....tun da suka shigo harabar the orenge palace qirjin ummita ke dokawa da matsanancin karfin gaske meenal dake tsaye kusa da Abdulshakur ta waigo inda take tsaye a bayanta , kallo ɗaya tayi mata ta fahimci halin damuwar da take ciki, ta ɗan matso kusa daita sosai ta kai bakinta daidai saitin kunnenta saboda qarar sautin daya karad'e harabar gurin tace "ki saki jikinki plz yanayinki zai fahimtar da mutane tarin damuwar da kike ciki , gashi idan baki manta ba kece wacce zata bada cikakken tarihin amarya, ki karfafa zuciyarki dan Allah kada ki bari tsoron ya mah'ruf yayi tasiri a zuciyarki ,kiyi kokari kiyi abinda zai hauka zuciyar ya mah'ruf dan ki fahimci tasirinki gareshi , na sanki nasan you can do more than that , ke din ta daban ce acikin mata , matar nuna wa ce sannan ta fita tsara ..
Tunda meenal ta soma magana jikin ummita ke kad'awa kamar mazari qirjinta na cigaba da dokawar da take tun farko "bazan iya ba meenal shi yasa tun farko nace karki zabeni amatsayin wacce zata bada tarihinki"
"Idan ban za'beki ba wa kike expecting na zaba ?
Ummita tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya ,
"kece mafi kusanci da rayuwata , kece kika san menal fiyye da kowa a duniya ,kuma nasan zakiyi active mai kyau shiyasa, sannan ina son kiyi active din da zai wargaza zuciyarsa da tunaninsa.
" ummita ...............
ta kira sunanta cike da kulawa ina sonki da ya mah'ruf bana son kina nisanta kanki da shi domin shima mijin nunawa sa'a ne wanda da ana likawa a goshi zaki iya likashi karewar zuciyarki , mijinki mijin da zaki yi tinkaho dashi ne bayan jini na yan'uwantaka kun dace da juna sosai fiyye da sauran ma'auratan duniya ,dukkaninku kuna wasa da zuciyoyinku ne amman batu na soyayya tuni kun kamu da matsanancin son juna babu wanda zai ganku bazai fahimci haka ba .
"wayyo menal ba zaki fahimta ba amman babu wata soyayyarsa a ciki zu.......
" Karki ce haka a ta wannan bangaren ,ko zaki boyewa kowa , bani ya kamata ki boyewa ba sannan ko rantsuwa nayi ba zanyi kaffara ba akan kuna tsananin son juna ke da ya mah'ruf irin taku kalar soyayyar kenan , Ki d'aure yanzu second game zamu fara karki sanya ke ko magana wani yayi miki agurin dinner din nan kiyi masa muga yadda zai nuna feelings dinsa ..
ummita ta buɗe bakinta da niyyar sake yin magana taji an bawa ango da amarya umarni shiga cikin hall dole ta tsuke bakinta .
a hankali suka jero ango sanye da wata dakakkiyar shadda gezner mai ruwan kasa , shaddar ta sha aiki zubi mai kyau har ajikin babbar riga, kanshi sanye da hula wanda ya dace da kayan jikinshi , kafarshi sanye cikin wani had'ad'd'en black shoe sai kyalli yake , haka itama amarya kalar kayan dake jikin ango take sanye dashi har kasa sai dai nata material ne hannunsu sarkefe cikin juna suke ta kowa ahankali domin shigowa inda tarin mutane suke zaune , nan take hankali masu video da masu ɗaukar hoto ya karkata garesu a tsanake suka shiga d'aukarsu , yayinda kawayen amarya na biye dasu abayansu har cikin hall inda sautin kida ke tashi nan take ango ya soma rawa tare da amaryarsa
Masu ɗaukar hoto nayi masu video nayi haka kawayen amarya da abokan ango na d'aukarsu a wayoyinsu da ipad saboda kyawun da sukayi mutane basu bar wayoyinsu sun huta daga ɗaukar amarya da angonta hotuna da video ba har sai da suka zauna a mazaunin da'aka tanada domin su .
Aka fara bude taro da addu'a sannan MC ya bukaci abbas babban abokin ango, ya fito a tsanake ya soma karanto tarihin abdulshakur ,makarantar da yayi tun daga kan kuruciyarsa ta primary da secondary ,har zuwa matakin jami'a daya kammala a ɗan fodio sannan ya da'ura daga inda had'uwar menal da abdulshakur ta samo asali ,abbas na kai wa nan ya juya ya kalli abdulshakur yace "ya naga kayi shiru kai da amaryarka me kuka tuna haka ?
"okay kun tuna ranar had'uwarku farko ko ? "kana tunanin irin harara da tsiwar daka sha agurin yayarta ko ? aka sa dariya ana tafi " ya sake juyowa ya fuskanci tarin jama'ar dake zaune suna kallonsa
" to muna murna muna godiya muna muku fatan alkhairi da kuka halarci wannan biki na babban aminina ..
Mc ya amshi lasifika a hannunsa yana barkwanci kana ya soma neman babbar kawar amarya , tunda sautin sunanta ya karad'e hall din zuciyarta ke rawa hankalinta ke kara tashi ita kaɗai tasan halin da take ciki a lokaci amman cikin taimakon Allah ta sanyawa jikinta jarumta tare da cijewa ta fito, a hankali take bada step zuciyarta na bugawa da karfin gaske haɗe da gyara zaman zaren styly din dake d'aure a kafad'arta wanda idan kagani zaka iya dauka gyalene nan styly din ne haka , har ta k'araso tsakiyar fili idanun tarin mutane dake zaune na kanta saboda wani irin azaɓaɓɓen kyau da tayi ko amarya sai dai ta nuna mata ita din amarya ce suhaimai kuwa tsabar gigicewa kasa tantanceta tayi bancin sunanta data ji MC ya ambata da bazata fahimci ko wacece ba ...
Kamar a mafarki Mah'ruf dake zaune kusa da jafar ya hangota tana bada step tamkar wacce ta fito gasar sarauniya kyau tana tafiya tamkar wacce kwai ya fashewa a cikin , da sauri ya runtse idanunshi yana girgiza kanshi sannan ya sake ware idanunshi tarrrrrr akanta "jafar idanuna ne ko kuwa , kamar fat lion dina nake kallo a tsakiyar fili can ?
"Itace mana wani abu ne ?
Ya bashi amsa batare daya kalleshi ba ko nuna wata damuwa " mah'ruf ya zuba mata ido kawai yana kallonta yana jin zallar 'bacin rai na ratsashi ji yayi a duniya ta gama wulakantashi da tozartashi , har lokacin imagine din ganinta haka yake ba kamar yadda ya bata umarni ba, har sanda ta amshi lasifika a hannun mc idanunshi na kanta yana mamakin karfin hali irin nata da rashin ɗaukar aurensa da daraja da tayi .
"masha Allah gaskiya ummita tayi kyau sosai kalli kaga yadda gabadaya mutanen dake cikin hall din suka maida hankalinsu gareta ,wani dogon tsaki mah'ruf ya ja ,cikin wani irin tashin hankali ya zabura ya mike tsaye jikinsa na kyarma , jafar yayi saurin kamoshi " ina kuma zaka ?
"dan girman Allah ka zauna karka hargitsa mana taro ga abu ya d'auko sugar ya karasa maganar haɗe da zaunar dashi akan kujerar daya tashi .
muryarsa a matukar fusace yace " kutumar uban taron dan me zaka hanani zuwa kalli fa yadda ake min wasa da aurena?
"Auren da kai kanka baka d'aukeshi da daraja ba dan me zaka damu kanka common my friend is better ka .......
"karka fada min maganar banza jafar ,sannan karka ɗauka ko kishin ina sonta nake no kishin aurena da cikina dake jikinta nake wa kar aje ayi min gangancin da zan rashi ya dafe goshinsa yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa " yarinyar nan tana ɗauke da cikina har na tsawon wata uku da wani abu ta yaya hankalina ba zai tashi ba kalli takalmin data saka mai tsini idan akayi kuskure ta fadi a irin wannan tafiyar shikenan zan iya rasa cikin jikinta yayi maganar cikin d'acin rai da tsananin bakinciki bai san subul da baka yayi ba sai daya ga irin kallon mamakin da jafar ya dinga binsa dashi kafin daga baya yace " what are you try to say mah'ruf ?
" ciki kayi mata na haihuwa ko me ?
"Idan ciki kayi mata a ina kayi mata yarinyar da bata tare a gidanka ba ?
"ban sani ba, kuma karka sake min wannan banzar tambayar irin ta mahaukata ,nida matata kake wani tsareni da idanu kana min folish question's "gud bazan sake ba, wannan kawai ya tabbatar min da kana matsanamcin son yarinya "aboki ka natsu ka sanyaya zuciyarka sannan ka godewa Allah daya azurtaki da samu mata kamar ummita arayuwarka , ka sauke wannan girman kan dake tattare da ƙwaƙwalwarka , ka lalla'ba matarka ku sasanta tsakaninku domin samun irinta da wuya .
" matarka tana da kyau na ɗaukar hankali matuka, ka duba ka gani duk fadin gurin nan sama da kasa mata ne kala daban daban amman kalli yadda ake kallon matarka .
Mah'ruf yayi shiru rungume hannuwanshi duka a qirjinshi idanunsa na kanta tana jujjuya jikinta gabadaya fuskarshi babu annuri ko kaɗan .
Ummita bata kalli inda yake zaune ba tayi sallama sannan ta soma bada tarihin amarya kamar yadda babban abokin ango ya bayar dana ango cikin tsadadden turancinta
"Ina kowa fatan alkhairi sakamakon halartar wannan taron na yar'uwarta masha Allah guri yayi guri alhamdullahi wannan amarya Kamar yadda kuka sani yar'uwace ta jini kuma babbar aminiya ce gareni , kamar yadda kuke gani amarya ce kyakkyawa son kowa kin wanda ya rasa ....
raf raf hall ya sake d'aukar tafi "ita wannan amarya ta kware gurin iya girki sosai ga kuma kwalliya uwa uba riko da addini da tsananin hakuri a zahirin gaskiya ango ina maka albishir ka dace da mace ta gari , ina kowa fatan alheri , sosai idanun mutane suka saidu akanta waɗan da suka santa nan suka shiga bada nata tarihin da irin ilimin da take dashi baka jin sautin komai acikin hall din sai tafi raf raf yayinda masu daukar hoto da video suka yi caaaa akanta suna aikinsu cike da kwarewa mah'ruf kuwa ya cika yayi fam jira yake jafar ya sake yin magana ya ɗauke shi da wani mahaukacin mari , Cikin Sa'a ta kallo inda yake tana rausayar da kwayar idanunta..
Wata ƙatuwar harara ya galla mata yana mata alama ta bar gurin da idanunshi amman ko gezau batayi ba hasalima nunawa tayi tamkar bata sanshi ba, mutane kuwa sai mamakin tarin iliminta suke a dan kananan shekarunta da basu wuce shatakwas a duniya ba.
bata mikawa mc lasifika ba har sai data kai inda take da niyyar tsayawa sannan ta mikawa mc speaker zata wuce, mc yayi saurin tsaidaita yana bawa mai hoto umarnin d'aukarsu, aiko ta gyara tsayuwarta a yangance tana sakar masa tsadadden murmushinta dake sake bayyanar da ainihin sihirtaccen kyawunta ..
take jikin mah'ruf ya dauki rawa ai bai san sanda ya mike tsaye ba sai gashi a tsakiyar fili agabansu yana raba idanu haɗe da ture mai ɗaukar hoto tun bai kai ga ɗaukar su ba "karka soma gangancin ɗaukar matata hoto da wani katon banza katon wofi yana gama fadar haka ya cafki tsintsiyar hannunta gam cikin nashi ya soma tafiya daita nan hankalin mutane ya dawo kansu menal ta cika da farinciki sannan ta sake gasganta zarginta akan yayanta shi kuwa jafar dariya har da rike ciki .
"Wai me ye haka ne plz ka barni nayi farinciki cikin mutane meye na wani katse min jin dadi ?
bai tsaya a koina ba sai a harabar gurin ya tsaya tare fuskantarta yana wurga mata wata ƙatuwar hararar data kad'a mata kayan ciki , batare da yace komai ba ya buɗe bayan motarsa ya nuna mata alamun ta shiga , dole ta shiga saboda ganin yadda fuskarshi tayi murtik , daga jikinta har kafafunta da zuciyarta rawa suke tsabar tashin hankali data tsinci kanta alokacin , ya shiga gidan baya inda ta zauna ya zauna yana sauke numfashi da karki sannan ya soma magana a fusace "lallai sai yau na yarda kin tabbata mahaukaciya wato da nace karki fito sai da hijab shine kika nuna ban isa dake ba ko?" kyace duk na gama haukana tsirara ma zaki fito duk abinda zanyi nayi ko ?
Tayi shiru taki cewa komai "shi kuma wanacan dan iskan banza kato da bai san ciwon kanshi ba sai wani lilleke miki yake kamar cingam kema da yake shasha ce da bakisan mutuncin aurenki ba har da wani gyara tsayuwar ɗaukar hoto ko?
A hankali ta furzar da iska tana juya masa keya alamun bata sauraronsa , matsota yayi sosai kamar zai shige jikinta dan har suna iya jiyo dumin juna, ya kai hannuwansa duka ya juyo da fuskarta gareshi "ga dan iska dole ki juya min keya , nan ma tayi masa banza taki cewa komai "ki koma gaba na mai dake gida kin gama naki biki..
Wani irin kallo ta watsa masa mai hade da harara sannan tace "kasan Allah wallahi babu wani gida da zan koma a yanzu ina tsaka da jin dadina , kai dan Allah malam ka sawwake min auranka da yake kaina ko dole sai nayi rayuwa da kai ?
"Haba duk kabi ka tauyeni ka hanani rawan gaban hantsi ,ka hanani na sakata na wala na gaji na gaji da auranka ka sakeni daga nan kowa yasan matsayinsa ....
hankalinsa yayi bala'in tashi bai taba tsintar kanshi cikin tashin hankali irin wannan lokacin akan furucinta na yau ba , muryarsa na rawa yace "haba fatlion kina cikin hankalinki kuwa kike wannan maganar ?
Ta kalleshi shekeke ,
sosai ta hango tsagwaron kishinta acikin kwayar idanunshi fiyye dana sauran lokutan baya , ko ba'a faɗa mata ba ta tabbacin soyayya ce ba kishin aurensa dake kanta ne yakewa ba .
Sai data sauke naunayen ajiyar zuciya sannan tace "kwarai kuwa ina cikin hankalina domin kuwa bazan iya cigaba da zama da kai ba ,kana zagina da cin zarafina da rashin d'aukata da daraja , kai biyayya fa ba hauka bane ni dai na gaji kawai ka sawwake min ....
Tsurawa ƙaramin bakinta ido yayi saboda ganin yadda take faɗar duk abinda ya fito bakinta batare da wata shakka ko fargaba ba ,hankalinsa ya sake tashi matuka duk yadda yayi kokarin shawo kanta ta koma gaban mota su tafi gida suyi magana a can taki ....
Ciki hall kuwa tuni aka soma ciye ciye da shaye shaye da rawa .
"kina ji ...."
"Ina jin me ? Ta katse masa hanzari tana yatsina fuska
"Babu abinda zanji daga bakinka dan duk abinda zaka faɗa ba saurararka zanyi ba ni dai ka barni nayi life dina ,ka sakeni na aure wanda nake so yake sona ta karasa maganar kamar zatayi kuka tana fidda numfashi da kyar tana jin wani irin abu akan shi da bata taɓa jin irinsa ba " tabbas tasan maganar meenal gaskiya ne ta kamu da matsanancin soyayyarsa , tana dai ƙaryata hakan ne domin bata son ta bawa hakan mahaimaci a rayuwarta , duk abinda take ji akanshi zata d'aure zatayi rayuwarta babu shi .
Shi kuwa wani irin gumi ne ya rufeshi sharkaf ta ko'ina ajikinshi dafe yake da saitin zuciyarsa tunda ta soma magana ya kasa ɗauke idanunshi akanta yana jin zafi acikin zuciyarsa , ya tsani yaji tace bata son shi ,bare aje ga batun saki.
a zuciyarsa yake aiyana muddin yayi sakacin rabuwa daita kanshi ya cuta , wani naunayen ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya kai duka hannuwansa bisa kuncinta ya tsuwara kyaukyawar fuskar idanunshi yana kallonta, ba wai yana mamakin dukkan maganganun da ta fada masa ba ne "a’a ya san ummita zata iya faɗin abinda ya fi haka akanshi ,sai dai kuma a halin yanzu yana mamakin kanshi da ya kasa ɗaukar mataki akan ta ,a hankali zantuttukan abokin shi jafar suke dawo masa cikin kwakwalwarsa ,jafar ya bashi tabbacin lallai yana son ummita ...
Shima dai ya rasa gane kanshi yanzu sonta yake ko kuwa kishin aurensa dake kanta yake ? ya rasa gane wane mataki zai ɗauka aciki soyayyarta ko kishin aurensa yake?
Take wani bangare na zuciyarsa yace kishinta kake mana , kyakkyawar zuciyarsa kuwa cewa tayi "kai malam duk inda kishi yake so na nan daskare ka yarda ko karka yarda kana son fatlion , haka itama tana sonka jikinsa a sanyaye ya kusanto da fuskarshi daidai fuskarta hancinsa akan hancinta sannan bakinta daidai bakinsa idanunshi na kallon cikin kwayar idanunta yayinda a hankali ya dinga shafa fuskarta da hannayensa duka wani irin shock da shauki ta ji ya ziyarci ilahirin jikinta tamkar wacce aka jona jikinta da wutar lantarki.
duk abinda ummita ke ji a sansar jikinta haka shima ma’aruf yake ji a jikinshi fiyye da koda yaushe bata ankara ba kawai ta ji ya hade bakinsu guri daya ya farawa bakinta wani irin tsotsa na fitar hankalin , ya rike fuskarta gam Yana shafawa saboda kokarin cire bakinta da take son yi , take jikinsu ya dauki rawa da shiga wani yanayi mai tafiyar da ruhi ,mah’ar ya ɗauki tsawon lokaci yana shan bakinta batare da gajiyawa ba , sannan ya Sakar mata bakin suka dinga sauke ajiyar zuciya a tare, fuskarta cike da shagwa'ba ta kaiwa kirji shi duka sannan ta fashe da kukan shagwa'ba "akan wani dalili zaka sha min baki bayan ba sona kake ba ?
" ba ka sona haka nima bana sonka saboda haka kar sake min irin wannan gangancin dan bana son irin wannan mu’amular na shiga tsakanin mu . ....
a hankali ma’hruf ya sauke hannun shi daya a kasan mararta yana shafawa ahankali yana kallonta yana jin wani irin feeling din dan’shi ko yar’shi dake kwance agurin "idan zan soki zaki soni fat lion ........?
Yayi mata tambayar yana cigaba da shafa mararta wanda hakan ke sake haddasa mata wani shaukinsa ajikinta 'sarai ta fahimci wayo yake son mata dan ya fahimci feeling's dinta akanshi , yatsina fuska tayi sannan ta cire hannunsa dake maranta "kai ma kasan abinda bazai taɓa faru ba kenan atsakaninmu ka soni ko ni na soka har abada it can .....
"Shiiiiiiiiiii karya ne fat lion kina sona kiyi tunanin abinda ya faru a kwanakin baya da kika hanani zuwa gurin matata ......, taja tsaki a zuciyarta "Kana tunanin abinda nayi a wancan ranar duk cikin soyayya ne?" nup kama daina wannan tunani domin kuwa nayi ne ba dan wata aba soyayya ba, nayi ne dan kawai na kuntatawa waccan dakikiyar matar taka mai kwakwaluwar kifi ,
dan haka ka daina wannan tunanin dan bazan taba sonka ba ?
Ya kashe mata idonsa ɗaya yana busa mata iskar bakinsa ta cigaba da magana " "alhamdullahi Allah yasa nayi nasara kuntata mata bisa zagina datayi na nuna mata ita din karamar ........
"shiiiiiiiiiii ya katseta "karki sake zagin matata agabana ina sonta ina ganin mutuncinta sannan tana da daraja acikin zuciyata ta ja tsaki a kasan ranta "kama hadiyeta idan zaka iya karewar soyayya tana gama zancen zuci ta juya zata buɗe murfin motar ya cakumota gabadaya ya matse ajikinshi yana sakin numfashi "bafa zan yarda ki koma ba, matukar na barki kika koma zan.......
Shiru yayi ya kasa maganar yana sauke numfashi itama numfashin ta sauke mai zafi ....
A galla sun ɗauki tsawon minti goma sannan ya sausauta rikon da yayi mata ya zira harshensa cikin kunnenta tayi shiru ta natsu saboda ta ɗauka magana zai yi mata amman sai taji yana tsotsar cikin kunnenta yana hura mata iskan bakinsa ,take tsigar jikinta suka mike tsaye ta dinga jin zirrrrrrrr ... zirrrrrrrr ajikinta ..
"Shike nan mu hakura da son juna ,tunda daman bamu taso akan haka ba , amman at least fat lion mu mutunta aurenmu ,wannan shigar da kikayi sam bata dace ba sai Allah ya tambayeni akan yadda na baki kulawa , ki taimakeni ki suturarta kanki kada wutar Allah ta cini jikinta na rawa ta goce kunnenta a daidai saitin bakinsa "naji ..
"Zaki yi min wannan taimakon ?
"Nace naji dan Allah ka sakar min jiki nasan anan can ana nemana .
"ai ni da wannan shigar ne banason ki koma cikin hall din ,wallahi da nasan shigar da zakiyi kenan da ni da kaina zanzo na daukeki ..
"amatsayina na wa kenan da zaka zo ka daukeni ?
"A matsayinki na matata mai sona ya bata amsa yana d'age mata girarsa "na faɗa maka ka daina tunanin subai'a zata soka "Ki kalli cikin kwayar idanuna ki sake furta min abinda kika faɗa yanzu ,yayi maganar yana shafa fuskarta tayi saurin runtse idanunta gam zuciyarta na matsanamcin bugawsa "bazaki iya fada ba ,kenan karya kika faɗa min cewar baki sona ?
Ta sake runtse idanunta gam saboda wani shauki dake dibarta zuciyarta na budewa soyayyarsa na samun masauki na musamman..
"komai zaki faɗa zuciyar mah'ruf ba zata ta'ba amincewa ba , saboda dukkanin alamomi son sun gama nunawa a tare dake kina son mah'ruf......
" Mahruf yana cikin nan ya nuna daidai saitin zuciyarta " ko kallon fuskarki akayi za'a tabbatar dan haka ki daina waskewa .. ...
Dan takaicin abinda yace bata san sanda ta fashe masa da kuka ba, sake matsowa yayi sosai jikinsa na kad'awa "plz karki min haka ta d'ago idanunta da suka cicciko da ruwan hawaye tana dubansa " karki yi kukan nan saboda bana son ki bata kwaliyar fuskarki mamakinsa ya sake mamaye zuciyarta tana kallonsa ya ciro hanky a gaban aljihun gaban rigarsa ya shiga ɗauke mata hawaye
" karki yi kukan nan saboda bana son ki bata kwaliyar fuskarki
ta sake maimaita abinda ya faɗa shiru sukayi suna kallon juna kwankwasa glas din motar da akayi da karfi ya dawo dasu haiyacinsu mahruf yayi warning yaga jafar ne tsaye dan haka ya soma ƙoƙarin fitowa yana cewa "karki ki fito haka .
"Lafiya malam ?
"Itace ta kawo haka kazo ka takure yarinyar mutane kana rage zafi daita idan anyi magana kace baka sonta . "uhmmmm ance ba'a sonta kuma baza'a sota ba meye matsalarka ?
"Karya ne wallahi kana sonta tunda ka iya dirka mata ciki dan girman Allah ka faɗa min a ina kayi mata ciki kuma tasan da zamansa ?
yayi masa banza tare da ciro wayarsa ya soma neman layin suhaima, kira biyar yayi mata sannan ta ɗauka tana magana da kyar ,dan ranta a mutukar 'bace yake saboda duk abinda ya faru akan idanunta da y'an'uwanta ya faru hajiya rahma ce tayita bata baki, if not taso ta biyoshi ta sauke musu hauka ,"ina kika ajiye wayar ?
"Tana cikin Jakata "okay fito mu wuce gida "okay kawai tace ta katse kiran hajiya rahma ta kalleta "mah'ruf ne ?
Ta gyada mata kai alamun eh "me yace miki ?
"Wai na fito mu wuce tayi shiru bayan kmr minti biyar tace "ki saki ranki ki tashi kibishi karki sake ki nuna masa komai da sannu zamuyi maganinsa ta mike tsaye ta suri jakarta ta fito harabar hall din kai tsaye inda taga su mah'ruf ta nufa tana cika tana batsewa jafar yayi murmushi "yau fa kana da aiki agabanki ga gimbiyarka sai cika take tana batsewa kasan fa akan idanunta komai ya faru "to ina ruwana ta fashe ma karewar cika tun kafin takaraso ya buɗe mota ya zira jikinsa ciki, ummita na zaune hawaye ya cika mata ido wani irin kallo ya bita dashi da tsantsar mamaki a fuskarsa a ransa yaja tsaki "ki tashi ki koma gaba ki bawa matata guri ,kuma bance ki fito waje batare da kin lullu'be jikinki ba, "da me zan rufe jikin nawa da "ban sani ba .
Ya faɗa yana bude murfin motar haɗe da kareta da jikinshi har ta koma gidan gaba ta zauna duk jafar na hankalce dashi ..
a matukar haukace suhaima ta karaso jikin motar ko kallonsa shi da jafar batayi ba ta bude gidan baya ta shiga ta zauna tana huci ,
Mah'ruf ya dawo gurin jafar "da wannan iskancin da guest in kayi daita ai ,mah'ruf yayi murmushi idanunshi na kallon bangaren da take zaune "kai dan Allah ban son iskanci idan ma ina bukata ba sai ka ankarar dani ba nasan yadda zanyi ..
ummita tayi shiru tana kallonsa , glss din motar bai hanata kare masa kallon tsab ba, yana magana da jafar da gani hira tayi musu dadi dan har sun tsarke hannunwansu cikin juna , take kwakwaluwarta ta shiga lissafin komai daya gabata tsakaninsu ,"ka soma zuwa hannu ya mah'ruf , zan tafiyar da akalar soyayyata acikin zuciyarka daki daki to the extended Sai ka furta abinda ke cikin zuciyarka, sai na tabbatar da na ruguza zuciyarka da komai naka da soyayyata hatta wannan ɗan iskan girman kan da kake ji dashi sai na sauke maka shi ...
Sun dade zaune acikin motar basu yi auni ba suka ga mutane suna ta wucewa kafin kace me mutane sun fara yashewa a harabar gurin , can sai gashi ya shigo motar bai ce musu kala ba yaja mota ya bar gurin a daidai bakin kofar gida Alhaji Ibrahim ya tsayar da mota mai gadi ya buɗe masa tangamemen get din gidan ya shiga tun kafin ya daidaita parking ummita tayi wani irin zabura har dukiyar fulaninta na kad'awa da niyyar fitowa" malama kibi a hankali mana ,ta dawo ta zauna sosai tana kallonsa fuskarta dauke da murmushi ya tsura mata idanunshi yana cizan lip's d'insa sannan yana daidaita tsayuwar motar cigaba da kallonsa tayi daga karshe ta riko hannunsa daya cikin nata tana murzawa alhankali tare da langwa'bar da kanta gefe kamar wata abar tausayi "me kuma nayi a hankali fa zan fita ?
"karka damu zan kular maka da kaina kaji mijina.....
sake tsareta da idanunshi yayi cike da mamakin kissa irin nata, yarinya ƙarama daita amman ta kware a iya kissa haka ......
A tsanake ya lumshe idanunshi da niyyar yi magana tayi saurin d'aura yatsanta akan lip's d'insa "plz ka kular min da kanka kamar yadda zan kular maka da kaina i love you more than you know sannan ta kai wa tafin hannunsa hot kiss da lip's d'insa Sannan ta buɗe motar ta fito sauran kaɗan ta kifa saboda abinda tayi masa .
bude idanunshi yayi yana hangota "ina ma wannan memont din ya zamo gaskiya ya tsinci zuciyarsa da faɗar haka kafin yayi wani abu tuni ta 'bacewa ganinsa ,ya furzar da iska ya juya baya inda suhaima take zaune zuciyarta na daf da tarwatsewa "ki dawo gaba .
"muje kawai "ban gane muje kawai ba direba zaki maidani ko me ?
"Dan Allah Malama ki dawo gaba banson shirmen kishin banza da wofi ,babu yadda ta iya ta dawo gaba tana zuba masa ruwan bala'i "saboda baka da zuciya sai wani biyewa yarinyar da bata sonka kake ,kana wani biyota abaya acikin mutune Sai kace bunsuru ko kunya bakaji ba , yarinyar sai kace wata diyar gwana ..
"da wannan iskanci da kuke ai gara ka kawota gidanka gabadaya .....
ilahirin jikinsa rawa ya kamayi saboda jin maganarta dole ya gangara gefen titi ya juyo a matukar fusace yana daka mata tsawa tare da cewa " idan ni bunsuru ne ke kuma me zaki kira kanki dashi ?
Yayi mata tambayar yana kallonta tayi shiru tana jan tsaki " okay tsaki ma zaki yi min tunkiya mara mutunci har ni zaki kalla ki cewa bunsuru akan matata ta sunah ....?
Yayi maganar yana figar motar da gudun gaske bai ko ganin sosai cikin tsananin 'bacin rai da bakinciki da takaici abinda tayi masa , bai tsaya a koina ba sai a kofar gidansu yana isa yaja wani wawan birki "oya fitar min a motata...
"haba habibi daga wannan maganar zai zama tashin hankali ........?
bai tsaya sauraronta ba ya fito daga cikin motar ya zagayo inda take ya bude yana ƙoƙarin fito daita "ka tsaya na fita da kaina ,kin tsayawa yayi, ya fito daita daga cikin motar tana rusa kuka a rikice ta karaso garesa tana rokonsa "kayi hakuri dan girman Allah na tuba bazan sake ba "Allah ya tsinewa uwar wanda bai sake ba , zaki san kin kirani da wannan kalmar " kije na sakeki saki daya ..... .
hankalinta ya tashi muryarta na rawa tace "haba habibi kana cikin hankalinka kuwa kake cewa ka sakeni "okya bari na kara miki wani sakin sai ki fahimci a wani yanayi nake ciki, ya buɗe bakinsa da sauri ta kai hannuta duka ta rufe masa baki .. ........
TWO FRIENDS BSBS
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~TRUE LIFE STORY~
FREE NOVEL
AL'QALUMAN
*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
PAGE 51
.....Gabad'aya jikinta rawa yake tsabar tashin hankalin data tsinci kanta ciki adalilin sakin da mah'ruf ya furta mata , bakinta na rawa ta soma magana cikin muryar kuka "dan girman Allah kayi shiru habibi karka sake furta kalmar sake gareni zuciyata zata tarwatse zan mutu habibi ,ina sonka mijina ,ina maka son da babu mahalukin da zan iya yiwa kamarsa ,bazan iya cigaba da rayuwa babu kai ,ka tausaya min mijina .......
A matukar fusace ya buge hannuta dake bakinsa tare da tsareta da manya idanunshi yana sake jin matsanancin sabon 'bacin rai mara iyaka kafin daga bisani ya katseta ciki fushi da tsawa " you are very stupid dake da shegiyar soyayyar da kike min , "a duniya babu tozartacciyar masoyiya kamarki suhaima ...
"da na san haka kike Wallahi da tun farko ban takura kaina gurin aurenki ba ,nayi nadama wallahi amman babu komai , Allah daya haɗa ya raba sai kibi wani jirgin .......
yana gama fadar haka ya juya ya buɗe motarsa a fusace yana huci ya shiga ya murd'a key ya bar unguwar a guje zuciyarsa kamar zata tarwatse ...
Juyawa tayi da kuka ta shiga gidansu tana zunduma ihu tamkar wata mahaukaciya sabuwar kamu "wayyohlly Allah na shiga uku na lalace , karo suka ci da zulaihat dake ƙoƙarin fitowa sakamakon sautin muryarta data jiyo, da sauri zulaihat taja baya tana dafe goshinta , cike da matsanancin tashin hankali tace " suhaima lafiyarki kuwa kike wannan zunduma ihun waye ya mutu ?
"Wayyo Allah nah zulaihat na mutu na lalacewa ta faɗa jikin zulaihat tana sake fashewa da kuka ..
Zulaihat ta d'ago kanta daga jikinta tana sake tambayarta a rud'e kirjinta na bugawa da matsanancin karfi "ki faɗa min abinda ke faruwa mana kin tasani gaba kina risgar kuka, sai data ja majina tace "wayyo Allah ni suhaima na mutu karshena yazo tunda mah'ruf ya sake ni .....
"What ?"when ?
Tayi mata tambayar ajere tana girgiza kai jikinta na sake ɗaukar rawa " me kika ce suhaimai ?
" Mah'ruf ne ya sakeni, ya sakeni ,ni yanzu yaya zanyi da rayuwata ? "bazan iya rayuwa babu shi ba ku taimakeni yan'uwana kar na rasashi idan na rasa shi mutuwa zan yi nima zaku rasani har aba .....
zulaihat tayi saurin kamo hannunta tana toshe mata baki hakan yasa ta kasa k'arasa maganar suka k'arasa bangarenta dake zaman jiran gawar shanu dan kar mahaifiyarsu taji
hankalinta ya tashi ..
Ta zaunar daita a bakin gado tana cewa "garin yaya haka ta faru ?
"Akan wannan muguwar tsinanniyar yarinyar nan ce ummita shine ya ... ....
ta kasa k'arasa maganar saboda kukan daya ci karfinta "wallahi bazan iya rayuwa babu shi ba aunty tayi maganar tana fixge dankwalin kanta tayi cilli dashi a tsakiyar d'akin tana wani irin kuka .
jikin zulaihat na rawa ta janyo wayarta ta shiga neman layin hajiya rahma bayan ta ɗauka ta koro mata halin da ake ciki , ko cikakken minti ashirin ba'ayi ba ta bayyana a gidan , nan suka kulle kansu a d'akin zulaihat suka yita rarrashin suhaima daga karshe suka yanke shawarar zuwa gurin baba na isheri domin karkato da hankalin mah'ruf .
suhaima tayi shiru tare da rafka uban tagumi tana kuka cikin zullumi da rashin sanin abun yi, dan gabadaya maganganu y'an'uwanta basa shigarta duk da bata cire tsamammanin akan shawararsu na taimaka mata ba, tasan matukar suna da hali zasu taimaka mata ta koma gidan mijinta "yayarmu dan girman Allah kar a ɗauki dogon lokaci ,aiki nake so mai zafi cikin gaugauwa bana son na rasashi a rayuwata ."bazaki rasashi ba suhaima ki bani nan da kwanaki biyar zuwa sati da kanshi zai zo har inda kike nayi miki wannan alkawarin.
ta rungumeta a jikinta tana janyo numfashi da kyar "na gode yayarmu Allah ya bar mana ke ina alfahari da ke nasan zaki iya komai ,hajiya rahma ta shafa bayanta tana cigaba da rarrashinta sai gurin sha daya saura hajiya rahma ta bar gidan shima ɗan mijinta ya azalzala mata ne if not Sai ta kai shabiyu .
Mah'ruf zaune shiru akan kujera mai zaman mutun d'aya ya da'ura hannunsa ɗaya a saman goshinsa yayinda d'ayan hannun ke bayan keyarsa yayi pillow dashi, yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa .
a hankali ya daura kafafunsa duka a kan Centre table din dake gabansa ya mike su yana girgizasu ,sosai ƙwaƙwaluwarsa tayi zurfi cikin tunanin sakin da yayiwa suhaima , gabadaya zuciyarsa babu dadi , sai dai bai yi nadamar sakin da yayi mata ba , cikin haka mama ta sauko daga samanta ta ganshi zaune cikin yanayi na damuwa da tashin hankali , kallo ɗaya tayi masa ta fahimci yana cikin zallar damuwa , take yar farar data sauko dashi akan fuskatar ta ɗauke ,ta karasa kitchen ta d'auko masa hollodian milk mai sanyi ta d'aura akan tire da glass cup ta fito ta d'aura tiren akan ƙaramin table ta tsiyayya hollodian a glass cup .
har sanda ta gama tsiyayawa bai san da zuwanta gurin ba , sai daya yaji tafin hannunta cikin sumar kanshi sannan ya motsa fuskar a murtike tamkar wanda aka yiwa mutuwa ,ya haɗe hannuwansa duka ya shafa fuskarshi batare daya yi magana ba ,
itama bata ce masa uffan ba ta mika masa cup din dake cike da hollodian data tsiyaya masa "ungo ka sha kaji sanyi .
jikinsa a matukar sanyaye ya kai hannunsa ya amsa yana sauke naunayen ajiyar zuciya sannan ya kai bakinsa ya kur'bi kaɗan ya ajiye cup akan table muryarsa a kasalance yace "na gode mamana "
"Me ke damunka baba babba ? Tayi masa tambayar tana tsareshi da idanunta ,da kyar ya buɗe bakinsa yace "
Babu komai mamana "
" babu komai shine duk jikinka ya sake haka? "ka faɗa min gsky karka min karya mana " hannuwanta duka ya kamo cikin nashi ya rike gam yana kirkiro murmushin dole "karki damu mamana zan sanar miki abinda ke damuna zuwa gobe inshaallahu , ya faɗa mata haka saboda yasan halinta matukar taji abinda ya faru tsakaninsa da suhaima tabbas zata takura ya dawo daita a daren, shi kuma abinda ba zai so faruwarsa kenan ba dan bai shirya dawo daita gidansa a halin yanzu ba, yafi son ko zai dawo daita sai ta taga rayuwa ta shiga hankalinta ta yadda zata san matsayinsa da darajarsa, bare baya tunanin sake rayuwa daita ,duk macen da zata iya kallon idanun mijin aurenta ta kirasa da kalmar bunsuru rayuwar aure daita bashi da faida ....
Murmushi mama tayi "fatan dai ba wata damuwar bace kou ?
Ya d'age mata girarsa d'aya alamun "eh .." to allah ya kai mu goben yasa muna da rai da lafiya , a hankali ya motsa bakinsa ya amsa da "ameen ..
Da sauri ummita take saukowa daga step har lokacin bata cire kayan dake sanye a jikinta ba , turus tayi sakamakon ganinsa zaune shiru tayi dan a tunaninta tuni ya dade a gidansa shi da matarsa .
mama na ganin saukowarta ta yunkura ta mike ta ɗauki abinda ya sauko daita tayi hanyar sama tana mata magana a hankali cikin muryar rada ta yadda mahruf ba zai ji ba "kije ki kwantar masa hankali da alamun yana cikin damuwa " tsuke ƙaramin bakinta tayi tana bin mama da kallo a ranta tace "haka kawai ya kwaso damuwarsa naje ni ya sauke akaina ....
Bayan barin mama parlour'n ya tsura mata idanunshi yana kallonta batare da yayi mata magana ba har sanda ta shige kitchen ta dibo abinci a plet ta fito ta wuce shi tana taka step da sauri sauri "fat lion .......
Ya kira sunanta da kasalalliyar muryarsa dake cike da tashin hankali , tsayawa tayi cak batare data juyo ba "ki daina irin wannan tafiyar da karfi plz ....."
Har lokacin bata ce masa qala ba ta cigaba da tafiyarta da karfi kamar yadda tayi niyya har ta sauka akan step tare da zancen zuci "ji min mutun da iyayi tsiya ko meye ruwanshi da tafiyata oho ?
"wayyohlly Allah ya faɗa da sauri yana dafe daidai saitin zuciyarsa a dalilin yadda ta k'arasa tafiyar da karfi .
ahankali ya tura hannunsa ɗaya cikin sumar kanshi yana chakud'awa tare da ciza lip's d'insa na kasa "i love you more than you know ya furta kalmarta ta karshe garesa a wanin da suka gabata daman yasan karya ne ba gaskiya ta faɗa masa ba ,kissa ne kawai irin nata ya san ba zata taba son shi ba gashi kai kuma ka kamu da matsanancin soyayyarta ba inji cewar kyakkyawar zuciyarsa..
A hankali ya shiga girgiza kanshi yana karyata zuciyarsa yana cigaba da jin abinda yake ji akanta ,yayinda ko wani part na jikinsa ke sake bud'ewa suna kar'bata acikin zuciyarsa da bata matsayi mai mahimmanci a rayuwarsa .... ..
Yana nan zaune har sanda kowa na gidan ya shigo , su meenal kuwa tuni an zarce daita gidan mijinta dake labak estate dake abulegba , ya mike akan kujerar ya kwanta yana tunanin ummita, yana son ya kice tunaninta a zuciyarsa amman ya rasa dalilin da yasa tunanita yaki barinsa hasalima sai sake kawo masa farmaki yake .... .
"to kod'an cikinsa dake jikinta ne ?
Yayi wa kanshi tambayar yana dafe goshinsa , take zuciyarsa ta amince da hakan ,yana son faɗa mata tana dauke da cikinsa ko dan tasan yadda zata dinga movement dinta amman yana fargaba bai san me zai faru ba idan tasan da zaman cikin , da karfi qirjinshi ke dokawa kamar zai fito waje saboda tsananin tunaninta daya addabi zuciyarsa, ya takure jikinsa guri daya tare da lumshe idanunsa yana shaƙar sanyayyen Kashim turarenta dake makale da kayansa ,
kusan karfe dayan dare yayi agurin yana kwance tana tunani batare da bacci yayi nasarar daukarshi ba.
bangaren suhaima kuwa itama kasa runtsawa tayi ko abinci daren kin ci tayi duk irin fama da zulaihat ta dinga yi daita taci abinci kin tayi har ta gaji ta kyaleta, ta barta da tunanin neman mafuta, gabadaya tunaninta kaf ya tafi ne akan yadda zata koma gidan mijinta da kuma yadda zata raba auren ummita da mijinta .. ....
ummita ta sake saukowa cin abincin dare tayi mamakin ganinsa kwance bai wuce ba ta k'arasa har inda yake kwance ta tsugunna gabansa tana kallon kyakkyawar fuskarsa mai tattare da haiba zuciyarta na sake samun natsuwa dashi , a hankali ta kai hannunta fuskarshi ta shafo kasumbarshi tana lumshe kyawawan idanunta , duk yana jinta ya sake lafewa yana sauke numfashi a hankali tayi kasa da hannunta zuwa faffad'an qirjinsa mai cike da yalwan gashi kwance luf ta soma shafawa tana cigaba da kallonsa .
a qalla ta ɗauki sama da minti goma tsugunne a gabansa tana shafa sumar fuskarshi zuwa qirjinsa tana kallonsa sannan ta yunkura ta mike tsaye da niyyar barin gurin on-expecting taji ya riko hannunta tare da fizgota ta fado saman fad'ad'd'en qirjinshi tana sauke numfashi haɗe da furta "wayyo cikina .....
ta soma ƙoƙarin mikewa daga jikinshi tana yatsina fuska da jin haushin abinda tayi gashi ya ka mata tana kallonsa da shafa jikinsa ,sake matseta yayi ajikinshi sosai yana fidda numfashi mai haɗe da shaukinta bai san sanda yace "sorry nayi kuskure bansan zaki ji ciwo a cikinki ba ya kike ji yanzu ko zamu hos.........
saurin datse harshensa yayi kafin ya k'arasa abinda yake son fadi ,
ta watsa masa wata ƙatuwar harara tana yatsina fuska wani irin kallo ta dinga masa kafin daga baya tace "plz ka sakar min jiki ta yunkura zata sake mikewa da karfi yayi saurin kai bakinsa cikin kunneta yana hura mata iskar bakinsa "plz ki taimakeni ki daina abubuwa da karfi irin haka ,da fa ba haka kike abubuwanki ba me yasa yanzu kike yin haka ne ?
"Ra'ayi ne ko dole sai na cigaba a yadda ka sani ?
"Yes ya faɗa tare da zarce wa da shafa jikinta , "kiyi hakuri ki daina zan ji dadi idan kika daina ,ba tayi ƙoƙarin dakatar dashi daga abinda yake mata ba,dan haka nan ta dinga jin wani irin dadi na ziyarar jikinta , kamshin turarensa da take shaka a halin yanzu yana sake haddasawa jikinta jin wani iri .....
yayinda feeling d'insa ke kawowa sansar jikinta farmaki ,fuskantar ya hade da nashi idanunsa na kallon cikin nata " "kallon me kike min har da shafani ko soyayyata ce ta hanaki runtsawa ?
tayi shiru haɗe da shigewa jikinsa tana sake shaƙar kamshin turarensa me kashe mata sansar jiki ....
" Fatlion ina matukar kishin aurena dake kanki fiyye da tunaninki haushinsa ya kamata ta tsani taji yace yana kishin aurensa dake kanta , kenan ita ba zai yi kishinta ba sai dai na aurensa ?tsaki taja a kasan ranta batare da tace masa komai ba
kusan minti goma suna haka yana yawo da hannunsa a sansar jikinta ita kuma tana faman lumlumshe idanunta alamun bacci, d'agata yayi suka bar parlour'n zuwa d'akinta ya kwantar daita shima ya kwanta ya zagaye cikinta da duka hannuwansa suna fuskantar juna yayinda hancinsa ke gugan nata, bakinsa daf da nata yana busa mata hucin numfashnsa me tafiyar da ruhi .
A tsanake ya dinga rabata da kayan jikinta yana ajiyesu a gefe haɗe da tabo wasu wurare ajikinta daya san dole idan ya ta'ba zata ji feeling d'insa ,taja numfashi da kyar ta sauke tana kokarin shigewa jikinshi, shi kuwa a tsanake ya dinga yawo da harshensa akan lip's d'inta kafin daga baya ya haɗe bakinsu guri daya ya shiga tsotsan bakinta tamkar wani mayunwacin zaki dan a matukar bukace yake daita sai dai ba zai iya kallon idanunta ya amfana da jikinta ba, yasan muddin wani abu ya shiga tsakaninsu tana sane kashinsa ya bushe agurinta .
kusan awa daya ya ɗauka yana juya harshensa cikin bakinta batare daya cire ba gabadaya ya manta da wata suhaima a rayuwarsa , itama ummita ya mantar da ita komai bata gane komai da kowa sai shi da sakoninsa a haka har bacci 'barawo yayi awon gaba dasu cike da shaukin juna sai goshin asuba ya farka ya maida mata kayanta ya shiga bayin dake cikin dakinta yayi wankan sarki dan a wasanin da yayi daita yayi realizing ya fito
ya qarasa inda take kwance ,kissing din goshinta yayi cikin zuciyarsa yace "mayya yarinya tayi nasarar dasa soyayyarta cikin zuciyarsa sannan ya fita zuwa masallaci ...
Yana fita ta sauke naunayen ajiyar zuciya dan ba wani bacci take ba , mikewa tayi a hankali ta shiga bayi tayi tsarki saboda yanayin jikinta daya ɓaci sakamakon hannunsa ɗaya kwana yawo a sansar jikinta sannan ta dauro alwala ta fito ta sauya kaya tana jin tafiyar tafukan hannunsa a fatar jikinta, tayi sallah zuciyar na makale da tunaninsa tana jin wani dadi na ratsa sansar jikinta da zuciyarta ," ina ma zasu kasance tare kamar yadda suka kasance a daren jiya ? duk da basu jiyar da junansu komai ba illa romacing dinta daya kwana yi .
Mikewa tayi ta faɗa saman katifa duk juyi sai ta tsinci kanta cikin yanayi na daban da bata taba tsintar kanta ciki ba sai akanshi ,ta san mijinta na daban ne acikin maza kuma na kece raini,sannan mijin yayi ne da kowace mace zata so mallaka har ma tayi alfahari dashi , "ki mika wuya kawai ummita ki rungume mijinki ,ki janyoshi jikinki ki bashi kulawar da zai soki ,ki manta komai kuyi rayuwarku ....
lamo tayi tana runtse idanunta da tunanin hanyoyi da zata bi domin mallake zuciyarsa da komai nashi ...
wuni ranar a kwance tayi shi cike da kewarsa sai dai har yammacin ranar bataji duriyarsa acikin bangarensu ba, shi kuwa yaki dawowa gidan ne saboda mama dan karta rutsashi da tambaya ..
Bashi ya shigo gidan ba sai gurin goma na dare kai tsaye part din mama ya shiga ya ganta kwance alamun ta soma bacci bai yi kokarin tashinta ba ya juya ya nufi dakin ummita, kwance ya isketa ta takure jikinta guri daya tana bacci cikin rigar bacci mai sharara kallo ɗaya yayi mata ya k'arasa shigowa da sauri ya haye saman katifa yana had'iye abinda ya tsaya masa a makoshi, ya kwanto jikinta ya kai bakinsa cikin kunneta ya soma hura mata iskar bakinsa kamshin turarensa ne ya kaiwa hancinta ziyara a hankali ta soma jin wani sanyayyiye dadi na shigarta ta sauke naunayen ajiyar zuciya sai dai ta kasa bude idanunta har sanda ya kamo ya kwantar daita ajikinsa suna fuskantar juna a hankali suke shaƙar numfashin juna kafin daga baya ya kai bakinsa dai-dai bakinta yana tsotsar pinky lips dinta har yayi nasarar cafko laulausan harshenta nan ta bud6e idanunta tarrrrr akan shi wata irin kunya yaji ta mamaye ilahirin jikinsa amman jin ta kai hannuwanta duka ta kamo fuskarshi tana busa masa numfashinta yasa ya sake rungumeta a jikinsa yana cigaba da sarrafa harshenta cikin bakinta cikin wani irin yanayi na shaukin juna suke exchanging numfashin , take yanayin fitar numfashinsu ya sauya suka rud'e tare da fita haiyacinsu , ya kai hannunshi kasanta yana shafa mararta zuwa pent dinta yana jin wani irin farinciki mara misaltuwa saboda jiyo tudun cikinta , cike da shaukinsa ta tura hannunta cikin sumar kanshi ta soma wasa da gashinsa tana sauke numfashi , wani irin numfashi yake fizgowa da karfi yana fitarwa, bai ankare ba ya ji ta cafke harshensa dake cikin nata ,ta soma sarrafashi tana tsotsar bakinsa kmr yadda taga yana mata , sai daya gama yamutsata sosai, da ragewa kanshi zafi sannan ya barta ya soma ƙoƙarin mikewa ta riko tafin hannunsa gam cikin nata tana narke masa ajiki tana fidda numfashi sama sama
da rausayar masa da fararen idanunta ,ya lura kwarai da zai dara daga abinda yayi zata bashi haɗin kai ,kokarin cire hannunsa yayi acikin nata amman taki sakar masa tana sake narke masa dole ya rankwafo jikinsa ya kai bakinsa cikin kunneta "menene fatlion ?
"Me kike bukata ?
Yayi mata tambayar yana hura mata iskar bakinsa cikin kunneta take tsigar jikinta suka mike gabadaya kamshin turarensa ya addabi hancinta da sake tunzira zuciyarta akanshi da matsanancin sha'awarsa ,yayinda iskar bakinsa da yake hura mata ya sake kashe mata jiki "kin yi shiru ki faɗa min idan akwai abinda kike bukata daga gareni saboda Ina son wucewa gida yayi maganar yana manneta da qirjinshi da tsura mata ido ,sai numfashi take fitarwa tana sake narke masa ajiki "baza kiyi magana ba ?
nan ma shiru tayi taki cewa komai duk da so take tace kar ya tafi ya barta ya kasance tare daita amman bazata iya furta masa haka ba ,
ta shige jikinsa sosai tana shaƙar kamshin turarensa ya daura hannunsa akan sumar kanta yana shafawa ahankalin zuwa gadon bayanta , ya zare hannunshi ya janyo blanket ya lullu'be mata jiki sannan ya sauko ya durkusa daidai fuskarta "zan wuce gida ki kular min da kanki ban da tsalle tsalle plz yayi maganar tamkar wani maraya "idan kina bukatar wani abu ki kirani tayi shiru tana mamakinsa "lallai namiji fa bai da kunya tsab ta gama karanceshi so yake ya mallaki jikinta cikin sauki sai dai ina bazata bari ba zata cigaba da rud'ashi kamar yadda yake rud'a mata jiki ..
*******
Hajiya rahma ke tafiya da baya da baya tana kokarin shigowa bukkan boka na isheri har ta karasa shigowa bukkansa sannan ta juyo da gangar jikinta tana kallo cikin bukkan inda ta iske bokan zaune babu komai ajikinsa daga shi sai wani dan kanfai da iya gabansa kawai ya rufe gabansa wani kasani acikin bakin dutse .
ya kalleta yana washe wakeken bakinsa tare da bushewa da mahaukaciyar dariya " shadiya yau kece a gari ?
"Nice aiki yanzu magani yanzu ta samu guri ta zauna can nesa kaɗan dashi tana kunshe miyon bakinta saboda warin da bukkan keyi "ya jikin alaja ? ya tambayeta cikin yaren yaroba yana jan layi biyu akan kasa da yatsun hannunsa .
" tana kan samun sauki dai "ai na faɗa mata abinda zatayi taki, daga karshe ma ta ɗauke kafafunta a gurina ,na faɗa mata zata samu lafiya amman lallai sai ta bada rayuwar mahaifinku domin nata rayuwar , hajiya rahma ta jinjina kai da girman al'amarin dan tasan wannan ba abu ne mai sauki ba , a yadda hajiyarsu ke son mahaifinsu ko farcensa ba zata iya bayarwa ba bare rayuwarsa ...
Boka ya soma buga kasa domin son sanin abinda ke tafe daita kusan minti goma yana aiki zana kasa sannan yaja wata ƙatuwar numfashi da ajiyar zuciya atare sannan ya soma magana cikin harshen yaroba "wannan yaron zai yi wahala ku iya mallakarsa kamar yadda kuke bukata saboda ta kowani bangare zagaye yake da tsari, iyayensa suna tsaye akanshi shima kuma haka babu yadda zaku iya dashi..
"yanzu babu abinda za'a yi yanzu ?
"Babu kuma duk inda kika je kudinki kawai za'a ci sannan ko anyi masa aiki daga karshe abun zai iya taba duka zuriaku saboda karfin addu'ar dake zagaye dashi ,dama baya tsaye gurin ibada ne akwai aikin da zanyi da kanshi zai dawo wanda
dawowarsa kuwa zai yi daidai da mallakarsa gaba-daya amman yanzu kije gida tukunna idan an kwana biyu ki dawo mu duba mugani "bama bukatar 'bata lokaci aiki mune bukata boka dan yar'uwata tana cikin wani hali taki ci taki sha ka sake dubawa idan akwai yadda za'a yi "babu shadiya idan akwai zan miki duk inda zaki akanshi kudinki za'a ci a banza irinsu asiri baya cinsu idan ma yayi tasiri na wani lokaci ne ..
Babu shiri hajiya rahma ta baro gidan boka tana surutai "yanzu me zata cewa suhaima bayan tayi mata alkwarin mah'ruf da kanshi zai dawo gareta ...
Jugun jugun sukayi a daki hankalinsu a tashe suna tunani mafuta dan kuka ma kasawa suhaima tayi sai dai idanunta sun kankace sun koma tamkar garwashin wuta naunayen ajiyar zuciya hajiya rahma ta sauke "ina gani mu dan dakata tukunan kamar yadda bokan yace "ni dai yayarmu kisan yadda za'a yi mah'ruf ya maida ni gidansa ta kowani hali ne ,ko kisa dady ya nemi abbansa ya bashi hakuri nasan muddin suka sa baki zai maidani.
"shikenan ki kwantar da hankalinki zan sanar masa idan Allah ya taimakemu ya maidake sai ki shiga hankalinki ,ki iya bakinki , kiyi taka tsantsa kiyi masa biyayyar karya na sha faɗa muku shi sihiri baya tasiri sai da biyyaya bawai da kun kama maza a hannunku shikenan ba ,ki kawar da idanunki akan duk abinda zai yi da yarinyar akwai makirci kala daban daban da zan koya miki ina tabbatar miki muddin kika rike biyyaya da waɗan makirci wallahi kina zaune zai dankarawa shegiya saki uku rasss ku matso kuji atare suka matso daga zulaihat har suhaima tayi musu rad'a kunne ,wani irin ihun dadi suhaima ta saki "dan Allah yayyarmu ki san yadda zaki yi na koma wallahi zanyi duk abinda kika ce nan suka cigaba da tautaunawa a tsakaninsu har yamma hajiya rahma na gidan, har sai data gana da mahaifinsu sannan ta bar gidan , faɗa dady yayiwa suhaima sosai sannan yace zai nemi Alhaji Ibrahim , bai yi sanya a gwiwa ba ya nemi Abba saboda shi kanshi baya jin dadin zaman ya'yansa gida gara sakin suhaima za'a iya gyarawa tunda saki daya ne , zulaihat ce dai sai hakuri .....
Abba yayi matukar mamaki jin bayanin dady daga karshe yace karya damu da izinin Allah kamar mah'ruf ya mayar da suhaima d'akinta ya gama ..
Karfe tara daidai Abba ya kira mah'ruf lokacin daya shigo parlour'n Abba , sai da gabansa yayi mummunar faduwa saboda ganin mahaifiyarsa da mama da injiniya har ma da Hajiya inna, guri ya samu ya zauna cike da biyyaya yana ƙoƙarin gaishesu inna tayi saurin katse shi "amman babana bansan tsami bane kai sai yau ta yaya dan rashin tunani , da rashin hankali zaka saki matar arzikinka, yarinyar mai biyyaya da sanin ya kamata da son yan'uwanka , shine dan ka iya wulakanci ka rasa wacce zaka saka sai ita sannan kayi mukut da bakinka da rashin hankali ...
tsaki yaja saboda takaicin maganar Hajiya inna ransa a matukar 'bace ya soma magana "kin san abinda tayi min da zaki zo kina damun mutane , wallahi idan kika hassalani zan mata mai gabadaya na huta .
" wanda ya fasa ya raina uwarsa da ubansa dan me shegen girman kan tsiya wa ka cuta kanka dan bazaka ta'ba samun kamarta ba ehee ..
"Hajiya dan Allah kiyi hakuri ki bari muyi abinda ya taramu anan kai kuma kar na sake jin bakinka idan bani na nace kayi magana ba. Abba yaja numfashi sannan ya cigaba "d'azu mahaifin matarka yazo da batun sulhu ina umartarka da kayi hakuri ka maida matarka d'akinta albarkacin mahaifinta daya tako da kanshi ..
Mah'ruf yayi shiru har sanda Abba ya dasa aya sannan yace "shikenan naji Abba dan bazan iya bujerewa umarnin ka ba amman gaskiya tare da subai'a dan gaskiya ina bukatar matata a gidana "me ?
" ai wallahi baka isa ba makiri ina allonka allonka yana jahannama "oho wato anje ayi maka asirin agumawa shine har da wani zakewa matata......kamar wani sha sha
"ai sai yanzu na fahimci inda abun ya nufa shiyasa ka saki yarinyar mutane ba laifin tsaye bare na zaune "wai inna meye haka ne matata ce fa subai'a me yasa kike son takurawa mutane da shiga rayuwarsu ne ?
" uwarkace karewar mata,kai ku zama kashi awaki ma amman ba zata tare a gidanka ba, kai auren ma zan raba gabadaya na huta da wannan jarabar "wannan ne kuma baki isa ba ,kuma allonki ne a jahannama ba nawa ba , haka kawai kin damu rayuwarki ki damu ta mutane ..
TWO FRIEND'S (BSBS)
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~TRUE LIFE STORY~
FREE NOVEL
MY YOU TUBE
CHANNEL
*HAUSA BAKWAI*
AL'QALUMAN
*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*
~DEDICATED TO~
*SA'ADATU AMINU UWAR GIDAN ƊAN GAYU ,UWAR FADEL DA AMAN DA SAURANIYAR MATAN DUNIYA (KHADEJAT) KAWATA INA KYAWUNKI*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
PAGE 52
"kai kar na sake jin bakinka a nan Inna abokiyar wasanka ce ? Inji cewar abba ya faɗa a matukar fuskance "ka barshi Ibrahim ya ci mutuncina dan ba laifinsa bane, na dade da sanin an rigada an mallake masa zuciya bashi da yadda zai yi sai yadda aka yi dashi , duk abinda yake nasan ba haiyacinsa yake yi ba, shiyasa ma ba zan ji haushinsa ba ,tunda aka kanainayesa da jikar agumawa ai sai yadda Allah yayi , dan ma bai d'and'ani zumarta ba ai nasan da sai ya wankeni da mari ta k'arasa maganar cike da maseefa da tashin hankali tana zabgawa mama ƙatuwar harara .
tsam mama ta mike tana ƙoƙarin barin d'akin , ganin haka yasa hajiya umma ta mike itama suna fita Abba ya rufe mah'ruf da faɗa "ina ganinka da hankali a she abun ba haka bane, a gabanmu kake fad'awa mahaifiyarmu abinda kaga dama ?
Mah'ruf ya sunkuyar da kanshi kasa kamar zai yi kuka ganin ran Abba ya ɓaci jikinsa a sanyaye yace "kayi hakuri Abba "shi kam injiniya kasa cewa komai yayi dan takaici , dan sai da yace kar a sakota cikin zance Abba yace sam dole sai ta sani yanzu ga abinda zuwan nata ya haifar "inna kiyi hakuri dan girman Allah inji cewar abba "babu komai Ibrahim banyi fushi ba dan nasan bayin kansa bane dan yaron nan tun farko ba son ummita yake ba, wannan yarinyar suhaima yake so daga baya aka bi dare aka bi duhu aka neman hauka min shi ..
mah'ruf ya d'ago ya watsa mata harara yana aika mata da mugun kallo "suwa suka bi dare .....?
"I think dukkaninmu umarnin rayhan muka bi "zanci mutuncika mah'ruf idan na sake jin ka furta wani abu "kayi hakuri bazan sake ba yayi maganar yana furzar da iska ..
"karki damu inna yanzu komai zai zo karshe ko cewa kika yi baba babba ya saki ummita a yanzu babu mai cewa a'a cikinmu domin gabadaynmu mallakinki ne sai yadda kika yi damu .
" ban dani dan ina bukatar matata ma'hruf ya fadi haka a kasan zuciyarsa "ka tashi ka wuce gobe inshaallahu matarka zata dawo d'akinta , a matukar zuciye ya mike tsaye zuciyarsa na tafarfasa ya fice .
Shiru ne ya ratsa d'akin Inna bata sake cewa komai ba, injiniya da abba suna zaune a gabanta suna tunani ,har ga Allah abinda mahaifiyarsu keyi yana matukar damunsu ba dan komai ba sai dan suna son tayi kyakkyawan karshe , suna tsoron ta mutu da hakin rayuka dayawa akanta ,babu wanda zai tallafa mata idan hakin mutane ya soma bibiyarta wanda basa fatan hakan ..
A hankali injiniya ya soma magana cikin zafin rai "Inna ki yiwa Allah da manzansa ki daina abinda kike yi ,a kullum maganarki bata wuce ta mairo da diyarta ,idan baki son mairo ita Ummita menene laifinta ?" Ummita fa jininki ce tunda jinin yaya Ibrahim ce me ya sa ba zaki rungumeta ba ,ita fa rayuwa babu tabbas, yadda Allah ya kaddarowa bawa bai isa ya canzawa kansa ba ,idan yaya Ibrahim ba zai iya faɗa miki gaskiya ba ni zan faɗa miki saboda ina son kiyi kyakkyawan karshen dan babu ruwan Allah da cewar mairo matar d'anki ce idan kin zalinceta bazai barki ba "dakata injiniya magana ta kare muyi abinda ke gabanmu "no ka bari mu fadawa mahaifiyarmu gaskiya duk duniya muni muka fi kusanci daita dole mu faɗa mata gaskiya ya kamata ace Inna ..."nace ya Isa abar maganar dan Allah abba ya karasa maganar cike da sarewa "bar shi ibrahim ya faɗa mun magana son ranshi Allah yasa shima ya haifa , shi ba magana zasu faɗa masa duka zasu masa mai goyawa karya baya kawai me nayi ?
"Dole ne sai na so mairo da tsatsonta ko dole sai so auren ummita da baba ?
Injiniya yayi shiru yana duban Inna cikin sarewa da tsantsar mamaki ai ko mutuwa tana jin kunyar mahaifa agaban uban ya ki dinga ikirarin bakya son yar da Allah ya soma bashi a duniya ,jikinsa a sanyaye yace hajiya Inna ..."hajiya Innar ubanka ? " ka min shiru gwanin iya magana da tsara zance , shi Ibrahim din bai da bakin magana ne sai kai uban kankaba kinibabbe ? Abba ya dubeshi yana masa alamar ya bata hakuri ,ya furzar da numfashi sannan yace "kiyi hakuri hajiya Allah ya huci zuciyarki "ka rike hakurinka dan babu abinda zan yi dashi ,
soyayya ce babu dole, bana son mairo yau bana son gobe Kuma banga uban daya isa ya sani na sota ba bare tsatson mairo, bari kaji ko duniya mairo zata haifa wa Ibrahim wallahi bazan so su ba gara na so bare akan ya'yan mairo tun farko nace banason hada iri daita aka fi karfina , to batu na soyayya ba isa a tursasa zuciyata ba "kiyi wa Allah kiyi hakuri hajiya Inna ni kaina ina nadama rashin bin umarnin ki amman babu yadda zanyi tunda hakan qaddara......
"ka min shiru ba da kai nake magana ba , ka bari na gama da wannan uban yan iya tsara maganar tukun abba yaja bakinsa yayi shiru "uban yan iya magana ko zaka iya saka min soyayyarsu a zuciyata ne ?
Shiru injiniya yayi bai ce uffan ba "ba zaka iya ba ,dan haka daga yau idan ina maganata karka sake min maganar mairo da tsatsonta idan kuna kaki zaka haɗu da fushina .......
Ta dubi abba "kai kuma kasan yadda zaka yi matar babana ta dawo gidansa a gobe goben nan tana gama fadar haka ta mike fuuuuuuuuu ta bar d'akin ,hawaye ne ya zubo daga idanun abba yana takaicin irin halaiyan mahaifiyarsa, kallon abba injiniya yayi wanda shi kaɗai ya rage masa a duniya shine mutumin da baya son ganin fushinsa ko ɓacin ransa bare akai ga zubar hawayensa yau shine da kansa yake zubarwa "kayi hakuri yaya bari naje na samu hajiya Inna gaskiya zuciyata bazata ɗauki ganin hawayenka ba abba yayi saurin dakatar dashi "sagir.........
Injiniya ya tsaya yana dubansa " ka rufa mana asiri yanzu ba lokacin yin magana bane bana son wani sabon tashin hankali muyi hakuri irin tamu uwar kenan sai dai muyita addu'a Allah ya canza mana ita, ka dawo ka zauna , a matukar zuciye injiniya ya koma ya zauna sai dai ya kasa furta daidai da kalma daya zuciyarsa na wani irin zafi .
Bayan injiniya ya zauna Abba ya dawo natsuwarsa ya soma yiwa injiniya magana cike da nasiha da rarrashi da kyar ya samu ya kwantar masa da damuwarsa dan Allah yayi injiniya da zuciya ,abba
ya kira mahaifin suhaima ya sanar masa da batun dawiwarta , lokacin da labarin ya iske suhaima har da suman dadi tayi ai kuwa tun daren ta soma haɗa kayanta.
daren rana Abba ya taso keyar injiniya da mah'ruf zuwa bangaren hajiya Inna domin su bata hakuri sai da Abba ya kai ruwa rana kafin inna ta sauko da kyar tace ta yafewa injiniya ,shi kuwa mah'ruf washe baki tayi tace "ai ba'a shiga tsakanina da babana ko an shiga ma kunya za'a ji da kanmu zamu shirya ko babana ? ya watsa mata harara batare da yace mata komai ba ..
Washegari da misalin karfe tara na safe a gidan mahruf yayi su hajiya rahma da zulaihat , mah'ruf na jin motsin shigowarsu, ya fito ya kulle kofarsa ya fita dan bai son su hadu bare su gaisa ,sun gyara mata ko'ina a cikin gidan ban da dakin mahruf sannan suka wuce da daddare still suka sake dawo wa domin rako suhaima ..
Satin suhaima daya kenan da dawo wa gidan ma'hruf amman har lokacin babu abinda ya shiga tsakaninsu ,baya cin abincinta , baya zuwa inda take idan ta shigo d'akinsa yayi kicin kicin da ranshi , yana kwance sanye da farar riga mai budadden gaba da farin wando iya gwiwa ta shigo d'akin cikin kayan bacci masu shara shara babu abinda ya boye na jikinta ga zubabbun dukiyar fulaninta a zahiri ana iya gani , sai dai ko ina ajikinta kamshi yake fiddawa ,ta tsura masa ido tana kallon jikinsa mai matukar kyau kwance da gashi yana fitar da haske ta lumshe idanunta tana bala'in son mijinta , kuma zatayi komai dan taga ta rayu daga ita sai shi sannan ta fitar da wacan yar iskan fatlion din acikin rayuwarsa
Ta hau saman gadon ta kwanta lamo ajikinsa tana sakin numfashi wani irin shaukinsa taji a sansar jikinta lokacin data tsinci kanta kwance a tattausan jikinsa, ga kamshin turaren jikinsa gyaraye dana dakin suna kaiwa zuciyarta farmaki hakan yasa zuciyarta sake macewa akanshi shi din ma'aboci son kamshi ne a koda yaushe ka kusanto inda yake cikin kamshi yake ta tura hannunta cikin rigarsa ta soma shafa gargasan gashin dake kwance a qirjinshi cak ya rike hannunta ya soma ƙoƙarin mikewa ta rigashi tashi ya koma ya kwanta ya juya mata baya ,ta sake kwantowa bayansa tana shige masa ya matsa yana jan tsaki ,ta hau kanshi ya tureta ya ɗauki pillow ya koma kasa ya kwanta ta biyosa ta manne masa "dan Allah kayi hakuri habibi wallahi bazan sake ba duk abinda kake so shi zanyi koda kuwa ganinka nayi tare da Ummita kuna autayya bazan damu ba tunda nasan matarka ce ta sunah zaka iya yin komai daita wancan ranar ma sautsayi ne wallahi na tuba bazan sake ba ya tureta ya mike yana jan tsaki ya koma kan kujeran kushin mai mazan mutun ɗaya dake d'akin ya zauna rigingine idanunshi a runtse yana kallon sama , ta durkusa gabansa tana dubansa cike da sanyin jiki tana rokonsa ,ta kusan minti talatin tana rokonsa sannan ya furzar da numfashi ya soma motsa labbansa "Komai son da nake miki bazan taɓa wulakata Ummita akanki ba, idan kinsa yaudara ce da karya acikin zuciyarki tun wuri ke daina damun rayuwata , idan kuma har yanzu zuciyarki bata amince da rayuwa tare da ummita ba hanya a bud'e take na karasa miki sauran sakinki dan bazan iya zama da matar da ba zata bi dokata ba ,dole kina son zama dani ki girmamani , ki girmama duk wanda nake tare dashi dan bazan lamunci rashin mutuncin ba ya qarasa maganar yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa "naji kayi hakuri nayi nadama a ran shi yace Karki yi ai daidai nake dake da kyar ta samu ta shawo kanshi suka daidaita ,tun daga ranar ladabi da biyyaya kuwa babu wanda bata yi masa haka ma yan'uwansa tana binsu yadda ya kamata barin inna komai ta samu inna da mama .
Karfe ɗaya na rana ummita tana tsaye a kitchen kusa da mama tana kwa'ba fulawa suna hira cikin sanyayyiyar muryarta ta kira sunan mahaifiyarta "mama .....
"na'am mamana ta amsa mata tana sake matsowa kusa daita "da zaki taimaka min mama da kin yi min d'an wake nan dan wallahi idan nayi da kaina bazan iya ci ba, ta k'arasa maganar tana langwa'bar da kanta cike da shagwa'ba.
"a'a bazan yi ba idan kin matsu da ci ki yi da kanki , kukan shagwa'ba ummita ta soma yi yadda kuka san wata ƙaramar yarinya tana yi tana bubbuga kafa tare da riko hannun mama cikin hannunta dake da fulawa "haba mamana , ki taimaka nifa mamarki ce zan sa miki albarka idan kika min.....
mama ta zaro ido waje tana murmushi cike da farinciki "wannan ai wayon shafa min fulawa kike "haba mama wallahi idan nayi bazan iya ci ba mama tayi murmushi tana kallonta " babu abinda zanyi kalli yadda kika 'bata min jiki kika bata naki "to kiyi hakuri mama zan goge miki ta dauko towel din da suke amfani dashi a kitchen ta soma goge mata ..
" Shikenan na hakura amman ki cigaba da aikinki idan kin gama ga girkin dare nan yana jiranki "shikenan mama duk da dai bacci nake ji amman zanyi , naso ina gama cin d'anwaken na kwanta na huta .
a hankali ta cigaba ta abinda take suna hira da mama gwanin sha'awa ,cike da tsananin son juna da kulawa mama tace "ummita ko baki da lafiya ne kika ja bakinki kiyi shiru ..?
Ta waigo inda mama take "me kika gani mama ?
"Gani nayi kin dashe kinyi fari kamar wacce shawara ta kama ,idan kinsan baki da lafiya ki faɗa min ta karasa maganar tana duba idanunta yayi fari "kin gani kalli yadda idanunki yayi fari ya dashe kamar baki da jini "ummita tayi murmushi "lafiyata lau mamana babu abinda ke damuna idan akwai zan faɗa miki dan bani da wacce ta fiki, numfasawa mama tayi tace "shikenan Allah yasa haka suka canza hira zuwa wata daban ..
Har sanda mah'ruf ya shigo basu sani ba , jin motsinsu a kitchen yasa ya tsaya a tsakiyar parlou'n yana kallon saitin kitchen din , bai ga mama ba saboda tana daga gefen ummita ya tsaida idanunshi kyam akan ummita yana kallon sama qirjinta da suka ciko suka sake tsayawa cak dan har yana iya hango saman dukiyar fulaninta , gashi tayi kyau sosai sanye take cikin jallabiyar daya siyo mata yellow wanda akayi adon duwatsu madadin tayi rolling din mayafin kayan sai ta ratayashi a wuyanta gashinta ya zubo bayanta kayan sun mata kyau matuka, domin sun fito da ainihi kyawun fuskarta da sirrin kyawun da Allah yayi mata , tunda ya siyo mata kayan bata taɓa sakawa ba haka nan yau tayi tunanin sakawa dan ta burgeshi ...
qirjinta taji yana dokawa da matsanancin karfi ta dinga jin idanu a jikinta hakan yasa ta fahimci ya shigo dan haka ta d'ago kyawawan idanunta ,take idanunsu ya tsarke cikin juna tsaye ta ganshi yana cigaba da kallonta da narkakkun idanunsa masu narkar mata da zuciya , lumshe idanunta tayi tana sake tsareshi da idanunta ganin ta tsaya taki cibaga da abinda take ta leko ganinsa yasa ta fesar da numfashi sannan tayi kasa da muryata " kawo na saka miki d'anwaken kije , ta waigo inda mama take tsaye tana dubanta sannan ta cire hannunta cikin robar fulawa batare data wanke hannunta ba ta fito a tsanake daga kitchen din ta tsaya gabansa tana kallonsa tana murmushi ,shima har lokacin idanunshi na kanta ya kasa daukesu .
ganin yadda yake binta da mayaattacen kallo kamar zai cinyeta yasa cikin sanyayyiyar muryarta tace "kayan da ka siyo min nasa ....
"na gani you look so beautiful sai dai duk kin 'bata kwaliyarki da fulawa ya faɗa yana kashe mata idonsa ɗaya haɗe da kai hannunsa zai goge mata inda ya ɓaci , qarar turo kofar kitchen din da mama tayi ya katseshi a tare suka kallo kofar kitchen din ,runtse idanunshi yayi yana shafa gaban goshinsa tace "bari naje sama na goge jikina na dawo ta kwasa a guje , bai san sanda ya biyo bayanta aguje ba yana takaicin gudun data yi ,koda ya shiga d'akin har ta shiga bayi ta wanke hannunta tana tsaye a gaban madubi tana goge gashinta da goshinta inda fulawa ya 'bata .
ya rike kugunsa da hannu ɗaya yana ciza lip's d'insa na kasa tare da tsura mata idanunshi bata ji motsin shigowarsa ba , a hankali ya shiga d'aga kafafunsa ya takowa inda take a daidai lokacin ta juyo da niyyar dawowa kasa inda yake , laulausan suman kanta ya sauka akan fuskarsa kaɗan ya rage bai shigar masa ido ba , ware idanunshi yayi yana kallonta yana shafa idonsa "zaki kashe min ido ne ki cuci matata ? "sorry ban ..ban sani ba tayi maganar tana murmushi ya matsota sosai kamar zai shige jikinta wani azaɓaɓɓen kamshi jikinta ke fiddawa mai sanya natsuwa da kwantar da hankali "da alamun yau kina cikin farinciki ko zan iya sanin dalili ?
Ta sake yin murmushi wanda ya bayyana tsantsar kyawunta da dimple dinta "abun dariya na zama ?
"A'a " ke dai faɗa min menene dalilin dariyar ? yayi maganar kamar zai rungumeta a jikinshi ,
"No naga fuskarka ta dawo irin nawa " Kina nufin irin fuskar zaki ?ya tambaya yana sake matsota ?"no no ta faɗa tana ja baya da sauri ya sake matsota yana ƙoƙarin damkota zuwa jikinsa ta gauce zata gudu ,ya kai hannu zai kamota "zo nan sai kin faɗa min gaskiya nasan ba wannan ne dalilin da yasa ki dariya ba "ta fixge tana dariya tana neman hanyar gudu yayi saurin tareta yana son kamota , ta rasa inda zata shiga domin buya kawai ta faɗa bayi ta maida kofar zata rufe yayi saurin tura kofar ya tsaya a bakin kofar rungume da hannuwansa duka a qirji yana shafa lip's d'insa "common Ina Kuma zaki boye anan ?
ta kalleshi a matukar tsorace tana girgiza masa kai a hankali ya dinga takowa har ya shigo cikin bayi ya rungumeta ya zira hannuwansa ta bayanta ya zagaye kugunta dashi , ya daura kanshi kan kafad'arta "na sanki fatlion murmushi ma wahala yake miki bare dariya faɗa min dalili dariyar ina son sani dan nima na
ta yaki .......
lafewa tayi ajikinsa tana sakin numfashi sama sama tana jin wani iri a gaba-daya ilahirin jikinta a lokacin data shaki kamshin turarensa gabadaya kamshin turarensa ya buwayi hancinta ji tayi tamkar su kasance a yadda suke har abada , shiru suka yi a tare suna musayar numfashin juna a hankali ta lumshe idanunta ,shi kuwa tunanin abinda zai mata yake wanda zai sake tsuma zuciyarta da farinciki .
jin yadda yayi shiru ya matseta ajikinsa yasa ta qara taku biyu , ya biyota tana rungumeta a jikinshi suka tsaya daidai saitin shawa "ba zakiyi magana ba ?
tayi shiru tana fixgo numfashi da kyar ya kai bakinsa daidai saitin kunneta "idan ba kiyi magana ba zamu tabbata a haka " ta lumshe idanunta "zan so haka ta faɗa aranta tana jin wani irin shaukinsa from know where yana mamaye jikinta , "Karki 'boye min mana ina son sani yayi maganar yana kissing din cikin kunneta da gashinta ya sake maida bakinsa cikin kunneta take jikinta ya soma rawa sakamakon kissing din kunneta da yake , gashi ya matseta a qirjinsa da kyar nunfashinta yake fita ,jin yanayinsa na sauyawa ta hanyar jin motsin jijiyarsa yasa tsoro mai tsanani ya kamata ta dimauce ta gigice a hankali ta kai hannunta ta kunna shawa
on expecting yaji saukar ruwa a jikinsu a matukar gigice ya sausauta rungumar da yayi mata ,kwawawan idanunshi masu matukar kyau da ɗaukar hankali ya zuba mata yana kare mata kallo , da kyar ya janyo numfashi idanunshi na kanta yayinda ruwa ke cigaba da sauka ajikinsu matsowa yayi sosai ya shige jikinta ya kaiwa wuyanta kiss ya sanya hannunwansa duka ya rungumeta tare da fatan samun saukin zugin da zuciyarsa ke masa akanta tunanin halin da baby'nsa zai shiga da ita kanta a dalilin ruwan dake zuba ajikinsu yasa ya kashe shawan yana haɗe rai kamar tunda aka halittosa a duniya bai taɓa dariya ba ,ta kalleshi taga ya haɗe fuska jikinta ne yayi matukar yin sanyi jikinta a sanyaye ta riko gefen gashin kanta daya sauko kafad'arta tana matsewa zuciyarta na harbawa da kyar ta samu ta sauke kwakwaran ajiyar zuciya da karfi , ya fito da harshensa ya lashi lip's d'insa can kasan makoshi yayi magana "me yasa kike careless da kanki ?tayi shiru taki cewa komai , ya kamota jikinsa ta lafe cikin jikinsa tana jin dadi a ranta lumshe idanunta tayi ta zagaye hannunta a bayanshi tana sauke ajiyar zuciya yayinda a hankali ya dinga hura mata iskan bakinsa ,ya kai bakinsa cikin kunnenta "bana son kina careless da kanki saboda
Ina matukar son kasancewa dake ,ki dinga yi komai a hankali karki sake kuskuren bari ruwan sanyi irin wannan ya taɓa jikinki muje ki sauya wasu kayan zan wuce gida ya karasa maganar yana kissing din wuyanta wayyo Allah ji tayi kamar yana fizgar ranta ne tana jikinshi yana kissing dinta suka fito ,manne masa tayi tana jin idan ya barta bazata iya cigaba da numfashi ba dan wani irin salon yake mata cikin kunneta da wuyanta ....
Zareta yayi ajikinsa ya k'arasa jikin wordrob dinta ya bude, wata jallabiya baka ya fito mata dashi ya dawo inda take tsaye takure da jikinta ya soma ƙoƙarin cire mata kayan jikinta ,taki "bani zan sa da kaina "ban yarda ba da kaina zan canza miki wani dare ne jemage bai gani ba ?
"Daren mutuwarsa ta bashi amsa da haka tana runtse idanunta ya zare rigar yayi filingin dashi ta saura daga ita sai pent da bra "Shima wannan daren na zuwa ko bajima ta kamkame jikinta "gaskiya ni dai ka rufe idanunka to "ya d'age mata girarsa daya yana girgiza mata kai alamu a'a "to ka samun kayan haka bana son ka......tayi shiru ta kasa karasa maganarta "bakya son naga jikinki ?ta daga masa kai ya tabe baki "to ke me zai hana ki rufe naki idanun ,ta sake girgiza masa kai tana juya masa baya tana kallon gaban mirrow batare da tasan nan ta kalla ba , ta miko masa hannunta "bani rigar na sa da kaina , madadin ya mika mata ,sai ya cire wandonsa ya saura daga shi sai rigar jikinsa da boxes ya ƙara taku daya ya ɓalle bra dinta "na rigada nayi niyyar saka miki kaya da kaina ki bari nasa miki na kama gabana "Amman Dan Allah ka rufe idanunka to " naji kema ki rufe idanunki ki tsaya da kyau ,tayi kamar yadda yace , ya zare bra dinta yana kallonta ta cikin mirrow, wani irin dokawa qirjinsa yayi duk da ba wannan ne karo na farko daya soma ganin dukiyar fulaninta ba amman sai da shaukinsu ya debesa yaji jijiyarsa tayi wani irin haniniya ta harba, ya kai hannunsa jikin kugunta yayi kasa da pent dinta yana cigaba da kallon qirjinta zuwa cikinta daya tasa kaɗan jin shiru yayi yawa tace "ka samin plz na soma jin sanyi ya haɗeye abinda yaji ya tsaya masa a makoshi ya kasa sanya mata rigar ya matsota ya zira bakinsa cikin kunneta ya shafa cikinta "kina da jiki mai ɗaukar hankali fatlion wani irin zirrrrrrrrr taji a gaba-daya jikinta tana buɗe idanunta karaf suka faɗa cikin nashi zaro ido tayi tana juyowa da sauri ta fizge rigar hannunsa ta kare jikinta tana bata fuska cike da shagwa'ba tace "me ye haka ne ? "me nayi ?yayi mata tambayar yana tsareta da manya idanunshi ya cire rigarsa ya rataye ajikin handle din kofa yana
takowa inda take ta faɗa saman katifa ta rasa ina zata rufe ajikinta ,kawai ta kai rigar ta rufe kasanta dashi bar qirjinta ya kwanto jikinta ya rankwafo jikinta batare daya danneta ba zubawa dukiyar fulaninta idanunshi , tayi saurin lumshe idanunta tana zumburo masa baki "dan Allah ka bari na sa kaya , ya harareta yana dallare mata baki sannan ya kai bakinsa saitin nata ya fara tsotsan lip's dinta har yayi nasarar bude bakinta ya fara tsotsa tamkar ya samu lolly Popp yana shafa sumar kanta zuwa qirjinta shiru tayi jikinta na rawa tana jin dadin yadda yake tsotsar bakinta ya kai hannunsa zai shafa qirjinta ta rike hannunsa gam tana girgiza masa kai idanunshi cike da shaukin qaunarta ya zare bakinsa cikin nata yace "why me yasa baki so na
ta'baki ? " Bana son abinda zai saka mahaifiyata cikin damuwa "kamar ya ?"kamar yadda hajiya Inna take buƙata, ya ja tsaki ke yanzu idan na ta'baki wa zai sani ko zuwa zaki yi ki faɗa mata ? "Ni dai a'a banaso, bana so bana son damuwa da tashin hankali ,ganin bashi da niyyar magana ta janyo rigarta ta zara daga kwance da take yana kallonta ta rufe masa abinda yafi kauna daga gareta ya kai hannunsa zai zare rigar ta saka masa kuka dole ya kyaleta zuciyarsa na tafarfasa ya janye jikinsa yana janyota jikinsa ya k'arasa saka mata riga ya mike ta riko hannunsa ya juyo "meye kuma ya faɗa a fusace? "ka bari t shirt dinka da wandoka ya bushe "baza'a bari ba ya fixge hannunsa a fusace ya maida wandonsa ya dauki rigarsa ya kakkabe ya zira ya fita daga d'akin ta sauke nannauye ajiyar zuciya ta rufe kanta da hula dan kar mama ta fahimci wani abu daban, ta fito daga dakin zuwa parloun kasa gabanta na fad'uwa bata ga mama ba ta zauna akan kujera tana tunani kala kala can kamar minti goma sai ga mama ta sauko tayi saurin cewa "mama da wani aiki zan soma dan na gama da wuri ?"kinci dan wanke ne ? ta girgiza mata kai "ki ci tukun sai muyi aikin tare,ummita ta yatsina fuska yama fita araina wallahi da dai ma zan samu mangaro ko tsamiyar biri mama ta bita da kallon mamaki " mangaro ko tsamiyar biri anya kuwa ba ciki ga ummita ba ?" Tace wannan tace wancan Allah dai ya taimaketa ba wani abu ne ya shiga tsakaninsu da mah'ruf ba ta shiga uku a gurin hajiya Inna ,ta matso da sauri ta zauna kusa daita ta kamo yatsun hannunta tana dubawa da idanunta "ciki ne dake ummita ? Tayi mata tambayar hankalinta a tashe .
Wani irin luguden bugu qirjinta yayi da matsanancin karfi a tsorace ta kalli mama "a'a wallahi mama bani da komai "kinga samu natsuwa wani abu ya taɓa shiga tsakaninki da baba ne ? ta sake girgizawa mama kai "ki bude baki kiyi min magana mana "wallahi a'a mama, haba mama kamar wata wawiya ina ji fa ina ganin abinda hajiya Inna take miki acikin gidan nan dan me zan aikata wani abu wanda na san zan sakaki cikin wahala,shiru mama tayi batai magana ba , Allah ki yarda dani wallahi babu abinda ya taba shiga taakaninmu "ni ba wai ina yaki da aikata sunanh ma'aiki bane ina jin tsoron fitinar tsohuwar nan ne duk da Allah shine abun tsoro "karki damu mama Allah babu komai banida komai, naunayen ajiyar zuciya mama ta sauke "bazan hanaku ba tunda ba haram bane ... "kai mama wallahi babu wannan a tsakaninmu muje muyi aiki , idan zakiyi aike kasuwa kisa azo min da mangaro tana tafiya gama ta faɗa kitchen mama ta bita da kallo" ummita yanayinki ya nuna kina dauke da ciki ,idan kici abinci sai kinyi amai ga yawon bacci da za'bar abinci ,duk abinda bakya ci da shi kike ci yanzu ta zan yarda ?"ta yadda ta rantse miki mana ai tasan mahimmanci rantsuwa kuma ma ta yaya baba zayi mata a ciki a gidan nan ? Kitchen din ta biyota .
*****
duk sati suhaimai take zuwa gidan gaishesu wanda rabin yinin tana yinsa ne a bangaren inna ko ta shiga bangaresnsu ummita bata dadewa bisa umarnin hajiya inna kuma duk shigowarta bata haduwa da ummita har ta gama abinda zatayi ta fita , shi kuwa mah'ruf duk abinda take bata burgeshi yanzu gabad'aya hankalinsa baya gareta yana kan ummita da cikin jikinta, ya zubawa sarautar Allah ido ne har sanda cikin jikinta zai bayyana kanshi yaga yaya hajiya inna zatayi zata yarda ummita ta tare a gidansa ko kuwa ?
Sannu a hankali cikin ummita ke fitowa kasancewar lokacin ya shiga wata na biyar ,kowa ya ganta yaga me ciki sak , a wata ranar asabar din karshen wata , suhaima ta kawo ziyara , ta soma da bangaren mama tana shiga ummita na karasa saukowa a take gabansu ya fadi, tayi sororo tana kallonta da mamaki ganinta , tayi saurin murza idanunta tana sake kallonta cike da mamaki saboda ganin abinda ta gani ,ummita ta kawar da idanunta akanta ta soma tafiya zuwa dining area da sauri suhaima ta karaso gareta tasha gabanta "ke meye wannan ajikinki kamar ciki "ummita ta watsa mata katuwar harara " uwar ciki ne ba ciki ba , ta sake kura mata ido "ta yaya ga ciki ina gani ki karyatani "ina ganin kin soma soma shaye shaye ko kuma haukan gado ya soma taɓa tunaniki shiyasa kikaga haka dan Allah Malama ki ban hanya na wuce tayi maganar tana bin gefenta da sauri suhaima ta fice daga dakin ta nufi bangaren inna nan ta shiga labarta mata abinda ta gani "ke suhaima ba dai ciki ba cikin lafiya kar kishi ya rufe miki ido fa? "wallahi inna ciki ne ajikin yarinya kuma na haihuwa "bari naje na ganowa idanuna idan kuwa ciki gareta da gaske zataci bantar uwarta a gidan ta fadi haka tana gyara daurin zaninta ta fita ta bar suhaima da zullumi da faduwar gaba "wayyohlly na shiga uku Allah kasa cikin bana mahruf bane ta furta jikinta na rawa .
kai tsaye part din mama hajiya inna ta shiga ko sallama batayi ba ta soma kwalwa ummita Kira "ke ummita kina ina fito nan munafurkar Allah, ummita data shiga kitchen d'aura Ruwan zafi ta fito tana yatsina fuska "lafiya kike min irin wannan Kiran mafarautan "Kiran uwarki da wadan can dangin uwarta take nake miki tayi maganar tana kura mata ido wani iri razanannen ihu ta kurma
"Dan uwarki cikin waye ajikinki a she da gaske ciki gareki makira uban wa yayi miki ciki ?
Kan kace me parlour'n mama ya sauya da mutane har mama da hajiya umma da hajiya saudat
"ba zaki faɗa cikin uban waye ajikinki ba yar banza, wato abun kunya zaki janyowa mutane a gidan nan ?Inna ta sake kurma ihu wannan karon har injiniya da Abba sun shigo sukayi cirko cirko suna mazurai " wayyohlly Allah na shiga uku duk irin tarbiyar da Ibrahim ya baki ki rasa abinda zaki saka masa dashi sai da wanna ......
"kinsan Allah ko fadi uban da yayi shiri shiri ya dirka miki ciki ko kuma yau kubar min gidan dana ke da uwarki bayan ki amshi takardar sakinki daga hannun jikana, ita kuma wannan shashar uwar taki ta amshi sakinta daga dana daga yau bana son ganinku cikin ahlina ,dan wallahi bazan zauna gida daya daku ba ....
"Kai Ibarahim ka saki mairo ko na tsine maka albarka muddin bata fadi wanda yayi mata ciki nan ba gabad'aya jin haka yasa ummita ta rude ta gigice idanunta suka rufe dan tuni hawaye ya ɓalle a idanunta ta matsa kusa da inna Dan tasan yadda abbanta ke gudun bacin ran inna zai iya yi mata komai ciki kuwa har sakin mahaifiyarta, bata jin nata sakin bakinta da jikinta suna rawa tace "
wallahi inna bani da ciki bani da komai ta ina zanyi ciki ?
"Ta uwarki da ubanki ta fixge hannunta da ummita ta riko " na rantse da girman Allah inna bani da ciki idan kuma tabbas inda shi to bansan wanda yayi minshi ba ta k'arasa gurin hajiya umma "dan Allah ummah ki faɗa wa inna gaskiya wallahi bani da ciki karta sa Abba ya saki mama gara ni tasa ya mah'ruf ya sakeni "dukkaninku za'a saka kuma a yanzu, ina bazai yiwu ba cikin shege a gidan dana .. ......
TWO FRIEND'S (BSBS)
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~TRUE LIFE STORY~
FREE NOVEL
AL'QALUMAN
*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*
~DEDICATED TO~
*MUHAMMAD AUWAL JININ JIKINA INA SONKA FIYYE DA SON DA NAKE WA KAINA, ALLAH YA RAYA MIN KAI YA KARE MIN KAI A DUK INDA KAKE ,GABA'DAYANMU MUNYI KEWARKA JIDDAH MENAL UWA UBA NI , ALLAH YA DAUKA YA HASKAKA RAYUWARKA YAYI MAKA SUTURA*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
PAGE 53
... Gabad'aya mutanen dake tsaye a parloun hankalinsu yayi matukar tashe sannan fuskokinsu cike yake da matsanancin mamaki furucin hajiya inna ga ummita .
" dan me hajiya inna zata dinga irin waɗan nan magangun mai tattare da cin zarafi da tozarci akanta ? " ta ya mace da aurenta zata dinga tuhumarta ? kallon hajiya inna suka ci-gaba yi babu wanda yayi magana a cikinsu gudun jaraba da bala'inta .
A gigice cikin tashin hankali tace "kai injiniya kira min Ummu salama a wayarka kace tazo yanzu yanzu ina son ganinta , injiniya ya kalleta yana son yin magana ta d'aga masa hannu da sauri" dakata bance ka karanto min dogon turanci ba , abinda na saka kawai zakayi min idan kuma bazakayi bane ka sanar dani nasa wani ya kira min salama ...?
Take injiniya ya soma neman number aunty Kira ɗaya ta ɗauka ya isar mata da sakon hajiya inna tare da katse kiran ya tsaya rungume da hannuwansa ya zubawa hajiya inna idanunshi hankalinsa ya rabu kashi biyu .
"Ko cikakken minti talatin ba'a ɗauka ba sai ga aunty ta k'araso gidan hankalinta a tashe tace " me ya faru na ganku haka duk kunyi cirko cirko? babu wanda ya buɗe baki yace uffan sai hajiya inna "ina fa lafiya salama wannan yar iskar yarinyar ce take ɗauke da ciki ,abinda ya bani mamakin shine a ina ta samo cikin ita da ba tarewa ta yi a gidan mijin ba ?
" gata nan ta tsaye ta kafe mutane da idanuwa kamar na agolar nufawa ta gaya miki uban da yayi mata ciki dan wallahil azim baza'a likawa babana cikin shege ba tunda nasan ko giya iyamurai ya kwankwad'a bazai aikata komai da wannan abar ba ..
a lokacin daya abba da hajiya umma har ma da mama suka runtse idanunsu tsabar bakincikin jin kalmarta ta karshe, wani irin numfashi mama ta dinga saukewa mai haɗe da tashin hankali jikinta na daukar rawa ta bude idanunta ta zubawa Ummita tana kallonta qirjinta na dokawa " tabbas ciki ne ajikinta .
Aunty da ranta yafi na kowa ɓaci tace" haba hajiya inna ta ya mace da aurenta zaki ce a ina ta samu cikin ?
" a matsayinki na babba bai kamata kiyi wannan tunanin ba ,sannan ba abun mamaki bane aga ciki ajikin ummita bare har ki dinga dangata jikarki da cikin shege ..
Ummita ta matso kusa da aunty ta riko hannuwanta duka hawaye na zubowa daga idanunta "aunty ki fahimceni wallahi bani da ciki , dan Allah karki yarda da maganar Inna wallahi sharri take son min saboda bata sona ,bancin haka ta ina zan samu ciki ?
"Ta gidan uwarki da ubanki shegiya mai kan maciji , wallahi idan baki fad'i inda kika kwaso wannan abun kunyar ba sai kun bar gidan d'ana yau ba gobe ba irin tsiya irin jaraba kawai irin danasani har kullum bazan daina bakinciki hada iri da uwarki ba ,Kallon inna ummita take hawaye na cigaba da gangaro mata jikinta na mazari tamkar mai jin sanyi .
Jiki aunty a sanyaye ta riko hannu ummita cikin nata saboda rawar da jikinta yake "kin kwantar da hankalinki saboda cikin jikinki zai iya samun matsala , ummita tayi saurin girgiza mata kai wasu sabbin hawayen na gangarowa bisa kuncinta "bazan iya ba ! Bazan iya kwantar da hankalina ba aunty ,ki taimakeni duk abinda zai faru karki bari abbana ya saki mamana gara ni tasa ya mah'ruf ya sakeni.....
"shikena amman kiyi shiru ki natsu ki bar kukan nan haka bari na kira wanda zai raba wannan gardamar domin inna ta tabbatar da gaskiyar lamari .
" Wa zaki kira ?
inji cewar hajiya inna da maganar ta kaiwa kunnuwanta ziyara
"Mah'ruf zan kira dan shi ne wanda zai faɗi uban cikin jikinta , nashi ne ko akasin haka "
"Ke salama fita daga cikin idanuna na rufe, Kema an koya miki munafurci da makirci ko ?
"na kiraki a matsayinki na diyar cikina shine ɗan munafurci zaki d'aurewa karya gindi kice sai ma'hruf yazo ,yaron da kin san halinsa ko cikin banashi bane haka zai kakabawa kanshi , wallahi karki soma kiran shi dan ko an kira shi cewa zai yi nashi ne ni kuma ko sama da kasa zasu haɗe bazan yarda a lika masa mugun iri ba, ki dai tambayeta uban da yayi mata ciki ....
nan take zuciya ta ɗauki ummita ta saki hannu aunty tayo gurin inna dake tsaye tana yatsina fuska "wai hajiya inna me na kashe miki a rayuwar duniya ?
"me nida mahaifiyata muka tsare miki a rayuwa?
" wace irin tsana ce wannan ? "wace irin kiyayya ce haka ? idan ma kina tsanar mahaifiyata dan ta kasance yare nifa me nayi miki tunda daga tsatson d'anki na fito ?
"Baki sona baki son ganina cikin farinciki ,kin fifita sauran jikokin akaina kin fifita bare akaina me nayi miki ? "Ban cancanci ki tsaneni ba saboda ni din jininki ce kece kika haifi mahaifina , kina kin mahaifiyata amman ita tana sonki kullum .... "mahaifiyarta tana miki biyayya, tana gudun 'bacin ranki duk abinda kike mata bata taɓa d'aga ido ta kalleki bare ta furta kalmar ta gaji dake ba , hajiya inna ya kamata a ce kin rangwanta mata wannan kiyayyar da ki ke mata wacce ta ja nima kike min ....
kuka take sosai tana farfad'awa hajiya inna duk magana da tazo bakinta mama ta k'araso gareta cike da sarewa "Ummita kiyi shiru bana son sake jin bakinki idan kika sake fad'awa hajiya inna wata kalma bazan yafe miki duniya da lahira ba, ta kare maganar tana zubar da kwalla mai zafi tana jin wani zafi a qirjinta bazata iya cigaba da ɗaukar wannan nauyin ba dole ta bar zuri'a hajiya inna haka ,koda kuwa hakan zai zamo sanadiyyar rasa rayuwarta ......
Baka jin sautin komai a parloun'n sai na sheshekar kukan ummita a hankali mama ta isa gaban hajiya inna zuciyarta na zafi "kiyi hakuri inna dan Allah bazata sake ba...
"Dakata........
hajiya Inna ta katseta tana kallonta shekeke "ni za'a kawowa gulma da munafurci da tsigudidi da annamimanci wanda aka gada sai da yarinya ta gama ɗebe min albarka sannan zaki ce baki yafe ba ,Allah yasa ki tsine mata karewa rashin yafiya wannan ba matsalata bace matsalarki ce da ita kadai gareki , ciki kuma sai dai kusan yadda zakiyi dashi dan wallahi babana bazai amshi cikin da banashi ba .
"hajiya Abba ya kira sunanta ban ce ka saka baki ba idan kayi kuskuren saka min baki zan tsine maka wallahi "Idan kuma kafi bukatar tsinuwar tawa ne bismillah , take Abba yaja bakinsa yayi shiru gumi na cigaba da tsatsafo masa ta ko'ina ajikinshi bai taɓa bakinciki da nadamar kasancewar hajiya inna mahaifiyarsa ba sai yau , zuciyarsa zafi take masa a hankali gefen kanshi ya soma sarawa ya kai hannusa ya dafe goshinsa yana jin wani irin zafi mara misaltuwa "ya Allah wannan wace irin uwace gareni ...? "Allah kaga halin da nake ciki Allah ka kawo min ɗauki da gaugawa..
"Haba Inna abinda kikeyi sam bai dace ba duk fa abinda kayi na alkhairi ko sharri kanka kayiwa ba wani ba , sakayyar duniya kuwa tun a nan duniya yanzu ake ramawa mutun "to zageni agabansu suji dadin zagina daman ai kune kuka fara bada kofar zagina a gidan nan , ku dana haifa kun zageni waye ma ba zai zageni ba ?"ku cigaba da zagina har muhammadu Abdullahi mahdi ya bayyana , Allah yasa kuma kun haifa duk abinda kuka min shi za'a yi muku, "inna lillahi wa Inna lillahi rajiun suke furtawa gabad'aya jikinsu na ɗaukar rawa tare da zubewa a gabanta injiniya yayi ƙoƙarin riko hannunta ta fixge a fusace haka ma aunty "karki soma kai hannunki jikina ke kaɗai Allah ya bani mace acikinsu amman baki da amfani agurina , har ki tsaya gaban waɗan nan kina faɗa ina faɗa ai ke kika bawa wannan jairar damar zagina ku cigaba da zagina karku daina ta karasa mgnr tana zubda kwalla katseta aunty tayi "kiyiwa girman Allah kiyi hakuri Inna ki fahimceni ,wallahi wannan cikin na jikin ummita na mah'ruf ne shi ....
"Dakata Allah ya isa ban yafe miki ba tunda kika ce cikin shi ne ,kuma kika sake cewa cikin jikinta na shi ne na rantse da girman Allah zan tsine miki salama ....
Babu abinda Abba da injiniya suke furtawa sai kalmar Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun , idanunsu ya rikide yayi jazir , ita kuwa hajiya umma bakinciki da takaici ya hanata magana ta juya ta kalli inda suhaima ke tsaye kamar wata photo copy tana kallon kowa tana nad'e magana , a matukar fusace tace "tsayuwar me kikewa mutane, ana maganar family issues meye naki na tsayawa ?
"Maza kama gabanki ta karasa maganar da tsawa,tsawar da hajiya umma tayi ne ya dawo daita haiyacinta take jikinta ya kama rawa simi simi taja jikinta a sanyaye ta fice tana addu'ar Allah yasa cikin bana Mah'ruf bane dan idan cikin ya kasance nashi wallahi sunan shi zubabbe , tana fita umma ta bar parlour'n itama zuwa part dinta ..
Ko second biyu ba'a yi da fitar Hajiya umma ba sai ga ma’aruf ya shigo, a natse yake kallon kowa daya bayan daya sanye yake da blue jeans blueblack da t-shirt ja mai kwala, yayinda kwalar ke zagaye da kalar blueblack da bakin hannun rigar kamar yadda wandon jikinsa yake , kallo ɗaya yayi musu ya fahimci kalar tashin hankali da suke ciki .
Gaba-daya ya maida hankalinsa akan mama saboda fahimtar da yayi kuka take, da idanunshi ya soma tambayarta abinda ke faruwa bata iya ce masa komai ba har sanda ya maida idanunshi kan ummita wacce ta dawo tamkar wata zautacciya tana sambatu .
aunty ta kira sunanshi a tsanake "babana..........
ma’aruf ya waigo a hankali zuwa inda take durkushe gaban hajiya inna ka samu guri ka zauna, ya kasa bin umarnin aunty dan babu abinda yake son ji sai abinda ya sa mamansa kuka da fatlion dinsa ,kusan minti goma ma’aruf yaki zama yana tsaye qirjinsa na dukan tara tara .
A hankali aunty ta soma magana kamar haka "a halin yanzu hajiya inna taga ciki a jikin matarka shine take son sanin cikin waye a jikinta ,naka ne ko akasin haka ...?
Parlour'n ya sake d'aukar shiru baka jin motsin komai sai na sheshekar kukan ummita kowa so yake yaji abinda zai ce , ya tsurawa ummita idanunshi cike da tausayawa itama zuba masa rauraunun idanunta tayi wanda suka karaya cike da tashin hankali "kayi shiru kana kallon mutane cikin waye ajikin matarka ?inji cewar injiniya yayi maganar a fusace ......
"Karku matsa masa ku gigita shi ya fad'i abinda ba daidai ba ,kai babana kalleni nan ka faɗa min cikin jikin ummita na waye ?ya sake yin shiru yana kai hannunsa bayan keyarsa ya tsosa yana mai tsananin jin kunyar mama dake gabansa wacce ta langwa'bar da kanta idanunta cike da kwalla .....
"Karka cuci kanka ka faɗa min gaskiya duk da nasan cikin nan ba naka bane amman zan so naji daga bakinka ..
Idanunsa ya ɗauke akan mama ya tsaida akan hajiya Inna "nawa ne Inna ,cikina ne a jikinta na tsawon wata biyar da sati biyu wata irin zabura hajiya inna tayi daga zaunen da take ta mike tsaye tana dubansa jikinta na rawa.
"cikinka ?
Lumshe mata idanunsa yayi tare da d'aga mata kai alamun eh .
"Shikenan hajiya inna kin ji gaskiyar lamari daga bakinsa dan ha.......
tasss tasss kake ji akan kuncin injiniya daya soma magana , yayi saurin zaro idanunshi waje tare da dafe kuncinsa "kai na tambaya dan ubanka ? ko da kai nake magana ? Tayi maganar a fusace sannan ta dawo gaban ma'hruf ta tsaya kyam tana huci "kai kalli cikin kwayar idona ka sake maimaita abinda ka faɗa yanzu ,dakewa yayi yana kallonta cike da dakiyar zuciya yace " Allah Inna cikina ne ajikinta "Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun "a gidan ubanwa kayi mata ciki d'aukarta kake zuwa hotel ko me ?
Ya watsa mata harara "ta ya zaki min irin wannan tambayar nida matata ta sunnah, koma a ina nayi mata tunda nace nawa ne ba shikenan ba nifa banason matsala da damuwa, to meye ma abun tara mutane kan ɗan wannan abu saboda Allah ? Kamata yayi ki kirani ni dake na fahimtar dake ba wai .....yayi shiru ya kasa karasa maganar saboda idanun mama dake yawo ajikinsa dan
tunda ya soma magana idanunta ke kansa sai data yayi shiru sannan ta sunkuyar da kanta tsabar kunya da farinciki daya lulku'beta, ta dinga jin kamar kasa ta tsage ta shige ciki sai dai me yasa ummita zata karyata maganar a lokacin data tambayarta ?" me yasa zata karyata hajiya inna alhalin tasan gaskiya, dan taya za tayi ciki batare da ta aikata abinda zai sa cikin kasancewa ba ? "Har da rantsuwa akan bata da ciki kai dan yau sai dai ka barshi kawai ,ta fadi hk a cikin zuciyarta .
ummita kuwa wani irin shock ne ya kama ilahirin jikinta ta tsaya tamkar wata wawiya tana kollon bakinsa da yake musu bayani cike da mamaki , take hajiya inna ta rusa ihu da kuka a lokacin daya .... ..
Abba da injiniya kuwa hamdala suka dinga yi a cikin zuciyarsu tare da bawa hajiya inna hakuri, katsesu tayi cike da maseefa "ku daina bani hakuri munafukan banza kawai tayi maganar kamar wata zautacciya ..
ummita na gama jin bayanin mahruf wanda ya tabbatar musu da cikin da hajiya inna take magana akanshi gaskiya ne ta sake shiga rud'ani da tashin hankali "yaushe hakan ta faru bata sani ba ? a sanita dole sai mace da namiji sunyi auratayya sannan za'a iya samun ciki ta ya ita nata cikin ya samu babu auratayya ?
"Kai impossible wannan cikin ba gaskiya bane ,dan haka bai taba faruwa a tsakaninsu da mah'ruf ba bare ya kai ga ciki ,ya dai faɗa ne kawai dan ya kareta daga maseefar hajiya inna amman ina ita ina wani ciki ana zaman kalau "
aunty tace " inna ki daina kuka yarinyar nan fa matarsa ce halak malak da jama'a suka sheida haka ,ciki kuma na faɗa miki gaskiya saboda ni na dade da tabbacin cikinshi ne saboda tun lokacin da cikin ya samu ma’aruf ya zo har gida ya faɗa min sai dai yace kar na sanar da kowa......
"Amman kuwa kin cuceni salama kinsan da wannan abu shine kika boye min saboda baki kaunata "ba haka bane inna sirrinsu ne wannan "ki min shiru munafukar Allah ,shi sirrin yaci kutumar ubanshi Allah ya isa ban yafe ba "kai kuma munafuki kana tafiya suki suki kamar mutumin kirki ashe sharri ne fal acikinka ya d'age mata girasa ɗaya yana cizan lip's d'insa na kasa alamun meye illar abinda yayi ...
"Ai dole kayita zariya a bangarensu tunda an yi maka d'and'ani haukaci kana zariya kamar zatiyar wando wallahi zaka san ni kake dagewa gira, dan wallahi sai na baka mamaki akan wannan ganganci da kayiwa rayuwata ,sau nawa ina maka kashedi akan haka ?" kace kiyi maganarki a banza na d'auketa .....
Juyawa Ummita tayi bayan ta gama jin bayani hajiya inna tana kuka ta nufi d'akinta nan take ma’aruf ya biyo bayanta yana kiran sunanta "fatlion ! fatlion !! taki tsayawa ta shige d'akinta .
ko da ma’aruf ya shigo dakin ya sameta tsaye ta bawa kofar d'akin baya tare da rungume hannunwanta duka a qirjinta tana kuka...
ya k'araso kusa da ita jikinsa a sanyaye " fat lion ya Kira sunanta muryarsa a kasalance tayi masa banza ya sake matsota sosai kamar zai shige jikinta dan har tana jin hucin numfashnsa a gefen wuyanta.
" nasan za ki ji babu dadi game da abinda ya faru da kuma abinda hajiya inna ta yi miki , tabbas kina dauke da ciki kuma wallahi cikina ne, nasan ban kyauta miki ba na aikata kuskure mafi muni agareki wanda sanadiyyar haka inna tayi maiki tonon silili da aibantawa , wallahi ban yi miki haka dan na kuntata miki ba ko nayi silar da za'a tozartaki ba , nayi ne saboda wani dalili nawa ,naki nasar miki ne saboda ban san yadda zaki ɗauki abun ba amma kiyi ha.......
Tun ka fin ya k'arasa abinda yake son fad'i ta juyu da sauri ta rufe masa bakinsa da hannunta ɗaya tana kallon cikin kwayar idanunshi dake cike da damuwa da ruwan kwalla ya cire hannunta "am really sorry ya faɗa yana kallon cikin idanunta dake zubar da ruwan hawaye ....
"ka daina bani hakuri sannan ka daina fadar ina dauke da ciki ,nasan ka fada ne dan ka kareni agurin hajiya inna ba wai da gaske cikin gareni ba ...
Ya matso jikinta sosai har suna iya jiyo numfashin junansu "it's true fatlion kina d'auke da cikin mah'ruf shuaib , nayi auratayya dake batare da saninki ba ,idan baki manta ba akwai ranar dana na iskeki a dakin kina daga kafa da kyar har na kaiki gurin wata nurse ta dubaki lokacin mama ta tafi cotonue , lokacin na kaiki gurin likita ta duba min ke saboda abinda na aikata miki , sannan ina lokacin da kika yita amai har doctor Husain ya zo ya dubaki ,shi kuma a ranar yake faɗa min ciki gareki shiyasa naki yarda yayi magana a gabanki ,na dade ina son fada miki amman zuciyata ta dinga kwabata saboda sanin halinki ..
Tayi sororo tana kallonsa kafin daga bisani ta soma girgiza masa kai "ko ka rasa tunaninka ne ya ma'hruf ta yaya kake cewa ina da ciki ?
Ya rungumeta tsam ajikinshi yana shafa bayanta bakinsa na kan sumar kanta daya gama wargajewa a bayanta "ta yadda nayi miki bayani .
a hankali take zubar da hawaye da sheshekar kuka "ki kwantar da hankalinki ,ki daina kukan nan haka, ba fa mugun abu mukayi ba ni burina yanzu bai wuce kiyi hakuri ki yafe min saboda nayi tarraya dake batare da saninki ba ta soma ƙoƙarin zare jikinta daga nashi "karka sake ƙara min damuwa akan wanda nake ciki ni bani da komai tayi maganar tana ja da baya tana ƙoƙarin juyawa ya riko damtsen hannunta ya manneta da bangon d'akin zuciyarsa na dokawa da sauri , ya kai hannusa daya jikin bango ya tokare ya matsota sosai yana ƙoƙarin shigewa jikinta ya haɗe goshinta da nashi hancinsa na gugan nata zuciyoyinsu ya dinga harbawa a tare ,a hankali suka sauke numfashi , ma’aruf ya lumshe idanunsa sannan yasa hannun shi daya ya talla'bo fuskarta yasa kwayar idanunshi cikin nata kana ya kira sunanta "fat lion ina me neman afuwarki please sannan ki yarda da cikina dake jikinki ummita ta marairaice fuskar tana dubansa "kice kin yafe min ko hankalina zai kwanta , jikinsa a sanyaye ya haɗe fuskarsu waje ɗaya "talk to me fatlion zuciyata na son jin wani abu daga bakinki ya k'arasa maganar yana goga hancinsa akan nata yana busa mata iskar bakinsa da numfashinsa kafin daga baya ya hade bakin su guri daya ya shiga tsotsa lip's dinta batare da ta shiryawa hakan ba.
kokarin hanashi take amman ta kasa aiwatar da komai dan tuni har ya zarce da romance dinta sun dade a haka rungume da juna gam gam yana tsotsan bakinta ...
Buga kofar d'akin da a kayi ne yasa mah'ruf janye jikinsa daga nata ya nufo bakin kofar ya bude ganin mama yayi tsaye rike da akwatin kayanta , mika masa tayi" muje ka rakani inda zan shiga mota zuwa kasar haihuwata ..
"What mama Ummita ta furta da karfin gaske tana karasa fitowa daga dakin da sauri "karki min haka mama yaya kike son rayuwarta ta kasance kina gidan nan ma yaya na kare bare baki cikinsa "akwai Allah sannan ga mijinki nan zai kula dake fiyye dani.
"wani miji mama ni bani da wani miji, wallahi ba zaki bar gidan nan ki barni ba kafarki kafata duk inda zaki ummita da hankalinta yayi kololuwar tashi ta fadi haka fuskarta tayi ja saboda kuka , jikin mama babu kwari ta soma jan akwatinta tana tafiya "haba mamana karki min haka idan kika barni yaya kike son nayi ta shiga binta tana rike da akwatin "ba tun yanzu ake bukatar na bar gidan nan ba , lokaci bai yi ba sai yanzu ,ni kaina na gaji da zama a cikin gidan nan tayi maganar a daidai lokacin da suka k'araso tsakiyar parlour'n inda mutane suke tsaye, jin abinda mama ta faɗa yayi mugun taga hankalin Abba take jikinsa ya kama karkarwa gumi na sake tsatsafo masa injiniya ne yayi karfin halin fita ya kira hajiya umma da baba sarki .
Hajiya umma ta shigo hankalinta a tashe, mama ta isa gaban Abba ta durkusa har kasa kanta a sunkuye "to Ibrahim lokaci yayi da zan bar maka gidanka da ahlinka zan tafi sai naji daga gareka Allah ya sadamu da alkhairi, idan nayi maka laifi a zamantakewar da muka gudanar ka yafemin ni dai baka min komai ba tana gama fad'ar haka ta yunkura ta mike ta isa gaban hajiya inna "inna kiyi hakuri dan girman Allah yau zan bar gidan Ibarahim dinki nasan kina kinsa da kuntata masa ne saboda ya aureni, a yau ki cigaba da son d'anki kamar yadda kike ada saboda zan barshi bari na har abada ..
Abba ya ja dogon ajiyar zuciya da karfi yana mai runtse idanunsa jikinsa na wani irin rawa, bai taba tunanin mama zata iya furta abinda ta faɗa a yanzu ba ,bai san ciwo da rad'ad'in barinsa zai daga masa hankali irin haka ba ,parlour'n ya kara rikicewa da kuka da rud'ani jin furucin mama mah'ruf kuka ummita kuka mama da sauran mutane kuka abun ya citura wata razananniyar
kara ummita ta saki mai karfi tace "nashiga uku Allah karka jarabi iyayena da wannan maseefar Allah idan hukunci ne ka hukatani amman ka bar iyayena su rayu kamar yadda suka d'auko rayuwarsu, "hajiya inna yau burinki ya cika amman da ikon Allah sai kinga ......
mama tayi saurin toshe mata baki tana girgiza mata kai "kul naji kince mata wani abu saɓanin alkhairi "haba mama me yasa zaki hanani magana "inna mahaifiyar mahaifinki ce , duk nan babu wanda ya isa ya faɗawa inna maganar daya gadama ban taka masa burki ba bare ke diyar cikina ta k'arasa maganar tana ƙoƙarin barin parlour'n Mah'ruf ya amshi akwatinta tare da rike hannunta "muje mama ai kinyi hakuri na tsawon shekaru tunda kin gaji babu mai takura miki ana aure dan ibada ne ,Allah daya halicci aure shi hassalata saki dan haka....
yayi kasa da kanshi yaki duban inda abba yake sannan ya cigaba da magana "Abba ka sawwakewa mama aurenka dake kanta kawai ta huta da wannan bala'in na hajiya inna ya karasa maganar yana sharce kwallar idanunsa tare da kallon hajiya inna yaji mai za tace , zata saduda ko kuwa tafi bukatar tafiyar mama ...
Wani irin ihu ummita ta zunduma "wayyo Allah na shiga uku karku bari mamana ta rabu da babana ,wallahi ina son su tare banason na rabu dasu , ta isa gaban mama tana hawaye wallahi idan kika tafi zan kashe kaina duk ku huta ..... .
a matukar tsorace mama tace "karki aikata sabo mana , rabuwa kaddara ce babu abinda zai sameki you will be fine ummita adduata tana tare dake dan Allah ki kwantar min da hankalinki kinji mamana kinga bake kad'ai bace ki zauna gidan ubanki tare da mijinki .
"mijin banza mijin wofi me zanyi dashi wallahi babu abinda zanyi dashi nafi bukatar ke da mahaifina tare ,yadda ta dinga wasu abubuwa kamar zararriya ya d'aga hankalin mama matuka .
Mama na kallon Ummita ta k'arasa kusa da ma'hruf ta fixge akwatin kayanta dake rike a hannunsa "dan me zaka goyin bayan tafiyarta? " kana bakinciki ganinsu tare ne ?
Girgiza mata kai yayi yana cewa "wallahl azim nafi son ganinsu tare "
"karya ne kai ga mahaifiyarka tare da Abba shine ni kake son raba tawa mahaifiyar da mahaifina ,wannan itace kalar taka soyayyar ga mama ?
"daman duk soyayyar da kake nuna mata shekara da shekaru karya ce ?
"Are you out of your sence ki natsu kiyiwa mutane shiru anan sannan ki shiga hankalinki kasancewarki diyar mama kawai kike amman soyayya dake tsakanimu ta wuce misali ,mama tayi niyyar tafiya da kanta I can't stop her wallahi bazan hanata tafiya ba dan nafi son rayuwarta akan komai , tsawon shekaru bata taɓa tunanin tafiya ta barmu ba ,ta ɗauki tsawon shekaru tana addu'a dan yau ta furta zata barmu sai nace a'a "bazan hanata ba sai dai na goya mata baya dan na samu kwanciyar hankalinta .
"to ni ban yarda ba ban kuma amince da wannan tsarin ba banason rabuwarsu nafi son na gansu tare "na rantse da wanda ya busa min numfashi matukar mama ta bar gidan nan sai dai ku farka kuga gawata tana gama fadar haka ta kwasa da gudu tayi hanyar step tana wani irin kuka da sauri ya saki hannu mama ya biyota aguje itama mama bata san sanda ta biyo bayansu tare da sauran jama'a ba.
Ummita na shiga dakin ta shiga bubbude dorowar bedside dinta ta dauko magani ciwonta , gabadaya ta zazzaga a tafin hannunta tana ƙoƙarin zubawa a bakinta ya banko kofar dakin da karfi ya shigo bai tsaya wata wata ba ya buge hannunta yana fuskantarta "kina hauka ne ko kin fara shaye shaye ne ?
" zan miki rashin mutuncin da baki taɓa especting daga gareni ba .. "dakata malam babu ruwanka da rayuwata waye ma kai meye hadinka dani ,mama ta k'araso gurin da suke ta d'aga hannu sama zata sauke mata mari , yayi saurin rike mata hannu "dan Allah mama karki mareta ki barta taji da halin da take ciki ,mama ta fashe da kuka tare da zama a gefen katifa, hajiya umma da injiniya da abba har ma da aunty suka shiga bata hakuri da bata baki .
"ku daina bata bakinku bafa zan zauna ana wulakantani ba meye aibuna ? "Meye laifina
"Me mahaifiyarku take son nayi mata?" iya biyyaya ina mata ko ita ta kawoni duniya iyakacin abinda zan iya mata kenan ,gara na kama gabana wallahi bazan zauna ba ......
jin furucin mama dake shiga kunnuwanta yasa ta soma yin kasa mah'ruf yayi saurin tarota jikinshi yana taɓa mararta jin numfashinta ya dauke yasa gabadaya a gigice ya soma kiran sunan mama "mama ta suma ....
gabadaya sukayo kanta, suna kiran sunanta "ummita ummita shi kuwa mah'ruf sai fatlion yake kira yana rungumeta daita tsam a faffad'an qirjinshi "dan Allah mama kiyi hakuri kice kin fasa tafiya wallahi idan wani abu ya sameta nima zaki rasani ,kiyi hakuri mama karki rasa yayanki alokacin ɗaya ...
Hannun ummita mama ta riko cikin nata tana kuka "ummita karki min haka ki tausaya min ganin yadda duk suka rud'e babu wanda yayi tunanin a yayfafa mata ruwa yasa aunty fad'awa bathroom ta dibo ruwa da sauri mah'ruf ya karbi roban ruwa, ya shiga shafa mata a fuska ,amman shiru bata motsa ba ,a matukar haukace mama ke girgiza ummita tana kuka tana kiran sunanta "ki tashi dan girman Allah wallahi na fasa tafiyar karki mutu ki barni idan kika mutu bazan taɓa yafewa kaina ba, saboda nice sanadi shima Abba a zabure yake girgizata wani ruwan ya sake tsiyaya mata amman shiru taki motsowa .
hankalin kowa yayi bala'in tashi fiyye da tunanin mai karatu sunanta kawai suke kira "shikenan ta mutu ta mutu "bata mutu ba mama mah'ruf ya faɗa a gigice yana sake janyota jikinshi ya zauna akan tayis ya rungumeta yana girgizata "fatlion karki mutu ki barni ki rayu saboda ni dan Allah . gabad'aya ya rud'e ya gigice ya d'ago fuskarta Yana busa mata numfashinsa a cikin bakinta da hancinta tare da zira yatsun hannuwansa duka cikin kunnuwanta a hankali ya haɗe bakinsu guri daya gabadaya ilahirin jikinsa rawa yake gumi na tsatsafo masa ..
Tsura masa ido sukayi suna dubansa kafin daga baya suka soma barin d'akin daya bayan daya saboda ganin abinda yake mata , waje sukayi gabadayansu suka tsaya cirko cirko suna addu'ar kowa hankalinsa a tashe yake ban da hajiya inna , wacce bata cewa kowa komai ba dan tasan ko tayi magana babu mai kulata ta nufi dakin inda ta iske Mah'ruf zaune rashe rashe rungume da ummita a jikinsa yana tsotsan bakinta da iyakacin numfashinsa mutuwar tsaye tayi tana kallonsu cike da mamaki idan ya tsotse bakinta sai zare ya sake maidawa haka ya dinga yi daga karshe ya zarce da romacing dinta yana tsotsan bakinta yana zuba mata sambatu, babu shiri ta juya da sauri ta bar dakin sai lokacin ta fahimci abinda ya fidda mutane daga dakin, tana fita ya sake damkar bakinta yana hura masa iska ta hancinta da karfi ..
Wani irin atishawa ta saki da karfi haɗe da sakin numfashi tare da kiran sunan mama "karki barni mamana karki tafi ki barni ina bukatarki ya mike tsaye rungume daita ajikinshi ya kwantar daita a saman katifa ya riko laulausan tafin hannunta ya rankwafo jikinta yana gyara mata kwanciya sannan ya zauna gefenta yana rike da hannu daya ,dayan hannunsa ya kai gefen fuskarta yana shafawa a hankali yana sauke numfashi, yafi karfi minti talatin a gabanta yana kallonta ya kai hannunta dake rike cikin nashi yayi kissing yana d'aura dayan hannunsa ya haɗe guri daya "ta matso ruwan hawaye "ina mamana ta wuce ko ?
Ya girgiza mata kai "ta fasa tafiya ki kwantar da hankalinki ki sanyawa zuciyarki natsuwa kinsan mama bazata iya barinmu ba.
"zata iya ya ma'hruf naga hakan a cikin kwayar idanunta ni dai ka dakatar daita duk lalacewar gidan nan nafi son ganita cikinsa, idan bata ciki rayuwata zata tagyyara "babu inda zata muna tare ya fadi haka yana kai hannunsa kan cikinta jin yana motsi har lokacin ya sauke naunayen ajiyar zuciya kana ya kai bakinsa cikin kunneta "am so happy cikina yana nan lafiya.
cikin kuka tace "ni ina ruwana da wani ciki ta zabura zata mike yayi saurin matseta gam a faffad'an qirjinshi "dole kuwa kiyi ruwa dashi wannan cikin rayuwata kenan ,akan cikin nan babu abinda bazan iya yi ba, babu wanda zan iya d'agawa kafa "To ni wallah ka rabani da cikin nan idan ma gaske ne dan banason shi ,me zanyi da cikin wanda bai sona bai kaunata . "okya kiyi hakuri sannan ki taimakeni ki bari ki haifa min cikina sai mu rabu tunda kinfi bukatar haka ...?
Tayi shiru zuciyarta na wani irin zugi "ai nasan zaki fi buƙatar rabuwar mu ko ba haka ba ? "ban sani ba matukar na tabbatar da cikin babu abinda zai hanani zubar dashi ,"karki soma wannan gangancin ,ayi ɗaya kacal na sameshi kinsa walahar da ake sha kafin a samar d'a ... ?
Taja tsaki tana kawar da fuskarta gefe "dan girman Allah ka rabu dani ka rabani da wani zance ciki "Bazan iya rabuwa dake ba fatlion saboda aurenmu auren zobe ne, bazan iya barinki ba duk runtsi duk wuya muna tare dan haka ki daina kawowa zuciyarki rabuwa a tsakaninmu ,
da kyar ta samu ta raba jikinta da nashi ta soma ƙoƙarin saukowa "ki kwanta ki huta babu inda mama zata,
ta girgiza masa kai "ina son ganin mamana bai ce mata komai ba ya riko hannunta suka fito yana rike da hannuta ..
Suna gama saukowa ummah ta nufo gurinsu" sannu ummita ta rungumeta ajikinta tare da manna mata kisss a goshi tana shafa gadon bayanta "kin kwantar da hankalinki mamanki ta fasa tafiya ta barki ,kuna tare muddin rai kinji diyata.
"inji uban wa ai tafiyar uwarta dan ada huta roro, dole ta wuce kuma tare da diyarta idan mutuwa zakuyi idan sun tafi sai ku mutu mu gani amma dole sai ta bar gidan nan kuma a yau daman nafi son barinta gidan sai gashi kuma ta bukata huta roro ta tafi na huta da jaraba ..
Abba ya motsa bakinsa zai yi magana hajiya inna tayi saurin dakatar dashi "karka sake naji bakinka ka rubuta mata takardar sakinta yanzu yanzu da zafi zafinsa ka bata dan ....
" Ba zai rubuta ba mah'ruf ya katse mata hanzarin ta hanyar faɗar hk " ko kin raba auren nan bazaki raba zukatan mutanen gidan nan da kaunar mama ba ..
" Da yarda Allah sai kin mutu ki bar wannan auren hajiya inna ,baki isa kisa Abba ya saki mama ba, ko da kika ga dazu na goyi da bayan ya sawwake mata bawai har cikin zuciyata nake son Abba ya saki mama ba ,na fadi haka ne saboda rabata da bala'in da maseefarki sannan na gani idan nace ya saketa zaki hana a she kema abinda ke ranki kenan ,to ko mutuwa zakiyi sai dai ki mutu amman abba da mama mutu ka raba suna nan tare daram .
"oho to bari kaga yadda karfin ikona ya kai yau idan bani da iko akanka ai ina dashi akan ya'yana Ibrahim sagiru ta kira sunan Abba da injiniya a tare suka d'ago suka zuba mata ido suna kallonta jikinsu na rawa "me ye matsayina agurinku ?
"Mahaifiya suka fadi haka jikinsu na sake rawa "to ina umartaku a yanzu
da ku sa ma'hruf ya saki ummita saki uku rasss .......kuma a yanzu idan ba haka ba duk sai na tsine muku albarka duniya tayi muku dumi sannan aljannarku dake tafin kafafuna zan danne bazan taɓa daga muku kafa ba, jin haka yasa hantar cikin mah'ruf kad'awa a hankali jikinsa ya soma rawa tamkar mazari yana kallon inna cike da mamaki.
Abba da injiniya kamar zasuyi kuka "ya mah'ruf kaji abinda Hajiya inna take buƙata ka aiwatar aikaina ka sakeni kamar yadda ta bukata kowa ya huta dan ni kaina bana bukatar zama da kai ,ya watsa mata kallon banza mai haɗe da harara hankalinsa bai tashi ba sai daya ji saukar Muryar abba cikin kunnenshi "ka sawwake mata baba Allah yasa hakan shine mafi alkhairi ...
kallon Abba ya dinga yi shesheke kamar wani mahaukaci tare da kallon sauran mutane dake gurin ,gabadayansu sukayo kanshi suna umartashi bai san sanda ya isa gurin Hajiya inna ya rike hannunta "haba inna karki min haka kiyi hakuri dan girman Allah karki sa Abba cikin wannan lamarin, ni ne fa babanki ma'hruf da kike so fiyye da komai .
"Ina sane da hakan ,sai dai tuni na soke maka wannan matsayin ba dai akan wannan matar ka rufe idanunka kana min tozarci ba ?
"na tuba Inna ki yafe ni , "baka isa ba sai ka rabu daita ya mike ya isa gurin ummita ya riko hannuwanta muje ki bawa inna hakuri ina bukatar rayuwa dake bazan iya rabuwa dake ba ..
"taja ta tsaya tana kallonsa sannan ta soma magana a tsanake "zaka min wata alfarma ?
Ya d'aga mata kansa da sauri yana sanya kwayar idanunshi cikin nata "ka sake ni kamar yadda ta bukata sannan ka fita cikin rayuwata bana bukatarka .....
"Idan kina bukatar na sadaukar miki da rayuwata zanyi fatlion amman bazan iya sakinki ba ya k'arasa maganar yana ƙoƙarin zubda hawayen dake idanunshi , cike da sanyi jiki take kallonsa ta kai hannunta fuskarshi tana shafawa batare da tasan ta aikata hakan ba tana kallon cikin kwayar idanunshi da suka canza kala tsabar tashin hankalin da yake ciki .
" dole ka sawwake min aurenka inna bata son zamana da kai ni kuma bazan iya rayuwar kunci ba ,bazan iya irin rayuwar da mahaifiyata tayi ba "Ki yarda ki amince ki kasance tare dani bazan bari wani abu ya sameki ba sannan bazan iya sakinki ba, ki kasance tare dani fatlion dan wallahi bazan iya barinki ba ,Allah ne kaɗai yasan abinda zai same ni idan kika bar rayuwata haushin furucinsa take ji ,a da taso tayi rayuwa dashi amman a yanzu bata bukatar haka cike da jin haushi ta fixge jikinta ta juya cikin sautsayi kafafunta suka gurd'e tayi kasa zata kifa kan cikinta yayi saurin tarota ya mannata da qirjinsa , wani irin bugawa qirjin inna yayi da wannan abu, ta zaro idanunta tana kallonsu zuciyarta cike da bakinciki a fusace yake kallonta numfashinsa kamar zai bar jikinsa "me yasa kike sakaci da kanki da rayuwarki ? "Me yasa bakya tunanin halin da zan shiga akanki ? ta hura masa hanci hawaye na zubo mata " hannun sa ya kai ya rike kafad'unta dashi yana sake kallon kwayar idanunta da tsare gira " I love you fatlion ! I love you fatlion !!
Yan wattapad Sai hakuri yan what's app zasu rigaku samu saboda matsalar network
TWO FRIEND'S BSBS
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~TRUE LIFE STORY~
FREE NOVEL
AL'QALUMAN
*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*
~DEDICATED TO~
*MUHAMMAD AUWAL*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
PAGE 54
Tsaye ummita tayi tana bin mah'ruf da idanunta waɗan da suka koma jajaye tsabar hawayen dake zubowa daga cikinsu tana jin kalmar daya furta kamar almara tare da yin nazarin furucinsa mai kama da sake kusancinsu tare , wani sanyi ne ya dinga taso mata yana ratsa sansar jikinta ,jinin jikinta ya ninka gudun da yake fiyye da farko, hatta ɗan cikinta sai da yayi tsalle ya cure guri guda , gabad'aya ta kasa motsi dan kalmar i love you fatlion ba iya zuciyarta kaɗai ya tsaya ba har cikin jininta take jin tafiyarsu ..
"yau ita mah'ruf ya furtawa wannan tsadadden kalmar mai dadi da sanyaya zuciya ?"anya kuwa wannan drama ba'a mafarki yake faruwa ba ?
" tasan mahruf fiyye da kowa mutumin daya girma da kiyayyarta shine yanzu tsaye a gabanta yake furta wannan kalmar gareta anya kuwa ba yayi hakan dan hajiya inna taji haushi bane ?
Hannuwansa dake kan kafad'unta ya cire ya zuba cikin aljihun wandonsa haɗe da tsura mata idanunshi yana kallonta , da sauri ta share hawayenta dake sake turereniyar gangarowa haɗe da girgiza masa kanta yayinda soyayyarsa ke sake fixgarta da karfi ,tabbas tasan ita kanta ta kamu da mahaukacin qaunarsa sai dai duk runtsi baza yarda ta amince masa a karon farko ba ,zata adana nata soyayyar ba zata ta fito da nata fili ba ....
Shima zuba mata idanunshi yayi yana jin zallar farinciki da fargaba na ratsashi a lokaci daya qirjinsa ke wani irin mahaukacin dokawa kamar zai fito waje jikinsa a kasanlance ya buɗe bakinsa " babu ta yadda zan iya rayuwa babu ke ya furta yana sake kusanto jikinshi da nata qirjinsa na dokawa da matsanancin karfi ,still shiru tayi taki cewa komai tare da tsura masa idanunta dake cigaba da zubar da hawaye , " there's no way to survive without you fatlion I love you with all my heart banason na rasaki , banason rasaki a rayuwata saboda mahimmancinki abinda ya faru ba laifi bane , sannan babu yadda zanyi da rayuwata da hakan bai kasance ba a wancan ranar ta ya samuwar wannan cikin jikinki zai kasance ?
"Ki fahimceni wallahi ban cutar dake ba , ta dubeshi cike da sarewa zuciyarta na tsalle abu biyu sun haɗe mata a lokaci daya farincikin jin kalmar da tafi bukata agareshi da bala'in hajiya inna , idanunta na zubar da hawayen farinciki da bakinciki ta juya tana kuka , yayi saurin fizgota ta faɗa fad'ad'd'en qirjinshi suna kallon kwayar idanun juna "me yasa zaki wuce ki barni ? "Ina zaki ki barni yayi maganar a fusace take jikinta ya kama rawa tana son barin wajen ne saboda idanun inna dan tasan abinda mah'ruf yake bakaramin kona mata zuciya yake ba , hakan kuma zai sa taji haushin mama fiyye dashi mah'ruf din .
"tambayarki nake ina zaki ki barni ? nasan nayi kuskure , duk yadda nake ƙaryata gaskiyar dake zuciyata yau gashi ta bayyana kanta a idanun shakikaina wand'a duk duniya su nafi jin kunya fiye da komai ,na soki tun ban san sonki nake ba, na shiga tashin hankali iri iri a kanki , zuciyata ta shiga rud'ani da tashin hankali akanki , idanuna sun sha kwana a buɗe saboda tunaninki ,
ban taɓa sanin mahimmancinki ya yiwa zuciyata tasirin da ni kaina bazan iya magance matsalar ba sai lokacin da zaki auri rayhan wanda nasan aurensa daidai yake da rasaki da zanyi gabadayan ,na shiga damuwa da tashin hankali mara misaltuwa akanki , duk abubuwan da suka faru ban yi dan tuntata miki ba , a yanzu da nake jin kalmar rasaki na sake tabbatar da irin qaunar da nake miki ,ina sonki fiyye da komai da kowa dake cikin duniyar nan .....
" kin amince da irin soyayar da nake miki ?
Tayi saurin girgiza kanta alamun a'a "me yasa ?"why fatlion ? ya faɗa a tare ..
Ta cire hannunsa dake kafad'arta "dan Allah fatlion ki fahimceni karki min haka don't do this to me, ki fahimci yadda nake sonki dan Allah karki barni , karki bar magangun hajiya inna su yi tasiri arayuwamu alhalin muna tsananin son juna.....
gaba-daya maganarsa sake Kunno mata emotion din soyayyarsa suke da take ƙoƙarin dannewa a cikin zuciyarta, a hankali take cigaba da rera kukan farinciki da bakinciki "Allah na gode maka da kawo wannan ranar ina cikin koshin lafiya a gaban kowa mahruf ke nacin yana sona ya kamo yatsun hannunta cikin nashi yana muzwa yana kallon cikin idanunta yana girgiza mata kai alamun ta daina kuma ya fixgo numfashi da kyar "ina fatan ki fahimceni ki ajiye maganar hajiya inna agefe is normal thing ...
"A yanzu ne kake son na fahimceka ? "tayi masa tambayar tana tsareshi da raunannun idanunta , shiru yayi qirjinsa na bugawa da matsanancin karfi idanunshi da suke cike da tashin hankali ya sake zuba cikin nata yana kallon kwayar idanunta "ka manta lokacin da ka dinga ikirari kana fad'awa duniya cewar baka sona me zakayi da subai'a ?"Idan kai ka manta ni ban manta ba yana cikin kwakwaluwata sannan yanzu kace you're in love with me ta ya kake son na fahimceka ?
kai kullun tunanin kanka kake da muradin bawa zuciyarka abinda take so , as you wish it happen today ,fellings dinka kawai ka sani you don't care about my feelings batun hajiya inna kuma wannan ya rage gareka dan nima babu ruwana kuma ba matsalar subai'a bane , da ka sakeni , ko ka cigaba da rayuwa dani am not care , am nat scared dan ita kalmar ma da kake magana akanta ban santa ba bare zuciyata ta amince min da ita , tana gama fadar haka ta juya.
"fatlion Ki tsaya kiji ya dawo daita gareshi jikinsa na rawa ya talla'bo fuskarta da hannuwansa duka "dan Allah ki fahimceni "I know I hurt you tare da yi miki abubuwan da basu dace ba amman ba wai dan bana sonki bane hasalima soyayya ce amman daga yanzu komai zai kasance miki yadda kike so ,mah'ruf zai zame miki yadda kike bukata ,ki kalli cikin kwayar idanuna zaki fahimci gaskiyar dake cikinsu "oh my goodness ta furta tana runtse idanunta wasu tsiraran hawaye masu zafi suka zubo mata "ni yanzu me kake son nayi maka bayan ga abinda hajiya inna tace ?" Is to late now plz ko ina sonka son bashi da wani amfani "is not too late fatlion I said that I love you with all my heart ya faɗa yana bin iyayensa da kallo wand'a suka dawo tamkar poster tsaye suna kallon ikon Allah ,hajiya umma kuwa tafi kowa murnar faruwa wannan abu ,taji dadi yadda ya furta yana son matarsa a gaban hajiya inna , kuma duk runtse duk wuya bazata yarda ya saki ummita ba ,sai dai duk abinda za'a faru ya faru amman baza ta yarda ba ..
Kallonshi kawai ummita take bata ko iya kiftawa idanunta a hankali ya hura mata iskan bakinsa da sauri ta lumshe idanunta , wata kalar kunya ce ta rufe a lokaci daya , gabadaya jikinta rawa yake ta juya zata wuce ya riko hannunwanta duka cikin nashi dole tayi kasa da kanta ta kasa kallonsa "kasa d'agowa tayi , cikin wani salon magana yace " ki fahimceni babu wanda ya isa ya raba aurenmu zamu rayu tare ...
" no ya mahruf this no possible "me yasa ba zai yiwu ba ?
ta sake juya ya rikota cikin zafin nama " Ki tsaya ki fahimceni mana plz fatlion don't do this , don't do this to me , ki fahimci iri zafi da rad'ad'in da zuciyata take ciki a yanzu , plz don't do this , hajiya umma ta k'araso garesa cike da tausawa halin da yake ciki ta dafa kafad'arsa "ka barta tukunna a gama da wannan matsalar "no hajiya Ki bari na sake fahimtar daita dole ta fahimceni ,ni wannan itace babbar matsalata ba wancan damuwar ba, dole hajiya umma tayi shiru tana runtse idanunta "uhm ina jinki ? ta tsura masa idanunta " dan girman Allah ka rabu dani , da kace ba zaka taɓa sona ba yanzu kuma kazo kana min nacin magana ɗaya ,a gaskiya ka daina min naci dan bana sonka , kuma bazan taba son mah'ruf ba , idan ma kana tunanin subai'a zata soka ka cire hakan a cikin zuciyarka dan subai'a bazata so mah'ruf ba ,"dan girman Allah ki fahimceni "wai me zai na fahimta idan dai son da ka furta ne gaskiya bazan fahimta ba , "ya mahruf zan so ka tuna wani abu saboda Allah da saboda kai da ni ,ya tsuke bakinsa cikin zafin rai yana kallonta ," ina son rayuwar farinciki wa kaina banason abinda zai dangwamar dani cikin tashin hankali da damuwa , zai fi kyau ka nisanta kanka dani tunda ba'a sonka dani nima kuma bana sonka , bazan iya irin rayuwar auren da mahaifiyata tayi ba " amman ni ina sonki ,kuma mahaifiyata tana son aurena dake meye damuwarki da wata hajiya inna ?
"ni hajiya inna ba damuwata bace tunda ba itace ta kawoni duniya ba ,ina dai kyautata mata ne darajan su abba , ba zata zama matsala a rayuwata dake ba, abinda zai daga min hankali shine rashin sona da kika furta bakya yi a yanzu shine damuwata kuma shine matsala ..
Bangaren suhaima kuwa tunda ta bar gidan hankalinta yaki kwanciya, ta kira gidansu mah'ruf yafi sau goma ,amman magana ɗaya dai ake faɗa mata wacce kwakwaluwarta ta kasa ɗauka a karo na karshe ne aka faɗa mata abinda yafi komai daga mata hankali "suhaima subai'a ta rigada ta kwace miki miji ,ta ɗauke miki hankali miji ,bayan cikin da yayi mata har da nasaran sace zuciyarsa tayi , wannan gobarar tafi karfinki ba zaki iya kasheta ba sai wani ikon Allah ta runtse idanunta tana furta " wayyohlly zan iya kashe kowace irin gobara ce muddin akan mah'ruf "to sai kinji duk abinda ake ciki zan sanar miki sai ki san matakin da zaki ɗauki amman wannan yarinyar tayi nisa acikin zuciyarsa tana gama fadar haka kira ta kashe wayarta suhaima ta mike daga zaunen da take ta soma Zariya tana furzar da iska "cikin mah'ruf ai tunda ban dauki cikinsa babu shegiyar da zata haifa masa ta shige dakinta da sauri kamar zata kifa ...
A parlou'n mama kuwa tunda mah'ruf ya soma dramar soyayyarsa idanun hajiya inna ke kanshi ta kasa ɗaukewa ta tsura musu ido tana kallonsa ta a jin zallar 'bacin rai na ratsa kowa ni sashi na jikinta ,ji tayi duk duniya babu mahalukin daya taɓa 'bata mata rai kamar mah'ruf ya gama wulakanta kanshi daita kanta , data san haka zai dawo akan mace da tun farkon tafiyar bata bari an saka mata sunan mahaifinta da mijinta ba bare ta dauki soyayyar duniya ta 6daura masa, ranta a matukar 'bace tace "yanzu na sake tabbatar da cewar ba'a barka haka ba akwai wani kulli a karkashin kasa da aka kulla ,Kiri kiri yarinya tace ka saketa ba tayin aurenka bata sonka amman dan naci irin na asiri sai wani rawar jiki kake kana furta ta fahimceka, fahimtar uwarka da ubanka zata maka illa ka dankarawa shegiya saki uku rasssss ka huta ,ka zauna da matarka mai kaunarka ,kasan Allah ko mutuwa zaka yi sai ka rabu da kwallon mangoro ka huta ,kai yanzu nan burgewa kayi ka tsaya kana wannan shirmen a gaban mace kai dole da ayar tambaya cikin wannan lamari tabbas biri yayi kama da mutun asirin agumawa yayi tasiri amman kasan Allah wannan asirin bazai tasiri akan ba sai na karya shi yau dan muddin ina raye sai na rabaka da wannan abar sai na karya asirin da aka maka ta karasa maganar tana nuna sa da yatsanta ,a natse ya d'ago da idanunshi ya zuba mata su "wato dai ita hajiya inna tayi nisa bata jin kira mugun halinta dashi zata mutu ,duk yadda ya'yanta dasu kansu ke kokarin daurata akan hanya taki canzawa, bazata taba canzawa ba ,bazata taɓa fahimta ba duk abinda suke faɗa mata banza ne 'bata bakinsu kawai suke ,kai jama'a ko mutuwar rayhan babba aya ce gareta amman saboda daurin kai taki saduda ya k'arasa zance zuci yana jan katuwar tsaki ,itama hajiya inna tsaki taja tana Allah wadai da shi ....
Aunty jikinta na rawa ta matso gurin hajiya inna tana bata hakuri da kokarin shawo kanta" baba babba kazo ka bawa inna hakuri "sau nawa zan bata hakuri yayi maganar a zuciye jikinsa na rawa ?
na rigada na bata iya hakurin da zan iya bata, ku dai ku cigaba da bata hakuri zata hakura amman wallahi duk abinda zatace tace amman bazan iya sakin matata ba tunda ina sonta itama kuma nasan tana sona kawai dai bata son faɗa ne ,a gabanku ni babu ruwana data fada da karta faɗa ba damuwata bace as far as ina sonta ,soyayyar da nake mata ya isa ba sai ta soni ba ....
Ya dawo gurin ummita ya rike hannunwanta duka cikin nashi "Kina jina ki kwantar min da hankalinki zan killace ke da mama bazan taɓa barin ku dangwama cikin wahala da kuncin rayuwa ba ,ina son mama fiyye da tunaninki " taho muje ya riko tafin hannunta Kema mama taso muje , abba idan zaka biyomu kai ma bimillah kai duk ma wanda yaga zai iya biyo yazo muje mu bar mata gidan tayi rayuwarta ita kaɗai , babu mutsu mama ta biyo bayansa itama hajiya umma ta biyo bayansu abba kam kasa tashi yayi duk abinda yake son yi kenan amman rawan da jikinsa yake yasa ya kasa aiwatar da haka .
suna fita ko minti goma basu yi ba sai ga baba sarki ya shigo a daidai lokacin da numfashin abba ya soma ƙoƙarin d'aukewa....
TWO FRIEND'S BSBS
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~TRUE LIFE STORY~
FREE NOVEL
AL'QALUMAN
*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*
~DEDICATED TO~
*AMEENA AUTAR HAJIYA*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
PAGE 55
gaba-daya hankalin sauran mutane dake gurin ya ƙara tashi har hajiya Inna , suka yi kan abba hajiya inna na kiran sunanshi "Ibrahim! Ibrahim !! aunty ta fashe da kuka haɗe cewa "hajiya kinga abinda kika haifar ko , ya Ibrahim na iyakacin kokarinsa gurin miki biyayya ,yana gudun ɓacin ranki idan ya rasa ranshi ke zakiyi hasara saboda bazaki sake samun kamar shi ba, dan Allah ki hakura ki barshi ya k'arasa rayuwarsa da 'yarsa da matarsa ta k'arasa maganar tana sake rushewa da wani kuka .
"Ibrahim ka buɗe idanunka ni ne babu abinda zai faru ,ba zaka
rasa matarka da yarka ba, a gaugauce injiniya ya dibo ruwa ya kawo ya soma shafa masa a fuskarshi zuwa qirjinsa amman shiru bai motsa ba , kallonsa kawai hajiya Inna take bata ko kifta idanunta ga wani kalar tashin hankali daya bayyana akan fuskarta, gabad'aya jikinta rawa yake daga karshe ta soma furta kalmar data ji ta karad'e parloun'n wato " Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun tana cigaba da kallonsa tana jin sabon tashin hankali, ganin tsayuwa na neman gagararta yasa ta zube kasan tayis ta rushe da matsanancin kuka "shikenan na rasa d'ana , Ibrahim dina ya mutu ya barni jikinta ba ƙaramin mutuwa yayi ba, ta sake fashewa da wani gigitaccen kuka "shikenan na cuci kaina na kashe d'ana da kaina da gaske mutuwa zaka yi ka barni ? Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun Ibrahim karka mutu ka barni ,
haka ta dinga furta kalmar inna lillahi wa inna ilaihi rajiun tana maimatawa a zahiri da badini tana jin jikinta kamar ba nata ba , kuka take sosai tana jan gindi domin son Isa inda yake .
Cike da tsananin tashin hankali injiniya ya kira layin doctor husai yana ɗauka ya sheida masa abinda ya faru ko cikakken minti goma doctor husain bai ɗauka ba ya k'araso . gabadayan suna tsaye akan abba sun kasa motsawa jikinsu na rawa hatta hajiya saudat ta shiga tashin hankali ganin halin da abba yake ciki ,likita ya ɗauki minti goma yana duba abba sannan ya d'ago ya tabbatar musu da "damuwa ce tayi masa yawa, zuciyarsa na daf da tsayawa a ko wani hali matukar bata samu hutun da take buƙata ba , amman a yanzu inshaallahu da zarar anyi masa allura ya samu hutu na wani lokaci zai dawo daidai jakar aikinsa ya d'auko ya soma yi masa allura , gabad'aya suka tsura masa ido , fuskarsa sharr sai dai da gani yana cikin damuwa da tashin hankali , hannunsa injiniya ya riko cikin nashi yana mai tsananin tausayawa d'an'uwansa , gabad'aya kana kallonsa zaka san damuwa tai masa mummunar kamu shi kanshi wani irin zazzaɓi ne ya rufeshi.
kusan minti biyar injiniya na rike da hannun abba yana zubar da hawaye ,hawayensa dake diga a saman hannun abba ne ya farkar dashi ya bude idanunshi kaɗan yana sauke numfashi, take injiniya ya furta kalmar alhamdullahi "sannu yaya bai iya furta komai ba yayi shiru yana kallon injiniya idanunshi cike da kwalla numfashinsa na sama da kasa ..
Alhamdullahi da hajiya inna taji suna furtawa a hankali, ba tasan sanda tayi wata irin zabura ta k'araso inda suke ba "yana raye bai mutu ba inji cewar baba sarki ,"alhamdullahi Allah mun gode maka ta furta tana share hawaye idanunta jikinta na rawa .
Da kyar aka samun numfashin Abba ya daidaitu , a hankali yake bin mutanen dake gurin da kallo, shiru parloun'n yayi baka jin motsin komai sai na saukar numfashin mutanen dake zaune a cikinsa .
"a soma kira min ma'hruf tukunna tunda an samu Ibrahim din ya farfaɗo sautin muryar baba sarki ta ratsa kunnuwansu sannan ya maida hankalinsa gurin hajiya inna wacce tayi tsuru tsuru cikinta na kad'awa a kan yanayin Abba bata son rasa d'anta duk duniya babu abinda take so da kauna kamar shi , tafi son shi fiyye da sauran ya'yanta bujerewa umarninta
yasa take nuna ko'in kula akansa ..
"Kinyi shiru hajiya kamar bakece silar faruwan komai ba ? injiniya ya buɗe baki ya soma magana "baba ka taimaka ka saka baki mairo ta dawo gidan nan banason ta bar rayuwar yaya ,barinta rayuwarsa ba karamin hasara bane ..
"Ai sagiru al'amarin mahaifiyar taku ne abun tsoro , shekara da shekaru har yanzu ana kan abu daya , abu yaki ci yaki cinyewa me take son ayi mata ?
"Wani irin hakuri ne ban bata ba Allah take son ya sauko daga sama ya bata hakuri ko me ?" kin shiga rayuwar d'akin kuma kina son shiga rayuwar jikokinki dan rashin imani irin naki ,ya k'arasa maganar yana takaicin halinta .. adaidai lokacin da injiniya ya samu layin ma'hruf .
"Ma'hruf na tsaka da tuki yaji kira a karo na uku gefe ɗaya kuma ga kukan da Ummita keyi yana damun kwakwaluwarsa ,a hankali ya soma rage gudun da yake tare da gangarawa gefen titi yayi parking ya bala'in had'e ranshi yana dubanta.
kwakwaluwarsa ce ta shiga tunani abinda ya kamata yayi mata sai dai yanayin daya tsinci kanshi ciki adalilin kallonta da yayi ya shafe komai da yake ji , baya jin zai iya yi mata wani abu saɓanin rarrashi saboda tsantsar soyayyarta da yake jin yana bin dukkan sansar jikinshi , gaba-daya ya manta mama da umma dake cikin motar ,ya matso kusa daita ya riko laulausan tafin hannunta cikin nashi ya matse gam yana ci-gaba da kallonta "dan Allah ki daina kukan nan yana ci min rai yaya kike son nayi ?"nima Ina cikin tashin hankali fiyye da wanda kike ciki ,tabe bakinta tayi haɗe da fixge hannuta "ina ruwana da tashin hankali da kake ciki kowa tashi ta fisheshi ni abbana ...
" ka maidani gida ina son sanin halin da yake ciki nayi nadamar biyoka da nayi alhalin abbana na cikin wani hali .
yayi shiru yana kallonta ta kawar da kanta gefen titi alamun bata son ganin fuskarshi ,yana shirin magana wani kiran ya sake shigowa wayarsa ,ya lumshe idanunsa ya buɗe yana saukesu akan wayarsa ya ɗauka domin ganin mai damunsa da kira da sauri ya ɗauki wayar ya manna a kunnenshi sakamakon ganin sunan wanda ya kira "dady ..... ya kira sunan zuciyarsa cike da mummunar damuwa .
"kana ina ?
Yayi saurin katse shi da sauri na kusan karasawa gida ,"maza ka dawo yanzu yanzu baba sarki yazo yana son ganin mama da umma ya fad'i haka ne saboda yasan muddin yace shi yake son gani ba zai dawo ba, naunayen ajiyar zuciya ya sauke sai lokacin ya tuna suna tare dasu ya juya baya a hankali inda suke zaune suna karanto duk addu'ar data zo bakinsu domin samun natsuwar zuciya ya sauke wayar a kunneshi "lafiya baba ? mama ta Kira sunanshi hankalinta a tashe tana addu'ar Allah yasa ba wani abu ne ya samu abba bayan fitowarsu ba .
"Wai baba sarki ne yazo yake son ganinku bari na juya, ya soma ƙoƙarin juyawa haɗe da cewa "ke kuma karki sake damuna, dan kukanki yana damun kwakwaluwata ya cilla motarsa kan titi ya figa aguje .
Minti goma sha biyar ne ya kawo ma'hruf gida ,mama da umma da ummita suka shigo ma'hruf na bayansu , Abba na ganinsu ya sauke naunayen ajiyar zuciya ya gyara daga kwanciyar da yayi ya zauna yana kallonsu zuciyarsa na dokawa hawaye na sake zubowa daga idanunsa ..
Guri suka samu suka zauna bisa ga umarnin baba sarki ,kallonsu
abba yake yana jin sanyi a ranshi su kaɗai suke sakashi farinciki a duniya .
A hankali baba sarki ya cigaba da magana "Rayuwa dai duk yadda Allah ya rubuto babu wanda ya isa ya canza ta, ita kaddara kuma tana kan kowa hajiya ki maida hankali ki,karki bari ki mutu da hakin rayuka da yawa akanki kina abu tun da sauran kuruciya har zuwa yanzu da rai ya kai gargara kina kan abu daya kamar addini .....
" a yanzu dai bazan sake miki nasiha akan abubuwan da kike saboda na gaji da halinki, na gaji da yi miki nasiha , sai dai Allah na ganin komai kuma shi zai hukuntaki bisa abinda kike saboda baki dalili ko hujja na tsanar baiwar Allah nan maryam , babu abinda tayi miki illa tsabar kabilanci dake damunki akanta , tana binki tana miki biyyar da ko hausa fulani da kike son Ibrahim ya aura albarka ,a irin biyayyar da take miki kina ganin da bahaushiya ce zata jura ?
" Sannan yadda kike tunanin da iko da gadarar kina da karfi da iko akan yaran nan haka nima nake dashi a matsayina na kanin mahaifinsu .
Baba sarki ya juya ya dube Abba cikin sarewa yace "ban lamunce maka rabuwa da matarka maryam ba har abada sai da mutuwa ta rabaku haka kaima ma'hruf ka ɗauki matarka ka wuce daita , Kema mairo ki koma d'akinki matsawar zaki fahimceni barinki rayuwarmu ba ƙaramar hasara bace ..
A qalla baba Sarki ya ɗauki kusan awa uku yana magana yayi da mama sannan ya juyo ya dubi hajiya Inna, sannan ya dubi sauran jamar dake gurin a karshe ya mike tsaye duk mazan suka mike Abba zai tashi ya dakatar dashi "kayi zamanka Ibrahim na yafe Allah ya baka lafiya Allah yayi maka albarka , ka daina biyewa shirmen mahaifiyarka saboda babu biyayya ga bawa a gurin sa'bon Allah , ita mahaifiyarka ce kayi mata biyyaya daidai yadda Allah yace amman gurin sakin aure babu wannan biyayyar ko ta tsine maka babu abinda tsinuwarta zata maka gabadaya suka rufa masa baya har hajiya Inna suka bar ummita da Abba da mama .
Mama ta mike ta nufi d'akinta tana kuka tana tausayawa kanta da diyarta a hankali shima Abba ya yunkura da kyar yabi bayanta a bakin gado ya sameta tana zubar da hawaye ya zauna kusa daita ya riko hannunta "ki ƙara hakuri Maryam , nasan kina hakuri dani sai dai ina neman alfarma ki ƙara hakurin , kuma hakurin nan naki ba zai tashi a banza ba , sannan ki daina kuka dan babu rabuwa atsakaninmu har abada muna tare a gidan duniya har ma aljanna kece shugaban matana aljanna ,maryam ina girmamaki ,kina da kima da daraja a idanun Ibrahim ke din yar aljanna ce , Allah ne gatana dake bazan iya rabuwa da me gatantani ba muddin ni zan d'aga miki kafa ki shiga aljanna na daga miki maryam daga yau sunanki yar aljanna kalamai masu sanyi da kwantar da hankali abba ya dinga furtawa mama wanda ya kwantar mata da hankali har yayi nasarar yaye mummunar damuwar data kama zuciyarta ..
A can parloun'n kuwa tashi ummita tayi ta shigewarta d'akinta yana dawowa bai ganta ba dan haka ya biyota dakin ya zauna kusa daita "ki daina kukan nan haka zai iya haifar miki da wani ciwo ya riko hannunta cikin nashi ya tsarke waje ɗaya yana kallonta ,a hankali ya dinga ji wani maganaɗisu sonta na shigar shi yayinda sha'awarta ke bijiro masa, bakinsa ya kai cikin kunnenta yana busa mata iskar bakinsa yana sakin numfashi "ki tashi mu wuce gidanmu mu fara sabuwar rayuwar ta fahimta .
"kayi tafiyarka dan babu inda zani bai san lokacin daya birkitota saman ruwan cikinsa
ta kwanto a saman fad'ad'd'en qirjinshi dukiyar fulaninta suka sauka a fuskarshi a hankali ta furta ashiiiiiiiiiiii...
bakinsa ya kai saman dukiyar fulaninta ya manna musu kiss take tsigar jikinta suka mike ya ɗauki minti goma yana kissing brest d'inta yana goga mata kusaunbar fuskarshi ya karshe ya kamkameta a jikinsa ya haɗe bakinsu guri daya ya shiga tsotsa da kyar ta samu ta fixge bakinta da yake aikin sarrafawa ta sakar masa kuka "ni ka kyaleni banaso abinda kake min "dole ki so yarinya yanzu ma kikayi register..
"Ki ko yarda ko karki yarda ina sonki fatlion cikin kuka tace "you no tru love me sam bazan yarda da hakan ba duk bakin daya ki ko ya dawo yace yana so ba abun yarda bane ,"common listing to me fatlion sheshekar Kuka kawai take .......ki fahimceni fatlion ni kome zaki ce sai dai ki faɗa amman bazan taba yarda ba ,zuciyata bazata taba yarda da bakya son mah'ruf ba in dai zuciyar mah'ruf zata soki dole kema ki soshi i will not let you down idan ma har da gaske bakya sona shijenan nima na hakura ..
Jikin ummita yayi mugun sanyi kunji ba ai daman tasan ba son tsakanin da Allah bane ,soyayyar karya ce taya ma zata yarda dashi ? tashi yayi ya zauna yana shafa cikinta "bari na kawo miki abinci kici nasan ke da babyna kuna jin yunwa tayi shiru tana jin maganarsa tamkar a mafarki ta ɗan mintsi kanta dan tabbatar da shi din ne ko kuwa mafarki ne jin zafi ya ratsa jikinta ta tabbatar da gaske ne ya cigaba da shafa cikinta "ki kwantar da hankalinki muyi zamanmu lafiya ko dan kwantar da hankalin iyayenmu ba dole sai mun so juna ba amman musan mahimmanci juna ya k'arasa maganar yana kai wa gefen wuyanta kiss ta soma ƙoƙarin janye jikinta ya sake janyota "ki dana fizge jikinki ajikina kinsan ....
Shiru yayi sakamakon turo kofar d'akin da akayi meenal ce ta shigo sai dai da sauri ta juya "meenal ya kira sunanta da sauri ta amsa da na'am tana sake dawowa d'akin ta tsaya "ina yini yaya ?
Bai amsa gaisuwarta ba ya sauko daga kan gadon "ki kular min daita plz taci abinci dan bana son wani abu ya taɓa lafiyar babyn jikinta zanje na dawo sauran kaɗan dariya ta subuce mata tace "tam yaya ko dai naje na dibo abinci ne ka bata da kanka ?
Ya watsa mata wani mugun harara "abinda na sakaki kenan dan ubanki da zaki miki wata irin tambaya ?
tayi saurin sunkuyar da kanta "to ai nima ba dadewa zanyi ba yanzu zamu wuce da Abdulshakur "wuce kije dan ubanki kai tsaye kuwa ta wucewarta tana murgud'a masa baki "kaji min yaya haka kawai zaka wuce akaina kai me yasa bazaka tsaya ka kula daita ni nayi mata cikin ?
Yana fitowa idanun mutanen gidan yayi masa caaaa dan duk sun dawo parloun'n daga rakiyar baba sarki ya bala'in sha mur ya wuce d'akin mama nan ma tare da mama rukkaya ya gansu juyawa yayi zai fita mama ta kirashi "baba ya juyo batare daya shigo ba "kana bukatar wani abu ne ?ya girgiza mata kanshi "kaje ka sake bawa inna hakuri kai da ummita yace "naji atakaice ya sake juyawa ..
Kai tsaye kitchen ya nufa ya ɗauki plet da spoon ya buɗe kula ,ya zuba jollofy din shimkafa wanda taji naman rago ya diba ya dauki ruwan roba ya nufi d'akin tana zaune har lokacin ,menal na zaune kusa daita tana tambayar yadda abun ya faru ,yana k'arasa shigowa ya tsareta da idanunsa yana watsawa menal kallon banza ,sannan yace "dan ubanki ba tafiya kika ce zakiyi ba zaman uban me kike wa mutane ?"ummm ammmm "yi min shiru stupid daman gulma ne ya kawoki oya maza kafin na kirga uku ki kama gabanki tsimi tsimi ta mike ta fice tana gunguni ,ya k'araso har kan gadon ya zauna ya ajiye roban ruwan akan bedside d'inta yana kallonta yana mata magana gabadayan jin maganar tashi take wani iri ,ta saita zuciyarta sosai tana son amincewa zuciyarta abinda yake faɗa mata gaskiya ne , amman wani bangaren na zuciyarta yana karyata haka saukar muryarsa tayi a cikin dodon kunnenshi "bude bakinki kici abinci yayi maganar yana tsare gira kamar wanda bai taɓa dariya ba , ganin haka yasa ta motsa labbanta a hankali "na koshi ,"ban gane kin koshi ba me kika ci ? yayi maganar a fusace "bake da kike d'auke da ciki ba ko ni yunwa nake ji common ki bud'ewa mutane baki kafin raina ya ɓaci ,kin bude bakin tayi har sai daya kai spoon bakinta sannan ta buɗe tana yatsina fuska a hankali ya dinga feeding d'inta tana amsa har sai daya tabbatar data koshi sannan ya barta ya bata ruwa ta sha yana kallonta yana qarasa cinye sauran abincin bayan ya gama ya rike plet da hannu daya, dayan hannunsa ya riko hannunta "oya muje mu bawa hajiya inna hakuri "hakuri kuma ?ta faɗa kamar zata yi kuka "eh haka mama ta bukata kuma kinsan dole a cika umarninta shiru tayi batare da tace komai ba ta sauko ta biyo bayansa...
Da sallama suka shiga d'akin inna , shiru babu alamun motsin kowa dan haka ya sake sallama yana tsayuwa a tsakiyar d'akin idanunshi an kan ummita , gunjin kukan hajiya inna daya ji ne ya tabbatar masa da inda take hankalinsa a tashe yace "ki tsaya anan bari na fara shiga, shiru tayi masa tare da lumshe masa idanunta ya kutsa cikin uwar d'akan inna tana zaune akan gado ta jingina bayanta da abun gadon , kafarta ɗaya a kan ɗaya tana girgizawa, hannunwata duka suna kan katifa tana kallon celling d'akin kuka take sosai kamar wacce aka sheidawa mutuwarta a lokacin ,ya k'araso ya zauna kusa daita ya riko hannunta "why hajiya inna kukan me kike yi? " komai ya rigada ya wuce yanzu ma zuwa muka yi mu baki hakuri dan Allah kiyi hakuri ki yafe mana ya sake matsota "muna matukar sonki ,shi yasa muke kyamatar wannan qabilancin dake damun zuciyarki dan idan kika cigaba Allah zai hukuntaki akan haka ,ta sake rushewa da wani kuka "akan maryam Ibrahim ke neman mutuwa ya barni kenan yafi sonta akaina ?"a'a inna ita fa matarsa ce ,ke kuma mahaifiyarsa ce bama za'a hada ba , muhallin uwa daban na mata daban ,zai iya rabuwa da mama ke fa kuna tare muddin rai kuma ina da tabbacin abba yafi sonki akan mama kinsan wani abu ?
Ta girgiza masa kai "idan ana zaman lafiya zaki fahimci abba yafi sonki akan komai dake cikin duniya ki duba yadda yake gudun ɓacin ranki ,duk abinda kika ce shi yake yi wannan kawai ya isa ki fahimci tasirinki garesa dan Allah kiyi hakuri kinji inna ki daina kin mama ...ta numfasawa tana sauke ajiyar zuciya ya tashi ya dawo parloun inda ummita ke tsaye " shiga ki bata hakuri ,ta yatsina fuska alamun bata son shiga "bana son mutsu ko gardama kiyi abinda na saki "kai baka bata hakuri ba ?"kina hauka ne ina baki umarni kina tambayata ?
Hanyar dakin ta nufa ta shiga tayi sallama a ciki inna dake zaune tana ganinta ta ɗauke kanta ta tsaya daidai saitin kafafunta jiki a sanyaye ta kai hannunta zata taɓa kafafunta tayi saurin janye kafarta shiru ummita tayi tana dubanta cikin haka mah'ruf ya dawo d'akin ya tsaya a bayanta tare da riko hannunta ya daura kan kafafun inna "kiyi hakuri dan girman Allah , muna sonki kiyiwa daraja annabi ki sawa aurenmu albarka kamar yadda kika sawa kowa naunayen ajiyar zuciya ta sauke "Allah yasanya albarka "ameen ya cire hannunsa ya dawo kusa daita ya zauna "na gode inna Allah ya qara miki lafiya da nisan kwana ummita ta juya cike da sarewa ta koma d'akinta ta rafka tagumi "inna fa har yanzu batayi na'am daita ba ,me ye abun yi ?ta yiwa kanta tambayar sama da mintuna hamsin tana zaune tana tunani shi kuwa mah'ruf daga bangaren inna gida ya wuce saboda baba sarki ya tabbar masa da kada ya kuskura ummita ta kwana a gidan ..
Jin ance a daren za'a raka ummita gidanta yasa meenal fasa wucewa ta dawo gurin Ummita tana kwashewa da dariya "wannan love haka daman nasan sai kun haukacewa juna "Ummita ta ta'be baki "a ina kenan ake wani love ?
"kin dai kasa fahimta ne ni da yayanki babu wannan a tsakaninmu "na dai ji adai tausaya ma yayana dan naga ya rufta da yawa karki wahalar min dashi wannan rud'ewar da aka faɗa min yayi akan za'a rabaku ya ..
"Dan Allah meenal ta daga mata hannu ,"nayi shiru oganinya kuma uwar gidan mahruuuuuuu...
Bari na kirawo wacce zata cancara miki kwaliya ummita taja tsaki .
Tun akan hanya ya kira suhaima yace "ta tattara komai data sanin nata dake bangarensa ta maida part dinta ,dan nan bangarensa Ummita zata zauna kafin a gyara part dinta , hankalinta ya sake bala'i tashi amman ta danne tace "to sai ka k'araso .
Karfe shida daidai mama ta kira ma'hruf ,ya zo cikin farin yadi mai sharara tamkar wani sabon ango ya zauna kasa a gaban mama cike da girmamawa hannunsa d'aure da agogon fata baki ,ummita mama ta kira sunanta ta fito daga uwar d'akanta sanye cikin wata had'ad'd'en shadda gezner mai ruwan kasa cikin jikinta daya ɗan taso ya sake kara mata kyau ainun , hannunta d'aure da farin agogon magnet mai bakin fuska mama ta nuna mata kusa dashi da hannunta ta zauna jikinta na fidda wani kamshin mai sanya natsuwa da kwantar da hankali ,a hankali mama ta soma musu nasiha tana sake tunatar da junansu hakkin kansu daya rataya a wuyansu sosai ummita take kuka " Ummita ga amanar d'ana na baki kada ki curta min d'a , kaima baba ga Ummita nan ka riketa amana kada kaga yar'uwarka ce ka nemi take hakin suhaima akanta Allah ba zai barka ba ,ta sake duban ummita bana son azo min da wani matsala idan naji matsala kece kuma ki kuka da kanki dan nasan halin mahruf haka nasan halin suhaima, cikin kuka tace "inshaallahu zan kiyayya "Allah yayi muku albarka kana iya wucewa "a'a mama bari kawai na wuce daita yanzu banason wani hayani ,da yake tasan halinsa ba tace masa komai ba har sanda ya sanyata gaba suka fito zasu wuce mutane suka masa caaaa aikuwa yace "babu wanda zai biyosa baya son hayaniya a zo daga baya kamar wani biki za'a wani kwashi jiki ,haka mutanen gidan na kallonsa ya wuce daita tun tana kuka yana jinta har kukan ya tsaya ya kasance hawaye ne kawai ke fita ya wuce daita part d'insa ya kwanta ya daura kanshi a kan pillow ya janyota jikinshi "wai ba zaki daina sheshekar kukan nan ba sai na canza miki ?
Tayi masa bazan kiran jafar ne ya shigo wayarsa yana ɗauka yace "dan ubanka a she komai ya daidaita tsakaninka da matarka shine ko labari babu ?
"A ina kaji ?
"Yanzu nazo gida sakina ke faɗa min "ai kuwa zan sake canza mata .
"Dan girman Allah ka rufa min asiri ni ne na tambayeta ummita shine take faɗa min abinda ya faru karka ballo min ruwa dan kulawar da nake samu adaina bani tsaki mah'ruf ya ja "aikin banza kai yanzu har canzawarta zai dameka ?
"Sosai kuwa abinci wani guban wani ni ita nake so .. kit ya katse kiran bai ce mata komai ba ya janyeta a jikinsa ya fice daga dakin bata kara ganinsa ba sai dare ya shigo yace tazo taci abinci babu mutsu ta mike dan fuskarsa babu alamun wasa
Ko gurin cin abinci Ummita bata kalli inda ma'hruf yake ba, mamakita a cunkushe a zuciyarsa ya d'ago ya sanya kwayar idanunshi cikin nata cike da jin haushi taki cin abinci, suhaima na kallonsu dadi ya cikata ganin ba wani alamun tana farinciki da tarewarta .
Muryarta cike da kissa tace "haba ki saki jikinki kici abinci karki takura babynmu tunda sai kinci sannan shima zai samu yaci ummita ta galla mata harara "meye matsalarki dani karki dameni cikinki ko nawa ? Ta faɗa a fusace tana watsa mata harara ..
"Shiiiiiiiiiii karki zageta daga abun arziki ko sa'arki ce ? mah'ruf yayi magana yana tsareta da manya idanunshi "idan kika sake faɗa mata bakar magana zan..
"No habibi ka barta nifa banji komai ba kasan lamarin masu ciki sai a hankali "nata har da iskanci ki soma cin abinci tun raina bai gama ɓaci dake ba, batace komai ba ta maida hankalinta ga plet din gabanta daga ma'hruf har ummita babu wanda yaci abincin karki sai tsakura da sukayi, bata wani ci abincin ba ta mike ta bar gurin ta dawo part dinta ,kwanciya kawai tayi tana juyi bacci ya kauracewa idanunta, tunaninta duk yana kan ma'hruf data baro tare da suhaima a hankali nadihar mama ta shiga dawo mata ..
Suhaima kuwa kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha dan dadi musamman ta bugawa Hajiya rahma waya ta fada mata komai, dadi ya cikata tace "kin gani ko makirci ma kawai ya isheki da haka zamuyi nasara akan shegiya daga karshe ki fitar daita ,wani irin ihun dadi suhaima ta saki sakamakon wata mugun kirsa da hajiya rahma ta faɗa mata "kai yayarmu Allah ya bar min ke ai kuwa zanyi tunda asiri yaki cin tsinannu ai mayi maganinsu ta hanyar makirci nan suka cigaba da hirarsu ta mugunta ....
*****
Tsawon sati guda Ummita bata wani sakewa da mahruf zai shigo d'akinta ya kwanta idan ranar kwanta ne ranar da ba kwanta ba zai shigo ya duba lafiyar jikinta amman har lokacin zuciyarta bata gama amincewa dashi ba duk abinda yake mata da ido kawai take binshi shima bangarensa bai damu haka bai matsa ba yana son ta fahimci sonta yake ba wai jikinta yake bukata ba ..
Ranar asabar da misalin karfe tara na safe yana zaune akan kujera mai zaman biyu system ne a gabansa yana aikin tura sakonin yayinda ummita ke tsaye a bakin dres mirrow sanye da dogon wando da riga iya gwiwa tana gyara gashin kanta daya zubo bayanta tana ƙoƙarin bude kwalbar kwallacca murfin ya caki farcenta ta saka ƙara tana yarfan da hannunta ,ya d'ago a gigice ya tashi jikinsa na rawa ya k'araso gareta ya rike hannuta yana kallon yadda gurin yayi ja "sorry ya saki hannu da sauri ya nufi inda man zafi yake ya d'auko ya dawo gareta ya lakato zai shafa mata tayi saurin ɗauke hannunta .
"Karka damu ba wani abu bane fa zanyi manage ,ta wuce shi yayi shiru tare da cilla da man akan gado yana jan tsaki ,ya koma gurin zamansa zuciyarsa na dokawa da matsanancin karfin gaske ..
yana tsaka da aiki ya soma tarin karya da sauri ta dawo kusa da shi ta zauna " sannu me ya same ka bari na kawo maka ruwa tayi saurin mikewa jikinta na wani irin rawa sauran kaɗan ta tunsura ta tsiyayo ruwa a cikin glass cup ta miko masa ya kalleta yana girgiza mata "karki damu ba sai na sha ba zanyi manage tayi shiru tare da tsura masa fararen idanunta tana kallonsa kirjinta na wani irin mahaukacin bugu .. "wannan kawai alama ce ta muna tsananin son juna , idan ma za'a iya bincikar zuciyarki za'a iya samun soyayyarki ta dara tawa yana gama maganar ya dauke kanshi ya cigaba da aikinsa .
Jikinta a sanyaye ta fice daga d'akin gabadaya tana sauke numfashi "wayyo Allah nah Allah ka taimakeni bana son ya fahimci irin son da nake masa ranar menal ta kawo mata ziyara sun dade a parlou suna hira har sanda mah'ruf ya fito ta gaishe cike da girmamawa ya amsa atakaice ya wucesu suka koma daki suka cigaba da hirarsu a hankali suhaima tazo ta la'be tana nad'e abinda suke cewa .....
Ranar monday da misalin karfe shida na yamma Ummita ta fito daga d'akinta tana sha'awar cin indomi gabad'aya jikinta a mace yake taku daya biyu tayi akan step kawai taji tayi kasa gabad'aya an hantsilata take ta saki wani razananniyar ƙara ta soma mulmula daidai lokacin da ma'hruf ya shigo yana ƙoƙarin kulle motarsa ya jiyo 'kararta ya shigo gidan aguje hangota yayi kwance a karshen matattakala dafe da cikinta da mararta ya saki wata gigitaccen ƙara tare da kiran sunanta a matukar firgice" fatlion karar da yayi yasa suhaima fahimtar ya dawo gidan .
ta fito a gigice ta tarar dashi ya daura hannunsa duka a saman kanshi tsabar rudewar jinin daya gani a kasa ,ta karasa inda ummita take jujjuya kai , wani irin azaɓaɓɓen dadi ne ya kamata ,aranta tace" magana takare Allah kasa cikin ya zube daga nan ita da samun wani cikin sai dai taga ana yi dan duk abinda zatayi zatayi amman bazata yarda har ta samu cikin da zata haifa ba ita tana zaune ,amman dan tsanani makirci sai tayi kan Ummita da sauri ta dagota ta rungumeta ajikinta tana kiran sunanta" Ummita Ummita garin yaya haka ta faru? idan ma wani abu kike so ai sai ki faɗa min Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun, sannan ta waigo tana kallon inda ma'hruf yake ga mamakinta sai taga hawaye yake zubarwa haushi da takaicinsa ya kamata, zuciyarta ta dinga tuttukin bakincikin mara misaltuwa amman haka ta waske tace "habibi ka taimaka mu kaita hospital tun wani abu bai samu cikin ba.
hankalinsa a tashe ya k'araso ya ɗauketa ajikinsa ya rungume yana kallon fuskarta "shikena na rasa babyna "sakacinki ya janyo zanyi hasarar babyna ya sanyata a bayan mota har lokacin idanunta na runtse sai dai bakinta bai daina salati ba da sauri suhaima ta shige bayan motar ta zauna tare da daga kan Ummita ta daura saman cinyarta tana Mata sannu .
gudu kawai yake akan titi ita kuma suhaima tana yadda zata dannewa ummita makoshi ta rabata da rayuwarta gbdy ikon Allah ne kawai ke tafe dashi dan bai san inda yake wulla motar ba har suka kawo asibiti ..
Nan da nan aka dauko gadon marasa lafiya aka daurata aka shiga daita ciki ya biyosu agigice shi da suhaima gaba-daya ya gama sadaukarwa dansa ko yarsa ya zama tarihi ,qirjinsa har dagawa yaje tsabar tashin hankali da yake ciki ya kasa zaune ya kasa tsaye sai safa da marwa yake a tsakanin dakin daaka shiga daita yayinda suhaima ta zauna akan jerin kujerun dake ajiye agurin tayi tagumi munafurci,cikin ranta tana addu'ar Allah yasa cikin ya zube ..
Tsawon lokaci babu wanda ya cewa d'an'uwansa komai kowa da kalar tunanin da yake, zuwa lokacin zuciyarsa ta shiga sake sake da faduwarta, sama da awa daya doctor husain ya fito suka rufeshi da tambaya "yaya dai doctor cikin ya zube ne ?
Tausayinsa ya kama doctor ganin yadda ya dawo yace "ana bukatar jini amman dai zai fi kyau ...
"cikin jikinta fa ? mahruf yayi saurin katseshi ta hanyar fadar haka "bamu gama gano matsayinsa ba tukun jini dai muka fi bukata kafin mu karasa bincikenmu amman ka kwantar da hankalinka ...
TWO FRIEND'S BSBS
💗💗💗💗💗💗
WANNAN CE
QADDARARMU
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
~TRUE LIFE STORY~
FREE NOVEL
AL'QALUMAN
*AYSHA A BAGUDO*
*FAIZA HAMMADU*
~DEDICATED TO~
*NURATU IBRAHIM YAURI YAR KWANA NAYI MISSING DINKI*
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
PAGE 56
"Inshallahu babu wata matsala , jikinsa duk a sanyaye ya rufawa likita baya zuwa wani d'aki inda za'a ɗibi jininsa , cikin kankanin lokaci aka gwada jinin ,koda likita ya faɗa masa jininsu ɗaya da ummita bai yi mamaki ba ,dan a yadda kamanninsu yake zai wuya hakan bata kasance ba .
ya kwanta akan wani madaidaicin gado aka dibi jininsa leda biyu ana gama diba likita yace " ka huta bayan ya bashi maltina likita, yayi shiru a kwance yana tunanin ummita da cikinsa , zuciyarsa cike take da matsanancin fargaban game da halin da cikinsa yake ciki , ya lumshe idanunshi tamkar mai bacci alhalin ba baccin yake ba, a hankali gefen kansa ya dinga sarawa dan shi kanshi jin jikinsa yake tamkar mara lafiya saboda tashin hankali da yake ciki ,suhaiman ta shigo in da yake kwance zuciyarta fal da bakinciki adalilin jininsa da yayi daidai dana ummita , taso a sha wahala gurin samu jinin ko kafin a dawo ta karasa barzahu .
ta zauna kusa dashi ta riko hannunsa cikin nata tana taya shi jimami tare da kwantar masa da hankali yayinda a zahiri kuma addu'a take Allah yasa cikin ya bare ..
Kusan awa biyu likitoci na tsaye akan ummita sannan doctor husain ya dawo d'akin suhaima na ganinsa ta mike tsaye daga zaunen da take a gaban mahruf ya zauna akan kujerar data mike ya fuskanci mahruf yana mai tausaya masa ganin yadda hankalinsa ya tashi , cike da rawar jiki mahruf ya mike zaune yana duban doctor "Yaya take doctor ya cikin jikinta ?
"Bana son mu rasa cikin nan , wannan cikin sanyi idaniyan mama ne dani kaina , tunda mama tasan da cikin nan farincikinta ya karu , bama ita ba duk wani masoyinta yana farinciki da tayata murna dan Allah karka faɗa min cewar mun rasa babynmu .......
"mahruf doctor husain ya kirashi bai amsa ba illa idanu daya bishi dashi "mu muslimai ne masu imani , sannan imaninmu bazai cika ba har sai mun yarda da kaddara mai kyau ko akasin haka, take wani sanyi ya lullu'be mahruf sai dai hankalinsa ya sake kololuwar tashi "shikenan da alamun na rasa cikina yayi maganar a kasan zuciyarsa .
Dor'ctor husain ya cigaba da magana bayan ya sauke naunayen ajiyar zuciya "mama mai ilimi ce bazata ji babu dadi aranta ba sannan ba zataji haushi bisa hukunci ubangijita ba.
Allah kan jarabi bawansa da kaddara na bakincikin dana farinciki domin ya jaraba imaninsa ya gani ko bawansa zai amshi jarabawarsa da hannu biyu biyu ,ina son ka ɗauki abinda zan faɗa maka amatsayin kaddararku yayi saurin cewa "karka ce na rasa babyna na wata biyar going to sex mouth dake jikin ummita ......?
Doctor husain ya tsura masa ido yana had'iye wani miyau daya tsaya masa a makoshi Karo na farko kenan da doctor Husain yaji mah'ruf ya ambaci sunan ummita a hankali ya d'aga masa kanshi alamun "eh yana kallonsa "cikin jikinta ya fita ko ince tayi nakuda ta haifi abinda ke cikinta wanda ya kasance twins Kuma duk maza , wani irin ƙara mahruf ya saki yana ƙoƙarin durowa daga kan gadon a gigice suhaima tayi saurin dafe kafadarsa tana bashi hakuri gaba-daya ya dimauce jin maza har biyu yayi hasara "kayi hakuri habibi, haka Allah ya kaddaro mana wallahi ummita ce bata jin magana ,tana da d'aurin kai tunda ta dawo kullum sai nayi mata magana akan tsalle tsallen da take da cikin gashi ta janyo munyi hasarar baby har biyu ta k'arasa maganar tana kuka wanda da gani na munafurci ne .
"kayi hakuri ka kwantar hankalinka ka mika lamurranka ga Allah sai ya sake bamu wasu masu albarka abun yayiwa doctor Husain Dadi ,dan yadda suhaima ta nuna damuwarta tayi matukar burgeshi , da ana samun kishiyoyi irinta da wasu matan basuyi bakinciki dan za'ayi musu kishiya ba .
tunda doctor da suhaima suka fara magana ya zuba musu ido kawai yana kallonsu jikinsa na rawa har suka gama bai iya cewa komai ba domin bai san abinda zai ce ba, ko yace ma zai magana muryarsa bazata fito ba ya lumshe idanunshi hakan ya baiwa kwallar dake cikin kwarnin idanunshi damar zubowa "farkon yayan da zai samu ya rasa, shi kaɗai yasan halin da shi da mama zasu shiga akan rasa ya'yan nan yana matukar kaunar ciki ko yace Allah ya jarabeshi da cikin , a hankali ya furta ya Allah ka bani wasu masu albarka ....
Doctor yace "ameen" muje ka kai ni naga yarana yayi maganar yana jin zafi acikin ranshi ,doctor ya Mike shima ya sauko daga kan gadon da kyar yake daga kafafunsa suka fita tare ..
Suna fita suhaima ta hau tikar warar shaku shaku tana jin farinciki mara misaltuwa, sai da tayi rawar sosai sannan ta kira number hajiya rahma "yayarmu albishirinki ? a can bangaren hajiya rahma tace "goro "ki tayani murna cikin wannan yar iskan ya zube ,a she ma yan biyu ne ,shi kanshi bai sani ba sai a yanzu "ke dai bari yayarmu yau ina ciki murna da farinciki mara misaltuwa kamar an sani a aljanna haka nake jina , can tayi shiru tana sauraron hajiya rahma sannan ta sake kwashe da dariya tana rawa da juyi "ke dai bari yayarmu ni dama an bar ma zance zuwa gurin malamin nan wannan makurcin ma ya isa wallahi "okya shikenan maje din ai zata sani ne sai tayi nadamar zamowarta kishiya agareni tana ji tana gani zata bar min mijina ,shima ɗan iska wai har da kuka yayi fa, ta k'arasa maganar tana kwashewa da wata dariya sannan tayi mata sallama ta fito da sauri tana neman inda suka shiga ..
Shiru yayi tsaye yana duban jariran ya'yansa waɗan da an gama halintta masu komai masu tsananin kama dashi sai dai sunyi kankanta da yawa , take wasu zafafan hawayen suka zubo masa jikinsa na rawa ya sake matsowa garesu sosai yana dubansu ɗaya bayan ɗaya yana jin soyayyarsu na sake shigarsa ,bai ma san yana tsabanin son baby's d'insa ba sai daya rasasu ,ya yarda da kaddara amman har da sakaci ummita ....
doctor husain ya dafa shi "kaga yadda sukayi kankata ko ?
Ya kada masa kai batare da yace komai ba "wannan kankantar nasu nada halaka da rashin kusantarta da bakayi da alamun tunda aka same su wani abu bai sake shiga tsakaninku ba ,ya sake yin shiru yana cigaba da kallon yaran yana hawaye bai taɓa yiwa abu kuka ba duk tsananin abu ya kan daure amman ya rasa dalilin da yasa ya kasa daurewa wannan rashi da yayi doctor yace "kayi hakuri ba kai ba koni naji rashin dadin komawarsu Allah dai ya bamu wasu masu albarka .
Still bai ce masa komai ba juya ya nufi d'akin da aka kwantar da Ummita doctor husain bai yi kokarin biyosa ba
ya zuba duka hannuwansa cikin aljihun wandonsa ya tsaya a tsakiyar d'akin bayan ya shigo yana kallonta kwance daga nesa tamkar wata matacciya , alhankali ya dinga d'aga kafafunshi har ya k'arasa bakin gadon ya tsaya yana cigaba da kallonta da kyawawan idanunshi da suka koma ja yana jin kamar ya tasheta ya saka mata kuka ....
suhaima ce ta shigo ta tsaya kusa dashi tana faɗa masa kalaman rarrashinta na karya kafin daga baya ta janyo masa kujera "ka zauna habibi kar juya ya debeka bai yi mata mutsu ba , ya zauna batare daya ɗauke idanunshi akan ummita ba , "ka natsu dan Allah nan da wani lokaci zamu sake samun wasu ka sani ma ko nice zan kawo maka kyawawan baby's tayi maganar tana satar kallonsa domin taga reaction d'insa akan abinda tace , ya kai hannusa saman hannunta tayi saurin damkewa "na gode suhaima yayi shiru yana lunshe idanunshi sai a yanzu yake kaara sanin mahimmancinta arayuwarsa, tana tsaye akansa da alamuran gidansa shi kuwa me zai yi ya faranta mata ?
"Ka soni so na har abada habibi ,ina sonka son da ban ta'bawa yiwa wani mahaliki irin shi a duniya ba...
jin amsarta ya fahimci a filli yayi maganar ya sake damke hannunta gam cikin nashi yana murzawa ..
Jikinsa a sanyaye ya ciro wayarsa ya bugawa Abba ya sanar dashi abinda ya faru da Ummita ,abba yaji ciwon abun sosai dan shima ya kwallafa ranshi akan cikin amman tunda ga yadda Allah yayi ikonsa hakuri zaiyi , lokacin da mama taji har da kuka tayi a boye , hajiya Inna kuwa tamkar wacce akayiwa albishir da gidan aljanna daman kullum addu'a kenan Allah yasa cikin ya zube da cikin dan ita har lokacin bata yarda cikin na mahruf bane.
a parloun'n mama yan'uwa suka cika ana jajantawa juna , Inna kuwa na d'akinta tun da tace wa Abba Allah ya kyauta bata sake tofa albarkacin bakinta ba sannan bata tako part din mama ba ,duka gidan hankalinsu ya tashi hajiya umma tayi kuka sosai ba dan mahruf ya kasance d'anta ba saboda mama ne dan lokacin da zance cikin ummita ya fito taji dadi sosai mama zata sake samun zuri'a amman sai gashi sun rasa take ta soma magana "anya kuwa babu sanya hannu a fitar cikin nan ,jikina na bani akwai wani abu .. ?
Mama tayi saurin cewa "kai haba mufa muslimai ne bai kamata muna kawowa zuciyarmu irin wannan tunanin ba , Allah ya bayar kuma ya amshi abunsa , dole hajiya Umma tayi shiru ..
aunty ma data zo sai da tace akwai wani abu "ina jin tsoron dagin suhaima fa sam babu imani a zuciyarsu zasu iya aikata komai gaskiya ban yarda da zamansu tare ba gara ummita ta koma bangarenta daga kwana biyu har sunyi wata a guri daya .
mama tace " koma dai menene mu barwa Allah komai zato zunubi ne koda ya kasance gaskiya ne muyi musu addu'a kawai "kunji matar nan wai muyi musu addu'a suwa kenan ..?
"Kinga ni diyata kawai na sani ,kuma ita kadai zan yiwa addu'a ba waɗan nan shedanun ba, kune baku da labari auren ita dayar yaya suhaimar ya dade da mutuwa wai mijin ya bude wordrob din kayanta zai dauki turare yaci karo da tukunyar tsafi shine fa yayi mata dukan mutuwa ya korota gida da takardar saki uku.."to Allah ya kyauta ya ganar dasu gaskiya suka ce "ameen daga nan suka shiga shirin zuwa asibiti .
Duk yadda suhaima ke rawar jiki akan ummita a banza dangin ummita suke kallonta har ta sha jinin jikinta ta kebe kanta gefe dan irin kallon tuhumar da suke mata babu sauki ..
Ummita bata farfaɗo ba sai cikin dare kuma har lokacin mahruf yana tare daita zuciyarsa cike da tausayinta, ta wani bangare kuma zuciyarsa na jin haushinta ganinsa har da gangancinta yasa suka rasa babynsu ..
A hankali ta bude idanunta sama tana kallon celling d'akin jikinta babu kwari ta waigo inda mahruf yake zaune kusa daita idanunsu ya tsarke cikin juna take ta gano inda take da abinda ya faru daita ,yadda taga ya dawo a cikin lokacin kankani yasa tausayinsa ya kamata musamman yadda ta lura yana son cikin jikinta addu'a ta soma yi Allah yasa bai rasa cikin ba , ta kai hannunta saman cikinta taji wayam babu tudun cikinta ta sake waigowa inda yake da saurin
Saurin kawar da fuskarshi yayi yana sauke numfashi da kyar , shiru yayi cike da d'acin zuciya alhankali ya soma magana "burinki ya cika tunda gashi kinyi sanadin da na rasa babyna ,daman kuma kin furta sai a zubar min dashi ,sai ki kwantar da hankalinki banda ma bakinciki irin naki ai kanki zaki yiwa yan'uwa amman kika bari gangancinki ya janyo aka rasa ....
ta tsura masa idanunta tana kallonsa ranta na kuna da kyar ta bude bakinta "ta nan kuma zaka biyo ?"Bata nan zan biyo ba ta sama zan biyo har suhaima nayi miki magana ki daina tsalle tsalle amman kika mata banza wa kika cuta yanzu ?" Ni ina da wata matar da zata haifa min yara kanki kika cuta wawiya kawai da bata san ciwon kanta ba ,ta yunkura da kyar ta mike zaune ta zuba masa idanunta dake narkar masa da zuciya sai dai yau babu abinda yayi tasiri acikin zuciyarsa illa haushinta da bakinciki "me yasa tun farko bata haifa maka ba ?
"Ko ita baka auratayya daita ne ?
"Kin min shiru da wannan banzar dakikiyar kwakwaluwartaki ,ko dan baki ga na rufeki da mahaukacin dukan hasarar ya'ya maza biyun da kika janyo min saboda bakinciki irin naki ,koda yake daman ba tun yanzu nasan da zaman kina min bakinciki akan duk wani abun farincikin da zai sameni a rayuwata ba ...
Bata san sanda ta riko hannunwansa duka cikin nata a gigice ba "yara biyu maza fa kace ?
ya galla mata katuwar harara yana ƙoƙarin fixge hannunsa cikin nata "ban sani ba ta narke idanunta cikin nashi tana girgiza masa kai "wallahi yaya ba da ganga bane , banyi maka ganganci ba ,ko zanyi ganganci ,bazanyi ganganci da rayuwata ba , wallahil azim kitchen zani domin dafa indomi saboda shi nake kwadayin ci kawai naji an turo ni ta baya amman nafi tunanin su....
"Shiiiiiiiiiii karki sake ki sako sunan matata ciki daman kina da niyyar aikata hakan kije ke da Allah dan bani da abinda zan miki .
jikinta na rawa ta sake damke hannunta cikin nashi "wallahi ba da ganga nayi ba babu sanya hannuna ka fahimceni wallahi turoni akayi ,ya soma ƙoƙarin zare hannunsa yana jan tsaki ta sake riƙe yatsunsa gam "shikenan koda bazaka yarda dani ba ka rufa min asiri dan Allah karka fadawa mama hankalinta zai tashi ,nasan muddin ka faɗa mata ɗauka zatayi da gaske ne da karfi ya fixge hannunsa ta koma ta kwanata sharaf akan katifa tana kuka kwakwalwarta na neman mafuta ranar dai karasa kwana tayi cikin kukan rasa ya'yanta yana zaune yana jinta yayi mata banza ..
Washegari tun da sassafe suhaima ta tashi ta haɗa break fast ta nufo hospital tana shiga ta isa gaban gadon ummita tana taɓa jikinta "sannu ummi ya jikin .?
Tayi mata banza batare data kalli inda take ba har tagama zuba surutunta ta samu guri ta zauna kusa da mahruf tana tambayarsa mai jiki "da sauki kawai yace atakaice ..
Yan'uwana suka cika asibiti banda mama domin duba jikin Ummita duk bayan minti ashirin mahruf zai shigo duba jikin ummita sai dai byn ya jiki baya sake cewa daita komai zai fice ,tun aunty na basarwa har sai da ta kirashi gefe "haba baba me yasa kake yin haka ?
"hakuri duk zamu taru muyi ka saki ranka ka nunawa matarka kulawa gaskiya bana jin dadin wannan shan kamshin da kake ,ya kake son yarinyar nan tayi ,ka kuwa san yadda uwa take ji akan ya'yanta idan ta rasa ? " A yanzu ita kadai tasan abinda take ji a zuciyarta , ya dai jita amman baya jin zai wani saurara mata a yanzu .
satin ummita daya aka sallamesu jiki a sanyaye ummita ta fito tana takawa aunty ta buɗe mata gaban mota ita da suhaima suka dawo gidan baya mahruf ya tada mota suka bar hospital zuwa gida bai tsaya akoina ba sai a tafkeken get din gidan yayi hon mai gadi ya bude musu, ya shigo kai tsaye inda aka tanada domin ajiye motoci ya nufa yayi parking daya bayan daya suka fito ummita na takawa a hankali sakamakon kafafunta da sukai nauyi saboda allurai da'akayita mata a asibiti ganin yadda take tafiya tamkar wace kwai ya fashewa a cikin ya tsura mata ido yana kallon every step of her wanda ke sashi jin wani irin sanyi a sansar jikinsa tuntube tayi sakamakon idanunshi dake yawo ajikinta "washhhhh Allah ta faɗa tana tsayawa haɗe da runtse idanunta aunty tayi saurin dafata "menene ummita ?
Ta runtse idanunta "kafata aunty " me kafarki tayi ?
"Ta rike bana jin zan iya takawa ..tayi maganar tamkar zatayi kuka a hankali ya k'araso ya tsuguna a gabanta ya rike daidai idon sawunta yana mammatsa mata kafar, batare daya kalleta ba ya dinga murza gurin , mutuwar tsaye suhaima tayi zuciyarta na tafarfasa tamkar ta kama da wuta kusan minti goma sannan ya d'ago ya sanya kwayar idanunshi cikin nata "how do you feel now ?
"Better ta bashi amsa tana rausayar da idanunta cikin nashi ya lumshe idanunshi tare da mikewa tsaye taku daya tayi ta sake tsayawa tana kiran "wayyo Allah bazan iya ta ... ..
bai tsaya jin abinda zatace ba ya sureta ya rungumeta ajikinsa ya soma tafiya daita a hankali take kallonsa tamkar wani sabon halitta a gabanta, yana jin yadda take kallonsa har ya isa bangarenta yana ƙoƙarin kwantar daita akan kujera a parloun, amman still bata daina kallonsa ba ya kwanto jikinta sosai har suna jiyo numfashin juna "kallon fa na menene ko na canza miki ne?tayi saurin runtse idanunta tana sauke ajiyar zuciya adaidai lokacin da aunty ta shigo haka nan taji gabanta ya fadi ta shiga bin parloun da kallo duk an gyara ko'ina, a hankali idanunta ya sauka a bakin kofar dakin ummita ta tsurawa gurin ido tana nazari kamar an fasa gurin , gabadaya yanayin gurin ya bambamta ,bata yi sanya a gwiwa ba ta ciro wayarta ta shiga neman layin malam musbahu ..
tana tsaye mah'ruf ya fita ya bar part din zuwa na suhaima, Suhaima kuwa a parloun'n ta tsaya tana zaria tana ciza lip's dinta bakinciki kamar ta mutu, ranta duk babu dadi taji haushin daukar da mah'ruf yayiwa ummita, can tunanin shirinta ya fado mata a hankali ta gizgiza kai tana murmushin mugunta "wallahi kota karfin bala'i sai na fitar dake a gidan nan, ba dai kema kin iya kissa ba , babu fa abinda ya samu kafarta tsabar iskanci ne kawai , haka ta dinga zance zuci daga karshe ta sake yin murmushin mugunta "na gama cika aikina na farko yanzu zamu shiga na biyu da ni kike zance ,makircina na biyu banyi niyyar aiwatar dashi yanzu ba amman zanyi dan kuntata miki ,zan sa ki shiga haula'i ,zan sa kiyi kuka jini da idanunki ,zan yi abinda da bakinki zaki furta bakya auren mah'ruf tana cikin zance taji sallamarsa tayi sauri juyowa tana hadiye maganarta ta k'araso jikinsa ta rungumeshi "sannu habibi ta kamo shi ta zaunar dashi bari na kawo maka ruwa ka sha nasan ka gaji ta rikosa ta zaunar dashi, taje ta bude fridge ta d'auko ruwa mai sanyi ta tsiyaya a glass cup, ta dawo inda yake ta zauna tare da mika masa ka sha kaji sanyi nasan har yanzu kana tattare da damuwa, dan Allah ka bari komai mai wuce a zuciyarka , ya amshi ruwan ya sha kadan ba dan yana bukatar sha ba .
"Habibi ta Kira shi tana kallon cikin kwayar idanunshi shima ita yake kallo "dan Allah ka natsu ka daina yawon damuwa da damuwar ummita dan wallahi da gangan tasa mukayi hasarar babymu ,kawai dai ban faɗa maka abinda naji tana fadawa amina da tazo last week ba, dan banason haddasa fitina amma wallahi tana sane ta bari mukayi hasarar babynmu ya tsura mata idanunshi sosai hankalinsa a tashe yace "ki faɗa min me ya faru ?
"Banason haddasa fitina dan haka ba sai na faɗa maka ba kayi hakuri kawai ni zan sameta nayi mata magana ta karasa magana tare mikewa taku daya tayi ya fizgota da karfi ya kafeta da idanunsa "kina hauka ne ki faɗa min .......
ta sauke naunayen ajiyar zuciya tana jin dadi sannan ta kai hannunta ta janyo jakarta ta ciro wayarta ta kunna masa voice note din data nad'a a ranar da menal tazo , take ya soma jin magana kasa kasa hirar ummita da meenal ,meenal ke faman bata hakuri ita kuma ummita na cewa "gsky bana son cikin nan duk yadda zanyi a ciresa zanyi, yana gama ji yayi wata irin zabura ya mike kamar mahunwanci zaki jikinsa na rawa take zufa ya shiga tsatsafo masa kamar ana watsa masa ruwan zafi a jikinsa ya juya a fusace tayi saurin riko hannunsa da sauri jikinta na rawa "haba habibi kai kuwa ina zaka daga jin magana ?
"Ban faɗa maka dan kaje ka sameta ba ,na faɗa maka ne dan ka sani , sannan ka daina yawon damuwa akanta tunda tana sane ta zubar "ki barni naje na ladabbatar da jikinta sannan na sheida mata nasan abinda tayi .
"no ko zakayi wani abu ba yanzu ba ka bari sai aunty ta bar gidan nan dan yanzu kana zuwa zata ɗauka ko ...
"Ko me ?
"ni dai plz dan Allah karka janyo min bakinjini agurinsu azo ana jin haushina ni kuma banason na samun matsala da yan'uwanka kaga ita tasu ce duk runtsi duk wuya bazasu sa ta bar gidanka ba nifa ?
Yayi shiru yana huci sannan ya koma ya zauna jagwab akan kujera yana fidda hucin numfash mai zafi ta dawo kusa dashi da kyar ta samu ta shawo kanshi..
Cike da sanyi jiki ya mike ya nufi d'akinsa ya faɗa kan gadonsa ransa duk babu dadi yana kwance ta biyosa ta kwanta jikinsa tana shafa kirjinshi ya mike "ki barni bana jin dadin zuciyata ya barta ya shige bayi ta girgiza kai kawai tana jin haushi "to ni meye nawa wallahi bazaka shiga hakina akan wannan shashar ba tayi tsaki ta fita , yayi wanka ya canza kaya zuwa kananan kaya riga blue da ratsin yellow duk ransa a bace yake hakan bai hanashi kyau ba kasa ya sauko bai yi mata magana ba ya wuce dining table , tana ganinsa ta mike ta zuba masa abinci ta turo gabansa ya soma cin abinci yana kallon agogon daya sha ado ajikin bango parloun'n dake walwali da hasken fitilu ya kara haskaka wa ..
Bai wani ci abinci kirki ba ya mike ya fita batare da yayi mata magana ba kai tsaye gidansu ya nufa ya wuce bangaren mama a parloun'n kasa ya sameta dan haka shima ya samu guri ya zauna suka gaisa "ya me jiki ?
"Taji sauki dazu muka dawo gida "to Allah kara sauki karka sakawa zuciyarka damuwa Allah daya bayar zai sake baku wasu masu albarka kamar ya fadawa mama ganganci da ummita tai masa sai dai ya share yana tare da mama har kusan magariba sannan ya wuce massalaci yayi Sallah ya koma gida part din suhaima ya wuce ..
Ranar dai bai sake daura idanunshi akanta ba sai washegari shima ya shiga ne saboda aunty dan yasan muddin ya fita bai shiga gurinsu ba zatayi magana , sama sama yayi abinda ya kai shi batare daya kalli inda take ba zai wuce gurin aiki ta dakatar dashi tana nuna masa abinda aka ciro "daga ina aka ciro wannan sharmen ? "a bakin kofar shiga dakin ummita gasu nan layu ne "to me ya kawo layu nan ?
"Kai da matarka za'a tambaya tunda kune a cikin wannan part din yayi shiru yana nazarin maganar idan dai zai fahimta zargin matarsa take ?
TWO FRIEND'S BSBS
0 comments:
Post a Comment