Page 1
Al ameen a zaune yake akan kujerar Palo Sai girgiza k'afa yake ko ba afada ba kasan ransa a mutukar bace yake ya zubawa kofar dakin dake palon ido, amnah ce tafito daga dakin tana tauna cingam taci uban kwaliya mayafi a sakale akafadarta ko kallon inda al ameen yake batayi ba tayi hanyar waje.
Wani mugun kallo al ameen yaringa binta dashi har sai dataje bakin kofa ya daka mata wani uban tsawa"ke gidan uban wa zakije?
Dakuma izinin wa"? Yace yana Mik'ewa tare da nufarta, amnah itama d'aura fuska tayi tace "gidan ubana zanje mana tunda nagaya ma zanje ai nafita hakkinka" "to babu inda zakije Indai zaman aurena kike wai tsaya ma tukuna wai meyesa kika rainani ne Amnah Dan kinga ina sanki shiyasa kike tunanin zan zuba miki ido kina abunda ranki keso kifita lokacin dakika ga dama kidawo lokacin da ranki keso wai nan da igiyar aure akanki"? "Dakata a
AL ameen amnah tace tana daga masa hannu nifa bazai yiwu ka maidani matar kulle ba wlh Sam bazai yiwu ba awaye na nake zaka iya tuna alkawarin daka min kafin muyi aure na bazaka ringa min kulle ba duk kawayena dasukayi aure bahaka mazajensu ke musu ba sai ni zaka ringa yiwa haka inzan fita unguwa karinga kafamin dokoki kenan kana bani lokacin dazan dawo, kasuwa nan ma kabarni naringa zuwa hanani kake yi ka gwamace kaje dakanka ka siyo ko ma menene alhalin baka San irin abinda nakeso ba to a gaskiya ni nagaji da irin wanan abun wlh bazai yiwu ba sai lokacin daka ga dama zaka ringa barina ina fita unguwa ba Dan haka kaga tafiyata" tajuya tana k'ok'arin barin palon tunda tafara magana AL ameen yaji zuciyarsa na masa wani irin zafi idonsa ya kad'a yayi jajir sabida bacin rai cikin zafin nama ya fincikota kafin tabar Palon yace "wlh amnah kika sake kika bar gidanan bada izinina ba wlh sai na sakeki inkin d'auka karya nake gwada fita nan da kofar gidan kiga Dan na lura kwata kwata bakida hankali bakisan darajar aure ba abaya inkin fita nabarki wlh yau dai kika k'i bin umarnina Allah Sai na sakeki kuma I mean it" fincike hanunta tayi daga rukon dayayi mata tace " to Sai me Dan ka sakeni sai aka ce maka Dan mun rabu bazan cigaba da rayuwa ba,kalleni dakyau kaga tayi juyi agabansa wlh ko yanzu na rabu dakai saurayi ne zai aureni ka manta rububina ake lokacin daka zo Neman aurena na rufe ido na zabeka sai ayanzu daka ke ganin ka mallakeni zaka min rashin mutunci," takawa tayi taje gabansa ta tsura masa ido tace karka yaudari kanka al ameen bazaka iya Sakina ba nariga nayi niyyar fita nothing can stop me not even you" tace ahankali tana jifansa da wani irin murmushin datasan yana narkar masa da zuciya tace bye tajuya tayi waje, "Amnah! Amnah! Amnah! Al ameen yaringa kwalla mata kira amma ko juyowa batayi ba tacigaba da tafiyarta binta yayi dagudu adai dai lokacin datake k'ok'arin bude kofa tafita yace" wlh amnah this time around am serious if you step your foot outside am going to divorce you Allah dagaske nake" juyowa amnah tayi ta sakar masa murmushi taciro eye glass dinta daga jaka ta manna a fuskarta tace "hurry up cos am going" ganin tajuya tana tafiya ne yasa yace" amnah na sakeki saki daya inkinje gidanku karki sake kidawo gidana"wani irin bugawa kirjinta yayi tasaki jakar hanunta ta juyo yana kallonsa baki asake cikin tsananin mamaki Dan bata tab'a tunanin ko giya AL ameen yasha zai iya sakinta ba Dan tasan bazai iya rayuwa babu ita ba lura datayi da irin San dayake mata,AL ameen juyawa yayi yabarta agurin yanufi Palo yana share hawaye Dan shi kadai yasan irin halin dayake ciki,Amnah kuwa kasa kwakwaran motsi tayi sai data samu minti kusan talatin tana kalon kofar gidan kafin ta iya Jan k'afarta tabar gurin tana hawaye,ahaka ta k'arasa bakin titi tana zubar da k'walla har sai da tasamu abun hawa ta gaya mishi inda zai kaita tana hawa tafashe da wani irin kuka tare da d'ora hannu aka tana tashiga ta lalace.
Kubiyoni Dan kusha labari karku bari abarku abaya taku ce har kullum 💅💅SADNAF 4 REAL💞
[8/5, 8:54 PM] Sadnaf: R🅰SHIN H🅰KURI
Written by
💅💅 *SADNAF*💞
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS (P.M.L.)
*Wanana page din naki ne ke kadai mhiss B_hal mah love for you is unconditional you always support me in one way or the other Allah yabarmu tare*
Page 2
Direct gidan wata kawarta ta wuce Alawiyya tana sauka takarasa gidan da gudu ko sallama batayiba tahau k'wallawa alawiyya kira,Alawiyya dake kitchen tana girki ta fito a gigice tana sallati,apalo Amnah ta zube taringa zunduma ihu "Alawiyya nashiga uku na lalace Al ameen ya sakeni" inna lillahi wa inna ilahi rajiun" Alawiyya tace tana sakin cokalin hanunta " Al ameen din ne ya sakeki"? wani iri kuka Amnah takara fashewa dashi tace cikin sheshekan kuka " wlh ya sakeni"Alawiyya zama tayi kusa da ita tace " nasan zaa rina wlh bansha gaya miki ba karki zauna haka ba kikace min kin yarda da irin San da Al ameen ke miki ai ga irinta nan duk San dayake miki bai hana ya sakeki ba,kece bakisan yanzu a zamanin nan wlh sai ka tashi tsaye sosai akan mijinka inkana so ka zauna lafiya watakila ma wata ya hango awaje shiyasa ya sakeki, Amnah duk kawayenmu dakika sani ba wacce tazauna haka kowace sai data hada da addua amma ke kad,ai ce acikinmu kika zauna haka kika dage Al ameen na mugun sanki ai muma mazajenmu na na sanmu amma duk dahaka bamu zauna haka ba,acikinmu ke kika auri talaka mai mulkin tsiya mai kafa dokoki na masifa nan in wani Abu ya taso na hidima Baya barinki kizo sai anci Saa ai ga irinta nan kin zabe shi a cikin duban masoyinki shi kuwa ya saka miki da saki wai tsaya ma tukuna ya akayi ya sakeki mai ya hadaku"? Tunda Alawiyya tafara magana Amnah keta kuka tana cije leb'e sai data kwashi kusan minti goma kafin ta zayyanewa Alawiyya abunda ya hadata da Al ameen,wani mugun tsaki Alawiyya tayi tace "kiji fa akan kince zaki je gidanku ya dage baza kije ba har da saki hmmm wlh kinyi sake Al ameen ya rainaki idan ba haka mai abun saki anan sai kace Wanda yake jiran kiris ya sake ki, kingani nan wlh Aminu bai isa yamin rabin abunda Al ameen yake miki ba farkon Dana aure shi na lura yana da taurin kai Dana ga alamar zai ban ciwon kai tuni nayi maganinsa wlh yanzu sai yanda nayi dashi amma yanxu ke kin zauna haka wlh kin ringa kunsar bakin ciki,yanzu dai share hawayenki nabaki shawara"dagowa Amnah tayi ta zuba mata ido tana share hawayen fuskarta"kina jina Amnah kinsan dai bazan baki gurguwar shawara ba kizo yanzu muje in rakaki wajen mallamina ya kama miki Al ameen sai yanda kikayi dashi Indan bahaka ba wlh ko ya maidaki nan gaba sai yakara sakinki," ajiyar zuciya Amnah tayi tace " Alawiyya kin mantani ne nasha fad'a miki babu bin mallamai a cikin tsarina wlh bazan tab'a zuwa wajen wani da sunan ya mallakemin miji ba nima karan kaina mallama ce akwai ayoyi acikin Qurani da Idan na rubuta nasha Allah zai karkato min da hankalin mijina amma batun ki rakani wajen wani mallami bai taso ba Idan kinada wata shawarar ki bani Dan gaskia bazan iya rayuwa babu Al ameen ba INA mutukar San mijina ban San meyesa na biyewa San zuciyata ba nabari Al ameen ya sakeni,"tab'e baki Alawiyya tayi tace "Amnah ai dadina dake bakya jin shawara ke gashi ya sakeki ai zai iya rayuwa babu ke tunda ya sakeki ni dama shawarar dazan baki kenan tunda bazaki d'auka ba shikenan, "yanzu haka zakice Alawiyya Nazi wajenki Dan kisamarmin mafita na yanda zan shawo kan Al ameen ya maidani dakina batare da kowa yasani ba," tab'e baki Alawiyya takarayi tace " ai nasan bacin rai ne yasa ya sakeki amma nasan zai maidaki karki damu shawarar dazan baki itace fad'an dakuke yawan yi dashi akan fita unguwa ne ko bahaka ba"? G'yada kai Amnah tayi tace "hakane" "to abinda zaayi shine kibi umarninsa kidaina fita unguwa sai ya baki izini," waro ido Amnah tayi tace "tabdi kinsan kuwa indai ta Al ameen ne bazai tab'a bani izini ba dan dana biye mishi wlh sai nayi wata uku ban fita ba," "kash dadina dake gajen hakuri kibari na mutu mana kafin ki binne ni kina jina ai zaki ringa fita a duk lokacin dakikeso" yamutsa fuska Amnah tayi tace kamar ya"? Murmushi Alawiyya tayi tace " nufina zakina fita ko bai baki izini ba" kina nufin naringa satar fita( miss collapse) kenan?" "Kwarai kuwa Dan koni nan da kika gani Yawan fitar danakeyi bada izinin Aminu nake fita ba ke in gaya miki gaskia yawancin matan auren yanzu rabi bada izinin miji suke fita ba, mazan yanzun ne tsinan taurin kai da kulle na masifa kana kunshe a gida bakasan mai ke faruwa ba kamar ke da bakya zuwa kasuwa ai bakisan abinda ake yayi ba sai abinda miji ya siyo miki amma da ace kina fita kasuwa kina ganin abubuwan da ake yayi kinga ai baza abarki abaya ba ko bahaka ba"? " hakane amma Alawiyya kinsan duk matar data Fita bada iznin mijinta ba malaikun rahama tsine mata suke har ta dawo " nasani Amnah sai kayi ta istigifari inka tara fitar da yawa sai ka nemi yafiyar mijinka shikenan fa" anan Alawiyya taringa yiwa Amnah hud'ubar tsiya sai data tabbatar Amnah ta dau shawararta sanan suka rabu.
Amnah daga gidan Alawiyya gidansu ta wuce jiki asanyaye tana shiga gidan ta tarar da mahafiyarta azaune a tsakar gida tana tankade sallama tayi umminta ta dago ta amsa tare da cewa" aa Amnah kece kike Tafe da yamma nan",murmushin yak'e Amnah tayi tace " ee wlh ummi durkusawa tayi ta gaisheta ta amsa, Amnah zama tayi agefenta ta ajiye mayafinta a gefe takarbi rariyar daga hanunta tacigaba da tankade,"ina Al ameen din"? Ummi tace tana murmushi ras gaban Amnah ya fad'i tayi sauri tace "Ummi yayi tafiya yau shine yace nazo gida kar na kwana ni kadai inya dawo zai zo ya daukeni"eyy wane gari ya tafi"?" Kaduna ya tafi" " Allah yadawo dashi lafiya" ameen Amnah tace tacigaba da tankadenta.
Karfe 10 na dare Amnah na kwance akan gadon umminta sai juyi take takasa bacci sai hawaye take sharewa dan sai yanzu take jin wani masifafan San mijinta tunowa tayi jiya uwar haka tana kwance a kirjin Al ameen suna hira juyi tayi ta d'auki pillo ta rungumeshi tsam a kirjinta tana tunanin Al ameen gani tayi bazata iya jure rashinsa ba,janyo wayarta tayi tayi dailing numbersa yana gab da shiga tayi sauri katse Dan tunani tayi inta nemeshi zai rainata haka tayi ta yi akarshe ta kashe wayar gabad'aya ta kara rungume pillon tana tunanin Al ameen.
Bangaren Al ameen ma kusan hakan ne Dan tunda Ya koma cikin gida ya shige daki ya zubawa hoton Amnah ido wani irin Santa na ratsa shi dauko hoton yayi daga side bed ya rungume a kirjinsa yafara magana shi kad'ai "Amnah y? Amnah meyesa kika tunzurani na sakeki, Amnah kinsan irin San danake miki kuwa?Amnah sabida kishinki danakeyi yasa bana so kina yawan fita bazan iya rayuwa babu ke ba amma gashi kin tunzurani na sakeki" kara kankame hoton yayi a kirjinsa ya runtse idonsa ya kwanta yana tunaninta sai daya samu minti ashirin a kwance kafin ya tashi ya ajiye hoton ya d'auki mukullin motarsa ya bar gidan Dan ji yayi gabadaya gidan na mishi zafi, gidan amininsa ya wuce Habib yana zuwa ya sameshi a kofar gida a zaune shi da dansa, parking yayi ya nufi wajensu ya mika mishi hannu sukayi musabiha Habib yace" daga ina haka naganka a firgice",ajiyar zuciya Al ameen yayi yace abokina INA cikin wani hali kasan banida sama dakai komai nawa kasani" "hakane nura maza shiga cikin gida kacewa umma Ina zuwa Habib yacewa dansa ya mayar da hankalinsa kan Al ameen daya sunkuyar dakai Ina jinka" akan dai Amnah ne yau takaini bango wlh sai data tunzurani nayi abinda bana so" Habib dasauri yace "badai sakinta kayi ba" girgiza kai Al ameen yayi cikin takaici yace na "saketa wlh" "innalilahi wa inna ilahi rajiun Habib yace yana girgiza kai banji dadin abinda kayi ba mai ya kaika ka saketa" ? " kasan me tamin ne anan ya kwashe komai ya fada masa" " ajiyar zuciya Habib yayi yace duk dahaka da baka saketa ba da ka kai zuciyarka nesa" " ya zanyi Habib Amnah ta rainani bata bin umarnina kwata kwata ko Dan taga ina Santa ne shiyasa takemin haka Habib wlh yanxu haka zazzabin rabuwa da ita nake bazan iya rayuwa babu ita ba ya zanyi? " yakuwa zakayi R🅰SHIN H🅰KuRINKA ya janyo ma"bazaka gane ba Habib ko kaine abinda zakayi kenan mai shawara" shawara ka maidata dakinta"zan maidata ba yanzu ba sai tashiga hankalinta duk da nasan nima sai dai na d'aure" ahaka suka tab'a hira sukayi sallama Yakoma gida shima yakasa barci sai juyi yake sleeping dress dinta ya dauko ya rungume a kirjinsa har sai da bacci barawo ya saceshi.
[8/5, 8:54 PM] Sadnaf: R🅰SHIN H🅰KURI
Written by
💅💅 *SADNAF*💞
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS (P.M.L.)
Page 3
Wasa wasa sai da Amnah tayi kwana uku a gidansu Al ameen bai waiwayeta ba Wanda hakan yayi masifar dagawa Amnah hankali har wani Dan rama tayi,kullum zuba ido take taga Al ameen ya kirata amma shiru,mahaifiyarta na lura da ita sabida ko abinci kasa ci take yanzu haka ma mahaifiyarta zuba mata ido tayi tana kallon yanda take juya cokali takasa shan shayin,gyaran murya tayi tace " Amnah nikuwa lafiya kike kuwa kwana biyu tunda kika zo na lura kina cikin damuwa akwai abinda kike boyemin,anya ba yaji kika yo ba dan Ina lura Al ameen baya kiranki awaya keda idan kika zo gida minti minti yake kiranki har sai ya zo d'aukarki,kifadamin gaskiya Amnah me ke faruwa?" Amnah d'aurewa tayi ta dak'e tace "wlh Ummi ba abinda nake boye miki muna waya da Al ameen amma ba sosai ba sabida garin da sukaje ba network sosai munfi yin text dashi," to yaushe zai dawo"? "Gobe yace min zai dawo" Allah yakaimu lafiya" bari na leka makaranta" " to Sai kin dawo" tana ganin Umminta ta fice daga gidan ta fashe da kuka wani tunanin tayi ta mik'e zumbur ta zura hijabin mahaifiyarta ta d'auki mukulli ta kulle gidan ta nufi gidanta.
B'angaren Al ameen ma kuwa d'auriya kawai yake dan a kwanaki ukun nan baya iya bacci ba ya iya cin abinci ko kasuwa yaje waje d'aya yake samu ya zauna yazuba tagumi yana tunanin Amnah,yasha d'auko waya dan yakirata sai yana dab da shiga sai ya katse,kan gadon barcinsu sleeping dress din Amnah ne kala kala ya kwanta akai ko ya rungume wasu,yanzu haka ma tun daya dawo daga massalaci ya cire doguwar rigar jikinsa yayi rub da ciki yana tunanin Amnah, tafiyar yan mintuna ne yakai Amnah kofar gidanta ahankali takarasa gabanta na fad'uwa gwada tura kofar tayi a hankali taji ya bud'u tayi sauri ta shige cire takalminta tayi taringa tafiya cikin sand'a ganin bata ganshi a Palo ba yasa tacire hijabinta rigar roba roba ne ajikinta Yakama jikinta tsam, d,akinsu ta wuce direct Dan tana kyautata zaton yana can,daga labulen d'akin tayi tahango shi akwance yayi rub da ciki,dagudu takarasa kan gadon tafad'a kansa ta kankameshi tareda fashewa da kuka,Al ameen daya tafi tunanin Amnah adai dai wanan lokacin jiyayi kamar a mafarki Amnah ta rungumeshi jin sheshekar kukanta ne yasa ya tabbatar ba mafarki yake ba,wani irin juyi yayi ya rungumeta,kamar zai maidata ciki, dagota yayi yazuba mata ido itama ta zuba mishi ido,tana San magana katseta yayi da sauri yahade bakinsu yafara mata wani irin zazzafan kiss yana lashe hawayenta,gabad'aya sun fita hayyacinsu Dan maida ma da martani take sosai Dan tayi missing dinshi sosai sai daya rabata da kayan jikinta gabad'aya cikin rawar jiki kamar bai tab'a saninta ba yana dab da cima burinsa ta hankadashi,dagowa yayi cikin tashin da rinnanun idonsa yace" precious mai haka"janyo bargo tayi takara rufe jikinta ta d'aura fuska tace " kamanta ka sakeni,"matsawa yayi kusa da ita yajanyota yafara magana cikin rawar murya "precious aranar dana sakeki na maidaki Amnah bazan iya rayuwa babu ke ba,Dan Allah kiringa bin umarnina,kidaina bari muna samun sabani dake, ba kulle nake miki ba ina kare hakkin aure ne,matar aure kirki killace kanta take bai kamata taringa yawo kwaro kwaro ana ganinta ba,ke ba makaranta kike zuwa ba, ke ba aiki kike ba amma kullum ace kin fita kinga irin wanan ba tsari shiyasa nake hanaki fita akai akai kinji,"Amnah har da zatayi masa musu amma data tuna shawarar da kawarta Alawiyya ta bata ne yasa tace" insha Allahu nadaina,"wani irin murmushi yasaki yace "promise" gyad'a kai tayi itama tana murmushi,"thats my baby come here" yace yana janyota hade bakinsu yake k'ok'arin yi ta kau dakai,cikin mamak'i yake kallonta yace "lafiya kuwa" ? Zumbura baki tayi tace cikin shagwaba " yanxu da banzo ba bazaka tab'a nemana ba kaga kenan nafisanka tunda ni nakasa jurewa sai Dana kawo kaina" " wlh precious nafi kaunarki ai dama niyyata ina tashi inayi wanka gidanku zanje in taho da matata dan wlh Allah kadai ne yasan yanda nayi missing dinki bari na nuna miki how much I miss you janye bargon data lullub'e jikinta dashi ya wular,yafara ai ka mata sakoni ko ina na jikinta,nikuwa na wawuro kafafuna nayo waje dan wanan wasan yafi karfina,tabbass (ayau nagane cewa mata da miji sai dai Allah ba q shiga tsakanin mata da miji)
One hour later
Al ameen na kwance akan gado yazubawa Amnah ido datake taje gashin kanta,zai magana kenan wayar Amnah yafara ringing,wurgar da comb din hanunta tayi tace "nashiga uku Habibi ummi ke kirana mai zance mata" zama yayi dasauri yace kice mata gidan Alawiyya kikaje dubata batada lafiya gaki nan zuwa,"gyad'a kai tayi dasauri ta daga wayar tayi mata bayani kamar yanda Al ameen yagaya mata,ta katse wayar tana dafa kirji,tace "Dan Allah ka tashi ka maidani gida" tashi yayi yanufi toilet yayi wanka yafito yashirya cikin kana nan kaya,Amnah kuwa ta zuba mishi ido,Dan wani kyau taga Al ameen yakarayi " hada ido sukayi ta mudubi yasakar mata murmushi,yajuyo yanufi wajen datake a zaune yace "precious ya zaayi kenan yanzu inkin koma gida kicewa Ummi nakiraki yau zan dawo da yamma zan biyo in d'aukeki" " aa kabari gobe sai kazo ka d'aukeni tunda nariga nace mata gobe zaka dawo"wlh baki isa ba yau zanzo ind'aukeki kinsan d'aurewa nakeyi rashinki a kusa dani daga kasuwa zanzo mutafi ki tanadeni Dan yau ba bacci sai na rama kwanakin da bansha madara ba" yace yana kane mata ido, sunkuyar dakai tayi tana murmushi,ya rik'e hanunta sukayi waje.
Gidansu ya wuce da ita, shi kuma ya wuce kasuwa,da yamma karfe biyar akofar gidansu Amnah tayi masa yashiga suka gaisa da Ummi har da guntun tsarabarshi,Amnah tafito suka tafi,aranar soyewar da Al ameen da Amnah sukayi ba amagana Dan dab suke dasu kone, ahaka suka ringa gudanar da soyayyarsu kamar zasu maida juna ciki,bayan kwana biyu Amnah na girki a kitchen wayarta dake Palo yafara ringing,fitowa tayi dagudu ta d'auki wayar taga Alawiyya ke kiranta dagawa tayi cikin dok'i suka gaisa anan Alawiyya ke fad'a mata tazo yanzunan tazo taga kayan da aka kawo daga Dubai,Da har Amnah zata ki zuwa amma ganin ta kwana biyu bata fita ba yasa tayi sauri ta kashe girkin datake ta yafa mayafi tayi waje, adaidaita sahu ta Tara tahau tanufi gidan Alawiyya yana tafiya Al ameen na dawowa.
[8/5, 8:54 PM] Sadnaf: R🅰SHIN H🅰KURI
Written by
💅💅 *SADNAF*💞
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS (P.M.L.)
Page 4
Al ameen parking yayi yanufi kofar gidan dan dama yunwa ce ta koro shi baya iya cin abincin kowa inbana Amnah da ummansa ba,turus yayi daya tura kofar yaji alamar a rufe mamak'i ne yarufeshi dayaji kofar a kulle ya kara turawa yaji a rufe,mukulli yazaro daga Aljihunsa ya bud'e kofar yana mamak'in inda Amnah taje batare da izininsa ba,zama yayi a Palo yana tunanin inda Amnah taje,wayarsa ya d'auko dan yakirata yaji inda taje,ko mai ya tuna oho ya ajiye wayar,kitchen yanufa dan yaga ko tagama girkin daya sata dan sai daya mata waya kafin yataho,tukunyar dake kan gas ya bud'e ga mamak'insa sai yaga ruwa akwance asaman jollof din shinkafar,wani irin bak'in ciki ne ya lullub'e shi yamaida murfin tukunyar ya rufe yafito daga kitchen din yanufi 3/seater ya kwanta dan ji yake kamar zuciyarsa zata fad'o dan bak'in ciki,tunanin yafara yi inda Amnah taje har takasa tsayawa ta karasa girkin daya sata takuma kasa kiransa awaya ta sanar dashi,can kasan zuciyarsa kuwa tunanin yaringayi da Amnah ta Dade tana fita bada izininsa ba yau ne dai Allah yayi asirinta zai tonu,wani irin bak'inciki ne yakara lullub'e shi Al ameen mutum ne da bai iya bacin rai ba atake zazzabi ya rufeshi,tunanin matakin dazai d'auka akanta yafarayi yana jijjiga k'afa.
Amnah kuwa tafiyar yan mintina ne yakaita gidan Alawiyya,da sallamarta tashiga gidan,tasaki shewa tana karasawa palon dagudu"shegu manyan gari yau kune a gari,"Amnah tace tana Tafawa da wasu kawayenta biyu da take mutukar ji dasu siyama da firdausi Dan dama su hudu ne a click dinsu dukansu sunada aure makaranta d'aya sukayi kowace mijinta nada rufin asiri,dan cikinsu babu wacce batada mota Amnah ce kawai batada mota a fad'arsu ita ke auren talaka wanda a tunanin SADNAF ba talaka ta aura ba mai rufin asiri ta aura tunda yaci karfin b'ukatun gidansa sai dai R🅰SHIN godiyar Allah, Firdausi CE ta murmusa tace "shegiyar yau mijin naki yabarki kin fito kenan",tabdijan Alawiyya tace "satar fita tayi wanan mijin nata ne zai tab'a barinta tafita,ai kema kinsan bazai tab'a barinta ba,tab'e baki siyama tayi tace"lailai kam yanzu girl friend haka zaki cigaba da zama namiji namiki abinda ransa keso,sai yaga dama zai barki kifita Dan masifa,ni wlh dama mai citta kika aura bazan ji haushi ba,shine bashida k',udi shine mai mulkin tsiya,kizo muje a rakaki wajen teacher ayi mishi maganinsa kinki,d'aura fuska Amnah tayi tace" kunga banasan irin wanan mijina duk da talaka ne yanada rufin asiri dai dai nashi kuma ahaka nakesan shi ni auren soyayya nayi kuda kukayi aure dan k'udi da mijinku baya ya k'afa muku mulkin tsiya sai kucigaba da zamanku ina farinciki da yanda Allah yabarni ke kuma dama kirana kikayi dan kusani agaba kucimin mutunci," Amnah tace tana kallon Alawiyya,haba girl friend ya zamuyi muci miki mutunci kema kinsan bazai yiwu ba,dama Firdausi ce jiya ta dawo daga Dubai ta saro kaya masu Dan banzan kyau shine nace bari nakiraki ki kigani,tab'e baki Firdausi tayi tana kallon Amnah up and down,tace " girl friend Dan Allah dubi doguwar rigar da kika sa old made design am sure mijinki ne yasiyo miki, am sorry to say friend acikinmu kece bakya shigar manyan mata,though nasan your husband can not afford to buy latest designers wear for you,mu friends dinki we can afford to be sincere wlh banajin dadin ganinki ahaka pls kiringa zuwa muna rakaki kasuwa kina siyan kaya masu tsada kidaina bari yana siyo miki kaya masu araha Wanda low class mata kesawa,kituna fa muna yan mata duk wani designer kaya ajikinki ake fara gani,amma daga aurenki da mutumin nan kin dawo wani iri to be frank am not happy the way I use to see you,duba cikinmu babu wacce bata Jan mota, amma ke a k'afa kike yawo," "enough of all this nonsense Amnah tace tana daga mata hannu, inaso kisan wani Abu Firdausi all fingers are not equal, kowa a duniya da kika ganshi da destiny dinsa,Allah yariga ya tsaramin rayuwata ya tsara muku naku kuma Alhamdulillah ina farinciki da yanda Allah yabarni Dan nafi dubu dubu sunfini,dan haka ku k'yalleni ni, in wanan rubbish din kika kirani kufad'amin intafi dan mijina aiki yasani nafito," Amnah tace tana d'aukar mayafinta "calm down friend mai yayi zafi haka tace tana zaunar da Amnah kiyi hakuri Alawiyya tace tana zaunar da Amnah " wasu arnen material Firdausi takawo mana daga Dubai kingansu"wani leda ta janyo taringa zaro wasu tsala tsalan material masu masifafan kyau,Amnah da ranta yake a bace tuni ta duro daga kan kujera ta dauki materials din tana gani,sabida mace ce ita mai San gayu sosai,Wanda yanda tanuna farincikinta a filli ne yasa su siyama suma dadi ya kamasu Dan suna so suga sun farantawa Amnah rai,"Alawiyya ce tacigaba da magana kinsan bikin Aisha zaayi kanwar Firdausi ending of the month shiyasa ta siyo mana Dan musa ranar dinner,"kai amma fa material din yahadu cewar Amnah"sai k'udi ba Firdausi tace tana jijjiga k'afa yanzu abinda zaayi kuzo mutafi mu kai dinki inyaso gobe ko jibi sai mushiga kasuwa musiyawa material din kayan had'i "girgiza kai Amnah tayi tace gida zan tafi Dan mijina yasani girki wlh bangama ba na fito bari nakoma gida kar ya dawo ya tarar bana nan,Ku kaiwa telan ai measurement dinmu d'aya da siyama,a takaice karfi da yaji suka tsara Amnah ta rakasu wajen dinki ba ita ta tafi gida ba sai wajen karfe shidda.
Adai dai wanan lokacin Al ameen Kamar ya fashe dan bacin rai idonsa akan agogo,ganin shida tayi Amnah bata dawo ba yasa yatashi yaje ya kulle kofa tacikin gidan,yakoma kitchen ya dafa indomie Dan bak'aramin yunwa yakeji ba amma abun mamak'i yakasa cin indomien Dan bak'inciki ture fillet din yayi gefe yanufi band'aki Dan yayi alwala,adai dai wanan lokacin Amnah ta dawo,tana ganin motarsa awaje ta d'ora hannu aka Dan tasan yau mai kwatar ta a hannun Al ameen sai Allah,cikin rawar jiki da fargaba takarasa kofar gidan taringa kwankwasawa ahankali ganin takusa minti sha biyar babu alamar zaa bud'e ne yasa tafara kwankwasa da karfi Al ameen kuwa yana kan sallaya yanaji ana yaki tashi Dan yasan Amnah CE,ganin tana bugawa da karfi ne yasa ya mik'e a fusace yanufi k'ofa yana bud'ewa Amnah taja da baya gabanta yayi wani irin fad'uwa dan idon Al ameen ya kad'a yayi jajir, jijjiyoyin kansa sun ta tashi,zubewa tayi akasa tahada hannayenta alamar ban hakuri,Al ameen da ya zuba mata ido cikin tsananin fushi yace kitafi gidanku na sakeki saki d'aya yajuya yabarta agurin a sandare.
[8/5, 8:54 PM] Sadnaf: R🅰SHIN H🅰KURI
Written by
💅💅SADNAF💞
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS (P.M.L)
page 5
"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun Amnah taringa maimaitawa tana dafe da k'irjinta,jitayi wani irin jiri yana dibarta,sai data samu minti 40 a zaune takasa k'wak'waran motsi ahankali taji zuciyarta ya rage mata nauyi,ta mik'e ta nufi bakin titi ta tari abun hawa tanufi gidan Alawiyya kasa kuka tayi sai data je gidan adai dai lokacin Alawiyya ta caba ado tana jiran dawowar mijinta,ganin Amnah a tsaye ta zuba mata ido ne yasa tasaki sallati tana k'arasawa wajenta "Amnah lafiya kuwa yana ganki haka?mai yadawo dake duk maganan nan datakeyi Amnah ido kawai ta zuba mata takasa magana,Alawiyya hanunta ta ruk'o tashigo da ita ciki ta zaunar da ita, tace" Amnah pls fad'amin mai yafaru,sai anan Amnah tafashe da wani irin kuka tana rik'e k'irjinta,"innalillahi wa inna ilahi rajiun"Alawiyya tace tana zaro ido,"badai Al ameen kara sakinki yayi ba"? Girgiza kai Amnah tayi tace da karfi "ya sakeni Alawiyya yakuma sakina kinjanyo min ya sakeni" tace tana kara fashewa da matsanacin kuka,dafe k'irji Alawiyya tayi tana sallati tace "saki saki fa kikace anya Al ameen bashida tab'in hankali kuwa yanzu ko sati biyu baayi daya sakeki ba yanzu yakara sakinki mai ya mayar da aurene,"? Kuka Amnah kawai take takasa magana,Alawiyya wayarta ta d'auko takira mijinta tace mishi ankirata a gida zataje anjima zata dawo,ta kashe wayar mayafinta ta d'auko tacewa Amnah ta tashi sutafi gidan Firdausi, Amnah ta mik'e suka nufi gidan Firdausi,akan hanya Alawiyya takira Siyama tace duk yanda zaayi tafito yanzu suhadu a gidan Firdausi dif takashe wayar,tafiyar minti goma ne yakaita gidan Firdausi, tana parking Siyama na parking, hanun Amnah taruk'o suka nufi cikin gidan siyama taringa tambayarsu da lafiya Alawiyya tace tadai biyo su taji koma menene, Firdausi tana zaune ahakimce akan kujera tana Dana remote yar aikinta na goge goge, ganin su Alawiyya sun shigo da sallama ga Amnah na kuka yasa ta mik'e ba shiri tace lafiya mai yafaru Alawiyya,zubewa Amnah tayi akasa tacigaba da kukanta,Alawiyya tayiwa su Firdausi bayanin abinda yafaru,sallati suka saki gabad'aya suna tafa hannu,Firdausi tace " bantab'a ganin dabba irin Al ameen ba idan ba haka ba mai abun saki anan da matarka tafita bada izininka ba," zama tayi agefen Amnah tacigaba da magana "wlh Amnah Al ameen ba mijin aure bane Sam tsakanin sati biyu ya sakeki saki biyu nan da sunan yana sanki, kwata kwata shekararku biyu da aure,zan baki shawara karki sake ki koma gidansa wlh karamar bazawara yake so ya maidaki,Alhamdulillahi da baki haihu dashi ba,Dan iska kawai,"dagowa Amnah tayi tace karki kara cewa Al ameen dan iska duk halin Dana tsinci kaina aciki Ku kuka jawomin ina zaman zama na kuka kirani ga irinta nan Ku kuna gidajen mazajenku nikuma kun kashe min aure Al ameen yanada zuciya aiki yasani fa na fito",katseta Siyama tayi tace "duk dahaka Amnah bai kamata ace duk zuciyarsa bai San darajar aure ba kina dan kuskure sai saki ya biyo baya mai ya mayar da aure ne, yanzu fa igiya d'aya ya rage,agaskiya kin nunawa Al ameen bazaki iya rayuwa ba sai dashi shiyasa yake miki haka,wlh baya sanki shawarar dazamu baki ki hakura dashi kawai idan ba haka ba ko komawa kikayi sai yakara yanke sauran igiyar," dagowa tayi da rinannun idonta tace "yakuke so inyi da San danake mishi wlh bazan iya rayuwar aure da wani in bashi ba,Al ameen na balain sona nasani kawai zuciya CE dashi da R🅰SHIN H🅰KURI," "aikuwa R🅰SHIN H🅰KURINSA zai janyo mishi ya rasaki gabad'aya kuma inya rasaki wlh nasan Wanda yafishi komai ne zai aureki kuma saurayi" Alawiyya tace tana tsaki,"Amnah goge hawayen fuskarta tayi tace "wlh duk ba wanan ba bansan mai zancewa Ummi ba waccan sakin daya min banfad'a mata ba karya na mata ga wanan ma bansan ya zangaya mata ba,wlh Ummi tanada hawan jini kulluk hak'uri take bamu da muzauna agidan mijinmu lafiya duk tsanani duk wuyan aunty Aisha da Aunty Amrah babu wacce ta tab'a zuwa gida da sunan yaji amma gashi ni danake karama anyi min saki har biyu" tafashe da kuka mai cin rai, kallon juna su Firdausi sukayi tayi sauri tazauna a gefen Amnah tace" kina nufin Ummi batasan Al ameen yasakeki dafarko ba"? Gyada kai Amnah tayi,Firdausi tace "to ya akayi kika koma"? Amnah bata labarin yanda taje gidan tayi,suka saki sallati," haba no wonder shiyasa Al ameen ya rainaki bai d'aukeki abakin komai ba ya zaayi ya sakeki ki kuma kai kanki wajensa haba wanan zubar da mutunci ne wlh kamata yayi ace kin bashi wahala kafin ki koma yaji ajikinsa,kinsan sabida ke kika kai kanki shiyasa yakara sakinki ,dan yasan bazaki iya jurewa ba sai kin kara komawa wajensa dakanki,wlh kin nunawa Al ameen bazaki iya rayuwa babu shi ba,shiyasa yake miki haka,girl friend idan kinaso ki koma wajen Al ameen tunda kina sanshi sai kin shirya narakaki wajen teacher ankama miki shi an d'aure yanda ko uwarsa CE tace ya sakeki bazai iya sakinki ba Amnah ba azama haka wlh namiji gindin jaka ne inya tashi yimiki akuyanci sai kin tsani kanki wlh shiyasa babu macen da take zama haka" Firdausi tace tana dafata,girgiza kai Amnah tayi tace"babu bin mallamai a tsarina nadade ina fad'a muku,"to inkuwa haka ne wlh bazaki koma gidan Al ameen ba inkuwa zaki koma wlh said yaji ajikinsa sosai yagane kuransa zaki koma kin yarda? Gyada kai Amnah tayi,"Firdausi tace yauwa yanzu ki kwantar da hankalinki kiyi zamanki anan ga d'aki can kiringa kwana aciki mai gidan part dinsa na sama bama zai San kina nan ba,kinga har adaidaita Ummi bazata tab'a sani ba kinji girl Friend ki kwantar da hankalinki pls muje inrakaki kiyi wanka kiyi sallah inzubo mana abinci,mik'ewa Amnah tayi tabi bayan Firdausi, su Alawiyya suka mata sai da safe,Firdausi ta dawo ta rakasu suka tafi.
B'angaren Al ameen kuwa bayan yashiga gida kuka yafashe dashi yana Dana sanin furta sakin dayayi apalo ya zube yana surutai shi kad'ai "Amnah meyesa kike wahalar Dani? meyesa bakyasan bin umarnina duk abinda zai haddasa matsala a tsakaninmu shi kikeyi" haka yayi ta surutu shi kad'ai said kace zararre,can ya mik'e yanufi band'aki ya wanke fuskarsa yad'auki mukullin motarsa yanufi gidan abokinsa Habib,yana parking yaga motarsa na fitowa da alama fita zasuyi dan dashi da matarsa ne,saukowa habib yayu yanufi wajensa,ganin haka da Al ameen yayi shima ya fito daga motar,musabiha sukayi, Habib ya zuba mishi ido,"lafiya kuwa kaganka kuwa kamar Wanda ya shekara yana jinya,"hawaye ne suka cicciko a idon Al ameen, ya kau da kai yace nakara Sakin Amnah,sallati Habib yayi da karfi yana ja da baya "Al ameen anya kanada hankali kuwa,mai ka mayar da aurene INA hankalinka ina iliminka,kake Abu kamar jahili," Habib wlh raina ne yabaci,alokacin anan ya labarta mishi abunda Amnah tayi mishi,"haba Al ameen wlh dan tafita bada izininka ba bai kamata ka saketa ba,da ranka ya baci ai da sai kabar gidan gabad'aya ahankali zaka ji ranka yarage baci, amma yanxu gashi ka dau mataki acikin fushi acikin sati biyu kayi saki biyu,wlh INA jiye maka R🅰SHIN H🅰KURINAN naka wlh zakayi Daka sani yanzu fa igiya d'aya tak ya rage,"goge fuskarsa Al ameen yayi yace"wlh sai Dana saketa naringa danasani wlh zuciya CE ta debeni,yanzu dan Allah karakani gidansu ," agogon hanunsa ya duba yace "kafara kiranta awaya ka bata hakuri inyaso said muje gobe.
[8/5, 8:54 PM] Sadnaf: R🅰SHIN H🅰KURI
Written by
💅💅 SADNAF💞
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS ( P.M.L.)
page 6
Al ameen jiki a sanyaye Yakoma gida,sai dayayi sallah,yafara kiran layin Amnah,adai dai lokacin Amnah tana kwance ta rungume pillo,Firdausi na zaune a gefenta tana d'ebe mata kewa,tana jin wayarta na wakar "wayyo mijina k'aunarka na tsumani babu kamarka a fadin duniyar nan" habawa wani irin mik'ewa tayi ta d'auko wayar,Dan tasan Al ameen ke kiranta,Firdausi da sauri ta fusge wayar daga hanunta,tace " kinada hankali kuwa mutumin daya w'ulakantaki yamiki saki biyu acikin sati biyu shi zaki daga wayarsa yanzu,haba ke kuwa kinunawa Al ameen kuskurensa yaji ajikinsa,duk wani Abu dazai hadaku yanzu ki gujeshi,inkika d'aga wayarsa yanzu wlh rainaki zaiyi amma inya sha wahala kafin ki koma gidansa wlh zaiyi shak'ar sakinki nan gaba zai kuma San darajarki," rau rau Amnah tayi da ido hawaye na zubo mata,tace" Firdausi bazaki gane ba wlh bazan iya jurewa ba ina balain San Al ameen bana k'aunar abunda zai rabamu ko na minti d'aya,nikadai nasan abunda nakeji azuciyata" tace tana share hawayen dake zubo mata tausayin Amnah ne yarufe Firdausi,tace "I know how you feel sai kin d'aure zaki iya karbarwa kanki yanci agurin Al ameen idan bahaka ba wlh bazai tab'a sanin darajarki ba" gyada kai Amnah tayi tace nagane Allah yabani ikon d'aurewa"ameen Firdausi tace awanan lokacin Kiran da Al ameen yayi wa Amnah yayi goma sha,inda akarshe Amnah taga bazata iya jurewa ba ta kashe wayar gabad'aya ta fashe da kuka, sai dakyar Firdausi ta rarrasheta,tayi shiru ta kwanta amma batun bacci awanan Daren babu shi awajen Amnah,haka ma Al ameen hankalinsa bak'aramin tashi yayi ba daya ga Amnah bata daga wayarsa ba,aranar bacci baiyi yunkurin d'aukarsa sam sai sintiri yake ad'akin yana Allah Allah gari ya waye, yaje gidansu Amnah Dan yasan bak'aramin fushi Amnah tayi dashi ba tunda gashi tak'i daga wayarsa haka yayi ta gwada wayarta yaji akashe.
Washegari karfe bakwai a gidansu Amnah tayiwa Al ameen,inda wani Almajiri ne yamishi iso yashiga gidan,a tsakar gida yasamu mahaifiyarsu Amnah a zaune tana rik'e da wani k'aramin Qurani tana karantawa,Al ameen tsugunawa yayi har kasa ya gaisheta ta amsa da faraa tana tambayarsa lafiya daga ina haka da sassafe ko dai Amnah ce ba lafiya,hakan dayaji ne yasa jikinsa yayi sanyi Dan yanzu yasan Amnah ba gida tazo ba,kakalo murmushi yayi da bai kai lebb'e ba yace mata dama dubiya yazo kusa dasu shine yace bari ya biyo ya gaisheta,addua tayi masa sosai ta nuna jin d'adinta inda akarshe ta d'auko wani Leda tabashi tace yabawa Amnah sak'o inji yayarta Amrah,karba yayi tare da godiya yayi mata sallama yafito,yana hawa motarsa ya kife kai a sitiyarin yana tunanin inda Amnah taje Dan yasan yayyenta ba a garin nan suke aure ba to ina taje, d'auko wayarsa yayi yakara gwada layin Amnah yaji still akashe,girgiza Kansa yayi cikin takaici yana mai jin haushin kansa, shawara yayi da yaje gidan Alawiyya ya duba ko tana can,aikuwa dayaje,Alawiyya CE masa tayi batazo ba ita yau takeso ma taje gidanta,Al ameen jinta kawai yayi bai yarda ba dan yasan Alawiyya aminiyar Amnah ce, kwantar da murya Al ameen yayi yana r'okonta da ta taimaka mishi ta fad'a mishi gaskiya yasan yayi kuskure,da Har yabawa Alawiyya tausayi amma data tuna irin sakin w'ulakancin dayayiwa Amnah,sai tace masa ita wlh batasan inda Amnah take ba,ahaka ya juya ya nufi gidan abokinsa Habib Dan bai San sauran gidan k'awayen Amnah ba.
Amnah kuwa bacci barawo dayayi nasarar saceta,mafarkin Al ameen tayi ta yi yana kuka yana bata hak'uri data farka da kuka ta tashi,adai dai lokacin Firdausi tashigo bayan ta sallami mijinta yatafi aiki tashigo ta duba taga ko Amnah ta tashi,ganin Amnah a zaune tana kuka ne yasa tayi sauri tak'arasa wajenta tana tambayarta lafiya,anan Amnah ke labarta mata mafarkin datayi da Al ameen, kwantar mata da hankali Firdausi tayi tace mafarkine kawai,inda Amnah tace"nasan Al ameen yana cikin damuwa dan Allah kibarni in daga wayarsa bazan iya jure ganinsa cikin tashin hankali ba,"au haka zakice ai gashi shi ya jure yanaso yaganki acikin tashin hankali,ki tashi kiyi wanka ni inzubo mana abinci,"Firdausi tace tana ruk'o hanunta,cikin yan mintuna Amnah tayi wanka tafito ko mai bata shafa ba ta zura doguwar rigar da Firdausi ta ajiye mata akan gado tasa,ta zauna ta janyo wayarta ta kunna,aikuwa yana kunuwa kiran Umminta ya shigo hankalinta bak'aramin tashi yayi ba,data ga k'iran mahaifiyarta,d'aurewa tayi ta daga tayi amsa sallamar da ta mata cikin kinkina,Umminta tambayarta tayi da taga sakon da Amrah tabayar abata,eee kawai tace Dan bata San wane sako take fad'i ba anan Ummi ke fad'a mata ta d'auka wani matsalar ne data ga Al ameen da sassafe Ashe biyowa yayi su gaisa,eee kawai Amnah tace tana zare ido dan Sam bata gane inda zancenta ya dosa ba,jin mahaifiyarta na yaban halin Al ameen dakuma ta rik'e aurenta da kyau duk abunda tagani mai dadi ko Mara dadi tayi hakuri karta sake ta bijirewa umarnin Al ameen,kuka ne yaso ya kubuce mata,amma ta d'aure tace insha Allahu,ahaka tayi mata add'uoi sukayi sallama tana kashe wayar Amnah tafashe da kuka dan sai yanzu tagane Al ameen yaje gidansu,kiran Al ameen daya shigo wayarta ne yasa ta rungume wayar tana kuka,Dan jin kiran take a zuciyarta amma takasa dagawa,ahaka Firdausi tashigo yar aikinta na biye da ita abaya da faranti ahannu,juyawa tayi takarbi farantin tacewa mai aikinta ta tafi,wajen Amnah tak'arasa tana mai bata hakuri,anan Amnah ke mata bayanin abunda ya faru Wai tabarta ta d'aga wayar tunda Al ameen yaje nementa girgiza kai Firdausi tayi tace ba yanzu ba sai yasha wahala sosai,plate ta tura gabanta shak'e da Chips da kwai tahada mata shayi tace tasha kau da kai tayi tace bata jin yunwa a lokacin Al ameen yamata miss call yafi a k'irga shigowar text message ne yasa Amnah ta Mik'e cikin rawar jiki ta bud'e tafara karantawa,tana murmurshi tana kuka,Dan Al ameen text yamata masu sanyayya zuciya yana nuna mata irin San da yake mata dakuma nadamar sakinta dayayi,ahaka yayi ta turo mata text masu kashe jiki inda Amnah taringa r'okon Firdausi tabarta tayi mishi reply tace sam bayanzu ba.
Al ameen kuwa gabad'aya ya susuce yarasa inda ke mishi dadi,ya rame yayi bak'i inyaje kasuwa waje d'aya yake samu ya zauna yayi ta tunanin Amnah sati biyu kenan da rabuwarsu amma jiyake yafi shekara biyar da rabuwa da ita, bikin wani abokinsu zaayi Faisal shima yataka rawar gani sosai a bikin Al ameen, zirga zirgan dasukeyi ne na shirye shiryen bikin ne yasa Al ameen yarage damuwa sosai,Faisal shine Wanda zai Auri kanwar Firdausi shamsiyya,suma bazama suke ba kullum cikin fita kasuwa suke hakan ne yaragewa Amnah damuwar datake ciki dan sune kan gaba wajen shirya bikin dayake Amnah akwai San biki, gashi yanzu mai hanata basa tare ballantana yahanata rawar gaban hantsi,anan Tasha Al washin ba event din dabazataje ba Dan dinki iri d'aya Firdausi tayi musu Har agama bikin.
[8/5, 8:54 PM] Sadnaf: R🅰SHIN H🅰KURI
Written by
💅💅SADNAF💞
Page 7
Sati uku kenan da rabuwar Al ameen da Amnah,Al ameen bak'aramin rama yayi ba duk Wanda ya sanshi a da inya ganshi yanzu sai yasan yana cikin damuwa,d'auriya kawai yake,mahaifiyarsa ma sai data gane akwai abinda yake damunsa,Dan dayaje gaisheta sai data tsorata da yanda taganshi,ba irin tambayar da bata masa ba akan yagaya mata damuwarsa yaki yace ba abinda yake damunsa baya jin dadi ne,b'angaren Amnah ma haka amma ita tata damuwar dasauki,saboda tana shiga cikin mutane kuma shirye shiryen bikin da sukeyi yasa batada lokacin zama tayi tunanin amma can k'asan zuciyarta tana nan da tunanin Al ameen duk dare sai tabud'e texes d'in da Al ameen yake turo mata ta karanta,su ke deb'e mata kewa daddare,wani sa'in har d'aukar wayarta take tayi hidden number takirashi inya d'aga taji muryashi dadi yabi ya isheta sai taji damuwar datake ciki ya ragu,ahaka suke cikin wanan halin har aka fara bikin k'anwar Firdausi shamsiyya da Faisal abokinsu Al ameen, tunda aka fara bikin bawanda Al ameen yaje Dan bayaso kwata kwata yashiga cikin mutane,yafiso ya keb'e shi kad'ai,inda ita kuma Amnah tunda aka fara bikin take cikin farinciki Dan mace ce ita mai San ado da kwalliya taga kuma intayi adon yazamana biki zataje,kyau iya kyau kam Amnah tayi Dan su hudun nan sai dasuka sha gyaran jiki, dayake Amnah black beauty ce sai gyaran jikin yafito da ainihin kalarta,tun ranar talata aka fara biki, inda su Amnah sune kan gaba awajen sabida Firdausi kusan ita ta d'auki nauyin yin event guda biyu sai biyu da ango yahada shima,abinda yayi daga kan Firdausi Alawiyya Amnah da Siyama babu wacce tayi k'aramin shiga shiga suka ringayi na kece raini tunda aka fara bikin, sister eve da Firdausi tahada ran Saturday kiran ango tayi tace shi kad'ai suke so yaje gurin sai abokanansa guda biyar, hakan kuwa akayi,Faisal samun abokanansa yayi Wanda yake ji dasu su biyar ciki harda Al ameen, dakyar suka shawo kan Al ameen yace zaije Dan ce musu yayi bayasan zuwa ko ina ganin ran Faisal ya baci ne yasa ya amince da zaije,ranar Saturday kuwa karfe bakwai aka fara gudanar da biki, inda su hajiya Firdausi suka sa wani rantsattsan material mai kyaun gaske,Firdausi da Amnah shiga iri daya sukayi,siyama da Alawiyya shigarsu ma iri daya fad'ar kyaun da Amnah tayi awanan lokacin bata baki ne,Dan kalar material din orange da baki bak'aramin kyau ya mata ba,Dan k'aramin net ta yafa tasamu waje d'aya ta zauna Dan acikinsu hud'u itada Siyama keda Dan nutsuwa,amarya ta Dade da zama a high table,ango bai karaso ba da abokanansa hakan ne yasa Firdausi kiranshi taji lafiya mai yahanasu k'arasowa tundazu,hakuri Faisal yabata da gasu nan sun kusa k'arasowa nan kuwa Al ameen ne yake ta bata musu lokaci Dan shi hanya yake nema kawai dazai ki zuwa ganin sun Riga sun sako shi agaba ne yasa ya tashi ya shirya cikin wani bugaggen shadda fari da bak'i yasa bakin hula da takalmi shima yayi kyau babu laifi ahaka suka fito suka nufi wajen bikin,da isarsu Hall din suka nufa,Al ameen yace su shiga yana zuwa bari ya amsa waya,daga amsa wayar zama yayi akan motar ya bude gallery yana kallon hoton Amnah Dan aikinsa kenan,ciki kuwa da isowar ango cigaba akayi da gudanar da biki cikin tsari, inda su Firdausi keta kaiwa da kawowa,ango da amarya na fitowa tsakiyar fili su Amnah suka je suka musu liki suka koma suka zauna itada siyama sai hotuna suke adai dai wanan lokacin Al ameen yashigo Kansa tsaye filin ya nufa yaje yaringa musu liki yana gamawa yafita waje ya zauna akan mota,kiran wayar daya shigo wayar Amnah ne ya katse musu hotunan dasukeyi,ganin yayarta Amrah ke kiranta ne yasa ta mik'e tayi waje Dan ta amsa,waje tasamu kusa da wani mota ta tsaya ta daga wayar tareda sallama,anan suka gaisa suka fara hira,Al ameen dake zaune akan mota,yana danne danne a wayarsa kamar cewa akayi ya d'ago karaf idansa ya sauka akan Amnah dake tsaye tana ta k'yalk'yala dariya,murje idonsa yayi Dan ya tabbatar da idonsa ba gizo yake masa ba,durowa yayi daga kan motar daya tabbatar da idonsa ba gizo yake masa ba,taku hud'u yayi yaje gaban Amnah adai dai lokacin da Amnah tagama waya tana k'ok'arin komawa ciki,ganin Al ameen agabanta ya zuba mata ido kamar maye ne yasa taja da baya dasauri tana kallonsa,Dan bata yarda Al ameen bane,jin datayi yakira sunanta da Precious yasa ta tafi da gudu ta rungumeshi tareda fashewa da kuka,wani irin kankameta Al ameen yayi kamar zai maidata ciki,ya dago fuskarta yahau mata wani irin mahaukacin kiss,da ta biye mishi amma tunawa datayi suna wajene yasa ta cire bakinta daga nashi,dasauri ya kara ruk'ota idonsa ya kada yayi ja, yafara janta yakaita cikin mota yatayar yaja mortar da gudu,Amnah kuwa duk a tsorace take Dan kamar ba Al ameen ba yabi ya susuce,yana tuki yana mata kiss ahaka suka k'arasa gida,ko kofar motar bai tsaya rufewa hanun Amnah yaja kawai sukayi ciki,tun a Palo yaringa aika mata sakonin mai wuyan fassaruwa Amnah data Dade tana missing din Al ameen tuni ta biye mishi,Sadnaf tuni itama tayo waje Dan wanan wasan manya ne,a takaice aranar ba bacci awajen wanan masoya,sai karfe ukun dare suka dagawa juna k'afa Dan tunda suka auri juna wanan shine karo na farko da zasu rabu har tsawon sati uku basa tare,tare sukayi wanka suka yi alwala suka zo suka rama sallolinsu,bayan sun idar,Al ameen ya durkusa agaban Amnah tare da kamo hanunta,sai daya mata kiss a goshi yafara magana" Precious pls karki kara min irin wanan hukuncin wlh sai ayau na dawo dai dai bazan iya rayuwa babu ke ba,Amnah ina masifar sanki nayi nadamar sakin Dana miki tun aranar na maidaki pls ki ringa gudun bacin raina inada masiffaffen zuciya,wlh zan iya mutuwa ina rasaki gabad'aya saura igiya d'aya da rage a tsakaninmu ki taimaka min Dan Allah murike igiya nan gam, nayi alkawari zan nakai zuciyata nesa,pls" yace yana rungumeta,itama durkusawa tayi agabansa tace Al ameen we are meant for each other San danake ma yafi wanda kake min domin wlh dani keda ikon saki duk abinda zaka min bazantab'a sakinka ba dan Allah Dan Annabi Habibi karinga kai zuciyarka nesa R🅰SHIN H🅰KURINKA zai janyo mana mu rasa juna gabad'aya yanzu saura igiya d'aya kana yanke shi shikeknan bamuda wani chance din sai dai ka auri wata na auri wani "shhhhhhh yace dasauri yana kamo kafad'arta "insha Allahu kece mata ta har a gidan aljana kidaina kawo mana rabuwa,you are meant for me alone,jikinnan naki nawa ne ni kad'ai bazan tab'a bari ya subucemin' ba yace yana shafa jikinta, Dana ga ranar da zaki zama mallakin wani yaji abinda nakeji ajikinki gwara naga mutuwa ta promise me Amnah bazaki tab'a rabuwa dani ba," I promise " Amnah tace tana murmurshi rungumeta yayi sosai yace "I love you" tace "love you too" daganan fa duniyar ma aurata suka kara lulawa.
So akwai dadi inkayi dace da Wanda yake K'aunarka kake K'aunarshi babu abinda yakai moment dinan dadi but unfortunately R🅰SHIN H🅰KURi kan janyo mana mu rasa junanmu fans, readers, kubiyo SADNAF KUSHA LABARI COS THIS IS TRUE LIFE STORY SO TOUCHING❤
[8/5, 8:54 PM] Sadnaf: R🅰SHIN H🅰KURI
Written by
💅💅 SADNAF💞
*IN DEDICATION TO ALL ADCHOST STUDENTS ONE LOVE KEEP US TOGETHER*❤❤❤
PURE MOMENT OF LIFE WRITER (P.M.L.)
Page 8
Can b'angarensu Firdausi kuwa neman Amnah suka ringayi basu ganta ba cikin tashin hankali sukayi ta kiran layinta yana ringing bata d'auka ba,a lokacin kuwa wayar Amnah nacikin motar Al ameen,Firdausi hankalinta yafi nakowa tashi dan tunani taringayi ko saceta akayi daga zuwa amsa waya a waje, Alawiyya ce ta kwantar musu da hankali tace watak'ila
Wajen Al ameen ta tafi dan hanya take nema dama, hakan da Firdausi taji ne yasa tace inkuwa hakane Amnah tayi asara tunda takasa hak'uri a k'watar mata 'yancinta da wanan bacin ran aransu aka gama biki inda Firdausi tasha al washin indai gobe takirata still bata d'aga ba zasuje gidanta su duba.
Washegari sai k'arfe goma sha d'aya su Amnah suka tashi daga bacci dan sun dade basuyi bacci mai cike da nutsuwa irin wanan ba,tare sukayi wanka,suka shiga kitchen suka had'a breakfast,sukaci,sai da Al ameen yaci ya k'oshi ya tuna wayarsu na cikin mota,tashi yayi ya d'auko musu wayar,zama yayi yana duba yawan miss call din dasu Firdausi sukayiwa Amnah,d'agowa yayi ya kalli Amnah yace" Precious ki gaya min gaskia agidansu wa kika zauna damuka rabu"? Amnah dayake she is straight forward bata b'oye mishi komai ba tafad'a mishi a gidan Firdausi ta zauna takuma labarta mishi taso ta nemeshi su suke hanata",girgiza Al ameen yayi nan da nan ransa ya b'aci,kiran sunanta yayi ta amsa jiki asanyaye "kina so muzauna dake lafiya? gyad'a kai Amnah tayi,Amnah wlh wayanan k'awayen naki ba k'awayen arziki bane,so suke su kashe miki aure, suna so su rabamu,idan bahaka ba Amnah su yakamata sufara Neman yanda zasu shiryamu,amma dayake yan iska ne su suna zaune anasu gidan mijin ke kuma suna so ki zauna a gidansu,Precious pls idan kina sona ki watsar da k'awayen nan naki zan maye miki gurbunsu,su suke dagula miki lissafi ni nasan duka mazajensu sunfini wadata,amma kema kinsan ina iya bakin k'ok'arina dan naga baki nemi komai kin rasa ba,yau da gobe ta wuce wasa nasan baki damu da finki dasukayi ba amma kinsan zuciya wataran zaki iya fara hangen daular dasuke ciki," dasauri Amnah ta d'ago tana kallonsa,"haba Al ameen kasan kuwa hangen niimar da Allah yayiwa wasu ba halina bane dan ni ina godewa Allah a matsayin daya ajiyeni," "karkiyi misunderstanding dina Amnah yau da gobe wanan k'awayen naki tsaf zasu iya samun nassarar hure miki kunne, dan Allah ki rabudasu indai kinasan farinciki na," hawaye ne yahau zubowa Amnah tace" kasan tare Muka taso dasu tun a secondary school sabida k'awancanmu iyayenmu suka kulla zumunci,yanzu tashi d'aya Habibi sai ka rabani dasu,takarasa zancen tana fashewa da kuka,rungumeta yayi yahau share mata hawaye,yace "Amnah ba rabaki zanyi dasu gabad'aya ba kiringa baya baya dasu dan Allah kidaina bari suna shiga jikinki sosai kinji,gyad'a kai tayi yace yauwa precious dina, mik'ewa yayi dan ya tayar musu da engine dan basuda chaji awayoyinsu,ganin yabar palon ne yasa Kausar ta mik'e dasauri tanufi d'akinta,ta turawa Firdausi text da zata kirata anjima sun daidaita da Al ameen yanzu haka ma tana gidanta,kashe wayar tayi bayan ta tura text din,tafito Palo tasamu Al ameen, aranar Al ameen ko waje bai leka ba dan yanda yake tarairayar Amnah ko lokacin da take amarya baiji da ita haka ba.
Firdausi kuwa tana ganin text din da Amnah ta turo mata ranta bak'aramin baci yayi ba su siyama suka ce mai nata aciki tazuba musu ido indai namiji ne zai mata halin nasu dahaka suka tattara Amnah suka watsar.
Al.ameen kuwa soyayya dasuke zubawa da Amnah ba a magana dan kowane acikinsu so yake yaga yafarantawa dan uwansu rai,dan Al ameen motarsa yabarwa Amnah yakoya mata yanda ake driving,ita take zuwa ta saukeshi a kasuwa adawowa sai yadawo a ana haya ba yanda batayi dashi akan yabari sai yasamu kud'i yasiya mata nata motar,yaki,ahaka suke zaune cikin so da kulawa kowane yana gudun bacin ran dan uwansa duk da harshe da hakori ana samun sabani, Al ameen yana k'ok'arin kai zuciyarsa nesa, itama tana kafa kafa da abinda zai bata masa rai,watarana bayan Al ameen yafita kasuwa Amnah tagama aikace aikacenta tana kwance a Palo suna chattn da habibinta dan indai yaje kasuwa sunta chattn kenan suna video call,sai dai in customers ne suka mishi yawa shine zai ajiye waya dan ya sallamesu,sallamar su Firdausi ne ya katse mata chattn din datake,da murna taje ta rungumesu d'aya bayan d'aya dan ta Da
dade bata gansu ba,cikin rawar jiki taringa kawo musu kayan motsa baki,sukuma binta kawai suke da kallo dan wani kib'a suka Kara ganin tayi,zama tayi a gefen Firdausi tace " wanan kallo haka dakuke bina dashi sai kace Baku sani ba,"murmushi Alawiyya tayi tace gani mukayi kinyi kib'a kinyi haske shiyasa muke kallonki," kwanciyar hankali nasamu shiyasa kuka ga na canja,tab'e baki Firdausi tayi tace "kwanciyar hankali kika samu mana tunda mijinki ya rabamu dake karfi dayaji,yanzu fisabilillahi Amnah haka zaki zubawa Al ameen ido yaraba dangantakar dake tsakaninmu,yazo yagamumu tare amma kibari ya rabamu," Amnah daga mata hannu tayi tace " Firdausi dan Allah kubarni na zauna a gidan mijina lafiya yanzu yafi kowa kusanci dani shi zanbi nasamu aljanata,karku manta igiya d'aya yamin saura yanzu,dole inyi taka tsantsan ina biye muku zan iya rasa aurena,girgiza kai Siyama tayi cikin takaici tace "yanzu Amnah kina nufin mune shaidanun dazasu kashe miki aure, babu matsala zamu tafi bamu zo da niyyar kashe miki aure ba so da k'auna yakawo mu bamusan mun zama annoba ba,kutashi mutafi kafin mu kashe mata aure, Siyama tace tana mik'ewa tsabar takaici Firdausi kasa magana tayi mik'ewa sukayi, sukayi waje Amnah ta bisu da gudu tana basu hakuri akan bahaka take nufi ba dak'yar Alawiyya tashawo Kansu Firdausi suka hakura ciki suka koma suka tab'a hira Amnah ta musu girki sukaci,anan suke ce mata zaayi bikin wata kawar Firdausi yar gidan chairman suna gayyatar ta karta yarda tayi missing din bikin dan zaayi shagalgula sosai,cemusu tayi zata gayawa Al ameen inya barta zataje inbai barta ba ba Inda zataje dahaka sukayi sallama suka nufi gidajensu.
0 comments:
Post a Comment