Nazeer yana zuwa gidan Firdausi a fusace ya fito daga motar ransa a mutuk'ar b'ace ya nufi palonta ganin bai ganta a Palo ba yasa ya shiga d'akinta nan ma bata nan babu inda bai shiga ba a cikin gidan bai ganta ba,bakin gate ya nufa ransa na suya ya tambayi mai gadi inda Firdausi take,ce masa yayi tun safe da Firdausi ta fita bata dawo ba,girgiza kansa yayi ya duba agogon hanunsa yaga k'arfe shidda saura mintuna,zama yayi akan motarsa yana ta girgiza k'afa idonsa akan gate yana ta tunanin irin matakin dazai d'auka akanta,tunani ya hau yi inda taje bayan ta bar office d'insa,horn d'in da yaji ana tayi ba kakautawa ne ya katse masa tunanin da yake dasauri mai gadi ya bud'e gate d'in Firdausi ta danno hancin motar ta tana ta surfawa mai gadi zagi wai ya dade bai bud'e mata ba,bata lura da Nazeer dake zaune asaman motarsa ba dan a inda suke parking motoci yayi parking,kanta tsaye ta nufi Palo tana ta surutu ita kad'ai sai kace mahaukaciya,tana dab da shiga ciki taji an daka mata wani uban tsawa ance,
"Keeee daga gidan ubanwa kike"? Nazeer yace yana durowa daga saman motarsa.
,Firdausi ba k'aramin tsorata tayi ba dan har zubewa tayi akasa,zare ido ta hau yi tafara magana cikin kinkina tana gidansu taje,adai dai lokacin da Nazeer ya k'arasa wajen da take,mik'ar da ita yayi yaja hanunta da k'arfi suka shiga palon Firdausi gabanta sai dukan uku uku yake dan tunda take dashi bata tab'a ganin b'acin ransa kamar haka ba,wancakalar da ita yayi ta fad'a kan kujera yace
", Firdausi da izinin wa yau kika fita,jiya bana miki warning kar na sake na ga k'afarki a waje ba, kin rainani ko ban isa namiki umarni a matsayina na mijinki ki bi ba ko?, sabida rashin mutunci har gidan Amnah kika je kika fasa mata show glass kika ji mata rauni a goshi,Firdausi nagaji da halinki dan kin ga na zuba miki ido shi yasa kike abinda ranki keso wlh darajar little kike ci da tuni na Dade da sakinki,amma yanzu zan d'au mataki akanki watak'ila kya nutsu ki shiga hankalinki," Firdausi tana jin mai yace ta waro ido ta had'e hannayenta alamar rok'o dan yanzu inya saketa ya tona mata asiri,dasauri tafara,
"Dan Allah dan annabi Nazeer kayi hakuri sharrin shaidan ne karka sakeni karka manta fa dan Ina sanka nake kishinka,Nazeer Kau da Kansa yayi sabida mutum ne shi mai rauni da tausayi " Firdausi ki tashi ki tafi gidanku sai na nemeki ba sakinki nayi ba,inaso nasamu nutsuwar zuciya kema kisamu nutsuwa dan naga alamar kishin nan na neman ya zautar dake kije gidanku in ki huta in an kwana biyu zan nemeki Nazeer yace yana mai kara kau da kansa dan bayaso su had'a ido da ita, mik'ewa Firdausi tayi taje ta tsaya a gabansa tana hawaye,
"Nazeer yanzu akan Amnah zaka ce na tafi gidanmu,?
Yanzu idan kayi min haka kayimin adalci kenan?kayi min kishiya daga tafiyata ka kuma rasa wacce zaka aura sai kawata sanan kace kar nayi magana Nazeer?dukana fa kayi ka hanani kuka baka fad'amin zakayi aure ba sai zuwa nayi na tarar ka auri kawata kasan irin wanan auren yafi kowane ciwo,kasan irin zafin dana keji a zuciyata kuwa",ka tab'a zuciyata kaji irin rad'ad'in dana keji Nazeer ."
Firdausi tace tana kamo hanunsa tare da aza hanun a k'irjinta dake harbawa da sauri da sauri, tunda tafara magana jikin Nazeer yabi yayi sanyi yafara tunanin kuma kamar bai kyauta mata ba inya ce ta tafi gidansu amma saboda kar ta rainashi ta kuma d'auka bazai iya bane yasa ya cire hanunsa daga k'irjinta yace,
"Firdausi na gaji da abinda kike min ne dole nace kitafi gidanku dan bazaki tab'a canjawa ba yanzu dan Allah dubeki kamar mahaukaciya sabon kamu tun safe haka kike yawo ko wanka bakiyi ba sabida kin d'orawa kanki masifa watak'ila ko abinci ma baki ci ba,dubi shigar dake jikinki Firdausi kamar ba matar aure ba,ji uban attach da kika sa akanki,sau nawa nace miki kidaina kar'in gashi?sau nawa nace kidaina aske gashin girarki,tun da ga lokacin dana aureki nake hanaki irin wayanan abubuwan kin k'i daina wa,All these while Firdausi hakuri nake dake ban tab'a miki magana ba nan hakkina na aure ban isa ki bani cikin dad'in rai ba sai kince na baki kud'i dan nayi aure Firdausi kina da bakin magana"
,ajiyar zuciya yayi ya cigaba da magana "Firdausi I mean what am saying kije gidanku iyayenki suyi miki fad'a zan nemeki ki tabbata gobe ban same ki a gidan nan ba" ya juya yayi hanyar waje,kuka ta rushe dashi taringa ita zai wulakanta dan yayi sabon aure babu komai Allah ya saka mata.
Tana ganin ya fita ta tsayar da kukan data keyi ta d'ora hannu aka tafara tunanin yanda Nazeer kesan ya ruguza mata plan,take dabara ta fad'o mata Jakarta ta bud'e dasauri ta d'auko wayarta ta kira hajiya Aliya mahaifiyar Nazeer,bugu biyu ta d'auka ,
fashewa tayi da kuka tafara ce mata Nazeer ya saketa yace ta tafi gida dan yayi sabon aure," sallati hajiya Aliya ta rapka ta tambayeta ta dawo ne yaushe Nazeer ya saketa,kuka ta k'ara kecewa dashi tace babu abinda tayi masa jiya ta dawo yau kuma ya saketa wai ta tafi gidansu,sallati Hajiya Aliya takara yi tace tayi hakuri kar taje ko ina bari ta k'irashi dif ta kashe wayar Firdausi ta daka tsalle tace "Nazeer naka wasa ne wlh sai ka saki Amnah ni duwawu ce zama dani dole" yar aikinta ta k'ira awaya tace mata tayi sauri tazo ta d'ora mata abinci ta dawo.
Nazeer kuwa yana isa gida a Palo ya Tarar da Amnah taci kuka ta gode Allah,da sauri ya k'arasa gurinta yana
"Subhanallahi Amnah mai ya sameki kike kuka"?
Juya mishi baya tayi tafara magana cikin shagwab'a tana " ba kai ne nace kar ka dau mataki akan Firdausi ka k'i ba,so kake duniya ta zageni ace daga tarewa ta nazo ina had'aku fad'a",
Murmushi yayi ya juyo da ita yana k'ok'arin magana yaji wayarsa na ringing ganin mahaifiyarsa ke k'iransa ne yasa ya cika Amnah da Sauri ya d'aga wayar tare da sallama,hajiya Aliya rufeshi tayi da fad'a tana
"Naziru kana da hankali kuwa akan me zaka saki Firdausi so kake ka janyo wa Amnah bak'in jini ace sabida ka aurota ka saketa,mai tayi ma da zaka saketa".
sallati Nazeer yayi yace " Hajiya ban saketa ba fa cewa nayi ta tafi gidansu sai na nemeta Hajiya daga dawowarta jiya jiyan nan baki ga yanda ta d'aga min hankali ba kinsan mai tayi min kuwa anan ya labarta mata abinda Firdausi tayi mishi"hajiya Aliya tace
"duk da haka bai kamata kace ta tafi gidansu ba dan Amnah zaka jazawa bak'in jini nace karta je ko ina kabarta da halinta ka cewa Amnah karta sake ta kulata duk abinda zata mata inyaso sai ka mata gargadi akan duk lokacin data k'ara zuwa gidan Amnah zaka dau mumunar mataki akanta kaji ko Allah dai ya shiryeta.
Nazeer cewa yayi " hajiya wlh idan ba gidansu taje ta kwana biyu ba bazata tab'a shiga hankalinta ba dan Allah ki barta taje bayan kwana biyu na d'auko ta wlh baki ga rashin hankalin data zo tamin ba""Nasani kadai k'yalleta nace hajiya tace a dan tsawace ta kashe wayar,bin wayar yayi da kallo ya girgiza kai Amnah kuwa tuni ta hau murna,tace " Dan Allah kayi hakuri yanzu inkace ta tafi Allah laifin kaina zai dawo bazaka gane ba".
"Shikenan Allah ya shiryeta"yace yana mik'ewa tabi bayansa sukayi d'akinsa.
Firdausi kuwa hankalinta bai kwanta ba sai da Hajiya Aliya ta k'irata tace tayi wa Nazeer magana ta kuma yi mata nasiha data K'wantar da hankalinta ta rik'e Amnah hannu bibbiyu,suna gama wayar tace "munafika kawai zaki ci ubanki bari nagama da danki indawo kanki".
Washegari Nazeer yana barin gidan Amnah,gidan Firdausi ya wuce dan ya duba ta kafin ya tafi office,yana zuwa ya tarar da ita suna ta gyaran gida it a da mai aikinta bak'aramin mamaki yayi ba dan Firdausi bata aikin komai sai dai yar aiki tayi,tunani ya hau yi na gyaren me takeyi, tana ganinsa ta saki murmurshi tana masa sannu da zuwa wani mamakin ne ya kara rufeshi,ganin da yar aikinta a Palo ne yasa ya hau sama ya nufi palonsa yana tunanin abinda ya kawo sudden changes d'in zama yayi ya d'aura fuska, Firdausi kuwa ta zauna a kasa tana kara gaishe shi," ke yau kuma wani sabon munafircin kika koyo yaushe Rabon da ki gaisheni bak'i zakiyi naga kina gyara"? Nazeer yace yana kallonta, d'agowa tayi tace "wlh babu wani munafirci dana koyo jiya nayi wa kaina fad'a nasan na dade INA maka ba dai dai ba dan Allah Nazeer kayi hakuri banzan sake ba insha Allahu" tace hawaye na zubo mata nan kuwa a zuciyarta da zaka duba wani irin tafasa yake kamar ta shak'e Nazeer takeji kawai tayi hakan ne dan ta cima burinta.
Tunda ta fara magana Nazeer ya saki baki yana kallonta mamaki ya gaza boyuwa a fuskarsa wani farinciki ne ya lullub'eshi yafara magana"Firdausi am I dreaming or something kece kuwa,"? Gigiza kai Firdausi ta karayi tana share hawayen fuskarta "waw can't believe it zo! zo !zo nan Nazeer yace ya na nuna mata cinyarsa,mik'ewa tayi a hankali taje ta zauna akan cinyarsa yace " yauwa tawan ko ke fa,dan Allah ki kwantar da hankalinki ki rik'e Amnah da hannu biyu inkika yi haka hankalina zai fi kwanciya kiringa bin umarnina dan Allah kidaina wanan yawace yawacen nan da kikeyi,duk abinda na hanaki Indai bai sab'awa Allah ba kiringa k'ok'arin daina,ni kuma insha Allahu zan yi iya k'ok'arina naga na faranta miki kinji" gyada kanta tayi tace insha Allahu a takaice aranar acikin farinciki Nazeer ya wuni yana
murna Firdausi ta canja halinta dan daya zo barin gidan ma saura kiris taja hankalinsa ya sadu da ita sai daya kai zuciyarsa nesa ya kwantar mata da hankali da ta yu hakuri gobe itace da girki.
Inda a b'angaren Firdausi tayi hakan ne dan ya saki jikinsa da ita ya ci abincinta ya kuma d'ora kansa a pillow
Ita dai burinta Amnah ta bar gidan by fire by force.
Amnah kuwa ta saki jikinta da Nazeer sosai ta cire komai a ranta dan ba laifi shima yana da caring dan dai kawai yanayin aikinsa dake hana shi yayi wasu abubuwan.
washegari da Firdausi zata k'arbi girki kamar karsu rabu da Amnah dan Nazeer yana samun nutsuwa sosai a wajenta ba a iya auratayya ba tsaftar jiki da na muhalli ga uwa uba iya girki,dan kwana ukun da yayi awajenta har wani fresh ya karayi dan har abinci take zuba mishi a flask ya tafi dashi office ba kamar da, da sai yaje office zai nemi abincin da zai ci ba.
Firdausi kuwa aranar tamkar sallah take awajenta babu inda bata gyara ba ita da mai aikinta,dan gadon Nazeer ya shimfid'u da sabon bedsheet mai tsada ga layya data sa mishi a karkashin pillownsa,kud'i tabawa mai aikinta taje ta yo mata cefane tayiwa Nazeer girki dan yace bai zai tab'a cin abincin 'yar aiki ba shiyasa ta sha alwashin yi girkin da kanta duk da bawani iya girki tayi ba,inka d'auke indomie da shayi data iya dafawa,K'arfe biyat dai dai tagama girka tuwon shinkafa da miyan agushin dayaji nama da danyen kifi har wani karni karni miyan keyi mai kuwa asaman miyan zaiyi kwalba d'aya duka garin maganin ta juye a miyan ta jera abincin a palonsa ta Shiga wanka tazo taci kwalliya da wani arnen material tasha makeup kamar zata je biki tazo ta zauna a Palo tana ta duba agogo .
Nazeer kuwa daya tashi daga office sai daya fara zuwa gidan Amnah,kamar kar ya taho Dan baya gajiya da ganinta dak'yar ta yarda yaci abincin data girkawa ita da mai gadi sanan ya tafi dan har yafara jagwalgwala ta ta gudu. Yana tafiya taji wani kishi ya rufeta.said da aka fara kirayen kirayen sallah Nazeer ya isa gidan Firdausi a lokacin ta cika tayi Pam kamar ta fashe dan bak'in ciki.R🅰SHIN H🅰KURI
Written by
💅💅SADNAF💞
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS (P.M.L)
*DEDICATED TO AUNTY SIS💞 THANKS FOR YOUR LOVE AND SUPPORT*💞💞💞
Page 22
Firdausi tana jin kiraye kirayen sallah amma ta kasa tashi tayi sallah sabida masifa data sa a ranta sai girgiza k'afa take idonta a bak'in k'ofa,tana jin dirin motarsa ta kara d'aura fuska,wani tunani tayi,na kar ya d'ago plan d'inta tayi sauri ta saisaita fuskarta ta kirkiro murmushin dole ta mik'e tana amsa sallamar daya yi, ledar hanunsa ta k'arba tana mishi sannu da zuwa ya amsa shima yana sakar mata murmushin zama yayi akan kujera yana kallonta dan Rabon daya ga tayi kwalliya haka kawai batare da unguwa zata je ba in zai iya tunawa tun tana amarya,zama tayi a gefensa tace "ya office d'in "?
Murmushi ya k'ara sakar mata yace " fine wlh kinyi kyau fa sai kace amarya yaushe Rabon da ayimin irin wanan kwalliyar ai na manta" dariya tayi tace babu wani nan kaine dai ba ka lura,ya Amnah ?" Murmushi ya saki daya bayyana hak'orinsa hakan kuwa ba k'aramin sosa wa Firdausi rai yayi ba, cemata yayi "tana nan kalau yanzu da zan dawo ma na biya na dubata tace a gaisheki" .
"Ina amsawa tace tana mik'ewa dan tuni taji kamar ta shak'e shi d'aurewa kawai takeyi ce mishi tayi ya tashi yaje yayi alwala yayi sallah abincinsa na jiransa,a tare suka nufi b'angarensa yana shiga d'akinsa ya saki baki yana bin ko ina da kallo juyowa yayi ya kalli Firdausi yace " kina ta kasheni da mamaki yau d'akina ne ya samu wanan gyaran lailai ni auren dana k'ara gaba takaini tunda gashi kin gyara halinki yanzu bazan ringa fargabar kwana a gida ba dan wlh na tsani k'azanta dan Allah ki cigaba da wanan halin naki kinji".
Murmushi tayi tace "insha Allah" b'andaki ya wuce tayi sauri ta kara gyara pilonsa data sa laya ta feffesa turare a d'akin tabar d'akin tanufi palonsa dan ta sauko masa da abincinsa kasa.
Sai da Nazeer yagama sallolinsa yayi wanka ya nufi Palo,a zaune ya tarar da Firdausi sai murmushi take ita kad'ai nan kuwa hararowa take har Nazeer ya saki Amnah,tana ganin ya fito ta mik'e ta ruko hanunsa,"lailai yau mum little kina ji dani sai kace ango" Nazeer yace a lokacin da yake zama a kasan carpet data jera kulollin," ai yau da kaina nashiga kitchen nayi maka girki, wlh sai Dana kwashi awa uku ina girkinan duk saboda in faranta ma shi yasa nakeso ka cinye abincinan tas naji dadi,"murmushi yayi yace " yau da kanki kika shiga kitchen tsakani da Allah ba 'yar aiki ce ta girka ba,".
"Wlh ni da kaina na girka bari na zuba ma kaci kaji," bud'e kulollin tafara yi shi kuwa ya zubawa abincin ido amadadin yaji kamshi na tashi karni yaringa ji da kamshin curry,tana fara debo miyar yaji wani irin amai na san taso mishi tunani yafara yi na hanyar da zai bi yak'i cin abincin dan already cikinsa a cike yake da zai iya d'aurewa yaci da yaci amma ina ganin abincin ma dayake amai yakeji maganarta ne ya katse masa tunanin da yake," bismillah tace tana tura masa plate d'in gabansa,murmushi yayi yace Firdausi kinga sabida baki damu da kisan abinda nakeso da abinda bana so ya janyo miki bakisan abinda nafiso naci daddare ba,bana cin Abu mai nauyi daddare nafi cin Abu mara nauyi da kinsani kin tambayeni na fad'a miki abunda zaki dafamin,"tunda yafara magana hankalin Firdausi ya tashi tafara tunanin dubu darinta,murmushi ta saki Wanda bai kai zuci ba tace " badai kana nufin bazaka ci ba,bayan uban wahalar nan dana sha kaga hanunna fa har konewa yayi,yanzu dai kaci abincin ko yaya ne,next time na ringa tambayarka abinda zan girka dan yanzu idan Baka ci ba baka min adalci ba.
Murmushi yayi yace "wlh ina ci abinci mai nauyi daddare ciwon ciki nakeyi yanzu dai ki ajiye min abincin gobe sai ki dumama min nayi breakfast dashi anjima inaji yunwa kya dafamin indomie".
"Kace kawai bazaka ci girkina ba ka biya gidan amaryarka kaci,duk wahalar nan dana sha tsakani da Allah kamin adalci ,kaga ka sage min gwiwa next time bazan yi abinda zai faranta ma ba dama ni nasan Baka sona,yanzu idan Amnah ce tayi girki ka isa kace mata bazaka ci ba" Firdausi tace tana fashewa da kuka tare a mik'ewa.
Hanunta ya ruk'o da sauri yace "Allah firdausi ki yarda dani bana cin abinci mai nauyi daddare amma gobe I promise zanci ki dumama min kinji" gyada kai tayi,ya hau share mata hawaye,daga nan kuma yau hau wasani da ita,dayake a gwiwa take sabida shaye shaye dan tayi tuni ta hau mayar masa da martani anan cikin palon komai ya wakana, barci mai nauyin gaske yayi awon gaba da ita,d'akinta ya shiga ya d'auko mata sleeping dress ya zura mata ya kinkimeta yakaita d'akinta ya kwantar da ita, ya shiga band'akinta yayi wankan tsarki ya fito ya kwanta a gefenta shima barci yayi awon gaba dashi.
Firdausi ba ita ta farka ba sai wajen k'arfe hud'u da rabi, mik'ewa tayi da sauri ta zauna tana karewa d'akinta kallo juyawa tayi ta kalli Nazeer dake barcinsa hankali kwance,sallati tayi tafara tashin Nazeer ,a firgice ya tashi ya zauna yana tambayarta lafiya? ce mishi tayi mai sukeyi a d'akinta ya akayi bai tasheta ba ya tashi su tafi d'akinsa anan takeso su kwanta,tsaki yayi ya koma ya kwanta yana,
"Dan ban tasheki ba kika tasheni mai da d'akin naki dan mun kwanta dan Allah koma ki kwanta ni barci ne a idona" cikin tashin hankali tafara magana
"Dan Allah mu tafi d'akinka mu kwanta wlh ni nafi jin d'adin barci acan kana nufin duk gyaran d'akin nan danayi ya tashi a banza" tace tana k'ok'arin d'agoshi " tsaki yayi ya tashi ya bar d'akin tayi sauri tabi bayansa tana zai mata asara biyu, d'akinsa yanufa yana zuwa ya janyo pillon tsakiya ya jefar akan lalausan carpet d'in tsakiyar d'akin ya kwanta, Firdausi na shigowa d'akin sallati tayi data ganshi akasa tace "mai haka mai kazo ka kwanta a kasa wa ka barwa gadon,"
cikin fushi yafara magana" dalla mallama kin takura min kin koroni daga d'akinki na dawo d'akina ma bazaki barni nayi barcina ba wai mai kikeso ne? Shiru tayi bata ce masa komai ba aranta kuwa tunanin yanda Nazeer ya ruguza mata plan take,sai kallon pillon data sa layya a ciki take,Nazeer kuwa dayaji kiraye kirayen sallah tashi yayi yace "kin ma taimakeni ma bari nayi alwala nayi sallah,band'aki ya nufa dan yayi alwala tabi bayansa da kallo yana shigewa ta fashe da kuka dan bak'in ciki ahaka ya fito ya sameta,sakin baki yayi yana kallonta cikin mamaki,yace mata lafiyarta kuwa? Ko kallonsa batayi ba shi kuwa daya ga tana bata mishi lokaci ya zura doguwar riga ya dau carbinsa yana ta tashi tayi wanka lokaci na tafiya ya fice daga d'akin.
Ahaka Nazeer ya dawo ya sameta tayi zurfi a tunani sai shara k'walla take dan tunani taringayi hanyar daza tabi ta fita dan ta koma wajen mallaminta ta gaya mishi,sai tsinewa Amnah take a zuciyarta,tab'ata da Nazeer yayi ne ya dawo da ita hankalinta,
"Wai Firdausi mai yake damunki ne ko wanka bakiyi ba ballantana kiyi sallah yanda na fita na barki haka na dawo na sameki,mik'ewa tayi tafita ta bar d'akin dan wani haushinsa take ji,ahaka Nazeer ya shirya ya fito ya sameta a Palo yace mata zai fita,d'agowa tayi ta kalleshi tace mishi ga abincin dayace ta dumama masa,agogon hanunsa ya kalla yace mata yayi latti ta bawa almajirai inya je office zai kirata ya gaya mata abinda zata dafa masa kud'i ya ajiye mata akan kujera yafara k'ok'arin ficewa," yanzu haka mukayi dakai Nazeer kai fa kace in dumama maka da safe zaka ci"
A hasale yace " baki ga nayi latti bane ko dai wani Abu kika sa a abincin nan ne kika dage sai naci? "
"Mai kuwa zansa ma a abinci naga kai kace a dumama da safe zaka ci naga kuma bai kamata ka fita da empty stomach ba,"? Tace tana zumburo masa baki,kallonta ya tsaya yi yana mamakin abinda yasa ta canja take yafara zargin watak'ila she is up to something idan ba haka ba mai yasata kuka anan ya hau tunani iri iri dayaga yana b'atawa kansa lokaci ya fice yabar gidan,yana fita tayi tsaki tace " shege dan bura uba yasa nayi asarar kud'ina wlh sai ya biyani kud'ina bari ya dawo" wayarta ta janyo tayi dialing lambar Alawiyya dan ta labarta mata abinda Nazeer ya mata, sai data mata miss call uku ana hud'u ta d'aga tana ce mata hello,
Alawiyya tace " lafiya kike k'irana mara mutunci kinbi kin haukace akan namiji har ni zaki wulak'anta na biki gidan Amnah batare da izinin Mijina ba,dan wulak'anci ki baro ni a wajen ko sisi ban fito dashi ba ahaka na kama hanya na dawo saura kiris aurena ya mutu sabida dana dawo zuwa nayi na tarar da abbansu Fadeel ya dawo"
"dalla mallama baki ga halin danake ciki ba ranar bazaki yimun uzuri ba".
" Firdausi babu ruwana da halin da kike ciki nidai ki rabu dani kifita daga hark'ata babu ni babu ke dan banaso aurena ya mutu"dif Alawiyya ta kashe wayar tabi wayarta da kallo tana mamak'in Alawiyya,k'iran Siyama tayi itama taji tana d'agawa Siyama itama ta hau surfa mata zagi tana Allah ya kara da aka mata kishiya,Firdausi sabida mamak'i kasa magana tayi har Siyama ta kashe wayar,jikinta ne yabi yayi sanyi tana tunanin aminan nata had'a baki sukayi wajen juya mata baya,a takaice mallaminta ta k'ira a waya ta Sanar dashi yanda sukayi da Nazeer,tace mishi ita dai ya taimaka mata ko nawa ne zata bayar dan a saki Amnah,inda mallam Dogo ya mata alkawari akan idan Amnah ta k'arbi girki tazo akwai abinda zai bata da wanan maganar hankalin Firdausi ya kwanta.
Nazeer kuwa daya bar gidan Firdausi sai daya biya ta gidan Amnah tukuna dan ya dubata,tunda ga bakin gate yaringa jiyo kamshin girkinta har ya shiga cikin gidan dan a waje yayi parking,a kitchen ya sameta tana kwashe doy'ar data soya taci kwalliya da english wears tayi masifar kyau,ta baya ya rungumeta ta saki Murmushi tana gaishe shi,a takaice dak'yar Nazeer ya tafi dan sai daya cika cikinsa ya tafi da wani a flask.
A haka Firdausi ta gama girkinta,aranar da Amnah ta k'arbi girki Nazeer na fita office, Firdausi itama taje gurin mallaminta ya bata garin magani yace tayi turaren wuta dashi ta k'ira sunan Amnah sau uku zata ga abinda zai biyo baya,kud'i ta bashi masu yawa ta taho gida tana murna,'yar aikinta tasa ta nemo mata garwashi tashige can d'aka ta zuba garin maganin akai,tana ganin hayaki yafara tashi ta hau k'iran sunan Amnah da k'arfi, adai dai lokacin Amnah tana kitchen tana abincin rana wani irin duuum taji a kunenta can tafara ganin duhu sallati tafara yi tana adduar duk da yazo bakinta a karshe taringa maimaita laqadja'akum rasullah min anfusikum,har karshe zubewa tayi a kasa sakamakon wani jiri daya deb'eta.[8/5, 9:00 PM] Sadnaf: R🅰SHIN H🅰KURI
Written by
💅💅SADNAF💞
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS (P.M.L)
Page 23
A hankali tafara dawowa dai dai bata fasa addu'ar da takeyi ba,bakinta na d'auke da adduoin da Ummi ta koya mata,mik'ewa tayi a hankali ta cigaba da girkinta har ta gama tana adduoi,tana barin kitchen palonta ta nufa taje ta kunna karatun Qurani a k'aton blue tooth dake palon,taringa bin karatun hankalinta a kwance bata kawo komai a ranta ba tacigaba da ayyukanta a karshe ta shiga band'aki ta shek'a wanka taci kwalliya tana jiran dawowar Nazeer, aikuwa zamanta da minti goma sai gashi ya shigo,wani irin murmushi ya ringayi har ya zauna ita kuma ta k'arbi ledar hanunsa tana tambayarsa lafiya kuwa mai yake sa shi farinciki haka, bai bata amsa ba illa ma cigaba da yayi da kallonta can yafara magana yana,
" Wlh Amnah ba komai kesani farinciki ba illa jin dadin mallakar ki danayi a matsayin mata wlh Amnah nayi dace da mace ta gari inasan inga mace ma a bociyar addini yanzu shigowar nan danayi na dana jiyo karatun qurani bakisan farinciki daya lullub'eni ba dan gidan da ba a karatun qurani ba gida bane kango ne yanzu idan Allah ya azurta mu da zuria suka taso suka ga haka kinga kin taimakeni babu su babu jin wanan kad'e kad'en zamanin tunda basu taso sunga mahaifiyarsu naji ba,Dan kinsan uwa itace ginshikin tarbiyyar yayanta,Allah ya bamu zuria dayyiba", murmushi tayi tace ameen tana mik'ewa,hanyar d'akinsa tayi ya mik'e yabi bayanta dan yasan ruwan wanka zata had'a masa.
B'angaren Firdausi kuwa zuba ido take taji labarin wani Abu yafaru taji shiru dan da Nazeer yaje mata sallama a ranar daddare tambayarsa taringayi ya Amnah take,yace mata tana nan kalau tama ce a gaisheta tunin annurin fuskarta ya kau Wanda saura kad'an Nazeer ya d'agota sai data d'aure ta hadiyi bak'in cikinta har ya tafi,yana fita ta d'auki wayarta ta k'ira Mallam Dogo tace mishi tayi turaren babu abinda yasamu Amnah,anan Mallam Dogo yake ce mata dama yana shirin k'iranta ya fad'a mata gaskia Amnah a shirye take duk jifan da zasuyi mata bazai kamata ba sabida ta dogara ga Allah tana kuma tak'ama da ayar Allah hanya d'aya zaabi tasamu nassara shine tabari sai Amnah na period ko da janaba a jikinta sai ayi aiki akanta,dan Amnah bata rabo da Alwala a jikinta, tsaki Firdausi taja tace yace kawai bai iya komai ba Amma ya zai ce Amnah tafi k'arfinsa ya dai ci kud'inta Allah ya isa bata yafe ba ta kashe wayar batare da ta jira taji mai Mallam Dogo zai ce ba.
Tun daga lokacin Firdausi ta kasa zama waje d'aya daga taje wajen wancan mallamin sai wajen boka babu inda bata zuwa dan tayiwa Nazeer asiri ko Amnah dan su rabu Amma shiru kake ji dan Nazeer shima a tsaye yake baya wasa da adduoi dan zama da Amnah yasa yak'ara dagewa dan duk dare zai ga ta tashi tayi sallah rakaa biyu tayi adduointa kafin ta koma barci bata tab'a yarda ta kwana da janaba a jikinta dan in sau goma zai sadu da ita sai tayi wanka,Amnah kuwa dagewa tayi sosai da addua dan tunda abun nan ya faru da ita ta dage dan tasan watak'ila Firdausi ke Neman kawo mata hari tunda tasan halinta hakan ne yasa ta d'age ko aiki takeyi idan bata karatun al qurani to zata mak'ala ear piece a kunenta tana ji.
Firdausi kuwa ita da Nazeer kullum sai sunyi fad'a dan tafito ta nuna mishi true colour d'inta ita bata San Amnah ta kuma ci alwashin sai taga bayan aurensu,Wanda hakan yasa Nazeer ya fita daga hark'ar Firdausi gabad'aya idan ranar girkinta ne yana dawowa daga office d'akinsa ya ke shigewa ya rufo k'ofarsa yafito da abincin da Amnah ta zuba mishi yaci yayi nak,Firdausi kuwa inta ga haka kwana zata yi tana buga k'ofar d'akinsa tana surfa mishi zagi,a takaice sai da Firdausi ta zama tamkar mahaukaciya,dan masifa dan yanzu abokanan shawarar ta duk sun juya mata baya,babu irin kud'in da bata kashe ba agarin bin mallamai da boka har gold d'inta taringa siyarwa ita dai Nazeer ya saki Amnah Wanda a karshe data ga alama Nazeer ma mahaukaciya ya maidata dole kesa wa yazo ranar kwananta,ya kwana a gida,hakan kuwa yasa wataran da itace da girki yana dawowa yana shigewa d'aki tahau buga masa d'aki da k'arfi kamar zata b'alla a fusace Nazeer yazo ya bud'e k'ofar yana tambayarta da lafiya wani wulak'antaccecn Kallo ta mishi ta shige d'akin ta zauna a gefen gado tana harare harare sakin baki yayi yana kallonta ransa a mutuk'ar bace dan Firdausi ta fara kai shi bango,a tsawace yace mata mai take nema a d'akinsa ,itama tace hakkinta tazo ya bata dan rabonsu da ita tun lokacin da tayi pretending d'in ta shiryu,kau da Kansa yayi yace bazai iya ba,ya janyo pillonsa dan ya bar mata d'akin ta janyo rigarshi tana bai isa ba yaushe Rabon da ya tab'ata tunda ya auri Amnah ya dai na saduwa da ita,ranar girkinta ma sai yaje gidan Amnah yaci amanarta kafin ya taho gidanta dan haka bata yarda ba,fusge rigar shi yayi, yayi hanyar fita daga d'akin,da sauri tak'ara shan gabansa ta cakumo wuyan rigarsa cikin zafin nama Nazeer ya d'auketa da mari d'aya sa ta tuna lokacin da aka haifeta, birgima ta hau yi akasa tana ta daina gani ya cire mata ido,ko saurarenta baiyi ba yabar d'akin aranar ko runtsawa baiyi ba sabida Firdausi cika gidan tayi da ihu,kasa ma nutsuwa yayi,yayi nafilar daya saba sabida ihun da Firdausi take, Allah Allah ya ringa yi asuba tayi,k'arfe hud'u da rabi nayi yayi alwala ya nufi massalaci daga can ya wuce gidan Amnah.
B'angaren Amnah kuwa hankalinta a kwance yake dan bata da matsalar komai dan Nazeer yana iya bakin k'ok'arinsa dan yaga ya faranta mata,dan haka kawai ma zai ce ta shirya suje su gaida su Ummi kuma indai suka je sai ya musu alheri,sai ayanzu ma takejin dad'in aure dan Nazeer bashida saurin fushi ga hakuri,wani kib'a Amnah ta karayi tayi haske sabida kwanciyar hankalin data samu,yanzu wata uku da aurenta da Nazeer tana d'auke da ciki wata d'aya bata fad'awa Nazeer ba sabida tafiso sai cikin ya k'ara girma sai ya ta fad'a mishi,matsalarta k'waya d'aya ce Nazeer bashida k'arfin sha'awa kamar Al ameen dan sai Nazeer yazo yagama kwana biyunsa a wajenta bai sadu da ita ba,sai dai kawai yayi wasani da ita yayi barcinsa hakan kuwa na damun Amnah dan tariga ta saba da training d'in da Al ameen ya mata.
Nazeer lokacin da ya k'araso gidan Amnah k'arfe shidda na safe daga shi sai jallabiya da carbi a hannu a lokacin Amnah tana zaune a Palo bayan ta gama gyare gyarenta tana bin karatun quranin da ta kunna kamar daga sama taga Nazeer ya shigo palon mik'ewa tayi da sauri tana tambayarsa lafiya kuwa da sassafen nan d'aga mata kai yayi yace mata lafiya,gaishe shi tayi ya amsa yana nufar d'akinsa bin bayanshi tayi har ya shige d'akinsa,doguwar rigar jikinsa ya cire ya kwanta dan kansa kamar ya fad'o sabida ciwo ya kuma San rashin barci ne ya haddasa masa ciwon kai,Amnah zama tayi w gefen gadon tana k'ok'arin magana yayi sauri ya dakatar da ita ta hanyar d'aga mata hannu yace "dan Allah kibari ina tashi daga barci zan miki bayani" juya mata baya yayi ko minti uku baiyi ba sai minsharinsa taji,blanket ta janyo ta k'ara rufe mishi jikinsa dan lokacin sanyi ne ta fito daga d'akin tana mamak'in abinda ya kawoshi gidanta da sassafen nan alhalin ba itace da girki ba, tunani ta hau yi ko fad'a sukayi da Firdausi dan Nazeer ba abinda ya tab'a fad'a mata game da zamansu da Firdausi sai dai kawai yace mata Firdausi na gaisheta,Wanda tasan fad'i kawai yake Firdausi bazata tab'a cewa a gaisheta ba,ganin tunanin data ke bashine mafita ba yasa ta mik'e tashiga kitchen dan ta d'ora breakfast.
Firdausi kuwa sai da ta ji fitar Nazeer tayi shiru ta daina ihun da take dan ta d'auka zai zo ya rarrasheta,mik'ewa tayi ta nufi d'akinta ta kwanta fuskar nan tata a kumbure ko sallah batayi ba tafara tunanin abinda zata yiwa Nazeer barci sama sama ne yafara d'aukarta ko mai ta tuna oho ta mik'e ta zauna tana mitsitsika ido palon kasa ta nufa taje ta zauna tana girgiza k'afa ganin har k'arfe shidda da rabi Nazeer bai shigo ba yasa ta mik'e da sauri tayi waje,Inda ake parking motoci ta duba taga ko motar Nazeer na gurin,tana ganin motarsa bata wajen wani irin ashar ta saki tana "kutumar ubancan yau ake yinta a gidanan an dade ana cin amanata yau wlh bazan yarda ba sai naci uban Nazeer" fuuuuuu ta koma ciki kamar zata tashi sama,tana shiga hijabi kawai ta d'ora akan sleeping dress d'in jikinta ta d'auki mukulin mota tayi waje.
K'arfe 7:15 ta isa gidan Amnah motar Nazeer data gani a k'ofar gidan ne yasa tafi to daga mortar da gudu ta fara buga gidan da k'arfi kamar mahaukaciya,da Sauri mai gadi yazo ya bud'e yana waye, tureshi ta yi daga gabanta da k'arfi sai da ya hantsila ta shige da gudu,Amnah da tana cikin shafa mai k'wank'wasa gate da aka ringa yi da k'arfi ne yasa ta fito a gigice ta nufo Palo ta ma manta towel ne a jikinta, sai data fito ta tuna tana k'ok'arin juyawa taga Firdausi ta shigo a guje,ware ido tayi tana kallonta Firdausi kuwa ta kama kug'u tafara magana,
" to yar iska k'wartuwa jarrababbiya maciya Amnah kinyi asara wlh, kin aure min miji kinzo kuma kina so ki k'wace min shi k'arfi da yaji dan Allah bakiji kunya ba yar gidan Mallam mustapha,yau fa kwana ne amma dayake ke jarrababbiya ce kin kirashi a waya yazo gidanki wanan masifa dame yayi kama kullum sai kin ja hankalinsa yazo ya kwanta dake kin koya mishi jarraba k'arfi da yaji, yanzu ma dasassafe nan daga zuwa massllaci ya zarto wajenki al halin nice da girki amma duk ililminki bakisan inya sadu dake lokacin girkina haramin ne,yanzu daga zuwanshi kin ja ya sadu dake shegiya jarrababiyya sai ki koma ciki ki fad'a masa yafito mutafi."
Tunda ta fara magana Amnah ta saki baki tana kallonta dan gabad'ya Firdausi ta canja mata sai kace mahaukaciya,girgiza kai Amnah tayi tace
"Firdausi na Riga na miki illa tunda na auri mijinki kema ki koyi jarrabar ko kya samu ki janyo hankalinsa,koda kuwa yana wajenki gangar jikinsa ne agurinki ruhinsa na wajena,in yana wajenki jinsa yake kamar akan k'aya har sai ya dawo wajena yake dawo wa dai dai,girl friend yanzu ma zuwan nan daya yi wajena munyi round one,barci ya d'aukeshi,shiyasa nayi wanka ina jiran inya tashi muyi round two,dan Allah ki juya ki tafi kar ki katse mana jin d'adi."
Tunda tafara magana Firdausi taji kamar guduma take k'wada mata k'irjinta kamar ya fad'o sabida bak'in ciki da gudu tayi kan Amnah tana,
"Allah ya tsine miki albarka Allah ya isa tsakanina dake,tace tana kamo towel d'in Amnah tana girgizawa, k'ok'awa suka farayi, Nazeer dake bacci hayaniya yaringa jiyowa daga Palo kamar a mafarki ya mik'e da sallati ya nufi palon dan yaga mai ke faruwa
[8/5, 9:00 PM] Sadnaf: R🅰SHIN H🅰KURI
Written by
💅💅SADNAF💞
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS (P.M.L)
*JINJINAN BAN GIRMA GAREKU MALLAMAN TRANSCONTINENTAL INA MUTUK'AR ALFAHARI DAKU WANAN SHAFIN NAKUNE*
*AUNTY AMEENA*
*AUNTY AINAU*
*AUNTY SURAYYA*
*AUNTY SADIYA*
*AUNTY NAFEESA*
*AUNTY SAUDAT*
*MOMI ADNAN*
*Allah ya barmu tare*💘💘💘💘💘💘💞💞💞💞💞💞
Page 24
A b'akin k'ofar d'akin ya tsaya yayi folding hanunsa yana kallonsu ransa a mut'ukar b'ace,yana tunanin lokaci yayi daya kamata yayi maganin Firdausi,
Keeeeeeee yace a tsawace "cikata" Nazeer yace a lokacin dayake k'arasawa wajensu,dasauri Amnah ta tureta tana rik'e towel d'inta Firdausi ta juyo tana kallon Nazeer cikin b'acin rai tace, "kayi asara wlh jarrababe ko kunya bakaji ba ka taho nan kana cin amanata daga zuwa massala"!!! Bai bari ta k'arasa ba ya d'auketa da tagwayen mari ya k'ara kifa mata mari,Amnah da sauri taje gurinsa tana so ta rik'e masa hannu sabida k'ara daga hannu yayi yana k'ok'arin k'wada mata wani marin,ture Amnah yayi dan Firdausi ta kai shi bango, abunka da farar mace tuni bakinta yafara jini yatsun Nazeer akwance a fuskarta magana Nazeer yafara yi cikin tsananin b'acin rai har yana in'ina," nagaji da abinda kike min Firdausi nagaji kin hanani zaman lafiya banida nutsuwa a gidana kin hanani barci na zo nan dan insamu nayi barci kin k'ara biyoni,kin raina ni baki d'aukeni a matsayin miji ba inkina zagina kamar kinsamu sa'anki ba dole bane zama dake inata hak'uri dake kin kasa ganewa har sai da kika k'ureni dan haka Firdausi ki tafi gidanku na"da gudu Amnah taje ta toshe bakinsa tana girgiza masa kai tana "pls karka Yanke hukunci a cikin fushi karkayi abinda zai sa kazo kana nadama pls kayi hakuri" Amnah tace hawaye na zubo mata dan tasan d'acin da mace takeji a zuciyarta idan Aka furta mata Kalmar saki,cire hanunta yayi daga bakinsa yace
" Amnah na gaji da abinda take min, na gaji dan bakisan abinda take min bane tunda na aureki nayi bankwana da kwanciyar hankali a gidana, kullum a fargaba nake in ranar girkinta ne bazan iya ba,na gaji Firdausi ki tafi gidanku na sake ki saki d'aya idan kinyi hankali na dawo dake", Amnah runtse idonta tayi da k'arfi hawaye na zubo mata dan Sam bata ji d'adin sakin da Nazeer yayi wa Firdausi ba,Firdausi kuwa kasa k'wak'waran motsi tayi dan bata tab'a tunanin Nazeer zai iya sakinta ba, k'irjinta sai dukan uku uku yake zubewa tayi a kasa ta fashe da kuka, Nazeer ya juya ya koma d'akinsa,Amnah dayake mace ce mai rauni da tausayi tuni itama tafara kukan,cak Firdausi ta tsayar da kukan da take tace,
"Kukan me kikeyi Amnah abinda kike so kenan a sakeni ki zauna ke kad'ai kin aure min miji na k'yalleki hakan ma bai isheki ba sai da kika rabamu hankalinki ya kwanta,Amnah bazan tab'a yafe miki abinda kika min ba sakayyar da zakimun kenan na hallacin dana miki" mik'ewa tayi tana share hawaye tayi hanyar waje Amnah da tunda Firdausi tafara magana take kuka dagudu taje tasha gaban Firdausi tana so ta bata hakuri,Firdausi ta tureta gefe ta fice waje tana kukan bak'in ciki.
Amnah d'akin Nazeer ta koma da gudu,tana shiga ta tarar dashi a zaune a gefen gado ya dafe kai dan Firdausi bak'aramin chaza masa kai tayi ba,zama tayi a agabansa ta tank'washe k'afarta ta kamo hanunsa tafara magana tana hawaye,
"Nazeer kayi hakuri nasan abinda Firdausi tayi ma bata kyauta ba kayi hakuri Allah ya huci zuciyarka amma ina Neman alfarma dan girman Allah ka dawo da ita d'akinta idan ba haka ba ni duniya zata zaga ace na auri mijin kawata nasa Kuma an saketa,baku tab'a rabuwa ba sai da ka auroni,yanzu kafin ta tafi kaji mai tace pls Nazeer badan halinta ba ka dubi girman Allah ka dawo da ita idan ba haka ba wlh mutane ni zasuyi ta zargin nasa a saketa" ta k'arashe zancen cikin rawar murya.
Cire hanunsa yayi daga nata yafara magana rai a b'ace,
"Amnah bazaki gane ba na dade ina hakuri da Firdausi, wlh da banida hakuri da tun tana amarya zan saketa zakiyi mamak'i inace miki tunda na aureta bata tab'amin girki ba sai dai 'yar aiki tayi min,banda manyan laifukan data ke min nake shanyewa wlh idan ba sakinta nayi ta je ta d'ana zaman gida ko na wata uku ne ba bazata tab'a chanjawa ba,dan haka kiyi hak'uri bazan iya dawo da ita ba yanzu sai ta kwana biyu a gidansu da kaina zanje insamu mahaifiyarta inyi mata bayanin abinda tayimin,ke Kuma kidaina tsoron Abinda mutane zasu ce dan mutane ba a iya musu ko da ban saketa ba bazasu rasa abun cewa ba akanki dan haka ki kwantar da hankalinki kinji".
Gyad'a kanta tayi tana share hawayen dake zubo mata dan har ga Allah ba haka taso ba," yauwa dan Allah maza kawo min breakfast naci yunwa nakeji"bata ce komai ba ta tashi tayi hanyar waje tana gyara towel d'in jikinta shi Kuma yabita da kallo yana tunanin hankalin da Amnah ke dashi duk rashin mutuncin da Firdausi tayi mata bata gani ba,take rok'on a dawo da Firdausi.
B'angaren Firdausi kuwa tana barin gidan Amnah, gidanta ta wuce tana isa tafito daga motarta da gudu ta zube a Palo tana rusa kuka dan sai yanzu taji kamar ta had'iyi zuciya ta mutu dan bak'in ciki zagaye palon tafara yi tana tunanin yanda zata koma gidansu ta zauna dan rabonta da gidansu ma ta manta,takuma San yanzu mahaifiyarta tana fushi da ita,dan Firdausi tun daga lokacin tayi aure taga ta samu duniya ta tattara kanenta da mahaifiyarta ta ajiye a gefe kasancewar mahaifinta ya rasu ana dab da aurenta da Nazeer,Kuma mahaifinta ba mai k'arfi bane huluna yake siyarwa na manya da yara,mahaifiyarta da suke k'iranta da Aunty ita Kuma kayan kolli take siyarwa a gida, da yamma Kuma tayi awara na siyarwa da haka suke samun abinda zasu sa a bakinsu tun lokacin da Aunty taga Nazeer yazo Neman auren Firdausi Tarasa inda zata sa kanta dan d'adi,dan tana tunanin karshen wahalarsu yazo amma abun mamaki Firdausi tana auren ta daina waiwayarsu dan sai tayi shekara bata je gidansu ba,sai dai in kanenta ne suka je gidan zata bada sak'o akai wa Aunty,Nazeer ne ma yakan je gidan inya samu sarari yaje su gaisa ya musu goma ta arziki dan mahaifinsu Firdausi mutumin kirki ne shi yasa Nazeer yasha alwashin taimaka musu bayan ya rasu inda Aunty data ga Firdausi ta watsar dasu,itama tayi k'ok'ari ta cireta aranta dan akwai rashin lafiyar da tayi kamar zata mutu Firdausi bata zo ta duba ta ba har ta warke shiyasa ta k'ara rik'e Firdausi a zuciyarta.
Firdausi d'akinta ta nufa tana kuka tana had'a kayanta tana Kuma tunanin da wane ido zata kalli Aunty dan Rabon data sa Aunty a ido ta manta,sai yanzu tafara nadamar watsar dasu datayi,cikin sanyi jiki ta had'a kayanta a cikin akwati ta kwashe duk wani Abu datasan na kud'ine ta nufi d'akin Nazeer ta hau yi mishi bincike,wani dan k'aramin brief case tagani tana bud'ewa taga kud'i ne yan d'ari biyar Biyar a cike da sauri ta rufe akwatin tana murna tayo wajen data sa akwatinta ta bud'e tasa briefcase d'in a ciki takai akwatin cikin mota,ta fara bin gidan da kallo tana k'walla dan tana tunanin yanda zata bar tangamemn gidanta ta koma gidansu mai d'aki uku amatse a haka ta shiga mota tana fargarbar yanda zata had'u da Aunty.
Sai data tsaya a hanya ta sisiyi kayan abincin da kayan amfani gida,kafin ta k'arasa gidan,tunda ga nesa tafara k'arewa gidansu kallo sakamakon chanjawa data ga gidan yayi,ya koma ginin zamani harda fenti,sai data k'araso k'ofar gidan ta k'ara tabbatar wa gidansu ne cikin sanyi jiki ta fito daga motar, ta samu wasu yara dasuke wasa a k'ofar gidan tace musu su shigar mata da kayan abincin ciki,Aunty dake wanke waken suya dazata yi awara dashi anjima,ganin yara nata shigo da kayan abinci ne yasa tafara tambayarsu da ga ina amma yaran basu bata amsa ba sakamakon yar rige rigen dasuka ringayi suna shigo da kayan,sai da suka gama shigo dashi Firdausi ta shigo da sallama tana sunkuyar da kai,
Aunty bokitin hanunta ta wular tana
"Wacece wanan?wa nake gani a gidan nan? Ko dai mafarki nakeyi? Firdausi kece a gidan nan? Hawaye ne ya hau zubowa Firdausi ta durkusa a kasa tace "Aunty nice" had'e rai Aunty tayi tace " lafiya mai kika zo nema a gidan nan ai na d'auka kin chanja wata uwar yaushe rabonki da gidanan wai ke nan kin samu duniya sai ki tashi ki kwashe kayanki ki koma dashi Alhamdulillah bamu dogara dake ba da Allah muka dogara,Kuma Alhamdulillah muna cikin rufin asirin Allah dan bamu rasa ci da sha ba,sai ki tashi hajiya ki barmin gida tun kafin na rakaki da muciya" Aunty tace tana duba inda ta ajiye muciya,kuka Firdausi ta fashe dashi tana" Nazeer ya sakeni"juyowa Aunty tayi da sauri tana kallonta cikin fad'uwar gaba taringa karanta innalillahi wa inna ilahi rajiun a zuciyarta amma a fili had'e rai tayi tace "au sai da aka sake ki kika San kina da gidan da zaki zo to ba a gidana zakiyi zawarci ba tashi kibar min gida" a takaice da k'yar Aunty ta barta ta zauna da sharad'in ita zata ringa soya awaran,da duk wani aikace aikacen gida,aranar Firdausi taci kuka ta gode Allah hankalinta bai tashi ba sai data ganta agaban murhu hayaki yabi ya cika mata ido kuka taringayi tana rok'on Aunty ta taimaka mata bazata iya ba,Aunty ta daka mata tsawa tace mata tun asali da icce suke amfani takuma sani dan haka tunda ta kaso aurenta rayuwar data bari abaya zata zo ta cigaba da yi.
B'angaren Nazeer kuwa bayan yaci abinci gidansu ya wuce ya fad'awa Hajiya Aliya abinda ya faru,inda ta nuna rashin jin dadinta ta umarce shi da in an kwana biyu yaje ya dawo da ita,daya tashi tahowa ya taho da little wacce Keda shekara uku da rabi mai kama da babanta,Amnah ya kaiwa ita wai taringa deb'e mata kewa Wanda hakan yayiwa Amnah d'adi sosai dan zama kad'aicin kan dameta.
[8/5, 9:00 PM] Sadnaf: R🅰SHIN H🅰KURI
Written by
💅💅SADNAF💞
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS (P.M.L)
PAGE 25
A ranar bacci bai ga idon Firdausi ba sabida zama tayi tana tunanin irin matakin da zata d'auka akan Amnah dan da akwai yanda za tayi ta kashe Amnah tsaf zata kasheta dan k'iyayya tunowa tayi yanda take fantamawarta ita kadai lokacin da ba a auro Amnah ba,kaf cikin kawayenta babu Wanda ya kamota dan har sha'awarta suke wai sai gashi Amnah duk tazo ta ruguza mata rayuwa jin dadin da take, wani zazzafen hawaye ne ya zubo Mata ta share hawayenta tana tunanin gurin wane mallami zata je da zai mata aiki akan Amnah ba tare da yaci kud'inta ba take ta tuna wata hatsabibbiyar kawarta Zulfa'a wacce take auren wani hamshakin mai kud'i sun had'u ne a dubai a inda take bata labarin itace ta hud'u a gurin mijinta amma yana aurota duk ya sakesu yanzu ita kad'ai ce awajensa sai yanda ma tayi da mijin da kuma danginsa,dan ko yaransa ma sun koma family house d'insu da zama ,da sauri Firdausi ta janyo k'aramin wayarta ta kunna tafara neman lambar zulfa'a a wayarta,luckily kuwa ta samu lambar wani irin ajiyar zuciya ta saki tana godewa Allah dan gani take kamar burinta ya gama cika Nazeer ya Saki Amnah,dialing d'in number tayi taji a kashe,ajiye wayar tayi da zumar gobe zata gwada layin watak'ila bata barin wayarta a kunne in tana barci,da wanan tunanin Firdausi tasamu barci ya d'auketa dan gani take burinta ya cika.
Amnah kuwa a ranar daddare kasa bacci tayi dan gani take kamar itace silar sakin da akayiwa Firdausi tashi tayi ta zauna tana kallon Nazeer dake barcinsa hankali kwance,tashinsa ta farayi ya bud'e idonsa a hankali ya zauna yana ce mata lafiya,sunkuyar da kanta tayi hawaye ya hau zubo mata tafara mishi zancen ya dawo da Firdausi,kallonta ya tsaya yi cikin mamak'i take yaji ransa ya b'aci anan ya rufeta da fad'a akan Firdausi zata tashe shi yana cikin barci karta k'ara masa irin wanan zai dawo da ita ba yanzu ba,kwanciyarsa ya koma yayi ya juya mata baya,Amnah kuwa cikin sanyi jiki ta bar d'akin ta nufi d'akinta ta gyarawa little kwanciya ta nufi band'aki dan tayi alwala.
Washegari tun k'arfe bakwai na safe Firdausi ta hau gwada layin Zulfa'a still a kashe a haka ta kammalla ayyukan gidan tana gwada wayar dan kanenta duk boarding sukeyi,tana gamawa ayyukanta d'akinsu ta shige ta zube a kasa tana rik'e k'wank'wasonta dan gajiya,dan rabonta data yi aikin wahala irin wanan har ta manta,komai sai dai ayi mata dan ko undies d'inta 'yar aikinta ke wanke mata,hawaye ta share tana kuma gwada wayar zulfa'a amma still a kashe,shigowar Aunty ne yasa ta ajiye wayar,Aunty tace,
"ke tashi ga wankina can kiyimin zanje kasuwa,ina dade ban dawo ba sai ki d'ora abincin rana," Firdausi cikin kuka tafara cewa "wlh Aunty ni ban iya wanki ba ki bayar ayi miki zan bada kud'in," wani mugun harara Aunty ta watsa mata tace " bazan bada wankin ba, ke zaki mun wai baki iya wanki ba, ki taso a gidanan kice min baki iya wanki ba wlh ke zaki min wanki nan, nan gidana ne sai yanda naga dama zanyi,kema yanda lokacin da kike gidanki kike abinda ranki keso bakya ganin girman kowa wai ke kin auri mai kud'i to yanzu dai ba a gidanki kike ba dan haka dole kiyi abinda na saki matsawar kina gidanan,ki tashi yanzun nan kiyi min wankina kafin na dawo" Aunty tace tana barin d'akin kuka Firdausi ta k'ara fashewa dashi sai data gaji dan kanta ta yo waje, ganin tulun wankin da aka ce tayi ne yasa ta k'ara wage baki tana kuka,komawa tayi d'akin ta k'ara d'aukar wayarta tana gwada layin Zulfa'a luckily kuwa taji ya fara ringing zama tayi da sauri ta kankame wayar a kunenta tana jiran taji an d'aga amma shiru ba a d'aga ba sai data mata miscall wajen talatin bata d'aga ba ,ita kuma bata hakura ba, Zulfa'a kuwa a lokacin ganin bak'uwar lambar ke k'iranta yasa bata d'aga ba dan bata d'aga lambar da bata sani ba,ganin mai k'iran bai fasa k'ira ba yasa ta d'aga a fusace tana "wayene"? Da sauri Firdausi ta gaisheta tafara cewa " hajiya Zulfa'a nice fa Firdausi 'yar kano da muka had'u dake a dubai wajen siyan Gold,"
"Ooooo Firdausi kece kiyi hakuri wlh na rasa contact d'ina ne ya kike"? Da sauri Firdausi ta fara cewa,
" 'yar uwa dan Allah ki taimakeni ina cikin tashin hankali yanzu haka ina gidanmu mijina ya sakeni,"subhanallahi mai yafaru haka" anan Firdausi ta labarta mata komai da irin mallaman data bi dan ta raba Amnah da Nazeer amma sai ci mata kud'i suke sun kasa rabasu, murmushi Hajiya Zulfa'a tayi tace " tun farko laifinki ne da baki nemeni ba da tuni wanan yar iskar ta dade da barin gidanki,dan kingani nan boka na aikinsa kamar yankan wuka,anan wajen da kike zaune zai miki aiki amma fa sai kin kashe kud'i" da sauri Firdausi tace " ko nawa ne zan biya wlh indai zai iya min aiki akan Nazeer ya saki Amnah na kuma mallakeshi sai yanda nayi dashi wlh ko da motata ce zan siyar yanzu ya zaayi ki rakani dan Allah ",
" Eee to gaskiya yanzu haka ina abuja naje ganin ginin da ake min,gobe nakeso da sassafe na kama hanyar Maiduguri dan acan yake nima akwai aikin dana keso yamin,in zaki iya zuwa Abuja ki sameni yau,gobe sai mu wuce tare shikenan," da sauri Firdausi tace " ba matsala yanzun nan zan kamo hanya pls ki turomin address d'in inda kike a abuja,katse wayar tayi da sauri ta d'auko k'aramin kit d'inta tasa kayanta kala biyu tasamu bak'in Leda ta juye duk kud'in da take dashi a ciki,ta d'auki atm cards d'inta tasa a jakarta, doguwar Riga kawai ta zura tayi waje da sauri ta hau motarta ta d'au hanyar abuja kasancewarta mace Mara tsoro bata tsoron driving mai nisa.
A takaice haka Firdausi taje ta samu Zulfa'a a abuja washegari suka wuce Maiduguri inda sai da suka k'ara kwana daya kafin su samu ganin boka kitif, daya kwashe kayansa agaban ma'aki wanda sallamar sa itace " boka kitif mai farinciki da aikin assha "to kana fad'ar haka ka gama faranta masa rai, suna zama ya hau musu bayanin abinda ke tafe dasu inda ya kalli Firdausi yace mata" gaskiya Amnah tana da tsari a jikinta sosai iyayenta ma a tsaye suke akanta kuma shi da aljannu yake aiki inya ce shi zai tura tsaf zata k'ona su dan haka sai dai yayi aiki akan Nazeer ya tsaneta daga nan sai ya saketa,wani irin murmushi Firdausi ta saki ta hau mishi godiya kamar zatayi sujada inda a karshe ta ce ya mallake mata Nazeer sai yanda tayi dashi tana kuma so ya maidata d'akinta,kafin ya saki Amnah ta mata wulak'ancin da bazata tab'a manta ta ba,wani ruwa ya janyo kamar jini yace tana komawa kano tayi wanka dashi karta goge jikinta har sai ruwan ya bushe dan kansa, ya kuma bata layya da aka sossoka allura a ciki yace ta binne aranar da ta koma Nazeer zai maidata d'akinta sai kuma yanda tayi dashi,Firdausi sabida murna duk kud'in dake ledar ta ajiye masa agabansa,atakaice haka suka baro Maiduguri Firdausi kamar ta taka rawa dan murna dan har ta fara hararo irin rashin mutuncin da zata yi wa Amnah,basu suka iso kano ba sai washegari da safe.
Sai data iso kano ma ta tuna Aunty aiki ta sata batayi ba ta tafi ji tayi bata wani tsoro tunda tasan yau zata koma gidanta,kanta tsaye ta shiga gidan ta samu Aunty na wanke wanke a tsakar gida,sallama tayi,Aunty ta amsa tana hararta tare da tambayarta daga ina take,durkusawa tayi har kasa kamar gaske ta hau mata karyar wai akwai kayan da tayi odernsu ne aka k'irata a can abuja kayan barayi sun sace shine taje can taringa zirga zirgan zuwa police station, sai yau ta samu ta dawo,tsaki Aunty tayi ta cigaba da wanke wankenta,Firdausi kuwa tayi sauri ta shige d'aki ta cire kayanta ta d'auki jarkar ruwan nan da aka bata ta shige band'aki ta watsa ruwan ta fito tana ganin Aunty ta shige d'akinta tayi sauri ta nufi soron gidansu ta hak'a rami ta binne layan ta koma d'aki ta zauna tana murmushi ita kad'ai.
B'angaren Nazeer kuwa tun lokacin daya saki Firdausi yaji kamar an yaye mishi damuwa,dan yanzu hankalinsa ya kwanta,bashida fargabar komai dan Amnah tana k'ok'arin kula da duk abinda yakeso yana kuma jin d'adin yanda take kula da little dan tamkar "yar cikinta ta d'auketa sai dai abinda ke rage masa jin d'adi shine tun lokacin da ya saki Firdausi Amnah ta rage walwala kullum sai dai tayi tagumi tana tunanin hakan kuwa na damunsa dan har tambayarta yayi abinda ke damunta tace masa ba komai,nan kuwa Amnah rashin dawo da Firdausi d'akinta ne yake damunta dan haka kawai jikinta ke gaya mata Firdausi zata iya mata mugunta dan tasan halinta tasan mai zata iya aikatawa shi yasa ta k'ara dagewa da addua.
Adai dai lokacin da Firdausi ta binne layar nan Amnah da Nazeer bayan sunyi break fast,Nazeer yaringa kalan Amnah sabida wani kyau dayaga ta k'arayi dan ko ina na jikinta ya k'ara ciccikowa,nan da nan yaji yana sha'awarta d'aukarta yayi,ya kaita d'aki yafara wasani da ita inda a karshe suka rayya suna,Amnah ta shige band'aki dan tayi wankan tsarki,Nazeer shi kuma a lokacin barci yad'an fara fusgarsa,zumbur ya mik'e ya zauna sakamakon muryar Firdausi dayaji ya karad'e d'akin,take yaga d'akin na juya mishi sai daya koma ya kwanta bayan minti biyar yafara dawowa dai dai,take yaji yana San ganin Firdausi ya mik'e da sauri dan ji yayi in bai ganta ba komai zai iya faruwa dashi ,kayansa ya hau sawa adai dai lokacin da Amnah ta fito daga band'aki sakin baki tayi tana kallonsa tace, " ya naga kana sa kaya bakayi wanka ba ahaka zaka tafi office d'in,bai ce mata komai ba yayi sauri yayi waje, bin bayansa tayi da sauri kafin kace me har ya hau mota ya bar gidan, Amnah zama tayi a Palo tana mamakin inda Nazeer zai je har ya kasa tsayawa yayi wankan tsarki ya fita ahaka,mik'ewa tayi tana tab'e baki tanufi d'akinta dan tayi walha.
Nazeer kuwa tafiyar minti goma sha biyar ne yakai shi k'ofar gidansu Firdausi yana zuwa ko iso bai bari anyi mishi ba ya fad'a cikin gidan,a lokacin Firdausi tana waya da Zulfa'a kamar a mafarki taji sallamar Nazeer,wani irin shewa tayi tacewa Zulfa'a "lailai boka kitif aikinsa kamar yankan wuka ko awa biyu ba ayi ba ga Nazeer a gidanmu," wani dariya Zulfa'a ta kwashe dashi tana ba ta fad'a mata ba,kashe wayar tayi ta fito fuska a d'aure,Nazeer a lokacin yana gaida Aunty data fito daga d'akin data ji muryarshi,hakuri ya hau bawa Aunty na saki daya yiwa Firdausi,Aunty tace mishi ba komai akarshe ta k'ara mishi nasiha na yacigaba da hakuri Firdausi,duk maganar Aunty take hankalinsa baya wajenta yana wajen Firdausi data tsaya a bakin k'ofa tana harararshi,a takaice sai da Firdausi tayiwa Nazeer wulakanci San ranta kafin ta kwashe kayanta ta bishi,inda suna cikin tafiya tayi mishi umarnin yafara kaita gidan Amnah tukuna kafin ya kaita gidanta,Nazeer kuwa cikin rawar jiki ya dau hanyar gidan Amnah dan haka kawai yaji yana tsoron Firdausi ga wani irin Santa dayaji yana Ratsa shi.
Wai ya labarin Al ameen ne?
Tunda ga lokacin da Amnah tayi Aure Al ameen ya tabbatar da ya rasa ta har abada inda yayi kuka, yayi kuka,yayi nadamar biyewa zuciyarsa,dan R🅰SHIN H🅰KURIN SA, yajanyo ya rasa wani b'angare na rayuwarsa dan yasan da wuya ya samu mace mai so ta faranta mishi kamar Amnah,a ranar da aka kai Amnah gidan Nazeer ranar dan k'aramin hauka ya kusa yi dan yana tunanin Nazeer shima yagama sanin Amnah yaji shima abinda yake ji,ganin zuciyarsa na Neman bugawa yasa yafito ya hau mota yanufi cikin gari inda yan shaye shaye suke zama yana zuwa yace su bashi abinda zai sha ya manta Amnah,da sauri wani a cikinsu ya bashi kayan mayye mai k'arfin gaske a take ya shanye duka,cikin minti talatin ya bugu yafara surutai yana kiran sunan Amnah tazo ta bashi kayan dad'insa karta bawa Nazeer,tunda ga lokacin Al ameen ya koyi shaye shaye da zarar yaji Amnah ta fad'o masa zai d'aga kwalba ba irin magiyar da hajiya Mariya bata mishi ba akan ya daina zata samo mishi wacce tafi Amnah,yaki yace shi da aure har abada.
0 comments:
Post a Comment