Page 31
...............“Muje”. Ya faɗa a hankali. Babu shiri nai azamar ɗago idanuna na kallesa, duk da ni yake kallo ban janyeba, cikin harɗewar harshe nace, “Anan zan... zan kwana?”. Tamkar baiji abinda naceba ya ɗauke kansa, dubansa yakai ga sararin samaniya daketa sake caƙuɗewa da duhu, batare da yace min uffanba ya raɓani ya nufi gate. Hawayen da nake maƙalewa suka silalomin a kumatu, a fili nace, ‘Dan ALLAH kar kaimin haka nidai’. Kamar yasan mi nake faɗe ya juyo yayinda ya buɗe ƙofar gate ɗin zai shige, “Karki bari na dawo na sameki a nan gurin”. Yafaɗa yana nunoni da ɗanyatsa alamar gargaɗi. Hannu nasa na share hawayen fuskar tawa kafin na taka nima zuwa gate ɗin. Maigadine kawai ke bin jam'i a bakin gate ɗin da yake anaji daga cikin gida. Ganin yayi tsaye yana kallon maigadin ne yasa nima naja na tsaya, sai da aka sallame sallar da dama zaman tahiyar ƙarshe suke. Kamar jira, ana yin sallama maigadi na miƙewa ya nufosa. Fuska a haɗe Jay ke kallon maigadi, baiko amsa gaisuwar da yake masaba da sannu dazuwa yace, “Ka bautama UBANGIJI tamkar kana ganinsa, dan idan kai baka ganinsa shi yana ganinka, MANZON ALLAH ya horemu da zuwa masallaci muyi sallah cikin jam'i, miyasa kai kafi zaɓar yinta kai kaɗai a cikin gida? Shin tsaron gate dan kar wani ya shigo yafi maka muhimmanci akan zuwa ka samo cikakkiyar ladar da mahaliccinka kaɗai ke badata? Daga yau ina mai baka shawara a kowanne lokacin salla ka kulle gate ɗin nan idan yazama dole saika zama mai tsaron mutanen cikin gidan kaje kai sallah cikin jam'i”. Kan maigadi a ƙasa yace, “Nagode sosai Alhaji, ALLAH ya saka da alkairi ya kareka kaima, ya ƙarin haƙuri?”. Cikin lumshe ido Jay yace, “Alhmdllh, abokinku ya tafi ya barmu”. Hawayene suka ziraro a fuskar maigadi, hakan yasa Jay yin gaba shima yana haɗiye abinda ya tokare maƙoshinsa.
Jiki a saɓule nabi bayansa mukabar maigadi na kuka, sai naji nima hawayen nawa na sake gangarowa, dukda bawani sanin gimba nai sosai ba mutuwarsa ta taɓani ainun, mutum mai fara'a dason mutane.
Yana gama buɗe ƙofar da keys ɗin daya ciro a aljihu iskar na tasowa, hakan yasa muka shige da sauri saboda irin mai ƙasarnan ce sosai, da sauri na maida ƙofar na rufe na jingina jikinta ina sauke numfashi da share fuskata da hijjab ɗin gudun kar wadda ta hau ta shigarmin ido.
Boss kam ya kunna fitilar falon saboda an kunna Gen..., a take haske ya gauraye ko ina, baice dani komaiba ya nufi sama abinsa. Tafiyarsa kawai zaka kalla zaka fuskanci yana cikin damuwa, dan a sanyaye yakeyinta. da kallo na bisa har saida ya ɓacemin, na sauke ajiyar zuciya ina lumshe idanuna, a ƙasan raina addu'a nake ALLAH yasa idan iskarnan ta lafa yace zai maidani Masarauta.
Tunda ya shiga bedroom ɗin sai ya shiga yatsina fuska, shaf yama manta ko gadonsa bai samu arziƙin gyaraba yau, duk yanda yake jinsa a matuƙar gajiye haka ya daure ya shiga kakkaɓe gadon, ya gyarashi tsaf kamar ba yanzu za'a kwanta a kansaba, fitowa yay ɗaukar tsintsiya, duk da sarai yaga Bilkisu dake tsaye jikin ƙofa har yanzu yay tamkar bai gantaba yaje ya ɗakko kwandon da kayan sharan ke ciki yazo ya sake hayewa sama.
Da kallo na bisa, haka kawai sai naga kamar bai daceba, dan da alama shara zaiyi da kansa, bayansa nabi jikina duk a saɓule, ga kaina namin wani irin ciwo ƙasa-ƙasa, ga yunwa dan rabona da abincin kirki tun breakfast ɗin safe, a garinsu marigayi fura kawai nasha rabin kofi itama sai da aka takuramin. Duk da sallamar da nayi bai ɗago daga abinda yakeba, nasan salon amsa sallamarsa a ciki-cikine hakan yasan ban damuba dan nasan dai ya amsani, nace, “Bara in share”. Kamar bazai kulani ba, sai kuma ya miƙamin tsintsiyar ya fice.
Ajiyar zuciya na sauke na cigaba da sharan a sake ganin ya fita saini kaɗai. Tsaf na kammala sannan na nufi toilet, shima dai yana buƙatar wankin dukda bawani datti yayba na tashin hankali, tsaf na gyarashi cike da ƙarfin hali. Ina fitowa daga bayin shima yana shigowa ɗakin, saurin ɗauke kaina nayi daga garesa saboda ganinsa a tuɓe babu riga sai dogon wando kawai da farar singlet yana waya, ya zauna a bakin gado
n yana cigaba da wayarsa, kusan mintuna biyu ya juyo inda nake tsaye, yatsunsa biyu ya murza sukai ƙara, hakan yasa na ɗago kaina garesa, alamar nazo yaymin. Ahankali na taka zuwa garesa, ya miƙamin wayar batare da yace komaiba ya bar wajen. Duk da bansan ko waneneba haka nai sallama, muryar Ummah naji ta amsamin, hakan yasa na gaisheta cike da girmamawa, itama daga can da kulawa ta amsamin tare da min ta'aziyya. Nai mata godiya Nabeelah ma ta amsa muka gaisa, sai aunty Batool itama, daga nan mukai sallama. Wayar na ajiye masa bakin gado na fita falo, Zama nai a kujera ina jiran ya fito naji hanlin da nake ciki, harga ALLAH bana fatan kwana a gidannan. Nai zurfi a tunani da jiran fitowarsa kira ya shigo wayata, gyara zama nai na cirota a aljihu, Amaturrahman ce, dan haka na ɗaga muka gaisa, daga can tace, “Mun jiki shirune, ca muke tun biyar zaki dawo?”. Ɗan murmushin ƙarfin hali nayi, kafin nai mata bayanin yanda zata iya fahimta, nakuma nuna mata cewar bamu dawoba muna ƙauyen su gimban sai dai gamu nan a hanyar dawowa” addu'ar isowa lafiya tai mana kafin mu yanke wayar. Na faɗama Amaturrahman hakane da tunanin idan boss ya fito zaiji tausayina ya maidani can a daren nan.
Jawaad daya samu yay wanka da ruwa mai ɗumi sosai sai yaɗanji daɗi da sauƙin nauyin jikinsa sai dai na zuciya, yay alwala ya fito, ƴan dube-dube ya hauyi sai dai babu ko alamarta a ɗakin, guntun tsaki yaja yana lumshe idanunsa, dan shi kaɗai yasan ya yakeji, ga yunwa ga gajiya ga damuwa, dan shi babuma abinda ya sakama cikin nasa bayan coffee da yasha a office sai ruwa da yayta sha a garin su Gimba. ita kanta tausayinta yakeji gashi bawani ƙarfine da itaba ta tashi daga ciwo shekaranjiya jiya. Wadrobe ɗinsa ya buɗe ya ɗauki jallabiya fara tas ya saka mata turare sannan yasa a jiki, harya shinfiɗa abin salla sai kuma ya kalli ƙofa, koya kirata bazai yuwu tajiba saboda iskar da ake a waje abun babu sauƙi, tamƙar zata ɗauke rufin kwano, danma duk Windows ɗin sashen a rufe suke shiyyasa sukejinta da sauƙi su.
“Ki taso kiyi wanka”. Ya faɗa kawai daga ƙofar ɗaki ya juya abinsa dan yasan zata iya jinsa daga inda take. Ba ƙaramin wintsilawa kayan cikina sukaiba lokacin da furucinsa ya isomin cikin dodon kunne, sai dai koda na ɗago tuni ya juya sai ƙamshinsa daya barmin. Rasama wane tunani zanyi nai, mi yake nufi da nazo nai wanka? ‘A toilet ɗinsa?’ na faɗa a fili kamar zanyi kuka. saukar ruwan sama babu zato ya sakani miƙewa zumbur dan naji tsoro wlhy, gashi da ƙarfi ya sauka dukda p.o.p hakan bai hanani jin ƙararsaba akan rufin, to nidai dama can akwai tsoro idan ana ruwa, nafi buƙatar naga mutane a kusa dani hankalina yafi kwanciya, balle wannan da ruwan ya kasance kaso biyu a cikin uku iskace ma, wani wal garin yayi na walƙiya, labulen Window'n da ba'a sakiba sai glass ɗin kawai aka rufe yasa naga tamkar inuwar mutum a wajen, jikina har rawa yake na tashi na nufi ɗakin boss da ɗan gudu-gudu sauri-sauri har ina neman faɗuwa, wayatama anan na barta saman kujera. Na maida ƙofar da ƙarfi na rufe ina rumtse idanu da sakin nishi mai ƙarfi, har yanzu ƙirjina sai wani ɓal-ɓal yake badawa.
Shidai Jay salla yake, amm duk da haka ya jiyo yanda Bilkisu ta rufe ƙofa da ƙarfi, koda ya idar bai juyi ya kalleta ba, ya miƙe domin kawo isha'i da yaga lokacinta yayi. “Sallarce bazakiyi ba komi kike nufi?”. Da sauri na buɗe ido ina kallon bayansa daya juyamin. Murya a raunane nace, “Ai idan naje gida duk zanyi fa?”. Cikin takaici Jay yace, “Ainan ɗin jejine ko? Karki bari na ɓata miki rai a darenan Miemaa, ƙyaƙy! tom”. Daga haka ya kabbara sallarsa.
Jin yanda yay maganar a kausashe na tabbar zai aikata duk abinda ya faɗa ɗin, haka na nufi toilet ɗin ina ƙunƙuni a raina, wannan wane irin abune haka, miyasa tunda anga hadarin baza'a kaini inda nakeba sai a wuto dani nan, nidai komai dare saina bar gidanan ehe. Da wannan ƙunƙunan a cikin rai na shiga bayin, ruwa mai zafi na haɗa dan jikina bala'in ciwo yakemin sosai, banga wani soso ba bayan nasa a bayin, haka na ɗauka nai wankan da shi ina maijin daɗin ruwan, sai da na kammala nai alwala sai kuma
naji ƙyanƙyamin maida kayan dana cire, to amma idan ba su ɗinba mizan saka? Nida bazan fita da tawul ba gaskiya, to idanma na ɗaura tawul inada kayan dazan saka ɗinne a ɗakin.........?
Wata irin ƙara na saki jikina na masifar rawa saboda ɗaga kan da zanyi idanuna sukai tozali da wata iriyar mummunar halitta baƙa ƙirin da jajayen idanu, jikinta dai zam maciji, amma kan bana maciji baneba...
A rikice Jawaad dake addu'a ya miƙe saboda jiyo ƙarar Bilkisu dake bayi, ALLAH ya sosa bata kulle ƙofarba, ya tura da ƙarfi babu ko neman izini ya shige, dai-dai bily tai baya zata faɗi saboda numfashinta daya ɗauke dan firgici, tallafota yay ta faɗo jikinsa, yayinda idanunsa kebin halittar dake silalawa ta Window zata fice da kallo. Sai da ta gama ficewa tsaf sannan ya maido kallonsa kan Bilkisu, saurin kauda idanunsa yayi dan babu komai a jikinta, ya jawo tawul dake ciƙin ƴar drawern glass na toilet ɗin ya yafa mata sanann ya ɗaukata cak batare da yace komaiba ya fita da ita. Saman gadonsa ya shimfiɗeta, dukda ya yafa mata tawul sai da ya sake jan bargo ya rufa mata har saman ƙirjinta, tsaye yay yana ƙarema fuskarta kallo tamkar maison gano amsar tambayoyin zuciyarsa akan fuskartata, tsahon mintuna kusan goma kafin yabar wajen ya koma toilet ɗin yana dube-dube, babu komai kam, sannan a mamakinsa Windown kaɗan ya ɗaga, hanyar da yabi baikai faɗin da halittarnan zata iya shiga da fitaba, ‘mikenan?’ ya tambayi kansa, dagacan gefen zuciyarsa ta bashi amsa da (Aljanu). “Aljanu!” ya maimaita akan laɓɓansa har sau biyu. “Hummm!” ya sake faɗa a fili yana ɗibar ruwa kaɗan a ƴar roba dake toilet ɗin ya fita. Iskar hadarin ta fara lafawa, sai ruwa da ake yaf-yaf na farkon damuna, dan daya fara da ƙarfi sai kuma ya koma ɗaf, sai kuma ɗan yaf-yaf, sai dai walƙiya da aketa faman yi harda cida mai ƙarfi lokaci-lokaci. Zama yay a gefen gadon kusa da cikin bilkisu tare da ajiye robar ruwan a ƙasa batare da ya shafa mataba ya faɗa tunani. Abinda ya faru a jeji ɗazun, kalaman baba ƙaura, kalaman abokan ɗan fir'auna, ainahin abinda Gimba ya gani har yazo ya faɗa masa a randa aka shirya juya ɗaurin auren Qaseem da bilkisu zuwa Azeema da Qaseem bilkisu da ɗan fir'auna, Accident ɗin ɗan-fir'auna, mafarkinsa, sai abinda ya gani yanzu wanda ya firgita bily. Ya shiga saƙa waɗanan abubuwan dake gogayya da juna daki-daki a muhalli guda. Yay murmushi mai ciwo saboda amsar data zo masa a zuciya lokaci ɗaya. Cikin zafin nama ya miƙe, Ranƙwafawa yay kan bilkisu ya shafa mata ruwan daya dumtso a hannu, a take ta kawo numfashi mai ƙarfi.
A hankali na buɗe idanuna, sai kawai a bazata naci karo da fuskar boss dake ranƙwafe kaina daf da tawa, dan har inajin saukar numfashinsa akan tawa fuskar, gabana ya faɗi, nai saurin fara waige-waige danson kauda fuskata. Saukar tattausan tafin hannunsa naji saman fuskar ya sake juyo dani garesa. Duk yanda naso janye idanuna da suka shige cikin nasa na kasa, kallon ido cikin ido mukema juna karon farko, wani irin abu mai wuyar fassara ke fitowa daga ƙwayoyin idanunsa masu girma da sirkin jaa suna shiga cikin nawa, atake naji tsigar jikina na tashi, ƙofofin gashina na buɗewa gashin na miƙewa, jinina dukya tsinke lokaci guda yana wani irin gudu a cikin jijiyoyi, sai kawai na saki kuka a hankali.
Jawaad da har yanzu idanunsa ke kafe a cikin na bilkisu yaɗan murza babban yatsansa daga jikin hancinta har zuwa ƙasan idonta ya kwashe hawayen dake fitowar ya maida yatsan baya jikin ƴan uwansa, dan har yanzun tafin hannunsa na tallafe da kuncinta na haggu. Ahankali ya furta, “Tabbas ƙaddararki da tawa a haɗe take Miemaa, zan bada ƙarfina da lokacina wajen binciko abinda ya ƙullemu ƙarƙashin inuwa ɗaya insha ALLAH”. Yana gama faɗar hakan ya saka ɗayan hannunma a gefen kumatuna na haggu ya ɗauke duk hawayen dake zuba a idanuna guda biyu, sannan yaja baya tare da miƙewa tsaye yabar wajen.
Lumshe idanuna nai a hankali kalamansa namin kaikawo tsakanin zuciya da ƙwaƙwalwa, a hankali nima kalaman baba ƙaura da abinda ya faru yau a jejin suka shiga dawomin daki-daki. Jin an ruƙo hannuna nai saurin buɗe ida
nuna, boss ne riƙe da riga a hannu, batare da yayimin maganaba ya ɗaga kaina a hankali ya ziramin wuyan, sannan ya kamo hannuna ya taimakamin na saka, ɗayanma haka. Juyawa yay yana faɗin, “Ki tashi kiyi alwala ki sauke nauyin sallolin dake kanki”. Daga haka ya fice a ɗakin. Dukda tsoron dake a raina haka na miƙe dan nima rashin yin sallar cizon raina yake sosai, sauka nai daga gadon, rigarsa ce t-shirt mai guntun hannu, dukda a ido bata da girma sai gashi takai min har kusan quarter ɗin cinyata, na ɗauki wandon dana gani gefena, a raina nake raya ‘Ni balki, nice kuma da saka kayan boss yau?’. Sauƙina wandon irin mai taushin nanne da roba acan ƙasansa, sannan a sama ma robace harda zariya. zariyar naa ɗaure sannan a tsoro-tsoro na nufi bayin ina addu'a a cikin raina, saida na leƙa na tabbatar babu komai sannan na shiga batare dana rufeba na ɗauro alwalar na fito. Nayi namakin ganin hijjab a ajiye, da alama tun ɗazunma ya ajiyeshi, haka na ɗauka na saka na fara sallolin da suka shigemin.
Jawaad kam koda ya fita sashen Uncle Nasir ya nufa, a falo ya iske yaran harda mamansu suna kallo, duk gaidashi suka shigayi da masa ta'aziyyar Gimba, ya gaisa da Ammi ma, sannan ya zubama Ameera harara da faɗin, “Wannan banzar shigan fa? Ko ɗan kwali babu kanki”. Cike da taoro Ameera ta miƙe tana faɗin, “Dan ALLAH kayi haƙuri Yah Jay”. Bai sake tanka mataba, amma kallon da yake mata ya isheta shiga uku, da gudu tai ɗakinsu domin suturta jikinta, dan dama ya hanasu shigar banza tun yana zaune a sashen (karku manta bayan rasuwar mama Maryam Uncle Nasir shine ya cigaba da riƙon Jay har yay aure). Baya musu wasa idan yaga kan mutum yana rawa, shiyyasa suke masifar shakkarsa, gashi dama baya shiga shirgin ƴammatan gidan saboda gudun raini, samarinma kansu ba kowa ke ganin fuska daga garesa ba sai sa'anninsa dana sama dashi, suma ɗin bai maida kansa sakarai a garesuba ana dai mutunta juna. Raihana da itama ta nutsu waje guda ya kalla, “Tashi ki samo min abincin mutum biyu”. Tashi tai da sauri ta nufi kitchen, itadai Ammi batace komaiba, dan macece mai mutunci da sanin ya kamata, yanda Jawaad ke tsaye kan ƴaƴansu ita daɗi yake mata, dan shakkarsa na hanasu aikata abubuwa masu yawan gaske, har ranta kuma ƙaunar Jay take dan ita dai halayyarsa birgeta yake sosai.
Suna ɗan taɓa hira da Ammi akan rasuwar gimba Raihana ta fito ɗauke da ƙaramin basket na kaba mai ƙyau a hannu, tace, “Yah Jay gashi, ko nakai can?”. Batare da ya bata amsaba ya miƙa mata hannu alamar ta bashi, kawo masa tayi tana godema ALLAH a ranta, dan dama bason kaiwar takeba kar taje can ya sakata wani aikin kuma, dan hankalinta nakan film ɗin da suke kallo. Yana amsa ya miƙe yayma Ammi sallama ya fita.
Bayan na kammala sallolin sai kawai na ɗauki Alƙur'anin dana gani a ɗakin na shiga karatu cikin sanyin murya da rauni, dan inayi hawaye na zirara tamkar an buɗe fanfo.
Wani irin sanyi Jay yaji a ransa, ya ƙaraso cikin ɗakin sautin muryar bilkisu na ratsa zuciyarsa, sai yaji wata nutsuwa mai daɗi na saukar masa har cikin gaɓɓai. Bai dakatar da itaba ya ajiye basket ɗin ya fita, mintuna kaɗan ya dawo ɗauke da kifuna biyu sunata turiri alamar tea ya haɗo musu. Motsinsa ya sani rufe alkur'anin saboda nakai inda zan iya tsayawa, sonake na roƙesa ya maidani masarauta tunda har yanzu da sauran dare, ƙarfe goma da mintuna Uku.
Ido muka haɗa dan shima kallona yake, na maida kaina ƙasa ina juya abinda zan faɗaɗin da lanƙwasa yatsun hannuna madaidaita, “Dan ALLAH Yayah dare baiyiba, tunda ruwan ya ɗauke ka kaini can koka kaini gidan Dad na kwana”. Jin shiru bai tanka minba na saci kallonsa, shayinsa ma yake sha tamkar bai jiniba, kuma tsabar wulaƙanci kallona yakeyi. Kusan mintuna uku yace, “Taso kici abinci”.
‘Yah ALLAH, wai da wane yare zan fahimtar dashi ya fahimtane?’. Na faɗa a zuciya idanuna na cika da ƙwalla, Ban karaya ba dai, duk dan ya barni nafi nabi umarninsa, babu musu na miƙe zuwa garesa, batare dana cire hijjab ɗinba nai yunƙurin zama ƙasa. Gadon ya nunamin da hannu yana sake tamke fuska. Yanzunma dai Umarni nabi na zauna dukda ba ha
ka nasoba, ya miƙomin kofin shayi kawai. Ƙananun kofunane dan basu wuci rabin kofi ba, tea ɗin ma kuma bai cikaba, cikin dauriya da fatan maidani masarauta na hau sha, sosai yayi daɗi abin mamaki, bansan na shanyeba balle dama yunwa nakeji.
Kofin da yasha nashi tea ɗin ya ajiye, ya buɗe kular dake cikin basket ɗin ya ɗiba abinci dai-dai misali, nidai kallonsa nake ƙasa-ƙasa, tashi yay ɗauke da filet ɗin a hannu ya koma saman kujerar ɗakin, “Ga abinci nan” yay maganar batare da ya kalleniba. Duk da inajin kunyarsa yunwa nakeji sosai, idanma nace bazanciba zan cutar da kaina matuƙa. Kofin na ajiye na ɗiba dai-dai misali. Koda wasa ban ɗago kainaba harna kammala, na miƙe na tattare har filet ɗin daya gama shima na fita dasu duk da a tsorace nake.
Jay ya bita da kallo harta fice, a ransa yake faɗin, ‘Ahaka sai ka ganta kamar wata saliha, sai dai shegen taurin kaine da ita da tsoro ko farar kura ta shafa mata lafiya’. (Jay a rage sa ido dai. Lol😂).
Babu jimawa na dawo ɗakin, zuciyata na sake tunzurani akan na sake roƙonsa dai. Yana zaune inda na barsa ya baza takardu a table ɗin gaban kujerar yanata rubutu, na ƙaraso bakina ɗauke da addu'ar neman nasara a kansa, jikin hannun kujerar na duƙa ina mai narke murya dan yaji tausayina. “Amaturrahman ta kirani akan sunga ban dawoba, ni kuma na sanar mata muna hanyar dawowa, kuma zan koma masarauta, nasan sunacan suna jirana”. Aikin gabansa kawai yake kamar bai jiniba, na kuma raunana murya da faɗin, “Boss Please, idan na kwana a gidannan da safe wace amsa zanba mutanen gidan dasu Amaturrahman ɗin?”.
Karon farko Jawaad ya saki lallausan murmushin da har haƙoransa suka bayyana, dukda yana cikin halin damuwa da alhinin rasuwar gimba sai ta bashi dariya, fuskarsa ɗauke da murmushin har yanzun ya ɗago yana kallonta.
Wani irin daɗi naji ganin yana murmushi, a tunanina naci nasara, sai gani nai ya ɗauke kansa ya maida ga abinda yakeyi batare da yace komaiba, “In faɗa miki amsar da zaki basu idan sun ganki kin kwana anan da safe?”. Ya faɗa tamkar bashine yay maganarba. Ganin bance komaiba ya ɗago yana kallona, “Ko bakiso na riƙe kayata? Dan ƙyautace, idan ta ƙara wasu mintuna zata zama ta kuɗi”. Baki na tura masa dan haushi, nace, “Inaso”.
Jay dake kallonta har yanzu yakai yatsansa dab da bakinta ya ɗallah yana faɗin, “K kullum bazaki daina bani ciwon kaiba yarinyarnan?”.
Saurin ɗaura hannuna nai saman bakina dan zafi, idanuna har sun cika da ƙwalla, saurin rufesu nayi dan karsu zubo, boss mugune yasin, ina tausayinsa ashe bama abin tausayi baneba........
Ture takardun gabansa yay ya miƙe, a gaban bily dake durƙushe jikin kujerar da yake zaune yaje yay wani ɗan dirƙuso da kowa yasan maza da iya salonsa, da sauri-sauri zuciyarsa ke gudu, lumsassun idanunsa nakan fuskarta datai fayau saboda ramar da taɗanyi.
Saukar numfashinsa a saman fuskata da mayen ƙamshin turarensa ya sakani ware idanu dan mamaki, ko kaɗan ban san sanda yazo daf daniba, a take jikina ya fara tsuma, ya saka hannunsa akan haɓata ya ɗago fuskata da ƙyau, saurin lumshe idanuna na sakeyi ina ambatar sunan ALLAH a raina, dan wannan al'amari nasa yafi ƙarfina da wayona. Cikin taushin muryar da bansan yanada itaba, yay magana a hankali “Na maida amsata bakiso?”.
Da ƙyar na iya haɗiye yawu ina jinjina masa kaina alamar “eh” banason, dan burina kawai ya tashi wlhy.
Jay da shima baisan mike damun kansaba ya kuma matsar da fuskarsa daf data Bilkisu, a hankali ya busa mata iska saman idanunta dake rufe, mar-mar ta farayi da idanun saboda iskar da yake busa matan.
hancinsa ya ɗora saman nata yana gogawa, cikin magana raɗa-raɗa da ko kana kusa dasu da wahala ka jinsa yace, “Duk masu suna Bilkisu jarumaine, miyasa ke kike matsoraciya?”..................✍
(😂😂Saura naji wani yace maganar Jay ba gashkiya bane, kowa yasan mu jarumawane masu Suna Balkisu. Lol🚴🏼😜).
BARKANMU DA JUMA'A.
Kunata jira ko😑, ALLAH ina fara editing barci ya ɗaukeni, saida na tashi na tsinta wayar a gehe🤣.
Asha weekend lahiya🚴🏼🚴🏼🚴🏼😍😍😍😍🤗
ZAAF
AFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.
SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.
HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO
MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.
MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.
BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....
abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.
Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899
sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.
Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300
Sai kunzo😍😍😍😘.
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
Bilyn Abdull 📚:
SURPRISE💁🏻
Wannan page sadaukarwa ne ga iyayen yaran da suka kuɓuta, gaskiya ina tayaku murna matuƙa gaya, mungodema UBANGIJI daya maido mana dasu garemu da gaggawa cikin ƙoshin lafiya kuma, ƴan uwa wannan yana sake nuna mana mu duƙufa addu'a wa ƙasarmu, aikin bana shugabanni bane kaɗai, dan idanma munƙi addu'ar mune zamusha wahala, shugabanninmu mutanene tamkarmu, suma basu isa tsaremu ba sai wanda ya haliccemu, aduk yanda rayuwa tazo mana mu amsheta matsayin jarabawa mu godema ALLAH, UBANGIJI yafi kowa sanin halin da muke ciki, muyi ƙoƙarin cinye jarabawa sai muzama masu nasara, zage-zage marasa amfani nakasace irin ta zuciya, ALLAH yay mana ni'imomi masu yawa miyasa bazamu gode masaba sai ƙoƙarin aibanta waɗanda suke mutane kamarmu da hangen gazawarsu, sai dai taimakon addu'oinmu zamu samu tsaron da muke buƙata a yankinmu, muyi haƙuri mu duƙufa wajen faɗama ALLAH kukanmu, mu gyara mu'amulanmu ga junanmu mu kanmu, dan bazamu kasance azzaluman junaba sannan muce zamu samu shugabanni adalai, mugyara sai ALLAH shima ya gyara mana danshi mai rahamane. ALLAH ya kawo mana haske da kwanciyar hankali, ya dafama shugabanninmu suma akan ƙyawawan ayyukansu, saɓanin haka ALLAH ka magance mana badan halinmu ba😭🙏🏻.
Page 32
.................Ganin yanda ta tsume sai ta bashi dariya da tausayi, ya dungure mata kai yana miƙewa da faɗin, “Yarinyarnan ki rage tsoro”.
Ni kaina bansan na sauke wani kakkauran numfashiba tare da komawa na zauna daɓar, nai azamar cusa kaina tsakanin cinyoyina ina mai godema ALLAH daya tashi. A raina sai ayyana rashin kunya irin na maza nakeyi, suyi abu kuma su fuske abinsu tamkar basuyiba.
Jay da tuni ya koma kan aikinsa yaɗan kalleta ya maida kansa ga rubutun da yakeyi, haka kawai yanaso ya ganta a yanayin tsoro dan ƙyau take masa. Bai sakebi takantaba ya cigaba da haɗa bayanai akan case ɗin mutuwar Gimba, ya ɗaukama kansa alwashi sai yabi kadin jininsa, duk masu hannu a cikin wannan al'amarin kosu ubanwaye saiya soya musu gyaɗa bisa tafin hannu. Ganin lokaci yaja sosai Bily na a yanda take tun ɗazun ya sashi sake kallonta, muryarsa babu alamun wasa yace, “Miemaa!”.
Gajiyar dake tattare dani tasa har barci ya saceni a haka ban fargaba, a bazata naji ya kira sunana, na ɗago da sauri na kallesa, shima ni yake kallo, sai dai fuskarsa babu walwala sam. “Tashi kije ki kwanta” ya faɗa yana nunamin gado da idanu. Yanda ya tsuke fuska babu sauƙi yasa na miƙe babu musu dan nasan dai kwana anan dole ya tabbata, zuwa nai na kwanta a bakin gadon sosai, naja bargon na rufama jikina batare dana cire hijjab.
Jay daya kuma maida hankalinsa ga aikinsa yace, “Kicire wannan hijjabin tunda ba cinyeki za'ai a ɗakinba”. ‘Boss matsala’ na ayyana a cikin raina ina zame hijjab ɗin naja bargon har saman wuyana.
Duk da azabar ciwon kai da ya keji haka ya jure yana cigaba da haɗa bayanan, sai kusan ƙarfe ɗaya saura ya miƙe, kallo ɗaya yayma sashin da Bilkisu take kwance ya fahimci har yanzu idonta biyu, baice komaiba ya cire jallabiyar jikinsa yasa t-shirt fara akan boxer ɗinsa ya haye gadon shima, sai dai ba kwanciya yayba, zama yay ya jingina bayansa jikin fuskar gadon ya kashe fitilar ɗakin yabar iya ta gefen gado. Bargon yaja ya lulluɓe iya ƙafafunsa zuwa cinya, ya lumshe idanunsa yana maijin zafi da ƙirjinsa ke masa wanda yaketa ƙoƙarin dannewa, tunɗazun dannewa kawai yake dan bayason ya ƙuntata zuciyar yarinyarnan da laifin daba nataba, yana buƙatar jin wasu abubuwa daga garetane shiyyasa ya kawota nan dama. Rayuwarsa da gimba ta shiga kokawar dawo masa cikin zuciya, yarone mai mutunci da sanin mutuncin duk wanda zama ya haɗashi dashi, yasha saka Gimba manyan ayyuka masu haɗari akan aikinsa kuma yay masasu cikin ƙwazo, gimba na ɗaukarsa tamkar yayansa da suka fito ciki guda, tabbas yayi rashi wanda yasan bazai taɓa maye gurbinsaba har abada, danshi tuni yabar ɗaukar gimba matsayin drivern sa kawai jinsa yake a jininsa tamkar ɗan uwansa abokin farin ciki da baƙin ciki. Wata ƴar ƙwalla ta taru mai akan fatar idanu kaɗan, hannu yasa ya shareta yana mai jero masa addu'oin ne
man gafara a cikin zuciyarsa. Ya ɗau tsayin mintuna goma a haka kafin ya juya ya kalli Bilkisu, ɗauke kansa yayi murya cike da ɗaci yace, “Miyasa kika dawo gidan su Hudah da zama?”.
Banyi tunanin ya fahimci idona biyu ba har yanzun, na rumtse idanuna da ƙarfi ina sauke ajiyar zuciya, batare dana motsaba nace, “Ƙaddarar maraici”.
Idanu Jay ya tsurama bayanta, tsawon sakanni ya ɗauka a haka kafin ya sake ɗauke kansa daga gareta, “Ina dangin mahaifinki suke? Misa basa cikin rayuwarki?”.
Hawayene masu zafi suka silalomin, dan yau kan Boss ya taɓomin inda yafi ko'ina ciwo a zuciyata, zaune na tashi na jingina da fuskar gadon nima, hawaye na ƴar tseren fitowa na shiga bashi amsa kai tsaye, dan na fahimci so yake kawai yasan wacece niɗin kafin zuwana gidan su aunty Shahudah, batare dana kallesaba nace, “Har iyayena suka bar duniya su dukansu basu taɓa sanar dani wata matsala dake tsakaninsu da duk danginsu ba, dukda nasha musu tambaya sai dai babu wanda ya taɓa bani amsa ƙwaƙwƙwara a cikinsu, kullum amsarsu a gareni itace, (komai da lokacinsa, idan lokacin yayi zan sani) tun ina damuwa da abun harma na ciresa a zuciya, dama ba komai ke sakani kwaɗayin son jiba sai yanda nake ganin sauran yara ƴan uwana sukan shirya a ranakun juma'a da Sallah suje gidajen danginsu, sai dai ni daga gareni ba haka baneba, tunda na girma nai wayo a gidan haya mai ɗauke da ɗakuna kusan arba'in na buɗi ido na ganmu, bara dai na maka gwari-gwari zakafi farimtata.
Ni dai sunana Bilkeesu ɗiya ga malam Ado makaho, ƙwarai mahafina makahone da ko tafiya baya iya yi sai da ɗan jagora, Sai mahaifiyata Asiya.
A shekarun baya can mahaifina yana ɗan gani da ido ɗaya, amma da ga baya wahalhalun rayuwa suka ida rufe ɗayan idon yazam gaba ɗaya, mahaifiyata ma tana da nakasar ƙafa, dan kuwa gurguwace bata ma iya tafiya sai dai jan jiki. A matsayin da iyayena suke kawai zai nuna muku ni ba kowan kowa bace ba, dan kuwa muɗin talakawane irin tiɓis ɗinan da a kullum sai an nemo za'aci. Abin da zai matuƙar birgeka a rayuwar iyayena shine sam mahaifina baya bara balle aje kan mahaifiyata, duk da baba baya gani bai yarda zama maroƙi ba, dan a ganinsa UBANGIJI ya masa dukkan gata da ya bashi rai da lafiya, idaniyar ganice kawai bashi da ita. Sana'ar mahaifina itace sai da kayan ɗinki irinsu zare, allura, almakashi da dai sauran kayan nau'in ɗinki tsiraru dai-dai arziƙinsa, a gaba ɗaya jarin idan zaka dinƙuleshi waje ɗaya bazai wuce na naira dubu goma sha biyarba, wataƙil ma na zurma da yawa. Dalilin kamewarsa na janye kansa da ga ƙasƙancin bara ne ya ja hankalin mafi yawan telolin anguwarmu zuwa sayayyar kayan ɗinki a wajensa. Sai mahaifiyata da ke saida kayan kuka, kuɓewa busashshe, kayan ƙamshi harda daddawa domin kare mana mutunci itama. Gidan da muke gidan hayane mai ɗauke da ɗakuna kusan arba'in, dan irin dogon gidannan ne da akan jeranta ɗakuna reras da ga farkon baranda zuwa ƙarshe tamkar gidan karuwai, ba wani faɗine da gidan ba, amma kowa iyakar mu'amularsa a ƙofar ɗakinsa ne da bazata gaza taku goma ba, babban kicinne guda ɗaya a gidanmu dake a farkon shigowa gidan wanda ya gama cuɗewar baƙi saboda mafi yawancinmu girkin icce mukeyi, masu arziƙin cikinmu ne keda lasisin dahuwar abinci saman gawayi, can da ga ƙarshen gidan kuwa banɗakine guda biyu, na kashi da wanka, wanda suka ɗaine duk yawan mutanen gidan ke shiga, shiyyasa mafi yawanmu zaki samu kowa da fo ɗinsa na kashi a ɗaki ko ƙaramin botikin fenti, da safe idan bakai azamar tashi kai wanka ba to fa ka tabbata ƙila sai dare ko goshin magriba zaka samu damar yinsa, shiyyasa da yawanmu mukan jera kwana biyu babu wanka.
Tunda na taso a gidan na ganmu, hakama mafi yawan waɗanda suke gidan haka na tashi na gansu, dan har takai mun wuce ƴan zaman haya sai dai ƴan uwa. mahaifina da mahaifiyata duk haifaffun garinne, kuma dukkan danginsu suna ciki suna rayuwa, hasalima akwai masu arziƙi a ciki. Sai dai kowa yasan halin zuciya irin ta wannan zamanin, inhar baka da shi to kaida banza duk ɗaya kuke, kai tsaye ma ake mantawa da kai a cikin dangi. To ballema irin iyayena da suka kasance n
akasassu, inhar za'a iya mantawa da mai ƙafafu da hannu da idanu saboda talauci ya masa katutu ta yaya kake tunanin ba za'a manta da musakan iyayena da bayan rauni da ALLAH ya jarabcesu da shi na halittar jiki harda talauci ba?. Ni kaɗai iyayena suka haifa a duniya, nima an jima ba'a sameninba, sai da ga baya ALLAH ya azurtasu da samuna matsayin ƴa ɗaya tilo a garesu, duk da talaucin iyayena da kasantuwarsu nakasassu ni ƴar gatace, dan gwargwadon iko iyayena tsaye suke a kan bani tarbiya, nakanje makarantar gwamnati kamar yanda sauran ƴaƴan gidanmu ke zuwa, hakama ina zuwa islamiyya. Sai dai aduk lokacin da aka buƙaci wani abu da ga makaranta da yafi ƙarfin ƙarfinmu hankalin iyayena kan tashi da ni kaina, wannan yasa da yawan lokuta karatun nawa ke kwan gaba kwan baya, dan kuwa ƴan ajinmu sunsha tsallakewa gaba su banni da maimaita aji saboda rashin kuɗin abu idan an buƙata tamkar ba makarantar gwamnati ba. Badan bani da ƙoƙari bane, a wannan ɓangaren ma ina sahun farko na gwarzayen yara masu ƙwaƙwalwar karatu da fahimtarsa, sai dai rashin kuɗi ke daƙileni a kulum..........................
Tunda Bilkisu ta fara bama Jay labarin rayuwarta idanu kawai ya kafeta dashi ko ƙyaftawa bayayi, ko sau ɗaya bai katseta ba har saida takai aya, fuskarta shaɓe-shaɓe da haye ta juyo tana kallonsa. “Wannan itace asalin Bilkisu da take gabanka, mai rawa da bazar Dad, badan shi ba babu mai sanin wannan BILKEESUN bare ya bibiyi tarihinta, Yah Jawaad, bazan bijirema aurenkaba, dan har yanzun bansan asalin ƙullashi ba, sai dai kasani rashin auren Yah Qaseem tamkar butulcine daga alkairan Dad a gareni, ya ɗaukeni a lokacin da kowa ke ƙyamata, ya mini gata a lokacinda masu gata ke gudun raɓata, ya tsaftace rayuwata a lokacin da datti mai ciwo ke lulluɓe da ita, shin baka ganin ya cancanci fiye da auren jininsa a gareni koda kuwa matarsa bata ƙaunata?”.
Jawaad dake kallonta idanu jazur ya ɗauke kansa daga gareta a karo na farko, murya a dakushe yace, “Bazan musa miki cancantar Dad da abinda yafima haka daga garekiba, sai dai ni Jawaad Abdul-Aziz Yusif nace bai cancanci samun sadaukarwar komai daga gareki ba”.
Sosai nai masifar waro idanu ina ture bargon da naketa faman rufe jikina dashi da, nama manta boss ne a gabana, dan haka cikin zafin rai nace, “Kai wanene da kake tunin Dad bai cancantaba? Yaushe ka sanni harda zaka iya aza mizanin cancantarsa da kalaman son sakamin shakku da baƙantasa a gareni, y.......”
“Yah isheki!!”. Ya faɗa cikin daka tsawa yana ɗaga hannu tamkar zai makeni. Baya nai da sauri ina mai rumtse idanu dan nama sadaƙar mazgenu zaiyi.
Jawaad ya rintse hannun da yakai zai maketa yana lumshe idanunsa tare da danne lip ɗinsa na ƙasa da haƙori tamkar zai hudashi, kusan sakan ashirin suna a haka kafin shi ya fara buɗe nasa idon da hannun yaja goran ruwa dake bed side drawer yasha, ahankali abinda ya tokare masa maƙoshi ya faɗa, ya maida jikinsa ya jingina da gadon yana ƙoƙarin dai-daita nutsuwarsa.
Nima jin bai makeninba yasa na buɗe idanuna, karan farko a rayuwata da nakejin zafinsa, miyasa yakeson aibantamin Dad ɗina bayan shine yaymin gatan da har shiɗin ya shiga cikin jerin masu sanina....?
Jay daya ji ƴar nutsuwa tazo masa ya sauke numfashi daɗan ƙarfi, batare da ya juyo ga bily ba yace, “Ina su Firdausi da iyayenta?”. Kamar bazan tanka masaba sai dai nace, “Tun randa na baro gidan bayan kwaɗama Jazuga abu ban sake waiwayarsa ba saboda inajin tsoro, Nima babban burina a yanzu sanin halin da suke ciki, musamman dana yawaita mafarkinsu a kwanakinan”.
“Miya hanaki waiwayarsu bayan lafawar abubuwa?”.
Kallonsa nai da mamaki, nace, “Taya za'ai batun kisan kai ya iya lafawa? Kasheshifa nayi da wannan hanun nawa”. Nai maganar ina mai fashewa da kuka da nuna masa hanun nawa.
Murmushi naga yayi, dukda dagani kasan na takaicine hakan bai hanani jin ciwoba. Ya juyo sosai yana kallon hannuna da nake nuna masa, sai kuma ya ɗauke kansa. “Wace anguwa su Uwargida suke?”.
“Harna baro gidan bansan anguwarba nima”. Baice komaiba ya sauka daga gadon,
saurin ɗauke idona nai daga garesa ganin gajeren wandone a jikinsa wanda iyakarsa rabin cinyarsa. Bai sake cemin komaiba tsahon lokaci yanata safa da marwa a ɗakin, nidai gittawarsa kawai nake iya hangowa ban yarda na ɗago na sake kallonsa ba. Yazo gabana ya tsaya, hakan yasani ɗagowa na kallesa a tsorace, “Wa bincikenki ya nuna yayma Amina fyaɗe?”. Wani irin muguwar bugawa ƙirjina yayi akan wannan tambaya batare da nasan dalilin hakanba, maimakon na bashi amsa sai kawai na fashe da kuka.
Tsura mata idanu kawai Jay yayi cike da mamaki? Yanzufa ta bashi labarin komai tiryan-tiryan, amma ya mata tambaya ta saka masa kuka. A dake yace, “Qaseem ne?”. Kasa bashi amsa nai saboda wani irin juyawa da kaina keyi tamkar ana bugamin guduma, da sauri nakai hannu biyu na riƙesa ina faɗin, “Ya ALLAH kaina”.
Babu shiri Jawaad ya durƙusa a gaban gadon ya tarota ganin zata faɗi, saurin kwantar da ita yay ya kama kan ya riƙe cikin hannunsa yana janye nata hannun, addu'a ya shiga yimata jin kan ya ɗauki wani mugun zafi maiban mamaki, ga jikinta ya ɗauki wani irin rawa. Cikin matuƙar sarƙewar halshe take faɗin, “Kamin addu'a, kamin addu'a dan ALLAH, kaina zai fashe, wayyo kaina”.
Tsahon lokaci yana mata addu'a har tai shiru, jikinma ya daina rawar da yakeyi, bai dainaba cigaba yay da mata har saida yaji zafin kan ya ragu sosai barci ya ɗauketa kafin ya miƙe, alwala yaje ya ɗauro yazo ya saka dogon wando ya kabbara salla.
Kusan ƙarfe uku da rabn ta farka, nama manta a ina nake sai dana gansa a zaune da alkur'ani a hannu sannan na tuna. Yunƙurawa nai na tashi da ƙyar dan jikinna kam ciwo yake min, nima alwalar na ɗauro nazo bayansa na saka wani abin sallar na tada.
Jay duk yanajin motsinta, sai dai baiyi maganaba saboda karatun da yakeyi.
UBANGIJI mai rahama da jinƙai sai ya bama Bilkisu da Jawaad damar raya wannan dare da ibada har akai kiran sallar asubahi.
★★★★★★★
Tunkafin ya dawo sallar asuba na gyara ɗakin na wanke har toilet, ina cikin gyaran falon saman ya shigo, dauriya kawai nakeyi dan wani irin barci nakeji fiye da zato, batare dana kallesa ba nace, “Ina kwana”. “Lafiya, waya saki wannan aikin?”. Kaina a ƙasa har yanzu nace, “Babu kowa”. Gaba yay yana faɗin, “Ki barsa iya nan kizo ki shirya na ajiyeki inada ayyuka da yawa yau”. ban iya cewa komaiba harya shige, dubana na maida ga agogon falon, ƙarfe shida da minti talatin da huɗu. Ƙarasa mopping ɗin nayi da sauri-sauri.
Yanda tai gyaran gadon sai ya kasa daina kallonsa, da ƙyar ya iya ɗauke idanunsa, abu ya ɗauka ya fita daga sashen gaba ɗaya yana jaddadama Bilkisu tai wanka kafin ya dawo.
Kayan sharan naje na ajiye na nufi ɗakin, a gaggauce nai wankan dan banason yazo ya iskeni, babban tawul da yafi kowanne girma na ɗauro na maida hijjabi jikina na fito, ina isa gaban mirror yana shigowa da sallama, ALLAH ya soni ban cire hijjabinba, na amsa masa kaina a ƙasa. Ledar hannunsa kawai ya ajiye saman gado ya nufi toilet yana faɗin, “Ga kayan da zaki sakanan”.
Sauri-sauri na shirya cikin doguwar rigar dake cikin ledar ruwan sararin samaniya, sai sabon hijjab har ƙasa fari tamkar wata matar liman, na fita dan bana fatan ya fito ya samini a ɗakin.
___________________
Misalin ƙarfe bakwai da mintuna arba'in Bilkisu da Jawaad suka fito daga sashensa.
Addu'a naketayi a raina ALLAH yasa karmu haɗu da kowa, ALLAH kuwa ya amsa min ma muna fitowa ashe motar da zamu fita na a kusa. Da kansa ya buɗemin na shiga, sannan ya maida ya rufe ya zagaya mazaunin driver. Bazan ɓoye mukuba banason tuƙinsa, dan na kula ya iya zuga gudun tsiya a hanya. To amma babu yanda na iya.
Haka muka tafi babu mai cema wani uffan a cikinmu, sai dai naji daɗi sosai yanda naga mun nufi masarauta kai tsaye. Yauma kamar ranar a ƙofar farko ya tsaya, waya ya ɗauka yay kira. bayan ya ajiye wayar ya juyo yana kallona.
“Ya sunan anguwar da kuka zauna?”. kaina a ƙasa nace, “Bankaura”. “Zaki zauna a gida yau sai gobe idan ALLAH ya kaimu zaki koma aiki, ki dage da addu'a, kina dai ganin duk abinda ke faruwa”.
Kaina na jinjina masa nace, “Insha ALLAH, amma dan ALLAH miyasa jiya kace ban cancanci nai sadaukarwa ga Dad ba?”.
Shiru kamar bazai tankaba, kusan sakan biyar sannan ya juyo yana kallona, “Lokaci zai nuna mana komai, babu abinda zaki iya fahimta a yanzu sai ruɗani, kije idan lokaci yay zaki sani”. Kafin nace wani abu su Amaturrahman da Amintacciyar baiwar gimbiya sun fito a mota. Gaishesa sukai cikin girmamawa, ya amsa shima fuska aɗan sake yana faɗin, “Kucema Ummu ga amanarta nan ban ciba”. Dariya Amintacciyar baiwar gimbiya tayi tana faɗin, “Jiya kam ai tayi faɗa tamkar ta ari baki anƙi maido mata ƴarta”. Murmushi Jay yayi kawai yana ɗan kallon gefen da Bily take suna magana da Amaturrahman kafin ya ɗauke kansa.
Sallama yay mana ya tafi, Muna shiga daga ni har Amaturrahman barci muka kwanta dan shi nakeji fiye da komai a yanzun.
__________________________
Jay yana ajiye Bilkisu Office ya nufa, ayyukane fal kansa har baisan da ina zai faraba, yana zama abinda ya farayi shine bige-bigen waya, a kiran farko Umarni ya bada a nemo masa gidan da Bilkisu ta sanar masa sun zauna da iyayenta a Anguwar Bankaura, tare da ainahin maigidan da halin da gidan yake ciki yanzun. Kira na biyu kuwa Ainahin gidansu Baba makaho inda aka haufesa yasa a binciko masa shikuma a Anguwar Tudin Jarƙasa.
Sunyi zaman awa biyu shida su Aliyu, duk da yaga ɗacin ran da Rose takeyi baibi takanta ba, bayan sun kammala ta buƙaci yin magana dashi, ca yay mata bashi da lokaci yanzun kam saita bari wani lokacin. Cike da takaici ta riga kowa fita. Haka ya cigaba da rage akainin gabansa.
Misalin sha biyu yabar station zuwa Barrack ɗin sojoji da suka fara zuwa jiya kafin su tai jejin nan, ya samu ganawa da Lieutenant General a tsaitsaye dan ya iskesa yana shirin fita, ya sanarmasa wajen baba ƙaura yazo. Lieut G ya saka wani soja yayma Jay rakkiya har gidan da baba ƙaura yake zaune a cikin Barrack ɗin.
Baba ƙaura ya tarbi Jay da murmushinsa mai tsayawa mutum a rai, bayan sun gaisa ya sake yima Jawaad ta'aziyya. Jawaad yay masa godiya akan gudunmawar da ya basu jiya. Fuska ɗauke da murmushi baba ƙaura yace, “Yaro bani nayiba ALLAH ne yayi”. “Hakane baba” Jawaad ya faɗa cikin sake tabbatarwa. shiru suka ɗanyi na wasu sakanni, baba ƙaura yace, “Mike tafe da kai?”. Ɗagowa Jay yay ya kallesa da ƙyau, ya tsufa sosai sai dai yana tare da ƙarfinsa, bashi da tsaho sosai sannan shiba wada bane, ya risinar da idanunsa yana faɗin, “Maganganunka na jiya baba na kwana juyasu a rai, sai dai har safiyar yau ban iya samo amsar ko guda ba, baba mika sani a kanmu?”. Murmushi baba ƙaura yay idonsa akan Jawaad, yace, “Yaro bansan komai a kanku ba, hasalima jiya na fara ganinku a iya tsahon rayuwata, kowane irin mutum a duniya yanada baiwarsa, ni tawa baiwar kenan, fahimtar wasu abubuwa daga mutane, akwai mutane masu irin wannan baiwar tawa da yawa a duniya, sai dai mafi yawansu sunfi zaɓar aikata saɓon ALLAH da tasu damar, sai kaga mutum ya zama ɗan tsubbu ko naɗama kansa wani girman da zai halakar da mutane daga barin ALLAH, ko ya maida baiwar tasa ga zalunci da neman duniya. wlhy kaji na rantse maka bansan komai daya shafekuba face abinda UBANGIJI ya bama idanuna ikon gani tattare daku jiya.....”
Cikin jinjina al'amarin baba ƙaura Jay yace, “baba ko zamu iya sanin abinda ka fahimta ɗin?”
Murmushi Baba yay da faɗin, “Yaro minene sunanka?”. Jay yace, “Jawaad”. “Masha ALLAH, malam Jawaad bawani abune na gani a rayuwar kuba, domin kuwa ƙaddarar da duk ke cikin rayuwar kowanne ɗan adam wannan ɓoyayyen sirrine daga taskar ALLAH, abinda ALLAH ya bani ikon gani tattare daku kawai shine rayuwarku na ɗaure da wani al'amari mai girma, sannan kunada taurari masu ƙarfin haske da suka hana duhun dake zagaye daku tasiri, dan har na waccan yarinyar sunfi nakama haske, abinda nazarina ya bani bayan faruwar abubuwa a dajin nan shine akwai sihiri mai ƙarfin gaske jingine da jininku, su wanene sukai muku? Miye dalili? Saboda mi? Daga yaushe ne? Shine ban saniba sai abunda ALLAH yasio sanar daku nan gaba”.
Cikin ɗaurewar kai Jawaad yace, “Amma miyasa kanema sanin sunan mahaifinta?”. “Saboda duhun dana gani biye da bayanta yafi naka rintsi”. “Duhu kuma baba?”. “Ƙwarai duhu ɗana, amma da sannu zai yaye insha ALLAHU bisa rahamar ALLAH, shawarar dazan baku shine ku dage da addu'a da sadaka musamman a cikin wannan watan mai albarka na Ramadhan da zamu shiga nanda kwanaki uku idan munada rabon kaiwa. Kunika ciyar da bayin ALLAH fiye da yanda kukeyi a baya, ku saka dubunnan marayu farin ciki fiye da yanda kukeyi a baya, ku kaima UBANGIJI kukanku fiye da yanda kukeyi a baya, sannan a daren jiya naga wani haske dake nesa da kai na tunkaroka, sai dai yana nesa dakaine, bansan tayaya zakaje garesaba koshi yazo gareka”. Da sauri Jay ya kalli baba ƙaura, “Baba ko hakan nada nasaba da mafarkin da nake mai sarƙaƙiya?”. “ALLAH kaɗai yasan gaibu Jawaad, amma tun yaushe ka fara mafarkin?”. Jimmm Jay yay alamar tunanin, yace, “Baba idan har ban mantaba na farayinsa a daren da muka dawo daga wata horaswa daga ƙasar America ne, shekara kusa ɗaya kenan, sai da danayi sau ɗaya ban sakeba sai a watanan nan naketa maimaitawa, bayan ɗaurin aurena da ita sai kuma ya canja salo”. “Ikon ALLAH,to shidai mafarki sirrine yaro, sannan akwai abinda yake ishara daga UBANGIJI a cikinsa, akwai wanda shaiɗanu ke jinginuwa a cikinsa, akwai wanda keda alaƙa da saka abu a rai, to amma kozan iya jin wani abu daga mafarkinka?”. Babu musu Jay ya faɗa masa na farko da wanda yay a ƙarshe washe garin ɗaurin aurensa da Bilkisu bayan sallar la'asar. Baba ƙaura ya daɗe baice komaiba, yanata juya abun a ransa amma bai samu wani hasken da yake buƙataba, ya ɗago ido ya zubama Jay na tsahon lokaci kafin ya janye, “Alƙar jini a cikin jini yanada nasaba da kamar kun haɗa jini kenan nidai a nawa ɗan sanin da UBANGIJI ya banifa, amma sanin gaibu sai ALLAH”. Sam Jawaad bai fahimci komai daga kalaman baba ƙauraba, dan a iya saninsa babu ta inda yakeda dangantaka da Bilkisu sai ta wajen su Hudah..... Baba ƙaura ya katse masa tunani da cewar, “Sarƙaƙiyar dake ɗaure da rayuwarku tanada nasaba da wani zalincin mai tushe daga wasu jininku, UBANGIJI shikaɗai yasan sirrin dake ɓoye dai, amma a mafarkinka mutum kake gani yana sanar dakai kokuwa?”.
“Da farko dai bana ganin kowa, amma daga bayan nan mace nake gani, gashi na santa a mafarkin, sai dai dana tashi fuskarta saita ɓacemin, duk iya hasashena bana tunota”.
“To UBANGIJI shi kaɗai yasan dalilin sirranta maka ita a zahirin taswurar zuciya, kuje kucigaba da addu'a, ALLAH bai manta da al'amarinku ba. Ga wannan gadalin (maganin), karkaji komai sanine daga abinda ALLAH ya sanar dani nima, saboda bibiyarta da ake ana tsoratar da ita dalilin abinda ke hannunta nasu ALLAH bazai basu damaba insha ALLAH, a zubashi a Abu mai tsafta, a karanta Ayatul kursiyyu (itace aya ta 255 a suratul baƙara), suratul Yunus aya ta 79~82, Suratul Ɗaha aya ta 65~70, Suratul Kafirun, Al-Ikhlas, Al-Falaq, An-Nas, a tofa ciki, A shafe jiki da shi akuma ringa sha safe da yamma, sannan ai turare da wannan. Insha ALLAHU duk wani baƙin aljani da aka haɗata dashi zai gusa, zaku samu haske mai yawa akan al'amarin cikin amincin ALLAH, sihirin dake jikinku zai warware da izinin UBANGIJIN al'arshi.
Ada Jawaad ya tsani irin waɗanan abubuwan, amma jin baba ƙaura ya ambata harda ayoyin ALLAH saiya amsa yay godiya, sunɗan ƙara tattaunawa yay masa sallama ya tafi.
Daga Barrack ɗinan tasha ya nufa inda gimba ke hawa motar garinsu idan zaije gida weekend.................✍
😉🤫👍🏻😘.
ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.
SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.
HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO
MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.
MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.
BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....
abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya
500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.
Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899
sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.
Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300
Sai kunzo😍😍😍😘.
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
ƘWAI cikin ƘAYA!!
Bilyn Abdull ce🤙🏻
BOOK TWO
Page 33
...............A ɓangaren gidan Dad komai ya ƙara caƙuɗewa, yakasa barin ƙasar koda kuwa zuwa Niger ne, komai Shahudah batayi yanzu banda aikin kuka da kiran Jawaad, ta tabbatar musu indai basu rabata da Habib sun maidata gidan Jawaad ba saita kashe kanta, kullum cikin lallaɓata suke da mata alƙawarin samun Jawaad duk rintsi kuma har ƙarshen rayuwa, zakuma su rabashi da bily koda tsiya dan ita kaɗai ta mallakesa, acewarsu tabari ya gama hayaƙin rashin mutuncinsa yanzun sunada hanyar maganinsa ne.
Qaseem kan tun bayan barin Jay asibiti da Bilkisu ya shiga wankama Doctor mari akan ya buɗe masa ƙofa, cikin gigitar azaba Doctor ya buɗemasa ƙofar ya fita, koda ya fito sai bai iske su Jawaad ba, cike da mahaukacin gudu ya ɗauka motarsa ya fice daga asibitin. Marukan da yayma Doctor ne yasaka sauran Doctors ɗin asibitin alwashin ɗaukar mataki, atake suka kira police, ko jinin dake fita ta hancin Doctor basu tsaida masaba saida ƴan-sandan sukazo suka gani.
Qaseem daya fita yana can yana bilayin neman su Jawaad titi-titi bayan yaje gidansu ance Jay baizo nanba, ya nufi gidan Jay na A.Y street ne ƴan-sandan da aka tura kamashi da yawun hukumar lafiya ta ƙasa sukai ram dashi, duk yanda yaso musu taurin kai da nuna musu shiɗin wanene ɗan wanene sunƙi saurarensa. Dan kuwa dai shima Doctor ɗin da ya mara ɗan wani ƙusane a ƙasar, gashi ma'aikaci a asibitin gwamnati, shiyyasa kamun Qaseem ya taho tun daga sama.
Yau tsahon kwanakin Qaseem biyu kenan a police station batare dasu Dad sunma saniba, su duk tunaninsu Qaseem na gidansa ne tunda fushi yake dasu bazasu ganshi a yanzuba.
Salman ma dai daƙyar suka lallashesa ya haƙura da batun barin ƙasar, dan yacefa shi lokacin mutuwarsa baiyiba da zai tsaya ɗan-fir'auna ya sakashi cikin jerin waɗanda zai watandarsu kamar kajin salla, da farko Mom masifa ta fara masa, da dai taga babu ci sai ta koma lallaɓashi har Dad ɗinma, da ƙyar ya haƙura akan shifa da yaga wani motsi zai ware abinsa, da wannan ajandar tasa suka yarda, ba komai yasa basason yay nesa dasuba sai sanin halinsa musamman akan shaye-shaye, shiyyasa basason yay nesa dasu, ALLAH dai yasosu abin bai nisaba suka tsaya kansa ya haƙura.
Momy dake haɗama Dad tea takai dubanta garesa, yay shiru tamkar babushi a d/table ɗin, gaba ɗaya rikicewar da gidan yayi yasa sun fita hayyacinsu daga ita harshi, wani irin jin ƙarin tsanar Bilkisu tai a ranta, dan kuwa a ganinta duk itace sanadin komai, shigowarta rayuwarsu ne ya tarwatsa musu gida, da Dad bai jajubo musu itaba da yanzu suna zaune cikin kwanciyar hankalinsu, siririn tsaki taja tana mai dangwarar masa da kofin tea ɗin gabansa. Kallonta yay da mamaki, yace, “Lafiya kike tsaki? Bayan kinsan abinda nafi tsana kenan a rayuwata?”.
Momy ta kuma jan wani tsakin tana cigaba da zuba masa farfesun bindin sa ɗin da takeyi, “Bakai nakema tsakiba nikan Dadynsu, sanadin tarwatsewar gidana na tuna, lokacin da zaka ɗako yarinyarnan dana nuna ɓacin raina fushi kaitayi dani, ka ringa nunamin batada maraba da ƴaƴanmu jininmu a wajenka, gashi kaga sakamakon daya biyo baya ai, ka ɗakkota daga inuwa ita ta turamu rana, ranarma mafi munin zafi da ƙuna, nikam dai wannan zuminci naku ai ALLAH ya tsine mar (Wa'iyazubillah, Mom zuminci ya wuce tsinuwa, dan yana ɗaya daga cikin hanyoyin shiga aljannah🙄).
Dad yace, “Humm, wlhy kuma kingafa Aysha duk da wannan abun daya faru sai ban daina jinta a rainaba, a ganina yarinyarnan bata da laifi akan rikicinan, daga gidanku aka harɗa komai, kekuma gashi bakison laifin danginki sai nawane sakarkaru ko?!”. Yanda yay maganar da zafi-zafi ya saka Momy kallonsa da mamaki fuska a yatsine tace, “Ikon ALLAH, kaifa nagama sammun yarinyarnan yafi cinka fiye da kowa a gidannan kai da wannan shashashan Qaseem, to wlhy inma ban ɗauki matakin ƙarshe akan yarinyarnanba kuce ba sunana Aysha Humaira ba Mtsowww!!” ta ƙare maganar da buge table ɗin ta tashi tabar wajen.
Duk wannan abu dake faruwafa tsakanin Dad da Mom Shahudah da Aamilah na zaune a D/table ɗin suma, Aamilah dai earpiece ne a kunnenta tanajin waƙa, shiyyasa batasan mi tsoffin nata je tattaunawa ba, Shahudah kam cikin damuwa take mai gusar da hankali, zuciyarta gaba ɗaya tana ga Jawaad da tunanin ina Bilkisu?, dan a yanzu dai wannan matsalar tafi cin zuciyarta fiye da komai, ɗan-fir'auna tasan ko kotune Dad sai ya kaisa ya saketa, inmafa bai saketanba ita ahaka zatai aurenta tunda ai bada soyayya tsakaninsu aka ɗauraba, a ganinta tunda babu soyayya ai auren bai ɗauruba kenan (Hudah Kai a tukunya😖😂 lol).
Buga table ɗin da Mom tayine ya maido hankalinsu kansu, duk suka bita da kallo kafin su kalli Dad da shima kallon Momyn nasu yake rai a matuƙar ɓace.
Aamilah dai baki ta taɓe ta cigaba da sauraren waƙarta dacin abinci, Shahudah ce dai ta kalli Dad ɗin bayan ɓacewar Mom a idanunsu. “Dad wai faɗa kukeyi ne?”. Huda tai maganar tana mai tsatstsare Dad da manyan idanunta da suka koma ƙanana a yanzun saboda tsabar yawan kuka. Kansa ya girgiza mata yaja bowl ɗin data saka masa farfesun ya fara shan romon kawai dan kauda hankalin Shahudah daga abinda take zargin.
___________________________________
Jawaad kam daga wajen baba ƙaura tashar da Gimba ke shiga mota idan zai tafi gida ya nufa. Wajen bawani babban tsasha baneba, dan motocin garin su Gimban ne kawai sai masu ƙarisawa cikin ƙauyikan dake maƙwaftaka dasu. Kowa na sabgar gabansa daga masu talla har matafiya da masu sauka, sai ƴan mashinan Napep dake ɗaukar masu shiga cikin gari idan an saukesu a tashar. Sai da ya gama ƙarema wajen kallo daga cikin motarsa kafin ya ɗauki glasess ɗinsa baƙi ya toshe idanunsa dashi, baya wani cikin mood ɗin farin ciki, hakan yasa sam fuskar babu alamun sauƙi balle rangwame. Tamkar zakin dake taƙama bayan yaci ya ƙoshi haka ya fito daga motar, dama tun fakawarsa mafi yawan jama'ar dake kai kawo a wajen suka zubama motar ido da tsumayen waye zai fito daga cikinta, dan kuwa dai taci ta ƙoshi ita kanta motar balle kuma mamallakinta a ganinsu dole ya zama abin kallo. Yako zama abin kallon dan shi kansa saida ya takura dajin yanda idanu ke yawo a kansa har jinin jikinsa na tsitstsinkewa. Guntun tsaki yay yana sake ɗaure fuska, ya fara taku a hankali yana tunkarosu kansa tsaye.
Tuni da masu kallon nasa da masu gulma suka nutsu, aka shiga gaishesa da tambayarsa ko akwai abinda yake buƙata?. Ta cikin glasess ɗinsa yake ƙare musu kallo ɗai-ɗai, sukam sam basa ganin idanun nasa, sai ƙyawun da glass ɗin yayma fuskarsa ba ƙaramin ɗaukar hankalinsu yayba. Jawaad ya shiga ƙarema saurayin dake gabansa tamkar zai duƙa kallo, nuni yay masa da hannu alamar ya miƙe da ƙyau. Babu musu kuwa ya miƙe. “Inason ganin shugaban wajen nan naku ne”. Jay yay maganar yana maida hannunsa guda cikin aljihun wandonsa. Kafinma saurayin yace wani abu wani dattijo da kallo ɗaya zakai masa ka fahimci wahalace ba tsufaba ya ƙaraso wajen yana mai amsa maganar Jay data shiga kunnensa. “Gani nan Alhaji, barka da zuwa, naɗan zagayane kama ruwa shiyyasa”.
Shi dai jay kallonsa kawai yake harya dasa aya. Dattijon ya kuma faɗin, “Muje daga cikin runfa Alhaji nan kaga rana na dukanka”. Babu musu Jay ya bisa suka shiga rumfar da ƙuda keta faman bi saboda sanyinta, ga robobin abinci da sukaci harda na fura duk ƙudan ya baibaye, gefe kuma masu saida abincinne ƴammata da yara ƙanana abin gwanin ban tausayi. Shi kallonsu yake da tausayawa sukuma suna kallonsa da birgewa da sha'awa. Duk da Jay yaji ƙyanƙyamin tebiran dake wajen matsayin abun zama haka yay shirin zaunawa akai da farin wandonsa tas daketa ɗaukar ido. Da sauri dattijon nan ya dakatar dashi, abin sallar dake can kan babbar tabarma shimfiɗe ya ɗakko bayan ya bugata ƙura ta tashi, yazo ya saka masa kan bench ɗin. Jay baice komaiba ya zauna duk da itama dai sallayan sai a hankali.
Dattijo yace, “Alhaji bara a kawo maka ruwa ko fura”. Da sauri Jay yace, “A'a nagode karka damu, tambaya nazo yi”. Dattijo yace, “ALLAH yasa na sani to Alhaji. Jay yaɗan gyara zamansa, idanunsa dake cikin glass kafe akan Dattijo, yace, “Akwai wani yaro saurayi da bazai wuce shekaru talatin da ɗaya ba mai suna Gimba, duk ƙarshen mako yake zuwa nan ya shiga mota ko kun sanshi?”. Cike da jimami Dattijo yace, “Tabbas munsan Gimba, ai a wajenan kaf Alhaji babu wani driver da zai ce maka baisan marigayiba, danshi mutum ne na mutane ga barkwanci ga alkairi”. Jay Cikin nuna alamun kamar bai sani gimban ba yace, “Naji kace marigayi; kana nufin ya rasu ne?”. Zama Dattijo ya gyara yana matsar ƴan ƙwalla, “Alhaji ashe bakasan ya rasuba? Ai jiya-jiya akai zana'idarsa ma, muma yau labari yake zuwa mana akan duk yanda abun ya faru, ance ogansa da yakema aikine yajasa cikin ƙungiyar asiri, dama anata ƙananun magana akan yanda Gimban kema mutane ɓarin abin arziƙi a garin musamman a irin wannan watan na Ramadhan dazai kama, to dai kasan mutanenmu da kwaɗayi, dukda anajin tsoro dai haka ake amsa a lashe, sai ya gusa kaji anayi dashi, saifa yanzunne da suka tsotse jinsa zance keta fitowa abubuwa gasu nandai barkatai babu daɗin ji”. Tunda Dattijo ya fara magana jikin Jay ke wani yaamm na mamaki, haka kuma aka maida zancen rasuwar gimban ahi baida labari?, kai ɗan adam sai dai ka gansa ka barsa da halinsa kawai, baiji komai a ransaba tunda yasan ba hakan bane, abinda kawai ya ɗauka jahilci ne ke aiki cikin ƙwaƙwalen kansu. Ya gyara zamansa cike da ƙwarewa cikin salon aiki yace, “Ai nima akan batun mai gidan nasa nazo daman, yanzu haka mun kamashi a hannu bincike mukeyi, idan ka bamu haɗinkai kaima kanada naira dubu hamsin sabbi ƙar a takarda. Jimm Dattijo yayi yana ninƙaya a nazari, mikuma ya tuna sai ya kalli Jay yace, “Nikuwa mina sani akan wannan zance Alhaji?”. A karan farkio Jay yay murmushi, “Ba canai ka saniba daman ai, sonake dai naji abinda ka sani ɗin, ranar juma'a Gimba yazo tashar nan taku?”. Dattijo yace, “Eh to kamar dai yazo”. Jay daketa dannewa bayason ya tsoratashi yace, “Banason ƙwana-ƙwana a magana, ka fitomin a mutum mu wanye lafiya”. Ya ƙare maganar da zare glass ɗin idonsa sukai ido huɗu da Dattijo. Sosai kwarjinin Jawaad ya sake cikama Dattijo idanu dama wajen baki ɗaya. kasa jurar kallon idon da Jay ke masa yayi ya duƙar da kansa. Jawaad yay wani munafukin murmushi yana ɗauke kansa shima, “Yaya zan samu amsar gaskiya?”. Kai Dattijo ya ɗaga batare da ya yarda ya sake kallon Jay ɗinba. “Tabbas yazo nan ranar juma'a nayan an sakko masallaci”. “A motar wa ya tafi gida?”. “Bai shiga motar kowaba ranar a tashar nan”. Cikin ƴar fusata Jay yace, “To motar wa ya shiga?!”. “Ni...ni bansanshi ba Alhaji”. Murmushi Jay ya sakeyi irin na zan lailaya kanka a titi ɗinan ya ɗaga jacket ɗinsa ƙaɗan yace, “Kalli nan”. Koda Dattijo ya ɗago yauy arba da bindiga sai ya waro idanu waje, kafin kace kwabo zufa ta gama jiƙesa. Jawaad yace, “Saika zaɓa, amsata ta gaskiya kokuma rasa numfashi?”. “ALLAH ya baka haƙuri oga, wlhy inada iyali da ƙananun yara a gida, abinne wuya garesa shiyyasa”. “Kai kake ganin wuyarsa”. Cewar Jay yana haɗe fuska fiye da farko. Cikin kakkausan murya yasake faɗin, “A wace mota gimba ya tafi gida ranar juma'a?”. “Tare da ɓaleru” Dattijo ya faɗa da sauri kamar zai haɗiye harshensa.
Jay ya sake zare glass ɗin idonsa a karo na biyu, sun sake kaɗawa sunyi ja da ɓacin rai, “Wanene Ɓaleru?”. Ya faɗa yana ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya da harɗe hannayensa saman ƙafar yanaɗan juya glasess ɗin hannunsa idanunsa kafe akan dattijon. Kan Dattijo a ƙasa yace, “Shima ɗan garinmu ne, zanma a iya ce maka kamar abokai suke da marigayi gimban, dan duk sa'anni ne kuma unguwarsu ma kusan ɗayane”. “Ina zan samesa yanzun?”. “Wlhy oga ban saniba, kawai dai nasan yana anan birni shima yana aikin drivernci a wani gida”. Miƙewa Jay yayi tsaye da cewar, “Koma ina yake ni zan memosa, ba'a cin kuɗina a matsayin cin hanci, amma ina biya idan na saka aiki, zan baka aiki nakuma biyaka yanzunan, ya rage naka kaimin da gaskiya kokaci amanata idan anzo an biyaka abinda yafi nawa, biyoni”.
Jiki a saɓule dattijo yabi bayan Jay har zuwa isa inda ya faka motarsa. Jawaad ya buɗe motar ya shiga ya zauna batare daya rufeba, ƙafafunsa duka a waje, takarda ya ciro da pen ya kalli Dattijo dake tsaye, “Ka iya karatu ne?”. Da sauri Dattijo yace, “Eh nayi sakandire Oga”. Jay baice komaiba ya maida kansa yay rubutu da hausa a takardan sannan ya miƙa dattijon tare da kuɗi bandir ɗin ɗari biyar. “Wannan aikin zakaimin, ga kuɗin aikinka nan”. Daga haka ya shige motar sosai ya rufe abinsa yaymata key tare dayin reverse yabar wajen.
Ganin lokacin sallar zuhur yayi sai ya tsaya yay sallah kafin ya ƙarisa station, tunkan ya shiga office ɗinsa ya samu kira daga sir Ahmad, fasa shiga nasa office ɗin yay ya nufi na Sir Ahmad ɗin. Ba'a masa iso dan zai shiga office ɗin sir Ahmad, knocking kawai yakeyi a bashi iznin shiga. Yanzunma kansa tsaye ya isa yay knocking ɗin, daga ciki sir Ahmad ya bashi izinin shiga dan yana kallonsa.
Cikin girmama ya gaishesa, Sir Ahmad ya rufe file ɗin gabansa yana kallon Jay ɗin dake zaune, “Ina ka shige hakane tun ɗazun nake aike a kiramin kai?”. “Am sorry sir na fitane”. “Okey to ya ƙarin haƙuri?”. “Alhmdllh sir”. “To ALLAH ya gafarta masa, ya raya abinda ya bari. Na kiraka ne dama akan Qaseem, wai yau kwana biyu yana hannun police”. Cike da mamaki Jay yace, “Police kuma? Basusan shiɗin wanene ba?”. Murmushi Sir Ahmad yayi yana kwantar da bayansa jikin kujera, “Sun sani sarai, gabace da gabanta, ya mari wani Doctor ne a General hospital shekaranjiya lahadi harya fidda masa jini, to Doctor ɗin ɗan Alhaji ɗan-iya warzu ne, shinefa yakai maganar hukumar lafiya ta ƙasa baki ɗaya, sukuma suka saka aka kama Qaseem ɗin”. Huci Jawaad ya furzar , shi shaf yama manta yabar Qaseem ranar a asibiti, yaso ya koma amma sai aka samu akasi, ya tabbata dalilin abinda ya faru ranarne Qaseem ya mazge Doctor, shi baisan yaushe Qaseem zai daina halin ƴan danbe ba ya rage baƙar zuciya. Yace, “Yanzu miya faru to Sir?”. Sir Ahmad yace, “I.G ne ya kirani da safen nan yake sanar min cewar shi Warzu yace sai anje kotu, shikuma yaga ɗaya daga cikin yaranane shiyyasa ya kira ya sanarmin dan anrma lauya, kuma ko babansa ma bai saniba”. Murmushi ne ya kufcema Jay, dan kuwa dai yasan lallai da Dad yaji da ba'a zauna lafiyaba, dan inma ɓakin son ƴaƴane Dad yatake Warzun ya shanye. “Miya baka dariya?” Sir Ahmad ya faɗa yana tsatstsare Jay da idanu. Kai Jawaad ya shafa yana ƙara sakin wani murmushin, “Sir abinne nasu ne ai, ni nasan Dad da yasan Qaseem na cell da yanzu garinan ya fara yawo a gajimare dan rikicinsa, kafaɗamin wane station ne? zanje na fiddosa yanzun insha ALLAH”. “To aini banƙi in baka damar cirosanba, kaima rikicin naka nake tsoro ai, dan baka da maraba da Dadyn naku, ta wani wajenma ka fisa zama ɗan ƙunar baƙin wake, nikuma banason ka haɗa harƙalla da Warzu dan shaiɗanin mutumne da kake ganinsa kullum cikin manyan kaya”. “Karka damu Sir salin alin zamu dawo”. “To shikenan gashi, saika nema lauyan Qaseem ɗin kuje tare”.
Sallama Jay yaymasa ya fita.
Bai koma office ba ya sake ficewa, harga ALLAH bazai iya jurar tuƙiba, haka yake shi baison tuƙi saita kama dole, dolene yasan mafita, to amma shikam ‘Wane driver ne zai iya maye masa gurbin Ginbansa?’ yay maganar cikin rai zuciyarsa na masa zafi. Office ɗin Jabeer ya shiga, babu jimawa suka fito tare. Jabeer ɗinne ya jasu, sai da suka fara tafiya yaɗan dubi Jay ɗin daketa faman danne-danne a tab ya ɗauke kansa ya maida ga titi “Na zatafa wajen rasuwarnan ka koma?”. Jay da bai ɗagoba bai kuma fasa abinda yakeba yace, “A'a, dama sonake sai gobe idan ALLAH ya kaimu mu koma mu duka”. “Okey ALLAH ya kaimu” cewar Jabeer yana maida hankalinsa ga tuƙin.
Asibiti suka fara zuwa wajen Doctor Ballo Warzu, cikin girmama ya tarisu yana tambayar jikin Bilkisu?, mafi yawan amsarsa Jabeer ne ya bashi ita, sai da suka gama gaishe-gaishensu sannan Jay yay masa magana akan abinda ya kawosu, da tambayar miya faru bayan tafiyarsa?. Labarin komai Dr Bello ya basu, Jay ya dafe kai cikin takaici.
Shi dai Dr Bello haka kawai komai Jay yayi ƙyau yake masa da burgesa, haka ALLAH ke sakama bawa ƙaunar wani batare da wata manufa ba, yay murmushi yana kallonsa, “Karka damu abokina na haƙura indai nine, bansan ɗan uwanka bane dana barsa tun a ranarma baza'a kai hakaba saboda kai, naga rashin hankalin nasa ne yayi yawa shiyyasa naga gara aɗau mataki, amma yanzu kam yaci darajar mai daraja”.
Fuskar Jay ɗauke da guntun murmushi yace, “Nagode Doctor ALLAH yabar zuminci”. Shima Doctor godiya yaymusu, ya kuma rakosu har inda motarsu take, sai da yaga fitarsu sannan ya koma office yana kiran babansa a waya.
★★★★★
Tunda suka shigo police station ɗin aketa basu girma, kai tsaye office ɗin d.p.o suka nufa, inda acan ɗinma dai suka tarbi juna da girmamawa kafin a ɗaura da gaisuwar mutunci. Jay da kansa yayma d.p.o bayanin abinda ya kawosa, ya kuma nuna masa lawyer'n Qaseem ɗin da ya shigo a bayansu dan shi isowarsa kenan. A take anan aka kashe magana babu zancen zuwa kotu sannan aka kawo musu Qaseem. Babu abinda akai masa, dan ko hararsa babu wanda yayi tunda aka kawosa gurin saima girmamawa, ko kayansa ba'a cire masaba, sannan ba'a haɗashi da kowaba a cell.
Kallon ido cikin ido sukaima juna shi da Jay, kowa ya ɗauke nasa fuska a tamke, Jay ya fara miƙewa ya fice abinsa, hakan yasa Qaseem jan tsaki, rai a ɓace ya kalli d.p.o yace su maidashi cikin cell ɗin. Duk kallon mamaki suke masa, Jabeer da yasan wasan ya dafa Qaseem ɗin yana magana a hankali, kamar Qaseem ɗin bazai yardaba sai kuma miya tuna oho masa ya nufi hanyar fita Jabeer da lawyer ɗinsa suka take masa baya.
A jikin mota suka iske Jay tsaye yana magana da Engineer ɗin da zai masa gyaran gidansa da Bilkisu zata zauna. Suna isowa yana ajiye wayar dan sungama. Sake ma juna kallon ido cikin ido sukai shi da Qaseem, cikin ɗacin rai Qaseem yace, “Miyasa ka cironi? Minene haɗina da kai?”. Murmushin rainin wayeo Jay yay masa yana lasar lip ɗinsa na ƙasa, yaɗan ɗage gira cike da salo dukda idanunsa na cikin glass ne, hannayensa duka cikin aljihun wandonsa suke, Yace, “Inada business da kaine shiyyasa”. Wani kallon banza Qaseem yayma Jay shima, yace, “A kasuwa ka ganni?”. Jay ya sake murmusawa tare da ciro hannunsa yaɗan sosa gefen girarsa da ɗan yatsa yana karyar da wuya, “Karkai taurin kai, akwai tagomashi mai yawa da riba”. Qaseem yaja tsaki ya motsa zaibar wajen yana faɗin, “Zanyi maganin tsagerancinka ne yaro kwanan nan”. Cike da rainin hankali Jay yace, “Ai zuru batacin zuru, sai dai a haɗu ai zuru-zuru. Nabaka nanda kwanaki bakwai kacal zaka nemeni da kuɗinka ma”. Qaseem yay wata dariyar kai banzane ya wuce motar lawyer ɗinsa batare da yabama Jay amsaba....
Jawaad yay wani lalataccen murmushi yana zare gilashin idonsa, sai da Qaseem ya shiga motar sannan ya maida glasess ɗinsa yay salute ɗin motar da faɗin, “YANZUN MUKA FARA”. (Bari na ƙarasa maka jikan Yusufa🤣. WASAN😉).
____________________________________
Ƙarfe sha biyu da wasu mintuna na farka, ni kaɗaice a ɗakin, na sauka daga gadon ina addu'a da miƙa, naji daɗin jikina sosai gaskiya, rashin barci ai masifane. Wanka na shigayi, amma abin mamaki sai nai karo da Jini, cikin mamaki nace, “Jini kuma? To duka yaushe ma nai wankan tsarki? Kofa sati biyu banyiba”. Mamaki tamkar zai kasheni nai wanka na fito. Ina shiri ina juya al'amarin cikin raina. Shigowar Amaturrahman ne ya sakani juyawa na kalleta. Tai murmushi da faɗin, “Amarya saifa wani Shining kikeyi miye sirrin ne?”. Murmushin yaƙe na mata kawai bance komaiba, itama tai dariya kaɗan, “Kefa tuni na lura irin Marwah ce, muskilanci ya muku yawa, idanma an zauna hira daku daga eh sai uhm sai a'a kuka ƙware yi, badai haka za'aje anama Yayan namu dunɗun dunkum ba kamar hadarin maraice?”. Bansan sanda na ƙyalƙyale da dariya ba babu shiri, dan harga ALLAH taban dariya musamman yanda tayi da fuska sanda zatai maganar. Ta ɗagamin gira da cewar, “Ko kefa, gashi na sakaki kin dara, ki shirya muje Ummu na jiranki, yau dai tace sai taga ƴarta”. Naji daɗi a raina, sai dai ina ɗanjin tsoro-tsoro, nice yau zan gamu da Sarauniyar gagara badau gaba ɗaya, ni Bilkisu ɗiyar baba makaho da Asiya gurguwa, ALLAH sarki duniya, duk abinda kaga ba'a gani saboda ƙanƙantarsa wataran zai fito kowa ya gansa saboda girmansa, wataran kuma sai tsufa ya sakayashi, a ƙarshe mutuwa ta ɓoyesa. Tsaf na shirya da taimakon Amaturrahman cikin siket da riga na atanfa da sukaimin ɗas a jiki, dukda dai basu kama jikina ba, duk yanda tasi hanani na saka gyale kasawa nai saida na saka sannan muka fito.................✍
Barkanmu da dawowa, ina fatan kunyi weekend cikin ƙoshin lafiya😉😘😘😍😍😍😍.
Masu kira akan zasu sayi ƘWAI CIKIN ƘAYA!! bafa shi ake tallaba, muna tallar buks ɗinmune guda goma na zafafa gasunan, duk wanda bai sayaba ya motso ya saya karya bari romon daɗi ya wucesa🤗🤗🚴🏼
ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.
SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.
HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO
MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.
MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.
BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....
abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.
Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899
sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.
Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300
Sai kunzo😍😍😍😘.
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
ƘWAI cikin ƘAYA!!
Bilyn Abdull ce🤙🏻
BOOK TWO
Page 34
...................Katafaren falone daya amsa sunansa falo, komai yaji iyakar ji fiye da tunanin mai hasashe, ga wani sassanyan ƙamshi mai kashe lakkar jiki da tsaida gudun jini na tashi, lallai wannan baiwa ta isa a kirata sarauniya, ta haɗu tama gaji da haɗuwar, ga kwarjini irin wanda kowa yasan masu mulki dashi. Tana kishingiɗe ne amintacciyar baiwarta na gefenta da alama hira sukeyi, dan fuskokinsu dukansu ɗauke suke da murmushi, sai bayi biyu kawai a falon, ɗaya na tausa mata ƙafafu ɗaya na yanka mata tufa a ƙaramin filet. Sallamarmu ta sakata maido fararen idanunta kanmu, da sauri Amaturrahman ta tareni tana faɗin, “Gaskiya Ummu sai kin biya”. Murmushi Gimbiya Munaya tayi mai ƙayatarwa, cikin nutsatstsiyar muryarta tace, “Amaturrahman kin maidani kakarki a gidannan, nakula kema auren kikeso”. Da sauri Amaturrahman ta matsa gefe tana tura baki gaba da faɗin, “Ni ALLAH banason aure ina tare dake da Abbu da Mommah”. Dariya hadiman sukayi, nima dai murmushi nike, dan saita tunomin da Nabeelah. Gimbiya Munaya dake murmushi ta miƙomin hannunta da yasha adon jan lalle, “Kinga ɗiyata manta da wannan zo naji ɗuminki kinji”. Jikina har rawa yake saboda yanda tamin tamkar mahaifiya, na taka a sannu cikin nutsuwa gareta, durƙusawa nai kaina a ƙasa, ina faɗin, “Barka da rana Ummu”. Ina jiyo fitar sautin murmushinta, ta ɗora yatsunta saman haɓata ta ɗago kaina, “Nagode da wannan girmama ɗiyata, ALLAH yay miki albarka kinji, kiyi haƙuri da rashin ganina tun zuwanki”. Murmushi na mata ina ƙasa-ƙasa da idanu, dan bazan iya kallonta kamar yanda take kallona ba, nace, “Babu komai Ummu”. Murmushi ta sake yi, tare da zaunar dani sosai, ta sallami bayinta guda biyu, daga ni sai Amintacciyar baiwarta da kuma Amaturrahman data koma can cikin kujera tana kumbura wai ance za'a mata aure. itafa ta rantse bazatai aure tabar Ummu da Abbu ba. (Kujimin ƴa, to itama munayar ai sunƙumota Galadima yay daga gabansu hajiya innaro😂).
Cikin nutsuwa da hikima Gimbiya Munaya kejan Bilkisu da hira, abin gwanin sha'awa, babu wani nuna ƙyara ko izzar mulkin kasancewarta ƙasan ƙasa da ita, haka gimbiya Munaya take, bata yarda ƙasƙantar da waniba a rayuwarta, tace tasan ciwon ƙasƙanci, bazataso yima waniba, ita tasan wahalar da zuciyarta tasha lokacin da suke ƙarƙashin mulkin mallakar Innaro a gidansu. (hajiya innaronmu ta mutumci kwanciyarki lafiya cikin ƙasa matar Faruku😂🤗, karkimin fatalwa da daddare kuma yasin😤).
Yanda Sarauniya ta iya hira har bansan sanda nake bata duk amsar data buƙata daga gareni ba, har takai munyi zurfi sosai a hirar fiye dazaton mai hasashe, kiran sallar zuhur ne ya tashemu, muka koma ɗakinmu domin yi, nidai banyi yunƙurin yiba tunda naga jini a jikina dukda dai kaina a ƙulle yake.
Muna cin abinci kira ya shigo wayar Amaturrahman, ɗaukata cike da zumuɗi tana faɗin “Meenal kun tahone?” bansan mi akace mata daga canba naji cike da murna ta sake cewa, “Wlhy da gaske nake tana nan har sai lokacin tarewarta”. Daga inda nake ina jiyo ihunsu, itama ta miƙe tana rawa da ihu. Nikam mamaki suke ban, Amaturrahman irin tsagwaron izza da mulkinan na ƴaƴan sarakuna sam batayi, ko kiga tana wulaƙanta bayi tana takasu yanda takeso, abinda kawai na fahimta tarbiyyace daga iyayensu hakan, An nuna musu bayin gidansu mutanene tamkarsu masu daraja da mutunci, shiyyasa sam basa tozartasu.
Ban tambayeta su wayeba muka cigaba da ƴar hirarmu, dukda nifa dauriya kawai nake hankalina ya rabune kashi-kashi. Ba'afi mintuna talatinba saiga ƴammatan ranar da muka taɓa haɗuwa a Saloon tare da su Amaturrahman ɗin, Meenal da Amatullah, ashe tafiya sukayi shiyyasa ban gansuba tunda nazo. Suka rungumeni cike da murna, ni harma mamaki suka bani, gasu suma da shegen kauɗi, aiko yinin yau dai kaina har ciwo yake saboda surutunsu, amma zamana dasu ya ɗeben kewa sosai, sai nake ganinsu kamar su Ummie. Muna tare Zuhrah ta kira waya, yanda sukaji muna waya da ita tana tsokanata Amatullah ɗiyar Buzaye mai cike da sirrin ƙyau ta fige wayar ta saka a hansfree kowa yanaji, a cewarta suma yanzu ai ƙawayen Zuhrah ne, duk ƙawayena sun zama nasu suma.
Abin mamaki da daddare saina nema jini na rasa, baƙaramin ɗaure kaina al'amarin ya sake yiba, ni a ƴan kwanakinnan sam bama na ganema kaina, daga wannan al'amari ya wuce sai wannan, ALLAH na gode maka da wannan jarabawa, ya rabbi ka bani ikon cinyeta, ka ƙaramin haƙuri da juriya.
(Amin Sakwara🚴🏼)
____________________________________
“Nifa wannan wasan naku dariya yake bani kaida Qaseem Boss, gashi yanzu Mami ta sake tunzura komai ya ɗau zafi, shi bazai yarda da ƙaddara bane ba?”. Murmushi Jay yayi baice komaiba, sai ƙoƙarin saka waya da yake a kunne. Daga can Abbati yay sallama. Amsawa Jay yay suka gaisa. Yace, “Ina fatan yau zaka tashi aiki da wuri dan inason ganinka, banason kuma a wuce yau saboda muhimmancin zaman”. Daga can Abbati yace, “Babu damuwa, ai kama yanka akan gaɓa, dan inason na shigo namaka ta'aziyya dama, zan shigo bayan magriba da safe sai na wuce”. Jay yace, “Kai malam nifa yanzun ƙattai sun daina kwanarmin a gida inada iyali”. Ba Abbati ba hatta da Jabeer dariya ya kwashe da ita harda ƙyaƙyƙyewa, Jay ya mangarema Jabeer kai tareda ranƙwashi mai zafi, yace, “Kaima ɗan iska na wayar zan kamaka ne, masu zuwa lahira da ido ɗai-ɗai”. Bai jira amsar abbati ba ya yanke wayarsa. Jabeer dake sosa inda Jay ya ranƙwashesa yana tuƙi yace, “Oho dai, ai sa idon namu mai lasisi ne, ni nama taɓa ganin munafukin soyayya irinka?, ALLAH zan cema sarauniya karta bar Mami ta tare har sai kazo da kanka ka furta kana SO da hawaye”. Taɓe baki Jay yayi da kwantar da kansa jikin sit ya lumshe idanunsa, a hankali yace, “Idan namata ciki a waje saiku barta ta tare ɗin, koku bari saita haihu kukaita da ƴar ko ɗan”.
Jabeer dake ƙumshe dariya yace, “Ainasan kai waliyyine bazakai hakanba”.
Shiru Jay yay tamkar bazai tankaba. Sai kuma zuwa can ya zubama Jabeer ɗin harara ya ɗauke kansa.
Kasa daurewa Jabeer yay ya kwashe da dariya yana dukan sitiyari. Jawaad yay guntun tsaki da faɗin, “Kaifa wani lokacin baka da man kai, ka isheni fa”. Jabeer dake dariya yace, “Baka da amsa yanzu, sai mun isa inda zan saida wannan jaridar tukunna”. Banza Jay yay masa bai sake magana ba, saima kansa daya sake kwantarwa jikin kujerar yay luf.
Gaba ɗaya a wannan yinin Jay yayisa cikin aiyuka, Baibar Office ba sai bayan sallar isha'i, haka ya tashi a gajiye, gida ya wuce kai tsaye dan Abbati harya kirasa ya sanar masa ya iso, ada idan zasu haɗu A.Y street suke haɗuwa, yakan daɗe bai kawo aboki family house ɗinsuba sai idan ta kama dole, to a yanzu wancan gidan a hargitse yake dan amma fidda komai na cikinsa aiki akeyi tuƙuru da sauya fasalin abubuwa.
Tare suka shigo da Abbati dake ɗauke da jikkar Jay ɗin a hannu, basu zauna falon ƙasaba saboda yay datti sosai, suka haye sama, anan yabar Abbati shikuma ya shige bedroom dan yaɗan watsa ruwa. Ya sauke idanunsa akan gadonsa ya lumshesu yana maijin wani iri, jiya iyanzu suna nan tare. Wasu abubuwan data dingayi ya tuna, babu shiri murmushi ya suɓuce masa, aransa mamaki ma yake yanda take matsoraciya ya akai ta shiga aikin nan? Bashi da mai bashi amsa dan haka ya nufi bayi, bai wani jimaba saboda yanaso su tattauna da Abbati ya kwanta da wuri, yay shiri cikin kayan barcinsa farare tas masu taushi wandon har ƙasa. Dama ya sayo musu abinda zasuci a hanya, hakan yasa yana fitowa ƙasa ya sauka ya ɗakko filets ya dawo inda Abbati ke zaune yana kallo. Sake gaisawa sukai, Abbati na juye kajin a filet Jay kuwa na daga can wajen D/table yana haɗoma kansa Shayin da shansa ya zame masa jiki yanzun, takai har idan baima shaba bayajin daɗi.
“Ni ina nawa shayin?” cewar Abbati. Hararsa Jay yayi ya ɗauke kansa ya maida ga tv, “Sai kazauna tunda ni matarkane na kawo maka”. Abbati ya miƙe yana faɗin, “Kazama matata aiban moreba Yasin, ina zani da gabjejen ƙato kamarka”. Murmushi kawai Jay yayi ban sake tankawaba, saima shayinsa da yakesha hankali kwance har Abbati shima ya dawo ɗauke da nasa.
Bayan sun sake gaisawa sukai jimamin rasuwar Gimba sosai sannan Jay ya ɗora da faɗin, “Bana babu Gimba, dama shike tsaye akan rabon kayannan na azumi Abbati, narasa wazan ɗauka yay aikinan, gashi ya kamata ace tun jiyama aka fara rabonsu kamar yanda marigayi yakeyi”. Abbati yace, “ALLAH sarki rayuwa kenan, ALLAH ya gafarta masa, lamarine na mutane sai addu'a, sam bama tsoron ALLAH, wanda ya bada baiji ƙyashiba sai kaga masu rabawa sun zama azzalumai, amma kuma wai da an tashi zagin shugabbani suma sunada bakin jefa nasu”. Jay yace, “Humm, ai Abbati ɗan adam barshi yanda ka ganshi kaji, lokacin daka bashi zuma ya lasa zai sanar maka da daɗi yama gode maka, amma da saɓanin hakan ya gitta kafi kowa muni a idonsa. Manta da wannan maganar muyi wadda ta fita muhimmanci. Yanzu dai kafinma akai ga mahanar fidda kayan, kayan abincinmu da zamu saida sunada yawane?”.
“ALLAH na tuba boss ai suma ɗin dai kamar ƙyautarne, tunda ana saida musu ne bisa farashi mai matuƙar sauƙi, duka stores ɗinmu cike suke da kayan abinci kamar kowacce shekara, idanma munada ƙarancin wani abu to manja ne gaskiya”.
“Karka damu, batun manja nayi magana da Jessica ɗazun, insha ALLAH zuwa jibi zai iso, inason linka kayan da ake rabawarne, to da nayi tunanin sayen waɗanda muke dasu a ƙasa, sai dai ɗazun kuma wani tunani yazo mani, gara mu saya hannun ƴan kasuwa, shikuma namun mu saida musu akan farashin da aka saba ɗin bisa ƙaramar riba”.
“Banƙi ta takaba Jay, amma kaima idan ka sayi namun ai zaka samu sauƙi, dan naga wannan karon abubuwan sun taso da yawa, ga maganar gyaran gida naga ka saka, hidimar aure ta wuce wasa ai”. Ɗan lumshe idanu Jay yay yace, “ALLAH zai rufa asiri Abbati, muyi hakan kawai, inason zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu a kammala siyayyar, dukda guri ya ƙure zuwa jibi sai a fidda kayan, kayanmu kuma da za'a saida yakamata kuma ku fiddasu ai”.
“Eh dama munyi dasu Labaran gobe idan ALLAH ya kaimu za'ai baja koli, shiyyasama nace zanzo na sameka yau ɗin, zan ɗauki hutun sati guda wajen aiki insha ALLAH muga an raba kayan yanda ya kamata mabuƙata sun samu”.
“Nagode sosai Abbati, nayi magana da Alhaji Garba yadi, amma Jabeer ne zai tsaya nan ɓangaren shi da su Aliyu dan aikin yamaku yawa kuma, inason wannan shekarar insha ALLAH muhaɗa da tufafi wa ƙananun yara suma, ni kuma inason hankalina ya tsaya wajen gyaran gidannan ne”.
Cikin jin daɗi Abbati yace, “ALLAH ya saka maka da alkairi ya ƙara buɗi, ALLAH yasa baɗi iwar haka muna nan muna shagalin sunan babys ɗinmu. Murmushi kawai Jay yayi baice komaiba. Sun cigaba da tattaunawa har kusan 12 sannan suka kwanta, Abbati a ɗakin baƙi da Jay ya shiga ya taimaka masa suka gyara, shikuma ya koma ɗakinsa ya kwanta.
WASHE GARI.
Washe gari Jay suka koma garin su Gimba, ta'azziya suka sakeyi, shima kuma aka sake masa dukda wasu harda munafunci dan sun dasa ƙananun magana akan Jay ɗan ƙungiyar asirine, shine yakai Gimba ma aka shanye nasa. Kasancewar shi mutumne mai saurin fahimtar abu kafin su baro garin ya karanci abubuwa masu yawa daga mutane, ya kuma saka an bincika masa inda ɓaleru yake ta hanyar iyayensa da basusan dawan garinba. Zuwa Azhar suka baro garin.
Tunda suka dawo daga garin su gimba aiki yake babu hutu, kiran sallar la'asar ne kawai ya tadashi, bayan an idar office ya dawo ya ɗora daga inda ya tsaya. Zamansa baifi da mintuna goma ba Hafiz dake ɗauke da takardu a hannu ya shigo office ɗin da sallama..
Batare da Jay ya ɗagoba ya amsa masa. Hafiz ya zauna a ɗaya daga kujerun gaban tebirin yana faɗin, “Yauwa boss ga file ɗinan na gama tattare komai, abinda ya rage mana kawai yanzun shine bin sawunsa kawai, kaga dai dukkan abinda muke buƙata mun riga mun gama samunshi”.
Jawaad ya ɗago yana ɗan bubbuga pen ɗin hannunsa akan laɓɓa, takardun da Hafiz ya ajiye ya ɗauka, sai da ya gama dubawa sannan ya sake ɗagowa ga Hafiz ɗin, “Kamar ba komai ne anan ba ai Hafiz, Rose ta baka dukkan bayanan dake hannunta ne? akwai kuma bayanan Restaurant ɗinan shima ban gansaba anan?”. Hafiz yace, “Oh sorry, wlhy nama shafa'a sosai, na gidan cin abincin nan kamar suna hannun Mami ne fa, jiya naso amsa, sai kuma na iske batazoba, bara na amsosu, saina haɗo dana hannun Rose ɗin”. Dakatar dashi Jay yayi ta hanyar ɗaga masa hannu. “Rose ta fita ita da Aliyu, Miemaa Kirata ta kawo, nima akwai aikin dana sakata ma ita da Dawood shi ya kawo nasa ita shiru kakeji”. Miƙewa Hafiz yay zuwa gaban landline ɗin office ɗin yana faɗin, “Bara muji to kota kammala duka”. Jay baice komaiba ya cigaba da aikinsa, yayinda Hafiz yay waya department ɗin su Bilkisun. Baifi mintuna goma da ajiye wayarba akai knocking ƙofar.
★★★
Tunda nazo office ban gansaba, ban kuma je inda yakeba, ina namu office ɗin na duƙufa dukkan ayyukan dake gabana, sai hirarmu da bata ƙarewa ni da Ummie.
Kasancewar jinin dana gani jiya tun a daren na nemesa na rasa yasa dukkan sallolina yau nayisu batare dana sake ganinsa ba kuma. Mun fito sallar la'asar kowa ya koma kan aikinsa. Nayi nisa sosai akan aikin da nakeyi saƙon kira daga office ɗin Boss ya sameni. Dukda nasan dalilin kiran sai da gabana ya faɗi, dama tun ɗazun Dawood ya sanarmin ya kai masa aikin daya sakamu tare saura ni yake jira. Miƙewa nai na tattare files ɗin guda biyu na fita.
Da sallama na shiga office ɗin bayan nayi knocking an bani izinin shiga, naɗanji sanyi ganin akwai Oga Hafiz a office ɗin, shinema ya amsan sallamata, dodon nawa kam bai ko ɗagoba, gaba ɗaya hankalinsa nakan Computer, inama shigowa ƙarar danna keyboard ɗinsa ce ta fara tarata, yanda yake dannawar da sauri-sauri yasa akejin ƙararsu sosai. Da fara'a oga Hafiz ya tarbeni, na gaishesa ina miƙa masa file ɗaya a cikin biyun dana shigo dashi tunda nasan dama shine wanda zan baiwa. Ɗayan kuma na matsa tebirin boss na ajiye, murya a sanyaya nace, “Barka da yamma”. Batare daya ɗagoba yace, “Barka” ya cigaba da aikinsa. Duk da yanda yaymin ɗin haka na sake dannewa nace, “Gashi na kammala, sai dai result ɗin sayin hannun nasa ɗin bai fitaba”. Dakatawa yay daga abinda yakeyi ya ɗago min manyan idanunsa da a yau suke farare tas, sai dai sunɗan kumburo alamar cike suke da gajiya, sauri janye nawa nai lokacin da sautin muryarsa ta fara isowa cikin kunnena. “Wakika kaimawa?”. Yay maganar har yanzu idanunsa a kaina dan inajin yanda suke shiga ɓargona. Cikin nutsuwa ta nace, “Sir danaje office ɗin Umar bayanan saina gamu da Hashim”. Cikin kaushin murya yace, “Hashim! Kina nufin shi kika bamawa!?”. Yanda yay maganar ya sani ɗagowa na dubesa da sauri. Dan masifa har fararen idanun nan dana gani yanzu sun sirka da ɗan ja, na kula da yashiga ɓacinrai zakaga idanunsa sun sauya kala. A ɗarare na ɗaga masa kai kawai. Uffan bai sake cewaba ya ɗauki wayar landline yay kira.
Hafiz da duk yana zaune yana kallonsu ya kalli Bilkisu, “Mami garin yaya kika bama Hashim bayan bashi akace ki bamawa ba?”. Kaina a ƙasa nace, “Wlhy ni bansan akwai matsalaba ne, na fito shikuma zai shiga office ɗin shine yake tambayata ko lafiya? Nikuma nace masa wajen Umar nazo, shine yace bara ya ajiye masa anjima saina dawo na amsa, to kafin na koma ɗinne kuma mukai fitar ranar, jiya kuma banzo office ba, ɗazun nakoma amsowa danna tattare komai shine Umar ɗin ya sanarmin bai bashiba, amma ya fita idan ya dawo zai tambayesa koya mantane”
Hafiz ya ɗan girgiza kansa da faɗin, “Ki ringa kula kinji, duk wanda ba'ace kibama abububa kidaina bashi, wannan aikin namu da kike gani kowa takansa yakeyi, shiyyasa zakiga a komai ana taka tsantsan, bara ni naje wajen Hashim ɗin da kaina Boss”.
Jawaad ya dangwarar da kan wayar a ƙasa saboda yakasa samun Umar ɗinma, bai cema Hafiz komaiba harya fice.
Kansa ya dafe cike da takaici, ya miƙe tare da tura kujerarsa baya da ɗan ƙarfi ni harma na tsorata, yay taku ɗaya biyu kafin ya juyo yana kallona, yanda ya matso daf dani yasani maida kaina ƙasa, yaɗan buga tebirin da faɗin, “Wai sai yaushene zaki daina bani ciwon kai ne yarinyarnan? Wataran saina sauya miki kamannin fuskarnan taki maikama data mage idan baki dawo hankalinki ba” yay maganar da yunƙurowa kamar zai makeni. Baya nai da sauri, cikin zafin nama na tura kujerar na miƙe tsaye, dan yanda ya fusato ɗinan nasan iya makeni zaiyi ɗin.
Jay da takaici yake neman shaƙema numfashi yace, “Zonan, idan kuma kika bari ni nazo saina karya ƙasusuwanki”. Idanuna cike da ƙwalla na kallesa ina tura baki, kafin na samu damar bashi haƙuri yace.
“Ni kike murguɗama baki?!”.
Saurin ɗagowa nai ina ƙwalalo idanu waje, kujimin sabon sharri, ni yaushe na murguɗa baki dan ALLAH jama'a?. ganinfa da gaske ni yake nufowa fuska a ɗaure sai na fara ja baya, bai fasa biyoni ba kamar yanda ban fasa tafiya da bayaba ina yarfe hannu, jinai tamkar na saki fitsari, yayi bala'in ɗaure fuska yanda na tabbatar yau idan ya kamani sai ya karyanin da yake faɗa. cikin sarƙewar harshe nace, “Ni wlhy ban murguɗa maka baki ba fa Sir, kuma ALLAH bani da lafiya ma”. Nai maganar dai-dai na dangane da bango, shikuma ya iso daf dani.
Ina rufe baki ana turo ƙofar, ido huɗu mukai da Rose, kafin bakina ya iya sake furta wani abu naji an fisgoni na faɗo saman ƙirjin mutum.............✍
ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.
SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.
HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO
MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.
MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.
BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....
abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.
Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899
sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.
Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300
Sai kunzo😍😍😍😘.
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
Billyn Abdul:
Page 35
.................Rintse idanuna nai da azabar ƙarfi, a duk lokacin da jikinsa ya taɓa nawa nakanji tamkar na taɓa wuta, daga randa mukaje ɗakko gawar Gimba kuma sai na rage jin hakan, sai dai sam banason yace zai taɓani, amma a mamakina yau sai naji tamkar an azani bisa wutar. A take jikina ya fara karkarwa saboda azabar da nakeji, cikin gangarowar hawaye bisa idanuna nace, “Boss dan ALLAH ka matsa, wlhy jikinka tamkar wuta nake jinsa”.
Yanda ta ƙare maganar da fashewa da kuka tana neman silalewa ƙasa yasaka Jay ja baya cikin ɓacin rai, dan shi kalamanta zafi sukai masa a zuciya, cikin kaushin murya yace, “Qaseem ne kawai idan ya taɓaki baƙyajin zafi tunda shi kikeso?”. Idanuna na shiga lumshewa ga zufa sai karyomin take a jiki saboda azabar da nakeji, na shiga girgiza masa kawai, “Kaimin addu'a, fatar jikina jinake tamkar ana ɗayemin itane”. Yanzu kam da mamaki yake kallonta, dan yanda jikinta ke wani irin karkarwa da zufar da takeyi ta cancanci a fahimceta, kalaman baba ƙaurane suka faɗo masa cikin rai, addu'ar ya shiga karantowa yana tofa mata, idanunsa harsun ƙaɗa sunyi jazur saboda yanda yakeji a cikin ransa, gaba ɗaya yakan rasa wane tunani zaiyi akan lamarinnan, idan ya zurfafa tunaninma sai kiji kansa ya fara matsanancin ciwo, dole yake ajiye batun ya shiga wata sabgar badan kuma al'amarin baya cikin ransa baneba. Ahankali Bilkisu ta shiga sauke numfashi, zufar na tsafewa sanyin ac na ratsata, kusan mintuna goma suna a haka.
Rose da tunɗazun tai sumar tsaye tai Luuuu zata faɗi saboda wata hajijiya data rufe ganinta. Da sauri Hafiz da isowarsa kenan dasu Jabeer ya tarota. tai ƙoƙarin ƙwacewa jikinta na rawa zata sake danna kai cikin office ɗin idanunta na zubar hawaye Hafiz yay saurin sake fusgota, cikin tsawa-tsawa yace, “Rose! Minene kikeyi hakane?”. Wasu irin zafafan hawayene suka shiga rige-rigen sake gangaro mata saman kumatu, ta tsare Hafiz da kallo, hannu na rawa ta nuna ƙofar office ɗin Jay, “Boss fa rungume da yarinyar nan”. Cikin takaici Hafiz yace, “Idan ya rungumeta sai akai me? Ba matarsa bace! matarsa ce ita halalinsa, ke kanki shedace akansa, inda Jay yana harkar mata ke zai fara lalatawa ai” ya ƙare maganar da balla mata harara yaja tsaki ya juya yabar wajen.
Da sauri Rose ta maida kallonta ga Jabeer da Aliyu. Tace, “Kunajinfa miyace, miyasa Hafiz baya ƙaunata?”. Ɗan murmushi Jabeer yay yana girgiza kansa, “Hafiz ba ƙaunarkine bayayi ba, gaskiya ya faɗa miki, Mami matar Jay ce yanzun”. Daɓar Rose ta zauna ƙasa tana faɗin, “Jesus, shikenan na mutu Jabeer, yaushe akai musu auren?”. Duƙawa Aliyu yay gabanta cikin taushin murya yace, “Baki mutuba Rose, kisama ranki haƙuri dan ALLAH karki tada hankalinki kinji, ALLAH ya rubuta itace matarsa, kema naki mijin nanan zuw.......” “Aliy daina faɗamin maganar banza kaji, ni boss zai yaudara, dama tunda naga yarinyarnan na shige masa nasan zatai abinda yafi haka, nasan asiri tai masa kawai”. Ƴar Dariya Jabeer yay shima ya duƙa gabansu, “Rose na faɗa miki gaskiyar magana? Boss shike bin Mami ba ita ke binsa ba, tunda muke da ita bata taɓa nuna wanima a cikinmu ya taɓa koda birgetaba, shi kansa farautar soyayyarta yake amma sam taƙi bada ƙofar hakan, kullum ma nunawa take ita batama taɓa fahimtarsa ba, itaɗin mace ce mai AJI!, shine babban maganin asirinta akan zuciyar Boss, yakamata ki fahimci yana son mace mai suna mace, ma'ana mai Ajiiii!!”. ya ƙare maganar cike da salon iskanci yana salute ɗinta, miƙewa yay tare da mata nuni ta miƙe dan tayi sagafene tana kallonsa da fassara maganganunsa sala-sala.
Sam Jay baiga Rose ba, Bily kanta data ganta halin data shiga yasa tama manta da ganin nata, ruwa ya ɗakko ya bata, babu musu ta amsa, yanda tasha ruwan sosai har mamaki ta bashi, ta miƙa masa kofin tana godiya, baice mata komaiba sai nuni da yay mata data tashi takoma kan kujera.
Nima ina buƙatar hutawar, dan haka na tashi na koma saman kujerar na zauna tare da lumshe idanuna.
Sosai nakeji a jikina kallona ake, ina buɗe idanu muka haɗa ido dashi, ɗauke kansa yay tamkar baniɗin yake kallonba, nima na janye na
wa a raina ina jinjina yanda ya ƙware a iya kallon mutum.
Babu wanda ya sake shigowa office ɗin har aka kira sallar la'asar, shine ya fara shiga ya ɗaura alwala sannan yace naje nayi nima, lokacin dana fito tsaye na gansa, bance komaiba na nufi hanyar fita yana biye dani.
Daƙyar Aliyu ya lallaɓa rose suka bar ƙofar office ɗin Jay, kuka take rurus cin ƙarfinta, a zuciyarta tana ayyana matakin gaggawa da zata ɗauka akan Bilkisu nan bada jimawa ba, bazai yuwu tazo jiya-jiya ta samu abinda ita ta kashe shekaru masu yawa tana bibiyaba, dolene kodai ita ta samu, kokima su rasa gaba ɗaya. Da wannan ƙudirin tabar office yau.
Yau tare dashi mukabar office, a ƙasan raina cike nake da tuhumar ina Yah Qaseem ya shiga? Sam bana ganinsa a office tunda na dawo, mike faruwa dashi ne? Inason tambayar boss inajin tsoron buyaginsa. Munyi nisa a tafiya batare daya kalleniba yace, “Jazuga bai mutuba”. Da wani irin matsanancin sauri na juyo na kallesa, harma na manta dawa nake na kafesa da idanu ko ƙyaftawa banayi”. “Malama idanun nan sunmin yawafa”. Kumbura fuska nai na ɗauke kaina jin abinda yace, sai kuma na kasa haƙuri naɗan sake kallonsa na risinar da kaina, cikin zumuɗi nace, “Dan ALLAH da gaske boss?”. yace, “Mun fara ƴar wasane dake?” kaina na girgiza masa dukda nasan bani yake kalloba. Shiru bai sake cewa komaiba, har muka isa masarauta, dukda inason jin ƙarin bayani haka na daure na danne a raina, idan taƙamarsa jan aji gidan ya taras.
A cikin ran Jay wani irin haushine ke cinsa, mamaki da takaicin miskilancinta yake, yayi shirune yaji kozata tambayesa cigaba labarin amma yanda yay shiru itama ta tsuke baki, shikuma inhar ba ita tanema jin yanda akaiba bazai faɗa mataba. Babu wanda ya sake yin magana tsakanina da shi har yasamu guri yay fakin gab da sashen gimbiya, dan yanzu shi babu shamaki an bashi damar shigowa cikin masarauta a duk sanda yaso. Yunƙurin buɗe motar nai ya riƙo hannuna. Daƙyar na iya danne abinda nakeji na kallesa, ganin ni yake kallo sai nai ƙasa da kaina, sakarmin hannu yay yana faɗin, “Saiki jira na gama tunda ba tauneki zanyi ba”. Nidai bance komaiba, ya miƙa hannu sit ɗin baya ya ɗakko leda viva sabuwa. “ga wannan, duk yanda zakiyi amfani dasu na rubuta miki, Karkiyi wasa Miemaa, dan ina buƙatar matata a kusa dani” yay maganar ahankali yana kafeni da idanu, saurin sadda kaina nai dan naji wata irin bahaguwar kunya ne. Jay dake kallonta yay wani lallausan murmushi da cigaba da faɗin, “dolene ta hanyarki zan gano bakin zaren matsalarmu, hakan kuma bazai yuwuba kai tsaye sai da taimakon UBANGIJI”. Kaina a ƙasa nace, “Insha ALLAHU zanyi Sir”. “ALLAH ya tabbatar”. Ya faɗa batare da ya da ɗauke kansa daga gareni.
Nima saina fita a motar ɗauke da ledar da bag ɗina, ta sashensa na zagaya na sake masa godiya sannan na shige, tuni an amshi kayan hannuna tun fitowata a motar.
Jay daya kafeta da kallo ta cikin mota yaɗan lumshe idanunsa yana sauke ajiyar zuciya lokacin data shige. Shima fitowar yayi. Masallacin masarauta yay salla har isha'i, kafin ya samu damar ganawa da gimbiya a tsaitsaye. Yamata bayanin abubuwa da dama a gurguje, itama ta sanar masa ƴar firar da sukai da Bily da abinda ta fahimta. Duk yanda taso yaci abinci ƙinci yay yauma yaymata sallama ya wuce.
______________________
Tun daga wannan ranar gimbiya ta sake jan Bilkisu jikinta, riritata take tamkar uwa da ƴa, gefe ɗaya tana koya mata dabarun rayuwar aure cikin hikima kamar yanda itama Mommah tai mata gata, sannan a hankali take fahitar wasu abubuwa daga Bilkisu ta cikin hira. Magungunan da Jay ya kawo mata Amintacciyar baiwar gambiya tsaye take akan Bilkisu dan ganin tayisu kamar yanda ake buƙata, ga maganin sanyi shima da ake bata acewar gimbiya shine matakin farko.
Kullum da safe driver zai kaita office da yamma idan an tashi Jawaad ya ɗakkota ya maidota, dukda babu wata hirar arziƙi a ciki, yakuma daina raɓarta koda wasa, yanzu sam basama haɗuwa sosai a station ɗin saboda baya zama aiki yaymasa yawa, su kansu yana wajigasu da ayyukan sosai.
A haka aka shiga wata mai albarka na rama
dhana, manya da ƙananun yara harma da tsaffi kowa ya tashi da wannan ibada a baki cike da ɗoki da fatan kammalawa lafiya. Yayinda Bilkisu ke kallon ikon ALLAH wajensu gambiya dangane da alkairin da ake fita dashi domin talakawa. Abin sai ya birgeta, a cikin ranta tana fatan kwatantawa taji idan zata iya watanara, sannan har yau da take nufar sati na biyu a masarautar bata taɓa gamo da Sarki Sameer ba, Safah ta sanar mata yaje saudia hutawa shida amaryarsa da suke kira Ammi, sai azumi yaje tsakkiya zai dawo sukuma su tafi Umarah
★★★★
Jay da muƙarrabansa sunyi busy matuƙa, ga aiki ga aikin sa kai gana hidimar bayin ALLAH duk ya haɗama kansa, burinsa ya kammala abubuwa da yawa cikin watannan, baya neman Bilkisu ne dan yana tausayinta sosai, ga azumi ga rana dan ruwa bai zaunaba sosai, gani yay ta rame masa a kwanakinan sosai sai tai haske kuma.
Abin mamaki Rose kuma saita shiga ja baya dasu, har takai saida Jay yamata magana da kasa, ranar kam dai yaga taɓara da iyayi, gashi yanaji da azuminsa. Shidai ya lalaɓata kawai dan yana buƙatar nutsuwa baison hayaniya.
Tuni yasa ana bibiyar masa bayan Ɓaleru duk inda ya sanya ƙafa batare da shi ya saniba, bayason kamasa a cikin watannan mai albarka shiyyasa yay tamkar ya manta da al'amarinsa, ga jikin ɗan-fir'auna da har gidan su Shahudah suka ɗauka ya mutu na nata sauƙi da warwarewa.
______________________
Kwanci tashi babu wahala wajen UBANGIJI azumi yakai tsakkiya, a daren sha bakwai sarki Sameer da Amaryarsa suka dawo, anyi murna da dawowar tasu sosai, dan ranar kam kowa ya shaida hakan a masarautar gagara badau, ranar gimbiya da kanta taima Takawa abincin buɗa baki a kicin ɗinta na sirri da babu mai shiga sai ita saiko Amintacciyar baiwarta. Tunda ta tafi ɓangarensa su bily basu sake jin ɗuriyartaba sai washe gari, sai a randa za'a ɗau azumi na sha takwas ne suka ganta, shima dan tasaka a kira mata bily ne.
Cikin girmamawa na gaisheta kamar yanda na saba, fuskarta ɗauke da murmushi ta amsa min tare da kamo hannayena cikin nata. “Ɗiyata dama nasa a kiramin kene saboda zaku wuce Umrah gobe idan ALLAH ya kaimu ke da su Amaturrahman, an kammala miki komai insha ALLAH” Dama Boss ya sanarmin tun shekaranjiya, sai dai na nuna mata farin cikina sosai akan hakan itama tamkar bansan da tafiyarba, nakuma mata godiya. Ta cigaba da faɗin, “Naso ace tun farkon azumi kika tafi, sai dai mijinki ya sanarmin hakan bazai yuwuba saboda aikinki, dan akwai wata auntyna matar yayan abokin Takawa tanada makaranta ta musamman domin koyar da amare, ana gyaran jiki da komai a ciki, koya girki da dukkan dabarun zaman aure, itama ƴar nan ƙasarmu ce, dalilin ƙaddara ta shigo rayuwarmu, mun kaita domin neman magani sai yayan abokin Takawa yace shifa yayi mata, wannan shine dalilin zamanta a can itama”. Fuskata ɗauke da murmushi nace, “ALLAH sarki”. Itama murmushi tayi, “Yanzu dai yayi dukkan cuku-cukun daya dace a wajen aikinku insha ALLAH keda nan sai saura kwana biyar tarewarki, inason naga kin zama cikakkiyar mace mai amsa suna mace a fadar mijinta, mijinki babban mutumne sannan yanada wasu sirrika dake kaɗai zaki fahimci kayanki anan gaba, shiyyasa nakeso a gyaramin ke yanda ya kamata domin zukatan maƙiya su girgiza, waɗanda suke ganin baki kaiba su fahimci kin musu zarrah ta har abada kinji”. Hawayen dake ziraromin na share, bansan irin godiyar da zanma wannan baiwaba a rayuwata, itaɗin ta musamman ce a cikin jerin abubuwa masu muhimmanci da suka shigo rayuwata, ALLAH ya biyata da aljannarsa.
Washe garima naje wajen aiki, sai dai yau bashi ya maidoni ba sawa yay sabon direbansa ya maidoni, gobe idan ALLAH ya kaimu kuma bazanje aikiba, dan ƙarfe huɗu zamu wuce, share hawayen dake zubomin nake akan abinda ya faru tsakanina dashi yanzu a office ɗinsa. Na roƙesane akan zanje gidan Dad nai masa sallama, dama tun farkon azuminan naketa masa magiyar ya kaini na gaishesa, bai taɓa kulaniba sai yau da yanema marina a office, yajamin dogon gargaɗi akan inhar na sake masa maganar Dad ALLAH sai ya fasan baki. Sake share hawayen nai zuciyata namin zafi da takaucinsa,
ni bansan mi Dad yaymasaba haka da zafi shi da ahalinsa, inason ganin koda mutum ɗayane a cikinsu amma abin ya gagara, sam yanzu bana ganin Yah Qaseem, narasa ina ya shiga baya zuwa Office, mike damunsa? Minene matsalarsa? Haka kawai bazai bar zuwa office ba ai?. Zafin boss yayi yawa, nikuma har zuwa yanzun ban taɓa jin sonsa a rainaba, nasan dai zan iya haƙurin zaman aure dashi amma badan inajinsa a raina da kalmar soyayya ba, bansan miyasa hakanba, har zuwa yanzu Yah Qaseem ne kaɗai a zuciyata, shi nakeso, shi na fara so, sai dai shikuma banajin sha'awar zama dashi matsayin miji, bansan miyasa hakanba shima. Ya ALLAH ka kawomin ɗauki bisa ruɗaɗɗen tunanina daya banbanta dana sauran mutane a yanzu.
Har muka bar ƙasar bana cikin walwala sam, sai wata irin matsananciyar damuwa da na tsinci zuciyata a ciki, wannan dalilin yasa har jirginma ya tashi ban tuna shine hawana na farkoba, Safah na lafe a jikina tana barci har muka sauka. mun sami tarba ta musamman daga wasu manyan mutane da bansan matsayinsu ba, sai dai ina tunanin waɗanda Gimbiya taban taƙaitaccen labarinsu ne ranar, sai dai wannan nafi ƙyautata zaton abokin takawane da iyalansa ba waccan mai makarantar bace da naji nafi ɗokin gani. Ƴan uwa abu mafi ɗaure kaina shine, maimakon najini cikin farin ciki da zuwa ƙasa mai tsarki a karo na farko a rayuwata sai saɓanin hakan ya biyo baya, kallonsu nike kawai tamkar wata sakarai, ƙirjina na wani irin zafi, sai can ƙasan zuciyata kuma nakejin wani irin sanyi dake kawomin sassauci a cikin ƙirjina kaɗan-kaɗan. Darene sosai, dan haka makwanci kawai aka bamu da abinci, nikam bammaciba na kwanta.
__________________________
Yau tunda ya tashi aiki wanka kawai yaje yay a gida ya kimtsa, sabon drivernsa mai suna Sadiq ya ɗaukesa sai gidan Alhaji Babba dan acan yake buɗa baki yanzun kullum, wataran kuma gidan Ummah babba, kokuma gidan Ummah ƙarama idan ta ishesa da ƙorafi. Haka kawai yau yakejin tamkar wani abu dake nesa dashi yana tunkarosa, minene? A ina yake? Itace amsar dakanzo masa akai-akai cikin shauƙinsa.
Shi dai Alhaji babba kallonsa kawai yake amma baice komaiba, sai da suka dawo salla sukai zaman buɗa baki sannan, ya kai dubansa ga Jay da keta juya cokali cikin kofin kuni yana ɗan murmushi. “Wai nikam gwauron nan yau miya saka farin ciki haka?”. Kallonsa Jay yay fuskarsa ɗauke da murmushin har yanzun, yace, “Babu komai Baba, kawai dai”. Murmushi shima Alhaji baban yayi, “Kawai dai haka ka tsinci kanka kaima ko?”. Kai Jay ya jinjina masa yana lumshe ido. Alhaji babba yace, “Nima haka na tashi da farin ciki, sai nakeji tamkar wani abu dana daɗe da rasawa zai dawo gareni, sai nakeji kamar wani abuna mai muhimmanci ya haɗu da abuna mai muhimmanci, sai nakeji kamar wani abun da na daɗe ina neman amsarsane lokacin sanin amsar yayi, a daren jiya nayi mafarkin ƴaƴana guda biyu cikin farin ciki, tabbas Jawaad inaji a raina wani abu mai daraja da haske na matsowa zuwa garemu”. Jawaad sauraren Alhaji babba kawai yake yana murmushi irin wanda ya kasance mai tsada a garesa, ya ɗora kansa a kafaɗar kakansa yana sake ƙawata murmushinsa, “Ya ALLAH ya tabbatar da wannan hasashe naka ya zama alkairi kakana”. Shafa kansa Alhaji babba yay yana murmushi da faɗin, “Amin ya rabbi jikallena, amma yakama ka dawo nan kwanaki goman nan na ƙarshe muyisu tare cikin ƙololuwar ibada, ka ajiye duk wani aiki gefe”. Jay ya tashi zaune sosai yana kallon kakan nasa, yace, “Nima nayi wannan tunanin, sai dai banason takura maka da yawa”. Ranƙwashi Alhaji babba ya kai masa bisa kai, Jay yay saurin kaucewa yana dariya da haɗe hannayensa waje guda alamar na tuba.
Bayan sun dawo daga salla suka iske Ummah babba da ƙarama sunzo, dama sunce yau zasuzo. Jay ya zauna tsakkiyarsu yana dariya da faɗin, “Saini ɗan gatan ALLAH, Ummahs ɗina duka tare dani”. Atare sukai dariya da riƙe hannayensa, Ummah babba tace, “Ja'iri kamar ya wani damu damu?”. Karyar da kai Jay yayi ya ɗora saman kafaɗarta, murya a sanyaye yace, “Idan ban damu da kuba dawa zan damu Ummah?, kuɗin duniyatace, sannan haskena, aikine kawai ke hanani rawar gab
an hantsi”. Guntuwar dariya tayi da shafa kansa, ta sumbaci hannunsa tana mai saka masa albarka.
Kasancewar basu da ishashen lokaci suka fara tattaunawa akan maganar lefe da dama shine ya kawosu. Da farko Jawaad yace su barsa zaiyi, amma sukace sam bazai yuwuba, na farkoma dan an nuna musu fin ƙarfine Uncles ɗinsa sukace zasuyi, to wannan kam suma sune zasuyi insha ALLAH.
Jawaad yay shiru yana murmushi dajin ƙaunarsu mai narkar da zuciya na ratsasa, zamansa ya gyara a kujerar daya koma shi kaɗai yana kallonsu, “Nagode sosai iyayena, kun sharemin hawayen maraici tuni, bani da abin biyanku sai dai naita muku addu'oin gamawa da rauwa lafiya, idan na ganku saina manta bani da Uwa, idan kuka kalleni sai nake ganin Mah-mah har yanzu tana tare dani, ida har tabar duniya ina roƙon UBANGIJI yasa ana nuna mata dukkan alkairanku ga gudan jininta, idan tana duniya ina fatan ganinta na bata labarin alkairanku ga gudan jininta, ku......” “Ya isa haka kaji Muhammadu, insha ALLAH inaji a jikina BILKEESU tana raye, insha ALLAH kafin nabar duniya saina ganta” Alhaji babba yay maganar yana share hawayen da suka ɗan zubo masa. Ummah da Ummah ƙarama ma kuka suke, Jay gwanin dakiya babu hawayen zahiri saina zuci kawai.
____________________________
Kasancewar nazo babu tsarki sai yau nake fatan samu lokacin da zamuyi sahur saina duba, naji wani nishaɗi ganin ya ɗauke harda tsallena a bayi, wanka nayo da brush na fito, cikin tsokana Meenal tace, “Gandiya halan yau kin musulunta ne? Naga wanka da asubar fari”. Murmushi nai mata ina zama domin busar da kaina da hand drayer ɗin dana gani saman mirror ɗakin, nace, “Oh da kafira kike kallona?”. Dariya sukayi ita da Amaturrahman dake ƙoƙarin shiga yin brush itama, tace, “Ai kima godema ALLAH ke kina zuwa yana ɗaukewa, ita tana shigowa yana zuwa”. Cikin ɗan zaro idanu na kalli Meenal ɗin, sai kuma na langaɓe kai nace, “Kai harfa kin bani tausayi babie”. Filo ta ɗauka ta jehomin ɗaya ta jefama Amaturrahman. Da gudu Amaturrahman ta shige bayi tana dariya, nikuma na cafe wanda ta tillomin. “ALLAH karkiji wasa meenal tausayi kika bani” nai maganar da ɗan mata gwalo. Ƙwafa tayi da faɗin, “Wlhy duk zan rama, ke saurama ƙiris na raman ai, zaki gane kurankine”. Murmushi nai mata bance komaiba na cigaba da busar da kaina.
Bayan munyi sahur salla mukai muka sake kwanciya barci, mune bamu tashiba sai sha ɗaya, shima tadamu akazo akayi. shiri mukai a gaggauce na tafiya massallaci, nidai Kasa daurewa nai na tambayi Amaturrahman Auntyn da Ummu tace tanada makaranta gidansu kuma na kusa da inda zamu sauka?.
“Lah Bily ai yanzu bazakiga Umm-Anum ba, sun shiga ittifaqi, kinga gidansu nan, duk Ramdhan idan mukazo bama ganinsu muma sai ranar sallah”. Da mamaki nace, “Basu da yara?”. Tace, “Sunada yara biyu mana, mace da namiji, namijin ya girmemu da kusan shekara biyar, sunansa Anwar, sai macen Anum, tare suke shiga ittifaqi. Tunkan na gansu naji sun matuƙar burgeni har ina zumuɗin ganin nasu mai ban mamaki, dan tunda Ummu taban labarin matar a taƙaice saita kasa barin zuciyata. Yanda na iso da ƙuncin zuciya a yanzu sai ba hakaba, fes nakejin raina cike da nishaɗi da farin ciki da shauƙin ganina a ƙasa mai tsarki, santin da banyi a daren jiyaba sai gashi a yau inayinsa, dan har muka isa massallaci bakina bai hutaba, Safah kam bata gajiya damin bayanin komai dalla-dalla. Lokacin dana ganni gaban ɗakin ka'aba sai kawai nakejina tamkar wata sabuwar Bilkisu ce tsaye ba wadda tazo da ƙunci ba, hawaye masu ɗumi na ziraromin bisa kumatu, abinda ban taɓa tunaniba koda a mafarki, wani nauyin zuciya da ƙunci da damuwar da natsinci kaina a gaba ɗaya cikin shekarunan sai naji tamkar an yayesu an zubar tare da ruwan wankan dana samu tsarki ɗazun da asuba. UBANGIJI mai rahama, UBANGIJI mai ni'ima.
Muna zaune a wajen mutanen kirki, larabawan usul masu ƙyawawan zuciyoyi, bamu rasa komaiba, ibada muke babu wasa dansu Amaturrahman sun horu sosai, sannan sunada ilimin addini suna kuma aiki dashi, Umm-Aban koda yaushe cikin kulawa take damu sosai, nasamu sauyi iri-iri da ha
ske a rayuwata a cikin kwanakinan goma da mukai na Umrah, babu abinda mukeyi banda ibada, duk wata shiririta mun ajiyeta gefe, a kullum safiya bayan sahur muna waya da gimbiya, hakama su Ummie duk saina kirasu, Boss kam ko filashin bai taɓa haɗamu ba, sannan dukkan numbers ɗin ƴan gidanmu bana ganinsu a wayata yanzun, bansan yaya akai hakan ta kasanceba tunda nidai ban gogeba.
Yau take salla, sosai massalacin ke cike, bayan an idar da sallah sai na dingajin juwa, duk yanda naso dannewa hakan ya gagara, bandai sanarma su Amaturrahman ba dan karsu tada hankalinsu, miƙewa nai da nufin na ɗan samu waje inda babu yawan mutane na huta ko zanji nutsuwa sai kawai hajijiya ta kwasheni. Sama-sama na jiyo wata nutsatstsiyar muryar ta ambaci “Yah ALLAH”. Sai jina nai a jikinta. Cikin ɗan larabcin da nakeji kaɗan-kaɗan na tsinci tanama wani wanda bansan ko waneneba magana akan ya bata ruwan zam-zam dake hannunsa. Gabana yay wata masifar faɗuwa jin muryar data amsa mata, murya irin wadda wajan mutum ɗaya na santa, muryar dake sakani bugun zuciya, muryar dake saka jinina gudu cikin jijiyoyi, da ƙyar nai ƙoƙarin ɗaga idanuna dake neman rufewa na sauke a kansa dai-dai ya miƙo ƙaramar goran ruwa wa matar da har yanzu nike a jikinta.............✍
ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.
SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.
HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO
MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.
MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.
BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....
abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.
Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899
sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.
Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300
Sai kunzo😍😍😍😘.
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
0 comments:
Post a Comment