~TRUE LIFE STOY~
FREE NOVEL
~NA~
*AYSHA A BAGUDO*
~DA~
*FAIZA HAMMADU BARAU*
~DEDICATED TO~ MIMI'S QUENN ( MY DARLING)
WATTPAD@HAU'ESH
PAGE 1
Kwance ummita take a kan doguwar kujera mai zaman mutun uku a parlourn mahaifiyarta mairo, idanunta sanye da farin glass wanda ya zame mata jiki , hannunta riƙe da littafin bulugul-maram tana nazarin karatun da malamin islamiyyar su ya koyar da su jiya, sosai tayi zurfi cikin nazarin, dan bata son ta zama koma baya a duk abinda ya shafi ɓangaren karatunta, bata son malamin ya yi tambaya a kan darasin sa bata kasance cikin mutum ta farko da zata soma d'aga hannunta domin ba da amsar tambayar da yayi ba.
Shiru ɗakin baka jin motsin komai sai bugun zuciyarta da iskar fankar parlour'n dake kad'awa a hankali, tana cikin karatun ta ja numfashi ta tsaya tare da sauke nannauyen ajiyar zuciya had'e da Jan tsaki a cikin ranta , saboda jin motsi da sautin muryar wanda yake ƙoƙarin shigowa ɗakin ,yaya Ma'aruf ne tsaye a bakin dokin kofa ya d'age labulen parlour'n, shi bai shigo ba, shi bai koma ba, yana faman cicciza lip's dinsa na ƙasa, sanye yake cikin wani had'ad'd'en farin yadin Aba , ɗinkin rigar dai-dai gwiwarsa, hannunsa d'aure da agogon fata baƙi sajen fuskarsa na kwance sai sheki yake zubawa, ga wani mayataccen kamshin turare da ya cika mata hanci tun tsayuwarsa, gashin kan nan nasa ya sha gyara tare da askin afro kamar Ko da yaushe, yayin da idanun shi ke kallon cikin ƙuryar parlour'n yana fuskantarta, ku san minti biyu ya d'auka tsaye a gurin sannan ya ƙarasa shigowa ciki parlour'n bakinsa d'auke da sallama wanda yayi a ciki shi ma ta san yayi ne ba dan ita ba.
Kallo ɗaya tayi masa ta d'auke idanunta a kanshi tana sake sauke ajiyar ba tare da ta amsa masa sallamar da yayi ba, haka da tayi yayi bala'in taɓa zuciyarsa, take yaji wani duhu ya gilma a saman zuciyarsa dama gangar jikinsa, kamar yayi mata magana sai kuma ya shareta dan ya fita jin duk wani abinda take ji dashi, idan takamarta miskilanci ne to shi ya doketa, kuma idan da sabo ya riga da ya saba da wannan mugun halin nata kamar na mutanen farko, tunda ba yau ta saba yi masa ba, sai dai duk sanda tayi baya sanya gurin cin ƙaniyarta, ko yanzu ma tunanin abinda zai mata yake wanda zai dagula mata lissafi , zuciyarsa ke umartarsa da ya ƙarasa gareta ya soma da yayyaga littafin da ke riƙe a hannunta, sannan yayi mata dukan mutuwa ya nuna mata bakin rijiya ba gurin wasan makaho bane, Amman tunawa da yayi a cikin ɓangaren su yake yasa ya ɗauke idanunshi a kanta yana jan dogon tsaki, sannan ya samu guri can nesa kaɗan da inda take kwance ya zauna yana cewa "Mamana kina ina idan ba kya ciki nasan inda dare yayi min, dan bana kaunar zama muhalli ɗaya da wannan fat lion din?
Maganarsa ta doki kunnuwanta sannan ta wuce har cikin tsokar dake maƙale da zuciyarta sai taji tamkar ta tanka masa, amman tayi shiru dan ta san mama tana ciki ɗakin, ƙarshe ta sha duka a gaban wannan mugun azalumin, dan haka ta ja tsaki a cikin ranta ta juya masa baya, ta ci-gaba da karatunta, tayi tamkar bata san da wani halitta zaune a gurin ba, shi kuwa sai girgiza ƙafarsa ɗaya yake yana ciccin magani da jan tsaki .
Ko cikakken minti biyar bai yi ba sai ga mama ta fito daga uwar d'aka "A'a a she ma'aruf ne saukar yaushe a garin kai da muke sa ran ganinka gobe?
Sai da ya gaisheta sannan yace
"Ban Dad'e da dawowa ba nace na shigo mu gaisa da mamana"
"Madalla ɗan albarka ka kuwa kyauta da kazo gare ni, ya ka baro mutanen Kano fatan duk suna lafiya?
"Lafiyarsu lau duk sun ce a gaishe ku "Mama ta fad'ad'a fuskarta da murmushi
"muna amsawa"
Bayan sun gaisa da mama ma'aruf ya ɗan tsaya yaji ko ummita zata gaida shi kamar yadda sauran kannensa ke rawar jikin gaida shi a ko da yaushe, abin mamaki ya ji tayi shiru taƙi cewa komai bare ta waiwayo inda suke , hakan ne yasa ya tattara hankalinsa da idanunshi inda mama take, sai dai ransa yayi bala'in ɓaci.
"Har yaushe zata daina mishi kallon gani-gani?
"Tabbas lokacin yayi da zai tsananta cin ƙaniyarta, yayi wa kansa alqawari sai ya gyara mata zama, lumshe idanun shi ya yi har sanda yaji sautin muryar mama cikin kunnenshi.
"Ke ummita maza tashi ki kawo wa yayanki abinci ki had'o Masa da ruwan zafi " wacce aka kira da ummi ta zunburo baki ta ajiye littafin hannuta tana ƙoƙarin mi'kewa, taji yace "No mama Karki damu kanki a koshe nake fa, Sai da na cika cikina ɓangaren jiniya sannan na shigo nan"
Ya fad'i haka ne saboda baya bukatar ummita cikin lamarinsa, shi asalima baya son kasancewarsa a duk inda take kallonta kawai na haddasa masa ciwon kai da ɓacin rai mara misaltuwa, duk cikin family's dinsu babu wacce ya tsana kuma baya son kasancewa tare da shi kamarta, ko kaunar ganinta baya son yi, yana jin da yana da hali da ya gogeta a cikin ahlinsa ..
"To ai shikenan Wani abincin zaka ci da rana a dafa maka ? Mama ta fad'i haka tare da zama tana Janshi da hira.
"karki wahalar min da kanki mamana daga nan gidan big sister zani ba kuma zan dawo ba Sai dare "
"Tou shikenan idan kaje ka gaishe min daita"
Cike da sanyin jiki ummita ta miƙe tsaye ta d'auki littafinta ta nufi d'akin mama tana cewa
"Aikin banza kawai malam, ai ko ba kace a barshi ba, daman ba wahalar da kaina zanyi gurin wani kawo maka abinci ba, dan mai iyayin tsiya kawai taja tsaki ta zube a kan bed tana sakin numfashi ..
Ma'aruf ya dad'e a ɓangaren Mama suna zantawa sannan yayi mata sallama ya bar part din, Kai tsaye gidan big sister ya nufa a nan ya wuni zur sannan ya koma gida .
******
Kamar kowane dare, karatu take a parlour'nsu har sai da taji kanta yayi mata nauyi alamun yana buƙatar hutu, sai faman hamma take zubawa idanunta sun Kad'e sun yi jazir sai kace wacce tasha kayan maye.
"ya dai?
"Lafiya kuwa Ummita yau ma ko ciwon kan ne ?
"Ki fa dinga sararawa kanki da yawon karatu, kallon yaya rayhan tayi, dan tuni har ta soma ganinsa dishi-dishi.
"wallahi yaya ba ciwon kan bane amman dai ina jin kaina yayi min nauyi ba kaji yadda nake jina ba yanzu, tayi maganar tana hamma yayinda ta miƙe tsaye domin shiga d'aki, tsaki yaya rayhan ya ja "ba dole ki yita Jin kanki yana miki nauyi ba, ta ɗan tsaya had'e da juyo wa suna fuskantar juna kafin daga baya ta sakar masa murmushi.
"ya kake son nayi yaya ?
Dole nayi karatun nan da, domin bana son na zamo koma baya,nafi son komai aka tambaye ni na zamo farko gurin bada amsa ko baka jin daɗin yadda sakamakona yake fitowa?
"Ina ji mana amman duk da haka kina buƙatar hutu ko dan ki dinga dan bani lokacinki"
Murmushi ta sake sakar masa "shikenan zan yi kokari yaya yanzu dai sai da safe ta furta da wani guntun munafikin murmushi wanda iyakarsa gefen baki "okay my wife sai da safe Allah tashe mu lafiya daga inda yake ya huro mata iskar bakinsa murmushi kawai tayi tana juya masa baya shima y asan bazata maida masa Marta ni ba"
A hankali ya miƙe ta nufi waje inda mazan gidan dana unguwa ke zaune suna shan iska har ma'aruf wanda shi yake riƙe da wayarsa yana charting da budurwa meenah...
*******
Washe gari ummita a hankali take d'aga kafafunta tana tafiya Kamar bata son taka ƙasa dan ku san duk sauran yan uwanta sun dad'e da dawo daga makaranta, tana shigowa harabar gidan da yaya ma'aruf ta soma cin karo, tana ganinsa tayi tsalle kamar wacce aka tsinkara ta manne a jikin bagon tana jiran ya wuce sannan ta shige ciki ..
kallonta Kawai yayi kana ya girgiza kai duk da sauri yake saboda abokansa da ke waje zaman jiransa hakan bai sa yaji zai iya barinta ba, dan haka ba zato ba tsammani taji ya cafki tsintsiyar hannunta cikin nasa,cikin tsoro ta juyo suna fuskantar juna dan dama ta kawar da fuskarta gefe saboda bata son ganin fuskarsa , ranta a matuƙar ɓace tace.
"Wai meye haka malam?
Bai ce mata komai ba ya soma ja hannunta da ƙarfin tsiya tana turjewa."Wai meye haka yaya ma'aruf nifa bana son wulakaci, ta yaya ban shiga shirginka ba ka dinga k'ok'arin shiga nawa ?
"Karya kike fat lion ke kika soma Shiga shirgina dan haka dole nima na shiga shirginki,ni zaki gani ki wani manne da bango kamar kin ga mugun abu?
"Ni ka sakar min hannu dan Allah "
yaƙi sakinta saboda ya d'auki alqawarin sai yayi maganin iskancin da ke damun tunaninta,kai tsaye part din su ya nufa da ita aiko take jikinta ya kama rawa dan ta san mai kwatarta a hannunsa sai Allah , addu'a ta shiga yi a cikin zuciyarta Allah ya kawo mata d'auki saboda ganin yana k'ok'arin sunce belt d'insa, a hankali ta soma motsa bakinta "plz me zaka min Yaya ma'aruf ?
"kwakwalwar ki da tunaninki nake son wanke miki ya bata amsa yana tamke fuska, sake tsurewa tayi ganin har ya gama sunce belt d'insa ya zare daga jikin wando ya cilla Saman katifa.
tace "plz kayi hakuri wallahi na bar duk abinda nake maka,tsaki ya ja had'e da d'aukarta ya makata a saman katifar "ai daman kullum idan kika zo hannu haka kike cewa kin bari gobe idan kinga idanun mutane ki ƙara, gara ma ki yiwa mutane shiru dan abinda zan miki har ki mutu ba zaki manta da ma'aruf ba a rayuwarki dan yau hukuncin ki sai nayi sex dake ...zaro Ido tayi a matuƙar tsoro ce, bakinta da zuciyarta rawa suke gurin cewa.
"me kace yaya ma'aruf?
"Shegiya abinda kunnenki yaji shi nace ...."
Kafin tace wani abu ya fixgota ta fado jikinsa ya zare karamin hijab din da ke sanye a jikinta yayi Jifa da shi ƙasa ya fara romancing dinta a zafafe " ita kuwa take ta shiga aikin tutturesa da kuka amman bai ma san tana yi ba ,haka yayi ta abinda yaga dama da ita, jin bata motsi ya bar abinda yake sai alokacin ya lura da yadda bata fitar da numfashi .
Kiran sunanta ya shiga yi amman shiru yasa hannunsa ya tallabota jikinsa yana kai hannunsa dai-dai hancinta nan ya fahimci suma tayi da sauri ya shiga bayin dake manne da d'akin ya dibo ruwa ya ɗan watsa mata kad'an taja dogon numfashi ta bud'e idanunta a tsoroce, tana kallonsa babu riga a jikinsa jikinta ya kama rawa ganin haka ,yace "relax ba abinda zan miki matsoraciya kawai ga tsoro ga ban tsoro maza ki tashi Ki gyara fuskarki ki fitar min a d'aki ..
Ahankali ta janyo hijab dinta ta sanya jikinta na rawa ta soma tafiya har ta isa bakin ƙofar d'akin ba tare da ta d'auki jakar makarantarta ba taji sautin muryarsa "fat lion .... baki d'auki jakar makarantarki ba, bata juyo ba har sai da ta Kai ga fita daga d'akin gaba d'aya sannan ta juyo tana kallonsa a yatsine "ka miko min ta fad'i haka tana Miko masa hannunta "
"Wannan kuma karya ki yarinya,idan kina buƙatar jakarki ki dawo ki d'auka idan ba kya buƙata gud kina iya tafiya abin ki wannan ba damuwar ma'aruf bane.
"to baza a dawo ba, ɗan iska mai fuska biyu ni daman na dad'e ina tunanin dalilin da yasa na tsaneka a rayuwata, ashe dai kai ɗin tantiri ne mai fuska biyu a baki Allah a zuciya fir.....
K'ok'arin cafkota yayi aiko ta kwasa a guje tayi hanyar bangarensu tana haki ..
Tana barin wajen ya kwashe da dariyar mugunta sannan ya soma gyara jikinsa "shegiya a she dai karyar rashin kunya kike ,da kin tsaya Kinga yadda zanyi da ke ,sauya wasu kayan yayi saboda na jikinsa sun ɗan soma yamutsewa wayarsa ce ta d'auki ƙara ya d'auka tare da d'aukar jakar makarantata ya fito daga d'akin yana waya da d'aya daga cikin friends d'insa "jafar gani nan fitowa plz yayi maganar yana ajiye jakar makarantarta a bakin kofar d'akin ya san ko ba ita ba wani zai gani ya shigar mata da shi ya kama gabansa ..
Bayan ya fito suka gaisa da sauran abokansa sannan ya ja jafar suka nufi unguwar marcas gurin budurwarsa suhaima dan tunda ya dawo bai sanyata acikin idanunshi ba tsaye suke a bakin Ƙofar gidansu, Murmushi ta sake sakar masa mai narkar da zuciya a karo na biyu, "ai na d'auka ba zaka zo yau ba " girgiza kai yayi cikin farin ciki ya lakuce mata hanci
"kema kin san dole zan zo naga gimbiya ta sake yin Murmushi mahruf dina ....."na'am suhaima dan Allah mahruf karka juya min baya dan mutuwa zan yi idan haka ta faru ina maka son da ni kaina ban san adadinsa ba, tun daga ranar da muka had'u na rasa gane kaina da tunanina da na rasa ka gara na mutu tun kafin lokacin "bana son jin wannan maganar taki, sau nawa zance miki ki daina batun mutuwar nan?
muna tare fa kina cikin zuciya kece mace ta farko da zuciya ta zaɓa domin inganta rayuwata idan babu ke suhaima nima am nothing, baza ki mutu ba sai mun kai ga mallakar juna mun tarawa mamana ya'ya da jikoki masu kyau da ban sha'awa ya ƙarasa faɗar maganar yana tsareta da manyan idanunshi gaba ɗaya ya susuta mata zuciya yadda yake caring dinta a soyayya yasa Kullum take jin matsawar ba shi ba ba zata Iya rayuwa da kowa ba, tana alfahari da shi domin samun irin ma'aruf babban sa'a ce, duk macen da ta san ciwon kanta dole tayi farin ciki ga shi ita Allah ya bata shi ba wayonta ba balle dabararta .. .
Juya idanunta tayi cikin son burge shi sannan ta sake gyara tsayuwarta tace ya kamata ka koma gida kaga yamma tayi kar a yi ta nemanka ta fad'i haka cikin tsigar tsokana, harararta yayi Shi ma cikin sigar wasa yace "shikenan tunda kin gaji da ganina zan wuce"
"no kar kayi tunanin haka ai bazan ta'ba gajiya da kai ba na san kana daf da sallamata,Kuma wannan shi ne lokacin wucewarta Murmushi yayi "ke ko"
Ita ma Murmushi tayi tana kashe masa Ido suka yi sallama cike da kaunar juna. A hankali ta juya ta nufi cikin gidan su tallafa kansa yayi cikin wani irin shaukinta .
A Mota ma hirar suhaima suke tayi da jafar har suka kawo gidan su Jafar ya sauke shi ya kama hanyar gida,Ko da ya ƙaraso unguwar su har an soma kiraye kiraye sallah dan haka ya tsaya yayi sallah sannan ya shiga gidan a dai-dai zauren gidan suka ci karo da ummita, kasancewar gurin da duhu sakamakon ba a kunna inji ba, ba tare da ta san da zuwansa ba shi ma bai san da ita ba, baya tayi zata faɗi ƙasa ya yi saurin tallabo kugunta , tare da riƙe hannunta d'aya ita ma riƙe yatsun hannunsa tayi gam cikin nata saboda tsoro, cikin haka gurin ya gauraye da haske a matuƙar tsorace suke kallon ƙwayar idanun juna, wani sabon baƙon al'amari ne ya bakunci zuciyar su, a qalla sai da suka d'auki sama da minti goma suna kallon junansu sannan ya dawo hankalin sa ya tattarata ya yi wurgi da ita, cikin hargagi da matsanancin 'bacin rai yace.
"ke kina hauka ne?
"Ko wani abu na damun ƙwaƙwalwar ki ?
"wallahil azim kiyi hankali da ni fa idan ba haka zan iya karya ki a gidan , dube ki kawai mammuna mai shegen munin tsiya fat lion kawai, oya live this place stupid Kawai"
"Babu Inda zani tunda ba ganganci nayi ba sannan ai kaine fat lion din bani ba,kuma ai kaine kake ƙoƙarin had'a jikinka da nawa me yasa ba karni na fad'i ba idan ma mutuwa zan yi na mutu ?
"yi min shiru stupid Kawai ke bacin alaƙa ta jini ke kin isa ki tsaya kusa da ni ballantana har kiyi tunanin zan iya had'a jikina da naki ko da yake ke ɗin dakikiya ce ba zaki gane ba, bari kiji ko d'azu da kika ga na had'a jikina da naki ba wai da son raina bane, kawai a lokacin ina jin babu hukunci da ya dace da ke sama da wannan ne, sai daga baya na gane ci baya ne a gurina ko wani abu zan yi da mace ba dai ke ba ..
"Ke ko fuskarki mutum ya kalla babu abinda zai ji bare ya ...."
"Dakata Malam kada ka sake ce min dakikiya ko mummuna dan ko makaho ya shafa ya san waye mummuna cikin ni da kai...."
zaraf taji ya cafki tsintsiyar hannunta Wanda yaji tamkar bai riƙe komai ba saboda rashin kauri Yayinda kirjinsa ke faman dokawa Kamar zai fito waje "ni kike maidawa magana Ina fad'a kina fad'a sa'anki ne?
"Dan ubanki ko Usman bai isa ina fad'a yana fad'a ba bare ki kucaka da ke,da loma d'aya zanyi dake na gama dake ..
"eh din an maka kayi duk tsiyar da zaka yi idan har ba zaka daina furta wannan Kalmar gare ni ba har abada ba zan daina mai da maka da martani ba,idan kuma baka daina ba wallahi sai na dinga maka abinda yafi wanda nake maka yanzu, tayi maganar kanta tsaye ba tare da wani tsoro ko fargaban ba ..
"Ya ƙaraso gabanta Sosai yaja ya tsaya tare da tsareta da manyan idanun shi A hankali ya saki tsintsiyar hannunta had'e da turata tayi baya har gefen kugunta ya bugi bangon gurin, Aiko ba tare da ɓata lokaci ba ta ɓare baki ta soma Kuka saboda taji zafi sosai hannunta riƙe da kugunta ta kurma ihu "Wayyohhhyyy Allah yaya Ma'aruf zai kashe ni, bata san sanda tace
"Allah ya isa mugu kawai bazan taɓa yafe Maka ba har duniya ta nad'e, ko kabarinka naci da wuta bazan yafe Ma.."
Ai kafin ta ƙarasa ya buge mata baki "shiiiiii ki yiwa mutane shiru da wannan ru'ba'bben bakin naki wawiya kawai na sake jin kin bud'e wa mutane wannan banzar bakin naki da duk doyi yake sai na cire miki haƙora na sake jin kin yi magana"
hannuwanta duka tasa ta rufe bakinta da shi tana kuka,shi kuwa jin kukanta yake har cikin ransa ana cikin haka sai ga rayhan .
"haba haba ma'aruf wai me yarinyar nàn ta tsare maka a gidan nan ne kake matsa mata irin haka?
Murmushi gefen baki ma'aruf ya yi sannan yace "eh an matsa mata ko zaka dau matakine ?
"zan kuwa d'auka yanxu tunda ba Imani gare ka ba Kuma ba tsoronka ake ji ba
"Toh bismillah Ina jiranka idan ka Isa ka nuna 'kwanjinka a kan na taɓa wannan wawiyar yarinyar mai shegen munin bala'i"
"ke umminah tashi Ki shiga cikin na gama da wannan banzan mara mutunci har ni zai ce zai fad'awa babu daɗi,matsa naji masa ciwo, zai san koni waye yau ya ware hannunsa yana k'ok'arin kai wa Ma'aruf naushin wasa aiko ma'aruf bai d'auki abin da wasa ba ya zuba masa naushin fuska kafin kace me tuni fad'an ya zama gaske .
"Kai Kai !! meye haka?
" me kuke k'ok'arin yi ?
"Ba dai fad'a za ku yi ba kamar wasu yara ƙanana ba, haba rayhan kai da Ɗan uwan naka za kayi fad'a?
" toh ma tukunna me ya had'aku?
"Hajiya samunsa nayi yana cin zalin Ummita, ni fa dama wasa nake masa kawai naga ya mai da abin faɗa "
"to to yanzu na gane dalilin fad'an dama a kan wannan Mara kunyar kuke fad'a,gaskiya duk kun zama manya kwabo, "Kai yanzu meye ruwanka da zancesa da Ummita Kamar baka san halin Wannan shegiyar yarinyar mai rashin kunyar tsiyar ba.
"Koma dai menene Ai karfinsu ba d'aya ba, Kuma ma Ummita har yanzu yarinya ce ta yaya zai dinga biye mata,a gidan nan bayan ke da ma'aruf babu mai complain din ummita kowa tana zaune da shi lafiya ni na lura ma shi ne ke shiga harkarta ki gaya masa ya daina bana so matuƙar zai dinga sakata kuka zan canza masa, tunda ya soma magana ma'aruf ke hararsa ba tare da yace masa komai ba, dan shi bai ga abinda zai ce masa ba ..
"Toh shikenan naji ku yi hakuri dukan ku, ke Kuma sai Ki wuce ki bawa mutane guri koh, ummita ta juya ranta a ɓace tayi bangarensu tana shiga taji ance" koma kiyi sallama ai ba d'akin kafirai ba ne da za ki shigowa mutane ba sallama, ta juya tsumu- tsumu tamkar kazar da Kwai ya fashewa a ciki ta koma ta tsaya a bakin kofa tana sake goge hawayenta sannan tayi sallama "Assalamu alaikum"
"wa alaikumussalam mama ta amsa mata ta shigo tana ɓacin rai "toh ko kefa, ke da wa kika shigo kina wa mutane 'bacin rai dasu goge hawaye?
Kamar jira take a tambayeta ai ko take ta ɓare baki ta soma kuka har da sheshsheka"
wallahi mama idan ma'aruf ya sake shiga sabgana sai na masa abinda ba a taɓa masa ba "
"Oho ki ce dama ke da ma'auf ne toh kun fi kusa babu ruwana, "Allah ya sauwaka min mama ina ruwana da shi qazami ma irinsa Wallahi idan ina kaunar mutuwata to ina kaunarsa, ni dai mama kiyi masa magana ya fita rayuwata ..
"Allah ya shirye ki Ummi, ta wucewarta kitchen, Tana cewa "ban san yaushe zaku daina wannan halin naku ba Kullum Kamar wasu karnuka saboda fad'a gwamma ku gyara halin ku musamma ma ke da kike mace, gidan wani Zaki,"haba mama ko yaushe bayansa kike bi, ba Kya son laifinsa ai daman ni nasan ba zaki goyi bayana ba "
"Kiy iwa mutane shiru Ba ga irin rashin kunyar nan ba Ina magana kina bani amsa Allah dai ya shiye ki"
Ɓangaren ma'aruf kuwa tsaki yaja ya nad'e hannayen rigarsa ya nufi d'akinsa kai tsaye toilet din dake cikin d'akinsu ya shiga , tap ya kunna ya tari ruwa a cikin madai-daicin bucket ya soma wanka yana tunanin iskanci da ummi ke masa,Sam ya rasa dalilin da yasa ta raina shi, abinda yayi d'azu yayi ne dan ya tsorata Kuma ta dinga jin tsoronsa ashe a banza, ba canzawa zata yi ba,amman ya san maganin abun, ya ci alwashin gyara mata zama Koda kuwa hakan zai yi sanadiyar rugujewar zumuncin da ke tsakaninsu Yana wanka Yana tuna irin abinda zai wa Ummita dan su fita rayuwar juna , yana fitowa daga wanka ya shirya, ya fito yayi hanyar ɓangaren mahaifiyarsa yana shiga ya samu kannensa jidda da meenal suna cin abinci,suna ganinsa suka had'a baki gurin masa sannu da zuwa Amma bai amsa ba ya nufi uwar dakan inda yafi tunanin ummansa take suka kama kallon kallo , Jidda tayi ƙasa da muryarta dan kar ya jiyoyata tace" yanzu haka shi da Ummita ne "
Meenal tace
"su suka sani da matsalar su ni na rasa wannan bala'i sam basa shan inuwar juna ,"ai Kuma duk Yaya ne ya soma nuna mata tsana, ko nice fa ?
"banyi maka laifin komai ba kace zaka tsane ni ai sai inda ƙarfina ya tsaya,ni fa bana ganin laifin ummita dan ko nice zan yi fiye da abinda take yi masa, kullun a gurinsa ita ce mummuna, ita ce wawiya,ita ce fat lion jidda na kawo wa nan suka kwashe da dariya".
kai yaya bai yi ba kinji wani Suna Wai fat lion, ni na taɓa ganin a ce ana son uwa ba a son 'ya ?
"Ai kuwa gashi kin gani a gurin yaya ma'aruf Kullum Yana manne da uwarta amman baya kaunar ya bud'e Idanunshi ya ga diyarta, suna cikin hirar ummansu ta fito daga d'aki Kuma duk ta saurare abinda Suke tautaunawa tace "toh ya isa magulmata sai ku yi abinda ke gabanku idan Kuma Kuka bari ya jiyo ku wannan matsalar ku ce babu ruwana dan ko hakuri bazan bayar ba ..
*Two friend's ( b s b s*)
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~TRUE LIFE STORY~
FREE NOVEL NOT FOR SELL
AL'QALUMAN
*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*
~DEDICATED TO~
MARYAM ALHASAN D'AN IYA
(MARYAM OBAM)
YOU ARE BEST FRIEND FOREVER AND EVER, AKWAI AMANA 'KAWARMU ALLAH YA BARMU TAREN TARE SON SO FI SABILILLAH 🥰🥰
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
PAGE 2
.....Suna cikin haka sai gashi ya fito daga d'akin mahaifiyarsa fuskarshi a d'aure tamkar hadari, suna ganin shi kowacce ta shiga hankalinta tare da shan jinin jikinta ,hatta murmushin dake kwance akan fuskarsu sai data d'auke saboda irin kallon daya dinga aiko musu dashi ..
Tsaki yaja saboda duk yaji abinda suka faɗa , Ahankali ya d'auke kyawawan idanunshi akansu Yana mai zabga masu harara, sannan ya nufi hanyar fita daga d'akin "tafiya zaka yi tun baka ci abinci ba? umma tayi masa tambayar tana dubansa .
ya ɗan tsaya tare da juyowa ya sake tsayawa yana fuskantarta kamar yace mata baya ci ,zai ci a d'akin mama ,amman yasan halinta yana faɗar haka zata ji babu dadi, dan haka yace "ki bawa meenal ta kawo min part din mama, idan na fito daga part din Abba zanci acan ya k'arasa maganar Yana juyawa ya fice daga parlour'n.
Ko bayan daya fita ma babu wacce tayi ƙoƙarin sake yin magana daga menna har jiddah, illa ƙoƙarin tattara parlour'n da meena take k'ok'arin yi ta shige kitchen, ita Kuma jidda ta nufi d'akinsu tana zancen zuci ..
Da sallama ɗauke a bakinsa ya shiga part din Abba ,Abba dake zaune sanye da shadda blue ,yayinda babbar rigarsa ke ajiye a gefe Yana duba wasu mahimman bayanai, ya
dakata da abinda yake , ya amsa sallamar ma'aruf tare da d'ago fuskarsa Yana murmushi "A'a maaruf ne ?
"Har ka shigo kenan ?
"D'azu nake tambayarka gurin mamanka akace baka shigo ba tukuna "
A ladabace ma'aruf ya fara ƙoƙarin rusunawa kanin mahaifinsa har kasa yana gaishe dashi "Abba barka da dare ?
"Barka ma'aruf ya ƙoƙarin ?
"Alhamdullahi Abba ya fama da jama'a ?
Abba ya fad'ad'a fuskarsa da murmushi "jama'a kam gasu muna fama dasu ,sai dai muce alhamdullahi " shiru ne ya ratsa d'akin yayinda Abba ya cigaba da abinda yake shi kuwa ma'aruf bai sake cewa komai ba ,sannan baka jin motsin komai sai na iskar fankar d'akin da saukar numfashin ma'aruf dake zaune har lokacin ƙwaƙwalwarsa bata daina tunanin rashin kunyar da Ummita tayi masa d'azu ba ,abubuwanta na damunsa sannan tana bashi mamaki , abu mafi muni agaresa wai akanta yau suka kusan yin dambe da rayhan ?
Rayhan fa shine mafi kusanci a garesa bayan yan'uwansa ,tun tasowarsu babu wanda ya ta'ba jin kansu , komai tare suke ,duk hargitsi da bala'in da akayi a tun lokacin ganiyar kuruciya shi da rayhan lafiya lau babu abinda ya shiga tsakaninsu ,sai akan Ummita, yarinyar da ya fi tsana arayuwarsa ....
Wannan yasa gaba-daya yaji ya sake tsanarta kuma yana jin har ya koma ga mahalincinsa ba zai taɓa kaunarta ba ..
a qalla ya kusan minti talatin zaune agurin batare da yace komai ba, har sanda Abba ya sake d'agowa yana dubansa "lafiya ma'aruf na ganka haka ko akwai abinda ke damunka ne?
Alhankali ya d'ago har lokacin fuskarsa babu Annur ,da kyar ya iya buɗe bakinsa "babu komai Abba "kai dai ka sanar min idan akwai damuwar ne ?
murmushin karfin hali ya qaqaro "babu komai Abba ya fadi haka saboda yasan abba baya son ganinsa cikin damuwa akoda yaushe yafi bukatar ganinsa cikin farin ciki, kular abincin da aka kawo masa ya turo gabansa "ga abinci nan kaci daga ni baka ci komai ba" ban ci ba amman nasa akai min bangaren mama acan zanci "to shikenan idan ka shiga kace wa mamar taka tazo ""
Har ma'aruf ya mike Abba yace "ammmmm gobe akwai takardun da zaka saka hannu kai da Rayhan ƙarshen watan nan idan Allah ya kai mu nake son ku fara fita office "
"Okay Abba mun gode Allah ya ƙara girma da nisan kwana "ameen, ma'aruf ya karasa mikewa cike da kwarin gwiwa ya nufi bangaren mama ..
Zaune ya iske mama hannunta a daidai gefen kugun Ummita tana shafa mata man zafi, yayinda ummita ta runtse ido tana kuka tana ganinsa tayi saurin tamke fuska tana sauke hijabinta hawaye na gangaro mata sallamarsa tasa mama ta fahimci abinda yasa Ummita sakin hijab dinta da sauri , mama ta amsa masa tana maida idanunta ga Ummita "wai ma garin yaya kika ji ciwo irin haka da alamun kamar kashin gurin ya goce?
Kuka ta sake sanyawa mama shi kuma ma'aruf ya k'arasa shigowa ya zauna yana ware kafafunsa ,suka gaisa da mama batare da wata damuwa ba ya janyo tiren dake ɗauke da kular abincinsa ya buɗe ya soma ci ...
Da kyar mama ta ciwo kan ummita ta gaya mata yadda akayi ta ji ciwon ,lokacin da take bayani mama ta zuba mata ido sannan tace "nasan ai haka nan ma'aruf ba zai taɓa lafiyar jikinki batare da kinyi masa wani abu ba , nasan ƙarshenta rashin gurin kunya kika ji ciwon , "ke dai ba aikin ki rashin kunya ba ai kaɗan kika gani .
Muryarta cike da shagwa'ba tace "to mama ai shine yake shiga lamarina , amman kullun sai kiyi ta ganin laifina ta k'arasa maganar wasu sabbin hawaye na gangaro mata, haka nan yau ma'aruf ya tsinci kansa da jin kunyar mama akan abinda yayi gaba-daya ya kasa ci-gaba da cin abincin da yake , yayi shiru kawai yana sauraron kukanta ,har cikin zuciyarsa yake jin babu dadi ,mama ta wuce komai agurinsa, matsayin mahaifiya ce gareta ,bata haɗa shi da komai ba ,tunda suke rigimarsu da Ummita bai taba jin kunyarta irin ta yau ba ,da zai iya ,daya kaunaci Ummita koda cikon cokali ne ko dan darajar mahaifiyarta da mahaifinta da suka ɗauki soyayyar duniya suka daura masa amman bazai iya ba ...
Bazai iya mu'amala daita ba sam baya jin zai iya aikata hakan gara dai kowa yayi lamarinsa .....
"shikenan kukan ya isa haka ,idan kuma baza kiyi shiru ba sai ki cigaba ,dan mugun halinki ne ya jawo miki ,kai kuma ma'aruf ban ce ka raga Mata ba, Sau dubu tayi maka rashin kunya ,kayi mata dukan Kawo wuka tunda ita takamarta taurin kai da rashin kunya "
mama ta fada tana ƙoƙarin mikewa zuwa uwar d'aka "na gode mama Allah ya bar min ke ,domin ke din ta dabance ,ba Kya goyon bayan karya ,mama takarasa d'akin ta d'auko hijab dinta ta fito ta bar musu d'akin ta nufi bangaren Abba ..
Ta kasan idanunshi yake Kallonta tana goge hawaye batare da yace mata komai ba ,yayinda ita kuma ta cigaba da kukanta ,suna cikin haka yaya rayhan ya shigo d'akin da sauri ya karaso gareta tare da riko tafukan hannunta duka cikin nashi " wayyo my ummita me ya sameki ? Waye ya 'bata miki rai ?
"Waye yayi silar zubar hawayenki ?
Yayi mata tambayar ajere.
"Ki fada min bana son ganin digar hawayenki, ina jin zafi acikin araina a duk sanda naga kina kuka , ki taimkeni ki faɗa min nayi miki alqawarin zan rama miki kinji yar kanwata ya k'arasa maganar yana matse hannayenta cikin nashi haɗe da kai su daidai saitin bakinsa ya dumbata .
ganin yadda ya rud'e ya gigice yasa ta kirkiro dariya dole "babu komai fa yaya "ke dai faɗa min gsky ko ma'aruf ne yanzu na zubar masa da hakoran gaban bakinsa ? ya fadi maganar yana jan kumatunta ...
Kallon inda ma'aruf yake zaune tayi, taga ko kallon inda suke bai yi ba bare yasan da zamansu agurin , asalima kwanciya yayi rigingine akan kujera idanunsa na kan tv..
"shi ne ko inji cewar yaya rayhan ?
Muryarta Ahankali tace "kuguna ke min ciwo inda ya tureni ,shine yanzu mama ta shafa min man zafi ,wai dan na faɗa mats dalilin ciwon shine ta daura min laifi ,yaya ban san me yasa mama take yin haka ba ,kwatanta kwata bata sona, ta karasa maganar idanunta na ciccikowa da ruwan hawaye "no ki daina cewa haka mama na sonki fiyye da komai dake cikin duniyar nan ,kece fa duniyarta bata da wacce ta fiki , duk wanda zata so karere ne kece gold agurinta ,karki sake 'bata ranki kinji baby nah...
Ahankali ya dinga rarrashinta yana kwantar mata da hankali, yana goge mata hawaye yana janta da hira ,ita kuma sai murna take tana farin ciki ,dariyar ta yaya rayhan yake tayi acikin zuciyarsa batare da tasani ba ,Ahankali hirar tasu ta canza salo zuwa bangaren soyayyar su kuma har lokacin ma'aruf na zaune yana kallon first match din da'ake bugawa tsakanin bacerlona da arsenal sosai yayi zurfi a kallonsa , rayhan ya ɗan kai hankalinsa garesa ya lura gaba-daya hankalinsa baya gare su dan haka yayi kasa da Muryarsa sosai yana fuskantar Ummita sosai "my baby har yanzu fa ban ji gamsashiyar amsa daga gareki ba ?
Cikin karyar da murya Ummita tace "gamsashiyar amsar me ?
"Ni fa yaya rayhan banason abinda kake min da kuka ta qarasa maganar "subuhanallahi !"meye kuma abun kuka ana daga tamabayar amsar soyayya?
"kuka Ummita take sosai ganin haka hankalinsa yayi matukar tashi "shikenan kukan ya isa haka, yana taɓa min zuciya hanky d'insa ya ciro ya mika mata "oya goge hawayenki bana son ganinsu suna bugar min da zuciya ..
Kin amsa tayi tana sake matso ruwa daga idanunta ,ganin bata da niyyar amsa ,ya soma goge mata "ki daina min asarar hawayenki Please , a daidai wannan lokacin ma'aruf ya mike idanunsa na kallon kofar fita "idan ka gama wannan banzar shirmen naka kaje Abba na neman ka ,yana gama faɗar haka ya sa kai yana ƙoƙarin fita, fuskar rayhan a daure yace "naji amman ka sani idan wannan abun da nake yi ne shirmen ashe bani kaɗai nake yi ba ,wasu suma suna yi ya fad'i hk yana ɗauke kanshi zuwa ga ummita yayinda tuni shi ma'aruf ya fice daga d'akin.
"ke kuma ba zaki bar kukan nan ba gashi kinsa ana mana wani kallo ko?
Cikin sheshekar kuka tace "ka manta da wannan banza ,amman yaya rayhan bana so abin.....",tam naji nima na bari shikenan ?
Murmushi ta sakar masa yayinda shi kuma yake cigaba da share mata hawaye "kullun na ganki qara kyau kike min "kai ma haka yaya rayhan "a haka Ummita ina wani kyau anan ",Yes of course ai duk kafi mazan family's d'in nan kyau da natsuwa da haiba, yaya rayhan kasan me ?
Idanunshi kawai ya zuba mata yana kallon yadda take motsa labbanta da yadda take wasa da yatsun hannunta "sai kin faɗa my quenn tayi shiru tare da tsura masa idanunta ,jin tayi shiru yace "ina sauraron ki beauty ,kasa cewa komai tayi tana cigaba da wasa da yatsun hannunta saboda idanunshi "ki fada min abinda kike son fad'a zuciyata ta soma rawa ?"just tell me beauty ina sauraronki "ganin yadda ya rud'e yaji damuwarta kuma ita gskya take son ta fada masa, ya daina damun kansa akanta ,dan ita babu soyayya acikin tsarinta ,tsarinta ta samu wadataccen ilimi tayi zurfi a karatu har sai taga karshen biro amman ayanzu da yake zaune yayi bake bake agabanta tamkar zai maida ita jikinsa, kunyarsa ce ta kamata har taji bazata iya kallon idanunshi ta faɗa masa haka ba "dan haka tace masa "yaya rayhan ka kwantar da hankalinka babu komai fa "karki min haka mana Ummita idan kika boye min abinda zuciyar ki take son Fadi kinsa kin cutar da zuciyar yaya rayhan ɗinkin ?
"Subai'a tun randa aka haifo ki duniya na daura idanuna akanki Allah ya jarabeni da matsanancin soyayayarki ta d'ago cikin sauri ta tsura masa ido " haka ne subai'a kinsa wannan ba tun yanzu ba, tun daga wannan lokacin tunanina da hankalinka da komai nawa ya tattara akanki da lamarinki ,ina qaunarki zan so ki kaunace ni ,zan so na zama zabin zuciyarki ,zan so ki soni fiyye da kowa da komai dake cikin duniyarki,ki kaunace dan Allah ki sakani aranki kada ki sakani a zuciyarki ...
Narkar da fuskarta tayi "kai yaya rayhan duk ni kaɗai ai soyayyar tayi min yawa "no no batayi ba abinda ke cikin zuciyata kenan, zan so da zarar iyayenmu sun tambaye ki zabinki na zamo nine sawun farko "kai yaya rayhan tayi maganar tana murmushi sun dade a parlour'n suna hira yana lalla'bata har sai daya ga alamun tasoma gyangyadi sannan ya barta ya wuce ...
Washegari
bayan ma'aruf ya dawo daga gurin suhaima yarinyar da yake jin duk duniya babu wanda ya isa ya shiga tsakaninsu sai Allah daya haliccesa , a kofar gida suka haɗu da Abba, daya fito daga cikin gida jikinsa sanye da shadda fari da babbar riga , fuskarsa kwance da ruwa alwala da alamar masallaci zashi ma'aruf cikin hanzarin ya ƙara so garesa, Abba ya zuba masa ido yana murmushi lokacin da yake ƙoƙarin karasowa garesa , rage tsawonsa yayi gurin gaisheshi Abba ya amsa tare da cewa " shiga kayi alwala kazo mu wuce masallaci tare " da hanzarin ya shiga a harabar gidan ya tsaya daga can bangaren dama ya isa ya kunna fonfo yayi alwala ya fito suka wuce masallaci tare .
Bayan sun idar da Sallah tare suka jero suna hira Ahankali Ahankali tamkar wasu aminai har suka karaso gida,kai tsaye suka wuce zuwa bangaren Abba in da ma'aruf ya samu guri ya zauna akan kujerar mutun ɗaya ,Abba na matsanancin son ma'aruf a duk cikin ya'yan yan'uwansa babu wanda yake so kamar sa , tun da aka haifeshi ya dasawa zuciyarsa kaunarsa har ila yau , bai taɓa haɗa shi da komai ba, ko ƴaƴan cikinsa baya jinsu kamar yadda yake jin ma'aruf a cikin zuciyarsa , shima haka ne a ɓangaren ma'aruf din baya wasa da al'amarin mama da Abba yana son su fiyye da komai na rayuwarsa baya wasa da al'amarin su, document Abba ya mika masa "gashi ka sanya hannun, ka cike duk inda Yakamata, idan kaga rayhan ka min shi yazo ya cike nasa " ma'aruf ya amsa da "tam Abba, Ahankali ya fara ƙoƙarin cike komai da'ake bukata ya ajiye a saman madaidaicin center table din dake parlour'n , "har ka gama Abba ya amsa yana dubawa tare da tsurawa rubutunsa ido "eh ya bashi amsa yana shafa sumar kansa ,sosai Abba yake kallon rubutun nasa sam bakace hannu ne ya rabauta shi ba saboda daidaituwar rubutun, bayan ya gama kallon rubutun yace "kana iya tafiya "Ma'aruf ya yuya a natse yana yiwa Abba sallama ya fita daga part din zuwa bangaresa .
*******
Yau ta kama lahadi ma'aruf ne ya fito cikin kananan kaya wandon jeans baki da riga fly amirates baki da ratsin yellow ajiki, kansa sanye da facing cap kafafunsa wasu haddadun takalmin canvers ne mai ɗauke tambarin Gucci ,Yayinda kunnensa ke manne da eipice hannunsa rike da wayarsa iphone x sai kamshin turaren viso dake tashi ajikinsa yayi kyau sosai tamkar ka suresa ka gudu, Ahankali yake taku kamar wani mace ,a daidai harabar gidan suka haɗu da himaya kawar Ummita kallo daya yayi mata ya ɗauke idanunsa akanta ya cigaba da tafiya,
Da wani irin mayataccen kallo tabi shi kafin daga baya bakinta na rawa tace "yaya ma'aruf ina yini ?banza yayi mata a daidai lokacin daya k'arasa jikin motarsa ya buɗe shige ya bar gidan ..
jijinta a matukar sanyaya ta nufi bangaren su ummita tana mita aranta ,Ummita na ganinta ta saki fuska tana murnar ganinta ta taso ta runguneta "kai himaya kamar kinsa ina son ganin ki wallahi dazu na gama cewa zanje gidanku .
"ayya ai shikenan na hutar dake tunda gashi nazo ,ke wai meke damun yayanki
Yanzu muka haɗu dashi ?
" wanne kenan a cikinsu "wannan mai mugun girman kai da d'acin rai har yaushe zai daina wannan d'acin ran nasa?
" na gaida shi ko amsa min bai yi ba bare ya kalli inda nake sai ma fizgar motarsa da yayi ya fice" shiru Ummita ta ɗan yi tana yatsina fuska sannan tace "wannan ai kullum haka yake bashi da wani aiki sai fushi da girman tsiya idan Kinga hakoransa waje to Yana tare da wancan tsohuwar kilakin budurwar tasa ne "ke ma meye abun damuwa dan bai amsa ki ba ,nan gaba ko kingansa karki sake kallonsa bare ki gaisheshi, idan kuma kinsa zaki dinga gaida shi ne idan kinzo karki sake zuwa gurina ta karasa faɗar hk tana hararar himaya ,dariya himaya ta saki da karfi "ikon Allah ke kuwa me yayi zafi shi ba wuta ba naga yayanki ne?
"a'a ni yayyena guda biyar ne kacal ,yaya Usman ,yaya rayhan ,yaya sadam ,yaya Abdurrahaman sai yaya Malik Amman Banda wannan ɗan girman tsiya ,dan haka daga yau idan dole ne gaisuwar taki waɗan nan dana lissafa miki su zaki gaisar ,idan ba haka ba mu raba hanya tuni wuri, dan bana son shishigi da neman suna ta juya tana ƙoƙarin zama akan kujerar mutun daya.
himaya ta biyo bayanta tana mamakin mulkin da mallaka irina Ummita, ita lallai sai abinda take so za'a ,yayinda ita mutun bai isa ya sata yin abu dole ba, guri ta samu kusa da kujerar da take zaune ta zauna "shikenan Ummita bazan sake gaishe shi dashi ba daman saboda ke nake gaisheshi amman tunda baki so shikenan , anyi na farko anyi na karshe ,"better Ummi ta fad'a tana tamke fuska .
"amman ke ummita mai yasa kike nuna masa kiyaye irin haka alhalin dan'uwa ki ne na jini "babu ruwanki da wannan tsakaninmu kuma ba dole sai kin sani ba ,ke dai kawai kiyi abinda nace "
"Anki Allah sai kin gaya min ,nice fa "ko kece fa sai akayi yaya ?
ta karasa mgnr daga fuskarta sama....
Murmushi himaya tayi "ki fada min tunda nice ta hannun damanki Ahankali ta kamo hannunta cikinta "Ummita zanyi wata magana amman karki ji haushi na Please "uhnmmm ina jinki tayi saurin katseta still fuskarta a haɗe "sai naga kamar kina son ma'a....."dakata dan Malama karki kawo min wannan banzar maganar nan ,wallahi idan aka jera min dubun su yaya ma'aruf babu abinda zanyi dasu .
"duk kyawun nan nashi Ummita ?
"Kwarai kuwa babu abinda zanyi dashi saboda ba kyau akewa ba hali a akewa ,wallahi idan nace miki ma'aruf yayi min karya ne" ke bancin gidan nan gidan mahaifina ne wallahi da zan iya barin gidan nan naje gaba nayi rayuwata saboda bana qaunarsa ,ke nifa sam bana jinsa tamkar dan'uwa ....
"Bani ba ko wata yace yana so wallahi matukar ina da yadda zanyi to zan faɗa mata gaskiya "haka suka ci gaba da hirarsu wanda duk sama sama ummita take amsa mata har daf magariba suna tare sannan himaya ta wuce ....
Two friend's bsbs
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~TRUE LIFE STORY~
FREE NOVEL NOT FOR SELL
AL'QALUMAN
*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*
~DEDICATED TO~
MARYAM ALHASAN D'AN IYA
(MARYAM OBAM)
BEST FRIEND FOREVER AND EVER, AKWAI AMANA 'KAWARMU ALLAH YA BARMU TAREN TARE SON SO FI SABILILLAH 🥰🥰
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
PAGE 3
.....barin ma'aruf gida ,bai zarce ko'ina ba sai unguwarsu suhaima sakamakon kiran da tayi masa akan mahaifinta na son ganinsa .
tun kafin ya qarasa, ya ciro phone d'insa ya fara dialing din number suhaima domin sanar daita zuwansa , ba'a ɗauki wani lokaci ba, ta ɗauka cike da shagwa'ba da kashe murya "hello my habibi ,my baby ,my love, my everything .
Ma'aruf yayi tsadadden murmushinsa wanda ke sake bayyana kyawunsa yana saka phone din a speaker sannan ya cigaba da driving "Allah ya qarawa gimbiyata lafiya duk ni kaɗai godiya nake , murmushi tayi tamkar tana gabanshi wanda har sautin muryarta ya bayyana "matsayinka ya zarta haka a gurina "zaka zo ɗin ne ko ka fasa zuwa? tayi maganar muryarta can kasa tamkar wacce ke koyan magana dan bata san abinda zai ce mata ba , dan tasan halinsa baqaramin aikinsa bane yace mata ba zai zo ba ....
"Ran gimbiya suhaima ya dade gani nan hanyar qarasowa ,me kika tanadar min ?maganarsa ta kashe mata sansar jiki har tsigar jikinta suka mike ta lumshe idanunta , sake fad'ad'a fuskarta tayi da fara'a tace "mai habibi nah yake bukata daga gareni ?
"Kar ya damu ya fad'i duk abinda yake so ,a shirye suhaima take data mallaka masa ...
Kad'a kai yayi yana murmushin jin dadi haɗe da shafa sitiyarin motar sannan yace "Karki damu ba na bukata komai sama da ganin kyawawar fuskarki.....
koda yake yau zuwan ba naki bane na dady ne fatan zan same shi ?
murmushin farinciki ta saki tana kamkame wayar a kunnenta " yana nan yana zaman jiranka babu in da yaje ,yace yau sai yayi 4 eye's da wanda yayi nasarar sace rayuwar suhaimar sa .
Murmushin gefen baki yayi sannan yace "Okay ai ta kwana gidan sauki yau zai ganni , ba ganinna ba har kunne da kunne zamu yi dashi ,
sai na qaraso ya fad'i hk yana katse Kiran tare da shafa sajensa,wani irin juyin farinciki suhaima tayi har da tsalle , take ta shiga rawar jikin tarban masoyinta ..
Lokacin ɗaya isa suhaima ta gama shirya masa komai na tarbanshi cikin girmama wani irin mayataccen kallo ma'aruf ke binta da shi saboda kyawun da tayi masa , ya taso daga inda yake zaune ya zauna kusa daita har cibiyoyin su na zozan juna take suka ji wani irin zirrrrrrrr a gaba-daya ilahirin jikinsu ,hannunta daya ya kamo cikin nashi yana murza Ahankali tare da sanya kwayar idanunshi cikin nata "kinyi kyau sosai my suhaima kamar na cinyeki ,kullun na kalleki qara kyau kike min meye sirrin ne ?
"Kai habibi ai duk kyawuna ban kai ka ba ..
"Shiiiiiiiiiii ya d'aura hannunsa kan lip's dinta "Karki fadi son ranki Mana ,nifa tsintar dame nayi ,bancin soyayya babu ta yadda za'a yi na ....
"Zaka fara kou ?
"Ai gaskiya ne ....
Matso da fuskarta tayi daf da nashi suna shaƙar numfashin juna kusan minti goma ma'aruf bai ɗauke kwayar idanunsa cikin nata ba har sanda ta lumshe idanunta
,murmushi yayi yana cizan lip's dinta na kasa ,ya san yadda soyayyarsa tayi tasiri a zuciyarta, ba zata iya jurar kallon kwayar idanunsa na tsawon lokaci ba muryarta a matukar sanyaye "am missing you habibi do you also miss me ? Tayi maganar muryarta a raunane tamkar zata shige jikinsa ,tuni jikin ma'aruf yayi mutu yanayinsa ya soma canzawa
Yayi baya ya jingina jikinsa da kujerar da yake zaune yana sakin numfashi "abinda kika rigada kika sani ne suhaima kullun cikin missing ɗinkin nake "ta kwanto ta shige jikinsa ta rungume shi tsam ajikinta tana fidda numfashi "nasani habibi ,nasan kana sona sosai ,sai dai nawa yafi naka tayi maganar tana sake shige masa tamkar wanda za'a kwacewa ,jin tudun dukiyar fulaninta yasa komai ya soma kwace masa numfashi ma da kyar yake fitarwa , Ahankali ya sanyawa jikinsa dakiya ,dan baya so ya dara daga rike tsintsiyar hannunta, saboda ita din matar da yake buƙatar killace wa ce a gidansa ba wai shashanci ba ,ya kuma san halin rigimarta bata iya jurewa kusancinsu , sau tari shine ke control if not da tunin an wuce gurin , mikewa yayi tare daita ya tsaida ita bisa kafafunta "ya kamata kiyi min iso gurin dady kou?
Hannunsa ta riko cikin nata tana murzawa "kaci wani abu mana kafin nan tayi Maganar tana sake shigewa jikinsa " bana buƙatar cin komai suhaima asalima bana tare da kishi ko yunwa ,"na sani ai kullun haka ne , bansa lokacin da zaka fara cin abun hanuna ba "share wannan maganar muyi abinda ya kawo ni kema kin san ba wani cin komai zanyi ba .
"muje ta faɗa cikin killer voice dinta ..
Tafiya ɗaya biyu ya zare hannunsa dake cikin nata batare daya ce mata komai ba hakan nan yake jin tsoronta yau .
Kai tsaye parlour'n mahaifinta Alhaji Muhammadu canji ta nufa dashi ,tare suka jero tana karairaya tamkar zata balle ,a adaidai bakin kofar parlour'n ya ja ya tsaya al'amun tayi masa iso, ta shiga ko cikakken minti goma bata yi ba ta fito "bismillah habibi ta faɗa ahankali cike da sanyi jiki saboda ganin irin kallon da yake mata ,
Ahankali ya sanya kanshi cikin had'ad'd'en parlour'n da ya qawatu da kayan more rayuwar duniya , babu abinda babu acikinsa,sannan babu parlour'n yake sai kamshin turaren dana room freshener dake gauraye da sanyi ac ,ya qarasa har gaban mahaifinta tare da rusunawa kansa a ɗan sunkuye a kasa "Abba Barka da warhaka ?
Tsura masa ido mahaifin suhaima yayi na wani lokaci yana kallonsa , sannan ya amsa yana mika masa hannu, amman ma'aruf yaki mika masa hannu illa cigaba da rusunawa da yayi , abinda ya ƙara burge mahaifin suhaima kenan ,wannan shine karo na farko daya sanya yaron a idanunshi, amman lokaci ɗaya yaji ya tafi da hankalinsa, akwai natsuwa da hankali a tattare da yaron, uwa uba tarbiyya, duk inda ya fito ya samu wadatacciyar tarbiya ,irin wanda yake buƙatar a tattare da ya'yansa , gaba-daya sai bai ga aibun da mutane suke kawo masa akan yaron ba ko da yake ai ba'a sanin halin mutun a fuskarsa ..
Bayan sun gaisa , mahaifin suhaima yayi wa ma'aruf umarnin da ya tashi ya koma kan kujera ,yana ƙoƙarin mikewa suhaima ta qaraso cike da shagwa'ba ta riko hannunsa zuwa kan kujera dake fuskantar mahaifinta , jimmmm kaɗan mahaifinta ya kalleshi "daman ni nace suhaima ta turo min kai saboda tun fara zuwanka gurinta na kasa sukuni da samun natsuwa ,inata zullumi da fargaba akan batunka da ita, sakamakon zantuttukan mutane daban daban da nake samu akanka waɗan da suke ganin kamar ba aurenta zaka yi ba ,yaudara ce kawai dan haka ina son sanin abinda ke kawoka gurin suhaima, neman auren suhaima ko akasin haka?
Ma'aruf ya ɗan yi murmushi "karka ji komai dady da gaske ina son suhaima Kuma so irin na aure , sannan bani da tunanin komai akanta sai alkhairi ,ina son suhaima Kuma ina son ta zamo uwar ya'yana , ni kaina ina son manya su shigo cikin maganar ,sai dai zuwa yanzu ina neman alfarma zuwa lokacin da zan soma aiki, inshallahu zan turo manyana.
Dady yayi shiru kafin daga baya yace "alhamdullahi naji dadi sosai da wannan albashir ,baka da matsala Allah ya nuna mana lokaci, sai abu na gaba waye mahaifinka ?"
Mahaifina Alhaji shu'abu ya rasu shekaru goma da suka wuce ina tare da kanin mahaifina ne Alhaji abdulhamid mai oil & gas , "Masha Allah ba dai hamid mai oil &gas ba?
" shine kanin mahaifina
Ma'aruf ya fad'i yana shafa sumar kansa ,mahaifin
suhaim ya jina kai" lallai da alamun suhaima zata fi sauran yan'uwanta mata samun ingantaccen gidan aure" a qalla sun kusan awa ɗaya suna tautaunawa kafin suyi sallama ya wuce ....
Tun daga wannan lokacin idan ma'aruf yazo gurin suhaima , kai tsaye ake barinsa shiga da motarsa cikin gidansu sabanin da dayake parking a waje ..
*****
Da misalin ƙarfe tara na dare ma'aruf ya sanyo hancin motarsa cikin unguwarsu bayan ya dawo daga yawonsa, a daidai kofar gidansu ya tsaya batare daya kashe motar ba, yayi hon
jikinsa tattare da gajiya.
Mai gadi ya k'arasa cikin sauri ya buɗe masa tafkeken get din gidan ya sanya hancin motarsa ya shigo harabar gidan yayi parking sannan ya shiga gida.
kai tsaye ɓangaren mama ya nufa ,ya isketa zaune a parlour hannunta rike da plet tana cin farfesun naman kai , suna zaune tare da ummita suna hira ya k'arasa shigowa tare da sallama .
mama ce kawai ta d'ago ta kalleshi haɗe da amsa masa sallamar da yayi, amman Ummi ko kallon inda yake batayi ba bare tasan da zaman mutun agurin sai ma maida hankalinta da tayi zuwa ga tv ..
Guri ya samu ya zauna yana kiran "washhhhh Allah na gaji mamana...... "
Mama tayi murmushi tana yi masa sannu "ga ruwa ka ɗan sha ta kai hannu ta dauko robar ruwan faro dake ajiye a gefenta ta mika masa ya amsa "yauwa Mamana kamar kinsa ina tattare da kishi "ai jiya ba yau ba ma'aruf kai ma kasan nasani ,ta k'arasa maganar tana sake fad'ad'a fuskarta ..
Kusan minti biyar ya ɗauka zaune yana Kallon mama sannan yace
"Mama .....
Ta waigo Ahankali ta zuba masa idanunta "ya'akayi ma'aruf ko kana son wani abu ne ?
" a zuba min abinci tun karin safe ban sake cin komai ba ......
shiru Ummita tayi batare da ta kalleshi ba ta soma wasa da yatsun hannunta ranta a matuƙar 'bace ganin yadda ya wani narke fuska , tsaki taja a kasan zuciyarta "aikin banza kawai mutun taje ga uwarsa masa mana yayi mata shagwa'ba tana cikin zance zuci taji sautin muryar mama
"ummita tashi ki zubawa yayanki abinci, sosai taji zuciyarta ta buga ,kamar ba zata tashi ba saboda sanin halinsa dan zai iya cewa baya ci tare da disgata ,ko bama haka ba ita kanta mama yanzu zata iya mata fada a gabanshi abinda tafi tsana kenan , duk da haka sai data dan jira kaɗan taji mai zai ce ko ita mama ,sannan ta tashi taje ta zubo masa tana yatsine yatsine fuskar shi kuwa ma'aruf ko kallon inda take bai yi ba , lokacin da take miko masa abincin ne mama tace "ina kaje ne yau, sakina tazo ne manka ?
Tsigil ummita ta ca'bi bakin mama
" wacce sakina ta gidan iyanmu ko ta nan ?
"ta gidan baba sarki sai da tayi tambayar sannan ta fahimci kuskuren da tayi ,five seconds ya d'auka zaune yana Kallonta da tsantsar mamaki a fuskarsa, tsareta yayi sosai da sexy eye's dinsa ya kasa kawar da idanunsa akanta , duk ƙoƙarin d'agowar daya ga tana yi izuwa kallon fuskarsa hakan bai sa ya dauke idanunshi akanta ba karaf idanunsu ya tsarke cikin juna ....
Wata uwar harara ya banka mata lokacin da ya ga tana ƙoƙarin sake yin magana "kika sake naji kin sake cewa wani abu anan sai Kinga abinda zan miki "to to ni ance maka maganarka zanyi ? Yana gama faɗar haka ya mike ya fice daga dakin zuwa nashi batare da yaci abinci ba.
"kin gani kou ,kinsa ransa ya ɓaci ke kinsa ba shan inuwa ɗaya dashi kike yi ba meye na saka bakinki cikin maganarsa ?
"To ai ni ganin nayi me zai yiwa aunty sakinar gidan sarki data zo nemansa , ni wallahi takaici yammata dake biyosa nake dan ni banga abun bi agurin yaya ma'aruf ba, Allah kuwa mama ke ma har da dariya kina wani nuna kinji dadi , wallahi faɗa ya kamata ki dinga wa masu biyosa wannan ba mutuncinsu bane .
" Karki ji yadda nake ji idan sun zo "kun ji min ikon Allah , Allah ya bawa d'ana farinjini kice na dinga kore masa yammata, a'a ba'a yi haka dani ba ,maza tashi ki bishi da abincinsa sauran kiyi nasa rashin kunya ..tana jin mama ta share dan bata jin zata sake shiga d'akinsa har ƙarshen rayuwarta ...
Shiru yayi a d'akinsa, shi kaɗai bayan ya tattara hankalinsa da tunaninsa guri daya kafin daga baya ya janyo wayarsa ya shiga duba sakonnin da aka a turo masa ta what's app da facebook Instagram wanda mafi yawon sakon yammata ne masu barar soyayyar sa ,Ahankali ya shiga karantawa daki daki, yana cikin karantawa ne rayhan ya shigo dakin yana dafa kafadarsa , d'ago kai ma'aruf yayi Ahankali yana dubansa tare da cire hannunsa ya ajiye wayar yana ƙoƙarin mikewa rayhan yayi saurin riko tafin hannunsa "haba ma'aruf kar dai fushi ka ɗauka dani nifa wallahi da wasa nake maka abinda ya faru ?
"To ni da gaske na dauka dan kuwa tuni na rufe babinka a rayuwata, tunda ka nuna kafi son fat lion akaina ....ya k'arasa fad'ar haka yana ƙoƙarin zare hannunsa cikin nasa ,"kowa ya tsaya matsayinsa bazan hanaka shigar mata fada ba Sannan bazan hanaka mu'amala da ita ba, halaka dai na yanke da kai har abada ..
"Karka ce haka ma'aruf , ko ba zaka duba halaka ta jini da yan'uwankata ba , ka duba darajar iyayen Ummita gareka ,ka duba matsayin da suka baka Arayuwarka akwai qauna mai girma atsakaninka dasu " And so ?
"Shi kad'ai ya isa ka daina zurfafa qiyayyarka ga tilon diyar da Allah ya mallaka musu ,sannan ita kanta ummita guda nawa take bare ka ..... "dakata rayhan me ma ya kawoka gareni "me ye damuwarka dani ?
"Ko kazo ne ka bata min rai da wannan surutun naka ?
"Babu komai kawai dai ina jin babu dadi araina ne akan lamarinka da ummita ,bana jin dadin abinda kake mata ummita yarinya ce har yanzu da kuruciya tattare daita "a'a ko haihuwarta ma ba'a yi ba tukuna ,ita baga ganin irin tsanar data min sai nawa kake gani har kake ganin laifina akanta saboda ni ba zuciya bace akirjina ....
Har rayhan ya buɗe baki da niyyar sake yin magana ma'aruf yace "bana son sake Jin komai daga gareka kaje kawai kayi rayuwarka ,nayi tawa ba dole sai kayi mu'amala da ni ba ,"bai kamata ka damu kanka akan dole sai na daina kinta ko akasin haka ba, tunda wannan ba wani sabon abu ne ka rigada ka saba ga...sai kuma yayi shiru yana jan tsaki..
Iskar bakinsa ya furzar ya dafe gaban goshinsa Ahankali ya soma jan kafafunsa ya k'arasa gurin kujerar mai zaman mutun daya dake ajiye a dakin ya daura kanshi ..
Matsowa kusa dashi rayhan yayi , "shikenan ma'aruf kayi hakuri bazan sake shiga maganar ku da ummita ba amman dan Allah ka daina mata dan "Please ya faɗatare da daga masa hannu al'amun ya kyaleshi ..
Barinsa rayhan yayi ba dan yaso ba sai dan sanin halinsa da yayi idan yace Yes ,Yes ne idan yace no,no ne,idan kuwa ya kafe akan abu to zai yi wuya a sashi dole ..
"Allah dai ya baka hakuri kuma ya huci zuciyarka ,yasa ka gane kuskure ne abinda kake yi ,bazan gushe ba gurin maka addu'a ,saboda bayan halaka ta jini akwai sirrin qauna atsakaninmu ,har kullun ina sonka ma'aruf "jeka kawai dan Allah, ka ma daina sona daga yau , dan ni tuni nayi deleting dinka arayuwata.
"sabod ina kula ummita kou ?
Wani duba ma'aruf yayi masa sannan ya ja dogon tsaki "I don't know what to say but I feel like that ya fad'a Yana runtse idanunshi .
"Haka ne ma ,ba wai kana jin kamar haka bane " dan darajar Allah rayhan karka sake min maganar fat lion anan ..
I don't like it dan a duniya idan akwai halittar dana tsana itace ,kai tun da aka haife yarinyar nan na daura idona akanta naji na tsaneta, kawai wani lokacin darajar mama ne ,kuma bana tunanin zan sota har karshen rayuwata .....
Dariya sosai rayhan yayi "oh ma'aruf sai dai abarka da halinka ,"tam naji abarni dashi ,dan Allah ka wuce karka samin ciwon kai "ko baka faɗa ba tafiya zanyi gurin my quen amnan ka d'aure dai ka sota koda cikin cokali ne... ya faɗa yana juyawa ya fice daga dakin yana murmushi tare da cewa "Allah ya ganar da kai illar abinda kake yi ...
ummita dake tsaye a parlourn ma'aruf hannunta rike da kular abincinsa tana sauraron abinda suke tautaunawa,jin motsin fitowar yaya rayhan daga dakin yasa ta koma da baya ta la'be abayan kofa tana jan tsaki " to dama wa yake kaunarka, koni har karshen rayuwata bazan taɓa sonka ba
Two friend's (bsbs)
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~TRUE LIFE STORY~
FREE NOVEL NOT FOR SELL
AL'QALUMAN
*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*
~DEDICATED TO~
MARYAM ALHASAN D'AN IYA
(MARYAM OBAM)
BEST FRIEND FOREVER AND EVER, AKWAI AMANA 'KAWARMU ALLAH YA BARMU TAREN TARE SON SO FI SABILILLAH 🥰🥰
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
PAGE 4
..... Ahankali hawaye ke zubowa daga idanunta a lokacin , ta ajiye kular dake rike a hannunta haɗe da durkushewa agurin tana son sanin abinda yasa yaya ma'aruf ke mata irin wannan qiyayyar .
"me yasa baya sonta ?
"Me yasa baya son kusancinta dashi ?
"Tun farko shine ya soma nuna zallar qiyayyarsa gareta , tun tana d'aukar hakan a matsayin rashin haɗuwar jini har ta girma ta fuskanci tsabar qiyayya ce kawai ke d'awainiyya dashi wanda ko a gaban mahaifiyarta baya iya 'boye haka .
Kuka take sosai tana girgiza kai, domin zuwa lokacin babu abinda ke d'awainiyya da zuciyarta kamar qiyayyarsa, baka jin motsin komai a parlour'n sai sautin kukanta ..
Wani irin yunkurawa ma'aruf yayi a matukar fusace ya soma ƙoƙarin fitowa daga bedroom d'insa sakamakon sautin gunjin kuka da yake ji ya shiga cikin kunnuwansa ..
Tana cikin tunani da sheshekar kuka taji alamun motsin fitowarsa daga bedroom d'insa , jikinta na rawa ta soma ƙoƙarin goge hawayen dake kwance akan kuncinta, bata gama gogewa ba , taji tsayuwarsa a gabanta yana mata wani irin kallo mai tattare da tsana da jajayen idanunsa da suka canza kala yana fidda wani irin numfashi tamkar zaki ..
a matukar firgice ta mike tsaye jikinta na wani irin rawa yayinda take qirjinta ya shiga dokawa da sauri tamkar zai fito ..
Ya tsura mata ido yana kallonta cike da zallar tsanarta , ta bala'in bashi haushi sakamakon tunanin da zuciyarsa ta yi akanta ,ya ƙara taku zuwa inda take tsaye tana kyarma ..
Da sauri ta qara yin baya yana biyota har sai data kurewa bango, taja ta makale gabanta na faduwar ,shima ya ja ya tsaya yana fuskantarta ,
tayi saurin yin kasa da fuskarta qirjinta na dokawa "wayyo Allah na shiga uku ,me yasa na tsaya har ya fito ya same ni ?
Cike da tsanarta ya sa hannunsa ɗaya ya dafa bango yayi mata katanga tare da sunkuyo da kanshi daidai fuskarta ,yayinda fuskarshi ke murtuk tamkar hadari Muryarsa a kausashe yace "ke uban me kike wa mutane anan ?
Ta bude baki zata yi magana ya katseta da sauri ta hanyar cewa
" Shiiiiiiiiiii yi min shiru yar iska manafukar Allah daman 'labe kike wa mutane kou... ?
Maganar sa ta doki qirjinta da kunuwanta alokaci ɗaya har yayi nasarar shiga zuciyarta ya samu kyawawan mazauni a tsokar dake makale da qirjinta ,take taji hankalinta yayi bala'in tashi ,gaba-daya ta rasa me ya kamata tayi , ta d'ago kanta ahankali ta mai da idanunta kan kular data shigo dashi ko zai fahimci abinda ya kawo ta d'akinsa domin ya cire zarginsa gareta ,a kallon da take wa kular abinci ne wasu sabbin
hawaye sharrrrrrrr ....
sharrrrrrrr .. suka sake gangaro mata .
ta kasa tsaida kukanta tana dubansa zuciyarta na sake tsanarsa "okay da alamu kinji duk abinda muka tautauna da rayhan kenan , shiyasa kike hasarar hawayenki ba ?
"ai ba karyar na faɗa masa ba ,abinda ke cikin zuciyata kenan , babu abinda ke cikin raina kamar zallar tsanarki, dashi na girma fat lion banga Kuma mahalukin da ya isa ya kankare wannan tsanar ba , bana sonki !bana sonki !! Ke mai sonki ma bana qaunarsa kamar yadda kema nake hango tawa tsanar acikin kwayar idanunki.
"Tayi saurin runtse kyawawan idanunta saboda d'acin kalmar gareta .....
"Okay kina kuka ne saboda bana sonki ko me ? Yayi mata tambayar yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa ..
Tsareshi tayi da idanuwanta masu matukar kyau da haske , batare da tace masa qala ba, shima tsareta yayi da idanunshi yana mata kallon kaskanci da wulakanci ,a qalla sun ɗauki tsawon minti biyar suna kallon cikin kwayar idanun juna batare da kowannensu yayi d'an'uwansa magana ba ..
" Da ido yayi mata alamar ta fita a d'akin ,
" ba mutsu ta raba ta gefensa zata wuce sai dai muryarta a raunane tace "zan wuce ..
"ki wuce mana na rike ki ne da zaki wani tsare mutane da wannan banzar idanunki naki dake firgita mutane ?
"Gaba-daya ke abar tsoro ce ga al'umma ,kuma abar gudu kwata kwata baki ...
"Dan Allah malam enough ,"enough is enough yaya ....."ya isa ba dogon turanci na nema daga gare ka ba matsawa kawai zaka yi na wuce, dan bana son jikina da naka su haɗu, tayi maganar a dake , sai dai zuciyarta cike take fal da matsanancin tsoro da fargaban abinda zai mata .
"Ware idanuwanshi yayi sosai cike da mamakinta yayinda ya dinga jin wani sabon tsanarta na huda zuciyarsa tare da samun kyawawan mazauni daban a sansar jikinsa .... .
" Ta hura hancinta sanan ta sanya bayan hannunta ta goge fuskarta "ka daina mamaki abinda na faɗa ... dana bari shashin jikina ya haɗu da jikinka gara na haɗa jikina da bakin jaki......
"Abu na gaba da zan faɗa ka sani ba wai zuwan kaina nayi d'akinka ba aikoni mama tayi kuma ga sheida nan idanunka sun gane maka , ka daina tunanin ummita zata nemi kusanci da kai dan har abada ummita bazata yi zuwan kanta ba ,nasan zuwa yanzu kasan dalilin zuwana ,tun taso wata ni nan ban san me ake kira la'be ba ,sai dai naji labari abakin mutane bare na rasa wanda zan wa sai kai ,ni nan nafi karfin nayi maka la'be .....
"Yi min shiru stupid fat lion..... ni zaki haɗa da bakin jaki ?
"An haɗaka da bakin jaki me zaka yi ?"ai sanin haka ne kawai baka yi ba amman kafi kama dashi kamarku ɗaya tamkar an tsaga ƙara..
Shiru yayi kawai yana facing dinta yana kallon yadda take motsa bakinta cike da bakin ciki mara misaltuwa yayinda tsanarta ke sake qaruwa a cikin zuciyarsa tare da bin kowane part na jikinsa tsawon minti biyu yana kallonta ya rasa takamaimain abinda zai ce mata ....
Murmushin yake tayi wanda yafi kuka ciwo ," ashe dai babu dadi ?
"A she haɗa mutun da dabba babu dadi ,a she hakan na saka zuciya jin wani irin har ta nemi tarwatsewa ,amman kai kake takarkarewa ka dinga kiran mutane da fat lion ,tare da muna nan kalamai iri iri.........
"Kasani daga yau na kashe wannan sunan daga bakinka , karka qara kirana dashi idan kuma baka daina ba zan .......
Wata muguwar tsawa ya buga mata take tayi shiru da bakinta ta ƙasa qarasa maganarta zuciyarta na harbawa da sauri, cike da ɓacin rai yace "dan ubanki me zaki iya yi idan ban daina ba?
Ta zumburo masa baki tana tunanin abinda zata faɗa masa mai zafi ,da zai 'bata masa rai ,shi kuwa tsareta yayi da sexy eye's din shi kafin daga baya yace "ba zaki wuce bane ko kuwa sai naci ubanki a yanzu , idan kuma kika sake furta wata magana mara daɗi anan sai na miki azaba mai rad'ad'i ....
sai na miki jina jina wawiya kawai mai fuskar samudawa ...
Wani murmushin takaicin ta sake yi sannan tace "uhnmmm sannu mama da Abba ,kana bani umarni kamar ka haifeni ,okey kayi sauri kayi min jina jina ina jiranka ?
"Allah yaya ma'aruf ka kama kanka dani dan abubuwan ka sun fara damuna ,ka mutunta sauran girmanka ,kafin na maka abinda ba kayi tunani ba, koda yake ai ba girma a tare da kai bare....
cikin zafin rai yace "dan ubanki ni kike fad'awa wannan magana ?
laulausar tafin hannunsa ya kai daidai gefen wuyanta zai fixgota da karfi da niyyar ingizata waje ya huta da kallon fuskarta .....
hankalinta ta soma ƙoƙarin kwatar wuyanta daga garesa saboda wani azaɓaɓɓen zafin da taji ya ratsata ,ta fizge wuyanta da kyar ta juya da sauri.. ya sake riko hannuta cikin nashi , ta juyo a matukar firgice ai ko ta faɗa saman qirjishi batare data shiryawa hakan ba ,yayi baya zai fad'i cike da tsoro tasa hannuwanta duka ta riko shi sosai a jikinta , suka haɗe guri ɗaya sannan suka yi luuuuuuuu suka faɗa kan kujera mai zaman mutun uku dake parlour'n, hancinta ya sauka a daidai inda yafi jin kamshi turare a qirjinsa, shi kuma fuskarsa ta haɗe da qirjinta a matukar firgice suka d'ago idanunsu ya kalleta itama ta kalleshi atare suka zaro idanuwansu....
take kuma zuciyoyinsu ya dokawa da matsanancin karfin gaske ,Kusan sumewa ta so yi agurin yayinda shi kuma ya bita da wani wahalallen kallo aranta tace " wayyohlly Allah yau na shiga uku ... gaba-daya ta kasa motsi ajikinsa duk ta rikice sakamakon sansar jikinta dake budewa, wani irin yanayi ta tsinci kanta wanda bata taɓa jin makamancin sa ba ...
so take ta mike daga jikinsa amman hannuwansa duka dake zagaye da qugunta yasa ta ƙasa mikewa ta ɗan motsa dan ya sakar mata jiki amman yaki ,illa wani kallo daya dinga binta dashi wanda bata san ko na menene ba.. aiko take idanunta suka cicciko da ruwan hawaye ganinta kwance ajikinsa sun tsurawa juna ido,'bangaresa kuwa wani irin takaici ke tattare dashi na ganin yanayin da suka kasance wanda yafi komai ciwo a rayuwarsa, ransa idan yayi dubu to a matukar 'bace yake......
Ahankalin ya ci gaba da Kallonta da mamaki a saman fuskarsa ummita kuwa kallon yanayinta kawai zaka ka gane kalar tashin da take ciki, Kallonta yake yana jin zafi acikin zuciyarsa da gangar jikinsa Ahankali suka dinga fidda ajiyar zuciya ..
Mama taji shiru har goma ta kusan bugawa bata ga ummita ta dawo ba dan haka ta kira number ma'aruf wayar tana ringing amman ba'a ɗauka ba ,duk ta damu saboda tasan ƙarshenta tayi masa halin nata ne ,shi kuma babu hakuri ya tsareta a d'akinsa .....
kusan minti goma suka ɗauka a haka sannan ta kai hannuta daidai saitin qirjinshi da niyyar mikewa ya buga mata tsawa "if you touch me I will finish you ,zan miki dukan mutuwa idan hannunki ya taɓa qirjina ...
tsawar daya buga mata ne yasa gaba-daya ta sake daburcewa ta rud'e ganin yadda yake Kallonta a kaskance, muryarta na rawa tace" ka... ka sakar min jiki to....
sai lokacin ya lura da hannunsa dake daidai kugunta , runtse idanunsa yayi ,zuciyar na wani irin harbawa da zafi, ahankali ya ware duka hannuwansa alamun ta tashi, jikinsa har rawa yake saboda bakin ciki kasancewarsu tare , ai ko yana gama ware hannuwansa ta mike da sauri ta bar d'akin tana haki .
Cikin sauri ta shiga Bangarensu tayi hanyar dakinta ta faɗa saman gadonta tana runtse idanunta tare da kudundine jikinta gurin ɗaya dake wani irin kyarma....
tsigar jikinta kuwa ban da mikewa babu abinda yake, duk inda ta motsa tsigar jikinta yrrrrrrrrrrrrr take jinta ta makure sosai tana fidda numfashi sama sama "Allah kayi min tsare da yaya ma'aruf , duk sharrin da yake bina dashi Allah ka mayarsa ,wata zuciyar tace "dan'uwanki ne fa ....,?
"Kai wannan baya daga cikin ahlinmu ,ni ina ganin shi ba ma d'an umma bane ,an canza mata shi a asibiti dan gaba-daya halinsu ya bambamta da nata mama ga kirki sanin Yakamata da mutumtaka .
Bata ji motsin shigowar mama ba sai jin sautin muryarta tayi akanta " ke me ya zaunar dake daga kai abinci ?
Ummita ta bude idanunta da kyar batare da tace mata komai "kina jin mutane suna magana amman kinyi shiru?
" me ke mun ki naganki haka ?
Ummita dake kwance tana fidda numfashi sama sama sakamako tafin hannun ma'aruf dake kai kawo ajikinta , muryarta a sanyaye tace " babu komai mama .
"Babu komai shine zaki zo ki takure kanki ? Ummita ta kad'a wa mama kai "to ai shikenan Allah ya yaye miki idan ma wani abu ne ke damunki .."
Shi kuwa ma'aruf kasa zama yayi a d'aki saboda wani bakon al'amari daya tsinci kanshi ciki mai wuyar misaltuwa ,shi bama zai ce ga abinda ke damun zuciyarsa da ga gangar jikisa ba ,haka nan ya dinga ji zafi acikin ranshi , zuciyarsa na quna tamkar ana tsomata cikin wuta , zumbur ya mike ya fito wajen gidan yana shawagi da tunani iri iri , dafa kafadarshi yaji anyi ta baya, ya juyo idanunsa a fusace da niyyar yiwa wanda ya dafa shi maseefa,karaf idanunsa ya sauka akan Yusuf makwafcinsu kuma abokinsa dan tare suka taso, sukayi karatu, jami'a ce kawai ta raba tsakaninsu, kowa ya tafi jami'ar da yake so ..
hannu Yusuf ya miko masa suka gaisa "dama ashe Kai ne tsaye a nan na ɗauka rayhan ne ?
Yusuf yayi magana fuskarsa cike da fara'a " "eh wallahi ..
ma'aruf ya faɗa yana furzar da iska ta bakinsa mai zafi " ya kake ka dawo lafiya?
" alhamdu lillah ya faɗa atakaice ,"me ke faruwa da kai ne haka duk sai naga kayi wani sukusuku kamar wani mara lafiya ?
Yusuf ya faɗa tare da gyara tsayuwarsa yana fuskantar shi sosai , ma'aruf ya dubi kanshi sama da kasa sannan ya sauke ajiyar naunauyen zuciya ya maida idanunshi ga Yusuf dake tsaye a gabansa ya ɗan ciza lip's d'insa " babu abinda ke damuna ya faɗa atakaice dan ya soma gajiya da Yusuf har sai da ya sanin fitowar da yayi , dan Yusuf ba dai surutu ba ko aku ta shafa masa lafiya .
Yusuf yayi murmushi yana shafa kanshi yace " dama fa Ina cewa zan kira ka a waya sai kuma gashi mun hadu.
" Ya rabbi ya furta a kasan zuciyarsa sai dai babu yadda ya iya dan haka azahirance yace" toh Allah yasa lafiya ?
"a'a lafiya dama magana ne akan Ummita a firgice ma'aruf yace "wace ummita?
" ummita naku mana don Allah ina son in tambayeka ne ko an tsaida Mata miji ?
Wani irin banzar kallo ma'aruf yayi masa sannan ya amsa a ciki "uhnmmm ?
"Kenan kana nufin ba'a
mata miji ba ?
",Eh ya bashi amsa a qaugauce .....
"Amman na tambayi meenal tace min am mata miji " maganata zaka yarda dashi ko ta meenal ?
" Ta ka "to ba'a mata miji ba, idan kana sonta ne ka shigo sahun masu nema aurenta yana gama faɗar haka ya juya ya barshi tsaye yana zance zuci "mahaukaci banza kawai ,ai daman sai irin mahauka ne zasu zo nemanta har kuce kuna son wannan wawiyar yarinyar ,wani me cikakken hankali ne zai zo ...?
"Ai gara ka kwashe mana ita mu huta akan rayhan dina ya aureta .. ..
"Kai tsaye part dinsu ya nufa inda ya iske meenal da jidda suna kallo a zeeyworld a fusace yace "Sannnku manufukai banza wato shine har kuke fadawa mutane a muku miji kou ?
' toh wallahi idan kukayi wasa sai na kai hotunku masallaci ko za'a samu wanda taimaka muku ... .
"wai meya faru ne ma'aruf ? Inji cewar umma .
"Barni dasu Hajiya ai sun san abunda suka yi," toh ai shikenan kun fi kusa Hajiya tayi wucewarta ta barsu "ke jidda me kika gayawa Yusuf ? Nan da nan idanunta ya cika da hawaye tace" wallahi ya'ya bani bace meenal ce..
"okay dama ita naga alamar ta fiye rawan kan tsiya daita da wacan fat lion din mai tsiffar namun daji "toh ku shirya dan zan ci ubanku daya bayan daya a gidan nan ,duk ga saninku can anyi musu aure ko kunya bakwa ji , za'a taimakawa ɗaya daga cikinku amman dan iyayi da bakin ciki kice an mata miji "to uban wa kika tsayar mata dashi ?
"yaya ma'aruf dan me Yusuf zai rasa wacce zai ce yana so a gidan nan sai ummita wannan ai dis great ne wallahi ..
"Eyeeeeee wace ce ita da ba zai ce yana sonta ba ,ko kina nufin tafi karfinsa ne ko me ?
"Ai ya ma'aruf ba sai an fada ba,kai kanka kasan da bambancin tsakanin ummita da Yusuf sam ba'ajinta bane , bambancin ma bayyane yake, yaje gaba ya nemi matarsa amman ina ummita tafi karfinsa wallahi , ba zato ba tsammani taji saukar mari a kuncinta "ubanki da wannan maganar da kike faɗa .
Tayi saurin dafe fuskarta tana dubansa "idan baki sani ba ai Yusuf ne dai-dai ita," wa kika taɓa ganin yazo gidan nan da sunan yazo gurinta zance ?
"Wallahi idan na sake jin kin cewa wani am mata miji sai na balbaleki a gidan nan "
"Tana kuka tace "ai ita ce bata son kula samari .. asalima abakinta naji tana cewa duk wanda ya tsaida ita anyi mata miji , ya kai hannu ya shafa goshinsa na second biyu sannan yace "duk sanda tace haka ki ƙaryatata agabansu yana gama faɗar haka ya juya fuuuuuu...
"ai kin gani ba....?
" sai dana kwa'beki saboda gudun haka kika ki , gashi kin jawo kanki shan mari da tsakar dare nan kina zaman zamanki "to ni yanzu meye laifina anan aunty jiddah ?
"Oho miki ke dai kika sani ,ni dai Kinga shigewata babu ruwana wallahi .....
Zuciyarsa na matuƙar zafi ya dawo cikin d'akinsa goran ruwan ya ɗauka tare da kafa shi a baki sai da ya shanye tas sannan yayi wurgi da robar ,bedroom d'insa ya shiga ya d'auko hoton suhaima ya rungume ajikinsa yana jin wata irin soyayyarta na ratsa kowani sashi na jikinsa ,shi dai yana sonta sosai sai dai sha'awarta biyo bayan soyayyar da yake mata tunda yasan duk inda so yake dole sha'awa tana biye ....
Two friend's (bsbs)
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~TRUE LIFE STORY~
FREE NOVEL NOT FOR SELL
AL'QALUMAN
*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*
~DEDICATED TO~
MARYAM ALHASAN D'AN IYA
(MARYAM OBAM)
BEST FRIEND FOREVER AND EVER, AKWAI AMANA 'KAWARMU ALLAH YA BARMU TAREN TARE SON SO FI SABILILLAH 🥰🥰
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
PAGE 5
.......meenal d'akinsu ta nufa ,ta iske jiddah har ta soma bacci , ta samu guri daga nesa can daita ta faɗa kan katifa ta kwanta tana sauke numfashi, tana kwance har kusan minti goma bacci bai samu nasarar d'aukarta ba tana shafa inda ya ma'aruf ya mareta haɗe da tunanin maganganunsa akan Ummita , hannu tasa tana tashin jiddah. "aunty jiddah ! aunty jiddah !!
"Wai me ye ne kin zo da wahalarki kenan kou ?
"no ba wani wahala bane aunty jiddah ki tashi magana zamuyi ?
"Gaskiya ni bacci nake ji amman kiyi ina sauraronki .
" daman akan abinda ya faru d'azu ne , na fad'awa ummita abinda ya ma'aruf yace gobe ko kuwa ?
Jiddah ta gyara kwanciyarta sannan tace "wannan kuma damuwarki ce ki faɗa mata ko karki faɗa mata babu ruwan, may be marin da kika sha d'azu ne bai isheki ba ,kiyi harama ki sake janyowa kanki ,ni dai Kinga bacci zanyi na gaji da matsalarki...
meenal ta ta'be baki batare da ta sake cewa komai ba sai dai
ta kudiri aniyar sai ta sanarwa ummita abinda ya ma'aruf yayi ..
******
Ɓangare ummita kuwa kwance lamo ta rasa abinda ke mata dadi ,sai faman juyi take akan katifa , ranar bata yi isasshen bacci ba, gaba-daya abubuwan da ya ma'aruf ke mata ne yake dawo mata daki daki suna samun muhalli a cikin zuciyarta tana auna su 'kwa'kwaluwarta tare da yi musu kyawawan ma'aji a in da baza su goge ba , sosai ta dinga tunani har tsakiyar dare tana sak'e sak'e a ranta, sannan bacci barawo ya saceta.
Washegari
Ummita tsaye a d'akinta sanye cikin wando da riga na makarantar islamiyya, wando blue ruwan sararin samaniya, da rigar fara sol har kasa mai ratsin blue ajiki ,rigar ta sha guga sosai sai kyalli take, ta ɗan murzawa fuskarta farar hoda kana ta tsurawa fuskarta ido na second biyu sannan ta ɗauki agogonta a saman Dress morrow ta d'aura a tsintsiyar hannunta ta sanya farin hijab ta dan turare mai sanyi kamshi a kayanta , ta ɗauki jakarta ta rataya a kafadarta ,duk yadda ummita take tamke fuskarta amman sai da tayi looking attractive , kasa ta sauko a hankali fuskarta a d'aure ta tarar da mama ta gama shirya dining table , kai tsaye ta wuce dining taci abinci sama sama tana duba agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunta karfe 9 na safe ne yanzu.
mikewa tayi ahankali ta isa gurin mama tace "zan wuce makaranta daga nan zan biya gidansu himaya na dubo jikinta wai bata jin dadi.
"uhnmmm karki biya daga makaranta ,ki bari idan kin dawo gida sai nasa sale ya kai ki ai zai fi ko ?
zumburo baki tayi " kai mama ai da y'an ajimu zamu gaba-daya fa "to na hana, ki wuce ki tafi sai kin dawo Allah ya tsare "ameen ta faɗa a cikin ranta sannan ta fice daga part dinsu tana rausaya .....
Adaidai bakin kofar part d'insu meenal ta ganshi tsaye sanye cikin kananan kaya da jaket mai hula a saman rigar , hannunsa ɗaya rike da waya yana daddanawa yayinda ɗayan hannun ke cikin aljihun jaket din ya yi crossing legs d'insa ..
taji kamar ta koma da baya ta kaucewa maseefarsa ,amman ta d'aure ta sanyawa jikinta jarumta kamar koda yaushe idan sun haɗu ,ko ba dan haka ba ma ko saboda su meenal ta d'aure ,dan kullun sune ke biyo mata su wuce , yau da alamun sunyi makara ne yasa taji su shiru .
shi kuwa tun
ta howarta yasan itace ke tafe amman yaki d'agowa dan baya son kallon lion face dinta d ..
Qirjinta na dokawa ta dinga daga kafafunta har ta qaraso daidai inda yake tsaye batare da ta kalleshi ba ta taɓa ta gefensa har kafad'unsu na gogar juna , saurin goce kafadarsa yayi cikin izza da dakiya ya sake kawar da fuskarsa da hankalinsa kan abinda yake batare da ya yarda ya kalli ko ɗan yatsanta ba ..
Naunauyen ajiyar zuciya ta sauke lokacin data sanya gangar jikinta ciki parlour'nsu meenal cike da natsuwa , bakinta ɗauke da siririyar sallama ,har kasa ta durkusa a gaban hajiya umma ta gaishe da ita sannan ta k'arasa d'akinsu meenal , ko cikakken minti biyu ba tayi ba suka ta fito gaba-dayansu ,tun a lokacin meenal taso ta sanar mata amman ganin sunyi latti yasa ta bar maganar har idan sun taso ...
Tafiya suke a hankali duk da lokaci ya tafi amman hakan bai sa ummita d'aga kafafunta ba ,"muyi sauri mana kin san fa lokaci ya tafi ,"idan zaki iya jerawa dani haka mu cigaba da tafiya ,idan bazaki iya ba ki qara mai kawai ,dan daga haka bazan qara sauri ba.
"dole ki fad'i haka mana tun da kinsa duk rabbin malaman makaranta sonki suke yi ,babu wanda zai yarda a cikinsu ya taɓa lafiyar jikinki ni kuwa fa ...?
Murmushin gefen baki kawai tayi tana sake lankwasa kafafunta "karki damu kema kinsan matsawar muna tare babu mai ta min lafiyar jiki ...
duk inda suka wuce idanun jama'a na kansu ko in ce yana kan ummita .
Har suka qaraso gurin wasu maza kusan su biyar zaune kowane a cikinsu hannunsa rike da sigari suna zuka a hankali tana fitar da hayaki ,ganin ummita yasa gaba-daya hankalinsu ya karkata akanta ,tun daga sama har kasa suke binta da wani mayataccen kallo, daya daga cikinsu ne ya soma magana ahankali "kai friend's yarinyar ce haɗuwarta na kasheni kullun na ganta zata wuce sai naji kamar na fizgota gareni ,wallahi ina maseefar jinta araina.
"ai yarinya ce gsky ta haɗu babu karya dan bata da makusa, nima da zan samu zan d'ana, dan irinsu wuyar sha'ani garesu ,basa kula 'yan zaman banza irinmu ,kai ba ma haka ba ko aurensu kaje nema ba'a baka ba .
mus'ab yayi murmushi yana kada sexy eye's dinsa kamar mai jin bacci irin nasu na yan shaye shaye "tunda raina ya biya sai na d'and'ani zumarta ta kowani hali....
Wanda ke zaune a gefensa ya kwashe da dariya "kai mus'ab ban da saka rai a irinsu fa "kai ka share tunda na kwadaitu dole na lasa " shikenan idan ka lasa ni ne second ..
"Ni Kuma third suka sake kwashewa da dariya har sanda suka ga bacewarsu ummita ..
Haɗe rai sosai mus'ab yayi "wannan zumar tawa ce ni kaɗai ku dai yan tayani farauta ne ,take suka shiga tsara yadda zasu samu nasara akan ummita ..
*****
Akan hanyar dawowarsu daga islamiyya tafiya ummita take yi , cike da natsuwa take ta kawa ahankalin kamar mai tausayin kasa ,
yayinda gefenta meenal ce take bata labarin abinda ya faru daren jiya, har ma da marin data sha a hannun ya ma'aruf "amman ke ummita me yasa baki son kula samari alhalin kina samun masu tsananin sonkin da aure ?
" ni an ji babu me zuwa gurina koma nace babu wanda ya taɓa cewa yana sona as age of 17 ....amman ke meye dalilinki nakin kulasu ?
"Babu wanda ya isa ya hana faruwar haka ,dole kiyi aure ,ai duk ɗan sunah baya gudun aure ,ko ya ma'aruf ma da alamun ya soma gajiya damu, faɗa fa yayi sosai jiya har da gori ...
Shiru kawai ummita tayi mata amman gaba-daya ranta idan yayi dubu to a ɓaci yake. ..
har suka qaraso kofar gidansu bata furta komai ba,sai hancinta kawai take hurawa tana cizan lip's dinta na kasa , hawaye ne yake ƙoƙarin zubo mata tayi saurin danne zuciyarta.
cike da sarewa meenal ta dubeta ummita "shirun nan naki fa yana bani tsoro, ba wai na faɗa miki bane dan kije ki sameshi ,abinda yasa ma na gaya miki, ji nayi idan ban faɗa miki ba tamkar na munafurceki ne ,kuma na boye miki abu mafi muhimmanci ga rayuwarki ,ko babu komai ummita ya ma'aruf me kaunarki ne tunda yaji zafi akan kina korar samarinki ,a daidai harbar gidansu ummita taja ta tsaya tana fuskantar meenal tare da d'aura hannunta bisa kafad'arta "wannan ba qauna bace meenal duk cikin salon qiyayya ce , amman kinsa wani abu ?
Meenal tayi saurin girgiza mata kai a tsorace ",ina da type din namijin da nake so a rayuwata ...
"ina son namiji kamili mai nuna ko in kula ga lamuran mutane, mai Jan aji da kuma miskilance ....
ta ware kyawawan idanunta sosai sannan ta cigaba "Kinga duk cikin masu zuwa gurina babu mai wannan siffofin dana lissafa miki.
"to amman ai ya rayhan yana sonki kuma shima babu laifi yana da nashi daidai gwargwado "manta da wannan ni nafi son wanda zan so da dukkanin zuciyata ba wanda yake sona ba ......
Meenal tayi sororo tana kallonta ,inda mata ke da muradin auran masu son su da tattalinsu, ke kuma ra'ayinki daban,koda yake dama haka kike duk abinda ake so da yayi ke baki cikinsa sai wanda aka gama yayi, ko wanda ba'a so ....
"Kullun cikin mamakin wannan halin naki nake ...
Murmushi ummita tayi "meenal kenan ki daina mamaki saboda kin rigada kin san halina ba tun yanzu ba , kin san Allah sai na yiwa ya ma'aruf magana ko da itace zata zamo maganarmu ta karshe dashi arayuwata ..
Tana gama faɗar haka ta cire hannuta a kafadar meenal ta juya ta cigaba da takawa ahankalin, meenal ta biyo bayanta da sauri ",haba ummita dan me zakiyi masa magana bayan kin san halinsa ?
A fusace tace "Ke me yasa kika faɗa bayan kinsan halina ba tun yau ba ?
"Kinsan ba'a gulma dani , ba'a cin naman wani dani ,sannan duk wanda akace ya fadi abu akaina sai na same shi nayi masa magana ,idan kin manta halina gashi na tuna miki sai ki ɗauki hakurin hukuncinsa gareki dan babu makawa sai na taresa ......
"inna lillahi "ki yiwa Allah ki rufa min asiri wallahi ko aunty jidda taji sai tayi mugun sa'bani "oho ni dai babu ruwana gobe ma duk abinda akayi kizo ki faɗa min ina maraba da hakan ta haɗe hannuwanta guri ɗaya alamun godiya.....
doguwar hanyar da zata shigar daita har cikin gidansu anan suka ci karo dashi ya fito da sauri da alamun fita zai yi, ta gefenta ya wuce yana kawar da jikinsa dan ma kar ya ra'bu da ita, tana murmushi ta jiyo tana kallonsa har zai karya kwana zuwa harabar gidan tace " fat lion da iyakacin karfinta.......
Cak ya ja ya tsaya kamar an dasa shi kafin daga baya ya juyo ahankali yana fuskantarta da idanunsa masu matukar bugar da zuciyar duk wacce ta kalli cikinsu,
so yake ta maimaita abinda tace dashi take ko da kanta ,hannuta ta daga masa ",yes da kai nake zaka qaraso ne , ko ni nazo da kaina ?
Qirjinsa ya nuna da yatsan hannunsa alamun shi , lumshe masa kyawawan idanunta tayi sannan "tace Yes of course da kai nake fat lion bari na qaraso tunda kai ka kasa ..
tasoma takowa Ahankali kamar batason taka kasa yayinda qirjinta ke lugude , a daidai lokacin meenal ta qaraso tana ganin abinda ke faruwa ta juya da sauri dafe da kirjinta "shikenan na shiga uku yau a gurin ya ma'aruf..
Har ta qaraso idanunshi na kanta ta tsaya can nesa kaɗan dashi wanda bai fi taku biyu a tsakaninsu ba ,ta kyata masa yatsun hannunta biyu a daidai kunnenshi domin ta dawo dashi hankalinsa da yayi nisa gurin tunani "ya ma'aruf ko me kake da suna oho...
Koda yake ba dan haka yasa na tsaida kai ba ..
Na tsaida kai ne saboda ina son sanin me ye damuwarka da subai'a ,"me subai'a ta maka ?
"Me subai'a ta tsare maka arsyuwarka ?
"Shin ko akanka nake da zaka damun kanka da lallai sai na kula samari ?
"nice nan bana ra'ayin kula su,kuma babu wanda ya isa ya sani kula samarin da ba type dina ba ,ina nan a cikin gidan tunda ba gidanku bane gidan ubana ne har sai na samu wanda yayi daidai dani ,da irin abinda nake so ga namiji,dan ba kowani kwashe kwashe zan kwasawa kaina ba ,ko a Shari'ance ance dole sai nayi zance da samari sannan zanyi aure arayuwata ?
Shi Shari'a Muslunci is different with morality wannan ya zamo karo na karshe daga yau karka sake damuwa da zuwan masu sona tun. .....
Ji kake Tasssss Tasssss Tasssss marin ya ma'aruf sai da ummita taji wani jiri ya dibeta har zai yaddata Allah ya jiho ya rayhan yayi saurin rikota cikin zafin nama saboda ganin tana shirin faduwa "yar iskar banza da wofi har ni zaki kalla ki dinga fadawa son ranki , sa'anki ne ni dan ubanki ?
"A she daman baki da hankali ?
Allah sarki ya rayhan ji yayi kamar shi aka mara har cikin zuciyarsa yaji zafin marin da ma'aruf yayi mata ..
Ita kuwa kwanciya tayi lamo a qirjin rayhan yadda ya tarota tana zubar da hawaye har ta soma jika masa gaban rigarsa "yar iska ni an ce miki rayhan ne ko waɗan can yan iskan masu zuwa suna nacin sonki ?
"Sannan idan kin ga dama ki kula masu zuwa gurinki ,idan kin ga dama karki kula su wannan ruwanki rayuwarki ce ,kece zakiyi kwantai kowa yayi aure ya barki ki zama jaka mai aikace aikace gidan ,stupid Kawai as age dinki ,bari na faɗa miki abinda baki sani ba kina qara shekara biyu nan gaba kin zama tsohuwa duk wanda ya kwasheki wallahi tsohuwa ya aura ....
Yayi taku ɗaya zuwa biyu ya zagayo ta inda fuskarta take "listing to me idiot idan kika sake kirana da fat lion I will deal with you stupid Kawai more than donkey's ...
Duk maganganu ma'aruf rayhan ji yake kamar ya rama mata, tunowa ma'aruf ne yasa yayi wani dogon numfashi dan zai iya maida maganarsa babbar magana tare da gaba , shi kuwa ma'aruf ido ya tsura musu ganin yadda yanayin rayhan ya canza alokaci daya ....
Cike da matsanancin tashin hankali ma'aruf ya juya ya isa in da motarsa take parke ya buɗe ya shiga, shi kuma rayhan yayi cikin gida daita tana rabe a gefen jikinsa yana bata hakuri , har suka shiga part dinsu , mama dake zaune ta lumshe idanunta saboda tasan duk yadda aka yi ita da ma'aruf ....ya zaunar daita yana bata hakuri yana tambayarta abinda ya hadasu taki ce masa komai sai kuka take har da shesheka kukan da mama take jinsa har cikin ƙwaƙwalwarta ,a duniya idan akwai abinda ta tsana bai wuce kukan ummita ba ,gashi me dalilin sata kukan rayuwarta ce bata haɗa shi da komai ....
Ana cikin haka meenal tashigo tana kuka ta rungume ummita ajikinta "sai da nace karki yi ummita karki sameshi da maganar amman kika yarda, kalli da yadda fuskarki tayi ta k'arasa maganar tana shafa daidai inda ya mareta, ya rayhan yace "au kinsan abinda ya hadasu ne ?
Kai ta d'aga masa alamun tasani sannan ta zayyano masa abinda ya faru da abinda ummita ta faɗa wa ya ma'aruf...
Ahankali mama ta buɗe idanunta "sai kiyiwa mutane shiru mara jin magana "haba mama da me zata ji mari har uku fa bayan zaginta da yayi inji cewar rayhan" ka barni da yarinyar nan rayhan wannan ai rashin kunya ne har yar'uwarki na baki shawara kice sai kinyi saboda gaki tattacciya, zaki tashi ki 'bacewa ganina anan ko sai na qara miki wani marin ..
"Haba mama Allah sai dai ki haɗa dani ki mara ,"hannu ummita ya kamo" tashi kije ciki kinji my everything yayi mata maganar adaidai kunnenta, ta soma tafiya tana kuka "gaskiya mama bai kamata kice mata haka ba ,zai sa taji kamar kin tsaneta ne shine fa yake fara shiga rayuwarta, ina ma ruwansa da masu zuwa ba'a kulasu ban da dai bakin ciki irin nasa, an ce masa tayi kwantai ne da zai dinga neman talla da ita ?
"uhnmmm rayhan kenan kai ma kana yi kamar ba kasan ummita ba .....
Two friend's ( bsbs)
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~TRUE LIFE STORY~
FREE NOVEL NOT FOR SELL
AL'QALUMAN
*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*
~DEDICATED TO~
MARYAM ALHASAN D'AN IYA
(MARYAM OBAM)
BEST FRIEND FOREVER AND EVER, AKWAI AMANA 'KAWARMU ALLAH YA BARMU TAREN TARE SON SO FI SABILILLAH 🥰🥰
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
*RIGIJI GABJI,RANAR KUKE JIRA YAU GATA TAZO MASOYA*
*MARUBUCIYAR NAN TAKU WADDA TA SABA KAWO MUKU LITATTAFAI INGANTATTU MASU TSUMA ZUCIYAR ME KARATU WATO HASSANA D'AN LARABAWA*
*MARUBUCIYAR*:
SANADIN HOTO
Da
HASSANA DA HUDSAINA
*YAU TA SAKE DAWO MUKU DA SABON LITTAFINTA WANDA YA ZARCE DUK LITATTAFANTA A KOMAI WATO CIN AMANAR RUHI,KAI DAGA JIN SUNAN KUN SAN AKWAI TAFKA TAFKA DA K'ULLE K'ULLE ,AMMA ZATA WARWARE MUKU K'ULLIN DA ZARAR KUN BIYA 200 DOMIN SAMUN LITTAFIN,KAR KU BARI YA WUCEKU ,DOMIN WANI IRIN LABARI NE DA BAKU TAB'A CIN KARO DA IRINSA KO MAI KAMARSA BA,FAD'AKARWA ,NISHAD'ANTARWA,ILIMANTARWA,TAUSAYI,DA SOYAYYA ME TSAYAWA A ZUCIYA ,TARE DA WATA IRIN CIN AMANA DA BAKU TAB'A RISKAR IRINTA BA,KU DAI KU HANZARTA NEMAN MARUBUCIYAR DOMIN KU SIYA KU KARANTA AKAN KUD'I K'ALILAN 200*
*ZAKU IYA NEMANATA AKAN LAMBARTA KAMAR HAKA,08080049548 DAGA NAN ZATA GAYA MUKU YADDA ZAKU BIYA KUD'IN ,KU DAI KU HANZARTA KAR AYI BABU KU ,KU TUNA DA SUNAN LITTAFIN*
CIN AMANAR RUHI KARKU DAKE A BAKU LABARINSA
🥰🥰🥰🥰
PAGE 6
...Cike da tausayawa meenal ta sake matso hawayen dake cikin kwarnin idanunta suka gangaro bisa kuncinta tana duban fuskar mama cike da jin haushi da takaicin maganarta ,
ta kasa fahimtar wani irin matsanancin so mama take wa ya ma'aruf , "wacce irin shakuwa ce haka a tsakaninsu da har zata fifita shi akan diyar cikinta ?
Mama bata ganin laifinsa akan komai da zai aikata ,sannan bata son taji an fadi laifinsa akan komai matsawar kuwa ayi kuskuren faɗar laifinsa a gaban ta yanzu ne zata nuna bacin ranta, kallon mama mennal take har zuwa lokacin wacce abubuwan da ya ma'aruf ke wa tilon diyarta sam baya damunta wani lokacin ma har karfin gwiwa take ƙara masa .....
kusan minti shabiyar da barin ummita parlour'n amman hawaye ne yake cigaba da zubowa daga idanun meenal, barin ma data tuna itace silar komai ,tunda ta rigada tasan muguwar tsanar da suka yiwa juna ...
Sautin muryar mama ce ta doki kunnen meenal "Ki tashi ki wuce tun baki qarar da ruwan hawayenki a banza ba.. meenal ta marairaice murya tace "haba mama ki daina yin haka , da me kike son taji ?
"mari fa ba d'aya ba har uku ya ma'aruf yayi mata a kuncinta , ai hakan bai kamata ba a matsayinsa na babba , gaskiya mama ki dinga adalci daga ya ma'aruf har ummita naki ne kamar yadda kowa ya sani ,ki daure ko sau ɗaya ne kiyi masa magana akan abinda yake yiwa ummita nasan zai fahimta..
"Wallahi muddin kece kika faɗa masa illar abinda yake yi am very sure zai fahimceki kuma ya daina saboda yana matukar jin maganarki ,
yana ganin girmanki fiyye da uwar da ta kawo shi duniya....
"kema kinji abinda kika ce, mutumin dake ganin girmana da muntuncina, mutumin da zai iya tsallake maganar uwar data kawo shi duniya akaina, shine mutumin da kike tunanin na yiwa magana dan ya hukunta diyar cikina bisa ga laifinta..
"To na zaunar dashi na karanto masa me "nace masa me ya hukuntata ko me kike son nace masa?
" ki ce masa duk abinda zai had'asu da ummita ban da duka ,murmushi mama tayi "kai meenal an gaisheki mai yar'uwa kema sai kiyi yar'uwartaki faɗa ta daina abinda take yi ,rashin kunyarta bata karewa akan kowa sai d'ana "to mama ai shine yake farawa "ke dai tashi kije ki cire uniform kici abinci ki hutawa ranki da wannan damuwar ita kanta wacce kike fushin akanta ma killa tayi bacci.
Ta mike ranta a matukar 'bace "Allah tunda abun ya zama haka da Abbanmu zan hadashi tun da ba jaka bace, ina laifin yayi mata faɗa amman komai duka .
"Ni dai babu ruwana kije kiyi abinda ke gabanki, ai duk rashin kunyarta ne ya jawo mata ,ni nasan ma'aruf matukar bata shiga lamarinsa ba ,ba zai shiga nata ba dan haka ko gobe tayi masa rashin kunya ya ninka mata fiyye da wanda yayi mata yau a fusace ta bar part din mama tana gunguni dan taji zafi sosai ..
rayhan dake zaune ya tasa mama gaba da kallo ya girgiza kai "gaskiya mama zaki jawo ayi bala'i a gidan nan ,zaki sa mu samu matsala da ma'aruf akan wannan duke duke .
"wannan kuma damuwarku ce kun fi kusa idan dai ummita ce kaima baka tsira ba agurinta , zuciyarsa na matukar zafi ya mike ya fito daga part din mama ..
Ummita kuwa tana shiga d'akinta ta zube akan katifa , wani sabon kuka ya kufce mata , numfashinta ne ya soma canzawa ya dawo yana fita ahankali tamkar mai cutar asma .....
yayinda zuciyarta ke mata wani irin zafi tana harbawa da sauri ,gefen guda kuma wani irin azaɓaɓɓen ciwo kanta ke mata, hannuwanta duka tasa ta rike kanta da taji kamar zai fita a saman wuyanta , juyi kawai take akan katifa,tsawon lokaci tana kwance tana fama da ciwon kai da ciwon zuciyata gashi bacci yaki d'aukarta bare ta rage jin azabar da take ji a sansar jikinta hatta kayan makarantar dake sanye ajikinta ta kasa cirewa ,jikinta yayi wani zafi tamkar garwashin wuta , cikin haka meenal ta shigo d'akin, ta qaraso da sauri saboda ganin yadda take rike da kanta, dafe da gefen zuciyarta, muryarta a marairaice kamar zatayi kuka tace " sannu ummita meke damunki ?
"Ko kanki ke ciwo ?
"Zuciyata meenal zuciyata zata buga zafi nake ji ......"sannu kema dan Allah ki daina biyewa ya ma'aruf ki dinga barinsa da halinsa ,
Kin san halin ya ma'aruf bashi da kyau ta kowani fannin ..ki rabu dashi Allah zai saka miki mugu kawai ta ta k'arasa Maganar tana rungumota jikinta" ki rabu dashi Allah zai saka miki "bafa zan barshi ba meenal dole na dinga kwatowa kaina 'yancina , har yaushe abubuwa zasu daidaita a tsa....
tari ne ya tsarketa, ta dinga tari tana sake dafe dai-dai saitin zuciyarta.. da sauri ummita tayi hanyar fita domin kawo mata ruwa ..
cikin wani irin yanayi ta yunkura ta mike ta fito zuwa parlour'n kasa, akan step suka haɗu da meenal hannunta rike da cup din ruwa,tayi saurin kamota jikinta "sannu ummita da kinyi zamanki adaki "kamota tayi sosai suka sauko ta kwantar daita akan kujera mai zaman mutun uku tana jero mata ......
Mama ta leko daga kitchen saboda jin motsin mutune ganin yadda meenal ta riko ummita dake faman runtse idanunta tana jujjuya kai yasa ta fito da sauri zuwa gareta fuskarta tattare da damuwa ..
ko cikakken minti biyu mama ba tayi tsaye akan ummita ba ya rayhan ya shigo part din ....
muryarta a raunane irinta marasa lafiya ummita tace" yayaaaaaaa.........
da sauri ya nufo inda take haɗe da cewa "mama lafiya "me ke damun sarauniyata ?
Ya faɗa tare da ƙoƙarin taɓa wuyan ummita. .
"Murmushin yake mama tayi "kai kasan son jiki irin na ummita ina ganin zazzaɓi mari za'a yi... "wasssssss mama kaina zai cire,zuciyata zafi .... tayi maganar hawaye na gangaro mata ,maganar da ummita tayi yasa mama yin shiru cikin damuwa ,ya rayhan yace "plz mama bari na ɗauketa na kai ta hospital ,ina masjid jikina ya bani sarauniyata babu lafiya shine nazo" mama a kira min doctor husain...
Mama bata ce komai ba illa ciza lip's dinta da tayi tattare da damuwa "karki damu yanzu zan Kira shi , mama ta nufi hanyar d'akinta cikin sauri ,shi kuma ya rayhan ya zauna kusa da ummita ya kamo hannuta ya haɗe cikin nashi yana faman yi mata sannu "Allah ya baki lafiya my princess inshaallahu zaki samu sauki ..
"Ya rayhan jikinta yayi zafi sosai ,wai me yasa ya ma'aruf ke yin haka ne? Kwata kwata babu emani acikin zuciyarsa ko daraja mama ya kamata ya daina wasu abubuwan jin furucin meenal dake shiga cikin kunnenta yasa ta soma yin kasa daga jikin ya rayhan tana kiran sunan
"meenal .......
"na'am ummita "dan Allah karki sake ambaton suna nan sa anan ina jin kamar na mutu ,zuciyata na sake jin ciwo mai rad'ad'i ...."sannu shikenan na daina ....
******
Dr husaien zaune a gabanta bayan ya gama aune aunensu na likitoci ya daura mata drip ya tsura mata ido kawai yana Kallonta fuskarshi ɗauke da damuwa ,
muryarsa can kasa ya kira sunanta "ummita meke damunki ?
"Tunanin me kike yi haka da har zuciyarki ke daf da kamuwa da ciwo mai tsanani ?
"faɗa min meye damuwarki a rayuwa ,?
Tayi shiru ta kasa ce masa komai "ina sauroronki ki faɗa min abinda ke damunki kafin na sheidawa iyayenki jininki ya hau fiyye da ka'ida watakilla su zaki sanar musu da damuwarki .
"Doctor kai taimaka karka sheida masu komai ina tausaya musu, ina tausayawa halin da zasu shiga ,na fi jin tausayinsu akan kaina, plz karka faɗa musu wallahi babu abinda ke damuna idan kuma akwai zan faɗa maka ..
"No ummita akwai damuwar dake damun zuciyarki idan kika cigaba a haka ciwon zuciya zai kamaki jininki ya hau sosai ,dan haka ki faɗa min tun wuri ayi maganin matsalar ko
"Kin fi son Sai lokacin da ciwon zaici karfi ajikinki , mutuwa ta riskeki sannan suji abakina ?
"Ni doctor tare da irgiza masa kai "to ki cire damuwa aranki ,kina yawan damun zuciyarki da tunani shiyasa zuwa yanzu ta soma samun rauni ,har kika fara jin ciwo ,da zaran ciwon ya kama zuciyarki gaba-daya shikenan sai mutuwa ko kina son ki mutu tun yanzu ne ?
"inshaallahu ma babu abinda zai sameni kuma nayi maka alkawarin bazan sake damun zuciyata ba, "kenan kinsa abinda ke damunki har jinin ya hau ?
Sake girgiza masa kai tayi "a sanina bani da damuwar komai sai ta karatuna .
Girgiza kai yayi "Allah yasa amman ya kamata dai su sani "don't worry doctor tunda ciwon bai rigada ya kamani ba kaga ai bai kamata a faɗa musu abinda zai tada musu hankali ba ,shiru yayi ya cigaba da bata kulawa yana tambayarta "me matakin karatunki ?
ahankali ta motsa bakinta ,"bana na qare secondary school ina jiran result ne "kenan zaki cigaba ?
"Sosai kuwa shine cikar burina " kina ganin abbanki zai barki ki cigaba da karatu ?yayi mata tambayar yana tsareta da idanunsa"gaskiya bazan sani ba ko zai bari amman nasan dai zai barni inshaallahu "Allah yasa" matakin karatun addini fa kin sauke ne Alqur'ani ne?
"Eh nayi sauka tun shekara biyu data gabata yanzu shahada zan amsa sabon wata inshaallahu .
Doctor ya jinjina kai tare da yaba mata hakan yasa yaji ta sake shiga ransa tambayoyi ya cigaba da yi mata har sanda meenal ta sake shigowa " sannu ummita Allah ya baki lafiya ?
"Ameen ta faɗa tana lumshe mata ido "guri ta samu ta zauna kusa daita tana cigaba da yi mata sannu, yayinda bacci ya soma fizgarta dan har ta soma ganin mutanen dake zaune dishi dishi , mama ta sauko tana yi mata sannu ,"doctor meke damunta ne ko sai mun dangana da hospital saboda naji tana ta complain din zuciyata ?
muryar doctor husaien taji cikin kunnenta " "Hajiya muje daga waje ina son muyi wata magana mai mahimmanci "okay doctor Allah yasa ba wata damuwar bace ?
Doctor yayi gaba mama ta biyo bayansa
da sauri ummita ta kamo hannun meenal "dan jiyo min mai likita zai faɗa mama ...
"kamar la'be zanyi musu kenan bayan kin sha cewa babu kyau ",eh la'be haramu ne ba kuma shi nace kiyi musu ba , jiyo min kawai abinda zai faɗa mata zakiyi nasan ko tsaya wa kika yi a gabansu mama bazata koreki ba akwai abinda bana son doctor ya sanarwa mama ne ..
Kamar bazata tashi ba sai kuma ta mike tabi bayansu ...
Suna ƙoƙarin fitowa daga part din sai ga ya rayhan "yauwa doctor ga rayhan nan kana iya masa bayanin komai sai ya sanarwa abbansu , rayhan likita yace akwai magana mai mahimmanci da zai faɗa dangane da Ummita sai ka sauraresa ta fadin haka tana juyo ta dawo ciki ,ganin haka yasa meenal dawowa da sauri ta zauna batare data ce komai ba .
"Uhmmmm likita ina sauraronka, ka yi shiru kamar baka san da tsayuwar mutun ba sautin muryar rayhan ta ratsa kunnuwan doctor Wanda kana jin muryarsa kasan cike take da rauni da kuma fargaba .. naunauyen ajiyar zuciya doctor ya sauke "daman jinin ummita ne ya hau sosai fiyye yadda ake bukata shine ma abinda ya haddasa mata zazzafan ciwon kai da zafin zuciya wanda idan ba'a hattara ba komai zai iya faruwa daita ,girgiza kai ya rayhan yayi yana bin likita da kallo "to meke damunta ?
"Me ye hadinta da ita ?
"Wannan amsar na gurinta duk da nayi iya kokarina naga ta faɗa min ,ku dai bita a hankali nasan zata faɗa doctor ya k'arasa maganar yana mikewa ya rayhan hannu shima ya mika masa sannan ya wuce ..
Jiki a sanyaye ya shigo part din inda ummita ke kwance zuwa lokacin bacci ya ɗauketa gabanta ya durkusa ya tsira mata ido yana dubanta soyayyarta da tausayinta na sake huda zuciyarsa..
Parlour'n yayi shiru baka jin motsin komai sai numfashin mutanen dake zaune a cikinsa.
*****
bangaren ma'aruf kuwa kai tsaye gidansu suhaima ya nufa ,cike da rawar jiki batare data yi la'akari da yanayinsa da yake ciki ba ta faɗa jikinsa har yana iya jiyo dumin manya dukiyar fulaninta ,runtse kyawawan idanunshi yayi yana jin kirjinsa na dokawa , idan akwai abinda ya tsana bai wuce yaga tana yi masa tallar Brest dinta ba ,zareta yayi a hankali ya zauna tare da d'aura kafarsa ɗaya kan daya yana kare mata kallo can yayi gyaran murya "suhaima ...
"Na'am habibi "banason abinda kike min bana son kina.....saurin dafe goshinsa yayi saboda bazai iya qarasawa ba "uhmmmm ina jinka me akayi ,kuma meye baka so ?
tayi maganar tana sake matsowa inda yake yayi saurin dakatar daita "kinsa abinda kike yi kuma kinsa bani da interest so stop it I don't like it ,ba shashanci ne ya kawo ni gurinki ba aurenki zanyi dan....
Kawai yaji ta rushe masa da kuka "dan kaga ina rungunarka shine zaka dauka yar iska ce ni ,wallahi duk soyayarka ce ta sa kaga haka amman babu komai na gode da fassarar da ka min ta fadi haka tana matso ruwan hawaye ,hakuri yake son bata tare da fahimtar daita amman ya kasa kawai yayi shiru ya cigaba da kallonta ..
Gaba-daya suhaima ta kasa gane kanshi
A kallon da take masa yanzu ta fahimci akwai abinda ke damunsa ,shi yasa yaji haushinta dan ta shimfida masa brest dinta ,sau nawa tana yi masa bai taɓa cewa baya so ba sai yau ,
Ganin idan suka cigaba da shirun itace zata kwana ciki dan tasan halinsa idan zasu kwana tare tunda yayi irin wannan shirun bazai yi magana ba , ahankali tayi ta bashi hakuri tana lalla'bashi batare da tayi kuskure gurin salon bada hakurin ba ,bare yayi mata sha bala'i, ko ɗaukar fushi daita ..
har yaje gidansu suhaima abinda ummita tayi masa na damunsa cikin ransa ,sam ya kasa boye damuwar da yake ciki , har ya dawo gidan bai bi ta kan kowa ba d'akinsa ya shige ya kulle kansa ..sai gurin takwas na dare ya fito daga part sanye cikin riga hamles fari da wando three quarter Sai kamshi turaren 24k yake zubawa yana taku ahankali cike da izza..
Bangaren mama ya soma shiga ya iske ummita kwance kanta babu dankwali sai gashin kanta da yayi mata hijabi, tautaunawa suke ahankali wanda ba zai ce ga abinda suke magana ba tsakaninta meenal ba ,binta yayi da wani irin kallo bai san sanda ya lumshe ido ba, ahankali ya qarasa shigowa parlour'n yana binta da kallo rigar jikinta da kallo, idanunsa bai tsaya ko'ina ba sai kan yalwataccen sumar kanta mai sheki ,duk ajikinta babu abinda ke ɗan daukar hankalinsa kamar sumar kanta shima yasan yana da nasaba ne da son macce mai gashi da yake ,
tana ganin shigowarsa ta haɗe rai tamkar wacce aka aikowa da sakon mutuwa , ta janyo hijab dinta dake gefenta ta rufe gaba-daya jikinta har fuskarta ta runtse idanunta gam ..
Ganin ya samu guri ya zauna yasa meenal mikewa tsaye ta gaida shi aciki ta fice dan har lokacin haushinsa take ji ...
Two friend's (bsbs )
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~TRUE LIFE STORY~
FREE NOVEL NOT FOR SELL
AL'QALUMAN
*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*
~DEDICATED TO~
MARYAM ALHASAN D'AN IYA
(MARYAM OBAM)
BEST FRIEND FOREVER AND EVER, AKWAI AMANA 'KAWARMU ALLAH YA BARMU TAREN TARE SON SO FI SABILILLAH 🥰🥰
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
PAGE 7
...Har lokacin da yake zaune yana fuskantarta zafi yake ji a cikin zuciyarsa ,kallonta kawai yake yana jin zallar tsanarta da 'bacin rai mara misaltuwa, ban da furzar da huci babu abinda ke ta fita daga bakinsa , shi kaɗai yasan yadda yake ji a cikin zuciyarsa ,damuwa ne suka taru suka addabi zuciyarsa, lamarin suhaima da ummita koda yake shi al'amarin ummita qarami ne akan na suhaima.
a tun a wannin da suka gabata zuciyarsa ta soma yakiceta a muhallinta , ba dan baya son mallakarta s matsayin matar aurensa ba sai dan tsoro , tsoro alamarinta da rayuwarta yake bashi ,baya jin tafiyarsu zata d'aure har zuwa ga aure .....
"idan kana tunanin gujeta mata me kake tunani mahaiifinta zai d'aukeka ?
zuciyarsa tayi masa wannan tambayar mai cike da tarwatsa zuciya ..
"Tabbas maganar da mutane suka faɗa masa akanka zai tabbatar gaskiya ne ba karya ba ,zai tabbata kai din mayaudari , abinda ya kamata kayi kawai ka kauracewa zuwa gurinta na wani lokaci har zuwa sanda manya zasu shiga zance ya zanta da zuciyarsa yana sake furzar da iska mai zafi, yana cikin wannan tunanin ne mama ta sauka ..
"A'a Ma'aruf yaushe ka shigo?
Ahankali ya d'ago kyawawan idanunsa masu matukar kyau waɗan da suka wadatu da gashin gira dana ido ya zuba mata , sanye take cikin wata had'add'iyar doguwar riga majeter colour da jerin s stone tun daga sama har qasa , tayi kyau sosai a cikin rigar bama za kace itace ta haifi ummita ba, ko kuma ta dade a gidan miji kafin ta samu haihuwar ummita ba saboda yanayin tsarin jiki mai kyau da Allah yayi mata ..
Muryarsa a kasalance yace "ban jima da shigowa ba "
"A zubo maka abinci ne ?
" zubo min mamana tun safe ban ci komai ba "
"me yasa kake son zama da yunwa ?
"Ka daina barin kanka da yunwa ina ma kaje duk yau ban jika ba a gidan nan ?
"Ina gida ai tun safe sai gurin biyu na rana na fita zuwa gurin suhaima. "ayya ya suhaima take ?
"Tana lafiya tace a gaisheki "aiko ina godiya da gaisuwa ya dai kamata ka kawo min ita ta ganni na ganta muyi ido da ido daita sannan muyi kunne da kunne ta qarasa maganarta tana nufar dining table ..
"Ai dole ma tazo taga mamana idan batayi miki ba dole a canza ta ..
Murmushi mama tayi sannan tace "wannan gaskiya ne amman ai nasan ma'aruf dina bazai taɓa zaɓen tumun dare ba ... tana magana tana zuba masa abinci a plet ,ta dawo inda yake ta miko masa .
ya amsa yana kallon abinci "mama abincin nan fa yayi yawa "kai da kaci iya cinka ka bar sauran ,"na rasa dalilin dayasa baka son cin wadataccen abinci shiyasa gaka nan jiya iyau kullun ba kibar arziki "kiba fa halitta ce ma ba wai cin abinci ba, mama bata sake cewa komai ba shi kuma ya fara cin abinci , parlour'n yayi shiru kowa da abinda yake tunani gaba-daya tunanin mama ya tafi ne akan rashin lafiyar yarinyata Khadeeja ce ta shiga ta katse shiru da parlour'n ya ɗauka "ya ma'aruf wai in ji sakinar gidan baba sarki tace kazo tana son ganinka ,a fusace ya d'ago tare da galla mata wata uwar harara "get out tun kafin inzo in tattakaki anan ubanki zan mata idan nazo ..
Juyawa ta shuri takalmanta ta bar parlour'n tana qunkuni ganin yadda yayi mata kamar itace tace sakinar ..abinci daya kasa cigaba da ci kenan ya shiga jan tsaki "kai kuwa ma'aruf ba'a yin haka ya kamata kaje kaji me zata ce maka "rabu daita mama yar rainin hankali ce wai kamar sakina dan ta rainani zatace wai ni take so ina zan kaita mama ?yayi maganar yana furzar da iska "au batun na soyayya ne ai na ɗauka ko sada zumunta za'a yi , Allah ya sawwaka to me zai hana ka duba lamarin idan zai yiwu sai ka haɗa su su biyu da suhaimar "to ai ko ita suhaimar ma bangama tantancewar aurenta ba bare sakina da girme ta girmeni mama tayi mursmush irin nasu na manya sannan ta mike a hankali ta isa inda take ummita ke kwance ,ta yaye mata abinda ta lullu'be jikinta dashi "sanyi kike ji ne kika wani lullu'be jikinki haka ?
Muryarta a raunane tace "a'a mama na fi so jina haka "ma'aruf ya ta'be baki saboda yasan saboda shi tayi haka , aransa yace aikin banza yarinya ko kallo baki isheni ba "tou ai shikenan mama ta nufi hanyar step "ka daure qarasa cin abinka "ai wannan sakon ya 'bata min rai bazan iya sake cin komai ba ..
"Ka dai bi ahankali dan Allah karka je ka biyewa son zuciyarka ta fad'i haka tana taka step ɗaya bayan ɗaya ..
Ya ɗan dade zaune agurin yana tunani har sanda bacci yayi nasarar daukar ummita ,
Ganin tunanin ba zai bar kanshi ba yasa shi mikewa tare da zura takalmi ya isa inda ummita take ya kai hannunsa kai tsaye ya yaye abinda ta lullu'be jikinta dashi turus yayi saboda ganin bacci ya ɗauketa ,tsura mata ido yayi yana kallon shashin hannunsa kwance akan kuncinta kasancewarta fara , ahankali yaga ta motsa tana juyawa tare ƙoƙarin sake jan hijabinta bata samu nasarar janyowa ba, ta mirginowa zata fad'i ma'aruf na kallonta kamar ya tara duka hannunwansa saboda bata kariya , amman ya share dan bai son jinta a kowani Shashi na jikinsa aiko dum kake ji a kasa ta fado bisa kafafunsa da sauri ta bude idanunta sukayi 4 eye's dashi .....
Ido cikin ido suke kallon juna fuskar kowannensu cike da mamaki ," a fusace yace "dan malama tashi akan kafafuna tayi shiru tana rike da gefen cikinta "ki tashi stupid ki koma d'aki kin wani zo kin kwanta anan salon kowa sai ya fahimci baki da lafiya ya fad'i yana rakata da ƙatuwar harara , kallonsa kawai tayi ta 'bata rai ,batare da tace masa komai ba ta soma ƙoƙarin mikewa dan tayiwa kanta alkwarin ba zata sake shiga lamarinsa ba matukar ba rashin mutunci yayi mata ba ,hanyar step ta nufa yabi bayanta da harara dan baya son abinda zai haɗa shi da yarinyar .....
bangaren su meenal da jiddah da sa'ada zahra suna tsaye kowa wacce tana faɗin albarkacin bakinta akan ummita da abinda ya faru ,wasu suga laifin ummita yayinda wasu suga laifin ma'aruf ,yazo zai wuce su ,suka gaishe shi ,babu wacce ya amsawa acikinsu har ya isa makeken parlourn Abba .
Guri ya samu ya zauna a gefen abba tare da risinawa "ina yi Abba "
Abba dake kan kujera sanye idanunsa cikin medical glass tana rike da jarida yace "Lafiya lau ma'aruf ya kake fatan kana lafiya?
"Lafiya Abba "
"Kuna nan dai kuna shirin soma zuwa office Kou?
"Inshaallahu Abba ni kusan na matsu mu soma fita zaman ya dameni wallahi "
Abba yayi murmushin jin dadi "shi yasa kake qara shiga raina saboda himmarka , Allah yayiwa rayuwa albarka "ameen ya amsa "Abba ya mike "bari naje na sake ganin yanayin jikin mamana yinin yau duk bata ji dadi ba, har likita yazo ya min dubata ,mikewa yayi a daidai lokacin da wayarsa tayi qara bai ɗauka ba saboda suna tare da abba ,tare suka fito , shi ya nufi hanyar fita waje ,shi kuma Abba ya nufi bangaren mama ..
Yana ƙoƙarin fita waje yana danna number jafar kira daya jafar ya d'auka "kaga manya inji kanana wai ina kake shigewa ne kwana biyu shiru ko gurin suhaima kake lalla'bawa ne ?
"Kaga dan iska yaushe kazo gurina da baka ganni ba bare kace gashi gashi ?
"meye labari ne ina son zamu shigo gobe tare da Sa'id inshaallahu"Allah ya kawo ku lafiya "ina waccen sarkin rigima ?
Tsaki ya ja yana canza salon maganar tare da katse kiran ,yana gama katse kiran jafar kira suhaima na shigowa, yaki ɗauka tayi kira ya kai sau biyar amman yaki ɗauka daga karshe ma ya kashe wayar gaba-daya .. ..
Washegari duk ahlin dake rayuwa a gidan kwansu da kwarkwata babu wanda bai shigo duba jikin ummita ba, hatta kakarsu jiniya da bata son ummita da mahaifiyarta sai data shigo duba lafiyarta, shi kuwa ya rayhan kamar shine yake jinyar tsabar fargaba har wata doguwar rama yayi duk wata kula wa da kula da shan maganinta shine ..
Bayan sati daya
Ummita taji sauki sosai sai dai har lokacin bata zuwa ko'ina tana kwance a parlour'n su tana kallo twist of fate , Khadeeja ta shigo, ta miko mata wata farar envelope mai shegen kyau daga ni bana kasar nigeria bane kin amsa ummita tayi ,illa binta da idanu da tayi tana kallonta "ki amsa mana kina wani kallona .
"nayi me dashi ?
"Ke akace na bawa ?
"Inji wa kenan fa ?
"idan kin buɗe zaki ga ko waye tayi shiru tana tunani ,ita kuwa Khadeeja ta ajiye mata envelope a saman cinyarta ta juya tana magana ahankali "dadina dake yangar bala'i mijin da zai aurenki yana da aiki wallahi..
ta dade zaune agurin bata san lokacin data wuce ba ..
Ahankali ta mike tsaye daga zaunen da take ta soma takawa zuwa hanyar d'akinta ta zauna a gefen gadonta tana sake juya envelope din .. kafin daga baya
a hankali ta buɗe envelope wasu takardu ne suka zuba ta d'aga greating cards din farko mai ɗauke da sakon murnar samun lafiyarta, na biyu dana uku kunshe suke da kalaman soyayya masu tsuma rai da sanyaya zuciya a kowane kasan greatig card din sunan hafiz almustapha ne a rubuce .
Tabi katunan da kallon mamaki ba wai burgeta ne basu yi ba ,mamakin nisan tafiyar da suka sha kafin su iso gareta tare da dinbin al'ajabi yadda mai sakon yasan halin da take ciki alhalin sun ɗauki tsawon shekaru batare da sunyi arba da juna ba ..
Ranar had'uwarsu ta karshe ranar yake sanar mata zai koma makaranta yayi wani cos na tsawon shekara biyu , a lokacin ne ta rokeshi da kada ya sake kawo mata ziyara arayuwarsa dan ita babu ajandar yin soyayya nan kusa asalima babu batun soyayya agabanta..
A lokacin ta fuskanci maganar datayi ta maseefar bata masa rai matuka ,domin ya juyata da mummunar fassara " nasani subai'a ni ne baki so ba wai soyayyar ce bata gabanki ba ,nasan ni ke kidina da rawana, tabbas nasan ni ne baki so kuma baki damu da halin da zan shiga ba ....
Ajiyar zuciya ta sauke alokacin da abubuwan da suka fara suke dawo mata " idan har soyayya ta zame mata dole tabbas ya rayhan yafi cancanta taso domin shine mutun na farko daya soma furta mata kalmar soyayya arayuwarta, tun lokacin da take da shekarun da basu wuce goma a duniya ba, lokacin tana aji daya a secondary..
Shi kuwa almustapha malaminta ne wanda natsuwarta da kaifin baserarta da saukin kai, su suka fara cusa kaunarta a zuciyars malam hafiz almustapha kusan a cewarsa tafi kowacce daliba fahimtar darasi da yake daukarsu history ,ya jima yana dakon soyayyarta kafin cikin dabara ya fahimtar daita take ta sanar masa ita yarinya ce bata isa aure ba ,kuma karatu zata yi cikin murmushinsa mai bugar da zuciya yace " nima ai yaro ne har yanzu subai'a , ban isa aure ba zan jiraki har zuwa lokacin da zaki girma ki gama karatunki sai muyi aure , lokacin da yayi kokarin kawo mata ziyara kuwa dakatar dashi tayi saboda gudun bacin rain ya rayhan da kuma rashin amincewa da zance ,duk da bata son ya rayhan bazata so ya ganinsa cikin damuwa ba .....
"Hafiz almustapha ta furta ahankali tana runtse kyawawan idanunta ..
Two friend's (bsbs)
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~TRUE LIFE STORY~
FREE NOVEL NOT FOR SELL
AL'QALUMAN
*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*
~DEDICATED TO~
MARYAM ALHASAN D'AN IYA
(MARYAM OBAM)
BEST FRIEND FOREVER AND EVER, AKWAI AMANA 'KAWARMU ALLAH YA BARMU TAREN TARE SON SO FI SABILILLAH 🥰🥰
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
PAGE 8
............ Tana zaune a gurin shiru hankalinta yayi nisa cikin tunanin hafiz almustapha .....
kusan minti goma ta ɗauka zaune tana nazarin katuna nan daya turo mata a matsayin tuni ga soyayyarsa .
ta rasa a wani muhalli
ya kamata ta'a ajiye lamarinsa , motsin shigowa d'akinta da'ake ƙoƙarin yi ne yasa tayi saurin dawowa haiyacinta haɗe da tattara katunan greating card din ta tura a karkashin pillow baccinta ta maida idanunta kan kofar shigowa ..
Mama ce ta shigo tana dubanta a tsanake sai dai fuskarta cike take da damuwa "yaya dai ko jikin ne naga kin dawo d'aki ?
Murmushi tayi wanda ya bayyana kyawun fuskarta sannan tace "A'a mama nifa na rigada na warke sumul, babu abinda ke damuna, sannan babu inda ke min ciwo.
Naunauyen ajiyar zuciya mama ta sauke ahankali "har na ji sanyi a cikin zuciyata dan bana son ciwon kan nan naki mai naci tsiya ...
"mama kenan kina nuna kamar kina sona alhalin ni nasan ba haka bane , "Allah ko saboda bana bin bayan karya akan gaskiya ba ?
Ni tashi kije ga rayhan can yana jiranki a parlour'n , ummita ta mike daga zaunen da take tana yatsina fuska "kai nifa na soma gajiya da nacin nan nasa .
"lallai ummita wuyanki ya isa yanka rayhan din kike cewa haka ?
" mutumin daya damu dake ya damu da lafiyarki ,rayuwarsa ce kawai ba zai iya baki ba ,ke ko bayan raina nasan ba zaki yi kukan maraici ba matukar rayhan kika aura..... matsalar dai uwarsa, fitinarta nake tsoro bancin haka ni kaina mai tsayawa rayhan ce, ai duk mai son naka ya gama maka komai a rayuwa .
Ummita ta ta'be baki "ni kuma Kinga bana kawo ummansa a raina, ko dan ɗan nata baya cikin zuciyata ne ban sani ba.. "ke rufe min baki kullun maganar kenan ba'a miki ba , naga ranar da zaki ce ga wanda zuciyarki take so, ki dai tsaya kallon ruwa ....
tun kina samun masu sonki har kizo ki rasa .
"haba mama karki min baki mana ke fa mahaifiya ce, idan kina furta haka komai zai iya faruwa dani fa ,"ba baki bane ummita ni kaina nafi son kiyi aure da Karachi shekarunki..
"Ni mama wani aure zanyi yanzu nida nake son na cigaba da karatuna "ni dai nafi son kiyi aureki yanzu saboda .. ..
"na haifa miki jikoki tun kina raye ba ?
Tayi hanzarin katseta ta hanyar fadar haka tana murmushin tsokanar mahaifiyarta "wallahi zan murd'e wannan bakin rashin kunya ...
Ummita ta matso sosai da bakinta kusa da mama "to ga bakin ki murd'e... mama ta kamota da niyyar murd'e bakin aiko ummita ta rungumeta tsam ajikinta suka zauna a gefen gado suna murmushi tare da fuskantar juna "ummita ..
mama ta kira sunanta a tsanake "na'am mamana ,duniyata,
farincikina "ki dinga hakuri da rayuwa ummita ,ki dinga danne abinda baki so a cikin zuciyarki, banason yadda kuke yi da ma'aruf, sanin kanki ne bazan tsani ma'aruf saboda ke ba ,kin tashi kin buɗe idanunki kin ganshi a d'akin nan muna rayuwa ....
" duk abinda zai miki kiyi hakuri ki ɗauka tamkar nice nayi miki , ni nasan haka nan ma'aruf ba zai tsaneki ba ,akwai dalili da yasa ya tsaneki .
"me ye shi mama ?
"Me ye dalilin tsanarsa gareni ?
"Nima ban sani ba sannan bansan dalili ba amman da zaki canja ummita da zaku dinga shiri dashi "babu wani dalilin tsanar dake tsakaninmu , ni sam bana buƙatar shiri dashi a rayuwata , gara kowa yayi lamarinsa kawai ,ta fad'i haka tana mikewa mama ta riko hannunta cikin nata ta sake kallon mama taga har lokacin ita take kallo tana murmushi wanda tasan na dole ne dan ƙoƙarin shawo kanta "a lokacin da ban samu haihuwarki a rayuwata ba, na shiga kuncin rayuwa da takurawar uwar miji ,wanda har lokacin dana haifeki kika girma wannan tsanar tana nan ba taje ko'ina ba, a lokacin ma'aruf shine .."
Mama dan Allah ki bar zancesa haka wallahi yana sani jin fad'uwar gaba tare da haddasa min mummunar ciwon kai mai tsanani,ko ba ma haka ba tarayyarmu dashi risky ne gaskiya ta k'arasa maganar tana zare hannunta cikin na mama ...
Mama ta girgiza kai kawai tana jin babu dadi a ranta ,ita kuma ummita ta langwa'be kanta gefe tamkar abar tausayi
"Shikenan jeki Allah yayiwa rayuwarki albarka ..."ameen mamana na gode, Allah ya rayamu tare kiga ya'ya na ....
"Ameen mama ta furta a kasan ranta tana lumshe ido, ita kaɗai tasan yadda take jin bakinciki rashin jituwar Ma'aruf da ummita, Allah ya sani tana matukar kaunarsa bata jin akwai abinda zai sa taji ta tsaneshi .....
Cike da sanyi jiki take saukowa tana taka step a hankali har ta iso garesa idanunshi na kanta ya kasa ɗauke idanunshi akanta ,wani sanyayyen dadi ne ya mamaye zuciyarsa ganinta kaɗai yana sanyashi jin farinciki mara misaltuwa ,har ta zauna nesa kaɗan dashi bai dauke idanunshi akanta ba "ina yini ya rayhan ?
Matsowa yayi sosai tamkar zai shige jikinta yace "Lafiya lau my princess me kike yi a sama tun d'azu nake zaman jiran gimbiya?
"Nothing kawai tace atakaice tana cizan lip's dinta na kasa, ya sauke naunauyen ajiyar zuciya sannan yace " my princess lokacin aurenmu ya kusa fa tunda aiki ya kankama ...
"dawa kenan lokacin auren naku yayi kusa ?
A matukar firgice qirjinshi na dokawa yace "wace irin magana ce wannan? dake mana, da zaki min wata irin tambaya?
Ta sauke numfashi da ajiyar zuciya a tare "gaskiya ni ya rayhan ba yanzu zanyi aure ba tukuna ,kai aure ma sai yadda hali yayi ......
yayi shiru yana Kallonta da tsantsar mamaki a saman fuskarshi yayinda ilahirin jikinsa ya ɗauki kyarma ,sake matsowa yayi sosai ya kamo hannayenta duka biyu cikin nasa yana cigaba da kallonta tana murmushin yake ...
"Haba me yasa zaki min haka ummita,bayan kinsa yadda nake sonki arayuwata ?
yayi maganar yana matse hannunta gam cikin nashi , runtse idanunta tayi saboda rad'ad'in data ji ya ratsa tafukan hannunta "wayyo hannuna ya rayhan "yayi saurin sakar mata hannu ya dafe kanshi da hannunsa ɗaya , can kuma ya tsura mata ido, yayi mata kallon second biyu sannan yace "zan jiraki har sanda zaki gama karatunki ,bazan takuraki ba har sai idan kece kika fahimtar dani ....
Still shiru tayi taki cewa komai ,ganin tayi shiru taki cewa komai yasa ya d'aura kanshi a gefen kafad'arta ,tana jin yadda zuciyarsa ke dokawa da karfin gaske...
"Subai'a shirunki na nufin abubuwa dayawa gareni ,zai fi dacewa ki buɗe bakinki ki min magana ,"zaki aure ni na jiraki har ki gama karatunki ko kuma na qara gaba ko Allah zai had'ani da wacce zata so ni?yayi maganar kamar zai yi kuka ..
Yanayin yadda yayi maganar yasa jikinta yin sanyi ,hankalinta ya tsananta tashi, zuciyarta ta cika da tausanyinsa , tabbass a soyayya idan akwai wanda ya dace taso kuma tayi rayuwa dashi to shine .....
Runtse idanunta tayi ,sai ga wasu tsiraran hawayen sun gangaro daga cikin idanunta , tausanyinsa yayi mugun kamata sosai , sam bata jin sonsa acikin zuciyarta ,bata jin ko tana sonshi zata iya aurensa ,yafi cancatar ta yakice sonshi ko dan tsanar da mahaifiyarsa take wa mahaifiyarta ......
Can kasan makoshinsa ya sake cewa "zaki aure ni subai'a ?
" ki taimaka ki faɗa min abinda ke zuciyarki wallahi muddin na rasaki mutuwa zanyi, zan mutu subai'a ,idan na mutu karkiyi kukan mutuwata dan kice sila ...
daga yau zan sakawa raina takaitacciyar rayuwar da zanyi tun da baki so na ...
Cike da sanyi murya tace "ka daina cewa bana sonka ya rayhan ,kai fa d'an'uwana ne na jini, ta ya ma zance bana sonka ?
"da gaske subai'a kina sona kuma zaki aureni ?
Yayi maganar hawaye na gangaro masa,dan Allah kice zaki aureni ko ruhina zai samu salama "I will think about it ya rayhan , ka bani lokaci dan yanzu I have no idea to say anything . .......
Ta fad'i haka zuciyarta na wani irin tsalle tamkar zata fasa kirjinta ...
Bai san sanda ya rungumeta ajikinsa yana murna yana shafa bayanta, yana zuba sambatu iri iri "kiyi tunani mai kyau akaina , Allah yasa zuciyarki ta amince dani amatsayin abokin rayuwarta ,suna cikin wannan halin ne ya ma'aruf ya buɗe kofar parlour'n ya shigo idanunsa ya sauka akansu , ya tsaya turuss yana kallonsu makale da juna ga rayhan na kuka yana rokonta ta so shi ..
wani irin dogon
tsakin ya ja wanda yasa take suka dawo da hankalinsu bakin kofar da yake tsaye ,take ummita ta soma ƙoƙarin ya rayhan ya sakar mata jiki amman yaki .
"Allah ya shiryeka rayhan ,yanzu daman wannan iskanci kukeyi? "amman dai kunyi hasarar rayuwa
"Yanzu wannan ce irin taku kalar soyayyar ?
"Idan baka ji kunyar yin irin wannan kazamar soyayyar a part din mama ba ,kaji kunyar aikata hakan a matsayinka na suruki ga muhalin ,ka wani zo ka tasa yarinya qarama gaba kana kuka saboda baka san ci....
"Dakata malam babu ruwanka da shiga lamarin mata da miji, ina ma ruwanka da kuka na ?
"Idonka ko nawa da zaka dinga gayawa mutane son ranka kamar kai da kaninka ?
" idan kaji haushi kai ma kaje kayiwa taka ......
Jikin ummita na rawa tayi ta ƙoƙarin zame wa daga jikin ya rayhan dan wata irin azaɓaɓɓiya kunya ce ta kamata a lokacin kasancewar wannan shine karo na farko da jikin wani namiji ya rabi nata irin haka "aikin banza aikin wofi kawai ,ni ina naga wannan stupid time din yaja tsaki tare da juyawa zuciyarsa na tafarfasa ya nufi d'akinsa .. ..
Hannuwansa duka yasa ya kamo fuskarta dashi yana kallon cikin kwayar idanunta , ban da godiya babu abinda ya rayhan ke yiwa ummita ita kuma tana kuka "ki daina kuka ummita ni ina sonki koda kuwa bakya sona ,zan rayu dake muddin rai mutuwa ce kawai zata rabani dake ,zan koyar dake yadda zaki soni muddin muna tare ,zanyi komai dan ki soni zan zamo tamkar bawanki ....
Mikewa tayi jikinta na rawa ta nufi hanyar d'akinta tana kuka har da shesheka "me yasa na amince masa da zanyi tunani akansa alhalin bana sonsa ?
"why why subai'a me yasa kika yi haka ?"kamata yayi ki fahimtar dashi matsayinsa ba wai ki daurawa kanki nauyi ba ..
Ta dade kwance tana kuka tana bleming kanta, har kusan magariba tana daki kwance a d'akinta taki saukowa kasa , shigowar mama uku tana tambayarta ko lafiya take.."Tace lafiya lau.. daren ranar ma kasa runtsawa ,yadda taga rana haka taga dare cike da tunane tunane tana assessing maganarsa ta runtse idanunta tana lissafin yadda zata goce masa batare da wata matsala ba ....
Washegari ma shigowarsu meenal da sa'ada ne yasa ta ɗan warware ta saki ranta .
******
Tun karfe tara na rana Sa'id da jafar har ma da tahir abokansa suka kawo masa ziyara kamar yadda suka sheida masa ,
hayaniyarsu ce ta cika d'akin haɗe da sautin music ,sai dai duk abinda suke ,ban da Ma'aruf dan hankalinsa baya garesu yana ga sakonnin da suhaima ke turo masa .
_slm fatan kana cikin koshin lafiya ?me nayi maka ?ka share ni ka daina daukar kirana gashi Ina kewarka habibi, ka manta da rayuwar suhaima kou? kana can kana harkokin gabanka ko ?ni ina nan ina fama da tunaninka, duk motsi duk second kana cikin raina ,duk yini yau kana makale a zuciyata na kasa samun sukuni _
Yana gama karantawa wani sakon na shigowa
_help me with happiness ma'aruf Na rasa gane kaina ka taimaka bana cikin natsuwarta ,if not zaka ganni a unguwarku_
Wannan sakon nata yasa ya gyara kwanciyarsa ya tura mata text .
_ki hutawa rayuwarki suhaima .. Cool ur maind temper and remind d good things in your life na tabbata zaki sami natsuwa ba sai kinzo inda nake ba, dan zuwanki babu abinda zai kareki dashi sai zallar damuwa, idan na samu dama zan shigo kina raina_
Sai yamma sosai su jafar suka fito wajen gidan inda suka saba zama , yayinda Ma'aruf ke cikin part dinsa yana shirya kansa cikin riga t shirt mai ruwan haske da wando baki ,turare mai sanyi dadi ya ɗauka ya fesa a ilahirin jikinsa ya fito yana ƙoƙarin daura agogo a tsintsiyar hannunsa, ɗaya fito sai daya zarta dukkanin abokansa a kyau da komai ,Jafar ne yayi masa gurin zama ..
ma'aruf tare da abokansa a majalisar kofar gidansu suna shapter wanda hirar duk akan kwallo ne ,yayinda a hankali su ummita suka sanyo kai suna fuskantar get din gidansu dawowarsu kenan daga makaranta yamma, kowace sanye take da uniform din mahad ,tunda suka dosu idanun Sa'id ke kan ummita gaba-daya ya bar abinda yake ya tattara natsuwarsa kacokan akanta har suka qaraso daf dasu , dukkaninsu babu wacce bata yi gaisuwa ba saɓanin ummita da ko kallon inda suke batayi ba, ta ɗauke kanta daga jafar har Sa'id da tahir ita suka bi da kallo a natse take takunta kamar koda yaushe wanda rashin kibarta ne ke sake bata damar rausaya jikinta .....
har lokacin muhd Sa'id gaba-daya ya tattara hankalinsa akanta yana binta da wani mayataccen kallo kamar tsohon maye....jin duk sunyi dip a hankali ma'aruf ya maida hankalinsa kansu ,gani yayi muhd Sa'id ya shagalar ga kallon ummita ,da saurin ya ta'ba kafarsa muryarsa can kasa tamkar ta me koyan magana yace "kai meye haka ka wani zama kamar wawa ?
Firgigib muhd Sa'id yayi saurin dawo hankalinsa yana shafa sumar kanshi sannan ya sauke ajiyar zuciya "gaskiya yarinyar nan masha Allah ,Allah yayi halitta,duk sanda zan ganta gaba-daya sai na rasa kuzarina da natsuwata ma'aruf ya ta'be baki yana dubansa a kaikauce tamkar bai ji abinda yace ba , jafar yace "ummita ko ?
Muhd Sa'id ya lumshe masa ido alamun "eh "
"Ai gaskiya yarinyar tayi sai ka fara neman fada a gurin yayanta ..
Ma'aruf yayi shiru yayi tamkar ba dashi suke ba "aboki kaji abinda jafar yace ka taimaka ka....
"Dan Allah dan Annabi ban son shirmen banza anan wannan yarinyar ma ka cireta aranka dan rayhan ne yake sonta ,ko ma ba haka ba wallahil azim ban saka bakina ko mutuwa zakayi sai da ka mutu.......
Jafar ya kwashe da wata uwar dariya "ai nasani... "nima wallahi tsokana ce kawai , kai Sa'id idan har da gaske kana sonta ka nemi Sa'a agurin Allah sannan ka tunkareta ba tsoro , Sa'a ce soyayya sai kaga kayi nasara akanta , maganar ummita suka cigaba da yi, hakan yasa ran ma'aruf ya dinga ɓaci zuciyarsa ta cure guri daya ya rasa abinda ke damunsa ....
tsam ya mike a cikinsu ya soma takawa a gefen titin unguwarsu hannanuwa duka zube cikin aljihunsa wandonsa, bayansa suka bi da kallo cike da mamaki a hankali jafar ya biyosa "ya zaka barmu zaune ?"dan Allah ka daina nuna zallar qiyayyar yarinyar nan agaban kowa ko babu komai jininka ce ita dole idan an tsaga jinin ummita aga naka haka kaima "stop telling me this nonsense i don't want hear anything from you just go ......
"Ka barni karka cigaba da bina bana son damuwa cak Jafar ya tsaya yana dubansa ,shi kuma ya cigaba da takawa ko ina zashi oho jafar ya furta haka a ranshi ...
********
Da misalin ƙarfe takwas na washegarin ranar ummita tana zaune a parlour'n ita da sa'ada tana yiwa Ahmed dan big sister lesson kasancewar yazo musu hutu ,saifullahi kanin ya rayhan ya shigo parlour'n a guje wanda bai wuce shekara bakwai ba yana haki "aunty ummita wai kizo kin yi bako..
daga mama har ita ummita suka bishi da kallo ummita ce tayi karfin halin cewa " waye bakon ?
"Wani mai kyau ne bansan shi ba , ummita ta kalli mama wacce daman ita take kallo "kaje kace masa bana nan..
"dan Allah kinje mana baki san ko waye ba inji cewar sa'ada "karki 'bata bakinki gurin cewa naje dan babu inda zani kin sani .......
"kinga Malama maza dan Allah ki tashi kije mama ta faɗa tana harararta ummita tayi shiru kuma taki mikewa "ba da ke nake magana ba kina jin
Mutane wallahi ki yi ahankali da ...
Da sauri ummita ta mike tun kafin mama ta sake furta wani abu ta fito saifullahi na biye daita .....
Hannunta rike dana saifullahi suka nufo harabar gidan kamshi turarensa mai sanyi ya ziyarci hancinta, wadataccen hasken fitilun daya Wadaci harabar gidan shi ya hasko mata farar luxus dinsa dake parke da alamar bakon ne mammakinta ,domin matashin ne jingi a jiki motar ya rungume hannunsa sam bata gane ko waye ba ,bata son yawon samari ba dan abbanta baya so ba, sai dan raayinta ne rashin son kulasu ...
Naunauyen ajiyar zuciya ta sauke lokacin da idanunta gane ko waye tsaye tun daga sama har ƙasa take kare masa kallo
Takalmin karfashi baki ne wuluk sai shadda jikinsa fara sol agogon dake d'aure a hannunsa yafi komai daukar hankalinta yadda yake kyalli kiyasaninta ya tafi ne akan diomond ko gold ne, fari ne tasss dogo yana da hanci mai kyau a fuskarshi, bakinsa wawakeke , kallo daya tayi masa ta tabbatar ilimi da natsuwa haɗe da jin dadi sun gama ratsashi fuskarta babu yabo babu fallasa ta isa inda yake ,fuskarshi kunshe da murmushi shima ya nufota "Barka da fitowa ranki ya dade muryarta aciki tace ",Barka da zuwa ya hanya ?
"Lafiya lau gimbiya ya kamo hannun saifullahi "abokina yaya sunanka ?
Yaron ya rusunawa ya cire glass din idanunshi yace abbanmu yace "sunana saifullahi ,yace aunty ummita ta daina ce min saif kaima idan kace saif sai na faɗawa Abba ,muhd Sa'id yayi murmushin jin dadi "karka damu ni ma saifullahi zance maka kaji ,kawo glass din na saka maka naga ka kasa sakawa ..
Da sauri ummita tace "no karka saka masa ",kai aunty ki bari a saka min bayan kinsa ina so "maza cireshi ko na mareka saif me yasa baka jin magana ?
"ayi masa hakuri aunty kar amaresa yaro ne bai san komai ba tukuna yaja saifullahi jikinsa "yi hakuri abokina zan siyo maka dan karami yanzu ga na Sweet Kai da sauran yan'uwanka "sababbin kudi masu yawa ya mika masa ai kuwa saifullahi yayi cikin gida da gudu yana murna suka bishi da kallo ya saki wani kyakkyawan murmushi daya kawata fuskarshi ", Hajiya subai'a ya gari ya jin dadi?
Daure fuska tayi sosai tace "alhamdullahi ya zauna akan motarsa yana fuskantata "nasan zakiyi mamakin jin na kira sunanki alhalin ke baki Sanni ba ,amman idan kika kwatanta da kalmar malam bahaushe yace mai son d'an tsuntsu ......
Yayi shiru yaki garasawa yana Kallonta ta ɗauke kanta gefe tare da furta "amman dai da zaka min karin haske akan abinda yasa ka kirani zai fi ko ..?
Ya gyara zama "amman dai kinsa karin maganar nan da'ake cewa soyayya gamon jini ni kam na dade ina ji sai dai ban amincewa ba sai a yammacin jiya na dada tabbatarwa kaina jiya nazo kun wuceni zaune tare da yayanki ma'aruf gaba-daya kika ta fi da imanina na kasa fahimtar a wani hali nake dole na maida hankalina zuwa ga neman alfarma agurin yayanki ya ban wahala dan cewa yayi kar damu kaina akaina akwai wanda ke sonki , ba wai yau ne karo na farko dana taɓa ganinki a gidan nan ba , duk zuwa sai na ganki amman sam ke baki kallon inda nake asalima wani bangare kike kallo, ki taimkeni karki ga ina surutu kiji haushina ba laifina bane laifi zuciyata ce da tace subai'a kawai take so, atakaice dai na kamu da matsanancin soyayyarki mai girma a zuciyata yadda har nake jin ba zan iya cigaba da rayuwa ba matukar babu ke sai dai ina neman alfarma amincewar ki ki so ni koda cikin chokali ne ..
Ta ɗan tsaya tana kallona ina assessing maganarsa cikin zuciyarta tace" kai wannan mutumin ba dai surutu ba ,shima kallonta yake fuskarsa shimfide da murmushi ta ɗauke kanta gefe tana jin yadda zuciyarta ke dokawa saboda irin kallon da yake jifanta dashi
Two friend's (bsbs)
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~TRUE LIFE STORY~
FREE NOVEL NOT FOR SELL
AL'QALUMAN
*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*
~DEDICATED TO~
MAIMUNA MATAR ABDULLAHI
BEST FRIEND FOREVER AND EVER, AKWAI AMANA 'KAWARMU ALLAH YA BARMU TAREN TARE SON SO FI SABILILLAH 🥰🥰
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
PAGE 9
..........a qalla sun ɗauki sama da minti goma a tsaye bai sake yunkurin furta mata komai ba , illa kwayar idanunshi dake yawo a sansar jikinta wanda hakan ke sake harzuka zuciyarta, gaba-daya ta rasa hanyar da zata bi domin kufce masa , sosai ƙwaƙwalwarta ta shiga tunanin neman mafuta , dan dole tasan abun yi tun kafin ya qarar mata da ruwan jiki da waɗan nan mugayen idanuwan nashi masu bugar mata da zuciyata , bugu da qari bata son wan can kinibabben ya fito yayi mata shishigi , a hankali ta kamo lip's dinta na kasa ta soma ciccizawa ba tare da ta kalli inda yake zaune ba ...
Shi kuwa zuba mata idanunshi yayi sosai yana jin wani zallar farinciki mara misaltuwa na ratsa ko wani shashi na gangar jikinsa , ji yake tamkar ya sureta ya gudu gidansa daita so that daga baya an daura musu aure ...
"Kinyi shiru subai'a kin ki cewa komai, kin barni ni kaɗai ina ta faman zuba kamar ruwa ,a ranta tace "ai kama fi ruwan zuba dama shiru kayi zai fiyye maka alkhairi da wannan zubar da kake ....
ya shafa gaban goshinsa "shikenan tun da ba zaki yi magana ba a hakan ma na gode da lokacin da kika bani ,da farko dai subai'a sunana muhd Sa'id idris, mu huɗu ne a gurin mahaifinmu wanda ya kasance ɗan
Beru de change , nayi karatuna daga primary school zuwa jami'a, da farko dai nayi irin business din mahaifina kasancewar shine abinda na taso na tarar ana yi a gidanmu kafin daga baya na koma makaranta inda anan muka haɗu da yayanki mar'shub a halin yanzu dai nafi karfi a harka canji saboda yanayin yadda ƙasar tamu take , ban taɓa aure ba sannan bani da budurwa sai yanzu zuciyata ta kamu da matsanancin soyayayarki , wannan shine ta'kaiccen tarihina subai'a ina fatan za'a amshi bukatata mu dunkule mu zama abu ɗaya ....
Still dai shiru tayi masa tana wasa da yatsun hannunta , sai da suka sake kwasar minti goma kan ummita na kasa batare da tace masa komai ba , shi kuma yana aikin kallonta ko kifta ido baya son yi , komai nata yayi masa babu makusa ajikinta idan Allah ya taimake shi ya aureta zai ji dadin rayuwarsa da ita , yayinda ita kuwa ummita tunanin kalma ɗaya data dace ta faɗa masa wanda zasu rabu lafiya take , dan har ga Allah sam bai burgeta da komai ba asalima haushi yake bata .
tun daga kyan shi, kwaliyarsa , zuwa tsararrun takalmansa, kamshin turarensa ya ɗan bata sha'awa , abu uku ne kawai yasa taji a ranta ba zata iya sauraron kalaman soyayyarsa ba , ko bashi wani muhimmin abinda yake so daga gareta daidai da cikin cokali ba taji zata kaunace shi a cikin zuciyarta ba kasancewarsa abokin ma'aruf .....
"mutumin data fi tsana a duniya ,mutumin da take jin har ta koma ga mahalincinta ba zata taɓa barin wata mu'amula tashi ga tsakaninsu ba , mutumin daya tsaneta ya kuma tabbatarwa duniya da haka , ai ko ta rasa wanda zata so ba zata so Muhd Sa'id ba har abada uwa uba aikinsa daya ambata a yanzu shine mafi munin Sana'r data fi tsana arayuwarta , yayinda mafi yawa daga cikin yammata jahar Lagos suka fi bukatar auren 'yan canji saɓanin ita da ko burgeta basa yi , gaba-daya atsarinta bata da ra'ayin auren mai sana'ar canji ,sai kuma lura da tayi da yanayin tsarin maganarsa wanda sam ba taji abinda ya burgeta acikin maganganunsa ba , ya cika surutun tsiya kamar aku turu , yana magana bakinsa na yauki kamar ana kad'a miyar kubewa ....
"subai'a ya sake kira sunanta muryarsa a kasalance kamar zai yi mata kuka "ki taimaka kice min wani abu mana ko zan ji dadi ..
"baki ji yadda zuciyata ke cike da matsanancin tsoro da firgicin jin abinda ke kunshe a cikin zuciyarki ba " duk da ina cike da fargaba zan so naji wani abu daga bakinki ,ina jin tsoro subai'a gaba-daya yanayinki ya firgitani har cikin zuciyata nake jin komai ..
ta d'ago kanta a hankali murmushin maganarsa na ƙoƙarin subce mata akan fuskarta amman tayi saurin dannewa , sosai tayi ƙoƙarin boye sirrin zuciyarta dan su rabu lafiya ..
Shima murmushi yayi wanda daga ni na karfin hali ne " kin yi shiru dogon lokaci tunanin me kike yi subai'a ?
Muryarta a matukar sanyaye tace "ina tunanin kalma ɗaya da zan sanar maka ta gaskiya sai dai na rasa , amman zan so ka hakura dani ka nemi wata ....
"akan wani dalili subai'a ?
Tayi shiru taki cewa komai "dan Allah karki min haka na rigada na gama ruftawa akan 'kaunarki bazan iya son wata ba , kiyi hakuri kiyi tunani akaina mana ,har ga Allah. ina sonki kuma aurenki nake da buri yi " "shikenan naji zanyi tunani ....
Wani had'ad'd'en murmushi ya sakar mata kamar wanda aka yiwa bushara da gidan aljanna ,"na gode !na gode !! subai'a zan baki zuwa jibi idan kuma sun miki kaɗan na qara kimi " sunyi Allah ya kai mu "na gode sosai zan so ki sanar dani makarantar da kike yi . runtse fararen idanunta tayi saboda ya kusan kaita makura da surutu da kyar ta buɗe baki tace "a halin yanzu zan iya cewa bana karatu kasancewar mun zana jarabawar wannan shekarar amman zan cigaba da zarar sakamakon ya fito..
"cigaba fa kika ce auren fa sai yaushe subai'a ?
zaro idanun da yayi a firgice da maganarta da sauri , yasa ta ta'be baki tare da cewa "za'a yi idan lokaci yayi "kowane lokaci a cikin lokacinsa kike tunda aure baya hana karatu haka karatu baya hana aure ..
"Gashi ni kuma bana son haɗa abu biyu a lokaci ɗaya "shikenan Allah ya nuna mana lokacin ,Allah yasa dani za'a yi " Allah ya kiyaye ya tsareni da mugun abu ta faɗa acikin ranta ,"ba kice ameen ba subai'a "ikon Allah ko kai ka rada min sunan nan iyakar kiran da zaka min kenan ,me zai hana ka kirani da sunan da kowa ke kirana da dashi ...
tayi maganar tana shan kamshi tare da hura hanci ..
"To to shikenan na daina zan kiraki da duk wanda kike so, ko wani special name kike bukata daga gareni an ready for it "bare ma bana bukata tayi maganar atakaice.
murmushi ya sake yi "shikenan gimbiya bari na kyale ki haka nasan kin gaji sosai ya mika hannu gaban motarsa ya dauko envelope fari ya dawo gabanta ya tsaya "ga wannan kya sha ice cream , ta makale hannunta taki amsa ,shi kuwa yaki janye hannunsa ya tsareta da idanunshi gaba-daya ya makance akanta , a sanyaye tace "bana bukatar haka na gode "haba kyautar soyayya ce fa menene abun kin amsa ,nima fa wata rana zan fanshe dan ko tunanina akayi acikin kwana ɗaya na gode bare aka haɗa da mafarkina ....
Ta sake haɗe fuskarta sosai tamkar wacce aka aikowa da sakon mutuwa ,iya gaskiya ta gaji dashi , shi da kanshi ya fuskanci haka, "subai .....amm ummita zan wuce ba dan na gaji da ganinki ba sai dan nasan kina buƙatar hutu na gode sosai da lokacinki da kika bani sai jibi idan Allah ya kai mu ..
Taji dadi sosai da zai tafi a ranta "haba mutun kamar aku bai gajiya da magana "Allah ya bamu alkhairi " ko na rakaki zuwa kofar shiga cikin gida ..?
Ta d'ago da niyyar cewa a'a idanunta ya sauka akan ma'aruf , sanye cikin riga mai ruwan zuma da wando baki , kunnenshi makale da waya yana magana a hankali idanuwansu ya tsarke cikin juna ,ganin su yasa ya kasa cigaba da wayar da yake, yayi sororo yana kallonsu , kallo ɗaya tayi masa ta ɗauke idanunta akanshi tana jan tsarki a ranta , tayi tamkar bata ganshi ba , shi kuwa kasa cigaba da wayar da yake yayi ya tsura musu ido ko kiftawa ya kasa yi , ba wai mamakin ganinsu tare yake ba , a'a karfin halin muhd Sa'id din ya gani alhalin ya sheida masa wanda ke da muradin aurenta ,yanzu idan rayhan ya gansu tare bazai taba yarda babu hannunsa a ciki ba asalima haushinsa zai ji .....
Ɗan karamin tsaki ummita taja a cikin ranta dan ita kanta bata so ya fito ya ganta tare da muhd Sa'id ba , sai dai babu yadda zatayi ,a hankali ya ma'aruf ya
tsuke bakinsa tare da ɗauke idanunshi akansu zuwa wani bangare ya cigaba da wayarsa ..
Ganin ya ma'aruf yasa ta sake tamke fuskarta tamau dan kar yaji dadin a cikin ransa ,dan tasan dole zai yi farinciki ganin ta sausari daya daga cikin abokinsa dan burinsa kenan ya ganta tsaye da kowaye a matsayin tana zance , shi kansa muhd Sa'id yayi matukar farinciki da ganin da ma'aruf din yayi musu tare.
ya ma'aruf yana gurin tsaye yana waya sukayi bankwana ,lokacin ne wasu friend's dinsa suka fito daga bangarensa suna magana dashi suna shirin shiga mota har shi, amman gaba-daya hankalinsa yana kan Muhd Sa'id da ummita dake tsaye ...
"Kamar muhd Sa'id idanuna suke gani Kou ?
Inji cewar alkasim "shine mana me nene son yarinyar yake ko akwai wani abu ne ?
"Babu komai wallahi mamaki dai nayi dan ban taɓa ganin yarinyar tsaye tare da wani namiji ba, gsky zanyi farinciki matukar ya samu karɓuwa a gurinta, dan gaskiya ummita tayi ,irin matan da'ake yayi ce ,matar fita wacce za'a a jiye a gaban mota ce ,duk wanda yayi sa'ar mallakarta ya more..
"babu ma wanda zai sameta sai abokina inshaallahu dashi za'a yi , zan bawa abokina shawara tunda har yayi nasarar da aka tsaya dashi ya kula sosai da duk wani motsinta saboda yarinya ce da wani zai iya yin wuf daita , kai acikin gidan nan ma akwai masu hari ,dan haka zan faɗa masa ya nuna mata so iya so da kulawa fiyye da kansa sannan ya nace da iyakacin karfinshi duk wuya duk runtsi ya K'arasa maganar yana ƙoƙarin kunna mota ...
"Wannan gaskiya ne ,ni kaina nayi mamakin kula shi da tayi "ba abun mamaki bane alkasim ikon Allah yafi gaban haka , sai kaga idan rabonshi ce komai ya daidaita a tsakaninsu,"ai dana san za'a iya kula kamar muhd Sa'id ,da tuni nima na sanyo kai ,dan ko ni yarinyar tayi min fuska ne ban samu ba shiyasa na tsaya matsayina ," wannan kuma bahagon zance ne ,karka zowa mutane da karys ka maida miyonka kawai dan abokinka ya rigaka..
duk maganar da suke ma'aruf bai yi ƙoƙarin cewa komai ba, illa maida hankalinsa da yayi akan suhaima dake zuba masa shagwa'ba ta cikin waya..
Ahankali ummita ta juya ta soma tafiya taji sautin muryar muhd Sa'id " dan Allah ki bari na rakaki mana Wallahi ban gaji da ganin wannan kyakkyawar fuskartaki ba karaf maganarsa ta shiga cikin kunnuwan ma'aruf ......
Ya ɗan yi shiru yaji amsar da zata bashi ,
ba tare data juyo ba tace "a'a na gode sai da safe ,tsayawa muhd Sa'id yayi yana Kallon yadda take d'aga kafafunta tamkar bata son takawa aranshi yace , " wannan yarinyar ba dai yanga ba ..yana tsaye har sai daya daina hangota sannan yayi murmushi ya qarasa inda su ma'aruf suke,ya mika musu hannu har ma'aruf suka gaisa , "abokina daga yau fa sunanka mai nasara dan da alamun kasamu karɓuwa inji cewar jafar "ina fa na samu karɓuwa sai zuwa jibi zan san matsayina nasara ko akasin haka ," Allah ya daura ka akanta ai da alamun zakayi nasara tunda har an saurareka ,"Allah yasa jafar ,kaga da yadda na samu ma ta min magana ,wannan yarinyar ba dai yanga ba, komai nata sai tayi yanga, maganarta kallonta kai komai ma nata ,har wani gumin wahala na haɗa tsabar firgici gaba-daya suka kwashe da dariya ban da ma'aruf " abokina ai kayi jarumta daman irin waɗan nan mata firgita mata suke nan dai suka cigaba da hirar ummita ....
kai tsaye ta zarce ɓangaren su gaba-daya mutanen dake zaune a parlour'n sun tattara hankalinsu akan kallo ,sai data yi sallama sau biyu sannan mama ta amsa mata ,ta zauna kusa da kujerar da maman take "mamana na bi umarninki naje na dawo ...."ko ke fa mamana sannu da zuwa ?Sannan ta mayar da hankalinta kan wasan da suke kallo challenge daga tashar kasar India..
Shad'aya daidai aka gama shirin gaba-daya yaran dake zaune suna kallo sun soma gyangyadi a gaban tv, ya rage daga mama sai sa'ada da ummita ,mama ta kallesu "ku tashi yaran nan suje su kwanta dare yayi kuma ku kwanta karku kasa tashi da asuba kusan gobe muna da baki , maza ummita kashe tv ki taimakawa Sa'adatu da yaran nan ...
"Tam mamana "
ummita ta K'arasa gaban tv ta kashe, sannan ta dawo ta taimakawa sa'ada tashin yaran tare da rakasu bangarensu, sannan ta dawo ta wuce d'akinta ta d'auro alwala tayi gado ta kwanta lamo tana tunanin ,"me zata cewa Muhd Sa'id idan ya dawo jibi ?
"me kuwa zaki ce masa da ya wuce baki son shi ya ƙara gaba ko zai dace...zuciyarta ta bata wannan shawara, take ta amince ,shawarar ta samu kyakkyawan mazauni a cikin ƙwaƙwalwarta , da wannan shawarar ta samu bacci yayi awon gaba daita ..
******
Washe gari
bangaren hajiya inna cike yake da jikokinta ciki kuwa har da ummita .. yaran aunty sha'awa ne suka kawo musu ziyara , sosai parlour'n ya hargitse da hayanirsu , hirar yaushe gamo suke sosai, kowacce ka kalli fuskarta kunshe take da murmushi da farinciki " ni kam ummita ina ya Ma'aruf ne ?Tunda muka zo ban sanya shi a idona ba ?
Ummita tayi mata banza kamar bata jita ba sai
Meenal ce tayi magana " ina ganin kamar ya fita "
ayya ya ma'aruf kenan akwai natsuwa wallahi ,kun san me wallahi ina addua Allah ya bani miji irinsa mai kyau da tsafta , ga fashion na ɗaukar hankali uwa uba miskilancinsa ....
ummita najin inda maganar ta dosa ta sake haɗe rai batare da ta tofa bakinta ba , Maryam tayi tsigil tace "ina ma ya ce .....
"Ina ma yace me ?
"Yarinya rufawa kanki asiri damu kanmu kafin yaji ki ya haɗa har mu yaci kaniyarmu inji cewar meenal ..
Khadeeja ta kwashe da dariya "gaya mata dai dan wallahi ba zai duba bakuntarku ba, dan haka ki canza maganarki tun wuri , ki dai fadi wani abu ban da wannan da kike shirin faɗa "
" ummita kinyi shiru ba kice komai ba "uhmmmm naji abun na kune shirme zalla ...
a ganina idan ba kaddara ba me za'a yi da wannan mugun kinibabben ?
"ni wallahi ban taɓa jin ya burgeni ba ,ku ko a kafa aka d'aura min shi wallahi kama shi zan yi na kunce na gudu uwa duniya bare inshaallahu hakan ma ba zai taɓa faruwa ba ," wani kyau ne dashi da har za ki wa kanki fatan Allah ya baki miji irinsa ?
Gaba-daya suka zaro idanu waje cike da mamakinta "eh wani kyau garesa kun wani kafe ni da idanuwa kuna kallona bayan gaskiya na faɗa ?
"Ni ban ga komai ajikinsa na kyau ba ,sam idanuna basa ganin kyaunsa idan ma yana dashi kenan "kai ummita wannan kuma karya ne kice ya ma'aruf bai da ..... "dakata maryam faɗa min abu daya mai kyau ajkinsa ?
"Bafa zaki gane ba tun da kullun kallon tsoro kike masa ,mu dai mun san yana dashi kuma dole mu yaba baiwar da Allah yayi masa " aslamiyya tayi tsigil tace ",,haba ummita meye haka ?
"wai me ya ma'aruf ya miki haka ne kika tsaneshi ?
"Dadin abun dai babu abinda zaki nuna masa sai dai ma ya nuna miki yarinya ?
Ummita ta ta'be baki "wannan kuma karyarki yarinya ,karki fad'i son zuciyarki "ba zan yi karya ba, mu ajiye maganar akwai yar tsama a tsakaninmu "me yake dashi idan ba zallar muni ba ?
' Karki sake cewa yana da muni idan bakya son shi, mu muna son shi a duk yadda yake tun da jininmu ne, ai ba haka kike wa ya usman ba ko dan shi dangin mahaifiyarki ne ?
"to an faɗa yana da muni yana da muni sai kiyi abinda zakiyi.... aslamiyya ta bude baki zata rama meenal tayi saurin toshe mata baki "dan Allah mu canza hira abar maganar yaya haka ,kema ummita plz Kar abun ya zama faɗa ......
daga ummita har aslamiyya sun shaka sosai sai hura hancin suke kafin daga baya ummita tace "usman daban kinibabbe daban bama matsayinsu daya ba dan haka kar a sake haɗa ya usaman da wani banza can mai kirar samudawa .....
Tana gama faɗar haka ta gyara zamanta tare da maida hankalinta kan amar daya shigo yanzu , cikin haka inna ta fito a dudduke daga uwar d'aga tana gyara d'aurin dankwalinta "ihun me kuke yi haka duk kun cikawa mutane kunne?
ta fad'i tana ƙoƙarin zama akan daddumarta tare da janyo wani ƙaramin gwangwani ta ciro goro ta soma gogawa ..
Meenal tayi saurin cewa "babu komai inna kawai dai hirar duniya ce, ta fad'i haka ne saboda sanin halin innar da tayi, dan tana jin akan me ake maganar sai ta maida abun bala'i karshe laifin ya koma kan ummita ..
"ke aminatuwa karki min karya fa naji an ambaci sunan babana ta karasa maganar tana watsa garin goro a bakinta "a ina inna ?
"gsky babu wanda ya kira sunan ya ma'aruf anan "ai shikenan "ke Khadeeja maza tashi kije bangaren mairo ki tambayo ko an gama ,ace har yanzu alkubus din bai yi ba gashi har yara sun fara jin yunwa, shiyasa tun safe nace aje kwakwa uku gidan hajiya rabi a siyo musu , dan kinibibi akace za'a yi"
"Kai inna me yasa kike yi haka ne ?
" mu bama jin yunwa yanzu duk sanda aka gama zamu ci "un go nan jaira na sake jin bakinki sai na cireki acikin jikokina ,ke kuma tsayuwar uwar me kike yi Khadeeja ba ai ken ki nayi ba kika tsaya min aka ?
Khadeeja ta fita tana gunguni, ta bar inna tana minta zagin mama ..
Bayan kamar minti goma saifullahi da Ahmad da Khadeeja suka shigo parlour'n hannunsu rike da manya kuloli guda uku , suka k'araso inda suka saba ajiyewa inna kular abincinta suka ajiye ,inna ta buɗe kulolin tana ta'be baki sai data kirge naman cikin miyar sannan ta soma da zubawa jikokinta na bangaren diyar macce , sai data zuba musu enough sannan ta zubawa kanta ta turawa meenal kular gabanta, ummita ta mike ta isa gaban meenal ta zauna har ta tsoma hannu inna tace "kai kai karki kuskura ki saka mata hannu kije gurin uwarki, nasan naki na can ta ajiye miki, dan kibibi shine zaki wani tsoma hannu cikin wanda na tsakurar mata"
Tsaki ummita ta ja " to wannan na ga damar ci dan haka karki takurawa rayuwata, idan kuma kikace zaki takura min bismillah sai abamu fili mu bawa hammata iska yanzu ,daman cike nake dake ..
aiko gama maganar ummita ke da wuya gaba-daya suka kwashe da dariya da ihu "kai ummita Allah barmana ke kina maganin inna wallahi ..
shi yasa nake son zuwa gidan nan ko dan chapter nan taku inji cewar maryam ....
Ammar yace "ai sai mu baku fali mu ga wanda zai yi nasara tsakanin ke da inna "kai ma kasan ko waye zai yi nasara inji cewar ummita "
"Bana son cika ba fa "kai raba ni da zance wannan tsohuwar da bata ajiye komai ba sai rikicin gangan "un go yar banza uwarki ce mai rikicin ganga bani ba .....
Two friend's (bsbs)
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~TRUE LIFE STORY~
FREE NOVEL NOT FOR SELL
AL'QALUMAN
*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*
~DEDICATED TO~
MAIMUNA MATAR ABDULLAHI
BEST FRIEND FOREVER AND EVER, AKWAI AMANA 'KAWARMU ALLAH YA BARMU TAREN TARE SON SO FI SABILILLAH 🥰🥰
WATTPAD HAUESH
PAGE 10
......Ummita ta maida hankalinta gurin cin alkubus batare da ta sake yin magana ba , parlour'n ya ɗauki shiru na wani lokaci can meenal tace " hajiya inna dan Allah man shanu baya cikin sinadarin masu karin lafiya bayan dadin abinci da yake sawa?
ta faɗa tana kallon face din hajiya inna ,ummita ta riga hajiya inna magana "amman dai alkama tana cikin abinci mai gina jiki da inganci ko inna?
Hajiya inna da ammar suka kwashe da dariya tare da fadin "ai kuwa meenal man shanu har kusan zautar da wasu yake lokacin da suke cinsa, ita kuwa alqama karfi take sawa kamar doki dan idan ba'a yi Sa'a ba sai kiga mai ci ya haɗa har da tukunya alkubus din ,ke har ma da wacce ta yi alkubus din Idan bata kauce ba..
" uhmmmm bari kuga na mike kafin ku tashi kuyi kaina gaba-daya suka sake kwashe da dariya , ai ko take ummita ta haɗe rai "ba fa santi muke ba hajiya inna da zaki fad'i haka har da wasan zagin uwa ...
"Ke ni rufe min baki daman wa yace ku na santi ?
"Ba kuyi sanyi ba tun da gashi nan ammar ya tareku dan karku fadi, take suka kalli bayansu da gefensu duk kwanuka da kofina ne ya jera musu ummita ta jefa mishi gutun kashin da yake hannunta aiko kashin ya sauka akan goshinsa ,ya saki ƙara tare da rike gurin yana juya kai "dan wulakanci ce maka akayi santi muke ?
"Kunga muguwar yarinya da mugutar tsiya irin ta gado shine kika jefa masa bkashi
a idanu salon ki nakkasa min shi , ammar miko min kashin na rama maka, ai ko ummi ta mike da gudu tayi bayan kujera dan tasan halin hajiya inna zata aikata, ta rama masa, duk da wasa take masa saboda tafi son sauran jikokinta akanta, hajiya inna tayo kanta gadan gadan zata kwad'ata mata kashin ummita tace "kai hajiya inna karki jefa min wallahi da wasa nake masa ban san zai samesa a ido ba"
"dan uwarki haka ake yin wasa a garin tsohuwarki ?
"ki ɗauki kashin da kika gama tsotsewa ki jefa masa a goshi amman kice wasa kike masa ,kinsa Allah sai na rama masa ko mutuwa zakiyi ,ummita najin haka ta nufi kofar fita , ai ko daga ammar har su meenal dariya suka kwashe dashi har da rike ciki dan shi ma wasa nake bawai kashin ya same shi a ido bane .
ummita na ƙoƙarin fita daga parlour'n ba zato ta faɗa a kirjin mutun wanda bata san ko waye yake ƙoƙarin shigowa ba , a hankali dukiyar fulaninta ya sauka akan fuskarsa sannan ya zarce zuwa faffad'an kirjinshi , wani sabon bakon alamari ne ya bakunci tsokar dake makale da kirjinsa most especia daya ji tudun brest dinta a saman qirjishi take ya ɗauke numfashi tare da runtse idanunshi da sauri, yana jin zallar takaicinta kamar ya hankad'eta daga jikinshi , tuno mama yasa ya kasa aikata hakan .
Gaba-daya ahlin dake cikin dakin babu wanda zuciyarsa bata buga ba tsabar tsoro da firgici duk suka baza idanuwansu suna jiran ganin abinda zai faru , a hankali ya soma ƙoƙarin janye jikinshi daga gareta yana sauke boyayyiyar ajiyar zuciya ..
Ita kuwa ummita Kamshin turarensa daya kaiwa hancinta farmaki ne ya an karar daita da wanda sukayi karo , lumshe fararen idanunta tayi,take gabanta ya shiga dukan uku uku hankalinta yayi mugun tashi ,a hankali ilahirin jikinta ya ɗauki kyarma... ta soma furta kalmar "inna lillahi wa inna lillahi raji'un a kasan ranta yayin kirjinta ke dokawa da karfin gaske , ya ɗan tsaya yana kallonta fuskarshi kunshe da matsanancin 'bacin rai da takaicin haɗa jikin da sukayi daita ,yana jin tamkar ya shakota ya rufeta da dukan mutuwa amman darajan mama bazai iya aikata hakan ba dan haka ya ja tsaki yana watsa mata harara,
ita kuwa jira kawai take taji saukar mari a saman kuncinta amman taji shiru ....
kamshin turarensa da takunsa yasa bugun da zuciyarki yake Karu hakan ya sake bata damar fahimtar kusantota yake dan haka ta sake runtse idanunta gam tana ɗauke numfashi tare da qamewa guri ɗaya har sanda ya zo ya wuce ta inda take tsaye sannan ta sauke naunauyen ajiyar zuciya tana buɗe idanunta a hankali.......
kallon juna suka shiga yi da su meenal yayinda kowacce a cikinsu tashiga hankalinta ta kame kanta tare da yin godiya da bai mata komai ba .
A hankali ya samu guri kusa da Hajiya inna ya zauna yana sauke numfashi ,sai dai har lokacin zuciyarsa ita yake kallo wasu wurare daban daban na bud'ewa a cikin zuciyarsa mai tattare da tsantsar tsanarta "gaskiya babana baka kyauta min ba wallahi ,ai daka naɗawa jairar yarinyar nan duka..
" wai daga .. ..."dan Allah inna banason damuwa kaina ciwo .. "kai kuma matsalarka kenan da an d'auko magana kace kanka na ciwo , bakinka jikinka duk ciwo suke mutun kamar bayahude ,kai dai wallahi matarka na da aiki ja "plz inna kaina zai cire yayi maganar yana dafa goshinsa dan yasan idan ba haka yayi ba bazata barshi ya huta da surutunta ba ..."
"tam ai shikenan nayi shiru , ku kuma kun wani zaunewa mutane kun tsaremu da idanuwa , barin ma wancan jairar mai idanu kamar na agolar nufawa, naso ya waske min ke da mari na huce takaicin abinda kika yiwa Ammar"
"ai sai kisa yanzu a waskeni da mari tunda jakarki ce ni daga wasa shima me yasa ya jera mana kwanuka ?
Jin abinda ya fito a bakin ummita yasa cikin rawar jiki meenal ta yunkura ta dafa kafad'ar aslamiyya muryata can kasa kamar zata yi kuka "aslamiyya bani da sauran gurin zama anan ,zan gudu wallahi idan kun tashi ku biyo ni tayi hanyar fita , ɗaya bayan ɗaya suka dinga tsilalewa suna barin d'akin kar zunubin ummita ya shafe su .
"shikenan Allah ya baki Sa'a ki cigaba ba dai takamarki maida wa mutane magana ba ?
"idan shi bai nada miki na jaki ba , zan biya sadam yayi miki dan banza dukan da zaki kasa tashi , kai kuma bari na kawo maka magani ka sha kaji babana, bana son wannan ciwon kan naka na gado ,ni bama ciwon kai ba a rayuwata bana son naji baka da lafiya ,da kayi ciwo gara ace nice bani da Lafiya .......
ummita ta kalleta a sukwane tana ta'be baki, "aikin banza idan kin isa ki cire masa ciwon ma gaba-daya tayi maganar a cikin ranta yayinda a fili taja tsaki tana motsi da bakinta yana jinta ya share dan yau baya jin kulata .
"Amar miko min mayafina dan Allah gashi can a bayanka " "Ammar na shirin mika mata , inna ta kwalla masa kira"ammar "na'am inna gani nan zuwa ya mike da sauri ya nufi uwar d'akan inna "kai wannan jara da yawa take , ina ma Allah zai kashe min ke na huta da jarabarki dan kinji zan moresa shine na kiransa Allah dai yasa nima ba gurguwa bace da kafafuna .. ..
Wani irin fad'uwar gaba ma'aruf yaji from know where ,amman still bai d'ago idanunshi ba, har sanda ta raɓa ta gefenshi zata ɗauki mayafin on-expecting taji anyi sama daita .....sai gashi
ta dawo kasa dummmmmmm kamar buhu ta baje a kasa tayi zaman 'yan bori a gabansa , gaba-daya gigicewa tayi tashiga wiki wiki da idanu , batasan ya aka yi hakan ta faru daita ba, sai dai ganinta tayi a saman kafafunsa bakinta ya bugu da kasa taji wani irin azaɓaɓɓen ciwo ya ratsa bakinta ,a hankali ta kai hannuta daidai bakinta zaro idanuwa tayi a matukar firgice tana kallonsa jini ta gani ......
shi kuwa tamkar ba shine mutumin da yayi kwallo daita ba, idanunshi na runtse tamkar mai yin bacci, ba shiri jikinta na rawa ta juya tana kallon uwar d'akar inna , tare da addu'ar Allah yasa inna da amar basu ga abinda ya faru ba , bare suyi mata dariya ,kuma tasan dole sai sun sanarwa kowa kodan ayi mata dariya . ...
" cikin wani yanayin na nuna ko in kula da jan aji tare da tsantsar miskilanci ya soma buɗe idanunshi a hankali , aiko yana gama budewa idanunshi suka sauka a kanta durkushe tana kallonsa wani irin zirrrrrrrr ... taji a gaba-daya illahirin jikinta har cikin tsakiyar kanta tamkar an jona mata wutar lantarki , zuciyar bala'i take son masa amman ta kasa bude bakinta ,a halin da take ciki ma koma tace zata yi magana bakinta bazai iya furta komai ba
daskarewa tayi agurin haɗe da zuba masa fararen idanu tana cigaba kallonsa kafin daga bisani ta samu kanta da d'aukewar numfashi ..
tunda take bata taɓa tsintar kanta cikin wannan yanayin mai wuyar misaltuwa ba da kasa aikata komai garesa ba , haka nan yau ta ke jin ta kasa ɗauke idanunta akanshi sannan ta kasa furta komai garesa ....
shi kanshi tsura mata idanunshi yayi masu matukar kyau da tsoratarwa yana kallon lumsamsun idanunta masu matukar haske da mamakin rashin ɗaukar mataki akan abinda yayi mata kusan minti biyu suna kallon juna kafin daga baya "ya watsa mata harara "
Take tsoron yanayin yadda yake kallonta ya mamaye zuciyarta da gangar jikinta wanda tasan wannan kallon da yake mata na gargadi ...
Amman tayi tamkar bata san abinda hakan yake nufi ba ,ganin taki mikewa bisa kafafunsa tana kallonsa cike da tsoro yasa muryarsa a kausashe yace " uwar me kike jira ,common get up from my .....
ai tun kafin ya K'arasa tayi zumbur ta mike jikinta na rawa ...amman hakan bai sa tsoronta ya fito fili ba dan tana isa daf da bakin kofar fita , ta tsaya tana watsa masa harara tare da cewa " aikin banza kawai idan mugunta abun yi ne mutun ya ci gaba, da sannu Allah zai yi mutun da kaidinshi ,
kuma ban yafe ba Allah yayi min bakar isar da bata da magani tana magana tana ƙoƙarin ficewa daga d'akin batayi taku ya kai biyu ba taji an fixgo hannuta ...
A tsorace ta saki wata razananniyar qara jikinta na ɗaukar rawa kamar mazari.....
Two friend's (bsbs)
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~TRUE LIFE STORY~
FREE NOVEL NOT FOR SELL
AL'QALUMAN
*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*
~DEDICATED TO~
MAIMUNA MATAR ABDULLAHI
BEST FRIEND FOREVER AND EVER, AKWAI AMANA 'KAWARMU ALLAH YA BARMU TAREN TARE SON SO FI SABILILLAH 🥰🥰
WATTPAD HAUESH
PAGE 11
...... ..a tsawace ya buga mata wata razananniyar tsawar data firigita zuciyarta tayi saurin kamkame shi ajikinta batare da tasan tayi hakan ba..
" rungumeshi da tayi yasa ya dinga kallonta da bayyananne tsoro a kwance saman fuskarshi take ya had'iye wani emotion daya ziyarci zuciyarsa da gangar jikinsa , fuskarshi babu walwala ya sauke naunauyen ajiyar zuciya ,kusan minti biyar tana rungume ajikinsa ,ya waiga gefen hagu da damansa bai ga alamun kowa ba ,ya ja ɗan qaramin tsaki, bai so jikinsa ya haɗu da nata ba ,yanzu idan wani ya gansu haka yace me ?
Bai ma da tabbacin duk abinda zai faɗa a yarda dashi a wannan lokacin ,bari ya hanzarta tun kafin wani ya gansu ..
Muryarsa a tsarke yace "ke kina hauka ne da zaki haɗa jikinki da nawa ,har ma da wani lefe wa ?
Yayi maganar yana bambareta ajikinshi "kin wani manne ajikina mutane yar iska banza kawai jarababbiya .....
Ta buɗe baki da niyyar magana yayi saurin daga mata
"shiiiiiiiiiii tare damke tsintsiyar hannuta cikin nashi dan sai ya azabtar daita akan Allah ya isan da tayi masa , shiru tayi tare da lumshe fararen idanunta,"kin ma rainawa kanki hankali, me zaki ce da kika wani bude wannan rubabben bakin naki da duk doyi yake ?
"Wallahi naji kince tak nan sai kinga yadda zanyi da namanki "
ta sake buɗe idanunta tana kare masa kallon tsab taga yadda yanayinsa ya sake saiyawa fiyye da dazu ,hankalinta yayi mugun tashi da rawar jiki tace "to ..ka sakar min hannu na kama gabana .
"shi kuma Allah ya isan da kika min fa?
" kina nufi ya tafi a banza ne ?
Ta daure fuska sosai ta soma ƙoƙarin cire hannunsa dake rike da nata tare da neman hanyar guduwa " ka sakar min hannu dan Allah ,kana min shishigi fa , bana son abinda kake min ,bana son kana shiga lamarina"
"Ni ne ma nake miki shishigi ,nake shiga lamarinki ,sannan baki son abinda nake miki ?
ya faɗa yana d'age mata girasa ɗaya cike da jan aji "ai kafi dan dako sanin kana min shishigi ..
muryarsa cike da miskilanci yace "waɗan banzayen samarin naki ne 'yan dako , muje nayi miki hukuncin Allah ya isan da kika min sannan ki faɗa min irin shishigin da nake miki albashi daga yau sai na daina ,dan idan akwai abinda ke 'bata min rai kuma na tsana bai wuce mu'amula dake ba ko shiga lamarinki"
"Kasan Allah to wallahi bazan koma cikin wancan d'akin ba ,duk abinda za'a yi sai dai ayi anan amman bazan komai ba"
......
yayi murmushin gefen baki wanda da gani na takaici ne sannan yace "kinsa Allah sai kin koma da kakafunki kuma har da guzirin izaya" ......
ya K'arasa maganar yana tsura mata idanu yana karantar yanayinta wanda da kyar ta sake fuskantarahi tayi masa kallon second biyu tare da sauke ajiyar zuciya, da alamun tsoro a tattare da ita ,dan kallo ɗaya yayi mata yasan dauriya ce kawai tattare da ita amman zuciyarta cike take fal da matsanancin tsoronsa ...
Ya ji dadin sosai acikin ransa sannan ya cafki bayan wuyanta yayi cikin d'akin inna da ita , yana K'arasa shiga d'akin ya wurgata a tsakiyar parlour'n ta zabura ta mike tsaye tana haki , "oya start frog jump"
da sauri ta ware fararen idanunta duka akanshi tana kallonshi a tsorace tare da nuna kirjinta da ɗan yatsanta "ni din ce zanyi tsallen kwado ?"
"Kwarai kuwa yarinya yau tsallen kwado nake da bukatar ganin kin yi ,ta haka ne kawai zan iya bambamceki da kwado ko fat lion , kinga ma idan aka ci sa'a sai sunanki ya tashi daga fat lion zuwa frog" ......
Ta zumburo masa karamin bakinta yayinda muryarya cike da shagwa'ba tace "gaskiya ba zan iya ba ...
"Karki yi kiga yadda zanyi dake yanzu ,"wallahi bazan yi ba dan ban ma iya ba,kuma ban san yadda ake yi ba" ....
ya girgiza kai kawai yana cizan lip's d'insa na kasa " ammar ....ya kwalla masa kira ,ammar dake kwance a uwar d'akin inna ya fito da sauri "gani yaya "
"ka iya tsallen kwado ai ?
ammar ya girgiza masa kai alamun ya iya, "ok Koya wa wannan mai fuskar zakin "
"an gama yaya "
Ahankali amar ya fuskanci ummita dake tsaye tana cika tana batsewa ,ya kunshe dariya dake ƙoƙarin subuce masa saboda ganin yadda ta cika bammmmm tana jira a taɓa ta fashe da kuka .. "kinga ummita haka zakiyi ya sakala hannuwansa duka ta karkashin kafafunsa ya kamo kunneshi sannan ya soma tsallen kwado , yayi kamar sau uku yana zuwa yana dawo wa sannan ya tsaya yana dubanta "tou hajiya ummita haka zakiyi ...
"Gwada mugani ko zaki iya" "......
Muryarta na rawa tace " baza'a yi ba gara kawai a harbeni gabad'aya nasan ba'a kaunata a gidan nan da dai nayi wannan abun mai azabar tsiya , ni dama ba'a danginku na fito ba" ta K'arasa maganara hawaye na gangaro mata "amar yi tafiyarka ai ka gama mai wuyar idan ta isa kar tayi" ....ya fad'i haka ya koma ya zauna akan kujera ya daura ƙafarsa daya kan daya yana jijjigawa batare daya kalli inda take ba , Ummita ta kalleshi zuciyarta na wani irin tsalle tasan tunda ya dage sai tayi dole tayi dan tasan halinsa bashi da kyau a kowane fanni kuma baya ya fiya komai kankantar mutun idan yayi masa abu sai ya rama ko ya hukunta mutun da azaba mai rad'ad'i shiyasa gaba-daya tun tasowarsa ake jin tsoronsa ita kaɗai ce a duk cikin family dinsu take ramawa da rashin nuna jin tsoronsa ,sai duk wannan mugun halin nasa Allah yayi shi da nasibi da kwarjin jama'a duk inda ya shiga sai ya tara mutane ....
Ta sauke naunauyen ajiyar zuciya
a daidai lokacin da inna ke fitowa daga uwar d'akanta hannunta rike da magani da ruwa ta miko masa "ungo ka sha ,ka daina biyewa wannan yar banzar... hawan jini kawai zata daura maka kamar yadda ta daurawa uwarta, wannan ja'irar cutar ce ta kama ka bata da arasa dadi ma zata ji yar mai mugun halin tsiya ....
"Inna ki bar magani nan naji sauki , ni doguwar magana ce kawai ban so ...
Ta zauna kusa dashi tana ajiye cup din ruwa matsalata da kai kenan ba'a maka gwaninta babansa" tayi maganar tana sake maida hankalinta kan ummita,
"ke zaman me kike wa mutane ?" maza tashi ki bar min daki na sarara"
"Ga wanda ya tsaidani nan , kice ya sallameni na kama gabana dan ni ba iya abinda ya sani zanyi ba"
... " me zaki yi masa ?"
"Wai tsallen kwado zanyi..... gashi ni kuma tunda nake a rayuwata ban taba yi ba, sai dai naga ana yi ..
ta K'arasa maganar kamar tana matso hawaye "inna ta kwashe da dariya tana tafa hannu .
" kai babana kasan ta kan sharri , wallahi har ka wanke min zuciya , bari na kawo maka dorina mai baki shida , tana tsallen kwadon kana tsallawa ja'ira"
........
"kai inna saboda kin tsane ni Kou , shine zaki kawo masa dorina har mai baki shida kamar wata diyar cikinsa ko wata jaka , wai ma inna me na tsare muku ne a gidan ke da shi"
"Baki tsare min komai ba sannan baki min laifin komai ba , laifin ki daya ne da kika zo duniya ta tsatson mairo ...
"Yadda gaba-daya uwarki bata da muhalli a cikin zuciyata, haka ne yasa kema bana jinki a cikin raina ,sai dai kiyi hakuri bazan iya haɗa soyayyar jikokina da naki ba"
idanun ummita suka sake kadawa suka cicciko da ruwan hawaye ,tana janyo numfashi da kyar ta fesarwa tana sauke ajiyar zuciya har makoshinta na lotsawa tsabar bakinciki , ma'aruf yayi shiru bai san sanda ya juya ya kalli inda ummita take ba, ya tsura mata ido yana karantar yanayinta , da kyar ta sake d'agowa ta masa kallon minti biyu ta sake sauke ajiyar zuciya ........
ya ɗauke idanunshi akanta "kiyi abinda na sakaki ki kama gabanki dan ban son ganin wannan banzar fuskartaki"
"ke kuma inna ki daina abinda kike bai da kyau , wannan tamkar sabo ne , da Ummita da sauran jikikokin ai duk abu daya ne tunda ta rigada tazo ta tsatson d'anki "a'a ma'aruf da bambamci sosai ,idan kana min irin haka zamu samu matsala da kai "
"Mun dade ba'a samu matsala dake ba ....
"Kayi shiru kar wancan yar banza taji ta ɗauka ka damu daita ne barin taji zamuyi faɗa ai dadi zata ji ,kai dai kayi shiru kawai"
..."ni dai karki sake zagin mama anan gaskiya "kar muyi haka da kai Ma'aru sau tari sunan da take Kiransa dashi kenan "bari na shiga na dauko maka dorinan"
.....
da kyar ummita ta yunkura ta mike zuciyarta na dokawa kamar zata fasa kirjinta jikinta a matukar sanyaye ta kama kunnuwanta duka zata fara sai ga ya rayhan da ya Abdurrahaman sun shigo bakinsu ɗauke da sallama ,da idanu ya rayhan bi ummita dashi yana kallonta da tsantsar mamaki a saman fuskarshi da sauri ya k'araso gareta a dai-dai lokacin da har ta fara, ya kamo hannayenta duka biyu ya mikar daita tsaye yana cigaba da kallonta tana zubda hawaye gani yadda hawayen ke gangarowa bisa kuncinta yasa gaba-daya ya rud'e hankalinsa ya tashi ko ba'a faɗa masa ba yasan ita da ma'aruf ne tunda gashi zaune cikin saurin yace "no my princess karki min hasarar hawayenki ta runtse idanunta gam hawaye suka K'arasa zubowa , ya saki hannunta daya yana goge mata hawaye" karki yi kuka waye ya taɓa min gimbiyata ?
"Gaskiya za mu samu matsala da ko waye fa a gidan ina dalili a dinga wahalar min da Mata"
alhankali ya zaunar daita shima ya zauna" plz karki bata fuskarki da hawaye I don't want see your tears"ya faɗa yana ciro hanky da sauri ya cigaba da goge mata,
"ma'aruf ne Kou ?
Barni dashi nasan yadda zanyi dashi ,ƙarin girma zanyi miki ta yadda dole ya girmamaki ,ya ɗan kalli inda ya Abdurrahaman yake tsaye " wa me yasa Maaruf baya min kara ?
" abinda bazan taba masa ba shi yake min akan ummita" ..
Ya Abdurrahaman yayi murmushin takaici sannan ranshi a bace ya zauna yana fuskantar Ma'aruf "gaskiya baya kyautawa, ni kaina ina jin haushin haka "kullun sai na samu labarin abinda yake mata ,dan Allah ka kyale yarinyar mutane haka ta huta"
ya rayhan ya dubi ya Abdurrahaman "Ni dai yaya ka faɗa masa babu ruwansa da ita" ,duk ma abinda tayi masa ya dinga faɗa min tunda ni zan aureta zan san abun yi"
yayi maganar yana juyowa inda Maaruf yake zaune " dan Allah ka bar min lafiyarta haka ta huta bana son ganinta cikin damuwa da tashin hankali idan wani abu ya sameta baka da hasara, idan ma ya zama dole sai ka hukuntata ni ka dinga hukunta ni ba sai kaci zalinta ba ya K'arasa maganar yana mikar daita tashi mu bar d'akin kafin inna ta fito suyi miki taron dangi"
Bai d'ago idanunshi ya dubesu ba har suka bar parlourn ya ja tsaki a fili sannan ya gaida ya Abdurrahaman aciki ya mike sambal akan doguwar kujerar mai zaman mutun uku ya kwanta ya dafe goshinsa da hannunsa ɗaya ,dayan hannun ya daura a saman cikinsa . ..
Su ummita basu K'arasa fita daga d'akin ba Inna ta fito daga daki tana washe baki "ungo ka zane min ja'ira yarinya mara kunya?
" babana karka barta ka lallasa mini ita" ,
"da sauri ummita ta dawo ai ba sai kinsa ba , idan zaki iya ai sai kiyi da kanki ta bata amsa tana sake yin gaba " ai kuwu Ma'aruf najin haka yayi wata irin super sai gashi abakin kofa ya damki kunkurunta " me kika ce munafuka? Ta saki ƙara "Ni wallahi ba ba munafuka bace ya rayhan yayi saurin rike hannunsa "dan girman Allah ka rabu daita ka rama akaina "
Maaruf yace " baka isa ba ita da tayi laifi ita zan hukunta ,ka duba duk yaran gidan nan babu wanda ke min irin abinda take min ,",kayi hakuri dan bazata sake ba saketa "kar ya sake ni ya kashe ni kawai kowa ya hutu ai kuwa tana gama faɗar haka ya yarfa mata mari ..
ya sake daga hannun zai kara mata ya Abdurrahaman ya tare sa " haba Ummita , kema kina da neman fitina ana kwatarki a hannunsa amman bakinki ba zai mutu ba ,a she kema dai da na ki halin ake ganin nasa" ? Kuka take sosai har da shesheka jin abinda ya Abdurrahaman yace , bakin ya rayhan ya mutu ya rasa me zai ce sai kare ummita yake dan kar maaruf ya ƙara mata
Sai daya furzar da iska mai zafi kana yace "ka mata gargadin ," ta kiyayi min rashin kunya ,ta daina faɗa min duk abinda ya fito daga bakinta ,kai ko aurenta kayi ,kayi make sure bata shiga hurumina ba, idan kuwa tayi ganganci sai na... .?"
" me zai faru Ma'aruf ?
"Enough Ma'aruf
bana son haka ,banason abinda kake min wannan ya zamo karo na karshe da zaka sake marinta a gabana ,bana jin zuciyata zata cigaba da daukar haka" .....
"Kai rayhan ina ruwanka?
" ban gane ina ruwana ba ta yaya zai dinga mata izaya irin haka, kalli yadda ya rike mata naman ciki yana ƙoƙarin illata yarinyar mutane "
" ai kana ji kuma kana gani tunda kai ba makaho bane
abinda tayi a yanxu agabanka ne kuma har yanzu bakinta yaki mutuwa amman da yake bakason gsky kake hakikance wa "a'a Inna karki ce haka ai ba karfinsu daya"
ba inji cewar ya Abdurrahaman "yi min shiru anan ,ka wani k'ame da wani gutun gemunka irin na munafukai"
""tsit ya Abdurrahaman ya kama baki yayi shiru cike da mamaki yana kallon Inna " babana Sau dubu ta zageka sau dubu kayi mata dukan mutuwa Ni na saka kuma babu abinda za'a yi ,ko ubanta bai isa ba bare ku"...
" Wannan ai daurewa karya gindi ne ,sam ba'ayin haka ,ai yanzu a gabanki nayi mata faɗa ,nasan itama da nata ,amman nashi yayi yawa .. Ma'aruf bai ce komai ba ya koma ya zauna yana huci ..
"To be the last time da zai kai hannunshi jikinta wani kallo Ma'aruf ya watsawa rayhan cikin yanayin maganarsa a hankali "ka canza tunani ɗaukar mataki babu abinda zan mata matukar zan faɗa tayi shiru ,duk sanda zan faɗa ta faɗa sai na taɓa lafiyar jikinta naga abinda za kayi"
Ummita da gudu ta juya tayi part dinsu tana kuka ko kallon mutane dake Parlourn bata yi ba , ta wuce ɗakinta tana kuka tana magana " ya Abdurrahaman me sonta shima ana so a shiga tsakaninsu , tunda bai taba mata faɗa ba sai gashi yau har da bata rashin gaskiya ita kuwa Inna dai so take kowa ya tsaneta ko cikakken minti goma batayi ba ya rayhan ya shigo "come on my princess ya fad'a tare da jawo hannuta sai lokacin tasan ya shigo haɗa ido sukayi na minti biyu wanda suna iya jiyo numfashin juna tuni idanunta suka sake kadawa "kiyi hakuri my princess komai lokaci ne ,shiyasa nake son kibani dama na daukeki na killace ki a gidana idan na aure bazaki sake zuwa gidan ba sai na tabbatar da Ma'aruf bai gida ,bazan bari ki haɗu dashi ba bare ranki ya baci .... ....kafin haka zan so ki fita harkarsa duk abinda zai yi karki sake kula sa ko daga kai ki kalleshi shi din kamar mahaukaci yake idan yana faɗa ana faɗa kin san halinsa ba tun yau ba sai kici maganin zama dashi sosai ya rayhan ya dinga mata nasiha yana kwantar mata da hankali har ta samu natsuwa "
waje kuma Ma'aruf ne da Abdurrahaman sukayi niyar zuwa masallaci sallah, suna tafiya Abdurrahaman na bashi hakuri da fahimtar dashi abubuwa da yawa akan ummita saboda yaga kamar ransa ya 'baci sosai ,"ka daina tsanarta haka Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama yace "idan zaka so mutun ka so shi kaɗan saboda wata rana zai iya zama makiyanka haka zalika idan zaka ki mutun kaki shi kaɗan saboda watan zai iya zama mayinka , ma'aruf ummita jininka ce halak malak ka daina cin zalinta ka guji ranar da hakkinta zai bibiyi rayuwarka ,, ina tabbatar maka zakayi nadama ranar da hakurin mama ya kare saboda kana kin yarinyarta ne without any reason ,sam ma'aruf baya ma sauransa gaba-daya hankalinsa yana wani gurin .....
******
Da daddare da misalin karfe bakwa da rabi hajiya ummah mahaifiyar Ma'aruf tasa aka yi mata kiranshi ,a hankali ya shigo bakinsa ɗauke da sallama ta amsa a ciki batare da kalleshi ba ,ya samu guri ya zauna
agabanta a kan kafet a babban parlour'n ta ya tankwashe kafafunsa sanye take cikin fari dogon wando da red din riga mai karamin hannu sai farar facing cap daya daura a kanshi duk cewar kayan shan iska ne na gida hakan bai hana kayan suyi masa kyau ba ..ganin yadda hjy umma ta haɗe rai yasa gabansa faduwa jikinsa a sanyaye ya gaisheta wannan karon ma aciki ta amsa idanunta cike da damuwa sosai ta maida gabadaya hankalinta a kanshi a matukar fusace ta soma "Ma'aruf ya d'ago ahankali ya kalleta a tsorace dan yasan duk abinda yasa tayi kiran sunansa kai tsaye abu ne mai mahimmanci ,dan ita mace ce mai tsananin hakuri da kawaici sannan bai taba jin ta ambaci sunansa ba ,wannan shine karo na farko "dan haka ya tattara duka hankalinsa akanta "hjy umma ya bata rai sosai "wai yaushe zaka canza ne ?
Yaushe zaka daina musgunawa yarinyar mutane ?
"Me yasa baka da alkunya da sanin yakamata?
Ahankali ya sunkuyar da kanshi saboda fahimtar inda maganarta ta ta dosa "sam baka da alkunya wallahi yarinyar nan fa bata da wani dan'uwa mafi kusanci da sukayi rayuwa a daki daya sai kai ,idan baka sake daita ba dawa zaka sake ?
"Kullun kana dakin uwarta amman saboda baka da mutunci itace abar wulakatawa gareka "me yarinyar mutane ta maka ?yayi mata shiru yaki cewa komai " tambayarka ne dan ubanka kabani amsa me tayi maka ?
"Bata jin magana ne sannan bata da kunya .."shikenan dalilin ?ya daga kai yana shafa sumar kanshi "kai kunyar ce da kai?
" da anyi magana kace yara basu da kunya , "to banaso takurawar ta isa haka , daga yau karka sake na sake jin ka taba lafiyarta a gidan dan bana so idan duka da zagi ya zame maka ibada kazo ga kannen naka nan ,bana so kaji na fada maka "tou hajiya ya faɗa yana dubanta "kiyi hakuri inshaallahu na daina "Allah yasa ta faɗa tana mikewa tayi cikin d'akinta jiki a sanyaye ya fito daga part din zuwa nasu ummita ya nemi guri kan doguwar kujera ya kwanta yana tunani ..
ranar ko abinci dare kasa ci yayi duk da irin faman da mama ta dinga yi dashi, tunaninshi ya tafi ne akan yadda zai yi aure ya tattara ya bar gidan gabad'aya ....
Two friend's (bsbs)
0 comments:
Post a Comment