*_WATTPAD:_* _BilynAbdull_
*_TELEGRAM:_* https://t.me/joinchat/TIsXYRvhtri2kQ9E4x7w6g
Page 26
BARKA DA JUMA'A
..............Jawaad da yay ɗan jim fuskarsa ɗauke da murmushi yana juya maganar gimbiya ta ƙarshe a ransa, koba komai ya sakejin kimarta, domin ta nuna tanada ƙyaƙyƙyawan tsari da tausayi akan talakawa. yace, “Shikenan ranki ya daɗe, ke uwace, kinada damar yanke duk hukunci daya dace a kanmu koda babu saninmu, sai dai ina neman alfarmar zuwa na sanarma kakana da kuma ƙannen mahaifiyata, zuwa gobe insha ALLAH zan dawo na sanar miki yanda mukayi”.
“Wannan tunanin naka shine ƙyaƙyƙyawan tunani da yakamata ya fito daga bakin jajirtaccen ɗa mai riƙo da tarbiyyar magabatansa, kaje ka sanar musu ɗin babu damuwa, sai dai zan baka shawarar koda likita yace zai sallami bilkisu kace ya jinkirta zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu, dan nafison da an sallameta kawai nan za'a wuto da ita”.
Kansa ya jinjina mata. Ta ɗauki ɗaya daga cikin wayoyinta masu azabar ƙyau ta miƙa masa, “Kasaka Number ka anan, saika ɗauki tawa yanda idan sun amince ɗin zakai kirana ka sanarmin basai kayi wahalar zuwa ka koma kawomin bilkisu ba kuma”.
Tasowa jay yay ya amshi wayar, Number sa ta musamman da wanda ya yarda kawai kuma yakeda kusanci dashi matuƙa kawaine ke da ita ya saka mata, sanan yay kira yaga tata, saving yay mata da Jawaad A yusif ya maida mata yana godiya.
_______________________________
Tare Jawaad suka dawo da dattijon nan dan zai juya dasu Amaturrahman masarauta.
Shi kaɗai ya shigo ɗakin da sallama ciki-ciki kamar yanda ɗabi'arsa take ta rashin son hayaniya, babu kowa a ɗakin, Safah kaɗaice kwance tana barci a gadon da Bilkisu ke jiyya, mamaki ya kamashi da tunanin ina suke har ita Bilyn?. kafin yay yunƙurin yin wani abu aka buɗe ƙofar toilet, Bilkisu ce ta fito ɗaure da zani, ta yafa ƙaramin towel a kafaɗarta da alama wanka tayo saboda yanda ruwa ke jiƙe da fuskarta, duk tsefaffen gashinta ya kwanto goshinta da gefen kumatu.
Wani faɗuwa gabana yayi dan banyi tunanin iske kowaba tunda su Nabeelah sunce zasuje sallah, Mama kuma tunda ta gasamin jiki ta fita akan zata ɗauraye kwankikan da akaci abinci, bawani ƙwarin jikin nakejiba dama, dan dukan da sukaimin yasa jikina yin tsami ko ina ciwo yakemin, wai danma Doctor ya bani maganin ciwon jiki nasha. Nakasa koda ɗaga ƙafata da sunan juyawa baya, sai kawai na duƙe a wajen inaji tamkar ƙasa ta tsage na shiga ciki dan matsananciyar kunyar data riskeni, nice yau tsaye gaban boss babu riga? Dagani sai zani da ƙaramin towel ɗin dana yafo a kafaɗa, kaina sanye da hular wanka, dukda nasan fuskata kawai zai iya gani da hannayena zuwa gwiwa, sai ƙafafuna suma iya rabin ƙwairi dan zanin ya sauka min ƙasa sosai duk da ɗaurin ƙirji nai dashi, hakan ba ƙaramin abun kunya bane a gareni.
Ɗauke kai Jawaad yay daga kallon daya kafeta dashi yana mai lumshe idanu a hankali da furzar da sassanyar iska daga bakinsa, baice da ita komaiba ya juya ya fita zuciyarsa na gudu da sauri-sauri.
Hawaye nake kashirɓan da bansan dalilinsuba sam, dukda naji ƙarar buɗe ƙofa da rufewa alamar ya fita na kasa miƙewa tsaye bare na tashi. “Bilkisu lafiya kuwa? Ko jiri kike ganine?”. Muryar mama ta dawo dani hankalina. Saurin ɗago kaina nai ina share hawayen da suka jiƙen fuska, ganin dagani sai ita a ɗakin yasani sauke numfashi ina mai ɗaga mata kai alamar juwarce. Kwanikan hannunta ta ajiye tazo ta taimakamin na tashi tsaye, da taimakonta muka ƙarisa bakin hadon dan a gaske yanzun saima nakejin tamkar juwarce tazomin, ita ta taimakamin na shirya, ina kammala shiryawa su Nabeelah da Amaturrahman da Marwah na shigowa. Sannu suka yimin kafin Amaturrahman ta shiga tada Safah tana faɗin Su zasu wuce gida, jinai kamar nace su zauna, amma banda wannan ikon, ga Safah ta sanya kukan shagwaɓa akan itafa anan zata zauna tare dani. Ina mamakin wannan irin ƙauna da Safah ke nunamin.
Kafin kowa yace wani Abu boss ya shigo ɗakin da sallama. Nidai ƙasa nai da kaina ban yarda nako saci kallonsaba, tambayar da yakema Safah akan mitakema kuka kawai naji, Na
beelah ce ta bashi amsa da cewar tace bazata tafiba anan zata zauna wajena. Banji ya bata amsaba, sai saukar hannunsa naji akan nawa dake riƙe dana Safah, a take tsigar jikina ta tashi, gashi har yanzu akwai damshin ruwa jikina dama, ya cire hannunta batare da yace uffan ba, binsu da kallo nai ta ƙasan ido har sukaje gab da ƙofa. Ranƙwafawa yay yaymata maganar da duk bamujiba a cikin kunne, ta ƙyalƙyale da dariya tana tsalle, shima wani shegen murmushi ya saki maiban mamaki, Safah tace, “Amma Yayanmu (Yanda taji Nabeelah na faɗa) kafin goben zaka rama mata dukanta ko? Inba hakaba saina saka Abbu ya turo sarkin tsabga na masarauta ya musu dukan mutuwa da dorinarsa”.
Janyeta yay daga jikinsa da take neman shigewa yana lumshe idanu, a hankali yace, “Karki damu zan rama mata da kaina”. Sosai ta shiga daka tsallen murna Nabeelah da Mama na dariya harma da Amaturrahman, Marwah ce dai tai murmushi kawai tana rakuɓewa a jikina, juyowa yay muka haɗa ido nai saurin janye nawa, da hannu ya yafito Marwah alamar taje itama. Da sauri kam ta nufesa cike da ɗoki harda murmushin daya bama kowa mamaki, dan tunda tazo taƙi sakin jiki da kowa. Hannunsu ya kam suka fita, Amaturrahman taimin sallama tabi bayansu tare da Nabeelah da zatai musu rakkiya, mama kuma ta bisu da kalaman godiya dana addu'a. Nima haka godiyar nake musu har suka fice.
Bayan wucewar su Amaturrahman Jawaad bai koma cikiba, mota ya shiga yabar asibitin. Kai tsaye gidan Alhaji baba ya nufa, harya zauna kusa da Alhaji baba baisan ya shigoba, saida Jawaad ya kwanta tare da ɗora kansa a cinyar kakan nasa sannan ya kawo numfashi. Cike da mamaki jay yace, “Tunanin mikake haka da zurfi sofo?.”
Shafa kan Jawaad yay cikin ƙoƙarin danne damuwarsa yace, “Kaima zaka tsufan wataran ai, ango mai rinton mata, yaya kukayi dasu a masarautan?”.
Dariya Jay ya ƙyalƙyale da ita yana faɗin, “Ashe dai ni jarumine tunda gashi na ƙwace kuma dole a barmin. Ka fara gayamin damuwarka Baba sai na faɗa maka nima”. Jay yay maganar cike da kulawa ga kakan nasa abin ƙaunarsa. Sosai Alhaji babba ya sake danne halin da yake ciki ya nunama Jawaad bashi da wata damuwa, badan Jawaad ya aminceba ya haƙura, sannan ya zayyane masa duk yanda sukai da gimbiya Munaya. Alhaji babba yace, “Banƙi ta tataba, sai dai kuma kai kana ganin babu damuwa?”.
Zaune Jawaad ya tashi sosai, yace, “Amincewarka ni itace kawai tawa baba, dan kaine zaka hangomin abinda ya dace da wanda yake kuskure saboda kana gaba dani, dalilan data kawo na komawarta gidan Dad abin dubawane, nikuma gashima ban shiryama maganar tarewar tataba saboda akwai ayyukan da gidan da zan ajiyeta yake buƙata, tunanin da nake dai bai wuce dama ta koma gidan Ummah babba ba, dan dama ni ban tsara zata koma can gidanba saboda haɗarin dake tattare da hakan koda Qaseem da Hudah da Momynsu.
Alhaji baba yace, “Lallai kayi tunani mai ƙyau, yanzu dai ka bata dama, dan kowa yanama Uwargidan sarki ƙyaƙyƙyawan sheda akan adalci da shiga matsalar talakawa da ƙarfinta da dukiyarta, to akanku wannan ba sabon abu bane, bakuma yauta faraba, shiyyasa banajin wani ɗar balle tunanin akwai wani manufa a lamarinata”
Jawaad yace, “Shikenan Alhajin ALLAH zanyi yanda kace”. Daga haka hira sukaɗan taɓa zuwa sallar la'asar, daga nan Jawaad yay masa sallama ya wuce gida, dan a matuƙar gajiye yake, rabonsa daya huta tun daren alhamis ranar laraba kenan, gabaɗaya bai hutaba, a hankali ya furta, ‘Dukta cinyemin lokaci ta gajiyar dani’ ya ƙare maganar daɗan lumshe idanu ya buɗe akan titi.
iske gidan nasu yay kaca-kaca anata hayaniya, dai-dai sashensa yay fakin inda ya saba, ya fito fuska ɗaure batare da ya kalli kowaba a cikinsu ya shige abinsa, dan ya fahimci cecekucen maganar aurence suke har yanzu, shikam a tsarinsa duk abinda ya gama da matsalarsa to yagama kenan baya sake waiwayensa sai dai kuma sabo idan ya taso.
Yanda suka ganshi a tsume yasa aka rasa mai tunkararsa da magana dukda kuwa shigowar tasa suke jira dama, Hatta da Momy da Shahudah duk suna gidan sunzo saboda mama Atika data buƙaci ganin Momy, ga k
ukan da Shahudah keta dirja tunda Jawaad ya baro gidan. (Kaike musu yanda kaso ace ɓarnar motace, inba kaiba saiwa ɗan Abdul'aziz😂, kaikeyi kayi kuma kamar bakaiba dole a ganka a ƙyale🤣🤣).
Yana shiga falonsa ya dannama ƙofar key yana jan wani wawan tsaki, a kwanakinnan ko shara sashen baya samu saboda yaraba hankalinsa biyu, ga matsalar aiki ga matsalar cikin gida, duk ƙura ta kwanta bisa kayayyakin falon, haka ya tsallake yanzunma ya haye sama, canɗinma dai yay ƙurar sosai, bai kulaba ya ƙarasa bedroom, shi daɗan sauƙi saboda ana zama, gadonma a gyare yake, ga mayen ƙamshinsa daya kama ɗakin na nan, kayan jikinsa kawai ya rage, dagashi sai boxer ya haye gadonsa yana lullumshe idanu. Cikin ƙanƙanin lokaci barci mai nauyi yay awon gaba dashi (Barcin bayan la'asar baida ƙyau Jay🤦🏻). A hankali numfashin Jawaad ya ƙara nauyi alamar barcinsa yayi nisa, mafarki mai sarƙaƙiya, wanda a cikinsa aka sake maimaita masa kalmar “(Ƙaddarar haɗuwar Jini a cikin jini da zai zama jini a yanzu ta zama tabbatacciyar alaƙa da zata zama sanadin buɗe ma'anar jini a cikin jini, takuma warware sirrin ɓoye, Kuzama masu addu'a, dan lokacin da ƙullalliyar sarƙaƙiya mai cike dacin amana zai bayyana yayi, dolene maciya amana, amana tacisu suma, dolene waɗanda sukai shuka su girbe abarsu dai-dai da abinda suka shukaɗin tun a duniya kafin aje babbar kotu kowa ya amshi sakamakonsa, dolene gorar da azzalumai suka fafe dan tafiya ta buɗe a yanzun da suke gab da kaiwa ƙarshen tafiyar tasu, ɗan zaki ya girma, kaine jagoran fidda ƘWAI CIKIN ƘAYA, karkuyi wasa da addu'a!! dan itace babban takobinku na yaƙar wata riundina ta azzalumai masu son zuciya, gaggawarku zaizama sanadin tonuwar wasu jinane da aka kwarayar. wannan itace ƙaddararku, ƙaddara mai sarƙaƙiyar data saƙa jini a cikin jini, karku manta! Addu'a!! Karku manta!! Karku manta!!)”. Cike da firgici Jawaad ya farka, ya jiƙe sharkaf da gumi dukda kasancewar yammace mai cike da ni'ima canjawar iskar farkon damuna, ɗan zafi-zafin dake garin bashida gallazawar da zatakai mutum da irin wannan zufar da yakeyi, gaba ɗaya jiyay ɗakin na juya masa tamkar hajijiya, ya dafe kansa da hannu yana karanto addu'oin da duk sukazo masa kan harshe. Ya ɗauki tsahon mintuna zaune kafin yaji ɗakin ya tsaya dai-dai, ya sauke hannunsa yana furzar da iska zazzafa, idanunsa sunyi wani irin kaɗawa sunyi jazur, wannan wane irin mafarkine haka? miyasa yaketa maimaita kansa garesa? Akan wa ake masa wannan nunin?; ‘Ya ALLAH ka warwaremin abinda banida ilimin saninsa, ka haskamin abinda ya kasance duhu a gareni, ka jagoranci tunanina akan abinda kakemin ishara dashi acikin barcina’. Idanunsa ya sauke akan wayarsa dake haske, kamar zai share sai kuma dai ya ɗauka, ashe yayi barci mai tsaho, ga magrib harta gabatoma, saƙon da'aka turo masa ya buɗe, sanin muhimmancin wanda ya turo masa saƙonne yasashi nutsuwa ya karanta abida ya rubuto.
“Oga na shirya faɗa maka komai a yanda yake, ina kuma buƙatar a bani matata itama, amma akan farashin kuɗaɗe, kabani address ɗin inda zamu haɗu, sannan kazo da naira miliyan hamsin, nikuma zan baka labari mai matuƙar tsada akan kai kanka bayan nata itama”.
Naka ɗan fir'auna.
Ƙaramin tsaki Jawaad yaja yana mai dafe goshinsa da hannun damarsa tare da murzashi da ƙarfi, da ace ya iya kuka akan komai da a yau zama zai kawai yayta kuka har sai ya ƙoshi dan kansa yay shiru, to amma a tsarin wannan harƙallar kuka a garesa kasawace. Miyasa ɗan fir'auna yace yanada labari a kansa? Kenan shima su.... Ya haɗiye abunda ke neman toshe masa numfashi da sauri yana girgiza kai da faɗim, ‘No...’ bazai kasance hakaba. Komawa yay baya ya sake zubewa a gadon, ƴar ƙarar da agogon ɗakin yayce ta sakashi miƙewa kuma zumbur. Toilet ya nufa, ya sakarma kansa ruwa na tsahon lokaci kafin yay wanka ya fito ɗaure da alwala yay gaggawar shiryawa ya fita.
_____________________________
Ganin mutane sun sassauta zuwa dagani sai Mama a ɗakin da Ummie yasa nai dauriyar tattaro dukkan abinda ke raina ina mai kallonsu, “Mama!”. “Na'am Bilkisu ya akai?”. Tafaɗa tana ɗago kanta ta kalleni, Ummi
e ma daina latsa wayar tai ta maido hankali kanmu. Cikin bama kaina ƙwarin gwiwa nace, “Mama dan ALLAH mi yake faruwa? Gaba ɗaya tunanina ya kulle bana fahimtar komai daga kalaman mutane wanzu daga safiyar yau har kawo yanzun?”.
Murmushi maman Amina tayi, sai kuma ta taso zuwa inda nake ta zauna a bakin gadon, hannunta ta saka ta kamo nawa, har yanzu fuskarta da murmushi, “Bilkisu ya kamata dama kisan miya farun kodan kiyaye girman nauyin dake kanki a halin yanzun, danke ɗin matar aurece da haƙƙinta ya koma kan wani”. Banji komai dangane da kalamantaba face wani mummunan faɗuwar gaba da harbawar zuciya, ta cigaba da faɗin...................
Wani irin mazarin rawa jikina ya shigayi hawaye na rige-rigen sakkowa akan kumatuna, cikin matuƙar rawar leɓe dana harshe nace, “Mama! Ki..k...kina nu..fin ni aka ɗaurama aure da BOSSS!!!?”. Mama tace, “Bafa bos nace mikiba, Jawaad! Nace”. “Innalillahi....” Na shiga ambata, yayinda Ummie ke ma mama ƙarin bayanin cewar Boss ɗin ai Jawaad nake nufi nima, haka muke cemasa a wajen aiki. Mama tace, “Ayyo, aiban fahimta bane ƴannan”.
Komai nama daina fahimta, wani irin zazzafan zazzaɓi nakeji yana saukarmin, cikin lokaci ƙanƙani nafara rawar sanyi, tunani kalma ɗaya acikin abinda mama taimin bayani na kasa nutsuwar yi, ni Bilkisu Adam makaho ce aka ɗaurama aure da Boss ɗinmu, JAWAAD ABDUL-AZIZ YUSIF!!? dama na jima zuciyata na kokwanto akan rashin damuwar da bangani a tattare da Momy ba akan aurena da Yah Qaseem, miyasa Momy ta zaɓi rabani da masoyina wanda na ɗauka dukkan yardata na bashi? Bazan ɓoyeba ina ƙaunar Yah Qaseem sosai, sannan ban tsani Boss ba dan yanada nagartar da dukkan macen ƙwarai zataso mallakarsa matsayin mijin aurenta, to amma yaya zanyi da aunty Shahudah da dukkanma ahalina? Wannan kuwa bai zama cin amanaba ga Dad da halaccinsa a gareni?. ‘To ai bake kika ce a ɗaura miki aure da boss ɗinba ko’ wata zuciya ta ayyana min daga can gefe kuma wata tace, ‘Bakuma kowa zai fahimci bakida hannu a cikiba kamar yanda mama ta faɗa miki dangin Momy na ambata hatta da Yah Qaseem dayasha gargaɗinki akan mu'amularki da Boss ɗin’. Sharr na matso wasu hawaye masu zafi da suka cikan ido. A fili na furta, ‘Innata miyasa rayuwa takemin hakane? Miyasa duk yanda naso ƙoƙarin raɓar duniya saita goce mani? Tunda na rasaki keda Abba ban sake hawa dokin da yay daidai da cikar dukkan burukanaba, dana hau matakin nasara sai ƙaddara ta sake zuwa ta datse zaren da nake tafiya da ƙwarin gwiwata a kansa, kune kuka sanarmin duniya ba komai bace face wani filin gwagwarmaya na ƙwanji da zuciya, kune kuka tabbatarmin jajircewa na iya zama babban ƙawance da duniya koda duniyar bata buƙatar hakan, miyasa ni tawa jajircwwar a kullum nisantani take da tawa duniyar, shin gaggawa nake a cikin al'amarina shiyyasa nake durƙushewa kafin nakai kokuwa tawa ƙaddarar kenan kullum a curkuɗe?....”
“Wannan ai itace tabbatarciyar nasara kuwa Bilkisu, duk ɗan adam ɗin dakeji a zuciyarsa shine kaɗai wane, shine kaɗai za'aita kira wane daga farkon ƙarni har ƙarshensa to ya tabbata akwai ganganci da tarin wauta a al'amuransa, nasarar mai nasara itace ƙalubale, kadingaji kamar baka kaiba, baka cancanci kaiwaba, bazaka ka kaiba, sai kaga watarana ka kai harma ka wuce, lokacin da wani yake ganin ya rigaka ɗauka baka da damar ƙwata babu zato saiya suɓuce masa wajen hura hanci da gadara kai ka tsinta a ƙasa amatsayin shara kaci kai nagartar da har abadan bashi da damar hangokama, wannan rubutacciyar ƙaddarace ga mafi yawan mutane marasa gata, duk wanda ake ganin bai kaiba ko bazai kaiba shike wucewa wataran bilkisu, Jawaad shine mijin da yafi cancanta da nasararki, UBANGIJI kuma yafiki sanin miyasa ya zaɓa miki shiɗin, karki damu da adawa ko tunin kinci amana, a sannu duhun da kike ganin yana binki zai yaye yazama haske, a sannu waɗanda suke ganin keɗin baki cancantaba zaki zame musu hasken da zai mamaye rayukansu, ba'a cika baki da nasara, ba'a cika baki da farawa, ba'a cika baki da iyawa, ba'a cika baki da cancanta, ba'a gadara da abinda baka da ikon dawwamar dashi a hanunka tunda kaima a wajen wa
ni aka amsa aka baka, dagaske duniya rigar aro ce bilkisu, duk taƙamarka da ita da alfahari wataran saika tuɓeta da mutunci koda ƙasƙanci, duk abinda kaga kayi a duniya koka tsinci kanka kafin kai anyi dubunka masu ninkin banikin ɗinsa, bayanka kuma wasune zasu amsa su dama ko kaƙi ko kaso. Dan haka ki godema ALLAH da ni'imar da yay miki na mallakar miji mutumin kirki da bai ɗau duniya komaiba matsayin, dukda tarin dukiya da ALLAH ya bashi tun yana ƙanƙaninsa, shiba duniyar bace a gabansa, dan da itace bazai taɓa rabuwa da ƙyaƙyƙyawa irin Shahudah ba data haɗa komai na gata da nasaba ya ɗaukeki a matsayin ƴar riƙo a gidansu, wadda suke kallo ƙasƙantacciya a cikinsu. Akwai hikima mai yawa a al'amuran UBANGIJI bilkisu da jahili baya ganinsu ta fuskar data dace kinji”.
Kaina na gyaɗa mata a hankali, dan kalamanta sun sakani jin sanyi a raina, sai dai ina jinjina yanda zan rayu da mutum murɗaɗɗe mai wulaƙanci da ƙasaita irin Boss, aɗan zaman danai dashi na fahimci abinda ba'a sakashiba sam baya burgesa balle ya tsoma kansa. To miya kawosa cikin nawa lamarin ni kuma?.
Wannan itace tambayar data tsayamin a rai har dare.
_______________________________
Zaune yake a ɗaɗɗaure, an ɗaure masa idanu da jan ƙyalle, bakinsa ma a liƙe yake, shi kansa baisan a ina yakeba, abinda kawai ya sani da zai iya tunawa shine.
Ranar juma'ar da aka ɗaura auren su boss, lokacin da ake tsaka da wannan dambarwa ta neman sanin wanda ya rikita tsarin auren, yabi sahun masu gani da ido babu damar tofa albarkacin baki, har aka gama rikicin massallaci aka nufi gida, baiga boss ɗinsaba, dama baisa ran ganin nasanba a wannan lokacin, ganin su dad sun ɗunguma gida shima saiya hau napep domin komawa gidan ya ɗau jikkarsa ta tafiya gida weekend kamar yanda ya saba, dama sunyi sallama da boss tun a daren jiya, hakan yasa bai damu daya kirasaba koya jirasa. Shiru gidansu boss yake babu wata hayaniya, dan duk suna gidansu Shahudah, Mama Atika da mama badiyya dake fama da jiyyane kawai a gidan sai hadimai da samari waɗanda baza'a rasaba da suka dawo daga wajen ɗaurin aure. Jikkar kayansa ya ɗauka ya fito bayan sunyi sallama da baba mai gadi, cike yake da nishaɗi akan yanda auren ya kasance, Boss ya samu wadda yake masa fata tun sanda ya fara ganinsa tare da ita, yana gab da barin layin wayarsa tai ring, cirowa yay ya duba, gani mamansace yay murmushi tare da ɗagawa yana waige-waige, saida ya tabbatar babu kowa ama kusa dashi balle yay tunanin za'a jisa kafin ya fara maganarsa kai tsaye cikin zaurence kamar yanda suka sabayi. “Mamana albishirinki?”..............✍
Karku rikice, muje zuwa page 27, danjin ina aka dosa, nasan dai dayanku sun fahimci kowanene ma kafin akai ƙarshen zance😉🤫👌🏼.
ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.
SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.
HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO
MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.
MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.
BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....
abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, gamai buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu. 09032345899 sai kunzo😍😍😍😘.
Musha weekend lfy. Maybe kuma ku ganni lahadi koma gobe idan ALLAH ya kaimu😍😍😍😘.
ALLAH ka gafartama iyayenmu🙏🏻😭
Billyn Abdul:
Page 27
.................Daga can akace “goro yaron alkairi”. Ya cigaba da faɗin, “Da alamafa damunar bana zatai ɓarna, dan na hangi ɗakunan mutane da yawa sun buɗe ta sama batare da sun fargaba, kuma lallai bular zata zubda yoyon ruwan da zai iya haifar da ambaliya”. dariya ta tuntsure dashi daga can, tace, “Ɗan alkairi kana nufin dai dara zataci gida kenan, ɗan zaki yafara buɗe idanunsa ga rundunar kuraye masu gudun tseren neman abinci koda bai kasance halalinsu ba?”. “Ƙwaraima kuwa mamana, bana sanar miki wani ƙwai dake cikin ƙaya ya bayyana ba kwanakin baya, kuma duk haɗarin maciji ya gama shawaginsa ya barsa dan ya gagara haɗiya”. “ƙwaraima kuwa ka sanar min da wannan, a farautar zaki yaci karo dashi kenan matsayin abinci?”. “Hhhhh mamana kina birgeni da saurin ramfo zance, to wlhy ina mai tabbatar miki da hakaɗinne ta kasance, tsagerun dawa na tunanin Zaki yafi ƙarfin ruwan ƙwai sai gashi harma yana ƙoƙarin damƙosa cikin ƙayoyi”. “Kai ɗan alheri karka sa farin ciki ya karni yau ɗinan ban kalmashe bakin buhun dana farama ɗureba, yanzu dai ina fatan kana hanyar gidane?”. “Hasashenki baya zama kuskure mamana, mu haɗu acan na baki sauran bayani, dan kuwa garin bita da ƙullin ƴaƴan kura sun rufta damisa da ƴaƴan fadarta a ramin ɗan zaki, shiko ya afka musu ƙasa yasa ƙafa yatake harma da share wajen kwanciya domin buƙatar hutu”. Wata irin dariya ta shigayi mai cike da nuna tsantsar farincikinta data daɗe da mantawa da samunsa, yau ɗan nata ya biyata da daddaɗan labari. tace, “Ɗan albarka wannan zinaran kalamai naka sunfi ƙarfin saurare a salula, garzaya gida nima ina gab da iskoka, dan tun safe na nema alfarma ga Uwargida sarautar mata akan zuwa na duba mai babban suna”.
“Babu damuwa mamana ina tsumayenki acan, alkairin ALLAH ya cigaba da baibayeki tare da nasarar cigaba dayin haƙo a ramin azzalumai batare dasun fargaba har sai kinkai musu wuya lokacin sungama shiga tarko”.
Murmushi tayi daga can tana faɗin “Amin ɗan albarka” kafin ta yanke wayar, shima ya tura tasa a aljihun yana murmushi. Cigaba yay da tafiya harya fito titi, napep ya tara takaisa inda motocin ƙauyensu ke tsayawa, duk da garinsu ba ƙauye bane sosai dole muce dashi ƙauye, dan kuwa a ƙarƙashin wata ƙaramar hukuma yake, saidai yamafi l.g ɗin dukkan abubuwan cigaba, gashi a bakin titi kuma babu nisa da babban birin jiharsu. A mamakinsa ana saukesa falletsetsiyar mota na cin birki a gabansa, baiyi mamakin hakanba, dan kasancewarsa drivern boss yanada alaƙa da sanin mutane manya sosai ta fannoni da dama, lokaci-lokaci kuma yakanci karo da wasunsu koda ace shi ya mantasu dan dama dalilin shige da ficin boss na aiki yake sanin nasu. Wanda ke ciki ya sauke gilashi yana murmushi, sosai gimba ya zaro ido irin na bazatar ganin wanda bai zatoba, “Lah Ɓaleru! Dama rai kanga rai? wane mai gangancine yay kasadar baka idanunsa kaketa haska hanya dasu cike da ɗaukar faɗi?”. Dariya na cikin motar yay har yana bugun sitiyari, yace, “Gimba kaidai baka rabo da shaƙiyanci, kasan ɓalerun naka da shige-shige, ko iska ta shafamin lafiya. Daga ina haka zuwa ina?”. Gimba yace, “Wlhy gida nai, zamuje hutun ƙarshen mako domin ganawa da iyali”. Ɓaleru yay ƴar dariya da faɗin, “Mutumina baka wasa da gona, shiyyasa kullum gatanan cikin yabanya take, banga laifinkaba, yi birgimarka ka more mata sune jin daɗin duniyar ai dama. Shigo mu haura dan nima dai can na nufa ɗin”. Babu musu Gimba ya shiga yana maida masa murtanin shaƙiyancinsa, saida suka ɗauki hanya ɓaleru yace, “Nifa mamaki oganka ke bani, gashi jinin manya, ɗan tsohon shugaban ƙasa mai tarin dukiya, shi kansa ƙwaron kansane dan ya tara bayan wanda aka tara masa, amma abin mamaki kamar shima baya mora balleku ƴan muna jira ALLAH ya baka mu samu”. Murmushi gimba yayi, cikin son kare boss ɗinsa yace, “Ai abin nagartace, sai dai irinku ƴan ƙwanta ka mutu mu haye basa ganewa, komai boss yake da tsari a cikinsa, shi bai ɗauki wannan dukiyar da ta tsolema kowa idanu wata tsiyaba, marasa nasaba da itama amfanuwa suke da tagomashinta amma ta ƙyaƙyƙyawar hanya, bai yarda da almubazzaranci ba, amma shi kogine maiba na kus
a harma dana nesa, alkairinsa dake jiƙe dani ALLAH kaɗai yasan iyakarsa, sai dai ba'a iya ganinsa da idon gani saina zuciya”. Wata irin mahaukaciyar dariya ɓaleru ya kece da ita wadda harta bama gimba mamaki, kafin yabi ba'asinta ɓaleru ya jefa masa handkherchief a fuska, daga haka bai sake banbance fari ko baƙiba sai a washe garin safiyar yau daya jisa a ɗaure, idanu a rufe, bakima a ɓame. A zuciyarsa ya ayyana, ‘GADAR ZARE akaimin da wanda na sani kenan?’. Murmushi yay na takaici wanda a zuciya ya kasance dan babu bakin yinsa. Da ƙarfin masifa aka fincike abinda aka sa masa a baki, azaba ta sakashi sakin wani irin gurnani sai dai jarumta ta hanashi nuna gazawa. Yace, “Suwanene ku? Miyasa kuka kawoni nan? Minai muku?”. Banza akai masa babu amsa, yasan akwai mutum tare dashi, dan yana jin hucin numfashi kasancewarsa mutum mai basira da wata ɓoyayyir baiwa. Yay ɗan yi murmushin ƙarfin hali yana mai motsa jikinsa kaɗan, ɗauri akai masa bana wasaba, hakan yasa daƙyar yake iya motsawa. Kusan minti biyir yana jiran tsammani kafin a saka masa abu akan kunne.
Wata mahaukaciyar dariya aka sanya mai dogon zango daga cikin abinda basirarsa ta ankarar dashi wayace, daƙyar mai dariyar ya tsagaita daga can, kafin ya fara magana a kausashe. “Yaro ashe kaima tsagerane ban saniba, kai wanene daka isa tono abinda ke ɓoye? Ƙaramin naman daji abincin karnuka dakai har kakejin kakai zarra wajen yimana kutse a al'amuranmu? Banida lokacin doguwar magana dakai, yanzu za'a sakeka kai gudun mutuwarka kafin jininka ya zama halattacce ga bakandamiyarmu, wanda kakema aikinma bai isaba balle kai direbansa hhhhhhhhhhhhhh!!!!!”.
Wata dariya gimba ya kwashe da ita shima, a kausashe yace, “Faɗan sunƙuru alamace tamai tsoro, idan kuncika maza kufito filin yaƙi mai nasara saiya ɗauki kambu, boss kainuwane dashen ALLAH, zakine mai yagalgala mazan da suke kiran kansu mazanma balle ku mata maza masu ɓuya a rumfar..........
Kafin Gimba yakai ƙarshen zancensa an cire wayar daga kunnensa, taune leɓensa yay da ƙarfi. Kafin a maida masa baki a rufe, Bai sake jin motsin kowaba har yammaci, yana nan ɗaure babuci babu sha tun safiyar jiya rabonsa da abinci, garama ruwa yasha bayan fitowarsu massallacin juma'a, tun yana samun garkuwa daga yawu har shima yay tifƙewar da harshe bai iya juyashi ya zama abun mai gudana, ƙishirwa abune dake saurin illata mafi yawan halitta mai rai, balle irinshi mutum mai matuƙar son ruwa. Alamun duhun magriba da hasashe ne nashi yaji ya sake ɗaure garin, a wannan lokaci yaji an fara kuncesa, har aka gama tas bai motsaba bai kumace ƙalaba. Jansa aka shigayi keeeyyyy har zuwa waje, bashi da ƙarfin kare kansa dan haka ya salama bakinsa ɗauke da addu'a, tafiyar kusan mintuna uku kafin ai wurgi dashi.
Numfarfashi ya shiga saukewa a gwame, yakai hannunsa da ƙyar ya janye ƙyallen da aka ɗaura masa a fuska, baya ganin komai da ƙyau saboda idanunsa sun kwana sun yini a rufe, ga duhun magriba, saidai ya fahimci dajine yake. Da sauri ya shiga laluban wayarsa dake aljihu wadda suka gaza gani bisa kariyar ALLAH, ya kasance mai saka waya silent saboda baison takurama Boss ɗinsa da shigowar kira, a hankali ya saba da hakan har takai bayama buɗeta koda basa tare, tun ɗazun yakejin sautin shigowar kira dama, daƙyar ya iya ganin Number boss saboda idanunsa basa gani sosai sun masa nauyi ainun. Kai tsaye WhatsApp ya shiga, yay azamar danna recording ya fara magana a galabaice.
“Boss banjin zankai labari, dan basu kamani dansu barniba, akwai babbar ƙura a gabanka da bazan iya buɗe maka haske a kantaba yanzu saboda ƙarancin lokacin daya ragemin a duya, itace musabbabin shigowata rayuwarka tun fil'azal ka gafarceni da ɓoyewa, dama nabari ka fita daga wannan matsalar rikicin aurenne idan nadawo muyi magana, saidai ALLAH bai ƙaddara hakanba, amma nagodema ALLAH da wadda zata baka abinda yafi nawa tana raye, kai ƙoƙarin zuwa gidan Alh al..alhaji............ Ya kasa ƙarasawa saboda rawar da jikinsa ya fara na tunkarowar wata muguwar halitta garesa maiban tsoro. Jifa yay da wayar bayan ya ɗaga ɗanyatsansa saƙon ya tafi
kasancewar baya rufe data shi dama can. Baya ya fara jan jikinsa yana karanto duk addu'ar data zo masa, yayinda shikuma wannan halitta ke biyosa danƙyas-danƙyas tana buɗe baki da lashewa alamar dai taga abinci. Babu zato gimba yaji yay baya, ashe wajen gaccine mai zurfin gaske dan akan tsauni suke. Wata irin wahalalliyar ƙara ya saki data bada amsa kuwwa a dajin yay ƙasa.......
Wata irin mahaukaciyar dariya dahar saukarta ke kamar ƙasar dajin na girgiza ce ta fara ratsa tsaunika, anyita da tsayi kusan na mintuna biyar kafin ta lafa wani irin yare ya biyo baya da muryoyin mutane masu yawa. Duk wanda zai iya nutsuwar saurarar yaren zai fahimci kalaman cikinsa shirkace kawai ake ambato. (Wa'iyazubillah 😭ya ALLAH kasa mufi ƙarfin zukatanmu, ya rabbi ka saka duniya a tafukan hannayenmu karka sata a zukatanmu, kaiconmu, kaicon burikanmu kaicon son duniyarmu).
_________________________________
Ana sallar magriba su Momy suka koma gida akan su Uncle Nasir zasu zauna da Jawaad domin yasa ɗan-fir'auna ya saki hudah.
Momy da Shahudah ciki suka shige sukabar Aamilah na waya a barandar shiga falonsu.
Da mamaki Aamilah ke kallon akwatinan da aka jibge a harabar gidan gaban motar Qaseem, ƙiyyy!! Sautin jawo abu ya karate kunnuwanta, kallon wajen da ƙarar ke zuwa tayi, Qaseem ne jaye da jikkan gana must go irin ƙatuwarnan sabuwa dal, amma tsabar yanda yasa ƙarfi wajen janta har hannu ɗaya ya fincike yana lililo, duk dai ya ganta yiyai tamkar basan da zamantaba, baba maigadi dai tun ɗazun yana hangen Qaseem ɗin daga ɗakinsa, tsabar baison yafito ya gansa ya sakashi aikin tayashine ya sakashi maƙalewa cikin ɗakin yana leƙensa ta Window. Jikkar ya dangwarar ya sake juyawa zuwa sashensu, daga shi sai gajeren wamdo da baƙar singlet datai mugun fidda masa siffarsa ta ƙaƙƙarfan namijin dake cin ƙarfe. Saida taga ya shige kafin ta juya da gudu gulma na cinta har saura kaɗan ta faɗi, ALLAH dai ya ara mata damar dafe ƙarfen da aka ƙawata barandar ƙofar falon nasu dashi, ƙara kwasa tai a gujen ta shiga tana ƙwala kiran Momy dake sama abin duniya ya isheta ga Shahudah tsaye kanta tana ribzar kuka da mata fitsara. Sosai kiran da Aamilah ke mata ya firgitata, ta miƙe zumbur ta fito tanabi matakalar benan da gudu-gudu. “Haba auta wannan wane irin kirane haka kamar wata baƙauya, miya farune shin kikemin kiran mafarauta?”. Baki Aamilah ta cuno bayan ta murguɗama Momy kamar wata sa'arta, kafin cikin taɓara tace, “Kajimin Momyn nan, dama kika samu na taimakeki na kawo miki labarin da ɗuminsa, toga ɗankican yana haɗa kaya da alama barin gidan zaiyi”. Sosai gaban mom ya faɗi, batama tsaya saurararta wanne a cikiba ta fice daga falon da sauri, dafa mata baya Aamila tayi tare da Shahudah data fito idanu a kumbure.
Qaseem dake ta faman lodama ƙatuwar motarsa kayan yayma momy dake masa magana kallo ɗaya ya ɗauke kai batare da yace da ita ko ci kanki ba. Muryarta har zuga take na alamun ɓacin rai tace, “Qaseem wai badakai nake maganaba? Shin mikukeson maidanine a gidannan kai da Shahudah? shin bazaka nutsu kai ka fahimci uzirinmuba, Na shiga uku ni Aysha, wane irin mugun asiri wannan yarinyar ta haɗaku da shine kaida yaronan Jawaad da kuke ɗaukar kowa ɗan iska akan lamarinta?”. Cikin zafin murya Qaseem yace, “Nifa kin bala'in cikani da surutu hajiya, Please ki barni nai aikin gabana Mtsooww!!”. Ya ƙare maganar dajan wani wawan tsaki yana ɗauke kansa ya cigaba da loda kayansa a motar. Mutuwar tsaye kawai Momy tai tana kallonsa, Aamilah ta kwashe da dariya tana kallonsu, “Faɗan Uwa da ɗa abin birgewa, kucigaba da gashi guys”. Baki Shahudah ta taɓe tana mai juya manyan idanunta alamar zubama Qaseem harara, tace, “Ɗan jaraba duk bakai kaja manaba, wani iyayi da ƙwala kai a farantinne ya kaika nacema banzar yarinyarnan ƙazamiya mara gata, idan da baka maƙale matanba ta gidan uwarwa aurena da naka zasu haɗu ballema har bb ya aikata haka, asararre kawai mai baƙar zuciyar tsiy.....”
Jikake tasss!! Qaseem da babu wanda ya lura da isowarsa gaban Shahudah ya sauke mata wani wawan mari, ƙasa ta zube tana garsheƙ
ar kuka daja masa ALLAH ya isa, to daman zuciyar ƴan mazan a kusa take, neman wanda zai amayarwa yakeyi, gashi ya samu cikin sauƙi, dan haka ya shigar tamkar an aikosa. Duk ihun da Aamilah keyi da Momy bai sauraresuba, sai ma tsarabar mari Aamilah ta samu itama, Momy kuwa ya hankaɗeta. Qaseem yanada Masifaffiyar zuciya irin wadda idan ta yunƙuro ɗinan sam bayajin bari, dan tamjar zugasama yake, sannan shifa cinnakane baisan na gidaba. Wanna. mugun zuciyan da ALLAH ya basu shida Jawaad itace ta hanasu zama ƙarƙashin inuwa ɗaya, dan kowa yanaji da kalar tasa, kawai shi Qaseem yafi Jawaad saurin fushine, dan Jawaad na dannewa yay kawaici har saika kaisa ƙarshe, amma ga Qaseem sam ba haka bane, sha yanzu magani yanzu, ga kuma ɗanbanzan riƙo saikace dangin kutare🤦🏻.
Iya gwargwadon iko babu algus Shahudah ta daku harma da Aamilah daya koma haɗawa daga ƙarshe, dama yanajin haushinsu akan abu biyu, dukan Bilkisu da jimata ciwo, saikuma gudunmawar da suka bada akan ai masa aure da Azeema. Daƙyar da suɗin goshi baba mai gadi da kuku suka amshi Shahudah da Aamilah a hannunsa, dan yay musu kaca-kaca abinka da farar fata, Shahudah harda fasa mata baki akai jini sai ɗiga yake. Yace, “ƙananun marasa kunya, daga yau idan harku kun cika tsagerune dan ALLAH kusake shiga cikin al'amurana”. Kuka kawai suke daga su har Momy, babu wanda ya iya tanka masa har kuku da baba mai gadi suka gama loda masa kayansa a motar, sashensu ya koma ya ɗakko sauran tarkacensa ya shige mota ya fice batare da ya sakebi takantaba.
Kai tsaye gidansa ya zarce, dama harya ajiye mai gadi tun jiya, kodaga waje kasan gidan ya haɗu, ya mugun ƙawatuwa da shukoki masu ƙamshi da daɗi, ga ƙamshin sabon fentima na tashi. Dakansa yayta shiga da kayan, da yake ALLAH yayisa mutum mai hanzari da zafin nama sai gashi ya gama sakasu ciki tas.
★★★★★
Bayan barin Qaseem gidan babu jimawa Dad ya dawo, iske Momy yay zaune ta zabga tagumi, Shahudah na kwance barcin wahala yay gaba da ita ta ɗora kanta a cinyar momyn. sai Salman da Aamilah dake lido a d/table. duk sannu sukai masa, ya amsa yana zama kusa da momy tare da kamo hannunta cikin nashi. “Humairah mike faruwane?”. Muryarta na rawa tace, “Qaseem ne ya tafi?”. “Ya tafi? Ina ya tafi to?”. “Muma bamu saniba, ya kwashe duk kayansa na gidannan”. Cikin taune leɓe Dad yace, “Bari dai zamuyi magana, yanzu tare nake dasu Alhaji Nasir suna falon baƙi, mun kira yaronan ne da aka ɗaura aurensa da mamana zaizo”. Zumbur Momy ta miƙe jikinta har rawa yake ta ture kan Shahudah batare data tuna tana jikinta tana barciba, tace, “Ya yarda ɗin zaizo Dadynsu?”. Fuskarsa ɗauke da murmushi yace, “Eh ya amince, drivern Alhaji Nasir ma yaje ɗakkosa”.
________________________________
Bayan Jawaad ya dawo daga sallar magriba shiryawa yay ya amsa kiran da Alhaji babba yay masa, kansa ciwo yake masa, amma bashi da ikon bijirema kiran kakan nasa, ballema yaji muryarsa wani iri kamar yana tare da damuwa, tun da ranama ya fahimci hakan, ya haƙurane kawai ya barsa da yace masa babu komai..
Fitowa yay yanata baza ƙamshi, sai dai fuskarnan a cinkushe babu walwala. ya tsaya suka gaisa da mai-gadi har yake tambayarsa gimba bai shigo bane?. mai-gadi yace, “Aiko bai isoba Oga, ni harma na fara tunanin ko lafiya? Dan tunda ya tafi bamuyi wayaba kuma kaga har lokacin daya saba dawowa ya shige amma shiru”. Jimm Jawaad yay alamar tunani, dan shima dai tunda gimba ya tafi basuyi wayarba kam, to wannan hargitsicinne ya ɗauke masa hankali gaba ɗaya har bai ɗauki hakan komaiba. Ya ɗan sauke numfashi yana kallon mai-gadin. baba bara dai naje na dawo, idan har lokacin bai shigeba saina nemesa naji mike faruwa?”. Mai gadi yace, “To to ba laifi oga, ALLAH ya maidoka lafiya”. “Amin” Jawaad ya faɗa yana ficewa, sai dai acan ƙasan zuciyar tasa maganar gimba taƙi gushewa.
A ƙofar gida ya iske Alhaji babba zai shiga massallaci, dan haka yay fakin anan waje ya fito suka shiga tare, bayan sun fito Alhaji baba yay sallama da mutane maƙwaftansa da ragowar ƴan anguwa masu salla anan kamar yanda ya saba, kafin ya kama
hannun Jawaad dake masa shagwaɓan shifa fura zaisha, Alhaji babba ya bada a siyo masa. Alhaji babba dake murmushi ya tsaya yana dungure masa kai, “Kai miyasa idan rikicinka ya motsa babu wanda ka raina saini? Kaje kaima su Mariya mana”. Fuska Jawaad ya yatsine saboda ciwon da kansa ke masa yace, “Nidai ka daina sawa gaban mamana na faɗuwa a darenan, kabama Tanimu ya sayo mani inba hakaba bazan sake zuwa kwana gidanka ba”. Dariya Alhaji babba yay da jan hannunsa suka cigaba da tafiya, yace, “Yoni ALLAH na tuba aina yayeka da zuwa kwanarmin gida, matarka ta jajiba nima na huta da rigimarka hakanan”. Jawaad yace, “Basai na ɗakkota muke kwana anan ɗin tareba”. “Bana gayya, ku zauna gidanku nima aure zanyo”. Ciki dauriya Jawaad ya ƙyalƙyale da dariya, koba komai yarage nauyin da zuciyarsa tayi da tattaunawa da kakan nasa, shi kansa Alhaji baba sai yaji damuwarsa ta sassauta.
Bayan sun zauna Alhaji baba ya zubama Jawaad fura mai ƙyau da daɗin gaske da bai rabo da ita ya dubesa, cike da jin daɗi yake shan furan sanyinta na ratsa masa zuciya da ƙirji. “Muhammad kasan miyasa na kiraka kuwa?”. Kallonsa Jay yayi ya girgiza kansa batare da yace komaiba. Alhaji baba ya ɗan sauke numfashi, murya a sanyaye yace, “Akan matarkane” Saida Jawaad ya haɗiye furan daya sha kafin yace, “Matata kuma?”...............✍
Ƙyan alƙawari cikawa, sai dai wanda na ɗauka ni ya gagara cikar dalilin birkicewar wattpad, harna fara canja page ɗinma sai ALLAH ya taimakeni ya dai-dai ta🤦🏻, page ɗinnan kaɗai gareni babu nagobe saboda matsalar wattpad ɗinan ta ɗauki hankalina banyi typing ba, ƴan telegram sunce a turo muku kawai, amma da wuya kujini gobe idan ALLAH ya kaimu zan samu nayi typing ɗin jibi idan munada rabon kaiwa. Gaisuwa ga kowa da fatan alkairi😍😍😘😘.
ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.
SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.
HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO
MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.
MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.
BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....
abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.
Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899
sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.
Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300
Sai kunzo😍😍😍😘.
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻
Billy Abdul, [12/15/20, 12:50 PM]
Page 28
................Alhaji babba ya gyaɗama Jawaad kai alamar eh ita. Cike da mamaki Jay ya ajiye kofin hannunsa yana tsatstsare kakan nasa da idanunsa cike da sonjin ƙarin bayani.
Murmushi Alhaji Babba yay masa tare da kamo hanunsa, “Daina tsareni da waɗanan idanun naka ba wani abu bameba, kawai inason sanin dangin mahaifinta ne”. Sassanyar ajiyar zuciya Jawaad ya ɗan sauke, kafin shima ya riƙe hanun Alhaji Babba da ƙyau a cikin nashi, “Baba nima inason saninsu, sonake kawai wannan ƙurar ta lafa itama ta sakejin sauƙine”. Alhaji babba yace, “Kayi tunani mai ƙyau, inason kayi ƙoƙari ka bincika, sannan yaya maganarka da mutanen gidanku? Da kuma maganar shi wanda kasa ya auri yarinyarnan ta wajen Ali?”.
Murmushi Jawaad ya ɗanyi ya ɗauki furarsa zai cigaba da sha, ganin zai basar da zance Alhaji babba yace, “Nasanfa ka jini”. Ƴar dariya Jay yayi yakai kofin bakinsa, “ALLAH ka iya rigima kaima tsohon nan, karka damu ina sane da komai”. “Nasan kana sane da komai Muhammad, sai dai hankalina ya tashi matuƙa jin ba mutumin kirki bane habibun, kajifa wani suna da Nasiru ya kirashi dashi ranar”.
Jay yay murmushi kawai batare da yace komaiba.
Sun cigaba da hirarsu har zuwa ƙarfe tara ya fita, yaso zuwa asibiti, amma ganin dare yayi sai ya haƙura ya nufi gida abinsa. A gate ya tsaya ya tambayi mai-gadi ko gimban ya dawo?. mai-gadi ya tabbatar masa da bai dawoba, ya kira wayarsa kuma gashi tana ring amma ba'a ɗagaba.
Sosai abin ya ɗaurema Jawaad kai, daga baya kuma ya ajiye tunaninsa akan inhar da safe bai dawoba zaisa abi bayansa garin nasu aga ko lafiya?. Da wannan tunanin yay shirin barci ya kwanta.
_________________________________
Su Dady sun karɓi baƙuncin surikinsu habib, duk yanda Dad yaso su Momy su zauna basai sunzo falon baƙiba hakan ya gagara, dole ya barsu sukabi bayansa, ba ƙaramin tashin hankali Shahudah ta shigaba da ganin wanda ake kira wai matsayin mijinta, daka gansa kaga cikakken tantiri marajin magana, cike da isa ya zauna a kujerar da aka nuna masa sai wani cika yake da batsewa.
Ya kafe Aamilah da Shahudah da kallo yana wani lasar laɓɓa tamkar tsohon maye, ko kunyar su Dad bayaji, dama daya shigo babu wanda ya gaida, bama su ishesa kallon arziƙiba.
“Wace cikar tawa anan?” yay maganar cike da gadara. Babu wanda ya tanka masa a cikinsu, sai Shahudah da Aamilah da suka zuba masa wata shegiyar harara. Ya bushe da dariyarsa mara daɗin ji yana faɗin, “Dama ace ana auren yaya da ƙanwa wlhy da duk haɗawa zanyi hhhhh! Dana kwashi gara aradu...” cike da tsiwa Aamilah da tafi Shahudah jin hausa tace, “Uwarkane garan shege mai suffan aljanu.....” wata wuta data gitta ta idanunta mai stars ce ta hanata kaiwa ƙarshe, lokaci ɗaya jinta da ganinta ya ɗauke baki ɗaya ta zube a jikin Dad daya tarota. Babu wanda yaga sanda Ɗan-fir'auna ya ƙarasa gaban Aamilah sai ƙarar maruka sukaji kawai.
A fusace Dad yace, “Kai ƙaramin ɗan tsagera, wanene ubanka da har zaka mararmin yarinya a gabana?”. Kallon dad ɗan fir'auna yay ya watsar, kafin cike da gadara yace, “Sanin ubana a gareka dattijo ai tamkar yankewar numfashinka ne, dama kun kiranine domin kuci zarafina komi? kunga dalla malamai ku bani matata na wuce na fasa zaman....” da sauri Uncle Uwaisu ya taresa cikin lallashi yana bashi haƙuri, amma fir ƴaki sauraren kowa, Aamilah dai ta farfaɗo da ƙyar bayan an zuba mata ruwa, Shahudah na rakuɓe lungun kujera sai tsiyayar da hawaye takeyi jiki na rawa, harga ALLAH tsoronsa takeji, a ranta kuwa ayyanawa take ashe Bilkisu baturiyace, dan ɗan-fir'auna ALLAH ya bashi baƙi, wanda daga gani kasan shaye-shaye ya sake taka rawar gani wajen ƙara masa shi. Da ƙyar suka samu ɗan-fir'auna ya zauna bayan an saka Shahudah da Aamilah sunbar falon, Salman kam yay laƙe kamar baya falon (hege yaga maza🤣😜).
Duk yanda su Uncle Nasir sukaso lallaɓa ɗan-fir'auna akan ya saki Shahudah yace shifa sam baisan wannan zanceba, dan yanzuma da shirin ɗaukar matarsa yazo yana buƙatar abinsa, tunda yana zamansa aka kawo masa tallansu. Har ƙasa Momy ta duƙa tana kuka da roƙonsa amm
Billy Abdul, [12/15/20, 12:50 PM]
a sai dariyar wulaƙanci da cusa haushi yake musu.
“Kungafa kubar ɓata lokacinku akan roƙonama, tayaya kuke tunanin zanyi sake da wannan babbar kaddarar ne haka, yo ko shugaban ƙasa ai nafishi hura hanci yanzu akan wannan cikar tawa, ku manta kawai a saimin royal bed zan kama hayar gida aje aimin jere gobe, babu damuwa idanma kunkai sati danshi shiri wuyane dashi, ko a hotel mayi amarcin satin guda kafin ku kammala surukai..” ya ƙare maganar da miƙewa yay salute nasu zai fice. Da sauri Dad yace, “Nawa kake buƙata a biyaka ka sakarmin yarinya?”.
Tsayawa ɗan-fir'auna yayi, ya juyo yanama Dad wani matsiyacin kallo maiban tsoro, sai kuma ya bushe da dariya tare da dawowa da baya. Yace, “Zan iya amsar kuɗi na saketa pale, tunda yanzu na auri ƴarka ka zama pale ɗina nima, ammafa kasani saina ɗanɗana kona sati ɗayane dan yawuna ya biya, a shiryata da safe nazo na amshi kayata, nanda sati biyu saiku cakemin naira miliyan hansin na baku ƴarku, idan haka bai mukuba kuma banida matsala, iyakaci inta mata ciki duk bayan wata tara ta ringa juyen jajayen ƴan dugwi-dugwi irinta, koba komai na samu surukai masu kuɗi nima nan gaba tunda naga jar fatar ake yayi yanzun” ya wani ɗage musu gira cike da barikanci yay ficewarsa.
Babu wanda bai jiƙe da zufaba a falon, tun fitar ɗan-fir'auna babu wanda ya iya magana sai kuka Momy dake tashi. Salman ya miƙe cikin raɗa-raɗa yace, “Wlhy kuyi ƙoƙari ku biyashi, dan wannan dagani zai iya take mutum ya yanka tamkar ya yanka kazar gidan gona, ku rufa mana asiri dad dan kuwa su momy sun kwaso mana bala'i, wlhy barin ƙasarnan zanyi idan an gama watandarku na dawo zaman gaisuwa”. Ya ƙare maganar da ɗai-ɗai yana kallon ƙofa, da gani kasan a tsorace yake (Kana bani yaji Salman🤣, lusarin banza😠).
WASHE GARI.
Dad na zaune a harabar gidansa abin duniya ya taru ya masa yawa, tunda ya dawo sallar asuba bai iya shiga cikiba, a daren jiya da ƙyar suka samu Shahudah tai barci, dukta gama fita hayyacinta.
Baƙon da aka turo daga masarautane ya samu isowa, ya ƙwanƙwasa gate mai gadi ya leƙa, sai da suka gaisa sannan yace, “Magatakarda ne daga masarautar gagara badau, an aikoni domin isar da saƙo ga Alhaji Ali ko yana nan?”. Mai-gadi yace, “Ƙwarai yana nan, sannu da zuwa bara a sanar masa”.
Sai da baba mai-gadi yay sallama sau kusan uku sannan Dad ya jisa, bai amsaba sai zuba masa idanu da yayi. Baba mai-gadi yace, “Alhaji baƙone wai daga masarauta”. “Masarauta kuma? Ni miya haɗani da masarauta malam Amiru?”. “To Alhaji wlhy ban saniba, yadaice daga can yake”. Da hannu kawai Dad yay nuni alamar baƙon ya shigo. Baba mai-gadi ya koma domin shigo dashi.
Sai da baƙo ya zauna a kujerar robar da baba maigadi shima ya ajiye masa sannan suka gaisa da Dad, cikin nutsuwa magatakarda ya korama Dad bayani akan gimbiya ta bada umarnin Bilkisu zata koma masarauta da zama har sai ranar tarewarta gidan mijinta. rasa abinda ma zaice Dad yayi, sai tsurama magatakarda ido yay kamar zai haɗiyeshi dasu. Har magatakarda yaymasa sallama ya tafi bai dawo hayyacinsa ba, sai faman juya takardar hannunsa da magatakarda ya kawo yakeyi, shi yanzu abin tambayarsa anan Bilkisu ce takai ƙararsa masarauta kokuwa Jawaad? Kai yasan halin Jawaad da shegen taurin kai, bazai taɓa kai magana masarauta ba dan tsaurin idonsa bazai barsa ganin ya gaza ba. To amma bai zaton Bilkisu nada irin wannan wayon, kuma itada takema kwance a asibiti. Gaba ɗaya ransa ya kuma jagulewa, cike da sassarfa ya tashi ya shige ciki.
★★★★★★
Jawaad kam koda ya gama shirinsa na office ya fito sai ya iske Gimba bai dawo ba, mamaki ya kuma cikashi, dan jiya bayan ya dawo ya kira Number gimba har sau biyu kafin ya kwanta amma ba'a ɗagaba, yanzu kam yafara tunanin babu lafiya, akwai wani saurayi a gidan da aikinsa kawai kula da flowers ɗin gidanne, garinsu kusada garinsu gimba yake, hakan yasa Jawaad ya kirashi yanama tsaka da aikinsa na bayin fulawar. Durƙusawa yay yana gaida Jawaad, Jawaad ya amsa da masa nuni ya tashi. “Banace ka dainamin irin wannan gaisuwarba Balarabe, kadaina min wannan durƙuson kamar
Billy Abdul, [12/15/20, 12:50 PM]
wani mai neman gafara kaji”. fuskar balarabe ɗauke da murmushi yace, “Alhaji nagode sosai, amma nariga na sabane, koba aiki nake ƙarƙashin kuba aika girmeni nesa”. Girgiza kai kawai Jawaad yayi, ya ciro kuɗi a aljihunsa ya miƙa masa 3k, “Balarabe ajiye aikinnan naka zakai dan ALLAH kaje garinsu Gimba ka ganomin ko lafiya yake? aikasan garin ko?”. Da sauri balarabe yace, “Eh Alhaji, ai daga garinsu zuwa namu da ƙafama muke zuwa, kuma har gidansa na sani tunda naje sunan yaronsa da aka haifa masa na ƙarshenan mai sunanka”. “Okey Alhmdllh, kayi ƙoƙari kaje yanda zaka dawo da wuri, bani number ka na kira kaga tawa, daka isa kasan halin da yake ciki ka kirani na sani kafin ka juyo”. Cike da girmamawa balarabe yake sauraren number da Jay yake faɗo masa yana sakawa a wayarsa nokia, bayan ta cika ya kira shima jay yaga tashi.
Mota Jawaad ya shiga, yau da kansa yay driving, kai tsaye asibiti ya nufa, sai da yaje suka gama magana da likita sannan ya nufo ɗakin da Bilkisu ke jiyya. Sallama yay suka amsa, kafin ya tura ƙofar ya shiga.
Kasa ɗagowa nai in kallesa, dan wata matsananciyar kunyarsa nakeji a raina, cikin girmamawa ya gaida mama, aunty Batool ma ta gaidashi da tsokanarsa, gaisuwarta kawai ya amsa bai maida mata magana akan tsokanarsa da takeba, na ɗago ido kaɗan nai masa kallo ɗaya na janye da faɗin, “Ina kwana”. shiru kamar bazai amsaba, sai da ya ajiye kwalin maganina daya ɗauka yana dubawa sannan yace, “Lafiya ya jikin?”. Ahankali nace, “Naji sauƙi”.
Jawaad ya ɗauke kansa daga Bilkisu ya maida ga mama, “Mama Doctor ya sallameta, saiku haɗa kayanku, zanje office yanzu, nanda awa ɗaya zuwa biyu zan dawo sannan ai kun kimtsa”. Mama tace, “To to Alhmdllh, ALLAH yasa haka shiyafi alkairi, to amma kayanta fa? Kasan komai yana can gidan”. Ɗan jimm Jay yayi idonsa akan Bilkisun, ya sauke numfashi kaɗan yana ɗauke idanunsa, “Inaga mu manta da zancan zuwa gidansu yazu, bara naje na samo mata wasu kayan kawai”.
Jin abinda yake faɗama mama yasa na ɗago da mamaki na kallesa, hakan yay dai-dai da shima ya juyo gareni, idanunmu ne suka shige cikin na juna, nai azamar janye nawa da fargabar ina kuma zan koma? Badai gidan nasaba? yanzu har rashin gatana yakai irin haka da.......
Katsemin tunani yay da cewar, “Dami-dami kike buƙata?”. Idanuna cike da ƙwalla na ɗago na kallesa, ganin har yanzu ni yake kallo saina maida kaina ƙasa, muryata cike da tahowar kukan da nake dannewa nace, “Miyasa bazan koma can ɗinba?”. Banza yay bai amsa minba, hakan yasa hawaye masu zafi suka silalomin akan kumatu. Sautin siririn tsakinsa kawai naji, cikin faɗa-faɗa yace, “Haka na gadama dole kuma hakan za'ayi, idan kuma kika nema dagulan lissafi ALLAH yau ɗinan zaki tare”. Babu shiri na ɗago kai da sauri, wata uwar harara ya zubamin. Dole na maida kaina ƙasa. Wata ƴar ƙwafa yayi, sai takunsa ya biyo baya, kafin naji buɗe ƙofa da rufewa alamar ya fice abinsa. Koda na ɗago sai naga ashe daga ni sai shine ma a ɗakin, sam banji sanda su mama suka fitaba, dukda inajin motsin ruwa a bayi alamar ɗaya na ciki ɗayane ya fita.
Gaba ɗaya zuciyar Jawaad a jagule take, sai dai jarumtarsa ta ɓoye hakan, shi mutumne tamkar kowa, yana farin ciki yana baƙin ciki, yana shiga matsala yana shiga tashin hankali, kawai dai ALLAH yayisa mai zuciyar dakiyane kamar yanda ALLAH yay mafi yawan maza da juriya akan abu komin zafin da sukeji akan al'amari. Tafiyar da bata wuce mintuna goma ba ya isa wani haɗaɗɗen boutique, yanda suka tarbesa zai tabbatar maka da an masa farin sani a waje, sai gaidashi suke cike da girmamawa. Wani mai tsananin kama da Jabeer ne ya fito daga wani lungu, ganin Jay ya sashi faɗin, “Yah Jay barka da zuwa”. Kallonsa Jay yay daɗan murmushi yace, “Yauwa Kabeer, ya kasuwar?”. “Alhmdllh Yayah, kanason wani abune?”. Kai kawai Jay ya kaɗa masa kafin ya miƙe a kujerar da yake zaune. Yana gaba Kabeer na biye dashi har wajen da kayan mata suke, tsala-tsalan jallabiya da ƙananun kaya harma da ɗinkakkun atanfofi da shadda duk sunda. Ahankali yake binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya, karon farko a rayuwarsa da yazo saima ma
Billy Abdul, [12/15/20, 12:50 PM]
ce kaya shi ɗaya, ko sanda suna tare da Shahudah hakan bai taɓa faruwaba, dan ita a tsarinta bata sayen kaya anan saina ƙasashen ƙetare, hakan yasa koda yaga abu ya burgesa baima taɓa wahal da kansa wajen saya matanba.
Ganin ya kasa ɗaukar komai kabeer yace, “Yah Jay aida ka kira ka faɗi duk abinda kake buƙata bama saika zoba”. Guntun murmushi jay yay masa kawai daɗan taɓa kafaɗarsa, kafin ya fara nuna masa duk abinda yay masa wanda ya ƙiyasta a ransa zaiyi dai-dai da jikinta, saida ya ɗauka kaya kusan kala goma sha biyar, sannan ya ɗauka takalma uku da hijjabai huɗu ya zaɓi akwatin da za'a zubasu. Yasan dolene ƴa mace budurwa kamarta ta buƙaci kayan ciki, to amma shi ta ina zai fara tunda ba sanin seize ɗinta yayba. Kallon sashen da kayan suke yay, gasunan kala-kala kuma duk seize ɗin da kake buƙata zaka samesu, yaɗan yatsina fuska kafin ya nufi wajen, amfani yay kawai da yanda yake hasasota cikin idanunsa ya ɗauka matasu aka haɗesu da waɗancan. Card ɗinsa ya bama Kabeer, ganin kabeer na wani noƙewa akan baza amshi kuɗinba dan harya kira Jabeer ya sanar masa ga Jawaad ɗin a wajen yace karsu amshi kuɗi su rubuta su aje idan yazo zai biya. (Wajen na Jabeer ne, ƙaninsa kabeer ke kula dashi sai sauran ma'aikata). Cikin sosa ƙeya Kabeer yace, “Yah Jabeer yace karna amsa”. Sosai Jay ya kafesa da idanunsa da yau gaba ɗaya babu haske a cikinsu saboda damuwa. “Kiransa kai ka faɗa masa nazo?”. Kasa cewa komai Kabeer yay sai faman susar ƙeya yake, Jay yay gaba a binsa zuwa mazaunin kabeer ɗin da yake shine mai amsar kuɗi. Ɗaya daga cikin yaran wajen ya kira ya duba masa kuɗaɗen duka kayan aka zubasu a akwati, shikuma ya saka card ɗinsa ya cire adadin kuɗin yay ficewarsa aka bisa da kayan.
★★★★★
Fitar jay babu jimawa a asibiti Qaseem yazo, cike da mamaki Bilkisu ke kallonsa jikinta sai rawa yake dan tunda ta kwanta a asibitin nan sai yau ta gansa, baiko kalli mama ba balle ta samu darajar gaisuwarsa ya finciki hannun Bilkisu dake zaune bayan ta kimtsa suna jiran dawowar Jawaad, da sauri mama ta riƙe Bilkisun da faɗin, “Lafiya kuwa Qaseem? Ina zaka kaita?”. Wani banzan kallo ya mata yana figar bilkisu batare daya tankaba, itako kuka take iya ƙarfinta da roƙonsa ya sake mata hannu karya jimata ciwo, amma sam yaƙi sauraren kowa. Tun suna ɗaukar abin wasa har yanema fin ƙarfinsu, dan Doctor ma yazo ya basu sauran maganin bilkisun shima ta ritata dashi. Rikici bana wasaba ake kwasa da Qaseem har ALLAH ya maido Jawaad asibitin. Tunda ya gabato wajen yakejin hayaniya, cike da mamaki ya shiga dan ƙofar a buɗema take. Idanun sane suka fara sauka akan hannun Qaseem dake riƙe dana Bilkisu, tuni idon ƴan mazan ya rufe, a wata irin matsananciyar tsawa yace, “Qaseem sake mata hannu!!”. shi Qaseem ma sai yanzu yaga Jawaad ɗin, shima a fusace yace, “Anƙi a saki ɗin, koka saketa, koma karka saketa zan wuce da itane”. Saukar wani bahagon bugu kawai Qaseem yaji akan damtsen hannunsa, ai baimasan ya saki hannun Bilkisu ba saboda gaba ɗaya jijiyar hannunsa ta saki lokaci guda saboda azaba, kafin ya gama dawowa hayyacinsa Jay yaja hannun Bilkisu dake kuka sun fice daga ɗakin. Ganin haka yasa Doctor saurin rufe ƙofar ya kulle danya bama jay damar barin asibitin gaba ɗaya.
Kuka bily take cin ƙarfinta har suka hau titi, jin ta cika masa kunne yasashi taka wani wawan birki da batasan sanda tai tsale ta koma jikinsa ba. Sai jinta kawai tayi zaune ɗare-ɗare bisa cinyarsa ta cusa kanta a ƙirjinsa tare da ƙanƙamesa. ALLAH ne yaso Jawaad ya tsaida motar, da babu abinda zai hana su kife a hanyarnan. Gaba ɗayama sai ya kasa cemata uffan, sai rumtse idanunsa da yay yana mai cije leɓensa na ƙasa da masifar ƙarfi kamar zai hudashi.
Jin shiru mun tsaya ga ƙamshin turarensa yay mugun addabar hancina haryazama shine iskar da nake shaƙa ya sani ɗagowa, sosai na zabura ganina a jikin boss ɗare-ɗare, innalillahi.... Na shiga ambata ina rawar jikin sauka, harna koma inda na baro bai motsaba, nikuma ban iya kallon fuskarsa ba saboda tashin hankali da matsananciyar kunyar dana tsinta kaina a ciki. Jin tsahon mintuna biyar yaƙi cewa komai yaƙ
Billy Abdul, [12/15/20, 12:50 PM]
i kuma ya cigaba da tafiya yasani satar kallonsa ta gefen ido ina share hawayena da sukaƙi tsayawa. A kife yake kan sitiyari bana ganin fuskarsa, tsorone ya sake kamani, murya na rawa nace, “Dan ALLAH kayi haƙuri, wlhy tsorata nayi”. A fusace ya ɗago yana watsamin wani irin harara, yanda idanunsa sukai matuƙar jazur fiye da farkone ya kuma ɗagamin hankali. A kausashe yace, “Idan baki rufemin bakiba saina canja miki kamannin fuska! Saboda na raboki dashi kikemin wani kukan banza da wofi?!!”. Da sauri na shiga girgiza masa kai ina mannewa da ƙofa, dan yanda yay maganar tamkar zai haɗiyeni ɗanyane, ni tun lokacin da naga fushinsa nake tsoron cigaba da ganin hakan. Yay ƙwafa da ƙara zubamin harara, “Share waɗanan banzayen hawayen”. Saurin saka ƙasan hijjab ɗina nai na goge tas kamar yanda ya buƙata, sake ɗauke kansa yay daga gareni Batare da yace komaiba ya tada motar da fusgarta muka cigaba da tafiya.
Duk da hankalina a tashe yake da yanda yake zuba gudu a titi ban sake gigin yin wani abuba, sai kaina dana tusa a cikin cinyoyina ina addu'ar ALLAH ya kaimu lafiya dukma inda muka nufa.
A halin da yake ciki yanzu bazai iya shiga masarauta hakaba, hakan yasa yay fakin daga waje, fita yay da waya a hannu, bayason kiran gimbiya dan haka ya maida akalar kiransa ga dattijon nan, bugu biyu kuwa ya ɗaga suka gaisa, Jawaad yay masa bayani a taƙaice. Dattijo ya amsa masa da sujirasa gashi nan zuwa. Babu jimawa kuwa yazo tare da Amaturrahman data rikice da murnar ganin Bilkisu. Basu wani ja zanceba ya basu Bilkisun batare da yace mata uffanba akan hakan, saida ya juya zai shiga motarne ya dubeta sau ɗaya ya ɗauke kansa da faɗin, “Ki shirya gobe zaki koma aiki, zan biyo na ɗaukeki” daga haka yay tafiyarsa. binsa tai da kallo har saida ya tada motar yabar wajen itama suka shiga motar dasu Amaturrahman suka fito da ita.
__
Asibiti Jawaad yay niyar komawa dan yayma Qaseem dogon gargaɗi, sai dai tunanin barinsa ya samesa har gida ya sakashi sharewa, juya kan motar yay zuwa station zuciyarsa fal tunane-tunane, ga aiki jibge a gabansa da baisan iyakaba, ga kuma matsaloli kala-kala da yarasa makamar dazai kama domin fara warwaresu. Saƙon ɗan fi'auna ne yazo masa arai, har ya shiga office ɗinsa yana juya zancen a ransa, ‘Mi ɗan fir'aunan ya sani a kansa da haryake iƙirarin ya basa har naira miliyan hamsin domin ya sanar masa? Shin waishi yaron nanma wanene shi? Kuma a ina su Momy suka samosa?’. Wannan tunanin da yazo masa a raine ya sakashi dakatawa daga ƙoƙarin kunna Computer gabansa da ya kai hannu zaiyi, komawa yay jikin kujera ya kwanta yana lumshe idanunsa.
A haka Aliyu ya shigo ya samesa, sai da yay masa sallama har biyu sannan ya farga da shi, ya buɗe idanunsa da tashi zaune sosai, tie ɗin wuyansa ya sassauto ƙasa yana kallon Aliyu daya zauna. “Boss lafiya dai?”. Aliyu ya faɗa idonsa akan Jawaad, sassanyan numfashi jay ya sauke da cewa, “Lafiya lau Aliy”. Badan Aliyu ya yardaba ya ƙyalesa, saima takardun hanunsa ya miƙa masa yana masa bayani. Jawaad ya amsa ya duba ya sake miƙama Aliyun, magana suka ɗanyi Aliyu ya tashi ya fita.
Koda Aliyu ya fita Jay kasa haƙuri yay ya ɗauka waya ya shiga neman ɗan-Fir'auna, tana gab da katsewa aka ɗaga, daga can wanda ya ɗaga ɗin ko sallama baiyiba balle batun gaisuwa yace, “Mai wayar yayi Accident yana asibiti”. “...Accident?” jay ya maimaita da maɗaukakin mamaki tare da sake kiran wayar dan har an katse.............✍
ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.
SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.
HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO
MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.
MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.
BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....
abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai buƙata zai
Billy Abdul, [12/15/20, 12:50 PM]
iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.
Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899
sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.
Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300
Sai kunzo😍😍😍😘.
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻
Bilyn Abdull 📚:
Page 29
...............Yanzunma dai saida taje gab da yankewar aka sake ɗagawa, sai dai yanzu ba'ace komaiba, cikin ɗan zafi-zafi Jay yace, “A wane asibiti ne?”. Ɗan jimm wancan yay, sai kuma cayay General”. Yanke wayar kawai Jay yayi batare da shima yace komaiba, maida akalar kiran yay ga Jabeer, bigu biyu ya ɗauka, bayan sun gaisa Jay yace ya fiyo zasu fita. Iyakar abinda yace kenan ya katse kiran ya miƙe, rigar suit ɗinsa daya cire tun shigowarsa yay hanging a bayan kujerar zamansa ya ɗauka, tare da ƙaramar bindiga ya tura a gefen ƙugunsa ya fice.
Tare suka fita shi da Hafiz da Jabeer, dan Aliyu akwai aikin da yakeyi. Koda suka isa General hospital emergency suka nufa kai tsaye, tunda ance Accident can tunaninsu ya fara basu su duba farko. Hafiz ne yay tambaya duk da basu da tabbas ɗin cikakken sunan ɗan-Fir'auna bayan Habib, sudai ma'aikatan asibitin dake Emergency ɗin basu ganeba, amma alamun da suka gani na cewar su hafiz jami'an tsarone yasa doctor zagayawa dasu kaf gadajen dake cikin Emergency room ɗin suna dubawa, babu ɗan-fir'auna anan ɗin. Doctor yace, “To akwai dai wani da aka kawo tunda safe yayi accident, mun bashi ɗaki awa ɗaya data wuce, al'amarinsa akwai ruɗarwa, daga baya ƴan uwansa sukazo suka ɗaukesa duk da yana cikin mawuyacin hali”. Jabeer ne yace, “Suka ɗaukesa kamar ya? Baiji ciwo bane?”. “Yaji ciwo sosai yallaɓai, dan ko farfaɗowa ma bai gamayiba mundai dubasa babu karaya sai raunika?”. Kafin Jabeer ya sake magana Jay dake gefe yana latsa waya tamkar ba saurarensu yakeba yace, “Miye sunansa?”. Yay maganarne ba tare da ya ɗagoba, dan yasan idan har Dr Tayyeb ya gansa tsorata zai yaƙi faɗar komai.
Dr Tayyeb dai yasha jinin jikinsa akan Jay, sai dai da yake bai ganin fuskarsa da ƙyau sai ya daure yace, “Kamar dai Habibu ƙaura suka bada a jikin katin”. Jay baice komaiba dan ya fahimci dai ɗan fir'auna ne, sai kawai ya nufi hanyar fita. Ganin haka yasa su Jabeer yima Doctor sallama suka biyoshi. Acikin mota suka iskoshi, sai da suka shiga suma Hafiz yace, “Boss yanzu a ina zamu ganosa kenan?”. Jawaad da har yanzu hankalinsa naga waya batare daya ɗagoba yace, “Anguwar kuke”. Tada motar Jabeer yay sukabar asibitin batare da sun sake cewa komaiba, dan sun lura akwai abinda yakeyi mai muhimmanci a wayar.
Sun shiga Anguwar Kuke, inda Jay ya sanar musu dai-dai inda zasu tsaya, a tare suka fita a motar, Jawaad yay gaba suka bisa a baya har zuwa jikin jan gate, gidan bawani gidane mai ƙyauba, dan irin ginin da ɗin nanne, sai dai a da ɗin maishi ya kasance mai arziƙi, a rufe ƙofar take, hakan yasa Hafiz ƙwanƙwasawa. Kusan mintina biyar suna tsaye kafin a buɗe a fusace, kodamar tambayarsu suwanene su? wanda ya buɗe ɗin baisamuba Jay ya turashi gefe ya shige su Jabeer na biye dashi. Duk tsagerancin tsagera idan yay gamo da wanda ya fisa tsageranci nutsuwa ya keyi, hakan yasa saurayin bai iya cewa komaiba ya maida ƙofar ya rufe shima yabi bayansu dan ya gane Jawaad.
Ɗunbin mamaki da al'ajab ne ya sakasu tsayawa cak a ƙofar falon, dan kuwa gungun samarine da adadainsu zai iya kaiwa goma tsai-tsaye da candles kunne a hannu sun zagaye katifar da Ɗan-Fir'auna ke kwance a tsakkiyar falon, dukansu idanunsu a rufe suke babu mai magana bare motsi. Jabeer da Hafiz ne kawai sukai magana tare da jan birki, Jawaad kam uffan baiceba sai kafawa matasan idanu da yay a ransa yana nazarinsu. Hannu yasa da ƙarfi ya bugi ƙofar falon, a take duk suka dawo hayyacinsu, suka juyo suduka suna kallonsa. Su Jabeer dai abin ya firgitasu, amma a mamakinsu sai sukaga Jawaad ya danna kai cikin falon kamar baiga abinda yake faruwaba. A baɗini shima kuma lamarin ya firgitashi, sai dai ya danne saboda shi mutumne mai kasadar tunkarar abu kai tsaye, ko aiki suka fita duk haɗarin waje baya shakkar shigewa gaba.
Cike da takun nutsuwa Jay ya ratsa ta tsakkiyarsu yana addu'a a ƙasan ransa har zuwa gaban katifar da ɗan-fir'auna ke kwance samɓal jikinsa duk raunika wasu ansa bandage, yay wani irin kukkumburewa a fuska saboda buguwar da yayi. Sai da yay masa kallon mintuna uku kafin ya ɗago ya kalli samarin da suma
suka kafeshi da kallo tamkar zasu cinyesa ɗanye. Yi yay tamkar bai fahimci kallon da suke masaba, cikin Kakkausan lafazi yace, “Dami yay Accident ɗin?”. Wanda yake gaba gab da katifar sosai ne ya fara hure candle ɗinsa, sannan ya juya ga sauran yay musu nuni dasu zauna. Babu musu duk suka zauna ƙasa suka tanƙwashe ƙafafunsu hannayensu riƙe da candles ɗinsu har yanzu kuma a kunne. Sake maida dubansa yay ga Jawaad yace, “Yakamata mu fara sanin baƙonmu ai”. Sake ɗaure fuska Jay yayi, kamar bazai tankaba sai kuma ya gyara tsaiwa da faɗin “Nine na kira waya ɗazun”. Karon farko saurayin da babu alamar mutunci tattare dashi yay murmushi da cema Jawaad, “Hutawarka lafiya babba, haɗari yay da mashin yau da asuba, sai dai abin ya haɗa da mabiya sahu”. Jawaad tsaf ya fahimci ma'anar kalamsa, amma sai yay kamar bai ganeba yace, “Amma miyasa kuka ɗakkosa daga asibiti? Suwaye ke bibiyar sawun nasa?”. Gayen yace, “Babba! wannan wasane tsakanin rindunar mafarauta guda biyu, suntaɓo inda za'a maida gayya da gayyane, dolene tsakaninmu a fidda wanene sarki wanene bawa, zasu biya diyyar jini da jini karka damu, koma gefe kawai kasha kallo dan muna respecting ɗinka Babba, aishi sheri ɗan aikene maishi yake komawa, balle idan ka haɗu da waɗanda suka fika iya sherin, zamu zuba dasu muga wazai kwashe, idan har sukaci nasara a kanmu na rantse da jinin babata saina yanke kaina da hannuna da takobin da aikinta kawai shine shan jini”. Kafin Jay ya ƙara magana Ɗan-fir'auna yay wata irin mimmiƙewa da saki razananniyar ƙara data firgita su Hafiz dake a farkon shihowa Falon basu ƙaraso ba, shi kansa Jawaad sai da ya toshe kunensa. Abin mamaki sukam abokan ɗan-fir'auna ko gezau, saima sake miƙewa da sukai da candles ɗinsu a hannu suka kuma zagayeshi.
Bayan wasu mintuna ɗan-Fir'auna yay shiru sai numfashi yake da sauri-sauri, kafin kuma a hankali ya nutsu waje guda numfashin na komawa normal. Sake komawa sauran sukai suka zauna, na ɗazun nan dai me ya sake magana, “Babba karka damufa, nasan akwai harƙalla tsakaninka dashi, zai miƙe nanda kwanaki kaɗan tunda gashi ya farfaɗo, alfarmar da muke nema gurinka kawai likitan dazai dinga zuwa gida kullum yana duba masa waɗanan raunikan”. Cikin haushi Hafiz yace, “Kai kushiga hankalinku, kufaɗa mana abinda ke faruwa?”. Kafin wancan yace wani abu Jay yay wani munafukin murmushi da yima Hafiz magana da ido ya ɗauke kansa tare da nufar hanyar fita. Hafiz ya sake kallon Ɗan-Fir'auna yana mai girgiza kansa, “Shikenan za'a kawo muku likita”. Shima yana gama faɗa yabi bayan Jay ransa a ɓace. Jabeer da baice komaiba sai nazarin kayan dake cikin falon shima yabi bayansu..
Kusan a tare suka fito, suna shiga mota Jabeer yace, “Boss miyasa za'a kawo musu likitan da suka buƙata? Bayan dukkan alamun mutanen banza ya bayyana a garesu”. Numfashi jawaad ya sauke a hankali yana kallonsu, “Wato Jabeer kowane aiki akwai salon da yake zuwa da shi, waɗannan yaran da kake ganinsu duk a tafin hannuna suke, dan duk wani binciken daya dace na kammala yinsa a kansu, mubisu a sannu domin samun abinda muke buƙata yanda ya kamata”. Kai duk suka jinjina masa cike da gamsuwa, dan sunsan bazai jefasu a hanyar da bazasu ɓille ba.
Sunbar anguwar Hafiz da Jabeer nata tattauna al'amarin, Jay kam dai yayi shiru, dan kuwa shi kaɗai yasan mi yake tattaunawa da zuciyarsa. Jabeer yace, “Wannan duniya nada abin mamaki da al'ajabi da bantsoro, rayuwar waɗannan mutane ta ƙanƙanin lokaci kawai ka gani ta isa saka zuciyarka tsorata da sake tsarkake girman ALLAH”. Cike da damuwa Hafiz yace, “Yaran nanfa kamar ba ainahin musulmai baneba ma, sannan dagani kaga ƴan Cultism”. Jay dai duk dai yana saurarensu, har suka iso station, office ya wuce ya cigaba da aiki biyu, na office dana zuciyarsa. Kalaman abokin ɗan fir'auna yaketa harhaɗawa waje guda da nazarinsu.
Misalin biyar da wasu mintuna na yamma yaɗan fita wani waje, yanason zuwa ainahin inda suka taɓa haɗuwa da ɗan-fir'auna a ranada Gimba ya kawo masa zancen abinda ya gani. sai dai kuma hakan bata samuba saboda yana hanya kira ya shigo wayarsa daga balarabe, a amsa kuwwa ya saka
wayar ya amsa masa sallama da gaisuwar da yake masa. “Ka isa garin nasu ne?” yay tambayar wa balarabe. Daga can muryar balarabe cike da damuwa yace, “Ganima harna dawo Alhaji, tun inacan naketa kiranka baka ɗagaba. sai dai baizo gidanba ma ashe, kuma mamansa tace har waya sunyi lokacin dazai taso”. Babu shiri Jawaad ya taka burki, yace, “Kana nufin canba gidaba tun ran juma'ar?”. “Eh wlhy Alhaji hakane”. Mutuwar zaune Jawaad yay a cikin motar, gabansa sai wata irin mahaukacin faɗuwa yake, cikin rawar jiki ya ɗauka wayar ya katse kiran balarabe ya fara laluben Jabeer. Yana ɗagawa ko sallama bai masaba yace, “Jabeer maza dubamin daga ina Gimba yake a halin yanzun?”. Daga can Jabeer yace, “Ƙila matarsa ta riƙesa bata gaji da ganin kayantaba”. A tsawace Jawaad yace, “Jabeer kabar wasa mana!!, ka nemomin yaron mutane Jabeer Please”. Ya ƙare maganar a hankali tamakar zai fashe da kuka. Hankalin Jabeer ne yay matuƙar tashi, baƙaramin girgiza zuciyarsa tayiba da jin yanda Jawaad yay magana da tsawa da sanyin murya kuma a ƙarshe. Jabeer yace “Yi haƙuri, yanzu kana Office ne?”. “Gani nan zuwa” kawai ya iya cemasa ya yanke wayar. Reverse yay tare ya figi motar da shegen gudu ya koma station.
A office ɗinsa ya iske Jabeer na jiransa, har wani jiri-jiri yakeji saboda tashin hankali, sai da ya zauna sannan Jabeer yace, “Mike faruwa da gimban?”.
“Jabeer nima ban saniba, ranar juma'a ya tafi weekend amma bai dawoba, shinefa nasa a bisa aga ko yana lafiya, amma sai aka tararma baijeba”.
Cikin ɗaurewar kai Jabeer yace, “Ya salam to ina yaje shiko? Yanzu abinda zamuyi bara mu bibiyi layin sa, ina fata kunyi waya dashi bayan tafiyar tasa?”. Kai kawai Jawaad ya girgizama Jabeer, yana faɗin, “Na kirashi jiya amma bai ɗagaba”. Jabeer yace, “Tunda dai kiran ya shiga zai taimaka mana”. Wayar kawai Jay ya miƙama Jabeer baice komaiba. Gaba ɗaya Jay ya kasa zaune ya kasa tsaye, sai faman zagaye office ɗin yakeyi, Jabeer kuma nata ƙoƙarin ganin ya samo inda gimban yake, a haka Aliyu da Hafiz suka shigo suka samesa harma da Rose da dawowarta kenan daga tafiya. Haka suka duƙufa su huɗu suna taimakawa Jabeer. Inda alama ke nuna musu wayar gimba na nan ɗinne ya tada musu hankali har suka kasa aminta suketa sake ninƙayar bincike. Cikin girgiza kai Jabeer yace, “Kai abinnan akwai rikitarwa, mizai kaisa wannan dajin mai haɗari? Inaga bara nai magana da kamfanin layinan dan muna buƙatar bayanan da yafi haka”. Hafiz yace, “Hakan shine zai taimaka mana Jabeer, danni kainama ya kulle gaba ɗaya”.
Jawaad dai yama kasa cewa komai, zaune yake kawai tamkar butunbutumi. Aliyu ne yay kiran wanda yake musu aiki a kamfanin layin da gimba ke aiki dashi, bayan sunyi magana ya ajiye wayar Jabeer ya tura musu Number gimba.
Ganin magriba tayi Aliyu yace, “;
Boss ka kwantar da hankalinka, ni ina ganin ko wasune suka Kidnapping ɗinsa bazasu kaisa wannan jajejinba, kawai sunyi hakane domin rikita mana tunani, idan muka kwantar da hankalinmu zamu fahimci komai cikin sauƙi, yanzu dai Ma'aruff ɗin yace daganan zuwa safiya zai turo mana komai, inaga muje muyi salla da addu'ar ALLAH ya kuɓutar dashi a duk inda yake, a kuma hannun duk wanda yake”.
A tare suka amsa da amin har Jawaad.
Koda suka fito daga salla Jawaad ya tafi gidane kawai cike da matsananciyar damuwa, bai shiga gidaba sai da yay sallar isha'i.
A wannan dare idan har akace Jawaad yay barci to ɓarawone, kwana yay miƙama UBANGIJI kukansa akan gimba da murɗaɗɗun al'amuran dake faruwa a tsakaninan, roƙon ALLAH yake ya bashi ƙarfin zuciya dana jajircewa, ya kuma haskaka masa abinda yake a duhu daya gaza fahimta. Mutuwar ɗan-fir'auna, ɓatan gimba, mafarkinsa, dalilin aure da akaso yi tsakanin bilkisu da wanda ba mutumin kirkiba, damuwar da yaga Alhaji babba jiya a ciki. Duk wanda ya roƙa UBANGIJI yana mai ƙasƙantar da kai da fatan samu bai yanke ƙauna daga rahamarsaba ALLAH sai ya amince masa, ya kuma dafama al'amarinsa ta inda bai zato ko tsammani ba.
Jawaad ya tashine da wata irin dakiyar zuciya, duk wani ɗigon tsoro da fargaba daya haifarmasa da ruɗa
ni da kasala a daren jiya sai yaji sun gudu, ya tashi cike da yaƙinin son tunkarar abinda ke tunkarosa. Dolene koda zai halaka da izinin ALLAH sai ya gano suwaye suka kashe ɗan fir'auna, miyasa suka kasheshi?, minene a binne da rayuwarsa da ɗan-fir'auna yaso sanar masa, yanaji a jikinsa kisan ɗan fir'auna nada nasaba da abinda ya shafesa, minene shi? Wannan ne bai saniba.
Ƙarfe bakwai na safe ya gama shirinsa yabar gidan, yau ko gadonsa bai gyaraba, saƙo ya gani daga gimbiya Munaya akan zatasa akai Bilkisu wajen aiki basaima ya wahal da kansaba, idan sun tashi sai ya dinga maidota da kansa.
Yaji daɗin hakan, dan dama yanata juya yanda zai dinga yawonan batare da wataran yay lattiba shiɗinan gwani ayyuka da yawa. Station ya nufa cike da zumuɗin son zuwa yaji ya ake ciki akan gimba.
________________________________
Tunda muka shiga cikin masarauta notin kaina ya nema kwancewa, karon farko a tarihim rayuwata dana fara shigarta, ƴan uwa bansan yanda zan musalta muku abinda na ganiba, abinda kawai zan iya ce muku masarautar gagara badau wani katafaren garine kawai mai zaman kansa dake ɗauke da ɗumbin al'umma kala-kala masu abubuwan kallo. Kaina bai sake kuncewa ba sai da muka shiga sashen da naji ance na sarauniyane mahaifiyar su Amaturrahman, wato garin daɗi na nesa, angulu data leƙa masai. Nidai bana cewa uffan, binsu kawai nake tamkar raƙumi da akala. Mun yada zango a katafaren ɗakin Amaturrahman da Meenal sai Amatullah idan tazo daga Niger. Amaturrahman ce ta tsaya kaina da hidima har saida nai wanka na canja kaya aka kawo abinci ta takurani naci sannan ta barni na huta, muna zaune tana ɗan jana da hira saƙon gimbiya ya iso garemu daga amintacciyar baiwarta akan tace na kwanta na huta, kuma a bani dukkan kulawar data dace.
To lallai naga hidima mai ban mamaki da al'ajabi wadda har kuka sai da nayi, ashe nima mutumce mai daraja irin haka? Ɗawainiyar da akeyi dani ta zabtare kaso mafi yawa na damuwar da nake ciki akan abubuwa kashi-kashi da basu ƙirguwa, tunda Safah kuma taji labarin nazo tadawo ɗakin su Amaturrahman ta tare tanata min hira. Banga gimbiya ba har dare yay muka kwanta, da safe kuma na tashi da shirin fita aiki kamar yanda boss ya tabbatarmin zasu zo ɗaukata, sunata barcinsu nai shirina tsaf, na cika wayata da caji dan haka nai tunin tanan zai kirani, sai dai kusan 7: 00am saiga ɗaya daga cikin bayin gidan tazo isarmin saƙon kira, bin bayanta nai muka fita, mun isa wajen Amintacciyar baiwar gambiya dake falon farko tana jiranmu, na gaisheta da girmamawa saboda babbar mace ce, itama cike da fara'a ta amsa min tana faɗin, “Sarauniyar gagara badau na gaisheki baƙuwar alkairi, baki samu ganinta bane tunda kika iso saboda takawa yana mura, tana sashenshi tun jiya tana bashi kulawa, akwai driver dake tsumayenki a waje ta bada umarnin a kaiki garesa”. Fuskata ɗauke daɗan murmushi nace, “Nagode mama, ALLAH ya bama maimartaba lafiya mai amfani da nisan kwana”. “Amin ya rabbi” ta amsamin damin nuni Abinci da aka ɗora akan babban yire wai na breakfast ɗina, badan nasoba ta tsareni naci sannan tayomin rakkiya waje.
Duk azatona gimba zan tarar, sai dai na iske saɓaninsa, da alama madai wannan acikin masarautar yake shima, dalleliyar mota baƙa wulik yaymin nuni dana shiga bayan mun gaisa, tamkar kazar da ƙwai ya fashema a ciki haka na shiga zuciyata najin tarin ƙaunar waɗanan adalan mutane, ada nazata idan na rasa mafakar gidan Dad bazan sake samun watantaba, sai gashi alkairai nata niye da rayuwata. Tafiya muke ina tunani kala-kala a cikin raina ciki harda fargabar haɗuwata da mutum biyu, wato Boss da Yah Qaseem, tayaya zanyi aiki cikin nutsuwa a tsakkiyar waɗanan zakunan?.
★★★★★
Jay da isowarsa kenan babu daɗewa yana zaune a kujerarsa ta office yana ɗan taɓa aiki da tsumayen su Jabeer, baifi mintuna gomaba suka shigo a jere su huɗu har Rose data dawo jiya, gaisuwa sukai cikin musabaha Rose kuma ta gaishesa kafin duk su zauna, binsu kawai da kallo Jawaad yake. Jabeer ya nuna masa takardar dake hanunsa yana faɗin, “Wannan sune bayanan da Ma'aruff ya kawo yanzun nan”. Jay
ya ɗago idonsa daga rubutun da yake yayma Jabeer kallo ɗaya ya ɗauke, “Ka buɗe mugani” ya faɗa hankalinsa akan Computer ɗin gabansa, sai dai sam bama ya fahimtar aikin da yakeyi ɗin.
Buɗe takardar Jabeer yayi, cikin nutsuwa yake bin komai da kallo daki-daki, a firgice ya kalli Jay cikin rawar harshe yace, “Ka duba wayarka, alama ta nuna kaine wanda ya turama saƙo na ƙarshe ta manhajar WhatsApp a ranar asabar da ƙarfe shida da mintuna talatin da huɗu (6:34pm), sai kiran wayoyi barkatai da akai masa amma babu wanda ya ɗaga a ciki, kuma wayardai tana a cikin jejin nan da muka gani jiya, abin farin cikin kuma har yanzu layin yana kan waya yana aiki alamar wayar tana a kunne”. Duk saurarensa suke, yayinda Jay keta ƙoƙarin duba saƙon Gimba, tabbas kuwa ya tura masan, amma sam hankalinsa bai kaiba saboda hidimarsa bata barima ya leƙa wata kafar yanar gizo ba a gaba ɗaya satinnan daya gabata. Babu wanda hankalinsa bai tashiba a cikinsu da wannan voice note na gimba, tuni jijiyoyin kan Jawaad duk sun miƙe ruɗu-ruɗu, muryarsa cike da damuwa yace, “Hafiz kaima Sir Ahmad magana ina buƙatar helicopter”. Cikin matsanancin tsoro suke kallonsa su duka, Aliyu yace, “Boss wannanfa dajine mai haɗarin gaske da ko soji suna masa shiri na musamman kafin su shigesa, idanma sun shigan ƙalilanne a cikinsu ke dawowa da ransu, baka tunanin ma wayar aka kai can dan a kauda mana hankali”. Cikin rufewar ido Jawaad ya bugi tebir ɗin gabansa, “Aliy!! ya kakeso nayi ne shin? Nabar yaron mutane mai mata da ƴaƴa har uku da uwa da ƙannen da suka dogara dashi a hannun waɗanda suke azzalumai?. Aliy ta dalilinafa suka kamashi, wlhy kaji na rantse maka sai ƙafata ta taka wannan jejin koda kuwa Gimba bayacan kokuwa nima ajalina nacan!”.
Babu wanda bai firgita da alwashinsaba a cikinsu, sunaji suna gani ya fice daga office ɗin, basu da zaɓin daya wuce goya masa baya dan wannan shine alƙawarin da suka ɗaukama kawunansu duk rintsin da ɗayansu zai shiga suna tare dashi ɗari bisa ɗari. Cikin mintuna ashirin suka samu amsar helicopter daga hukumar sojoji tare da soji biyu da zasuyi musu rakkiya bisa tsayawar Sir Ahmad.
Office ɗin Jay ɗin dai suka koma suna tsare-tsaren yanda zasu tunkari Jejin.
A dai-dai wannan lokacin motar masarauta ta kawo bilkisu, godiya naima drivern da ko sunansa ban saniba na fice, shi kuma ya juya inda ya fito.
Kaina tsaye office ɗinmu na nufa, a raina sai jina nake wani iri idan na tuna waifa akwai aure a kaina yanzun, aurenma na Boss. kowa yazo sunata aiki, shigowata yasa sukaimin caa da ido har gabana na faɗuwa da tunanin shikenan na mutu kowa yasan komai. Ummie ta taso da gudu ta ɗaleni tana murna, “Babie ALLAH banyi zaton ganinki ba yau a office”. Murmushi nai mata ina amsa gaisuwar sauran daketa min yaya jiki, sai naji daɗi da Ummie bata sanar dasu komaiba sai rashin lafiya.
Na zauna a mazaunina idona akan Ummie da itama ta jawo kujerarta jikin table ɗina ta zauna. “Yanzu angonki yazo ya gama haukatamu da masifa anan”. Ta ƙare maganar da dariya. ɗan hararta nai na ɗauke kai bance komaiba, danni kam dama ta ambatosa jinai gabana ya faɗi. na shiga duba aikin dana bari, Ummie kuwa na cigaba da tsokanata dan na tanka amma na shareta kamar banajinta.
Dawood daya shigo yanzun ya ƙaraso gabana yana faɗin, “Bily Boss na kira”. Babu shiri na ɗago ina kallonsa, shiko yay ƴar dariya yana zama a kujerarsa dake kusa da tawa, “Kitafi da addu'a a baki dan wlhy yau a sama yake, yanzu naje office ɗinsa jinai kamar nai fitsari a tsaye da yanda yaketa masifa”. Ban iya cewa komaiba, Banida ikon kuma cewa bazanjeba, dan haka na miƙe cike da haushi na fita har Ummie namin dariyar ALLAH yasa aiki za'a bani dan taga kwana biyunnan hutawa kawai nake tunda bana zuwa office, ban kulataba na fice abina.
Ina fitowa na hangesu sun fito tamkar zakuna, kowa fuskarsa a ɗaure musamman ma boss, gabana ya faɗi, a fili nace, ‘Ni balki ina kuma zamuje haka?’ bani da mai bani amsa na isa inda suke, babu wanda ya saurari gaisuwata ma a cikinsu, Jabeer ya nunamin na shiga mota da boss yake, gaba na buɗe na shiga
, dai-dai da isowar Rose wajen, hararata tayi tana jan tsaki, ta buɗe indasu Aliyu suke ta shiga, Hafiz kuma ya shiga kusa da Boss.
Mun fara tafiya Hafiz ya miƙomin bindiga, juyowa nayi zan amsa na samu damar satar kallon boss, kansa a duƙe yake yana sakama bindiga alburusai, amsa nayi na juya zamana nidai a raina ina addu'ar ALLAH ya maidomu lafiya...............✍
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
Billyn Abdul:
Page 30
................Daga station Barrack muka nufa, acan muka iske jirgi mai saukar ungulu dake jiranmu.
Motar na tsayawa Jawaad da Hafiz suka fita, kafin bily tai yunƙurin fitowa Hafiz dake kallon Jay yace, “Boss amma Mami jiya ta fito asibiti miyasa baza ai mata afuwa da tafiyarnan ba?” Jay dake daƙilar waya ya ɗago yana kallon Hafiz, sai kuma ya dafa kafaɗarsa da hannunsa da ya ciro aljihu, “Nasan tana buƙatar hutu Hafiz, sai dai nima bansan miyasa nakejin kamar tafiya tare da ita yanada nasaba da nasararmuba”. Hafiz ya jinjina kansa yana murmushi, shima Jay ɗin murmushi yayi ya ɗauke kansa.
Ganin sun fita nima na fito, ido muka haɗa da boss dake ƙoƙarin saka waya a kunne da alama kira yayi, duk yanda naso janye nawa na gaza, dan tamkar ya ƙulleni ne da idanun nasa yayi. Murya ƙasa-ƙasa tamkar mai gudin wani ya jisa yace, “Koma ciki ki jira”. Ƙasa nai da idona ina sauke ajiyar zuciya, na buɗe motar na koma ciki ina kallonsu. Sojoji uku ne suka ƙaraso wajen, daga inda nake banajin mi suke faɗa su da su Oga Jabeer, boss dai na gefe yana waya har yanzun.
Bayan Jawaad ya kammala waya da Alhaji babba akan a tayasu da addu'a shima nufar inda su Aliyu suke tsaye tare da sojoji ukun nan yayi, cikin mutunta juna suka gaisa, wanda ya kasance babba a cikinsu mai yawan shekaru kuma ya kalli Jay yana faɗin, “Jejin nan jejine mai haɗari, Sojinmu sunsha wahala sosai a cikinsa kafin ALLAH ya kawo mana ɗauki ya haɗamu da Ƙaura na bakin kadarko, a bakin jajenin yake rayuwa shida iyalansa, sannan a cikin jajen yake farauta, sai dai wani babban al'amari ya faru a shekaru biyu da suka wuce wasu azzalumai suka tashi gidansa dukkan iyalansa babu wanda ya tsira sai shi, shima dai ya rasa hannunsa guda, daga nan ne muka ɗakkosa mukazo dashi nan yay jiyya har ALLAH yasa ya warke, yaso komawa jajenin saboda ya saba sosai dacan, yakan faɗa mana zama a cikin gari shi baya masa daɗi, to adai taƙaice har zuwa yanzu da nake muku magana bamu barsa ya komaba, dan yama tsufa kawai jarumtace irin ta mutan da da ALLAH ya azurta da sani.........” isowar ƙaura da wani soji wajen ya saka Lieutenant General Mubarak Kambawa yin shiru, ya zubama waje ɗaya ido. Duk juyawa su Jay sukai suma suna kallon inda yake kallo, tsohone mai shekaru da yawa wanda basusan adadiba, babu wani gashi a jikinsa da zaka iya gani baƙi sai wanda UBANGIJI ya ɓoye. Yana sanye cikin kayan fatu, ya ɗaura fatar zaki a ƙasa yay riga data damisa wadda take tamkar ƴar shara, dan kai kawai aka fitar sai gefe da gefe akai mata maɗauri, yana rataye da jikkar fatar kura a wuyansa, sai dai bashi da hannu guda. Daka gansa kaga ƙauran kuwa. Yanda sukaga lieut.. General na gaidashi cikin girmamawa yasa suma suka gaidashi da girmamawa, dan koba komai ya wuce uba sai dai kaka. Dattijo ƙaura dake amsa musu idanunsa kafe akan Jawaad ko ƙyaftawa bayayi, ya saki murmushi yana kauda idonsa daga kallon Jay ɗin. babu wanda kallon bai bama mamakiba hatta lieut.. General, dan haka yaja Ƙaura gefe guda.
“Baba nasan baƙwa kallon banza, akwai matsalane? Dan na lura ka kafe yaron can da kallo har murmushin ka ya kasa ɓoyuwa” murmushin yanzuma Ƙaura ya sakeyi tare da juyawa ya kalli Jay da Jabeer ke taimakawa yana saka bullet proof jacket a jikinsa kafin ya sake maidowa ga lieut.. General yace, “Shima sojan kune yallaɓai?”. Lieut... General yace, “A'a baba, sune nai maka bayani ai zakuyi tafiyar”. “Oh na shafa'ane wlhy, kasan ƙwaƙwalwar yanzu sai a hankali takan manta wasu abubuwan”. L. General dai murmushi yayi kawai, dan yasan wanene baba ƙaura, yakuma tabbata akwai abinda ya gani tattare da Jawaad, amma tunda yake wani kakkaucewa bayason ya sanine, dan haka ya ture maganar Jawaad gefe ya shiga masa bayani akan taimakon da sukeso yayma su Jay saboda sanin sirrin jajen da yayi. Sunɗan tattauna sannan suka dawo inda su Jay da suka gama shiryawa tsaf suke harda Bilkisu data fito bisa umarnin Jawaad bayan yaje da kansa har cikin mota ya taimaka mata ta saka bullet proof jacket ɗin itama suka dawo wajen tanata sinne kai saboda kunya, yayinda Rose ta shaƙa tai fam da haushi tamkar zata f
ashe.
A bazata sukaji Ƙaura yace, “Yarinya yaya sunanki?”. Duk juyowa sukai su duka suna kallonsa dason ganin dawa yake tsakanin bily da Rose?. Sai sukaga da Bilkisu yake dan itace gab dashi kuma itace ta gaidashi tunda sai yanzu ta ganshi, gashi ta kafeshi da idanu tamkar maison tuna inda ta sanshi. Tambayar da yaymatane yasata dawowa hayyacinta, tace, “Bilkisu”. “Balqeesa! mai gadon zinari kenan” baba ƙaura ya faɗa yana wani murmushi tamkar yanda yay ɗazun akan Jay. Jawaad zaiyi magana L. General ya riƙe masa hannu yana girgiza kai alamar kar yace komai. Komawa yay ya tsaya badan yasoba danshi al'amarin tsohon ya fara bashi haushi. Sarai ƙaura yaga abinda Jawaad yayi, danta wutsiyar ido yake kallon duk miotsinsa, amma sai yay kamar hankalinsa akan Bilkisun kawai yake. Har Lieut.. General ya basu Umarnin shiga Jirgin Ƙaura ya sake jefama Bily tambaya. “Balqeesa! yaya sunan mahaifinki?”. Yanzunkam ba Jawaad kaɗaiba kowama abin yazo masa wuya banda Rose, ahaka zasuyi tafiyar da wannan mutumin mai shegen tambaya da bin ƙwaƙwƙwafin mutum?. A miskile Bilkisu ta amsa masa da “Adam makaho”. Duk ido suka zubama Ƙaura suji mizaice, amma sai ya ɗauke kansama gaba ɗaya kamar bashi yay tambayar aka bama amsa ba.
Ganin yanda yay ɗin yasa L.. General cemusu su shiga. Haka duk suka fara shiga suna ƙunƙuni da hararar baba ƙaura daketa murmushin da basusan inda ya dosaba. Jay ya matsa ya kama hannun Bily dake tsaye tamkar wadda aka tsayar, ajiyar zuciya ta sauke dan tayi nisane a tuno mafarkinta na daren jiya wanda ayanzu ta tuna acan taga fuska wannan tsohon. Baba Ƙaura dake biye da bayansu ya ƙure hanunsu dake cikin na juna da ido yana murmushinsa har yanzu, sai da suka taka ƙafarsu zasu hau jirgin yace, “Sara da sassaƙa baya hana gamji tohowa”. Daga Jawaad har Bilkisu sunji furucin baba ƙaura sarai, harma Jay ya juyo zaiyi magana sai kuma ya fasa.
“Karka damu yaro faɗi duk abinda ke ranka, nima nawa nake faɗa dan bana bari a ciki ta kasheni. Ƙwai cikin ƙaya na gani ajiyar ALLAH”. Karan farko da kalaman tsohon suka saka gaban Jawaad faɗuwa, kalmar Ƙwai cikin ƙaya idan bai mantaba ya taɓa jinta a cikin mafarkinsa mai Sarauniyar da har yau basan inda ya dosaba. Har suka zauna idonsa bai daina kallon baba ƙaura ba da yay biris da kowa tamkar bashi ya gama takale-takalen maganaba yanzun.
Gaba ɗayansu duk da addu'a a bakinsu har jirgin ya ɗaga sararin subahana.
Duk da wannan shine karona na farko a hawa jirgi abin mamaki babu wani tsoro ko ƙauyanci tattare dani, kodan helicopter ne oho, nasan dai lokacin da zamuyi sama na riƙo hanun wanda bansan wanene ba sai da muka dai-daita na fahimci Rose ce, aiko tacika tayi fam da haushi, har nai mamaki da bata turo hannunaba, sai daga baya na fahimci Boss dake facing ɗinmu ne yaymata shamaki da hakan dan duk abinda zamuyi zai iya gani.
Haka mukai ninƙaya a tafiya idanuna sun gaza daina kallon tsoho mai kayan fatu, har jirginmu ya samu sauka. Jejine maiban mamaki da al'ajabi, bakajin komai sai kukan tsuntsaye da mabanbanta sauti da zuciya bazata iya hasaso minene ba. Kowa kagani hankalinsa a tashe yake da wannan jeji amma banda tsohon nan. Haka muka firfito kowa na karanta addu'ar da tazo masa a baki, wani irin makeken ruwane kwance ƙar-ƙar har haskensa na ɗaukar idanu a gabanmu, Oga Aliyu yace, “Ikon ALLAH, amma a taswurar jejin nan bamuga wannan ruwanba sam, ko masu zanen taswirar basu san da shi bane?”. “Wlhy Aliyu wannan shine abinda nake ayyanawa a raina yanzun” Jabeer ya faɗa murya a harɗe.
Tsohon nan ya bimu da kallo ɗaya bayan ɗaya sai kuma ya girgiza kansa da faɗin, “Wannan ruwa zuwayyene ba zaunanne ba”. “Kamar ya?”. Suka kusan haɗa baki wajen tambaya.
Ƙin basu amsa yay, saima kallonsa daya maido gareni, “Ɗiyata Balqeesa bismillah saka ƙafarki a ruwannan” sosai naji gabana ya faɗi, idanuna suka cika da ƙwalla, ganin babu wanda yay magana a cikinsu yasa na ɗaga ƙafa zan nufi ruwan. Caraf aka riƙomin hannu, basai na juyaba ƙamshinsa kawai ya bani amsar shine, murya a kausashe yace, “Baba ya zaka turata shiga wannan ruwan maikama
da ruwan tsafi?”. Mu duka kallonsa mukai, Jawaad da shima maganar ta suɓuce masane kawai babu shiri yay saurin dafe kai da faɗin, “Sorry, ina nufin ruwan daga gani yanada ban al'ajab, tunda nake ban taɓa ganin ruwa mai ƙyawunsa ba da ɗaukar ido irin haka”. Murmushi mai sauti mukaga Baba ƙaura yayi, cikin ɗauke kai daga garemu yace, “Dole saimun ƙetarashi zamu kai inda muke hari, anmana katanga da shine domin mu juya, kuma wlhy kunji na rantse wannan yarinyar kaɗaice zata ƙetarashi kafin mu sami hanya, dan tanada taurari masu ƙarfin gaske”. A take duk suka zubamin ido, ni kaina wata irin jarumta nakeji da dakiyar zuciya da bansan yaushe na sameta ba. Hafiz yace, “Kana nufin har kai da akai iƙirarin kasan ciki da bai ɗin jejin?”. “Yaro, baiwa kowa da irin tasa, wani har yabar duniya babu mai fahimtar tasa, wani ko harmutsin duniya ke bayyana tasa, waniko nasarorinsane, wani ko hatsabibancinsa ne, wannan idanun da kake gani ALLAH kaɗai yasan ajiyar da yay a cikinsu”.
Kai kawai duk muka shiga jinjina masa, boss yace, “Inhar zata ƙetara ruwannan sai dai tare dani”. Murmushi baba ƙaura yay kawai ya nuna mana hanya.
Sai da mukaje gab da ruwan yace, “ku tabbatar a tare ƙafafunku suka sauka, kuma da bismillah”. Umarninsa mukabi mukai yanda yace, ni dai harda ƙarama wata addu'ar nayi, wani irin azabar sanyi ne mai keta fata da tsoka ya shiga cikin jijiyoyi ya gauraye da jini ne ya riskemu lokacin da ƙafafunmu dake cikin takalma suka sauka cikin ruwan, atake muka fara rawar ɗari dagani har boss, maimakon muyi ƙoƙarin komawa baya sai naji ya fisgi hannuna mun sake saka ƙafafunmu na haggu suma, abin mamaki sai gamu mun jiƙe da zufa sharkaf dalilin zafin daya riskemu kuma a yanzu tamkar ana tafasamu a garwashi, zafin bashida maraba da wani zafi dana taɓaji kwanakin baya da bazan tuna dalilin jinsa ba. Sake fusgata Boss yay muka cigaba da tafiya dukda azabar dake ratsa jikkunanmu. Wani irin mahaukacin ihu ne mai ƙarfin gaske ta karaɗe jejin, gaba ɗaya ruwan da muke tsakkiya ya koma jini, da farko na tsorata, amma addu'ar da naji Boss ya kamo yanayi tuni nima na karɓa masa ina mamuƙeshi. Ɗaf ruwan ya ɗauke lokaci ɗaya tare da kukan, sai ƙarar iskar guguwa mai ƙarfin gaske da mukeji tana tinkaromu, a take muka daina ganin komai saboda guguwar tai mana ruf. Wata muguwar shaƙa naji anmin a wuya, nai ƙoƙarin fincike hannuna cikin na boss danna ƙwaci kaina amma hakan ya gagara, ashe shima shaƙesan akai, da hannuna na haggu na shiga laluben abinda ya shaƙenin, dan idona a rufe yake saboda guguwar data lulluɓemu. Ɗumbin mamaki ya kamani jin jikin mutumne da gaske, jikin da ya taɓa riskata a cikin wasu darare da sam na mantasu a cikin ƙwaƙwalwata, cikin amincin UBANGIJI Hannuna ya sauka a nasa wuyan shima, na damƙi sarƙar dake wuyan na fincika da masifar ƙarfin dana san daga UBANGIJINA ne kawai. A take jejin yay wata irin girgiza tare da wasu irin gigitattun ƙararraki ta mabanbanta muryoyi. Daga haka ban sake sanin mike faruwa ba.
Yanda aka shaƙe bilkisu haka shima Jawaad aka shaƙesa, sai dai shi saɓanin itane, maimakon ya samu nasarar fisgar sarƙar wuya sai yasamu nasarar ciran wani abu dake hanun wanda ya shaƙesan, danshi hanunsa yay ƙoƙarin cirewa daga wuyansa da aka shaƙe.
Da sauri yay azamar taro Bilkisu jikinsa ya rungumeta da ƙyau yana cigaba da karanto addu'a, isakar data lulluɓesu ta fara washewa a hankali har suka bayyana filin subahana, babu wancan ruwan da suka riska a farko, hasalima wajen tsaunine.
Su Hafiz da suka samu kariyar UBANGIJI daga wannan guguwa da basusan daga ina ta ɓulloba duk suka miƙe daga rumfar da Baba ƙaura yay musu da jikinsa. Dan ranƙwafe yake kansu ya baza hannayensa tamkar maison tattaro wani abu.
Gaba ɗayansu kansu Jay dake durƙushe a ƙasa kan Bily bisa cinyarsa yana girgizata sukai, baba ƙaura yay murmushi yana mai ɗaga hannayensa sama da zuba kirari wa UBANGIJIN AL'ARSHI, idanunsa na zubda hawaye, sai yanzune ya fahimci ƙaddarar zamansa cikin gari na tsahon shekara biyu bayan halaka masa iyalinsa da akai, UBANGIJI mai hikima, UBANGIJI mai rahama, sarkin da baya
zalinci ya kuma haramtashi a tsakaninmu, sai da ya kammala miƙa godiyarsa ga ALLAH kafin ya nufi su Jay da duk suke kan Bilkisu kowa na ƙoƙarin faɗama Jawaad taimakon da zai bata kozata farfaɗo, masu cewa ya murza hannu nayi, masu cewa ya murza ƙafa nayi, masu jajen ina za'a samu ruwa a zuba mata nayi. Shikuma sai faman girgizata yake yana faɗin ainahin sunanta na yanka wato BILKEESU!!.
Murmushi baba ƙaura yayi tare da katsesu baki ɗaya, “Bazata taɓa farfaɗowa a hakaba ko zaku kwana kanta”. Gaba ɗayansu shi suka juyo suna kallo, sai dai babu wanda ya iya cewa wani abu a cikinsu. Shima bai sake faɗar komanba, sai nuna musu su koma gefe da yay da hannunsa, babu musu sukabi umarninsa aka barshi daga shi sai su Jawaad ɗin. durƙusawa yay kusa da Jawaad murya ƙasa-ƙasa yace, “Iskar numfashinka ce kawai zai taimaki nata dawowa gangar jikinta ɗan saurayi, ka ɗaura bakinka kan nata ka zuƙo insha ALLAHU zata farfaɗo”.
A hankali Jawaad ya lumshe idanunsa tare da ranƙwafawa bisa fiskar Bilkisu ya aza bakinsa saman tattausan lips ɗinta, numfashin dake fita ta hancinsa yana sauka akan fuskarta, ya tura harshensa cikin bakinta dake ɗan buɗe kaɗan ya shiga hura mata iska tare da shanye yawun bakinta babu ko ƙyankyami, wani irin numfashi mai ƙarfi ta kawo tare da ƙanƙame hanunsa dake cikin nata ta damƙe laɓɓansa itama. Da sauri Baba Ƙaura yace ta farfaɗo?”. Yay maganar da bubbuga bayan Jawaad ƙaɗan.
Jay ya janye bakinsa dake cikin na Bilkisu da ƙyar yana sauke numfargashi da sauri-sauri, wani irin tsitstsinkewa jinin jikinsa keyi, baba ƙaura yay murmushi tare da ɗora hanunsa akan na Jawaad da ƙofofin gashi duk suka buɗe. A hankali Jay ya buɗe lumsassun idanunsa yana kallon Baba ƙaura kamar yanda itama Bilkisu ta buɗe nata a hankali akan fuskar Jawaad. “Da bakajin sha'awarta a matsayin mata ko?”. Gaban Jawaad ya faɗi yana mai al'ajabin ya akai tsohon ya sani?. Murmushi baba ƙaura yay yana ɗauke kansa ya maida ga bilkisu, “Yanda bakajin sha'awarta itama haka batajin komai game dakai dama kowane namiji a duniya, sai wanda sukaso yimata wasa da hankali a kansa, ada ita kaɗaice da wannan matsalar, amma dalilin aurenku kaima hakan ta shafeka, sun riga sinci buri mai tsanani a kanta, wanda hakan bamai yuwuwa bane a garesu cikin sauki sai idan ALLAH ya ƙaddara hakan, akwai al'amari mai sarƙaƙiyar gaske tsakaninku, sai dai inaji a jikina komai yana gab da warwarewa dalilin abu uku wanda nima ALLAH bai bani ikon saniba, ka jajurce wajen tsananta bincike zaka fahimci komai da yake komai dangane daku. Bazan ɓoye makaba, wanda kukazo nema a wannan Jejin baya raye, sai dai jininsa shine jini mafi haɗari dazai zamarma duk wanda tsiyayar dashi tauraruwa mai wutsiya, ki adana wannan tsintuwar ta hannunki tamkar yanda kika adana ta farko, sai dai zasu cigaba da tsorataki domin bibiyar kayansu dan kin raunanasu sosai, duk randa ta uku tazo gareki suka zama huɗu dana hannun mijinki komai zai buɗe”. Baba ƙaura ya miƙe yana ɗan murmushi da binsu da kallo tamkar yanda suma suke kallonsa har Bilkisu, ya sake cewa “ƘWI CIKIN ƘAYA AJIYAR ALLAH”. ya juya ya barsu.
Da ƙyar Jawaad ya iya maida kallonsa ga Bilkisu, ya kamo hannunta dake rumtse ya buɗe a cikin nashi, Wurine baƙi mai girma tamkar wanda ta taɓa tsinta a ɗakinta. Zumbur ta tashi zaune jikinta har yana rawa, dan sai yanzu ta fargafa a jikin boss take kwance. Wasu hawaye masu zafi suka fara zirara a kumatunta suna sauka bisa fuskarta.
Shidai Jay kallonta kawai yakeyi, ɓullowar su baba ƙaura ya sashi faɗin. “Shiii!!!” yana mai ɗora yatsansa akan bakinsa. Saurin kallon inda yake kallo tayi itama, su Jabeer ne ɗau da mutum bisa buzu. Atare suka miƙe ita da Jay harsu Hafiz suka iso inda suke suka ajiye gawar Gimba da duk fuskarsa tai kaca-kaca da raunuka tamkar yakushi. Durƙushewa Jawaad ya koma yayi gaban gawar, hanunsa na rawa yakai kan fuskar Gimba ya shafa, idanunsa sun sake kaɗawa sunyi masifar yin jazurr, jijiyoyin kansa sunyi ruɗu-ruɗu. Su Hafiz sai sharar ƙwalla sukeyi suma.
Ɗagowa Jay yay yana kallonsu, dagani kasan shima kukan zuci yakeyi, ya maida duba
nsa ga Baba ƙaura dake riƙe da farin ƙyalle a hannu. Baba ƙaura ya girgiza masa kai da lumshe ido alamar ban haƙuri. Juyawa yay yana kallon Bilkisu dake kusa dashi tsaye tana kuka iya ƙarfinta. Ya dafe goshinsa yana murzashi da ƙarfin gaske, soyake yayi hawaye tamkar yanda suma sukeyi kozaiji daɗi, sai dai sunƙi fitowa, sai zuciyarsa dake wani irin zafi mai azabartar da gangar jiki da ƙwaƙwalwa. Miƙewa yay daga gaban gawar ya kamo Bilkisu dake tsaye. Jikinsa ta faɗa tare da sake fashewa da kuka mai huda zuciyar mai sauraro.
Baba ƙaura sai basu baki yake da nuna musu muhimmancin ƙaddara da karɓarta a duk yanda tazoma bawa, sannan mutuwa alƙawarin ALLAH ce ga kowane mai rai dake doron ƙasa, shi da ya tafi ba gaggawa yayba, mu da muke raye bamuyi jinkiriba, ALLAH yay alƙawarin kwanansa ya ƙare, waɗanda suka kashesha sanadi suka zama, da sunyi haƙuri ma aranar zai bar musu duniyar dama. Da waɗan nan kalaman hikima Baba ƙaura ya shawo kansu har suka ɗakko ledan da sojoji kan saka gawa kafin a kaita inda ya dace idan har basu da damar binneta a wajen yaƙi. Haka aka saka gawar Gimba da cikin hikimar UBANGIJI babu abinda tayi tamkar yanzune ya rasu.
Bily bata iya shiga cikin jirginba saida taimakon Jawaad, yanzunkam kusa dashi ya zaunar da ita, dan shima yana buƙatar jin ɗuminta.
Dukda halin da ake ciki hakan ba ƙaramin zafi yayma Rose ba, har cewa Jay take munafuki a cikin zuciya, a ganinta shida yake gudun taɓa macen daba matarsa ba yau wane gulma ta kaisa mamuƙar wannan yarinyar kuma? Taja tsaki a cikin ranta tana ɗauke kai, ta tsani yarinyarnan wlhy, kuma itama tana gab da salwantar mata da rayuwa inhar bata fita rayuwar boss na, yarinya ƙarama sai baƙin karuwanci?.
Wannan zantuntuka sune Rose taita tattaunawa da zuciyarta har jirginsu mai saukar angulu ya sauka a garin su gimba tamjar yanda Jawaad ya yanke shawarar suyi kawai. Ya kuma kira Sir Ahmad ya sanar masa halin da ake ciki, hakama Alhaji Babba.
______________________
Tunda Jawaad ya kira Alhaji babba ya sanar masa inda zasuje da rokon a tayasu addu'a sai ya kasa zaune ya kasa tsaye, haka ya tara tsoffin anguwarsu sukai shawara akan subi makarantu yanzunan a dasa saukar Alkur'ani mai girma, tare da masallatai idan lokacin sallar zuhur yayi, ya kira Ummah babba da ƙarama ya umarcesu da yin abincin sadaka su bada a fitar a rabama mabuƙata.
lokacin dasu Jawaad ke cikin wancan mawuyacin halin addu'oin bayin ALLAH ne dana ƙananun yara keta riskarsu, tareda farin cikin mabuƙata da aketa rabama lafiyayyen abinci harda abin sha.
(Duk wanda yace ALLAH ya tsira wlhy, bawa saki kowa ka kama ALLAH shine shugaba mai kallon motsin kowa hatta da ƙwaron da idanu basa gani, mai bada kariya ga kowa ta inda bakai zatoba, mubar zagin shugabanni na duniya da suka zama wakilanmu akan san zuciyarmu, mubar ɗaukarsu matsayin waɗanda zasu bamu kariya ko farin cikin duniya domin suma mutanene tamjarmu, basu isa sanin abinda yake ɓoyeba sai wanda ALLAH yaso su sani, mu aje shirmen siyasa gefe muyima ƙasashenmu addu'a da shuwagabanninmu wannan shine nasararmu).
________________________
Su Jawaad sun isa da gawar Gimba ƙauyensu, inda helicopter ɗin da suke ciki ya sauka a filin makarantar primary ɗin dake gab da gidansu gimban, daga nanne aka ƙarasa da gawar bayan su Baba ƙaura sun fara isa gidansu Gimba sun isar da saƙo maiban tashin hankali.
Faɗa muku yanda abubuwa suka cabe a wannan lokaci abune mai wahala, dan matarsama suma tayi saida aka zuba mata ruwa, haka ƴan anguwa da danginsa sunata kuka dan gimba mutumne na mutane, sannan yanada son zuminci, duk alkairin da yake samu ga Jawaad bai yarda yaci shi kaɗaiba hatta da wanda ba nasabama ci suke shima.
Gimba shi kaɗaine ɗa namiji wajen iyayensa, babansa ya rasu tun suna yara, mahaifiyarsu itace taita ɗawainiya dasu har girma, sai ƙanwarta dake aure birni da bata gajiyawa da taimakonta da marayun ƴaƴanta har suka girma, yayi karatunsa har zuwa diploma saɓanin ƴan uwansa mata da ke tsayawa iyakar secondary ake musu aure, shine ɗa na farko, sa
i ƙannensa shida duk mata, huɗu sunyi aure harda zuri'a sai biyu na nan suna karatu, harma Jawaad ya ɗauka alƙawarin zuwa ya roƙa mahaifiyar su gimban dan suci gaba da jami'a idan sun kammala sakandiri ɗin da suke aji shida yanzu, a lokacin gimba yata murna dan dama burinsa kenan. Matar gimba ɗaya da yara uku duk maza, yaronsa na ƙarshe sunan Jawaad ya saka masa yana kiransa da suna yayana. Adalilin Hajiya Safara'u ƙanwar mahaifiyarsu dake zaune birni ya samu aiki a ƙarƙashin Jawaad, (zuwa gaba lokaci zai fiddo mana wacece Hajiya Safara'u).
Mahaifiyar Gimba mace mai haƙuri da sam batai kukaba saina zuci itace tace Jawaad ne zaima gimba wanka tare da ƙaninta mai suna Ibrahim wanda ya kasance dattijo ne sosai.
Su Jawaad suna can suna ƙimtsa gawar Gimba su Alhaji Babba suka iso kusan mota huɗu, harda jama'ar gidansu Jawaad wato kawunnansa.
Jawaad da kawu Ibrahim sun suturta gawar gimba tamkar yanda shari'a ta koyar, kafin mahaifiyarsa da ƴaƴansa harma da ƙannensa su shiga suyi sallama da gawar, daganan aka fito dashi domin miƙasa maƙwancinsa na gaskiya. Kuka sosai ya tashi a gidan maiban tashin hankali har aka fice da gawar daga gidan zuwa ƙofar gida inda su Alhaji babba da mutanen gari suka haɗu wajen sallatarta.
Masha ALLAH yayi jama'a kam har abin ya bama mutane mamaki, sai dai UBANGIJI shiyasan ajiyar da yay a wannan waje. (ALLAH ya gafartama gimba da iyayenmu da dukkan musulmai da suka rugamu tafiya😭🙏🏻).
Bayan an dawo daga kaisa su Jawaad basu tafiba, suna a cikin garin har gabanin magriba ana amsar gaisuwa dasu shi dasu Hafiz, Jabeer, Aliyu, sai Bilkisu. Sojojin da sukai musu rakkiya da Baba ƙaura sun wuce tun bayan da aka dawo daga binnesa. Rose ma lokacin da su Sir Ahmad zasu tafi dasu Alhaji babba bayan sallar la'asar Jay yace ta bisu. Bilkisu kuwa tana ciki tare da matar Gimba, batasan yaya akai sukasan ita matar Jawaad baceba, sai kawai ganitai anata nunata da faɗin itace matar ogan marigayi Gimba. Haka zasuyita jera mata addu'a da yabon halin Jawaad bisa ɗawainiya da taimakon da ƙauyen yake samu daga Jawaad ɗin ta dalilin gimba. Haka sukaita mata komai a girmame tamkar tafi kowa. Ita harma kunya ta komaji akan yanda suke matan.
Wajen ƙarfe shida saƙo ya iso mata akan ta fito inji boss zasu wuce. Haka ta tashi ta kimtsa jiki a saɓule dan ta amshi hijjab ɗin matar gimba ta saka tun ɗazun saɓanin da da take da baby hijjab kawai. Sunata mata godiya da addu'a, ƙannensa suka rakota har waje inda motar da zasu tafi take.
Sau ɗaya na kalli Boss na ɗauke idanuna saboda wani irin tausayi yake bani, na ƙaraso inda yake tsaye na gaishesu tare da sake musu gaisuwa, murya cike da damuwa ya amsa mani yana min nuni dana shiga motar daya buɗemin. Ni da shi da Jabeer ne a baya, ina jikin ƙofa yana tsakkiya Jabeer kuma a ƙarshe, sai Aliyu da zai ja motar Hafiz na gefensa. Haka muka wuce sunata mana addu'oin sauka gida lafiya.
Sosai Aliyu ke sharara gudu kasancewar garin yay wani irin ɗaurewar hadarin farkon damina mai cike da iska a ciki, babu mai magana a motar sai zancen zuci, cikin awa ɗaya da mintunan da bazasu gaza ashirin da bakwaiba muka iso cikin gari, zuwa lokacin garin ya sake yin duhu, gana hadari gana magriba, anata salloli a masallatai. Nayi zaton masarauta zasu kaini, sai naga an nufi gidansu Boss, koda mukazo gate sai yace basai Aliyu ya shiga da motarba bara mu sauka anan su wuce kar hadarinan ya riskesu..................✍
(Dolene koda zai halaka da izinin ALLAH sai ya gano suwaye suka kashe ɗan fir'auna, miyasa suka kasheshi?, minene a binne da rayuwarsa da ɗan-fir'auna yaso sanar masa, yanaji a jikinsa kisan ɗan fir'auna nada nasaba da abinda ya shafesa, minene shi? Wannan ne bai saniba.)
dolene jiya kushiga ruɗani akan mutuwar ɗan fir'auna bayan farkon page na nuna bai mutuba, nima sai a Comments ɗinku na fahimci kuskuren danayi na koma na duba page ɗin, wlhy hankalina sam bai kaiba ko'a wajen editing, rayuwace abubuwa sunma ƙwaƙwale yawa, kana gabas tunaninka na yamma, amin afuwa ɗan fir'auna bai mutuba🤦🏻. anahin abinda naso sakawa a
wajen shine (Dolene koda zai halaka da izinin ALLAH sai ya gano suwaye suka so kashe ɗan fir'auna, miyasa sukaso kasheshi?, minene a binne da rayuwarsa da ɗan-fir'auna yaso sanar masa, yanaji a jikinsa masu son kisan ɗan fir'auna nada nasaba da abinda ya shafesa, minene shi? Wannan ne bai saniba).🤗🙏🏻
ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏🏻.

0 comments:
Post a Comment