawa cikin gigitar data risketa batare datayi hasashe ko shiyaryama zuwan wannan daren ba.
Abinda yay matuƙar birge Jay da mamakin matar tasa shine Jarumtar da bai zatoba daga gareta, ko sau ɗaya batai yunƙurin hanashi yin yanda yaso da ita ba, ta miƙa masa dukkan ragama baki ɗaya cike da juriya da dauriya da sadaukarwa, sai saukar ɗumin hawayenta kawai yake ji da ajiyar zuciyarta tamkar zata shiɗe. (Uhumm) baiji daga garetaba dangane da ɗaga murya balle akai ga kwakwazon da duniya zata fahimci ana dai-dai wajen. duk yanda yaso yin juriya wajen binta a hankali shima dan nuna tausayinta hakan ya gagara, komai ya ƙwace masa a lissafi itaɗin kawai yake gani abu mafi daraja da martaba a garesa a wannan daren dama cikin duniyar baki ɗayanta. Ƙaunarta da tausayinta na ratsa dukannin tsoka da ɓargon jikinsa da jijiyoyi yana gaurayewa da jininsa, bashi da bakin musaltawa, bashi da kalaman kwatantawa, bashi da ƙarfin shelantawa, abinda kawai ya sani shine itaɗin tadabance, idan yace tadaban yana nufin tadaban har ƙarƙashin ruhinsa. Nutsuwar da ya daɗe yana hasashenta a zahiri da mafarkinsa daga gareta yama riski fiye da hakan.......
A zahiri Bilkisu ta hana kanta kuka mai sauti, amma wahala iya wahala shanta take a hannun Jay, yanda kawai take fitar da numfashi ɗai-ɗai zai baka tabbacin baije da wasaba. Hawaye kam ai wasu basa direwa wasu ke gangarowa. shi kansa bai fahimci ya tafka ɓarnaba sai da komai ya lafa, Sosai tausayinta ya sake mamayesa, taimakon gaggawa ya shiga bata ta kowace hanya data dace. Yanda take kuka sosai sai hankalinsa ya sake tashi, amma haka ya daure ya gasa mata jiki dan yasan shine babban gatan dazai mata a yanzun. Sai da ya tabbatar ta samu ƴar nutsuwa sannan ya barta ta ƙarisa gyara jikinta shi kuma ya fito ya cire bedsheet ɗin da duk yaɗan ɓaci, tunani yake anya kuwa baiji mata ciwo ba?....... Da sauri ya waiga bayansa jin kukanta, zanin gadon daya fara jawowa ya saki ya nufeta dan bai zaton zata fito ba, tarota yay jikinsa yana magana a hankali dan shi kansa muryarsa gaba ɗaya ta wani dadushe kamar mai mura, “Miyasa zaki fito kinsan bazaki iya tafiya ba?” Yay maganar yana kwantar da ita akan sofa.
Hawayen dake ziraromin na share, dan ni kaɗai nasan azabar da nakeji, babu inda kemin daɗi a dukan jikina, dai-dai da bakina ɗaci yakemin sam babu ɗanɗano, tausayin dukkan matan da aka kusancesu ta ƙarfin fyaɗe ya kuma mamayemin zuciya, shiyyasa Amina ta koma kamar wata ƙaramar mahaukaciya a lokacin.......
“Ya isa haka kukan mana uhmyim, kinga jikinki harya ɗauki zafin zazzaɓi, ina cewa matar tawa jarumace ashe raguwace?”. Haushi maganarsa ta bani, dan haka nasa hannayena biyu ina kai masa ƙananun duka a ƙirji. Hannayen nawa ya riƙe yana ƙaramar dariya, “Oh to yi haƙuri jarumace, giwar mata, bara na duba wajen nagani bakiji ciwo ba”. Ƙanƙamesa nai ina sake fashewa da kuka, nace, “Ni dai a'a, banji wani ciwoba”.
Jay yay murmushi kawai yana girgiza kansa, miƙewa yay ya ƙarisa cire zanin gadon ya shimfiɗa wani, rigarsa mai ɗan kauri data kai mata har cinya ya saka mata, yasa towel ya tsane mata kanta sosai gudun kar mura ta kamata, dama ga jikinta yay mugun ɗaukar zafin zazzaɓi, tausayinta duk ya gallabi ransa, cak ya ɗauketa dan harta fara barci ya maidata saman gadon ya kwantar, so yake tasha magani amma baison tadata, dan haka ya ɗakko man zafi kawai ya shafa mata a jiki kozataji ƴar nutsuwa.
Gaba ɗaya a hidimar Bilkisu Jawaad ya kusa cinye wannan dare, sai da ya tabbatar komai yayi masa yanda yake buƙata sannan ya samu shima ya kwanta, wani irin zafi yaji jikinta ya ɗauka, sai sauke ajiyar zuciya take a jajjere cikin barci, fuskarta ya ƙurama idanu yana kallon yanda ta ɓata fuska alamar dai bata jin daɗi har a cikin barcin. Yaɗan lumshe udanunsa ya sake buɗewa akan fuskarta yana wani ɗan murmushi, ƴar yarinyar nan itace ta nema zautar masa da tunani, “UBANGIJI mai hikima, UBANGIJI mai rahama da jinƙan bayinsa” yay maganar a fili tare da sumbatar goshinta da laɓɓanta da sukai jazur sosai saboda wahalar da sukasha a hannunsa. ‘Yanda take mai sanyi haka komanta yake mai sanyi’ ya ayyana a ransa yana rungumeta tsam cikin jikinsa har saida ta motsa sannan ya sassauta mata. A haka shima barci ɓarawo yay awon gaba dashi.
★★★★★★
DARE MAIBAN MAMAKI.
Dolene mutane masu yawan gaske su kira wannan dare da sunan dare maiban mamaki da ruɗani tare da tashin hankali ga wasuma maybe. Dan kuwa lokacin da Jawaad ke angwancewa a lokacin wasu cikin matsanancin ruɗani suke, dan duk wani azzalumi dake da alaƙa da wani ɓoyayyan sirri daya shafi waɗanan ma'aurata da hikimar UBANGIJI ta dunƙule waje guda wannan shine mafarkin da suka tsinci kansu a ciki a wannan dare.
(Ƙudirar UBANGIJI ta tabbata, rahamarsa ta yalwata, izzar mulkinsa ta Ƙaddara haɗewar jini dake cikin jinin da kuka salwantar, azzalumai lokaci yayi, UBANGIJI ya ƙulla rugujewar zaluncinku ta inda bakuyi zato ko tsammani ba, wannan ruɗanin shine nai muku hasashe, kuma gashi ALLAH ya tabbatar dashi, dama na faɗa muku wannan shukar saita fito da izinin UBANGIJI tai yaɗon da zata zamewa rayukanku barazana, nakuma tabbatar muku kafin kubar duniya sai kun wulaƙanta, duk wanda yaci amana dolene amana ta cisa shima, gashi kuwa ALLAH ya tabbatar da hakan, ku fara gudu maƙiya ALLAH, na ce ku fara gudu tun yanzu.......”
Dukkanin wanda keda alaƙa da wannan mummunan kalamai a cikin mafarkin a wannan dare hankalinsa a tashe ya wayi gari, domin dai wata shukace da suka binne a wasu shuɗaɗɗun shekaru take nuni da tayi tsiro da yaɗo harta saki ƴaƴa, suwaye ƴaƴan? A ina suke? Tayaya aka samesu bayan irin da suka shuka sunada tabbacin basu bar ko fure ajikin itaciyarsa ba, itaciyar kanta saida suka busar da ita balle ai tunani tayi yaɗon ɗa? Mike shirin faruwa dasune? A ina kuskuren yake? Ya akai mai gidauniya bai taɓa gano musu hakanba? Shima bai gani bane? Kokuwa ya gani ya ɓoye musu?.
Lokacine zai basu wannan amasar damu kanmu masu bibiyar labarin😵.
★★★★★★★
Rashin yin barci da wuri ya sakasu makara da asuba, dan sanda Jawaad ya farka wasu masallatan ma harsun kusa idar da salla, akan fuskar bily ya sauke idanunsa dake cike da barci, ya sauke siririyar ajiyar zuciya tare da tashi zaune da ita a jikinsa, idanu itama ta buɗe a hankali, sai dai suna haɗa ido tai saurin maidawa ta rufe tana ɓata fuska. Murmushin da bai niyyaba ne ya suɓuce masa, a zuciyarsa yake ayyana ‘sai shagwaɓan tsiya’ A fili kuwa sumbatar laɓɓanta yay, cikin raɗa-raɗa yace, “Good morning my Heartbeat”. Saurin cusa kanta tayi cikin ƙirjinsa. Iska ya hura mata cikin kunnenta yana murmushi, “Ko a ɗan ƙarane” yay maganar yana ƙoƙarin cusa hannaunsa cikin rigarta. kukan taɓara ta sakar masa da sauri jan jikinta baya. “Matsoraciya” ya faɗa yana sauka daga gadon gaba ɗaya.
Lamo nayi kwance zuciyata na tariyomin dukkan abinda ya wanzu a daren na jiya daya tara abubuwa masu yawa a cikinsa, darene da zuciya bazata iya mantashiba ta kowacce irin siga, dan yazo da abubuwa kala-kala a cikinsa. Har yanzu jikina akwai zazzɓi, ga ciwon kai da bala'in ciwon jiki, babu inda bayamin ciwo a jikin nan nawa wlhy. Ina jin motsin fitowarsa amma nakasa motsawa, tunanima nake tayaya zanyi tafiya ni balki........? Cak aka ɗagani sama, wata nannauyar ajiyar zuciya na sauke ina ɓoye kaina a ƙirjinsa dan banaso ko ido mu haɗa, wata irin matsananciyar kunyarsa nakeji fiye da da. jina kawai nai cikin ruwan zafi, hakan yasa na ƙanƙamesa sosai. A cikin kunnena yace, “Sorry daure, kaɗan za'ayi”. Kaina na ɗaga masa ina haɗiye kukan dake neman tahomin. Yanda ruwan yaɗanyi zafi sosai sai naji daɗi dan har jikina ya gasamin gaba ɗaya dukda inata noƙewa, har aka gama hannayena suna naɗe a ƙirjina. Saida ya bani towel na ɗaura sannan na samu nutsuwa duk da dai shima bawani babba bane amma yafi dai babu. Matsowa yay zai ɗaukeni bayan na kammala alwala. kaina a ƙasa cikin dakusashiyar muryata nace, “Zan iya tafiya da kaina”. Baice komaiba ya ɗan matsa baya ya bani hanya. Cikin dauriya na fara tafiya a hankali ina matse idanu, dan zafin nakeji, sai dai ba sosai dazai cutarba, bakamar na daren jiya dana ringajin tamkar ana yayyankani da wuƙa ba.
Kallonta Jawaad yake cike da nazari harta fice, yanda take tafiyan batason haɗa ƙafafunta sosai ya sakashi jin dolene ya dubata kodai ya jimata ciwon da gaske?. bayanta yabi shima. taimaka mata yay ta saka doguwar riga da hijjab shima ya saka jallabiya ya jasu jam'i duk da garima harya waye.
Bayan sun idar fita yay daga ɗakin, babu jimawa sai gashi ya dawo ɗauke da madaidaicin kofi daketa fidda turiri. Kwance ya sameta a inda tai sallar ta ƙudundune da hijjab, tea ɗin ya ajiye ya ɗakko magunguna ya ajiye sannan ya ɗagota jikinsa harma ta fara barci, “Sorry, tashi kisha tea da magani saiki kwanta”.
Duk yanda na marairaice masa akan na ƙoshi bai saurareniba, sai da ya tabbatar nashaye tas sannan ya bani maganin nasha. Da taimakonsa na koma saman gado, harna fara lumshe idanu naji yana buɗemin jiki, sauri buɗe ido nayi da riƙe masa hannunsa ina ɓata fuska, dan nazata ƙarawar zaice zaiyi. “Na shiga uku, dan ALLAH kayi haƙuri, wlhy ka maimaita mutuwa zanyi”.
Dukda ta bashi tausayi saida yaji dariya na neman kufce masa, ya dai daure ya haɗiye kayansa yana wani binta da kallon ƙasan ido, harta fara hawaye. Ɗauke idonsa yay daga fuskarta batare da yace komaiba ya maida inda yake son ganin.Ya kuwa ji mata ciwon da yay hasashe, sai dai bamai ɗaga hankali bane, amma zaiso a dubata gudun kuskure, tsabar son ya tsokane saiya ranƙwafo kanta kamar da gaske abinda take gudun zaiyi. jiyay kawai ta fashe masa da kuka jikinta ya fara rawa kamar wadda ta hango dodo. Dole ya danne dariyar da keson ƙwace masa ya rungumta. “Wasa nake miki niba ƙarawa zanba yi haƙuri”. Da ƙyar ya samu tai shiru har barci yay awon gaba da ita saboda maganin daya bata yana saka barci, ga kuma dama bawani isashen barci sukaiba. Sai da ya tabbatar barcinta yay nisa sannan ya gyara mata kwanciya ya sauka daga gadon bayan ya lulluɓeta da bargo. Dukda shima barcin yake buƙatar yi bai kwanta ba, wayarsa dake a drowan gefen gadon ya ɗauka ya fita falo.
10:30am
Ring ɗin wayarsa ne ya sakashi farkawa daga barcin daya ɗaukesa anan falon bisa doguwar kujera, kwance yake a rubda ciki, hakan ya sakashi miƙa hannu bisa centre table ɗin dake gab dashi ya lalubi wayar batare da ya buɗe idanunsa ba, guntun tsaki yayi sannan ya buɗe idonun da ƙyar ya kalli wayar. Ganin Jabeer ne ya sakashi ɗagawa yasa wayar a kunne, cikin muryar barci ya amsa masa sallama suka gaisa. Daga can Jabeer ya sanya dariyar shaƙiyanci, “A lallai boss Mamin mu batazo da wasaba, ka kalli agogo kuwa? Kaine da barcin safe har goma da rabi?”. Idanu Jay ya lumshe ya sake buɗewa akan agogon falon, kafin yace, “Kai ka sani dai ɗan sa ido” yay maganar yana tashi zaune da ƙyar. Dariya Jabeer yayi daga can, “Bari nakira anjima, dama akan maganar da mukai dakai jiya ne”. Jawaad ya ɗan sauke numfashi a hankali, “Karka damu gani nan zuwa station ɗinma”. Kafin Jabeer yace wani abu ya yanke wayar.
Ɗakinsa ya nufa inda ya tarar bily na barcinta har yanzu, sai da yaje gareta ya taɓa goshinta, zazzaɓin yaɗan sauka amma ba duka ba. Baice komaiba ya ƙarisa bayi domin yin wanka.
Shiri yayi cikin ƙananun kaya da sukai masa ƙyau, yana fesa turare ya jiyo ana knocking turaren ya ajiye ya fita, yasan bazai wuce Nabeelah ba, dan ya kira Ummah yace ta turo masa ita, Ilai kuwa itace ɗin tsaye a bakin ƙofar, Nabeelah da Ummah ta sakata zuwa akan dole kawo breakfast taja baya ganin Yah Jay ne ya buɗe ƙofar yau da kansa, saurin durƙusawa tai ƙasa tana faɗin, “Yayanmu dan ALLAH kayi haƙuri, na tuba wlhy bazan sakeba, ranarma suɓutar bakine”. Shi dai baice mata komaiba ya bata hanya ta shigo, juyawa yay ya koma ɗakinsa. Ta sauke ajiyar zuciya da ƙarisa takowa cikin falon sosai, basket ɗin hannunta ta ajiye saman centre table ta zauna tana waige-waigen ta inda Bilkisu zata fito, zamanta babu jimawa ya fito daga ɗakin yana waya, basket ɗi data ajiye ya yaye ɗan ƙyallen da aka rufo a kansa, kulolin ya buɗe duka, baice komaiba ya zauna a kujera da faɗin, “Tashi Ki haɗa min coffee”.
Nabeelah da aka nutsu kamar ba itaba tace, “to” tana miƙewa, tasan wannan ƙyaletan da yay ba yana nufin ya bartaba, akwai abinda yake shiryawa, Ummah ce dukta jamata, tayi alƙawarin bazata bari su sake haɗuwaba har sai bayan wata biyu, amma aunty Batool ita da Ummah yau suka zuga Abbah yace itace zata kawo breakfast. Ummah bata wasa wa yaranta akan aikin gida da girki, duk taɓarar Nabeelah da shegen surutu komai ta iya na mata, sai dai son jikin jaraba, wani lokacin sai Ummah tai mata wuju-wuju akan aiki take tashi tayisa. Kitchen ta nufa ta haɗa masa coffee mai daɗi kamar yanda tasan yanaso sannan ta kawo masa. Har yanzu wayar yakeyi, dan haka yaymata nuni da abincin da hannu. Komawa ta sakeyi ta ɗakko filet tazo ta haɗa masa abincin shima ta koma gefe ta zauna, tana son tambayar Bilkisu tana tsoron sake yin laifi a garesa.
Abincinsa ya cigaba da ci yana wayar har zuwa wani lokaci, kafin ya ajiye ya maida hankali ga cin abinci kaɗai. Ita dai tana zaune ne tanata satar kallonsa da gulmarsa a zuciya harya kammala ya miƙe yana goge baki da tissue, yay magana batare da ya kalleta ba. “ki tabbatar kin gyara gidan nan, idan kin tashi karki nutsu kiyi da ƙyau kinji, ki kuma tasheta da rawar kankin nan kiga yanda zan sauya miki kamanni”. Fuska Nabeelah ta kumbura tana faɗin, “ALLAH kuwa yayanmu ni yanzu na daina rawar kai”. Juyawa yay ya zuba mata harara ya nufi hanyar fita, harya kama handle ɗin ƙofar kuma sai ya juyo, “Idan ta tashi ki kirani”. “To yayanmu”.
Sadiq da tun ɗazun yazo gidan saboda kiran da Jawaad yay masa akan yazo zasu fita, ya taso daga wajen maigadi da yake zaune suna hira ganin Jawaad ya fito, sai da suka gaisa sannan ya buɗe masa ƙofar ya shiga ya zauna. Zagayawa yay shima ya tada motar suka fice a gidan bayan sun gaisa da maigadi daya buɗe musu gate.
Duk da ba aikine ya kawosa office ɗinba saida ya shiga suka gaisa da Sir Ahmad da yayta tsokanarsa. Office ɗinya ya buɗe ya shiga, komai tsaf babu wani datti sai ƴar ƙurar da ba'a rasaba. Yana zama babu jimawa su Aliyu na shigowa.
Yanda suke wani binsa da kallon shaƙiyanci ya sakashi haɗe fuska yana harararsu. “Malamai miye namin wannan kallon ƙurullar?”. Dariya duk suka sanya masa hatta Aliyu da bai cika tsokana ba. Jabeer yace, “Kuji kama kaifa jama'a, waya ce da kai wani abu anan dan ALLAH?”. Jay ya sake zuba masa harara yana ɗauke kansa, “Ai nasan zakuce ɗinne musamman ma kai da babu abinda ka iya sai shegen gulma ko mace ta shafa maka lafiya”. Yanzunma dai dariyar suka sanya suna cigaba da masa sherin wai ƙyallin angwaci yake kamar wata ɗan daren sha biyar.
Shiru yay musu sukai sherinsu suka gama sannan suka zauna.
Hafiz ya maida dubansa ga Jay dake duba file ɗin da Jabeer ya basa, “Boss wai mike faruwane haka? Gaba ɗaya mun kasa banbance komai tun daga yinin jiya har safiyar yau ɗin nan? Gashi kuma kazo office bayan munsan kana hutu?”.
Jawaad ya ajiye takardun yana sauke nannauyan numfashi, miƙewa yay ya ɗakko wani file a drawer bayansa, yana daga tsaye ya ranƙwafo ya dafe tebirinsa da duka hannayensa, dara-daran idanunsa da tun daren jiya haskensu bai gama dawowa ba ya zubamasu Aliyun, cikin ɗacin murya yace,“Hafiz nima wannan amsar nake nema, nakasa fahimtar komai, komai sake ruɗar dani yake da dilmiyani a kogin ruɗani..... a daren jiya wani ya shigar min gida domin cutar da Miemaa, lokacin inacan wajen kama ɓaleru”.
A tare suka ɗago suna kallonsa fuska cike da tashin hankali. Har haɗa baki suke wajen tambayar baidai cutar da itaba ko?.
Kansa ya girgiza musu yana miƙewa tsaye sasai, “Babu abinda yay mata, sai itacema ta jijji masa ciwo, ta faɗamin a bubuwa da yawa masu kamanceceniya da yanda akaima matar Jabeer fyaɗe.
Jabeer yace, “Boss da gaske?”. Kansa ya sake jinjinawa kawai yana mai datse haƙwaransa waje guda saboda azabar zafin da zuciyarsa ke masa.
Su duka ukun tsaye suka miƙe, suma cikin zafin ran da akan daɗe ba'aga Jabeer da shi ba yace, “Boss anya ba Qaseem bane?”.
Kafeshi da idanu Jay yayi kafin ya janye yana wani ɗan murmushi mai ƙona zuciya, “Jabeer! Ba Qaseem bane, a yanzu bashi nake zargiba sam, tako wace siga na auna Qaseem bai hau mizanin bincikena ba, Idan har wanda nake zargi ya zama shiɗinne da gaske to lallai ƙungiyace dasu, dan adaren jiyan Miemaa ta samu nasarar cirar zobe daga hanun wanda ya shigo gidannan, kuma zoben tabbas na taɓa ganinsa a hannun kusan mutum huɗu, abinda ya kuma ɗauremin kai basuda wata alaƙar zahiri dake a bayyane su duka huɗun kuma”.
Aliyu ne yay ƙarfin halin cewa, “To boss indai basu da alaƙar zahiri tayaya zamuyi tunanin haɗasu a kamanceceniyar laifi?”.
“Ƙyaƙyƙyawar tambaya Aliy” Jawaad ya faɗa yana fuskantarsa da ƙyau, hannayensa duka biyu ya zura cikin aljihun wandon sa ya zagayo ya sake zama a kujerarsa. suma duk komawa sukai suka zauna.
Jay ya ɗauki coffee ɗin da Hafiz ya ajiye masa yakai baki yana faɗin, “Akwai kamanceceniya mai yawa Aliy, musamman idan muka saka abubuwa da yawa da suka faru a tsakanin nan a mizani guda, babu abinda yafi ɗaukar hankalina wajen kamantasu sai maganar fyaɗen nan, dan haka zamuyi amfani da wannan damar mu canja salon bincikenmu. Fyaɗen da akaima Amina, Matar Jabeer, Nazifa, yayar Ummie, da ƴar mai aikin gidansu Nazifa daya faru kwanannan duk basu da banbanci, a tunani na hankali da yazo a zahirance zai bama mai nazari wahala wajen fahimta musamman daya kasance ba'a guri ɗaya al'amarin ya faruba, hasalima ba lokaci gudaba, idan har zamuyi aki da hankali kuma amsar ƙarshe itace ba mutum ɗaya ke aikatawa ba kenan. Da akwai aikin dana shirya dunƙule yaran suyi da, dan a jiya harma na sakasu zuwa gidana zamuyi magana sai ban koma gida akan lokaciba, to yanzu zamuyi amfani da wannan damarne, saboda su abin ya faru da wasunsu, sunsan zafi da raɗaɗin da akeji”.
Cikin farin ciki Hafiz yace, “Wannan tsarin yayi wlhy Boss, amma nima ga tawa shawaran”. Gaba ɗayansu hankalinsu suka maida ga Hafiz ɗin, ya gyara zamansa sosai yanda zai faɗi komai dalla-dalla. “Kunsan a yanzu bazai yuwu kai tsaye mu iya binciko waɗanda akaima fyaɗe irin nasu ba, fitowarma fili zaisa masu aikatawar su ɗauki mataki suma, haka bayyanar yaran kai tsaye zai dawo da hankalin masu aikatawar kansu”.
“Ƙwarai kuwa hakane Hafiz”.
“Yauwa to mizai hana mu taimakama yaran su buɗe wata ƙungiya haka ta ƙarɓar ƙorafin waɗanda akaima fyaɗen koma a wane yanayine, matanmu su zama sune masu ƙungiyar a bayyane, mukuma mu koma ta bayan fage wajen tsayawa tsayin daka ga masu shari'a su ringa yanke hukuncin daya dace cikin ƙanƙanin lokaci, na tabbata hakan zaisa mu sami dukkan damar da muke buƙata kodan sakacinma da kotuna keyi akan wannan matsalar, kunga mun jefi tsuntsu biyu da dutse guda, zamu sami abinda muke buƙata, zakuma mu taimaki yaran da ake zalinta musamman waɗanda iyayensu basu da ƙarfi akan tsaya masu bayan an cutar musu da ƴaƴansu”.
Tafama Hafiz suka shigayi dan shawarar tashi tamusu yanda suke buƙata. A take kuma suka tsara komai yanda ya kamata. Suna cikin tattaunawar su Zuhrah suka iso office ɗin kamar yanda Jay yay kirasu tunkan ya baro gida akan su samesa nan.
Ummie ce tai musu jagora har office ɗin na Jay, Sai da suka gaishesu duk cikin girmamawa kafin su basu izinin zama. Shine ya fara magana cikin dakewar nan tasa da kowa ya sani musamman akan abinda ya shafi aiki, “Inason ku bani dukkan hankalinku nan”. A take duk suka sake nutsuwa garesa fiye ma da yanda yake buƙata.
“Ku dukanku a yanzu zaku kasance wajen aiki ɗayane, ina mai gargaɗarku da bama buƙatar wasa, daga yau zaku ajiye wani ƙawancenku gefe kuyi aiki tamkar bakusan kankuba, zaku fito a ƙungiyance domin karɓar kukan iyayen da akaima ƴaƴansu fyaɗe. Wannan itace hanya ta farko da zaku iya fahimtar dukkan abinda kukai buri. Sunan ƙungiyarku, lauyoyin da zasu taimaka muku, harma da alƙalai mun tanada, ku naku kawai sauraren duk waɗanda matsalar ta shafa. Baku kaɗai bane a ƙungiyar, akwai matan su Jabeer, dan irin matsalar data faru da ke Nazifa da sister ɗin Ummie data rasu da Amina itace irin hanyar da akabi akaima matar Jabeer fyaɗe kafin aurensu da wasu ƙawayenta biyu data sani”.
Duk kallonsa sukai cike da ɗunbin mamaki, Nazifa dake sharar hawaye tace, “Yaya kuma suma ba'a gane wanda yay musunba har yanzun?”.
Cikin tsananin takaici Jay yace, “Ba'a ganeba, hasalima daga ƙarshe a lalace shari'ar ta ƙare tunda babu wasu hujjoji da zasu tabbatar da wanda ya aikata ɗin. Abinda yasa mukai tunanin kufito a ƙungiyancan dan bazai yuwu mu iya gane waɗanda akaima irin wannan kalar fyaɗen ba saita siyasa, suma waɗanda akayima ɗin ta wasu hanyoyi wasu rashin gata ya sakasu sunyi shiru, wasu kuwa sakacin shari'a yasaka zancen wucewa tamkar ba'ayiba. Ku jami'an tsarone shiyyasa muke fatan ƙungiyar da zata fito daga ƙarƙashinku ta banbanta da sauran ƙungiyoyin, mukuma zamu tsaya a bayanku mu baku dukkan gudunmawa ta ɓangaren shari'a dan acanne ake ruguza komi da make ƙwarin gwiwar ƙungiyoyin dake faɗi tashi akan wannan matsalar. Dan haka aikinku zai kasance da manufa biyu....”
Kasancewar hakan burinsune sai duk suka amsa cike da farin ciki da zumuɗi.
A nutse Jay ya ƙarayi musu bayani suma su Aliyu suka ƙara musu da nasu.
★★★★★★★
Ring ɗin wayatane yasa na farka, na buɗe idanuna da ƙyar ina tashi zaune, saman mirror ɗinsa na hango wayar, dan haka na sauka a kan gadon ina cije baki, duk da Alhmdllh naji daɗin jikina bakamar a daren jiya ba da ɗazun da safe, ganin Ummu ce da kanta tai kirana na ɗan zaro ido waje na ɗauki wayar da har ta katse, ina ƙoƙarin kiranta kiran ya ƙara shigowa, cikin ladabi na ɗaga tamkar ina a gabanta na gaisheta Ina hawaye.
Daga can gimbiya tai murmushi tana gyara kishingiɗar da tayi jikin mai martaba, “Haba ɗiyata, miye kuma abin kukan, baki da lafiyane naji muryarki haka? Ayi haƙuri to, shiyyasa naƙi kiranki ai sai yau, duk kuna lafiya ko?”. Kaina na ɗaga tamkar ina gabanta nace, “Lafiya lau Ummu, barci na tashi ne, sai kaina dake ciwo kaɗan, inasu Safah? Tun jiya naketa zuba idon zuwansu amma shiru”. “kisha magani to, ALLAH ya ƙara sauƙi, Karki damu zasuzo insha ALLAHU, yanzuma na kirakine akan zuwansu Anuwar anjima kaɗan dan zasu wuce gobe idan ALLAH ya kaimu”. Cikin jin daɗi na share hawayena Ina faɗin, “ALLAH ya kawosu lafiya Ummu, to suzonan su kwana dan ALLAH”. “A'a babu batun kwana ɗiyata, ai ba'a kwana gidan amarya, zasuzo dai zuwa dare su dawo, ki tabbatar mijinki da Anuwar sun haɗu dan munyi waya dashi ɗazun yace baya gida”. “Insha ALLAHU Ummu zanyi ƙoƙari”. “To shikenan, sai anjima na kiraki kinji, kidage da shiga ruwan zafi karkiyi son jiki”. Kunyace ta kamani, a raina ina tunanin kodai shine ya sanar mata..... “Kina jina” magarta ta maidoni hankalina. “Eh Ummu”. “Bawai ina nufin ki shiga ruwan zafi idan babu abinda ya faru ba, tunda nasan kina fashin salla, bakuma saina buɗe miki abinda nake nufiba, ayita haƙuri danshi zaman aure haƙurine, allah yay miki albarka”. Hawayena na share nace, “Amin Ummu nagode”.
Rashin ganinsa a ɗakin ya sakani jin daɗi bayan na ajiye wayar, cikin dauriya na gyara ɗakin tsaf, na fito ɗaukar kayan shara naga Nabeelah, sosai naji daɗin ganin nata, itace tace nabar sharar ita zatayi, ban musa mataba na shiga nai wanka da sake gasa jikina sosai, hakan ba karamin nutsuwa ya ƙaraminba. Koda na fito saina koma ɗakina nai shiri, ina cikin shirin Nabeelah ta kawomin abinci, dan tunda taga yanayina ta tambayeni lafiya nace mata banida lafiya duk sai naga jikinta yayi sanyi. Yunwa nakeji sosai shiyyasa na zauna naci abincin. ɗakinsa na sake komawa ɗaukar maganin dan naji daɗinsa, ina buɗe box ɗinne Nabeelah ta shigo da sallama da waya a hannu, a kunne kawai ta sakamin batare da tayi maganaba. Ɗagowa nai zan tambayeta wanene? Muryarsa ta shiga dodon kunnena.
Saida na lumshe idanu na buɗe sannan na amsa masa sallamar tasa,
“Amarsu kin tashi?”. Ya faɗa cikin zolaya.
Jinai tamkar na nutse dan kunya, dukda bana gabansa, nai saurin saka hannuna na rufe fuskata ina murmushi da faɗin, “Nidai ALLAH a'a”. Ina jiyo sautin murmushinsa shima, yace, “Nidai nasan amaryata amaryace ƴar gaske, yaya jikin naki?”. Batare dana buɗe fuskarba nace, “Da sauƙi”. “Alhmdllh ai haka akeso, kinci abinci ko?”.
“Uhm naci”.
“Tom kisha magani ki sake kwanciya ki huta karki biyema surutun Nabeelah, Gimbiya ta kirani akan baƙi zasuzo kuyi sallama, zanyi ƙoƙari na dawo da wuri nima insha ALLAH. ga Sadiq nan zai kawo cefane Nabeelah tayi girki”.
“ALLAH ya dawo dakai lafiya to”.
“To nagode, amma mizan ɗan samune Noor-Jahan?”. A marairaice nace, “Mi kake so?”. yace, “Komai aka bani inaso mana”. Duk da ina tsananin jin kunya nace, “To rufe idonka”. “Na rufe ruf Matar Jay”. Yay maganar cikin sanyin murya kamar ba shiba. da saurin na yanke kiran ina dariya, ina gani ya sake kira naƙi ɗagawa, saima maganin na ɗauka na fita falo wajen Nabeelah.
Babu jimawa da zamanmu Sadiq ya kawo cefanan da yace, karon farko da zan fara girki a gidana dukda Nabeelah tace na barmata zatayi kar yazo ya gani yay faɗa, ban sauraretaba dan nima inason ƙarfafa jikina ai. Tare mukai girkin cikin nutsuwa da salon da Umm-Anum ta sake koyar dani, dan danan gidan ya kaure da ƙamshi, muka kammala tsaf muka gyara kitchen ɗin sannan.
Kusan ƙarfe uku na rana saiga su Anum, Anuwar, Abdul-Rahman, Abdur-raheem, Ameen, Meenal, Amaturrahman, Amatullah. Tuni muka rungume juna dasu Amaturrahman kamar mun shekara da rabuwa, su dai su Abdur-raheem dariya suketa mana.............✍
Inacan ina muku dogon page, kunanan kuna ƙwalama sunana kira😣😫, ku baku ganeba ne, duk randa nai posting da wuri to nayi typing ɗin dare ne ya kwana, idan kuma ban samu damar yiba dole sai randa zan tura nakeyi, ga aikin gida ga uzurorin rayuwa🤦🏻😓, gashi yanzu anzo gangara typing ɗin na buƙatar nutsuwata sosai, amma idan naga wani Comments ɗin har mamakin mai rubutashi nakeyi wlhy. ALLAH dai ya dafa mana kawai, duk ƙoƙarinka baka isa yima kowa yanda ya dace ba, ALLAH kaɗai ka iyama ɗan adam da halinsa wlhy😂🚶🏻
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
0 comments:
Post a Comment