Kwanci tashi har anyi azumi takwas, agida tasame shi yana shirin komawa Azare "tazauna tana kallan shi"Yaya D'an Sarai tafiya ba sallama?Yacigaba da shirya kayan shi a jaka ba tare daya d'ago ya kalle taba"ai naje gidan akace kin tafi Hayin-Dogo"haka ne to yaushe za ka dawo? Yarufe jakar yad'auki agogo yana d'aurawa a hannun damar shi"sai ALLAH ya kaimu sallah idan muna raye,ta taya shi kwashe kaya zuwa mota yayi sallama da Inna suka fito,tajingina da motar tana kallan shi cikin kissima wani abu a zuci yana zuba ruwa a lagireto har yagama yashiga mota yazauna yana d'aura belt.
Yad'anyi murmushi"duk kinyi wata iri ko za ki bini ne?Ta turo baki gaba"da inada wannan damar ai da ba haka ba wallahi.Baiyi magana ba,yabata wasu kud'i"bayawa.Tasa hannu biyu takar6a"nagode Yaya D'ansarai ALLAH yak'ara bud'i,suka d'aga hannu suna ma juna adabo.
Sun dawo makaranta suka tarar da Asma'u kanwar Sudaida ta ci kuka ta gode ALLAH idanun ta sun kumbura sun kad'a jawur"lafiya Asma'u? A tare suka tambaye ta,sai tasake jin wani sabon kukan ya kufce mata tafi minti goma sannan tafara rage sauti tana ta jera ajiyar zuciya"ke wai kukan me kike yi ana tambayar ki kin ma mutane shiru wacece sa'ar ki anan? Khausar ta tambaye ta.Taja majina tana hura iskar bakin ta"labarin zuciya a tamabayi fuska ranta in yayi dubu ya 6aci,cikin hawaye tafara magana"wai arasa wanda za a bani a matsayin mijin aure sai Yaya D'ansarai...wasu hawaye masu d'umi suka sake zubowa sharrr...sharrr...Sudaida tamik'e zaune da sauri kamar za ta hantsila,duk suka bita da kallo ganin yadda tayi sai kuma ta koma ta kwanta batayi magana ba dan ta ma rasa abinda za ta fad'a wallahi.
Asma'u tacigaba bayan kowa ya san Alk'asim nake so amma ance a ah wai shi yaro ne ko Secondary bai gama ba,takad'a kai cikin takaici"saboda ALLAH wai Yaya D'ansarai. Khausar takalleta cikin natsuwa"bakya san shine? Dasauri tace"eh mana me zanyi dashi bak'ink'irin dashi kamar bak'in gashin kanshi...bata gama rufe baki ba taji saukar mari hagu da dama"Yaya D'ansarai kike za gi?To dame kwad'o yafi gaya?Ba gwamma shi bak'i kyakkyawa bane.Asma'u tamik'e cikin hawaye"amma wannan rashin 'yanci da yawa yake,ga mari ga tsinka jaka?Takalle ta "wallahi Yaya Sudaida bana san shi,tafita a d'akin da gudu cikin shashshekan kuka.
Tadunk'ule hannu ta naushi iska"da kin tsaya k'aramar mara kunya da kinga yadda zan yi dake.Khausar takalle ta"ai baki isa ki kuma dukan taba akan me? Dan tace ba ta san shi shine ya zama laifi?Yaya Julaibib d'in?Kwarai kuwa shi wanene da kowa sai ya so shi so?Wa kika ta6a gani ko jin labari kowa na doron duniya ya so shi? Ko wanda yayi mu an samu wanda basa san shi ta hanyar k'in yadda da duk abinda yace ayi,da wanda yace abari,bare wani Julaibib ordinary human being,ai dama na dad'e ina zargin wani abu bani da tabbasss shiyasa naja bakina nayi shiru; to amma yau na samu yak'ini san Julaibib d'in nan ki keyi,to dake dashi d'in duk sai kuje kuji da manufurcin ku,ai shima ina lura da takunshi akanki.Yaya Khausar daza kice haka shi kuma Sinan d'in ina zan kai shi?Tawatsa hannu"ke kika sani...
Cikin bugun zuciya tafara harhad'a littafan data barbaza a kan gado da niyyar yin nazarin su,ta tsuke baki tana yamutsa fuska Khausar tayi yar dariya tana rage kayan jikinta za ta shiga wanka Asma'u ta D'ansarai bak'ak'e biyu kila za su iya samar da wankan tarwad'a ko fari ko sarauniyar Sinan?Bata kula taba tamak'alama wayar ta earphone tana k'ok'arin toshe kunnuwan ta dashi. Khausar ta fizge"ke malama kirufa mana asiri karki zama kanwar kurma,so nawa ni da ke munajin bayanan da likitoci k'wararru a bangaran kunne,mak'ogwara da hanci(E N T) sukeyi,yawan amfani da earphone yana kawo matsala a bangaran ji"tagyad'a kai "naji bani wayata.Tamik'a mata, kita shi kisan abinda za ki d'ora tunda su Mama basa nan ko miyar shuwaka za ki mana mun kwana biyu bamu ciba wallahi,ta san Sudaida bata so dan tayi tsokana tafad'a. Yaya Khausar"ai bazan hana kiyi idan kina so ba"kuturu da kud'in shi alkaki ba sai na k'asan kwano ba?Gaskiya ne to d'anje kifara wanke min shuwakar kafin in fito wanka.
Kwana biyu da maganar ranan Asma'u ce da aiki tasame ta a D'akin-girki tana kad'a miya sai ta kar6i maburgin barin taya ki,Asma'u tad'anyi murmushi "Yaya Sudaida saboda ALLAH ko kuma cin tuwon kishiya...?Duka biyun.Sukayi dariya, Asma'u tana zuba mata garin kuka tana cigaba da burgawa har suka gama, tad'an jefa kanwa kad'an wucewar wasu yan dak'ik'u tasauke to d'orama Yaya Aminu ruwan da zata dama mishi custard aranta tana mita"gaskiya Siddika ta shiga uku da shan kunu,ga fa kunun tsamiya can Inna ta aiko mai dashi amma duk da haka wai dole-dole sai ta dama mishi custard,ruwan yana tafasa ta dama tajuye mishi a flask.
Tamatsa gefe tana cema Asma'u ai dai na taya ki,dan haka zo ki dora ruwan tuwon ki. Takalli Asma'u da natsuwa bayan tad'ora ruwan "waye yace za a ba ki Julaibib a matsayin mijin aure?Tayi d'an tsaki"na manta.Kin manta?Eh,to ban sa a ka ba inji 6arawon tagiya,sai kuma tayi kwafa"ba Hajiya ce da wannan neman maganar ba,haka kawai ga wanda zuciyata take marari... Tad'auki flask batace kome ba tajuya tafita. Asma'u tabita da kallo"yauma kinji haushi dan na ce ba shi nake so ba ko?Tad'an motsa kafad'a,sai dai kiyita jin haushin me zanyi dashi?Tad'auko garin dawa za tayi talge dan har ruwan ya tafasa.
Littafan tane a saman tebur ta barbaza, nazarin su take so tayi d'aya bayan d'aya saboda ranar Litini za su fara jarabawa,tad'auki littafin lissafi tana dad'ayin nazari akan darasin da aka musu wancan makon Simultenous Equation sai dai ko dak'ik'u goma bata had'a ba taji ta gaji,ta kasa fahimtar kome duk da kuwa a wajan lissafi babbar k'waruwace,ita dai azumi yana ba ta wahala da mutum zai iya biya a mishi aikin ibada to ita dai azumi za ta dinga biya,kome a wahale takeyi,ta ture littafin gefe idan ba haka ba yanzun nan kanta zai fara ciwo kuma yau itace da aikin abin bud'a baki,a hankali taza me takwanta a doguwar kujera gwamma tad'an rintsa kafin lokacin aiki yayi,tad'anyi tsaki tun yanzu jikinta ya mutu murusss... ALLAH dai yasa Umma karta ba ta aiki me wahala.
Kamar a mafarki tashak'o k'amshin arabi'an perfume tare da sallama.Dasauri tabud'e idanunta da suka canja kala dan bacci ya fara awon gaba da ita,yana jingine da k'ofar shigowa yayi sharrr...sharrr dashi cikin farin yadi me k'ananan huji-huji kana hango farar singilet d'inshi, bak'in gashin kanshi ya sha gyara yanata kyallin hair fruits,ba laifi yafara maida jikinshi sai taji dad'i a ranta.
Tamik'e zaune cikin mamaki"Yaya D'ansarai?Yabar duba wayar hannun shi yad'ago yana kallanta "na'am,ina ta sallama baki amsa ba szumin tun yanzu ya fara duka kenan.Tayi murmushi"tad'anyi tsaki kai dai bari kawai, wai ba ka ce sai sallah za kazo ba?Yak'arasa shiga D'akin-shak'atawar"eh,yau da safe nazo anjima kad'an zan koma na manta wasu muhimman takaddune abinda yadawo dani kenan,yad'aga kiran daya shigo wayar shi, baiyi magana ba bayan sallamar da yayi,sauraro yakeyi... zuwa wasu yan dak'ik'u ya amsa da"nagode Maimun musha ruwa lafiya.Yasa wayar a aljihu,yana d'ago kai caraf idanunsu yahad'u yakauda kai...daga can tsakar gidan suka fara jiyo Asma'u cikin nishad'in ta,tana rera wasu baiti daga cikin baitocin wakar Sadi Sidi Sharifai da Maryam A.Baba(Sangandale)suka rera...tana tafe tana tafa hannaye.
🎶🎵Taho malam,taho gani nan da soyayya nafito daga gida🎵🎶
🎶🎵Ina shaidama a yau ne nasamu sak'onka, ina zaune a gida sai naji shi begen ka🎵🎶
🎶🎵Shine nafito in duba ko zan ganka🎵🎶
🎶🎵Amsar sak'onka na yarda in zam matar kazamo megidahhh...🎵🎶
Tana shigowa suka bita da kallo.Kunya da haushin shi suka rufe ta,tayi jimmm...fuska a yamutse tagaishe shi,bata jira amsawar shi ba ta d'auki abinda yashigo da ita"tin-opener"a saman tebur tajuya.Asma'u yakira ta.Sai tayi kunnan uwar shegu tak'ara sauri.A k'ofa sukayi kaci6is da Mama,takalleta da kulawa"saboda ALLAH Asma'u a wannnan gwalagwalan kwanakin nagoman k'arshe kika tsaya rera wak'a...?Tayarfe hannu "dan ALLAH Mama kiyi hak'uri kar Umma tajiyo ki, yanzu tashigo gidan daqowarta daga unguwa. Astagfirullah...Mama tayi murmushi"ALLAH yadad'a shirya ku.
Sudaida tabishi da kallo bata ga wani yanayi a fuskar shi ba,yakalli agogon dake d'aure a hannunshi na dama,lokaci ya ja gashi har Matsirga yake so yaje kafin yawuce. Yad'an kalle ta"ke na wuce.Ta taka mishi har k'ofar gida inda ya ajiye mota"Yaya Julaibib ALLAH yatsare hanya, musha ruwa lafiya.Amin Sudaida nagode.Tajuya zuwa cikin gida tana zancen zuci"Yaya Julaibib bai san da maganar Hajiya akan an ba shi Asma'u ba. Asma'un kawai Hajiya tafad'a ma.
Yau take sallah...kowa kagani yayi sharrr dashi dashiga ta burgewa ya kure adaka.Bayan an sakko daga sallar Idi Hajiya da wasu daga cikin jikokin ta suka mata rakiya zuwa gida.Me musu fid'an ragon sallah har yazo na Hajiya yake fara gyarawa kafin yawuce sauran gidajan, suna d'an hira da Sudaida tana kallan yadda yake yi cikin sauri da k'warewa.
Julaibib yashigo da sallama,yana sanye da babbar riga,'yar ciki da wando na farin voil,takalminshi sau ciki da hular dara bak'a, k'amshin arabi'an perfume d'inshi ya cika tsakar gidan kamar lokacin yake fesawa, gyaran fuskar dayayi sai yak'ara mishi kyau"har ka cire kwalliyar sallar?Ba dole ba autan Inna,zanyi aikin fid'a da farar shadda ne?Zai shiga d'akin Hajiya yace "ka daiyi sauri kagama dan ga na Inna can yana jiranka.Tabi bayan shi zuwa d'akin.
"Happy Eid-eel Fitr sarauniyar Sinan.
D'an gajeran sak'on Sinan daya shigo wayar ta kenan,tayi murmushi.Tazauna tana kiran A'isha dan Kafanchan ta tafi wajan Kaka acan tayi sallah. Tad'aga da sallama,Sudaida ta amsa sannan tad'ora"zakara ya ja kaza kinyi sallah lafiya?Ta amsa"a ah mantawa kikayi takalmi ne yaja k'afa.Sudaida taja tsaki "ai wallahi sa a ma kika ci dana kira ki,keda za kiyi zaman ki shi Hashim d'in yazo nan yayi sallar wai sai kawai kika wani bishi...A'isha ta tari numfashi" ke dakata haka malama karki d'oramin jakar tsaba kisa kaji sudinga bina,wannan sallar nafara zuwa Kafanchan?Ni ba wajen shi naje ba wajan Kaka naje.Tasake jan tsaki"ba cinya ba k'afar baya. Itama ta amsa"a ah ALLAH yasa k'afar kafad'a ce, ke kika sani,ba Khausar wayar.Yaya Khausar gida tawuce ni ina gidan Hajiya.Tam barin kirata sukayi sallama. Asama taji Hajiya tana fadin"to na samo maka matar aure.Matar aure wace iri kamar yaya? Yatambayeta cikin rashin fahimta.Takalleshi"au ka manta yadda mukayi dakai cikin azumi?Ba ka ce in samo maka bane?Yakama kai"Innalillahi,Hajiya ni fa wasa nake miki.Tawatsa hannaye "kai kajiyo, amma dai aikin gama ya gama duk dai ban fad'a ma kowa ba sai yarinyar,to amma tunda kaima na fad'a maka to zan fad'a ma Iyayan na ku kowa yaji yakuma sani.Wacece ita?Tagirgiza kai"uh uh ba yanzuba ina so ne tad'an kara girma da hankali lokacin an kawar da Yayyinta.
Shi da Sudaida suka kai juna.Yakauda kai cikin rashin sanin abun fad'a,yasauke numfashi,d'an madaidaicin kofin hannun shi ya ajiye a saman tebur."akara maka ne?Yakalli Hajiya kamar be ji abinda tafad'a ba na'am, a ah Alhamdulillah wannan d'inma ban shanye dukaba, yad'auki murfin yarufe kofin.Yad'an karkace kad'an yaciro rafar yan naira ashirin guda d'aya ya'ajiye agabanta"Hajiya ga nawa goron sallar ba yawa. Tayi murmushi"Julaibibi me yawan kenan ALLAH yayi albarka nagode madallah.Sai ga Nasmat ta shigo da babban foodflask cike tam da tuwon sallah"godiyar me wannan tsohuwar take yi?
Idanun ta yasauka akan kud'in takama ha6a wai wai wai sai ta zauna"Hajiya lillahi warasulihi keda mutuwa tafara k'wank'wansa miki k'ofa me za kiyi da sababbin kud'i?Tamik'a mata hannu kawo su kawai,to ke me ma za ki siya ne? Hajiya ta d'auki kud'in ta"zancen ki dutse,zan kuma rasa ba ki, ki zauna jiran gawon shanu kinji ko?Takalli Julaibib"Autan Inna yau take sallah fa.Yamata wannan rikitaccen kallan na shi yayi-yayi tadaina kiranshi da wannan sunan amma tak'i "yan mata kyau da sallah idan tawuce sun zama jakai.
Tagalla mishi harara"wallahi ALLAH yasauwak'e ai kaima ka san ba ma cikin irin wad'annan kucankan 'yan matan. Adai fad'ama wanda bai sani ba"ai kaima ka sani kana kuma gani ganin idanunka.Yad'an kalleta"uh ke dai abar tuna ba ya kawai wai gyartai ya ci sarauta,yajefa mata rafar 'yan naira biyar guda d'aya"ga shinan gaba d'aya 'yan matan dake zuri'ar Hajiya za ku raba,kowacce ki tabbata kin ba ta dan ba wacce zan kuma ba sisin kwabo na, yanuna Sudaida sai ki fara da ita.Tasa kud'in a jaka tabbb... Wannan shine tazo muji ta tawuce ta bayan kunni wannan nawane ni kad'ai kai dasu wallahi...bai saurare taba yama Hajiya sallama yatashi yatafi.
Yaya Julaibib tabishi zaure.Yajuyo "na'am.Dan ALLAH rake za ka siyo min idan za ka dawo anjima.Yakalleta cikin natsuwa"Sudaida a ina zan samu rake yau sallah fa ai basa fitowa. Tad'an marairaice "ALLAH bayan sallar la'asar za a samu wanda yafito.Yad'an motsa kafad'a"idan an samu to.Nasmat da Sudaida su suka gyara naman suka soya ma Hajiya,dan dama sun iya kome an horasu da aiki.
Yadda yake juyi a kan gadon cikin sulusin dare dan ba ya jin bacci,haka yake juya kalaman Hajiya"to na samo maka matar aure...amma dai aikin gama ya gama...yagyara rufa yana dad'a d'ora kanshi a saman matashin "hummm...wacece matar?Wacece ita? Yakad'a kai cikin sauke numfashi"ALLAH yajik'anki Megado... Wani tunani yad'arsu a zuciyar shi game da Sudaida,sai kuma yagirgiza kai"abun dakamar wuya...toh yanzu da Hajiya take wannan maganar "idan yarinyar bata mishi ba fa?Yana jinjina irin zaman da za ayi na har k'arshen numfashi ne fa, yagyad'a kai"abu mafi sauk'i suyi magana da Hajiya tafad'a mishi ko wacece,idan bata mishi ba toh a canja mishi da wata tun kafin Iyaye suji maganar.
Daga masallaci sallar asubahi yaje yasa mu Hajiya da maganar amma fau-fau tak'i yadda suyi ta"wai ai yarinyar da d'an sauran ta,za ta fad'a mishi a lokacin daya da ce,kuma ba ta dawani makusa dole ma ya so ta tunda itama macece.Dole ya hak'ura yatattara yakoma inda yafi wayau...Ko hutunan da suka d'auka dasu Hajiya bai tsaya ya kar6a ba,dan Hajiya tace bata san wani hoto a waya,dole suka kira Misbahu me hoto ya d'auke su na kati,bai ma yi sallama da yan'uwa kamar yadda yasa ba ba.
Tana wanke kayan makaranta Asma'u takawo mata waya"ga shi ya damemu da kira.Waye?Bata yi magana ba ta ajiye wayar a gefen ta,tajuya tayi tafiyarta. Aka sake kira tad'aga tana d'an turo baki kamar yana ganin ta"ni dai ALLAH na yi fushi.Shi yasa nake ta kira kika k'i d'agawa?A ah wayar tana d'aki na sa ta a caji,ni kuma ina tsakar gida ina wanki,ALLAH da gaske Yaya D'ansarai naji haushi dana je gida neman ka Inna tace wai asubanci kayi.To kiyi hak'uri. Nayi. Yauwa nagode ALLAH yamiki albarka. Amin. Sudaida...yakira ta. "Na'am.Baki fad'amin hotunan da mukayi a masallacin Idi sunyi kyau ko basu yi ba?Tayi yar dariya"sunyi kyau musamman wanda muka yi da Hajiya.To d'an turo min ta whatsapp"tabbb...ai kawai kayi hak'uri idan kadawo ka gani ganin idanun ka.Yayi murmushi "wato kin rama ko?To shikenan ki ajiye min,nima a makon nan zan shigo,kin ko ajiye min dambun naman ko duka kika ba wannan yaron?Ta gane wanda yake nufi amma sai tace"Yaya Julaibib wani yaro zan ba dambun nama har da na ka? Saurayin ki...yafad'a a dak'ile.Kai dan ALLAH Sinan d'in ne yaro?To dame kwad'o yafi gaya?Zak'i. Yabata amsa a tak'aice kafin tace wani abu ya katse wayar.
Julaibib Abdullahi D'ansarai...Yana gama degree d'in shi na farko ya d'ora degree na biyu(masters) a dai Islamic Studies baya wani samun zama kullum cikin zirga-zirga tsakanin Zonkwa da Zari'a har ya kammala kome sai karatu da za a fara ba kama hannun yaro yazo gida yayi mako d'aya sannan ya tattara yakoma dan cigaba daka inda aka tsaya,shi dai Musaddiq bai cigaba ba sai harkar kasuwancin su ya keyi,yana kuma yin kome tsakani da ALLAH,kome a rubuce yake sai Julaibib ya zo ya nuna mishi.
Sudaida tana zaune a tsakar gidan su Swachet wata yar ajin su ce ta je kar6o takaddun WAEC na shekara uku da suka wuce wanda Yayan ita Swachet d'in ya rubuta,tana so tad'anyi nazarin su,tana zaune zaman jiran Swachet takwaso matasu a d'aki.Tayi tsai...na wucewar wasu dak'ik'u da tunanin waye to da wannan aikin?Karo na uku kenan ana lek'owa ana komawa,to mutanan da suke shiga gida kai tsaye ko macece ko namijine indai ba mara gaskiya ba wazai yi haka?
Tamik'e cikin sand'a dan san ganin ko waye.Caraf idanun su yahad'u,tabud'e idanu cikin mad'aukakin mamaki da tsoro, tanuna shi da yatsa"Sinan kaine kake lek'e?Me kazo yi anan unguwar? Ya sosa kai yana mata d'an murmushi" wai dama kece?me kika zo yi anan?Tayi jimmm... tana mishi kallan nazari kamar ba shi da gaskiya sai waige-waige yake yi"kar mu maimaita tambaya ba amsa mana. Yasake sosa kai yana murmushi "Sudaida sarauniya ta... wallahi na fito shan iskane kawai, sai kuma naga wata kamar ke shine nake lek'awa,yakalli agogon dake d:aure a hannunshi "kai jama'a lokaci fa ba wuya,kin san yau akwai wa'azin maza a gidan bak'i, muje mana,yad'ago yana kallanta har yanzu itama shi take kallo "lafiya kuwa Sudaida?Tagirgiza kai"ni mamaki kake bani wai duk girman cikin gari karasa inda za kaje kasha iska har sai ka shigo nan daba bahaushe ko musulmi me sallah ko d'aya? Ni fa wallahi Sinan ba na ga ne ma wasu al'amuran na kafa gaskiya.Anya Sinan...?Yatare da sauri cikin dad'in baki da rantsuwar ba abinda yakawo shi,har sukayi sallama yajuya da sauri yabar unguwar. Takama ha6a "Sinan fa kamar ba shi da gaskiya tajijjiga kai akwai lauje cikin nad'i.
"Hey Ibrahim...
Swachet ta dafa ta,me kika fito yi a waje? Sudaida tajuyo cikin sauke numfashi,sannan tasa hannu tazame hannun Swachet daga kafad'arta"na sha fad'a miki mu addinin mu na musulunci yaba Iyaye girma na alk'adari akan Ya'yan su, mu kome sunan mahaifin kane ba ka kiran sunan shi kai tsaye ba dan ya haife kaba sai dai dan yaci darajar sunan mahaifin ka ko mahaifiyar ka,ni sunana Sudaida to banga dalilin da zai sa ke kuma kidinga kirana da sunan mahaifi na ba,wannan al'adar turawar ba da Sudaida ba gad'a da fatalwa.
Swachet tawatsa hannaye cikin halin-ko-inkula"ni banga wani abu ba fa.Takar6i takaddun tana gyad'a kai "tunda baki gane me nace miki ba ko?Tad'an ta6e baki tana yar dariya"Sudaida kin cika shagwaba tun muna JSS Class idan an miki abu sometimes sai kin turo d'an k'aramin bakin nan naki kamar gidan tsutsa gashi har yanzu as a matual baki bari ba haka zaki haifi Ya'ya idan sun baki haushi kidinga musu? Takai mata duka. Sukayi dariya.Muje in taka miki amma ba da yawa ba, dan akwai wanda nake jira.Sudaida takalleta da sauri"waye shi?Ko kema kin fara zuwa kwanan gidan ne.Tayi d'as da yan yatsunta"God forbid bad things ni da zan zama sister,ni bani da saurayi ma, sak'o kawai zai kawo min in kaima budurwar ta shi.
Tibishi yatare shi"wai har ka dawo sai kace akan k'aya kake?Yafad'a kujera tare da lumshe idanun shi na wucewar wasu yan dak'ik'u sannan ya bud'e su"ai ban ma k'arasaba na had'u da Sudaida.Yacire kofin bommi(ruwan kwakwa) dayake shirin kaiwa bakin shi,yana mishi kallan uku ahu"to me kake nufi?Ya ajiye kofin a saman tebur yahad'a hannayan shi waje d'aya yad'ora ha6arshi akai"wai tsoron yarinyar nan kakeji?Har yanzu baice kome ba,ya daiyi tagumi yana zancen zuci"zan bar abinda nafara kawai tun kafin wankin hula yakaini ga dare,kwata-kwata bani da kwanciyar hankali.Tibishi yaja dogon tsaki sannnan yamik'e yabar d'akin yana zagin Sudaida, Sinan,hausawa dama duk wani wanda yake sallah harda Katafawa yan'uwanshi a jinsi da d'aukacin masu sallah na doron duniya gaba d'aya.
Yatsaya a k'ofar D'akin-girkin yana kallanta tana kwasan tuwon dare,tayi kyau cikin riga da zani da d'ankwali na atamfa ruwan hoda da ratsin k'ananan filawoyi ruwan makuba,d'an k'aramin bakinta yanata kyalkyallin man le6e ruwan hoda"miyar me kikayi?Ta yamutsa fuska tana turo baki"labarin zuciya a tambayi fuska "miyar shuwaka.Yayi yar dariya"da kan ki? To Yaya Julaibib ya zanyi?Sarkin yawa ai ya fi sarkin k'arfi shi sukace suna so,na ce bazan yiba,Umma ta ce wai dole shi zanyi duk da itama fa ba wani so take yiba,ai wallahi gidan Hajiya zani bazan rasa abin sawa abakin salati ba.To yi sauri ki gama sai mutafi tare nima can zani barinje mu gaisa dasu Mama.
A gidan Hajiya tana cin sinasir da miyar taushe,Julaibib da Hajiya suna hirar data shafe su,saiga Sinan yashigo da sallama.Hajiya ta amsa sallamar"wa alaikumussalam lale maraba da Sinan,bismillah.Yashiga yazauna cikin girmama yana gaisheta.D'ansarai yad'aure fuska ko kallan shi bai yiba yacigaba da duba wayar shi.Sinan yakalli sarauniyar ta shi kamar itama batayi maraba da zuwan shiba,yad'an sosa k'eya bayan ya ajiye ma Hajiya ledar d'aya shigo da ita,Maltina da madara ta ruwane a ciki "Hajiya ba yawa ni zan wuce."Hajiya tamishi godiya da sa albarka.Har yasa takalman shi Sudaida ba ta da niyyar ta shi.Hajiya takama ha6a tana kallanta ta"Oh ni 'yasu, Sudaida kar6i nan tamata dak'uwa.Tamik'e tana k'unk'uni.
Shima Julaibib yamik'e"Hajiya magriba ta gabato.Tabishi da kallo "gaskiya ne gwamma ai harama dan a samu jam'i.Yazo yawuce su a k'ofar gidan kamar bai gansuba.Sinan yasauke numfashi "D'ansarai ALLAH yayi miskili,magana ta fatar baki bayan sallama rabon da muyi ta har na manta shekarar.Tad'an harareshi"ai dai ba ga ba yake yi dakai ba tunda zai maka sallama, rashin maganar ma ai kamawa takeyi a d'aure me d'aurewa.Yayi murmushi kawai"ba ta so ayi maganar Julaibib yanzu sai taji haushi,kad'an sukayi hira sukayi sallama dan anfara kiraye-kirayen sallah daga mabambantan masallatai.
Tibishi yatari numfashin ta ta hanyar kyalkyalewa da dariya"mahak'urci mawadaci ne Zigwai, yabud'e hannunshi na dama, ya fa riga ya shigo tsakiyar tafin hannunki kin riga kin mishi kattt...kisan mummuk'e, bashi da wani kata6us sai yadda mukaja da akalar shi musamma ma ke; yad'auki kofi yazuba mata bommi"sha kijik'a mak'oshinki "tanasha suna dad'a tattauna yadda za su 6ulloma al'amarin,yanzu abinda za ayi ki kirashi a waya yazo yad'auke ki,idan kuma bazai samu zuwa ba to da yamma yazo Fajumali-Hotel.
Tagalla mishi harara"kaima fa wasu lokutan shawarar ka ba ta d'auka bace.Kamar yaya ba ta d'auka bace?Tamik'e tana sa6a jakarta a kafad'a"to tayaya zan kama d'aki a Hotel d'in dake cikin gari tsakiyar hausawa?Sannan shi kuma kana ganin zai yadda ko hanyar yabiyo bare har aganmu tare?Yabata hannu suka tafa "shegiya yan mata wannan k'wak'walwar ta ki ba laifi tana ja,amma kafin ki wuce ya kamata kid'an bani na kashewa.Ta6alle jaka tawatsa mishi dubu biyu"kai kudin ka ba sa k'arewa a kome sai a burkutu(giyar k'ok'o) yanzu na san D'One zaka tafi.Suka fito yakulle d'akin yana bata amsa"kamar kin sani dan Alhamdu ma yana bina bashi.
Cikin fushi yashiga d'akin tana zaune a kujera tana chatting,sai ta ajiye wayar tana mishi wani murmushi tare da gewaye hannayen ta ajikin shi tana mishi wani irin salon jan hankali"hey dude just chill up" abinda take mishi ya ka sa daurewa,dan haka yabiye ma yarima aka sha kid'a,wucewar wasu dak'ik'u sai ga shi yana kwasar dariya,yad'an shafa cikin shi"wallahi yunwa nake ji rabo na da abinci tun na safe.Tajawo abincin gaban shi "kaci ka k'oshi dakai na nadafa maka,dan ka fara zama na musamman a cikin zuciya ta,tasake kashe murya da wani irin salon na yan duniya"Sinan ALLAH ban had'a soyayyarka dana kowani namiji ba,saboda samun irin ka a cikin maza sai anyi da gaske,ina sanka Sinan.Yayi murmushin jin dad'i "ALLAH dagaske Zigwai?
A yangance ta amsa"ga kai ga k'afa ai ba tambayar me aka yanka. Yakai loma bakin shi yana gyad'a kai"gaskiya na gani ganin idanu na, yagama cin abincin yamatsar da sauran gefe, wayar shi da aka kira ta katse musu hanzari, yad'aga cikin ladabi"a ah bana kusa amma dai yanzu zan zo,yakatse wayar yana kallanta "Babana ne yake son gani na yanzu.Tamotsa kafad'a"ba matsala,amma ai za ka dawo ko?Yamik'e"wannan dole ne bani mukulli idan nadawo ba sai nazo inata k'wank'wasawa ba koda kinyi bacci.tad'an taka mishi zuwa bakin k'ofa"kasiyo min balangu. Yagyad'a "kin samu balangu kin gama.
Tibishi yak'araso yana dariya"akwai ranar kin dillanci...a ranar za ka gane da gero ake koko.Zigwai ta 6ata fuska"gaskiya ka daina zagin saurayi na.Yashige d'akin yana zagin ta"kaji yar duniya,saurayin ki ko dadironki? Tawatsa hannaye "what ever,idan ba haka ba zan fad'a mishi.Yaja tsaki"idan kin fad'a mishi sai me?A saran wa? Kafin me riga yarufa,me bargo yayi gumi. Yak'arasa cinye abincin da Sinan yarage,yana ta janta da hira tace"a ah zo kawai kayi tafiyar ka dan yace zai dawo.Yamik'e"to sai da safe,yakamota yana k'ok'arin ba ta sumba,ta ture shi"katafi mana indai ba kwa6armuce kake so tayi ruwa ba.
Yak'ara matsawa kusa da ita"haba 'yan mata,dan dai d'an alakoran daza ki bani ai bazai sa ba bazai rage ba,tamu dake ba ta 6aci, yazuba mata idanu"anya banyi ihu da kirari na da6ama kaina wuk'a ba? Tagirgiza kai"bakayi haka ba Tibishi"marakiyi ai ba abokin tafiya bane" tamishi rad'a a kunni,ya bud'e idanu yana kallanta "ta jijjiga kai"na rantse da ALLAH da gaske nake yi,suka kyalkyale da dariya suka tafa"shegiyar duniya to mukwana lafiya,amma kirage min kayan dad'in daya kawo miki, tagalla mishi harara"ba zan ajiye ba d'an rainin hankali,kura da shan duka gardi da k'wace kud'i?
Tibishi yana hango Zigwai ta sauka a kan mashin yatareta"me za kiyi a cikin gari?Tamishi wani kallo"ji wata banziyar tambaya kai me kazo yi?Ni cikin gari wajan zuwana ne.To nima haka zani wajan Sinan ne kwanaki hud'u kenan baya amsa wayata na tura mishi sak'onni sun fi guda goma nan ma ba amsa dan haka zani ingani ganin idanu na ko lafiya?Yad'aure fuska"ke Zigwai ina fata kina sane ke ba wata tsiya bace a wajan Sinan? Tayi shiru, yakalleta"to rashin jinshi a waya kuma ya samo asaline da irin zirga-zirgan bikin shi daya gaba to,kin san suna gama WAEC za ayi auran to saura kwanaki sugama zana jarabawar. Dammm...zuciyarcta buga.
"Sinan zai auri Sudaida???!!!
Tayi d'as da yan yatsun ta"incredible! Haka mukayi da kai Tibishi?To ko ba haka mukayi ba to ke kina ganin kai tsaye za kice Sinan yabar auran tane bai d'auki ke wacce taci kai ba? (hauka)Tarik'e k'ugu tana kallanta d'ai-d'ai kun mutanan da suke kai-kawo a cikin hantsin saboda sanyin da akeyi, suna tsaye sai ga su Sudaida sun zo sun wuce a mota,tabi motar da kallo har ta harba saman kwalta.Sudaida ma tagansu"wai a wannan mugun sanyin amma tayi irin wannan shigar me kama da tsirara,takada kai"ALLAH yasauwake.Tibishi yasauke numfashi"muzauna musan na kwatanci fa,kar k'aramar magana tazama babba, tagirgiza kai"ni fa yau sai na ga Sinan.Yad'aga murya dan tafara bashi haushi"wai ba na ce miki Sinan ba ya gari ba?To indai haka ne gwamma in koma gida dan ba saboda kai nafito a wannan sanyin Jauran ba.Yad'aga mata hannu "sauka lafiya.
Sudaida tabishi da kallan tuhuma saboda karo na bakwai kenan ana kiran shi a waya yak'i yad'auko ta daga aljihu ma,bare yaga me kiran.Yad'an motsa kafad'a "share kawai.A share kamar yaya?Bai yi magana ba yaciro wayar a aljihu yana nu na mata kingani sunan Zigwai yafito 6aro-6aro a fuskar wayar sai yamayar aljihu yana mata bayani"wajan aikin mu d'aya dashi,to wasu takaddu yabani in cike,na kuma san tambaya ta zaiyi idan na cike su in kai office,ni kuma gaskiyar magana zuwa wajan ki yafi kai takaddun mahimmanci...ba zato sai ga Tibishi "jaba Sinan irin wannan abun da kakeyi ba kyau,ya kama ta aba duk me hakki hakkin shi.
Cikin fushi Sinan yatare shi da hayagaga har abun yaba Sudaida tsoro da mamaki saboda irin zagin daya mishi"dan abu kazan uban ubanka baza a bayar ba ayi wacce za ayi dan dan iska kawai...idanun Sinan sun kad'a jawur saboda 6acin rai yanuna Tibishi da yatsa "ka6ace min da gani kafin in 6alle ka.Au haka kace? Yajijjiga kai"eh haka nace dan abu kazan ubunka.Yajuya yana kwafa"na rantse da ALLAH Sinan za ka gane da gero ake koko,za ayi walkiya kuma kowa zai gani ganin idanun shi;kura ce lullu6e da fatar akuya.Sudaida takalleshi"me kalaman Tibishi suke nufi ne?Yawatsa hannaye "Oho mishi ba mamaki yaje ya shata ne bata fad'a mishi gaskiya ba,zanbi shawararki kawai gwamma muyi hannu riga dan nagaji da rashin mutuncin shi.Tayi tsai tana kallanshi "rashin mutunci,to me yahad'aku da yake maka rashin mutunci?Bai bata amsa ba yasauke numfashi, yabata tsaraban Kaduna sukayi sallama.
Tunda yakwanta yakasa bacci sai juyi yakeyi,zuwa can yamik'e yad'auki mukullin mashin yafita, gidan au Zigwai yatafi,tana tsaka da bacci yata sheta, tamik'e zaune akan gadan tana mitstsike idanu kamar gaske"na gaji da jiranka,tafara mishi abinda tasa ba, yarik'o hannayen ta,yakalle ta cikin natsuwa"Zigwai kiyi hak'uri da duk al'amuran da suka faru a tsakanin mu,kin sani aure zanyi,dan haka ba zan dinga barin matata ina zuwa wajan kiba,yaciro rafar d'ari biyar guda d'aya yad'ora mata a cinya "ga shinan ba yawa,amma a hakan idan kikayi maleji zai isheki kija jari, basai kin cigaba da sai da mutuncin ki a wajan sauran maza ba.Tafizge hannayen ta"me make nufi? Kana nufin mun rabu kenan? Incredible!rabuwa da kai ba abu me sauk'i bane,sai ta fashe da kuka,kuka me ta6a zuciyar duk wanda yaji bare kuma shi da ake kukan saboda ana son shi,ba a son rabuwa dashi.Idan yacigaba da zama za tasamu lagonshi dan haka yamik'e,dasauri tasha gaban shi"idan kamin haka kaci amanar kauna,wai duk irin sadaukarwar dana ba ka a soyayya?Yakalleta cikin tausayi da tafasar zuciya"ya bud'e baki zaiyi magana sai kuma yayi shiru,tagyad'a kai cikin hawaye"fad'i duk abinda za ka fad'a dan wanka da gari ba maganin yunwa yake yi ba"to kiyi hak'uri kawai ai ni da ke ba alk'awarin zama na har bada mukayi ba, bare kice na ci amana.Yajuya zai tafi.
Tafara mishi wani salo daya sa shi tsayawa"Sinan na yadda za mu rabu amma ina fata baza ka sani a kwandon sharaba,idan mun had'u zamu dinga gaisawa.Yagyad'a kai"dan wannan karki damu.Takashe shi da murmushi "saura abu d'aya tsakani na da kai,kuma alk'awari kayi ranar birthday d'ina za kazo"you're the special quest of honour" idan ka halacci wajan to ka gama biya ta,kuma ka fita ko ba sabulu.Karki damu. Tasake shi yatafi.
Tabishi yafito daga bayan labulen daya zagaye d'akin,nan yashige lokacin dayaji tsayuwar mashin yalek'a ta taga yaga Sinan ne, sukayi dariya suka tafa,yakai hannu zai d'auki kud'in a saman tebur tariga shi.Yakalleta "banga ne ba.Tagyad'a kai"ai nima zan fiso kaita zama cikin rashin ganewan,wallahi idan na ba ka dayawa dubu biyar.Yakarkace kai yana kallanta da mamaki"dubu biyar zan samu?Tazuba mishi idanu"to ina laifi dubu biyar a wannan marran,karanka ne yakama?Yakad'a kai"lallai kin cika yar duniya hayak'in taba.Takwanta tana dad'a jan bargo"maraina kad'an dai 6arawone,malam idan za ka kwanta kazo ka kwanta,idan ba ka jin bacci to ta shi kasan nakwatanci karka hanani bacci gobe sammako zan buga zuwa Zuturung. Yagalla mata harara"zuwa wajan wani dadiron na ki?Takyalkyale da dariya"ina da wani dadiro ne daya wuce kai?Hummm...bari dai mugama da wancan shegen bahaushen sai muzo mufara shirin aure.
Suna cin dafaffiyar masara tashigo da sallama tazauna tana gaishe da Hajiya tare da fad'in "Hajiya gani ance kina kirana"Hajiya tabita da kallanta nazari, tarame tayi wata iri ba ta cikin wal-wala gidan na tama yau kwanki biyar kenan bata zo ba,shine ta aika akira ta"kwana biyu ban gan kiba ko lafiya?Lafiya lau"ta amsa a tak'aice.Hajiya ta gyad'a kai"to d'auki masaran kici mana,ni fa gaskiyar magana yarinyar nan ba ta da lafiya,Julaibibi wai ko kuna ganin yadda take k'arewa kamar kud'in guzuri? Dammm...zuciyar shi tabuga daya d'ago Yakalle ta, yacigaba da kallan ta ba tare daya ce kome ba.Hajiya tagyad'a kai"ah to kaima ka gani ko?
To tunanin auran ne yamaida ke haka kome? Shima Sinan d'in kwana biyu shiru ko dai kunyi fad'a ne? Zuciyar ta tayi rauni,ba abinda take son yi sai kuka,bata 6ata lokaci ba tafara sharar kwallah a hankali sautin kukan kefitowa hawaye sharrr...sharrr...masu d'umi suka fara sintiri a fuskarta,tacigaba da kukan ta har da sheshshek'a;ba wanda yahana ta sai da taci tak'oshi sannan dan kanta tayi shiru,tahaye gadon Hajiya ta kwanta.Julaibib yayi shiru ran shi ba dad'i"mecece matsalar Sudaida ne?Kira yashigo wayar ta tad'aga da dishashshiyar murya"ina gidan Hajiya ne,tad'anyi sauraro...kayi hak'uri Sinan bana jin dad'i ne kabari sai gobe ko kuma kaba Yaya Khausar za ta ajiyemin...Cikin shashshek'ar kuka tace"to Sinan nagode...
Hajiya tata fa hannaye cikin sallallami "Oh ni jikar mutum hud'u,amma wannan yarinya ALLAH yashirye ki,ba yanzu nagama tambayar ki ko ba ki da lafiya ne kikace ke kalan ki ba?To ai shi kenan kowa rai yama dad'i barin me shine. Tamik'e tana sa hijab.Sai ina? Julaibib ya tambayeta.Tad'auki mukulli tana kallanta Sudaida "idan kin gama kwanciyar jin dad'in za ki tafi gida ban dawo ba to dama karki kuskura kibar min k'ofa a bud'e,tamaida kallanta ga Julaibib"gidan Sahura za ni.Hajiyarmu adawo lafiya,nima dana gama cin masarar hannuna zan tafi.
D'akin yayi shiru wucewar wasu dak'ik'u har yagama cin masarar ya ajiye totuwar yamik'e yana kallanta"tabbasss duk wanda yayi ihu to taimako yake nema"Sudaida ALLAH yadafa miki akan damuwar ki.A raunane ta amsa"amin Yaya Julaibib nagode.Yaja numfashi yafitar da iskar tabaki ta hanci"ni gobe zan koma makaranta, inaga sai ranar d'aurin aure Insha-ALLAH da sassafe zan taso,na san zan samu d'aura aure,su Nasmat duk sun fad'amin abinda suke so in sai musu,ke ma me kike so in sai miki?Tamik'e zauna da sauri cikin rawar muryar data rasa dalili"sai ranar d'aurin aure?Kana nufin bazan sake ganin kaba sai ranar da ALLAH yayi?Kwallah yacika idanun ta.Cikin rashin fahimta yakalleta"kamar yaya sai ranar da ALLAH yayi? Yaya Julaibib ranar d'aura aure to a ina zan ganka? Kuma ranar za a kaimu gidan aure,washe gari za ka koma makaranta to yaushe zan ganka? Kana nufin sai ranar danazo gida idan kana gari sai mu had'u?Ko zaka dinga zuwa gida na?Yagirgiza kai"me kike so Sudaida? Yayi tambayar da wata irin murya data sa Sudaida d'ago kai da sauri tana kallan shi cikin dukan zuciya.
Yadafa k'irjinshi dai-dai saitin da zuciya take"zuciyata ayan kwanakin nan tana min wata irin bugawa da ban san abinda zan kwatanta miki ba Sudaida, na kuma rasa gane dalilin haka,ni fa tun bayan rasuwar marigayiya(Bilkisu)har yanzu ban samu kwanciyar hankali ba,bana yin ishashshen baccin da masana a harkar binciken lafiyar d'an Adam suke bada shawarar a kalla duk dare kayi baccin a wanni takwas.
Yasake kallan ta cikin natsuwa "Sudaida kome da kika ga ina yi dauriya ce kawai; amma ciwon yana nan a zuciya ta kamar yan awannin da suka shud'ene,yad'an yi yake"koda yake baza ki fahimci radad'in rabuwa da masoyi ba!!!toh ina miki fatan alheri a gidan auran ki dafatan zama na har abada,mutu ka raba takalmin kaza,ina miki fatan samun babban rabo a alk'iyama Darul-karamah dake da zuri'arki...Yaya D'ansarai...yakauda da kai,yakuma riga ta magana"tunda baki fad'i abinda kike so ba,toh zan ba Asma'u gudummawa ta, zata kawo miki har gida.Bai jira amsawar taba yajuya da sauri yatafi.Tabi bayan shi da kallo dan ya mata susa a inda yake mata k'aik'ayi.
"Rad'ad'in rabuwa da masoyi!...
Tafad'a tasake maimaitawa,rad'ad'in rabuwa da masoyi!!! Sai tasa kuka wasu zafafan hawaye suka zubo mata sharrr...sharrr...wallahi Yaya D'ansarai nima ina jin rad'ad'in... wai...! wayyoh...! ALLAH na!!!!
Nasmat data shigo tayi tsai...tana kallan ta cikin nazari,tarik'e ha6a"ikon ALLAH nazaune ya fad'i,a zaure sukayi kaci6is da Julaibib yana cikin damuwa tana mishi godiyar gudummawar daya ba yar a ba ta,sai yamata wannan rikitaccen kallan na shi yayi kamar baiji abinda take fad'a ba yayi tafiyar shi,tana tunanin me yasa meshi tashigo, toh ga Sudaida itama a wani irin yanayi. Tazauna a gefen gadon sannan tadafa kafad'ar ta"jimamin rabuwa da Yaya D'ansarai ne yasa kike wannan kukan ko me? Tarungumo ta"ni fa na shiga rud'ani, Nasmat ban san abinda yake damun zuciyata ba wallahi,amma ko a yanayin bugawarta ta canja,tsoro nake ji... tasaki Nasmat tana tsaida kukan"Nasmat bana san auran nan...Dama kawai a kyale ni.
Takad'a kai"lallai ma Sudaida na ki wasa ne;kema kin san baza ta sa6uba... Idanun ta suka cika da kwallah"to ni wai ya zanyi ne? Ya za kiyi dame? Har ta bud'e baki za tayi magana sai kuma tayi shiru.Nasmat tayi yar dariya"Sudaida sarauniyar Sinan,kin san me? Kuka bai ta6a zama mafita a cikin matsala ba"ALLAH mahaliccin me kowa da kome za ki kaima kukan ki,zai taimake ki ta inda ba kya zato,nima na yadda ciki ba dan aci tuwo kawai akayi shiba,tabbasss a kwai abubuwan daya kamata yazama sirrin kane,sirri ne kawai tsakanin ka da zuciya.Tamik'e tana rik'o hannayan Sudaida"kin san a kwai makarantar Islamiyya lokaci kuma ya kusa,gwamma muje mu shirya dan ina tsoron ALLAH ina kuma tsoron dukan makaran Malam Jama'are da wannan shar6e6iyar dorinar,tamik'e suka kulle ma Hajiya k'ofa...
Ana dara ga dare ya yi...
Da sauran kuka anci gumba an hana maye.
2 Jumaada Thani 1441
27 January 2020
We Ibrahim's Daughters 👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs.
DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta'in
...GWAJIN DAFI💔
Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)
Shafi nagoma sha takwas.
Julaibib yana gidan Yaya Karima yana mata sallama Baban Abdul yashigo,yamik'a mishi hannu sukayi musafaha"Malam D'ansarai ya karatu? Yayar ka ta fad'amin wai gobe za ka koma nace haba-haba dai ba shekaran jiya kazo garin ba?Yad'an sosa k'asumbar shi"ai yanayin karatun ne sai a hankali.Baban Abdul yagyad'a kai "maganar iyali kuma shiru mak'atau bulaguro a k'iyama tun bayan rasuwar marigayiya,ga shinan kana kallo k'annin ka mata shida za a aurar.Yayi murmushi"ALLAH yaba su zaman lafiya,amma gaskiya ni yanzu ba aure agaba na.Baban Abdul yanu na shi da yatsa"kai Malam D'an Sarai kar kayi butulci fa...yatare shi da sauri"ba haka bane Baban Abdul,shi aure d'an lokaci ne idan lokaci yayi mutum ko bai shirya ba dole sai yayi.Haka ne kuma"To Ubangiji yaba ka macen albarka,amma idan a kasa himma abun zaifi tafiya yadda yakama ta,a kawo k'arshen zaman tuzuran cin nan.Yayi yar dariya kawai sukayi sallama.
Ango ka sha k'amshi.Yayi murmushi. To ya shirye-shirye ance aski idan yazo gaban goshi ya fi zafi ko?...Tacika shi da surutu yatare ta"Zigwai nagode da gaisuwa yakatse wayar. Tasake kira yad'aga,cikin dariya tace"haba na Sudaida ba da kan ka asare idan kaje gida kace ya fad'i,ai ban gama ba.Baki gama me ba?Kamar Yaya,me ye tsakani na dake? Babu,sai dai abu d'aya yarage a tsakanin mu,idan kuma kacika alk'awari to ba kare bin damo maganar birthday party na.Na sani ban kuma manta ba,zan cika miki wannan alk'awarin.Yauwa very good.Ita tariga shi katse kiran.
Umma tashiga d'akin tasame ta a kwance"ke Sudaida me yasa kin cika kafiya ne kamar mutanan farko?A raunane takalle ta"Umma kaina ciwo yake yi matsananci kamar zai rabe gida biyu.Umma tad'aga murya"ki shirya kutafi makaranta kin nok'e ba kya jin dad'i, kici abinci kin kafe ba kya jin yunwa,kisha magani kin bud'e taga kin watsasu waje,to me kike so a miki?Tayi shiru idanun ta sun ciko da kwalla.To ki tashi maza-maza kifita yana jiran ki a waje.Tamarairaice Umma...Umma ta tari numfashin ta,tanu na ta dayatsa"ke kul...tashi nace.Jiki a sanyaye tamik'e tana goge hawayen da suka zubo mata da gefen farin hijab d'inta.
Ba kowa a k'ofar gidan,sai kawai tayi zaman ta a d'an k'aramin dakalin dake tsakanin filawoyin wajen"Sinan gajiya yayi kenan yatafi?A hankali tsigar jikin ta yafara ta shi,sanyin yana ratsa ta, a takure tahad'a kai da gwiwa,tafara karkarwa hak'oranta suna dukan juna,tamik'e dak'yar zata koma gida.Yana tsaye ya nad'e hannayen shi a k'irji,yabi ta da kallo tana sanye da doguwar riga na atamfa me duhu da farin silifas, d'azu a gidan Hajiya riga da zani da dankwali na shadda ruwan toka ne a jikin ta,fuskar ta tayi fayau babu kwalliya,idanun ta sun kod'e dagani ba tambaya taci kuka ne fiye dana d'azu ta gode ALLAH.
Luuu tatafi kamar za ta fad'i saboda jirin daya fara d'iban ta,a hankali takoma ta zauna,tasa duka tafukan hannayenta tarufe fuskarta tana k'ank'ame jiki dan bata daina jin sanyin ba."Sannu Sudaida jiri ko? Tagyad'a kai. Sudaida yakira ta.Tacire tafukan hannayenta a fuska sannan takalle shi,yamik'a mata Farm-pride yoghort d'in hannun shi"ki daure kisha.Tawani marairaice"Yaya Julaibib bazan iya sha ba,amai zanyi.Yazauna a gefen ta sannan yayi k'asa da murya cikin rarrashi"haba Sudaida kiyi hak'uri kisha zai miki magani,rashin cin abincin ki ya dame ni,Sagir ya fad'amin kinfi mako d'aya a haka,kullum sai Umma ta tasa ki a gaba kike cin d'an kad'an,yabud'e mata "d'an daure kisha kinji ko?
Yaya Julaibib amai zanyi zuciyata tana ta tashi fa.Yagirgiza kai"uh uh kar6i kisha baza kiyi amai ba rashin cin abincin ne yasa miki ta shin zuciyar.Tasa hannu biyu takar6a,kad'an ta kur6a tamik'a mishi, yagirgiza kai"d'an kara...da haka har sai da tasha rabi,yakar6a yarufe yamik'a mata anjima kidaure kishanye zai miki amfani,kinga yadda kika zama kuwa Sudaida?Takaryar da kai gefen dama"kai baza ka shaba? Uh kisha kawai. Tamik'a mishi hannu"d'an ban dabino... baya rasa dabino a aljihu yasa hannu ya d'ibosu"guda uku suka rage.Tasa hannu biyu takar6a tana ci.
A mashayar"Beer Parlour"suka had'u da Zigwai.Yaja kujera ya zauna yana kallan ta tana shafama faratanta jan farce ja,tad'ago takalle shi"daga ina kake tun d'azu ka shanya ni?Daga cikin gari mana,na je samo kud'in kashewa ne tunda ke muguwa ce fiance d'inki ba shi da kud'i amma baza ki iya taimaka mishi ba.Tagalla mishi harara"in taimaka maka fa kace?Kai bakaji kunya ba kura da shan duka gardi da kar6e kud'i? Yamotsa kafad'a"a very stingy woman,ba wata kunya dana ji,kin san da ina dashi bazan tambaye kiba,tare ma zamu kashe su.
Tagama shafe faratan ta sannan tasa nailpolish d'in a jaka,tabi wajan da kallo ya cika dank'am da mutane maza da mata ga hasken disco light kore,ruwan bula da ja,wasu na shaye-shaye,wasu suna bin wakar da aka kunna a k'atuwar rediyon,tamaida kallan ta ga Tibishi "birthday party na bazai yiwu a ranar lahadi ba,na maida shi ranar juma'a.To saboda me?Tad'ora duka hannayen ta a saman tebur d'in"dole ranar juma'a zan yi shi saboda ranar juma'ace d'aurin auran Sinan ka gane manufa ta?Yajijjiga kai"na ga ne,kinyi tunani me kyau,amma fa a tsorace nake kar kwa6armu tayi ruwa.Yaba ta k'warin gwiwa "hey just chill up"kwa6armu baza tayi ruwa ba,duk abinda zai faru indai munci gari ba damuwa,ai ranar biyan buk'ata rai ba a bakin kome yake ba inji k'uda.
Da yammacin ranar laraba,rana tayi sanyi Hajiya takira layin Julaibib yad'aga da sallama yana yar dariya"Oh Hajiyar mu na yi kewar kifa"taja tsaki"kai tafi can kaba ni waje,ka yi kewa ta amma tunda kasa k'afa kabar garin nan kaka sa kirana?Ayya Hajiya ta ke kad'ai,kin san d'an makaranta yana fama da geron Sunday(garin kwaki\rogo)ba ta siyan katin waya nake yi ba.Yadda yayi maganar cikin jimami da tausayin kai yasa Hajiya tayi dariya"Julaibibi kana dani amma katsaya fatarar katin waya?To bari yanzu za kaji alert..Yauwa Hajiya ta nagode miki ba kad'an ba Ubangiji yak'ara girma.Amin Julaibibi. Hajiya ina cikin damuwa,na ka sa samun natsuwa.Ashsha me yake damun ka Julaibibi?Tun ranar dakika fad'amin kin samo min matar aure,Dan ALLAH Hajiya ba wai butulci zan yi da za6in ki ba,dan na san baza kimin za6en tumun dare ba,to amma alfarma d'aya nake nema kifad'amin wacece ita?Taja tsaki"na d'auka wata lalura ce ke damun ka?To yar gidan Kawun kace.Wane Kawun nawa?A ah to kuma nan d'aya ni dai nafad'a maka sai ta k'ara girma,yo data isa aure tare za a had'a dana su Sudaida ta k'arasa karatun a gidan ka.Yar karama ce kenan,ajin ta nawa?A ji d'aya take a ka'aramar Secondary idan kuma kana so ayi bikin ta girma a d'akinta to,kayi rainon ta yadda kake so.Yayi shiru kamar baiji abinda tafad'a.Hajiya tayi dariya"Julaibibi na to sai anjima ta katse wayar.Yahura iskar bakin shi bayan ya maida wayar shi aljihu,yayi tsai...cikin tunani Kawun nan na shi ai suna da yawa,kuma kowanne yana da tarin ya'ya mata,yayi iya tunanin shi amma bai canko ko wacece ba, yarik'e kugu yana bin d'akin na shi da kallo...
Sinan yana tsaye da mahaifin shi yana ba shi sak'on wasu kayayyaki da zai siyo mishi a Kaduna,Zigwai tak'araso wajan,tana sanye da matsatstsun riga da buje na material ruwan d'orawa an mishi d'inkin rashin mutunci da rashin sanin kimar kai,tantirancinta ya bayyana, tana rataye da bakar jaka,takalmanta masu rufi da tsinin diddige bak'ak'e"Sannu Alhaji tad'an rusuna tana gaishe da mahaifin shi,wani abu yadaki zuciyar Sinan, yad'auke kai daga kallan k'urullan da take mishi.Alhaji yakalle shi sai ya sunkwui da kai.Zigwai tayi wata yar dariya irin ta yan duniya"Malam Sinan angon Sudaida.Yad'ago yana murmushin yak'e,sai ta mik'a mishi envelop "sak'o nakawo maka.Yak'ar6a yana mata kallan tuhuma.
Tajuya tayi tafiyarta tana murmushi"za ka gane da gero ake koko, Sinan ai sai dai muyi biyu babu. Suka kalli juna shi da mahaifinshi "yadafa kafad'arshi,Sinan ba girma a ganka kana mu'amala da irin wad'annan k'adangarun barikin, ka san shaid'an baya raina k'ofa.Yagyad'a kai "Baba baka yadda dani bane?Sinan ba rashin yadda ce tasa na fad'a maka haka ba,illah gyara kayan ka...ai kai ba k'aramin yaro bane,sai dai tunatarwa tana amfanar da mumini,ai mun ba ka tarbiyya gwargwadon iyawarmu,idan kaje kayi wani abu sa6anin wanda muka d'oraka a kai,to ai ALLAH yana ji yana kuma gani wannan tsakanin ka dashi ne,bazai kama mu da sakaci ba,ni dai idan za kayi sara to kadinga duba bakin gatarin ka, kasan da irin mutanan da za ka dinga mu'amala, ina jiye maka kaidin irin wad'annan da suke ji kamar su juwo mutum ta k'arfin tsiya ya dilmiya. Jikin shi yayi sanyi,yayi nadamar abinda yafara "nagode Baba.Alhaji Kamal yashige motar shi yatafi. Yazauna a wajan cikin damuwa"to wai ma me yakai shi k'ulla mu'amala da Zigwai?
Sun gama jarabawa anyi speech and prize giving day anyi angama lafiya,kowa ya koma gida zaman jiran sakamakon girbe abinda aka shuka.Maganar biki ya dad'a kankama anata shirye-shirye,amare ana shan gyara Umma ce a wannan harkar dan kunsan ita bata d'aukar raini kona sisin kwabo ko ba dan ALLAH ba kowa sai ya bi.
Jajibarin auren su Sinan kai ya d'auki zafi baya samun zama,yana sa takalmi Tibishi yashigo yana kallan shi"maganar birthday party na Zigwai zan tuna maka fa.Yakalle shi rai a 6ace"Tibishi karabu dani,dan ba wannan ne a gabana ba.Yajijjiga kai"nima na sani to amma karka manta alk'awari kad'auka.Yagama sa takalmi yamik'e "Tibishi ta shi katafi akwai inda za ni,suka fito Sinan yakulle d'aki kowa yayi hanyar shi.
Bai dawo ba sai kwanciyar bacci a na ta dad'a gyara gidan amarya,sai da ya tabbatar kome ya kammala sannan hankalin shi ya kwanta, sai lokacin yasamu damar kiran Sudaida.Tana ganin kiran shi tad'an harari wayar tana k'unk'uni, sai da yakira sau uku sannan tad'aga"Sudaida sarauniyata...tatari numfashin shi"ni ba wata sarauniyar ka tunda tun safe baka nemi ni ba,na kira ka na jita a kashe,ni fa kana 6ata min rai. Wayyo ni Sinan to kiyi hak'uri ina can ina hidimta ma muhalllin kine,amma ko ina naje to tabbaci hak'ik'a kina cikin zuciya ta, ina son ki Sudaida... Tace hum...yacigaba'irin soyayyar da baza ta fad'uba,yayi yar dariya ALLAH dai yakai damo ga harawa ko baici ba yayi burgima,gobe war haka kin zama sarauniyar Sinan ta hak'ik'a,farin cikina zai fara daga gobe ne...yayita maganganun shi batace kome,basu wani dad'e yamata sallama dan zai kwanta ya gaji lik'is.
Farar rana me kyakkyawar suna, wato juma'a.Yan'uwa da abokan arziki cike da gidajan biki an karkasa ayyukan shi yasa nan da nan akayi aka gama.K'arfe sha biyu da rabi Julaibib yasamu isowa garin.Yashiga D'akin-shak'atawar Inna ana gaisawa.Yaya Karima takalle shi"ai na d'auka baza kazo ba.Yad'an shafa kwantaccen bak'in gashin kanshi"Yaya Karima yanayin karatun ne sai a hankali.
To ALLAH yataimaka.Amin.Yawuce d'akin shi dan shirin masallaci.Yana sanye da babbar riga,'yar ciki da wando na farar shadda getzner,hular shi k'ube da aikin babbar rigar shi ruwan toka da ratsin fari da bak'i, takalmishi sau ciki fari,agogo da zoben shi na farin azurfa sai d'aukar idanu sukeyi saboda hasken su, k'amshin arabian perfume d'inshi me dad'in shaka,ya cika wajan.Duk suka bishi da kallo.Yaya Karima tace "gaskiya autan Inna kayi sharrr...dakai kamar wani ango,Yayi murmushi kawai"kice ma Inna na tafi masallaci.
Yau gaba d'aya hud'ubar akan aure da ma'aurata akayi,bayan an idar da sallah anyi addu'o'i an shafa,auran Hashim da Aisha aka fara daurawa,sai Muhammad da Zainab,Abdullahi da Maryam,Abdulkarim da Nasmat,Huzaifa da Khausar...sai na Sinan da Sudaida da ake shirin d'aurawa,to amma wani wawan burki da aka taka sai da yatshi hankali jama'a,wasu suka fito daga masallacin dan ganin abinda yake faruwa.
Sinan ne yafito daga cikin motar yana sambatu da tam6elen mashayar...Su...Sud... Sudai...damata...ta..taceba...wanda...zai...raba ni da ita... alk'...wari...ba karyawa mutu ka raba takal...min kaza. Ciki da wajan masallaci kowa yayi d'ifff...ya cika da mad'aukakin mamaki na ganin Sinan a wannan yanayin, a hankali k'ananan surutai yafara ta shi.
Alhaji Kamal sai da numfashin shi yad'auke na wucin gadi yayi mutuwar zaune,dan abun ya kad'a shi"Innalillahi Wa'inna Ilaihi raji'un yake maimaitawa, Liman yakalle shi"dama ka san d'an ka yana shan giya? Yakad'a kai cikin damuwa "Liman bazan maka k'arya ba wallahil-azim ban sani ba,ban san kome game da Sinan ba sai halaye masu kyau.
Sinan d'in aka fitar daga masallacin dan yafara kakarin amai.Liman yakalli mahaifin Sudaida meye abin yi? Kafin yayi magana Alhaji Kamal ya amsa"ba za a d'aura ma Sudaida d'an giya ba,irin wannnan hukuncin zan zartar ko 'ya tace wallahi,dan haka ina rok'on alfarma a d'aura auran nan da k'anin Sinan,yanuna Hamidan dake zaune a gefen shi cikin 6acin ran abinda Sinan yayi.Liman yabi sauran jama'ar da kallo,yasauke numfashi"k'warai zan so haka,to amma wani hanzari ba gudu ba idan aka had'asu aure Sinan bazai barsu suyi zaman lafiya ba, zumuncin dake tsakanin su na shak'ik'an juna zai samu tasgaro, indai ba tsananin sa a a kaci Sinan d'in me hange nesa da maida al'amura ga ALLAH bane.Alhaji Kamalu kayi hak'uri,ni na san da wanda zan had'a auran nan yanzu da izinin ALLAH gida bai k'oshi ba ai baza a ba dawaba. Yaciro dubu ashirin d'in da kaba bashi zakkarsu dazai taho masallaci "yanzun nan zan d'aura auran Julaibib da Sudaida akan sadaki naira dubu ashirin lak'anan(lakadan) Masallaci yad'auki kabbara.
Alhaji Kamalu mutumin kirki me karamci shi yakar6ama Julaibib auran Sudaida, dubban nin jama'a sun shaida wannan aure. Hamidan yasauke numfashi,sai yanzu yashak'i iskar yanci dayaji ba dashi aka d'aura ba, yama Julaibib da Sudaida fatan alheri da sauran angwaye da amaren,yamik'e yayi tafiyar shi yana rok'ama Sinan shiriya...ALLAH kenan buwayi gagara misali,namiji baya auran macen da ba ta shiba,hakama mace bata auran mijin da bana ta ba...al'amarin aure,al'amarine daga Indallahi,shi yake had'awa sai dai wani yazama silar faruwar shi.
Baban Abdul dake gefen shi yayi murmushi"ango ka sha k'amshi,aure d'an lokaci ne,idan lokaci yayi ko ba a shirya ba haka dole za ayi...ka tuno hirar mu ta kwanaki?Wannan gaskiya ne shirye-shiryen a yi daga baya,yamik'a mishi hannu sukayi musafaha suna murmushi, wallahi shima haka yake ganin abun kamar almara,har suka fito yan'uwa da abokan arziki sun baibaye shi suna taya shi murna da fatan alheri"Dare ga mai rabo...hantsi.Sunan wani littafi na gwanarmu (Halima Abdullahi Amma)Ubangiji ya kyautata makwanci👏
D'ansarai...yaji an kira shi.Yad'ago kai bakin shi d'auke da addu'ar"Alhamdulillahil-lazi bi ni'ima tihi ta tummussalihat"jin an daki kafad'arshi.Aminu ne yazare mishi idanu"toh daga yau sai yau na zama surukin ka,dan haka ba sauran raini,idan ba haka ba in k'wace k'anwata ka gane ko?Kome girma-girma kamar tusar jaki. Julaibib yamishi wani kallo "ai aikin gama ya gama,wuk'a da nama yanzu a hannu na suke da dai kafin a d'aura ne to danaji kurarin ka,nagaba yayi gaba Alhaji...Su Musaddiq suka yi dariya.
Yara kowa yafara noman kare(gudu) dan yaje kai rahoto kuma kowa so yakeyi ace shine na farko, tun daga zaure Abdul yake k'walama Inna kira iya k'arfin shi har yashiga tsakar gidan,duk suna tsaye cirko-cirko cikin tararrabin abinda Abdul din zai shigo dashi na tashin hankali"lafiya kuwa Abdul?Sai numfarfashin gudun dayasha yake yi,yana haki da dariya yace"Inna Kawu D'ansarai aka d'aura ma aure. Asma'u dake tsaye kusa dashi batayi k'asa a gwuiwaba ta d'auke shi da wani bahagon mari,ji da ganin shi sai da ya d'auke na wucin gadi"wato wasan da takeyi da kai har yakai haka? Ka dinga mata kiran yan farauta tun daga waje duk ka tashi hankalin mu sannan kashigo mana da maganar banza"wa D'ansarai ya aura?K'anwar ubanka? Yadafe wajen dan ya maru idanun shi suka kawo ruwa,ya kasa magana sai kawai yajuya zai fita. Inna tarik'o rigar shi "Zo mana Abdul d'ina mai gida ran gida,me gida takobi...tayi furucin da sigar rarrashi,tasa hannu tashare mishi hawayen da suke zubo sharrr..."fad'amin gaskiya Abdul,me yafaru a masallaci... bata gama rufe baki ba sai ga Adnan yashigo da sallama,suka bishi da kallo, yaja kujera yazauna.Cikin jimami yafad'a musu kome. Masu murna na yi masu komawa gefe suna k'unk'uni na yi.Asma'u tajuya zata ba Abdul hak'uri taga ya fita.
Asma'u tana jin abinda Sagir ya gama fad'a takai goshinta k'asa cikin sujudush-shukuri "yanzu ne za suyi rawar gaban hantsi ita da Alk'asim,tad'auki jakar da Sudaida tace tashiga d'akin Yaya Aminu tad'auko takai mata gidan Hajiya.Tana dire jakar a k'asa tayi tsalle cikin ihun murna ta rungume Sudaida"albishirinku?Duk amaren da suka sha wanka da kwalliya suka bita da kallo.Ta lumshe idanun ta cikin jan numfashi "wai me yafi dad'ine an tambayi na d'aure? Saki...tayi lallausan murmushi sannan tabud'e idanun ta"toh an d'aure lafiya an kuma gama lafiya, sai dai an samu akasi Yaya Sudaida dai da autan Inna aka d'aura...
"Da Julaibib???
Suka had'a baki wajan tambayar ta cikin mad'aukakin mamaki.Nasmat ta san halin Asma'u ba mamaki tace da wasa take yi.A'isha ta d'aure fuska"ke Asma'u wacece sa ar wasanki a cikin mu?Tafara rantse-rantse gaskiya take fad'a...Daga tsakar gida suka fara jiyo tafa hannaye cikin sallallami.Nasmat talek'a Yaya Aminu ta hango suna masu Hajiya bayanin abinda yafara, a hankali tasaki labulan tana jijjiga kai"ga kai ga kafa ai ba tambayar me aka yanka.Maryam takada kai cikin damuwa "amma dai Sinan bai kyauta ba,ya 6ata rawar shi da tsalle.Zainab ta ta6e baki"wannan kuma ai can gasu gada kura ta ji kid'an farauta... kowacce ta tofa albarkacin bakinta.
Sheshshekan kukan Sudaida sukaji, gaba d'aya suka juya suna kallanta.Aisha tace kiyi hak'uri Sudaida ALLAH yaso ki da rahama yato na asirin shi,da an d'aura auran ne bayan kin zama matar shi fa? Ai ko za a raba auren ku a yadda yake son ki ai ba k'aramar tata6urza za ayi ba.
Takalli A'usha"wai da D'ansarai fa wannan me miskilancin tsiyan?Khausar tagalla mata harara sannan taja dogon tsaki"rainin hankalin ki yana da yawa wallahi.Su Aisha suka kyalkyale da dariya"duk miskilancin shi ai taku dashi ta zo d'aya,har hira fa kunayi.Takoma ta kwanta a ranta tana mita"maganar da sai ya ga dama yake yi.Aisha tasake kallanta"a shekarun baya dana fara k'orafi a kan halin shi kece fa me k'alubalantar kalamaina,bayani sosai kike min har nima daga baya nagane,tadafa kafad'arta haba ta D'ansarai ki daina asarar hawayen ki dan Julaibib mijin nuna ma sa a ne wallahi...tayi shiru kamar bataji me suke ta fad'a ba...tacigaba da zancen zuci"tabbass tana son Yaya Julaibib,to amma yanzu da fad'uwar tazo dai-dai da zama, kayan suka tsinke a gaban kaba sai ranta bai so ba. Tarintse idanu hawayen suka sake zubowa a kyakkyawar fuskar ta me d'auke da hasken amarci.Sinan baka kyauta ba, ka ci amanar k'auna, wato ranar da aka kira wayar shi a bai-bai yarufe ta,saboda sunan Zigwai suna sa ma maza suna sa ma mata,ashe kalaman Tibishi duk gugar zana ne,tadafe kanta daya fara barazanar ciwo,ai ko ba ta san Sinan to dad'ewar su tasa sun yi sabo na ban mamaki.
Biki sai yadad'a komawa gidan Inn,bayan sallar Isha'i kowace amarya aka sadata da d'akin miji gidan aure, aure yak'in mata inji hausawa...Su angwayan da tawagar abokan su,su suka yanke shawarar a fara raka Julaibib gidan shi.Aminu dake cikin tawagar abokai yarik'o hannun shi"dare fa na dad'a yi zo muje kama Innarmu sai da safe,dan ka san bazan lamunta kadinga share waje kana barin k'anwata a gida ba,yanuna shi da yatsa"sai fa ka kula da kyau idan ba haka ba har gidan zani in tasa k'eyarta zuwa gida.Julaibib yakai mishi naushi a kafad'a amma bai same shiba dan ya goce da sauri"kar ka 6alla min kafad'a kasa gobe in shiga uku,aikin billboards ne dani guda wajan takwas.To ni ai bata shafeni ba.Yagyad'a kai"gaskiya ne ba ka da asara ko na miyan bacci.
Inna tayi murmushin jin dad'i yau ALLAH ya nuna mata auran autan ta.Ta musu nasiha gaba d'ayan su sosai akan su zauna lafiya da matayan su.Alhaji Abdullahi shima ya d'ora"Ku kyautata musu Manzon ALLAH yace mafifici a cikin ku,mafifici a kyautatama Iyalin shi,ni na fiku kyautatama Iyalina,kuji tausayin su,kuyi hak'uri da dabi'unsu dan da k'ashin hak'ark'arin hagu aka halicce su.Yakalli Julaibib"Malam D'ansarai ai ka san ina yawan fad'a maka shi zaman aure gaba d'ayan shi hak'uri ne ko? Toh yau ka shiga daga ciki,yanzu za ka fara aiwatar da wannan nasihar a aikace,aure hak'uri ne,d'awainiyace me tarin yawa, shi yasa ake buk'atar juriya da jajircewa. Yarufe nasihar ta shi da wannan addu'ar ga wanda yayi sabon aure...
"Barakallahu lakum,wabaraka alaikum, wajama'a bayyana kuma fi khair.
Duk suka had'a baki wajan amsawa da amin,amin,amin.
Inna da Baba suka bisu da kallo bayan sunma juna sai da safe suna fita d'aya bayan d'aya daga D'akin shak'atawar,kowanne yayi sharrr... dashi cikin farar shadda.
Garin yayi tarwai da hasken farin wata, sassayar iska tana kad'awa a cikin daren,ga k'amshin furen filawar sarauniyar dare(Queen of the night) d'in k'ofar gidan yamamaye ilahirin ciki da wajen gidan. D'akin- shak'atawar a gyare yake, sai dai yau gyaran na musamman ne,k'amshin amarci ya cika ko ina.Suka zazzauna,aka d'an ta6a hira kamar yadda akan yi idan an rako ango sannan suka mik'e.Aminu yad'an daga murya "toh amarya mukwana lafiya, mun sai bakin ki akan kud'i masu tarin yawa,mun kuma damk'asu a hannun angon ki, dan haka yana shigowa mik'a hannu yaba ki yan kud'ad'enki,idan kuma kinci girma kin bar mishi to kinyi mafi kyawun karamci, duk ke d'in ce dai za ki amfana...Huzaifa yature shi"saboda ALLAH meye haka?Yad'aga mishi hannu"muje na ka gidan kaji abinda zan fad'a ma ta ka amaryar, suka fita suna mishi mita.
Julaibib yarakasu k'ofar gida yadawo bayan ya kulle ko ina.Yarike k'ugu a tsakiyar D'akin shak'atawar cikin karatun wasikar jaki na wucewar wasu dak'ik'u,yasauke numfashi sannan yasa hannu yad'auki ledar da Musaddiq yaba shi yanufi d'akin da sallama.Yashak'i wani k'amshin turarenta dana turaren d'akin,k'amshin ne me sanyin dad'i,ya lumshe idanu yana dad'a shak'ar k'amshin cikin jan numfashi...
Oh Ya Salam...dausayin ni'imahhh...
A hankali yabud'e idanun shi yana bin d'akin da kallo,kome an tsara shi,ya zauna a muhallin shi,abun ya burge,ya k'ayatar duk da anyi shi a k'urarren lokaci,yau d"in nan fa.
Shauk'in k'aunar daya mamaye ilahirin gangar jiki da sararin zuciyar shi tun bayan d'aurin auren sai yadad'a ninkuwa sau shurin masak'i,yaja stool yazauna yana k'are mata kallo tun daga k'afafunta da suka sha jan lalle da yarfin baki,har zuwa polish lace d'in data sa,zani da riga ruwan k'waiduwar kwai(beig)da mayafi ruwan kwai me shara-shara,k'ananan sabon kitson ta yar-yar-yar yadad'a fito da kyan fuskar ta,hannayen ta suma sunsha jan lalle da yarfin baki,d'an kunne, sark'a,zobe da siraran warawaranta na zinare sai d'aukar idanu sukeyi,ga kuma hasken amarci, yana kallan fuskar ta kome ya tarwatse mishi,murna ta koma ciki,saboda damuwa da tashin hankali dasu ke tattare da ita ruwan hawaye ne suka ta sinsitiri a kyakkyawar fuskar me d'auke da hasken amarci, yahad'e hannayen shi yad'ora ha6arshi akai"kar dai tsugune bata k'are ba...an sai da kare an sai biri?ALLAH dai yasa ba shi kad'ai yake kid'a da rawar shi ba!
'Sudaida..Yakira sunan ta cikin natsuwa.
Tayi shiru...sai yayi k'asa da murya "Sudaida ban san damuwar kiba,amma ina so ki sani daga yau,yanzu d'innan duk wata damuwa dakike ji da ita,to nima zanji kwatan-kwacinta,kiyi hak'uri ki bani goyon baya dan in samu k'warin gwuiwar faran ta miki,akowani irin hali da yanayi.Toh me zata cene?Wallahi wani iri take ganin shi, kamar wani bak'o,nauyin shi take ji,ga kuma kewa da rabuwa da gida dasu Nasmat da akayi shekara da shekaru ana gwagwarmayar rayuwa da makaranta, musamman Khausar da kullum suke kwana daki d'aya, gadon bacci ne kowacce da na ta,amma har wardrobe d'in su d'aya,suyi fad'a su shirya,toh wai yau kowa a wani muhalli na daban zai kwana,ga Aisha da ta musu nisa tana Kafanchan idan suna san ganin juna fuska da fuska to sai sunyi tafiyayyiya a mota, kewan kowa da kome yalull6eta sai kawai tasa kuka(Hummm Sudaida aure yak'in mata inji hausawa...toh yanzu kin shigo filin shukuwa... Sai ki had'iyi k'wayar hak'uri ki kora da ruwan jarumtaka da jajircewa dan aikin aikine wallahi"an ba kuturu tallan jakai)
Tun shigowar shi d'akin sai yanzu tacire tagumin datayi tad'an saci kallan shi,Bai cire kome nadaga shigar shi ba sai takalmi,k'afafun shi cikin safa.
Sudaida...
Yasake kiran ta"tashi muyi sallah...Tasunkwui da kai tafara shashshekan kuka. Tagirgiza kai"uh uh Sudaida yau fa ba ranar kuka bace,rana ce da za ki k'ara godema Ubangiji dan kin shigo gidan aure, auran nan kuma hanyace da zata sadaki da Darul-karamah..
Yad'auko Kofi yazuba madara yamik'a mata"kar6i kisha.Itafa ya dame ta,kad'aici take buk'ata wallahi,dan haka tace bata sha. Sudaida..Ta tari numfashin shi"Yaya Julaibib nifa gaskiya bazan iya zaman auren nan ba...tacigaba da kuka.
Yayi tsaiii...na wucewar wasu dak'ik'u yana kallanta"idan rai ya 6aci toh hankali yanemo shi,abinda yatuna kenan yamata uzuri dan shima yaji rad'ad'in rabuwa da Bilkisu fuj'atan. Yagyad'a kai"To naji, amma d'an daure muyi salla ko?Dak'yar tamik'e ita fa wani irin hali da yanayi ta tsinci kanta a ciki kamar almara. Bayan sun idar da sallar yayi wannan addu'ar ga wanda yayi sabon aure..
"Allahumma inni as'aluka khairaha wakhaira ma jabaltaha alaihi,wa'a'uzu bika min sharriha wa sharri ma jabaltaha alaihi"
Duk sukayi shiru na wucewar wasu dak'ik'u, a hankali yad'ago yana kallanta,sai yaciro wayar shi yasaita ta yana d'aukarta hotuna,tana d'ago kai caraf idanun shi yahad'u,tasunkwui da kai da sauri tana dad'a rufe fuskar ta da mayafin, bazato taji ya cire mayafin yarik'o ta yana d'aukarsu tare"Yaya D'an... sauran kalaman suka mak'ale saboda wannan rikitaccen kallannan na shi daya mata,ta turo baki gaba idanun ta sun cika da kwallah. Sai da yagaji dan kanshi yabari.
Hucin numfashin shi taji a gefen damanta,yayi k'asa da murya"ALLAH yabaki hak'urin zama dani...Yagewaye hannayen shi a jikinta"Kin gaji da yawa ya kamata kiyi wanka da ruwa me d'umi sai ki kwanta kiyi ishashshen bacci ko?Dak'yar tayi furucin"ni ba sai nayi wanka ba. Yagirgiza kai"uh uh sai kinyi wanka za ki kwanta... yasake ta"kije kiyi wanka,yajuya yafita.
Har tayi wanka takwanta sannan ya shigo tana kwance irin kwanciyar mage.Har kin kwanta"uhhh tace.Yaja stool yazauna yana kallanta"gobe fa sammako zanyi in koma makaranta kilama baki tashi daga bacci ba.Sai taji ranta ba dad'i.Tayi shiru kawai...ko za ki bini mutafi tare?Tad'an dago suka kalli juna"yad'age gira yana mata wani kallo"in shirya miki kayanki yanzu?Tawani marairaice tana zancen zuci"sai kawai aji tabi shi makaranta?Yayi yar dariya yana mik'ewa"kiyi baccin ki kinji,ni akwai nazarin da zanyi"Lailatun sa'ida...fi amanil-lah.Ya tafi D'akin- shak'atawa yana had'a wasu littafai da zai tafi dasu.
Sinan bai farka daga nannauyan baccin daya d'auke shi bayan ya gama aman giyar daya shaba sai cikin sulusin dare.Yafarka da wasu miyagun mafarkai daba su da tushe bare makama, yabi d'akin da kallo zuwa kayan jikinshi,yashiga rarraba idanu"me yakawo shi d'akin Hamidan kuma?K'wak'walwar shi tafara aika sak'onni zuwa bangaren tunanin shi"me yafaru dashi? Yaufa ranar d'aurin auren shine,rana ce ta musamman a gare su shi da sarauniyar ta shi,a kuma daren su nafarko cikin angwanci, yakad'a kai ai sam-sam baza ta sa6uba bindiga cikin ruwa, ruwa baya tsami banza,tar-tar yafara tuno abinda yafaru kafin gushewar hankalin shi.Dammm...Yaji rikitowar wani abu a k'ahon zuciyar shi,kafin kiftawar idanu yajik'e sharkaf da zufa kamar wanda yayi wanka da kayan jikin shi, da sauri ya sakko a gadon kamar zai hantsila yawuce D'akin-shak'atawa anan yaga Hamidan yana bacci a doguwar kujera,kuma d'akin wayammm ba kowa,ba kamar jiya da yan'uwa da abokan arziki suka cika ko ina ba.A rikice ya sunkuya dai-dai fuskar Hamidan yana kiran sunan shi,yasa hannu ya yarfe zufan dayake ta tsatstsafo mishi a goshi a karo na barkatai,yahadiye wani abu mezafi.
Hamidan yayi juyi sannan yabud'e idanu, dan a sama yaji kiran"tashi Hamidan ka zauna.Hamida yatashi yazauna yana kallan shi cikin 6acin rai,wallahi da shine babba sai ya zabga mishi barin makauniya dama da hagu,yakad'a kai"labarin zuciya a tambayi fuska sai kawai yajuya mishi keya.Cikin tashin hankali Sinan yace"dan ALLAH an d'aura aure na da Sudaida?
Yajuyo yamishi wani kallo"tabbasss an d'aura auren Sudaida amma da dan'uwanta D'ansarai dan Baba ma bai goyi bayan a d'aura mata aure da d'an giya ba,yanzu haka tana d'akin mijin ta...yatare shi cikin k'araji da tafasar zuciya"ya ishe ka! Yafad'a kujera yana Istirja'i k'urunk'usss...ta faru ta k'are an yima me dami d'aya sata. Idanun shi sun kad'a jawur Tibishi da Zigwai sun kai shi sun baro.
Yau bak'ar rana ce a gare shi me bak'in muni...yafara tuno abinda yafaru wayewar garin juma'a, a sanda hantsi yadubi ludayi yadawo daga ciro kud'i a ATM dazaiyi hidimar abun sha na walimar dare da za ayi bayan an kai amarya,yasa mukulli zai bud'e d'akin shi kenan sai ganin Zigwai yayi ta shigo gidan na su tak'aramar k'ofa, me gadi yana d'akin shi yana sallar walha,lallai idan ya barta Baba zai iya fitowa kowani lokaci,ga kuma bak'in yan biki,da sauri yazare mukullin daga jikin kofar yamayar aljihu,yaja hannunta da sauri suka bar gidan,suna fita yasaki hannun ta ya wanka mata mari san ya angijeta tayi baya tafad'i,yafara yarfa mata ruwan bala'i"dan abu kazan uban ki meye darin gamata da ke dahar za ki biyo ni gida? Ba mun gama ba,ba kare bin damo?Tawani marairaice"dan ALLAH angon Sudaida kayi hak'uri,ban san ranka zai 6aci irin haka ba, amma nima ai daga yau ba k'ari wankan wuta,na kira lambar ka sau shurin masak'i kaj'i d'agawa, kaga ai dole tasa, dan wajen Party yayi cikar farin d'ango amma ba special quest of honour,tacigaba da marairaita har tasamu fushin daya taso mishi yafara lafawa"dan ALLAH kazo muje ana gama yanka cake sai kadawo. Yagalla mata harara"baza niba ko dole ne?
Dasauri takai gwuiwoyinta k'asa tana mishi wani irin murmushi na yan duniya da jan hankali" haba Sinan dan darajar k'auna da soyayyar daka kema sarauniyar ta ka,yau d'aya dai karka watsa min k'asa a cikin idanu bayan na gama sakankan cewa,ai ka gani ko a jikin katin gayyata an buga kaine bak'o na musamman me girma.kuma na fad'a maka tuntuni ka kuma amince da haka,haba Sinan ai alkawari bai ce haka ba,da tun farko ka fad'amin baza kaje ba ai da na canja ka da wani,tamik'e cikin hawaye tana kallan shi"shine nan nagode...nagode tajuya tayi tafiyarta.
Yabita da kallo,sai yaji ran shi ba dad'i yasake kallan agogon dake d'aure a hannun shi,har yanzu k'arfe goman safiya bata k'arasa ba, bari kawai yaje tunda alk'awari yamata,zuwa goma da rabi sai yamata sallama yazo yak'arasa abinda zai yi kafin lokacin masallaci yayi. Da wannan tunanin yabita,yasha gabanta da mota yabud'e mota gidan gaba tashigo ta zauna"kiyi hakuri Zigwai.Tagirgiza kai"na hakura angon Sudaida,ALLAH zan so ganin ka anjima dan na aan wankan da za kayi zai bambanta da duk wani wanka da kata6a yi,yayi murmushi kawai.
Wajan party ya had'u da had'ad'd'un yan duniya hayak'in taba,dashi aka yanka cake,sai dai agurguje yake yin kome yana kuma yawan duba agogon dake d'aure a hannun shi dan kar lokaci ya shammace shi. Tabishi da kallo"wai wannan duba agogon na meye?Duba agogon me kuma?Sai ta share zancen"me zan kawo maka ne kad'an jik'a mak'oshi?Yaharareta.Tayi yar dariya "ka d'auka ba abinda zaka iya shane?Dan dai kak'i yadda ne amma bommi ba giya bane, ko a zuba maka d'an kad'an?Yagirgiza kai"a ah kusha abun ku,ni dai na san giya ne bommi,tunda idan mutum yasha yana gusar mishi da hankali.Tata6e baki "idan kai baka sha ba ai hausawa dayawa yan uwanka sun sha.Toh Ubangiji ya shirye su.
Taje tad'auko katan d'in lemun bakwai a raye(seven alive)ta6arke ledan a gaban shi tazaro d'aya, tabud'e murfin sannan ta d'auko kofi ta tsiyaya kusan rabin kofin sannan takalle shi"ko a cika maka kofin? Yamik'a hannu yakar6a "wannan d'in ma ya isa nagode, yana kai kofin tsakanin la66an shi tayi murmushin mugunta,ta dunk'ule hannu ta naushi iska"k'aramin arne ka had'u da gawurtacciyar arniya.Sinan sai dai muyi biyu babu,baza ka auri Sudaida ba nima ban aure kaba kowa yaji idan da dad'i.Tayi wata irin dariya irin ta yan duniya ganin ya shanye lemun duka "ALLAH yakai damo ga harawa...
Wucewar wasu yan dak'ik'u sai yafara gani garara-garara yanayin shi yana canjawa,d'aukacin jama'ar wajan yafara ganin su suna kasuwa kashi-kashi yana ganin Zigwai da Tibishi suna magana a gaban shi cikin dariya da tafa hannu amma bazaice ga abinda suke fad'a daga haka bai san abinda yakuma faruwa ba.Ashe maganin bacci da gusar da tunani,kuma wanda yawuce ka'ida(over dose) suka zuba acikin wannan lemun guda d'aya,sun kuma yi ma kwalin alamar dasu kad'ai za su gane.
A gida kuma Alhaji Kamal da Hamidan sun tun sha biyun rana suke neman Sinan amma ko sama ko k'asa basu ganshiba, hakama lambar wayar shi sun kira sau shurin masak'i na'ura me k'wak'kwalwa tana fad'a musu a kashe take,haka suka gaji sukayi shirin masallaci suka tafi.
Sinan sai da yayi bacin awanni biyu sannan suka tasheshi,har lokacin bai gama dawowa dai-dai ba,sai suka dura mishi giya nan fa yadad'a rikicewa.Wani abokin Tibishi yakalli Sinan"wannan ba yau za a d'aura mishi aure ba amma yazo nan yashare waje ko auran dole za a mishi? Dammm...zuciyar shi tabuga duk da yana cikin maye.Yata shi yana tangad'i da tam6ele yashiga mota.Yana tafe jama'a na kaucewa da ababan hawansu, yana kuma shan zagi da tsinuwa daga bakin wasu,saboda k'iris yarage yahad'a hatsari mummuna,a haka har ya isa masallacin juma'a wajan d'aurin auren...wasu zafafan hawaye suka zubo mishi"Zigwai tasa ya zubar da mutuncin shi dana gidan su abainan-nasi, kalaman Sudaida suka dawo mishi duk da k'anka'ntar shekarun ta amma tayi hagen nesan da san zuciya yahana shi hangowa...
Zama da madaukin kanwa...wai kai ba ka da wajan zamane sai acikin yan maro(wiwi)?...yatuno da maganar mahaifin shi na wancan makon"Sinan ba girma aganka kana mu'amala da wad'annan k'adangarun barikin... mun baka tarbiya gwargwadon iyawarmu... tunatarwa ce kawai...Yamik'e cikin tafasar zuciya "lallai yau za ayi ta tak'are me raba shi da Tibishi da Zigwai sai ALLAH Hamidan yakalle shi ganin yana bud'e kofa"Ina za ka a wannan daren Yaya? Ko kallan shi baiyiba yasa kai yafita.
Tana kwance hankali kwance iskar fanka tana kad'ata.Yadamk'o gashin dokin daya cika kanta tozon rak'umi guda.Zafi yaratsa ta tabud'e idanu cikin gigita,suka kalli juna,sai ta dad'a rikicewa.Yanemi abun duka bai samu ba dan haka yad'auki belt d'in daya gani a gefen gadon, yafara dukan ta ba ji ba gani sai da belt d'in yatsitstsinke amma duk da haka bai hak'ura ba,yafara tattaka sai da yaga ta daina motsi sannan yatsallaketa cikin jini yafita, amma har lokacin bai huce abinda suka mishi ba,wasu jijiyoyi sun fito a gefen kanshi kamar shatin bulala,ran maza ya 6aci iya 6aci.
Adaren yakoma neman Tibishi sai dai duk inda yasan zai ganshi yaje amma cikin rashin sa a bai ganshiba...tabbasss da aun had'u sai wani ya rasa ranshi ko kuma suyi mutuwar kasko.Yakama hanyar gida zuciyar shi a cunkushe, kaci6is sukayi da mahaifin shi da Hamidan za su tafi masallaci sallar asubahi. Sinan yasunkwui da kai ya ga 6acin ran da bai ta6a gani a fuskar mahaifin na suba"yanzu duk abin kunyar dakayi jiya hakan baisa ka kwana a gidaba? Yanuna shi dayatsa" anya Sinan,anya rayuwar gaba za tayi kyauvda albarka idan ba a tsaya an inganta rayuwar da ake ciki a yanzu ba? Anya Sinan kana tuna tsohon banza daga yaron banza yafara? Sinan yayi shiru a ranshi yana nadamar sanin Tibishi da Zigwai a rayuwarshi..Alhaji Kamal yakad'a kai"shikenan sai kaje ka shirya kafito masallaci, yakalleshi "kama rama sallolin jiya daka kwanta wannan baccin asaran?Tsoro yakama shi" shi Sinan yashiga ukun shi wallahi sai yanzu yatuna.Asanyaye yagirgiza kai"yanzu zan rama. Yakalli Hamidan"kaji,Ubangiji yashirye shi. Hamidan ya amsa da sauri amin Baba. Suka tafi masallaci kowanne ranshi ba dad'i.
Yana durk'ushe agaban mahaifiyar shi yana bata hak'urin abinda yafaru amma fau-fau tak'i sauraran shi, tanuna mishi k'ofa"ta shi kabani waje ganin ka yana k'ona min rai,Sinan ka bani kunya...tirrr da wannan halin na ka, albasa batayi halin ruwa ba wallahi. Yayi k'asa da murya "Mama bana shan giya,makirci kawai a ka kulla min...ta tare shi a zafafe" kai karka maidani sakarya,wa zai kulla maka makirci?Makirci da munafurci har yawuce wanda kadad'e kana aikatawa,ko kawai dan dubunka ta cika? Alhaji Kamal yashigo"haba Mamansu idan rai ya 6aci to bai kamata hankali yagusheba,d'an yau ne ka haifeshi baka haifi halin shiba.Takalleshi a rikice "yanzu kana goyon bayan shine,har kana ba shi lasisi?Tad'ora hannayenta aka"oh ni yar mutum biyu" na rantse da ALLAH Alhaji idan yaron nan bai tashi yafitaba to zan d'aga mishi nono...Tabud'e baki da niyar sake magana sai kalaman suka mak'ale saboda 6acin rai.Tasa hannu tashare hawayen daya zubo mata.
Sinan yasake shiga wani tashin hankalin gobarar gemu fiye dana d'azu"lallai ka shiga uku, rayuwarka tana cikin garari tunda har za kasa mahaifiyar ka zubar hawaye saboda mummunan laifin ka. Yanzu wa zai yadda dashi akan baya shan giya? Abu d'aya yasan yana sha a 6oye shine taba sigari,itama ba koda yaushe ba,wazai yadda dashi?Yadafa goshi"ko Alqur'ani d'ungurungum zai had'iye bashi da mafita. Nadama,haushi da bak'in ciki suka baibayeshi, kome yaji yafice mishi a rai.
Alhaji Kamal yadafa shi"tashi katafi d'akin ka.Gwiwa a sage yamik'e.Alhaji Kamal yakalli matar shi "abinda Sinan yayi tabbasss bai kyauta ba,kuma bana goyon bayan shi,to amma wani hanzari ba gudu ba, idan fa yatuba bai kuma aikata hakan ba har abadan duniya,to ALLAH me gafara ne,zai kar6i tuban shi ya yafe mishi tunda bamu yama laifi ba face mahaliccinmu gaba d'aya, dan haka karki tsananta,ke uwa ce addu'arki har kullum ita ake buk'ata, kullum addu'armu da fatanmu ace Ya'yanmu sunyi zarra fiye da duk wasu Ya'ya wajan natsuwa,sanin ya kamata, mutunci da tsantseni,to inga yanzu kin mishi baki? Bazai amfani kan shiba,bazai amfane muba,bazai amfanar da sauran al'umar manzon ALLAH ba,kin 6ata goma biyar bata samuba,baya ba zani kenan...
Yana rik'e da marik'in k'ofar d'akin shi kafin yamurd'a tabud'e jiri yayi awon gaba gaba dashi yifff...yasha k'asa.K:arar fad'uwar tashi megadi yaji.Yayi cikin gidan da sauri yana kiran Alhaji da Hamidan,sun yayyafa mishi ruwa amma shiru kamar an shuka dusa,dan haka suka wuce dashi asibiti.
Tsakanin d'a da uwa sai ALLAH, hankalin mahaifiyar tashi a tashe,takira Hamidan tana tambaya"ya jikin na shi?Yakalli roban k'arin ruwan da aka sa mishi a hankali yake d'iga a cikin siririyar robar yana shiga jijiyarshi zuwa cikin jikinshi"Mama ya samu bacci saboda allurar baccin da aka mishi,likita yace jininshi yayi mugun hawa.To Alhaji fa?Tasake tambayar shi cikin damuwa. Sun fita shi da likita.To Ubangiji yasa kaffarace nima anjima zan shigo. Yagyad'a kai"To Mama sai kin shigo a iso lafiya.Yauwa Hamidan ALLAH yamaka albarka.Amin Mama.
Tibishi yad'ora hannayen shi aka yana zare idanu"Holy ghost fire!...Inzayadami?(Me yafaru)Tafashe da kuka tana kad'a kai"ina katafi kabarni acikin wannan mawuyacin halin? Na neme ka a waya banji kaba.Yakoma yazauna"sha kuruminki Zigwai wayata nasiyar nayi kud'in mota zuwa Kafanchan kasuwar aladu, na kuma je da k'afar dama and'aukeni lodi mutanan k'asar China sunzo siya, lodin tirela hud'u mukayi,ba k'aramin kud'i nasamu ba,dan haka murabu da Sinan dan naga hak'armu baza ta tadda ruwaba.Me kake nufi? Yazuba mata idanu jikinta duk a farfashe yake"gaskiyar magana tunda Sinan yamiki irin wannan dukan kawo wuk'an to babu wata rana dazaki kuma mishi koda kun rage daga ke sai shi a doron duniya bazai kuma sauraran kiba.Tunda na samu abin yi kishare shi kawai,d'an iska yadaije amma ai munci gari,nima kwana biyu zan kiyayi zuwa cikin gari da duk inda nasan zai ganni,dan na san zai nemeni ruwa a jallo.
Takalleshi amma tunda bai auri Sudaida ba na san zai koma ruwa tsundum. Yamata wani kallon sauna"ke Sinan fa ba sin ki yakw yiba shishshigi da nacinki yasa kika samu kanshi,kuma koda kika samu kan shi ai ba wani d'ad'ashi da k'asa kikayiba,ak'arshe ma bazuwa yayi yaba ki hak'uri akan kuyi hannun rigaba? Yamik'e"nidai buri na ya cika,dama yarinyar ce bana so ta aure shi saboda girman kanta,kin san sannu wannan ta fatar baki bata ta6a cemin ba,duk da tasan nid'in abokin saurayin tane aibtasha ganin mu atare,idan nabari ya aureta to za ta rabamu tunda na san zaiji maganar ta dan yana son ta.
Zigwai takwanta"ai dai munyi biyu babu. Tibishi yakalle ta kisa ranki a inuwa,barinje kasuwa in miki siyayya,yana fita ta kyalkyale da dariya"haba Tibishi ai linzami ya fi k'arfin bakin kaza,kai ka had'ani da Sinan dan yazama saniyar tatsarmu,to mun tatseshi yadda yakamata, yanzu idanu na a bud'e suke ina ganin kowa garauuu ba ka da kud'in dazan aure ka,bari dai mucinye wanda kasamo,za ka nemeni ko sama ko k'asa karasa,garin zan bari dan yamin zafi saboda rashin Sinan, zan tafi wata jahar in bud'e sabuwar rayuwa da sababbin alhazan birni masu aljihu da kud'i ba irin kaba tsami ragowar burkutu giyar k'ok'o da hayakin maro da taba dayaci yacinye ka,sai na sai gida da mota,sannnan zan yi aure...toh maji magani an binne tsohuwa da ranta...
Haka ya yi an sai da gonar rago an sai mishi fura.
Farar dabara shiga rijiya da fura.
10 Jumaada Thani 1441
4 February 2020
We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs.
DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintinkau}
Bismillahi wabihi nasta'in
...GWAJIN DAFI💔
Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)
Shafi na goma sha tara.
Kwanaki biyu Sinan yayi a gadon asibiti yasamu sauk'i sai dai likita bai sallame shiba sai zuwa gobe.Yakar6i wayar Hamidan dan ta shi ko ta fad'i ko kuma su Tibishi sun sace ta,yadaddanna lambobin ta sannan ya d'ora lambar a kira.Tad'aga da sallama,wani abu yatsirga ilahirin jikinshi,ta kuma yin sallama jin ba ayi magana ba sai ta katse.Yacire wayar a kunnenshi yana jujjuya ta,idanun shi sun kad'a jawur,tabbasss kukan zuci yakeyi.Yaya Sinan ba a d'aga bane ko matsalar na'urar sadarwa?Yajuya yakalli Hamidan d'in,sai ya gyad'a kai"zan cigaba da gwadawa wata k'ila tashiga.Sai da ya danna kira sannan yace"Hamidan dan ALLAH kaje gida Mama tadama min kunun tamba.Yamik'e yana murmushi"a lallai yau jikin Alhamdulillahi,a had'o da abinci ko?Yagyad'a kai"amma me d'an ruwa-ruwa.
Yana fita yakai wayar kunnenshi,tad'aga da sallama.Yasauke numfash sannan ya amsa sallamar,yakira sunan ta Sudaida...Zuciyoyinsu suka buga,sukayi shiru na wucewar wasu dak'ik'u.Da rawar murya take fad'in"Sinan ya jikin?Ance kana kwance a gadon asibiti,Sinan me yasa kabiye ma son zuciya bayan ka san son zuciya 6acin ta...dama da gaske kura ce lull6e dafatar akuya?Sinan kai masoyina ne, wallahi ban ji dad'in abinda yafaru ba ko kad'an...ALLAH yashirye ka dana... yatari numfashin ta"na rantse miki da girman ALLAH bana shan giya"ba ka shan giya to ya akayi kasha? Ba fa a wasan kwaikwayo kafito ba.Yakad'a kai, matsalar kenan ba wanda zai gasgata shi"Sudaida na san na rasa ki,to amma duk da haka bazan barki cikin duhu ba,ranar wanka ba a 6oye cibi... yafara ba ta labarin had'uwarsu da Zigwai wanda shi kanshi yasha mamakin sauk'in halin ta,saboda irin wulak'ancin dayake mata,amma tashanye kullum bata fushi kwantar da kai take mishi na gasken-gaske da haka har taja ra'ayin shi yafad'a tark'onta.
Cikin kuka tace"ai na fad'a maka dabi'a tana na so,maganin kar ayi to tun farko kar a fara,dan shaid'an baya raina k'ofa.Sinan ina maka fatan alheri a rayuwa,dan ALLAH kacanja abokai da mutanan kirki.Nagode Sudaida,kema ina miki fatan alheri da samun natsuwa a gidan auren ki.Sudaida sarauniyar Julaibib.Yagoge lambar ta daga cikin wayar sannan ya ajiye,yana jin ranshi ba dad'i sunyi sabo na ban mamaki da Sudaida tun tana yar k'aramar yarinya...Lallai sabo turken wawa.
Julaibib daya jingina da k'ofar D'akin-shak'atawar yak'arasa shiga yazauna,ganin shi baisa ta daina kukan ba.Yakalleta cikin kulawa"kukan na menene Sudaida?Ai k'addara ta riga fata"rayuwar mu ba a hannu take ba,ALLAH ne yake tafiyar mana da ita,ta duk yadda ya so,shiyasa so ba samu bane,haka kuma samu ba so bane a wasu lokutan;yasa hannayen shi yagewayeta yana mata wani salo a hankali,yana kuma fad'a mata wasu kalamai sai ga shi tasa hannu ta share hawayen ta kuma yi shiru,tana k'ar6an sak'onnin dayake bata a ilahirin gangar jiki da sararin zuciya,wucewar wasu dak'ik'u sannan yad'ago fuskar ta suka kalli juna tayi saurin kauda kai"idan kunne na sun jiyo min dai-dai a cikin kalamanki naji kince shaid'an baya raina k'ofa ko? Ba baka sai kunne...jikin ta ya mutu murusss kai kawai tagyad'a.Yamik'a mata hannun damar shi "bani wayar ki.Tasa mishi a tafin hannun,yasa ta aljihu...
Sudaida...Yakira tatad'ago tad'an kalleshi. Kin san me yasa nakar6i wayarki?Uh uh.Yasauke numfashi"to na kar6i wayar ki saboda ba na so wata mu'amala tacigaba da kasancewa a tsakanin ku,yanzu ke matar aure ce,shi kuma wani k'ato ne daba muharraminki ba,ba dangin Iya bare na Baba;shi kuma shaid'an baya raina k'ofa.Yabata wata sabuwa galleliyar waya da layi sabo a ciki.Tasa hannu biyu ta kar6a"Yaya Julaibib nagode da da tunatarwanka.
Bayan sallar isha'i yashigo"Ina amaryar? Ta shaida muryar ko da acikin magagin bacci take, tafito sanye da hijab d'in data idar da sallah "sannun ku da zuwa...Yayi murmushi"yauwa amarya sha gud'a.Ya ba ta kunya ba kad'an ba,ta kuma ji abun banbarak'wai namiji da suna kande, wai Yaya Musaddiq da tsokanar ta,dama shi da Yaya Adnan sam ba shak'uwa a tsakanin su, wannan sauk'in halin sai Yaya Aminu.
Cikin girmamawa ta gaishe shi tare da tambayar ya Yaya Safiyya?Yagyara zama"ai itace ma ta ai ko ni,wai tana gaishe ki,kin san yanayin na ta,tafiyar wahala take mata amma dai za ta k'ok'arta tazo.
Taje takawo musu abinci Musaddiq yamik'e"a ah wallahi kuci kayan ku.Julaibib yazuba mishi idanu saboda me? Yad'an daki kafad'ar shi"ni kuma nawa da yake jirana a gida inyi Yaya dashi?Yamik'a mishi hannu sukayi musafaha.Suna tsaye a bakin k'ofa sukayi k'us-k'us d'insu sukayi dariya suka tafa.Tabisu da kallo"maza ma sun iya tsegumi?Tayi yar dariya wai itace ba su so taji kenan"Yaya Musaddiq mukwana lafiya.To Sudaida ALLAH yatashe mu lafiya.
Tana kwance cikin damuwa saboda fad'an da Julaibib yarufe ta dashi kamar zai ba ta na jaki,sannan ya hanata tofa albarkacin bakin ta, na ganin da yama k'anwar Sinan a gidan; kila zaton shi Sinan ne ya aiko ta tunda zai kira lambarta yajita a kashe,ita kuma Maman suce tabata turaran wuta da su humra kala-kala takawo mata,dama ta siya ta ajiye idan tazo gidan saita ba ta toh kuma ga yadda al'mura suka kasance.
Yanuna ta da yatsa idanun shi sun kad'a jawur"idan na kuma ganin wata ko wani a cikin gidan nan daya danganci Sinan na rantse miki da ALLAH abinda zan miki har ki mutu baza ki manta shi ba...Idanun ta suka ciko da kwallah Yaya D'ans...ke! nace ki rufe min baki ko?Yayi d'as d'as d'as da yan yatsun shi"baki sanni bane,yaja dogon tsaki yawuce d'akin shi.
Tasauke numfashi da ajiyar zuciya,tasa hannu tana share hawaye,tabi k'ofar da ake k'wank'wasawa da wani malalacin kallo,ta maida kanta jikin matashi tana dad'a gyara kwanciya.Aka cigaba da k'wank'wasa k'ofar,dole tamik'e cikin fushi tana jan tsaki a ranta tana mita"na ci dambun kuturu.Tasa hannu tabud'e k'ofar caraf idanun su yahad'u,ta gallama Sudaida harara. Sudaida tayi kamar ba ta gani ba,tayi d'an tsallen murna fuskar ta cike da d'okin ganin ta tafad'a jikinta"oyoyo Hajiyarmu sannu da zuwa...suka shige D'akin-shak'atawar,Hajiya ta ture ta"ke gafara can karki 6alla ni,tazauna a k'asa tana dafe k'afafu da alama ciwon k'afar yana son motsawa.
Da sauri Sudaida tad'auko man zafi ta d'urk'usa a gabanta tana murza mata a k'afafun tana maimaita"sannu da zuwa Hajiyar mu gaskiyar magana naji dad'in ganinki ba kad'an ba. Hajiya tasake galla mata harara"amma shine kika barni a waje ina ta k'wank'wasa k'ofa?Tayi yar dariya"kai Hajiya gidan amarya fa kikazo ni k'wank'wasa k'ofar kine ma yatashe ni daga bacci.Hajiya takalli agogon bangon dake d'akin sha d'aya saura minti goma na safiya"Toh ALLAH ko yasauwak'e da wannan baccin asaran. Tagirgiza kai"ba amin ba,ai lokacin abu ayi shi, amarci ai ba k'arya bane,ba kuma abinda ba ya sawa.Hajiya tazuba mata idanu cikin kallan nazari"amarcin ne yadad'a k'arar dake kamar bushashshen takand'a?Ke ko cikar d'akin bakiyi ba.Takai hannu tashafa wuyanta"sharri dai ba kyau Hajiya ni ba bushewar danayi wallahi,toh so kike kiga na zama ta shi da nishi?Tamata dak'uwa"kar6i nan aiko Iyayan ki na fi k'arfin in musu sharri bare ke karankad'a miya.Tad'an turo baki gaba"ai baza ki musu sharri ba tunda Ya'yan kine kina son su,nice dai ba kyau so.Hajiya takad'a kai kawai.
Ina Julaibibi ne rabona dashi tun shekaran jiya da daddare.Haushin shi yamamayi zuciyarta,to amma Hajiya babbace ko yaya tanuna wani yanayi za ta iya gano ta bare kuma yadda ta tsare ta da idanu.Tamik'e tana rufe man zafin"ke Hajiya ai yanzu ba da bane dazai dinga zuwa gidan ki yana share waje,ni kuma dawa zai barni? Hajiya ta tafa hannaye tana sallallami"ba shakka rasa kunya 6aren tanka...lallai wuyan ki ya isa yanka.
Sudaida tawuce tana dariya,ta kwana biyu bata shiga d'akin ba,k'amshin arabi'an perfume da k'amshin turaren d'aki ya gauraye sai yaba da wani irin nau'in k'amshi me sanyin dad'i wajen shak'a,carpet d'in d'akin kore da ratsin ruwan madara dawasu kyalli-kyalli masu d'aukar idanu,hakama labulayen d'akin ruwan madara da ratsin filawar rose yan shara-shara,sassayar iskar da take shigowa d'akin ta tagogin da suke a bud'e suna kad'a labulayen suna rangaji saboda rashin nauyin su,ya canja gadon daga inda tasani zuwa d'aya bangaren, wardrobe ma yacanja daga zuwa bangaren yamma,shoe-rack(ma'ajiyar takalma) cike tam da takalma mafi yawansu farare ne,kuma masu rufi(sau ciki)
Yad'ago yana mata wannan rikitaccen kallan nashi da yake ba ta haushi,yamaida kanshi ga tarin littafan daya barbaza a saman tebur,yana kuma yin rubutu a na'ura me k'wak'walwa da alama wasu abubuwan yake shigarwa"lafiya za kizo ki tsaya min akai bayan kingani ganin idanun ki aiki nakeyi.Wulak'ancin D'an Sarai har yakai haka?Ta tambayi kanta,zuciyar ta tayi rauni idanun ta suka kawo ruwa amma bata bari hawayen sun zubo ba,ta kad'a kai"ba kome dama saboda ka ma ake cin k'asa,tasaki marik'in k'ofar"Hajiya ce take magana.Suna had'a idanu yagalla mata harara "dama ai duk wanda kika ga ya ci kaza to shine da ita.Tayi kamar bataji abinda yafad'a ba.
Yasauke numfashi zuciyar shi ba dad'i ganin damuwar data shiga,ko kukan d'azu datasha kuka har tak'oshi yaji ba dad'i,to amma dole yayima tufkar hanci,kar garin kallon ruwa k'wad'o yamishi k'afa,ita da Sinan ai sun so juna, yau da gobe kuma bata bar kome ba,shaid'an baya raina k'ofa, dama ba abinda yake so sama da 6ata tsakanin ma'aurata,toh dole sai ya toshe duk wata kafa da yasan alak'a zata had'ata da Sinan dan yatserar dasu da auransu daga fad'awa halaka.Wani lallausan murmushi yasu6uce mishi "humm Sudaida za tafahimce shi,shi masoyin tane da babu kamar shi a doron duniya,shi da ita mutu karaba takalmin kaza,har lokacin da gangar jiki zai daina numfashi, rai yatafiii...
Yazauna suka gaisa da Hajiya.Tanuna shi da yatsa"kai Julaibibi kazama jarumi dan a haka nasan ka, karka biye ma wannan malalaciyar matar taka tamaida kai rago, ace kazauna kana sharar bacci har hantsi yadubi ludayi?Yashafa kwantaccen bak'in gashin kanshi yana d'an murmushi"Hajiya wane ni da wannan aikin;ai sai manya gatan wasa,amarya sha gud'a suka kalli juna shi da Sudaida tad'an harareshi tana turo ba ki gaba.
Wasu muhimman bayanai nake ta shigarwa ashafin mu na yanar gizo.Tagyad'a kai "Toh Ubangiji yayi jagora.Sunata hira da Hajiya cikin jin dad'i a wanta d'aya a gidan sannan takalle su"to ai na gaishe ku,barin tashi inje gidan Musaddiq jiya Safiyya bataji dad'i ba,wannan girman ciki ko yan hud'une a ciki iya ka kenan, ALLAH dai yaraba lafiya,suka amsa da amin. Julaibib yafita k'ofar gida inda ake sallama dashi.
Hajiya takalleta cikin natsuwa"wato kink'i tsayawa ki kwantar da hankalinki ki rungumi kaddarar Ubangiji ko?Tasunkwui da kai.Hajiya tacigaba shi aure dakike ganin shi ai ALLAH ne yake had'a shi ba mutum d'an Adam ba;ko shi Sinan ai ya dangana dan yazo har gida ya fed'emin biri har bindi, ban kuma kullace shi ba,na san shi mutumin kirkine,sharrin shaid'an dana zuciya ne suka rud'e shi,tanuna ta da yatsa"tun wuri ki saki ranki ki rungumi auren ki dan shine gatan ki na d'iya mace,ga sauran yan'uwanki can kowacce tayi sharrr gwanin ban sha'awa da kyan gani,ke kuma kinanan jiya i yau,ke da Julaibibi ai kun zama k'arfe da mayen k'arfe.Tayi shiru kawai a ranta tana mita"ai Yaya D'ansarai yakamata ajama kunne tunda shine baya son ta,auren dole aka mishi a tunanin ta"rashin sani karen gwauro yakori bazawara.Sukayi sallama tad'an ta ka mata zuwa harabar gidan.Tare suka koma ciki da Julaibib..Ke Sudaida zo nan...tayi kunnen uwar shegu tashige wanka.Yakad'a kai yana yar dariya"Sudaida k'uruci dangin hauka...
A sanda hantsi yadubi ludayi na safiyar talata,tana had'a lemun abarba da kashu ta toshe kunnuwanta da earphone,tana sanye da riga da zani na atamfa ruwan makuba da ratsin filawoyi manya da k'anana masu ruwan hoda da baki tayi wani irin d'auri na burgewa gashin kanta ta tubke shi da k'aton ribbon ruwan makuba,ta juya za ta d'auki siga caraf idanun su yahad'u, yana tsaye a k'ofa yanad'e hannayen shi a kirji,tad'auke kai cikin basarwa kamar bata ganshi ba,dan har yanzu a wuya take dashi, ba Yaya Julaibib d'in da tasani a da to yanzu ba shi bane,gaba d'aya ya canja Hali,d'azu-d'azu yagama yarfa mata ruwan bala'i wai yaran Kawun su yazo,ita kuma ta manta bata sa hijab ba tazauna suna shan hira da dariya.
Tagama aikinta tazo za ta wuce yatare hanyar yana kallanta cikin natsuwa kamar wani abu bai faruba,ko da yake shi tsakani da ALLAH yamata nasiha irin haka bai dace ba dan kayan sun kamata kome na ta ya bayyana,itace dai ta maida cibi yazama k'ari.Na yi sallama baki amsaba,na tambayeki abinci na nan ma kinyi shiru lafiya kuwa?Taturo baki gaba"shiruma amsace. Sudaida ba magana nake miki ba? Nan ma tayi shiru.Me yasa kike jamin zarene kin san halina fa. Tamishi wani kallo me kama da harara,cikin fushi tace"to sai me?Me tsoron ta mutu ai shi yake maho.Yayi jimmm...Yana cigaba da kallanta cikin nazari,wucewar wasu dak'ik'u sai yajuya...tabi bayan shi da harara"ALLAH raka ta ki gona...Yaja yatsaya zai juyo sai kuma yafasa yayi tafiyar shi kamar baiji abinda fafad'a ba.
Tana azkar d'in yammaci bayan ta idar da sallar la'asar tana tunanin a ina Yaya D'ansarai yatsaya bai dawo gida yaci abincin rana kamar yadda yasaba ba,duk da ba wani d'asawa suke yi ba,...shiru-shiru har bayan sallar isha'i haushin shi yakamata ita kuma ta k'i kiran shi a waya taji me yatsaya yi taje tayi kwanciyarta tana zencen zuci"wato ko da, da take son shi take kukan rabuwa dashi,to shi dai ba ta ita yake yiba tunda gashi suna zaman aure yana mata yadda yaga dama, tadad'a gyara rufa tana k'wafa aikin banza kawai tura agwagwa cikin ruwa,jikinta yayi sanyi "lallai san maso wani k'oshin wahala, har bacci yayi awon gaba da ita bataji shigowar shiba.
Da safe tana tsaye a jikin taga ta zubama motar Julaibib idanu,tun jiya bai fita da ita ba,sanda yadawo gidan tariga tayi bacci kuma bai tashe taba, anyama ya dawo gidan? dan yadda ta ajiye mishi abincin dare haka taba almajiri dasafe, bai ta6a ba,har d'akin shi taleka yanzu kuma ba ya nan,to ina yatafine?Wata kila tun daga sallar asubahi yawuce gidan Inna ko gidan Hajiya,ta lumshe idanun ta tana mamakin canjin halin Yaya D'an Sarai.
A hankali ake k'wank'wasa k'ofar. Tasauke numfashi,ranta ya mata dad'i Julaibib ne dan haka yake buga k'ofa na natsuwa.Tabud'e cikin d'okin san ganin shi ta ma manta da rashin jituwar su.Suka kalli juna yamata murmushi, murna ta koma ciki,zuciyarta tayi rauni,kwallah yacika idanun ta,ta rasa hujjar hakan wallahi, yarage fara'ar fuskar shi,yagyad'a kai labarin zuciya a tambayi fuska"ba kya maraba dani ko?Sai kawai yajuya, dasauri taruk'o gefen rigarshi tabaya"wallahi ba haka bane,yajuyo fuskar shi ba walwala"toh yayane?Taja da baya tabashi hanya dan yashiga,yakad'a kai"bazan shiga ba.
Tamarairaice"Yaya Aminu dan girman ALLAH kayi hak'uri kashigo,wallahi na yi kewarka ne,tunda aka kawo ni Lillahi warasulihi sai yau d'in nan kazo duk yadda muke da kai..tayi furucin da yanayin shagwa6a.Yashiga D'akin-shak'awar yazauna a kujera"to banda abinki Sudaida yaushe zan ta zirga-zirga a gidanki? Tashige D'akin-girki dasauri takawo mishi kunun tamba yasha madara "Yaya Aminu ga mutumin.Yabud'e kofin yagani"to nagode Sudaida,kad'an yasha saboda ya riga ya k'oshi,a gida ma yana da wanda bai shaba na wajan Innan D'ansarai.
Sun d'an ta6a hira sannan yace mata kishiga d'akin mijinki ki d'auko min mukullin motarshi zan kai ta gyara, ba yadda banyi dashi akan yad'auki tawa yayi tafiyar ba amma yak'i,sai tasha naraka shi yashiga motar haya,kuma a ranar yanada jarabawa...har tabashi mukullin yatafi hankalinta yayi mugun tashi"yanzu D'ansarai zaiyi tafiya yabar garin amma ko sallama bazai mata ba? Itako wace irin kiyayya yake mata haka? Ai ko kafin suyi aure yana mata sallama bare yanzu da take cikin gidan shi a k'ark'ashin igiyar aure.Tayi k'wafa"ai ba lallai ba tilas,yaje yadawo tana sauraren shi da duk ma wacce zai zo.
Kwanakinshi biyu da tafiya,shi bai kira ba, itama bata kira ba,a kwana na uku ne dai takasa daurewa dan abin tsoro yafara bata...sai taga bata kyau taba itace a k'asa dan haka tasauke ...rawanin tsiyar tanemeshi.
"Lafiya?
Tamabayar daya mata kenan daya d'aga wayar,bai kuma jira amsar taba yakasheTacire wayar daga kunnenta cike da mad'aukakin mamaki" wai me wannan mutumin yake nufi ne? haushi da damuwa suka kamata.. tajafa wayar a kujera ko tunanin taci screen bata yiba, tawuce D'akin-girki tasauke dafadukan taliyan data dafa, tazuba a faranti takoma D'akin-shak'ata dan taci, sai dai tanata kallan taliyar har yayi sanyi baza ta iya ciba,ai ko almajiri yana kwala barar"allazi wahidin"tabud'e k'ofa tajuye mishi duka a robar shi.Yakar6a da rawar hannu data murya.
"Iya ALLAH yabi yaki,ya yaye miki matsalar rayuwa.Tabishi da kallo tana fad'in"amin d'an Malam.Sauri yakeyi kamar zai ta shi sama dan kada sauran almajirai su farga da abinci a kwanon shi su rufar mishi, gashi kuma wasu gardawa ne guda biyu suka sashi ya barato musu abinci,idan bai kai musu ba ba k'aramin na jaki zai shaba,kuma ba shi da mataimaki sai ALLAH.
Abu kamar wasa k'aramar magana ta zama babba,yau makon Jukaibib d'aya kuma koda wasa bai kira taba...Abun yak'ara jefata a kokwanto da fargaba"to lafiya kuwa?Gashi ba wanda za ta tambaya,haba ai da kunya sai a mata tirrr...wasu kuma su mata dariya su d'auketa sakarya ita da mijin ta amma bata san a halin da yake ba?Taja tsaki"to shi d'in ya kira tane?Ko ko dai idan akak'i jininka ko ruwa kafad'a sai ace ka tada k'ura?Wucewar wasu dak'ik'u tana zaune tunani barkatai ya cika k'wak'walwarta ta rasa na za6a tayi shi da gasken-gaske,ta tsuke baki kamar za ta rufe shi tana fitar da iska,gaskiyar magana kawai ta kasa samun natsuwar zuciya dan haka tak'arya 6illenta tad'auki waya takira shi.
Bugu d'aya yad'aga kamar dama jiran ta yakeyi.Yayi sallama muryar shi a dake.Ta amsa sallamar tana gaishe shi.Asik'e ya amsa"lafiya...Gwiwoyinta suka sage,sharrr... sharrr...hawaye yafara sintiri a fuskarta shashshek'ar kukan na ta na fitowa a hankali. Yatare ta muryar shi ba sassauci"ke! Dakata, dakata haka malama! ni na ta6a fad'a miki ina sha'awar jin sautin kukan ki,bare yanzu da kike jinyi ki kirani?Yaya Jul...Kittt...Yakatse wayar. Haushi da mamaki suka rufe ta,ranta in yayi dubu ya6aci "Lallai ma D'ansarai...To ko da aka ba ka ni, idan ban maka ba sai ka sallame ni...tacigaba da kuka.
Julaibib yacire wayar a kunnen shi yana murmushi"kulawa yabawa ce,ya kamata yakoma gida haka dama kullum idan sunyi waya da Hajiya sai ta mishi ciwon bakin yaje ya share waje kamar mara Iyali.Baba ma jiya sai da yace"Malam D'ansarai ka k'ok'arta duk lokacin daka samu dama kazo gida wajan Iyalin ka kaji ko?Ya amsa da ladabi"eh Baba Insha-ALLAH. Yakulle k'ofar d'akin shi dan tafiya masallaci, masallatai mabambanta sunata kiraye-kirayen sallar azahar.
Da yammacin ranar talata rana ta tafi tana shirin fad'uwa,magriba na kunno kai tana zaune a tana nazarin littafan Islamiyyarta,motsin shigowar Julaibib taji yana shiga da kayayyaji D'akin-girki,sai da yagama yashiga D'akin-shak'tawar da wata babbar leda,a gajiye ya zauna yana kallanta yasa hannayen shi yana 6alle botirin gaban rigar shi,bata wani nuna d'okin ganin shi ba,fuskar ta ba yabo ba fallasa tace mishi"sannu da zuwa.Yagyad'a kai"yauwa yana cigaba da nazarin ta.
Sudaida...Yakira ta.
Bata d'ago ta kalle shi ba ta amsa "na'am.Duk sukayi shiru,ta sunkwui da kai amma ta kasa cigaba da nazarin kallan littafin kawai takeyi amma baza tace ga abinda aka rubuta ba. Ana fara kiran sallar magriba yafita.
Tana kwance bayan ta idar da sallar Isha'i,zuwa wannan lokacin zuciyar ta ta gama tafarfasa ruwan ciki ya k'one k'urmus har ya kama da wuta,zuciyarta tayi gobara saboda takaicin D'ansarai autan Inna;tayi kwafa taja dogon tsaki tun wajejen k'arfe goma sha d'aya da rabi na safiya Hanifa tazo tafad'a mata"Baba D'ansarai ya dawo,har ya bata Inibi da dabino me yawa, tashigo ma da Inibi tana ci,wani sanyin dad'i taji a ilahirin gangar jiki da sararin zuciyarta,duk da bawani d'asawa suke yiba,ta tambayeta to yana ina? Hanifa tace yana gidan su"Kawu Adnan shi da Babana(Musaddiq)
Nan da nan ta dad'a gyara ko ina tayi wanka tayi kwalliya tafeshe jiki da turare,ta turara d'akunanan gidan da turarukan d'aki ko ina yad'auki k'amshi da kyalli;to amma saboda tsiya d'inkin ludayi wai sai gab da magriba yaga damar shigowa gidan,kuma ko dak'ik'a goma cikakku bai yiba yasake ficewa,bai kuma sake shigowa ba sai yanzu awa biyu da idar da sallar Isha'i. Tamaida idanun ta tarufe kamar me bacci.
Yatsuguna yana tashin ta,dak'yar ta tashi tazauna tana turo baki gaba,yakoma kujera yazauna"zan samu abinci?Takauda kai"banyi girki ba,dan wanda tadafa mishi da rana,bayan la'asar tajuye ma almajiri.To ko shayi ne had'a min yunwa nake ji.Batayi magana ba dan dai ba yadda za tayine da baza ta had'a ba,tad'an ja tsaki"aikin banza harara a duhu,shi baya gajiya da shan shayi, shayin ma daba a sa madara sai kace jikan buzaye,tahad'a takawo mishi lokacin ya shiga wanka,yafito cikin fararen kaya na shan iska, botiran gaban rigar a bud'e suke gargasar shi akwance lufff...bak'ink'irin da shek'i.
Yad'auki shayin da bismillah yad'an kur6a sai yakalleta"me yasa kika samin siga bayan ga zuma?Tad'an harare shi"ni siga nake sawa a shayi,ai ba mutuwa za kayi ba.Yayi murmushi yana kad'a kai"k'uruci dangin hauka ga abinda aka tambaya ga amsar da take bayarwa "Sudaida mutan Matsirga suna gaishe ki,suna nan zuwa.Shiru ma amsa ce.Yabita da kallo"ke wai lafiyar ki kuwa? Ko dawowar tawace baki so?Ni fa shi yasa bana san zuwa,tunda raina ne yake 6aci.Tamishi wani kallo me kama da harara"na rantse da girman ALLAH ni...sauran kalaman suka mak'ale saboda haushin daya mamaye ta,takaicin ta ace yazo garin tun farar safiya,bai shigo yaganta ba,amma ya tafi Matsirga ba dangin Iya bare na Baba,dangin-dangirere wata tsohuwar budurwar shi data dad'e a kushewa,itace 'yar gwal har yanzu itace a sararin zuciyarta shi.Cikin fushi ta kwashi littafai da daddumar data yi sallah fuuu... Tawuce d'akin baccin ta.
Ya ajiye kofin shayin a saman tebur yayi shiru da yanayin damuwa"me yasa Sudaida take mishi haka?Ai itace k'arfin dawowar shi a yau,amma ta watsa mishi k'asa a cikin idanu;duk yadda ya d'okantu da ita a yau d'in amma da ta shi mazantakar tamotsa sai ya danne zuciyar shi bai bi ta d'aki kamar yadda zuciyar take raya mishi ba,ya kwaso wasu littafi yana nazarin su.
Tacire wayar ta a caji tahaye gado sannan ta kunna data,sak'onni suka dinga shigowa bata ta6a wayar ba har sai da suka gama shigowa sannan ta fara duba Status d'in su Khausar,haushi yadad'a kamata,ganin kowacce tana cikin shauk'in k'auna ita da masoyin ta...A status d'in A'isha ne taga Hashim ya zage yana daka shakwara a turmi tana ce mishi baiyi laushi ba sai ya k'ara dakawa,shi kuma yana fad'in nagaji fa gaskiya..ga wanda suke cin sakwaran da miyar Ogu suna dariya.
Ga na Khausar nan ita da Huzaifa sunyi wani irin kyau na ban mamaki gaba d'ayan su sun canja,ta d'ora ha6arta a kafad'arshi suna dariya, d'ayan kuma wasu irin kalamai ne na tsananin k'auna ta rubuta shi ga hoton zuciya an gewaye ta da adon filawar Damask rose-flower.
Na maryam kuma hummm sallah ba a magana,ta yi mugun mamakin abinda ta d'ora a irin yanayin zaman da tayi da kuma kayan jikin ta,a k'asa ta rubuta"My Snuggle...I miss you deadly... tabbb...ai bata gama kallo ba tabari tana zagin ta "abinda yasa meki ALLAH yasa kar yasamu sauran dangi.Tayita kira layin ta a kashe, duk da ta san taza6i wad'anda za su ga Status d'in na tane,amma ita sai hakan bai gamshe taba gaskiya.
"Nasmat tamata magana"
Hummm...Amaryar autan Inna kuna shan sharafin ku fa..
Sudaida ta6ata fuska"a ah abinda yafi sharafi muke sha.
Nasmat takyalkyale da dariya...nima naga alama shi yasa sai jefi-jefi a ke ganin ki online...har yanzu kanwa bata kar tsamin bane k'wannafin yakwanta?
Sudaida taja dogon tsaki"ke dai kika sani da neman magana ni sai da safe...kawai ta kashe data ta kwanta;bata duba sak'o ko guda d'aya ba,tunani barkatai ya cika k'wak'walwarta "hummm yunwar ya tashi"taja dogon tsaki wallahi ai ba lallai ba tilas.
Washe gari ma da sassafe yabar gidan wai suna da taro a Zango Urban kamar tace yasiyo mata d'anbagalaje amma ta shareshi,ta d'auki wayar ta takira Yaya Aminu tana tambayar shi"kaima kana Zangon ne?Eh Sudaida.Dan ALLAH Yaya Aminu d'anbagalaje nake so amma me taushi.Kai kai kai Sudaida ai gwamma me k'arfin kinga za ki motsa muk'amuk'inki da dasashi ko kuwa? Tad'an marairaice"Yaya Aminu ni dai me taushi.To zan siyo miki Insha-ALLAH. Yauwa Yaya Aminu wallahi, shi yasa nake son ka ALLAH yabarka da Sidddiqa tazama sarauniyar ka.Amin Sudaida. Sukayi dariya.
Abubuwa suke ta maimaituwa na rashin fahimtar juna a tsakanin su,musamman Sudaida da take d'aukar fushi a abinda bai kamata ayi fushin ba,abun ya k'i ci ya k'i cinyewa kamar cin k'wan makauniya.Yauma tunda yatafi masallaci sallar asubahi bai dawo gidan ba.A hankali taji ana k'wank'wansa k'ofar gidan ta san shine, dan taji tsayuwar motar shi.Tatashi tabud'e takoma tayi kwanciyar ta.Yatsaya a tsakiyar d'akin hannayen shi nad'e a k'irji.
"Sudaida bak'in Matsirga sun zo.
Dammm...zuciyar ta tabuga da k'arfin gaske.Tafara zancen zuci"Kutumelesi wato zuwa yayi dakan shi yad'auko su?Su suna da mutunci da kima a idanun shi,ya kuma damu dasu amma ita ko oho ko?
Tajijjiga kai wani...kumallon mata yata so mata har wuya,amma ba tayi ko kawa da zuciyar ta bata amayo shiba.Tad'ago takalleshi"Oh sun zo?Tagyad'a kai"toh sannun su da zuwa. Yabita da kallan nazari ganin tana dad'a gyara kwanciya har da jan bargo ta lullu6a"ke wai menene haka?Kitashi kije ku gaisa mana. Tayamutsa fuska sannan tajuya mishi k'eya "gaskiya ni har yanzu bacci ne a cikin idanu na kum...Yatari numfashin ta "Innar su Bilkisu ce fa?
Furucin shi yamata sukar wuk'a a k'ahon zuciya wallahi ta kasa daurewa,idanun ta suka kawo ruwa"shikenan kuma dan kayi bak'i bazan yi bacci ba,bayan idanu na har wani zafi da yaji-yaji suke min saboda rashin baccin?Ni fa na rantse da girman ALLAH bazan iya wannan zaman ba,tunda baka d'auke ni wata tsiya ba,toh ba dani ba wannan takuran,ko dan kaga gidan kane? Tagalla mishi harara"an hak'ura ana shan kukar k'azama kuma dole sai tayi tsada?Wallahi sai a hak'ura tunda ba mutuwa za ayi ba ehemmm.
Suka zubama juna idanu cikin kallan-kallo nawucewar wasu dak'ik'u kowa zuciyar shi ba dad'i. Sudaida tana jiran martani ne tayi abinda idan ta tafasa za ta k'one,sai shi kuma yamata shiru,dan yadda ta6ata mishi rai idan yatsaya toh aika-aika za ayi,sai kawai yagyad'a kai"ki cigaba da abinda kike yi,amma fa kowa yaci ladan kuturu sai ya mishi aski,wanda ya girmama iyayen wani to bana kowa ya girmama ba sai na shi.Yakai hannu yak'ara mata gudun fankar "shikenan kiyi baccin ki.Yajuya yafita fuskar shi ba walwala,labarin zuciya a tambayi fuska.
Tad'aga murya"eh yanzu kuwa zanyi baccin.Sai kuma tamik'e jikin ta yayi sanyi gaskiyar magana bai kamata tayi haka ba"ai bak'on ka annabinka, wanda yadamu dakai shine zai zo inda kake to bai kamata kanuna mishi halin-ko-inkula ba"bak'in karen masoyinka ai yafi farin ragon mak'iyinka.
Yayi jimmm...nawucewar wasu dak'ik'u a bak'in k'ofa,Sudaida ta k'i fitowa ta musu sannu da zuwa to me zai fad'ama Inna?Sai yajuya zuwa D'akin-girki yad'ibo musu kofuna da lemun biyar a raye da ruwa har zuwa lokacin bai samo amsar dazai ba Inna ba,yahura iskar bakin shi"lallai Sudaida zata gane da gero ake koko yacigaba da tafiya,zai fad'a mata Sudaida bata nan.
Yamurd'a k'ofar D'akin-shak'atawar da sallama yashiga,sai dai abun mamaki Baturiya da suna manga Sudaida yagani durk'ushe a gaban Inna tana gaisheta cikin girmamawa"kun zo lafiya? Yasu Malam da sauran mutan gidan?A Alhamdulillahi lafiya lau,duk suna gaishe ki,sannu mungode.Daganin yadda Inna take amsawa itama taji dad'in shimfid'ar fuskar da Sudaida tamata wacce tafi ta tabarma.Tamik'ama Bello hannu sukayi musafaha "d'an kanina kaga dana iya yaren fulatanci toh da yau duk hirarmu da fillanci za muyi shi. Bello yad'an bud'e idanu"kai dama baki iya ba?To kisa Yaya D'ansarai ya dinga koya miki mana,kinga lokacin da Adda batayi wannan tafiya me nisan nan ba to idan yazo da fillanci suke magana suyi ta dariya,ranan nan ma yace mata wai...Kai Bello Inna ta tari numfashin shi'ba na hana ka fad'an abinda ba a tambaye kaba? Sai yayi shiru.
Da sauri Sudaida tamik'e ta kar6i kayan ta zuzzuba musu lemon a kofuna sanna tashiga D'akin-girki ta d'auko musu abincin data dafa tajuye a food-flask tana mita a ranta"kai ALLAH yasuwake da halin D'ansarai yanzu da suna da yawa dole sai tayi wani sabon girkin. Inna tasha lemon amma tak'i cin abincin.Sudaida ta karyar da kai gefen dama"haba Innarmu idan baki ciba ai baza muji dad'i ba,ni 'ya ce awajen ki,uwa kuma ai bazata k'i cin abincin 'yar taba ko da tak'oshi za tasa albarka,Inna idan bakiciba sai inga kamar da wata a k'asa a yadda muka d'aukeki ni da Yaya D'ansarai ke ba haka kika d'auke muba...suna had'a idanu tad'an harare shi sannan ta kauda kai. Inna tace"ba haka babe Sudaida, karki kuma furta irin wad'annan kalaman,ni na d'aukeku kamar Ya'yan dana haifa,ALLAH yamuku albarka,yabaku zuri'a d'ayyiba. Dole ta d'auki cokali tayi bismillah sannan tad'an ci kad'an, Bello kuma yace shi baya shi dan bayajin yunwa yanata cin meatpie da su Inibin da Julaibib ya bashi.Da za su tafi Sudaida tabata turmin atamfa,taba da Shadda yadi goma da turare wai aba Malam tana kuma gaishe shi,tak'aro ma Bello meatpie dayawa dan jiya tayi kuma ba wanda yazo gidan shiyasa bai k'areba.Yakalleta yana ta murmushi "kince za ki Matsirga?Tagyad'a kai"eh Bello zamu zo Insha-ALLAH.Yamik'a mata hannu sukayi musafaha "Adda Sudaida sai kinzo zan tatso miki madarar saniyata da Malam yabani karsana guda biyu nawa ni kad'ai ina kaisu kiwo har rafin Matsirga nake kaisu susha ruwa sai mudawo gida,sukayi dariya.Sannan ta rakasu haraban gidan suka shiga mota.Sudaida tasunkuyo tana maimata" ALLAH yatsare Innarmu,ALLAH yakaiku gida lafiya.Amin Sudaida, Inna tadinga shi mata albarka,tasa gefen hijab d'inta tana share ruwan hawaye,yau mutuwar Bilkisu ta dawo mata sabuwa.Suka d'aga hannu suna ma juna adabo.Julaibib yaja motar cikin karsashi,yana murmushi jin dad'i abinda tama Innar Bilkisu ya kankare duk wani bak'in laifi data mishi dayake jin haushi...wata irin k'auna da kewar ta suka mamaye ilahirin gangar jiki da zuciyar shi.
Yadawo yatar da jarkokin kindirmo dana manshanu da sauran tsarabar da Inna takawo a inda yatafi yabar su.Yatsaya a gabanta hannayen shi suna cikin aljihun doguwar farar rigar shi,yakalleta cikin natsuwa"Sudaida ya baki adana suba?Saboda bani da buk'atar sune. Tagama wanke-wanken da take yi tamik'e tana yarfar da ruwan hannayen ta,tawani tsuke baki kamar me shirin yin fito.Yagyad'a kai"toh bani abinci sauri nake yi zan tafi Samaru.Cikin fushi tace"na rantse da girman ALLAH tun kafin wankin hula yakaika ga dare kasan inda za kaje kaci abincin ka,danni ba baiwa bace. Yazuba mata idanu"ji wasu soki burutsu da yarinyar nan take fad'a,yakalleta cikin natsuwa"nine bawan ki kenan, tunda duk rintse zan fita in nemo in kawo miki ki ci ko? Taturo baki gaba"ko bani dolen-dole kafita ka nemo,to ni guda nawa nake cin abincin?
Kinga ba wannan ba d'auko min abinci na fad'a miki sauri nake yi"na daina girki a gidan nan, tunda ko a tsarin shari'a ai cewa akayi miji yaciyar da matar shi bawai mace tayi girki ba.Yagyad'a kai"to amma dai yin girki a wajen mace dole ne,tunda kyautatawace idan miji yafita ya nemo muku,ke kuma sai ki dafa muku, a kuma al'adar duk mutanen dana sani galibi matane suke yin girki haka aka taso anayi Iyaye da kakanni tun tale-tale.Ba sai da so da k'auna za ayi hakan ba?Tafara k'unk'uni.Shima sai yanzu ya harbo jirginta...kumallon mata ke d'awainiya da ita,to amma me san d'an tsuntsu shi yake binshi da jifa.
Yarik'o ta tana k'ok'arin fizgewa sai yamata rik'on kura ta samu nama,sai ta koma tayi lamooo "Sudaida a duniyar ALLAH me namiki da bakya so na?Yad'ago fuskar ta suka kalli juna"haba Zaujatiii...Dan girman ALLAH fad'amin abinda zan miki dan in samu k'auna da soyayyarki.. yagewaye hannayeshi a jikinta yana mata wani salo...yayi k'asa da murya yana mata wasu irin kalamai na rarrashi da bambaki me k'aryar da damuwar data mamaye sararin zuciya.
Sak'onnin na shi yana shiga ilahirin gangar jiki da zuciyarta duk da bata so hakan ba amma zuciyar ta tak'i bujirema hakan,k'aunar shi da haushin shi yamamaye ta,sai kawai ta fashe da kuka ta k'wace tashige d'akin bacci tafad'a gado takifa fuskar ta a jikin matashi tana jin wani irin abu dabata san ko menene ba.
A tsakiyar d'akin yaja yatsaya yana kallanta"to meye abun kuka?Kai sha'anin mata a wasu lukutan sai su wallahi,banda dabi'arsu ta rauni da kuma dai shagwa6a wai tarwad'a da kukan k'ishin ruwa.Agefen gadon yazauna,yarik'o hannunta"kinga kukan ya isa haka share hawayen ki dan yana ta6a min zuciya,zai hadda sa min rud'ani fa...ta tureshi"Kalaman ka baza suyi tasiri a zuciya ta.Yagyad'a kai"toh na nawa kuma?
Yaya D'ansarai ba ka so na dan tunda aka kawo ni gidan nan nayi adabo da farin ciki,kazo garin nan tun farar safiya amma sai gab da magriba za ka shigo gidan, sannan sai kadinga nuna min wasu can sun fini mutunci tunda za kaje wajen su kasahare waje kuyi hira,ni kuma ko oho,idan nakira ka a waya sai kadinga min fad'a... kaza da kaza haka tadinga fad'in duk abinda yazo bakinta"ni gaskiyar magana na gaji da matsalolin ka,idan cuta tak'i ci tak'i cinyewa ai rai take nema.
Yayi yar dariya"wato laifi tudune...ba nine sama da ke ba?Ko ba aure tsakaninmu ai bai kamata zan fita kice min"ALLAH raka taki gona ba.Kin San wannan kalmar ta min ciwo ta kuma bani mamaki wai daga bakin ki tafito?Dan na miki fad'a akan abinda yake dai-dai?Dama gyara kayanka yana zama sauke muraba Sudaida? Tasunkwui da kai,itama ta gane tayi kuskure"Yaya D'ansarai...ta kira shi,sai kuma taja tayi shiru. Yakalle ta"na'am ya aka yine?Da rawar murya tayi furucin kayi hak'uri na gane kuskure na...Idanun ta yaciko da kwallah.
Tad'ora ha6arta a kafad'arshi ta dama" kayi hak'uri...Na yi Sudaida ni ai ina son ki a kowani hali da yanayi kece dai kika ce sai kina sona za kimin girki ko?Tayi shiru cikin alamar kunya.Yakalleta yanzu dan girman ALLAH babu soyayyata dank'are a taki zuciyar?Tad'an ta6e baki a zuwan furucin shi bai gamshe taba ko a kwalar rigarta.Tajanye ha6arta tana mishi wani kallo cikin turo baki gaba,da yanayin shagwa6a ta tambaye shi"me kake cewa?Shima yarama irin kallan data mishi"a ah bance kome ba.Takyalkyake da dariya. Yawatsa hannaye "magulmaciya kawai ana so ana kaiwa kasuwa;uhhh yakama ha6a"wato an hak'ura ana shan kukar k'azama...kafin yak'arasa tarufe mishi baki da tafin hannunta na dama"ai dai na ce kayi hak'uri...
Yasauke numfashi"ni dake muna san auren nan ba na dole aka mana ba,fad'uwa ce tazo dai-dai da zama,sai dai fa Sudaida bani da lafiya.Tad'ago tana kallan shi.Yalangwa6e kai "bakiga yadda na rame bane Zaujatiii... tamishi kallan tsafff sai taga hakan har a kan fuskar shi, tabud'e idanu cikin tsoro"toh me yake damun ka!
Kayi rashin lafiya ne ban sani ba lokacin kana makaranta?Yagyad'ai"eh ai kullum a cikin ciwon nake...Cikin fargaba tasake binshi da kallo"ciwon me?Toh me yasa baza kaje asibiti ba Yaya Julaibib?Ai ciwon son kine bana ganin likita ba,nayi fama da kewarki sau shurin masak'i Zaujatiii.. So ba k'arya bane,wani mikine a zuciya ta"Sudaida ki furta min kina so na,kina k'auna ta, za ki zauna dani,muyi hak'uri da juna tunda zo mu zauna zo mu sa6ane.
Tajijjiga kai"ni na yadda na amince,ina son ka,ina k'aunar ka akowani irin hali da yanayi mun zama k'arfe da mayen k'arfe Zaujiii... Yagewayeta da hannayenshi"hankali na ya kwanta, bani da sauran shakku,ba abinda za kimin yasake bani tsoro.Tayi murmushi"uh uh fa Yaya D'ansarai karkamin kurifa?Yagirgiza kai"ai nagane logonki yarinya,ba kuri bane,duk abinda za kiyi a banza wai talaka ya girmi sarki.Tagyad'a kai"ALLAH dan dai na tuba ne...sukayi dariya zuciyoyin su fesss...Hummm...Fushin masoya hutuhhh....
Nurse A'isha Muhammad Jibril{Asdilat for real💋} Ubangiji ya kiyaye min ke da kiyayewar shi,yatsare hanya,yakaiki Nursing School Mak'arfi lafiya. Ubangiji kama karatun na su albarka.Kasa su amfani kansu su amfanar da d'aukacin al'ummar Manzon ALLAH,da ita da duk wata Nurse dake fad'in KD garin gwamma da sauraran Jahohin mu na arewa,dana sauran yan'uwa musulmai na duniya kaafatan👏
Bar ganin ka ta ra...kiyayi me nema.
A sara a kasuwanci jari.
15 Jumaada Thani 1441
9 February 2020
We Ibrahim's Daughters👇
Asdilat KD...2geda with Ra'ibs.
DANGIN NONO WRITERS ASSOCIATION
{Da Inganci Mukayi Fintikau}
Bismillahi wabihi nasta'in
...GWAJIN DAFI💔
Almost true story
Daga alk'alamin🖊
Ya'yan Ibrahim
Saudat A.Baba (Asdilat KD)
Da
Bara'atu Ibrahim (Ra'ibs)
Shafi na ashirin.
Yaciro sakamakon jarabawarta a cikin jaka ya bata tana gani,ta samu sakomako me kyau credits shida har da lissafi da turanci"toh tunda kince kina so na,za kicigaba da karatun ki kwanan na.ALLAH da gaske Yaya Julaibib? Yagyad'a kai Insha-ALLAH.Tak'ank'ame shi tana bashi sumba da godiya...gaskiya na k'ara son ka ninkin ba ninkin,malala gashin tinkiya.Suka kalli juna suna dariya.
Safiyya ta haifi sankacecen yaron ta me girman ban mamaki.A gidan suka had'u dukan su suna ta hirar yaushe gamo ta baki da baki duk da kusan koda yaushe suna had'uwa a Whatsapp. Khausar tasake kallan yaron sannan tayi yar dariya"gaskiya Yaya Safiyya duk girman cikin nan ki ban zaci d'a d'aya za ki haifo mana ba. Tagalla mata harara"toh madallah ke idan kin ta shi sai ki haifo yan hud'u.Tagyad'a kai"za ko kisha mamaki. Zainab takama ha6a"ke Khausar yau she akayi daren da gari zai waye ne?Yi hak'uri Maman Hanifa.Safiyya tayi murmushin mugunta"ai akan tafe kan isa Khausar,ALLAH dai yabamu rai da lafiya za kiji jin jikinki,ki kuma gani ganin idanun ki...
Sai bayan sallar azahar Sudaida tawuce gidan Inna,anan ta tarar da Nasmat taje gaishe da Inna da bata ji dad'i ba kwanaki biyu da suka wuce.Tazauna tana tayata ninke kayan wankin Inna suna ta hirar su suna shan dariya, basuji shigowar shi ba sai ganin shi sukayi tsaye a bakin k'ofar yanad'e hannayen shi a k'irji"hirar me kuke yi haka ina ta sallama ba wacce tajini bare ta amsa.Nasmat tace"au yi hak'uri autan Inna bamu ji bane.Yagyad'a kai yana kallan Sudaida"d'an zo mana.
Tamatsa wajen shi suna k'us k'us k'us d'in su,Sudaida tana kyalkyala dariyar kalaman daya fad'a mata.Nasmat taja tsaki"ke tunda maganar taku ba tak'are bace,to nifa tafiya zan yi kina 6ata min lokaci sai kace ba gida d'aya kuka kwana ba.Yajuya jeki Zaujatiii wannan yar sa'idanu ce.Tad'an d'aga murya"Yaya D'ansarai karfa kamanta. Idan na manta ki tuna min tawaya kafin in dawo.To adawo lafiya.
Nasmat tabita da kallo"wato ke da D'ansarai abun nema ne yasamu matar falke ta haifi jaki. Kamar yaya?Tayi mumushi"ke dashi d'in duk kuna matuk'ar k'aunar junan ku,sai yanzu k'wak'walwata take hasko min wasu yanayi da nake gani a tattare daku na tsananin kishin juna a kowani hali da yanayi,kishi kuma baya k'ayatarwa matuk'ar ba soyayya,toh ALLAH ya dauwamar da k'auna har Darul-karamah(Aljannah) Sudaida tayi lallausan murmushi"ai ba ja kare ya mutu a juji.Ina son Yaya Julaibib amma halin miskilancin shi wasu lokutan yana bani haushi.Nasmat ta kyalkyale da dariya"miskili ka fi mahaukaci ban haushi.Abdul yashigo da rake ferarre,atile,yalon Bello da d'anbagalaje yakaima Inna a D'akin-girki wai inji Kawu,tana dubawa tamik'a mishi ledar "wannan dai Sudaida zaka kaima,maza tana D'akin-shak'atawa.
Nasmat ta tafi,amma ita har dare tana gidan.Bayan sallar Isha'i Alhaji Abdullahi yashigo. Tamik'e da sauri takar6i kayan hannunshi tana mishi sannu da zuwa,yasa6a babbar rigarshi fuskar shi cike da fara'a"a ah Sudaidan Malam D'ansarai ce?Ta sunkwui da kai.To sannu da zuwa,yashiga D'akin-shak'atawa ita kuma takai kayan D'akin-girki sannan taje ta gaisheshi cikin ladabi."Lafiya lau,kunanan lafiya ko?Tad'anyi murmushi tana murza zoben hannunta,itafa har yanzu nauyin Baba take ji tunda akayi auren nan. Yacigaba,
"ALLAH yamuku albarka,ayita hak'uri rayuwar duniyar ma gaba d'ayan ta hak'uri ce,idan akayi hak'uri da yawa aka jajirce, agaba sai kiga anyi nasara a koma menene.Yasa hannu a aljihun rigarshi yar ciki yad'ibo kud'i yan d'ari biyar dabai san ko nawa bane yabata.Tasake sunkwui da kai "Baba kabarshi nagode.Yakad'a kai"Sudaida kinga...tad'an d'ago takalleshi"ai ba wanda yake k'in alheri sai shaid'an, ke ai ya tace,a kowani lokaci naga dama zan iya miki kyauta ko da baki zo ba,to zan iya aika miki dashi har gidanki.Tasa hannu biyu takar6a"nagode Baba ALLAH yak'ara girma.Amin Sudaida. Yamik'e yatafi d'akinshi.
Har tafara bacci a gadon Inna yashigo gidan.Baba yarufe shi da fad'a"kai Malam D'ansarai ban sanka da yawo kamar wanda yaci k'afar kare ba ko da daba ka da Iyali bare yanzu, ina katafi ina ta kiran layinka bata shiga?Ya amsa da ladabi"amin afuwa Baba,wallahi Gidan-Waya natafi game da karatun Sudaida,sai kuma nayi rashin sa a sai mako me zuwa,ni kuma ba na nan, kuma na tsaya ganin Provost d'in makarantar ne. Wayata kuma mutuwa tayi saboda rashin caji. Yagyad'a kai"to ALLAH yataimaka,amma maganar karatunta ai ba damuwa ko da baka nan,zan sa Aminu yayi kome.Yakalle shi kwanaki nawa za kayi kadawo?Baba nima ban sani ba sai dai kawai anganni.
Yanunashi da yaysa"to kadinga kiyayewa da da da yanzu bambancinsu na da yawa,bazan ji dad'i ba idan kana tafiya kana share waje kayi zaman ka iyalinka kuma ko oho ba,a zaman takewar iyali ba abinci da abun sha kad'ai ake buk'ataba a ah har da kai gundarinka,kuma kullum kadinga tunawa kai shugabane za kuma a tambaye ka game da hakkin shugabancin da aka baka kana ji ko?Cikin girmamawa ya amsa"eh Baba nagode ALLAH yak'ara girma.
Inna takalkeshi"kai Julaibib dare na dad'ayi kashiga kaci abinci.To Inna,yashigo yazauna yana cin abincin,yana kallan labaran k'asa amma rabin tunaninshi na wajen Sudaida da take bacci,daya gama ci yakai kwanon D'akin-girki sannan yazo yatashe ta suka wuce na su gidan.
Dasafe Aminu yaje gidan suka tattauna akan karatun Sudaida.Yakar6i k'ananan hotunan ta, Sudaida tashigo da sallama ta ajiye jug d'in hannunta a gaban Aminu"dama ina ta sauri dan karka tafi.Yad'ora duka hannayenshi a saman tebur d'in"ban tafi ba amma ba sha zanyi ba.Tacire murfin"kagani Yaya Aminu kunun tsamiya ne mutumin ka.Yayi murmushi"toh idan nasha na ki inyi yaya da Innarmu da yake jirana? Julaibib yace wannan za kasha tunda kullum na Inna kake sha,da rana sai kasha wancan.Yamik'e kai Malam damun manya ai yafi na yara gard'i kusha abunku,yabashi hannu sukayi musafaha "ALLAH yakiyaye hanya,sai munyi waya.Julaibib ya amsa da amin,nagode.
Sudaida Ibrahim Me-Lambu ta fara karatun lissafi da kimiyyar na'ura me k'wak'walwa (Mathematics/Computer Science)sai dai tana shan zirga-zirga,lallai ilmi ba a samun shi da sauk'i, sai anyi gwagwarmaya kamar zuma yake ga zak'i ga d'ankaran harbi.Yau tana gidan Hajiya tana shan rake suna hirar Julaibib da suka gama magana dashi ta waya,shima yana can yana fafatawa da karatun.
Gajiyace da samun waje wai kuturu da gad'a,bayan ta gama shan raken bacci yafara kawoma idanun ta ziyara.Hajiya tatashe ta,tamik'e zaune tana mitstsik'e idanu"Hajiya lafiya?Tagyad'a kai"lafiya k'alau,kishiga d'aki ki kwanta a gado mana.Takalli agogon dayake d'aure a hannunta nadama tad'an yi tsaki"lokaci ya ja sosai,sai tamik'e tanasa hijab,tad'auki jakarta tara taya "Hajiya gwamma in tafi gida yamma tayi sosai. Hajiya tace shikenan sauka lafiya,sukayi sallama tatafi.
Bayan sallar Isha'i tana zaune tana nazarin littafan data barbaza akan daddumar datayi sallah, hankalinta yayi nisa akan karatun kamar a sama taji an maida k'ofar D'akin-shak'atawa an rufe,ba tare dataji motsin shigowa ba,tamik'e dasauri kamar za ta hantsila littafin hannunta yafad'i k'asa,tarintse idanun ta tana Istirja'i zuciyarta tana bugawa da k'arfi saboda tsoro, d'akin yayi tsit ba motsin kome sai karar agogon bango tik tik tik...Tasake kasa kunne,nan ma shiru bataji kome ba,sai tabud'e idanun ta wato kawai tsorata tayi?Takad'a kai"wallahi mutum rahama ne,yanzu ma dan dare yayi ne amma da gidan Inna za ta tafi,ALLAH yakaimu gobe na daina kwana ni kad'ai.Caraf idanun su yahad'u,yana tsaye nad'e da hannayenshi a k'irji, kafad'ar shi tadama rataye da jakar matafiya ruwan toka,yayi sharrr...dashi cikin farin yadi da farar hula zita.Tanunashi da yatsa"Yaya D'ansarai kaine da gaske ko kuma gizo ne?Yak'arasa kujera yazauna "matsoraciya kawai,to da gaske ni d'inne.
Tasauke numfashi"wai ALLAH to sannu da zuwa,sai kuma tad'an turo baki gaba"amma gaskiya ka tsora tani,kuma d'azu munyi waya amma baka fad'amin yau zaka dawo ba?Nasamu sarari ne shi yasa nace yau kome dare sai nazo na ga Zaujatiii...Takawo mishi ruwa da lemu,yad'auki ruwan yanasha yana mata kallan nazari ta dad'a ramewa.Ya ajiye kofin yarik'ota"Zaujatiii...me yake damun kine? Tad'ago kai takalleshi kamar bata ji ba"na'am me kace?Sai kuma tagirgiza kai"ni ba abinda yake damuna,tamik'e barin maka abinci me sauk'i ko yar dafadukar taliyace... yabita da kallo bawai jikin na ta yake k'arema kallo ba,a ah tunanin irin ramar datayi kawai yakeyi,kuma acewarta wai ba kome?
Yatashi yabita"ni fa bazanci wata taliya da daddaren nan ba gaskiya.To me zaka ci? Yakar6i albasar da take 6arewa ya mayar ma'ajiyarta"dafamin shayi kawai.Tayamutsa fuska "shayi dai shayi dai?Taturo baki gaba"nima gaskiya baza ka sha wani bak'in ruwa da daddaren nan ba,kai baka gajiya da shayi kamar wani d'an Niger?Yayi yar dariya"bari sujiki ba ruwa na,ke dan baki san sirrin da yake cikin wannan shayin nasu bane da neman shi zaki dingayi ruwa a jallo.
Takyalkyale da dariya"ALLAH yasauwake in nemi shayin da ba madara.Hum yarinya baki san amfanin wad'annan ganyayyakin bane. Takalleshi"toh meye amfanin su?Yagirgiza kai"zan fad'a miki amma ba yanzu ba.Sai yaushe?Sai lokacin dana koya miki sha,idan nafad'a miki amfanin nasu zaki yadda dani d'ari bisa d'ari dan kinji a jikinki,amma yanzu idan nafad'a miki,ba lallai ne kiyadda ba"gani ya kori ji.Tashagwa6e ni dai tunda baza kaci taliya ba to kaima baka shan shayin sai dai muje kaci donut da yoghort.Yarik'o hannunta"na yadda muje.
Dasafe tafito tsab cikin shigar kamala da mutunta kai"Tazauna a hannun kujerar da yake"Yaya D'ansarai taso ka kaini na kusa makara.Batare daya d'ago yakalle taba yanuna mata abinci"zauna ki karya kafin in gama abinda nake yi asibiti zamuje a miki General-check up. Tabishi da kallo cikin mad'aukakin mamaki"asibiti kuma? Tagirgiza kai ni dai gaskiya lafiya ta k'alau ba abinda yake damuna.Yad'ago yakalleta a gajerce yacigaba da danna na'ura me k'wak'walwa"kizauna kici abinci nace ko?
Ni fa banajin yunwa kuma ai...sai yad'aga mata hannu ya isa.Duk sukayi shiru nawucewar wasu dak'ik'u,tasake kallanshi"Yaya D'ansarai zan makara fa.Yayi kamar baiji abinda take fad'a ba.Haushi yakamata tamik'e tsaye"ni na tafi.Nan ma shiru yayi.Tajuya tayi tafiyarta tana surutai"da baka sa min rai ba da tuntuni banyi tafiya taba?Dama ai na saba tafiya ni kad'ai, ALLAH yasauwak'e maka wannan halin.
Da yamma tadawo daga makaranta a gajiye,ba abinda take buk'atar yi sai bacci danko jiya ba wani baccin kirki tayi ba Julaibib ya hanata sakattt...Tana shawo kwanar gidan su tahango wata mota me d'aukar hankali fara karrr...sai d'aukar idanu takeyi a cikin hasken rana,wata kyakkyawar macece me garin jiki wankan tarwad'a tabud'e motar tafito tanama Sudaida sallama. Sudaida ta amsa sannan suka gaisa a takaice... tacigaba da tafiyarta,matar tace"Dan ALLAH jimana "tajuyo tad'an kalleta sai ta matsa kusa da ita,matar tagyara farin medicated glass d'in data rufe idanun ta. Takalleta sama da k'asa wani murmushi yasu6uce mata,tanunata da yatsa "Sudaida ko?Sudaida tad'ago suka kalli juna,sai ta gyad'a kai kawai dan bata san a ina matar tasanta har tasan sunan taba.
Toh kiyi hak'uri na tsayar dake ba tare da kin san koni wacece ba,ina fata mijinki D'ansarai yafad'a miki zuwa na?Tak'ara kallan matar"wallahi ba k'arya hutu ya gama ratsata,ido ba muduba amma ai yasan kima,kayan jikinta na alfarma,a inda Sudaida taji dama-dama wai kibiya a cikin idanu shine shigar sanin darajar kai tayi harda hijab d'inta tsawonshi yawuce gwiwa da kad'an,tarasa amsar da zata bata tunda Julaibib bai mata maganar wata za tazoba gaskiya,sai tayi murmushi tana gyad'a kai"sannu da zuwa,toh bismillah "suka jera suna tafiya har tabud'e D'akin-shak'awa tanuna mata wajen zama taje takawo mata abin motsa baki suka sake gaisawa sannan tamik'e"bari a mishi magana.
Suka kalli juna yana mata wannan rikitaccen kallan nashi da bata so dan haushi yake bata,yafito daga wanka yana shafa mai.Yaya Julaibib wani irin mutum ne me tsatstsauran ra'ayi da baza ka ta6a gane inda yadosa kai tsaye ba a wasu lokutan."kayi bak'uwa. Fuskarshi ba walwala "wacece ita da baki san sunan taba? Tajuya"oho nima a ina nasan ta,kafito ka ganta mana ganin idanun ka.Sai da yagama shiryawa sannan yafito, yana ganinta yasaki fuskar shi yana mata barka da zuwa, yazauna suna gaisawa da tambayar me jiki."jiki Alhamdulillahi.Ni da Baban Humaima ne yana mota. Yafita yashigo dashi..
"Doctor Garga Ibrahim Manogi "babban likitane da ake ji dashi a Teaching Hospital na Zaria,k'wararre ne akan abinda yashafi k'wak'walwa(Neurology) likitan da akace sune ma idan sunje Shika lokacin da Bilkisu tayi hatsari, shine yake auren kanwar Innar Bilkisu.
Sudaida takawo musu abinci.Doctor Manogi yanaci yad'ago yana kallansu"gaskiyar magana abincin nan yayi d'an karen d'and'anon daya burgeni,kai Ustazu haka yake kiran Julaibib dole za kayi tumbi kwanan nan,yakalli Sudaida"kin gane ko idan ya6ata miki rai karki hana shi kome da yake so sai wannan Palatable girkin na ki tunda shi baya san cin abincin waje kinga ai kin horashi duk da ya iya dafawa amma dai kafin yadafa ai ya d'and'ana ko?Sukayi dariya.Doctor Manogi haka ALLAH yayi shi da sauk'in hali da raha sai yanayin shi yamata shige dana Yaya Aminu.Yakalli matar shi"Bongel Ustazu da matar shi basu burge kiba?Tayi murmushi"sun burgeni musamman ita, kaga bata sanni ba amma har tabarni nashigo mata gida duk da taji na ambaci sunan mijin ta,ka san wasu matan da kishin rashin hankali. Yad'an harareta"toh waya fad'a miki bata kishin shi? Kawai ta hak'urane dan ta san itace kad'ai a zuciyar shi, kin san jiya muna tare dashi bayan sallar magriba sai kawai yace min wai gida za shi,nayi-nayi dashi yabari yau mu bugo sammako amma yanok'e"wai ai yau d'in da sassafe zai dawo,amma kinga d'an rainin hankali gashi nan a zaune har bayan la'asar.Julaibib yasa hannu yana shafa kwantaccen bak'in gashin kanshi yana murmushi.
Bongel tad'an kalli Julaibib"ina son ganin Adnan Ibrahim Me-Lambu inji abinda yahana shi dawowa makaranta yayi B.ed d'in shi. Ai Adnan ya san dad'in kud'i ya zama d'an kasuwa kwanaki na mishi magana yace wai shi bazai iyaba wanda yayi abaya ALLAH amfana.Tace kash...na mishi sha'awar karatun saboda yaron yanada k'ok'ari yana d'aya daga cikin d'alibaina yan gaban goshi. Da muna magana ta waya daga baya na daina samun shi. Eh wayar tashice tafad'i yanzu wani sabon layine dashi.Ai ko zaka bani zamu muyi magana...
Sai yanzu Sudaida ta fahimci wacece ita.Bongel Lecturer ce,yaren turanci (English) take koyarwa a FCE Zaria,lokacin da Adnan yake karatu tasha jin sunan Malama Bongel a bakinshi da irin kirkinta,da taimakonta ga d'alibai,bata san d'alibai wad'anda basu da himma,tafi matsa ma irinsu da yawan tambayoyi dan zaburar dasu, masu san karatun suna zage dantse ko dan kar susha kunya a gaban d'umbun jama'a yan uwanshi d'alibai,yan abi yarima asha kid'a,yan kyalekyale suna adawa da irin halaiyarta musamman na zuwa musu aji a bazata ta na musu jarabawar gwaji,irin su Adnan a lokacin sune yan gaba gaba,baya yadda yarasa laccanta sai da dalili me k'arfi.Malama Bongel ALLAH yabata k'warewa da juriyar koyarwa,ga kuma ilmin tsurar shi Ubangiji me kyauta da k'ari ya ba ta,babban kuma abinda yak'ara mata farin jini shine bata kada d'alibai a jarabawarta (carry over)
Sunyi sabo da Adnan,saboda wani ciwo da yayi taje gaishe shi anan take tambayar shi d'an wani gari ne?Yafad'a mata Zonkwa,tayi murmushi kace kai d'an gidane,shikenan dazarar anyi hutu zata ba shi sak'o yakaima Innar Bilkisu a garin Matsirga,kanwartace uwa d'aya uba d'aya.A wasu lokutan ma takan ai ko shi takanas da kud'in mota yakai mata sak'o yakoma Zari'a a ranar. Malama Bongel tana da sauk'in kai,ba ta d'agawa da ilmin da take dashi,sai dai tana fama da ciwon idanu,tasha wahala dan akwai lokacin data ajiye aikin koyarwa saboda kome sai da lafiya akeyi, cutar glaucoma tayi mugun kamata,sai da suka tashi tsaye sannan tasamu lafiya,suka kuma ba ta medicated glass da take amfani dashi.
Sudaida tasake kallanta cikin zancen zuci"kowani d'an Adam tara yake bai cika goma ba,kowa da irin tashi matsalar.Wato wannan zuwan kuma Innarsu Bilkisu ce ba ta da lafiya kenan,dan dasafe taji Julaibib yana tambayar mai jiki tawaya lokacin datake shiryawa,sai dai bata tambayeshi waye ba lafiya ba,shima bai fad'a mata ba,dan idan bai ga damaba ko ta tambaye shi,shiru zai mata kamar baiji ba.
Shi kuma Julaibib sun had'u da Doctor Manogi ne a wani taran MSSN da akayi a jahar Taraba,sun fito sallah dan Julaibib shi yamusu limanci,suna yar hira yake tambayar shi shi d'an wani gari ne?Yafad'a mishi Zonkwa amma a Zari'a yake zama a halin yanzu dan shi d'alibine a jami'ar Ahmadu Bello.Doctor Manogi yanuna shi da yatsa"kar dai kai ne D'ansarai sarauyin wata Bilkisu data rasu?Yajijjiga kai"eh ni ne.Yace ALLAHU-AKBAR yamishi ta'aziyya sannan shima yamishi bayanin ko shi waye...daga nan hira ta 6alle har suka dawo Zari'a suka cigaba da mutunci da zumunci.
Sunyi hira sosai sannan suka shirin tafiya, Bongel tadafa kafad'ar Sudaida"naji kin fara karatu me tsada na masu k'wak'walwa,toh ina tayaki murna.Ki zage dantse kiyi ilmi kema kiba al'umma gudummawa da d'an abinda ALLAH yabaki,musulmin kwarai shine wanda zai amfanar da yan uwan shi da alherin shi.Sudaida kinyi sa ar kama zuciyar D'ansarai dan ba shi da wata magana sai taki,dan ALLAH kiyi hak'uri da shi, shima dole yayi hak'uri dake,zo mu zauna zo musa6ane,ALLAH yabaku zuri'a masu albarka. Sudaida tasunkwui da kai bata amsa ba tana d'an murmushi,ta bata wasu biscuit da alewa"gashi aba su Humaima"Bongel takar6a tana godiya"su Humaima sun gode.Doctor Manogi yamik'e yana kallan Julaibib"zaka d'auko jakar taka mutafine? Yayi yar dariya yana sosa k'asumbar shi"sai ranar jumma'a Insha-ALLAH. Yagyad'a kai'ALLAH ya kaimu,toh madam mu zamu wuce.Yaciro rafar kud'i yan ashirin guda d'aya ya ajiye mata a saman tebur,tamishi godiya.Sukayi sallama Julaibib yatafi rakasu.
Bayan sallar Isha'i yashigo ta mishi sannu da zuwa.Ya amsa da yauwa fuskar shi ba walwala takalleshi na wasu dak'ik'u"Yaya Julaibib za muyi bak'i amma shine baka fad'a min ba?Yayi kamar ba dashi take magana ba.Haushi yakamata. Yaciro wayar shi a aljihu sai ta fizge. Yad'ago yana mata wannan kallan da yake bata haushi,bai yi magana ba sai hannunshi daya mik'a mata alamar tabashi wayar,itama tayi kamar bataga abinda yayi ba"me yafaru ne ina maka magana kayi shiru?Oh baki ma san abinda yafaru ba ko?Tagyad'a kai"ALLAH ban sani ba.Yayi shiru kamar bazai yi magana ba zuwa can kuma yace"Da safe bana ce miki asibiti zamu tafi ba amma ki kayi tafiyarki makaranta saboda kin raina ni ko?
Tawani marairai"dan ALLAH kayi hak'uri, to amma Yaya Julaibib ni fa lafiya ta k'alau.To ramar me kike yine?Tashafa wuyanta"oh ni Sudaida kowa haka yake fad'a ni kuma ban gani ba.Yad'an harare ta"ni ai nagani bakya san abinci ne ai da safen ma bakici abincin ba kika tafi, yanuna mata ledar da yashigo da ita,tamik'e tad'auko faranti a D'akin-girki tajuye mishi balangun me koren tattasai,albasa,kabeji da cucumber ga yajin tafarnuwa,ta tura mishi gaban shi"ai na kine zauna ki cinye shi.Yaba kyauta tukwuici"sai ta mishi godiya dafatar k'arin bud'i amma har ga ALLAH ita ba ta wani jin balangu, yanka biyu taci,ta d'auki rakenta tafara sha.Shi kuma yana dad'a fad'a mata lallai ta dinga cin abinci kar cutar gyanbon ciki(ulcer)takama ta. Yaya D'ansarai ba fa rashin cin abinci yake kawo cutar gyambon ciki ba.Yabar rubutun da zai yi yakalleta"to me yake kawo shi? Ta6alli rake ta taune ta zuke ruwan tazubar da 6awon sannnan tace"rashin cin abinci akan ka'ida shi yake haifar da cutar gyambon ciki.Kamar yaya bangane ba.
Yanzu misali ka saba cin abincin safe k"arfe takwas kullum haka kake yi sai kuma kazo ka daina ci a dai-dai lokacin...toh shi ruwan matsarmama da yake d'iga ya narkar da abincin shima ya saba saukowa ya d'iga karfe takwas to kullum haka zai dinga d'iga ko kaci abinci ko bakaci abinci ba,idan akai rashin sa a bakaci a dai-dai lokacin ba to sai yad'iga a cikin cikinka shikenan wajen ya zama ciwo...ciwon da mutum zai zo yashiga wani mawuyacin hali na ni ya su.. Yakalle ta cikin natsuwa"ahab ba cinyaba k'afar baya...
Ni dai na fada'a miki ki dinga cin abinci"toh Yaya D'ansarai nahhh...tayi furucin da wani salo na yanga da shagwa6a.Suka kalli juna sukayi murmushi,bata gama shan raken ba ta ajiye dan yau tayi d'amarar hana karatun daren nan,shi dai kullum cikin bincike da nazari,a makaranta karatu a gida karatu?Rai ai dangin goro ne yana buk'atar ban iska...batayi magana ba kawai zama tayi a gefenshi ta gewayeshi,a hankali tafara mishi wani salo...salon daya tilas tashi ajiye littafin nazarin yafara bin yarima dan su sha kid'a.
Hantsi yadubi ludayi na alhamis bataje makaranta dan basu da lacca,tana kwance a doguwar kujera Hajiya tashigo da sallama, tamik'e zaune"lale marhabun Hajiyar mu,sannu da zuwa.Tasa hannu tad'auki ledar da Hajiya tad'ora a saman tebur"me nasamu haka? Tabud'e talek'a sai tasa hannu tad'auki guda d'aya awarar madarar shanu ce,tagutsira sannan takalli Hajiya "nagode ALLAH amfana.
Tanaci suna hira,Hajiya kuma tana ta kallanta cikin nazari dan yar shimice ruwan madara ajikinta,ta yi kyau sosai amma ta rame"ni wai ramar nan dakike dad'ayi to ko dai ciki ne dake?Sudaida takama ha6a"wuuu..ciki?Tad'an ta6e baki"uhun rufani ki saya.Hajiya takad'a kai"eh lallai ba shakka k'uruci dangin hauka,cikin ne kike neman tsari dashi?Ke ba a haihuwar aka haifoki? Ya'ya da kike ganin su ai rahamane jin dad'in rayuwa ne,su Khausar ba gashi har sun fara zuwa asibiti awon cikin ba.Tamaida bayanta jikin kujerar tana cin awararta"hu'un to ni dai Hajiya bani da wani ciki.Ai ban musaba"ALLAH na tuba shi ciki ai d'an dumane a hankali yake yad'o.
Julaibib yashigo da sallama yazauna a d'aya kujerar suna fuskantar juna da Hajiya"Hajiyarmu kin shigo?Ta amsa da eh Julaibibi.Yakalli Sudaida"lallai yarinyar nan,wasa tare ci bamban ko?Zanga me siyo miki rake anjima.Tad'auki ledar ta zauna a k'asa kusa da k'afafunshi"duba kagani,kaifa kake fad'in awarar madara bata dameka ba.Yad'auki guda d'aya"ai ba cewa nayi kwata-kwata bana ci ba.Tamishi wani kallo a marairaice"to afwan Zaujiii...yayi murmushi koma dai toshiyar baki kika bani yau dai baza ki sha rake ba,kema muk'amuk'inki su huta.Haba Zaujiii...kaima kasan"I can't do without sugarcane" tayi furucin da salon shagwa6a.Yamata wani kallo "au bama ni ba?Tasake wani narkewa"na rantse da girman ALLAH har da kai Yaya D'ansarai nahhh...Hajiya tagalla musu harara"oh Ya'yan zamani.Sudaida takalleta"da mukayi me kuma? Hajiya wai kin manta gidan amare kika zone?Hala kin manta hud'ubar dakika dinga manane a gidanki?
Takalleshi"Yaya D'ansarai kome tace mu muku indai bai sha6ama shari'a ba,ko menene shi bata togance ko abu d'aya ba.Hajiya tayunk'ura tamik'e"toh barin barku kuci karen ku ba babbaka.Shima yamik'e"Hajiya kiyi zaman ki,ni dama wayata dana sa a caji nashigo d'auka. Yacireta dan ta cika.Tagyara zaman hijab d'in ta"ai ba ganin ka yasani tafiya ba dama nayi niyya ne. Yasa wayar a aljihu"ALLAH huta gajiya Hajiyarmu sai nazo.Inji Sudaida.Tagyad'a kai"sai na ganki. Suka fita da Julaibib.
Bai dawo gidan ba sai da yamma tana D'akin-girki yamik'a mata raken"karki isheni da mita anjima.Tasa hannu biyu takar6a"shukran jazilan Ustazu. Yakalleta da sauri"au har dake? Yagyad'a kai tana yar dariya"har dani.Toh bar d'aura girkin nan kizo muje unguwa.Yaya Julaibib da wannan yammacin?Yad'aure fuska"ko da sulusin dare ne bazaki bane?Ta tsame hannunta daga cikin kayan miyar da take gyarawa"ALLAH yabaka hak'uri"ya amsa da amin.Kiyi sauri ki shirya ina jiranki a waje.Tabi bayanshi da kallo "zuciyar ta na raya mata wasu al'amura game dashi, takad'a kai"ALLAH yakyauta maka wannan halin wallahi.
Yana kallanta tafito amma sai da wasu dak'ik'u suka wuce sannan yabud'e mata motar tashiga tazauna tana d'aura belt.Ganin sun bar cikin gari yasa ta tambayeshi inda za su,amma yayi kamar bai ji taba.Itama sai taja bakin ta ta d'inke,tamaida bayanta jikin kujerar tare da lumshe idanun ta,tana sauraran wa'azin daya kunna na Ahmad Ibrahim(Bamba)sai da yatsai da motar sannan tabud'e idanun ta tana kallan wajen,nan kuma ina ne?Ta tambayi kanta"fito muje mana..taji maganar shi a sama,tafito suka jera zuwa gidan.
Inna tayi murna da ganin su kwarai, irin kambamawar data musu yasa jikin Sudaida yayi sanyi, wato su wasu irin mutane ne masu karamci da girmama d'an Adam,suna da shiga ran da ciresu a sararin zuciya bazai zama abu me sauk'i ba wai cire wando taka,shi yasa Julaibib yakasa mantawa dasu duk da babu wacce tazama sanadin had'uwar ta su a doron duniya.Inna tad'an kalli Julaibib"ai munyi waya da Bongel take fad'amin gobe zaka koma lallai abaka madara katafi musu da ita wai wanda suka tafi da ita sun tsaya a Gama-gira wajen wata k'awarta shine tabata duka,dama Maude nake sauraron shigowar shi in bashi yakawo maka ikon ALLAH kuma sai ga Ku.Ya amsa da ladabi"eh Inna nima ta kirani ta fad'a min,sammako zanyi a goben shi yasa nace barin zo in k'ar6a daga nan kuma Sudaida ta gaishe ki.Ai kuwa naji dad'i ALLAH yamuku albarka.Suka sake sabuwar gaisuwa da Sudaida tamata sannu da jiki.Jiki ai Alhamdulillahi naji sauk'i sosai.
Da zasu tafi Sudaida tace gashi ni dai nazo banga Bello ba.Inna tad'anyi murmushi"ai da ya san da zuwanki da bazai raka Malam Zango ba.To agaishe shi. Zai ji.Julaibib yamata alheri me yawa,ada tana damuwa da irin hidimar da yake musu har tazo ta daina,tun ranar daya kalleta cikin natsuwa da girmamawa"Inna ki d'auke ni matsayin d'a,idan kika d'auke ni a haka toh na san duk abinda zan baki zaki kar6ane da dad'in rai kina kuma shimin albarka tare da min addu'ar dacewa a doron duniya da lahira.
Megado ita tahad'a mu,koda ba ta, bazamu rabu ba dan kuma baku k'ini ba.Inna tajijjiga kai tasa gefen hijab d'in ta tana share kwallah"gaskiya ne d'an nan,toh ALLAH yamaka albarka,ALLAH yabaka zuri'a d'ayyiba,ALLAH yasaka maka da mafificin sakamakon shi, yasa hakan a mizanin kyawawan ayyukanka.Yanzuma irin addu'o'in data dinga musu kenan shi da Sudaida.Suna ta amsawa da amin,amin.
Gidansu Sudaida suka wuce...Sauran k'anninta suka dinga murnar ganinta,itama taji dad'i sosai dan basa wani zuwa gidan ta,to yaushe ma suke da lokacin yawo?Daga andawo makarantar boko za a tafi ta allo,ko ta Islamiyya da daddarene kawai suke da lokacin kansu,idan ma ranar ba a had'o mutum da aikin gida ba (home work)Tasaki hannnunsu,taje ta rungume Mama kawai sai tasa kuka,Umma,Julaibib dasu Asma'u suka bita da kallan mamaki yanzun nan fa tagama kyalkyala dariyar shirmen gwarancin da Nana take mata...
Mama tace ashsha"to me yayi zafi haka da idanu za suci wuta?Tana k'ok'arin d'ago ta Sudaida tadad'a k'ank'ameta.Umma ta fusata"ke menene haka yau naji shashanci rok'o a gidan bebe.Mama tad'aga mata hannu"na ki idanu 6arin mai a yashi.Umma takyalesu suna magana da Julaibib.
Mama tayi k'asa da murya"to d'agani tunda bazaki daina kukan ba.Tayi shiru tana share hawayen sannan tad'an marairaice "Dan ALLAH har yanzu baki zo na ganki ba,ai dama na san ke kad'aice za ki zo,ko Umma ce tazuga ki?Mama tayi murmushi"au dalilin kukan kenan?Eh mana Mama.To karki damu inanan zuwa ni ba wacce ta isa ta hanani zuwa inda kike.Yauwa Mama ALLAH yabar mana ke,suna ta hira sai da Baba yafito yace su tafi gida haka dare yayi gashi sammako Julaibib zai yi.Sudaida tabi Umma d'aki tafito daga bayi alwala tayi tanasa hijab Sudaida tashigo.Suka kalli juna sai Umma tad'anyi murmushi"za ku tafi ne?Ta amsa cikin ladabi"eh Umma.Kun san Umma Boss ce bata d'aukar raini.Tabata wasu humrah masu k'amshin fita hayyaci"gashi nan dama ke kad'aice ba a kai miki ba.Tasa hannu biyu takar6a tana godiya. Umma to yaushe za kizo? Ke! Umma tafad'a cikin d'an bud'e idanu.Sudaida tasunkwui da kai.Sai kuma ta sassauta murya"Sudaida me zanzo in miki ne?Duk abinda kike so kima Mama waya ko ni,ko ki turo mana ta sak'o a rubuce ba shikenan ba?A sanyaye tagyad'a kai sannan sukayi sallama.
Tafiyar Julaibib da yammacin ranar tadawo makaranta tana so tayi girki tatafi gidan Inna sai ga Asma'u tashigo.Tataro ta cikin murna 'oyoyo Yaya Asma'u sannu da zuwa.Ta amsa da yauwa tashige D'akin-shak'atawa,ganin haka yasa Sudaida tayi sauri tagama markad'a kayan miya taje suka gaisa,kamar kullum yau ma haka ta amsa gaisuwar cikin halin-ko-inkula tun bayan auren ta da Julaibib Asma'u take mata wani gani-gani data kasa gane manufarta.Tabi d'akin da kallo sannan ta sauke idanun ta akan Sudaida, tana sanye da riga da zani da dankwali na kamfala, ta ta6e baki"ina D'ansarai?Baya nan yatafi.Yatafi fa kikace?Tajijjiga kai"eh ya tafi.Toh yayi kyau... bani sak'ona sauri nake yi.Sudaida tagirgiza kai "bai bani kome in ajiye miki ba.Bata sake magana ba wayar ta taciro ta kirashi.Yana d'agawa ko sallamar daya mata bata amsaba tafara hayagaga...
kai D'ansarai haka mukayi dakai? Tayi shiru tana sauraranshi...wucewar wasu dak'ik'u sai kawai taja dogon tsaki"kai malami wallahi daga bayane sadaka da karuwa...eh to naji sai ta mik'a ma Sudaida wayar "Zaujatiii... kud'in dana baki kin kai gidan kud'in ne?(bank)A ah sai gobe Litini...Yauwa toh kiba Yaya Asma'u dubu goma a ciki,ki bar sauran idan nadawo nabaki duka sai ki kai kinji ko?To Yaya Julaibib, ALLAH yadawo dakai lafiya.Tamik'a mata wayar sannan take ta d'auko takawo mata,a wulak'ance takar6a kamar wacce aka bata najasa.
Sudaida takawo mata meatpie da lemu dan bata gama abinci ba.Tagirgiza kai"bani dankalin turawa da kwai zanje in soya a gida, tamik'e bani leda,inda suke ajiyewa ta nufa, Sudaida tabiyo ta da ledar tana fad'a mata amma fa kwan ya k'are.Sai tabi d'akin da kallo gwangwanayen madarar Nido tagari guda biyu dana Ovaltine guda d'aya sai siga me y'aya na kwali(cube sugar)sai tasa hannu ta d'auki gwangwanin madara d'aya da siga kwali biyu a ranta tana mita"ni nasan D'ansarai baya shan shayi da madara,yanzu nan ita za taita shansu? To aiko bazata shanyesu ita kad'aiba dan nima wannan ai yafi min dankalin.Sudaida tabita da kallo itama tana jiinjina k'arfin hali fin me kora shafawa irin na Yaya Asma'u.Toh sata za a kira wannan abun kome?Tunda bata tambayi wanda yasiyo ba.
Abinda Yaya Karima bata dashi kenan ganin gari da san na Bello-badin,ko wajen Inna taje haka take mata d'auki d'ai-d'ai d'in duk wani abu daya bata sha'awa,abin mamaki kuma Baturiya da suna manga,kamar ba Inna da Baba ne Iyayen taba dan su sun san mutumci da karamci wallahi.Idan an mata magana ta ta6e baki tana fad'in to menene a ciki? Sata a gida ai rance ne...bare ita ai bama sata tayi ba tunda a gaban idanu take d'aukar abu.To amma dai ai ba ace an ba taba kai ALLAH yasauwake. Takar6i ledar tasa a cikin sannan tajuya"sai anjima.To Yaya Asma'u ki gaida gida.
Kwana biyar bayan nan da yammacin la'asar tadawo daga makaranta kawai tawuce gidan Inna. Asma'u tana zaune tana cin dafaffiyar masara takalli Sudaida sama da k'asa bata amsa gaisuwar da take mataba,sai tambayar ta tayi"hala daga awo kike? Fuska a d'an yamutse dan tafara gajiya da irin abubuwan da Asma'un take mata tace"awon me? Asma'u tamata wani kallo me kama da harara "awon me mata suke zuwa yi a asibiti? Tamotsa kafad'a tare da watsa hannu"oho nima ban sani ba tunda ba ta6a zuwa nayi ba.Tawuce randar Inna tad'ibo ruwan sanyi,tashiga D'akin-girki tazuba abinci, tayi bismillah ta faraci.
Inna ta idar da sallar la'asar tajuyo tana shima Sudaida albarka"kin kyauta dakika bata wannan amsar.Ke Asma'u tanuna ta da yatsa"me yasa kike san zama babbar kwabo ne?Asma'u tamik'e"to yanzu Inna me nayi?Ni fa dama kullum a gidan nan a ban iyaba aka d'auke ni.Eh ai halinki yake ja miki.ALLAH yabaki hak'uri Inna ni tafiya ma zanyi,me zaki bani?Inna ta d'aure fuska"ba abinda zan ba ki sai dai in omon wanke-wanken da kika kawo min za ki koma dashi.Kai Inna haba-haba dai,tashige d'akin bacci tana fad'in"ni ai na ga abinda nake so,sink'in sabulu da man shafawa guda d'aya ta d'auko. Inna takalle ta"Asma'u na ba ki ne?Tayi yar dariya tana turawa a jaka"Inna kayan ALLAH ai na annabine,ba sid'i ba sad'ad'a ma kinyi kyauta ga wasu bare kuma ni?Tajuya na tafi Inna,idan Baba ya dawo a gaishe shi.Suka bita da kallo kowacce da abinda zuciyar ta ke rayawa.
Kwanci tashi a sarar me rai...Shekara d'aya da auren su A'isha,Khausar da Nasmat ne suka fara haihuwa,A'isha da Nasmat rana d'aya,ranar suna Sudaida tarasa inda za tayi ga makaranta,ana tashi Kafanchan tawuce gidan A'isha aka sha suna,ba ita taje gidan Nasmat ba sai da akaci aka kusa cinyewa dan ma na ka na kane...a yadda tagaji lik'is d'in nan,gida za ta tabi lafiyar gado.
Tak'arema jaririyar kallo tad'ago cikin murmushi "ALLAH na rasa da wanda tayi kama,ranar da aka haife ta sak babanta yau kuma ta canja batayi kama da ku ba, tamaida ita k'irji ta rungume ta lumshe idanun ta"ina son yarinyar nan ki bani ita mana.Nasmat tayi murmushi"ai dama ta kice na kuma bar miki.Tabud'e idanun ta suka kalli juna sukayi dariya.Nasmat ta kalle ta"d'azu dangin mijin ki bakiji irin habaicin da suke yi ba wai wasu sai dai suci su juye shi a masai,wani abin mamaki kuma Yaya Asma'u itace shugaba,sai da Hajiya ta musu wankin babban bargo sannan sukayi shiru.Sudaida ta d'auki kunun aya tana sha"kar ki wani ce abin mamaki,yau kika san Yaya Asma'u da halinta?A ah ai ni abinda yabani mamakin shin ke d'in ba matsayin kanwar ta kike ba? Tad'anyi murmushi"da ne nake kanwarta lokacin ina gidan mu,toh yanzu kuma ai k'aninta nake aure ina zaune a gidan shi,ita kuma dangin miji ce,wasu dangin mijin kuma ba mutunci suka sani ba.
Asma'un ce tashigo ma da Nasmat farantai takalli Sudaida sama da k'asa cikin ta6e baki "hamshak'iya,maduga ke sai yanzu kika ga damar zuwa? Komu da muke tare da Iyali ai hidimar su bata hana mu zuwa anyi kome damu ba,bare kuma ke da kike zaune ke d'aya ba wata hidima a kanki.Sudaida tayi lallausan murmushi"toh Yaya Asma'u dan ALLAH ina ruwan maza da wankan jego?Abinda tafad'a mata kenan tajuya suka cigaba da hirarsu dasu Nasmat.
Ta koma gida tayi wanka tana so tatafi gidan Inna,kiran Julaibib yashigo tad'aga da sallama"Zaujiii...afwan yanzu nake shirin kiranka "kasha ruwa lafiya?Yau banyi azumi ba Zaujatiii... bana jin dad'i.Wayyo! Sannu ai naji muryar ka wata iri,sannu kasha magani sai ka kwanta,dan ALLAH yau dai karka tsaya yin wani nazarin karatu,lafiya ai tafi kome.Toh nagode,kin tafi gidan Inna ne?A ah sai nayi sallar Isha'i.Kiyi zamanki ina hanya.ALLAH yatsare, yakawo ka lafiya.Amin,nagode Zaujatiii...Sai kuma tad'an turo baki kamar yana ganin ta"ni dai ALLAH na tsani dawowar cikin daren nan.Yayi murmushi"sai nazo kawai.
Jakar Magori take ji a k'aramar rediyo taji kwankwasa k'ofa,talek'a ta taga sai tagan shi a tsaye. Tabud'e ta k'ar6i jakar shi"sannu da zuwa Yaya Julaibib ina motar?Bazan iya tuk'i ba shi yasa nashiga tahaya.Har ta ajiye jakar bai shigo ba tasake fita sai taga a hankali yake tafiya,yashigo D'akin-shak'atawa yazauna tare da maida kanshi saman kujerar ya rufe idanun shi.Tazauna a hannun kujerar"sannu...ALLAH yasauwake.Bai amsa ba yamik'e wani jiri yakwashe shi luuu...sai ya durk'usa a gaban ta,yadafa gwiwoyin ta dan saura k'iris yasha k'asa. Sannu Yaya Julaibib. Yagyad'a kai ya yamik'e da sauri yafita,tabi bayan shi"Yaya D'ansarai ina za ka?
Abakin famfo yatsuguna yana amai,itama ta tsuguna tana ta jera mishi sannu, yagama aman yabud'e famfo yana taro ruwan da tafukan hannayen shi yana wanke kanshi zuwa fuskar shi.Yad'an kalleta yamik'e dakyar jikinshi a mace kamar yayi awanni yana aikin dabai huta ba,yasake kallanta...yayi magana amma bataji me yafad'a ba,tamatsa kusa dashi "me kake fad'a Yaya D'ansarai?Idanun shi sun k'ank'ance, luuu kawai taga ya tafi zai sha k'asa,a tsorace tarik'o shi wani abu mara dad'i ratsirga ilahirin gangar jiki da zuciyar ta,nauyin shi ya rinjaye na ta, gaba d'aya sukayi jikin bango,dakyar yasa hannunshi nadama yadafe bangon, kome yana hautsine mishi,kanshi na mishi matsanancin ciwo kamar zai rabe gida biyu,cikin dukan zuciya tafara kiran sunan shi"Yaya D'ansarai... Yaya D'ansarai... zuciyarta tayi rauni sharrr... sharrr...hawaye suka fara sintiri a fuskarta,jikinta yafara rawa"Yaya Julaibib ta fara jijjigashi sai tana Istirja'i dan wallahi a tsorace take,tana sake shi ko shakka babu zai zube mata a wajen,gashi baza ta iya rik'eshi gaba d'aya ba, k'arfin namiji da mace bambancin a bayyane yake.
Dak'yar tazame suka zauna a k'asa ta jingina bayanta da bango...tazuba mishi idanu a cikin hasken farin watan tana zancen zuci"gashi bata fito da waya ba bare takira wani daga cikin Yayyinta su zo su taimaka mata,takai hannu tana d'an ta6ashi"Yaya D'ansarai kata shi,Yaya D'ansarai dan ALLAH kabud'e idanun ka ka ji?Bazan iya bane dana kaika d'aki,a hankali yabud'e idanu yad'an kalleta sai kuma yamayar rufe...Tanata kallanshi tana ayyane-ayyane a zuci tana kukan shar6e, wucewar wasu dak'ik'u masu yawa sannan taji hucin numfashin shi me zafin gaske "Sudaida ki daina kuka naji sauk'i.Tahad'iye kukan tana kallan shi ta san fad'a kawai yayi dan hankalin ta yakwanta amma ko wannan hucin numfashin me zafi ai bana lafiya bane"Yaya Julaibib to za ka iya tafiya mutafi d'aki?Yagyad'a kai tamik'e tarik'o hannayenshi duka biyun sannan shima yamik'e suka tafi yakwanta, dan yak'i cin abincin data kawo mishi,shayin ma bai shaba...
Yi dai-dai dan dai-dai,dai-dai ne ba dan wasu sunyi dai-dai ba.
Facebook:سودة ا.باب
Facebook:Bilkisu Ibrahim Bilkisu Ibrahim
Email:Saudatibrahim333@gmail.com
23 Jumaada Thani 1441
17 February 2020
0 comments:
Post a Comment