idanunshi na runtse yake bawa kanshi shawara, ranshi duk a dagule ya mike tsaye a hankali yana layi tamkar wanda ya sha wani abun , da kyar ya iya buɗe bakinsa yayi wa mama sallama "mama sai da safe tare da ƙoƙarin fita daga ɓangaren gabad'aya , idanun mama na kanshi ta amsa masa "Allah ya tashe mu lafiya tana jin damuwa a cikin ranta saboda bata son ganin shi cikin damuwa .
a zafafe ya shige d'akinsa ya faɗa saman gadonsa hannunsa ɗaya dafe da goshinsa yana furzar da iska mai zafi " kar ka sake na sake jin ka shiga lamarin yarinyar mutane ,karka sake dukanta ,idan dukan ya zama dole , ka zo ga kannenka nan ka doke su , amman ita banason kana taɓa lafiyaryarta banaso" ...... maganganu mahaifiyarsa suka shiga dawo masa daki daki suna samu karɓuwa a cikin zuciyarsa naunauyen ajiyar zuciya ya sauke da karfin gaske yana fidda numfashi mai zafi " duk runtsi duk wuya bazan sake shiga rayuwarki ba ...... .ya furta hakan a kasan ranshi ..
Bangaren ummita itama kwance take a d'akinta har lokacin zuciyarta bata cikin walwala , ranta duk a 'bace yake , ta qullaci Ma'aruf kwarai da gaske a cikin zuciyarta , ba shi kaɗai ba hatta hajiya Inna tashiga sahu manya manyan makiyanta , ta san matsayinta da zata ajiye a cikin zuciyarta , ta sanyata a bagiren da babu wanda ya isa ya sauya ....
ban cin daraja mama ,da ita kaɗai tasan irin rashin mutuncin da zata shuka hajiya Inna , amman kullun maganar mama ɗaya ce gareta "kiyi hakuri ummita komai mai wuce wa ne har ya zamo labari , mai labarin ma wata rana baza'a ganshi ba , kawai ki share duk abubuwan da'ake miki matakin d'aukaka ne ,ki cigaba da addu'a Allah yana sane damu......
"bari na d'auko maka dorina mai baki shida tana tsallen kwado kana tsulawa yar banza yarinya ...
Wasu zafafan hawaye masu zafi da ciwo suka gangaro mata lokacin data tuno maganar hajiya Inna...
"Me yasa Inna ?
"Me yasa kika tsane ni haka ?
"da fari kin tsani mahaifiyata da bata rage da komai ba , kin fifita sauran surankanki akanta haka zalika kin fifita jikokinki akaina me yasa Inna ....?
Ta sake rushewa da wani sabon kuka "ki daina kuka ummita Inna da Ma'aruf ne kaɗai mutanen da suka tsaneki a cikin dangi bayansu kowa yana sonki dan me zaki damu kanki ?
"ki sharesu kiyi rayuwarki kamar kowa ,ko babu su a cikin rayuwarki zaki yi farinciki ....
Ta dade kwance tana zance zuci , kafin daga baya bacci barawo yayi awon gaba daita, da kyar ta samu ta tashi tayi sallar asuba ta koma ta kwanta .. ..
*******
Da gari ya waye ta tashi idanunta sun dan kunbura saboda kukan da tayi jiya ta ɗan dafe kanta da taji ya mata nauyi tare da sarawa kamar tana buga mata gudunma , hatta bangaren hango daidai inda zuciyarta take ji tayi yayi mata nauyi sosai sannan yana mata ciwo,
A hankali ta yaye bargon dake lullu'be da rabin jikinta ta zamo daga kan gado ta sauko ta tsaya gaban mirrow tana kallon idanunta da suka kunbura na two second sannan a hankali tayi
mika haɗe da sallati sannan ta shiga gyara d'akinta sai data gyara ko'ina sannan ta nufi bayi, ta soma da wanke baki sannan tayi wanka ta fito daure da towel tana goge jikinta har lokacin tana jin damuwa a ranta haka zuciyar bata daina mata ciwo ba .....hannu ta kai ta ɗauki man shafawarta piement lotion ta soma bin ilahirin jikinta dashi sai data shafe jikinta sannan ta nufi wordrob, ta buɗe inda bra da pant dinta suke ,ta d'auka ta feshesu da turare sannan ta buɗe bangaren kayanta ta ɗauki atamfar chigabi gold wanda aka yiwa dinkin riga da siket ta sanya ta shirya tsab ta shafa hoda kana ta fito ta rufo kofarta ta shiga dakin mama ta gaisheta "mama ina kwana ?
"Lafiya kin tashi lafiya ?
"Lafiya mama bari naje na gaida Abba na dawo "ai baya nan tun tara ya bar gidan nan tare dasu Ma'aruf ..saurin runtse idanunta tayi ,idan akwai abinda ta tsana bai wuce yadda iyayenta suke da close dashi ba tare da nuna masa kulawa ....mikewa tayi ta fito daga d'akin ta sauko parlour'n kasa ta ɗauki remote ta kunna ta,
tana zaune a dining tana breakfast meenal tashigo ,sosai ta maida hankalinta kan meenal dake ƙoƙarin karasowa inda take zaune "ummita gidan baba sarki zamu shine nace bari na zo na faɗa miki ko zaki "kuje kawai babu inda zani "
Meenal ta karaso kusa da ita sosai ta dafa kafad'arta "haba ummita karki ce haka mana, me yasa bazaki ba ?
"Ra'ayi cin buredi da sandi ko dole sai naje ....
" ni gaskiya dole sai kinje tafiya dake ai tafi dadi gaskiya, idan har da gaske ba zaki ba nima na fasa zuwa bari naje na fadawa su aunty jiddah su wuce kawai "better zauna ga guri nan muyi kallo "maza ki qarasa cin abinci kije ki canza kaya ki bita ku wuce mama ta fad'i haka tana saukowa daga step "amina jirata ta qarasa cin abinci .
"Inna kwana mama ?
Cike da sakin fuska mama tace "lafiya kalau amina yasu hajiya umma ?
"Lafiya lau kowa yake ..."
Azafafe ummita ta mike ta ture plet din abinci tayi hanyar step, taku biyu tayi ta tsaya sakamakon muryar mama data doki dodon kunneta "dan nayi magana shine kika tashi mama tayi magana, kuma dan bak'aramin so take wa ummita ba ?
" ki dawo ki qarasa cin abincin , juyowa tayi a hankali fuskarta a shagwa'be kamar zata yi kuka "ni na koshi "shikenan Allah ya shiryeki naga ranar da zaki canza ,shiyasa har abada ba zaki sha inuwa ɗaya da ma'aruf ba ,ke dai idan ba ra'ayinki ba ba zaki yi abu ba , kina da aiki domin idan kika je gidan miji kina irin wannan halin wuya zaki sha a hannunsa "a fusace ta juya tana taka step da karfi "ni babu wani aure da zanyi tayi murmushi "kai ummita rigima zauna mana amina ..
kai tsaye cikin d'akinta ta shiga, ta dauki bakar abaya ta ɗaura a saman kayan dake sanye a jikinta , ta nade kanta da mayafin abayar sannan ta ɗauki turare mai sanyi kamshi ta sake fesa a ilahirin jikinta ta karasa gurin takalmanta ta dauki cover shoe yellow mai ratsin baki ajiki ta sanyawa kafafunta , ahankali ta sauko tana turo baki tare da ƙoƙarin daurawa tsintsiyar hannunta agogo .
Meenal dake zaune a falon tana ganinta ta mike tsaye ,idanunta akanta meenal , ta kamo hannunta " kai gaskiya kin yi kyau sosai yar'uwa ina sonki ummita ta kwace hannunta tana bata rai "muje yar matsala banason dogon turanci ,kawai mutun na zaman zamansa zaki wani....
"Ni zaki zaga ba ita ba, tun da ni nayi miki dole, meenal ta sake kamo hannunta" mama mun wuce "to Amina yar albarka sai kun dawo Allah ya kiyaye hanya ku gaishesu , har zasu fita taji mama bata ce komai ba dan haka ta kwace hannunta cikin na meenal ta dawo ta rungume mama dake mike tsaye "mama kiyi hakuri ni baki min addu'a ba ..
"ai baki nema bane "to ai itama meenal bata rokeki ba ki ka yi mata " "to shikenan Allah yayi miki albarka, Allah ya shirya min ke shiri na addini muslunci sai kun dawo ,dan Allah karki yi faɗa da kowa .."naji mama amman kiyi addu'ar Allah yasa kar wanda ya shiga track dina "inshaallahu babu mai shiga tace "ameen uwa ta gari abar alfaharina ina sonki sosai mamana ta fad'i haka tana sakin mama kana ta juya ta sanya kai suka fice .....
"Ina sonki ummita , Allah ya nuna min aurenki , ya albarkace da samun zuri'a masu albarka ..
A hankali take taku kamar bata son taka kasa , cike da yanga da karairaya , har suka qaraso inda sauran yan'uwansu ke tsaye jikin mota tsayuwar jiransu , ammar na ganinta ya washe mata baki " kunga hajiya ummita gimbinbid'a ta ya rayhan kinyi kyau sosai , wani irin kyau kika yi kamar yanzu aka saukar dake daga sama "dan Allah malam dakata ya isa ban son magana da salo karka bari na sauke haushina gabad'aya akanka"
"wa ni ?
"Gaskiya ba'a yi haka ba ranki shi dade shiga mota muje , kyau kam kin yi sosai kuma dole a aya ba , tayi masa banza gabad'aya babu wacce ta kalla har aunty jiddah , ta samu guri ta zauna a baya saboda aslamiyya ta kame a gaban motar,tun da ta kame a gidan baya babu wanda tace wa qala
har suka iso gidan baba sarki hira ake amman ban daita sam bata saka musu baki ba illa wayarta data ciro ta shiga danne danne duk yadda ammar yayi ƙoƙarin janta da hira taki yarda ta saka baki ..
Suna shiga gidan baba sarki ,gidan ya hautsine da hayaniya da ihun aunty sakina da yaran gidan ,tazo da gudu tamkar wata yarinya ta rungume aunty jiddah ajikinta tana murna ganinta ,cike da farinciki ta janyo hannu aunty jiddah "muje daga ciki ,a babban parlour'n hajiya kulu suka zauna gaba-daya su .
Ummita kuwa tunda ta gaishe da mutane gidan tayiwa kanta mazauni a kujera mai zaman mutun ɗaya ta cigaba da game a cikin wayarta , bata sake kallon inda suke ba haka suma babu wacce ta saurareta murnar ganin juna kawai suke , cikin minti goma aunty sakina ta cika musu gabansu da ruwan sha da drinks har ma da smallchop's "kai yau ina da manya baki tun jiya na kasa samu isasshen bacci saboda zuwanku me zaku ci a dafa muku ?
Aunty jiddah tayi murmushi tace "kai daga zuwanmu sai dai zuwa anjima dan gaskiya yanzu a koshe muke ko ta fadi tana kallon sauran yan'uwanta duk suka daga kai alamun eh " hira suka shiga yi kowa na fadar albarkacin bakinsa amman banda ummita da ko ruwa bata sha ba, sai dai duk abinda suke faɗa yana shiga kunnenta can aunty sakina tace "wai ummita me kike yi a waya ne sama da awa biyu baki ce komai ba baki sha komai ba ,ga duk yan'uwanki na walwala ban da ke ?
aslamiyya tayi tsigil tana yatsina fuska tace"wai nan fushi take damu tun jiya taki yiwa kowa magana "
"akan wani dalili kenan ?
"Oho mata mu dai zamu yiwa mutun magana tun da mun san illar yin gaba a ddini , kuma mun san illar kasani ka take sani " aslamiyya meye haka idan zakiyi magana kiyi sak akan abinda akayi tambaya akai ba wai ki dinga fadar abinda bai dace ba ?
"Ce miki akayi tana gaba daku ko me ?
inji cewar meenal.
"Sai an faɗa mana, halinta ne bamu sani ba ko me ?
" ko me zatayi tayi ai bamu muka ce tayi rashin kunya har a samu damar jibgi banza aslamiyya ta K'arasa maganar tana kwashewa da dariya, sauran ma duk suka dara har ammar , "Inna jiya fa har da guzirin dorina mai baki shida Allah ya taimaketa ya rayhan da ya Abdurrahaman suka shiga tsakani da Allah kaɗai tasan irin dukan da zata sha inji cewar Ammar , sakina tace " waye ya jibgeta saboda Allah ?
"Wa kika sani daya wuce ya Ma'aruf shi tayi rashin kunya kinsan shi babu hakuri .....
Nan kuma hirarsu ta dawo kan Ma'aruf
Ummita tayi shiru taki cewa komai sai dai idanunta sun kad'a sunyi jazir ,ta lumshe fararen idanunta tana cizan lip's dinta na kasa a hankali.. ..
"Aunty sakina ta sake cewa " ummita kice wani abu ,akan Ma'aruf mana kinsan fa ni ina son ayi yar gida ne , "kin manta ne aunty sakina ni ba hanyarmu daya dashi ba ,da dai kun cigaba da hirarku zai fi "ai kunji mugun halin nata ba ..mutun da ɗan uwansa amman ya dinga nuna masa kabilanci..
A fusace ummita tace "an nuna abinda yafi kabilanci aikin banza aikin wofi ,saboda bani da aikin yi sai na zauna na biye muku ana hirar mutumin da a duniya idan akwai wacce ya tsana to nice ,Ke ni ko muna gud time dashi bani da lokacin da zan zauna ina maganar namiji ɗaya kullun kamar na rasa mashin shini ,ba baku da aikin yi ne dake da masu maganarsa , shiyasa kullun kuke bani haushi da bakwa gajiya da maganar mutun daya ,mutumin da arayuwarsa ma bai san daku ba sunan dai yana dan'uwanku ne ..
"Wallahi ni duk macen dake son shi kallon
hasararriya nake mata wacce ta rako mata duniya ,kuma wallahi tayi hasarar rayuwa maganar duk da zakuyi sai kun sako wani katun banza mai tsiffar samudawa a ciki "
"karki sake zaginmu ina ruwanki ko had'iye shi mukayi ,ko fadar sunan shi ?inji cewar aslamiyya
"An zaga sai kiyi duk abinda zakiyi banza kawai "ai kice banza ,mutun sai mugun halin tsiya "to kun fara ko ba dama ku haɗu sai kun nuna hali" hajiya kowa a nan yaji abinda take cewa akan yaya Ma'aruf ko shi ba d'an'uwana bane bai kamata ta dinga fadar munanan kalamai akanshi ba " to shikenan ya isa kar na sake jin kunyi faɗa akanshi ra'ayi mutun yayi hirar d'an'uwansa ra'ayi ne mutun yace bai so ,babu ruwanku ku da kukaji zaku iya ku cigaba,
Dukkanninsu sukayi shiru babu wace ta sake yin magana ,tunda ummita da aslamiyya ke tanka in taka aunty sakina Ke kallon ummita ta kasa ɗauke idanunta akanta idan ta fahimci maganarta daidai ,itace tayi hararrriya wacce tayi hassarar rayuwa tunda itace tafi zakiwa akan maganarsa kuma itace ke sonshi .... "
"Bama hirarsa muke ba Hajiya maganace ta kawo magana har...."nace ya isa banason jin sharhi , Allah ya kara haɗa kanku, gaba-daya ...suka haɗa baki suka amsa da "ameen Hajiya ..."
Hajiya ta maida hankalinta kan ummita "ummita ki dinga hakuri da yan'uwanki, baki da kamarsu suma haka ku zama tsintsiya madaurinku daya kinji,
ki dinga hakuri sosai Hajiya tayi musu nasiha sosai tare da cewa karta sake jin sunyi faɗa akan ma'aruf ,dan haka kafin ta baro parlour'n hajiya kulu tayi ƙoƙarin shirya su ,sai dai kowace a cikinsu taki sakin ranta sai fixge fixge suke barin ma aslamiyya dan tafi kowa daukar zafi ,yayinda aunty sakina Itama ta dauki zafi duk inda ummita tayi da ido take binta tana harararta tare da jin haushinta hatta aunty jiddah bata ji dadin abinda tayi ba ..
Bayan hajiya kulu ta koma d'akinta aunty sakina da aunty jiddah suka shige d'akin aunty sakina "kiyi hakuri sakina naga ranki ya baci kwarai ,haka halinta yake ni kaina bana jin dadin abinda take wa ya Ma'aruf , gaskiya ban taɓa tunani ummita zata iya faɗar abinda ta faɗa ba hasarariya mai hasarar rayuwa fa ?"kiyi hakuri ,sai dai zuwa yanzu ya kamata mu ɗauki tamaki akanta "kamar ya kenan wani irin mataki zamu dauka ? Inji cewar aunty sakina.
"Mu ware ta acikin mu mu nuna mata mu fi son ya Ma'aruf akanta Wallahi ban taɓa jin na tsaneta ba sai yau ,wannan shine karo na farko da naji na tsaneta , tsana fiyye da irinta ya Ma'aruf "Gaskiya ni dai bana cikin wannan tsarin naku ko kun juya mata baya ni dai ta zame min dole , dole nayi mu'amala daita inji cewar meenal atare suka juyo suka fuskanceta tsaye abakin kofar d'akin "aunty jiddah komai ummita zatayi bai kamata ba ,bai kamata kice haka ba "ki yi min shiru anan daman ba tun yau na fuskanci kinfi sonta akanmu ba wannan shine abinda zamu yi mata kuma babu fashi sai munyi ......
"ba haka bane aunty jiddah , matsayinku daya ke da ummita ,matsayi daya kuke dashi duka acikin zuciyata , dukanku nawa ne, idan ku ummita bata zame muku dole ba ni dole nace saboda ubanmu daya daita ke kuma uwarmu daya dake babu wanda zanki acikinki duk duniya a halin yanzu kune mafi kusanci da rayuwata "Please aunty jiddah karku yi haka wallahi mama bazataji dadi ba ,ni kaina dana sani ban janyota dole ba ,sai data ce bazata zo ba na takura mata ," aunty sakina kuyi hakuri ku yafe mata dan Allah zan mata magana nasan kuma za taji ta karasa maganar tana haɗe hannuwanta duka guri daya "tsaki aunty jiddah taja" ke a matsayin ki na wa kenan da zaki faɗa mata taji?
" yarinyar da uwar data haifeta ma bata isa ta faɗa mata ba taji
ba sai ke uwar kankanba tana gama faɗar haka ta nufi kofar fita ta tsaya a bakin kofar ta kira Maryam da Khadeeja da aslamiyya da Sa'ada har da kannen sakina amman ban da ummita..... parlour'n ya rage daga ummita sai Ammar su kuwa sun kulle kansu a daki ...
Wannan abu yayi mugun batawa ummita rai taji haushi acikin ranta take gefen kanta ya soma sarawa ta runtse idanunta kawai tana fidda numfashi sama sama tamkar mai cutar asma ...
a qalla sun ɗauki sama da awa ɗaya suna tautaunawa, acikinsu Maryam da meenal ne kawai basu bada goyon baya ba amman sauran duk sun amince da hukunci da aka zartar .. ..
Sai yamma lesss suka dawo gida kai tsaye kowace ta kama gabanta tana cika tana batsewa , meenal da da Maryam suka wuce bangaren su ummita, kowace tayiwa kanta mazauni "sannu da gida mama suka hada baki gurin faɗan haka "sannuku yan albarka kun dawo lafiya yasu hajiya kulu ?" Duk sunce agaisheki ",ina amsawa "akawo muku abinci ne ?
"Sai dai ummita dan naga itace kaɗai ce bata ci abinci ba amman mu a koshe muke" sosai mama ta maida hankalinta kan ummita dake zaune ranta a matukar bace kallo ɗaya tayi mata ta fahimci tana cikin damuwa "ummita ...... mama ta kira sunanta a tsanake
Ta d'ago kanta a hankali tana kallon mama tare da ƙoƙarin boye damuwarta , cikin kwayar idanunta mama take kallo tana karantan yanayinta "tashi kije ki rage kayan jikinki kizo kici abinci muryarta a sanyaye kamar zatayi kuka tace "to sannan ta soma balbale mabalin abayar jikinta ta cire ta ajiye agefenta tun kafin ta mike mama ta rigata tashi ta isa gaban dining tablet ta zubo Mata abinci jollof din kuskus ne wanda yaji kayan hadi kabeje da hanta da nama , ta dawo inda take zaune ta mika mata "maza kin ye ki bani plet mama ta fadi haka sanin da tayi ba wani abinci kirki take ci ba ..
A hankali ta soma tsakurar abincin tana kaiwa bakinta idanunta ya cicciko da ruwan hawayen tausayin kanta da mahaifiyarta da kuma bakinciki abinda su anty jiddah sukayi mata ne yake cin zuciyarta "ita kaɗai tasan yadda take ji ...
Ita kaɗai suka ware suka kulle kansu a daki ..
abun yaki barin ƙwaƙwalwarta tana son sanin abinda suka tautauna acikin daki kafin ta ɗauki mataki akansu ta sani idan kowa bai faɗa ba dole meenal zata faɗa mata ,da wannan tunanin ta karasa cin abinci , mama ta miko mata ruwa cike da kulawa ..
ko cikakken minti talatin da gama cin abinci bayi ba ,sai ga
fauziyya ta shigo da gudu ,bata kula kowa ba ta kalli ummita "aunty Ummita wai kizo inji abokin ya Ma'aruf " take ta haɗe rai dan sai lokacin ta tuno da muhd Sa'id "jeki ce banana haka kawai azo a damu mutun daga dawowarsa ni babu inda za.. "ke bana son shashanci kije mana kiji abinda yake tafe dashi ,ai ko baka son mutun baka nuna masa a filli ba ,sannu a hankali idan shi mai hankali ne zai fuskanta, karki kuskura ki furta kalmar kiyayya ga mutun cin zarafi ne babba in har ba'ayi dace da mai kyawun hali ba zai iya qullatarki har ma ya cutar dake tashi maza kije yana jiranki .....
Tun daga nesa da muhd Sa'id ya hangota ya fara aiko mata da kyakkyawar murmushi ya diro daga kan motarsa da yake zaune a lokacin data karaso "barka da fitowa tauraruwan taurari,tauraruwan matan duniya .. gimbiya a zuciyar said , tayi saurin ɗauke kanta daga garesa tana jan tsaki "ina wuni " ta faɗa atakaice lafiya lau yammtana ya mutanen gida ?
"Lafiya ta amsa a ciki ya sake yin murmushi "gani na dawo hajiya subai'a na cika alkawari ,ina fatan nima za'a cika min nawa alkwarin a sanar dani matsayin dana samu ko da yake tuni zuciyata ta gama amincewa na samu babban matsayi ina fatan hasashena ya zama gaskiya idanunshi akan ta ya karasa magana ....
Gaba-daya sai taji ta diririce tamkar ya daureta da irin mayataccen kallon da yake mata "kar ki kuskura ki furta kalmar kiyayya a gareshi cin fuska ne babba kalaman mahaifiyarta suka fado mata a hankali ta d'ago ido ta kalleshi har zuwa lokacin ita yake kallo qirjinshi na dokawa da matsanancin karfin gaske "uhm ke nake sauraro subai'a"tamkar kai ne ka rada min sunan muhd Sa'id..........
Ta faɗa tana tsareshi da fararen idanunta masu narkar da zuciya .
"kama yayi ka sake yanka min ragon suna da irin sababbin sunayen da kake kirana dasu ,Hajiya ,gimbiya tauraruwa ....."
Dariya muhd Sa'id ce ta katseta "au gimbiya subai'a kowane suna matukar yana da kyau gani nake ya fi dace dake ,karki ga laifina soyayayarki ce ta min yawa ,ganina da jina da komai nawa duk soyayayarki ta mallakesu bana iya yin komai sai da amincewar qaunarki .. amman dai mu koma baya kan abinda ya kawoni dan shi nafi bukata, nafi son na fara jin matsayina agurinki ..
Shiru tayi tare da tsurawa zanin atamfa dake d'aure ajikinta ido dogon lokaci shi kuma ya kasa ɗauke idanunshi akanta zuciyarsu cike da zullumi da tsoron jin abinda zata ce ,gyaran muryar da yayi ya sa ta dawo daga duniyar tunani ..
"So take ta faɗa masa gaskiyar abinda ke zuciyarta amman kalaman mama na tauyeta da kanainayeta , dan haka ta bude baki da kyar tace "Allah ya zaba mana mafi alkhairi mutun ai bazai ki mu.....ta datse harshenta wannan shine karo na farko data dade da nmj har ta furta wannan kalmar garessa sauran da ko kallon arziki Basu isheta ba Shima wannan adalilin samun damar shigowarsa gidansu if not bazata sairaresa ba ..." ina fatan ka gamsu "ko kadan kalamanta basu gamsar dashi ba domin ma'abota soyayya sun jima da fassara kalmar mutun bazai ki mutun ba da rashin samun karɓuwa a wajen yarinya ,sai dai wayo irin na muhd Sa'id bai bari hakan ya kayar masa da zuciya ba, ina ma laifi da yasamu kamar wannan kalmar agurinta ...duk da kalmar batayi masa ba amman zai yi mata kyakkyawan maajiye acikin zuciyarsa da ƙwaƙwalwarsa , a hankali ya kudirce a ransa matukar zata cigaba da fitowa ta sauraresa shi kuwa sai yayi kwance kwance ya warware duk kullin soyayayar kowa daga zuciyarta ya cusa nashi dan tunda Allah ya haliccesa bai taba jin ya so wani abu so mai tsanani irin soyayyarta ba ..
Cikin hikima ya cigaba da yi mata hira mai dadi har zuwa karfe bakwai ko kadan baya don rabuwa daita ,lokacin data bukaci suyi sallama bai Musa ba bayan ta tafi ya samu wani yaro ya damkawa masa ƙatuwar ledar daya ciro a bayan motarsa ya nuna masa ummita yace ya kai mata ,bai jira dawowar yaron ba yaja motarsa zuciyarsa cike da kaunar ummita.. ....
.... Two friend's (bsbs)
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~TRUE LIFE STORY~
FREE NOVEL NOT FOR SELL
AL'QALUMAN
*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*
~DEDICATED TO~
*FATIMA ABUJE BAGUDO*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
PAGE 13
.......a daidai bakin kofar part din su ummita ya rayhan ya ci karo da saifullahi rike da ledodi niki niki sai faman nishi yake .
ya kalleshi cike da mamaki kafin daga baya yace "kai kuma daga ina haka da kaya ?
" um amm ... abokin .ya ma'aruf ne yace na kawo wa aunty ummita" "abokin ma'aruf rayhan ya faɗa yana mamaki zuciyarsa na dokawa da matsanancin karfin gaske .
"wanne kenan daga cikinsu yayi maganar jikinsa na d'an rawa ?
"Ya Sa'id"
a hankali ya cigaba da bin fararen lododin dake rike a hannun saifullahi da kallo.
"ai yaya Sa'id yana da kirki sosai ko shekaranjiya yazo gurin aunty ummira har nima sai daya bani kudi kuma yace zai kawo min glass daidai size dina, bai kowa min glas din ba amman ya bani kudin yace na.. ......
"Yi min shiru magananne kawai , fadi ban tambayeka ,
tambayarka nayi da zaka hau zuba kamar ruwa ?
"Bani lododin ka ƙara gaba , saifullahi ya mika masa ledodin kama hanya ya wuce yana wagensa .
Rayhan ya bude ledar ta farko idanunshi suka karo da kaya na garari da kece raini a ciki, paper less kwaya uku kala daban daban baki mai adon ja da shudi, sai mai ruwan lemon da ruwan zuma , sai atamfa top wax kwaya hud'u , dakakkiyar shadda galila guda biyu purple da ash colour , baki daya su ukun ,ya dade yana bin kayan da kallo bakinsa bude zuciyarsa na cigaba da dokawa ,dayar ledar ya bude kayan kwaliya ne kala daban daban da takalma , hakan nan yaji zuciyarsa na tsinkewa haɗe da rawa rawa tamkar wanda ake bugawa guduma ..
a zafafa yasanya kai ya shiga parlour'n hannunsa rike da ledodin , daita ya soma cin karo zaune , meenal da maryam sun zagayeta suna tambayarta ita kuma tayi musu shiru tare da zabga tagumi dan ta rasa abinda zata ce musu ,meenal da maryam suna ganin shigowarsa suka mike tare da gaishe shi basu tsaya jin amsar shi ba, suka shige ɗaya daga cikin daku nan dake Parlour'n ..
Shiru yayi kawai yana kallonta zuciyarsa cike da jin haushi da bakinciki ,kallo ɗaya zaka masa ka fahimci yana cikin damuwa da tashin hankali ..
kusan minti biyu bata d'ago ta kalleshi ba , da alamun ma bata san ya shigo parlour'n ba, sosai tayi zurfi cikin tunani, gaba-daya ta rasa meke mata dadi ,kalmar data yiwa muhd Sa'id amfani dashi ta tsaya mata arai ,"mutun ai bazai ki mutun ba ,ita kanta ba tasan lokacin da kalmar ta fito daga cikin bakinta ba , ba abinda taso faɗa masa kenan ba ,maganar mama ce tayi tasiri a cikin zuciyarta ......
"anya kuwa bata yi kuskuren ba .....?
"Anya muhd Sa'id ba zai ɗauka ko tana son shi bane ?" kai ta ya ma zai ɗauka tana son shi ne,alhali gabad'aya kalmar bata yi kama da kalmar soyayya ba..
kusan minti goma yana tsaye yana dubanta zuciyarsa na harbawa batare da yace mata komai ba , jikinta ne ya bata cewar ana kallonta dan haka ta d'ago kanta a hankali karaf idanunta ya sauka akanshi tsaye ga wasu fararen ledodi masu matukar kyau a gefenshi ..
Wani irin kallo yake binta dashi mai cike da tsantsar 'bacin rai yayinda hankalinsa ke sake tashi ... muryarsa a kausashe ya kira sunanta "ummita daman kina sauraron wasu samari bayan ni ?
gabanta yayi wata irin muguwar faduwa ,take jikinta ya ɗauki rawa ta zuba masa fararen idanunta batare da ta ce komai ba shima idanunshi ya zuba mata "daman zaki iya kula wani bayan ni?
"Na ɗauka ni kaɗai kike bawa lokacinki a she kina sauraron wasu a bayan idona ?"na ɗauka rashin kula soyayyata da bakya yi wani al'amari ne daban da tare son cikar burinki ashe ni ne baki so...?
"Amman babu komai na gode ,Allah saka da alkhairi daman nasan hauka kawai nake akanki , ni kadai ke haukan sonki da damuwa da lamarinki, shikennan babu komai tunda kinfi .son muhd sa'id a kaina ga kayan daya aiko miki dashi nan yana gama faɗar haka ya juya.
da sauri ta mike ta riko hannunsa "ya rayhan tsaya kaji "
"me zanji me zaki faɗa min? ya katseta da sauri yana tsareta da idanunshi .
"yanzu na amshi kayan a hannun saifullahi har yana tabbatar min wannan ba shine karo na farko da muhd Sa'id yazo gurinki ba , runtse idanunta tayi tana jin wani irin kuna cikin ranta da zallar bacin rai , duk da tasan bata son ya rayhan daidai da kwayar zarra a cikin zuciyarta amman bata jin zata juri ganinsa cikin damuwa a dalilin muhd Sa'id ba ..
Shi din wani jigo gareta dama rayuwarta gabad'aya .
Muryarta cike da in.. ina tace "ni...ni..ban san wani muhd Sa'id ba da kake magana akan shi ba ka dai .....
"Yi min shiru karki min karya mana ko last week an fada min yazo gurinki ...
Sunkuyar da kanta kasa tayi tana jin fad'uwar gaba mara misaltuwa, ahankali ya soma ƙoƙarin zare hannunsa cikin nata , ta sake riko hannunsa sosai "kayi hakuri yaya hakan ba zai sake faruwa , ka faɗa min abinda kake son nayi ?
Naunauyen ajiyar zuciya ya sauke da karfi har tana iya jiyo yadda zuciyarsa ke dokawa da sauri "dan Allah yaya karka yi fushi dani wallahi ba son muhd sa'id nake ba , yanzu ma ba'a son raina na fita ba ,wallahi ka tambaya kaji , da umarnin mama na fita ba dan ina ra'ayin hakan ba.
yaya in dai zan so wani d'a namiji arayuwata kai ne ...
" kai ne fa yaya rayhan dina ,da ka soma sona tun bansan ni wacece ba , ka soni tun ban san kaina ba ,ka nuna min so da kulawa ,ka nuna min gata a cikin duka sauran yan'uwa kallonka nake a amatsayin wanda ya rage min a fadin duniya .... ta k'arasa maganar muryarta na rawa alamun tana son yin kuka dan har ta fara lumshe idanunta ..
take ya daburce ya riko duka hannayen cikin nashi ya isa gurin kujera ya zaunar daita shima ya samu guri ya zauna yana lakace mata hanci " naji bance ki min hasarar hawayenki ba ,sai dai hankalina yayi mugun tashi "me kake so nayi yaya ka fadi min duk abinda kake so ummita zata maka ?
"duk abinda kake so shi zanyi ka faɗa min sosai ta kashe masa jiki ya tsura mata ido ya kasa ɗauke idanunshi akanta ..
Wani sanyayyen dadi ne ya dinga zirayar tsokar dake makale da kirjinsa, fuskarsa kunshe da farinciki yace "bana son ki sake kula wancan muhd Sa'id din , ke bama shi ba , bana son ki ƙara kula kowani namiji bayan ni ..
Yayi maganar kamar zai shige mata jiki "duk duniya idan aka cire mama da Abba nafi sonki akan kowa burina bai wuce na cigaba da sonki tare da mallakeki a matsayin matar aurena sannan ki kasance uwar ya'yana , ummita idan na rasaki mutuwa zanyi ..ina sonki! ina sonki !!
ina miki son da ni kaina ban san adadin son da nake miki ba harufan baki sun yi kaɗan da kwatata mizanin kaunarki gareni , taɓa zuciyata kiji yadda take dokawa akanki kullun cikin irin wannan dokawar take ,nasan da zarar ta rasaki zata tsaya cak ta daina bugawa dan Allah ummita kada ki barni, kada ki auri wani da namiji ki barni , karki bari wani da namiji ya rugaza min zuciya a sanadiyyarki ya K'arasa Maganar cikin killer voice dinshi ..
Tuni jikin ummita yayi sanyi ,naunauyen ajiyar zuciya ta sauke da karfin gaske idanunta na kallon cikin kwayar idanunshi wani irin abu yaga suna fitowa daga cikin idanunta suna shiga nashi jikinsa ya mutu yaji kamar ya shige jikinta dan ji yake kamar za'a kwace masa ita .
"ka kwantar da hankalinka
yaya inshaallahu zan...sai kuma tayi shiru ta kasa karasawa tana gudun tayi subul da baka irin wanda tayi agurin muhd Sa'id ..
"Inshaallahu me ki faɗa min abinda ke cikin zuciyarki har yanzu Ban tabbatar da kina sona ko ina da matsayin acikin zuciyar ba ,ina son ki furta min matsayina daidai kwayar zarar ba zan raina ba , ina son najita daga bakinki tayi murmushin gefen baki "karka damu yayana ai ina sonka kai fa d'an'uwana ne"
"No ummita ba maganar soyayyar ta yan'uwantaka nake nufi ba ,ina miki magana ne akan soyayya irinta zuciya da zuciya irinta ma'aurata , ta bude bakinta kenan zatayi magana sai ga mama ta sauko dan haka tayi shiru da bakinta tare da zare hannuta cikin nashi , ta kalleshi tana murmushi ..."ga mama nan fa ..juyowa yayi inda yafi tunani ganin mama ,
Ganin mama tsaye yana dan bugar da zuciyarsa dan yasan babu abinda zata sake cewa ,dan haka ya runtse idanunshi gam tare da dafe gaban goshinsa da hannunsa ɗaya.
"rayhan yaushe kashigo ?
"Yanzu mama kuma fita zanyi yanzu "lafiya dai na ganka wani iri kamar baka jin dadi ?
"Lafiyata lau ..
Idanun mama ne ya sauka akan fararen lododin dake ajiye ,take ta fahimci abinda ya sauya rayhan ,ya ga ummita da bakonta kenaan , tana kallonsa ya mike ya fice daga parlour'n ...
Qarasawa mama tayi ta soma buɗe ledodin a hankali , itama ummita kayan take kallo masu shegen kyau da tsada maimakon taji son muhd sa'id a zuciyarta sai taji tsanarshi ta shigeta , tambayoyi birjiki tayi ƙwaƙwalwarta ,batayi mamakin kudin daya kashe ba dan tana da labarin yadda yan caji ke kashewa mata kudi idan suna son su .
Tunaninta anya muhd Sa'id yana da hankali da har zai kashewa yarinyar da bai gama sanin matsayinsa a zuciyarta ba ,wayan nan makudan kudin kayan sun isa hada matsakaicin lefe kai ko babba ma tunda dai ai kowa da bazarsa yake takama , anya kuwa mai cikakken tarbiya ne wannan ?
"kila da yana da masu faɗa masa yaji ,da bazasu bar shi yayi haka ba ..
Gashi a fuska yayi kama da natsatsu kuma ma'abocin ilimi amman idan mai hankali ne Yakamata ya jira lokaci , ba yanzu ne lokacin da ya dace yayi hidima ba duk wadatar shi ...
Hajiya mama data zuba tagumi cewa tayi "kai Allah kayi mana maganin abinda ba zamu iya magantawa kanmu ba ,"ummita halan yaron nan dan wani attaijiri ne acikin garin nan ..
Ummita ta yatsina fuska" mama wannan abokin ya ma'aruf ne , dogon fari sun ma taɓa shigowa tare dashi ," dan waye canji .. ni na manta sunan babansa amman idan kika gashi zaki ganeshi "ummita nifa abin ya bani tsoro dan gaskiya mutane ya yanzu abun tsoro ne, yanda zamani ta lalace don abun duniya ya zamewa jama'a karfa,kar dai yaron nan dan yanka kai ne muna zaman zaman mu lafiya ya cucemu, koda yake ai kince abokin ma'aruf ne?
ummita ta daga mata kai .
"kin ma sanshi fari sani , nima wallahi tsoro yake bani hatta kayan ma tsoronsu nake ,dan Allah mama a fitar dasu waje kawai a zubar , cikin haka su Maryam suka fito suka bi kayan da kallo kafin daga baya suka isa ga kayan "kar dai bakon ne ya kawo mana waɗan kayan ?
Meenal ta tambaya tana duba kayan daya bayan daya "shine kayan da suka 'batawa ya rayhan dina rai, baki ga yadda gaba-daya ya sauya ba Ni dai mama dan Allah asan yadda za'a da kayan nan if possible a fitar dasu a zubar.
"kin jiki da wata magana a'a bola za'a kai ba fitarwa ba inji meenal "kunga ni ki hado min nawa kawai nasha sha'anin dasu "kunga ni ku tattara kayan ku mai dasu cikin ledar na kaiwa abbanku yasan halin da'ake ciki kar daga baya yaga laifina "
"A'a mama karki nuna masa dan ni daga yau bazan sake fita ba tsoro yake bani ...
"Dole ki fita yarinya matsawar baki tsaida na aure ba , nifa aure nake son kuyi gabad'ayanku Allah dai yayi muku zabi na alkhairi tayi maganar tana nufar kitchen ..
Ganin yadda uwar gidansa ta rude lokacin daya fara ƙoƙarin duba kayan yasa yayi kokarin kwantar mata da hankali duk da shima al'amarin ya daure masa kai ,kalamai masu taushi ya shiga jero Mata, dan ta samu natsuwa yace "kinga ajeye min kayan anan gurinki idan Allah ya kaimu zamu haɗu da injiniya musan abun yi ...
*******
Ma'aruf iya tunaninsa ya tafi ne akan yayi aure ya tattara ya bar gidan ,ya daina ganin ummita, dan ganinta kaɗai na haddasa masa cuttuka kala daban daban, dan haka a daren ranar da kanshi ya samu Abba da zance , ahankali yake sanarwa Abba batun yana son aje masa gidansu suhaima neman aurenta..
Abba yayi shiru kafin daga baya yace " shikenan Allah ya bani iko "waye mahaifinta kuma a wani unguwa suke ,?
"Nan take yayi wa abba bayanin komai akan suhaima , bayan fitarshi da kamar minti goma mahaifiyarsa hajiya ummah tashigo kasancewar itace da girki, anan abba yake sanar mata abinda ma'aruf yake da bukata, murumushi tayi tace "haba baban yara , karma ka sauraresa duka yaushe ya soma aikin, kuma ma idan auren zai yi ai ga sakina gidan baba sarki nan ,yarinyar tana sonshi sosai , gida bai koshi ba za'a kaiwa waje ,bama haka ba ni fa ina da wacce zuciyata tafi kwanciya tayi rayuwa dashi ..
"Haba uwar marayu da yake hakan yake ce mata a tun sanda marigayi yayansa ya rasu "karki ce haka kiyi hakuri karki kawo masa matsala da aurensa ,ki barshi yayi yadda yake da bukata, kowa da ra'ayinsa ta yiwu da zabin naki da ita sakinar baya son daya daga cikinsu ,kiyi masa addu'ar Allah yasa ita yarinyar da yake so mai tarbiya ce "umma tace shikennan tun da haka kace ,Allah ya tabbatar da alkhairi amman idan son samu ne ya haɗa da sakina ya aurensu duka "
Abba yayi murmushi "hakan ma karawa yarona kwarjini zai yi ,sanan kuma d'ana yana da mazantakar da zai rike mata har hudu ba biyu ba ......
murmushi umma tayi "Allah idan bai aure sakina ba a yadda take son shi ba za'a shiga damuwa , taki kulawa kowa fa ,shi kuma da zarar anyi masa magana yace yayarsa ce ,shekarursu fa daya daita kwana arba'in ne a tsakaninsu "Allah dai ya tabbatar da alkhairi zamuyi magana dashi muji idan yana da bukatar haka duk mai sauki ......
********"
Kwanaki dayawa kenan da ummita taga ma'aruf ya fita harkar kwatakwata ko kallon inda take baya yi, duk abinda zata yi baya daga idanunsa ya kalleta , ta daura ayar tambaya akan lamarin, tunanin duniya tayi amman ta rasa gane dalili faruwar al'amari , a karshe zuciyarta ta fahimtar daita wata kila faɗa sukayi da sahebarsa suhaima , tunda gashi kwana biyu bata ji yace wa mama suhaima tana gaisheta ba, ko zama ayi hirarta da sauransu , taja tsaki ,"ai duk inda kaje neman aure da wannan mugun halin naka ,tsiya tsiya zaku rabu , babu shegiyar da zata 'batawa kanta lokaci akanka ,duk wata mai cikakken hankali da sanin ciwon kanta ba zata aureka da wannan bakar zuciyar taka ba .
"mutun da bakar zuciya kamar ta mutane farko ,tabbas faɗa ma sukayi tunda har a fuskar wayarsa ya cireta saɓanin da da itace akan wallpaper dinsa .....
A bakin kofar shiga part d'insu ta hangoshi tsaye rungume da hannuwansa duka akirji sanye cikin riga ta shirt ja da wando baki , yayinda gefenshi abokinsa jafar ne tsaye suna magana kasa kasa, tamke fuskarta tayi sosai tamkar wacce aka aikowa da sakon mutuwa ,tun daga nesa take kallonsu a wulakance
har takaraso bai yi kokarin matsawa a bakin kofar ba ,haka itama bata bude baki tace masa ya matsa ko zata wuce ba ,ta gefen jikinshi tabi ta raba tare da matse jikinta dan kar ya hadu dana shi, amman duk da haka sai data goga kafadarsa ta wuce ta kiyi masa magana ,sosai yaji zuciyarsa ta buga wani irin haushi yaji ya caki tsokar dake makale da kirjinsa kamar ya janyota ya waska mata mari amman ya kyaleta saboda tunanin maganar mahaifiyarsa ,
Shi ne abinda ya katse masa hanzari ,dan haka ya sauke hannuwansa ya tura cikin aljihun wandansa yayi hanyar harabar gidan batare daya cewa jafar komai ba , biyo shi jafar yayi a baya yana masa magana "na rasa gane kan wannan tsana dake tsakaninka da yarinyar nan ummita yaruwarka ce fa babu .....
"dakata dan Allah malam ya tsaya cak tare da juyowa yana fuskantar shi "me ye ruwanka ko me ye damuwarka ?
"Babu jafar ya bashi amsa a takaice ..
" To daga yau babu ruwanka da wata yanuwantaka dake tsakaninmu daita , dan muna yan'uwa sai akace ta dinga min abinda taga dama, kai ma kasan abinda take min amman sam baka ganin laifinta sai nawa ..
"Dan haka karka dame ni, kai kar ma ka sake min zamceta kayi abinda ya kawoka ka kama gabanka .....
Ya K'arasa maganar yana sake juyawa ya fita daga gidan gabad'aya...
ya karasa kofar gidansu ya zauna akan dogon banci , shima jafar zama yayi a kusa dashi bai sake yunkurin ce masa komai ba, a qalla sun kusan minti talatin zaune babu wanda yace kala ,a hankali jafar yaja qaramin tsaki bai san me ya kawo shi gidansu ba gashi ya bata masa rai a karon banza, daga gyara kayanka ....
har kusan la'asar Ma'aruf bai da niyyar sake yi masa magana tun yana charting da shiga bangaren adana lambobin mutane har ya gaji ya hakura ya mike ya soma ƙoƙarin barin gurin ,kallonsa kawai ma'aruf yayi yana ta'be baki sannan ya mike shima ya koma ciki yana furta shishigin banza kawai .. ... ..
******
Kullun muhd Sa'id zai zo gidan da zumar ganin ummita amman baya samun ganinta, yayi kokarin samun numberta agurin yaran gidan, amman tunda ya kira taji shine ta katse kiran bata sake ɗauka ba, hankalinsa ya tashi matuka kamar wani zautacce ya rasa yadda zai yi, ma'aruf ne kaɗai zai taimaka masa shi kuma basa shiri suke daita ba , gabad'aya ya kasa hakuri ya tabbatarwa kanshi da dole sai ya dangana ga Ma'aruf zai samu mafuta ...
****
Ma'aruf ya fita harka ummita kamar yadda mahaifiyarsa ta umarceshi, sai dai tsanarta na nan daram acikin zuciyarsa babu abinda ya ragu ..Yayinda
itama hakan ce gareta ....dan tsanar da tayi masa tana nan daram acikin zuciyarta ,wanda Ita kanta wani lokacin ta kan yi mamakin me yasa ta tsaneshi irin haka alhalin suna yanuwan juna ?
Ta tsaneshi ya tsaneta irin tsanar da zai so yaji wani mugun abu ya sameta ,itama yanzu da'ace za taji wani mugun bala'i ya sameshi dadi zataji sosai ...
A hankali ya sanyo kai zai shigo parlour'n mama , yaji tana bugan cikin mama tana son taji da gaske auren suhaima zai yi ko da wasa ne ba yi zai ba , tana son tasani da gaske ne abinda take son ta tabbatar kenan ...? Ya tsaya yaki shigowa zuciyarsa na dokawa da sauri
Muryarta ya sake jin ta doki dodon kunneshi "Da gaske mama zai aureta ?
"ban da abunki ummita ai wannan nufi ne na Allah "Kai mama babu wani aurenta da zai yi ,zai dai yaudari yar mutane ne kawai ba aurenta zanyi ba," ya shirya auren ne, idan ma auren zai yi yana da kudin auren ne ?
abinda ta faɗa wa mama ya bala'i tsaya masa arai ya ɗan cigaba da tsayuwa yaji me Mama zata ce " ai shi kudin aure ba'a tarasu ummita kuma ai yana da aikinsa ko...?
"Yaushe aka soma aikin da zai wani tattago muku aure, dan nasan Abba dake kawai yake son wahalarwa dan yasan ba sisinsa da zai kashe idan ma auren zai yi ...
"Ke kuma kina bakinciki ba ?
"Wallahi kamar kin sani mama ,idan kika ji yadda zuciyata take bakinciki idan Abba ko ke kuka yi masa ba..
"Banason cigabansa mama ,duk abinda zai zama bakincikinsa dadi nakeji, farincikinsa haushi zake ji ,"kul ummita bana so ..
"Bana son kina faɗar haka akansa "ki fita hanyarsa ummita ki daina masa mugun alkaba'i, idan baki daina ba zaki samu matsala dani"ai nasani mama kinfi son shi dani "kwarai kuwa shi nasani kafin na sameki a duniya ,ki daina masa mugun fata kinji na fada maki...
"To naji ...
"Ba to kinji ba kice kin daina "
"Na daina ta karasa maganar tana turo baki sai da yaji sunyi shiru sannan ya shigo bakinsa ɗauke da sallama mama na ganinshi ta saki fuska tana murmushi tare da amsa masa sallamarsa ita ko ummita duk da sanin mahimmanci sallamar kin amsawa tayi dan shima haka yake mata duk lokacin da sautsayi yasa ta shigo inda yake da sallama batare da sanin shine ba baya amsa mata , ya samu guri kan kujera mai zaman mutun uku ya kwanta yana "furta washhhhh Allah nah .."sannu ka gaji ko ya aikin ?
"Babu dadi mama munje mun tadda aiki sosai ,"to Allah ya taimaka yayiwa rayuwa albarka ,yace "ameen mama na gode sosai ina alfahari dake "nima haka a kawo maka abinci ?
"Sai zuwa anjima yasan ko yace a kawo fat lion ce zatayi ....
a parlour'n ya dauki shiru can ummita tace "mama ki aramin caza ,mama tace bazan bayar koda nasan inda tawa take bare banganta ba , ke ina taki?
" ta lalace tun zuwan su Maryam da tawa suke amfani fashi sun lalatawa mutun kayanshi ta k'arasa maganar cike da shagwa'ba " sai ki hakura ko kuma ki tambayi yayanki Ma'aruf tashi, ta kalleshi kawai ta watsar dan bazata iya tambayarsa ba ko mutuwa zatayi Gara ta margaya akan ta tambayeshi abu .....
Mama ta mike ta bar part din zuwa bangaren Abba dan itace da girki cikin haka sai ga maryam tashigo parlourn tana need din caza,ummita ta ta'be baki "gashin ta lalace sai kowa ya hakura " kai ummita ban da wulakanci fa "wallahi batayi nima yanzu na gama karamar murya agurin mama Amman ta Hana , Kawai Maryam taga tashin Ma'aruf da sauri tace "a'a ya Ma'aruf a she ka dawo ina yini ?
Bai kula ba ya dauko mata caza mai baki biyu dana iphone dana blackberry , har maryam ta juya ya kirata yace" gashi kiyi caji idan kingama ki ajiye min fuskar Maryam cike da mamaki tace" tau.....
Na gode Allah ya saka da alkhairi ...bai ce komai ba ya fice daga part din gabad'aya ..
Yana fita, aranta tace "anyi abu arziki nasan dan naji haushi ne ya baki ,taki na cika zan yi maza nasa tawa , dan mai mugun halin tsiya ...
Washegari da safe sai yaga cazar a hannun ummita a wajen kanta da alamun agurinta cazar ta kwanta dan yasan Maryam ba part din mama ta kwanta ba, kar'ba tayi a hannunta tayi amfani dashi bai yi magana ba dan baya son abinda zai sake hadashi daita ya dauki cazarsa ya saka cikin ajihunsa ya ƙara gaba .
*******
Tsawan watanni uku kenan da soma aikin ma'aruf kuma har lokacin bai taka zuwa gidansu suhaima ba, iyakacinsa daita waya shima ba koda yaushe ba, tayi naci tayi kuka amman yaki zuwa sai dai yayi alƙawarin duk randa aka je masa zai cigaba da zuwa gurinta kamar da, ɗan bazai juri zuwa tana cazashi da salonta ba .. ....
Two friend's (bsbs)
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~TRUE LIFE STORY~
FREE NOVEL NOT FOR SELL
AL'QALUMAN
*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*
~DEDICATED TO~
*JIKAR KULU*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
PAGE 14
......kamar yadda ma'aruf ya fahimtar da Abba cewar aure yake da bukata , haka shima rayhan ya cire kunyar dake tsakaninsa da abba ya sheida masa cewar ummita yake so da aure , wannan al'amarin yayi mugun d'agawa Abba hankali matuka, saboda a tsarinsa ba rayhan yaso ya auri ummita ba ,amina yake da burin bashi a matsayin matar aurensa ,ita kuma jiddah ta auri malik , amman babu yadda zai yi tunda har shi yaron ya rigada ta furta .
dan haka cike da sakin fuska ya bayyana farincikinsa a fili tare da sanya wa lamarin albarka , Abba bai yi sanya a gwiwa ba a ranar ya nemi d'an'uwansa daya rage masa a duniya injiniya sagir ,wanda ya kasance mahaifi ga rayhan . ....
Injiniya sagir da Ibrahim wato abba da mahaifin ma'aruf shuaib ,da mahaifiyarsu aslamiyya ummasalma , uwarsu daya ubansa daya , dukkaninsu ya'ya hajiya inna ne .
Shuaib shine babba , sai Ibrahim sai sagir wanda suke da tazara sosai atsakaninsa da Ibrahim , dan hajiya inna tayi bari biyu kafin ta haifeshi ,sai auta ummasalama ..
Sun taso cikin gata da kulawa agurin mahaifinsu alhaji Ma'aruf wanda ya kasance haifanfen jahar lagos , iyayensu ne suka zo cirena suka haifesu babu laifi mahaifinsu alhaji shehu shinkafi tsayayyen namiji akan iyalinsa yana da rufin asiri daidai gwargwado , yana daya daga cikin masu sauke abinci kayan masarufi acikin garin agege yana manya manyan shaguna a kwakwauku da ake sauke masa wake ,giro da duk wani nau'i na masa rufi ,ya shahara sosai ata wannan Sa'a, duk wanda ya kwana ya tashi yasan da zaman alhaji Shehu , ta kowani bangare yana kula da yaran sa da ƙoƙarin ganin ya basu wadataccen ilimi ,duk cikin yayansa babu wanda bai yi karatun boko ba dana addini ba sannan babu wanda bai mallakawa shago kayan masarufi domin tsayuwa bisa kafafunsa ,haka suka taso har girmansu maza suka yi aure haka ma matan sukayi suka gina babban family ..
a tun farko tasowarsu shuaib da Ibrahim sun taso da rufin asiri sosai ,yayinda shi injiniya babu , dan ko aiki ba yayi a lokacin ,duk da ya kammala karatunsa .
injiniya yayi karatu sosai , dan shi bama a kasar yayi karatu ba, yayi karatu ne a karkashin gwamnati jaha sakamakon injiniya sagir Ma'aruf akwai tarin ilimi dan akwai shi da nacin akan karatu .
gabad'aya karatunsu tun daga primary har zuwa University anan kasar sukayi , injiniya ne kawai yayi a wata ƙasa, ya fito da mafi kyawun sakamako kamar sauran yan'uwansa , basirarsa yasa jaharsa ke alfahari dashi , sai dai lokacin daya gama karatunsa ya dawo kasarsa ya rasa aikin yi ...
bai dogora da tarin dukiyar da Allah yayiwa yan'uwansa da danginsa ba ,sannan bai nakasa zuciyarsa ya koma zaman jiran tsammani daga garesu ba ,ya samu aiki a hukumar nepa , har zuwa sanda ya taka matsayin da yake yanzu da taimakon yan'uwansa , shekararsa biyu a ma'aikatar nepa ya samu canji wajen aiki zuwa hukumar kasa (land and survey) lokacin ummasalma tana matakin karshe a secondary ..
Shuiab da fatima auren zumunci akayi musu wato mahaiyar Ma'aruf da mahaifinsa ,ita hajiya fatima wacce ta koma hajiya umma a yanzu diyar yayan hajiya inna ce da suke ciki daya, asalima a hannunta ta taso har zuwa , lokacin data isa aure, shuaib ya ganta yace yana so cikin yarda Allah suka daidaita kansu har ta kai su ga aure .
shi kuwa Ibrahim a wani zuwa daurin auren abokinsa da yaje kasar cotono yagano mairo mahaifiyar ummita ,
Wanda ya rage sauran shekara daya ta kammala karatun ta na zama malamar likita .
"tunda ya daura idanunshi akanta ya rasa sukani da walwala har sai da yasa akayi masa magana daita ,mairo bata kasance mai son kula samari ba, amman haka nan taji zata iya kula Ibrahim saboda kamewar dake tattare dashi , cikin sa'a bai sha wata wahala ba ta amince da soyayyarsa .
bayan ya dawo gida yake sheidawa d'an'uwansa shuaib komai akan mairo ,kuma ita yake da burin ta zamo abokiyar rayuwarsa , shuiab ya jinjina girman al'amarin "lallai kace rabon amarya ne ya kai ka kwatano ina cewa kaje kana kin zuwa , Ibrahim yayi murmushi "wallahi yaya da farko ma ban so zuwa ba sai daka matsa a she akwai abinda Allah ya boye har yasanya min son tafiyar "to Allah ya tabbatar mana da alkhairi amman bahaushiya ce ko ?
"Eh to hausawa ne amman zaunanun garin ne ,dan acan aka haife iyayenta da kamaninta sai dai ta sheida min asalinsu 'yan auyo ne dake karkashin jahar jigawa zama ne ya kawo kakanninkakaninta ......
"Shikennan zan yiwa hajiya inna magana , shuiab bai yi jinkirin sheida wa mahaifiyarsu ba , tashin farko Hajiya inna ta hau bala'i " bata yarda a auro mata diyar agumawa jikar agumawa masu tallan kifi ba ,dangin matsiyata waɗan a kamun kifi zasu kare ...
Shuaib yayi kokarin yi mata bayani akan tushen yarinya kamar yadda dan uwansa yayi bayani amman fur taki tsayawa ta sauraresa , abu kamar wasa Hajiya inna taki auren Ibrahim da mairo, juyin duniya shaiab yayi daita tace" sam bata yarda ba , yayita bata hakuri da rarrashi saboda baya son dan uwansa ya shiga damuwa amman taki ....tace " tafi son ya auri real hausa babu jagwalgwalo ..
a lokaci tuni Ibrahim da mairo sunyi nisa a duniyar soyayyar da suke jin duk duniya babu wanda ya isa ya rabasu, wasa wasa hajiya inna taki amincewa har sai da magana ta kai gurin baba sarki wanda ya kasance kani ga mai gidan ita hjy inna wato kanin mahaifinsu Ibrahim , nan fa ya shiga yi mata nasiha da wa'azi ,tunda dai yarinyar muslimai ce ai aurenta ba zai zama da wani aibu ba , tayi hakuri ayi tunda shi Ibrahim din yana son yarinya , ta ɗauka wannan auren kaddara ce , da kyar dai sarki aminu wanda kudinsa ne ya bashi sarauta kamar yadda sarautar zamani ta gada ya shawo kanta ta yarda , a lokacin an haifi Abdurrahaman har ya kai shekara uku ..
batare da wani bata lokaci ba baba sarki ya taka har kasar kwatono domin nemawa Ibrahim auren mairo ,sai dai cikin rashin Sa'a suma iyayen mairo suka ki batun auren ,a cewar su bazasu bada diyarsu tillo mace ba , dan mairo ita kadai ce mace acikin family dinsu gabad'aya , duk maza ake haifa mazan ba wasu masu yawa ba duk daki bai fi ayi haihuwa maza biyu ba ,kamar yadda suke a d'akinsu maza biyu sai ita , shiyasa suka dauki son duniya suka daura mata basa son abinda zai nesanta ta dasu ,
sai da aka kai ruwa rana sannan suka ce zasuyi shawara a tsakaninsu , a wani zuwa da baba sarki yayi wanda shine zuwansa na biyar....
A lokacin tuni mairo ta daga hankalinta akan lallai ita Ibrahim take so, muddin basu bashi aureta ba ba zata taɓa aure ba , koma zata gudu ta barsu bazasu sake ganinta ba ,nan fa hankalin danginta yayi mugun tashi ,dan Allah yayi agumawa da son ya'ya barin ita tilo ,sannan suna kokarin suga sun bawa ƴaƴansu abinda suke ,sun amince
da zumar sai sun tura wani daga cikinsu zuwa kasar nigeria domin sanin inda dangin Ibrahim suke, hakan ce ta kasance musamman suka haɗa baba sarki da wakilinsu, ai kuwa wannan abu ya sake tsayawa hajiya inna rai, taji kamar ta mutu dan bakinciki , kwata kwata taji bata son mairo a ranta ,ta dinga bala'i "dan me za'a ce baza'a bawa Ibrahim dinta aure ba ,me aka fishi ?
" gata ko dangi diyar tasu fin shi tayi , ko diyarsu zinari ce ko me ?
"ko ma dai menene gashi kingani ,baza ziniri bace agurinki amman tafi zinari agurin danginta , dan da kinga bakar wahalar da muka sha da shuiab akan wannan yarinya ,da kanki zaki kirata da lulu'u karewar zinari saboda sanin darajarta , dan har ruwa muka tsallaka zuwa wani yankinsu ,kuma ita yarinyar nan ita Ibrahim ɗinkin ya gani yace yana so ,ya tsallake tarin yammata yan'uwa dana ƙasar shi, yaje wata kasar , ke dai abinda nake so dake addu'a Allah yasa alkhairi ce a tare dashi ....
A tsakanksnin wannan lokacin akayi auren mairo da Ibrahim bayan tarin dukiyar da iyayenta suka amsa bisa al'adar su ta agumawa , nan hajiya inna ta sake yarda da lallai mairo daban take acikin mata , amman da yake tsanar yarinyar ta rufe mata ido ta dinga zaginta tun kafin a kawota , duk wanda yazo mata Allah yasanya alkhairi ,"sai tace " kun taya ni dai da addu'a dan Ibrahim ya daukowa kansa bala'i da kanshi ,kunga abinda aka kashe ?
"An kai musu kudin kimanin miliyan ɗaya, bayan motar doya dasu manja komai dai na kayan abinci tamkar wasu dangin mayu , har da kwalekwale jirginsu su din kama kifi sai daya siya , ga kayan sakawa wai da kayan mijin ake fitar biki , Allah bai yi musu arzikin siya mata kayan fita biki ,wannan bala'i tsiyar da me yayi kama ?
Wasu su bata hakuri suce tayi addu'a ,yayinda wasu su ke zugata ..
Ibrahim ya gina gidansa da zasu zauna da amaryar amman inna tace sam bata yarda ba sai dai akawota nan gidan bangarensa , tun da mairo ta tare a gidan bisa umarnin hajiya inna , ta fuskanci akwai matsala domin ta lura da inna bata sonta domin kiri kiri take nuna mata kiyayya ..
Mairo ta ɗauki damarar hakurin zama daita da halinta ,dan bata da yadda zatayi ,ko babu komai uwar mijinta ce ,uwar miji kuma ba'abar wasa bace ,itace mafi girmamawa arayuwarta , tunda itace matar da ta haifa mata miji bare miji irin Ibrahim, ai dai komai zatayi tayi amman ta barta tayi rayuwa dashi ...
Iyayen mairo basu kawo mata komai ba ,daga sai wasu mata guda biyu suka kawota kuma sunan basu tafi ba suna jiran sauran yan'uwansu k'araso , sunyi kokari gurin kayan daki dan basu tsiya komai a kasar ba ,sai da suka zo Nigeria ,duk abinda ake na al'adar ƙasar shi suka saka mata a daki, tun nan inna ta raina kanta ta fahimci ba wai talauci da tsiya yasa aka amshi tarin dukiya daga hannun Ibrahim ba ,dan abinda aka saka mata a d'akinta ya haura miliyan uku , kudi na gugan kudi million biyar mahaifin mairo yasa aka damkawa Ibrahim check a hannunsa domin ya kara jari acewa, sannan yace su shirya shi da yan'uwansa da mahaifiyarsa zuwa kasa mai tsarki , suma tsaye inna tayi a lokacin da taji labarin bakin zagi ya mutu murussss ita da masu zagin ba'a kawowa amarya komai ba ..
Duk da wannan hidimar da akayi hakan bai sa inna taji kaunar mairo acikin ranta ba asalima sai kushe arzikin take ...
*******
Yan'uwa mairo sun sake damka amanarta a hannun hjy inna da fatima ,ita dai fatima ta amsa amana da zuciya daya habiya inna kuwa acikin zuciyarta take furta ban amsa ba dan bazan rike wata amanar diyar agumawa ba ...
Tun sanda mairo tasoma girki zata kawowa hajiya inna amman bata amsa tace" ita bata ce kayan karni ...
haka mairo zata juya da abincinta ,bai hana gobe idan tayi ta sake kawo mata ..
A sheakarar suka sauke farali amman banda Hajiya Inna da tace bazata , dan maka ita ba bakuwa bace taje, tayi maimaici har bazata kirga zuwanta ba , ita yanzu sai dai akirata da hajijiya ba hajiya ba....
dole aka maye gurbin kujerarta da hajiya Fatima ....
Bayan sun dawo aikin haji Ibrahim yaso mairo ta cigaba da karatun ta amman Hajiya inna tace sam ai tagama karatu ,su a daginsu matar aure bata zuwa karatu ta zabi ko aure ko karatu ,i dan kuma yawon tazubar za'a tafi na halin agumawa to a faɗa mata tasani , duk yadda Ibrahim yaso ya fahimtar da Inna Amman taki yayi shiru yana sauraronta inna ta hana mairo karasa karatunta amman ita tata diyar tana can jami'ar Ahmadu Bello University , to shi daman Ibrahim mutun ne nagartacce ga al'ummar unguwa ma sun san da biyyayarsa da dadin mu'amula bare akan mahaifiyarsa haka ya kau da idanunsa domin yiwa mahaifiyarsa biyayya ...
Bayan shekara daya shiru mairo ko batan wata batayi ba, nan hajiya inna ta sake ɗaukar karan tsana ta daura mata duk abinda tayi sai tace bata iya ba ko tace za'ayi musu halin agumanci "bata da aiki sai kiranta da juya dangin agumawa masu tallar kifi ,kaje ka dauko marasa irin haihuwa ,
kalmar dai tsiya da talauci babu ita dan idanunta sun gane mata zahirin wacece mairo , har zuwa lokacin da injiniya ya auri saudat diyar baba sarki inna bata canzawa mairo ba ,da auren ma babu abinda batace ba,"wannan shine auren da take so kuma take alfahari dashi ,Hausa da Hausa ba wake da shinkafa ba , auren saudat babu jimawa ta samu ciki ,wata tara cif ta haifo dan namiji yaci sunan malik .
Bayan wani lokaci ta sake yin wani ciki ,nan fa salo iri iri ya tashi gabad'aya ta koma gidan Inna ,tare suke zaman zagin mairo,sam inna bata son laifinta har manufuka Tasha Kiran Hajiya ummah wai saboda taga arziki shi yasa take shigewa mairo, a daidai wannan lokacin hajiya ummah itama ta samu cikin Ma'aruf nan damuwa ya taru yayiwa mairo yawa ,haka zata zauna ta dinga kuma tana kaiwa Allah kukanta, tunda har asibitin kasarta taje likitoci sun tabbatar mata da lafiya lau mahaifarta take , at any time zata iya samun ciki ,suka ce tazo da mijinta a duba ko daga garesa ne , shima koda aka gwada shi lafiyarsa lau kwayakwansa na move shima mai haihuwa ne, dan haka suka mika lamarinsu ga Allah tare da bautawa yaran yan'uwa duk dan da mairo tagani ta makale saboda Allah yayita da son yara ....
Saudat ta riga hajiya umma samun ciki amman cikin ikon Allah Hajiya umma ta rigata haihuwa ...
tsiransu kwana uku,
Dan haka aka haɗa suna, ranar suna dan hajiya umma yaci Ma'aruf sunan mahsifinsu ,yayinda dan saudat yaci sunan Aminu sunan baba sarki , tun da aka haifi Ma'aruf hajiya Inna ta ɗauki soyayyar duniya ta ɗaura masa, haka mairo itama tana son yaran duka itace ke d'awainiyya dasu barin Ma'aruf wanda tun da aka haifeshi uwarsa take cewa "mairo kinyi da ,ki shirya wannan d'anki ne halak malak dul sanda taji haka sai mairo tayi kuka dan murna "na gode yaya da karamanci wallahi koda baki mallaka min mai sunan baba ba naji dadin da wannan mutuntaka Allah ya raya mana shi .."ki daina kuka kema zaki haifi naki ,sai kin rike naki da hannunki lokaci ne , kowa da lokacin da Allah ya gaddaro masa ki daina sanya damuwa aranki ..
Da waɗan kalaman take jin sauki acikin ranta ..
Ita kuwa saudat bata son mairo na daukar mata yaro , sakamakon tana bayan inna yayinda ita hajiya ummah bata yarda da hakan ba ,suna shiri da mairo sosai saboda tana da saukin kai ,hakuri da sanin yakamata uwa uba kawaici akan komai idan ba'a an faɗa maka asalinta ba bazakace agumawa bace , Hajiya inna da saudat kullun cikin zagin mairo suke lura da hakan yasa injiniya ya hauta da bala'i yace idan batayi hankali ba zai iya sakinta akan mairo hakan yasa ta ɗan saduda ta rage shiga ɓangaren inna ..
Ma'aruf ya shaku sosai da mairo domin shine ya rada mata sunan mama har mama ya bita ,duk inda tayi yana biye daita ,itace koman shi, kashinsa fitsarinsa wankasa
lokacin da ya isa yaye Hajiya ummah ta damkawa mairo shi amatsayin na wacce zata yayesa ,hakan ko yayiwa inna ciwo dan duk cikin jikokinta tafi son ma'aruf saboda sunan mijinta da akasa masa babu bala'i da batayi a karshe ta dauko shi ta dawo dashi gurinta "idan fitsari abun yi ne kaza tayi ,aiko ranar bata runtsa ba ,yadda taga rana haka taga dare ,dole ta lallaba ta dawo dashi ba dan taso ba ......
A wani zuwa da yayan hajiya mama yazo da matarsa kawo mata ziyara, yaga irin wulakanci da'ake mata akan yara ,shine yayi mata alkwarin ida zai dawo zai kawo mata dansa usman .....
Wata rana mama na zaune tana kukan bakinciki abinda hajiya inna take mata da saudat , hajiya umma tashigo dakin hannunta rike da jakar kayan Ma'aruf , ta risketa cikin wannan hali tayi saurin ajiye jakar hannunta, ta karaso gareta tana dafa kafad'arta "menene mairo mai ya sameki ?
Gaba-daya ta rud'e kamar ba kishin sauri ba "ta d'ago kanta ta goge hawayen fuskarta "babu komai "matsalar haihuwa ke saki zubda hawaye ?
Hjy mama tayi shiru ta kasa magana "nasan itace kiyi hakuri wallahi idan da rabo zaki haihu idan kuma baki da rabo haka zamu hakura mu ɗauki hakan a matsayin *WANNAN CE QADDARARMU* amman ina muku fatan samu naku keda ibrahim ,kuma inshaallahu zaku samu "na gode sosai "karki min godiya ban daukeki matsayin kishin sauri ba matsayin kanwa na daukeki ,Ibrahim dan uwana ne iyayenmu uwa daya uba daya ko babu aure tsakanina da d'an'uwansa, ke din matar d'an'uwana ce ki kwantar da hankalinki ina matukar sonki har cikin raina , ga kayan baba can na kawo miki , ta nuna mata inda jakar kaya yake ,mun mallaka miki shi halak malak, nasan zai samu riko na mutunci da kyautatawa daga gareki tana gama faɗar haka ta mike ta bar d'akin ..
Wannan kyauta da Hajiya umma tayi mata ta faranta mata rai matuka, sai dai bata daura ranta da zuciyarta ba tunda tasan yadda Hajiya inna ke mahaukacin son shi ..
Hasashen Hajiya umma ya tabbata domin hjy mama ta maye gurbinta agurin Ma'aruf ....cikin haka aka kawo mata Usman ,tayi murna tayi farinciki ko yanzu an sake wanke mata zuciya ..
Ma'aruf da sauran yaran gidan duk suka dawo dakin mairo,anan suka taso tare da usman har zuwa sanda aka haifi jiddah ..
Shekarar jiddah biyar mijin hajiya umma ya rasu, mutuwa ta gigirsu sosai dan har sai da Ibrahim ya kwanta zazzaɓi ,
bayan Hajiya ummah ta gama takaba Hajiya inna tabawa Ibrahim umarni ya auri hajiya ummah .
"ka auri Fatima tunda ita wancan taki haihuwa sai wahalar da kanta take akan ya'yan mutane ,sai kuma ci take tana zuba kashi , babu abinda hajiya inna bata faɗa ba ..
Babu yadda Ibrahim ya iya da rayuwarsa haka ya auri hjy umma bisa umarnin mahsifiyarsa da kuma goyon bayan da mairo ta bashi ita kanta hajiya ummah bata so wannan hadin ba tayi ƙoƙarin kauce masa amman yadda mairo ta dinga rokonta tana kuka "yaya ki maimakeni , nasan halinki kinsan nawa ,na kuma san kina sona bil hakki da gaskiya, nasan ba zaki cutar dani ba ,da Ibrahim yaje ya auro wata gara ya aureki tunda nasan halinki kuma a karshe dole zai kara aure saboda bana haihuwa ,ki taimakeni ki amince da auren nan .....
Wannan aure shi ya dan sausauta wani tashin hankali a gidan, tsana da tsamgwama ya ɗan ragu
komai tare suke da Hajiya umma , bama zaka gane kishiyoyi bane babu abinda yake bambamtasu.
A wannan lokacin ummasalma diyar hajiya inna takare University kuma a shekarar tayi aure ,cikin ikon Allah ya albarkaceta da samun haihuwa da namiji wanda yaci suna kabir sunan mahaifin mijinta .. bayanshi ta haifi aysha lokacin da zata yi haihuwa ta uku ne Hajiya umma ta samu ciki murna agurin wannan family ba'a faɗa hajiya inna har da rawa tana cewa "Baga shi ba, ai na faɗa maka dangin juya ka auro ga masu irin haihuwa nan ka aura yanzu za'a soma cika maka gida da ya'ya, wallahi har kunya hajiya umma take ji , a zahirin gaskiya ba ita taso wa wannan cikin ba hjy mama tasowa wannan ciki amman babu yadda zatayi, al'amari Allah ne, bawa kuma bai isa yayi wa Allah shishigi ba, da dai tana da hali da ta cire cikin ta bata ko itama ta zama uwa rayuwarta ....
Two friend's (bsbs)
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~TRUE LIFE STORY~
FREE NOVEL NOT FOR SELL
AL'QALUMAN
*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*
~DEDICATED TO~
*UMMIN KADUNA INA ALFAHARI DAKE*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
PAGE 15
.....samun cikin hajiya ummah yasa gabad'aya hankalin alhaji Ibrahim wanda ya koma Abba bisa koyarwa hajiya mama ,ya kartata gurin hajiya Ummu , wannan abu ya damu hajiya mama matukar kuma abun ya tsaya mata a rai amman ta share taki nuna hakan ko a saman labbenta ta kawo ido ta saka ta sake nisanta kanta dasu tunda daman inna bata son kusancinsu da umma ,a bangaren hajiya umma kuwa babu wani sauyi tana nan kamar yadda suke ada , domin lokacin data lura hajiya mama ta d'auke kafafunta daga bangarenta ,ita bata yi hakan ba ,musamman take zuwa bangarenta su sha hira, ita kam tana tausaya mata sosai " da me zataji da rashin haihuwa ko kuma da damuwar hajiya inna da saudat?
Lokacin da hajiya inna ta lura da shige da ficen hajiya umma yayi yawa bangaren mama, ta dirke sabon bala'i iri iri "tana gudunki dan bakinciki amman kina shishige mata , bari garin neman suna kije ɗan cikin da kika samu a bar miki dashi , agumawa da asiri da bakin kishin tsiya babu abinda baza su iya yi akan kishiya , ke mutun nawa kika ga anyiwa kishiya acikin agumawa an zauna lafiya?
" mutanen da har tsafi suke akan abun duniya ,mutanen duk muslincinsu babu Allah aransu ke ......
"haba inna ki daina furta haka a gabanta babu dadi , wallahi bana jin dadi haka har acikin raina babu wanda ya isa ya baka ko ya kwace maka sai Allah.
"eh lallai wuyanki ya isa yanka fatimatu yau ni nake faɗa kina faɗa akan wannan diyar masu yin su.....?
"Koda yake ba laifinki bane ruwan azirki da kinibibi kika gani ,tunda ke naki uban talaka ne futik ,nan kuma kullum ana kawo miki toshiyar baki da siye miki zuciya daga wancan garin nasu ana baki duk abinda aka kawo mata ai dole ki dinga ganina a matsayin mahaukaciya " ko saudat da ban rike a hannunsa ba , ban ci wahalarta ta sisin kwabo ba , tana bin umarnina tana son abinda nake so ,ai kuwa sai Allah yayi mata albarka ita da ya'yanta .
"kiyi hakuri inna bana nufi na bata miki rai "ki min shiru idan na sake ganin kin tako waɗan tsilla tsillan kafafunki d'akinta sai na tsine miki albarka , ko da ban haifeki ba , naci kashinki kuma sai tsinuwata tayi tasiri akanki maza ki wuce bangarenki shasha da bata san ciwon kanta ba .....
sumi sumi hajiya umma ta fice daga d'akin zuciyarta tattare da bakinciki jikinta har rawa yake tsabar fargaba ,bayan fitarta Hajiya inna ta dubi mama "tam dagin agumawa kul kar naji kar na gani ,kar wani abu ya samu jikin jikin fatimatu dan nasan halinku da mugun asiri tana cikin fadar abinda ta gama ma'aruf ya fito daga cikin uwar d'akan mama "wai ke inna meye haka ne ?
"Kullun baki da abun zaki da aibun tawa sai mama me ta miki tun ba'a haifemu ba kike musguna mata har bisa ga yanzu ni fa wannan hayaniyar tana damun kwakwaluwata , wallahi idan kika sake zaginta zan gudu na bar gidan dan ihunki na damuna ..
inna tayi sororo tana kallon ma'aruf da bai wuce shekaru tara a duniya ba "ai bazan damu ba ko dukana kayi akan wannan abar ba , saboda daga kai har uwarka bakwa cikin hankalinku ,an rigada anyi muku asiri sai yadda akayi daku ..
Ransa a bace ya k'araso gaban inna ya rike mata hannu .ya shiga janta da iyakacin karfinshi "ki bar mana dakin mammamu Usman zo ka tayani mu fitar da wannan matar har usman ya mike mama tayi saurin kamo shi ta rungumeshi ajikinta zuciyarta na kuna da bugawa da karfi .
"Usman kazo mana ya sake faɗa yana cigaba da jan inna "ai nan ba d'akinku bane baba , ga uwarka ce wannan matar ba uwarka bace, ban da sharrin asiri me zai sa mutun yayi kyauta dansa , kalli can ka gani ta nuna masa jikin bango makeken hoton mahaifinsa ne ajiki "wannan shine mahaifinka hannuta ya sake yashiga kallon mama kafin daga baya ya karaso gurinta ya durkusa agaban yaana kallon fuskarta "mama wai ba kece kika haifeni ba ?
Mama tayi shiru ta kasa furta komai dan bata san mai zata faɗa masa ba , "Kece mamammu ni da usman idan bake bace wacece mamana da Usman ,kece kike mana wanka abinci da komai "makira kinyi shiru kina kina ji yana tambayarki ki faɗa masa gaskiya yasan uwarsa , yasan ba kece uwarsa ba ki faɗa masa ke baki da azirkin haihuwa sai mulmula kashi inna ta fadi haka tana dagawa mama tsawa , mama bata san sanda tace "eh bani ce na haifeka ba Hajiya umma ce wsnnan kuma shine mahaifinka ta nuna masa hoton da inna ta nuna masa ...
"yauwa kaji gaskiya yaro dan haka ka daina zakewa ,ma'aruf ya daura kanshi bisa gwaiwar mama "ina sonki mama koda bakece kika kawoni duniya ba ,bare kece mamana ki zo mugu garinku mu bar inna gidan nan ta fiyye bala'i mama tayi saurin rufe masa baki tana girgiza masa kai "aikin banza a haka zaki kare kina wannan kukan naki mara amfani ,kai kuma da kake cewa a gudu kai taɓa ganin zata wancan garin nasu taje da kai sai dai taje da wannan mai idanuwan kamar kifin cikin ruwa saboda shine dolenta ? dan haka daga yau ka sanyawa zuciyarka kai ɗan aro ne gareta ba dan cikinta ba ,dan aro kuwa baya taɓa zama naka tana gama faɗar haka
ta sanya kai ta fice daga d'akin , ranar wuni mama tayi cikin damuwa da kuka ma'aruf da Usman suna rarrashint "tabbas tasan mutanen garin su na asiri amman ita bata san ma a ina akeyi ba, kuma ko tasani zuciyarta bata da muradin cutar da wani daga cikin ahlin Ibrahim ..
Duk inda tayi ma'aruf na biye daita yana bata hakuri "mamana karki damu ki daina kuka idan na girma zan kwatar miki yancinki agurin inna har ma da mamansu rayhan ,bazan sake barin kowa ya takaki ba ,kinji mamana ki daina kuka ya janyo rigarsa yana goge mata hawayen dake zuba a idanunta ta rungumeshi ajikinta tsam "na gode d'ana Allah yayi maka albarka tana son ma'aruf sosai fiyye da Usman tana jin ko dan cikinta bazata yiwa son datake masa ba ....
Bangaren hajiya umma kuwa wannan tashin hankalin da buguwar zuciya da wuni ciki yasa zazzaɓi mai zafi ya rufeta , kwanata biyu tana fama da zazzabi daga karshe sai bleeding , abu kamar wasa sai da aka
danganata da hospital, ai Inna najin batun jini kawai ta daura hannuwanta duka bisa kai ta rushe da kuka "shikennan wannan diyar agumawar ta zubar min da ɗan Ibrahim ,zagi tsinuwa babu wanda hajiya inna batayiwa mama ba, tayi rantsuwa sai mama tabar gidan matukar cikin jikin ummah ya fita , da kyar dai likitoci suka tsaida jini , satin Hajiya umma daya a hospital sannan aka sallamita Hajiya mama kasa zuwa dubo umma tayi saboda tsoron jarabar inna sai dai ta tura ma'aruf yafi sau babu adadi ..
bata san dangin Abba na tsananin son ganin jikinsa a doron duniya ba sai da hajiya umma ta samu ciki ,sai tururuwan zuwa dubiya suke , shima kuwa Abba sai farinciki yake , tana jin zafin yadda abba ya dan sauya mata akan cikin jikin hajiya umma da bai wuce na wata biyu ba amman ta danne taki nuna masa ko a fuskarta sannan ba daina duk abinda take masa ba ..
******
Rukkaya aminiyar mama ce tun farkon kawo mama kasar ,sun shaku sosai itama bata taɓa haihuwa ba alokacin da'akawo mama ,sai daga baya akayi mata hanya gurin wani mai magani a ijoko sugar dake tsakanin ogun state , cikin yarda Allah ta dace dan Allah ya albarkaci da samun diya mace , shine ta til'asta mama da suje ta kaita ko zasu dace amman taki amincewa ,dan haka rukkaya taje mata da kanta ta amso mata magani , da kyar mama ta amshi magani dan cike take da tsoron abinda zai faru inna taga shigowar rukkaya dan bata kaunar ganin wani yazo gurinta ,mama ta soma shan maganinta da aminiyarta ta amso mata sai dai maganin akwai shegen yauki kamar kubewa , da maseefar daci duk lokacin da zata sha sai tashiga tashin hankali amatsayinta na dalibar likitanci tasan ko cikin ma tasamu maganin zai iya barar da ciki ...
Tayiwa rukkaya complain akan maganin "ki cigaba da sha haka maganin yake dacinsa bai hana ki samu idan da rabo ..
hajiya mama ta cigaba da shan maganinta tana kula da Usman da ma'aruf da suka zame mata sanyi idanunta ,kowa ya gansu sai yayi sha'awarsa saboda kulawar da suke samu da gata daga gareta , bata barin yi aikin komai komai ita ke yin kayanta hatta wanka a shekarunsu tara itace ke yi musu a cewarta ko sunyi da kansu ba fita suke yi ba , ganinsu yasa rayhan shima ke makalewa d'akinta ,bata koreshi sai ma janshi ajikinta da take , sai dai idan uwarsa ce tazo ta tasa keyarsa gaba wannan kuma babu yadda zata yi ,ita dai ido ne nata ..
Cikin haka malam na ijoko yace lallai sai an zo da mai shan magani gurinsa saboda akwai hadin da za'a mata kuma dole sai anan zata ci agabansa , mama ta rasa wacce karya zatayi tabi rukkaya suje ,kawai dabara tazo mata tace wa Abba zata garin su tunda duk kusan hanya daya ne, idan taje daga can ta karasa garinsu tayi kwana biyu ta fadawa Abba bai ki ba yace sai ta dawo tare da bata makudan kudi ta haɗa kayan Usman dana ma'aruf duk da tasan da wuya Hajiya inna ta bari dan duk zuwa bata yarda, haka zai karaci kukansa amman bazata bari ba ,abinda tayi tunani shine ya faru dan kuwa hanawa tayi ,Dole ta cire kayansa tana shirin wucewa tace "kema bazaki ko'ina ba dan ban yarda dake ba, zuwa zakiyi kiyi asirin da za'a cire cikin jikin umma , idan kuma kikaje wallahil azim abakacin aurenki da Ibrahim matukar ni na kawo Ibrahim duniya sai ya sakeki idan kika fita, ai bazaki sake fita kije wancan garin naku ba sai fatimatu ta sauka lafiya yar masu mugun halin tsiya wannan lokacin mama na jin tamakar ta biyewa hajiya inna ta faɗa mata son ranta amman bazata iya ba ,bata taso cikin irin wannan rayuwar ba, su sam agarinsu baa zagin babba , ijunansu ma girmama juna suke bare Hajiya inna da ta kasance uwar mijinta ai ko a garinsu akaji ta zageta sai an tsine mata .....
Komawa tayi d'akinta tayi zamanta tare da zabga tagumi har dare lokacin da Abba ya dawo ,yayi mamakin ganinta "baku tafi bane ?
"Inna ta hana ta bashi amsa tana sauke naunauyen ajiyar zuciya ,yayi shiru tare da tsareta da idanu ya kasa gane dalilin dayasa inna take masa haka , yayita bata hakuri "kiyi min hakuri Maryam duk laifina ne ,nine nayi silar komai ,amman kuma nima bani da dabara da "QADDARAMU" dole sai mun kasance a inuwa daya wallahi ban d'auko ki dan na kuntata miki ba ,ki min hakuri ki tayani yiwa mahaifiyata biyayya , dan mu rabu lafiya daita "Ni kuma na dangwama cikin damuwa da bakinciki kensn ?
ta furta haka tana kallonsa "shima kallonta yake saboda wannan shine karo na farko da ta furta wani abu makamanci ta soma gajiya ,ya riko hannayenta duka ya sake tsareta da idanu gbdy ya rasa dalilin da yasa tayi masa tambayar,ya d'ago habarta ya haɗa da nashi "kiyi hakuri "nasani akwai gajiya ni yanzu ko cewa kikayi kin gaji dani bazan ga laifinki ba saboda kinyi hakuri dani iya hakuri , amman rabuwa dake zai sa na dangwama cikin bakincikin rayuwa saboda sonki a jinina yake dan ......
tayi saurin mikewa dan bata son jin abinda zai sake faɗa , tasan yana sonta amman akwanakin nan ya sauya sosai d'akinta ta shige ya biyota , yana sake bata hakuri tana kokarin zubewa kan bed tana kuka yasa hannunsa ya rikota yana dukan bayanta yana bata hakuri ,ki bari muyi baccinmu Kinga yara har sunyi kuka take sosai tana jin kamar ta mutu shi kuma yana bata hakuri har sai datace ta hakura sannan ya barta ya cire kayansa ya kwantar daita ya kwanta abayanta ya rungumeta ranar ko abinci bai ci ba haka ko bangaren umma bai shiga ba .. ..
Cikin Hajiya umma nada wata uku ,mama ta fahimci tana da ciki sakamakon rashin ganin al'adar ta kimanin wata uku dan tun kafin tasoma shan magani amman ta share duk da tun zuwanta bata taɓa batan wata ba sai a wannan watannin baya zuwa wannan lokacin sai take ganin kamar ba gasky bane ..
ta cigaba da rayuwarta sannu ahankali cikin mata na girma da tsine na mama na bajewa da bin jiki ,zuwa lokacin sosai ta fahimci ciki gareta tayi kuka tayi murna ta godewa Allah, da tayi azumi tayi sadaka a danginta babu wanda bai san da samuwar cikin ba ,mota guda sukayi har mahaifinta suka zo dubata sai dai sun kama bakinsu sun yi shiru basu nuna wata alamar abinda ya kawosu ba .. dangin Abba kuwa gaba-daya hankalinsu na kan cikin hajiya Ummu yadda ake boye hajiya umma haka itama take boye cikinta , hatta mai cikin bata bari ya sani ba lokacin dai yaga ta kara kiba tayi kyau ,bayan wasu yan kuraje da suka fito mata a fuskarta babu wata alamar da zaka gane ciki gareta Amman sai da Abba ya dan fahimci wani abu yana cin abinci ya dubeta "ni kuwa maman yara sai nake kallon mai shigar ciki ko ma nace mai ciki ?
Murmushi tayi tare da cewa "Allah yasa hakan ta faru "ameen ina tsananin son naga kin haifa ko daya ne ,cikin jikin hajiya umma ina jin ina ma kece ke dauke dashi "
"Karka damu lokaci dai Allah ya raba duk wata mai dauke da ciki lafiya ..yace "ammen ki ƙara hakuri akan wanda kike dashi ina sonki ina son na kasance dake har karshen numfashina ,a aljanna ki zamo uwargidana malamai dai masu sanyi da kwantar da rai ya dinga furta mata yana janta da hira ...
Two friend's (baba)
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~TRUE LIFE STORY~
FREE NOVEL NOT FOR SELL
AL'QALUMAN
*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*
~DEDICATED TO~
*RAMLAT MANGA ABOKIYAR SHAWARA, ALLAH YA BARMU TARE ALLAH RAYAMANA MUWADDAH SON SO FI SABILILLAH*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
PAGE 16
.....kwasam hajiya inna tazo da tsirfan wani sabon salo, wai abba ba zai sake kwana a bangaren mama ba , bisa hujjarta ta mama bata haihuwa, dan me zai dinga hasarar spam d'insa a inda bai da amfani ,lokaci data fadi haka babu wanda bai girgiza ba ,sannan babu wanda bai ji kunyar maganar ba ,daga yau na kashe maka kwana a wancan d'akin sai dai ka tattara ka koma kwana a d'akin fatima, zai yi magana "no ibrahim don't say anything .... mama saurin fadar haka yin maganar cikin harshen turanci "babu komai inna yaje can din ya cigaba da kwana ita ai tafi bukatarsa kuma dana da can duk daya ne "ko baki ce ba kinibabba , ba zai sake kwana ba ,daga Hajiya umma har Abba basu so wannan tsarin ba, shiyasa duk suka shiga damuwa sannan babu wata mu'amula data sake shiga tsakaninsu, a qalla sai da suka ɗauki wata biyu suna cikin wannan damuwar batare da kowa ya sani ba suna neman mafuta daga Allah , yayinda ita mama ko ajikinta sha'anin gabanta kawai take dan bakincikinta ragu sosai ,a lokacin jin zuciyarta take cike da farinciki , bata jin damuwar komai duk abinda take so iyayenta suna mata , sakonsu kullun yana tafe sannan kafa bata yankewa daga gurin daginta ,idan wannan bai zo ya dubata lafiyarta ba, wannan zai zo ,sai dai idan sun zo inna tayi ta zage zagen ana yi musu zariya a gida ,sam inna bata son ana zuwa gurin mama tafi son ta ganta ita kaɗai cikin damuwa ,haka ta bangaren rukkaya da ma'aruf suna kwantarwa mata da hankali , kusan lokacin ma'aruf ke yiwa mata komai duk tana kokarin hanashi amman baya yarda, sai yace"ai shima ya girma yanzu ba zata sake yin aiki ba , da zarar ya dawo daga makaranta baya zuwa ko'ina yana makale da mama, duk mai son ganinsa sai dai ya biyosa bangaren mama ,mama naji dadinsa sosai , a wasu lokutan tana addu'a ta haifi diya mace ta bawa ma'aruf aurenta idan hajiya inna da danginta basu hana ba ......
Cikin haka injiniya ya samu labarin halin da'ake ciki ai kuwa shi da aunty Salma suka rufe ido suka ki bin bayan karya , suka yiwa inna tatas dan basu fiyye shakkarta ba, barin ma idan sun san bata da gaskiya , hatta baba sarki sai daya shiga cikin maganar sannan Abba ya dawo d'akin mama da kwana alokacin da cikin mama na wata tara Hajiya umma kuma tana wata goma haihuwar ce dai har lokacin shiru babu labari ..
da murnarsa da komai ya shiga d'akin mama kawai yaganta tana tsugunne tana murkususu rike da ciki da sauri ya K'arasa gareta yana kiran sunanta "Maryam! Maryam !! lafiyarki meke damunki?
"ai ko gama rufe bakinsa bai yi ba sai yaga kamar nakuda take . ...
Tsayawa yayi cak cike da matsanancin firgici da tashin hankali ya Daskarewa a tsaye yana sake kallonta cike da mamaki ,mafarki yake ko kuma gaske ne abinda yaga yana ƙoƙarin faruwa agabansa ...?
Cigaba yayi da kallonta ,"yaushe tayi cikin da har zata haihu ? Yayi wa kanshi tambayar idanunsa na tsaye kyam akanta ya kasa karasawa gareta haka ya kasa daina kallonta ..
Sunanshi data kira a galabaice yasa yayi saurin dawowa haiyacinsa gabad'aya ya rasa me ya kamata yayi a lokacin Kawai ya juya zai fita "bari naje na kira uwar marayu ya fita ,da kallo mama ta bishi tana ciza lip's dinta , koda ya shiga d'akin Umma kallonsa take saboda jikinsa da taga yana rawa gashi ya kasa magana illa hannunta daya riƙo cikin nashi sai dakin hajiya mama , a yadda ya barta a haka ya dawo ya sameta tana jujjuya kai , ita kanta umma mamaki tayi , sai dai tafi shi karfin hali ,dan tuni ita takarasa gareta tare da dafata " ikon Allah haihuwa ce nan ta kamota shima ya rikota , ahankali ta furta ga jakar kayan baby can ......
wani sabon mamaki, kenan ita ta gama shirinta na haihuwa, kai tsaye sai asibitin, suna zuwa akayi labour room daita tare da tambayar kayan haihu Hajiya umma ta mika musu karamin akwati ,ciwo kamar jira yake azo hospital sai nakuda zanga-zanga amman baby shiru, sai baby yayi kamar zai tawo sai ya koma yayi zamansa ,iya wuya mama tasha kwanata daya tana cikin wannan halin tun tana kuka ta dawo bata iya komai tace "Ibrahim ka kira min iyayena mutuwa zanyi , babu abinda take iya faɗa sai sunan iyayenta, tsoro ya kamashi kar azo wani abu ya faru daita ya shiga uku ,dan ko numfashi bata iya yi sosai , dan haka ya kirasu , jirgi suka biyo suka zo hankalinsu ya tashi matuka sai dai basu da yadda zasuyi sai addu'a gaba-daya suka tattara hankalinsu akan halin da diyarsu take ,wasu dagan cikin yan'uwa sun zo, amman daga saudat har inna babu wanda yazo suna gida abunsu , hankalin ma'aruf yayi mugun tashi , kasa komai yayi sai kuka yake yana addu'a akan Allah ya raba mamansa da cikin lafiya, ya shiga d'akinsa ya dauko bakinsa da yake ajiya kudi ,ya fasa ya je ya tsiyo sweet ya dinga rabawa yara da niyyar Allah yasa ,ya sake ganin mama arayuwarsa ,duk wanda ya bawa sadakar sai yace kace Allah ya sauki mamana lafiya ,idan baka faɗa ba ya kwace sweet d'insa ya bawa wani , akwana na biyu likitoci suka ce dole sai dai ayi mata aiki ,batare da bata lokaci ba Abba yasa hannu akayiwa mama cs, aka ciro mata kyakkyawar baby girl fara sol tamkar uwarta ,daga hajiya umma da Abba har su ma'aruf babu wanda yabi ta kan baby dan shi ,tun wahalar daya ga mama na sha , yaji ya tsani baby ,dan baya son abinda zai taba masa mamansa .....
Har dare babu wanda yazo daga inna har saudat gara ma saudat mutane basu ga wani laifinta ba , saboda itama jego take , amman duk da haka sai da injiniya ya tambayeta ko taje , tace taje shi kuma bai tsaya tambayar ko tazo ba...
****"
washegari ranar Abba ya shigo d'akin da mama take kwance ya zuba mata ido shi kaɗai yasan yadda yake jin kanshi a halin yanzu tsantsar kaunarta da tausayinta ne suka sake haɗe masa guri daga , ya ciro hancky daga a gaban aljihunsa ya goge hawayen da suka zo masa , tsawon lokaci yana zaune yana kallonta sannan ya tashi ya bar d'akin yana jin ciwon abinda inna tayi masa , har lokacin babu wanda yabi ta kan baby kawai farkawar mama suke son gani .
sai bayan da mama ta dawo daidai sannan Abba ya samu damar daukar jaririya ya dade yana kallonta yana jin dadi da farinciki yana murmushi har sujjada yayi , itama Hajiya umma tayi murna ta amshi baby tana mata addu'a, rayhan da Usman sunfi kowa zakewa gurin kallon baby Banda ma'aruf da har lokacin bai ɗauketa ba, asalima ko kallon inda take baiyi ba ....yana makale da mama kamar yadda Abba ke makale daita .
ranar asabar dayawa daga cikin dangin mama sun zo amman hakan bai sa Abba ya daga kafa ba yana nan manne daita yana sakar mata murmushi ..itama murmushi take tana kallonsa , tunda akayi aikin cikin Sa'a iyayenta suka koma ,kafin mahaifinta ya wuce ya sakar musu kudi sosai yace a kula da mama da babynta shiru mama tayi tana dubansa ta ɗan motsa bakinta sai kuma tayi shiru ya kalleta sannan yaje ya ajiye baby a gadon jarirai ya dawo ya rike hannuta "me kike son ki faɗa naga kamar akwai Magana acikin wannan bakin naki ?
ta maida kwallar data cika mata ido sannan ta sunkuyar da kanta cikin sanyi murya tace "inna kuwa tasan na haihu ?
Ya ɗan yi shiru " gaba-daya ya kasa bata amsar tambayar datayi , shi da akayi tambayar da ita mai tambayar sam babu kuzari attare dasu ahankali ya soma ƙoƙarin zare hannunsa cikin nata tayi saurin rikewa ,yayi shiru yana binta da kallo idanunsa har sun soma sauyawa daga farinciki zuwa bacin rai ,ya koma ya zauna suna fuskantar juna ya rasa me zai ce mata "ta san na haihuwa zuwa ne kawai bazatayi ta gani a inda ba na haifa ba ,na ɗauka haihuwar nan zai sa inna ta kaunace aranta amman shikennan babu komai ta saki hannunsa tana runtse idanunta tashi yayi ya bar d'akin dan ba zai juri ganinta cikin damuwa ba ..
Kwanansu hudu suka dawo gida mutanen unguwa dayawa sun shigo barka sai lokacin saudat tashigo tayi barka, mama ta amsa fuskarta a sake ko minti goma batayi ba ta wuce, da daddare sai ga aunty Salma tazo ganin jaririya ta ɗan dade suna barkwanci sannan tace tana zuwa , ta shiga bangaren hajiya inna faɗa tashiga yi ta inda take fita bata take shiga ba "ai wannan ya Ibrahim kike wa bakinciki inna ,dan shi zakiyi ban da maryam ba, itama me ta miki shekara kusan goma sha ana abu daya yakamata koma mene ne ya wuce an rigada an zama daya , can kuma ta koma rarrashinta kamar zatayi kuka "hajiya kiyi hakuri kije ki duba jaririyar nan bata yi miki komai ba laifin uwarta ai bazai shafeta ba ,da kyar aunty Salma ta tasa hajiya inna gaba suka je suka ga jaririyar da ko darajar ɗauka bata samu ba ,Abba na rawar jiki yaje zai dauko jaririya inna tace "barta tashi zanyi yanzu yana ƙoƙarin magana ta mike tayi waje ya girgiza kai sai da hawaye suka zubo masa "kayi hakuri yaya wannan lokacin bana kuka bane lokacin farinciki ne.
ana gobe suna abba yaje d'akin hajiya inna domin ta bada izinin sunan da za'a sakawa yarinya kamar yadda ta saba bawa sauran yan'uwansa umarni ,sai cewa tayi" kuje ku saka duk sunan da yayi muku amman banda sunana .......
Wani irin yanayi ya shiga mai wuyar misaltuwa ya dade zaune kafin daga baya ya mike ransa a matukar 'bace ya bar d'akin ,ranar suna yarinya taci sunan mahaifiyar Maryam subai'atu ..
Abba ya kashe kudi sosai haka dangin mairo sun nuna bajinta ,domin kuwa su nuna arziki haka abokan mutuncin da mama ke dasu na unguwa wanda sune suka rad'awa jaririya ummita sunyi hidima daita ..
Hajiya umma bata haihu ba sai data cika wata shadaya cif sannan ta haihuwa, kuma a gida kamar yadda tasaba haihuwarta yarinya taci amina ...
Ummita da ameena sun taso cikin kulawa da soyayyar mahaifinsu sun taso tamkar tagwaye ,kusan mama ke rainosu kwasam rashin lafiya ya kama ummita kowa yazo dubata ban da Hajiya inna Abba na kwance akan kujera rungume daita akirjinsa idanunsa a runtse yace "kowa yazo ya duba jikin ummita amman banda Inna, kiyayyar Inna ba'a kan Maryam kaɗai ya tsaya ba har akan yarinyar da bata san komai ba ya shafa.
rashin lafiyar ummita yasa mama ta fidda rai daita , ummita bata bacci ga yawon kuka numfashinta ya sha daukewa haka zasu rude ita da abba ,sai byn wani lokaci numfashin ya dawo ,atsakanin wannan lokacin mama ta rame sosai ta fita haiyacinta, wani lokacin haka zatayita kuka a daki ma'aruf da Usman suna rarrashinta ,yayinda ahankali tsanar ummita ke sake mamaye zuciyarsa, tun haihuwarta har zuwa yanzu mama bata huta ba, kullun daga wannan sai wanan,shi yasa kowa na rubbin daukar ummita Amman ban dashi , har ummita ta cika wata biyar da haihuwa bata da isasshen lafiya babu abinda hajiya inna bata ce ba "ai dole aga ba daidai ba tunda an tilasta Allah gurin neman haihuwa ayi dai mugani idan kalanzir zai yi tuyan kosai , sai da mama ta dangana da kasarta sannan ummita ta samu lafiya a gurin wani mai magani bayan an sage mata gefen bakinta tsagun da yayi mata maseefar kyau kasancewarta fara ..
watansu uku kamar bazata dawo ba sai data ga abban yayi fushi mai tsanani daita sannan ta soma zance komawarta ,
Rayhan na matukar son ummita kusan agurinta yake shiricewa sai ya kwashe lokaci mai tsawo yana tare daita wani lokacin sai dai mama tazo ta tarar sunyi bacci tare ummita na jikinsa ..
*****
Ahankali tsantsar kamanin ummita da mahaifinta ke sake fitowa , babu abinda ta dauko na mama sai farin fata banbancinsu da mahaifinta ita bata cika dariya ba saɓanin Abba dake da sakin fuska ga kowa, haka zalika kamar su ɗaya da ma'aruf hatta dimple da yanayin fuskarsu iri daya , shekarata ɗaya lokacin su ma'aruf suka cika shekara sha daya a duniya , aka fara yi mata shirin birthday din shekara daya dan lokacin tana tafiya har da gudunta ,Usman da rayhan sunyi murna sosai dan har gift suka kawo mata , amman banda ma'aruf wanda tsabar da miskilanci ke hanashi nuna farincikinsa akan komai, ummita na da burgewa da shiga rai kowa yana sonta Banda Inna da saudat tana yarda da kowa amman bada ma'aruf dan ko mama tasa ya d'auketa baya sakar mata fuska sanan baya wasa daita saɓanin Usman da rayhan ..
Lokacin da aka hallara domin birthday dinta kusan kowa yayi hotuna daita Amman Banda ma'aruf Dan yana d'aukarta ta saka kuka, yin duniya taki yarda dole ya sauketa cike da jin haushi tayi kyau sosai kowa yana son d'aukarta ita kuwa mama idan ka kalleta Bama zakace ta haihuwa ba dan babu abinda ya canza ajikinta mutane dayawa sun bawa ummita kyaututtuka ranar ummita tasha kuka saboda gajiya dan kowa nasan d'aukarta ..
Shekara ummita uku yanzu amman har lokacin mama bata sake samun ciki ba haka ma Hajiya umma bata da sai saudat ce ke haihuwarta mama ta godewa da Allah ɗaya bata guda dayan kuma tana yiwa waɗan da basu samu ba addu'a domin haihuwa rahma ce ,kace bari ma wani abu ne yafi ka zauna jugun a daki ..
*******
Dakin hajiya inna nan ne mattara hira , haka jikoki zasu cika dakin manya da kanana, duk lokacin da aka haɗu sai an san yadda ummita tayi kuka, sau tari idan za'a ta dawo mama daita zata ganta da kunburaren baki ko yakushi a fuska da sauransu ko ta tambayeta bata samun wani haske daga gareta dan tayi nauyin baki bata magana sai gwalangwancinsu na yara, yayinda meenal da saada abokan haihuwarta magana radau ,mama ta hana ummita zuwa d'akin inna bata son ana dukanta , amman haka ummita zata yita kuka ita abarta ,yanzu ma kuka take ita zata bi abbanta dake ƙoƙarin fita, amman mama sai kaucekauce take tana kokarin goyata ,Abba ya kalkeshe jikinsa a sanyaye ya janyo mama jikinshi ya rungumeta har ummita "kiyi hakuri ta kalleshi duk tayi kalar tausayi "kiyi hakuri da komai nasan duk ni ja komai dana makale lallai sai ke, ina sonki Maryan tamkar raina bazan iya rabuwa dake ba haka bazan taba canza uwa ba kuma ba zaki raba ummita da inna ba ,ummita jinita ce dole taso zuwa gurin inna ,ki bar min yarinya ta shawaginta cikin yan'uwanta a dakin Inna,kiyi addua Allah ya raya mana ita ,ahankaki ya saketa ya dauki ummita ya dake tsale tsalle ya sabata a kafadarsa ya nufi bangaren inna koda yashiga dakin cike da yara kasancewar weekend ce sunata tsalle tsallensu Hajiya inna na zaune ya sauke ummita ,aiko take tashige cikin yanuwanta, har gaban hajiya inna ya karasa suka gaisa ya dan zauna jin suna hira sannan ya tambayeta ko akwai abinda take so tace "a'a na gode allah yayiwa rayuwa albarka yayi mata sallama ya fita ya bar ummita ..
Two friend's (bsbs)
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~TRUE LIFE STORY~
FREE NOVEL NOT FOR SELL
AL'QALUMAN
*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*
~DEDICATED TO~
*AUNTY ZEEY MAMAMMU MAMAR MAI DAMBU , ALLAH YA BAR MANA KE MUNA SONKI FI SABILILLAH*
PAGE 17
........a d'akin Inna ummita ta yini ko abinci a nan taci cikin yara y'an'uwanta duk da irin kyara da kora da halin da inna ke mata hakan bai sa ta bar d'akin ba, ta makale abunka ga yaro sai dai duk a tsorace take da inna tayi magana take firgita daga karshe sai faɗa tsakanin ummita da sa'ada akan bebin roba , sa'ada ta kwace abunta ba sai dambe ya kaure atsakaninsu ba saboda ummita taki yarda ta bata bebinta ummita har da cizo saboda jin zafin dukan da Sa'ada tayi mata ,nan sa'ada ta rufe ummita da duka tana kuka , aka rabasu, ummita ta makale kafad'a ala dole sai ta rama tana kuka, rayhan ya shigo d'akin bai tsaya jin dalilin kukanta ba ya rama mata tare da d'aukarta ya saɓa a kafad'arsa yana rarrashinta, amman still tace sai ta sauka ta rama.
"kai rayhan fita daga idona dan me zaka daki Sa'ada akan wannan jairan tarinyar mai fadan rashin gaskiya "haba inna baki ga ba karfinsu ɗaya ba kuma ai Sa'ada tafi dukanta guda nawa jikin ummita yake ?
"Ban sani ba mara sanin ciwon kai ,ga jininka amman dan shishigi kake makelewa wannan abar "itama jinina ce kamar yadda Sa'ada take"
" Yi min shiru kuma ka fitar da yarinyar nan mai kai kamar na maciji daga dakina , yarinya sai jarabar kukan tsiya idan an barki daita iya mata zakiyi ? Cikin fushi ya juya ya fito daga d'akin ya kai wa mama ita tana kuka , mama ba tace komai ba ta karb'eta dan tasan za'a rina , tayi mata wanka tana rarrashinta daga nan sai bacci .
sannu ahankali suna girma kyawun ummita na sake fitowa sosai , duk tafi jikokin hajiya inna kyau , batun so a tsakanin inna da ummita babu shi dan gaba-daya tafi son ma'aruf acikin jikokinta , saboda me sunan babanta ne, sai kuma ya'yan saudat , zata iya hana kowa abu ta basu numfashinta ne kawai bazata iya cirewa ta basu ba ,Inna na son yaran fiyye da komai sai gashi Allah ya jarabi yaran saudat guda biyu da rashin jin magana da shaye shaye ga sata kamar me , malik da sadam babu abinda zasu gani matukar za'a siya to zasu ɗauka suje su siyar suyi shaye shayensu dashi ,ga rigima kamar me , da anji ihu a waje ba'a tsaya wa tambaya an san dasu ne hajiya inna da saudat babu Allah aransu suka lakawa mama cewar itace tayi musu asiri , da yarda Allah sai sharrinta ya koma kanta da yarta ..
Ita dai mama bata tanka musu ba , sai addu'a da tayi musu da itama sun sha mata satar shiru kawai take saboda gudun maganar hajiya inna .
*****
Ma'aruf yana bacci a d'akinsa ya dinga jin hayaniya da ihu , sai ya farka ya fito, yana fitowa sai yaga faɗa ake yi da sadam da wani yaro har anji masa ciwo duk jama'a unguwa sun fito suna ta kallo,masu zagi nayi masu addu'ar Allah yashirya sunayi, shi kuma daman irin wannan fad'ace fad'acen bata masa rai yake saboda baya son hayaniya, kawai yaje ya nemi guri yayi zamansa akan banci yayi tagumi yana kallonsu , hatta Malik kallonsu yake yana dariya dan dama basa shiri da sadam kusan dai yadda 'yan shaye shaye ke yi , da kyar aka samu aka raba faɗan , gashi inna da Hajiya saudat basa nan sai da suka dawo suka samu labari Hajiya saudat taje ta kai yaron da sadam ya jiwa ciwo da kwalba chemis domin ayi masa treatment, tana dawo kawai sai sautin muryar hajiya saudat yaji tana cewa "ma'aruf ana faɗa da ɗan uwanka dan rashin so shine ka zauna kana kallo ,da an kasheshi ma babu abinda zaka ce har da wani harde hannu....
abun yayi matukar bawa maaruf dariya Amman da yake miskili ne sai ya dake yaki yin dariya , sai rayhan daya zame masa dole ai ya tafi da gudu ya rabasu lokacin da aka d'auko katakobi za'a buga ma sadam abun yayi matukar bashi mamaki yaga bata nan lokacin da abun ya faru, muryarsa a da ke yace " waye ya faɗa miki ina nan ?
"Ya fad'i haka saboda ya samu damar cin uban ko waye , babu kunya ba tsoron Allah tace "ummita sannan ta juya ta shige ciki .
"Yayi shiru yana tunani yarinyar da ko magana kirki bata fiyye , sai dai bayi mamaki jin haka ba saboda ya ga ummita agurin lokacin da'ake faɗa yana kallonta ita da sa'ada sannan ya ganta lokacin da hajiya saude ta dawo suna magana , amman yayi mamakin yadda har ta iya munafurci haka hjy saudat na gama shigewa cikin gida , sai grama tazo ta sameshi " na gode babana Allah ya saka da alkhairi Allah ya bar zumunci ana faɗa da d'anuwanka shine ko ka shiga, ko kallon inda take bai yi ba ya shigo cikin gida yana ciccin magani yana dube duben inda zai ga ummita bai ganta ba dan haka yayi wanka ya fita,yana dawowa da ummita ya soma cin karo daita mari biyu yayi mata masu da kyau a gigice tayi d'akinsu tana kuka mama ta tambayeta "maaru ne ta faɗa tana kuka mama najin haka bata sake cewa komai ba ta koma kitchen tacigaba da aikinta..
ummita ta taso shiru shiru ba kamar meenal ba , batada wayon magana sai tsiwa , sai dai a ɗan girmanta Allah ya jarabeta da rashin jin magana mai tsanani itama ga yawo kamar wacce taci kafar kare daga school ne makarantar islamiyya yawon ya ciyota zata je abunta hankalin kwance , abu kamar wacce akayiwa asiri , domin sometime ko anje nemota sai dai a sameta ita kaɗai duk yara sun watse sun barta tana wasa, zata iya kaiwa har dare tana wasan kasa , ko abinci bata damu dashi ba kamar yadda ta damu da wasa , duk da wannan jarabawar da Allah yayi mata na yawo Allah bai barta haka ba , ya wadatata da tarin ilimin boko da Arabic ..wannan yawon shine abinda yafi komai d'agawa hajiya mama hankali da masoyanta , akwai lokacin data wuce yawo daga school akayi neman duniya ba'a ganta ba sai a bakin jobade hotel ma'aruf yayi nasarar ganinta, aiko tun daga can ya dinga dukanta yana ball da ita ,tasha zagi iri iri rana shegiya biri mai fuskar zaki wanda zaki kashe kike nema kece zaki mutu ki bar mana fat lion kawai , sai da yaji mata ciwo tukunnah ya kawota gida ..
tunda ummita take yawonta babu wanda ya taba dukanta sai ma'aruf , aikuwa ranar inna kamar tayi yaya dan dadi albarka kam ya sha daga karshe reshe ya juye da mujiya , dan zageta yayi tatasss , har sai daya sha mari gurin injiniya ,
kwana ummita tayi da zazzaɓi saboda dukan da taci agurin ma'aruf, mama kuka ummita shesheka kuka tana rungumeta ajikin mama jikinta yayi zafi sosai mama kasa runtsawa tayi tana tofeta da addu'a ...
ma'aruf ya kasa ya tsare akan ummita duk saboda mama, dan baya jin dadin ganin yadda yake ganinta cikin damuwa ,da zarar yaga ummita a waje zai korota gida , haka Usman da rayhan wanda su lalla'bata suke da rarrashi ta daina zuwa yawo ..
wasa wasa sanadiyyar dukan da ma'aruf ke ma ummita ya jawo rashin shakuwa a tsakanin ummita da ma'aruf daman shi bai damu da yara bane , da wuya ka ganshi rike da yaro ko yana wasa da yaro ..
Da kyar ummita ta daina yawo da taimakon allah da addu'r mahaifiyarta , sai kuma ta dawo mai shegen tsokanan bala'i , wata rana aunty Aysha diyar aunty Salma tace Suzu su rakata oshodi siyan ankon bikin kawarta ita da Khadeeja , bayan sun shiga mota , karen mota yace su bada kudi ummita tace kar aunty Aysha ta bayar sai sun sauka kafin su sauka ta kwace kudin motar a hannun aunty Aysha ta rike gam a hannuta , basu K'arasa inda zasu sauka ba direban ya juya kan motar yace kowa ya sauka anan , tayi murmushin tace "kin gani aunty daman nasan haka zasu yi , suka sauka , karen mota ya miko hannu ta bayar da kuɗi ,ta mika masa rabi kudi , aiko take karen mota yace bazai amsa rabi ba , ita kuma tace" bazata bashi duka kudin ba tunda bai kawosu inda zasu sauka ba yana zaginta tana ramawa sauran yanuwata suna ta hanata amma in taki , har abun ya zama bala'i ta nemi guduwa karen mota ya janyo hijabinta zai kai mata naushi, sa'ada tayi saurin riko hannunsa aiko naushin ya sauka akan idanunta , ita kuma ummita ta arce ta gudu basu sake ganinta ba sai da suka dawo gida , nan kuma bala'i ya kaure atsakanin har da dambe , sa'ada Khadeeja da ummita case har gurin injiniya da kyar ya sasantasu, lokacin dukkansu basu wuce shekara sha biyu ba, yayinda su ma'aruf suke shekara a shirin da uku ..
idan kuwa ummita taga Khadeeja ko meenal ko sa'ada sunyi shiri daban ko to match yanzu ne zata soma zaginsu ,ko islamiyya haka take da sakawa mutane suna kuma duk wanda ta saka wa suna zai bishi , idan suka sakamata an dinga bala'i kenan, idan tasa maka suna toh ya zauna kenan dan ko zaka mutu sai suna ya bika , dan dashi zata dinga kiranka dashi , ita kuma ba'a isa a kasa mata ba , meenal da ummita suna tsaye da wasu yan makarantarsu guda biyu a kofar gida sai ga raliya makwafciyarsu ta sha kwaliya sosai ,ummita tayi mata kallon sama da kasa " raliya yau to match kikasa haka lallai kan mage ya sake waye an yi wanka, wanka yabi jiki Allah yasa a d'ore ..
Cikin haka sai ga Khadeeja ta fito , ahankali idanun ummita ya koma kanta " a'a ke kuma ya haka kinyi shiri kamar wata almajira lafiya ko wani ne ya mutu a danginku ko me ya faru haka ?
dukkaninsu kallonta suke a hankali meenal ta kwashe da wata uwar dariya , ita kuwa ummita ko ajikinta da dai ta gama magsnarta ta fita harkarsu , duk abinda tayi akan idon ma'aruf da abokinsa jafar, shi kanshi jafar dariya yayi sosai har da rike ciki " wannan yarinyar case ce fa , "shiyasa na tsaneta , saboda bata kwantarwa da mama hankali ya K'arasa maganar yana jan tsaki yana tunanin irin dukan da zai yi mata idan ya ka mata ....
Ita kuwa Khadeeja da raliya ransu a 'bace suka nufi bangaren mama kai kara, baiwar Allah tana ganin fuskarsu gabanta ya fad'i tasan da dalili , nan suka shiga faɗa mata abinda ummita tayi musu hakuri ta basu tana rarrashinsu , tsokanar ummita na bakanta ran mama sosai ....
Ummta na son mahaifiyarta kamar me saboda tsanar data ga inna ke yi mata, hakan yasa bata ragawa hjy saudat da inna duk da mama na taka mata burki , mama sam bata takurawa ummita gurin aiki dan ta lura bata son yin aiki duk lokacin data sata yin aiki zata haɗu da 'bacin rai dan haka ta daina sakata komai idan ma'aruf ya shigo yaga mama na aiki ummita na kwance tana kallo ,haushi yake kamashi yayi mata duka sannan yace dole sai tayi ,sam basa jutuwa dashi dan haka tafi son rayhan da Usman basa takura mata sai dai su su taimaka ma mama suyi mata komai .
***
Wata rana ummita suka haɗu da rashida a harabar gidan ta fito daga ciki ita kuma ummita zata shiga cikin gida , rashida ta kalleta tayi murmushi tace "a'a su ummita dai "
Ummita ta ta'be baki tana kallonta batare da tace mata komai ba rashida ta dafa kafad'arta " ya naga kina haske haka ?
Rashida kanwar hajiya hjy saudat ce Kuma matar aure ce da ya'yanta , the nest thing ummita ta cire hannuta a kafad'arta tace ", a beg oooooo am not bleaching it my skin oooo am just glowing in grass and disiar kwanciyar hankali, I know you are my enemies members plz don't put eye's in my life , I know you have PhD in , plz minding your business and tell the enmis am doing well munafukai kawai ....tana gama faɗar haka ta juya tayi bangare su .
aiko a zuciye rashida ta koma cikin part din hajiya saudat ta koro mata duk yadda suka yi har da karya ko gama ji hjy saude batayi ba tayo part din hjy mama ta dinga zazzaga bala'i Wai ummita ta zagi rashida " aunty Rashida A she asaran kudin tara akayi ta ina na zageki ? "Faɗa min
maganata tayi kama da zagi ne bancin kalmar munafukai da nace "uwarki ce munafuka gata nan agabanki tsaye shegiya jikar agumawa masu asiri ..... tunda hjy saude ta soma zagin mama ta rike kirjinta da kanta da taji yana jujjuya mata , kuma hakan bai sa hajiya saudat tayi shiru ba, har sanda ma'aruf da rayhan har ma da Usman suka shigo parlour'n , take rayhan ya riko hannun hjy saudat shi kuma ma'aruf yayi gurin mama yana rungumeta ajikinsa tare da kiran sunanta .
" haba mama me yasa kike yin haka inji cewar rayhan , haka babu kyau fa har bangarenta zaki bita kina zaginta ,"kai kasan abinda shigiyar yarinyar nan tayi ne ?
"Koma me tayi mama bai dace ba dan Allah ki daina biyewa hajiya inna har part dinta ya kaita yana mata faɗa yana ƙoƙarin dawowa d'akin mama ya ga Usman da ma'aruf sun riko mama da sauri ya k'araso garesu a kidime yana duban fuskar mama kwata kwata bata numfashi da sauri ummita dake kuka ta bude bayan mota suka sata suka nufi asibiti daita, gwajin farko likita ya fahimci jininta ne ya hau nan suka shiga ƙoƙarin bata taimako gaugauwa ..
Likita ya fito daga d'akin yace mutun ɗaya ya biyosa dukkanknsu suka shiga dakin cikin tashin hankali ..
Da sauri ummita tashiga d'akin da aka kwantar da mama ta tsaya akan mama hawaye na zubowa daga idanunta, a lokacin tunanin rayuwar da ita da mahaifiyarta ke yi acikin gidan ke dawo mata , irin rayuwar kunci da suke yi da mahaifinyarta acikin gidan tamkar marasa galihu kallon mama take yi wadda ita kaɗai ce gatatan a yanzu a duniya gashi itama a kwance rai a hannun Allah a sanadiyyar rashin jin maganarta, sai ya'yan da ba nata ke jin maganarta da tausaya mata , tunanin yadda zata sauya rayuwarta ta zamo abar alfaharin ga mahaifiyarta take ,tana cikin wannan tunani taji ana sallama ta amsa haɗe da juyowa domin ganin mai shigowa ganin wanda yayi sallama yasa gabanta mummunar faduwa kafin tayi yunkurin mikewa ya soma surfa mata bala'i "shegiya munafuka, mayyah kin wani marairaice kamar ta Allah kina kukan munafurci wallahi yau shine zai zamo karo na karshe da mama zata samu wata matsala akanki shashar banza kowa yasan darajar uwarsa amma ban dake kamar ta rama amman taji hannun mama akan nata hakan yasa tayi shiru taki cewa komai ma'aruf na ganin mama ta farka ya K'arasa da sauri ya riko hannunta cikin nasa "sannu mama," ya ya kike jin jikinki yanzu?
" zuciyarki ta daina bugawa ? Gaba-daya yayi mata tambayar ajere yana kallonta jikinsa na rawa "alhamdullahi ma'aruf naji sauki sosai , ma'aruf Allah yayi maka albarka Allah yasa ka gama duniya lafiya , Allah ya jibanci lamarinka ban haifeka ba amman ka zame min abun alfahari ",ameen mama Allah ya baki lafiya ....
Kuka ummita ta fashe dashi haɗe da durkushewa kasa bisa gwiwonta ta rasa abinda zata faɗa tana bukatar rayuwar mahaifiyarta tana bukatar mahaifiyarta araye ...
Tsaki yaja yana fadin munafuka banza sai anyi magana kisawa mutane kuka kamar ta Allah , Usman daya shigo ya dafa shi "is okay ma'aruf ka rabu daita haka, yanzu ta lafiyar mama muke bai sake cewa komai ba, ya juya ya bar d'akin tare da kunar zuciya da kunar rai ,sun fi minti goma a tsaye sai daga baya Usman ya kamo hannuta jikinta na rawa yace "ki bawa mama hakuri ki bata hakuri cewar bazaki sake ba muryarta cike da kuka tace "bazan sake ba ta sake matsowa kusa da mama hawaye na zubowa daga idanunta ta kamo hannun mama cikin nata ta damke sosai tana kuka "mama kiyi hakuri ki
yafe min bazan sake ba " ummita na yafe miki duniya da lahira Allah yayi miki albarka Allah ya shirya min ke , Allah ya albarkaci rayuwarki ya baki miji na gari Allah ya juyo da hankalinki , Allah ya sanya miki natsuwa a zuciyarki , kiyiwa yayyenki biyayya ma'aruf da usman cikin kuka tace " ya Usman dai mama amman shi... ...sai kuma tayi shiru ta kasa karasa maganar ,kwana mama uku aka sallamota ta dawo gida ,bayan Hajiya umma da injiniya babu wanda yashigo dubata a manya gida sai kuma yara ..
ma'aruf ya sake tsanar ummita kamar me sakamakon bayanin likita na hawan jini ya kamata kuma yasan duk ummita ce sanadi , kwata kwata baya son ganin ummita ganinshi so take ta kashe mama a tunaninsa idan mama ta mutu su ne da harasa ita bata da ...
Tun daga wannan lokacin ummita ta dawo normal ta daina tsokanar kowa ta daina yawo duk wani rashin ji ta ajiye ta rungumi karatunta da mahaifiyarta sai dai duk wanda ya takata bata kyalewa sai ta rama koda kuwa hajiya Inna ce .....
Two friend's (bsbs)
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~TRUE LIFE STORY~
FREE NOVEL NOT FOR SELL
AL'QALUMAN
*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*
~DEDICATED TO~
*HUSAINA D'ANLARABAWA ABOKIYAR BESTY NAH, YAR PARTYN ABBA GIDA GIDA ,AKWAI AMANA DUK RUNTSI KANO SAI ABBA GIDA BIDA*🤗🤗
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
PAGE 18
..... Bayan shekaru huɗu da suka k'aru akan shekarun ummita , ta ƙara girma , kyawunta ya sake fitowa sosai , duk wani halitta na kyawun d'iya mace da daukar hankalin d'a namiji sun gama bayyana a jikinta, doguwa ce sosai sai dai yar sirirya ce , fara sol irin farin nan dake sheki tamkar wacce take shafa madara a jikinta , haka yanayin tsarin jikinta irin figure 8 din ce , mai cikakken kirji ce ,dukiyar fulaninta masu shegen kyau da ɗaukar hankali daidai kirjinta , sannan a tsaye suke cak masu gindin tasa , fatar jikinta a kwance take luwai luwai ga kyau ga laushi ko zata shekara bata shafa mai ba skin dinta bazai yamutse ba , tana da madaidaita faffad'an kugu mai haɗe da hips madaidaita , batun bombom sai zuwa gaba saboda rashin jikinta bai gama bayanasu ba ,tana da dara daran idanu masu kyau waɗan da suka wadatu da gashin ido masu matukar birkita kwalkwaluwar duk wanda ya kalli cikinsu , hakoranta masu haske ne dauke da dadashi mai duhu ,gata da siririn hanci da karamin baki da dimples Wanda ko magana tayi sai sun lu'bo ,ko cikin 'bacin rai take sai sun nuna , da zarar tayi murmushin kuwa ji zakayi kamar ka sureta ka gudu , sai wadataccen suman kai da gashin gira wanda suka kusan had'ewa da gashin kanta tsagun bakin da akayi mata suna sai maka mata kyau da sukayi kasancewarta fara , ga wani maseefaffen jin kai daya sarkafeta , da zarar ta gama aiki , sai karatu da kwanciya sai kuma kallo tare da narkewa a jikin mahaifiyarta, kullun mama na cigaba da rarrashinta tare da mata nasiha akan rayuwar duniya "tabbass nasihar mama na shigarta sosai , girmanta ya zama so boring saboda ta taso babu walwala da sakin fuska sannan babu yawon magana , acikin gidan taka tsantsan take da kowa har uban gayya ma'aruf, fuskarta babu annuri ko kaɗan , sai dai duk lokacin da aka ci mata fuska ko mamanta bata yarda sai ta rama , amman idan baka shiga lamarinta ba babu ruwanta da mutun .
Alhaji Ibrahim ya samu cigaba sosai a rayuwarsa bisa matsayin mahaifin ma'aruf daya maye gurbi a kamfaninsu na oil and gas gaba-daya su suna zaune a astate din small London dake unguwar daji, gidan da Alhaji Ibrahim ya ƙera yayi shi bangare bangare , kyakkyawan gida ne ginin zamani mai kyawun gaske ,samarin gidan sune ke zaune daga farkon shigowa, shi kuma injiniya yana ɓangaren hagu, alhaji Ibrahim na bangaren dama sai bangaren inna dana hajiya umma da Hajiya mama kowa bangarensa daban kuma duk sama da kasa ne har na hajiya inna bene ne sai dai ita a kasa take rayuwa saman tabarwa barwa jikokinta na gurin aunty Salma ....
A wannan lokacin Kabir dan aunty Salma yana da kanne huɗu Aysha, suwaiba wacce suke kira da aslamiyya ,Maryam ammar ,bangaren saudat kuma tana da yara bakwai abdulmalik ,rayhan Khadeeja ,Sa'adatu sadam , saifullahi sadiq.. a d'akin hajiya umma tana da yara huɗu Abdurrahaman ne ya kasance babba sai ma'aruf sai Hauwa wacce suke kira da jiddah sai ameena..
Har lokacin kan injiniya da Alhaji Ibrahim a haɗe yake Alhaji Ibrahim mutun ne mai mutunci da tarin tsaftataccen dukiya wacce ake sarrafata ta hanyar data dace .
duk yaran gida karatunsu na secondary a sanjosaf international School suka kammala ,ba kananan kudi Alhaji Ibrahim yake kashewa akan karatun ƴaƴansu dana kanwarshi ummusalma da injiniya yake ba ,ba dan gazawar iyayensu ba sai dan kyautata da kuma kauna irin ta y'an'uwanta ka ,har wannan lokacin Hajiya mama da Hajiya umma kansu a haɗe yake tamkar 'yan biyu hakan ya basu damar hada kan yaransu idan ba kayi musu kyakkyawan sani ba zai yi wahala ka bambacesu tsakanin dan wannan dakin da wannan d'akin ko kamanin yaran gida irin daya ne most especial ma'aruf da ummita tamkar an tsaga ƙara , komai nasu iri ɗaya ne babu wani bambanci idan ma akwai bambamci shi ya kasance namiji ita kuma ta kasance mace .
Ummita da ameena shakuwar da take tsakaninsu ta wuce a kwatantawa domin hatta bacci baya rabasu sukan kwana a duk inda suka so, sosai Hajiya mama ke jansu ajiki ,dan ita mace ce mai barkwanci ta mai dasu tamkar kawayenta duk inda take suna like daita har lokacin diyar hajiya mama ɗaya bata sake samun wani haihuwar ba .
kullum sake godewa Allah take da ya azurtata da samunta arayuwa, yayinda alokacin sheakarar ma'aruf ashirin da bakwai cif a duniya yana matakin karshe a jami'ar Bayero shi da rayhan shi kuma Usman yana cotonue gurin mahaifinsa, tun da suka kare secondary School mahaifinsa ya bukaci ya dawo ba dan ya musgunawa mama ba sai dan ya rage mata saukin wahala daga hajiya inna da take kallon kamar ana wahalar mata da ɗa da dukiyarsa ne, hakan kuma yasa ma'aruf ya fahimci lailai ba mama ce ta kawoshi duniya ba , duk da an sha faɗa masa hakan bai yarda ba ,ko daya san da hakan bai taɓa sauya mata ba ,yana nan tamkar ɗan cikinta dan ko mahaifiyarsa bata nuna masa wani abu ko nuna cewar itace ta haifeshi tsakaninsa daita gaisuwa dan komai nashi na dakin mama yayinda
Alhaji Ibrahim shi kuwa tamkar dan d'an'uwansa ya dauki Usman baya bambamta shi da ya'yan yan'uwansa ,sam bai ji dadin komawar Usman ba amman babu yadda ya iya tunda mahaifinsa yace zai dinga zuwan musu hutu duk lokacin da hakan ya samu ..
A zamantakewar mu'amula saudat har lokacin tana nan kamar yadda take ,bata da kirki sannan bata da haba haba da mutane saɓanin yaranta ,sam bata da .saukin kai ga zafin rai basu fiyye jituwa da mutanen gidan ba ga mugun son ya'yanta akan yayan mutane babu abinda bazatayi ba akan yaranta ta sha biyo ummita har daki akan sunyi faɗa da yaranta , idan ummita tayi galaba akansu haka zatazo tayi ta zage zage agaban hajiya mama Amman Sam bata d'aga kai ta kalleta sai dai idan ta fita , mama ta janyo ummita tayi ta rarrashinta tana mata faɗa, ummita ta rushe da kuka mama har ta yata kuka take tana son barin Ibrahim da danginsa amman idan ta tuna ummita sai ta sake sanyawa zuciyarta hakuri a lokacin takaicin kanta ta dinga yi da bata bar gidan tun kafin ta haifi ummita ba ,suyi rabuwar har abada .....
Bangaren matsalar inna kuwa ma'aruf ne ya ruguza dukkanin wani iskancinta da tayiwa mama yake rufe ido ya gurza mata har da dogon gaba ba ,gashi ita kuma Allah ya jarabeta da kaunarsa bata iya dogon fushi dashi ko fushi yayi daita sai tayi zazzaɓi dan haka ta rufawa kanta asiri ta dan saduda ta rage wani abun..
injiniya ya d'aukewa abba nauyi kai yara makaranta tun lokacin daya tsiyawa malik mota wanda ya soma dawo wa daidai shaye shayensa yayi sauki ba kamar da ba dan lokaci kokari ake a masa aure domin ya sake samun natsuwa dan tuni Abdurrahaman da Kabir sunyi aure , Abdurrahaman ya auri Aysha diyar aunty salma suna zaune a depemo shi kuma Kabir yana auren diyar aminin mahaifinsa ....
A daidai wannan lokacin walimar saukar Alqur'ani su ummita ya tashi ita da meenal da Sa'ada ,ana washegarin walimar mama ta bawa ma'aruf stone tace ya sawa ummita ajikin shaddarta sannan ya goge mata kayan ,babu mutsu ya amsa kayan darajar mama dan babu abinda zata saka shi yaki ,
gurin walimar ya cika makil da jama'a ,baka gane mutane kasancewar babbar makaranta ce data amsa sunanta ,sannan ta tattara manya malamai, kowace daliba ta sha farar shadda sol da a baya da mayafinta , maza kuma farar shadda kawai da hula , babu wanda bai je ba a family dinsu hatta ma'aruf yaje saboda mama , sai dai har lokacin da aka soma kiran dalibai uku uku suna karatu saboda da yawansu ummita bata hallara ba tana gida bata gama shirinta saboda sanyi jiki yayinda rayhan ke tsaye jaman jiranta yana tayata wasu abubuwa har sai da ran mama ya kai ga ɓaci sannan ta hanzarta ta fito cikin takunta na yanga ta shiga gaban mota suka bar gidan ,daf da inda jama'a suke yayi parking suka fito alokaci daya ,tana fitowa idanun mutane sukayi caaas akanta day day wani mutanen da basu kalleta ba saboda kyawun da tayi ahankali take taka kasa kamar mai tausayin takawa ya rayhan na biye da ita "ki saki ranki plz yau fa ranar farinciki ce duk yadda yake mata naci ,kin sakin fuskarta tayi saboda idanun mutane da taji suna yawo ajikinta gani faduwar gaba da kirjinta ke yi ,sake tamke fuskarta tayi har ta k'araso gurin zaman daliban amman bata daina jin idanun jama'a akanta ba yayinda rayhan wanda ke biye daita ya juya ya koma ,"wani malamin islamiyyarsu dake mugun sonta malam annafi ya dubeta yayi murmushin "nasan sai kinzo latti ai amman zamu haɗu a makaranta ne sai na miki bulala a shirin masu kyau , tayi murmushin kawai ta samu guri cike da sanyi jiki ta zauna akan kujerar data kasance tana jiranta , lokacin da aka kirata karatu babu wanda yasan an kiranta daga cikin yan gidansu saboda yawon mutane sai ma'aruf ne ya gayawa musu an kirata sannan suka tasu lokacin har ta fara karatun suratul Ibrahim cikin zazzakar muryarya mai dadi da saka natsuwa duk tarin jama'ar dake gurin babu wanda bai samu natsuwa a dalilin sautin muryarya data karade gurin ba , a hankali yan'uwa suka soma yi mata liki kowa na alfahari daita hatta malamai na alfahari daita ,ta samu kyaututtuka da dama sakamakon kokarinta da tsafta tayi hoto da kowa amman banda ma'aruf ko da mama tayi mata magana cewa tayi" ta gaji ta shige cikin
Agurin walima tayi samari daban daban da suka nuna suna sonta amman taki kula kowa .
Ummita bata kula samari duk wanda yace yana sonta shikennan sun raba hanya sai dai idan bai furta ba, zata iya cigaba da gaisawa da mutun amman da zarar ka furta ba ita ba kai har abada ka zama makiyinta ,manya mutane na sonta haka ya'yan manya masu arziki da kyau da manya gida da motoci amman ita ko ajikinta basa burgeta , har ake tunani ko aljannu gareta shi kuwa ma'aruf ya rigada yasan babu wani aljanu kawai tsabar iskanci ne ..
********
Back to the story
Two friend's (bsbs)
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~TRUE LIFE STORY~
FREE NOVEL NOT FOR SELL
AL'QALUMAN
*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*
~DEDICATED TO~
*KHADY PINKY YA KWANA BIYU FATAN ALKHAIRI*🤝🏻
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
PAGE 19
......Da misalin karfe uku na yamma injiniya ya shigo bangaren Abba ya same shi da baki mutun biyu , sun gaisa cikin girmama juna , bakin biyu suka mike tare da yin sallama , bayan tafiyarsu suka sake sabuwar gausuwa sannan suka fara zantawa a kan abinda ya kuno kai cikin iyalinsu wanda basa fatan ya zame musu damuwa ..
Dogon lokaci suka dauka suna shawara akan lalle bazasu bada diyarsu ga muhd Sa'id ba bisa wani dalili nasu duk da sun san mahaifin muhd Sa'id din tsohon dan canji ne a jahar lagos kasamcewa shi Abba mai yawan mutane ne yasan jama'a sosai ....
Abba yace "a bar komai a hannunsa zai san yadda zai bullowa lamarin , naunauyen ajiyar zuciya injiniya ya sauke yana duban Abba sannan suka rufe wannan babin suka shiga hirarrsu ta rayuwar duniya ..
Tunda sakon mahaifinta ya iso kunnuwanta ta kasa samun natsuwar zuciya ,take zazzafan zazzaɓi ya rufeta ta lullu'be jikinta kamkamewa guri ɗaya tana jin kamshin turaren jikinta, tasan muddin ta bujirewa umarnin mahaifinta akan aurenta da ya rayhan tamkar ticket ta rabawa wasu daga cikin mutanen gidan ,wanda hakan zai sa har su samu damar yin shishigi a cikin rayuwarta data mahaifiyarta wacce ba taji bata gani ba ,ita yanzu ba auren ya rayhan take ki ba illa jarababbiyar uwar mai mugun hali aurensa tamkar ta tsoma rayuwarta cikin bala'i da iftilain da mahaifiyarta ta tsinci kanta ciki tsawon shekaru wanda har yanzu tana kunsar bakinciki ,ji tayi kamar ta kurma ihu dan tashin hankali ,a bangaren ya rayhan kuwa tun lokacin da yaji ya soma murna gagara yayi bai gama abinda yake ba yazo ya sameta koda ya shigo bangarensu ya tambayi mama ita tace masa tana d'aki bata jin dadi amman tasha magani take yar fara'a daya shigo daita ta dauke ya nemi farincikinsa ya rasa .
"Da sallamarsa ya tura kofar d'akinta ya shigo, gabansa ne ya ɗan fadi saboda yanayin daya ganta ,amman ya dake ya k'araso inda take kwance tare da yaye bargon data lullu'be jikinta dashi ,ya tsaya yana kare mata kallo musamman yadda jikinta ke rawa, kusan minti biyu ya ɗauka cikin wannan yanayi yana kallonta kafin daga baya ya kira sunanta cike faduwar gaba "subai'a ......
Bata amsa ba ta lumshe fararen idanunta hawaye na kokarin zubo mata shiru yayi na yan mintina yana sake kare mata kallo " well I don't care all what you fell about our marriage as far as I still love you ya ja numfashi da kyar ya sauke sannan ya soma magana muryarsa a sanyaye tamkar wanda zai yi kuka "subaia nasan ba kya sona, amman zai iyakar kokarin naga na koyar dake yadda zaki soni a rayuwa subai'a You are so different daga cikin sauran mata ban taɓa sanyawa zuciyata soyayyar kowace diya mace ba sai ke ,da sonki na rayu na girma .
tasa hannu ta fixgo bargon dake rike a hannunsa ta rufe jikinta tana jan tsaki acikin ranta ,ya samu guri kusa da fuskarta ya zauna tare da buɗe daidai fuskarta ya tsura mata ido " my happiness my princess kada ki samu damuwa zaki so rayhan wuyarta dai su abba su kai min ke gidana nasan yadda zan ladabtar da zuciyarki ta soni yayi maganar tare da mikar daita zaune ta yatsina fuska tana runtse idanunta ,ya jingina bayanta da pillow shiru tayi tare da lulawa tunani ya riko tafukan hannuwanta sai lokacin ta ɗan dawo daga tunani ta buɗe idanunta, suka haɗa ido a lokaci guda wanda suna iya jin numfashinsu tuni hankalin ummita ya sake tashi murmushi yayi yana busa mata iskar bakinsa dan yasan kan yan kayansa yau sai yayi da gaske da duk rigimar da zatayi masa ,sannu a hankali ya dinga kwantar da kai tare da faɗa mata kalama masu sanyi har ta ɗan saki ranta ya dinga janta da hira cikin sanyayyiyar muryarsa yana mata hira yana jin tamkar ya shige jikinta domin ji yake kamar ya sameta a hankali ya jata zuwa parlour'n kasa ya zaunar daita bisa kujera yana kwantar mata da hankali tun tana sharesa har tasoma biye masa suka shiga hira har sanda meenal tashigo ya fita ya barsu tare yana damka mata amanarta tayi murmushi "karka damu yaya zan kular maka da sister ...
*****
Bayan sallar isha'i muhd Sa'id ya aiko kiranta tana jin haka tayi wata irin zabura tare da firgita ,wanda hakan yasa
ran mama yayi matukar ɓaci ganin irin yanayin kidimewar da yarta ta shiga lokacin daya ta dauke kanta daga kanta cikin rawar murya ummita take fadin ni dai mama kicewa sadiq yace masa bananan kawai Allah bazan iya zuwa ba .....
Meenal tuni ta mike ta fice daga d'akin domin bawa sadiq umarni yaje yace gata nan zuwa dan tasan dole mama ta tilastata fita ..
Hajiya mama ta girgiza kai "ummita ki natsu rashin zuwanki bashi ne mafuta ba , abbanki yace a natse zaki yi masa bayani an bayar dake a samu ku rabu lafiya dashi ta tsigar mutunci sai ku rabu a mutunce , goge idanunki maza kije ki dawo kinji diyar albarka , yayiwa rayuwarki albarka dake da zuriarki ...
A sanyaye ta fito zuwa inda yake wani irin mahaukacin ajiyar zuciya ya sauke fuskarsshi da zuciyar na cike da tsantsar farinciki mara misaltuwa amman sai da gabansa ya fad'i saboda kallon yanayinta kaɗai ya isa ya fahimci dole akayi mata ta fito muryarsa sanyaye yace "Barka da fitowa gimbiya kyakkyawa acikin matan duniya , tayi shiru taki cewa komai ,yau ko yar gaisuwar da yake samu daga gurinta bai samu ba ,ya tsura mata idanunshi yana nazarinta cike da tsantsar kulawa da soyayya kafin daga bisani yace "lafiyarki kuwa subai'a?
Ya tambayeta yana leka idanunta taja da baya da sauri saboda hucin Numfashina dake ƙoƙarin kawo mata ziyara ", lafiya me ka gani tayi maganar cike da dakiya da miskilanci ?
Yayi murmushi "haka dai na ganiki wata iri , kiyi hakuri idan na takuraki ne wallahi duk kwanakin nan na rasa gane kaina kowa ma ya rasa gane kaina hatta iyayena sun rasa sukuni saboda ganina cikin damuwa dan Allah subai'a karki barni , har cikin zuciyarta tsoronshi take ji saboda yadda yake yi kamar zai ɗauketa ..
Ya sake matsowa sosai ta sake ja baya da sauri yayi murmushin " kwana biyu dai da alamun laifi nayiwa gimbiya ..
Ta dan sake zuciyarta "ba kayi laifin komai ba muhd Sa'id gani nayi a matsayinmu na muslimai bai dace mu dinga yin irin wannan tsayuwar ba kusa da kusa gsky abun bai dace ba kasancewar mu ba jinsi daya ba...
Ya tsotsa keyarsa alamun jin kunya duk da ya fuskanci alkibilarta yaja baya yana fadin "kinfink gsky saurauniya matan duniya , matso ki zauna nan sai na koma kan mota ni na rasa gane abinda yake damu sarauniyyata yau ko bakya jin dadi ne ?
Taja tsaki cikin sirriyar muryarta ta yatsina fuska kamar taga kashi "kawai dai ina jin bacci ne yayi dariya " barci shalelena lallai kina jin dadi subai'a" yau ina mutumina saifullahi ne bangashi ba ?
"Yana tare da baba sun fita tare "wayyohlly gashi kuwa yau har da tsarabarsa nazo Allah yasa su dawo da ina nan ,bata san lokacin data buɗe idanunta sosai ba ta kalleshi "mafoluku suka je fa yayi murmushi ",Ni har kin bani dariya ina mafoluku ina nan ,nasan zasu bazasu wuce shad'aya ba ina nan har su dawo tayi saurin zaro ido "dawa zaka kai shad'aya "tare da matata subaia abar Sona mana kalamanshi suka daki zuciyarta taji ranta ya sake ɓaci cikin muryarta daya fi kauna da son ji tace "muhd Sa'id zan so ka sauraren i da kyau kuma ka fahimci Ni zan sanar da kai mahimayyar magana wanda tsantsar gaskiya ce "ina souraronki Sweet heart ta kara hassala "kasan hadisin nan da yake magana akan cika alkawari wanda annabinmu mai tsarki ya faɗa cewa alamomin munafuki guda uku ne bansani ba ko kasan shi ..?
"Akwai idan mutun zai yi magana yayi karya ko rashin cika alkawari ko mutun ya amince maka kayi masa ha'incin "haka ne malama subai'a nasani ,iza hadasa kazaba....."alhamdullahi daman nasan kasani tayi saurin katse masa hanzari kuma gaskiya hausawa sunce ɗaya ce daga kinta sai bata a zahiri gsky Sa'id batun yanzu ba muke tare da yayana rayhan zuwa yanzu har magabata sun shiga cikin maganar bazan yaudareka ba muhd Sa'id a jiya nayiwa rayhan alkawarin bazan sake sauraron kowa ba,shi kuma alkawari abin tambaya ne bancika sai nace zan cigaba da sauraronka koda gaisuwar mutunci ne mu dinga yi na gode matuka da irin kaunar daka min ina mai yi maka fatan alkhairi Allah ya hadata mai kaunarka fiyye da yadda kasoni na gode da dinbin alkhairinka gareni ina mai sake baka hakuri yanzu zan shiga na kawo maka kayanka ga mamakinta sai taga ya bushe da dariya ..
A matukar tsorace take kallonsa zuciyarta na wani irin dokawa "Muhd Sa'id ka fahimceni kuwa ?
Ya fuskamceta sosai zuciyar tana wani irin tsalle tamakar zata fasa kirjinshi tayo waje har lokacin dariya yake "fahimtar kalamanshi ne suka sani dariya subai'a"ai duk wanda kika yiwa wannan alkwarin kuma ya amince ya tabbata wawa ai ita budurwa ta mai rabo ce yadda na ɗauki soyayayarki a zuciyata ruwa da iska wuta da dukkanin tsanani bazasu sani in janye ba wallahi ko dan shugaban kasa ne yake sonki zan iya takara dashi koda zai yi amfani da karfin mulki ya tureni in har Kinga na hakura dake ki tabbatar da kin zama matar wani abinda bana fata kenan mutukar ina numfashi baki fahimci girman sonki a zuciyata ba shi yasa kike tunanin wannan kalamanshi zasu iya sawa na janye kudiruna akanki ..
Sheshekar kukanta ne ya dakatar dashi cikin Muryar kuka ",tace shikennan muhd Sa'id Allah ya gani ban yaudareka ba tunda na faɗa maka gaskiya kaki yarda shikennan Allah ya bamu alkhairi ta juya da sauri dan tana cikin damuwa kashi da kashi ga rashin son AUREN ya rayhan ga muhd sa'id ..cikin matsanancin tashin hankali yake kiran sunanta subai'a subai'a amman ina ko juyowa batayi ba illa kara sauri da wani irin gudu ya sha gabanta "dan girman Allah ki saurareni bai kamata ki dinga yiwa matsoyinki na hakika korar kare ba kisani girman sonki a zuciyata ya kai ko kara kika saka bazan ja baya ba bani nayi zuciyata ba gani nayi zuciyata ta aminta dake kaɗai zata iya rayuwa sonki shine rayuwata ina sonki subai'a ta galla masa wata ƙatuwar harara "gashi ni kuma bana sonka ba "
Yayi wani malalacin murmushi "tun farkon zuwa na fahimci hakan banason takuraki dan nasan kina jin bacci sai dai ina son kisawa ranki inshaallahu sai kin zamo mallakina ...
Ranta a matukar bace da maganarsa taja kafa ta shige cikin gida ya samo yaro ya tura shi da ƙatuwar jaka mai dauke da tambarin M.S STORE
Yayi gaggawar barin gurin gudun ko zata koro yaron da kaya ..
Babu ko sallama ta kutsa cikin part dinsu tayi jifa da hijabinta akan doguwar kujera ta zube akan kujera ta fashe da kuka bata saurari maganar da meenal take faɗa mata ba "menene ummita kina jina sai kuka kike ta dawo kusa daita ga a raunane tace ",me ya saki kuka ko yayi miki wani abu ne ?cikin kuka tace ",na shiga uku meenal mutumin nan ko maye ne ?
Tsananin tausayin yaruwarta daya gama karya mata zuciya ya sata kuma itama tarasa dalilin duk sanda zata ganta cikin damuwa hankalinta ke tashi fiyye da kowa kodan su kenan Allah ya bawa mahaifinsu a hannu kujera ta daura kanta mama ta sauko da hanzarinta ta tsaya turus tana kallonsu zuciyarta cike da ta bayoyi .
"Lafiyarku kuke kuka kamar an aiko muku da sakon mutuwa ?
Shiru sukayi kowace ta kasa furta komai "ke Amina ba magana nake muku ba ?
Cikin kuka meenal tace "mama nima gani nayi kawai tashi tana kuma bata faɗa min komai ba ..
Mama ta watsa musu harara ",shine dan shashanci baki san dalilin kukan ba sai kema ki kama " to yaya zanyi mata nima hakan na tsinci kaina da kukan "ke ummita kiyi magana kina jin mutane "cikin sheshekar kuka tace"wallahi mama wannan muhd Sa'id din bazai rabu dani ba kuka ya sake kufce mata "kiyi hakuri ummita shi kuka baya magani matsala Abba ya daga labule yashigo parlourn tare da sallama ,bazan iya hana rayhan aurenki ba ummita tunda yana sonki so kuma mai girma da din dadawa so nake ayi aurensa tare dana maaruf ni ya zauna akan kujera yana fuskantarta "ni kaina akwai wanda nake da burin yazamo miji gareki amman maganar rayhan ya dakushe wannan cikar burin nawa ...
"Bama kukan auren rayhan take ba wannan yaron abokin ma'aruf ne yazo shine tunda taje ta dawo da kuka taki yin wani bayani sai kuka Abba yayi murmushin "to kina sonshi ne ?
Abba yayi mata tambayar yana fuskantarta da sauri ta d'ago tana dubansa sannan ta shiga girgiza masa kai " to ita Amina meye nata na kika ?
Mama ta kalleta "wai nan yaruwarta take tayawa kuka "kunga kuyi shiru lokacin da yake gyara zamansa akan kujera "Amina subai'a dukkanku ku tashi kuje ku kwanta kunsa bana shiri da mai kuka aikiwa nan take suka shiga goge hawayensu "yauwa ko kufa yan albarka Allah ya albarkaci rayuwarku "sanar dani ya kikayi da bakonki baki sanar dashi abinda mamanki ta faɗa miki bane?
Ta sake goge hawayenta ",duk nasanar masa Abba cewa yayi ba zai rabu dani ba wai dole sai ya aureni ni kuma bana son shi takarasa maganar tana kuma "kai ummita wani lokacin kamar jaruma Amman kuka baya miki wuya in Banda abinki cewa akayi an bashi ke shi ba igiya zai sa yajaki ba to ina damuwa take ?
"Kin bi kin daga hankalinki kin daga na yar'uwarki to duk ku kwantar da hankalinku gobe zamu dauki matakin daya dace har shi Ma'aruf dan haka shine karfin zuwansa gidan har ya ganki ya ciro hancky a aljihunsa ya fara goge musu hawaye yana zolayarsu sai gasu suna murmushi Abba kenan mutun mai saukin kai ...
Two friend's (bsbs)
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~TRUE LIFE STORY~
FREE NOVEL NOT FOR SELL
AL'QALUMAN
*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*
~DEDICATED TO~
*AYSHA JB ,IYA RIGIMA , INA YINKI SOSAI ,INA SONKI SABODA SAUKIN KANKI INA SONKI DAN KIN IYA RIGIMA , INA YINKI DAN BAKYA FUSHI DAMAN KUMA AYSHA AKWAI SAUKIN KAI*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
PAGE 20
....kwance ummita take lamo akan gadon mama , sosai tayi zurfi cikin tunanin rayuwa yayinda idanunta dake kallon celling d'akin ke tsiyayar da ruwan hawaye , a hankali furuncin muhd Sa'id ke sake dawo mata daki daki har zuwa kan hukuncin abbanta akan aurenta da ya rayhan , zuciyarta ne ya cigaba da dokawar da yake kamar zai fito daga qirjinta , da kyar taja numfashi ta tsayar bayan ta lumshe fararen idanunta "yaya zanyi da rayuwata ?"
Ta yiwa zuciyarta wannan tambayar hawaye na sake gangaro ta gefen Idanunta " hakika auren ya rayhan shine babban kuskuren abinda zan yi a rayuwata....
"zan tafka kuskuren da har na koma ga mahalincina bazan daina nadama a rayuwata ba ..
"Hakika idan na aureshi zan dangwama cikin damuwa da bakinciki tattare da kunci mara misaltuwa ," bana sonka ya rayhan me yasa kake son dole sai ka aureni ...?
" matsawar ka aureni wallahi wallahi zamu dangwama cikin kunci da bakinciki dan ba zamu taɓa ji dad'in junanmu ba muddin rai ..
Tana cikin wannan damuwar ne mama ta buɗe kofar d'akin ta shigo tana ganin halin da take ciki zuciyarta ta harba amman sai ta girgiza kai tare da tsaida idanunta akanta tana jin matsanancin tausayin d'iyarta , ƙoƙarin had'iye nata damuwar tayi domin ta kwantar mata da hankali tace " ba zaki raba kanki da wannan damuwar ba sai ta illataki kou?
"Mama tayi maganar tana zama a gefen gadon tare da d'aga kan ummita ta d'aura akan cinyarta tana shafa sumar kanta.
" ki taimaki rayuwata ummita ki samawar zuciyarki salama, bazan iya jurar ganinki cikin damuwar nan ba ..."
kuka ummita take sosai har da shesheka tamkar wacce akayi mata wahayin mutuwar mama muryarta cike sheshekar kuka tace "bazan iya ba mama gara nayi kuka ko zan ji zuciyata ta rage rad'ad'in da take .... "
"kiyi hakuri mamana damuwarki na karyar min da zuciya ,kece farincikina nayi hakuri na tsawon shekaru amman bazan iya hakurin ganinki cikin damuwar nan ba" ta K'arasa maganar hawaye na zubo mata sharrrrrrr.........
"kwana biyun nan da kika sarkafi damuwa da tunani nima gaba-daya damuwa ta sarkafeni ki tausaya min mamana bana son ki shiga tashin hankali ...."
Suna cikin haka ma'aruf ya shigo d'akin bakinsa ɗauke da sallama jikinsa sanye cikin wando jeans da riga nevy blue mai dogon hannu sai dai ya nad'e hannu rigar zuwa gwiwar hannunsa yayinda kamshi turarensa na white aud ya mamaye d'akin ,turus yayi tsaye yana kallonsu cike da matsanancin mamaki "to me ya samesu haka suke kuka tamkar waɗan da aka aikowa da sakon mutuwa ? "
Take hankalinsa ya tashi saboda ganin hawayen mama a matukar sanyaye ya soma ƙoƙarin k'arasowa zuwa inda suke, sai lokacin mama ta lura da shigowarsa d'akin kasancewar kofar a bude take lokacin da tashigo ganin halin da ummita take ciki yasa bata maida Kofar ta rufe ba .
Mama tayi saurin goge hawayenta tana had'iye kukanta har sanda ma'aruf ya k'araso ya janyo kujera mirrow dinta ya zauna tare da tsura mata manyan idanunshi kana ya riko tafin hannun mama cikin nashi "mamana me ya saki kuka haka ?"
"Meye damuwarki dan Allah ki faɗa min bana son ganinki kina zubda hawaye banason damuwarki yayi mata tambayar ajere hankalinsa a matukar tashe , duk da yasan kukanta bazai rasa nasaba da ummita ba dan yasa itace dukk'annin damuwar mama .
mama tayi shiru ta kasa furta masa komai saboda bata son fallasa damuwarta har sanda ya sake magana sannan tace "babu komai ma'aruf damuwar ummita ce ta haddasa tawa banason ganinta cikin damuwa da tashin hankali , itace karfin gwiwata idan tana damun kanta da yawan tunani yaya take son nayi ....?"
Sai lokacin idanunshi ya sauka akan ummita dake kwance jikin mama ,tsaki ya ja acikin ranshi yana maida idanunshi kan mama dan bazai iya cigaba da kallonta ba , yayinda mama ke cigaba da shafa sumar kanta "to meye damuwar ? Ya faɗa yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa .
"wai akan aurenta da rayhan ne na faɗa mata ta ɗauki lamarin a matsayin *wannan ce qaddararmu* dani daita
"Bata son shi ne daman ko me ?"
"Eh bata son shi na sha fama daita amman taki gashi abbanku ya zartar da hukuncin da bazan iya bijere masa ba"
sai da ma'aruf ya ja numfashi kafin yace "amma na ɗauka soyayya suke daman can ?"
Mama ta girgiza masa kai alamun a'a.
"shikennan mama kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki ki daina wannan kukan komai zai zo da sauki , ni zan samu rayhan din muyi magana ta fahimta dashi dan....."
Katse shi mama tayi da sauri yi "a'a ka barshi kawai karka ce masa komai idan maganar ta kai ga kunnen abba ko inna wani tunanin za'a yi daban ni kuma banason tashin hankali a wannan halin da nake ciki" mikewa yayi tare da fad'in "Allah ya kyauta ,ya saki hannunta ni zan tafi asibiti duba jikin mahaifiyarta suhaima yayi maganar yana kallon mama "allah sarki a she bata ji dadi ba ?
"Wallahi yau kwanata uku kenan a asibiti " Allah ya bata lafiya ka gaishe min daita " ko kallonsa ummita batayi ba sannan ba tace uffan ba , amman aranta tana jin babu dadi , ya gansu cikin damuwa da tashin hankali amman shi yana ƙoƙarin zuwa neman gindin zama , ta rasa gane dalilin haushinsa da taji a ranta ,rud'ewar damuwar da take ciki ne yasa taji hak'an aranta ko me ita dai bata sani ba,amman bata taɓa jin haushinsa irin na yau ba .
Yadda bata kalleshi ba haka shima bai kyalleta ba, dan ya fita jin abinda take ji acikin ranta tana jin takunsa yana cewa mama" sai ya dawo , yayinda zuciyarta ya tsananta dokawa har sanda ya fice daga d'akin ....
*******
Abu kamar wasa cin abinci ya soma gagarar ummita uwa uba rashin isasshen bacci ga zuciyarta dake wani irin mahaukaci bugawa da karfin gaske , ko ya-ya ta motsa sai zuciyarta tayi rawa tare da tsinkewa , duk yadda ta kwanta bata jin dadin rayuwarta sannan bata iya runtsawa , yadda take ganin rana haka take ganin dare ,ta rame sosai saboda ta sakawa zuciyarta damuwa suna zaune tare da meenal a parlour'n mama suna hira dan ta ɗan rage mata damuwar data lura tana tattare daita .
"ummita ki rage damuwar nan ta soma fasa jikinki kowa ya ganki yasan kina cikin damuwa , ki d'aurewa zuciyarki ki aure ya rayhan zakiji dad'in zama dashi saboda yana sonki fiyye da komai,uwa uba gashi had'ad'd'en gaye ne shima" tsaki ummita taja kana tace "meenal kenan ki daina tuna min auren ya rayhan da zanyi saboda zuciyata sam bata son rayuwa dashi ,koda bamu san irin wahalar rayuwar da mama tayi a gidan nan ba ,mun taso mun ga wasu daga ciki , dan me zanyi farincikin aurena da ya rayhan?
" bakya ganin kamar tarihi ne zai sake maimata kanshi ?
mahaifiyarsa bata son mama bata kaunar ta bud'e idanunta ta ganni, nasan ko inna bata bamu matsala ba ummansa zata kawo bare kinsan bakinsu ɗaya ,ni bama matsalarsu ce tafi damuna ba illa rashin son shi da banayi ne damuwar" ta K'arasa maganar tana sauke naunauyen ajiyar zuciya.
"nasani ummita Kuma nasan zasu aikata komai amman idan har kin tabbatar da bakin son aurenki dashi kuma bazaki iya rayuwar hakurin da mama tayi ba ki sheidawa iyayenmu tun wuri" da sauri tace "bazan iya ba meenal ,bazan iya kallon idanun Abba nace masa banaso ya rayhan ba , ni dai kawai ki ta yani da addu'a Allah ya kawo min dalilin da zai sa a fasa auren nan ....." ta karasa maganar tana sauke ajiyar zuciya tare da runtse idanunta , "Insha Allahu zan tayaki addu'a mafi alkhairi Allah ya za'ba miki" meenal ta fada tana tausayawa yar'uwarta .."ameen meenal na gode da kulawarki "
dogon lokaci suka ɗauka suna muhawara a tsakaninsu yayinda kirjin ummita ke wani irin dokawa da matsanancin karfin gaske , babu abinda ke d'aga mata hankali kamar yadda bugun zuciyarta ke sake k'aruwa da tsinkewa .
********
Da misalin ƙarfe shabiyu na dare ma'aruf ya dawo daga birthday party d'in abokinsa saleem , lokacin da ya shigo gidan bai jin motsin kowa ba ,yana shigowa kai tsaye yayi bangaren mama dan yasan da wuya idan ta kulle bangarenta dan sai taga shigowarsa sannan take kullewa , a hankali ya murda kofa parlour'n Ya shiga ya kunna wutar parlour'n ya nufi hanyar kitchen dan samawa kansa abinda zai ci ,bayan ya fito daga kitchen hannunsa rike da plet yana kokarin kiran mama tazo ta rufe kofarta idanunsa ya sauka akan kujera , ummita ya gani kwance idanunta biyu , ayi Sa'a itama ta waigo idanunta inda yake tsaye take zuciyoyinsu suka buga a lokaci daya sakamakon idanunsu da suka sarke cikin juna , wani irin shock yayi da ganinta kwance a parlour a daidai wannan lokacin saboda bai yi tsammanin haka ba, kirjinsa ne ya dinga dokawa kamar zai fito waje, sosai ya kafeta da manyan idanunshi , Ummita ta tsura masa fararen idanunta dake bushe tana kallon shi saboda yanayin shigar da yayi , bata kushe shigar ba acikin zuciyarta , sannan kuma bata yaba ba , yayi kyau sosai har da su sarka a wuyansa ga agogo diamon me shegen kyau da tsada d'aure a tsintsiyar hannunsa ,sai kamshi turare white aud yake bazawa kamar a lokacin zai fita , ita kanta tasan yana da kyau na bugawa ajarida, ko da fad'ad'd'en kirjinsa aka bar mace dashi ya isa ya dilmiyar daita cikin tafkin sonshi ,shi din irin halittar da mafi yawa daga cikin mata ke muradin mallaka ne , uwa uba ga tsayinsa da tsarin jiki mai kyau da Allah yayi masa , shi ba mai kiba ba kuma ramamme ba ga idanuwansa kamar mai jin bacci .
gaba-daya tsurawa juna ido suka yi suna kallon kwayar idanun juna Bata an karaba taji yaja dogon tsaki ya juya ya bar d'akin , nan take zuciyarta ta raya mata yanzu haka daga wurin yan matansa yake,amman kuma kamar a buge yake,"to ko shaye shaye ya koma yi ne ?
Ta yiwa kanta tambayar ai kuwa Ummita batayi bacci ba sai juyi take a parlour'n har sanda mama ta sauko ta rufe ko'ina idanunta biyu "ki tashi ki koma sama ku kwana tare dasu asiya mana "a'a mama zan kwana a nan ki barsu kawai, mama batace komai ba ta koma d'akinta sai goshin asuba tukuna bacci barowa ya saceta.
washe gari Ma'aruf bai so tashi da wuri ba saboda gajiyar dake tattare dashi amman ihun hajiya inna ne ya tashe shi, ya yunkura da kyar ya fito daga shi sai gajeren wando short niker da vest "me ye haka ne inna duk kin bi kin cikawa mutane kune da ihu shiyasa fa nake Allah Allah na bar gidan nan na huta da ihunki ?
"dan wannan ihun naki zai iya sa mutun kamuwa da hawan jini, haba mutun babu hakuri komai ihu ihu ke ba kya gajiya ne da ihu?
"kai babana kamin shiru anan abu akayi kuma dole ne nayi magana ta fadi haka tana hakikancewa da tada jijiyoyin wuya "koma dai meye dan Allah kiyi shiru haka ina son na kwanta na huta, "to shikenan naji, wallahi anci darajar bacci zakayi da yau sai.... "aka ce ya isa kiyi hakuri ki koma part dinki "shikenan ta sake furtawa sannan ta juya shi kuma ya koma part dinsa yana jan tsaki "haba mutun sam shi yace ba zai yi hakuri ba, komai sai yayi magana "
Sai misalin ƙarfe shabiyu na rana ya fito koda ya fito side din mama ya nufa yana shiga ya iske baki mata guda biyu take ya fahimci shine dalilin daya sa ummita kwanciya a parlour jiya , ahankali ya samu wuri ya zauna yana jiran mama ta gama lazimin sallar walha data idar , can ya mike yana dan dube dube kamar mai nimar wani abu wanda hakan yasa bakin mikewa sukayi sama , mama na gama lazimi tace "ma'aruf ka shigo" "eh" kawai yace mata "toh aka wo maka breakfast ne ?
yace "a'a ba yanzu ba , bana jin cin komai" kallon sa tayi sosai "toh ai shikenan, ina kaje jiya ne baka shigo gida da wuri ba" a take zuciyarsa ta raya masa wani abu , may be ummita tayi gulmansa ne , muryarsa a sanyaye yace "birthday din Salem naje , shiru mama tayi ba sake cewa komai ba sakamakon karar da wayarsa ta ɗauka, ya mike ya bar d'akin cike da sanyin jiki yana mamaki acikin ransa ..
Kai tsaye ɓangaren inna ya shiga nan ma ko gaisawa basuyi ba inna ta jiho masa tambayar babana ina kaje jiya ?shiru yayi yaki ce mata komai "babana magana fa nake da kai tsiyata da kai wannan dan banza miskilancin naka "karki dameni tsohuwar nan dazu kin hanani bacci mai dadi yanzu kuma kina son ki dameni da tambaya to naje gidansu Salem ne .....menene kike tmbyta?
inna tace "aha shi yasa ban yarda da maganar jairan yarinyar nan ba ,nasan wani abu ne ya tsayar da kai dan baka yawon dare , dazu nake jinta tana fada wa uwarta " wai yawon dare kake yi har ma da shaye shaye ga jarabar son mata tsiya karewa ma son matanka ran da zaka bar duniya za'a haifi wata mace inji wannan jairar mara kunyar yarinya shine kaji ina surfawa ita da uwarta, kai kuma da ɗan banzan salo kazo ka hanani ,amman naci alwashin kamar a kunnenka dan kaji dadin murje bakin rashin kunya " ina ruwana da maganarta ke yanzu kin yarda da abinda ta fadawa kenan ?
" saurin girgiza kai inna tayi "ina fa zan yarda da maganar wannan makirar babana, ai nasan kai d'a na gari ne ba bata gari ba ,ai kaine kake shishigewa ita da wancan munafakar uwartata me fuska bi....."a'a inna abinda zai sa muyi faɗa dake kenan yanzu babu ruwanki ,bana son ana aibanta mama agabana "tunda kanwar uwarka ce ba ?
Tayi masa tambayar tana karkata kai "koma dai menene babu ruwanki ke ko yankani zasuyi gunduwa gunduwa karewa maganata ki barsu suyi .. ....
yana gama faɗar haka ya mike ya baro d'akin "ai kuwa basu isa ba daga ita har uwartata mai fuska biyu , bazan taɓa yarda ba, ace ana sonka amman an iya zama ana zaginka wannan ai cin amana ne ...
bayan ma'aruf ya fito daga cikin gidan ya wuce masallacin shida wani bako da sukayi .
Bayan kwana biyu
da yammaci ma'aruf ya dawo daga kallon ball hannunsa rike da farar leda guda biyu yana shiga ya tarar da abbati bakon da sukayi zaune
a harabar gidan akan daya daga cikin fararen kujerun dake ajiye agurin madadin ya shige ciki ,sai kawai ya nufi inda yake , abbati na hangoshi ya washe baki har sanda ma'aruf ya k'araso ya janyo masa kujera , ma'aruf ya zauna "ya'akayi ne abbati hope kana jin dadin garinmu ? Ya K'arasa maganar yana buɗe daya daga cikin ledaodin dake hannunsa, takecare way ya ciro ya bud'e kayan fruit ne acikin ya d'auki daya ya kai bakinsa abbati yayi murmushi kana yace "sosai kuwa ai garinku akwai dad'i ga sanyi ni'ima ni Ina ganin ma anan su mama Asiya zasu barni ..
A hankali suka shiga tautaunawa suna shan fruit har abbati ya shigo da zance ummita "kasan sa'insan dake tsakaninka da ummita yayi yawa ,kuma fa irin wannan abun soyayya mai karfi yake komawa "rufa min asiri ko an kasa a kasuwa bana so "Allah kuwa da gaske irin wannan abubuwan da gaske yana faruwa, sai kaji iyaye sun ce ka aureta.
" kai dan Allah malam ya kake zakewa haka dayawa bayan nace ka rufa min asiri , ko babu maganar auren dake kanta da rayhan bazan aurenta ba , kai ama ture komai, nifa idan na auri ummita to dole zanyi kwanan parlour ,Kai har kukan bakinciki sai nayi wallahi ma'aruf ya K'arasa maganar tare da cewa " dan haka maza maza ka rabani da zanceta , bari na samu wanda zan tura ya kai wa mama kayan fruit dinta ,Yana waige waige neman yaro sai ga ummita ta fito sanye cikin doguwar riga baka har kasa rigar tayi mata kyau sosai, sai dai ta rame fuskarta tayi fayat tamkar wacce ke jinya, kana ganinta kasan tana cikin damuwa, ma'aruf na ganinta yayi shiru haɗe da kawar da kanshi gefe guda saboda bayason su haɗa ido daita ,abbati yace "lafiya kuwa naji kayi shiru ?
" babu komai kamshin turarenta ne ya ankarar da abbati ,dan haka ya maida hankali gurinta "yauwa ga ma ummita nan ta fito idan zata koma ka bata ta kai wa mama fruit din "a'a ya bashi amsa ataikace "
"Ko me yasa .... ?
"kai nifa idan na raina kasuwa ko sautu banyi, dan wannan yarinya ni ba shiga shirginta nake ba"kana da gaskiya dan nima gani nake kamar bata da mutunci fa, tana da shan kamshi maseefa yarinya kamar jinin sarauta kowa kallon gani gani take masa ta gabansu ta wuce batare da tace musu uffan ba haka zalika bata kallesu ba duk da jikinta ya bata maganarta suke , Maaruf yayi murmushi yace "haba abbati yanzu daga zuwanka har ka fahimci alkibilarta?
"I think yau ne fa ka cika kwana biyar a gidan nan ?
"Ko yau nazo na karanceta tsab saboda ina da saurin fahimta , ba shi yasa na lura da rashin shirin da kuke ba , gaskiya yarinyar tana da girman kai da d'agawa ga dan iskan miskilanci ,magana idan za tayi da kyar, abinci idan zata ci a yangace ,kai komai nata daban ...
" haba kai da zaka ringa janta da hira har ku saba ...
" a'a babu ruwana ni kam na fita hanyarta tun daga tana min kallon gani gani , ma'aruf ya haɗe fuska sosai "amman shine dan wulakanci kake auna aure a tsakanina daita bayan ga suhaimata can yariya mai ladabi da biyayya da sanin darajar mutane ,yarinyar da ko kara na saka bazata matsar ba ..
take abbati ya shiga kawo illolin Ummita daya karanta agurin ma'aruf , shi kuwa ma'aruf sai kushe ummita yake agurin abbati yana ji dadi sosai acikin ransa dama haushi abbati yake ji saboda yadda yake shishigawa ummita ....
Two friend's (bsbs)
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~TRUE LIFE STORY~
FREE NOVEL NOT FOR SELL
AL'QALUMAN
*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*
~DEDICATED TO~
*HASSANA DAN LARABAWA BESTY NAH, ITA KAD'AI NAKE KIRA DA WANNAN SUNAN KAF MEDIA, SON SO FI SABILILLAH*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
PAGE 21
...... Ya rayhan ya lura gabad'aya da yadda jikin ummita ya sake yin sanyi a tun sanda maganar aurensu ta bullo ,sam ta rage walwala da farinciki saɓanin lokutan baya , shiru yayi tsaye a bakin kofar parlour'nsu yana kare mata kallo mai ɗauke da alamomin tambaya iri iri, a cikin ransa yake aiyana abubuwa da dama , sai dai baya son jin komai a halin yanzu , domin sanin halin da take ciki bashi da wani amfani tun da yasan abinda ke damunta .
"yasan abinda ya canzata haka , amman da sannu komai zai daidaita da zarar sunyi aure , tun da yasan ba wai son shi ne bata yi ba ,rayuwar aure ne kawai bata bukata yin da shi ,sai dai yayiwa kanshi alkwarin da sannu zai koyar daita yadda zata so shi .
ya dade tsaye yana kallonta yayinda soyayyarta ke sake k'aruwa tana huda zuciyarsa da gangar jikinshi , baya jin duk runtsi duk wuya zai iya hakura daita , zai rayu da ita muddin rai matukar yana numfashi ...
Zuciyarsa na wani irin matsanancin dokawa kamar zai fasa qirjinshi ya k'araso inda take ya ja ya tsaya yana cigaba da kallonta ta rame sosai har ana iya ganin kashin dake zagaye da wuyanta .
"tun lokacin daya shigo parlourn jikinta ya sanar daita ya shiga saboda jin kamshin turarensa bugu da ƙari idanunshi dake yawo a sansar jikinta, sai dai bata d'aga kanta ta dubi inda yake ba har sanda ya k'araso ya tsaya a gabanta tare da kafeta da idanunsa .. zama yayi a kusa daita still idanunshi na kanta yana jin babu dadi a ranshi dan baya son ganinta cikin damuwa .
kusan minti goma ya ɗauka zaune a gefen bata waigo kanta ta dubeshi ba sannan bata ce masa komai ba illa ajiyar zuciyar da take saukewa da kyar .
Gajiya yayi da zaman shiru , gashi ya lura bata da niyyar kulashi ko ce masa wani abu, kuma yasan halinta ko zasu kwana a gurin bazata yi masa magana ba matsawar bashi ne yayi ba .
jikinsa a matukar sanyaye yana dubanta ya kamo laulausan tafin hannuta cikin nashi ya matse da karfi .. ƙara ta saki mara sauti haɗe da cewa "ashhhhhh Please yaya zafi ......
A hankali ya runtse idanunshi sannan ya sausauta rikon da yayi hannun nata yace " am really sorry sauraniyata , kiyi hakuri nasan duk ni ne silar danuwar nan taki amman ......
"karka fad'i haka ya rayhan ba kai bane kawai dai bana jin dadin zuciyata ne ta katse shi ta hanyar faɗar haka .. ... "meke damunki tashi muje muga doctor husain ya duba min ke bana son ganin haka ?
Girgiza masa kanta tayi batare da tace komai ba , dan a halin da take ciki idan tace zata sake cewa wani abu to kuka ne zai biyo baya .
Hawaye ne ya cicciko a cikin kwarnin idanunshi saboda yasan shine silar fad'awarta rayuwa kunci a wannan lokacin, saurin maida hawayensa yayi ya shiga kwantar mata da hankali , sosai ya dinga rarrashinta yana kwantar da kai tamkar karamin yaro duk kalmar daya san zai sakata farinciki ita ya dinga furta mata dan kawai ta samu natsuwar zuciya, shi kanshi yana jin fiyye da yadda take ji a zuciyarta , tunda me ye amfanin kana son mace ita bata sonka ? "Babu zuciyarsa ta bashi amsa da haka ,"ya san ummita tana son shi amman ba son irin na aure ba ,shi da zai iya hakura daita wallahi daya barta ko dan kwanciyar hankalinta, amman bazai iya ba .....
" kullun zuciyarsa dokawa take akanta tare da ninkin kaunarta, itace rayuwarsa duk saukar numfashinsa da tunaninta yake sauka , komai zai yi sai tunaninta ya sanyo kai ciki , yanzu haka zuciyarsa ciwo mai tsanani take masa akanta , ko daya tuntubi likita ce masa yayi ya rage tunani domin yana daf da kamuwa da ciwon zuciya , itama kuma abinda ke rubuce a file dinta kenan.....
"Me ya kamata yayi yanzu ?"ya hakura daita tayi rayuwarta har sanda ta samu wanda take so ne ko kuma ya jajirce ya aureta suyi rayuwarsu a haka ?
Yana kallonta ta zare yatsun hannunta cikin nashi ta zame ta kwanta akan kujera idanunta sun kad'a , ta fara runtse idanunta a hankali har ta rufesu ruf tana fitar da numfashi sama sama tamkar mai cutar asma ...
hawaye yaga suna bin gefen idanunta ahankali yaji tana rera kuka mai taɓa zuciya , ya sake riko yatsun hannunta yana kiran sunanta "subai'a kiyi hakuri ! Kiyi hakuri !! zan.........
sai kuma yayi shiru ya dakata ya mike da wani irin sauri ya fita daga parlourn yana ƙoƙarin goge hawayensa ,kai tsaye ya nufi d'akinsa kawai domin yana son ya samu damar da zubar da hawayensa ko zai daina jin rad'ad'in da zuciyarsa ke yi ,ya rasa dalilin daya kasa furta mata abinda ke ransa tabbas ya so ya furta mata zai hakura ne daita amman ya kasa furta hakan sosai yake zubda hawaye ....
Bayan fitarsa daga parlour'n rushewa tayi da wani matsananci kuka, sosai take jin tausanyinsa a halin yanzu ko babu komai bai cancanci taki shi ba wanda ke sonka yafi wanda ke kinka , dan haka daga yanzu zata sanyawa zuciyarta hakurin aurensa zata rayu dashi tunda ko bata auresa bata da wanda take so a yanzu, zuciyarta wankakkace bata san komai akan soyayya ba,tasan matsawar suna tare da sannu komai zai shude ya zama labari "kayi hakuri ya rayhan zan daina sakawa zuciyata damuwa sai dai bazan iya sonka ba muddin rai ,zan rayu da kai ba dan ina sonka ba ta K'arasa maganar tana sake rushewa da matsanancin kuka ...
Ta dade agurin tana kuka sannan ta yunkura da kyar ta nufi d'akinta ..
zaune ma'aruf da jafar da abbati suke a Parlour mama suna kallo , sai ga Ummita ta sauko daga sama da niyyar kwanciya , kawai ta gansu zaune , bata ce musu komai ba ta soma gyara inda zata kwanta taji alamun ana kwankwasa kofa ,cike da sanyin jiki taje ta buɗe a yangance saifullahi ne hannunsa rike da pack din ruwan roba wanda ya siyo wa mama a super market a hankali ta bashi hanya ya shigo bayan ya shigo ta amsa tayi hanyar kitchen ta ajiye pack din ruwan sannsn ta k'araso ta zauna batare da kalli inda suke zaune ba duk da tana son tace musu zata kwanta , amman girman kai da miskilanci ya hanata magana , Ma'aruf kuwa kallo ɗaya yayi mata ya fahimci tana son ta kwanta ne, dan yanzu anan take kwana tunda akayi baki, amma daya lura baza tayi magana ba, a ranshi yace "bai da lokacinta idan ta matsu ta magantu ,dan haka ya sake ware kafafunsa suka ci gaba da kallo da jafar , jifa jifa suna hira akan kallon da suke .....
tafi awa daya zaune a gurin tana tunani yadda zata kwanta suna gurin ita dai komai za'a yi bazata ce musu komai ba , duk abinda take Maaruf na ankare da ita ,har sanda suka gama tukunna suka mike shi da jafar suka fice zuwa side d'insa suna fita jafar ya kwashe da wata mahaukaciyar dariya yace" kai Maaruf baka da kyau ka cika yarinyar nan fa , naga hankalinka ba'a kan kallon yake ba amma saboda ka kunata ka zaunar damu"
" ai kaɗan ta gani tunda takamarta miskilanci da girman kai "
"Ai idan miskilanci da girman kai ne kai ta gado ta wannan bangaren bai kamata kaji haushinta ba , daman kuma hausawa sunce mabiyinka mafiyinka , ita bata tsaya a girman kai da miskilanci ba har rashin kunya ,uwa uba nuna kowa ba kowa bane agurinta , well koma dai menene rayuwarta na burgeni dan bata shiga shirgin mutane ...
" ai yau ba dan bakin dake bangaren ba , wallahi a wurin zan kwana naga karshen iskancin miskilanci sai dai ta kwana a kitchen ..
" jafar ya sake dariya gaskiya Maaruf kana kunna yarinyar nan fa da yawa , ba abinda yafi bani dariya sai lokacin da tace wa abbati ya rage sautin ƙaran tv cikin sanyayyiyar muryarta kamar tayi kuka Ina lura da ita wayarta ma dake rike a hannuta a dole take dan nawa..
"Kai rabani da maganar yarinyar nan please "
"ni kuma kaga ina son maganarta ba ko ya suka kare da abokina ..?
Ma'aruf bai sake cewa komai ba ya juya ya koma ciki ya nufi part d'insa inda ya iske abbati yana shirin kwanciya . ..
Washegari suna zaune tare da abbati suna hira yana shan fruit ,yana son yaron sosai saboda yana girmama na gaba dashi abbati ya dauki kankana ya saka abakinsa yana cewa
"ai ba kasan wani abu ba d'azun mun sha hira da mutuniyarka ...
nan da nan Maaruf ya chanja fuska tare da haɗe rai "kar ka kar6a cewa mutuniyata Abbati idan ba haka ba zan canza maka .....
"to yi hakuri na daina" in jinka ma'aruf ya fad'a yana cigaba da shan fruit ," kasan me tace wai tana son tayi aure amma ita a ra'ayinta bata son ta auri mai kudi ko wanda yake bala'i sonta dayawa ,a'a ita tafi son ta auri mara kudi wanda take so, shi kuma yake sonta kaɗan saboda idan ta auri wanda yake bala'i sonta baza tayi masa biyayya ba amman idan ta auri wanda take so zata yiwa masa biyayya ..
" ni kuma nace mata data auri mara kudi talaka gara ta auri mai kudi dan ita kalar masu arziki babu ma talakan da zai zo yace yana sonta dan ko gidan mutun ya kalla ya isa mutun ya fahimci tafi karfinsa amman yarinyar nan tace Ina ita bata san haka ba sai mara kudi take so wanda zai kula daita ya bata farinciki da. ......
"Shiiiiiiiiiii plz abbati maganar ta isheni kwalkwaluwata ta soma birkicewa babu ruwana da maganarta fatan dai Bata zageni ba ?
Abbati yace " a'a "
Maaruf ya mike ya nufi kofar gida ya bar Abbati a gurin sake da baki yana zancen zuci " anya.. sai ya katse tunanin shima ya mike ya bi bayansa ..
washe gari Ma'aruf yana zaune a kofar shiga part din mama, ummita na zaune daga ciki sanye da hijabi akan dudduma shi kuma Maaruf yana chat da budurwansa suhaima , kana ganinsa kasan yana cikin farin ciki da annashuwa ,kamar ance ya juyo ya hango ummita a bayansa tana zaune ta zuba masa ido, sai da zuciyarsa ta buga da matsanancin karfin gaske a yadda take kallonsa yaji kamar ya tashi yaje ya yaryarfa mata maruka tare da kashedi zuciyarsa ta cigaba da dokawa da sauri ya ɗauke kanshi, a madadin ya cigaba da chart sai kawai ya zarce da kira layin suhaima suna gaisawa tare da furta mata kalamai masu sanyi ,yayi haka ne dan kawai Ummita taji haushi , yayinda ita kuma tayi kamar bata san da wani halitta agurin ba , sai ma tayi kamar wacce take lazimi Yana gun bai tashi ba daga karshe ma ya dinga bugawa friend's d'insa mata waya a ƙalla sai da yayi waya da mata sama da biyar kuma duk a handsfree yasa wayar dan taji ta samu damar kai gulma....
********
..Kamar kullun Abba zaune a tangamemen parlour'nsa bayan ya kammala da duk wani abinda ya zama al'adarsa , sannan ya bawa yaran dake ɗan taya sa hira umarnin shigowa , ya dade yana hirar da su cikin nishadi da farinciki , ya aika saifullahi yayi masa kiran ma'aruf , cikin haka ya rayhan da sadam suka shigo domin kawo gaisuwa ,can bayan kamar minti a shirin sai ga maaruf ya shigo parlour'n bakinsa ɗauke da sallama lokacin Abba na zaune yana shan caffe , ya amsa masa sallamar ,a hankali ya karaso har gaban Abba ya durkusa har kasa ya gaishe da Abba cike da girmamawa , "ma'aruf kana lafiya ?
"Lafiya lau Abba ya fama da jama'a ?
"Alhamdullahi ,nan suka shiga muhawara atsakaninsu har kusan karfe goma suna tare suna hira , sannan ɗaya bayan suka fara kokarin barin parlour'n , duk suka watse, kowa ya nufi bangarensa sai mutun ɗaya ne ya rage zaune kansa a kasa wanda ko dan hirar da'aka yi bai wani saka baki ba saboda ya fuskanci tun shigowarsa Abba yake binsa da kallo , hakan yasa yayi saurin fahimtar akwai wata damuwar, duk da yasan lokuta da dama Abba na kiransa idan yaga lokacin shigowarsa kawo gaisuwa yayi har ya wuce bai shigo ba, sai dai yau yanayinsa ya bambamnta da sauran lokuta, shiyasa ya kasa tafiya parlour'n ya ɗauki shiru na kusan minti goma yayinda a hankali abba yake nazarinsa sannan ya d'ago ya dube ma'aruf sannan yayi gyaran murya kana ya kira sunansa "ma'aruf ........
hakan yasa ma'aruf ya tattara dukkan natsuwarsa garesa ya amsa da "Na'am Abba yana gyara zamansa ya d'ago kanshi kaɗan batare daya dubi fuskar Abba ba.
"a halin yanzu muna shirin zuwa ga mahaifin ita yarinyar da kake so da aure, sai dai wani hanzari ba gudu ba , mahaifiyarka ta nemi wata alfarma wanda tun kafin na nemeka na fahimtar daita cewar sai na tuntubeka.
take gaban ma'aruf ya shiga dukan tara tara , "wannan maganar ya tsaya min a rai tun ranar da ta fara faɗa min shi , hankalina ya ɗan tashi kwarai sai dai a jiya data sake min maganar naji idan nayi shiru ban mata adalci ba a matsayinta na mahaifiya , sannan a yadda ta daukekeni da karanci matukar dai naga abinda zai amfanimu dani daita dole ne na nasanar , ma'aruf ya sake gyara zama qirjishi na harbawa da sauri tun bai ji maganar ba walwala ta ɗauke akan fuskarsa ," wannan maganar ba wata magana bace illa akan sakina .........
A matukar firgici ya d'ago kanshi gaba-daya yanayin buguwar da zuciyarsa tayi bata saisaita ba, yanayin yadda ya tsorota sai yaba mutun mamaki,yayinda Abba ke kallon ma'aruf yana sake nazarinsa , jikinsa ke wani irin rawa tamkar wanda aka jona masa wutar lantarki , take idanunshi suka Kada suka yi ja, buɗe idanunshi yayi sosai yace "wace sakina kenan Abba ?
"Ta gidan baba sarki Abba ya bashi amsa atakaice yana dubansa ," hakika mahaifiyarka ta nuna tana bukatar ka haɗasu da ita yarinyar da kake so , ka aurensu gabadaya domin gudun maganar da zataje tazo, atakaice dai mahaifiyarka tana umartaka ka auri sakina amman nace mata lallai sai naji ta bakinka jikinsa ne ya kama rawa har Abba na iya ganin yadda hankalinsa ya tashi dan haka yayi ƙoƙarin kwantar masa da hankali " ka kwantar da hankalinka itama sakina yarinya ce mai nagarta da tarin ilimi zakaji dadin rayuwa daita karka duba girman da tayi maka ,domin hakan bawani sabon abu bane, fiyayyen halitta Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama ya auri matar data girmeshi da shekara shabiya bare sakina da kwanaki arba'in kacal ta baka ya K'arasa maganar yana sauke numfashi still idanunshi na kanshi ....
Tun da Abba ya soma magana zufa ke tsatsafo masa ta ko'ina a sansar jikinsa , yana son katse maganganun Abba amman bazai iya ba .
wannan shirun da abba yayi ya san jira yake yaji daga garesa , gashi shi gaba-daya bashi da lakar iya furta wani abu ko ma ya bud'e bakinsa bai san me zai ce ba, gara kawai yayi shiru ya cigaba da jiran tsammanin ..
Tsawon minti goma suna zaune parlour'n ya sake ɗaukar shiru yayinda idanun Abba ke kansa "kayi shiru ma'aruf baka ce komai ba ko akwai damuwa ne ? Abba ya dafa kan ma'aruf
"Kaje kayi tunani akan lamarin mahaifiyarka sosai ,duk da zanso kayi aurenka kamar yadda ka dauko niyya, amman ka daure kayi mata biyayya ta hanyar amincewa da auren sakina .....
Da kyar ma'aruf ya bude bakinsa yace "shikenan Abba ba sai nayi wani tunani ba tunda har kai ma kaga tana da nagartar da zan iya aurenta ,Allah ya tabbatar da alkhairi ka fadawa umma na amince tayi min addu'a saboda zuciyata na buqatar haka daga gareta , tausayinsa ne ya kama Abba saboda yasan ya dai amince ne kawai dan ya faranta ransu ba dan yana so ba "Masha Allah , Allah yayiwa rayuwarka albarka , yadda kayi mana biyayya kai ma Allah ya baka ya'ya masu albarka da zasuyi maka biyayya , Allah ya tsare mana kai ,naji dadi kwarai da wannan labarin ...
sai magana ta gaba akan abokinka muhd Sa'id ina son ka fahimtar dashi anyiwa ummita miji kar ya sake takowa gidan nan da sunan yazo gurinta , sai dai gurinka wannan kuma bazan masa iyaka ba " sai daya tsaida zuciyarsa sannan yace "Inshaallahu Abba zanyi masa magana tun farko ma na fahimtar dashi "to shikenan kana iya tafiya ka soma shirin auran mata biyu a rana daya ai d'ana jarumi ne .. Abba ya fadi haka cikin tsigar wasa ,da kyar ma'aruf ya mike tsaye bisa kafafunsa ya baro parlour'n Abba zuciyarsa na wani dogawa ,yana layi ya nufi bangarensa dafe da kanshi daya ji yana sarawa tamkar zai cire yana shiga ya faɗa saman katifarsa , ransa duk babu dadi tunani kawai yake "shikenan shima ya zama ummita... auren dole za'a yi musu shi daita , Allah sarki haka ya ɗan ji tausayinta ya tsarga masa, wani irin yanayi ya tsinci kanshi ciki na zallar bacin rai "sakina kin cuci rayuwata bazan taba yafe miki ba kuma da ikon Allah bazaki samu yadda kike so ba, ko kin aureni gangar jikina kika aura ,farinciki kuwa sai dai kiga ana yinsa a wani muhalli amman ke kam kinyi bankwana da farinciki, ajiyar zuciya kawai yake saukewa yana tunanin mafuta yana jin kamar yayi kuka ,ƙwaƙwalwarsa ce tashiga shawagin da cajin neman abinda ya kamata yayi , dan dole yasan abin yi , gaskiya sakin kin cuceni kin yiwa rayuwata shishigi sam bani da Budget din auren mata biyu a rayuwata yayi maganar fili yana cizan lip's d'insa na kasa , mikewa yayi ya soma zagaye d'akin ....
Ranar shima yadda yaga rana haka yaga dare yana tunani yadda zai kaucewa auren amman duk yayi tunaninsa ya gama bai gano hanyar bi ba , daga karshe dai bayin dake makale da d'akinsa ya nufi yayi alwala domin kaiwa Allah kukansa nafila yayi tayi tare da neman zabin Allah....
Ummita ce rike da hannun nusaiba diyar aunty Asiya ,tafiya take a natse kanta sunkuye a kasa ta nufi gidan mama rukkaya aminiyar mama kamar ance mata ta d'aga kanta motar muhd Sa'id tagani tana kokarin shigowa layinsu, wani irin zafin nama da bata san tana dashi ba ta damki hannun nusaiba taku biyar ya shigar dasu harabar gidan, har lokacin qirjinta sai bugawa yake da sauri bata kaunar ganin muhd Sa'id arayuwarta , asalima tsoro yake bata, da sallama ta shiga cikin gidan, mama rukkaya dake zaune ta fad'ad'a fuskarta da murmushi" "ummita talaka yana ganin ku yau satina daya da dawo wa daga ilori amman ko sannu da zuwa ina Amina ?
Ummita ta ɗan saki fuskarta kadan ita kanta tasan basu kyauta ba tuni suka cinye soyayyiyar awarar garinsu amman suka kasa lekowa suyi mata sannu da zuwa ,ta zauna kusa da nadiya diyarta . "ai shiyasa nima naki shiga gidansu inji nadiya diyar mama rukkaya "tam kuyi hakuri gaskiya bamu kyauta ba, kullun muna cewa zamu zo ni da meenal to jikin nawa ni sai a hankali yau lafiya gobe babu, ya kuka baro mutane ilori ?
"Suna nan lafiya har nayo meenal tsarabar samari Fulani kyawawa sai ta kawo tukuici dan ke nasan cewa zakiyi baki da lokaci "gaskiya kam samari me ana zaman qalau ni neman kai ma nake yi dasu , sai dai meenal din kamar yadda kikace.
"neman kai sai kace wasu ciwo, ke dai baki ga samarin garinmu bane shiyasa da tuni kin mika wuya har da rawar jiki yarinya suka bushe da dariya mama rukkaya tace "kunga ni nayi nan da wannan shirmen naku ummita na son mama rukkaya saboda mace ce mai kirki da natsuwa da sakin fuska akwai ta da son mutane kuma tana son mama sosai ..
Muhd Sa'id yayi parking daidai kofar gidan da ummita ta shiga bai yaudari kanshi da tunanin in ya aika ta fito zata fito ba ,babban burina kawai idan ta fito zata shiga gidansu ya sake ganinta dan yasan ko yayi mata magana ba zata kula shi ba tunda sakon mahaifinta ya iso garesa ..
"Ya buɗe murfin motarsa ya ziro kafafunsa waje ya danna CD inda take wakar naramali ta fara tashi, a hankali yake bin su ,a haka awa ɗaya yazo ya wuce, ya canza wani waka, a haka wata awar ta sake shudewa ,jikinsa ya gaji matuka da wannan zama sai dai zuciyarsa bata gaji ba ,ya sawa ranshi
Sai ya ga abinda ya turewa buzu nadi ,kamar yadda ma'aruf ya sanar dashi ya hakura daita rayhan zasu bawa, amman shi ina ba zai iya wannan hakurin ba ,dan zuciyarsa ta kasa fahimtar haka ,zuciyarsa ta makance ta kurmance baya ji baya gani komai sai tarin kaunarta ,idan a lokutansa na baya za'a sanar dashi akwai ranar da zai tsinci kanshi cikin zazzafar so irin na wannan lokaci hakika daya ƙaryata mai magana ,a halin yanzu soyayya ummita ta canza masa rayuwar bakiɗaya , ya kuma yarda ya amince da gaske ummita bata son shi ,kuma bazata sake sauraronsa ba , idan haka ne menene abin yi a gareshi?
Ya shafa sumar kanshi "abin yi kawai ya zauna daga lokacin har zuwa kwanciyar bacci yasan dai dole ta fito ta tafi gidansu ...
Wani tunani yayi ina zai samu yaron da zai kira masa saifullahi yaron da yake kauna har cikin ranshi duk da jin kanin abokin takararsa ne bai sa ya tsani yaron ba saboda shima yayi imani yaron yana kaunarsa ,da wannan shawarar ya fito daga motarsa ya soma takawa da alamun a gajiye yake , cikin haka wata mota kiran bmw ta faka abayan motarsa , matukin motar ya fito zai shiga gidan da ummita ta shiga, da sauri Muhd Sa'id ya K'arasa garesa "dan Allah abokina idan ka shiga ka turo min ummita , Umar ya kalleshi da tunanin inda ya sanshi ,kamar daga sama ya tuno yana ganinsa tare da ma'aruf "okay Bari na duba maka gidansu domin a irin wannan lokacin zai yi wuya ka ....
"Karka damu tana ciki ,na jima anan ina jiran fitowarta ,dan a ƙalla tafi awa biyu ,ina nan ta shiga ....
Two friend's ( bsbs)
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~TRUE LIFE STORY~
FREE NOVEL NOT FOR SELL
AL'QALUMAN
*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*
~DEDICATED TO~
*RAHMA LADINGO YAR MUTAN NIJAR NA GODE KWARAI DA KAUNAR DA KIKE MIN ALLAH YA BAR KAUNA*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
PAGE 22
...."shikenan ba na shiga na turo maka ita " ummita shanyar da kika yi a waje ta bushe sai ki fita ki kwashe, "maganar Umar ce ta katse hirar da ummita da nadiya kenan "shiru tayi tana dubansa batare da tace uffan ba "to me maganar ya Umar yake nufi ?
" ba dai har zuwa wannan lokacin Mayataccen mutumin data taki fita saboda shi yana waje ba ?
"Take kanta ya d'aure "me kake nufi na baba, ba dai wani ta bari a waje ba tayi likimo anan ?inji cewar mama rukkaya dake tsaye a bakin dokin d'akinta "Allah Hajiya mutumin data shanya cewa yayi awa biyu yana jiranta dan taga zuwansa .
take mama ta d'aure fuska "gaskiya ummita baki kyauta ba yanzu .....
"Nifa ba gurina yazo ba abokin ya ma'aruf ne, idan kuma yace gurina yazo ai na rigada na faɗa masa babu ni babu shi ..
"Ke dai wallahi har yanzu kanki yana tukunya kin kiyin wayyohlly koda yake yan fari fa haka suke da saunanci , had'ad'd'en guy irin wannan mai tsada ga kirki wannan mutumin yasan kanshi sannan su ke tashe yanzu a cikin agege ta kowani bangare yayi kyau ilimi ga kudi daya zauna masa "malama ki tashi kawai ki tafi kar ya canza ra'ayinsa akanki inji cewar Umar .
cike da hassala tace "bafa zani ba sai dai idan jana zakayi ka kai ni gurinsa canza ra'ayi kuma da zai yi wallahi har da azumi zanyi dan murna tayi maganar kamar zatayi ..
"Ba zai jaki ba da kafafunki zaki haba ummita wulakanci fa babu dadi sannan ki dinga tausayawa uwarki a wannan lokacin aurenki shi zai sake kwantar mata da hankali ,idan kika auri irin wannan mutumin kin wuce raini a gurin sauran yan'uwanki , dan Allah ki d'aure kije kinji diyar albarka inji cewar mama rukkaya bata sake cewa komai ba ta soma kokarin mikewa sanin ko me zata fadawa mama rukkaya ba amincewa zatayi ba , taso ma ta fada mata hukuncisu Abba akanta amman kunyar faɗa take taji a bakin mama .
cikin siririyar muryata ta kira nusaiba da suka zo tare ta rike hannunta suka fice Umar yana mata dariya bata kula shi ba ta fice a ranshi rigimammiya sarkin shan kamshi wannan mijinki na da aiki dan ko da yangarki kaɗai aka barshi ya isheshi fama ..
muhd Sa'id daya soma cire tsakanin da fitowarta nan da nan fuskarshi ta washe tamkar wanda aka aikowa da sakon rahma ya nufota ..
Ta kalli inda yake ma sai take ganin kamar babbar asara ce a gurinta , tana tafiya a hankali kamar hawainiya shi kuma yana Binta a baya yana furta mata kalaman da take jinsu kamar wuta ake diga mata cikin zuciyarta , duk saukar kalmarsa daidai suke da ninkuwar bacin ranta ",idan kinyi fushi dani subai'a ba ribar da zakiji a cikin zuciyarki domin Allah ne ya jarabbeni da sonki, ba zan taɓa yin fushi dake ba koda kuwa zaki dinga min korar kare a unguwarku ,kin kasa gane shi so jarabawa ne, ni tawa jarabawar ita ce kaunarki ina sonki subai'a son da bazai misaltu ba ......
Yana wannan banzar shirmen nashi ne ta samu nasarar shigewa cikin gidansu da sauri kasancewar sunzo kofar gidansu .
murmushi yayi tare da d'aga murya " i love you subai'a more than words Allah ya bamu alkhairi ......
Zuciyarsa cike da nishadin ganinta ya cigaba da tsayuwa agurin baya jin zai iya barin unguwar ,so kenan bashi da magani sai hakuri yana nan tsaye sai ga ma'aruf da jafar sun fito fuskar ma'aruf a daure tamkar wanda aka aikowa da sakon mutuwa shi kuwa jafar yana ganinsa ya saki fuska cike da tausaya wa yayinda muhd Sa'id yayi hanzarin qarasawa gurinsu ya mika masu hannu suka gaisa sannan sukayo waje gaba-daya ..
a wannan lokacin da ummita ke sanar da meenal abinda ya faru , rufeta tayi da faɗa" banza kawai shine zaki zauna kina hasarar hawayenki akanshi ,in ban da kina son ya rainaki me zai hana ki fito ki zage danginsa kaf tunda shi mayatacce ne , idan kuma ke ba zaki iya ba tunda yanzu kin zama kurma , me zai hana ki kirani wallahi bazan duba halakarshi da ya ma'aruf ba, sai na zageshi tsab ,bayan ta gama maseefar ta koma rarrashin ummita dan a zahirin gaskiya babu abinda meenal ta tsana irin 'bacin ran ummita ...
Zaune su ma'aruf suke a kofar gidan yayinda Muhd Sa'id ke faman rokonsa "dan Allah abokina ka taimaka kasa baki a cikin lamarin nan , bazan iya hakura da yarinyar nan ba, sonta kullum sake k'aruwa yake a cikin zuciyata ,ni kaina ina tausayawa yanayin da nake ciki , wallahi babu wata macen da zan iya rayuwa daita bayan subai'a , subai'a daban ce "da kasan yanda nake jin yarinyar nan a zuciyata da tuni ka taimaka min ba wai ƙoƙarin nisantani daita ba , babu wata mace a duniya da nake so kamar subai'a i love her more than my life plz ma'aruf don't leave me like this ......
tun sanda muhd Sa'id ya soma magana Kirjin ma'aruf ke aikin dokawa da matsanancin karfin gaske ,yayin da zuciyarsa da ilahirin gangar ke kyarma yana jin maganarsa na masa kuwa a cikin kunnuwansa ....
gaba-daya ya kasa kwakwaran motsi a zaunen da yake , dan maganganun muhd Sa'id haushi suka dinga bashi, a matuƙar hassale jin sai cigaba da naci muhd Sa'id ke sake masa yasa , ya kira sunansa muryarsa a kausashe "muhd Sa'id ya isa haka please , na gaji !na gaji haba !! "Maganarka ta dameni , dan girman Allah
Ka canza magana kana caza min kwalkwaluwa da shirme me kake son nayi yanzu ?
" Yarinyar nan na faɗa maka an rigada an saida mata miji lokaci kawai yayi saura ,daɗin dad'awa Muhd Sa'id ko ba'ayi mata miji ba . ......
Sai kawai yayi shiru ya kasa K'arasa maganar yana huci tare da rike gaban goshinsa saboda kanshi daya ji ya soma sarawa , shi kuwa muhd Sa'id kasa motsi yayi tare da rakfa tagumi, da zullumi ,da rashin sanin madafar dafawa, a qalla sun ɗauki tsawon minti goma suna zaune ma'aruf bai sake yunkurin cewa komai ba, haka muhd Sa'id da jafar, jafar ya so yayi magana amman yana jin tsoron abinda ma'aruf zai faɗa masa dan yasan halinsa ....
Naunauyen ajiyar zuciya muhd Sa'id ya sauke da karfin gaske kana yace "kayi hakuri ma'aruf , abinda yasa kaga ina binka da batun yarinyar gani nayi yar'uwarka ce asalima a d'aki daya kukayi rayuwa ..
" Tabbass d'aki ɗaya muka rayu amman common magana baya had'ani daita bare kace nayi maka yakin neman soyayyarta ,idan ma maganar tashigo sai dai .....ya sake yin shiru yana cizan gefen lip's d'insa na kasa ,muhd sa'id yace "ina jinka sai dai me ?
Numfashi ma'aruf ya fitar mai zafi sannan ya cigaba "sai dai idan ta tashin hankali zamuyi sannan tayi min magana amman ni daita bama magana ?
jafar yayi murmushi yana sake duban ma'aruf " kai ban ce maka idan tasan muna magana da sadiya diyar aunty asiya sai tayi duk yadda tayi poison maid dinta ta daina min magana ba , to in gaya maka yau satinsu daya a gidan amman cikinsu babu wacce ta sake yi min magana ..
ni ko ajikina gaba ta kai ni, dan daga ita har su iskar data d'auko su ma bansan da zamanta ba ..
"Bangane ba har kiyayyar ta kai haka aboki ? Inji cewar muhd Sa'id
"ta wuce tunaninku , ni yanzu bata ita nake ba Matsalata ma ta isheni naji da bala'i da nake ciki , a kwananki baya da nake jin zuciyarta wasai nayi tunanin 'bata ma shegiyar yarinyar fuskar da take ɗaukar hankalin maza dashi , lamarinta na mugun daure min "
"To ita me yasa take yi maka haka ? Inji cewar jafar "kai muddin macen data san tana mu'amula daita take min magana sai tasan yadda tayi ta daina min magana jafar ya sake yin murmushi "bala'i kenan "sannan a yadda na lura daita bata son cigabana duk abinda na tsiya sai ta min bakinciki , kai ko shegiyar wayar nan na canza sai shegiyar yarinyar nan ta min bakinciki "
"Shekaranjiya da daddare suna zaune tare da sa'ada suna hira a parlourn na shigo da kudi , haka nan zuciyata tace na bata ta ajiye dan mama tayi bacci lokacin kuma bana son na taɓa kudin , da safe dana shiga amsar kudin sai mama take ce min kudin waye na bawa ummita ajiya ta barshi a parlourn an shigo ɗauke kudin ,nayi shiru saboda nasan har ga Allah ba daukesu akayi ba suna hannunta bakinciki kawai ne , banga laifinta ba sai nawa dan koma da kudina ba ina tsaye sai kawai mama ta d'auko kudin "na wane kudin?
ta min kudi "gashi ka cire kudin " naki kar'ba na qara gaba saboda bazan amsar kudin mama ba .
"gaskiya wannan yarinyar yar matsala ce mijinta na da aiki "
Murmushi muhd Sa'id yayi "babu wani aiki sai dadi da zan ji dan inshaallahu ni ne mijin " "kai raba kanka da Wannan yarinyar
"ai ni yanzu abinda yake bani mamaki "me nayi mata take min irin wannan tsanar , abinda yake bani haushi kenan daita ..
"Ban mata laifin komai ba ,amman take min bakinciki ,"a rayuwarta kowa so take ya tsane ni kamar yadda ita ta tsane ni ,wallahi darajar mama take ci saboda ita nake raga mata amman ,ranar da abun yayi spack dina zan iya canza mata kamani gaba-daya ....
" wallahi da ba dan bana son rayuwar waje ba ,a wannan lokacin da zuciyata ke zafi da tuni na bar gidan "to kaje ina ? "ai gidan nan dolenka ne, dan idan ka tafi abba bazai ji dadi ba "ni zaka ƙalla kace in je ina ?
"Bari na gaya maka idan ina ra'ayi da tuni an wuce gurin ,dan ina da kudin da zan iya kama kowani irin gida nake da bukata a fadin garin nan " ku nifa yanzu ta damuwata nake da yadda zan yakice auren sakina nake ba wata ummita ba, ya juya ya fuskanci muhd Sa'id " kai kuma idan kaga dama ka cigaba da sonta har zuwa sanda zaka matu, "yaya zanyi ma'aruf ?
"ina matsanancin sonta bazan iya daina wa ba , idan na rasa ta zan iya mutuwa zakayi hasarata ..
Tsaki ma'aruf ja "wannan kuma damuwarka ce ba tawa ba ,karka sake kawo min maganarta ka barni naji da damuwata a halin zuciyata ke ciwo har ina jin felling d'insa na Kuma san tunani ne yana cikin magana kawai idanunshi ya sauka akan wani matashi dake d'ayan ɓangaren da suke zaune wanda ya tsurawa kofar gidan idanu tare da tunani , hannuwansa duka zube cikin aljihun wandansa ,kamar an tsinkari ma'aruf ya mike a hankali shima duka hannuwansa soke cikin ajihun wandonsa ,har lokacin daya K'arasa gurin matashin bai sani ba , sautin muryar ma'aruf ne ya katse masa tunani "lafiya malam kake kallon gidanmu irin haka ? Ma'aruf ya fad'i haka saboda sanin yanayin garin yasa yayi masa tmbyr , a mutukar firgice matashin ya ciro hannunsa ɗaya daga cikin aljihun wandonsa tare da tsotsa keyarsa alamun rashi gaskiya "eh wani nake jira ......
Ya bashi amsa atakaice jikinsa na d'an rawa, hakan nan zuciyar ma'aruf taki amincewa dashi , ganin irin kallon da ma'aruf yake binsa dashi yasa yayi saurin juyawa ya soma tafiya cikin sauri ma'aruf yayi saurin biyo shi "ka tsaya mana ina kuma zaka ?
a daidai wannan lokacin tuni matashin ya karya wata kwana mai shegen duhu ya kwasa a guje ,gaban ma'aruf ya ɗan fad'i amman ya tsaya shiru yana bin bayansa da kallo cike da farga
******
Bayan kwana biyu
Abba da injiniya suka je gun mahaifin Suhaimah, an tarɓesu ciƙe da mutuntawa, aka saukesu a had'ad'd'en parlour'n gidan ,bayan sun zauna , suka ƙara gaisawa a tsakanin su , kan kace me tuni an ciƙe musu gabansu da kayan marmari da ruwan roba tare da sauran abubuwan sha , ko cikakken minti goma ba suyi ba sai ga amini nan mahaifin suhaimah guda biyu sun shigo , gaigaisawa suka shiga yi tare da mikawa juna hannu , bayan sun Gama gaisawa suka ce sune wakilan ma'aruf nan suka musu bayanin akan abinda ya kawo su ,sunzo nemawa d'ansu ma'aruf auren suhaimah ne , ba tare da Bata lokaci ba mahaifin suhaima ya amince musu , hade da tsaida ranar biki wata biyar masu zuwa kamar yadda aka saka na ummita da rayhan .. ..
Da misalin ƙarfe biyu na daren ranar , kwance yake a d'akinsa a saman tintimemiya katifarsa , sanye yake da boxer jikinsa iya cinyarsa babu komai sanye ajikinshi ,yayinda gashin qirjinsa dana cinyarsa ke kwance luf luf tamkar na jarirai sai sheke suke , haka jikinsa wani irin mayataccen kamshi turare yake fitarwa na white aud yayinda kunnenshi ke manne da waya yana hira da suhaima motsin dirowar mutane ya ji yayi shiru ya kasa cigaba da waya ,a hankali ya mike tsaye ya isa jikin window gilmawar mutan ya gani sanye da bakin kaya yana nan tsaye ya sake ganin wucewar wani a haka yaga wucewar mutun huɗu take gabansa yayi mummunar fadawa ya cila wayar saman katifarsa batare daya kashe ba .. ya bude kofar d'akinsa a hankali ya fito sannan ya janyo kofar ya rufe yana bin bango a hankali idanushi ya sauka akan mutane suna ƙoƙarin bude d'akin mama da key soma shiga "Inna lillahi wa Inna lillahi rajiun ya furta a kasan rashi "kar dai barayi ne suka shigo ?
Ummita dake kwance a parlourn sai faman juyi take saboda ta kasa bacci, wani juyi tayi ta sauya kwanciya idanunta na runtse tana son tilastawa kanta bacci sai dai tasan wannan karya ne , ba kasafai bacci a irin wannan lokacin take iya bacci ba saboda damuwar data yi mata yawa ,ta juya yafi sau arba'in a wani juyi datayi ne taji motsin ana buɗe kofar parlour'nsu take gabanta ya fad'i zuciyarsa tashiga dokawa ,da sauri ta zabura ta mike tsaye jikinta na wani irin rawa ta koma bayan kujera ta la'be, jikinta ne ya bata babu lafiya , duk wanda zai shigo bangarensu a daidai wannan lokacin ba mutumin kirki bane , dadin dad'awa mukulin parlourn na hannunta, gashi yanzu taji ana ƙoƙarin buɗe kofar , tana durkushe a bayan kujera taji motsin mutane suna shigowa daya baya har suka shigo duka tare da dallera parlourn da tochlight mai shegen haske domin ganin inda makunnin wuta yake, take parlourn ya karade da haske ,ta mutsetsike idanunta ta gani shin gaske ne ko karya , barayi take gani a cikin parlournsu sanye da bakaken kaya ko kuwa mafarki take ? Ta mintsini gefen cikinta domin taji mafarki take ko kuwa gaske ne zafin da taji ya ratsata yasa ta fahimta duk abinda suke idanunta na kallonsu, kowanensu sanye yake da bakeken kaya da maks na fuska wanda ya rufe kansu gaba-daya ba'a iya ganin komai nasu hatta tafin hannunsu ....
Gumi ne ya shiga tsatsafo mata a ilahirin jikinta tare da kyar ta tabbatar wa kanta komai karshe gareta a lokacin dataji tsayuwar mutun akanta kaminin minti goma yana tsaye akanta bayansa tabi da kallo tare da rufe bakinta da hannuwanta duka, tuni fitsari ya nemi kufce mata yadda jikinta ke rawa haka zuciyarta ke dokawa ,"zaki ku tsaya anan nida damusa zamu haura saman mu sauko daita nan "okay oga babu case kuje kawai "inna lillahi wa Inna lillahi rajiun ta furta jikinta na sake ɗaukar kyarma wannan maganar ta oga baa kunnen ummita kaɗai ta fada har kunnen ma'aruf ta fada dan a daidai lokacin yana jikin window ..ganin mutun biyu sun haura yasa ta rarrafa ta bar bayan wanda aka kira da zaki ta shige kitchen tana shiga ta mike a matukar gigice jikinta na rawa ta shiga bude kofar kitchen garin buɗe plet din abinci ya fado kasa jikake taratsatsa aiko ta saki wata razananniyar kara tare da fadin "wayyohlly Allah tana cigaba da buɗe kofar da sauri zaki ya haske kitchen din a daidai lokacin data gama budewa har ta sanya jikinta waje "ke ki tsaya tiaga ga yarinyar da muka zo nema aguce ta karasa ta kwasa aguje tana ihu ji tayi an fixgo da karfi aiko ta sake sakin wani razananniyar kara data karade gidan, manneta yayi sosai ajikinshi tare da haɗe bakinsu guri ɗaya .. kamshi turarensa daya kaiwa hancin ziyara yasa ta fahimci a kirjin wanda take kwance sosai ta sake shige jikinsa ta kamkameshi tana kuka da shaƙar mayataccen kamshin turarensa , idanu ya zubawa mata yana kallon bayan sosai zuciyoyinsu ke bugawa kusan minti biyar ya zare bakinsa cikin nata , muryarsa can kasa kasa tamkar mai koyon magana yace "kiyi shiru fa ki daina kukan nan zasu iya jiyoki ....
Two friend's ( bsbs)
0 comments:
Post a Comment