" yana ga kina mamakin ganina hajiya Amnah,ki rufe bakinki ki maida idonki ki daina mamaki dan baki isa ki rabani da mijina ba tare kika ganmu bayan cin amanata da kikayi har k'ok'ari kikayi wajen raba mu to burinki bai cika ba,dan kinganshi nan yaje ya dawo dani sai dai ki hadiyi zuciya ki mutu kuma yanda kika ganmu haka zaki hakura ki barmu ki koma gidan mahaukacin mijinki dan dashi kika fi dacewa ni zan tafi dan dama zuwa nayi na fad'a miki mijina ya dawo dani kidaina murna, kuma wlh sai kin bar gidanan"
tunda ta fara magana Amnah ke kallon Nazeer daya sunkuyar dakai ko k'wak'waran motsi ya kasa yi murmushi tayi daya bayyana hakorinta tace,
"Firdausi kenan akan mai zan rabaki da Nazeer ni nafi kowa murnar dawowarki dan nasan in ba shi da kaddara ya hau kansa ba babu Wanda zai iya zama dake sai shi,sanan ina so kisan Abu d'aya Firdausi yanda ban isa na rabaki da Nazeer ba,kema baki isa ki rabani dashi ba wlh, sai dai idan Allah ya hukunta cewar sai mun rabu shiyasa nake so nabaki shawara da ki yar da makamanki karki ja da yin Allah,amma kuwa in kika dage kece zakiyi nadama a karshe dan kingani nan da Allah subhanahu wata Allah na dogara duk rayuwar dazanyi tunda ga lokacin da ya halliceni har zuwa lokacin da zan koma gareshi yariga ya sani,da wanan nake baki shawara karki wahalar da kanki dan insha Allahu duk mugun nufinki akaina Allah bazai baki iko ba dan Allah ba azzalumin sarki bane,ban tab'a nufarki da mugunta ba duk wani Abu da kika k'ulla insha Allahu sai ya warwarwe da izinin Allah,dan haka ina so ki juya kibarmin gida ina murna sosai da dawowarki".
Murmushi Firdausi ta k'arayi tace " haka kika ce ko to mu zuba ni dake".
juyawa tayi,tayi hanyar waje zuciyarta na mata zafi,Nazeer yabi bayanta,Amnah tayi sauri ta kira sunanshi,juyowa yayi yana kallonta,Amnah ta nufi inda yake tsaye,ta tsaya a gabansa tace,
"Nazeer ina zakaje"?
Sai da ya kwashi minti biyar kafin ya iya magana dan ji yayi bakinsa ya mishi nauyi wajen magana,kau da Kansa yayi yace mata Firdausi zai kai gida,girgiza kai tayi hawaye na neman zubo mata,dan tasan Firdausi tayi nassara akan Nazeer,ce mishi tayi inya kai ta gida kar ya manta yayi wankan tsarki,ya kuma dage da addua,gyad'a mata kai yayi ya juya da sauri yayi waje sakamakon k'wala mai k'ira da Firdausi ta ringayi,yana zuwa ta rufeshi da fada kamar danta, Nazeer bai ce komai ba dan zuciyarsa wani irin tafasa yake dan yana bak'in cikin yanda Firdausi ke mishi amma ya kasa tab'uka komai.
Suna isa gida Firdausi ta ringa sauke ajiyar zuciya tana hamdala a ranta,dan Allah kadai yasan irin zaman kuncin datayi a gidansu, Nazeer b'angarensa ya wuce yayi wankan tsarki,ya d'aura alwala ya fito da zumar inyayi sallahr azahar sai ya wuce office,a Palo yaga Firdausi a zaune ta mimik'e k'afa sai murmushi take ita kad'ai tana surutai hanyar waje yayi tayi sauri ta kira sunansa,juyowa yayi yana kallonta,
" ina zuwa kake sauri haka" Firdausi tace tana mik'ewa,
"Massallaci zani daga nan na wuce office".
" ka dai San yau nice da girki ko,kar daga massalaci naji ka wuce wajen Amnah dan yanzu bazan lamunci wanan iskancin ba ni so nake ma na gaya ma gaskiya ka dawo da ita gidanan ,raba mana gida dakai yasa baka adalci watak'ila ma ba office kake zuwa ba, gidanta kake zuwa dan haka ka dawo da ita gidan nan ta koma can b'angaren da babu kowa,inaga kai ma hankalinka sai yafi kwanciya in muna waje d'aya da wanan zirga zirgan da kake".
Tunda ta fara magana yaji kamar yaje ya shak'eta amma abun mamaki ya rasa mai yasa ya kasa d'aukar mataki akanta,dan sai ya yunkura zai yi magana sai yaji ya kasa,hasali ma sai dai yaji yana bin umarninta kuma yana mamakin hakan a zuciyarsa, "kayi shiru ko bakaji mai nace bane Firdausi tace gabanta na dan fad'uwa dan tana tunanin ko dai asirin bai kamashi bane, " naji" yace yana juyawa tare dayin waje.
Firdausi tana ganin ya fita wayarta ta d'auka ta k'ira Zulfa'a tana d'agawa ta hau cewa,
"Kawata asirin nan kamar bai gama kama Nazeer ba dan naga baya bin umarnina sosai,dan so nake na mallakeshi sosai yanda duk abinda nace ayi a gidanan shi zaayi,Kinga zanji d'adin cin uban Amnah kenan kafin ya saketa dan yanzu ma haka ma nace masa ya dawo da ita gidanan,yanda zata gane shayi ruwa ne Wanda take takama dashi,shima sai yanda nayi dashi", dariya Zulfa'a ta kyalkyale dashi tace ta mata dai dai ta k'ara kiran Boka kitif tace mishi ya kama mata Nazeer sosai,da haka sukayi sallama ta kashe wayar ta k'ira boka kitif ta gaya mishi,inda ya mata alkawarin zai mata aiki akan Nazeer.
Nazeer kuwa bayan ya bar office gidan Amnah ya wuce,yaci abinci, yayi sallah daya tashi tafiya ya gaya mata yana so ya had'asu waje d'aya da Firdausi ta fara shirya kayanta,cikin mamaki take tambayarsa akan me zai had'asu gida d'aya da Firdausi alhalin yasan halinta an raba musu gida ma biyota takeyi tayi mata rashin mutunci ballantana yanzu kuma in an had'asu a gida d'aya,shiru yayi yana nazarin maganarta yaga kuma hakane shima bai San dalilin dayasa yake bin umarnin Firdausi ba,d'agowa yayi yace mata tayi hakuri ta koma can d'in shima zai fi samun kwanciyar hankali in suna waje d'aya bata ce masa komai ba sai girgiza kai datayi dan tasan ba yin kansa bane,tunda Firdausi ta dawo yazama wani iri.
A ranar daddare bayan sallar isha Amnah ta kira Ummi a waya bayan sun gaisa take ce mata dan Allah ta ringa sata a addua ita da Nazeer na Allah ya karesu daga sharrin Firdausi Inda ummi cikin tashin hankali take tambayarta da mai yafaru,anan take labarta mata da kuma yanda sukayi da Nazeer akan ta koma gidan Firdausi,Ummi ce mata tayi ta kwantar da hankalinta zata ringa sata a addua,da haka sukayi sallama,aranar Amnah kwana tayi akan sallaya tana adduar Allah ya kareta da Nazeer daga sharrin Firdausi,inda itama Ummi aranar itama kusan kwana tayi tana taya Amnah addua,da yake washegari juma'a wainar gero ta siyo mai yawa ta rabawa Al majirai da safe,da rana kuma tayi sadakar shinkafa da wake,da niyyar Allah ya kau da fitina daga gidan Amnah dan tana tsoron auren Amnah ya k'ara mutuwa a karo na biyu.
A takaice a haka Amnah ta koma gidan Firdausi,badan ranta naso ba,dan dai kawai tana tausaya wa Nazeer ne dan taga alamar Nazeer ma tsoron Firdausi yake,ita kuwa Firdausi dawowar da Amnah tayi gidan bak'aramin farinciki tayi ba dan rashin mutunci take wa Amnah San ranta,Nazeer bai isa yayi magana ba,inda ita kuma Amnah bata jurewa ko yaya ne sai ta rama dan sau uku kenan tana nadawa Firdausi duka dan har b'angarenta take zuwa ta nemi ta mata rashin mutunci,inda hakan ya d'aga hankalin Firdausi ta k'ira boka kitif tace masa Nazeer har yanzu ya k'i ya saki Amnah,ce mata yayi ta kwantar da hankalinta adduar da Amnah ta Dage takeyi ba dare ba rana shi yasa Al ameen ya kasa tsanarta ballantana ya kai ga sakinta amma yana nan yana aiki akansu, Firdausi kuwa ba k'aramin bak'in ciki ne ya rufe ta ba da taji mai yace a karshe ta ce masa tana so ya maida Nazeer mace indai yana b'angaren Amnah dan bata so Amnah tasamu ciki har su rabu da Nazeer,boka kitif ce mata yayi wanan yafi komai sauki.
Tunda ga lokacin in Nazeer yana b'angaren Amnah baya iya tab'uka komai gashi koda ma ba abinda aka masa namiji ne shi da bashida k'arfin sha'awa sosai,hakan kuwa bak'aramin d'agawa Amnah hankali yayi ba dan ko a da hakuri kawai take yi bawani gamsuwa take ba,tashin hankalinta kuma tunda ta samu ciki taji tana da k'arfin sha'awa dan ko kwana biyun dayake yi a wajen Firdausi d'aurewa kawai take,har kwanakinta ya zagayo, in kuwa kwananta ne ta lura da take takensa barci zaiyi bazai nemeta ba takan yi iya k'ok'arinta taga taja hankalinsa ya sadu da ita,kwatsam kuma sai gashi yanzu da cikinta yakai wata hud'u da take bukatar Nazeer sabida sha'awarta karuwa yake,sai gashi inya zo b'angarenta baya iya tab'uka komai sai yagama tayar mata da hankali zai hau girgiza mata kai yana hawaye yana ya kasa shigarta bai San mai yake damunsa ba,wanan matsalar data kunowa Amnah ne yasa ta fara rama dan a bak'aramin tashin hankali take ba,inda Firdausi ita kuwa tasan mai ta aikata,ranar kwananta ma har tura Nazeer take d'akin Amnah,inda inyaje sai dai ya tsokano Amnah aranar sai dai ta kwana tana kuka.
Wataran Amnah ita keda girki tun safe tarasa nutsuwarta dan ita kad'ai tasan halin datake ciki,bayan sun gama cin abinci Nazeer yayi tagumi yana tunanin matsalar da yake ciki,dan ko shi Kansa yana tausayawa Amnah sosai dan wata d'aya da sati kenan Rabon da ya kusanceta,ya kuma rasa dalilin daya sa sai yana b'angaren Amnah yake kasa komai,inda itama Amnah tana daga gefe tana kukan zuci dan Allah yasan tana cutawa hakurinta ya kusa karewa,ahaka Nazeer yaje ya kwanta cikin sanyin jiki,Amnah tabi bayansa,ganin ya juya mata baya ne yasa ta fashe da kuka, Nazeer shi ma ya mik'e ya zauna yana hawayen yana ya rasa mai yake damunsa ta tayashi da addua tacigaba da hakuri,jawota yayi yafara rarrashinta daga nan kuma ya hau wasani da ita, jikin Amnah har wani rawa yake, tana adduar Allah yasa ya iya biya mata bukatarta amma abun haushi sai gani tayi yafara girgiza kai,hankad'ashi tayi da k'arfi tabar d'akin da gudu,ta nufi d'akinta tana kuka, aranar sai data yi kukan rabuwa da Al ameen tayi ta tunaninshi dan wani sain har guduwa take dan jarrabarshi,dan ko period take baya barinta sai ya jagwalgwala ta,a ranar kwana Amnah tayi tana kuka barci bai ga idonta ba,inda a karshe ta fad'a band'aki tayi wanka tafito ta hau kan sallaya taringa kaiwa Allah kukanta,inda b'angaren Nazeer shima kukan ya fashe dashi yana tunanin yanda akayi baya iya biyawa Amnah bukatarta.
Washegari bayan Nazeer ya tafi office Amnah na zaune ita kad'ai ta rapka uban tagumi tana tunani dan Firdausi fantamawarta kawai take batada matsalar komai,Nazeer na fita take ficewa dan gani take ta gama da babin Amnah dan tasan Amnah tana cikin tashin hankali kuma duk abinan da ake bata San Amnah nada ciki ba,sallamar da akayi ne ya dawo da Amnah tunanin data tafi,dagudu ta mik'e taje ta rungume Aunty Aisha da Aunty Amrah da suka kawo mata
ziyarar bazata,su kuma suka saki baki suna kallonta dan gabad'aya ta rame kana ganinta kasan tasha kuka,Aunty Aisha mai tsananin tausayi nan da nan ta hau tambayarta mai ya sameta hawaye na zubo mata,hakan da Amnah tagani ne yasa kukan da take b'oyewa ya fito kuka tayi San ranta suma suka hau tayata duk da basu ji dalilin kukan nata ba amma sun San watak'ila Firdausi ce ta sako ta agaba,tambayarta suka tayi tace musu babu komai babu yanda basuyi da ita ba akan ta fad'a musu tak'i da suka zuciya sukace mata Ashe har akwai abinda zata b'oye musu,sanan ta sunkuyar da kai cikin tsananin kunya ta basu labarin,sallati suka saki gabad'ayansu suna mik'ewa a tare Aunty Aisha har da k'ara fashewa da kuka tana wanan ai ba k'aramin matsala bane da zata ja bakinta tayi shiru,irin wanan sai yakai ta hallaka,da sauri tayi waje tana dole ta sanar da Ummi basu ga ta zama ba,inda Amrah itama tabita abaya,Amnah k'iransu take amma ina tuni har sun bar gidan,komawa tayi ta zauna hawaye na zubo Mata ta na hararo irin kunyar da zataji insuka had'u da Ummi.
Su Aunty Aisha kuwa suna zuwa gida,suka labartawa Ummi komai basu b'oye mata ba inda Ummi ta hau sallati hankalinta a tashe tace bari babansu ya dawo su fad'a mishi wanan lamarin babba ne,aikuwa da Mallam Mustapha ya dawo Ummi zayyane mishi komai tayi shima hankalinsa ya tashi dan yasan 'yar tashi tana cikin jerin mata masu k'arfin sha'awa, atakaice Mallam Mustapha wajen wani babban mallami yaje mallam Isa inda ya mishi bayanin komai,a take yayi alwala yayi sallah raka'a biyu bayan ya idar yacewa Mallam Mustapha asiri akayiwa Nazeer,zai karya asirin da izinin ALLAH rubutu ya bashi yace abawa Nazeer ya shanye insha Allahu duk asirin da aka mishi sai ya karye,godiya mallam mustapha yaringa masa yadawo gida ya bawa su Aunty Aisha su kai mata dan sun kasa komawa bauchi,cikin murna suka nufi gidan Amnah.
[8/5, 9:01 PM] Sadnaf: R🅰SHIN H🅰KURI
Written by
💅💅SADNAF💞
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS (P.M.L)
PAGE 27
lokacin da su Aunty Aisha suka isa gidan suna zuwa suka tarar da Firdausi a b'angaren Amnah sai surfa mata zagi take Nazeer na zaune ya buga uban tagumi,hakan ne yabasu mamaki suka ja suka tsaya a bakin k'ofa suna kallon ikon Allah, Amnah kuwa tana durkushe a gaban TV stand d'inta tana gogewa ta shareta ta maida ta mahaukaciya dan aikinta kawai ta cigaba da yi dan idan da sabo ta saba,dan aikinta kenan in itace da girki tazo b'angarenta ta karaci rashin mutuncinta idan abun yayi yawa sai Amnah ta nada mata duka, wani doguwar Riga ne a jikin Amnah roba roba mai bin jiki, tunda Firdausi ta shigo bata d'ago ta kalleta ba,aikinta kawai take,Nazeer dake gefe kuwa sai cije leb'e yake jikinsa na rawa dan zuciyarsa wani irin tafasa yake dan tsananin bak'in cikin abinda Firdausi take wa Amnah amma abun haushi ya kasa d'aukar mataki sai dai ya zuba mata ido,Firdausi kuwa tana ganin Amnah ta barta sai haushi take ita kadai, wajenta ta k'arasa a fusace tafara dungure mata kai inda Amnah ta mik'e cikin zafin nama ta watsa mata zafaffan mari guda biyu,wani irin ja da baya Firdausi tayi tana dafe da kumatunta tana kallon cikin Amnah,matsowa ta k'ara yi tana kallon cikin dan ta gasgata abinda take gani,wani irin ashar ta kuntuma tace. "Kutumar uban can Amnah dama ciki ne dake bansani ba"?
Da Sauri Nazeer ya dago yana kallon cikin Amnah aikuwa cikinta ya d'an fito,hamdala ya hau yi a zuciyarsa yana godewa Allah,dan add'uarsa kenan kullum Allah ya bawa Amnah ciki, ji yayi Kamar ya je ya rungumeta amma ba hali.
Had'e rai Amnah ta yi tace,
", gashi kuwa kin ganshi ajikina ko na shege ne da kika wani ja da baya kina mamaki, ko dole ne in inada ciki kisani,"
Wani ashar d'in Firdausi ta kara kuntumawa tana " ina bazai yiwu ba wanan ba cikin Nazeer bane dan nasan babu yanda zaayi ma kisamu ciki dan Nazeer bashida!!!!!!!! Shiru tayi data tuna zatayi subutar baki, Aunty Aisha dake tsaye tana mamakin Firdausi da sauri ta k'arasa wajenta tana "ki k'arasa zancenki mana Nazeer bashida mai"? Atare suka juya suna kallon Aunty Aisha, Amnah ta yi sauri tace Aunty yaushe kuka shigo"?
" Firdausi dama haka kike wlh idan aka cemin zaki iya Rabin abinda naga kinyi yanzu wlh karyatawa zanyi,Aunty Aisha tace tana mata kallon mamaki,kama k'ugu Firdausi tayi tafara magana cikin rashin kunya, " wlh kidaina mamaki dan zanyi fiye da abinda kika gani yanzu dan ko kece watak'ila kiyi abinda yafi nawa ko kinsan ciwon kawa ta aure ma miji kuwa,duk mutuncin da mukayi daku,baku gani ba da kuka tashi bakuji kunyar d'aukar kanwarku kubawa mijina ya aura ba dan haka wlh tayi ta fuskantar tashin hankali da bak'in ciki a gidanan kenan har sai lokacin data bar gidanan da k'afarta dan na lura an kai sunan mijina wajen mallami bazai iya sakinta ba",
Murmushi Aunty Amrah tayi tace " aikuwa bazaki taba ganin ranar da zata bar gidanan ba wlh inkika ga tabar gidanan to ki tabbata mutuwa tayi aka tafi binneta ,sai dai ke ki tafi kibarta,kuma duk kulle kullen da kikeyi babu Wanda bamu sani ba kallonki kawai mukeyi,kuskure d'aya kikayi da kika manta ba aja da ikon Allah ki zuba ido kiga yanda yaran Mallam mustapha ke takama da ayar Allah,wlh asirinki yana dab da tonuwa gwara tun wuri ki gyara halinki," wani dogon tsaki Firdausi taja tace,
"Sannunku yan gidan mallamai ai nima da ayar Allah nake takama,ko kunya bakuji ba kun kwaso jiki kun taho gidan kanwa da sassafe za azo aci dankalin turawa acan kauyen da ake aure babu sai dai Asha koko da kosai,an!!!!!!!wani mugun mari Firdausi ta d'auketa dashi bata bari ta k'arasa zancen da take ba, "wlh zan barki kiyi komai amma banda tab'a min 'yayyena Mara mutunci kawai,dafe kumatunta tayi tana,
"Ni kika Mara Amnah wlh sai kin yi nadamar marina sau hud'u kenan kina gaura min mari,kuma wlh baki isa ki haihu a gidan nan ba sai dai ki haihu a gidanku zaki San kin mareni,"juyawa tayi ta kalli Nazeer dake zaune sai jijjiga kai yake idonsa jajjazur dan cikin zuciyarsa ji yake Kamar ya kashe Firdausi da duka amma ya kasa," sai ka tashi mu tafi ai tunda yau kwana na ne,ko kunya baka ji kana zaune wanan yar iskar take min rashin mutunci ita da 'yayyenta "wani tsakin ta kara ja ta kalli su Aunty Aisha da sukayi mutuwar tsaye suna kallon Nazeer,inda shi kuma Nazeer Kamar ya shige kasa dan kunya dan ya kasa ma d'agowa ya kalli inda su Amnah ke tsaye,inda Amnah sabida bak'in ciki hawaye ne ya hau zubo mata dan gabad'aya Nazeer haushi yake bata sai kace mace, wani tsawa ta kara daka mai tana ya wuce su tafi tace,ya mik'e a hankali ya sunkuyar dakai yana gaida su Aunty Aisha, had'a baki sukayi wajen amsawa dan tausayinsa da su ka ji gwarzan namiji irinsa ya had'u da hatsabibbiyar mace,ahankali ya fice daga palon, Amnah ta fashe da kuka tana zama,akan kujera tana,
"Nagaji Aunty wlh nagaji,bazan iya cigaba da zama da Nazeer ba,sai yanda Firdausi tayi dashi, ba ya iya komai Aunty,yaushe zan cigaba da rayuwa ahaka ina cutuwa wlh" tace tana kara fashewa da kuka,zama sukayi da sauri kusa da ita Aunty Aisha tafara cewa
"Kiyi hakuri Auta karkice kin gaji,ba yin kan Nazeer bane,da ahaka yake?,girgiza kai Amnah tayi tana share hawaye,tace toh kingani, wlh bayin Kansa bane asiri aka mishi,jiya baba yaje wajen mallam Isah ya gaya mishi matsalarki shine da yayi addua yace asiri aka yiwa Nazeer har kusantarki da baya iya yi,shine ya bada rubutu yace abaki ki bashi yasha insha Allahu duk wani sihiri dake jikinsa zai karye,kuma Auta kidaina sakaci da addua,dan itace takobin mumuni,insha Allahu in muka koma gida zamu gayawa Ummi ta k'ara aiko miki da Adduoin tsarin jiki,tunda naga Firdausi ta na cin alwashin sai taga bayan cikin dake jikinki,yanzu ya zaayi kisamu ki bawa Nazeer rubutun nan yasha,"?
" sai dai in ya dawo d'akina, dan yau ita ta k'arbi girki,kuma bata ma bari ya zo wajena idan itace da girki,sai taga dama,"
"To gashi nan ki b'oye har sai kwananki ya zagayo ki tabbata kin bashi ya shanye," Aunty Aisha tace tana mik'a mata rubutun da hannu biyu ta k'arba tana musu godiya,inda su kuma sukayi ta bata shawarwari na taringa hakuri da Firdausi a karshe sukace mata ta d'aukesu tamkar kawayenta duk abinda ke damunta taringa k'ok'ari tana fada musu karta b'oye musu komai dan bata da sama dasu, sai wajen k'arfe 12 suka bar gidan,Amnah kuwa bayan ta rakasu ta dawo sai murna take tana adduar Allah yasa asirin da akayiwa Nazeer ya karye.
Kasancewar ranar lahadi ne Nazeer babu inda yake zuwa amma sabida halin da yake ciki,kuma ranar girkin Firdausi ne yasa ya shirya ya tafi gidansu da little, dan tunda Amnah ta dawo ta k'wace 'yarta daga hanun Amnah,kuma bata samun kyakyawan kulawan daya kamata dan in zata fita yawonta ma barinta takeyi da 'yar aiki,shiyasa ya tafi da ita dan ya mayar da ita gurin Hajiya Aliyah.
Firdausi kuwa tunda Nazeer ya fita tafara safa da marwa a palon tana tunanin yanda zatayi cikin Amnah ya zube dan tana tsoron tazo ta haifi namiji,dan tasan familyn kowa addua yake Allah ya bashi d'a namiji,hararowa tayi yanzu idan Amnah ta haifi namiji shikenan ta gama cin gado,da sauri ta k'ira boka kitif yana d'agawa tahau gaya mishi yamata aiki akan Amnah cikinta ya zube,boka kitif yace mata indai cikin takeso a zubar sai tazo ta k'arbi abunda zai had'a da kanta,tayi amfani dashi cikin zai zube, cikin rawar jiki tace mishi zata zo amma sai jibi zata taho,lokacin Amnah ta k'arbi girki,ahaka sukayi sallama Firdausi ta na ta shirya irin muguntar da zatayiwa Amnah.
Ahaka Nazeer yagama kwanaki biyunsa a b'angaren Firdausi, ranar da zai koma d'akin Amnah da sassafe Firdausi tabar gidan ta dau hanyar maiduguri, Nazeer yana bacci bai bai ma sani ba,inda b'angaren Amnah ranar tamkar sallah take a wajenta dan ta na sa rai yau matsalarta zata zo karshe dan kwana biyun nan k'ara d'agewa tayi da addu'a bata barci.
Nazeer kuwa daya tashi yaga bai ga Firdausi ba da sauri ya nufi b'angaren Amnah yana dokin ganinta dan Firdausi gabad'aya hanashi ta yi yaje ya ganta,tun ranar da su Aunty Aisha suka zo a Palo ya tarar da ita ta na kwance akan 3seater,idonta a lumshe tana karatun Qur'ani,wani irin nutsuwa da farinciki,yaji ya rufe shi,yatafi ahankali yaje ya rungumeta,bud'e idonta ta yi ahankali ta zuba mai ido k'wala na zubo mata,girgiza mata kai yayi yafara rarrashinta yana shafa cikinta cikin farinciki,A takaice anan yayi breakfast ya shirya zai tafi office, Amnah kuwa ta shige d'akinta ta juyo rubutun a k'ofi tak'araso inda yake zaune,ta mik'a mishi,sai daya fara kallonta alaman yana neman Karin bayani,ta mishi nuni da hannu da yasha kawai,sai dai yayi bismillah ya k'afa kai ya shanye duka dan yasan Amnah bazata tab'a cutar da shi ba, yana ajiye k'ofin yaji kansa yafara juya mishi,ahankali ya kwanta,ya rik'e kansa bayan minti uku ya mik'e tsaye yana kallon Amnah wani irin runguma ya kai mata,ya d'agata sama yafara cewa ya warke,hanyar d'akinta yayi da ita ya direta akan gado,ya hau cire mata kaya, a takaice aranar Nazeer ko k'ofar gida bai leka ba dan sai da ya saukewa Amnah duk sha'awarta dan wani extra k'arfi yaringa ji,a take kuma ya hau tuna ya akayi ya dawo da Firdausi har tazo taringa rashin mutunci amma ya kasa d'aukar mataki akanta sai a lokacin yaji wani irin bak'in ciki ya rufeshi tsanar Firdausi ya k'ara darsuwa aransa, Inda Amnah aranar kukan farinciki kawai ta ringayi tana zubawa 'yayyenta addu'a dan tasan badan su ba da har yanzu tana cikin matsanacin hali.
[8/5, 9:01 PM] Sadnaf: R🅰SHIN H🅰KURI
Written by
💅💅SADNAF💞
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS (P.M.L)
*WANAN SHAFIN❤ NAKI NE KAWATA TA KAINA❤ UWARGIDA A GIDAN NURA TAKAWARKI LAFIYA ❤ KAWATA UMMIN AYSHA ,ILHAM DA AUTA ABDULRAHAMAN ALLAH YA BARMU ❤TARE KAWATA FIRDAUSI*
*JINJINAN BAN💝 GIRMA GAREKU💝 MEMBERS DIN💝 FIRDAUSI HAUSA NOVEL💝 NAGODE SOSAI DA K'WARIN GWIWAR DA KUKE💝 BANI*
Page 28
Nazeer kasancewar ranar bai fita ba zuba ido yaringa yi yaga k'arfe nawa Firdausi zata dawo dan bai sata a ido ba ma kwata kwata ballantana ta nemi izininsa,ahaka ya ringa zuba ido har akayi isha,ransa bak'aramin b'aci yayi ba Wanda hakan ya gaza b'oyuwa a fuskarshi, yana zaune a palon Amnah sai girgiza k'afa yake Amnah zama tayi a gefensa ta kamo hanunsa tafara mishi magana cikin sanyi murya
"Nazeer kayi hakuri dama nasan idan ka dawo hankalinka sai ranka ya b'aci amma inaso kasan wani Abu,kowane bawa a rayuwa sai Allah ya jarrabceshi,kai ma taka jarrabawar kenan ta silar Firdausi ka d'aure kaci jarrabawar nan insha Allahu Firdausi zata shiryu ni nagaya
ma,ka daina d'aga hankalinka akanta,Abu d'aya nake so dakai ka dage da addu'a sosai ka daina sakaci da addua ko a office kake karinga yi a zuciyarka duk abinda zatayi insha Allahu bazata ringa samun nassara akanmu ba,da haka zata gaji ta daina"
Tunda tafara magana ya juyo yana kallonta fuskarnan tashi a d'aure kamar itace Firdausin,
"Amnah bazaki gane abinda nakeji a zuciyata ba nagaji da halin Fridausi,bazata tab'a chanja halinta ba dan haka wlh hakura zanyi da iya gabad'aya na huta nafi samun kwanciyar hankali,yanzu ki duba kigani yau ban sa ta a idona ba ta fita, har yanzu kuma bata dawo ba,wai nan da sunan tana da aure,yanzu da ace little a gabanta take da ya zata bata tarbiyya tana wanan yawace yawacen,gaskiya Amnah rabuwa zanyi da Firdausi bazan ita ba" mik'ewa yayi ya nufi d'akinsa Amnah ta bishi da kallo ya har ya shige,tagumi tayi tana tunanin inda Firdausi taje har yanzu bata dawo ba.
B'angaren Firdausi kuwa ba ita ta isa Maiduguri ba sai wajen k'arfe biyar,tana zuwa ta kama hotel,tayi wanka taci abinci,tak'ira boka kitif a waya tace mishi ta k'araso anjima kad'an zata zo
Ana k'iran sallar magriba ta isa wajen boka kitif a lokacin babu mutane sosai agurin,sai daya gama sallamar kowa kafin yace mata tashigo,da k'irarin boka kitif mai farinciki da aikin asha ta shiga 'yar b'ukkar, zama tayi tana k'ara k'arewa wajen kallo,dan boka kitif ya shige ciki,jin motsin ya taho ne yasa ta zubawa 'yar karamar k'ofar ido dan taga shigowarsa dan ita har ta manta kamaninsa,abinda ta gani ne ya mutuk'ar razanata tana kau dakai,cikin fad'uwar gaba da tsananin tsoro tafara karanta innalillahi wa inna ilahi rajiun,boka kitif ne yashigo tsirara haihuwar uwarsa da ubansa ba komai a jikinsa,shi kuwa ganin yanda ta tsorata data ganshi, ne yasa ya kwashe da wani irin mahaukacin dariya,
Cikin rawar murya Firdausi tafara magana " Boka kitif mai haka zaka fito ba kaya a jikinka"? Wani dariyar ya k'ara kwashewa dashi yace
" yau yanayin aikin namu sai da fitowa ahaka hajiya ki juyo namiki bayanin yanda aikin namu yake karki b'ata min lokaci,"girgiza kai tafarayi da sauri tana,
" Gaskiya bazan iya juyowa ba boka kitif wanan fa haramci ne matar aure ce ni bai kamata naga tsiraicin wani ba ka taimaka kasa kaya dan Allah", wani mugun ashar ya d'ura mata yana,
"Karki raina min hankali kina nufin imaninki ya kai haka shine kike zuwa wajena,yau fa fitowa kikayi batare da izinin mijinki ba,ni ki juyo wankan magani zan miki kawai ki min aski da gashin zan had'a ayi miki aikin akan kishiyarki
Cikinta
ya b'are mijinki ya saketa"
Cikin tsananin tashin hankali Firdausi ta juyo ta kuma kau da kanta da sauri dan boka kitif bashida kyaun gani ko na sule biyar,ga wasu mugayen kuraje a jikinsa,
"Wanka kuma harda aski boka kitif gaskiya bazan iya,indai sai kayimin wanka nama aski zaka iya min aikin na hakura kaga tafiyata,mik'ewa tayi da sauri dan ta tafi,yayi Sauri ya damkota,ihu tasa,tana wayyo Allahna nashiga uku azo a ceceni,,
Boka kitif ya kwashe da wani irin dariya yana" baki shiga uku ba sai kinji aruwan cikinki,ke kin isa kizo nan baki biyamin bukatata ba ai baki isa ba sai nasha bakinki nasha nononki,na!!"
Wani razananan ihu
Firdausi ta kara saki data ji mai yake cewa tafara k'okarin fusge jikinta wani amai ne ya k'wace mata dan wani irin wari boka kitif yake yi,ganin ya nufo bakinta da wagegen bakinsa dake d'oyine yasa takara k'ecewa da amai,amma sabida kazanta boka kitif lashe aman yafarayi yana k'ok'arin had'a bakinsu,Firdausi kuwa tana ganin haka,tasa takalminta mai tsini ta bugi gabansa da k'arfi,wurgar da ita yayi,ya saki ihu,Firdausi ta kwasa aguje tayi waje, gudu take kamar ta hantsila,dan ba mayafi ba jakar da ta ciko da kud'i ga wayarta a cikin jakar,tana zuwa bakin titi,ta tsaya tana kuka,dan bata da kud'in da zata hau mota,ga ATM card d'inta duk suna cikin jakar,kuka taringayi wiwi tana tsinewa boka kitif,ahaka ta tsayar da abun hawa ta mishi k'watancen hotel d'in data sauka, ta hau ya kaita,mai gadin hotel d'in ta rok'i ya bata rancen kud'i zata bashi inta shiga ciki barayine suka k'wace mata jaka,cikin tausayawa ya bata d'ari biyar ta sallami mai abun hawa ta shige ciki da saurinta,tana shiga d'akin band'aki ta shige da gudu ta matsa MacLean a bakinta ta sakarwa kanta shower,sai data sami hour uku tana dirje jikinta kafin ta yarda tafito,aranar Firdausi taci kuka ta gode Allah,sai tsinewa boka kitif take,tunanin ta fara yi ta Inda zata fara dan duk wani Abu nata mai mahimmanci ta barosu acan, Dan duk wayoyyinta na cikin jakar,a takaice Firdausi sai data je banki tayi report d'in arm robbers ne suka mata sata, suka k'wace mata duk ATM cards d'inta,takardu suka bata tayi cike cike,suka bata wani su kayi blocking waccan,da haka tasamu tayi withdrawing kud'i tasiyi waya da sabon sim,Zulfa'a tafara k'ira awaya tana d'agawa ta hau bata labarin abinda boka kitif ya mata,dariya Zulfa'a ta kwashe dashi tace mata to sai mai ai is normal,you have to use what you have,to get what you want,is not everything money can buy,dan haka ba wani Abu bane dan boka kitif ya d'ana, girgiza kai Firdausi tayi tana wanan masifa da mai tayi kama,tambayar Zulfa'a tayi in ita ce zata yarda da boka kitif? Zulfa'a dariya ta kwashe dashi tana, na nawa kuma sai dai in ba biyan bukatar takeso ba,katse wayar Firdausi tayi hawaye na zubo mata dan tama rasa mai zata ce mata.
A takaice sai washegari Firdausi tabar Maiduguri, Wanda ba ita ta iso garin kano ba sai da aka fara k'iran sallahr ishai agajiye ta k'arasa gida ta nufi b'angarenta,turus tayi data ga side d'inta a rufe,akwatinta ta ajiye tayi b'angaren Amnah,a palo taga Nazeer a zaune yana kallon BBC, gabanta fara dukan uku uku, yake data ga yanda Nazeer ya d'aura fuska,sallama tayi,
Nazeer ya juyo yana kallonta cikin mamaki yana tambayarta lafiya,dan aranar da yaga bata dawo ta kwana a gida ba, washegari ya nufi gidansu Firdausi da sassafe,yana zuwa ya tambayi Aunty ko Firdausi tazo anan tace mishi bata zo ba Dan rabon data sata a ido tun lokacin da yazo ya maidata d'akinta,take Nazeer ya hau tunanin watak'ila Firdausi saurayine da ita a waje, cikin ladabi ya fad'awa Aunty irin abinda Firdausi ke masa, yayi hakurin amma yanzu yaga yana cutuwa dan haka tayi hakuri ya hakura da auren Firdausi cikin mota ya koma ya rubuta saki biyu a takarda ya koma ya bawa Aunty yace Idan ta dawo abata takarda Hakuri ya k'ara bawa Aunty daya ga tana hawaye ya d'auko rafar dubu ya ajiye mata agabanta yana tayi hakuri haka Allah ya hukunta sai sun rabu,amma insha Allahu zai na zuwa gaisheta shi da little,har yabar gidan Aunty kasa magana tayi dan duk da Firdausi bata kyautata mata bata so aurenta ya mutu ba.
Nazeer kuwa Sam bai gayawa Amnah sakin da yayi wa Firdausi ba daya dawo gida.
Nazeer mik'ewa yayi yace "Tambayarki nake lafiya mai kike nema a gidana ?" Firdausi kasa magana tayi jikinta ya hau rawa Dan tasan asirin data yiwa Nazeer ya k'arye,tsawan da ya k'ara daka mata ne yasa Amnah ta fito daga d'akinta da gudu,ganin Firdausi ta tsaya a bak'in k'ofa jikinta sai rawa yake yasa Amnah ta nufi wajen Nazeer da zumar ta bashi hakuri, kallon daya wurga mata ne yasa ta tsaya cak,
Wani irin murmushi Nazeer yayi yace " Ooh sai yau kika dawo daga yawon iskancinki,dasauri Firdausi tafara girgiza kai tana "wallahi ba yawon iskanci na tafi ba"
" To ina kikaje hajiya Firdausi "? In'ina Firdausi tafara yi Nazeer yace "well ba damuwata bace,kije gidanku na bada sak'o a baki"
"Kayi min rai Nazeer karka sakeni wlh na tuba",Firdausi tace tana zubewa a kasa,wani tsawa ya daka mata yana get out before I count 3,da sauri Firdausi tayi waje, Amnah tafara k'ok'arin ta bi bayanta,Dan Firdausi ta masifar bata tausayi,itama tsawan ya daka mata,na kar ya sake yaga k'afarta awaje,Amnah tsayawa tayi cak tana fashewa da kuka,Nazeer juyawa yayi ya nufi d'akinsa ya bar Amnah a tsaye tana kuka.
Firdausi kuwa dak'yar taje gida dan wani irin azabben ciwon kai taringayi,tana add'uar Allah yasa
Ba saki biyu yayi mata ba,lokacin data isa rarrab'ewa tafara yi a jikin bango Aunty ko kallonta batayi ba,ganin tak'i ta shigo ciki ne yasa Aunty tayi tsaki ta nufi d'akinta tana "ga sak'onki nan akan window", da gudu taje ta d'auko envelope d'in ta bud'e cikin fad'uwar gaba abinda tagani a rubuce ne yasa ta sakin ihu.
0 comments:
Post a Comment