ƘWAI cikin ƘAYA!!
Bilyn Abdull ce🤙🏻
BOOK TWO
Page 9
............A matsayinka na ubanwa?” cewar Qaseem a fusace.
Cike da rainin wayo Jay yace, “Lokacine zai nuna maka”.
Jabeer da ya shigo office ɗin kusan mintuna biyar da suka shuɗe, amma jaraba ta hanasu ganinsa yay gyaran murya.
Duk kallon ƙofar mukai, Cikin nuna alamun tamkar baima fahimci mike faruwa a office ɗinba ya kalleni tare da miƙamin kwalin dake a hannunsa, “Momcyn mu kikai wannan Office ɗin MM; daga nan ki wuce ƙasa naga ana nemanki”.
Kaina na ɗaga da sauri, na amsa kwalin na fice ina mai godema ALLAH da zuwan oga Jabeer da yay belina hannun waɗanan zakunan.
Babu wanda yay magana tsakanin Jawaad da Qaseem ɗin har Bilkisu ta fita, Jabeer ya maida kallonsa kansu yana ɗan murmushi, “Haba basawanmu, ya zaku saka yarinya tsakkiya kuna yaƙi? Ai saiku rikitata, miye nata a ciki tunda batasan miye tsakaninku ba?, yakamata kumata adalci, aiki take kamar yanda kuke aiki, ku sakata abinda zaku sakata matsayinku na waɗanda suke sama da ita, amma bawai ku sakata tsakkiya akan abinda ke zukatanku ba”.
Juyowa Jay yayi, kamar zaiyi magana sai kuma ya girgiza kansa kawai ya juya yana mai ɗaura hannunsa a kafaɗar Qaseem ɗin yaɗan bubbuga kaɗan ya koma mazauninsa. Binsa da kallo Qaseem yay cike da takaici da baƙin ciki, a ransa yana rayama kansa inhar Jawaad yay gigin cigaba da kutse a al'amuran Bilkisu wlhy wannan karon sai ya karta masa rashin mutuncin da bazai taɓa mantawa da shiba har ƙarshen numfashinsa, yaja tsaki tare da harar Jabeer ya fice daga office ɗin..
Jabeer dake binsa da kallo ya girgiza kai kawai sannan ya juyo ga Jawaad da ya cigaba da harkar gabansa, ƙarasawa yay ya zauna yana ɗora wayarsa a tebirin Jay ɗin, “Boss dan ALLAH son yarinyarnan kakeyi ne?”.
A bazata maganar ta zoma Jawaad, dan haka babu shiri ya ɗago idanunsa da sukai sirkin jaa da ƙara girma ya watsama Jabeer ɗin wata uwar harara, sai kuma yaja tsaki ya maida kansa ƙasa.
Jabeer ya haɗiye dariyarsa yana gyara zamansa, “ALLAH ba wasa nakeba Jay, kuma idan hakan ta kasance wlhy zanyi murna, dan nutsuwar yarinyar na burgeni, g......”
“Motsoww! Jabeer banason shirme, wace irin banzar maganace wannan, Please banaso karka sake”.
Hannu Jabeer ya haɗe waje guda alamar ban haƙuri, Jawaad ya kuma hararsa ya ɗauke kai. Shidai Jabeer yay murmushi kawai, cikin son kauda zancen yace, “Yanzu nakeji su Sir Ahmad sun sake shiga meeting akan batunnan”.
Jawaad da kansa ke durƙushe yana aiki yace, “Basai suyi tayiba tunda basu da tunanin kansu sai abinda aka ɗorasu a kai”. Jabeer yace, “Wlhy Jay ni mamaki suke bani ma, saboda ALLAH maimakon subama yarinya ƙwarin gwiwa akan abinda ta fara sai kawai su ɓige da tsugunne-tsugune, kai yanzu mi kake tunani akan batun?”.
Kallonsa Jay yayi fuska a taɓe, sai kuma yaja tsaki ya maida kansa ga abinda yakeyi, “Tunanin mizanyi akan wannan shirmen Jabeer, iyakaci suce zasu dakatar da ita na wani lokaci ta huta, ko su canja mata wajen aiki ai dai ko? Tunda basu isa suce ta ajiye aikiba akan hakan”.
“To ai babu wanda ya kamata kabari ya kasance a ciki” cewar Jabeer yana kafe Jay da idanu.
Shiru Jawaad yay bai tankaba, tsahon mintuna biyu harma Jabeer ya fidda rai da samun amsa sai yaji yace, “Akanmi zan hana ni kuwa? A matsayina kuma nawa? Dukansu ogannina ne, suna sama dani nesa ba kusa ba, to mizan iya musu kona hanasu?”.
“Jay! Saboda ina ƙwaɗayin yarinyar ta shigo tawagarmu”.
“Humm” Jawaad ya faɗa a taƙaice.
Jabeer da ya fahimci amsar kenan sai ya cigaba da faɗin, “Ba ƙaramar nasara bace hakan a garemu Jay, dan inaji a raina zata ƙara kawomana nasarori, amma kadaiyi tunani akan hakan”.
Ƙin cewa komai Jawaad yayi, hakan yasa Jabeer sakin zancen shima ya ɗakko masa na aikin da suka fara yau kawai, ananne Jay ɗin kuma ya bashi dukkan attention ɗinsa suka shiga tattaunawa.
★★★★★★★
lna fitowa daga office ɗin MM naci karo da Ummie, bansan miyasa na tsinci kaina da gyara yanayinaba na sakar mata murmushi, hararata tayi ita kuwa tana fusgar hannuna mukai gaba. Masallaci muka nufa dan lokacin sallar zuhur yayi.
Bayan mun idar da sallane mun fito Ummie ke tambayata akan ina naje? Mi kuma ya sami kana?. Ban wani ja zancenba na bata labarin abinda zan iya, sai dai ban bata labarin miya faru tsakanina da yah Qaseem ba da kuma ceton da boss yay min a hannunsa yanzun.
Sosai naga mamaki a wajen Ummie tattare da labarin nawa, harna kasa haƙuri nai mata tambaya, tai ƴar dariya kawai da cewar, “Abunne da mamaki ALLAH, wannan mutum mai fuska kamar hadarin tsakkiyar damina ɗin?”.
“Ba abin mamaki bane Ummie, ni kawai na danganta lamarin da abinda ya farune ranar, ganina yake kamar wata jarumar gaske, baisan lamarin duk buge bane kawai” sosai Ummie ta kwashe da dariya cike da shaƙiyanci, nakai mata duka ta kauce tana cigaba da dariyarta, sai da tai mai isarta sannan ta dawo tana bani haƙuri muka shirya, daga haka muka cigaba da tsokanar junanmu da aikin dake gabanmu kuma.
Har lokacin tashi yayi ban sake saka boss da yah Qaseem a idanunaba, dama bai zama lallai na gansunba kasancewar bani da hurumin hakan sai idan sune sukaso, haɗuwarmu a inuwa ɗaya dama sai da ƙwaƙwƙwaran dalili. Haka kawai na tsinci kaina da tsoron bin yah Qaseem, sai kawai nabi Ummie ta saukeni a gida
★★★★★
Bayan sallar magriba ina zaune a saman abin salla ina azkar aka turo ƙofar ɗakina aka shigo, kaina na ɗaga ina kallonsa, yanda fuskarsa ke a tamke saida naji gabana ya faɗi, amma sai na dake abina nace, “Yah Qaseem ka dawo?”. Baice dani uffanba sai wata uwar harara daya makamin, ɗauke idona nai tamkar ban ganiba, ya ida shigowa cikin ɗakin yana bin ko ina da kallo, bakin gado ya ƙarasa ya zauna, hakan sai ya sakani jin wani iri, dan kuwa ni kaɗaice a gidan, koda na dawo ban iske kowa ba, su mom basu dawo daga gidan rasuwaba. A daƙile yace, “Waye ya maidoki gida?”.
Kaina tsaye nace, “Ummie ce, na jiraka naga baka fitoba gashi magrib ya gabato, sai kawai na biyota”.
Shiru yay tamkar bazaice komaiba, sai numfashi yake saukewa da sauri-sauri, hakan yasani tsira masa ido, “Yayah lafiya kuwa?”.
Wata harara ya sake danƙaramin kamar idonsa zai faɗo ƙasa, “Uwar miye haɗinki da shi Jawaad ɗin? Da har zaku fita tare? Ban miki Warning akansa ba?”.
Zamana na gyara sosai akan abin sallar saboda jin ƙafata ta fara yami, duk da na lura bawai maganar wasa yakeminba inata ƙoƙarin dakewa.
Bansan yanda zan bashi amsa ya fahimtaba, amma ni banajin kuskure nayi tunda akan aikine ai. “Dake nake magana Bilkisu!!”. Saurin kallonsa nayi danjin yanda yay maganar a kausashe, nace, “Aiki muka fita fa”.
“Aiki? Duk jami'an dake cikin Station ɗin babu wanda zai ɗauka suje aiki sai ke?”.
“Yayah ni wlhy ban saniba”.
Saida yasake watsamin harara dayin ƙwafa sannan yace, “Su kuma waɗannan kayan na jikinkifa da nagani ɗazun? Ina kayan da kika fita dasu daga gida da safe?”.
Kaina tsaye nace, “A wajen aiki da muka fita ne a mistake jikinmu ya ɓaci, to shinefa sai... Sai... Sa.........”
“Sai ubanmi? Bilkisu!!”.
“Sai Rose ta bani wasu kayan na zanja”.
“Harda ita kuka fita?” yay maganar cikin kakkafeni da idanu. “Eh” na bashi amsa cike da ƙwarin gwiwa.
Karon farko da yaymin murmushi, ya sakko daga saman gadon ya zauna kusa da ni sosai ya tanƙwashe ƙafafunsa (Dan zuciyarsa tayi sanyi jin basu kaɗai bane, amma hakan ba yana nufin zaiƙi saka musu ido bane ba). Yanda muka samu kusancine ya sakani matsawa baya kaɗan, baice komaiba, saima hannuna daya kamo cikin nashi, nai ƙoƙarin amshewa amma sai ya hanani damar yin hakan, murya a sanyaye yace, “Bilkisu!”.
Amsawa nai idona na kawo ƙwalla, dan banason kama hannuna da yayi......
“Kinsan kuwa yanda nake sonki da kishin ganin wani ya raɓeki?”. Shiru nai bance komaiba, shima bai jira amsata ba ya cigaba da faɗin, “Daga yau karna sake ganinki da Jawaad, idan kuma ba hakaba to lallai zan saɓa miki kuwa! Domin koba aurenki zanba yayankine ni, dolene na saka miki ido gudun karki lalace”.
Yanda ya ƙare maganar sai yaban dariya, a raina nace, ‘Kaima ka samu dama ai lalatanin zakai’, amma a fili sai, nace, “Yayah nifa banice naje wajensaba, bayan na fito daga kiran da akai minne mukai karo dashi a hanya, shi kuma ya fito daga office ɗinsa, shine yace na biyosa, da farko ma bansan dani yake ba sai da ya sake aikowa sannan, amma dan ALLAH kayi haƙuri”.
Murmushi yay min yana jinjina kai, yace, “Nasan dama ba laifinki bane, amma zan takama al'amarin birki tunkan yay nisa kinji, ina sonkine da yawa shiyyasa bazan juri ganinki da waniba ballema maƙiyina Bilkisu...”
Ya ƙare maganar a hankali yana matsowa jikina sosai, gabana ne ya shiga faɗuwa, nai ƙoƙarin ja da baya amma sai hakan ya gagara saboda riƙon da yaymin bana wasa bane, sannan ƙarfina da nasa ba ɗaya bane, matsananciyar rawa jikina na fara sabida ƙoƙarin kawo fuskarsa kan tawa da yake, na shiga girgiza masa kai ina hawaye, roƙonsa nakeson yi, bakina sai motsawa yake amma na kasa furta komai, ya riƙe kaina da ƙyau yana ƙoƙarin ɗora bakinsa kan nawa na ƙwalla ƙara.
Da sauri ya sakeni shima yaja baya saboda tsorata da ƙarata, jikina sai ɓari yake na tashi a guje na shige toilet ɗina na banko ƙofar harda murza key. ‘innalillahi wa inna ilaihirraji'un’ naketa ambata, wace irin masiface kuma wannan ni Bilkisu, kuka na shiga rusawa a bayin sosai, duk da inajin ƙwanƙwasa ƙofar da yaketa famanyi yana kiran sunana da bani haƙuri banko tankashiba, kusan mintuna talatin naji shiru alamar yabar wajen, ban buɗe ƙofarba har sannan sai bayan wani lokacin sannan na buɗe kaɗan na leƙa, babu kowa a ɗakin saima ƙofa dana gani buɗe alamar ya fita, komawa nai toilet ɗin na ɗauro alwala na fito, sai da na sakama ƙofar key kafin na tada sallar isha'i.
Haka nai kwanciyata da yunwa ban fitaba duk da inajin motsin su mom da suka dawo kusan ƙarfe goma, ina idar da sallar asuba nai shirin barin gidan, dan gwarama na shiga gidansu Amina daga baya sai na wuce wajen aikin, bazanbi yah Qaseem ba. Sauri-sauri na kammala na fito, gabana ya faɗi ganinsa zaune a falo yana shan shayi alamar dai shima harya gama shirinsa, yanda ya tsatstsareni da idanu kuma ya sakani tsayawa cak nai ƙasa da kaina, “Kizo kisha shayi mu wuce, dan sauri nake yau”.
Bance dashi komaiba na wuce zuwa kicin, kaɗan na haɗa tea a kofi na zauna a kicin ɗin ina sha, dan kuku ma bai kai ga fitowaba, saurin kallon ƙofar nai jin an shigo, nai masa kallo ɗaya na ɗauke kaina gefe, baice komaiba nima banceba, sai ajiye kofin da nai na nufi ƙofa, matsawa yay ya bani hanya, a ɗarare na raɓashi na fita yabi bayana.
Badan raina yaso ba na shigar motar Yah Qaseem yau ɗinnan, shiru motar babu mai cewa komai ni da shi, ko redio bai kunnaba, tuƙi yake a hankali kamar bayaso, mun ɗanyi nisa da gida ina lafe a jikin kujera da karanto addu'ar neman tsarin ALLAH daga shaiɗanin dake ingiza zuciyar yah Qaseem ga abinda bai daceba gareni naji motar kamar ta tsaya, idanuna dake cike da barci na buɗe, naɗan waigo na kalleshi, ganin ni yake kallo sai na janye idanuna ina sake gyara zama, wlhy bazan ɓoye mukuba a tsorace nake, bani da ƙarfin dazan kare kaina ga murɗaɗɗan namiji irin yah Qaseem koda ace yay shirin cutar da nine, cikin dauriyar dole nace, “Yah Qaseem lafiya muka tsaya?”.
Ajiyar zuciya ya sauke a hankali, har lokacin inajin idanunsa na yawo a kaina, sai dai baice komaiba, kusan mintuna biyu suka sake shuɗewa, a bazata na tsinkayi muryarsa, yace, “Kiyi haƙuri Bilkisu akan abinda ya faru jiya, banyi hakan da niyyaba tunda kinsha faɗamin baƙyaso”.
Ajiyar zuciya na sauke inajin daɗin kalamansa, na share hawayen da suka zubomin, ba tare dana kallesa ba nace, “Na haƙura Yah Qaseem, amma dan ALLAH ka rufamin asiri, kaji tausayin maraicina ka barni da mutuncina, gidanku itace mafakata ta ƙarshe da nake alfahari da ita, idan shaiɗan ya lulluɓe maka ido ka tuzguɗemin ita bansan ina zan dosaba, haramunne a addininmu, sannan cutarwace a garemu, wannan ba shi bane soyayya kamar yanda yake a tunanin yahudu da nasara, ƙoface kawai ta saɓon UBANGIJI, kuma tushen fasiƙanci, daga kama hannuna da kakeson yi a koda yaushe matsala zata fara, tun inaji banason hakan wataran sai kaga shaiɗan ya ƙawatamin nafara jin daɗi, a tafi matakin sumbata, makulin buɗema shaiɗan ƙofa kenan da komai na baɗala zai iya wanzuwa tsakanin namiji da mace, duk takatsantsan ɗinmu wataran kafin mu farga sai akai ga aikata zina, ‘Wa'iyazubillah’. Yah Qaseem namiji da mace duk hukunci ɗaya garesu wajen ALLAH idan suka aikata zina, amma a zahirance ta rayuwar duniya mace itace ke fara ƙasƙanta a idanun al'umma makusantanta dama na nesa da ita, domin itace ke ɗaukar ciki, itace wasu almomi ke fara bayyana a gareta, farko rasa mutunci, ƙasƙanta mutincin gidansu dama ahalinta, tabon da zaita bibiyar rayuwarta har ƙarshen zuri'arta, ita ake fara aibantawa kafin abokin tarayyarta, itace ke rasa mijin aure, ita akafi nunama ƙyama, itace keda rauni. Abin tausayi da tashin hankali ƴa mace na fuskantar waɗanan matsalolin koda ace fyaɗe akai mata. Yah Qaseem indai sona kace da gaske dan ALLAH ka daina min waɗanan abubuwan, wlhy banaso, basa burgeni......”
Qaseem yaja wani bahagon numfashi saboda tausayi da bily ta bashi, harga ALLAH sonta yake da gaskiya ba yaudaraba, ALLAH ne ya jarabcesa da sonta batare daya shiryama hakanba, yanda take kuka sai ya kumajin tausayinta sosai a ransa, murya a sanyaye yace, “Na fahimceki Bilkisu, insha ALLAH kuma zan kiyaye, idan kin amince zanma Dad magana akan aurenmu”.
Sauran hawayena na share tare da kallonsa, ganin ni yake kallo sai na ɗaga masa kai alamar na amince. Ya saki wani murmushi najin daɗi yana sake tsatstsareni da idanunsa farare tas, a hankali ya furta, “Inasonki da yawa Bilkisu na, gara dai nayi na mallakeki kusa dani na huta da wa'azinnan”. Murmushi nayi ina ɓoye fuskata, shima yay ƙaramar dariya yana mai tada motar muka cigaba da tafiya. Hira yaytamin har muka ƙarisa station ɗinmu duk da ba amsa nake bashiba sai dai eh ko a'a da murmushi kuma.
BAYAN KWANA UKU.
A kwanaki ukunnan Boss bai sake shiga harkataba, harna ɗauka gargaɗin Yah Qaseem ne yasa ya barni, tunda ina ganin dai yana sama dashi. Shima a ɓangaren Yah Qaseem na samu sauƙin yawan kai hannunsa jikina da yakeyi, sai dai wasu take-taken Yah Salman a gidan yanzu suke cazamin kai, ya masifar samin idanu, kowane motsina sai ya tanka magana a kai, Aunty Shahudah cema naga dai tayi sanyi, bansan mike damuntaba, amma saina lura kamar bata cikin nutsuwarta.
Ban sake cema baba maigadi komaiba game da zancen Amina saboda saka idon Yah Salman a kaina, amma inata wasu shirye-shirye a gefe nabin matakan da zan gano bakin zaren, dan abinda baba mai gadi yayi ranar yana nan tsaye cak a zuciyata bai gogeba. Da wannan tunaninma yau na fita wajen aiki.
Tunda muka dawo sallar zuhur muna a office ɗinmu da boss ya dunƙulemu, kowa yana hidimar aikin daya dace, yayinda Ni da Ummie muna aikine muna ƴar hirarmu data shafemu, hakama sauran kowa nayi da abokin maganarsa, hakanne yasa ɗakin ɗaukar kananun surutai sama-sama. A bazata naji office ɗin ya ɗauki shiru tamkar ruwa ya cinye kowa, batare dana ɗagoba nai ƙaramar dariya ina faɗin, “Ummie mutuwace ta gitta a office ɗin namu ne?”.
Shiru naji Ummie batace komaiba, hakanne ya sani ɗagowa a tunanina batajini ba.
‘kutumelecy’...............✍
Assalamu alaikum.
Inason naɗanyi bayani da nake fatan a fahimceni, akan maganar aikinsu Jawaad, inason mai karatu ya fahimci wani abu anan, aikin da muka dangantasu dashi bawai yana nufin ainahin abinda ya shafi ma'aikatan zahirin bane, bamusan komai da ya shafesu ba, tayaya zamuce komai nasu sai ya shigo labarinmu, domin ba'akan hakan muke rubutu ba, da yawanmu ma idan za'a tambayemu bazamuce munsan waɗanan ma'aikatanba kai tsaye, domin su aikinsu bawai a bayyane yakeba kamar ƴan-sanda da dai sauransu da suke cikinmu ba, aikine na wanda kai kanka idan ba wani daliliba bazaka taɓa ka gansu suna yawo gama gari ba ko wani aikinsu a bayyane, so na danganta waɗanan jaruman littafine da hakan saboda mutunci da himma da ƙwazo na irin jami'anmu da mu kanmu bamu saniba, matasanmu kuma su zama masu himma dason bama ƙasarsu gudunmawa da zuciya ɗaya a kowace ƙasa suke ba lallai sai tamu ba, tom inaso ku kalli wannan kawai a matsayin labari bawai lallai abinda yake a zahiri ba, ko yake lallai mu bibiya, matsayinsu, misukeyi? Mizasuyi? Duk iyakarsa labari irin na marubuci {ƙirƙira}, bani da hurumin shiga abinda bani da lasisi a kai, domin bamma sani ba, waɗanan jami'an littafine bawai na zahiri dake aiki a ƙasarmu ba, idan kun kula sam babu wani sunan gari dake nunama a ina suke, ko a wane waje suke, musa a ranmu kawai ƙirƙirarren labari muke karantawa, ilimantarwa, nishaɗi, da faɗakarwa, ba akan kowaba, domin ba'akan kowan mukeyi ba, duk abinda zamu iya ganin yaci karo da waccan rayuwar ta zahiri to kawai fiƙira ce irin ta marubuci bawai dan inada ilimin sani ba ko bibiya balle bincika, ina fatan duk wanda ke bibiyar wannan littafi a ko'ina yake zai kasance maiyin ƙyaƙyƙyawan fahimta akan inda muka dosa, sannan abinda kake ganin na karkace ko shiga hurumin da banawaba ina fatan zakuyi gaggawar dawo dani hanya, ALLAH yasa mu dace, ALLAH kuma ya ƙarama dukkan jami'an tsaronmu lafiya da ƙwazo da nagarta a duk duniyar da suke.🙏🏻
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻
Bilyn Abdull 📚:
Page 10
............‘Kutumelecy’ na faɗa a cikin raina ina saurin janye idanuna dana ware a kansa da tsaida taunar cingam ɗin da nakeyi lokaci ɗaya, ganin yanda ya tsatstsareni da muggan idanunsa. Zungurin ƙafata dana ɗora saman tebir ɗina Ummie tayi.
Kallonsa na sake sata sai naga shima idanunsa yanzu akan ƙafar tawa suke harma da sauran ƴan uwana, da sauri na sauke ƙafar ƙasa na nutsu kamar yanda kowa yayi. Bai tankama kowaba ya ida takowa tsakiyyar ɗakin yana binmu da kallo daki-daki, har tsawon mintuna biyu muna a haka tamkar ɗan doka da ƴan gidan kallon ƙwallo ko ɓarayin agwagi, nidai sai faman jan addu'a nake saboda jin yanda zuciyata ke bugawa da sauri-sauri tamkar ko yaushe idan na samu kusanci da shi.
Ganin bazai tankaba sai muka shiga gaisheshi ɗaya bayan ɗaya, hannu kawai yake ɗaga mana amma bai sake kallon kowaba baikuma amsa mana da bakiba. Yaja kujerar dake gaban tebir ɗin Uchie ya zauna, bamusan mi suke tattaunawaba har kusan tsawon mintuna sha biyar kafin ya miƙe ya fice. Yana fita muka shiga sauke a jiyar zuciya, yayinda wasu suka shiga gulmarsa musamman ma matan cikinmu, nidai sabon cingam na ɓare na jefa a baki na cigaba da sabgar gabana.
________________________________
A gidan su Jawaad kam taron meeting Mom ta tara da ƴan uwanta, sunɗau tsahon lokaci suna tattaunawa akan Jawaad da maganarsa da Shahudah, duk da dai da farko Uncle Nasir yaso bijirewa, a cewarsa suma sunada ƴaƴan da zasu bama Jawaad ɗin ai ya aura. Shahudah ta kiya musu hankalin da bai kamata su sake sakata a sabgarsu ba.
Kuka mama Atika ta fasa musu, tare da ɗakko musu maganar data saka suka nutsu waje guda.
“Munsan Sabira tayi laifi da tafka kuskure a baya, amma kuyi haƙuri munada tabbacin zuwa yanzu ta magantu za'a samu gyara musamman idan mukai dubi da yanda take son yaron, amma ni na yarda da shawarar Nasiru, mu fara ma Jawaad maganar auren wata a cikin yaran gidannan, idan ya nuna rashin amincewa saimu tirsasashi ya maida Sabira ɗakinta, dan baikamata mu zubamasa ido yana yawo sakaka babu aureba, shekararsu kusan biyar kenan da rabuwa, amma yaƙi aure, inba neman matan banza yaron nan yakeba yaza'ai mutum mai lafiya kamarsa ace yanaƙin aure?, su waɗancan dangin uwar tasa sakarkaru da yake tsoronsa sukeji sun gaza masa magana kuma, tomu bai kamata mu saka masa idoba, dan kuwa mune duniya zata zaga basuba, amma yaya kuka gani? Danni dai shawarace na kawo matsayina na uwa a gareku, da Badiyya nada isashiyar lafiyama tare zamuyi muku, yanzu saiku zauna ku yanke shawara a tsakaninku” ta ƙare maganar da tashi ta fice daga falon.
Duk binta sukai da kallo harta fita, Uncle Sulaimam ya sauke numfashi yana faɗin, “Nidai ƴan uwana na yarda da maganar mama, dan nidai zaman Jawaad bayamin daɗi a haka, da Abdul-aziz nada rai bazai zubama gudan jininsa ido kamar yanda mu muka kasa riƙe amana mukaiba, duk da bana zargin Jawaad da neman mata, dan mu shaidane akan tarbiyya da sanin yakamata na yaron nan”. Duk shiru sukai basu ce komaiba, wasu na hararsa ta gefen ido wasu na ƙunƙuni a cikin rai, dan suma sunsan ƴaƴan Mama Badiyya sam nasa tare da burinsu a gidan, su kaɗaine masu ƙaunar Jawaad dan ALLAH badan dukiyarsaba. Jin shirun yayi yawane ya saka Mom yin magana. “Nima na aminta da maganar mama, kuma ina goyon bayan ɗan uwana Sulaiman”.
Daga maganar Mom sai kowama ya fara faɗar abinda ke ransa, daga ƙarshe dai suka ajiye shawara akan zama da Jawaad ɗin idan ya dawo aiki da wuri yau, kokuwa weekend idan ALLAH ya kaimu.
_________________________________
A makare yau Jawaad ya tashi a wajen aiki, saboda fitar da sukai shi da Hafiz zuwa wani waje da yamma, basu dawoba sai bayan magriba, akwai abinda zai ɗauka a office shiyyasa suka dawo, amma da daga inda sukaje gida zai wuce. Bayan ya tattaro abinda zai ɗakko a office ɗin nasa sai yaga lokacin sallar isha'i ma yayi, dan haka suka tsaya sukai a station ɗin.
Koda suka fito yunwar dake cin cikinsa yasa yace su tsaya wajen wani haɗaɗɗen gashin kaji, gimba ya amsa masa da girmamawa. gimba ne ya fita domin
amsowa, kasancewar wajen ba baƙonsu bane akaima gimba tarba ta sanayya, kamar yanda Jawaad ya bashi umarni takeaway biyu akayi sai fura da yogurt masu sanyi aka saka ɗaɗɗaya a ciki, gimba ya bada kuɗin sannan ya dawo mota suka ƙarasa gida.
Ganin da sauran mutane da keta shigi da fici a sassan gidan sai ya bashi mamaki, a ganinsa dai tunda anyi addu'an bakwai mikuma mutane keyi tunda ba taron biki bane. Saurin kauda abin yay a zuciyarsa dan a ganinsa hakan ba huruminsa bane, yaso shiga sashen Uncle Usman ya gaida Mama Zainab matarsa kamar yanda yakeyi kullum tunda akai rasuwar, sai dai a matuƙar gajiye yake, ga masifaffiyar yunwa dake cin hanjinsa.
Tare suka shiga sashensa da gimba dake ɗauke da tarkacensa, bayan ya ajiye masa a falon ƙasa yay masa sallama ya fita, shima bai iya ƙarasawa bedroom ba ya yada zango a falo, sai da ya huta na wasu mintuna sannan ya miƙe ya haura sama, duk da yana buƙatar fara cin abinci haka ya daure, dan shi mutumne mai yawan cin abinci, idan bai samu bane dai yakanyi haƙuri kawai. Ɗakin barcinsa ya ƙarasa ya watsa ruwa, kusan ƙarfe tara ya fito tsaf dashi sai baza ƙamshi yake. Ya shiga kicin ya ɗakko kofi da filet, a falon ƙasa ya zauna ya kunna tv domin kallon labarai, yana kallonne yana cin abinci, lokaci-lokaci kuma yakan amsa waya idan an kirashi, ya daɗe zaune a falon har aka kammala labaran kafin ya miƙe yay ciki dan yana matuƙar buƙatar hutawa.
SHAHUDAH
Saboda son haɗuwa da Jawaad yasa yau taƙi binsu Mom gida, a cewarta nan zata kwana, Mom bata hanata ba, suka tafi ita da Aamilah kawai saboda Salman ne yazo ɗaukarsu dama ba driver ba.
Wajen ƙarfe goma ta kammala kwalliyarta, tai shiga cikin kayan barci masu taushi da ƙyau, dan sunyi masifar fidda mata surarta, sai ƙamshi take kamar jikar gidan mai turare, a ranta ta ƙudiri aniyar maido hankalin mijinta kanta yau, dan ta gaji da wannan wasan ɓuyan da sukeyi, ta kuma shirya karɓar cikin da yake buƙata. (Karku manta Shahudah batasan Jawaad ya saketa ba fa😥🤦🏻, ɓoye mata shine kuskuren dasu mom suka tafka).
Hijjab ɗin mama Atika da ya kai mata har ƙasa ta ɗauka ta saka, babu kowa a sashen na mama Atika, itama tayi barci ma tun ɗazun, kai tsaye Shahudah ta nufi sashen Jawaad tanata zuba murmushi, dan ita kaɗai tasan abubuwan data shirya masa, yau ɗinan basai gobeba sai ta zautar da gayen nan, ta sake sakin tattausan murmushi lokacin data murɗa ƙofar taji ta buɗe. Jawaad ya manta shaf bai rufeba ya haye sama, sai da ta gama ƙarema falon kallo, komai tsaf tamkar ba namiji ke zauneba, tasan Jawaad yanada tsafta, sam bayason ƙazanta, duk jin kan nan nasa baya ƙyashin tashi yay shara yay morping wa sashen,, ya samu wannan horonne a zamansa da kakarsa Mama maryam, hatta da girki Jawaad ya iya, kawai rashin isashen lokacin kai ne ke hanashi yi. batasan miyasa bayason masu hidimaba. Ta sake sakin murmushi kafin ta fara taka steps ɗin a hankali tana wani yauƙi saikace tarwaɗa, a falo ta cire hijjab ɗin ta jefa saman kujera, ta kuma gyara rigarta da gashinta sannan ta nufi hanyar ɗakinsa.
Jawaad kam a gajiye yake matuƙa. hakan yasa yana shigowa bayan yay brush da alwala yay adduar barci ya kwanta, bai wani jima da kwanciyaba barci yay gaba dashi, fitilar gefen gado ce kawai a kunne, itama ta ɓangare ɗaya, hakan yasa ɗakin yay dim babu haske sosai, bai kumayi dunɗum ba. Shahudah data murɗa ƙofar ta shigo a hankali ta sauke ajiyar zuciya tana mai shaƙar ƙamshin da ɗakin keyi, komai na Bb'n ta daban yake dana kowa, bata ganin fuskarsa, dan ya juya ma ƙofar bayane, sannan ya lulluɓa da bargo saboda uban AC'n daya ƙure ɗakin da shi, ‘ko tsoron murama bayayi’ ta faɗa tana ɗaukar remote ɗin acn ta rage ƙarfinsa.
Jawaad da baisanma hidimar da akeba barcinsa yake hankali kwance da mafarki mai daɗi, hakan yasa yaketa faman sauke numfashi a hankali. Ya sauke ajiyar zuciya lokacin da Shahudah ta hawo gadon a hankali ta kwanto bayansa bayan ta ɗaga bargon ta shiga, itama ajiyar zuciyar ta sauke ƙwallan kewarsa na taruwar mata a idanu, jitake tamkar ta haɗiyesa ta hutama kawai. Cikin salon data shirya masa a wa
nnan dare ta fara yawo da hannunta a jikinsa, Jawaad dai bai motsaba, amma da alama jikinsa na karɓar saƙwannin Shahudah kamar yanda tai fata. Mafarkin da Jay keyi da saɓanin Shahudah yay dai-dai da abinda take masa a zahiri, hakanne yasa ta samu haɗin kan gangar jikinsa har takai ya gyara kwanciyarsa yana sake rungumeta, hakan yayma Huda daɗi kuwa, ta ƙara ƙaimi kan abinda takeyi, kamar wasa saiga tafiya tayi nisa a tsakaninsu, dan tuni ya fara maida mata murtanin sumbatarsa da takeyi.
Yanda take sauke numfashi ne da sauri-sauri akan fuskarsa ya sakashi farkawa, dan kuwa tabbas wannan al'amarin ya wuce a mafarki kawai, a matuƙar razane ya hankaɗeta daga jikinsa yana ambaton “Innalillahi wa-inna ilaihirraji'un. Wace ƴar iska ce haka ta shigomin ɗaki?”. Yay maganar yana ƙoƙarin kunna fitilar ɗakin.
Shahudah daya jefar gefe duk da taji zafi tai ƙoƙarin tashi zaune tana sauke numfashi a gwame, hasken daya gauraye ɗakin ne ya basu damar ganin juna. Kansa ya dafe yana ƙara ambaton “Innalillahi....” Shahudah ta matso jikinsa tana neman kwantawa a kafaɗarsa ya sake tureta a fusace, “Wai ke wane irin dabbanci ne wannan? shin baki da hankaline Hudah?”. Tabbas maganganunsa sun mata zafi, amma saita daure cikin dakewa da tsiwarta tace, “Dan nazo wajen mijina zakacemin banda hankali?, to ka ɗauka ni da kai duk mun zama mahaukatan”.
Karon farko Jawaad ya waro idanu waje, yace, “Miji!?, Hudah rashin ilimin addinin naki harya ƙara faɗaɗa haka? Kinga bani da lokacin wannan haukar tashi ki fitarmin daga sashe kafin na saɓa miki kamanni, kuma wlhy wannan yazama na farko na ƙarshe da zaki sake shigomin nan”.
Kuka Shahudah ta saki, ta nuna kanta tana faɗin, “Yanzu nan tsanar da kaimin bb har ta kai haka? To wlhy babu inda zanje, dan inada haƙƙi a kanka ai, duk ma abinda zakayi sai kaitayi, amma ka sani niba ƴar iska bace, amma wlhy da tuni naje na nema wani namijin a waj.......”
Mari ya kai mata tai saurin kaucewa, cikin daka tsawa yace, “Tashi ki fita a ɗakinan kafin na raba kanki da wuyanki wawuya kawai!!”. Saurin sauka tay a gadon, dan yanda ya harzuƙo ɗinan zai iya maketa, batasan ma bashi da wannan ƙarfinba a yanzu, dan ta sakashi a kwale-kwale. Da ƙyar Jawaad ya iya sakkowa a gadon saboda tashin hankalin da Shahudah ta sakashi, duk ƙoƙarin kame kansa da dauriyar da yakeyi yau ta kwanto masa liƙi, ya murzama ƙofar key ya dawo saman gadon jiki babu ƙwari. Gaba ɗaya kansa ya toshe, yama gaza yin tunani akan Shahudah.
Duk yanda Jawaad yaso yayi barci a wannan daren ya kasa, gashi maganin da yake sha ya barsa a office saboda ya ƙare ya sayosu jiya, sai kuma ya manta bai ɗakkoba, ya watsama jikinsa ruwan sanyi yafi sau shidda kafin asuba, sosai mararsa ke masa masifar ciwo, ko sallar asuba bai fitaba a ɗaki yayi, sai bayan ya idarne barci ɓarawo ya sacesa, shima a matuƙar wahale yayisa.
Shahudah kuwa da kuka rurus tabar sashen zuwa sashen mama Atika, a falo ta zube tacigaba da kukanta har barci ɓarawo ya saceta.
_______________________________
Yau ma har muka fito Office banga kowa a cikin ƴan gidanba, cikin nishaɗi muke ƴar firarmu da Yah Qaseem har muka iso, saida na rakashi har office da tarkacensa sannan na fito nima zuwa namu.
Ummie bata isoba, hakan yasa na zauna bayan mun gaisa da waɗanda na tarar, ƴan abubuwan da baza'a rasaba na shiga yi, gefe ɗaya kuma ina amsa hirarsu Dawood sama-sama akan aiki, a hankali mukaita ƙaruwa har kowa ya gama isowa, Ummie ta zauna saman tebirina tana faɗin, “Bily gulma da ɗumi-ɗuminta fa”.
Kallonta nai ina faɗin, “Ƴar sa ido mikika samo mana?”. Ƙaramar dariya tayi da sauke murya ƙasa tace, “Ankawo kuɗin Nazifa”. “Dan ALLAH da gaske?” nai maganar cikin waro ido waje bakina washe da fara'a. Ummie tace, “Wlhy da gaske nake, kema tace ta kiraki bai shigaba, amma ta tura miki saƙo ai”. Wayata na ɗauka ina faɗin, “Kashewa nai da zan kwanta, tunda na tashi kuma ban buɗe data ba, oh ni su Nazifa an mana wayo, da Al-mustaphan dai?”. “Shi kuwa” cewar Ummie tana dariya.
Fita mukai zuwa can baya nai
kiran Nazifa a waya, bugu biyu ta ɗauka tana faɗin, “Inba gulmaba Bily miye na kirana da farar safiyarnan?”. Dariya mukai ni da Ummie, nace, “Ai gara dai muci gulmar da ɗuminta basai ta huceba, yarinyarnan da gaske dai kin dage aure kikeso?”. “Ban isa bane?” Nazifa ta faɗa tana dariya. “Kin isa kuwa tsaf” Ummie ta bata amsa. Haka muka cigaba da hira cikin so da ƙaunar juna har bamusan lokaci yaja ba.
Daƙyar muka iya katse hirar muka koma office gudun kar'a nememu.
JAWAAD
Kamar da wasa ƙaramar magana ta zama babba, dan kuwa dai daga kwanciyar da Jawaad yay bayan sallar asuba sai zazzaɓi mai azabar zafi ya rufesa, duk yanda yaso ƙoƙarin tashi yay shirin office lamarin ya gagara. Wani wahalallen barcin nema ya sake awan gaba dashi bayan ya koma saman gado yaja bargo.
Gimba yay shiri da wuri kamar yanda yasan suna sammakon fita, sai dai yafi tsayuwar awa guda wajensu baba maigadi babu alamar boss ɗin nashi, dama kuma bai gansa a massallaci ba yau da asuba. Bai dai tambayi kowaba ya cigaba da jira har zuwa ƙarfe tara, zuwa lokacin dai kam abin ya fara bashi mamaki, abinda zai riƙe boss har ƙarfe tara bai fita office ba to lallai dole ya saka kokwanto a zuciyar duk wanda yake tare da shi, wayarsa yay kira har sau uku ba'a amsaba, ya sake daurewa dai ya zauna awa ɗaya ta kuma shuɗewa goma tayi. Yanzu kam tilas ya miƙe ya nufi sashen, yay knocking har kusan sau goma baiji motsin kowaba, hakan yasashi murɗa ƙofar, cikin sa'a kuwa ta buɗe, sai dai koda ya shiga babu kowa a falon, babuma alamar wani ya fito cikinsa. Nan kawai yake da hurumin shiga dan haka bai ƙara gaba ba ya juya ya fita. Yabar wayarsa a mota har baisan su Oga Aliyu nata kiransaba suma jin Boss baizo office ba, sun kuma kira wayoyinsa duka babu wacce ya ɗaga, shine suke kiran Gimban suji ko wani waje sukaje? Amma shima kuma bai amsa musu ba.
Misalin sha ɗaya da wasu mintuna sai ga Nabeelah da Ummansu sunzo gidan domin sake yima mama Zainab gaisuwa, dan rabonsu da gidan tun ranar rasuwar. Bayan sun shiga sashen mama zainab sun fito sai suka shiga wajen mama Badiyya don su gaisheta da jiki, basu jimaba suka fito zuwa sashen mama Atika, ananne suka iske Shahudah babu lafiya, tana kwance cikin doguwar kujera lulluɓe da bargo, sun mata addu'ar samun lafiya suka miƙe zasu tafi amma sai mama Atika ta tsaidasu da zancen auren Jawaad, murmushi Ummah tayi kawai, tabama mama Atika haƙuri akan zasu masa magana, baki kawai mama Atika ta taɓe, su Umma kuma suka fito abinsu Nabeelah nata ƙunƙuni akan ansama yayansu ido. Basuyi zaton samun Jawaad a gidaba, dan haka sukai yunƙurin barin gidan, Gimba daketa dakon jiran fitowarsu yay azamar isowa garesu yana gaida Umma, da mamaki ta amsa masa, “A'a gimba baku fita office bane ko dawowa kayi kai?”.
“Wlhy mama bamu fitaba, har yanzu boss bai fitoba, bansan ko lafiya ba? Nai knocking na kirashi amma duk babu wani amsa”.
Shiru Ummah tayi na wasu sakanni, sai kuma ta fasa shiga motar ta nufi sashen Jay, Nabeelah ma data tuƙosu harta shiga mota ta kunna ta kashe ta fito tabi bayan Ummah.
________________________________
kasancewar juma'a ce yau ɗin bayan an sakko salla mun fito zamu fita neman abinci saboda yunwar da nakeji mukaci karo da Oga Jabeer zai shiga mota, har mun gaishesa munwuce sai kuma yay kirana. Dawowa nai ina amsa masa da girmamawa, yace, “Shigo mota ki rakani wani waje”.
Duk da banso ba sai ban masa musuba na shiga Ummie kuma ta wuce tana min dariyar mugunta............✍
“Saura muji wani yace Hudah🙄 ehe😏.
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
Bilyn Abdull 📚:
Page 11
...............Tafiyar da batafi mintina talatin ba muka iso inda ya bani mamaki, bandai cema oga Jabeer komaiba har aka buɗe mana gate muka shiga. A dai-dai sashen da mukai salla ranar rasuwar Uncle Usman yay fakin, ya kashe motar yana faɗin, “Muje ko”.
Bance komaiba na buɗe murfin na fita kamar yanda shima yayi, yana gaba ina biye da shi har zuwa ƙofar falon, sai kalle-kalle nake ina ƙara jinjina girman wannan gida, koba'a faɗaba kasan an narkar da dukiya wajen ginashi, Oga jabeer ne yay knocking, babu jimawa akazo aka buɗe ƙofar.
Cikin murmushi Nabeelah data buɗe ƙofar tace, “Yah Jabeer sannu da zuwa”. “Yauwa Nabeelah” ya amsa yana mata murmushi shima. Sai da ya shige sannan ta ganni, cike da mamaki ta waro idanu alamar ganina a bazata da tai, kafin ta daka tsalle ta ɗaneni tana dariya, “Lah ƙawata dama rai kanga rai?”. Murmushi nayi ina mai jinjina wautar Nabeelah a raina, cikin surutunta tace, “Dama kinsan Yah Jabeer?”. Amsa na bata da cewar, “Eh, wajen aikinmu ɗaya”. Zata sake jehomin wata tambayar Jabeer ya katseta, “To Akku mai bakin magana kaimu ɗakin da yake”.
Yanda tayi da fuskane ya sakani yin murmushi, ita a dole taji haushin ance mata Akku, hannuna ta kama tana tuttura baki gaba tai mana jagora har sama, bansan minene ya kawomuba balle tunanin wajen wa mukazo, ni dai kawai inabin Umarnine. ‘Tabɗi’ na faɗa a raina saboda ganin yanda falon saman ya haɗu matuƙa shima, sai sassanyan ƙamshi ke tashi, muryar kamilar mace ta amsa mana sallamar da mukai tare da faɗin, “Jabiru sannunku, ku shigo mana”.
Oga Jabeer ya amsa da “Yauwa Umma, ashe kema kina nan?”. Tace, “Eh muma bamu jima da zuwaba, nazo na sakema Hajiya Zainab gaisuwane sai Gimba ke cemin basu fita Office ba, yanata jiran Jawaad ya fito bai fitoba, shinefa na shigo na iskesa kwance rijif cikin zazzaɓi”.
“Ya salam, wlhy muma a office tun ɗazu muke zuba idon ganinsa amma shiru, mun kirasa bai ɗaukaba hakama Gimba, tomu tunaninmu koma wani wajen sukaje tunda munga jiya lafiya lau yabar office, sai daga baya ne gimba ya kira yasanar mana ai baida lafiya, ko sallar juma'a ma da ƙyar in zai iya fita, shinefa nace bara mu sakko massalaci nazo naga jikin nasa, tunda su Hafiz sun fita wani aiki”.
Sosai gabana ya faɗi da jin sunan Boss a zancensu, harda ƙarin furucin rashin lafiya, banji amsar data bama Jabeer ba saboda tunanin dana tafi.......
Hannuna da aka riƙone ya katse mani tunani, na kalli Ummah data riƙonin nai ƙasa da kai ina faɗin, “Ina yini”. Ummah tace, “Lah kece Auntyna? Aini bamma ganekiba da farko wlhy nama zata Maman Areef ce (Matar Jabeer). “A'a Umma nice” na bata amsa kaina a ƙasa, kafin ta samu damar yimin tambaya Jabeer ya bata amsa da cewar, “A'a Umma ba Fannah bace, Mom ɗinmu ce, da alama ma kin santa kenan?”. Ummah tai murmushi tana zaunar dani a kujerar kusa da ita, tace, “Nasanta Jabiru, ƙawar Nabeelah ce ai, ina ka samo mana ita ne haka? Ko dai ta biyu ce?”. Yanzun kam ƙaramar dariya Jabeer yay yana girgiza kansa, “Wai Ummah ta biyu kuma? A wannan marrar ɗayarma ya aka ƙare, sai dai idan zaki nemarwa ɗanki ne, shine gwauro, wajen aikinmu ɗaya da Mom ɗinmu” ya ƙare maganar idonsa a kaina.
Dariya tayi tana sake riƙo hannuna, cikin sigar tambaya tace, “ɗiyata kina son ɗana?”. Kasa cemata komai nai sai ƙasa dana ƙarayi da kaina, a raina ina faɗin, ‘Ni inada Yah Qaseem ɗina’. Jin bance komaiba ta maida kallonta ga Jabeer,
Cike da mamaki tace, “Waima tsaya Jabiru, kana nufin itama irin aikin naku takeyi?”. “Sosaima kuwa Ummah” ya bata amsa cike da karsashi. Haɓa ta riƙe tana sake damƙe hannuna, “Oh ni ɗiyata, kekuma abinda ya burgeki kenan? To Nabeelah kinji fa jaruman mata, ba irinki matsoraciya ba” Nabeelah da mamaki ya kashe tace, “Wai dan ALLAH da gaske?”. Hararta Jabeer yay yace, “Da gaske mana”. Nabeelah tace, “Tab, wlhy bari Yah Jay ya warke nima ƴar sanda zan zama”. dariya Umma da Jabeer sukai mata, nidai na murmusa ina kallonta da faɗin, “Dakin burge kuwa, kinga ƙawata ta dawo kusa dani”. Da sauri ta cafe da faɗin, “Karki damu ƙawa in
a nan tafe, kam Nabeelah ƴar sanda, ashe zan ragargaji ƙattai”.
Jabeer yace, “ko kuma ke su ragargajeki ba”. Ɓata fuska tai da tura baki, “A'a wlhy Yah Jabeer kar kai min baki tun yanzu”.
Kafin ya bata amsa Ummah tace, “Kaga Jabiru kubar wannan ba gajiya zataiba, ku shiga yana ciki, amma ban saniba ko idonsa biyu dan Doctor ya saka masa ruwa tun ɗazun”.
Miƙewa mukai muna faɗin ALLAH ya bashi lafiya.
Oga Jabeer na gaba ina biye da shi har cikin ɗakin nasa da ya gama haɗuwa, babu wani datti balle tarkace, nayi zaton zamu sami matarsa a cikin ɗakin, amma sai naga shi kaɗaine kwance a kan gado lulluɓe da farin bargo, hannunsa ɗaya liƙe da ruwan da ake saka masa, ya ɗora ɗayan saman cikinsa, fuskarsa tayi wani irin fayau alamar yaɗan rame. Yauce rana ta farko dana iya masa kallon kai tsaye kuma na tsawon mintuna, ƙyaƙyƙyawane, komai nasa dai-dai da fuskarsa.........
“Momcy zauna mana” Oga Jabeer ya faɗa cikin katsemin tunani, kaina na jinjina na zauna saman stool ɗin daya ajiyemin kusa da gadon kaɗan, shi kuma ya zauna a bakin gadon kusa da shi, hannu yakai saman kansa yanason jin yanayin jikin nasa, ni dai ɗauke kaina nai na maida wajen kallon ƙaramin hoton dake drawer gefen gadon, da gani tsohon hotone, ƙyawawan mata da miji da suke a ganiyar shekarun ƙuruciya, sunyi ƙyau sosai da dacewa da juna, ga hoton ya ɗauku duk da bana wannan zamanin bane.
Jawaad ya buɗe ido a hankali saboda hannu da Jabeer ya ɗaura masa a goshi, akan Bilkisu dake saitinsa ya saukesu, ya ɗan lumshe ya sake buɗewa akan nata, sunɗan kumburo sannan sun sake girma, daga ciki sunyi jaa kaɗa alamar dai bayajin daɗi. Jabeer ya kalla kafin ya sake maida idonsa kan Bilkisu, ya kuma janyewa yabi inda yaga idonta na kallo shima, hankalinta nakan kallon hoton Mamansa da Abbansa daya ajiye a bed side drawer, shima Jabeer kallon wajen yayi, amma a mamakinsa sai yaga Jawaad yakai hannu ya juya hoton. Murmushi Jabeer yay yana girgiza kansa.
Hankalina na dawo ganin an juya hoton, nai saurin bin hannun daya juyaɗin da kallo har zuwa fuskar mamallakin hannun, idanunsa a kaina suke, dan haka na janye nawa ina ɗan yamutsa fuska, a raina nace, ‘Baida lafiya ma bazai bar shegen kallon mutane ba’.
Jabeer dake binsu da kallo shidai yay ƴar dariya kawai, kafin yace, “A kacema ka warke mu tashi muje kawai?”. Harara Jawaad ya zuba masa, sai kuma ya miƙa masa hannunsa da aka saka ruwan, yay masa alama da ido akan ya cire masa. Kallon ledar ruwan Jabeer yay, yace, “Ya za'a cire bai ƙareba?, saura kaɗan ai, kaɗan sake haƙuri”. Jawaad da sai yanzune zaiyi magana ya yamutse fuska da motsa laɓɓansa a hankali saboda rashin jin ƙarfin jiki, “To sannu likita, kaga ni ciremin, dama Ummah ce ta takura aka sakan”.
Kafin Oga Jabeer yace wani abu na katsesu da cewar, “Ina yini, ya jiki”. Ban yarda na kallesa ba. hakan yasan bansan a yanda ya amsa minba.
Kallonta Jawaad yay ya janye idanunsa, akan laɓaɓansa yace, “Alhmdllh”.
Sallamar Ummah yasa duk muka kalli ƙofa, tace, “A ya ake cire ruwan bai ƙareba?”. Jabeer yace, “Wlhy Ummah kema ƙya faɗa, cayay a cire wai”. Ummah tace, “Kaci gidanku Jawaad, saurin mikake to? Duk abinka dai bazaka fita aikiba yau, dan a gidannan ma zan yini, dan karna tafi ka saci jiki kace zaka tafi ma agogo sarkin aiki”. Fuska ya ɓata, yace, “Kai Ummah ni nagaji da kwanciyarnan, kumafa naji sauƙi” “Haka mukeso dama ai kasamu sauƙin, amma babu inda zakaje, barama na haɗa maka ruwa kai wanka kaji daɗin jikinka”.
Yanda ya cuskule fuska ni saima yaban dariya, a raina nace ‘duk girman ɗa a gaban uwa shi yarone’ Har Ummah ta nufi haɗa masa ruwan sai naga kamar bai dace ba ina zaune na barta da aiki, miƙewa nai ina faɗin, “Ummah ki barshi bara na haɗa, inane bayin?”. Murmushi Umma tayi tana kallon Bilkisu da yaba hankalinta, tace, “To ɗiyata kuma Yayata nagode kinji, ga shinan shiga”. Kaina na jinjina mata na nufi inda ta nuna mani.
Jabeer da yaji daɗin abinda Bilkisun tayi yay murmushi yana kallon Jay, “Jay wlhy yarinyar nan tanada hankali”. Banza Jawaad yay m
asa tamkar baijiba. Jabeer yace, “Nasanfa kaji minace”. “Malam ka cikani da surutu, zaka fita a ɗakinan fa” dariya Jabeer ya kwashe da ita, dan shikam dai ransa na bashi abubuwa da dama. Idanun Jawaad dake harar Jabeer tamkar zasu faɗo ya nuna masa hanyar fita. Jabeer yace, “ALLAH babu inda zani, dama kasamu mukazo dubaka, bara na kira su Hafiz nace karma suzo ka warke”.
Koda na shiga toilet ɗin saida na tsaya nagama ƙare masa kallo, ‘Humm’ kawai na iya faɗa, dukda babu wani datti sai naga dacewar fara wankewa kafin na haɗa ruwan, cikin mintuna ƙalilan na gama tsaftace bayin kafin na haɗa masa ruwa mai zafi sosai, a ganina idan yazo bai masa dai-daiba sai ya sake sirkawa, lokacin dana fito iskesa nai zaune a bakin gadon, kayan barcine jikinsa farare, wandon dogo har ƙasa, hakan yasa banji na takuraba, maganar aiki sukeyi yanzunkam, sai dai shi yana dafe da kansa alamar yana masa ciwo ko yay masa nauyi. nace, “An haɗa ruwan”. Jabeer ne kawai yacemin “Sannu da aiki” shiko baima kalleniba ya miƙe ya nufi bayin yana tafiya a hankali.
Bayan shigewarsa Oga Jabeer ya miƙe yana faɗin, “Bara na sayo masa abu na dawo, kiɗan gyara masa ɗakin”. Kaina kawai na ɗaga masa dukda banso hakanba, sai mita nake a raina akan ‘to ina matarsa da ita bazatazo ta gyaraba, ni kofa haɗa ruwan wankanma dan naga Ummah ce zatayi, a matsayinta na babba kuma bai kamata na bartaba bayan ina zaune a wajen’ haka naita mita ina aiki, na gyara gadon tsaf tare da jera filolin a wani style mai ƙyau, nidai kawai nayine saboda inason gyaran gado dama can, balle irin wannan da yaji kayan shinfiɗa na alfarma, ga filos da yawa. Ina cikin gyaran gadon ne Nabeelah ta shigo da kayan shara. Tace, “Lah ƙawata daga zuwa dubiya sai a sakaki aiki? Ummah tace kije ki huta bara na gyara”. Murmushi na mata nace, “A'a ki barsa kawai, ɗakinma ai babu datti”. ƙasa tai da murya tana kallon toilet tace, “Yayanmu ba'ai masa abin arziƙi ai, kaɗan daga aikinsa ya fito ya sakaki wani aikin kuma”. Tabani dariya yanda takeyi tana kallon bayin, nace, “Dama ya fito ya jiki”. Kafin na rufe baki ta fice a ɗakin da gudu tana faɗin, “Saikin fito, dama girki nake masa”. Kaina na girgiza kawai naci gaba da aikin ina jinjina wautarta, gata dai zamuyi sa'anni, amma nakula Nabeelah autace kodan shiriritarta.
Har na gama gyara komai tsaf bai fitoba, na kammala morping tsaf kafin na ɗauka turaren ɗaki dana gani saman ƴar dirowar farkon shigowa ɗakin kala-kala, ɗauka nai nahau fesawa jikin labuloli da saman gado dama ɗakin gaba ɗaya, a bazata naji an buɗe ƙofar bayin, hakanne ya sakani kallon wajen babu shiri, ai kallo ɗaya nai masa na juya da sauri na nufi ƙofar fita ɗakin, gwangwanin freshener ɗin na ajiye na ɗauki bokitin danai morping nai waje abuna.
Jawaad dai yana tsaye a ƙofar bayin yana binta da kallo harta fice, shima baiyi zaton samun kowa a ɗakinba shiyyasa ya fito kansa tsaye, dukda ma dai sanye yake da rigar wanka a jikinsa ba towel ba, cikin rashin jin ƙarfin jiki ya tako zuwa cikin ɗakin, har yanzu mararsa a ƙulle take, dukda dai bakamar jiya da dare ba, da kuma safiyar yau, danma ƙin faɗama Doctor ɗin ainahin abinda ke damunsa yay, cayay kawai zazzaɓine ke damunsa, shi kaɗai yasan yanda yakejin haushin Shahudah da kuma matakin dazai ɗauka a kanta. Idanunsa suka sauka akan gadon da yanda akaima filolin, kasa ɗauke idanunsa yay har na tsahon mintuna kusan biyu, sosai gadon yay masa ƙyau, sai yaga tamkar ba gadonsa ba.
Tunda na fito Ummah keta faman jeramin sannu, ni dai murmushi kawai nake, na gyara falon saman ma duk da babu datti, falon ƙasa dai Nabeelah na iske ta gyara harma tana morping. Kiran da Umma taimin daga kicin na amsa, ta miƙamin ƙaramin tire data ɗaura kofin tea a kai yanata turiri, “Yauwa ɗiyata dan ALLAH miƙama yayanku wannan ya fara sha kafin wannan uwar shiriritar ta kammala girkin, daga nan sai kiji ko yana buƙatar wani abun kuma”. “To” kawai na iya ce mata na amsa na fito. Koda na fito sai na roƙi Nabeelah tazo ta rakani, catai ALLAH naje ni kaɗai, dan inhar mukaje mu biyu cazai anmasa gayya.
Badan nasoba
na nufi saman ni kaɗai, addu'a nake a raina Oga Jabeer yazo mu wuce. Sai da nai knocking ya bani izinin shiga sannan na shiga da sallama, kaina a ƙasa ban yarda na kalli ko inaba sai gabana, saida naje dab da shine sannan na kallesa sau ɗauya na ɗauke idona, har ya saka kaya, baƙin wando da yellow ɗin riga folo, yana zaune ne a bakin gado da waya a hannunsa, hannunsa ɗaya dafe da kansa yanzu ma, nidai na ajiye tiren a gabansa ina faɗin, “Gashi inji Ummah, tace kanason wani abune?”. Banji ya tankaba, bankuma damu da yace ɗinba dama na miƙe zan fita.
“Zonan” ya faɗa a hankali. Dawowa nai ina jan numfashina da ƙyar, dan duk a takure nake, danma zuwa yanzu kamar naɗan fara sabawa da kasancewarmu tare zuciyata ta sassauta min wajen bugun da takeyi idan har muna tare. Nace, “Gani”. Shiru yaymin kamar ba shine yay kiranaba, sai da yaja wasu sakanni kafin ya nunamin dogon table ɗin dake a gaban gadon ta gaba, “Ɗauka waɗancan keys ɗin, kije Gimba ya kaiki station, zaki ɗakkomin abu a office”.
Duk yanda naso daurewa sai da gabana ya faɗi, ta yaya zanje na buɗe office ɗinsa nikam? A matsayin wa? Na shiga uku, mutumin nan nason jefani a matsala shidai na lura......
“Miemaa!” ya faɗa a ɗan tsawace ganin dukma bayanin da yake mata hankalinta baya tare da shi. Firgigit na kawo numfashi tare da kallonsa, yanda ya danƙaramin harara ya sakani saurin duƙar da kaina. “Ina miki magana kina wani banzan tunani”. “Sorry sir” na faɗa da sanyin murya, dan harga ALLAH banji miya faɗaba”. Ƙaramin tsaki yaja, ya miƙomin waya batare da ya ce min komaiba, amsa nai ina jiran ƙarin bayani, amma sai ya shareni yama ɗauki tea ɗinsa ya fara sha.
“Tashimin a kai kafin na canja miki kalar fuskarki”. Fuska na kumbura na juya na fita ina ƙunƙuni a raina.
Jawaad dake binta da harara yay ƙaramin tsaki da faɗin, “Miskilar banza kawai”.
Banason zuwa ni kaɗai, hakan yasani cema Nabeelah tazo muje ya aikemu, da yake batasan gaskiyar zancenba sai ta bini muka bar Ummah na haɗa masa abinci. A jikin mota muka iske gimba da alamar yasan da tafiyar, zai buɗe mana mota nace ya barsa kawai, murmushi yayi ya shiga mazaunin driver yana tambayarmu “ya jikin boss ɗin” da sauƙi, muka faɗa kusan a tare sannan muka gaidashi.
Tunda muka tafi Nabeelah ke zuba mana surutu, Gimba nata biye mata, nidai murmushi ne nawa idan sunyi wani abun dariyar, har mamaki nake yanda Nabeelah bata gajiya da zance saikace wata akku.
Nidai har Gimba yay fakin addu'a nake ALLAH yasa karna haɗu da Yah Qaseem, gefe kuma ga maganar shiga Office ɗinsa bansan yanda za'a fassarani ba, sauƙinma na taho da Nabeelah ne, tunanin zuwa office ɗin Oga Aliyu ko Hafiz nayi, saisu kaimu office ɗin, a ganina hakan sai yafi, jan Nabeelah nai zuwa Office's ɗin nasu sai dai munyi rashin sa'a duk a rufe alamar bamasa station ɗin kenan................✍
“Team Bil-Qas & Jay-Hud. Saura wani yace sunan baiyiba😏😜😂”
Fatan alkairi a gareku baki ɗaya😍😍😘👌🏼
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
Bilyn Abdull 📚:
Page 12
.............Babu yanda na iya dole naja hannun Nabeelah muka nufi office ɗin, sai dai tunma a hawan farko aka dakatar da Nabeelah, ni kaɗai aka bari na wuce, kamar na fasa kuka haka naji, sai dai nayi mamaki a raina yanda babu wanda ya tambayeni mizanje yi?.
Office ɗin na nan tsaf, duk da yau ba'a gyaraba tunda baizoba babu wani datti, yau kam ban cuci kainaba saida nagama ƙare masa kallo gabas da yamma kudu da arewa, hatta da hotunan saman tebir ɗinsa sai da na gama kalleso, tsabar jan magana irin tawa na zauna saman kujerarsa ina gwada yanda yake zama, nakai kusan mintuna huɗu ina shirirtata kafin kira ya shigo wayar da ya bani, ƙurama wayar ido nayi tamkar mai tsoron ɗauka har sai da ta kusa katsewa sannan na ɗauka nasa a kunne batare da nayi maganaba. Daga canma shiru anƙi cewa komai harna tsahon sakanni.
“Baki iya sallama bane?” muryarsa ta daki kunnena a bazata, idanu na zaro waje dan wlhy banyi zaton shi bane, nace, “Sorry Sir” bai amsa minba sai cewa da yay, ki buɗe ƙaraman drawer na jikin table akwai faran leda da kwali a ciki ki ciroshi” na amsa da “to”. Ina ƙoƙarin jawo ledan kwalin ya fita a ciki, hakanne ya sani cirosu ɗai-ɗai shi da ledan, haka kawai na tsinci kaina dason karanta abinda aka rubuta a kwalin, dan da alama na magani ne, shaf na manta da wayar a kunne take bai kasheba, na hau karatun rubutun jikin maganin ina faman zaro idanu saboda fahimtar danai maganin na miye. Daga can Jawaad da yaji a jikinsa akwai abinda ta nutsu takeyi wanda ya ɗaura zarginsa akan maganin cikin sanyin murya yay magana saboda cikinsa dake murɗa masa a lokacin, “Bincike kike mini?” a bazata naji maganar tasa, shiyyasa na saki kwalin ƙasa batare dana shirya ba, cikin rawar baki, nace, “A...a'a sir” shiru Jawaad baice komaiba idanunsa a lumshe yana faman cizon lip ɗinsa na ƙasa, sai da ya lafa masa sannan ya sake maida hankali akan wayar, nikam duk a tsorace nake, gani nake tamkar ya gane mi nakeyi, cigaba yay da lissafo min duk abinda yake buƙata, na sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya jin yabar waccan maganar, na ɗauka kwalin maganin na maida a ledar ina cigaba da ɗaukar duk abinda yace, inda kuma ya faɗa anan nake ganinsa, bayan na haɗasu na zuba a wata leda baƙa na fito.
A ƙasa na iske Nabeelah ta cika tai fam da haushi, taban dariya, hakan yasa na murmusa ina kamo hannunta, ƙwafa tai tace, “ALLAH yayanmun nan ko, saina rama abinda yay min”. Nace, “Miyay miki?” ta sake yin ƙwafa, “Bakiga yasa a hanani shiga office ɗinsa ba, ALLAH nima duk randa na fara aiki bazan bari yazomin office ba”. Yanzunkam kasa jurewa nai saida na dara, “Oh Nabeelah yaushe ya hanaki shiga Office ɗinsa, jami'anmu dai sun hanaki”.
“Kutt wlhy bakisan halinsaba ne, nasan shine yace karsu barni”. Nace, “To kiyi haƙuri, Yaya yayi laifi”. Tunanin zamu dawo yanzu da oga Jabeer yasa ban shiga ko inaba, Mun isa wajen Gimba ya ɗaukemu muka koma, yanzu kam a falon ƙasa muka iskesu harda su Aliyu, mamaki ƙarara na gani a idanun Rose saboda ganina, a tare na gaishesu gaba ɗayansu na ƙarasa gaban sarakin dake kwance a doguwar kujera, cikin girmamawa na ajiye ledan da keys ɗin da wayar a table ɗin dake gabansa nace, “Gashi”. Idanunsa dake rufe ya buɗe ya zubasu a kaina, “Dama tare da Nabeelah na aikeki?” yay maganar yana hararata. Ƙasa nai da idanuna ina girgiza masa kaina alamar a'a. Ƙwafa yay ya ɗauke kansa, ganin hakan yasani barin wajen da nufin bar musu falon ma.
“Waye zai ɗauke miki kayan nan”. juyowa nayi, kafin na ƙaraso wajensa Rose dake zaune a kujerar dake inda ƙafafunsa suke ta miƙe ta ɗauki ledan da cewar, “Ƙyale shashasha boss ina za'a kai?”. Banza yay bai tanka ba, niko na sake juyawa zan fita. “K! Ina wasa dake ko?”. Nazata da Rose ɗin yake hakan yasa nai yunƙuri cigaba da tafiyata Aliyu ya kirani.
“Momi zoki amsa ki kai masa sama kinji”. “To” nace, na dawo na miƙama rose dake ɗauke da ledan hannu alamar ta bani, wata banzar harara ta zubamin ta dangwarar da ledar ƙasa ta koma ta zauna, bance da ita uffanba na ɗauka ledar da keys ɗin na nufi sama, dama duk abinnan da ake tuni Nabeelah ta haye tund
a muka shigo ta gaida su Hafiz ta haye abinta.
Bily na gama hayewa Jawaad ya miƙe cikin dauriya ya ɗauki ɗaya daga ruwan da aka ajiyema su Hafiz yabi bayanta yana tafiya a hankali, dan inhar yace zaiyi hanzari dolene a fahimci matsalarsa, ca yay musu yana zuwa. Rose ta bisa da kallo a wani irin yanayi maisa ƙuna a zuciya, a ƙufule ta kalli su Aliyu tana faɗin, “Wai miye haɗin wannan yarinyar da Boss ne?, shishshiginta yayi yawafa” dukansu da mamaki suka kalleta, duk da sun fahimci tsagwaron kishi tattare da zancenta, Jabeer ya kare bakinsa da hannu yana dariya ƙasa-ƙasa, sai da Hafiz ya hararesa sannan ya haɗiye da ƙyar, ya kalli sama sannan ya maido dubansa ga Rose data sake cika fam. “Wai Rose kina nufin sonta yake?”. Da sauri tace, “Itaɗin banza, kaima kasan Boss ya wuce da ajinta, kawai dai itace ke shishshige masa”.
Hafiz yace, “Humm” Aliyu dake murmushi ne ya bata amsa, “Toke tunda kinsan haka miye na damuwar, dan ya sakata aiki sai ya zama wani abu, sau nawa ke ya sakaki ayyuka da sukafi wannan?”. Baki ta taɓe, cikin hausanta da bawani fita yakeba tace, “Amma tunda muke nama taɓa zuwa nan gidan ne? Itako daga gani tana nan tun ɗazun”. Cike da jin haushi Hafiz yace, “To idan ya sakko saiki masa wannan tambayar kuma ai”. Harar Hafiz tayi, dan tun dama can basa shiri, baya shiga sabgarta sai dole, dama sunfi ɗasawa da Jabeer duk cikinsu, Aliyu kuwa baida yawan hayaniya, dan harma yafi Jawaad rashin son magana. Babu wanda ya sake cewa komai, sai Rose daketa kallon hanyar benen tana cika da batsewa da sauke tagwayen ajiyar zuciya.
A sama kuwa koda na isa Nabeelah na bama kayan akan yace takai masa su ɗaki, har Nabeelah ta amsa zata wuce sai gashi ya hawo, hakan yasani saurin riƙo ledan saboda wata uwar harara daya sauke min, Nabeelah ta juyo zatai magana itama ta samu rabonta na harar, sakarmin ledar tayi da sauri tana barin wajen, ni kam dai ƙasa nai da kai kawai.
Duk abinda sukeyi Ummah na zaune tana kallonsu, sai dai tayi kamar batasan sunayiba.
Jawaad ya wuce ɗaki batare da yace komaiba, dan shikuma baima lura da Ummah ba, bayansa nabi gudun karna sake wani laifin. baice dani komaiba harna ajiye ledan nai hanyar fita. Na sauke numfashi ganin na fito lafiya, a raina ina mitar ‘mutum sai baƙar takura’ matarka dai taga banu yasin, a can ƙasan raina kuma tunani nake yanada mata to miya haɗashi da shan magani irin wannan?, nifa dukma sai naji inajin kunyar abun yasin, nikam bazan sake yarda idona ya shiga cikin nashiba, wannan abun kunya har ina haka. Muna a falon Nabeelah na fama dani akan abinci data zubo ya fito, bai kalli kowaba a cikinmu ya sauka ƙasa.
Ban sakko ba har saida suka tashi tafiya Jabeer ya ƙwalamin kira, lokacin dana ƙaraso duk sun fice daga shi sai Jabeer ɗin, inda yake Jabeer ya nunamin alamar yana kirana, na ƙarasa gabansa dan yanzu ya tashi zaune, batare da ya kalleni ba yace, “Ranar lahadi ƙarfe goma na safe kije ku haɗu da wannan yarinyar, Jabeer zai baki address ɗin wajen”. nidai nace masa to ina jiran ƙarin bayani, sai dai bai sake cewa komaiba, oga Jabeer yace, “muje to, Boss ALLAH ya ƙara sauƙi”. “Amin” ya faɗa akan laɓɓa, nima nace ALLAH ya ƙara sauƙi nai gaba batare da jiran ya amsaba, dan yaban haushi.
Ni da Jabeer a motarsa muka koma, su Aliyu kuwa suna a motar Hafiz da sukazo a ciki, ina kallon yanda Rose keta bina da baƙar harara nai tamkar ban ganiba.
Munzo fita daga layinne naga motar Mom zasu shiga su kuma, nace, “Lah ga mom can”. Jabeer dake tuƙi yace, “Ƙila itama zataje ganin boss ne ko?”. Kallonsa nai nace, “ganinsa kuma? Wai da gaske Ƴan uwansu ne?” dariya yay yana harba motar kan titi, yace, “Momin mu kemafa na kula akwai shiririta wani sa'in, bakiga gidansu ɗaya bane, ai da mom da Abban Jay babansu ɗaya, sannan Jay shine ya auri Shahudah kafin su rabu”.
Mugun waro idanu nayi baki a hangame, nace, “Wai dan ALLAH oga kana nufin dama shine mijin aunty Shahudah?”. Jabeer dake murmushi yace, “Ƙwarai kuwa, ammafa a da kenan, amma ke yaya kuke dasu Shahudah da har bama kisaniba?”. Daƙyar na iya ce masa
kamar yanda Mom suke da Abban Boss, nima da Abbansu Aunty Shahudah da Mamana babansu ɗaya”.
Kai Jabeer ya shiga kaɗawa yana faɗin, “Tab cakwakiya kenan, kice shiyyasa Qaseem beson kowa ya raɓu dake? Kodai ƴar gida zamuyi?”. Murmushin yaƙe kawai nai masa bance komaiba, danni gaba ɗaya kaina ya toshe, koda wasa ban taɓa kawo cewar boss mijin aunty Shahudah bane ba, to yama akai na kasa fahimta? Koda yake bai taɓa zuwa gidanba ina nan, bankuma taɓa ganin koda hotonsa ba a gidan, amma kuma inban mantaba nasha jin sunan Jawaad a bakin ƴan gidan, ‘ya salam, miya toshe min kaina haka?’. Har mukaje station wannan tunani ne keta kaikawo tsakanin ƙwanyata da zuciyata batare da nasan ma'anar hakanba, shima kuma oga Jabeer bai sake cemin komaiba saima redio daya kunna.
Koda muka iso office nabi oga Jabeer kamar yanda ya umarceni, ya bani ƙaramar takarda ta address ɗin wajen da boss yace sannan na fito. Na iske su ummie sunata shirin tashi, dan biyar tayi, ALLAH ma ya soni nayi sallar la'asar yanzu da muka koma gidansu boss, nima ɗaukar tarkacena nai muka fito tare, dan Ummie zanbi, na leƙa office ɗin yah Qaseem bayan na fito daga wajen oga Jabeer na iske bayanan ya fita wai. Daurewa nai na cire alaƙar Aunty Shahudah da boss data tsayan a rai ba gaira ba sabar na biyema Ummie mukaita hirarmu, har gida ta kaini, sai dai bata shigaba iyakarta gate na sauka ita kuma ta juya.
Na iske su a falo aunty Shahudah kwance Doctor na saka mata ƙarin ruwa, ba hurumina bane tambayar abinda ya sameta, na gaishesu tare da mata sannu cikin jimami sannan na wuce ɗaki abina. Bansan miyasa na tsinci kaina cikin rashin jin daɗin komaiba, nai wanka na canja kaya, ganinma magrib tayi saina bari nai salla sannan nai zaman yin azkar har aka kira sallar isha'i, itama tashi nai nayi sannan na fito falon dan sake duba Aunty Shahudah, dan banajin yunwa, tun abincin da naci a gidan boss bai sauka ba, duk da saida Nabeelah ma tai fushi sannan naci bayan ummah ta saka baki.
Na iske aunty Shahudah ta koma ɗaki, sai yah Qaseem kawai a dining yana cin abinci, sannu da dawowa nai masa, yay murmushi yana min alamar nazo. Ban musaba naje garesa, naja kujera nima na zauna, “Kinyi ƙyau” ya faɗa yana kashemin ido ɗaya, murmushi kawai nayi bance komaiba. Haka yayta ɗan jana da hira harya kammala, ya miƙe domin zuwa yay wanka, nima miƙewar nai nace bara na sake duba aunty Shahudah naje na kwanta na gaji.
Zaune na isketa Aunty Aamilah na bata magani, na sake mata sannu da ALLAH ya ƙara sauƙi na fito, ɗaki na koma nai kwanciyata duk da nasan gobe idan ALLAH ya kaimu babu aiki, amma inason na kira Dad da safe idan ya bari sai naje gidan Inna Zainabu na gaishesu, da wannan tunanin barci ya kwasheni.
A ɗakin Shahudah kam bayan fitowar Bilkisu Aamilah ce ta sauke ajiyar zuciya tana mai fuskantar ƴar uwar tata da ƙyau. “Sister ga shawara mana” Shahudah da duk tazama kalar tausayi ta jinjina mata kai alamar tana saurarenta. Aamilah ta sake jan numfashi kafin tace, “Ina ganin yarinyar nan Bilkisu zamu iya sakata tai mana wani abu” murya a dasashe Shahudah tace, “Ban ganeba Aamilah ”. “Sister ina magana ne akan Brother Jawaad, da nayi tunanin Broth ne a farko, sai dai daga baya nasan bamai yuwuwa bane, musamman idan mukai dubi da yanda basama shiri tun suna yara, sam jinin Qaseem da Jawaad bai haɗuba, bankuma san lokacin dazai haɗunba, so idan mukace zamu ɗorasa akan ya taimaka mana sai dai ya ɓata komai tunda dama can bason aurenku yakeba, yanzu da yarinyar nan ta shigo, sai naga mizai hana mu amfanu da ita, dan kinsan bata da yawan hayaniya da surutu, sannan mutumin dake da irinki bazai kalletaba da sigar birgewa balle akai ga so, ballantana zuciyarmu tayi tunanin ko zata iya cin amanarmu, ko shi yaji wani abu a kanta”. Shahudah datai shiru tana kallon Aamilah tace, “Maganganunki kawai naji Aamilah, amma ban gane ina suka dosaba sam, wane taimko zamu nema akan Bb?”. “Yauwa, yanzu kikai tambaya mai ƙyau Sisi na, inaji a raina Yarinyar zata taimakemu, sai dai bani da tabbacin wajen aikinsu ɗaya, duk da dai naga kullum tare take fita da Broth, ku
ma Broth da Brother Jawaad wajen aikinsu ɗaya ne, amma wannan ba wani abu bane, zamu iya tambayarta”. Kai kawai Shahudah ta jinjina alamar gamsuwa, Aamilah tace, “ki kwanta ki huta zamu tattauna zuwa da safe, tunda weekend ne tana gida babu inda take zuwa”. Nanma da kai Shahudah ta amsa mata..
★★★★★
Washe gari da safe na tashi nai ƴan ayyukan dazan iya harda kayana da sukai datti, na gyara ɗakina tsaf nai wanka sannan na fito, babu kowa falon dan har lokacin ma bana tunanin wani ya tashi a jama'ar gidan, kicin na nufa na samawa cikina abinci naci, kafin na sake komawa ɗaki na shiga neman Number dad da ya kirani kwanaki uku da suka shige, kusan duk Numbers nashi na ƙetare inada ita, dan yakan kirani lokaci-lokaci idan yay tafiya tamkar yanda yakema sauran ƴaƴansa, bata shigaba, na sake gwadawa har sau uku saina haƙura, bazan iya zuwa ko inaba bayan wajen aiki saida umarninsa, dan banida wani jagora sama da shi a halin yanzu a duniya, sai ko yaya Qaseem da nake fatan ya zama na biyu a matsayin miji. Na aje maganar zuwa gidan Inna zainabu akan sai idan ALLAH ya kaimu gobe, idan naje inda boss yace na gama abinda nakeyi sai na shiga wajen wanke kai daga nan na wuce can koda ban jimaba sai na gaishesu na taho gida, da wannan tunanin na miƙe da nufin zuwa gidansu Amina.
Harna fice babu motsin kowa, muka gaisa da baba mai-gadi na fice abina. Da sallama na shiga gidan, Amina dake a tsakar gida tana wanke-wanke ta amsa tana kumbura fuska, dariya nayi ganin yanda tayi, dan nasan dalili, ta ɗauke kanta da faɗin, “Munyi fushi, ki koma a binki”. Kafin nace wani abu mama tace, “Kwarai kuwa Amina ina bayanki”. Kunnuwana na kama duka biyu na kneeling alamar dai na tuba, dariya suka sanya daga mama har Amina da yayan Amina daya fito da ga bayi, shine yace, “A ni dai na yafe ma ƴar ƙanuwata, nasan aikine ke mata yawa”. Nace, “Yauwa Yayanmu, shiyyasa nake yayinka a koda yaushe”. yay dariya da haɗe yatsun sa babba da manuniya alamar dai-dai👌🏼 kenan.
“Oh, mu baƙya yayinmu kenan? To kin ƙarama kanki laifi har tsallon ƙwaɗo sai kinyi” Amina ta faɗa tana miƙewa ɗauke da kwandon data saka kwanikan. Mama tace, “A'a auta nimafa na huce, ama mai-gadon lu'u-lu'u haƙuri”. Dariya muka saka gaba ɗayanmu saboda furicin mama, Amina tace, “Shikenan na haƙura tunda mama ta saka baki, amma da yau ɗinan saina tsamar da ƙafafunki”. Harararta nai kafin na zauna a inda ta tashi na gaida Mama da Yaya Sule, daga nan muka hau hirarmu.
Wajen sha biyu Amina na tayani tsifar kai muna hira, mama kuma nata ƙoƙarin ɗaura awara da muka tace da Amina bayan munje munkai markaɗe, nace, “Amina!”.
“Na'am” ta amsamin tana leƙo fuskata. Ɗalli namata a fuska da ɗan yatsa, ta matsar da fuskarta tana ɓata fiska saboda zafi, niko na kwashe da dariya, “Ke ɗince kin wani kawomin fuska saikace maison leƙa ramin gwal”. Dariya itama tayi tana ranƙwashina a kai, “Ai bazakici bulusba kuwa”. “ALLAH da zafi” na faɗa ina harararta” tace, “Nima ai naji zafin shiyyasa na rama”. “Ba komai zaki gane shayi ruwane. Maganarnance dai zamu sake”. Shiru tayi kamar bazatace komaiba, tsifar da takemin ma ta koma min ita a hankali, na zungureta da hannu dan nasan ta faɗa kogin tunanin nata. Numfashi ta kawo a hankali, tace, ”Ina saurarenki”.
“Amina, a zaman da kikai gidanmu na tsahon wasu shekaru, nasan zakisan halayyar kowa dake cikin gidan nan”. Tace, “Hakane” “Alhmdllh, mizan iya sani akan Qaseem da Salman?”. Shiru tai na wasu sakanni kafin ta sauke numfashi, “Duk abinda kikeson sani zan iya faɗa miki Bilkisu inhar na sanshi, wanda kuma ban sanshiba zance miki ban saniba, kimin tambaya zanfi fahimtar mikike son sani game dasu?”.
Cike da gamsuwar maganarta nace, “Hakane, Qaseem da Salman suna neman mata?”................✍
Asha weekend lafiya🤫🤭😉😍👌🏼
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻
Yau ƴan wattpad sai haƙuri yaƙiyi wlhy, da ƙyarma nai copy ɗin wannan a can ɗin, amma zan cigaba da gwada muga in za'a dace😔
Ra muka shigo ta gaida su Hafiz ta haye abinta.
Bily na gama hayewa Jawaad ya miƙe cikin dauriya ya ɗauki ɗaya daga ruwan da aka ajiyema su Hafiz yabi bayanta yana tafiya a hankali, dan inhar yace zaiyi hanzari dolene a fahimci matsalarsa, ca yay musu yana zuwa. Rose ta bisa da kallo a wani irin yanayi maisa ƙuna a zuciya, a ƙufule ta kalli su Aliyu tana faɗin, “Wai miye haɗin wannan yarinyar da Boss ne?, shishshiginta yayi yawafa” dukansu da mamaki suka kalleta, duk da sun fahimci tsagwaron kishi tattare da zancenta, Jabeer ya kare bakinsa da hannu yana dariya ƙasa-ƙasa, sai da Hafiz ya hararesa sannan ya haɗiye da ƙyar, ya kalli sama sannan ya maido dubansa ga Rose data sake cika fam. “Wai Rose kina nufin sonta yake?”. Da sauri tace, “Itaɗin banza, kaima kasan Boss ya wuce da ajinta, kawai dai itace ke shishshige masa”.
Hafiz yace, “Humm” Aliyu dake murmushi ne ya bata amsa, “Toke tunda kinsan haka miye na damuwar, dan ya sakata aiki sai ya zama wani abu, sau nawa ke ya sakaki ayyuka da sukafi wannan?”. Baki ta taɓe, cikin hausanta da bawani fita yakeba tace, “Amma tunda muke nama taɓa zuwa nan gidan ne? Itako daga gani tana nan tun ɗazun”. Cike da jin haushi Hafiz yace, “To idan ya sakko saiki masa wannan tambayar kuma ai”. Harar Hafiz tayi, dan tun dama can basa shiri, baya shiga sabgarta sai dole, dama sunfi ɗasawa da Jabeer duk cikinsu, Aliyu kuwa baida yawan hayaniya, dan harma yafi Jawaad rashin son magana. Babu wanda ya sake cewa komai, sai Rose daketa kallon hanyar benen tana cika da batsewa da sauke tagwayen ajiyar zuciya.
A sama kuwa koda na isa Nabeelah na bama kayan akan yace takai masa su ɗaki, har Nabeelah ta amsa zata wuce sai gashi ya hawo, hakan yasani saurin riƙo ledan saboda wata uwar harara daya sauke min, Nabeelah ta juyo zatai magana itama ta samu rabonta na harar, sakarmin ledar tayi da sauri tana barin wajen, ni kam dai ƙasa nai da kai kawai.
Duk abinda sukeyi Ummah na zaune tana kallonsu, sai dai tayi kamar batasan sunayiba.
Jawaad ya wuce ɗaki batare da yace komaiba, dan shikuma baima lura da Ummah ba, bayansa nabi gudun karna sake wani laifin. baice dani komaiba harna ajiye ledan nai hanyar fita. Na sauke numfashi ganin na fito lafiya, a raina ina mitar ‘mutum sai baƙar takura’ matarka dai taga banu yasin, a can ƙasan raina kuma tunani nake yanada mata to miya haɗashi da shan magani irin wannan?, nifa dukma sai naji inajin kunyar abun yasin, nikam bazan sake yarda idona ya shiga cikin nashiba, wannan abun kunya har ina haka. Muna a falon Nabeelah na fama dani akan abinci data zubo ya fito, bai kalli kowaba a cikinmu ya sauka ƙasa.
Ban sakko ba har saida suka tashi tafiya Jabeer ya ƙwalamin kira, lokacin dana ƙaraso duk sun fice daga shi sai Jabeer ɗin, inda yake Jabeer ya nunamin alamar yana kirana, na ƙarasa gabansa dan yanzu ya tashi zaune, batare da ya kalleni ba yace, “Ranar lahadi ƙarfe goma na safe kije ku haɗu da wannan yarinyar, Jabeer zai baki address ɗin wajen”. nidai nace masa to ina jiran ƙarin bayani, sai dai bai sake cewa komaiba, oga Jabeer yace, “muje to, Boss ALLAH ya ƙara sauƙi”. “Amin” ya faɗa akan laɓɓa, nima nace ALLAH ya ƙara sauƙi nai gaba batare da jiran ya amsaba, dan yaban haushi.
Ni da Jabeer a motarsa muka koma, su Aliyu kuwa suna a motar Hafiz da sukazo a ciki, ina kallon yanda Rose keta bina da baƙar harara nai tamkar ban ganiba.
Munzo fita daga layinne naga motar Mom zasu shiga su kuma, nace, “Lah ga mom can”. Jabeer dake tuƙi yace, “Ƙila itama zataje ganin boss ne ko?”. Kallonsa nai nace, “ganinsa kuma? Wai da gaske Ƴan uwansu ne?” dariya yay yana harba motar kan titi, yace, “Momin mu kemafa na kula akwai shiririta wani sa'in, bakiga gidansu ɗaya bane, ai da mom da Abban Jay babansu ɗaya, sannan Jay shine ya auri Shahudah kafin su rabu”.
Mugun waro idanu nayi baki a hangame, nace, “Wai dan ALLAH oga kana nufin dama shine mijin aunty Shahudah?”. Jabeer dake murmushi yace, “Ƙwarai kuwa, ammafa a da kenan, amma ke yaya kuke dasu Shahudah da har bama kisaniba?”. Daƙyar na iya ce mas
kamar yanda Mom suke da Abban Boss, nima da Abbansu Aunty Shahudah da Mamana babansu ɗaya”.
Kai Jabeer ya shiga kaɗawa yana faɗin, “Tab cakwakiya kenan, kice shiyyasa Qaseem beson kowa ya raɓu dake? Kodai ƴar gida zamuyi?”. Murmushin yaƙe kawai nai masa bance komaiba, danni gaba ɗaya kaina ya toshe, koda wasa ban taɓa kawo cewar boss mijin aunty Shahudah bane ba, to yama akai na kasa fahimta? Koda yake bai taɓa zuwa gidanba ina nan, bankuma taɓa ganin koda hotonsa ba a gidan, amma kuma inban mantaba nasha jin sunan Jawaad a bakin ƴan gidan, ‘ya salam, miya toshe min kaina haka?’. Har mukaje station wannan tunani ne keta kaikawo tsakanin ƙwanyata da zuciyata batare da nasan ma'anar hakanba, shima kuma oga Jabeer bai sake cemin komaiba saima redio daya kunna.
Koda muka iso office nabi oga Jabeer kamar yanda ya umarceni, ya bani ƙaramar takarda ta address ɗin wajen da boss yace sannan na fito. Na iske su ummie sunata shirin tashi, dan biyar tayi, ALLAH ma ya soni nayi sallar la'asar yanzu da muka koma gidansu boss, nima ɗaukar tarkacena nai muka fito tare, dan Ummie zanbi, na leƙa office ɗin yah Qaseem bayan na fito daga wajen oga Jabeer na iske bayanan ya fita wai. Daurewa nai na cire alaƙar Aunty Shahudah da boss data tsayan a rai ba gaira ba sabar na biyema Ummie mukaita hirarmu, har gida ta kaini, sai dai bata shigaba iyakarta gate na sauka ita kuma ta juya.
Na iske su a falo aunty Shahudah kwance Doctor na saka mata ƙarin ruwa, ba hurumina bane tambayar abinda ya sameta, na gaishesu tare da mata sannu cikin jimami sannan na wuce ɗaki abina. Bansan miyasa na tsinci kaina cikin rashin jin daɗin komaiba, nai wanka na canja kaya, ganinma magrib tayi saina bari nai salla sannan nai zaman yin azkar har aka kira sallar isha'i, itama tashi nai nayi sannan na fito falon dan sake duba Aunty Shahudah, dan banajin yunwa, tun abincin da naci a gidan boss bai sauka ba, duk da saida Nabeelah ma tai fushi sannan naci bayan ummah ta saka baki.
Na iske aunty Shahudah ta koma ɗaki, sai yah Qaseem kawai a dining yana cin abinci, sannu da dawowa nai masa, yay murmushi yana min alamar nazo. Ban musaba naje garesa, naja kujera nima na zauna, “Kinyi ƙyau” ya faɗa yana kashemin ido ɗaya, murmushi kawai nayi bance komaiba. Haka yayta ɗan jana da hira harya kammala, ya miƙe domin zuwa yay wanka, nima miƙewar nai nace bara na sake duba aunty Shahudah naje na kwanta na gaji.
Zaune na isketa Aunty Aamilah na bata magani, na sake mata sannu da ALLAH ya ƙara sauƙi na fito, ɗaki na koma nai kwanciyata duk da nasan gobe idan ALLAH ya kaimu babu aiki, amma inason na kira Dad da safe idan ya bari sai naje gidan Inna Zainabu na gaishesu, da wannan tunanin barci ya kwasheni.
A ɗakin Shahudah kam bayan fitowar Bilkisu Aamilah ce ta sauke ajiyar zuciya tana mai fuskantar ƴar uwar tata da ƙyau. “Sister ga shawara mana” Shahudah da duk tazama kalar tausayi ta jinjina mata kai alamar tana saurarenta. Aamilah ta sake jan numfashi kafin tace, “Ina ganin yarinyar nan Bilkisu zamu iya sakata tai mana wani abu” murya a dasashe Shahudah tace, “Ban ganeba Aamilah ”. “Sister ina magana ne akan Brother Jawaad, da nayi tunanin Broth ne a farko, sai dai daga baya nasan bamai yuwuwa bane, musamman idan mukai dubi da yanda basama shiri tun suna yara, sam jinin Qaseem da Jawaad bai haɗuba, bankuma san lokacin dazai haɗunba, so idan mukace zamu ɗorasa akan ya taimaka mana sai dai ya ɓata komai tunda dama can bason aurenku yakeba, yanzu da yarinyar nan ta shigo, sai naga mizai hana mu amfanu da ita, dan kinsan bata da yawan hayaniya da surutu, sannan mutumin dake da irinki bazai kalletaba da sigar birgewa balle akai ga so, ballantana zuciyarmu tayi tunanin ko zata iya cin amanarmu, ko shi yaji wani abu a kanta”. Shahudah datai shiru tana kallon Aamilah tace, “Maganganunki kawai naji Aamilah, amma ban gane ina suka dosaba sam, wane taimko zamu nema akan Bb?”. “Yauwa, yanzu kikai tambaya mai ƙyau Sisi na, inaji a raina Yarinyar zata taimakemu, sai dai bani da tabbacin wajen aikinsu ɗaya, duk da dai naga kullum tare take fita da Broth, ku
ma Broth da Brother Jawaad wajen aikinsu ɗaya ne, amma wannan ba wani abu bane, zamu iya tambayarta”. Kai kawai Shahudah ta jinjina alamar gamsuwa, Aamilah tace, “ki kwanta ki huta zamu tattauna zuwa da safe, tunda weekend ne tana gida babu inda take zuwa”. Nanma da kai Shahudah ta amsa mata..
★★★★★
Washe gari da safe na tashi nai ƴan ayyukan dazan iya harda kayana da sukai datti, na gyara ɗakina tsaf nai wanka sannan na fito, babu kowa falon dan har lokacin ma bana tunanin wani ya tashi a jama'ar gidan, kicin na nufa na samawa cikina abinci naci, kafin na sake komawa ɗaki na shiga neman Number dad da ya kirani kwanaki uku da suka shige, kusan duk Numbers nashi na ƙetare inada ita, dan yakan kirani lokaci-lokaci idan yay tafiya tamkar yanda yakema sauran ƴaƴansa, bata shigaba, na sake gwadawa har sau uku saina haƙura, bazan iya zuwa ko inaba bayan wajen aiki saida umarninsa, dan banida wani jagora sama da shi a halin yanzu a duniya, sai ko yaya Qaseem da nake fatan ya zama na biyu a matsayin miji. Na aje maganar zuwa gidan Inna zainabu akan sai idan ALLAH ya kaimu gobe, idan naje inda boss yace na gama abinda nakeyi sai na shiga wajen wanke kai daga nan na wuce can koda ban jimaba sai na gaishesu na taho gida, da wannan tunanin na miƙe da nufin zuwa gidansu Amina.
Harna fice babu motsin kowa, muka gaisa da baba mai-gadi na fice abina. Da sallama na shiga gidan, Amina dake a tsakar gida tana wanke-wanke ta amsa tana kumbura fuska, dariya nayi ganin yanda tayi, dan nasan dalili, ta ɗauke kanta da faɗin, “Munyi fushi, ki koma a binki”. Kafin nace wani abu mama tace, “Kwarai kuwa Amina ina bayanki”. Kunnuwana na kama duka biyu na kneeling alamar dai na tuba, dariya suka sanya daga mama har Amina da yayan Amina daya fito da ga bayi, shine yace, “A ni dai na yafe ma ƴar ƙanuwata, nasan aikine ke mata yawa”. Nace, “Yauwa Yayanmu, shiyyasa nake yayinka a koda yaushe”. yay dariya da haɗe yatsun sa babba da manuniya alamar dai-dai👌🏼 kenan.
“Oh, mu baƙya yayinmu kenan? To kin ƙarama kanki laifi har tsallon ƙwaɗo sai kinyi” Amina ta faɗa tana miƙewa ɗauke da kwandon data saka kwanikan. Mama tace, “A'a auta nimafa na huce, ama mai-gadon lu'u-lu'u haƙuri”. Dariya muka saka gaba ɗayanmu saboda furicin mama, Amina tace, “Shikenan na haƙura tunda mama ta saka baki, amma da yau ɗinan saina tsamar da ƙafafunki”. Harararta nai kafin na zauna a inda ta tashi na gaida Mama da Yaya Sule, daga nan muka hau hirarmu.
Wajen sha biyu Amina na tayani tsifar kai muna hira, mama kuma nata ƙoƙarin ɗaura awara da muka tace da Amina bayan munje munkai markaɗe, nace, “Amina!”.
“Na'am” ta amsamin tana leƙo fuskata. Ɗalli namata a fuska da ɗan yatsa, ta matsar da fuskarta tana ɓata fiska saboda zafi, niko na kwashe da dariya, “Ke ɗince kin wani kawomin fuska saikace maison leƙa ramin gwal”. Dariya itama tayi tana ranƙwashina a kai, “Ai bazakici bulusba kuwa”. “ALLAH da zafi” na faɗa ina harararta” tace, “Nima ai naji zafin shiyyasa na rama”. “Ba komai zaki gane shayi ruwane. Maganarnance dai zamu sake”. Shiru tayi kamar bazatace komaiba, tsifar da takemin ma ta koma min ita a hankali, na zungureta da hannu dan nasan ta faɗa kogin tunanin nata. Numfashi ta kawo a hankali, tace, ”Ina saurarenki”.
“Amina, a zaman da kikai gidanmu na tsahon wasu shekaru, nasan zakisan halayyar kowa dake cikin gidan nan”. Tace, “Hakane” “Alhmdllh, mizan iya sani akan Qaseem da Salman?”. Shiru tai na wasu sakanni kafin ta sauke numfashi, “Duk abinda kikeson sani zan iya faɗa miki Bilkisu inhar na sanshi, wanda kuma ban sanshiba zance miki ban saniba, kimin tambaya zanfi fahimtar mikike son sani game dasu?”.
Cike da gamsuwar maganarta nace, “Hakane, Qaseem da Salman suna neman mata?”................✍
Asha weekend lafiya🤫🤭😉😍👌🏼
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻
Yau ƴan wattpad sai haƙuri yaƙiyi wlhy, da ƙyarma nai copy ɗin wannan a can ɗin, amma zan cigaba da gwada muga in za'a dace😔
a muka shigo ta gaida su Hafiz ta haye abinta.
Bily na gama hayewa Jawaad ya miƙe cikin dauriya ya ɗauki ɗaya daga ruwan da aka ajiyema su Hafiz yabi bayanta yana tafiya a hankali, dan inhar yace zaiyi hanzari dolene a fahimci matsalarsa, ca yay musu yana zuwa. Rose ta bisa da kallo a wani irin yanayi maisa ƙuna a zuciya, a ƙufule ta kalli su Aliyu tana faɗin, “Wai miye haɗin wannan yarinyar da Boss ne?, shishshiginta yayi yawafa” dukansu da mamaki suka kalleta, duk da sun fahimci tsagwaron kishi tattare da zancenta, Jabeer ya kare bakinsa da hannu yana dariya ƙasa-ƙasa, sai da Hafiz ya hararesa sannan ya haɗiye da ƙyar, ya kalli sama sannan ya maido dubansa ga Rose data sake cika fam. “Wai Rose kina nufin sonta yake?”. Da sauri tace, “Itaɗin banza, kaima kasan Boss ya wuce da ajinta, kawai dai itace ke shishshige masa”.
Hafiz yace, “Humm” Aliyu dake murmushi ne ya bata amsa, “Toke tunda kinsan haka miye na damuwar, dan ya sakata aiki sai ya zama wani abu, sau nawa ke ya sakaki ayyuka da sukafi wannan?”. Baki ta taɓe, cikin hausanta da bawani fita yakeba tace, “Amma tunda muke nama taɓa zuwa nan gidan ne? Itako daga gani tana nan tun ɗazun”. Cike da jin haushi Hafiz yace, “To idan ya sakko saiki masa wannan tambayar kuma ai”. Harar Hafiz tayi, dan tun dama can basa shiri, baya shiga sabgarta sai dole, dama sunfi ɗasawa da Jabeer duk cikinsu, Aliyu kuwa baida yawan hayaniya, dan harma yafi Jawaad rashin son magana. Babu wanda ya sake cewa komai, sai Rose daketa kallon hanyar benen tana cika da batsewa da sauke tagwayen ajiyar zuciya.
A sama kuwa koda na isa Nabeelah na bama kayan akan yace takai masa su ɗaki, har Nabeelah ta amsa zata wuce sai gashi ya hawo, hakan yasani saurin riƙo ledan saboda wata uwar harara daya sauke min, Nabeelah ta juyo zatai magana itama ta samu rabonta na harar, sakarmin ledar tayi da sauri tana barin wajen, ni kam dai ƙasa nai da kai kawai.
Duk abinda sukeyi Ummah na zaune tana kallonsu, sai dai tayi kamar batasan sunayiba.
Jawaad ya wuce ɗaki batare da yace komaiba, dan shikuma baima lura da Ummah ba, bayansa nabi gudun karna sake wani laifin. baice dani komaiba harna ajiye ledan nai hanyar fita. Na sauke numfashi ganin na fito lafiya, a raina ina mitar ‘mutum sai baƙar takura’ matarka dai taga banu yasin, a can ƙasan raina kuma tunani nake yanada mata to miya haɗashi da shan magani irin wannan?, nifa dukma sai naji inajin kunyar abun yasin, nikam bazan sake yarda idona ya shiga cikin nashiba, wannan abun kunya har ina haka. Muna a falon Nabeelah na fama dani akan abinci data zubo ya fito, bai kalli kowaba a cikinmu ya sauka ƙasa.
Ban sakko ba har saida suka tashi tafiya Jabeer ya ƙwalamin kira, lokacin dana ƙaraso duk sun fice daga shi sai Jabeer ɗin, inda yake Jabeer ya nunamin alamar yana kirana, na ƙarasa gabansa dan yanzu ya tashi zaune, batare da ya kalleni ba yace, “Ranar lahadi ƙarfe goma na safe kije ku haɗu da wannan yarinyar, Jabeer zai baki address ɗin wajen”. nidai nace masa to ina jiran ƙarin bayani, sai dai bai sake cewa komaiba, oga Jabeer yace, “muje to, Boss ALLAH ya ƙara sauƙi”. “Amin” ya faɗa akan laɓɓa, nima nace ALLAH ya ƙara sauƙi nai gaba batare da jiran ya amsaba, dan yaban haushi.
Ni da Jabeer a motarsa muka koma, su Aliyu kuwa suna a motar Hafiz da sukazo a ciki, ina kallon yanda Rose keta bina da baƙar harara nai tamkar ban ganiba.
Munzo fita daga layinne naga motar Mom zasu shiga su kuma, nace, “Lah ga mom can”. Jabeer dake tuƙi yace, “Ƙila itama zataje ganin boss ne ko?”. Kallonsa nai nace, “ganinsa kuma? Wai da gaske Ƴan uwansu ne?” dariya yay yana harba motar kan titi, yace, “Momin mu kemafa na kula akwai shiririta wani sa'in, bakiga gidansu ɗaya bane, ai da mom da Abban Jay babansu ɗaya, sannan Jay shine ya auri Shahudah kafin su rabu”.
Mugun waro idanu nayi baki a hangame, nace, “Wai dan ALLAH oga kana nufin dama shine mijin aunty Shahudah?”. Jabeer dake murmushi yace, “Ƙwarai kuwa, ammafa a da kenan, amma ke yaya kuke dasu Shahudah da har bama kisaniba?”. Daƙyar na iya ce masa
Page 14
Guys ɗinan anya kunaso na mutu da idanuna?, kusan words dubu uku nakeyifa a kullum amma sai naji kuna farautar ƙari🤔, aradu inason ƙulla shekara ɗari da idanuna kuyi haƙuri😂🤣😂. Ga zaɓin lokacin posting, 11pm ko kuma 6am. Waɗanda naga sunfi rinjaye sai abi ra'ayinsu. Amma masu cewa dama Jay yana dariya?? nima kun bani dariya wlhy sosai, waye baya ya dariya a duniya, sai dai idan bata kamaba😂. Harda ƙyaƙyƙewa zakuji yayima wataran🚴🏼🚴🏼👌🏼.
Ina muku fatan alkairi😍😘😍😘😘😘.
................Zagayen gidan gonar suka farayi suna hira mai daɗi da mutunta juna, sashen dabbobin da ake kiwo da sashen da ake noma, sashen kaji, kifi, su talo-talo, zabi, agwagi, kajin gida, zomaye, harda tantabaru, sai sashen itatuwan fruits, komai yana tafiya yanda yake buƙata, sun nufi inda Jawaad ya gyara shima suke fidda yankakkun kaji dasu zabbi da sauran duk nau'in ƙananun dabbobin da ake kiwo a wajen ana packaging nasu a ledoji a shiryasu a wasu robobi manya masu haske domin masu sari dake kaiwa birni, hakama ƙwan kaji da zabi dana talo-talo, sai inda ake tace tsaftatacciyar madarar shanu kuma ana sakawa a galoli shima, kowacce galon da adadin litar da take ci, da inda ake shirya dukkanin nau'in kayan itatuwa suma. Abin dai dolene ya burge mai kallo da ƙayatarwa sosai. Sai da suka shiga lungu da saƙo, ya kuma gamsuwa da yanda komai ke tafiya, yana ta ma ma'aikatan jinjina da sake basu ƙwarin gwiwa, inda yaga kuskure kuwa cikin hikima yake musu gyara ba yanda zasu fahimci gazawarsu ba, yanda yake tafiyar da al'amarinsu na ƙara masa girma a idonsu sosai da daraja. Bayan sun kammala zagayawa suka yada zango ƙarƙashin bukkar bunu da tasha gyara domin hutawa, gefenta kuma anyi ɗan gini mai 2 bedroom kawai, domin idan yazo da shirin kwana nan yake kwana ko gidan baba maigari, hirarsu suka cigaba dayi cikin nishaɗi, lokaci-lokaci Jay yakan amsa waya, wadda ta shafi aiki kuwa yakan tashi ya koma gefe idan ya gama ya dawo. Da rana sai ga abinci lafiyayye daga gidan baba maigari an aiko musu, harda fura mai ƙyau da tasha damu. Yini guda anan suka yisa, Jawaad yaji matsalolin jama'ar garinsa waɗanda zai iya kawo gyara da iya ƙarfin aljihunsa yace zaiyi, dan dama ya daɗe bai zoba kusan wata uku. wanda sukafi ƙarfinsa kuma zasu haɗa hannu domin neman taimakon wanda zai iya musu, Jawaad ya gaji mahaifinsa a abubuwa da dama, komai nashi na al'ummane, dukiyar da mahaifinsa ya bari bata rufe masa ido ya zama asharari ba, sai ya ɗora kyawawan aiyukansa akan wanda mahaifinsa ya fara, tare da nasa da ya ƙirƙira shima, yanda yake rayuwarsa a sauƙaƙe bazaka taɓa tunanin an tara masa irin wannan dukiyarba, dan ko iya gidan gonarnan ai al'amarine babba, balle kuma akwai wanima bayan wannan, bayan sauran abubuwa da shima nasa ƙoƙarin.
Bayan sunbar gidan gona gidan baba mai-gari suka koma, sun samu zama dashi da manyan gari suka tattauna akan maganar da sukai a gidan gona na abokansa, sai bayan sallar magriba Jawaad ya baro ƙauyen cike da tsaraba daga jama'a, duk da sunsan yanadashi hakan baisa suji ƙyashin ƙyautata masa da ni'imar da suma ALLAH yay musu ba. A hanya ya tsaya yay sallar isha'i kafin ya ƙarisa gidan Umma ƙarama. Tayi murnar ganinsa ita da yaranta, ya sauke mata tsarabarta anan da ɗibar mata wadda mutane suka bashi yay mata sallama ya tafi dan bai jimaba sosai, daga nan sai gidan Ummah babba, gidansu Nabeelah kenan, nanma sunyi murnar ganinsa, inda suka fara faɗansu shi da Batool kamar yanda suka saba, itama dai tsarabar ya ajiye musu ya tafi, a gida ya yada zango, kasancewar kowa ya shige sashensa shima nashi ya shige akan da safe zai fiddama kowa nasa kason, sauran ya kaima kakansa nasa shima, sai nasu Hafiz.
WASHE GARI LAHADI.
Washe gari lahadi, na tashi da burin abubuwa da dama, dan da daddare na samu Dad da yah Qassem ya kirashi, na faɗa masa zanje na gaida Inna zainabu yace naje sai driver ya kaini, na sanar masa zanhau napep saboda zan fara zuwa wajen aiki da aka sakani kafin naje canɗin idan na fito wajen saloon. Ina kammala gyaran ɗaki nai wanka, na fita nai breakfast sama-sama na koma ɗaki nai shiri. Doguwa
r rigace na saka ta Material baƙa da ratsin fari, ta zaunamin ɗas a jiki, gashi ta buɗe daga ƙasa bata wani matseniba sai a ƙirji kamar yanda tsarin ɗinkin yake, maɗaurin da akai mata na kama na ɗaure a bayana, sai ta kuma fita da ƙyau. Gashina dake a tsefe na kuma gyarama zaman ribbon, sanan na saka farar hula mai ƙyau, na kawo ƙaramin gyale baƙi na yana a kaina, tare da kalmashesa a ƙirjina ya rufe ruf na ɗora a kafaɗa ƙasanshi suka sauka bayana, basai an faɗaminba, ni kaina nasan nayi ƙyau, hakan yasa naita kallon kaina a mirror ina murmushi, a gurguje na ƙarasa kimtsawa na fito sagale da ƴar jikkata a kafaɗa ina ƙamshi mai sanyi, sai takalma masu ɗan tudu kaɗan, na riga na faɗama Mom zan fita dama tun da daddare, hakan yasa yanzu nai ficewata kaina tsaye tunda babu wanda ya tashi har Yah Qaseem da baisan zan fitaba, dan banfaɗa masabama gudun matsala.
Da ƙafa na taka har titi na tari napep na hau zuwa inda Oga Jabeer ya bani.
Bayan fitar Bilkisu daga gidan Mom ta fito daga ɗakinta, tanason tayi magana da Shahudah ne, shiyyasa tun ɗazun taketa dakon fitar bily, tana tsoron halin da Shahudah zata iya shiga da har bily zata sani, dan a ganinta bily ita kaɗaice bare a cikinsu da bai kamata tasan sirrinsu ba. Sam jiya batai barciba akan bayanin da Shahudah tai musu na zuwa ɓangaren Jawaad da tayi, ta fahimci sunyi kuskuren ƙin sanarma Shahudah gaskiyar lamari akan sakinta da Jawaad yayi tun lokacin da wancan al'amarin ya faru, ba damuwarta abinda Shahudah ta aikataba, damuwarta kar Jawaad ya sake gudun Shahudah akan hakan, dan ita kanta inhar zata faɗi gaskiya bata taɓa kama Jawaad da abun rashin gaskiya ba dangane da fasiƙanci, dan ko lokacin da basa ƙasar ma idan yaje musu hutu duk jarabar Shahudah da naci akan yazo suje club baya zuwa, ita kanta ma faɗa yake mata, shiyyasa da yaje take kame kanta. To tasan akan hakan Jawaad zai iya sake bijire musu ne dangane da maida Shahudah.
Tashin Shahudah kenan a barci tayo brush da alwala ta fito mom ta shigo, ƙarfe goma saura sai yanzune wai ake alwalar sallar asuba😭🤦🏻.
“Mom lafiya?” Shahudah dake ƙoƙarin saka gyale ta faɗa tana kallon mom. Mom ta zauna bakin gado tana faɗin, “Magana nazo muyi”. Zama Shahudah tai ta fasa sallan, Mom tace ba salla zakiyiba ne?” “Eh salla zanyi, amma muyi magana sai nayi daga baya”. “Karki damu tashi kiyi sallar zan jiraki”. Shahudah batace komaiba ta miƙe ta kabbara salla, wadda ALLAH kaɗai yasan mima take karantawa, dan a mintuna ƙalilan ta idar da kayarta ta dawo wajen mom dake zaune tai tagumi da juya abinda zai iya biyo baya a ranta. Motsin Shahudah ne ya maidota hayyacinta ta gyara zama, tare da kamo hannayen Shahudah duka cikin nata ta kafeta da idanu, “Shahudah magana zanyi miki, inason ki nutsu ki fahimta, domin muma a yanzu haka hanyar gyara ɓarnar da kikayi muke, munada tabbacin samun nasara kuma, abinda yasa muka yanke hukunci sanar mikin a yanzu dukda mun ɓoye a baya saboda gudun halin da zaki shiga, yanzu kam saboda karki sake ƙara tafka irin kuskuren da kikayi ranar na zuwa wajen Jawaad”.
“Mom ni dan ALLAH kimin magana kai tsaye, ki daina yimin wannan manya-manyan hausan naki da ba wani fahimtarsu nakeba, minene ya faru”. Yanda tai maganar da kumbura bakin shagwaɓa yasa mon yin ƴar dariya tana shafar kumatunta, “Nifa daɗina dake taɓara maman Dadynta, karki damu ai zan kaiki, kumani sonake ki iya hausar ai tunda yaren mamanki ce”. Shahudah batace komaiba sai ɓata fuska data sake yi. Mom ta ɗauka takardan data shigo dashi ta miƙama Shahudah. Babu musu Shahudah ta amsa tabuɗe takardan batare da tace komaiba.
Kasancewar Jawaad da turanci ya rubutama Shahudah takardan saki sai ta fahimci komai dallah-dallah. Hannunta na rawa da bakinta ta ɗaga takardar, “Mom kina nufin BB ne ya aiko min da wanan dan naje wajensa?”.
Kai Mom ta girgiza mata, “Badan kinje wajensa bane, wannan takardar shekararta biyar kenan a gidannan, mune dai bamu bakiba tun lokacin da akai rikicin zubar da cikin nan, munƙi bakine saboda gudun karki sake shiga wani hali akan wanda kika tsinci kanki a wancan lokacin, dan muna
ta ƙoƙarin duk bin hanyar data dace ki koma ɗakinki, sai dai zuwan da kikai wajensa ya ɗakko hanyar ɓata dukkanin shirin namu, shi bazai fahimci bakisan ya sakekiba, zai fassara abinne ta wata siga daban”.
Matsanancin kuka shahudah ta fashe dashi, ta dafe kanta dake juya mata lokaci ɗaya, yanda tai baya zata faɗine yasa Mom azamar tarota tana kiran sunanta a razane, rungumeta shahudah tayi tana kuma kuka tamkar ranta zai fita, sai dai ƙarancin tunaninta na raya mata cewar tamkar sakin a banzane, dan Jawaad yayi ƙarya ya kwana da yunwa, aurensu baida maraba dana zobe, babu kishiya babu saki, ta daka tsalle ta dire a gaban Mom tare da wawaso rantsuwa ta sake direwa akan baima isaba. Yanda ta birkicema Mom tana kuka da rantsuwar Jawaad bai isabane ya jawo hankalin Aamilah data fito falon ƙasa neman abinci, sai Qaseem dake a d/table zaune yana karyawa shima, a guje Aamilah tay sama, Qaseem ma ya miƙe yabi bayanta. Yanda Shahudah ta rikice Mom na rirriƙeta sai abun ya basu mamaki suka shiga tambayar mom ko lafiya?. Basu samu amsa daga bakin mom ɗinba sai a takardar sakin da Shahudah ta jefar ƙasa, Qaseem yace, “K dalla malama nutsu mana anan” yanda yay maganar a tsawace yasa Shahudah nutsuwa sai dai ta maka masa harara tamkar zata makesa.
Bai kulata ba ya maida dubansa ga Mom yana kaɗa takardar, “Ita wannan ɗin kuma daga ina Mom? Wata ya sake aikowa?” mom tace, “A'a waccance dai, kasan bata saniba, shinefa ranar Alhamis datasa muka barta can taje.........” Mom ta zayyanema Qaseem komai daya faru tsakanin Jay da Shahudah a daren juma'a wato ranar alhamis, wanda shine sanadin ciwonta. Jiyay tamkar ya make Shahudah dan takaici, Aamilah kam da yake Shahudah ta faɗa mata komai sai bataji abun a saboba, ya nuna ta da yatsa yana faɗin, “Kedai wlhy daƙiƙiyace, wai ubanmiye a jikin wannan wawan Jawaad ɗin da sauran maza suka rasa har kika nace masa?”. A fusace Shahudah tace, “Sai dai idan kaine daƙiƙin, kaiɗin ubanmiye a jikin yarinyarnan da sauran mata suka rasa ka nace mata (Bilkisu take nufi) (hakan ba sabon abu bane dan babu wani girmama juna a tsakaninsu). Duka yakai mata yana faɗin, “Idan kinajin iskancinki a gidannan kibar sakkoni, inba hakaba wlhy saina ɓallaki watan Shahudah. “Ka ɓallani ɗin tunda kai ɗin ubanane, saika gayamin banza na kasa maida maka amsa da wofi, uwarwa yama sakaka cikin maganar? Bansan shishshigi”. Dukan ya sake kaimata Mom ta tare. “Wai wane irin iskancine wannan!! Taya zaku sakani tsakkiya da shirme, ku barni naji da abinda ya dameni mana!!”. Duk dakatawa sukai kowa na huci kamar wasu ƴan dambe. Daga ƙarshe Qaseem ya juya zai fita Mom ta dakatar dashi ta hanyar kamo hannunsa, ƙin juyowa yay yadai tsaya, “Kayi haƙuri, ni banason wannan saurin fushin naka Qaseem, kasandai halin rashin kunyar Shahudah a gidanan, yakamata ka cigaba da haƙuri dasu a matsayinka na babba a cikinsu, kaji”. Ajiyar zuciya ya sauke, ya kaɗa kansa kawai. Tace, “To ku zauna muyi magana, Aamilah jeki kira Salman”.
BILKEESU
Gurin ya haɗu matuƙa, bawani mugun ƙato baneba, madaidaici ne da akayisa domin masu hutawa kawai, yasha gyara da korayen ciyayi da flowers masu ƙamshi, nidai saima na zama baƙauya, dan duk zamana garin bansan da zamansa ba, koda yake inama nake zuwa, dama yawona dasu Ummie ne idan mun dawo hutu, to ƙafarmu bata taɓa zuwa nanba kuma, sai dai a zahiri na kame kaina ina tafiya cikin nutsuwa, ƙarƙashin ɗaya daga cikin ƙananun bukkokin da aka ƙawata wajen na nufa, naja kujera ɗaya cikin huɗu dake a kowacce ruffa na zauna tare da ɗora jikkata akan tebir ɗin na buɗe na ciro waya. Motsi naji a kaina, dan haka na duba wanda yazo wajen, ɗaya daga ma'aikatansu ne, ya gaisheni yana mai dire tiren hannunsa. Amsa masa nai tare da jeho masa tambaya akan kuɗin abinda ya kawo, duk da bani nace ya kawoba, tunanina tsarinsu kenan. “Karki damu Madam, an rigada an biya” ya faɗa yana barin wajen. Binsa kawai nai da kallo harya shigema ganina, mamakina shine ‘waye ya biya?’. bani da mai bani amsa, hakan yasani kauda abin a raina na duba abinda ya ajiye ɗin. Popcorn ne sai robar ice-creem da Malt ɗaya da ruwa, n
a ɗauke idona inajan guntun tsaki tare maida hankalina ga wayata na fara tafama Oga Jabeer saƙo. Bayan na tura masa naga ya wuce sai kawai na shiga yin Game batare dana kula abinda aka ajiye min ɗinba dan a ƙoshe nake.
“Hy Babie!” aka faɗa dai-dai kunnena, a tsorace na ɗago idanuna dan a bazata abin yazomin, banji motsin kowaba. Ƙyaƙyƙyawan saurayi fari tas kuma ɗan gaye ya sakarmin murmushi da ɗage gira ɗaya sama, “Sorry na tsorataki ko?”.
Janye idanuna nayi daga kansa batare dana tanka masaba ko magana. “Kin cancanta” ya faɗa yana zama kujerar dake facing ɗina. Nanma dai ƙin kulashi nayi, yaja ɗan kwalin da Popcorn ɗin ke ciki ya fara ɗiba yana afawa a bakinsa tare da lumshe ido alamar dai akwai daɗi. Janye idanuna nai daga satar kallonsa na tura wayata a jikka na miƙe zan bar masa wajen. Da sauri shima ya miƙe yazo gabana ya tsaya, baya naja kaɗan ina ɓata fuska. Yace, “ALLAH bazaki tafiba sai kin kulani”. Na dafe kaina ina lumshe idanuna irin na ka kaini bango ɗin nan......
“Please babie kice wani abu mana”.
Nabuɗe baki zanyi magana kawai naji baƙon ƙamshin turare a wajen tare da motsi, waigawa nai saboda yanda, nakejin bugun zuciyata na sauya salo. Wanda nai tunanin kuwa shine na gani. ‘Boss!’ na ambata a cikin zuciyata, duk da ya rufe fuskarsa sosai da facing cap baƙa datai masa masifar ƙyau hakan bazaisa naƙi ganesa ba, ƙamshinsa ma kawai amsatace dan bana manta ƙamshin turarensa sam, dana jisa nake shaida yazo waje. sake ja baya daga gaban gayen da shima shi yake kallo nayi.
Jawaad kam yayi tamkarma bai gansu ba, sai ƙoƙarin buɗe gwangwanin Malt.. Ɗin da aka kawoma Bily kawai yake hankalinsa kwance, sai dai fuskarsa a matuƙar ɗaure take babu alamun sassauci, ya zaro wayarsa da ga aljihu tare da gyara zamansa, ya kwantar da bayansa jikin kujerar sosai ƙafa ɗaya kan ɗaya, sai kace wani saraki, yana sanye cikin ƙananun kaya da sukai masa masifar ƙyau da fidda cikar haibarsa, sai hula hana salla inji hausawa😂, a samanta an rubuta favourite da ruwan gwal mai ƙyalƙyali, idanunsa toshe da baƙin glasess, hakan yasa babu mai fahimtar ina idanunsa suke kallo kai tsaye. A zuciyata nace, ‘glass nama Boss ƙyau matuƙa idan ya saka, bansaniba koni kaɗai ke iya ganin hakan banda sauran mutane, amm.....
“Babie!” saurayin ya ambata da ɗan ƙarfi ganin hankalin Bily baya tare da shi. Kallona na maido kansa, nace, “Ba sunana Babie ba” yay murmushi mai ƙayatarwa, “To a faɗamin sunan mana uhum”. “Bana doguwar magana da wanda bai iya sallama ba”. kansa ya dafe alamar ya fahimci kuskurensa, yace, “Sorry Assalamu alaiki”. “Wa'alaikassalam”. Na amsa masa.
Murmushi ya sake yi, yace, “Na gode da kika tunatar dani abinda na manta, hakan na sake tabbatarmin na samu abokiyar rayuwa ta gari, irin wadda ta cancanci zama uwar ƴaƴana. Sunana Kamaludden shehu Manya, matar tawa fa?”. ni dariyama yaso bani wlhy, wai matarsa, daga ganin sarkin fawa sai miya tai daɗi. kaina na girgiza masa kawai na juya zan bar wajen, amma sai yay azamar sake shan gabana, “Haba babie, naga na gyara kuskuren da yasa aka ƙi kulani tun a farko ai, koda bazaki kulani a nanba ki bani Number mana. Sonake ya barni, shiyyasa na miƙa masa hannu alamar ya bani wayarsa na saka masa. Cike da ɗoki ya ciro wayarsa a aljihu ya miƙomin, sai dai kafin na kai hannu na amsa wani hannun ya amshe wayar..............✍
ALLAH ka gafartama iyayrnmu😭🙏🏻
Typing📲
ƘWAI cikin ƘAYA!!
Bilyn Abdull ce🤙🏻
BOOK TWO
Page 15
To yau page ɗin ƙwai cikin ƙaya na ƙuɗine, duk wanda ya karanta ina roƙonsa dan girman ALLAH ya biya da addu'ar ALLAH ya kawo mana iyakar tashin hankalin dake damun wasu yankuna namu na arewaci, dan ALLAH ina roƙon har ƴaƴanmu ku saka suyi wannan addu'ar a dukkanin sallolinsu biyar na wannan yinin, domin addu'ar yara abuce mai muhimmanci a garemu mubar sakaci da ita, idan baki aureba ki roƙa mana jama'ar gidanku suyi da kanninki, duk da munsan anayi dama, sai dai ina fatan wannan ta zama ta musamman domin ALLAH, dan ALLAH kar'a manta, kar'a manta, kar'a manta.
Ya rabbi ka kawo mana ƙarshen waɗanan tashin hankali, ya ALLAH ka ruɓanya rahamarka da rangwame a garemu, ya Rabbi ka yafe mana kurakuranmu, ya Rabbi kaimana maganin abinda bazamu iyaba harma da wanda zamu iya ɗin, ya rabbi ka taimaki bayinka dake cikin gararin rayuwa da hali na buƙatar agaji, ya rabbi ka kawoma muhallansu zaman lafiya, kasaka kwanciyar hankali a zukatansu suma su sami cigaba da rayuwa a yankunansu kamar kowa, ya rabbi ka kawoma ƙasarmu zaman lafiya baki ɗaya da dukkanin duniyar musulunci, ya rabbi ka bamu ikon cinye jarabawa kasa ta zama rahama a garemu duniya da lahira🙏🏻😭.
Idan kasan bazaka biyaba karka karanta, bayin ALLAH na buƙatar tallafin addu'oinmu, dan girman ALLAH karmu wofantar da lamarinsu saboda mu muna barci a gidajenmu da iyalanmu bayan munci mun ƙoshi, ba'a zahiri kawai nakeson ayiba har abaɗi ma ita mukafi buƙata😭.
Masu 6am sunyi winning, wannan shine zaizama lokacin posting ɗinmu kafin na daina fushi da kamfanin masu yellow'n tambari 🙄🙄🙄.
................Daga ni har shi kallonsa mukai. Nidai na sauke idanuna da hannuna a hankali ina haɗiyar yawu da ƙyar. Kamal yace, “Haba malam ya haka?” Jawaad bai tanka masaba, sai wayar daya daddana alamar wani abun yayi a ciki ya miƙa masa. A ƙufule Kamal ya amsa yana faɗin, “Wanan rainin wayone ai, ya zakazo ka shiga abinda bai shafeka ba?”.
Ban jira amsar da boss zai bashiba nabar wajen nidai, saboda wata muguwar harara daya makamin dan ya cire madubin idonsa.
Jawaad ya maida kallonsa ga kamal yace, “Karka damu ka kira Number dana saka maka zaka sameta”. Kamal yay ɗan shiru alamar nazari, sai kuma yay saurin taɓa hannun Jawaad dake shirin barin wajen, Jay ya juyo yana kallonsa, sai dai baice komaiba. “Sorry, dan ALLAH ko ƙanwarka ce dai?” wani munafukin murmushi Jawaad yayi tare da ɗagema kamal gira ɗaya sannan ya wani juya kansa da lumshe ido yabar wajen. Sam Kamal bai fahimci komai daga yaren na Jawaad ba, sai dai kuma ya haƙura akan zai nema waje ya zauna harsu tashi tafiya ya bisu a baya, dan shifa yaga matar aure.
Tsaye yazo ya sameni ina waya da Zuhrah, baiko kalleni ba yaja kujerar da ya fara zama ɗazun ya sake zaunawa yana maida glasess ɗinsa a ido kamar ma ya manta dani, nima ɗin dai ƙasa-ƙasa nake satar kallonsa yanda nasan bazai fahimtaba ina wayata, a ƙasan raina inata tunanin komi ya cema Kamal? Number wa kuma ya saka masa a waya? Dan nidai nasan baisan tawaba. Zuwan ɗaya daga ma'aikatan wajen ne ya sakani janye idona a kansa, umarnin kwashe kayan wajen ya basa tare da sake kawo wasu, dai-dai lokacin da muka ƙarisa wayar, sai da yabar wajen ne cikin dauriya nace masa, “Ina kwana sir”.
Shiru bai tanka minba, saima ya kalli agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa ya ɗauke kansa, duk a tsorace nake, gani nake zaimin faɗa akan ganina da Kamal, amma har aka sake kawo abinda ya saka ɗin baice dani komaiba.
Ni kuma har lokacin ina tsaye duk da ƙafafuna sun gaji haka na fuske abina, shiko ya buɗe sabon Popcorn ɗin da aka kawo ya hau ci yanayi yana danna waya, baifi ɗiba uku ba wata mata mai sanye da hijjab har ƙasa da niƙaf ta iso wajen, sallama tai mana, na amsa mata, shiko bangama ya motsaba har sai da taja kujerar gefensa ta zauna, sai da ta ɗage niƙaf ɗin tana gaishesa sannan na fahimci wadda muke jirace.
Batare da ya amsa mata gaisuwarta ba yace, “Kinsan irin ɓata mana lokacin da kikai?” haƙuri ta bashi. Kallona yay ya ɗauke kansa batare da yace komaiba, hakan ya sakani gyara kujera nima na zauna.
Munja tsahon lokaci tare da ita yana mata tambayoyi kala-kala, wasu ni kaina idan yayi hanjin cikina saisun kaɗa balle ita da akemawa, gaba ɗaya duk ya gama rikitata da gizagonsa, sai dai ina jinjina masa akan yanda ya samu ƙwarewa akan kutse cikin al'amuran mutum yay bincike, har kai da yakemawa ɗin ka kasa saita kanka wajen bashi amsa ta gaskiya, dan lokacin da yarinyar ta iso a take-takenta na farko banga alamun zata bada haɗin kai ba, amma yanda ya fara bi da ita sai naga tuni ta zurma tana faɗin harma wanda bai tambaya ba ɗin. Ina kuma ƙara samun ilimi na aiki nima a wajensa sosai. Lokacin da muka kammala anata kiran sallar zuhur, dan haka mukayi a cikin wajen har shima da wasu mutanen, dan akwai masallaci ƙarami da sukayi, hakan yasa wajen ya sake burgeni da ƙaramin nutsuwa. Koda muka idar tafiya tayi, nima na samu waje na zauna ina jiran ya fito nai masa sallama na wuce.
Kiran da ya shigomin a waya na ɗaga, Ummie ce, bayan mun gaisa take tambayata ina inane? Dan taje gidanmu akace na fita. Amsa na bata da cewar naje wani wajene, yanzu kuma zanje na wanke kai na wuce gidan inna Zainabu, daga haka mukai sallama akan zata sameni a wajen saloon ɗin ko gidan inna zainabu, na amsa da to na ajiye wayar. Ina ɗagowa muka haɗa ido da boss dake magana da wani da nake ƙyautata zaton sunsan junane. Janye idona nai kamar yanda shima ya ɗauke nasa, basu wani jimaba wancan yay ciki shi kuma ya nufi hanyar fita. Bin bayansa nayi ina ƙunƙuni, danni ɓatamin lokaci aketa famanyi.
Kusan a tare muka ƙarisa jikin motar da nake ƙyautata zaton da ita yazo, nayi zaton gimba ne ya kawosa, amma sai naga saɓanin hakan, dan mazaunin driver ya buɗe ya shiga, ta gefen nasa naje na tsaya, nace masa zan wuce gida nima.
Kallona yay ya ɗauke idonsa, sai da yay ma motar key, batare da ya kalleni ba yace, “Kina ɓatan lokaci fa, ko jira kike na ɗaukeki na sakaki ne?”.
‘Innalillahi...’ kuji sabon sharri, na faɗa a raina ina kumbura fuska, danni dama abinda nake gudu kenan yace mu tafi tare, to amma yaya zanyi, babu fuskar wargi a garesa, dan haka na zagaya na buɗe gefen mai zaman banza na zauna.
Baice komaiba yay reverse tare da harba motar saman titi da ɗanbanzan gudu. Idanu na lumshe ina faɗin ‘Ga wanda yafi Yah Qaseem shegen gudu da mota’. Babu mai magana a cikinmu, sai shi da ke murza sitiyarin a hankali tamkar bayaso. Bai tambayeni ina zaniba, nikuma ban sanar masaba inajin shakkar magana dan sai wani shan ƙamshi yakeyi fuskarsa a ɗaure sosai.
Tafiyar da bata wuce mintuna goma sha biyu ba muka iso wani waje, da mamaki na kalli abinda aka rubuta (LADIES MIRROR) sannan na kallesa shima, ta yaya akai yasan saloon zanzo to?, cikin ƙarfin hali nace, “Nifa ba nan nake zuwa ba”.
ATM ya miƙomin batare daya kula maganata ba, nai ƙasa da kaina ina sake faɗin, “Ai ambani kuɗin a gida”. Bai tanka minba nanma, sai ajiyemin atm ɗin da yay a kan cinya tare da ƙaramar takarda. Tamkar zan fasa kuka haka naji, na buɗe motar na fice ina sake juya al'amarin mutumin nan a raina, aunty Shahudah tasha wahala yasin, ni saima ta bani tausayi, ƙilama wannan halin nasane ya sakata gudowa gida ‘Mtsoww’. Da wannan tunanin na ƙarasa cikin wajen da ya gama haɗuwa, dan yafi inda nake zuwa nesa ba kusaba. gashi ƙaton gaske. Yanda ma'aikatan wajen suka tarbeni sai abin yaban mamaki, abin akwai birgewa. Sai da na zaunane bayan na sanar musu abinda nake buƙata sannan na sami duba takardar daya haɗomin da ita, sai naga ashe password ɗin Atm ɗin nasane ya rubuta min, samun kaina nayi dayin murmushi.
An wanke min kaina tsaf da tafin ƙafa, aka gyaramin ƙumba, wadda ta wanke min kance ta bani shawarar nayi kitso, a cewarta su inhar zasu maka aiki suna duba yanayin gashinka su ɗoraka a ƙyaƙyƙyawan tsarin da bazai karye ba, kuma zai dinga tsaho, daɗin hakan da mutane ke shigane ke sakasu sake dawowa daga nan saisu zama basu da wajen zuwa sai nan. Murmushi na mata, ina cewa “Kodai za'amin daɗin bakin ƴan kasuwa ne?”. Kanta ta girgiza tana murmushi, “Sam ba haka bane auntyna, duk abinda zakiji daga bakina shine gaskiya, Gimbiya tana ajiye ingantattun kayan aiki da nagarta a wajen nan, waɗanda daga kowacce duniya kake zaka yaba”. Kasancewar nasan boss ba jirana zai tsaya yiba sai nace, “Okey babu damuwa amin kaɗan to”.
Wani sashen daban da inda akai min wankin kai aka kaini, mutum uku kawai akema kitso, muka gaisa sannan na zauna nima, wadda zataimin ce ta iso kusa dani, muna cikinyi idanuna suka sauka akan ƙaton hoton dake sama a wajen, wanda naga wanima a can inda na baro, sai dai nesa da yay danine yasa banga waɗanda ke a jikiba, anan kam ras nake kallonsu kamar nayi magana su amsa, ƙyaƙyƙyawar mace hamshaƙiya ta gaske ce, tasha alƙyabba mai azabar ƙyau dake nuna jinin sarautace ita, gefenta ma ƙyaƙyƙyawan namijine mai tarin kamala da cikar haiba, kai tsaye na ganesa shi, dan kuwa dai sarkinmu ne Muhammad Sameer Saifudden, a raina nace ‘to ko matarsa ce wannan ɗin?’....... Maganar wadda kemin kitso ta katse min tunani da faɗin, “Duk wanda ya zauna nan baya gajiya da kallon hoton nan na sarauniya MUNAYA uwargida ga adalin sarkinmu, ita kanta wani lokacin har kishin hakan takeyi idan ta shigo takan juya hoton ya ɗau tsahon lokaci a kife”. Duk yanda naso shareta saina kasa, nai guntun murmushi, nace, “To miyasa zata barshi tunda ba dokar ƙasace ta tilasta a ajiyeba?”. kafin ta samu damar bani amsa, ƙyawawan ƴammata uku da yara biyu suka shigo wajen, biyu masu tsananin kama da Sarki Sameer, sauran kuma naɗan yanayi dasu sai dai basa tsananin kama, ukun zamu iya sa'anni dasu, biyun kuwa bazasu wuce shekara goma sha uku ba. Cike da girmamawa naga ma'aikatan na gaishesu, sai dai yanda suke amsawa babu wulaƙanci sai suka birgeni, gashi sai murmushi suke mana, nima sai na maida musu murmushin kamar yanda sukeyi, cikin manyan ɗaya ta miƙomin hannu mukai musabaha tana faɗin, “Kitsonki yayi ƙyau”. “Nagode” nace mata a taƙaice. Sauranma duk muka gaisa, suka kuma gaisa da sauran da muke zaune.
Ɗaya a Ƙaramar tace, “Aunty Amaturrahman nidai irin kitson auntyn nan nakeso” tai maganar tana nunani. Wadda aka kira da Amaturrahman ɗin ta amsa mata da cewar, “Okey Safah sai a miki ai, burina dai ayi kitson kamar yanda Ummu tace”. Ɗayar tai ƴar dariya idonta akan waya, tace, “Mudai dan ALLAH karki cikamana kunnuwa da ihunkin nan Safah, Marwah dai nasan bamai jinta, inba hakaba ALLAH muka koma saina bama kowa labari a masarauta har Momma”. Ɓata fuska yarinyar tayi, tace, “Ai bazanyiba, salon kisa su Jalaludden Su ringa rainani ko Aunty Meenal? Ni wlhy wajen Uncle Sauban zan koma india can babu ruwan mutum da wani kitso ko nabi Aunty Amatullah Niger”. Dariya sukai mata, banda wadda suka kira Marwah shugabar miskilanci da jin kai, daka ganta kaga Sarki Sameer Saifudden sak kamar yay kaki ya ajiye, ni dai ina saurarensu ne sama-sama. Bayan an gama minne na miƙe nai musu sallama na fita, ashe wajen ɗaukko Atm ɗin boss dana saka a jakka gudun basai naje wajen biya naita dube-dube ba na yarda ɗan abinda ID cards ɗina suke ciki da wasu passport ɗina dake a tare.
Ina cikin biyan kuɗin wayata tai ring, na kalla kamar bazan ɗagaba saboda sabuwar Number ce sai kuma na ɗauka na saka a kunne batare da nayi magana ba, daga canma shiru akayi, hakanne ya sani cewa, “Asslamu alaikum wanene?”. “Kin gama?” muryar wanda banyi zato ko tsammaniba ta daki kunnena a bazata. Da sauri na cire wayar a kunnena na sake kallon Number, gabana sai faɗuwa yakeyi, dan nasan nidai baida Number ta, jin an yanke wayar na amshi atm ɗin da ake miƙomin na fice da sauri domin tabbatarwa.
Jinai wani abu ya tsirgamin daga saman kai har yatsan ƙafa saboda ganin motarsa fake a inda ya tsaya ɗazun, a fili nace, “Mikenan? Zaunawa yay jirana?’. Azababben horn ɗin daya danna ne ya sani nufar motar tamkar mai tsoron hakan. Nasan duk abinda zan zaunayi bayan shiga motar laifi zai zama kuma, hakan yasa na buɗe na shiga. Baiko kalleniba ya tada motar muka fice. Sai da muka ɗauki hanya nai dauriyar cewa, “Dan ALLAH kayi haƙuri sir, wlhy nazata tafiya kayi ne, shiyyasa da suka ce na zauna sumin kitso na yarda”. harara ya ballamin ya ɗauke kansa ya maida ga titi. Ban sake cewa komaiba, nacigaba da kallon titi, kamar yanda shima yake gudu kamar shi kaɗaine a titin. Wayarsa ce ta shiga ruri, batare da ya kalli waye ba ya ɗaga da hannunsa na haggu yasa a Hans free, daga can akai sallama, ya amsa cikin ladabi tamkar bashiba, “Ya mukai da kai ranar juma'a akan zuwa meeting ɗin nan Jawaad?”. yay saurin dafe kansa da faɗin, “Oh ALLAH, kayi haƙuri Uncle, naɗan fita wani wajene amma insha ALLAH gani nan zuwa”. “To ALLAH yasa” daga can aka faɗa ana yanke wayar. Huci ya furzar yana ɗan bugar sitiyarin, Na ɗan saci kallonsa na ɗauke kaina, sai kawai naga ya canja hanya saɓanin inda muke. Nidai ban iya cewa komaiba, domin ko wainar dake cikin tanda a yau ta fini samun freedom ɗin kanta. Sai da naga ya shigo layin gidansune na iya kallonsa tamkar zanyi kuka. “Sir wlhy nifa akwai inda zanje”. bai kulaniba, yay fakin a waje batare da mun shiga cikin gidanba, sai da ya kashe motar sannan ya juyo ya kalleni.
A bazata kawai naji yace, “Inga kitson”. “Uhyim!” na faɗa ina ɗago kai da sauri da waro masa idanu cikin tsagwaron firgicin jin abinda yace. Banga alamun shi ya fuskanci abinda yay ɗin kamar yanada ban al'ajabiba, dan ya wani sake haɗe fuska fiye da da.
“Karki cinyeni da idanunkin nan malama, ɗaukesu a kaina, zan ganine idan sun iya sai nake kai matata can”.
Fuska na kumbura cikin suɓutar baki nace, “Aunty Shahudahr da batason kitso ɗince zataje?”. Saukar yatsun hannunsa kawai naji kan laɓɓana ya ɗallamin da ƙarfi, azabar zafin danajine ya sakani saurin dafe bakin idanuna na cika da ƙwalla na kalleshi, ya dallamin uwar harar tamkar zai haɗiyeni da idanun, saurin maida kaina nayi gefe hawayen da suka cikan ido suka sami damar silalomin, dan da gaske naji zafi. kafin nagama fita daga zafinne, naji hannunsa saman kaina ya zame gyalen dana yana da hular, ya saukesu saman kafaɗata, yana faɗin, “Magulmaciya waye ya tambayeki to?”. Maybe idan nace muku kaɗan ya rage zuciyata ta fito ta baki a wannan lokacin bazaku yardaba, jikina kansa tsuma yake, lokaci ɗaya dukkan ilahirin gashin jikina ya miƙe domin jin ya ja jelar gashina dake ɗaure da ribbon yana faɗin “Ashe ba ƙwaiƙwaido bace?” yay maganar a can ƙasan maƙoshi yana ɗauka hular yana ƙoƙarin maidamin a kai, na rintse idanuna ina fisgar numfashi da ƙyar tamkar mai Asthma, ya ɗauka gyalenma ya naɗamin kamar yanda ya gansa sannan ya kalleni fuska a matuƙar ɗaure, yace, “Kalleni nan”. Daƙyar na iya juriyar ɗagowa na zuba idanuna cikin nashi, yanda ya kafeni da idanu sai na kasa jurewa nai ƙasa da kaina saboda wasu abubuwa danaga suna fitowa a idanunsa waɗanda ban taɓa ganiba, ga idon ya kaɗa da jaa kaɗan tamkar wanda yake cikin fushi. Cikin ɗacin murya da saukemin wata harara mai firgitarwa da ban mamaki yace, “Hankalinki ya kwanta waɗanda kika fitama tallan jikin sun gani harsun tanka, Saina sauyama wannan fuskar taki kamanni idan na sake ganin kin fita ba hijjab”. Yana gama faɗa ya buɗe motar ya fice abinsa batare da ya sake kallona ba.
Tamkar sokuwa haka na bisa da kallo, shiko ko waiwayena baiyiba har ya isa jikin ƙaton gate ɗin ya tura ƙaramar ƙofar ya shiga. Baya nai luuu na faɗa jikin kujerar na jingina bayana, ina sauke wata nannauyar ajiyar zuciya da lumshe idanu, nace, ‘Na shiga uku ni balkisu’. naja kusan mintuna uku a haka kafin na samu numfashina ya dai-daita. Gaba ɗaya man kaina ya gama tsiyayewa, nama rasa yanda zan fassara abun nasa, nakai hannu na shafa laɓɓana da har yanzu sukemin zafi, sai kuma na buɗe ido na kalli mirror, har laɓɓana sunyi ja, a fili nace, ‘Mugu, aiko Yah Qassem dake dani bai kafan wannan dokarba saishi daga mijin Auntyna’. Sai kuma nai saurin dafe bakin na kalli inda ya tashi sai kace ancemin gashi ya dawo. Da sauri na sake rintse idanu da dafe kai, a fili na sake faɗin, ‘Ya rabbi ka kawomin ɗauki, Mutumin nan zai kasheni’. Sai kuma na harari ƙofar gate ɗin na buɗe motar da sauri na fice abina,
★★
Jawaad kam Haka kawai ya tsinci kansa dayin murmushi lokacin daya buɗe gate ɗin ya shiga gida, sai kuma ya taɓe baki tare da jan ƙaramin tsaki ya nufi sashen mama Atika yana ƙwafa mai nuna takaicin wani abu da har yanzu yake cimasa rai. yasan dai taron meeting ɗin bai wuce can ɓangaren mama Atika ba saboda shegen fitinar tsohuwar. Da sallama ya shiga, suka amsa kusan su duka alamar shi ake jira, wani iri yaji a ransa saboda ganin harda kakansa dasu Umma, yadai samu waje ya zauna sannan ya gaidasu.
★★★★★★★
A LADIES MIRROR kuwa lokacin da abinda ID cards ɗin Bily suke ciki ya faɗi akan idon Safah ne, amma sai taƙi magana, sai da ta tabbatar bily ta daɗe da barin wajen sannan ta ɗauka tana faɗin, “Lah Aunty Meenal diba kiga auntyn nan da nace amin irin kitsontace ta yarda”. Duk kallonta sukayi, Amaturrahman ta dalla mata harara da faɗin, “Shine dan iskanci bakiyi maganaba sai yanzun?”. Baki ta tura gaba tana langaɓe kai gefe, “To ai mantawa nayi ko”. Amatullah tai dariya da cewa, “Kai Safah lamarinki sai ke wlhy, saiki bada a ajiye mata dan nasan zata dawo nema”. Da sauri tace, “A'a aunty Ama mu kai mata dai”. Marwah da tun ɗazun bata kula kowaba tanata game a ipad ɗinta ta harari Safah. Ramawa Safah tai, cikin tsiwarta data gada wajen Munaya tace, “Miye kike wani hararana ke kuma malama?”. Lips Marwah ta cije like Sarki Sameer, ta ɗauke kanta batare data tanka mataba.
Duk yanda sukaso Safah ta bada a ajiyema bily saboda idan ta dawo nema ma'aikatan wajen su bata fir taƙi, daga ƙarshe Amaturrahman tayi kiran Ummu ta sanar mata, Sarauniya Munaya dake kishingiɗe a kilisarta ana tausa mata ƙafa ta girgiza kai kawai da lumshe ido, babu abinda Safah ta bari na halayyarta, ta tabbatar kuma akwai dalilin da yasata yin hakan, a hankali tace, “Kubarta tazo dashi, sai a nema yarinyar”. Amaturrahman tace, “Ummu yanzu nan biye mata zakiyi?” yanke wayar Munaya tayi batare da ta bama Amaturrahman amsaba. Dole badan sun soba akabi abinda Safah keso sukatafi dashi bayan an kammala musu kitso su duka kamar yanda Ummu ta korosu suyi badan sunso hakanba..............✍
Maison zuwa gagara badau ya shirya muje gaida Sarki Sameer Saifudden da gimbiya Munaya😉😉lol.
ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
0 comments:
Post a Comment