****************
"Umaima lfynki kuwa? Yarinya kin dau karan tsana kika dora akan mahaifinki bayan kinsan Allah ne ya hallata masa auren kin isa ki hana ne?
"Wllhi anti khady wannan cin amana ne yanxu shekaru nawa ne da rasuwar mom amma har ya manta da ita? Se kuma ta cigaba da kukanta anti khady ta sake baki tana kallonta sannan ta cigaba da cewa
"Nidai baxan goyi bayanki ba umaima wannan ai rashin gaskiya CE , Allah ya halasta masa auren mata 4 ke kice baki so yayi auren? So kike ya kare rayuwarsa haka?
"Anti kinga yarinyar karamace fah wllhi tun bata shigo ba ya daina kulamu kuma...
"Ki bude kunnuwanki kiji abunda zan gaya miki, ki tashi ki koma ki bawa mahaifinki hakuri ki rungumi kaddara ki xauna lafiya da matarsa Allah ne ya kaddara baki isa ki hana bah "
"Gaskiya nikam baxan iya bah, ynxu dama duk son da yakewa mom ya...
"Dakata umaima bari kiji labarin da baki taba ji bah, dad da mom dinku auren xumunci aka hadasu dad naku ba shi ya nemi auren mom naku bah biyayyace ta sa ya amince ya aurota har Suka xauna tsawon xaman da sukayi.dad dinku bai taba yin soyayya a rayuwarsa bah kuma....
"Wait..an..anti kina nufin duk xaman da sukayi babu soyayya a tsakaninsu?
"Bansani ba umaima Allah shine masani nidai nasan dad mutumin kirki ne yana da kara sosai har gobe baraa sami yaro mai biyayya irinsa bah a duk fadin danginmu"
Shiru umaima tayi tana tunani kanta ya kulle kwakwalwarta ya to she anti kady CE ta dafata a kafada tace
"Kiyi hakuri ya'ta nasan kina taya mom naki kishi but koda ace tana raye itama bata da ikon hana wannan auren kiyi hakuri ki shirya ki koma gun mahifinki"
"Zan koma amma ba yanxu bah, sai bayan bikin nasu "
"Shikenan xan kira dad na fada masa kada ya tada hankalinsa gun nemanki "
"Ok anti nagode"
Haka ta cigaba da xubda hawaye tana jin wani radadi a ckn xuciyarta.
*********
Shuairat CE a gaban dressing mirror tana kallon kanta tabbas ta canza ba kadan bah fatar jikinta se sheki yake ga gashin kanta da ya sha gyara se kuma dadaddan qamshin da yake tashi a jikinta murmushi tayi a yayinda ta cigaba da kallon fuskarta tana admiring din kanta lallai mr President yayi dace😀😀tunaninsa ne ya fado mata a rai fuskarsa ta hango , kyakkyawan karshene ita kanta tasan da hakan kuma yana da karamin ruwa idan bakasan shrkarunsa xaka CE Dan shekara 32 ne ta lumshe ido tana tuna farkon haduwarsu yana magana so cool yana da class sosai kuma yana da tausayi musamman idan ta tuna ranar da ya share mata hawaye lokacin da take kuka, shin zata iya soyayya dashi? Anya kuwa? Hmmmm ko kadan bata taba mafarkin cewa taxa auri babban mutum kamarsa bah sai kuma rayuwarta na baya ya fara dawo mata a kwakwalwa.....
Muje xuwa....
*Reefat*
[2/21, 2:39 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*41*
By *Reefat yahya*
*wacece shuairat*???
Alh Bello mamman hafaffen garin maiha ne na jahar Adamawa su hudu ne a gun iyayensu Ahmadu Salihu bello da kuma zainabu a can garin maiha aka haifesu duka amma shi bello ya koma garin mubi da xama gun wan mahaifinsa a can yayi primary da secondary sannan ya wuce jamia ta bayero Kano a can ya karanta bangaren education, bayan ya gama ya dawo gida a Yola yayi bautar kasa a wannan lokacin ne ya hadu da Fatima ya'r layinsu mahaifinta ne limamin unguwarsu a can karamar hukumar maiha ta jihar Adamawa.
Bayan ya gama bautar kasa akayi aurensu da Fatima shi kuma ya samu aikin koyarwa a makarantar secondary na technical school a can mubi.Bello da Fatima suna son juna sosai kullum suna cike da begen juma haka Suka xauna ckn rufin asiri , sun share sama da shekara 6 Allah bai basu haihuwa bah amma duk da haka bello bai taba nuna damuwarsa bah, Fatima tayi2 ya kara aure yaki sauraranta har ta gaji don kanta ta daina kawo masa xancen.kwatsam Allah ya bata ciki sunyi murna sosai hKa Suka kasance ckn farin ciki har Allah yasa ckn ya cika wata9 da yan kwanaki Fatima ta haifi kyakkyawan danta fari tas babu inda ya bar fuskarta cki kuwa har hasken fata saboda Fatima fara CE sosai, ranar suna yaro yaci suna Basheer.
Haka Suka cigaba da rainonsa har ya girma yayi wayo aka sashi makarantar firamari har ya gama Allah be kara basu wani rabon bah , basheer ya gama primary ya shiga secondary har ya kai ss1 sannan Allah ya bawa Fatima wani ckn batun murna kam baa magana basheer duk yafi xumudi akan cikin kullum hirarsa be wuce xancen a haifa masa kanwa ya'r kyakkyawa.
Bayan wata9 ciff Fatima ta haifi kyakkyawar ya'rta wacce tayi kama da bello tamkar anyi kaki an tofar yarinyar baka CE Amma ba sosai bah tana da Dan hasken fatA , haka aka saka mata suna Aisha ana kiranta shuairat.
Shuairat ta tashi ckn gata gaba da baya koina sonta ake musamman yayanta basheer baya barin kowa ya taba ta, a wannan lokacin Alh bello yana koyarwa a jamiar federal university of technology Yola. Daga kan shuairat haihuwa ta tsaya musu cak da wannan lokacin ko bari Fatima bata sake yi bah, haka Suka rungumi yara biyun da da Allah ya basu.bash ya gama secondary dakyar ya yarda ya tafi jamia wai shi baya son ya tafi ya bar kanwarsa dakyar aka lallabashi ya tafi jamiar Ahmadu bello zaria bayan ya kammala ya dawo yayi bautar kasa sai kuma aka daukesa aiki da state security service , shekaru sun gabata Alh bello yayi retire ya koma gida yana hutawa se kuma dansa ya samu canjin aiki xuwa fadar shugabankasa a wannan lokacin ne shuairat take Jin karshe a federal polytechnic dake can mubi har ta samu ta kammala inda ta karanta bangaren mass communication...
Wannan kenan shine takaitaccen tarihin rayuwarta.
A hnkli ta ja wani gauron numfashi kamar a mafarki take ganin duk abubuwan da suke faruwa a rayuwarta "ikon Allah kenan"
ta furta a hankali ynxu matsalarta shine ya xata fara nunawa mr President so? Anya zai kulata kuwa? Wane irin zama zatayi da umaima? Tabbas tana da aiki a gaba idan batayi da gaske ba xata fuskanci matsala a gidan wayarta ta hau ruri sunan shukrah ta gani nan ta daga
"Matar Yayan"
"Amarya bakya laifi ko kin kashe Dan masu gida"
"Lallai sai dai idan baa kashe din bah , ya kike ya gidan"
"Lfy lau yaushe zaki dawo"
"Umm..kinyi missing dina ne "
"Bani kadai ba harda angon mah"
"Bangane bah"
"Ehh..mana wai dama baki gaya mishi zakiyi tafiya bane?
"Y? Meyasa xan gaya masa?
"Hmm...dazu ya tura bodyguards wai yana son ganinki"
"Uhmm..yayi kyau"
"Munafuka kina so kina nokewa"
"Ehh..sai akayi yaya"
"Nidai ki dawo da wuri kan a buga mana news paper cewa mr President yana Kano"
"Wannan kuma maysalrku "
"Uhmmm..in tayi tsami ma ji"
"Babu abunda zakuji"
"Se anjima toh "
"Ok bye sai na kira "
"Ok takkia"
Tare Suka katse wayar shuairat tayi jugum tana tunani lfy mr President yake Neman ganinta?
Oho!
Nima nace oho! Ku biyoni
[2/21, 2:39 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*42*
By *Reefat yahya*
A bangaren mr President kuwa yana xaune a dakinsa yayi shiru yana tunani anya zasu zauna lfy da yarinyar nan? Ta fiye takama da nuna isa, ysushe sukayi waya amma taki ta sanar dashi cewa tayi tafiya?.mtsww meyasa ya nemi ganinta ma? Lols Reefat tace cos u miss her preety face" wayarsa ya cire yana son kiranta sau 2 yana dialing sai kuma ya fasa a karo na ukun ne yayi ta maza ya kira har ya kusan katsewa sannan ta daya ckn sanyin murya tace
"Ur excellency"
Haka kurum yaji dadin sunan da tayi adressin nasa da shi wani murmushi ne ya subuce a fuskarsa
"My stubborn first lady! Ya kike"
Murmushi tayi da jin sunan stubborn ta gane abunda yake nufi
"Am sorry ur excellency nayi tafiya ba tare da na sanar maka ba"
"Is ok! Zaki iya yin duk abinda kike so as of now b4 ki shigo gidana"
"Don't worry a gidanka ma abunda naga dama zanyi cos am d first lady"
maganar ya sashi dariya sosai yace
"Well..we shall c! Anyway dama ina son ganinki ne saboda ina son sanin programs naki da kuma amount da kike bukata"
"Ur excellency ka kwantar da hankalinka bana bukatar komi iyayena xasu min idan ma akwai bukatar hakan"
"Nasan da haka but is my duty ..anyway zan tura miki 2mil kiyi shopping idan akwai bai isa ba let me know"
"😳2wat? No! No! Me zanyi da 2milion? Walima CE zanyi fah n olredy iyayena sun riga sun tanada komi na walimar so no need pls"
"Bana son jayayya sai anjima"
Nan ya katse waya shuairat ta kurawa wayar ido tana nanatawa 2mil ? Hmmm lallai ma ai wannan almubazzaranci ne.mr president kuwa ya tsinci kansa ckn wani farin ciki haka kawai yana murmushi yana lumshe ido daga nan ya kira bash ya shaida masa yana bukatar account number din shuairat.
***********\\
Jirgin yamma Suka bi sai gasu nan a Abj shuairat ta kara haske fatar jikinta ta murje tayi kyau sosai duk Wanda ya daga ido ya kalleta dole ya kara kallonta a karo na biyu. Bash ne yazo daukansu ita da anti mairo da diyarta Sadiya wacce take saar shuairat daga nan Suka kama hanyar gida .
Gidansu a cike yake makil da jamaa babu masaka tsinke saboda saura 4days daurin auren shuairat , bangaren shukrah ta shiga a yayinda haj mairo ta wuce gun aminiyar tata ga danginsu nan birjik mutanen Adamawa kyawawa dasu falon shukrah a cike makil da jamaa ta sa kai tare da sallama shewa Suka fara yi wata ya'r kawun shuairat me suna Ummi ta tashi Suka rungumi juna da shuairat se ihu suke sai ga shukrah ma ta fito ta Ruga a guje Suka rungumi juna ta kalli shuairat tayi wani guntun dariya tace
"Gaskiya ne mata a gidan Dr Suleiman Muhammad first ladyn Nigeria da kanta, kasar ta kusa ta dawo hannunmu sai yanda muka juya ta"
Aikuwa sauran yan matan Suka fara shewa
"Aiyuriri ...mata a gidan shugabankasa Allah ya bar mana ke"
Dakyar shuairat ta samu ta shige dakin yayanta ita da shukrah da Ummi da kuma Sadiya.shukrah ta kawo musu lafiyayyen abinci ita da Sadiya Suka ci sukayi nak sannan aka baje a gado aka fara xuba shukrah tace
"Bestie kawaye nawa kika zaba"
"Ummi da Sadiya da maimuna ya'r anti luba sai kuma Hafsat mubi"
"Ok! Dama mr President ne ya turo yayanki yazo ya tambaya kuma tym din layinki baya shiga""
"Ok na kashe wayar ne tym da zamu tashi"
" mr President fah yana ji dake yarinya ! Kinga kalan zirga -zirgan da yan gidansa suke?
"Allah ko"
"Ehh ..mana wllhi ki rike tsohon nan da kyau don na lura yana sonki sosai"
Gaba daya Suka kwace da dariya Ummi tace
"Wa ya gaya muku shi tsoho ne? He is just 40 somtin ne fah "
Sadiya tace
"Gaskiya kam! Kimanta da zancen wani tsoho ki fito ki nuna masa so zalla Ku zauna lfy ya fiye miki wllhi, kuma kinga yana da wata shu'umar ya' mai shgen girman kai kada ki kuskura ki bari ta rainaki wllhi"
Shuairat tayi murmushi tace
"_ina nake da lokacin ta"
Mama CE tayi sallama a bakin kofar dakin shuairat ta ruga a guje ta bude ta fada a jikinta tana dariya
"Mama na I miss u"
"Ba wani u miss me bayan kinzo kinyi zamanki a nan baki nemi gani na bah"
"Wllhi Bahaka bane! Naga mutane sunyi yawa ne"
Daga nan tabi bayan Maman nata sukayi ckn gida.
Love u my fans😘😘
[2/21, 2:39 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*43*
By *Reefat yahya*
Karfe 4pm harabar city garden ya cika makil da manyan motoci kala2 idan ka duba can ciki bangaren da akayi decoration kuwa xaka bude baki ne galala tsantsan haduwar filin nikam xan iya cewa tunda nake ban taba ganin hadadden decoration irin haka ba😜😜😜 dama ansan city garden waje ne mai kyau kuma babu hayaniya se kukan tsuntsaye ga kuma flowers masu kyaun gaske anyi arranging kujeru kowane table kujeru hudu na zagaye dashi an rufesu da kyalle masu kyau colors daban2 wato multi color kenan haka nan bangaren da amarya zata zauna tare da kawayenta ma multi color ne abun de sai Wanda ya gani.
Idan ka duba kujerun sun cika da jamaa dangin mr President yan uwan marigayiya matarsa zainab dangin Maman shuairat da kuma dangin babanta ko ina dai manyan mata ne ansha ado na kece raini ga yan Adamawa kyawawa sun kara haska wajen both dangin ango da na amarya duka fulanin Adamawa ne idan kaga mummuna dai yan ganyan sodi ne😜😜 a dayan bangaren kuwa invited guest ne ga matan ~gidan gyara~ ~Nisaul jannah~ ~professional writters~ ~Hausa novel grp~ ~dangin juna~ ~qasaitattun mata~ da dai sauransu.idan ka duba wani bangaren kuwa *adda bena*CE da *m jabo* *pherty* *Maman shakur* *khaleesat haidar* *miemie bee* *Ummi Aysha* da sauran online writers nima a can na xauna ina watsa rubutu na. Yan gidan TV radio da news papers duk sun hallara ana daukan live a kowane tashar TV idan ka kunna xaa hasko maka walimar Aysha (shuairat) bello matar mr President😊, nayi rubutu har na gaji sai na taba miemie nace "amarya baxata zo bane" ta watsa min harara tace "tsiyata dake kenan rashin hakuri"😏 daga nan naja bakina nayi shuru wani dadaddan qamshi ne ya buga hanci na ina daga kai na hango shuairat tare da tawagarta😱😱😱
Mutuwar xaune nayi *halamcy* CE ta saka hannu ta tare min baki na Wanda saura kiris ya fada kasa...hmmm kawai na ajiye Biro na nace baxan iya siffanta irin wannan kyawun bah sai Ku jira *afrah* idan ta gama da jumaiya se ta siffanta muku kyaun da shuairat tayi.😊😊😊Amarya da kawayenta Suka sauna a filin da aka tanada musu nan kuwa yan jarida Suka fara daukansu hoto wal...wal hasken kamera kawai nake gani sai kuma aka bude taro da adua nan malama Maryam ta fara gabatar da waazi akan hakkin aure da rayuwar aure a musulunci.haka aka cigaba da taron masu video recording nayi masu daukan hoto nayi ga yan jarida iri2 ga reportrs din tambari magazine ga JF ma sun tura Mahmud Wanda kansa me kallon kasa yana jin wani radadi har ckn ransa .Karfe 6pm aka raba souvenirs iri2 har da kayan makeups a ciki abinci kuwa dama table by table aka raba daga nan akayi adua sannan kowa ya fara shirin komawa gida a yayinda wasu sukaje daukan pix tare da amarya dakyar ta samu hanya wannan ma don bodyguards ne.
😘😘😘
[2/21, 2:39 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*44*
By *Reefat yahya*
Yau aka daura auren Ayshat bello maiha tare da Alh Suleiman Muhammad mayo ( PhD) akan sadaki naira 100k jamaa da dama Suka halarci daurin auren manyan kusocin gwamnati tare da manyan sarakuna ta kasashe daban-daban ga mutane dai talaka da masu arziki , yan jarida suna nan birjik an daura aure lfy aka watse daga nan villa Suka wuce akayi hadadden reception kowa ya ci ya sha sannan aka watse ango de furkarsa na dauke da murmushi .
A can bangaren amarya kuwa ta sha kwalliya ckn wata hadaddiyar shadda masu kyau da tsada ga gwalagwalai carkaf a kunne da wuyarta tayi kyau tmkar a saceta a gudu tana zaune a bangaren shukrah tare da kawayenta.ta buga wani uban tagumi shukrah CE ta shugo tare da sallama
"Amarya bakya laifi ko kin kashe sultan lolz"
"Hmmm...lallai mah rufa min asiri kan a jiki"
"Tashi muje an tura camera man yazo ana ta daukar hotuna"
"Kuje Ku dauka nikam na gaji"
"Haba ranki shi Dade, kinsan gobe war haka fah ganinki sai da ticket ki tashi muje muyi last card pls"
"Mttsww...me wani na cewa last card sai kace mutuwa zanyi"
Su Ummi suna mata dariya haka Suka fita akayi ta daukan hotuna da yan uwa da abokan arziki.
Tun Karfe 5 shuairat ta shiga wanka tare da anti mairo har magrib suna ckn bayi shiru kawai kake ji na so zuwa in gano me ya sukeyi acan Amma ba dama haka na hakura na zuba ido.by 7 Suka fito amarya sai qamshi take tmkar anyi barin turare dakin mama Suka wuce ta saka wasu atamfa ya'r super mai uban kyau da tsada batayi wani makeup bah dakin babanta aka kaita ya mata nasiha sosai tAna kuka Suka koma dakin mama a can aka kawo mata dafaffiyar kaza ta sha hadi sosai dole ta cinyeshi Tass sabida anti mairo ta sata a gaba, mama CE ta shigo haj mairo tace
"Mutuniyar idan akwai abunda zaki gaya mata kiyi sauri cos ance by 8 zamu wuce da ita gidan mijin nata"
Mama ta sunkuyar da kai tace "ba komi duk abunda ya dace ki sanar da ita " daga nan ta tashi ta tafi haj mairo ta kara fesheta da turare sannan Suka wuce bangaren yayanta baya nan Mr president ya kirashi haka suka zauna ckn shiri by8 Suka ji tsayuwar motoci . duk yanda shuairat taso ganin mamanta don suyi sallama abun ya gagara firr mama taki fitowa haka Suka hakura yan raka amarya Suka shirya Suka fito shuairat kam se kuka take anti mairo na bata hakuri daga nan akayi mota da ita.
Motocine masu kyau se sheki sukeyi gasu nan birjik sai Wanda ka zaba daga nan Suka dau hanyar villa.
Bayan sun iso gidan aka wuce wani dankareren building upstairs ne mai kyau gaskiya bazan bata lokacina ina zayyana muku tsaruwar ginin bah kawai de kunsan gdn shugabankasa kam😀😀karshen kyawu kenan. Yan rakiyar amarya sun zaga building din ko ina suna ta yabawa , an nuna musu dakunan daga nan anti mairo ta sallami kowa ya rage daga ita sai kawayen amarya da wata yar mama se kuma kanwar baban su shuairat. Dangin ango sun shigo wasu mata kyawawa su 6 Suka shigo musu maraba tare da ajiye musu abinci mai rai da lfy sannan Suka tafi. Kawayenta daki daban aka ware musu ita amaryar kuwa da anti mairo zata kwana, bayan sunyi shirin kwanciya Karfe 11pm anti mairo ta ajiye shuairat ta fara mata nasiha..
"Baby kiyi hkri bansan ko kina son mijinki koma yaya ne ki daure ki fara sonshi ki koyawa kanki yanda zaki so shi , haka nan shima ki koya masa sonki ki dasa sonki a ckn zuciyarsa Ku zauna lfy.yi nayi bari na bari kuyi hkri da juna wannan shine zaman aure, bauta ne ya kawoki ba wani Abu ba aljannarki kika zo nema kiyi kokari ki kasance mai faranta ran mijinki.ki zauna lfy da kowa ki mutunta kowa nashi ki daraja iyayensa ki girmamasu ki kula da dukiyarsa da ya'yansa, fada da umaima ba naki bane ki kame girmanki kada raini ya shiga tsakaninku...haka dai anti mairo ta cigaba da mata nasiha masu ratsa jiki daga karshe Suka kwanta.
😍😍😍lov u all
[2/21, 2:39 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*45*
By *Reefat yahya*
Da misalin Karfe 9 na safe masu aiki sun gama gyara komai na gidan sai qamshin air freshener ke tashi an jera abinci kala-kala a dinning table.building din dakuna 4 a sama da babban falo a tsakiya da dinning table mai kujeru6 sai kuma dakuna 3 a kasa da kitchen da kuma dinning mai kujeru 10 ga wani tangamemen falo da kujeru duma2 har set 4 kai kayan more rayuwa dai an narkasu a wanga falon.
Shuairat tayi wanka tayi ado ckn wani uban leshi Wanda zai kai 100k golden n lemon green da milk color ta saka yan kunnen gold mai tsadan gaske tayi kyau sosai tana tsaye a gaban dressing mirror tana kallon kanta yanda ta chanza tayi kyau sosai, anti mairo ta shigo dakin itama ckn uban kwalliyarta tana murmushi tace
"Wow my baby is looking gorgeous kinyi kyau sosai I wish Mr president zai ganki yanzun nan"
"Tnx anti" ta fada tana murmushi anti mairo ta rike hannunta Suka bar dakin sai kuma ga sauran yan uwan nata sun fito kowacce ckn ado na alfarma tare da kawayenta anti mairo na gaba tana rike da hannun shuairat Suka fito sai zuba gaisuwa ake musu wani Dan building Suka nufa me karen kyau .
Sun shigo tare da sallama wani makeken falo ne a cike makil da jamaa mata zalla gasu nan birjik kowacce tasha ado tana ji da kanta ckn faraa aka karbesu daga nan aka fara gaisuwa.
Bayan kowa ya nitsu anti mairo ta fara magana
"Ga ya'rmu nan mun kawo muku sai Ku riketa da amana idan tayi abunda ba dai2 bah a nusar da ita ko kuma a sanar damu saboda karama ce , Allah ya basu zaman lfy da zuria dayyiba"
Gaba daya falon aka amsa da ameen .sai ynxu na lura da wata dattijuwa mai kyaun gaske kamarsu daya da Mr president tunda aka shigo da shuairat se murmushi take a hnkli ta fara magana
"Insha Allahu zamu riketa hannu2 Allah ya basu zaman lfy da ya'ya nagari"
"Ameen" aka sake amsawa daga nan aka kai shuairat kusa da wannan matar Suka gaisa ta rike hannun shuairat cike da so tace "ya'ta Allah ya miki albarka kiyi hkri nasan zaku zauna lfy insha Allah "
Bayan wani lokaci kowacce tana Dan tufa albarkacin bakinta tare da musu fatan alheri daga nan aka fara daukansu hotuna sai kuma kyaututtukan da shuairat ta samu na ban mamaki wato turamen zani ne da lesuna sai kuma kdade mai dumbin yawa kai sunga abun arzki kam daga karshe Suka koma bangaren ta.kowa yana yabawa dangin Mr president da irin karamcin su.
Wani bodyguard ne ya shigo ya sanar dasu cewa Mr president na son ganin shuairat tayi shiru bata CE komai bah anti mairo CE ta jawota xuwa daki ta kara fesa mata turarurruka iri2 sannan ta kara powder da lipstick tace mata
"Saura kije kina wani nokewa , feel free mijinki ne"
Murmushi kawai shuairat tayi tana mamaki halaye irin na anti mairo daga nan ta sauka zuwa kasa inda bodyguard din yake jiranta daga nan Suka wuce ckn mota ya kaita bangaren Mr president.
Sau daya ta taba zuwa amma yau taga komai ya canza mata an sake fenti da furniture's da komi a bakin kofa bodyguard din ya tsaya ta karasa.
Bata sameshi a falon farko bah don haka ta wuce personal falonsa ta shigo tare da sallama yana zaune ckn manyan kaya yayi kyau sosai ko don ta kwana2 bata ganshi bane oho ya amsa ba tare da ya daga fuskarsa bah yana danna waya da alama wani yake son kira ta nemi waje ta zauna suna fuskantar juna. Shiru sukayi sai kuma ta tuna cewa ynxu itace kasa dashi nan kuwa a hnkli ta furta
"Ina kwana ur xcelency"
Wani kayataccen murmushi ya sakar mata duk da cewa baya kallonta sannan ya amsa ckn wani salon ji da kai
"My first lady kin tashi lfy"
"Lfy alhamdulillh"
"Hw was ur nite ya bakunta"
"Lfy kalau"
"Daz grt, dama na kiraki ne ina son jin nawa zaa sallami frenz naki"
Shiru kake ji ta rasa me zata gaya masa yaji shirun yayi yawa don haka ya daga ido 😳😳😳 masha Allah haka ya furta a ckn zuciyarsa dama yarinyar nan haka take da kyau? Wow..she luks soo...btiful" carab Suka hada ido a dai dai lokacinda shuairat ta daga kanta , kowannensu yayi saurin dauke kai zuciyoyinsu ne ke harbawa.Mr president ya daure yace
"Kinyi shiru"
"Uhmm...gskiya nima bansani bah just give dem...
"No first lady! I hate dat word "bansani bah" ki gayamin pls"
Nan ma tayi shiru sai kuma ta tashi ya bita da ido har ta kai bakin kofa yace
"Ina zakije kuma muna magana"
"Uhm...zanje gun anti mairo ne"
"Zakije ki tambayeta nawa ya dace ?
Murmushi yayi yana tunani shi kadai cewa lallai akwai yaranta a tattare da ita
"Ok dawo ki zauna tunda baki sani bah lemmi tink on my own" ba gardama ta koma ta zauna yana danna waya can ya kara a kunne yace
"Ka tura sakon da na baka jiya ?
Ok yes ka hada duka ka basu a ckn gida "
Daga nan ya kashe wayar ya maida kallonsa gareta sun kurawa juna ido can shuairat ta kauda fuskarta yana Murmushi sannan ya fara magana
"Aysha ynxu idan aka baki mukamin first lady haka zaki dinga yi?
Ta daga kai ckn rashin fahimta yace
"Yes! Wat I min is dai komi sai kin tambaya ? Bazakiyi on ur own bah?
Ta zumbura baki tace
"Ni...ni nace a bani first lady ne dama"
A hnkli ya taka xuwa gabanta ya sunguna idanunsa a kanta suna fuskntar juna shuairat ta sunkuyar da kai tana wasa da warwaronta yasa hannu ya daga habarta Suka kurawa juna ido yace
" ke matata CE dole zaki koyi yanda zaki gudanar da wasu harkokin on ur own , u have to fight Aysha"
Bash ne tare da wani bodyguard Suka shigo tare da sallama ganin halin da Suka tarar da ogan nasu a ciki ne yasa Suka bar wajen shuairat kuwa kunyane ya kamata haka nan Mr president ma nan da nan ya tashi ya koma kujerar da yake da ya zauna ya dannawa bash kira a waya Suka shigo Suka sanar dashi cewa yayi baki daga England nan ya tashi Suka fita tare shuairat kuwa bodyguard Suka rakata ta koma bangaren ta.
😍😍😍👍🏼😘lov u all
[2/21, 2:39 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*46*
By *Reefat yahya*
Ta shigo bangarenta kawayenta suna mata tsiya Hafsat tace
"Ohhh shuairat an kasa hakuri a jira mu koma mana"
Ummi tayi dariya tace
"Gane min hanya dai da ana nokewa wai tsoho zaa aura ba zancen love gashi nan tun baaje ko ina bah an fara lumewa"
Suka fashe da dariya Suka shewa anti mairo ta shigo tana dariya tace
"Rabu dasu baby nah love kam kowa ma yana yi sai Wanda bai samu bah , Ku kuwa Ku tashi Ku tattara mu bar musu gida ynxun nan"
Suna dariya se kuma Suka hau godiya abun arzikin da Mr president ya aiko musu kowacce an bata kaya lace super da kuma Holland se kudi 120k shuairat kam mamaki ne karara a fuskarta sai kuma ta share zancen haka nan su haj mairo ma an basu kudade Masu yawa daga nan ta sake Jan kunnen shuairat akan zaman da zatayi a gidan tare da koya mata wasu dabarun sarrafa miji Wanda ba sai na fada bah😜 nan sukayi sallama shuairat ta fara hawaye haj mairo tace kul..karki bata kwalliyanki daga nan motoci Suka kwace su sai gida aka bar amarya daga ita sai halayenta sai kuma masu aiki.
Sama ta haura sai ynxu ta samu damar karyawa tea ta hada sannan ta Debi chips kadan da kwai ta zauna ta cinye tas sannan ta dawo falo ta kunna TV MBC ta kama tana kallon film din "triple X" yan uwan Mr president ne Suka shigo sun Dan taba hira daga nan Suka shaida mata cewa yau zasu wuce Adamawa wasu kuma Kano wasu kd da kuma Lagos, cin-cin doughnut da cake ta diba musu da turarurruka masu yawa ta basu suna godiya Suka tafi. Haka masu aikin Suka shigo Suka gabatar da Kansu nan ma ta kawo musu abubuwa iri2 suna yaba mata Suka koma bakin aikinsu.
A can bangaren Mr president kuwa wasu turawa ne Suka zo tayashi murnan auren da yayi maza 3 da mata 2 dukkansu manyan mutane ne masu fada a ji a can kasar England daga fadar sarauniya Suka zo don haka Suka nemi ganin amaryar tasa Mr president ya daga waya bayan ya Dan fita daga dakin da aka sauke bakin nasa layin shuairat ya kira ringing 2 ta daga
"Hello ur xcelency"
Wani yarr...yaji a jikinsa dakyar ya saita kansa yace
"Ki shirya baki nayi kuma turawa ne suna son ganinki"
"Eyya...Mr president y not su bari xuwa dare Allah na gaji ynxu bacci zanyi"
Tayi maganan ne ckn wani salon shagwaba murmushi yayi shi kadai yasan ma'anar yace
"Ok sorry ki huta zuwa daren sai ki shirya koh"
"Ok tnk u my dear"
Nan ta kashe wayar ya tsaya Jim...tmkar mai tuna wani Abu sai kuma ya nanata kalamanta na karshe "tnk u my dear" nan ya sake yin murmushi haka nan tun jiya yake jin kansa ckn wani nishadi daga nan ya koma gun bakin nasa ya basu hakuri cewa amaryar tasa tana tare da baki sai zuwa dare zasu gan ta haka Suka cigaba da hirarsu.
Bash da john suna zaune a waje John ya juya ya kalli bash yace
"Aboki Mr president fah ya fada tarkon son yarinyar nan ba kadan bah"
"Me ka gani john?
"Haba ...kana ganin yanda muka samesu dazun"
"Hmmm...next tym zamu hana kowa zuwa bangaren Mr president sai da izininsa cos yanzu yana da iyali bai dace ana shiga anyhw bah"
"Yes haka zamu yi"
Daga nan sukayi shiru shi kansa bash yana mamakin kalan soyayyar kanwar tasa da Mr president hmmm...mata kenan zasu maida tsoho yaro.
Shuairat kuwa tana zaune a falo har bacci yayi awon gaba da ita se bayan azahar ta farka tayi sallah sannan ta fada wanka, wani material pitch color ta saka dinkin buba da zani ta saka danyar gwal mai kyau ta fesa turare se qamshi ke tashi. Dinning ta wuce masu aiki suna tsaye a gefe aka zuba mata rice n chicken ta fara ci a hnkli tmkar bata so sai wani yauki take. wata mata ta shigo tare da wani Dan yaro nan kuwa ta gane sultan ne nan ta sake fuska tana faraa sun karasa falon ta musu tayin abinci matar ta jawo kujera ta zauna shuairat ta rike hannun yaron tace
"Boy zo mu ci tare" ba musu sultan ya karasa gunta ta daurashi a kafa nan ta fara bashi a baki suna ci suna hira masu aiki kam se yaba halayenta suke nan da nan anty khady ma taji son shuairat ya shige ta don ba haka tayi tsammanin ganinta bah ta dauka shuairat irin matan nan ne masu girman kai da wulakanta mutane.sunyi hira sosai bayan anty khady ta damka mata amanar sultan nan kuwa ta karba ckn jin dadi Suka rabu akan anti kadi xata koma yau.
Haka shuairat ta kasance tare da sultan tana biye masa duk abunda yake so shi zatayi sunyi game sunyi kallo sunyi karatu haka Suka kasance har lokacin sallan la'asar nan ma tare sukayi sallar shuairat ta masa wanka ta canza masa kaya sannan Suka tafi bangaren momsi( Maman Mr president )
Love u alll😘😘
[2/21, 2:39 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*47*
By *Reefat yahya*
Sun shigo falon tana tare da wasu mata su 2 nan shuairat ta gaishe su sannan ta zauna a gefe momsi kuwa wani irin dadi taji don anty khady ta shaida mata komai fuskarta dauke da murmushi ta fara Jan shuairat da hira tana tambayarta ko ta taba zuwan mayo belwa can Adamawa haka dai Suka cigaba da hira shuairat ta sake kadan suna hira sultan kuwa yana makale da ita, aka kawo musu fruits da drinks dakyar shuairat ta dau apple kwaya1 tana ci wannan ma saida momsi ta bata rai ne ta nuna mata cewa ta dauka nan gidan su ne ta daina jin kunya ta sake jikinta nan ne shuairat take tmbayar ina umaima aikuwa momsi ta zayyana mata daga biri har wutsiya sannan ta Dora da nasiha kan cewa tayi hkri da halayen da zata fuskanta gun umaimA haka dai Suka cigaba da hira har magrib sannan ta koma bangaren ta tare da sultan , bayan sunyi magrib da isha ta dibawa sultan abinci yaci ya koshi ta kunna masa cartoon yana kallo har yayi bacci nan ta daukesa ta kaisa dakin barcinta daga nan ta fada wanka.tana fitowa ta tsara wani uban kwalliya sannan ta fito da wani hadaddiyar dinner gown silver da duwatsu a jiki sai shinning suke ta sanya rigar mai dogon hannu pencil hand ya dame hannunta haka nan rigar dai-dai da jikinta ta saka wasu English diamond mai uban kyau ta daura wani red net daurin step har 6 tayi kyau sosai ta saka takalmin Vinci red color ta rike clutch purse din shima red ga red lipstick tayi kyau sosai woow....ta fesa turaren laylatul sahr da musk- almudhakkr se kuma far away , bleu feeling, diable bleue, to nyt , mekako Miami, Cuba , touch me da kuma esabella Curie.☺☺☺ turare 10...hmmmm qamshi kam baa magana ita kanta tasan ta hadu sosai.wayar intercom na dakin ne ya fara ruri ta daga wata mai aiki CE take sanar da ita cewa Mr president ya turo mota yana bukatar ganinta nan ta ajiye wayar ta kurawa fyskarta ido a ckn mirror tace
"Wow...yarinya kinyi kyau but hakan ya dace ta fita ne ko ta yafa gyale? Ahhh....turawa ne bata son su mata kallon bakauyiya don haka red net din ta dauko wani ta yafa sannan ta daurashi ta baya tayi kyau sosai😘😘😘😘.
A hnkli take takawa har ta fito falon ba kowa duk masu aikin sun koma bangaren su sai masu gadi a waje ta Tarar da bodyguard din 😳😳😳gaba daya Suka zuba mata ido dakyar ya saita kansa ya bude mata gidan baya ta shige daga nan ya ja motar .
Bangaren saukan baki sukayi parking ya bude mata kofa ta fito tana takun kasaita ta hadu da yayanta yana fitowa murmushi ta sakar masa sannan ta wuce ya tsaya galala yana kallonta har ta bace masa da gani yana tsaye yana mamaki shi kadai. Suna zaune a dinning area da alama ita ake jira Mr president ne yake fuskantar kofa tana shigowa ya kasa dauke idonsa a kanta tmkar a mafarki haka ya ganta kurrr ya ajiye ido ya kasa motsi tana murmushi ta karasa kusa dashi ta mika masa hannu nan ya tashi yana rike da hannunta gaba dayawa turawan sun shagala da kallonta basu taba ganin bakin fata kyakkyawa irin shuairat bah.Mr President ne ya katse musu tunani ta hanyar cewa
"Pls meet my wife mrs Suleiman"
Murmushi shuairat ta sakan musu sannan tace
"Hello everyone" tare da mikawa matan hannu sun gaisa ckn faraa sannan Mr president ya jawo kujera kusa da nasa nan ta zauna tare da cewa
"Tnk u Darling"
Ckn wani tsiga tana fari da ido Mr president kam se kallonta yake tmkar wata sabuwar hallita nan shuairat ta fara musu barka da xuwa tare da basu hakurin rashin xuwanta akan lokaci, haka nan ta sace zukatansu hira sosai sukeyi ckn harshen turanci Mr president in banda murmushi babu abunda yake shuairat ta bashi mamaki sosai nan da nan Suka fito da wayoyinsu aka fara daukan selfie an dauketa tare da Mr president ma sunyi kyau sosai nan aka fara turawa a instagram da Facebook ana taya Mr president murna. Daga karshe Suka gabatar da kyaututtukansu diamonds golds da dalolin amurka shuairat de tasha kyaututtuka da dama har wajen 12 sannan kowannensu ya koma masaukin sa shuairat ta tashi zata tafi Mr president ya rike hannunta sai kuma ya rungumeta gam a jiki, mutuwar tsaye tayi ta kasa motsawa Sun share minti 3 ckn wannan hali dai2 nan john ya shigo don kulle kofa aikuwa a 360 yabar bangaren ya tsaya a waje ya rike kai yana maida numfashi . Mr president ya motsa bakinsa a hnkli yace
"Allah ya miki albarka nagode sosai ki fitar dani kunya tnx much Allah ya biyaki"
"Amee..men" dakyar ta amsa daga nan ya sake ta yace
"
"Muje ki kwanta dare yayi"
Nan ya rike hannunta Suka fita gidan shiru sai securities ke kaiwa da komowa sunata kallon Mr president hannunsa tsarke ckn na matarsa suna taku a hnkli farinwata da hasken fitillun gidan sun haska koina , haka Suka cigaba da tafiya har xuwa bangaren shuairat aka bude musu kofa a tuaninta nan zai dakata da rakiyar se kuma taga ya biyota har dakin bacci ya bude kofar ga mamakinsa sultan ya gani kwance yana sharar baccinsa ya juya Suka hada ido tayi murmushi nan ya sake mata hannu ya koma kusa da sultan ya shafa kansa tare da tofa masa aduoi daga nan ya tashi yace
"Nagode sosai gud nite"
"Nite" ta fada a hnkli daga nan ya sa kai ya tafi tare da rufe musu kofar yana tafiya yana murmushi shi kadai yasan abunda yake ji.
😘😘😘😘ku biyoni kusha labari
*Reefat* ce
[2/21, 2:39 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*48*
By *Reefat yahya*
Shuairat ta gama shirin kwanciya tsaf tayi aduoin bacci ta kwanta sai kuma abubuwan da Suka faru tsakaninta da Mr president ne yake yawo a kwakwalwarta haka nan ta tsinci kanta ckn wani farin ciki he is so calm bashi da matsala tabbas idan haka yake toh lallai zasu zauna lfy.haka dai ta cigaba da sake sakenta har bacci yayi awon gaba da ita.
A bangaren Mr president ma hakan ta kasance Sam ..ya kasa yin bacci fuskar shuairat yake gani idan ya rufe idanunsa dama matarsa wayayyiya ce? Daman haka take da kyau? She is so cute n presentable.tabbas yayi dace kuma yaji dadin ganin sultan a dakinta da alama tana son yara kuma xata rike masa sultan da amana , haka nan ta faranta masa rai haka ya cigaba da sake sake har bacci ya daukesa ba tare da ya sani bah.
Asuban fari shuairat ta tashi tayi wanka tare da daura alwala tayi nafilfilun ta sannan tayi sallar asuba tayi lazimi bayan ta gama tayi adua ta shafa sannan ta koma bakin gado ta zauna a hnkli ta fara shafa kan sultan bayan wani Dan lookaci ya bude ido a hnkli tace
"Boy tashi kayi sallah koh"
Ckn muryan bacci yace
"Um um anty nikam ki bari ba ynxu bah"
"Haba my boy jiya fa cemin kayi kana son ka shiga aljannah ka tuna?
Kai ya gyada mata tayi murmushi tace
"Good! Duk Wanda baya sallah akan lokaci bazai shiga aljannah bah, oya get up"
Nan kuwa sultan ya tashi ya shige toilet yayi alwala ya fito ta shinfida masa sallaya ya tada sallah tana zaune tana kula da yanda yake sallar a natse lallai ko ya iya batayi mmki bah sabida a hiran da sukayi ya gaya mata akwai malamin da yake xuwa har gida yana karantar dashi.bayan ya idar da sallah nan ya koma gado ya kwanta shuairat tace
"Boy ba gaisuwa ne?
Murmushi yayi yace
"Morning anty!
Ta shafa kansa tace
"Morning my boy! Ynxu se mu dau Qur'an mu karanta koh"
"Anty bacci nake ji kuma kinsan anjima zanje skul "
"I knw my boy! But pls mu karanta koda 5pages ne se mu koma bacci koh
"No! 5pages yayi yawa"
"Ok 3pages koh"
Dakyar ta lallabashi ya karanta pages 2 na suratul baqarah sannan ya kwanta , ita kuma ta cigaba da karatu har 6:30 sannan ta wuce falo nan ta hadu da masu aiki suna xuba gaisuwa ta bukaci su kawo mata kayan makarantar sultan babu bata lkci kuwa aka kawo duk abunda zai bukata ta bada umarnin a shirya masa kayan kari sannan ta koma daki.
Karfe 7am masu aikin sultan Suka nemi izinin ganin sultan saboda xaa mishi wanka ya tafi skul, shuairat ta hana.ita kanta ta masa wanka ta shirya sa ckn kayan makaranta ya fito fes dashi ta fesa masa turare itama ta sha wanka tayi ado ckn atamfar super masu kyau ta ajiye dankwali ga gashin kanta ya kwanta a kafada tayi kyau sosai tana rike da hannun sultan Suka fito falo masu aikin Suka kura musu ido tabbas sunyi kyau sosai.
Dinning area Suka wuce a nan ta zuba masa abinci yaci sosai tana xuba mishi hira ckn raha tana biye wa duk shirmensa har ya gama aka kai jaka da lunchbox nasa a mota.an bude motar ana jiran fitowarsa shuairat ta rike hannunsa tace
"Muje ka gaida dady koh"
Ba musu Suka wuce bangaren Mr president masu aikin Suka xuba musu ido ckn shaawar ganin sabon chanjin rayuwa da sultan ya samu.a hnkli ta tura kofar dakin da take tunanin dakin barcinsa ne sabida basu tarar dashi a falo bah, ta shigo tare da sallama yana zaune da Qur'an a hannunsa bayan ya rufe qur'anin ya amsa sallamar nan Suka hada ido shuairat tayi saurin dauke kanta
"Good morning ur Excellency"
"Morning hw was ur nite dafatan kun tashi lfy mom sultan"
Wani kayataccen murmushn jin dadi tayi saboda sunan da ya kirata dashi
" lfy alhamdulillh dady sultan hop kaima haka"
"Alhamdulillh"
"Dady good morning"
Sultan ya furta bayan ya karasa kusa da mahaifin nasa
"Morning my boy "
"Laa..dady kaga anty ma boy take kirana fah
Murmushin jin dadi yayi yana kallon shuairat wacce kanta ke kallon kasa
"Dady kaga yau na karanta Qur'an har 2pages ni da anty
"Wow...am so happy my boy kip it up koh Allah ya muku albarka da kai da antyn naka "
"Ameen dady"
Shuairat ce ta katse hiran nasu ta hanyar cewa
"My boy kamanta mota na jiranka kar kayi latti let's go"
Ya tashi tsaye yace
"Bye dad na tafi"
"Ok takkia ayi karatu banda wasa koh"
"Ok dad zanyi cos anty tace idan ina karatu sosai zata siyamin yacht kuma zan shiga aljannah"
Dariya sosai Mr president yayi yana kallon shuairat gwanin birgewa yace
"Ok a dawo lfy"
Daga nan Suka fita Suka bar dakin ya bisu da kallon shaawa shi ganin shuairat yake tmkar ita ta haifi sultan nan da nan wani farin ciki ya ziyarci xuciyarsa ya manta da duk wani bakin ckn da yake cki a da tabbas maganar dadynsa gaskiya ne da yace masa shuairat zata zame musu alkairi a rayuwa zata kawo musu farin ciki , gashi tun baaje ko ina bah ya tsinci kansa ckn farin cki Mara misali.
Ku biyoni love u my fans masu turamin mssg ta private tnx alot I love u all😘😘😘
[2/21, 2:39 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*49*
By *Reefat yahya*
Shuairat ta raka sultan a bakin mota suna dagawa juna hannu har ya bace mata da gani sannan ta wuce bangaren momsi a falo ta sameta tana xaune da carbi a hannu ta karasa tare da sallama sun gaisa ckn girmamawa ta amsa tana mai faraa daga nan ta bukaci shuairat ta jira daddy ya fito su gaisa bayan yan mintuna Alh Mohammed ya shigo falon fuskarsa dauke da murmushi Suka gaisa da shuairat daga nan ta musu sallama ta koma bangarenta daki ta shige ta haye gado tayi kwanciyarta wayarta ce ta hau ruri layin anti mairo ta gani nan ta daga
"Ina kwana anty"
"Amarsu ta ango an tashi lfy ya gida ya kadaici"
"Alhamdulillh anty dafatan kuna lfy"
"Lfy me kikeyi haka"
"Wllhi ynxu na dawo daga rakiyar sultan ya tafi skul shine nace bari na samu bacci kadan"
"Kaji min yarinya da shirme..sultan kika aura ko ubansa? Bazaki je ki duba lfyar mijinki bah se dansa?
"Anti naje mun gaisa fah dazu"
"Haba baby..ynxu duk abubuwan da na gaya miki sun tashi a banza kenan? Mijinki ne bazaki je ki kula dashi bah ki tabbatar yaci abinci yayi shirin office sannan ki mike a gado wai bacci zakiyi ? Anya zaki sinana abun kirki kenan..
"Eyya fah anty..
Ta fada ckn shagwaba
"Eyya me? Ki tashi maza ynxun nan kije ki kula da mijinki ki tabbatar ya shirya ya fita office kan ki dawo kiyi baccin..aikin me zakiyi girki ko shara? Eyye..
Haka dai anti mairo ta dinga balbale shuairat da balai ba shiri ta tashi bayan sunyi sallama ta sake fesa turare ta kara makeup kamar yanda Antin ta umarceta ta tsaya a gaban dressing mirror ita kunyan masu aikin gidan take ji , ya zaayi ta dinga shiga tana fita a bangaren Mr president ? Ya ilahi ya zatayi?
Haka ta daure ta fito bayan ta yafa veil nata se uban kamshi ke tashi ta fito tana taku dai2 har ta fito nan bodyguards Suka bude mata mota duk da cewa ba wani nisa bane Amma abunka da manya haka aka ajiyeta a bangaren Mr president ta fito bayan an bude mata kofa ana xuba gaisuwa tana amsawa ckn sakin fuska nan Suka gaisa da yayanta shima se kallonta yake daga nan ta wuce ciki .baya falonsa don haka dakin bacci ta wuce direct ta kwankwasa tare da sallama ta tura kofar carab Suka hada ido yana tsaye ya gama shiryawa yana rike da turare a hnkli ta karasa tare da karban turaren a hNnunsa ba tare da tayi magana ba shi kuma ya bita da ido ta fesa masa koina ckn kasaita da wani irin salo, Mr president de ya xuba mata ido kawai bai CE ko uffan bah bayan ta gama ta ajiye ta sake daukan wani haka ta fesa masa turare har kala5 a hnkli ta daga kanta Suka hada ido ckn jin kunya tace
"Sorry ur exceelency na barka kai kadai "
Murmushi ya sakar mata daga nan ta juya ta dauko hulan da ta gani a kan gado ta saka masa a kai sai kuma tace
"Muje kaci abinci koh"
Falo Suka fito a Jere har dinning area ga abinci nan kala2 a Jere ba abinda babu ta tambayeshi abunda yake bukata yam freets ne da sausage rolls yaci sannan ya dora da coffee .ita kam bata wani sake sosai ba kunyarsa take ji chips da sauce din kwai take ci a hnkli tmkar bata so yana kurba coffee yana kallonta tana da natsuwa sosai tana yin komai ckn tsari babu rawar kai, samm...bai taba tunanin cewa haka halinta yake bah yana ganintane a matsayin futsararriya wacce zata...
"Mr president yaushe umaima xata dawo"
Muryar shuairat CE ya katse masa tunani har ga Allah shi ya manta da xancen wata umaima
"Ohh..umaima! I rily don't knw gskiya cos mun kwana2 bamuyi communicating bah"
"Haba dadyn sultan.. Me yasa?
"Mom sultan ni na haifi umaima at least I deserved som respect amma ta raina ni batajin magana ta ko kadan"
"C'mon dad sultan she is a kid lallabata zakayi ka...
"Aysha! Let's not talk abt dis ok!
"Ok sir! Am sorry kayi hakuri na shiga affairs din familynka koh...sorry"
Nan ta ajiye fork din hannunta ta tashi idanunta sun cika da kwallah tayi hanyar kofa ba shiri mr president yabi bayanta baiyi wata2 bah ya jawota ta fada jikinsa nan ta fara kuka a hnkli ya rungumeta yana shafa bayanta alamar rarrashi sai ajiyar xuciya take a hnkli ya furta
"Am sorry mom sultan I din min 2hurt u..
Ta cigaba da kukanta bata saurareshi bah haka Suka kasance ya sake cewa
"Pls mana Aysha wadu munyal( yi hakuri ..da yarensu😜) am sorry ok..
Ta dan sagaita kukan yana murmushi yNa shafa kanta dankwalinta ne ya zame zai fadi Mr president yayi saurin rikewa ..wow...kitsonta ne ya bayyana kanana masu kyau ga gashin ya bazu a baya da kafadanta ya kurawa gashin ido nan ta daga kanta da yake kwance a kirjinsa Suka kurawa juna ido , ita ta fara dauke nata shi kuwa murmushi yayi
"Ya'r shagwabar baba da mama ..am sorry koh"
Kai ta sunkuya ckn jin kunya sannan ta xumbura baki tana magana ckn shagwaba tayi rau-rau da ido tace
"Ba Kaine kamin tsawa bah"
Ya rike mata hannu yana murmushi yace
"Am sorry my first lady nayi laifi a yafe min ok!
Bash ne ya tura kofar tare da sallama carab Suka hada ido da shuairat yayi saurin sunkuyar da kai ya gabatar da gaisuwarsa sannan ya shaidawa Mr president cewa daddy na bukatar ganinsu da shuairat nan Suka amsa da cewa suna nan tafe , daga nan bash ya juya ya bar falon.
Shuairat ta sunkuyar da kai ckn jin kunya tace
"Nikam bazan kara xuwa side dinka bah kullum securities suyi ta kallona zasu ce bani da kunya"
Yana murza yatsunta a hnkli yana murmushi yace
"Toh me ne? Ba matata bace?
Ta gyara dankwalinta Suka fito ajere bodyguards Suka diban gaisuwa gun Mr president yana amsawa ckn sakin fuska da faraar da basu taba ganinsa dashi bah...
Ku biyoni😘😘😘
[2/21, 2:39 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*50*
By *Reefat yahya*
An kawo mota a gaban Mr president ya daga musu hannu alamar cewa da kafa zasu taka haka ko akayi suna tfya suna hira sama sama da shuairat ita kanta tana mamakin halayen Mr president da tana ganin tmkar idan sunyi aure zai wulakanta ta Amma sai taga sabanin hakan.
John ya bude baki yana kallonsu bash ya juya ya dafe kafadarsa yace
"Me haka john"
"Bash am rily happy 4mr president, ban taba ganin irin wannan murmushn a fuskarsa ba tun bayan rasuwar matarsa sai yau.lallai yana bala'in son wannan yarinyar"
Murmushn jin dadine ya bayyana a fuskar bash duk da cewa har yau in banda Mr president da daddynsa babu Wanda yasan cewa shuairat kanwarsa ce , ya juya yace
"Gaskiya naga alama suna son juna sosai , ni har kunyar shiga side din Mr president nake ji cos dazu ma na samesu suna soyewa"
"Hmmm..ai ni naga love jiya da dare, ina ganin Mr president ya tsufa Ashe de ya kware .kaga wani warm hug da ya bawa matarsa jiya? Na shiga basu ganni ba sai na fito ai @ 380...
Me bash zaiyi in ba dariya bah haka Suka cigaba da yaba irin kulawan da Mr president ke bawa amaryar tasa.
A falo Suka tarar da daddy da momsi Mr president ya wuce gun momsi tana zaune a 3seater nan yayi kwanciyarsa ya kwantar da kansa akan cinyarta tana dariya tace
"Hoo...boy baka San ka girma bane"
Shuairat kuwa mamkine ya bayyana a fuskarta wai dama haka Mr president yake xuba shagwaba a gun iyayensa? Muryan daddy ne ya katse ta
"Com hre boy! Rabu da momsi ai dama nagaya mata ni nafi sonka dawo nan ka kwanta"
Gaba daya Suka yi dariya shuairat kuwa kunyansu take ji ba gardama Mr president ya tashi ya koma kusa da mahaifinsa ya jingina kansa a jikin daddy .momsi tace
"Taho nan ya'ta wannan mijin naki bashi da kunya haka daddynsa ke biye masa suyi ta xuba shirme"
Kan shuairat na kallon kasa kawai jin momsi tayi kusa da ita tana daga kanta Suka hada ido momsi ta cigaba da cewa
"Ba kunya tsakanin mu ki daukeni tamkar mamanki kinji koh"
Kai ta gyada Mr president yace
"Momsi ita wannan ta fini shagwaba fah"
"Ba dole tayi bah! Ita karamar yarinya ce kai kuma fah?
Daddy yayi carab yace
"Shima karamin yaro ne a guna har yau ganin yaro nake masa"
Haka dai Suka cigaba da hirarsu ckn nishadi gwanin birgewa daga nan aka Dora da nasiha akan su xauna lfy haka nan momsi ma tayi tata nasihar mai ratsa jiki gaba daya jikinsu yayi sanyi kowannensu da tunanin da yakeyi a ckn xuci Mr president yana tunanin anya zai iya tunkarar shuairat a matsayin su raya sunnah har ya samowa iyayensa farin ckn da suke nema? Hmmm ...akwai aiki kenan.daga nan daddy ya sanar dasu cewa jirgin yamma zasu bi su koma Lagos yau.shuairat bata ji dadin hakan bah cos momsi na debe mata kewa, haka Suka kasance sannan Mr president yayi sallama da cewa zashi office. Daga nan itama ta koma bangarenta tayi lfyar gado nan bacci yayi gaba da ita.
******************
Bayan kwana2 da komawar su momsi da daddy zaman kadaici ya isheta sabida Mr president yana nan busy ckn kwana biyun basu hadu bah , sultan ne ke Dan rage mata kadaicin idan ya tafi skul kuwa shikenan zatayi bacci idan ta gaji tayi kallo tayi karatun Qur'an shikenan.
Yauma tana zaune misalin 2:30pm sultan se 5yake dawowa don yana xuwan islamiyya , ta rasa me zatayi sai ta bude watsap dinta rabon da ta shiga tun kafin aurenta yakai 1week kenan.aikuwa shukrah da princess meemah suna online nan Suka fara chatting shukrah na zolayarta wai amarci ya boyeta kurum ta daina hawa online, haka nan princess meemah tace tayi missing nata har laasar sannan ta ajiye wayar ta tashi don gabatar da sallah.
Haka rayuwa ta kasance har shuairat ta fara sabawa da al-amuran gidan shugabankasa , yau ta share 2weeks kenan a gidan kuma basa haduwa da Mr president idan taje sai ace yana meeting har 11 na dare zatayi ta jiransa bazata samu ganinsa bah sai dai ya tura text yana tambayar lfyarsu itada Sultan.
Da yamma tana xaune a falo ana sefe mata kai tana chatting da shukrah bodyguards ne Suka fara shigo da kaya bata damu bah, wata kofa aka bude Wanda tun xuwarta gidan bata taba ganin an bude part din ba sai yau...umaima CE ta shigo tare da sallama masu aiki suna mata maraba ko kallo basu isheta bah shuairat kuwa ko daga kanta batayi bah hakan ba karamin batawa umaima rai yayi bah.ckn gadara ta karasa kusa da shuairat tace
"Ke me kike ji dashi da baraki bude baki ki gaisheni bah"
Ko uffan shuairat bata tanka bah ta cigaba da danna wayarta masu aikin duk sun rakube a gefe saboda sanin halayen umaima
"Ba da ke nake magana bah ...
Shuairat tayi wani kayataccen murmushi tace
"Aw...dota! Welcome back kije ki huta daga baya ma tattauna koh"
"Dota! Umaima ta maimaita sunan "dankari ..Amma yarinyar nan ta raina mata wayo" ta nuna ta da yatsa
"Am not ur dota n I'll Neva b...mtssww matsiyaciya kawai"
Daga nan ta juya tayi shigewarta daki shuairat tana murmushi tace
"Drama queen is back zaa sha kallo kenan"
Bayan an gama sefe mata kan ta haura sama ta wuce daki, wanka ta fara yi bayan ta fito ta caba ado ckn wata gown black mai stones da adon fulawa golden n Orange tayi parking gashin kanta ta kwantar da jelar a gefen kafada nan tayi rolling da Dan karamin Orange veil tayi kyau sosai ta fesa turare sannan ta tsaya a gaban mirror tana murmushi tace
"Welcome back umaima sai kin raina kanki is time for d show"
Ta fito rike da wayarta a hNnu tana takawa a hnkli ta fito harabar gidan bodyguards Suka bude mota direct bangaren Mr president Suka nufa bayan anyi parking ta fito tayi shigewarta, dakin baccinsa ta shiga tasan war haka baya nan ta haye gadon tayi kwanciyarta.
Umaima ta shigo falon mahaifin nata tazo ta bashi hkri baya nan sai ta wuce dakin barci shuairat ta baje a gado tana chatting suna hada ido shuairat ta sakar mata murmushi umaima ta ja wani dogon tsaki juyawar da zatayi saura kiris suyi karo da Mr president.
Hmmmmmm muje xuwa
[2/21, 2:39 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*51*
By *Reefat yahya*
Rawar jiki umaima ta fara yi sabida ynxu tana shakkar dad nata baya sake mata nan ta fara in ina..
"Amm..am soryy dad..bansan baka"
Bai bari ta karasa bah ya sa kai a gefenta ya shige dakin shuairat kuwa tana ganin haka ta tashi tayi hugging nasa tare da ajiye masa Peck a kumatu ckn kissa tace
"Oh..my swt hrt I rily missed u"
Murmushi ya sakar mata shima yayi missing nata don sun kwana 2 basu hadu bah umaima ta gagara tsayuwa wani kululun bakin ciki ne ya tokare mata wai dad nata ya manta da mum nasu har zai iya soyayya da wata irin haka? Lallai maza mayaudara neh hawaye ne ya cika idanunta fal ya fara gangaro wa a fuskarta nan ta juya ta bar dakin da guduwa ta fito a bakin kofa Suka ci karo da bash tana ganinsa ta kara fashewa da kuka ba sai ya tambaya bah yasan matsalarta hannunta ya rike Suka wuce bangaren ta.
Shuairat kuwa tana ganin burinta ya cika ta zame jikinta daga na Mr president ckn jin kunya shi kuwa murmushn jin dadi yake yace
"Mom sultan 2days..ya kike ya boy naki"
"Lfy alhamdulillh ya aiki"
"Lfy kalau alhamdulillh hop kina tayani da adua..
"Uhmm..ta fada sai kuma ta tura baki ckn zolaya tace
"Ni da sultan muna fushi da kai"
Ya langabe kai kamar karamin yaro yace
"Eyya..
Am sorry ku yafe min ba laifina bane kinsan kasar tamu ce sai adua"
Murmushi tayi tace
"Haka ne ..Allah ubangiji ya taimaka ya bada saa..
"Ameen...my first lady nagode"
"Ka gaji koh..bari na hada maka ruwan zafi sai kaji dadin hutawa"
Daga nan ta wuce toilet nasa😳😳ita kam bata taba ganin haduwa irin haka bah, bayin ya tsaru sosai ta tsaya tana yan dube-duben ta dakyar ta gano heater din ta hada masa ruwan xafi sai kuma ta hada da turarukan wanka nan ruwan ya fara bada wani irin qamshi mai dadin gaske ta tara shi a Jacuzzi sannan ta fito ta sanar dashi nan ya fada bayin .
Tnx all
[2/21, 2:39 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*52*
By *Reefat yahya*
Sorry pals page 51 is not up2 d oda pages kuyi hkri somtin came up ina sauri ne daz y.
Mr president ya fito daga wanka shuairat bata ckn dakin Amma ta ajiye masa kayan da zai saka bayan ta feshe su da turaruka masu uban qamshi, ya gama shiryawa ya fito falo tana zaune a kujera tana danna wayarta motsin da taji ne yasa ta juyawa Suka hada ido ta sakar masa wani qayataccen murmushi ya maida mata martani nan ta tashi tayi serving dinsa wani lafiyayen jolof rice da hanta da kuma kayan lambu ta xauna a gefe yana ci a hnkli tana satar kallonsa. Mr president yana da kyau sosai komi nasa yana burgeta shuairat ar u inlov? No...it can't b wanann tsohon yasan love ne? Kawai he is nice to me daz all...
"My lady ar u ok"
Muryar mr President ne ya katse ta
"Yeah..am fine"
Ya bita da kallon tuhuma yace
"Are u sure?
"Am sure mr President.. Trust me"
"Ok tunda haka kika fada but gaskiya ban yarda ba.
"Ba komai fah"
" Allah yasa"
Haka Suka kasance har mr President ya gama cin abincinsa sannan Suka koma falo .
kusa dashi ta xauna a kujerar 2seater yana mamakin irin shige masa da takeyi duk da yasan dama suna zama tare Amma yau yaga changes a tattare da ita ko meyasa oho! News suke kallo shiru ya ziyarci falon kowa da tunanin da yake yi.
Umaima kuwa suna shiga falonta ta sake fashewa da sabon kuka tayi regretting dawowarta Amma skul nasu anyi resuming babu yanda da iya dole ta dawo ta cigaba da xuwa, bash kam tsayawa yayi yana kallonta ya rasa me zai gaya mata ta daina kukan da take yi.tayi kuka mai isarta sannan tayi shiru hanky ya mika mata ta share hawayen sannan tayi ajiyar xuciya yace
"Wia have u bin umaima"
"Um..um..naje gun sistan mom dina
"Kin sallami dad naki lokacin da kikayi tafiyar?
Shiru ba amsa ya cigaba da kallonta
"Talk to me umaima"
"A'a ban gaya masa bah"
"Umaima baki jin magana , tunda hakane ba ruwana dake daga yau kada ki sake nema na"
Yana gama fadin haka ya juya yayi ficewarsa . ta shiga uku nan kuwa ta sake fashewa da wani sabon kuka mai ban tausayi amma kash! Babu mai rarrashin ta.
Da yamma sultan ya dawo yaji labarin dawowar yar uwar tasa yayi murna sosai , dakinta ya wuce tana kwance a gado tayi shiru idanunta duk sun kumbura ta rasa me ke mata dadi a duniyar gaba daya sultan ne ya fada jikinta har ta wani tsorata sabida bata San da shigowarsa ba..
"My boy I missed u so much"
Ta kankamesa a jiki nan kuwa wani sabon hawaye ya fara fitowa sultan ya saketa yana share mata hawayen yace
"Muje ki gayawa anty nah me ya saki kuka kinji "
Ta bisa da kallon mamaki
"Sultan wace antyn taka?
"Lahh...baki San dad ya kawo mana wata anty kyakkyawa tana sona sosai tana kula dani a dakinta ma nake kwana ynxu tana ...
"Kai sultan waccan ba antynka bace kaji , kada ka sake xuwa kusa da ita koh..
"Um..um nikam ina sonta , don tana kula dani sosai har wanka ita take min tana koyamin karatun Qur'an tana taimakamin da assignment dina kuma tana...
"Stop it! Will u? Nace maka ba antynka bace , kuma ba wai sonka take bah munafurci ne ka dawo nan mu dinga kwana tare kaji"
"Bana so..nikam da anty nah zan kwana"
Ya fara kuka ya gudu ya bar dakin umaima ma kukan take yi tana nanata ..innalillahi shikenan shuairat ta mallake kowa a gidan har da kanin nata.ta kai minti 20 tana kwance tana kuka garam aka bude kofar dakin..😳😳🙊mr president ne tare da sultan daga ganin fuskarsa zaka San cewa ransa a bace yake baiyi wata2 ya wanka mata mari ji kake tasss....aikuwa umaima ta sake wani irin razananniyar kara shuairat tNa kwance a falo dama tana jin karan ta fito da wuri nan Suka ci karo da ladi mai aiki jikinta sai rawa yake
"Haj..Hajiya ki taimaka ki ceci umaima ..mr..
Bata karasa ba shuairat ta sauko a guje ta wuce part din umaima tana shigowa ganin mr President tayi ya sake kaiwa umaima wani Marin da saida ta ga taurari ckn Sauri ta karasa ta shiga tsakaninsu ran mr President sai tafarfasa yake umaima na kuka mai tsoma rai shuairat ta juya tana fuskantar ta tasa hannu zata rike ta umaima tayi saurin komawa ta baya ckn daga murya tace
"Don't dare touch me ...munafuka Allah ya isa sai...
Mr President ne ya sake yunkurin xuwa wajenta shuairat tayi saurin rike masa hannu tana kallonsa tace
"Pls...pls ur excellency ka rabu da ita she is just a kid ok"
Ransa a bace idanunsa sun kada sunyi ja..shuairat ta rike hannunsa tana ja a hnkli Suka bar dakin masu aiki suna waje sun rakube sai rawar Dari suke tunda Suka zo gidan basu taba ganin mr President ckn bacin rai irin haka ba ko me umaima tayi oho! Shuairat ce ta umarcesu da su kula da sultan da umaima daga nan ita kuwa dakinta Suka wuce da mr President suna shigar dakin ta tura kofa sai me😳? Hawaye ta gani a idanun mr President ya sunkuyar da kai kasa batayi wani tunani ba ta jawosa a jiknta ta rungumesa gam...tana shafa bayansa a hnkli shima hannu yasa ya kankameta😍😍😍
Ku biyoni...are dey in lov??🤔🤔
[2/21, 2:40 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*53*
By *Reefat yahya*
Sun kai 10mins ckn wannan hali sannan shuairat ta zame jikinta a bakin gado Suka xauna mr President yace
"Na mareta wit my own hands"
"Is ok mr President"
"Aysha I rily love umaima but bata respecting dina she is taking d advantage of d love I have 4her , tana yawan bata min rai kullum dannewa nake yi but now she pushes me to d wall"
"I know but kayi hakuri ka yafe mata koma menene she is still young ai"
"She is not young Aysha! Daddy da kansa yace ban bawa yarana tarbiya mai kyau ba, kuma Allah yasan nayi iya bakin kokari na but umaima is rily stubborn"
A hnkli ta sarke hannunta ckn nasa tace
"I knw dat but a hnkli zaka lallaba ta ba sai ka hada da duka bah, kuma adua zaka mata kaji koh my man"
Kai ya gyada mata sai kuma ta tashi ta debo pineapple drink me sanyi a firji ta xuba a cup ta dawo ta mika masa ba gardama ya karba ya kurba sau 3 sannan ya ajiye cup din a kasa yana kallonta yace
"Nagode Allah ya miki albarka tnx a lot ..am..
"Shhhh....yatsa ta dora a bakinsa tana murmushi tace
"Is my duty as ur wife, ina alfahari da kai kana da matukar girma da daraja a ido na I can do anything for u.kuma ina jin dadin aduar da kake min nima nagode sosai"
Shi kam yana mamakin hali irin na shuairat tana da tunani da kaifin basira sosai abun mamakin ma shine, bata nemi sanin laifin umaima ba kawai ta hau bada hakuri duk da irin kiyayyar da umaiman ke nuna mata Amma bata taba nuna damuwarta bah hakan ba karamin dadi yake ji ba ta wani bangaren kuma idan yayi la'akari da kulawar da take bawa sultan yakan jinjina mata tabbas yayi dace da mace ta gari.
( mata mu kula pls..mu rike ya'yan mazajen mu da xuciya daya muyi koyi da kyawawan halaye irin na shuairat banda hassada da kyashi , hakan zai sa mijinki ya girmamaki kuma ya kara sonki..Allah yasa mu dace Ameen)
"Mr president tunanin me kake ?
"Uhmm..ba komai nagode zan koma side dina ina Dan wani aiki ne"
"Ok muje na ma rakiya"
"No..don't worry kiyi xamanki ki huta "
"A'a muje zan tayaka hira idan kana aikin"
Ba musu Suka fito tare suna tfy har xuwa bangaren sa.
Umaima kuwa family doctorn su ne yaxo ya dubata ya bata magunguna nan kuwa zazzabi ya rufeta.
Kowace safiya shuairat tana xuwa tana duba jikinta duk da cewa umaima bata kulata Amma bata fasa xuwa bah haka nan sultan ita ta cigaba da kulawa dashi tana kuma kulawa da mijinta ba laifi ynxu ta saba da mr President sun fara shakuwa Amma ba wai can bah.
***********
Haka rayuwa ta kasance yau da gobe sai Allah ynxu shuairat ta share wata3 a gidan mr President kullum sai tayi waya da mama da babanta su Suka hanata xuwa , umaima kuwa babu abunda yake hadasu kowa na sabgar gabansa sultan kam ya gama shakuwa da ita kullum basa rabuwa idan yana gida dai suna tare a can bangaren mr President. Haka nan suna waya da momsi da daddy mah kullum, rayuwar gidan de gwanin shaawa masu aikin ma suna yaba halayen shuairat bata da girman kai ko kadan.matan ministoci da sauran abokan mr President duk sun saba da ita suna yawan kawo mata ziyara saboda faraarta.
Yau weekend babu aiki tun karfe7 shuairat tayi ado na gani na fada sultan ya koma bacci don haka ta fito ta wuce bangaren mr President , bedroom ta shiga yana zaune da carbi a hnnunsa a gefe ta xauna ta sunkuyar da kai kasa ya juya yana kallonta Murmushi ne ya subuce masa yasan akwai maganar da take son fada Amma ta kasa
"My lady ya dai"
"Ina kwana dad sultan"
"Lfy ya kuka tashi"
"Lfy alhamdulillh"
Sai kuma tayi shiru ta rasa me zata fada
"Fadi bukatar ki my lady"
Kai ta daga Suka hada ido yana murmushi yace
"Kina mamaki ne? Just tell me mene ne..
"Umm..ehmm..dama..
"Mom sultan go 2d point ok"
Ya fada a yayinda ya tallabo habarta ta runtse ido a hnkli tace
"Gida nake son xuwa gun mama"
"Mama's gal! Kin manta baba yace sai nan da 1 yr zaki fita?
Rau rau tayi xata fara kuka yana murmushi yana kallonta yace
"Oh no! Shagwaba again, gara ma ki Adana hawayenki cos babu inda zaki"
Hawayen da suke makale Suka fara gangarowa mr President ya zare ido yace
"Ohh...yi hakuri ba sai kinyi kuka bah tashi ki shirya muje koh don't cry pls"
Nan kuwa murna fal har ckn ranta taji dadi kawai ta rungumesa tare ta yi masa peck a kumatu tace
"Tnk u so much mr President nagode"
Daga nan ta tashi zata ruga a guje yayi saurin riketa yace
"Ke lafiyanki? AHakan zaki fita securities suna kallonki? Idan kinyi ma sai mu fasa xuwa sai ...
Bai karasa ba ta rungumesa ta baya ckn salon shagwaba ta fara magana
"Eyya fah...yi hkri toh na daina tsallen a hnkli xan tafi kaji"
Shiru yayi yana jin wani irin yanayin da ya kasa tantance ko menene dakyar ya furta
"Ok jeki ki shirya tare zamu je" nan ta bude kofa tana tfya tana murmushi ita kadai har ta fice daga bangaren nasa.
😘😘😘😘lov u all
[2/21, 2:40 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*54*
By *Reefat yahya*
Mr president yabi bayanta da ido yana murmushi tare da girgiza kai shuairat tana da shirme wllhi tana Abu kamar karamar yarinya.
Shuairat kuwa wani wankan ta sake yi tasha ado ckn wasu leshi maroon n golden da touches din milk color ta saka yan kunnen gwal tayi kyau sosai.
Karfe 8 ta gama shirinta tsaf haka nan ta shirya sultan ma ckn kananan kaya yayi kyau sosai sai qamshin turare ke tashi daga nan Suka wuce bangaren mr president a can sukayi kari ckn jin dadi suna ci suna Dan taba hira.
Karfe 10 na safe motoci sukayi parking a kofar gidan Alh bello maiha shuairat ta fito ckn xumudi ta fada gidan tare da sallama falon mama ta wuce suna zaune suna hirarsu ta fada jkn mama tana dariya farin cki ne bayyane a fuskar iyayen nata baba yace
"Ahh...ya'r baba wato kinfi son mamanki koh"
Nan ta tashi ta koma kusa da mahaifin nata tana dariya tace
"Ba haka bane fah..baba nayi kewarku sosai"
Daga nan Suka gaisa bash ne ya shigo yana hararinta yace
"Bansan yaushe zakiyi hnkli bah , dama kinzo da mr president shine kika baro shi a waje"
"Lalala..baby dama tare kuke shine kikayi zamanki baki sanar damu bah
"Toh baba nikam ba na manta bane"
Ta fada tana xumbura baki daga nan mama ta tashi ta koma ckn daki aka shigo da mr president dama sultan kam yana xaune a falon , ckn girmamawa Suka gaisa da surukin nasa sun Dan taba hira sama2 sannan yayi sallama ya tafi.shuairat kam ta haye gadon mamanta ta mike tana jin wani dadi, sultan kuwa ya sake sosai yana xubawa baba hira mama ta kawo masa abinci yaci sannan ta koma daki gun ya'rtata suna hira tana tambayarta zamanta kewar tasu , shukrah ta shigo Suka baje sunata surutu mama ta koma falo tabar musu dakin.shukrah ta gyara zama tace
"Mutuniyar kinga kyawun da kika kara kuwa? Sai wani shinnin kike ko dai..ta kanne mata ido daya shuairat ta buge kafadarta tace
"Munafuka! Toh ba abunda kike nufin bane
"Hmmm..wa yasani Abu a duhu..maybe rabo ya zauna naga sai wani kyau da haske kikayi"
"Shukrah kenan..baki da dama wllhi, don kina da ciki shine kike zaton kowa ma haka ne?
"Hee...wa yagaya miki ciki ne dani?
"Ahaf..tun yaushe naji labarin a gun Yaya"
"Hmmm..zai dawo ya sameni ai tunda Allah yayi shi da shegen suru2"
Shuairat ta fashe da dariya tana tsokanarta shukrah tace
"Ke dinma na baki nan da wata daya..naga wani kalan soyayyan da kuke har rakaki anguwa yake hmmmm"
"Oho dai..ki fama dashi "
"Baby me sirrin ne, naga alama fah mr president ya fada kuma naji labarin xuba love da kukeyi a gaban kowa ma Baku jin kunya"
"Ikon Allah..shiko Yaya dan sa ido ya koma! Lallai zan gayawa mr president "
"Keee..rufamin asiri wasa nake miki"
Haka Suka kasance suna yiwa juna shakiyanci .
Yinin ranar curr..tare sukayi ckn farin cki da walwala har xuwa 7pm sannan aka zo daukan su shuairat ta koma gida.
Karfe9 ta gama shirin baccinta tsaf xata kwanta sai kuma ta tuna tabar wayarta can falon mr president kuma tana son shiga watsap dole ta tashi ta Dora hijabi kan kayan baccinta ta nufi bangaren mr president.
Yana xaune a falo yana shan coffee idanunsa nakan TV yana kallon news, ta shigo tare da sallama can cki ya amsa ba tare da ya juya ya kalleta bah.wayar na gefensa akan kujera batayi masa magana ba taxo wucewa zata dauka ckn rashin saa tayi tuntube da kafar mr president tayi luuu...ta fada jikinsa jagwab Suka kurawa juna ido , turo kofar akayi tare da sallama umaima CE ta shigo suna hada ido da shuairat ta saki wani shuumin murmushi nan kuwa ta Dora bakinta kan bakin mr president ba shiri ta fara kissing nasa tamkar xata cinye shi.
Mutuwar tsaye umaima tayi ta fara jin haushin kanta tayi regretting xuwan da tayi ckn axama ta juya tabar falon shuairat na ganin haka ta cire bakinta mr president kam saura kadan ya suma..tunda yake a rayuwarsa bai taba shiga irin yanayin da yake cki a hlin yanxu bah, shuairat kuwa wani irin kunyarsa take ji ta kasa tashi daga jikinsa kuma ta gagara hada ido dashi.sun share minti 10 ckn wannan halin sannan ta tashi tmkar Mara gaskiya ta fara tafiya a hnkli rike hannunta mr president yayi sannan ya damka mata wayarta a hannu daga nan ta juya tayi tafiyarta.
Bacci ya gagaresu mr president shuairat da kuma umaima kowanne da kalar tunanin da yake dakyar bacci ya sace su.
Asuba tagari ....
😘😘😘
[2/21, 2:40 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*55*
By *Reefat yahya*
Haka rayuwa ta kasance shuairat ta share shekara daya a gidan mr president zaman nasu ba laifi tana bashi kulawa irin Wanda baa rasa bah, sultan kam ya manta da cewa shi maraya ne cos shuairat ta maye masa gurbin uwa tana basa kulawa fiye da komai.shukrah ta haifi danta namiji mai kama da ubansa sak aka rada masa suna Bello ana kiransa waleed. Ynxu kam duk fadin Nigeria babu inda baa San fuskar shuairat bah tana yawan xuwa gidan marayu tana tallafa musu haka nan ta bada shawara aka bude makarantun islamiyya da dama ga kuma masallatai, bangaren asibitoci ma sun bada gudunmawa.
Shuairat ta kara cika tayi kyau sosai alamar Hutu ya bayyana a jikinta ta kara haske sai sheki take yi, shuairat ce a kitchen tana bada umarnin girkin da zaayi yau surukan nata xasu kawo musu ziyara itama ta taba xuwa sau daya. Karfe 4 Suka shigo gidan ckn murna ta tare momsi direct dinning Suka wuce nan Suka gaisa ta xuba mata abinci ta tura a gabanta
"Hoo...shuairat daga xuwan mutum ki tura masa abinci a gaba "
Murmushi tayi tace
"A'ah momsi kamata ki fara da abinci kafin ki huta koh"
Ba gardama fara cin daga nan shuairat ta tashi taje gun daddy Suka gaisa.
Da dare suna xaune a babban falo a bangaren shuairat ita da momsi da sultan da kuma umaima suna ta hirarsu umaima bata sa baki bah don ta lura da shakuwar dake tsknin momsi da shuairat. Sultan ne ya juya gun shuairat yace
"Anty muje mu kwanta bacci nake ji"
Carab momsi tace
"Kaji min yaro! Dama kullum da ita kake kwana ne"
"Ehh..mana granny baki sani bah dakinmu daya da anty nah , ita take kula dani tana sona sosai"
Zare ido momsi tayi tana kallon shuairat har umaima tayi mamakin jin hakan shuairat kuwa ta sunkuyar ya kai kasa ckn jin kunya ta gane kallon da momsi take mata..Muryar momsice ta katse ta tana kiran ladi mai aiki ba bata lokaci taxo ta rintsina ckn girmamawa
"Ki raka sultan dakin baccinsa"
Dakyar sultan ya amince saida shuairat ta lallabasa tace masa tana nan xuwa.wayar hannu momsi ta fitar ta kara a kunne
"Ka sameni a falon matarka"
Daga nan ta kashe wayar ta juya tacewa umaima ki bamu waje xamuyi magana, nan ta tashi ta koma bangarenta.ckn kankanin lokaci mr president ya shigo falon tare da sallama ya nemi waje kusa da ita ya xauna nan ta fara magana
"Ina son jin meke faruwa a gidan nan"
Ckn rashin fahimta mr president ya daga ido ya kalleta
"Momsi wani Abu aka gaya miki ne? Nidai nasan ba komai muna xaman lfy da ita kodai tace na mata wani abun?
"Boy kenan.. Ka bani mamaki wllhi, ynxu da girman ka da ilimnka amma ka kasa sauke hakkin aure dake rataye a kanka?
"Momsi wane irin hakki? Wllhi muna xaman lfy da ita gata nan ki tmbayeta koh my lady na taba bata miki raine?
Sunkuyar da kai shuairat ta kara yi momsi ta ja tsaki sannan tace
"Ynxu irin xaman da kukeyi kenan? Tsawon shekara 1 da auren naku Amma ....
Ta kasa karasa maganar sabida nauyin Kalmar sai kuma tace
"Kasan idan Alh yaji wannan maganar ranku xai baci ba kadan bah, garama Ku daidaita tskaninku Ku wuce Kuban waje sakarkaru kawai"
"Kiyi hkri momsi Allah ya huci xuciyarki"
Shuairat ce ta furta a hnkli mr president kuwa kansa a kulle yake ya kasa gane me take nufi haka nan shima ya bada hkri sannan ya mata saida safe ya koma bangarensa, itama ta tashi tace
"Ni zan Kwanta maza ki shirya kibi mijinki ynxun nan"
"Mu kwana lfy momsi"
Daki ta wuce ta fada wanka bayan ta fito ta shirya ckn kayan baccinta ta fesa turaruka daban2 sannan ta wuce bangaren mr president wani irin kunya take ji gani take tmkar bodyguards din duka ita suke kallo.a hnkli ta turo kofar dakin tare da sallama yana xaune ya buga uban tagumi yana ganinta ya tashi a hnxarce ya karasa ya jawota tare Suka xauna a gadon yace
"Pls Aysha wane laifi na miki zaki hadani da momsi na Wanda bazaki iya gaya min bah..kinsan tunda muke bata taba fushi dani bah amma yau naga alamar hakan a fuskarta"
"Am sorry mr president wllhi ni...
"Just tel me Aysha me na miki"
Nan ta fashe da kuka tana cewa
"Ni..ni baka min komai bah kuma babu abunda na gaya mata"
Ya fara rarrashinta yace
"Ok naji ...ba laifinki bane , toh gaya min me ya faru"
"Umm...ba sultan bane ya gaya mata cewa kullum tare muke kwana "
"Ok..nagane, kinga ynxu sultan is 8yrs old tana ganin ya girma bai dace kuna kwana tare ba koh?
"Ah'ah..tana nufin cewa uhmm..uhmm"
Shiru tayi ckn jin kunya ta rufe ido tana murmushi dogon numfashi ya ja sai ynxu ya gane me momsi take nufi da cewa ya kasa sauke hKkin aure ...hmmm anya zai iya????
Masu karatu ya kuke gani hakan zata faru kuwa??
Hmmmm...muje xuwa
Love u oll😘😘😘
[2/21, 2:40 PM] Reefat: 💞NI DA SHUGABAN KASA💞
*56*
By *Reefat yahya*
Shiru sukayi dukkansu biyu daga karshe shuairat ta tashi zata fita yace
"Ina zaki ?
"Uhmm..falo zan koma can xan kwanta"
Wani irin kallo ya watsa mata ba shiri ta dawo ta xauna
"So kike ki tonamin asiri ko me? ..as from today ki tattara kayanki ki dawo nan da xama"
Ckn Sauri ta kura masa ido ya kada kai yace
" yes! Ki dawo nan mu xauna tare kinga babu wanda xaiyi magana koh, oya ki hau gado ki kwanta ba sai kinje falo bah"
Ba musu ta cire hijabinta ta hau saman gadon ta kwanta a gefe tayi aduointa ta shafa sannan ta rufe ido tana son bacci Amma ta gagara she is not comfortable.
Mr president kuwa ya tashi ya fada bayi ys watsa ruwa sannan ya fito ya saka kayan baccinsa ya fesa turare sannan ya kwanta a gfenta bata rufe da bargo ba ya kura mata ido na yan dakika sannan ya dauke kai.baccine yayi awon gaba dasu can tsakiyar dare ta mirgina ta koma kusa dashi ta kankame shi gam wutar dakin a kashe yake, ckn bacci mr president yaji alamar mutum a jikinsa a hnkli ya bude ido ya kunne side lamp tana baccinta ckn kwanciyar hnkli ya kura mata ido tana sauke numfashi a hnkli tayi masa kyau sosai ya juya zai kashe wutar ta Dan motsa nan ya koma ya kwanta a hnkli shima ya kara rungumarta.
Da asuba ita ta fara tashi a hnkli ta zame jikinta daga nasa ta fada bayi zama tayi a ckn bahon wanka tana lumshe ido tana tuna halin da ta farka ta gansu a cki, tana mamaki ya akayi hakan ya faru? Dakyar ta daure tayi wanka tare da yin alwala ta fito har ynxu baccin yake ta tsaya Jimm...hannu tasa a gefen fuskarsa tana shafawa a hnkli take ya bude ido tace
"Morning... Tym din sallah yayi"
Daga nan ta tada sallah tayi nafilfilu sannan tayi sallan asuba ta xauna tana Jan carbi ya fito ya gabatar da sallah haka Suka kasance har rana ta fito shuairat ce ta nade sallayar ta xauna a gefe tace
"Ina kwana"
"Lfy ya kike"
"Lfy alhamdulillh"
Da tashi ta kama hanyar fita dakin
"Ina zaki ?
"Nayi wanka Xan je dauko kaya a...
"Dawo ki xauna xaa kawo miki"
Ba musu ta koma kan gado ta xauna tana wasa da yan yatsunta.
Falo ya nufa bayan yan mintoci ya dawo ya shige bayin da alama wanka zaiyi.motsi take ji a falon ta fito don ganin waye ne ga mamakinta akwatunan ta aka jera da sauran kayayyakin da ta mallaka a dakinta , wani dakine da yake kusa da na mr president a can Suka shigar da kayan sai kuma mata masu aiki Suka shigo Suka gaisheta sannan Suka shige dakin take Suka ajiye komai inda ya dace Suka gyara dakin se qamshi ke tashi daga aka hada musu abinci a dinning.
Tsarin dakin ya birgeta kwalliya ta fara yi bayan ta gama ta saka wasu material masu kyau daga nan ta yafa veil ta wuce bangaren da momsi take Suka gaisa se kuma daddy shima ya fito ta ritsina ta gaida shi.sultan ya fado mata a rai a hanya Suka ci karo dashi yana ganinta a guje ya fada jikinta yana cewa
"Anty ina kika je nida jummai muka kwana jiya" ( jummai ya'r aiki CE)
Tana shafa kansa tace
"Sorry boy muje kayi brkfast koh"
Daga nan Suka wuce bangaren mr president don karya kumallo.
Bayan kwana4 su daddy sukayi sallama akan cewa zasu koma , momsi kuwa ta ajiye mr president da shuairat tayi musu nasiha sosai akan zaman ta kewar aure daga nan Suka fara shirin komawa.
0 comments:
Post a Comment