Tunda su Firdausi suka tafi,Amnah tafara tunanin yanda zata shawo kan Al ameen batare da ta fuskanci wata matsala ba,dan agaskiya bata so taga tayi missing din event din tunda taji yar gidan Chairman ce zatayi aure,ko bama haka ba Firdausi da manyan mutane take huld'a ga kayan dasuka nuna mata awaya zasu siyo su sa aranar tasan indai Al ameen yabarta taje gaskia bak'aramin dadi zata ji ba,ahaka taringa sak'a da warwara sai wajen biyar ta tashi tashiga kitchen ta d'ora favourite d'in da Al ameen yafiso,bayan tagama tafito ta shek'a kwalliya da wani English wears d'in da Al ameen ya siyo mata,dan Al ameen magriba agida take mishi,aikuwa karfe shidda da rabi agida tayiwa Al ameen, akwance ya sameta akan kujera idonta a rufe tana Jan carbi,sallamarsa datajine yasa ta mik'e dagudu taje ta rungumeshi dan irin welcoming din datake masa kenan tunda sukayi aure bata taba canjawa ba koda kuwa fada sukayi shiyasa Al ameen yake mutuk'ar Santa dan wasu matan insukayi aure ana gama cin amarci shikenan,yanda zasu kula da miji ma basu sani ba,shiyasa baya tab'a gajiya da Amnah light kiss yamata ta cika shi tana k'arbar Leda hanunshi tare da mai sannu da zuwa,zama yayi akan kujera ya d'orata akan cinyarsa yace" love of my life gaskia kinyi k'yau kayan nan sun amsheki,kyanta na biya kud'in wankan nan" yace yana shafo k'irjinta murmushi tayi tacire mishi hular kanshi ta tashi daga cinyarsa tace"muje kayi wanka kayi alwala ankusa kiran sallah,hanunshi taja suka nufi band'akin.
Karfe tara na dare bayan sun gama cin abinci,suna hira Amnah tayi mishi zancen bikin dasu Firdausi suka gayyaceta,ta rok'eshi da dan Allah yabarta taje tunda tana k'ok'ari taga ta faranta mishi dan Allah itama ya faranta mata ta hanyar barinta taje, tunda tafara magana yayi shiru,jin datayi yayi shiru ne yasa jikin Amnah yayi sanyi,tashi yayi ya zauna ya zuba mata ido,"dana fita su Firdausi suka zo"?tambayar da Al ameen yamata kenan ta sunkuyar dakai can ta d'ago tace mishi "eee kana fita ba jimawa suka zo,murmushi yayi yace "Amnah kinsan me haka kawai jikina yake bani wlh k'awayen nan naki zasu saki kiyi abinda zakiyi nadamarsa fatana dai Allah yasa karsu rabamu,
yaushe ne bikin",d'agowa tayi da sauri tana kallonsa da murmushi a fuskarta tace "on 28 of this month," "Allah yakaimu rai da lafiya yace yana k'ok'arin maida kansa kan cinyarta,kafad'unsa ta rik'e tace Habibi kana nufin zaka barni naje,"? "Zan barki kije amma da sharad'i d'aya event d'aya zakije" take murna datake Yakoma ciki, dan ta d'auka zai barta taje duka,dan yanda su Firdausi suka bata labari duk event d'in da zaayi babu na banza,k'irk'irar murmushi tayi tace mishi ta gode, Al ameen kuwa yayi deciding ne kawai zai barta taje badan ransa naso ba dan kawai ya faranta mata rai.
Washegari Amnah kiran Firdausi tayi awaya tafad'a mata yanda sukayi da Al ameen, anan Firdausi tahau cewa ina laifi acikin event hud'u yabarta taje d'aya anan tahau cemata karta yarda tayi missing din main event din dan gaskia bak'aramin haduwa zasuyi ba yanzu haka ma su siyama take jira su shiga kasuwa su siyo kayan dazasu sa aranar indai tasan zata je tasiyo da ita,batare da tunanin komai ba Amnah tace tasiyo harda ita,zata San yanda zata tsara Al ameen yabarta taje dahaka sukayi sallama.
Lokacin biki nata k'aratowa Amnah nata neman hanyar dazata bi Al ameen yabarta taje event biyu,inda shi kuma Al ameen yasiyowa Amnah wani tsadadden less da takalmi da jaka yace ta sa ranar bikin,ana saura kwana hud'u bikin su Firdausi suka kai mata katin da gate pass din event d'in dasuke ji dashi, dan bakowa aka gayyata ba sai Wanda ya isa, suka kuma bata material din dasuka dinka mata da komai nashi ganin hakan da Amnah tayi hankalinta ya tashi taringa adduar Allah yasa inta gayawa Al ameen yabarta. Al ameen daya dawo katin bikin ta nuna mishi yagani ya k'arba yana karantawa tundaga ran laraba zaa fara har zuwa asabar na ran asabar din Amnah keta addua Allah yasa Al ameen yabarta taje,duk partyn na dare ne, iya kamu zaayi on Wednesday kuma shi kadai zaayi da yamma k'arfe biyar, batare da ya d'ago ya kalleta ba yace "na ran Wednesday zakije dan naga alamar shi zaayi da yamma" yakarasa zancen yana mik'a mata katin bata k'arba sai cewa tayi "Habibi dan Allah kabarni naje guda biyu na laraba da asabar d'in pls karka hanani" d'agowa yayi fuska a d'aure yace "baki godewa Allah ma dana barki zakije Kamun ba kenan,Amnah wai yaushe zakiyi hankaline,ko har yanzu kin d'auka ke buduruwa ce, inaga dan baki haihu ba shiyasa har yanzu bakiyi hankali ba,inda bakida aure zaki iya zuwa duka, amma da aurenki kiringa Abu kamar buduruwa ina laifin guda d'aya dana barki kije,kinsan nabarki ne dan na faranta miki bawai dan inaso ba,amma dayake bakida tunani kinzo kina cemin inbarki kitafi guda biyu", Al ameen ta Inda yake shiga batanan yake fita ba,hakuri tayi ta bashi,akarshe ta tashi tabashi guri dan idan yafara fad'a kamar ya ari baki,kasancewar Amnah wayayyace tasan hanyar datake sauk'o da Al ameen inya hau,ahaka tasamu ya sauk'o kamar babu abinda yafaru,amma a Zuciyarta tana tunanin hanyar dazata bi taje event d'in ran asabar.
Ahaka aka fara bikin ran laraba karfe hud'u da rabi Al ameen yaje ya sauketa a inda ake kamun yace mata zai dawo ya d'auketa da magriba, Su Firdausi suna hangota sukaje suka rungumeta suna murnar ganinta inda ita batasu take ba had'uwar gurin ne ya girgizata, sukawa suna ganin haka suka jata gefe suka hau tsarata da ai bata ga komai ba sai ran asabar karta yarda tayi missing,anan ta kwashe yanda sukayi da Al ameen tafad'a musu,tace babu yanda ta iya sudai tayata da addua,ahaka suka cigaba da zugata har Alawiyya nace mata tabari suje gurin teacher aka mata Al ameen ya barta taje tak'i,ahaka akafara gudanar da kamun Wanda ya mutukar burge Amnah taji dama Al ameen kar yazo d'aukarta sai angama,ana kiran sallahr magriba Al ameen yakirata awaya data fito su tafi kaya Nik'i nik'i da aka raba a kamun su Firdausi suka rakota dashi,suka gaida Al ameen suka yi musu sallama suka koma ciki,girgiza kai Al ameen yayi cikin takaici dan ana ganinsu Alawiyya ansan basuda kamun kai na matan aure da da yarda zai rabasu da Amnah da yarabasu ahaka suka k'arasa gida Amnah nata zuba tana bashi labari,jinta kawai yake.
Tundaga ranar Amnah keta tunanin yanda zata je event d'in asabar dan bata so tayi missing dan taga alamar bak'aramin Abu zaayi ba lura datayi yanda akamu kawai aka kashe kud'i,acikin wanan halin take kullum,ran Friday suna zaune da Al ameen suna breakfast dasafe aka kirashi awaya,yanda gama wayar yayi tsaki,tambayarsa Amnah tayi da lafiya anan yake cemata kawunsa ne yakirashi wai gobe yashirya ya rakashi Abuja zai je yaga ginin da ake masa ran lahadi zasu dawo,wani irin farinciki ne ya lullub'e Amnah dan tasan tasamu hanyar dazata je bikin amma afuska rau rau tayi da fuska tana cewa ita karyaje zatayi missing dinshi,rarrashinta yahau yi yana cewa tayi hakuri ai kwana d'aya ne kawai.
A daren Friday d'in haka kawai jikin Al ameen yayi sanyi yaji kamar ana kara mishi wutan San Amnah soyayya sukayi sosai aranar inda wanan masoya suka ringayiwa junansu alkawarurruka,dak'yar suka rabu washegari dan Al ameen har cewa yayi yafasa tafiyar sai da kawunsa yabiyo ta gidansa ya d'aukeshi suka wuce.yana tafiya Amnah ta daka tsalle tana Murna tuni ta shirya kayanta ta nufi gidansu Firdausi da zumar gobe da sassafe zata dawo.
Al ameen kuwa dasuka isa abuja abinda kawunsa yaje yi k'arfe biyu suka gama,Al ameen kuwa dayaga haka sai yace mishi shi aranar zai juya,kawunsa tsokanarsa yaringayi da kawai yace bazai iya kwana ba Amnah ba,ahaka sukayi sallama Al ameen yajuyo da yayi niyyar kiran Amnah yagaya mata yana hanya yafasa yace bari yayi surprising d'inta da magriba ya k'araso gida ga mamak'insa sa i yaga gidan a kulle,atake ransa ya baci ya bud'e gidan ya shiga ya zauna apalo zuciyarsa na tafasa.
Amnah kuwa hankalinta kwance suka shirya suka nufi dinner sun sha makeup,suna isa taciro wayarta tayiwa Al ameen text kamar haka *Habibina ina nan ina zazzabin rashinka atare dani nayi missing d'inka sosai wayata babu chaji zai iya d'aukewa kowane lokaci,zan kashe wayata insa a chaji ina kuna zan kiraka miss you my heart desire*tana gama turawa ta kashe wayar.
Al ameen daya dafe kai sabida nauyin daya masa dishi dishi ma yaringa gani dan bacin rai shigowar text message wayarsa ne yasa ya d'auko wayar,yana gama karanta text d'in ya wurgar da wayar ya tashi a fusace yanufi d'akinsu yajanyo drawern mudubi yana Neman invitation card d'in da aka kawowa Amnah,a can k'asa ya zakulo katin yaduba sunan gurin da ake event d'in, yayi waje dagudu,yaja motarsa a 360 yanufi wajen bikin.
😭😭😭😭😭😭 Readers ya Amnah zatayi intaga Al ameen.
[8/5, 8:55 PM] Sadnaf: R🅰SHIN H🅰KURI
Written by
💅💅SADNAF💞
PURE MOMENT OF LIFE WRITER (P.M.L)
This page is for you mah one and only Aunty Khadijah yusuf ahmad(the chooseen) my one nd only mass communicator may Allah continue to guide u may he shower hex blesin nd grace upon u one love keep us together💞💕💞💞
Page 10
Ikon Allah ne kawai yakai Al ameen gurin dan wani irin tuk'in ganganci yaringayi yana isa, wajen yanuna wa wasu yan sanda biyu dasuke tsaye a bakin k'ofa katin bikin dan su barshi ya shiga, dayan ko kallonsa baiyi ba dan yaga alamar Al ameen dan rainin hankaline shi dazai zo da gate pass sai yazo musu da katin gayyata,d'ayan ne ma yace mishi ba wanan katin ne gate pass ba yaje ya samo gate pass sai subarshi ya shiga ciki,kasancewar Al ameen ransa a mutuk'ar bace yake dan jikinsa har wani rawa yake, burinsa kawai ya shiga ciki,wani kallon w'ulakanci yamusu yace musu dan Allah su bashi hanya ya wuce suna bata mishi lokaci,wani irin mari d'an sanda nan ya gaura mishi ya d'auki sandar hannunsa yana so ya buga mishi,d'aya dan sandan yayi sauri ya hanashi, awanan lokacin da zaa a iya bud'e zuciyar Al ameen agani wani irin tafasa yake kamaninsa ma ya canja,kan motarsa ya koma ya hau ya zauna,ciki kuwa Amnah hankalinta kwance suke shagalinsu taro yayi taro manya manyan Al hazawa ne awajen tunda su Firdausi suka shigo wajen wani Alhaji yasawa Amnah ido,dan duk a tunaninsa yan mata ne duba da irin shigar dasukayi,dan siririn net suka yafa su Firdausi har da bazo da gashi,kayan jikinsu ya damesu.
(hattara matan Aure yan gayu wayayyu muna kuskure bamu sani ba,dan yanzu abun mamaki ba a iya banbance buduruwa da matar aure,dan wlh akwai matar auren da kwata kwata baka isa kagane matar aure bace sabida shigarta bai nuna ita d'in matar aure bace,wai matar aure ce zaka ga ta kashe d'auri ta yafa mayafi a kafad'a tasa damamun kaya sai kamshi ke tashi a jikinta,tahau kan titi tana rangwada,wai nan matar aure ce wa kikeso ki burge yar uwa? Ki killace kanki kiringa taya mijinki kishi ta hanyar killace kanki inkikayi haka aganina shine kika waye dan kinsan mai kikeyi muna kuskure babba dan bamu sani bane ,mijinki kawai yakamata yaga adonki ki darajar auren dake kanki muringa gyara irin shigar damukeyi Allah yabamu ikon gyarawa Ameen)
Tunda suka Zauna Alhajin nan ya ringa kiftawa Amnah ido yana mata signa harara ta watsa mishi ta kalli su Firdausi tace " kiga wani dan iska acan sai kallona yake yana min magana da ido,nifa Dana San haka maza zasuyi yawa da banzo ba wlh dan gaskiya Al ameen yanada masifar kishi nima ina tayashi kishin kaina ni sai da muka zo ma nayi dana sani dubi shigar damukayi fa dan Allah,gaskiya goma nayi mutafi dan inaso na kira Al ameen,"katseta Firdausi tayi tace "kedai kin fiye San miji wlh Al ameen d'in ma baya gari kinbi kin d'aga hankalinki ina ruwanki da wani mutum inya gaji ya daina kallonki yana miki magana da ido, karfi da yaji Al ameen ya maidaki yar kauye idan bahaka ba mai a cikin shigarmu," d'aura fuska Amnah tayi tace "nidai nagaya muku goma nayi zan tafi na ma fasa kwana gidana zan wuce gudun tsautsayi dan wlh kuka kara zama sillar wargaje Aurena nidaku har abada dukanku nan babu wacce igiya d'aya ya sauka nawa kuwa har biyu ya sauka," shigowar Amarya ne ya katse musu maganar dasuke ,Firdausi mikewa tayi itada Alawiyya dan su suka San Amarya,tundaga bakin k'ofa aka fara yiwa ango da amarya yayyafin kud'i dan angon ba yaro bane shiyasa kusan abokanansa duk dattijawa ne,Alawiyya da Firdausi suma sun taka rawar gani sosai wajen yiwa amarya lik'i Siyama itama wata kawarta ta hango dasukayi islamiyya tare ta Mik'e taje wajenta,suka bar Amnah ita kad'ai azaune hakan bak'aramin bata mata rai yayi ba dan yanzu take datasani bata zo gayyar sod'i ba,duk haduwar wajen sai taji ya fice mata arai sallamar Alhajin nan kawai taji akanta ya zauna a kujerar dak'e gefenta,mik'ewa tayi a tsorace tace mishi yayi hak'uri ita matar aure ce, Alhajin nan yayi murmushi yace mata shima mijin aure ne,ganin Alamar dagaske Alhajin nan yake yasa tabar gurinsa taje tasamu su Firdausi dake ta hotuna da Amarya tace musu zata tafi ita wajen ya isheta haka babu Wanda tasani sanan wanan Alhajin ya takura mata,Firdausi d'aura fuska tayi tace dududu yaushe suka zo dazata ce sutafi karfa ta manta da mota d'aya suka zo kuma yanzu ma aka fara bikin dan haka tabari anjima k'adan sai sutafi,ranta a mutuk'ar bace takoma ta zauna,agogon hanunta ta duba taga goma tayi harda rabi,haka kawai taji hankalinta ya tashi gabanta na wani irin fad'uwa wani tunani ne yafad'o mata da yanzu Idan Al ameen yadawo yau fa? yafasa kwana wani irin dukan lugude zuciyarta yakarayi tabawa kanta ansa ai da yau sunana bazawara dan babu abinda zai hana ya sakeni, sallamar da Alhajin nan yakara mata ne yadawo da it's daga tunanin data tafi,cikin fad'uwar gaba ta mik'e batare da kalleshi ba tayi hanyar waje,yan sand'a nan suka hanata fita sukace sai sha d'aya aka musu umarni sufara barin mutane suna tafiya,hankalinta kara tashi yayi tanaso ta musu magana taji wanan Alhajin yamusu magana kasancewarsa baban mutum tuni suka bata hanya tafice dasauri Alhaji nabinta a baya.
Al ameen idonsa akan agogo da k'ofa har zuwan amarya da ango yana nan gurin azaune awanan lokacin sabida tsananin bacin rai dazai ga Amnah ba abinda zai hanashi ya daketa dasu Firdausi ganin har goma ta wuce basu fito ba yasa yaji wani Abu ya tokare mishi a mak'ogaro dan ko shi dayake namiji baya kaiwa goma awaje sai gashi matarsa takai har goma da rabi awaje yanzu kenan inyayi tafiya haka Amnah zata ringa mishi,tunawa dayayi da mazan dak'e wajen ne yasa ransa kara baci,dan Al ameen yana cikin maza masu bala'in kishi shi yasa ma yake hana Amnah fita, durowa yayi daga saman motar dan yashiga ciki kota karfi da yaji ne,yana taku d'aya yaga Amnah tafito tana waige waige Alhajin nan kuma yabiyota abaya yana mata magana,wani irin jiri Al ameen yafara ji,dan shigar dayaga Amnah tayi ko buduruwa CE tayi namijin kirki bazai kulata ba azahiri kuwa kayan jikin Amnah basu wani dameta ba kawai yanayin k'irar jikinta coca cola shape ne yasa zaka d'auka kayan sun dameta,dafa motar yayi dan kar yafad'i ya zuba musu ido,AAlhaji nan kuwa bin Amnah kawai yake cikin bacin rai tajuyo tahau yimishi ihu daya k'yalleta ita matar aure ce,Alhajin nan kuwa lashe lab'e yayi dayaga tudun k'irjinta dan net d'in shara shara ne, juyawa tayi dan tacigaba da tafiya Alhajinan net d'inta ya ruk'o Amnah ta juyo ta zuba mai tagwayen mari,ta juya dan tacigaba da tafiyarta Alhajin dake dafe da kumatunsa hanunta ya ruk'o yace tasan wa ta Mara kuwa,Al ameen kuwa hanunta daya rik'e ne yasa yaji kamar ancaka masa wuka wani irin zabura yayi taku biyu yayi yaje gabansu,alokacin Amnah Nata k'ok'owa dashi akan yacika mata hannu,hankadashi Al ameen yayi dakarfi sai da Alhajin ya tuntsira,yace "baka ji mai tace bane matar aure ce," Amnah sallati tasaki da karfi datayi tozali da Al ameen daya zame mata tamkar zaki,tsalle tafara yi tana ihu data shiga uku,Alhajinan karkada jikinsa yayi yace "banga alamar matar aure bace dan shigar datayi na yan mata tayi,Idan ma mijinta ne kai kayi asara daka bari matarka ta fito ahaka dan baka kishinta," yayi tsaki yajuya ya tafi,Al ameen karkarwa jikinsa yafarayi yajuyo yana kallon Amnah,Amnah inbanda tsalle babu abinda takeyi dan tasan yau tafaru ta kare,zubewa tayi akasa ta durkusa zatayi magana,Al ameen ya janyota ya zuba mata lafiyayyun mari guda biyu,yace "Amnah na tsaneki na tsaneki nayi nadamar aurenki da aurena akanki kika fito bada izinina ba kalli shigar dake jikinki, da aurena akanki wani ya rik'e miki hannu nahakura dake Amnah" wani irin ihu Amnah taringayi tana kayi tunani Al ameen karka sakeni igiya d'aya ya rage atsakaninmu,juyawa yayi yace kije gidanku nasakeki bani bake kije k'awayenki su maye miki gurbina dan kinfi jin maganarsu akaina zanyi k'ok'ari na yakice ki araina,kalmar sakin da ya ambata ne yasa Amnah suma na wucin gadi,Al ameen kuwa motarsa ya nufa yaje ya Tayar cikin bacin rai Amnah tabishi da gudu tana kuka,tana yayi kuskure ya tuna yanzu saki uku kenan yamata,ko kulata baiyi ba,yaja motarsa ya tafi,Jan k'afa Amnah tayi ta koma gefe ta zauna a kasa tafara kuka wiwi tana danasanin biyewa su Firdausi, gashi sun kaita sun baro,ciki kuwa Alawiyya ce tafara ankara Amnah bata hall d'in tasamu Firdausi tagaya mata hankali atashe suka yo waje dan su dubata,suka hangota a sauna akasa dirshan tacire gwagwaro sai kuka take 'yan sanda nan na tambayarta abinda yasa take kuka,mik'ewa tayi dagudu tanufi wajensu tafara gaurawa Firdausi mari ta gaurawa Alawiyya zata gaurawa siyama,siyama ta rik'e mata hannu kuka tafashe dashi tace " hankalinku ya kwanta kun kashe min aure burinku ya cika Al ameen yasha gayamin in rabu da Ku sai kunzama silar wargajewar aurena naki yarda ashe dai dagaske ne nayi Dana sani biye muku danayi,Firdausi datafisu zuciya cikin tsawa tafara magana" ke dan asara sabida namiji kike tada jijjiyoyin wuya har da marina sai me dan kun rabu da uwarki kika rabu ko da ubanki ,wanan talakan mijin naki dama talauci ne ya isheshi shi yasa yasamu tab'in hankali yake saki kamar mahaukaci ki gode Allah ma daya rabaki da mai tab'in hankali",irin kukan da Amnah takeyi ne yasa Alawiyya taji tausayin Amnah ya rufeta,hanunta ta ruk'o Amnah ta fusge ta kallesu tace "nagode Firdausi mijina mahaukaci ne siyama Allah ya saka muku da alheri Ku kashe min aure Ku kuma Bini da zagi da cin mutunci" katseta Firdausi tayi tace "mufa kidaina cewa mun kashe miki aure dan bamu zo har gida mun ja k'afarki ba da k'afarki kikazo,girgiza kai tayi batare da tace musu komai ba ta nufi bakin titi, Alawiyya ba abinda batayi ba Amnah tahau suje inyaso gobe su San yanda zasuyi Amnah ko kallonta batayi ba,tasamu abin hawa ta nufi gidansu,lokacin sha d'aya da kusan rabi,lokacin ko ina tsit,sai data je k'ofar gida gabanta ya hau fad'uwa dan batasan mai zata cewa Abbanta da Umminta ba, kawai sadak'arwa tayi ta kwankwansa sai data Dade tana kwankwasa,mallam Mustapha yazo ya bud'e sakin baki yayi yana kallonta.
[8/5, 8:55 PM] Sadnaf: R🅰SHIN H🅰KURi
Written by
💅💅SADNAF💞
PURE MOMENT OF LIFE WTITERS (P.M.L.)
*THIS PAGE IS FOR YOU MY ONE AND ONLY AUNTY,AUNTY SIS💞 U ARE SUCH A NICE PERSON MAY ALLAH GRANT YOUR WISH AND GUIDE YOU THROUGH THE RIGHT PART ILYSVM*😍
Page 11
Amnah zubewa tayi akasa gabanta na dukan Tara Tara dan tasan yau kashinta ya bushe,mallam Mustapha had'iye yawu yayi da k'yar yace "ke daga ina haka da tsakar daren nan kuma ina hijabinki ko mayafi kika fito haka sai kace ba matar aure ba" ? Kuka ta fashe dashi takasa magana,muryar Umminta taji daga baya tana cewa mallam kai da waye ne ganin Amnah a durkushe akasa ne yasa gabanta ya yanke ya fad'i tasaki sallati tace " Amnah mai kike nema daddaren nan ina mayafinki kika fito haka," zoki wuce" mallam Mustapha yace yana bata hanya,dak,yar ta mik'e ta shige ciki suka bita abaya suna ayyana abubuwa aransu a palo ta zauna tacigaba da kukanta Mallam Mustapha ya zauna akan kujera yana kallonta dan shi yanada sanyi bai fiye zafi ba sosai,Umminsu kuwa data zauna sai data karanta Allahuma ajirni fi musibati wa aklifnin khairin minha aranta ta ringa addua Allah yasa ba auren Amnah ne yamutu ba,mallam Mustapha ne yace " Amnah banasan shashanci kirufe min baki kinzo kinsamu agaba kina kuka baki fad'a mana abunda yafaru ba"daga ina kike da tsakar daren nan ina mijinki yake"?ai kamar zugata yake wani kukan ta kara kwashewa dashi,wani mugun tsawa Ummi ta daka mata tace "bazakiyi magana ba sai na hambareki Mara mutunci" " bita ahankali" Mallam Mustapha yace yana kallon Amnah, dasauri Amnah tashare hawayenta dan tasan idan Ummi ta fusata batada kyau,cikin rawar murya da kinkina tace Al ameen ne yasakeni,Mallam Mustapha runtse idonsa yayi da k'arfi yana sallati,Ummi kuwa ji tayi uwa ta buga mata guduma aka,zubawa Amnah ido tayi tana nazarin irin shigar dake jikinta ahankali tace " mai yahadaku ya sakeki"? Amnah kasa magana tayi tana tunanin karyar dazatayi amma kanta ya kulle,jin an daka mata tsawa yasa ta gigice tace biki naje nakai dare,Mallam Mustapha da ba k'aramin Abu ke bata mishi rai ba idonsa kadawa yayi, yayi jajir, yanunata da yatsa yace da wanan shigar kika je biki Amnah amatsayinki na matar aure tarbiyyar da muka baki kenan"? Kuka Amnah ta fashe dashi nadama yabi ya lullub'eta Ummi kuwa kallonta kawai take jikinta na k'yarma tace " Amnah shekrarki biyu da rabi da aure har kin k'arbi takardar saki Aisha da Amrah yau shekararsu takwas da aure babu wacce ta tab'a koda yaji acikinsu amma keda kike karamar cikinsu har kin k'arbi takardar saki,kasa magana Amnah tayi sai kuka wani bakin ciki ne yarufe Ummi ta mik'e a fusace tayi waje ta d'auko muciya tayi kan Amnah bugu d'aya tayi mata Mallam Mustapha ya k'wace daga hanunta Amnah kuwa tafara ihu dan a rayuwarta tana tsoron atab'a lafiyar jikinta, Mallam Mustapha cemata yayi ta rufe mishi baki kar ta Tara masa mutane daddaren nan,shiru tayi Ummi ta zauna tace kafin ta k'irga biyar tafad'a mata gaskiyar abinda yafaru Amnah da bata iya karya ba tunani tayi gwara ta gaya musu gaskia dan batada mafita ,kasa tayi da murya tafara labarta musu tundaga sakin da Al ameen yamata da farko har karyar datayiwa Ummi da tafiya yayi,dana biyu d'aya mata batazo gida ba,da wannan na karshen da yamata bata kuma boye musu ba sai data gaya musu duk abinda ta aikata aka saketa,Mallam Mustapha mutuwar zaune yayi dayaji saki uku Al ameen yayiwa Amnah,Ummi sabida tsabar yanda mutuwar auren gabad'aya ya girgizata kasa motsi tayi dan arayuwarta ba abinda ta tsana sama da mutuwar aure shiyasa kullum cikin yiwa yaranta nasiha take dasu ringa hakuri agidajen mazajensu,ko matan auren datake koyarwa kullum nasihar data ke musu kenan a zuciye ta mik'e ta rufe Amnah da duka Mallam Mustapha kwata kwata baiyi yunkurin hanata ba dan shima abinda yayi niyyar yi kenan sai da aure da gaji dan kanta ta k'yalleta itama kukan ta fashe dashi tana Allah ya jik'an aure dan aure shima rai ne dashi, Amnah inbanda kuka babu abunda take, magana Ummi tafarayi tana kuka" Mallam kajifa fita take bada izinin mijinta ba,bata bin umarnin mijinta sai na k'awayenta Amnah ni na koyar da ita tasan girman zunubin matar data fita bada izinin mijinta ba,tana da ilimi dai dai gwargwado amma ka dubi rayuwar data zabawa kanta,k'awayen nata data biyewa suna gidajen mazajensu,Amnah ina iliminki da tunaninki" Ummi tace tana kallonta cikin tak'aici "abinda kikeso kinsamu ni banga laifin mijinki ba d'aya sakeki ke kika janyowa kanki,amma fa kisani wlh wanan shashancin ba a gidana ba kina idda zan aurar dake ko wa nasamu kuwa da ace saki d'aya ne ko biyu da sai na kira mijinki na bashi hakuri amma kuwa tunda uku ne babu yadda zaayi wlh kina idda ina aurar dake Mallam Mustapha yace yana mik'ewa cikin bacin rai yanufi d'akinsa,Ummi kuwa aranar bacci bai yi yunkurin d'aukarta ba dan bacin rai,tunanin ta kwana tanayi na R🅰SHIN H🅰KURIn Al ameen ace saki uku acikin wata biyu sai kace ya maida auren wasan yara ina ma laifi datayi mishi laifi nafarko yazo ya fad'a musu su k'irata suja mata kunne amma sai saki kawai yaringayi,Amnah ma aranar barci bai yi gigin d'aukar ta ba illa ma kwana datayi tana tsinewa Su Firdausi,ga kewan mijinta daya dameta tuna irin soyayyar dasukayi adaren da zaiyi tafiya da irin alkawarurukan dasukayi wa juna ne yasa ta fashe da kuka mai cin rai dan tasan yanzu sun rabu kenan har abada,tsaki Ummi tayi tabar mata palon dan haushinta takeji.
B'angaren Al ameen kuwa yana isa gida zazzabin mai zafin gaske yarufeshi ga ciwon kai mai tsanani ganin bashida mataimaki sai Allah ne yasa ya kira Habib adaren daya taimaka yazo ya kaishi asibiti,yana ajiye wayar yafad'i kasa daga nan bai kuma sanin inda kansa yake ba,Habib hankali atashe yazo gidan ya kinkimi Al ameen yakai shi asibiti,aka yi emergency dashi dan abashi taimakon gaggawa,sai washegari k'arfe 9am Al ameen ya farka,dasauri Habib ya ruk'o hanunsa yana masa sannu,zubawa Habib ido yayi yadawo da kallonsa d'akin yana k'arewa ko ina kallo ahankali yafara magana yana tambayar mai yakawoshi asibiti,anan Habib ya labarta mishi yanda akayi,a take ya tuna mai yafaru yafashe da kuka yana damke hanun Habib,"shikenan tawa ta kare Habib rayuwata tazo karshe nasara Rabin raina har abada narasa ta Habib,na rasata,"yace yana mai fashewa da matsanacin kuka,fusge hanunsa Habib yayi daga ruk'on da Al ameen yamasa yace "ka kuma sakin Amnah ko"? " nakuma sakinta Habib bansan yanda akayi nasaketa ba" kallonsa Habib yaringayi cikin bacin rai yace " yamaka kyau ai R🅰SHIN H🅰KURINKA yajanyo ma ka rasata har abada yanzu kana ji kana gani zata auri wani"wani irin shak'a yakai masa "insha Allahu Amnah bazata tab'a zama mallakin wani ba,idan ina rayye bazan tab'a bari ta auri wani ba sai dai ta zauna ba aure nima na zauna ba aure bazan iya jure inganta da wani ba Habib,yace yana ture Habib,tari yafarayi sosai yana shid'ewa dagudu Habib yaje yakira likita,yazo ya dubashi yamishi alluran bacci,Habib yana ganin bacci ya d'aukeshi yanufi gidansu Al ameen dan yafad'awa mahaifiyarsa Hajiya mariya dan mahaifinsa ya rasu da dadewa,yana isa gidan tafara mishi tsiya da ko mafarki take yaushe rabonsa da gidanan tun d'aurin
auren Al
Ameen bayan gaishe gaishe da kayan motsa baki tasa aka kawo masa, sai da mai aikin ta tafi Habib yafara mata bayanin abinda ke faruwa na rashin lafiyar Al ameen da rabuwarsa da Amnah komai sai daya kwashe yafad'a mata,sallati taringayi tace" yanzu Al ameen saki uku yayi wa yarinyan nan mai hankali duk nasihar Dana mishi dayaringa hakuri yana kai zuciyarsa nesa wanan zuciyartasa da R🅰SHIN H🅰kURI zai janyo mai nadama wataran aikuwa gashi yana nadamar rabuwa da matar kirki yanzu da wane ido zan kalli mallama Ummi kai Al ameen bai kyauta min ba Sam kaima Habib kayi kuskure da Baka tab'a sanar dani abinda ke faruwa ba sai da komai ya k'wab'e" haka tayi ta jimamin abinda yafaru rashin lafiyar Al ameen bai wani dameta ba kamar yanda sakin dayayiwa Amnah ya dameta shiryawa tayi suka nufi asibitin a lokacin dasuka isa asibitin Al ameen bai farka ba, haka ne yasa tace Habib yakaita gidansu Amnah da isarsu tashiga gidan da sallama a tsakar gida ta tarar da Amnah tana shara tana share hawaye dan da asuba datayi sallah baccine yafara Neman d'aukarta Ummi ta daka mata tsawa data tashi taje takama aikin gidan babu ita babu Hutu tunda takaso aurenta,tana ganin mahaifiyar Al ameen ta wurgar da tsintsiyar hanunta ta tafi da gudu ta rungumeta tana kuka.
[8/5, 8:58 PM] Sadnaf: R🅰SHIN H🅰KURI
Written by
💅💅SADNAF💞
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS (P.M.L)
Page 12
Wani irin tausayin Amnah ne yarufeta taji itama hawayen yana neman zubo mata dan tasan irin San da Amnah takeyiwa Al ameen badan kaddara ba da Allah yariga ya hukunta sai sun rabu da ba abinda zai tab'a rabasu, d'agota tayi daga jikinta tace "kiyi hakuri kinji haka Allah yarubuta sai kun rabu da Al ameen, ina Mallama Ummi take? " cikin sheshekar kuka Amnah tace tana ciki,tare suka k'arasa palon Ummi tana zaune da littafin Al Qunut ahanunta murmushi tayi ta amsa sallamar dasukayi ta ajiye littafin tana "maraba shigo daga ciki" bayan yan gaishe gaishe dasukayi na kwana biyu da basu had'u ba kasancewar sun san juna tun kafin ma yaransu su had'a alak'a, shiru Hajiya Mariya tayi tana tunanin ta Inda zata fara can sai tafara magana"Mallama Ummi wlh bansan daga Ina zan fara baki hakuri bansan abunda ke faruwa ba Sam wlh sai yau,"katseta Ummi tayi dasauri tace" haba wane irin hakuri kuma ana zaune kalau wlh haka Allah ya hukunta sai sun rabu karki wani damu mu ma nan bamusan mai ke faruwa ba wlh sai yau ashe ya dade dafara mata saki d'aya bata tab'a fad'a ba sai yau data Kwab'e mata kuma duk abinda yafaru laifinta ne Hajiya ka Haifi da ne baka haifi halinsa ba,yanzu kamar Amnah ace taringa fita bada iznin mijinta ba,"" duk dahaka Mallama Ummi bai kamata ace yayi saki dan kawai tafita bada izininsa ba shi zama na aure sai da hakuri ba karamin abu kesawa arabu ba sai dai in cutarwa tayi yawa dole sai an rabu amma Al ameen bansan halin waya d'auko acikin yayana ba Zuciyar masifa da R🅰SHIN H🅰KuRi tun yana yaro haka yake wlh shiyasa nake yawan gayawa Amnah ta guji zuciyarsa,da yanzu ta gayamin farkon sakin daya mata ai danayi mishi fad'a amma bansan mai ke faruwa ba sai da Habib abokinsa yaje yagaya min ankwantar dashi a asibiti sanan yake gayamin dalili,gashi abun haushi sai yayi abu daga baya sai yazo yana nadama,"subhanallahi Ummi tace "mai yasameshi aka kwantar dashi a asibiti Amnah dake d'aki alab'e ajikin k'ofa tana jiyo hirarsu dafe k'irji tayi tafara sallati nan da nan hankalinta ya tashi,dan tasan sabida ita Al ameen ya kwanta rashin lafiya,kasa kunne tayi tacigaba da jiyo hirarsu,Hajiya Mariya gaya mata tayi itama batasani ba dan yanzu ma haka daga asibitin take yana bacci yanzu daga nan can zata wuce takuma d'ora da " Al ameen yayi asarar mace mai hankali banji dadin rabuwarsa da Amnah ba,"Murmushi Ummi tayi tace "bakomai Allah yayi ba matarsa bace sai sun rabu"Hajiya Mariya cewa tayi dan Allah akira mata Amnah tabata hakuri,da Ummi cewa tayi ta rabu da ita wane irin hakuri zata bata tarabu da ita,ita tajawo wa kanta,dak'yar ta yarda ta k'wallawa Amnah kira tana fitowa tabar palon,hakan da Amnah tagani ne yasa tayi sauri ta matsa kusa da Hajiya Mariya tace" Hajiya ya jikin Al ameen? Mai yake damunsa?awane asibiti aka k'wantar dashi? Duk ta jero mata tambayoyin lokaci guda,wani irin Tausayin Amnah ne yarufe hajiya Mariya dan tasan bak'aramin so Amnah kewa Al ameen ba duk da ya saketa bata ji haushinsa ba,'girgiza kai tayi cikin takaici tace " Amnah kiyi hakuri Al ameen bai miki adalci ba daya sakeki duk hallacin da kika masa kika zabeshi acikin masoyanki abinda zai saka miki dashi kenan bai kyauta ba sam R🅰SHIN H🅰KURINSA ya janyo masa yayi asarar macen da samunta sai antona kuka Amnah ta fashe dashi tana tuna had'uwarta da Al ameen.
FLASHBACK
Amnah itace yar auta a gidansu Ummi mahaifiyarta yayanta bakwai hud'u sun koma sai Aisha Amrah da auta Amnah,mahaifinta Mallam mustapha yana da kanti a sabon gari,darduma carbuna su ruwan zam zam da littatafai na addini yake siyarwa sai Ummi mahaifiyarsu dake koyar da matan aure da yan mata dan Allah ya hore mata ilimin addini,shiyasa yaranta dukansu sunada shekara goma sha biyar suke sauke Al Qurani mai girma da sauran littatafai na addini,ba laifi su Amnah sun samu tarbiyya kwarai dagaske Aisha itace babba sai Amrah sai auta Amnah,Aisha da Amrah suna gama secondary school aka aurar dasu, Amnah tun tana primary Allah yamata farinjini sosai dan Mallaman makarantarsu ma sunsha zuwa wajen Mallama Mustapha suna Neman auren Amnah,ahaka Har ta isa secondary school anan tahad'u dasu Firdausi suke k 'awancensu su hud'u,had'uwarta dash Firdausi ne yasa takara wayewa ba abarinta ta kula samari amma su Firdausi sai dasukayi San yanda sukayi suka zugata taringa kula samari aboye,tana cin kud'insu dan duk tafisu samun samari masu kud'i kuma bata kyashin ta kashe musu ahaka Har suka kusa gama secondary School,akwai wani saurayinta Nazeer d'an siyasa ne yana bala'in Santa ita kuma bata sanshi kwata kwata ganin dayayi Amnah batasanshi ne yasa yabiyo ta wajen iyayenta ya d'auka irin kwad'ayayyun iyayen nan ne yahau yimusu hidima sai da Mallam Mustapha ya taka masa birki tukuna amma duk dahaka bai rusuna ba mutane daban daban yaringa turawa gidan dan su nema mishi auren Amnah,inda akarshe sai da Mallam Mustapha yace suje ya daidaita da Amnah inta yarda sai yaturo manyansa,ba yanda su Firdausi basuyi ba akan Amnah ta yards da Nazeer tak'i dan suna balain cin kud'insa haka ma ya'yyen Amnah su Aunty Aisha dan suma duk da ba agarin suke aure ba suna samun nasu rabon suna shiga Ss3 Mallam Mustapha yafara hurawa Amnah wuta data fito da mijin aure dan tana gama secondary zai aurar da ita inda hakan ya d'aga hankalin Amnah sosai ganin Ummi tahura mata wuta ne yasa tahak'ura race Nazeer yafito Wanda yake jiran kiris dama dagudu ya tura manyansa aka kai kud'in aure.
Rabo
Su Amnah sunata shirye shiryen candy,Kasuwa suka Shiga su hud'u dan su fito da ankon da zasuyi ,sai da suka gama zagaya kasuwar basu samu kayan daya musu ba akarshe wani shagon da ake siyar da su atamfofi da material harda lesuna suka nufa,kasancewar su Firdausi yangan masifa da iyayi ne dasu wani kallon hadarin kaji suka farayiwa samari ukun dasukayi gani ashagon cikin samarin kuwa harda Al ameen a lokacin yana yaron shago,abunka da mutum mai zuciya tuni yaja tsaki yaje ya samu guri yazauna dan ya tsani mata masu iyayi shiyasa maigidansa kan ce zai sallameshi dan yana kora musu customers, dan yanzu inyaga zaki raina masa hankali Tas zai sosoka ma ashar inshi kad'ai ne ashagon yafasa siyar ma da abinda kaje siye shiyasa insu Faisal suka ga yan mata masu rawar kai suke rok'onsa dayaje ya zauna,dube dune su Firdausi suka fara yi suna yatsine yatsine,Amnah kuma tasamu guri tazauna tana satar kallon Al ameen dan haka kawai tana shigowa suna hada ido taji gabanta ya fad'i yakuma burgeta,Al Ameen daya d'auko wayarsa yana dane dane d'agowa yayi dan ya hararesu,karap suka had'a ido da Amnah take gabansa yafad'i sunkuyar da kai Amnah tayi dasauri Wanda hakan yabawa Al ameen dama ya kare mata kallo take yaji yakamu da santa,kau da kansa yayi dayaga tana shirin d'agowa yacigaba da dane danensa,Amnah cewa su Firdausi tayi dan Allah suyi su zaba su tafi lokaci na tafiya,bud'ar bakin Firdausi sai cewa tayi ita shagon babu kayan daya burgeta,a zuciye Al ameen ya d'ago yace su fitar musu daga shago tunda babu kaya daya musu cike da rashin kunya Alawiyya tafara CE mishi shi asuwa zai ce su fita yana dan jiran shago,ai tuni ya mik'e yana shirin k'wada mata mari Faisal ya hanashi,Firdaui zaginshi taringayi sukayi waje, Amnah ta tsaya tana basu hakuri,ko kallonta baiyi ba har suka bar shagon,dasuka bar shagon sai da sukayi fad'a dash Firdausi wai meyesa ta tsaya tana bawa gara hakuri,tunda Amnah takoma gida inbanda tunanin Al ameen babu abinda takeyi,haka ma Al ameen duk juyin dazai yi fuskar Amnah yake hangowa,tunanin yanda zai sameta yakeyi,Wanda ita kuma Amnah sabida kamuwa datayi da sanshi sai data koma shagon ita kad'ai da sunan taje siyan atamfa,aikuwa Al ameen daya ganta jiyayi kamar anyi mishi bushara da gidan Aljanna atakaice anan zazzafan soyayya yashiga tsakaninsu inda Nazeer sukafara shirye shiryen kai kayan sa rana Amnah ta badawa idonta toka tace ita ta fasa auran Nazeer,Mallam Mustapha kuwa yace bata isa ta maida shi k'aramin mutum ba nan da nan yace Nazeer sukawo kayan sa rana,hakan kuwa bak'aramin d'agawa Amnah da Al ameen hankali yayi ba,akarshe sai da Amnah tasamu Nazeer taringa r'okonsa da ya janye indai yana K'aunarta ita bata sanshi Nazeer kuwa babu yanda zai yi haka ya hak'ura daga baya ya koma kan Firdausi aikuwa bak'aramin murna tayi ba nan da nan suka daidaita manya suka shiga zancen,Mallam Mustapha yana ganin Nazeer ya janye yahurawa Amnah wuta tafito dawani ko ya aura mata Wanda yaga dama, Al ameen cikin rawar jiki yatura gidansu Amnah duk da bashida hali alokacin sai dai yayunsa su taimaka mishi dan ko gidan kansa bashida, Amnah kuwa bata damu da rashin kud'in Al ameen ba ita kawai shi takeso dan har su Aunty Aisha gori suka ringa mata da bata da rabo dan lefen da Nazeer yayiwa Firdausi sai kowace mace tayi fatan ina ma ita tasamu Amnah kuwa ko ajikinta,kusan lokaci guda aka sa ranarsu da Firdausi inda Al ameen yagaya mata sai dai tafara zama agidansu kafin yayi gini takuwa amince lefen ma daya mata akwatuna biyu ne kaya basu fi kala ashirin ba,sai da bikinsu ya matso aka rabawa su Al ameen gadonsu inda yayi amfani da kud'in yabude nashi shagon yazuba kaya Allah kuwa yasanya masa albarka yafara samu da haka yafara musu gini sai da Amnah ta shekara agidansu Al ameen kafin sukoma gidan kansu,soyyaya suke kamar zasu cinye juna sai dai yawan fita da Amnah keyi gidan kawayenta ke cimasa tuwo a k'warya inda dayaga abin nata na Neman wuce gona da iri yafara tunanin taka mata birki.
CIGABAN LABARIN
[8/5, 8:58 PM] Sadnaf: R🅰SHIN H🅰KURI
written by
💅💅SADNAF💞
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS ( P.M.L.)
_NOTE-Masoyana ina mai Baku hakuri bazaku ringa ganin post d'ina dawuri kamar yanda kuka saba ba,sabida munyi Resuming amma in sha Allah I will try my possible best naga ina k'ok'arin posting koda daddare ne Thanks for your love and support_
Page 13
Murmushi hajiya mariya tayi tace
"Karki damu Amnah zai samu lafiya insha Allahu lokacin danaje yana bacci bansamu ganin likita bama ballantana insan mai yake damunsa yanzu daga nan can zani karki damu kinji Allah ya musanya miki da Wanda yafishi",Amnah kasa amsa Ameen tayi dan wani irin d'aci taji a makwogaronta wai finally sun rabu da Al ameen sai dai ta auri wani cije leb'e tayi tana kukan zuci,afilli kuma sai tace
" Allah yabashi lafiya Hajiya dan Allah kice ina masa sannu nasan Ummi bazata barni ba danaje na duboshi"murmushi hajiya Mariya tayi ta maida hawayen dake k'ok'arin zubo mata sabida tsananin tausayin Amnah tace
"Zaiji insha Allahu ki kula da kanki dan kun rabu da Al ameen karkiyi tunanin mun rabu kenan zan ringa zuwa ina ganinki kema inkin gama idda kiringa k'ok'ari kina kawo min ziyara kinga da Allah yayi da rabo a tsakaninku da sai nafi kowa farinciki dan zan samu sauk'in rashin ki amma ya zanyi abunda Allah ya hukunta shine dai dai bari natafi Habib yana can yana jirana zan ringa k'iranki awaya" tace tana mik'ewa Amnah itama mik'ewa tayi tanufi d'akin Ummi taje ta gaya mata Hajiya Mariya zata tafi, d'aki takoma ta kwanta tayi rubda ciki tafashe da kuka tana danasani biyewa zuciyarta gashi sai yanzu dasuka rabu da Al ameen taji kamar kara mata wutan sanshi ake a zuciyarta,k'iran wayan daya shigo wayarta ne yasa ta Mik'e ta d'auki wayar ganin Alawiyya ce Ke kiranta ta cillar da wayar ta karaci ringing bata d'auka ba,zumbur ta Mik'e ta d'auko wayar ta kira Layin Al ameen taji akashe,haka kawai takeso taji muryashi ko zataji saukin abinda takeji a zuciyarta,layin Habib ta kira yanata ringing bai d'auka ba sai data mishi miss call biyu ana uku ya d'auka gaisawa sukayi da Habib adai dai lokacin da suka isa asibiti da hajiya Mariya, wani irin tausayin Amnah ne ya rufeshi dayaji tana tambayarsa ya jikin Al ameen, cemata yayi jikinsa da sauki,cikin farinciki tace dan Allah yabashi wayar, cemata yayi yana zuwa minti biyar zai kirata ya hadasu ya kashe wayar,Hajiya Mariya tunda Habib yafara waya tasan Amnah ce,girgiza kai tayi tanufi cikin asibitin Habib ya bita abaya.
Lokacin da suka shiga d'akin da aka kwantar da Al ameen a zaune suka sameshi ya jingina da pillo duk mai tausayi inya ganshi a lokacin sai ya tausaya mishi dan tunani zakayi ya shekara yana jinya gashi yayi zuru zuru,yana ganin hajiya Mariya tashigo ya sunkuyar dakai ita kuma ta zuba mishi harara,zama tayi akan kujeran dake gefen gadon Habib shikuma ya zauna agefensa yana mishi sannu dan agaskiya duk da Al ameen shi ya janyo wa kansa yana tausayinsa.
Wlh
Hajiya Mariya ce ta katse shirun tafara magana,
Al ameen yanzu abinda kayi ka kyauta kenan ace ka saki Amnah batare da ka fad'amin ba yanzu kana ganin kayiwa yarinyan nan adalci,dan kawai tana fita bada izininka ba sai ka saketa har saki uku,mai yasa baka kai zuciyarka nesa ba,sau nawa nasha ma nasiha akan karinga hakuri arayuwarka wanan R🅰SHIN H🅰KURIN naka wataran zai janyo ma ka aikata abinda zakayi daka sani, yanzu sai hankalinka ya kwanta ai tunda kayiwa yar mutane saki uku,yarinya nan ka manta irin San datake ma ka manta tun kafin kasan zaka fara kama kud'i take zaune dakai Wanda samunta a wanan zamanin sai an tona,akan ta fita bada izininka ka zuba mata saki uku mai ka mayar da aurene? cikin wata biyu kayi saki Uku sabida bakada hankali,ina laifin sakin daka mata na farko kazo ka sanar dani inyi mata fad'a amma dayake kai dan kanka ne shiyasa kai kadai karinga yankewa kanka hukunci,yarinyar data San darajar yan uwanka duk Wanda ya rab'eka tana girmamashi amma dayake kai butulu ne sakayyar dazaka mata kenan,yamaka kyau gashi tun ba aje ko ina ba ai kana da kasani ni ina nan ina Mata addua Allah yasa tana gama idda tasamu wanda yafika yasan darajar aure ta aura".
Al ameen jiyayi kamar ta buga mishi guduma yayi sauri yace
" ba ameen ba Hajiya babu wanda ya dace da Amnah sai ni bazamu iya rayuwa batare da juna ba,hajiya bansan ya akayi na saki Amnah ba dan Allah Ku taimaka min tadawo wajena".
wani irin tsaki Hajiya Mariya taja tace
"Tunda mu ma mahaukata ne ba katab'a jin inda akayi saki uku aka cigaba da zaman aure,ai Karasa Amnah kenan har abada R🅰shin h🅰Kurinka ya janyo ma ka rasata," wayar Habib dake ringing ne ya katse mata Maganar datake.
"Ungo Amnah Ke San dubaka" habib yace yana mik'a mishi wayar.
Cikin rawar jiki Al ameen ya karbi wayar yafara magana,
"Amnah Amnah Amnah kina jina," Amnah toshe bakinta tayi dan wani kuka ne yataho mata dataji muryashi,
" Amnah nasan kina jina dan Allah kiyi hakuri ki yafemin wlh bansan ya akayi nafurta miki Kalmar saki ba,dan Allah karki yarda mu rabu kinsan bazan iya rayuwa babu ke ba pls natuba bazan Sake sakinki ba zan ringa bari kina fita ko ina"
duk maganar dayake arude yake yinta kamar ba ahayyacinsa ba,kuka Amnah tafashe dashi tafara magana"
"is too late Al ameen mun riga mun rabu R🅰SHIN H🅰KURINka ya janyo mana mun rabu babu yarda zamuyi,saki uku kayimin sai dai mu hakura da juna",dasauri Al ameen ya girgiza kai yace
Saki d'aya ne Amnah naji wani waazi ance idan akayi saki uku tamkar saki d'aya ne dan Allah karki gayawa su Ummi saki uku nayi miki" kashe wayar Amnah tayi tafashe da matsanacin kuka dan tsananin tausayin Al ameen dan yama fita hayyacinsa gaba d'aya.
Hajiya Mariya ma barin d'akin tayi dan tausayin Al ameen dan tasan bak'armin so yakeyiwa Amnah ba mutum mai zuciya irinsa kafin aga kukansa ko lokacin dayake yaro sai an sha wuya sai gashi akan Amnah yana kuka lailai so mugun ciwone,addua taringayi a zuciyarta na Allah ya yaye musu San juna,takoma d'akin taringayiwa Al ameen nasiha da ya hakura da Amnah Allah yariga ya hukunta ba matarsa bace, Al ameen jinta kawai yake dan ayanzu ma yaji yafara San Amnah,ahaka aka sallamesu aka bashi shawarar daya daina sa damuwa aransa,zai iya kamuwa da hawan jini.
Tundaga lokacin da aka sallami Al ameen ya koma gida yazama kamar wani tab'abb'e dan duk wani Abu daya danganci Amnah kamar rigunanta turarenta dasu yake kwana kullum cikin waya suke da Amnah yana fad'a mata yanda bazai iya rayuwa tare da ita ba dakuma yanda yayi kewarta.
Babu dabarun da Amnah batayi ba dan tasamu tafita dan ta dubo Al ameen Ummi taki tace ita da fita k'ofar gida sai tagama idda Al ameen babu yanda baiyi ba dan yaganta abun yaci tura dan har k'ofar gidansu Amnah yake zuwa ya tsaya duk da kullum cikin waya suke yafi San yaganta,ganin babu yanda zaiyi yasa ya hakura ya koma yana lissafin lokacin dazata gama idda, dan wani jarrabta da Allah ya mishi shine na Tsananin Sha 'awar Amnah kamar bai tab'a saninta ba,itama Amnah kusan hakan ne dan kullum sai tayi mafarki da Al ameen dan indai zasuyi waya sai sunyi hirar dazai d'aga musu hankali shiyasa suka matsu su had'u.
AKWANA ATASHI
Yau Amnah tagama iddarta farinciki awajen ita da Al ameen ba a magana dan sun San sun kusa had'uwa,washegarin data gama idda taje tasamu Ummi a d'akinta ta rok'eta tana San ta fita akwai kayanta data kai dinki tana so tak'arbo,wani harara Ummi ta zuba mata tace mata d'inkin ba rabonta bane ta wuce taje ta mata wanki badai takaso auranta sabida yawo ba,ita da fita har abada sai dai in gidan mijinta zaa kaita, Ummi ta zura hijabinta ta tafi Tabarta a tsaye,hawaye ne ya zubo mata ta d'auko wayarta takira Al ameen dayak'i zuwa kasuwa yana jiran zuwanta,tana gama kora mai yanda sukayi da Ummi ya fashe da kuka yana shikenan tashi tazo karshe indai bai ganta ba yau mutuwa zaiyi,jin hakan da Amnah tayi ne yasa hankalinta ya tashi tuni ta d'auko hijabinta ta zura ta kullo gidan, tanufi gidan Al ameen.
[8/5, 8:58 PM] Sadnaf: R🅰SHIN H🅰KURI
Written by
💅💅SADNAF💞
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS ( P.M.L.)
PAGE 14
Tafiyar minti goma ne yakaita gidan,tana sauka ta rufe fuskarta da hijabi sabida kar yan unguwar su ganeta,ahankali tafara k'wank'wasa k'ofar gabanta na fad'uwa dan ta dade bata sa Al ameen a ido ba,Al ameen dake kwance acan d'aki tun lokacin da sukayi waya da Amnah ya kwanta yana ta tunanin hanyar dazai bi ya ganta,k'wank'wansa k'ofar dayaji anayi ne yasa ya tashi yana tunanin Wanda ke k'wank'wasa k'ofa dan makotansu tunda suka San sun rabu da Amnah ba Wanda yakara zuwa gidan ko yaran makota,yana zuwa bakin k'ofar ya tsaya yace,
"Wayene"? Gaban Amnah sai daya kara fad'uwa dataji muryarshi, "
"nice ka bude min kar makota su gani" Al ameen cikin rawar jiki ya bud'e k'ofar dayaji muryar Amnah,kurawa juna ido sukayi nan da nan hawaye ya hau zubowa Amnah wani irin jawota Al ameen yayi ciki ko K'ofar bai rufe ba ya rungumeta tsam shima yana hawayen,
"Amnah I miss you,bazan iya rayuwa babu ke ba pls karki gujeni" duk maganan nan da yake yana rungume da ita yana hawaye, Amnah kuwa tunda tajita a k'irjin Al ameen taji wani irin sanyi a k'irjinta wanan abinda ya tokare mata a k'irji tunda suka rabu ahankali ya ringa narkewa tanajin sanyi,k'ara rungumeshi tayi tana kuka,d'agota yayi suka kara zubawa juna ido,hawayen fuskarta yafara share mata
"Am sorry Precious duk ni najanyo mana R🅰SHIN H🅰KURINA yajanyo mun rabu,bansan ya akayi nakasa kai zuciyata nesa ba har sai dana datse sauran igiyar da ya rage a tsakaninmu," tunda yafara magana Amnah ta zuba mishi ido dan gabad'aya gani tayi Al ameen ya rame yadawo dan siriri kamar bashi ba dayake da murjajjen jiki,kasa hak'uri tayi tace
"Al ameen mai ya ramar dakai haka"?lumshe ido yayi ya bud'e ahankali yace,
" Rashinki akusa dani Amnah,wlh bana barci daddare tunda muka rabu,yanzu ma yaro nasamu nasa ashagona bana iya tab'uka komai abinci wlh Hajiya sai tayi dagaske nake iya ci,"tunda yafara magana Amnah hawaye yaringa zubo mata na tsananin tausayin Al ameen,
" Al ameen bakada laifi laifina ne ni na janyo ma shiga wanan halin da ban biyewa kawayena ba nabi umarninka da baka sakeni ba dan nasan kana K'aunata tunda muka rabu nake tunanin ta ina zan fara rayuwa bada kai ba,wlh bazan iya rayuwa da wani namiji ba,"hakan da Al ameen yaji tace ne yatayar mai da hankali tuni idansa ya k'ada yayi jajur dan kishi, hanunta yaja suka nufi Palo dan duk maganar dasuke suna tsaye a tsakar gida,zaunar da ita yayi akan kujera shikuma ya durkusa agabanta ya ruk'o hanunta yafara magana
"Amnah yanzu har kina tunanin auran wani Ina raye ba mutuwa nayi ba,Amnah wlh bazan iya rayuwa da kowace mace ba idan bake ba kema inaso kisa aranki bazaki iya rayuwa da kowane da namiji inbani ba"tunda yafara magana Amnah tasaki baki tana kallonshi aranta kuma tafara tunanin Al ameen yasamu tab'in hankali haka kawai sai taji sai yanzu take jin haushin sakin daya mata d'aura fuska tayi tafara magana
" kasan bazaka iya rayuwa babu ni ba ka sakeni saki har uku, kana nufin sai baka rayye sanan zanyi aure ina bazai yiwu ba Al ameen ina sanka dan sanka amma dole na auri wani tunda yanzu babu aure a tsakaninmu,zan zauna hakane batare da nayi aure ko kai kayi aure ba ai bazai yiwu ba Al ameen gudun irin wanan ranar nasha r'okonka da ka kai zuciyarka nesa karinga hakuri,idan bahaka ba R🅰SHIN H🅰KURINKA zai janyo mu rasa junanmu amma ina sai daka hau dokin zuciya ka datse sauran igiyar dake tsakaninmu babu yanda zamuyi daya wuce muringa addua Allah ya yaye mana San da muke wa juna,"
ihu tasa sakamakon rik'e mata hannu dayayi dak'arfi idansa ya k'ada sabida bacin rai dan tunda Amnah tafara magana yaji kamar tana watsa mishi ruwan zafi, magana yafarayi,
"Amnah yanzu aure zakiyi kibarni dama bakya sona yama zaayi kiyi tunanin auren wani kinsan kuwa yanake ji a zuciyata inaji kina ambatar auren wani kai kai kai innalillahi wa inna ilahi rajiun Amnah kinsan mai nakeji kuwa,kinsan yanda nake sanki kuwa Amnah I love you I can do without you",yace yana girgiza k'afadarta kuka Amnah tafashe dashi dan gabad'aya Al ameen ya d'aureta da jijjiyoyin jikinta,rungumeta yayi kafin ta Ankara ya had'a bakinsu waje day'a cikin rawar jiki ya cire mata hijabi yafara aika mata sakoni yana sumbatun yanda yayi missing d'inta shaidan kuwa yana daga gefe sai hura musu wutar sha,awa yake tuni Al ameen yazame kayan jikinsa da nata, Amnah tafara girgiza kai tana, yatuna babu aure atsakaninsu yanzu inya kusanceta sun aikata zina,salon wasan da yake mata ya canja Amnah takara fita hayyacinta,ahaka ya rikita ta sai dayasamu biyan bukatarsa da ita yafashe da kuka yana yayi asaran macen da sai atara mata dubu ba asamu irinta ba,Amnah kuwa sai da tagama shan dadinta😜 tafara sallati,
" innalillahi wa inna ilahi rajiun,tureshi tayi daga jikinta tafashe da kuka,Al ameen ka cuceni abinda ban tab'ayi ba kasa na nayi,Al Ameen mun aikata zina Al ameen kadan girman zunubin zina kuwa nashiga uku na lalace"shhhhhh Al ameen ya katseta yafara magana cikin sanyin murya shima hawaye na zubo mishi,
"Amnah nima ban tab'a aikata zina ba tunda nake arayuwata tsananin sanki da sha'awarki ne yasa nakasa hakuri sai dana kusanceki dani dake bayin kanmu bane mun kasa fin k'arfin zuciyarmu,am sorry,pls" yace yana kwantar mata da gashinta ita dai bata kula shi illa mik'ewa datayi ta nufi band'aki tayi wankan tsarki wani irin haushin Al ameen takeji kamar ta shak'eshi,tana fitowa daga band'akin taga Al ameen yayi tagumi yana kallon waje d'aya motsin bud'e k'ofar band'akin ne yadawo dashi hankalinsa mik'ewa yayi dasauri yanufi wajenta yana rik'e hanunta ta fusge tanufi wajen da kayanta ke zube tafara sa kayanta sai data gama sawa zata sa hijabi,Al ameen ya juyo da ita ya rungumeta yana bata hak'uri abinka da mace mai rauni tuni tahakura ahaka sukayi sallama yana lallashinta yana kuma jadada
mata irin San da yake mata.
Amnah sai data fito daga gidan ta tuna bada izinin Ummi tafito ba dasauri ta duba agogo taga biyu da arbain ita da ta fito k'arfe goma tuni hankalinta ya tashi dan tasan k'arfe goma sha biyu su Ummi ke tashi tunanin tafarayi na karyar dazata yiwa Ummi ahaka ta isa gida hankalinta a tashe,sallama tayi ahankali ta rab'e ajikin bango tana kallon Ummi dake kitchen tana girki fuskarta a d'aure,adduoi tafara ja a zuciyarta tayi sallama batare da ta Ummi ta juyo ba ta amsa sallamar tace,
"Daga ina kike "?
kame kame Amnah tafarayi tarasa amsar da zata bawa Ummi can dabara ce ta fad'o mata tace makociyarta ce ta haihu shine takirata awaya tafad'a mata shine taje mata barka,Ummi bata ce komai ba tacigaba da abinda take,Amnah kuwa data ga haka d'aki tanufa tana isa ba kin Palo Ummi tabiyota da muciya dagudu tayi d'aki tana ihu,Ummi ta rufe ta da duka tana
"Sabida kin rik'a nace karki fita ki fita bada izinina ba lailai kin nuna min halinki dole Al ameen ya sakeki wlh bari kiji ....
"wanan iskancin da yawon ba a gidana ba Ashe k'afarki kaikaiyi yake miki bazan lamunci wanan yawon naki ba,sabida bakida tunanin sabida satar fita aurenki ya mutu,shine dan rashin mutunci nima anan satar fitar zakiringa min to wlh bazaki kara wata a gidana ba ko wa nasamu had'aku zanyi idris dan uwanki zan yiwa tallarki ya aureki na huta Mara mutunci kawai"
Tunda tafara jibgarta taringa kuka sai data gaji dan kanta ta k'yalleta jin maganar da Ummi keyi ne ya d'aga mata ahankali wa tallarta zaayiwa idris driver cousin d'inta ihu taringayi tana rok'on Ummi tayi mata rai bata San Idris ko kallonta Ummi batayi ba tacigaba da aikinta.
Daddare bayan sallah isha Amnah zuwa tayi tasamu mahaifinta ta durkusa agabansa tafara magana tana kuka.
"Abba dan Allah dan Annabi alfarma nazo nema awajenka karkuyi min aure yanzu har yanzu ban samu nutsuwa ba dan Allah kubani lokaci kafin nan nasamu nutsuwa dan girman Allah da zaman dazanyi haka zan nemi admission incigaba da makaranta Abba a taimaka min" wani mugun harara Ummi ta watsa mata tace bata isa ba,Mallam Mustapha ya dakatar da ita yace Amnah ta tafi Allah yamata zabi mafi Alheri da wanan maganar hankalin Amnah ya kwanta ta koma d'aki ta Tarar da miss call d'in Al ameen rututu kiransa tayi suka cigaba da soyayyarsu inda Al ameen yanuna mata ya kagu yakara ganinta.
Ahaka rayuwa tacigaba da tafiya Amnah inta samu fita zataje gurin Al ameen su soyewarsu daga bata sai tayi ta data sani dan tasan haramci suke aikatawa ,samun admission d'in da tayi ne yakara sawa tasamu hanyar zuwa gidan Al ameen inda manema suka yo mata caa aka ita kuma Sam bata saurarensu dan Al ameen kamar yayi hauka inyaji wani nasanta dan har cid gareshi,kullum kara San junansu suke da sha'awa inda Amnah wataran bayan Al ameen yagama biyan bukatarsa da ita tafara magana cikin kuka
"Al ameen nagaji da irin wanan rayuwar abinda banyi ba abaya yanzu kasani inayi mun maida zina ba abakin komai ba Al ameen nagaji da sab'on Allah nagaji muhakura da juna Al ameen" Al ameen rungumota yayi dan ya rarrasheta yanda ya saba ta tureshi tana tagaji bazata iya ba,doguwar rigarta ta zura tasa hijabinta tabar gidan dagudu tana zuwa gida taji kamshin girkin da Ummi takeyi,taji zuciyarta na tashi band'aki tayi da gudu dan wani amai taji yataho mata.
[8/5, 8:58 PM] Sadnaf: R🅰SHIN H🅰KURI
written by
💅💅SADNAF💞
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS (P.M.L)
PAGE 15
Tun abakin k'ofar band'aki tafara kelaya amai,sai data gama tazauna tana maida numfashi,tsaftace gurin tayi ta koma ta kwanta akan gado,tafara tunanin mai yasa ta amai,gabanta ne yayi wani irin fad'uwa data tuna rabonta da period tun last month tunda take bata tab'a missing period d'inta ba,tunani tayi sai mace tasamu ciki take missing period,
"Inna lillahi wa inna ilahi rajiun nashiga na lalace Allah ka taimakeni kasa ba cikine dani ba ina zansa kaina,mik'ewa tayi dasauri ta nufi gaban mudubi ta tsaya tana K'arewa kanta kallo sai yanzu tayi noticing changes ajikinta K'irjinta yakara cika takara haske,salati taringayi ta koma kan gado ta zauna tana tunanin indai cikine da ita babu abinda zai hana ta zubar ko da zata rasa ranta dawane fuska zata dubi iyayenta tace Al ameen ne yamata ciki bayan sun rabu,Shigowar Ummi d'akin ne ya katse mata tunanin data ke,
" ke wane lokaci kika shigo"? Ummi tace tana daga bakin k'ofa zare ido Amnah tahau yi dan Ummi tana da saurin d'ago Abu, dasauri tace " yanzu nan nashigo fitsari ne yamatseni shiyasa banzo nace miki na dawo ba",tsaki Ummi tayi tace mata maza kizo kije ki juye abincin can a flask, ina dawowa yanzu",dasauri tace to gabanta na fad'uwa dan tasan indai taje Kitchen ta shak'i kamshin abincinan babu abinda zai hana ta tayi amai, tasan Ummi tas zata kaita lahira da duka,fitowa tayi daga d'akin tana dube duben karya dan so take sai Ummi tafita sai taje kitchen d'in,Ummi kuwa tana zuwa bakin k'ofar fita juyowa tayi tace,
"wai bazaki je ki sauke min abincin ba sai ya kone,kitchen d'in tanufa dasauri gabanta na mugun fad'uwa dan har zuciyarta tafara tashi, ajiyar zuciya tayi data ga Ummi ta fita aikuwa tana zuwa bakin kitchen sai amai, amai take sosai kamar zata amayar da kayan cikinta gashi tayi weak dak'yar ta gyara wajen,ta toshe hancinta ta juye abincin a kula,ta koma d'akinta ta d'auki wayarta takira lambar Al ameen a lokacin,yana rubuta mata text na rarrashi da ban hak'uri,yana ganin kiranta yayi sauri ya d'aga kuka tafashe masa dashi tace,
" Al ameen nashiga uku na lalace ka gama dani Al ameen ciki ne dani,"waro ido Al ameen yayi yace "what how can you be pregnant"? Kuka takara fashewa dashi tace " natab'a ma irin wasanan banga period d'ina ba last month yanzu ina dawowa gida nafara amai Al ameen am death and finished,nayi nadamar biye maka muna tare da aure akanmu bansamu ciki ba,sai da muka koma muna aikata haramci nasamu ciki,Ina zan sa raina dawane ido zan kalli Ummi intaji labarin nan kasan halin mahaifiyata yaya mahaifina zaiji dan girman Allah na zubar mana da mutunci wai ya zanyi ne ni Amnah Al ameen nashiga uku wlh bazan iya barin cikin nan ajikina,goben nan zan zubar na gwammace na mutu agarin zubarwa Al ameen,tak'arasa zancen cikin matsanacin kuka, tunda tafara magana Al ameen yayi mutuwar zaune yana mamakin wai Amnah keda ciki shi da lokacin dasuke da aure kullum sai yayi adduar Allah yabasu haihuwa sai gashi sai da suka rabu Allah yabata ciki,ajiyar zuciya yayi yafara magana,
"Amnah stop crying and listen to me pls kukanki na tab'a min zuciya,inaso kigane wani abu lamarin Allah da girma yake wanan cikin dakika samu shi zai kara uniting d'inmu,Allah yanasan mu tare baki samu ciki lokacin da muke tare ba sai da muka rabu,abin ki godewa Allah ne kinga mutane suka San kina d'auke da cikina dole su yarda mu dawo da aurenmu" Amnah cak ta tsaya da kukan data ke tab'i wayarta da kallo maida wayar tayi kunenta tace,
" Al ameen Ashe bakada hankali anya kasan mai kakeyi kuwa bayan kayimin saki uku zamu koma da aurenmu nalura kasamu tab'in hankali bakasan mai kake cewa ba samun cikin nan danayi dai dai yake da tozartarmu da tonuwar asirinmu most especially ni dana kasance mai k'wak'walwar kifi kayimin saki Uku nacigaba da zuwa wajenka,wlh nayi nadamar biye ma nayi nadamar biyewa San zuciyata na tsaneka Al ameen dan naga kamar bakada wadataccen ilimin islama gobe ka shirya zanzo ka kaini asibiti a zubar da cikin shegen dakamin" dif ta kashe wayar,tana d'agowa sukayi ido hud'u da Ummi dake tsaye tana karkarwa idonta ya kankance sabida bacin rai,nuna ta tayi da yatsa tace Amnah mai kunena ke jiyo min kina fad'a, ciki ne dake ? Amnah Jada baya tafara yi ido warwaraje amadadin tayi sallati sai tafara kulli nafsi za a ikatul mauti,girgiza kai tafara yi tana Ummi kiyimin rai wlh sharrin shaidan ne,zubewa Ummi tayi akasa ta runtse idonta dakarfi tafara karanta duk adduar data zo bakinta, Amnah inbanda ihu babu abinda takeyi dan halin data ga Ummi aciki tunda take bata tab'a ganinta haka ba,bud'e idonta tayi ahankali ta saukesu akan Amnah, girgiza kai tayi hawaye yafara zubo mata,tace
"Amnah cikin shege kikayo agidana,kina tsatsona kikaje kika aikata zina da Wanda kuka rabu yamiki saki uku,Amnah kinsan girman laifin zina kuwa?Amnah kinsan idan buduruwa ce ta aikata zina hukunci bulala Tamanin zaayi mata,idan kuma matar aure ce jifanta zaa ayi tayi har sai ta koma ga Allah, Amnah tarbiyar dana miki kenan,?kin kashe aurenki kin dawo gida kina bin namiji har gida kuna aikata alfasha gashi harda guzurin ciki baku samu zuria ba a lokacin da kuke zaman sunna,sai da kuka rabu kuna sab'on Allah kuka samu rabo Amnah acikin 'yayana kece kika fita daban, da ki Haifa min shege agidana ina Raye gwara na kasheki Amnah nima a kasheni dan na lura kema shaidaniyar kanki ce,"
mik'ewa tayi afusace ta wawuro wani k'aton katakon dak'e bayan k'ofa tayi kan Amnah dagudu Amnah tasaki ihu tana Neman wajen b'uya zagaye d'akin suka farayi da Ummi cikin tsanin fushi tayi taku hud'u da niyyar ta damkota aikuwa Amnah tayi tuntube da takalminta mai tsini data cire data dawo,ta tafad'i ta bugi cikinta wani irin mahaukacin ihu tasaki ta suma take jini yahau zubo mata,Ummi D'aga hanunta tayi sama tana godewa Allah tana kuka,dan tasan b'ari Amnah tayi istagifari tayi tayi na Allah ya yafe mata ya yafewa Amnah badan Allah yayi hukuncinsa ba cikin Amnah ya zube da bata San daya zata cigaba da rayuwa ba,ruwa ta d'ebo a band'aki ta watsawa Amnah,ahankali Amnah tafara motsi, can ta rik'e cikinta tana ta ihu tana kiran sunan Ummi data taimaka mata zata mutu,jini kuwa sai zubowa yake ajikinta,Hijabi Ummi tasa tayi waje,wani yaro ta aika yaje mata bakin titi ya taro mata mai taxi,cikin girmamawa yaron yatafi,hawaye ne suka zubo mata tasa hannu ta goge tana tunanin da yanzu cikin Amnah bai zube ba,mutanen unguwa daina ganin mutuncinta zasuyi 'yar cikinta ta aikata zina harda cikin shege,dawowar yaron da abun hawa ne ya katse mata tunanin datake,godiya tayi mai ta koma ciki,ta d'aga Amnah dake dafe da ciki tana ta sallati,zani ta d'aura mata akan skirt d'in jini sai bin k'afarta yake,tsawa ta daka mata data rufe mata baki taja k'afarta sutafi,dak'yar Amnah tak'arasa motar ta,Ummi ta rufe gidan tahau suka tafi asibiti.
batare da bata lokaci ba aka bawa Amnah gado,likita daya dubata cewa yayi wa Ummi sai an mata wankin ciki, dan cikin rabi ne ya b'are,hannu tasa takarda,abinda bai wuce awa d'aya ba aka wanke mata ciki Amnah bak'aramin wuya tasha ba tayi kuka tayi nadamar abinda tayi,da hankalinta ya d'awo jikinta tafara tunanin cikin jikinta ya zube,Hamdala taringayi tana godewa Allah.
Al ameen kuwa tunda Amnah ta kashe wayar yayi tagumi yana ta tunanin ta inda zai fara shawo kan Amnah,karta zubar da cikin dan a tunaninsa samun cikinta ne zai sa karsu rabu,tunda ba ajere yamata sakin ba saki ukun amadadin d'aya yake awajensa k'iranta yayi tayi awaya yaji ba a d'auka ba nan da nan hankalinsa ya tashi yafara tunanin ko Ummi ce tagano halin da Amnah ke ciki,mik'ewa yayi dasauri yanufi gidansu Amnah,yana isa gidan yaga da k'wado a gidan,jiki a sanyaye Yakoma yana tunanin Ina su Amnah suka tafi.
Bayan sallar magriba aka sallami su Amnah dan Mallam Mustapha dayaje gida yaga k'ofa a rufe k'iran Ummi yayi yace suna ina, tace musu suna asibiti,sallati yayi ya tambayeta Waye ba lafiya tace masa Amnah ce,k'watance yace ta masa tayi Mish k'wantacen asibitin dasuke cikin yan mintuna yaje ya sameta,tambayarta yayi da mai yake damunta,Ummi tace yabari sai sunje gida,tunda aka sallamesu Amnah ta ringa kuka tana tunanin yanda zata kwashe da mahaifinta inya ji mai ta aikata takuma San Ummi bazata tab'a yarda tarufa mata asiri ba dan a asibiti suke da tuni ta fad'a mishi.
Suna isa gida gabanta yafara dukan uku uku, apalo Ummi ta zauna,Mallam Mustapha ma yasamu waje ya zauna,yana cewa Ummi tambayarta fa yake mai yake damun Amnah har aka kwantar da ita,Amnah dake tsaye abakin k'ofar kuka ta fashe dashi tana
"Abba na tuba wlh sharrin shaidan ne,kallonta yake cikin mamaki ahankali yadawo da kallonsa kan Ummi data sunkuyar dakai tana hawaye,gabansa ne yafad'i dayaji Amnah nata cewa Sharrin shaidan ne tunanin yayi ko kamata Ummi tayi da wani,dasauri ya kau da tunanin haka daga zuciyasa yayi magana cikin fad'a da b'acin rai da Ummi ta gaya masa mai Amnah tayi take cewa sharrin shaidan ne,hawaye Ummi ta goge ta kora mishi bayanin abinda yafaru,sallati Mallam Mustapha yayi da K'arfi yana kallon Amnah cikin rawar jiki sabida halin da mallam Mustapha ya Shiga sai da ita kanta Ummi ta tsorota,Amnah kuwa tuni tasaki fitsari atsaye
" Amnah zina agidana harda cikin shege, Amnah wanda yamiki saki uku kika koma wajensa kuna aikata zina"innalillahi wa inna ilahi rajiun da abinda zaki sakamin kenan dan na barki ki cigaba da karatu, 'yar cikina da aikata zina,girgiza kai yafarayi shima hawaye ya hau zubo mishi,Amnah kuwa inbanda kuka babu abinda take tana ta tuba ayafeta,Mallam Mustapha shamatar Amnah yayi ya damkota abinda bai tab'a yi ba dan tsakaninsa da 'yayansa fad'a da nasiha Ummi ce ma mai duka, dukanta yake da kome yasamu sai da yaga ta daina motsi ya k'yalleta d'akinsa ya nufa yana istigifari Ummi ta Mik'e ta bi bayansa dan ta rarrashe shi.
[8/5, 8:58 PM] Sadnaf: R🅰SHIN H🅰KURI
0 comments:
Post a Comment